NAYI DACE KITTY ©Maryam Aminu Musa, wannan document din na kudine kuma mallakina ne ban yarda wata ko wani su juyamin ko su fitat dashi ba tareda iznina ba, masu son document su tuntuɓeni 08121957799 I Na kifa kaina cikin littafin da nake karantawa bana ma so na dago wani abun ya daukemin hankali,idan na Fadi wannan semester Ina cikin matsala,domin a yanzu ne na fara dandana me nursing ke nufi Ina jarrabawar 2nd semester level 3,dukda a baya nayi school of nursing Amma karatun Babu sau'ki Sunana bilkisu Abba adam,iyayena sun rasu,mahaifina ya rasu kafin zuwana duniya,sannan mahaifiyata ta bishi a ranar da ta haifeni,bazance banyi maraici ba Domin da iyayena nake kwana dasu nake tashi dukda ban taba ganin fuskokinsu ba Banda a hoto Saidai banyi maraici na gata ba,Domin mama ta d'aukeni ta zamarmin uwa,shekaruna ashirin da biyu a hannun mama,kasancewarta yayar mahaifiyata yasa ta rikeni tamkar ita ta haifeni Mama d'anta d'aya a duniya jabir,sai Kuma ni bilkisu,na samu gata a wajen mama,baba da jabir da ko iyayena iya abinda zasumin kenan so am so grateful Kira naji mama ta kwala min,fita nayi daga d'akin Ina bitar abinda na karanta na sameta da waya a hannu,kafin tayi magana nasan dalilin kiranta Cikin shagwaba na fara buga kafata a kasa nace "Mama gobe fa exam gareni 8:30,Dan Allah kice Yaya kawai ya sayi takeaway idan nayi girki akwai matsala" Ina maganar Ina sake duba littafin hannuna,murmushi umma tayi tace "To ni da zaici nawa girkin ai sai nayi ko?Kuma karatunnan tun Friday kikeyi,yau lahadi,ki godewa Allah fa kinyi iya abinda Zaki iya,ya kamata ma ki huta hakan,Amma jeki ki karasa ni nayi girkin" Kallan umma nayi yanda take smirking,ta sani Sarai bazan barta tayi girki Ina zaune ba,kicin na nufa da littafin nace "Bari na musu jollof din macaroni kawai me bushasshen kifi Dan aikin Naman ma wahala ne" Mama Bata tankamin ba har na Gama hada abincin inayi Ina karatuna,gaskiyar mama ce,Domin duk abinda na karanta alhamdulillah Ina jinsa a kaina,inada confidence a wannan exam din insha Allah Ina juye abincin a flask naji tsayuwar motar su yaya,cikin sauri na baro kicin din Domin d'auko gyalena,d'aya d'aya abubuwan da suka Sanya banason zuwan su Yaya da Rana kenan,bana sakewa saboda abokinsa Saleh Fitowa nayi na gaishesu na d'auko kayan abincin na ajiye ba tareda na kalli fuskarsu ba Tafa hannu Yaya yayi yace "Yauwa kanwata Yar albarka,Allah dai ya Raya Mana ke musha biki" "Ameen Yaya,Allah yasa kaima ka tsaida Mata Nan kusa mu huta" Dariya yayi ba tareda ya cemin komai ba,yayana playboy ne Amma fa na hausawa,yanada yammatan da bazan iya kirgasu ba,na rasa menene abin burgers a Tara Mata Banji maganar Saleh ba Kuma nasan Yana wurin,daga Kai nayi Domin mu gaisa' nasan shi dai ba miskili bane A baje na ganshi Kan kujera ya hada gumi idonsa yayi ja,kallon Yaya nayi nace "Yaya me ya sameshi?" "Kanwata zazzabi yake tun jiya da muka bar gidannan,shi Kuma bazai je asbiti ba,na manta ma.yace na bashi extra idan munzo gida" Tashi nayi na taba goshinsa,jikinsa yayi zafi sosai,kallon idonsa nayi da hannunsa nace "Malaria ce Yaya,Kuma allura zata fi saukar dashi da wuri,Bari na Masa pcm injection sai kuje asbitin daga baya" "Bazamu iya tafiya asibitin a haka ba?" Saleh ya tambaya Yana kallan jabir,girgiza Kai nayi ganin yanda idanunsa ke kokarin juyewa nace "Sai anyi allurar tukuna aje asibitin,Domin zaka iya galabaita kafin aje" Tashi nayi da sauri na d'auko first-aid kit Dina na had'a allurar,zama nayi a hannun kujerar da yake nace "Ba wani zafi zatayi maka sosai ba idan ka tsaya...." Kafin ma Nakai allurar hannunsa ya janye cikin sauri,t-shirt ce Mai karamin hannu a jikinsa,hannunsa yasa ya rufe wurin yace "Wai Dole sai allurar bazan Sha magani ba?" "Ha'kuri zakayi,allurar tafi saurin gauraye jiki ne Kuma jikina yayi zafi,ka Bari nayi yanzunnan" Babu kunya yake kokarin guduwa,yau Kam naga Namiji me tsoron allura,murmushi nayi nace "Haba Yaya Saleh,bafa wani zafi zatayi ba ka daure ka tsaya Mana,minti kad'an ne" Kallan allurar yakeyi kamar wata adda,girgiza Kai yayi yace "Nifa banaso" "Yaya Saleh allurarnan sai anyita ka tsaya kawai,Yaya Dan ri'keshi kad'an" Ri'keshi jabir yayi,wani kallo ya watsa masa ya sakehshi yana dariya Runtse Ido yayi ya kankame hannun nasa tareda cije baki,sakin Baki nayi Ina kallonsa,allurar Tana rufe a hannuna ko bud'eta banyi ba Ri'ke wurin nayi tareda Bismillah na saka allurar,wata irin firgita yayi yace "Wayyo!" Tareda Jan hannunsa wanda yasa allurar gaba d'aya ta goce Zareta nayi nace "Yaya Saleh Ashe Kai ragon Namiji ne?common allura ce fa,Allah ya taimaka da tuni ka jiwa kanka ciwo" Dayan bangaren na koma nace "Kayi ha'kuri,Amma sai Yaya ya rikemin Kai" Ai jabir kamar kiris yake jira ya ri'keshi Gam Gam,allurar na saka a hannun yayi Kara kamar karamin yaro,kankame jabir yayi harda tura kansa a kafadar jabir,wincing yakeyi nikuwa dariya ta Gama cina kawai na danne ta ne,Amma zabgegen saurayi kamar wannan da tsoron allura Wayyo yaketa nanatawa har na cire allurar,tashi nayi nace "Kayita lailaya wurin kafin kuje asibitin" D'aki na shige ba tareda waiwaye ba naci dariyata na gode Allah,kowane mutum akwai abinda bayaso Amma ban taba kawo Namiji zai tsoron allura ba 2 Kaina naji ya fara sarawa na rufe littafin na ajiye,lokacin hutawa yayi kenan Kar Kuma naje na rubuta rubbish Wattpad na bud'e na duba littafin da nake karantawa nayi cigaba da karantawa,a half har bacci ya debeni Washegari cikin doki na nufi makaranta, confidence sosai nakeji akan jarrabawar yau kuma alhamdulillah,na sameta yanda na shirya Mata Mun Gama exams lafiya na Kuma ci gaba da jigilar yiwa su Yaya girki,har yanzu Saleh kunyata yakeji tun allurar da na Masa ni Kuma bana nuna masa wani Abu dukda Yana bani dariya idan na ganshi A Dan hutun da muke na nemi makaranta ta bani takarda Domin na ziyarci wani asbitin na Karo ilmi kafin mu koma,a take aka bani approval,asbitin sharad'a na shiga na Basu takardar suka Kuma amince zan dinga zuwa Ina practicing acan Ina da matukar son karatu sannan ina kaunar field Dina,na samu matsala a shekara ta biyu wadda ta janyomin maimaita dukka shekarar,hakan ne ya karamin karfi gwiwar da na zage dantse da karatuna Tare da su Yaya muka fita suka ajiyeni a asbitin, bangaren haihuwa aka kaini Wanda nafi tsoronsa akan kowane bangare Labour room muka fara zuwa babbar nurse din na ordering Dina nayi abubuwa,zuciyata ta karaya ganin yanda Mata ke Shan wuya tun kafin ma haihuwar tazo Tsayawa mukayi Kan wata Mata dake jijjiga,hankalina ya tashi sosai da kyar na zama calm na tsaya a wurin Matar ta galabaita sosai,bleeding take Wanda har nurse din saida ya Bata tsoro Tun safiyarnan ake fama da wannan baiwar Allah sai biyar ta haihu,zuwa yanzu Kam na Gama karaya Dan naga iya ganina,Mata suna Shan bakar wahala wajen haihuwa Kallo d'aya matarnan ta yiwa jaririnta tace "Allah yayi maka albarka" Kalmarta ta karshe kenan wadda ta fito sarari Bata sake cewa komai ba,a gaban idona yau mutum ya mutu,mace ta mutu bayan haihuwa Fita nayi cike da tsoro,hawaye ke zuba daga idona Ina hango matarnan a cikin kwakwalwata Yaya na Kira Ina Kuka nace yazo ya d'aukeni,Ina shiga motar na fara musu sambatu "Yaya ta mutu,sanadin ta kawo Rai wannan duniyar ta rasa nata,Yaya yaronnan zai tashi maraya,a gaban idona ta mutu bayan Tasha wahala,Yaya...." Katseni yaya yayi hankalinsa na Kan tu'kinsa yace "Bilki,idan fa mutuwa ce kinyi sallama.da ita kenan,Babu abinda Zaki iya kiyi ha'kuri kawai shine,Allah da ya kawo jaririnnan duniya shi yasan yanda zaiyi dashi,kedai Baki kashe ta ba,Kuma tunda bazaki iya kasheta ki Raya ta ba mene na damuwa?muje na siya Miki shawarma kinji?" Takaici ne ya sake isata,maimakon naji sassauci sai naji zuciyata ta sake karaya,cigaba nayi da Kuka Saleh yace "Haba man,wannan wani irin rarrashi ne?mace ce fa Dole taji daban a ranta,kuma wannan rarrashin naka ai kaman kace ta sake yin Kuka ne,tsaya ka gani" Bude gaban motar Saleh yayi ya dawo baya inda nake,saukar da muryarsa yayi yace "Kiyi ha'kuri kinji kanwarmu, addu'a Zaki Mata da jaririn nata,Kinga ita fa tayi shahada aljanna straight zata tafi,Kuma Allah bazai bar abinda ta Bari ya wulakanta ko yasha wahala ba,ki zama mai juriya tunda haka yanayin aikinki yake,idan kina d'aga hankalinki bazaki dinga bawa marasa lafiya kulawar da suke bukata ba,nasan Zaki damu Amma ki takaita damuwarki" Naji Dan sauki a Raina da maganar Saleh,cikin shesshekar kuka nace "Yaronnan kamar ni yake fa Saleh,Nima haka mahaifiyata ta rasu,ya zai taso yaji?" "Ke me kikeji?akwai wannan kewar iyayen nasan Zaki jita a ranki,Amma gata dai kinsamu,kin Sami iyayen da suka maye Miki gurbin naki,kin samu gata daidai misali,ki sanyawa ranki shima wannan yaron zai samu gata fiye da naki ma,kiyi ha'kuri mutuwa ba Dadi Amma ki jure,kina aikin asbiti kinawa marasa lafiya Kuka ai Korarki zasuyi,share hawayenki muje kici shawarma,zan Baki labarin wata amarya da akazo da ita wajenmu ta zabi kayan gado" Jana ya dinga yi da Hira yana fadamin labaru na ban dariya,kafin muje sayan shawarma har na fara dariya Ana bani sharmar tawa na bud'e na fara ci,tayimin Dadi sosai,lumshe ido nayi Ina cika bakina da shawarmar,Domin tafi Dadi ka jita full a bakinka A jikina naji kaman Ana kallona na bud'e Ido na kalli Saleh,kallona kuwa yake Yana murmushi,ko a jikina na tura sauran shawarmar a bakina Yar da takardar nayi ina lashe hannu nace "Yaya Dan Allah mu koma Bata isheni ba wallahi,Kuma bamu siyowa umma ba" "Ba inda zamu koma,saidai mu sayi biredin a hanya muje gida ki had'a ni dama ba son sayenta nake ba gani nake asarar kudi ce,Kuma idan Kika Mana tafi dad'i" "To mu sayi biredin,ni yunwa ma Ta karamin" na fad'a Ina jingina da kujera,Saleh ne ya mikomin tashi yace "Nan gefen bakinki ki goge" Gogewa nayi na'ki karbar shawarman nace "Ka ci kawai idan munje gida zan had'a ai" Bata Rai yayi yace "Saboda na saka yawu shine bazaki kar'ba ba?" "A'a wallahi ba haka bane,kaci kaima naci ai,Kuma ta isheni" Hannu ya saka ya gutsire inda yaci yace "Yanzu Kam idan Baki kar'ba ba nasan kyankyamin hannun nawa kike Kuma na wankeshi a hanya" Kallonshi nayi na kalli shawarmar,naga ya Bata Rai,Mika hannu nayi na kar'ba tareda godiya na fara ci,Ina Jin idonsa na kaina nayi kaman bansan dashi ba,ita shawarma ba'a Mata cin gayu Tas na cinye na goge hannuna da bakina,a hanya muka tsaya muka sayi biredin kasancewar inada duk kayan hadin shawarmar Biredin shawarma Cabbage Naman kaza,rago ko Kuma minced meat(Amma minced meat bai fiye Dadi ba,ki yanka Naman rago kanana ki tafasa kiyi dashi tafi dad'i) Attaruhu Mayonnaise Ketchup (optional) Albasa (dafaffiya) Zaki hada nama da attaruhu da albasa a cikin sauce pan,da sauran kayan hadinki,sai ki shafa mayonnaise a jikin biredin shawarman da ketchup idan kinaso sai ki d'auko Hadinnan naki ki zuba sai ki saka cabbage ki rufe,anaso a saka kayan Hadin da zafinsu yanda zasu rage taurin cabbage din ko Kuma ki saka a microwave idan kin Gama Shikenan,all done abin 350_600 a sau'ka'ke Idan kaza Zaki saka Zaki cire Naman a tsaitsaye ne d'aya jikin kashin *Hadin mayonnaise* Kwai guda biyu Mai gwangwani biyu Leman tsami Vinegar Gishiri Zaki zuba kwai a blender ki kunna har sai yayi fari,sai ki saka lemon tsami da vinegar da gishiri kici gaba da blending,idan suka hade kwan yayi fari Kal,sai ki d'auko Mai ki dinga zubawa a hankali har sai yayi kaurin da kikeso sai ki juye,a sau'ka'ke Babu kashe kud'i ******** Shawarma tayi Dadi,Kuma kasancewar kananu nayi ni kaina naci kusan biyar,su Yaya da Saleh kuwa ba sai an kirga ba Lemon na'a na'a na had'a Mana (wannan sai next page zan bada shi insha Allah😋),muna ci muna korawa muna Hira har dare yayi Bayan sun fita na zauna Ina tunanin Saleh,a rayuwata inason Namiji Mai barkwanci Wanda na lura halin Saleh ne barkwanci da surutu,dadin dadawa Kuma gashi da iya magana da rarrashi Duk zuwan da sukeyi bana ma zama dasu balle na sauraresu,Amma zamana da Saleh yau yasa na fara Masa kallo na daban,yau Saleh ba ragon Namiji bane,cikakken namiji ne a wurina,Wanda yasan yanda zai tafi da mace Mamakin yanda ya rarrasheni cikin kankanin lokaci nayi na kwanta Ina dawo da maganganunsa,irin kallon da yakemin Ina cin shawarma da Kuma gentle man din da ya zama sanda ya mikomin tashi Tashi nayi zaune na zare Ido,meke damuna ne?Anya garau nake?na zauna Ina tunanin Namiji har na kusan minti biyar? Ba shiri na tashi na fita Palo,a zaune na samu mama Tana kallo nace "Mama zanje gidan Yaya" Amsawa tayi da to na fice Ina zaune a unguwar d'ambare,unguwa ce Mai karancin mutane saidai Tana da kyau Baba kabiru, mari'kina kenan sannan mijin mama,matansa hud'u,duk matansa guda uku gidajensu na hade da juna a bayan layinmu,mama ita kadai ce macen da aka Ware a gefe sannan itace mace ta.uku a cikinsu Hajiya itace matar baba ta farko,tanada 'ya'ya goma dukkansu Mata ne,ta aurar da takwas saura biyu da Kuma tarin jikoki a gidan Adda itace mace ta biyu,tanada yara bakwai,maza biyar Mata biyu,maza uku sunyi aure sauran duk sunanan Sai mama,ita Kuma d'anta d'aya tall jabir Maman dije itace amarya,Yayanta Kuma biyar,Mata uku maza biyu,duk kananu ne Gidan adda na shiga Domin shine da saannina,yayanta Mata biyu zulaihat da rukayya Samunsu nayi suna cin tuwo dumame,wanke hannuna nayi na zauna muka ci na tashi na Karo,a wajen abinci bana kunya ko a Ina ne,Domin a wurina wayewa shine na cika cikina na baiwa bakina hakkinsa Bayan mun Gama ci nake basu labarin Saleh,da Kuma abinda ya faru a asbiti,kallon juna sukayi zuka tafa sukace "Mukam Allah ya kaimu musha biki,Ashe ruwan idon da ake mijin na gida" Kwanciya nayi ba tareda nace musu komai ba,idan nai magana ma surutu zan karawa kaina nasan halin abuna Kuma nasan ba gskiya suke fad'a ba,ni ban yarda da love at first sight ba,yaushe ma nasan Saleh da zan fara tunanin aurensa,lalube ne nake a duhu bansan da wa zan Kare ba,nasan dai Saleh ya fara birgeni kuma zan daukeshi a matsayin abokina.....Amma me kuke tunani? Insha Allah zan dinga posting sau uku kawai a sati,Amma ya danganta da yanda zaku min votes and comments,idan na samu votes da yawa zanyi sau hud'u ko biyar ma,idan kuwa Babu zan dinga sakinsa sau daya a sati Littafi ne da zai tabo bangarori daban daban na rayuwa,girke girken zamani kala kala da yanda ake yinsu,kayayyakin gyaran jiki,yanda Zaki tsuma kanki ba tareda illa ba da sauransu, Vote Comment And tell me your opinions,tnxxx 3 Washegari male ward aka kaini,na aikatu sosai na gaji,Ana sallar azahar na d'auki hanyar gida Ina zama Kan kujera mama tace "Babanku yace yau zakiyi ba'ko" Maida numfashi nayi nace "Layi yazo kaina kenan,Amma kin sanshi mama?" Zama tayi kusa Dani tace "Eh to na sanshi,Amma shekararsa 7 a Russia Yana karatu,kamar ance engineering yake karanta,Dan gidan baba habibu ne bai Dade da dawowa ba,tun wancan satin babanku ke min zancensa yau dai zaizo" "To Allah ya kawoshi lafiya,yanzu fa ko bamu yiwa juna ba shi zan aura ko mama?" Dariya mama tayi tace "Eh to,ya danganta,idan mazan sukace basa so yawanci Ana ha'kura,Amma dai gaskiya duk Hadin da su baba keyi ba'a canzawa Kuma haka ake zama lafiya ba wata fitina" "To muma Allah ya had'a jininmu,Ina dai tsoron Yan kasar wajennan kad'an" Tashi nayi na shigo harkokina Ina tunanin irin mutumin da baba kabiru zai turomin Nayi mamaki ma da yakai yanzu bai min miji ba,yanda ka'idarsa take shi da baba habibu shekara 17_19 an yiwa yarinya miji,wasu ma tun suna secondary har su gama tukun ayi auren 6:00 naji Kira a wayarta da number da ban sani ba,Kai wayar kunnena nayi tareda sallama Da wani Ascent na daban naji an amsamin,irin bakinnan ya gaurayu da wani yare na daban,tamkar ma kamo hausar da zaimin yakeyi Da kyar ya samu yace "Nine baba ya turo Ina tsaye a waje" Riga da skirt ne a jikina na atamfa,mayafi na yafa na saka powder da man Baki na nufi d'akin mama Sallama nayi daga waje sannan na shiga nace "Mama wai yazo" "To jeki a dawo lafiya,a Kuma kula" Har na fita na dawo nace "Mama a kofa zamu tsaya ko?" "Eh d'auki kujerun robarnan ki ajiye muku daga gefe" Tafiya nake ba tareda Jin wani d'ar a Raina ba,ni dama tsoron fidda miji nake duk mazan tsoro suke bani,gara a zabamin ko banaso nasan su baba baza su min zaben da bai Dace ba,Kuma soyayya a wajena ba komai bace nidai naci na koshi nayi karatu nabi lafiyar katifa na Danna wayata. Kokari nake na maida fuskata neutral,ba yabo ba fallasa,karasawa nayi Ina murmushi na bud'e gate din ya shigo Wani irin kallo yakemin,irin kallon da zaka ji duk tsikar jikinka ta tashi,he was checking me out Matsawa nayi Amma dukda haka idonsa na bin duk motsina,gyaran murya nayi Domin na dawo da hankalinsa Kan fuskata Amma Ina... Kallona yake kaman Wanda aka bashi Riga akace ya 'kirga yawan zaren da aka sa'ka rigar dashi,banason kallo Sam,dukda kokarina na iya magana gaban mutane Amma da zarar hankalin mutum ya sauka kaina bana sakewa Kafata naji ta fara rawa nace "Sannu da zuwa,Bismillah mu zauna ko?" Hannu yasa ya shafi kujerar alamin yaga ko da 'kura,dukda Babu kurar saida ya Sanya handkerchief ya goge tukun ya zauna, murmushi yayi yanakallona Ido cikin Ido,a hankali na sauke kaina nace "Ina wuni,ya gida?" "Lafiya....so.....kene bilkisu?" "Eh" na amsa da kyar "Ni sunana sulayman,Kina da 'kirar jiki me kyau" Mamaki ne ya kamani da takaici,abinda zai fara fitowa daga bakinsa kenan?bance komai ba yace "Shekarunki nawa?" "22" na fad'a cikin sauri,sunkuyo kansa yayi sosai wurin kujerata,ji nayi kaman na gudu sai kuma na tuna a cikin gidanmu ne na dake "Baba yacemin kina karatu ko?me kina karanta?" "Nursing" na fad'a ina jin kaman zanyi Kuka,na takura sosai Dariya yayi yace "Oh nursing?kune masu dealing da su jini su fitsari,duk wannan kazantar ko?ugh,banason wannan aikin.kin kusa gamawa?" Cije bakina nayi nace "Saura shekara biyu" "Sai kin Gama kenan za'ayi aurenmu" Shiru na Masa yace "Ops sorry Ashe fa ku Nigerian girls bakwa zancen aurenki saboda mene ake Kiran abun?" Shiru nayi bance Masa komai ba ganin yaso ya fara da cin fuska,Banda ma ya Raina ni shi shekarunsa nawa a Nigeria?maybe ma irin kazamannan ne da Yana saurayi Bai kwantamin a Rai ba ko Dan yanayin kallon da yakemin min,tashi nayi nace Bari na kawo maka ruwa" Kallon hannuna yayi ya kalleni ya girgiza Kai yace "No dear,bakomai Nasha ruwa a hanya,tafiya zanyi sai wani lokacin ko?" Amsawa nayi da okay na d'auki kujerun nayi gaba,waiwayawa nayi na ganshi ri'ke da gate yana kallona ta baya,waving Dina yayi na kakalo murmushi nayi gaba Ina shiga naga mama na yanka kankana,zama nayi ba tareda nace komi ba na fara huce haushina Kan kankanar Fam nake cika bakina da kankanar,idan Raina ya back dama kan abinci nake hucewa,idan ba fruit ba to na samu snacks Kallona mama tayi tace "Me ya faru?" Domin tasan idan Ina tura Abu bakina haka to an ta'boni ne Hadiye kankanar nayi na Danna banana,Ina cin bananar nace "Mama yaronnan inaga Russia ta 'batashi,kinji wai aikina dealing muke da kazanta" "Shikenan abinda ya Baki haushi Zaki shanyemin fruit?" Hannu nakai zan sake d'aukan ayaba mama ta doke hannuna,numfashi naja na d'auke hannuna nace "Kuma yayita kallona duk yasa na tsargu" "Idan ya Kuma dawowa maybe bazaiyi haka ba,dama dai kasar wajen na cinsa ne Yanzu" "Allah yasa,Bari na d'auko wu'ka na tayaki" Muna had'a fruit din muna Hira har muka Gama,alwala nayi nai sallar magrib na saka kayan baccina Ina fitowa Palo naji tsayuwar motar su Yaya,komawa nayi na d'auko hijab na fito Ina musu sannu da zuwa Zama sukayi duk su biyun a gajiye suna maida numfashi,fruit din da muka had'a na d'auko na ajiye musu nace "Yau kunyi dare" "Kibari kawai,wasu Kaya ne aka bamu short notice wallahi,idan ba aikin Daren mukayi ba bazamu iya Gama kujera da gado a kwana goma ba" "Wai,sannunku ni yau tun azahar Ina gida" D'aukan bowl din Saleh yayi ya fara sha,hamdala yayi yace "Allah dai ya Miki albarka kanwarmu,yau dai Babu kuka ko?" Dariya nayi nace "Yau ai male ward naje" "Aikinku na birgeni,na fad'awa *rumana* ta cikeshi tace bataso" "Ai yanada wuya ba laifi" na fad'a Ina ajiye musu tuwon Daren da akayi "Dukda haka,Amma ai abun birgewa ne,kana saving Rayuwar mutane kana hulda dasu,ga Lada Kuma" Tunawa nayi da maganar sulaiman nace "Amma akwai dealing da kazanta" Ajiye bowl din da ya shanye fruit din yayi yace "Wani kazanta?ai ba kazantar ake dubawa ba,ribar ake dubawa,ka koyi akin,zaka taimakawa alumma,zaka taimakawa Yan uwanka,kaima ka taimaki kanka,ga albashi Mai tsoka idan kana aiki,nifa da ace inada wata kanwa Allah ko bata so sai tayi aikin Yana matukar birgeni" Murmushi nayi Wanda yakai har cikin zuciyata,sulayman ya gama kushemin aikina ga Saleh Yana yabonsa, hakan yasa na karawa Saleh mataki guda Akan mutuncinsa da nake gani Tashi nayi zan Basu wuri Domin suci abinci yaya ya kirani,amsawa nayi yace "Wa baba ya Aiko Miki" Canza fuska nayi nace "Wani ne,wai sulayman Dan gidan baba habibu ne da ya Gama karatu a Russia" "To ya Miki ne?" Ya fad'a Yana kashemin Ido,kallon Saleh nayi naga shima idonsa na kaina,kunya naji na canza zancen nace "Kaima yace zai kawo maka Mata wani satin sai ka shirya" Murmushi Saleh yayi yace "Kanwarmu mun kusa Shan biki kenan" Ji nayi yanayina ya sauya,domin Sam ban ma fara wani tunanin auren sulayman ba,ta Ina ma zan fara zama da sulayman a wannan yanayin da yake?zai canza ko bazai canza ba?wannan kallon bayan ni Mata nawa yake yiwa? "Allah ya Sanya alkhairi" Saleh ya katsemin tunani,d'auke kansa yayi daga gareni Yana kallon tuwon dake farantinsa,gani nayi kaman ya sauya Amma na share,me zai saka ya sauya daga zancen aurena?Kar na fara yaudarar kaina Washegari da dare baba ya kirani ya tambayeni Kan sulayman,ko inada abin fad'a?tabbatar Masa nayi Babu wata matsala na Kuma gode da zabin da yayimin,dukda cewa ni sulayman kwata kwata bai kwantamin a Rai ba Tun ranar da yazo ban sake jin duriyarsa ba,har akayi sati biyu,na ma manta da shi na shiga harkonina Nursery na shiga na asbitin yau,ji nake kaman nayi tsalle,Allah ya jarabceni da bala'in son yara,idan akace anyi haihuwa musamman ta jiki,to sai an gaji da ganina,idan kuwa naje barka na d'au baby to a 'kalla zanyi Masa pics sama da ashirin,sannan sai ance na bada shi zan bayar,sai gani yau a nursery kaman ance ma ga yara nan kisan yanda zakiyi dasu Cikeda murna nake bin gadajen yaran,yawancinsu ba wani ciwo sosai sukeyi ba Wata baby girl akayi discharging,bin yarinyar nayi da kallo tayimin kyau sosai,izini na nema na Dan d'auki pics dinta Ranar dai ba wani aiki nayi ba Banda wasa da yara da d'aukan pics,Abu d'aya ya gajiyar Dani feeding dinsu Amma shima cike da d'oki na yi Kiran Yaya nayi nace idan sun tashi da wuri su biyo su d'aukeni Domin bazan it tafiya da azahar ga wadannan kyawawan furannin Ina gani ba 2:30 Yaya ya kirani yace suna waje,daga yanda na shiga motar ma yasan yau nayi aiki me dad'i Waiwayawa yayi yace "Ya dai bilki,ko an fara biyanki ne kike ta murmushi bakinki ya kasa rufuwa?" "Ai baza'a biyani ba Yaya,yau bangaren yara naje,wayyo Allah na Yaya kaga yanda yaran suke, innalillahi babies akwai kyau,Bari kaga hotunansu da na d'auka" Nuna musu pics din na fara yi Domin Saleh ma ya waiwayo,d'auke Kai Yaya yayi yace "Duk kyan yarannan Dole nayi tu'ki" Driving ya fara Saleh ya nuna wani baby yace "Wannan fa?Masha Allah kaman lafiyayye" "Eh ya samu lafiya dama jaundice ce ta kamashi me Dan karfi amma ya warke baka gani ba harda wasansa,Bari kaga video" Videon yaran na nuna masa lokacin da nake bashi Madara,Yaya ma rage gudu yayi ya waiwayo yace "Nidai asibitinnan da zasu bi shawarata da sun barki anan,na tabbata sai kin fi iya aiki" "Ka Bari kawai Yaya,naji dadin aikin yau" "Ai yara akwai abun sha'awa mu gani" Karbar wayar tawa Saleh yayi Yana kallon hoton babies kala kala,wasu ya nunamin wasu ya wuce,har mukaje gida muna Hira Kan babies,Yaya shiru yayi Yana kallonmu Yana murmushi Text ne ya shigo wayar tawa Saleh ya kalla ya mikomin Budewa nayi na karanta _anjima zanzo,around 5_ _Okay_ na tura masa nayi saving number ,ina tunanin yau Kuma Dame zaizo,a 2 weeks dinnan dai ya kamata ace ko text ya turomin Muna komawa gida na sanarwa mama "Ai Sai ki had'a masa wani abun tunda ya fad'a zaizo" "Wainar da zamuyi ai zan iya Kai masa ko?" Na tambayi mama Ina cigaba da suyar wainar "Eh Zaki iya,zata Masa Dadi ma tunda ya jima bai ci ba" "Mama Yana da aiki ne?" "Eh,ai tun kafin ya dawo baba habibu ya Samar Masa aiki a Nan KEDCO,ba dai wani aiki ne Mai kwari ba Amma tunda suka d'auko maganar aure nasan zai iya rike iyali da albashin nasa" Wanka nayi bayan na gama suyar wainar na saka doguwar Riga ta material na d'auki pink hijab na yafa sannan na zuba Masa a flask,na zauna zan fara ci ,jabir ya kiranu a waya yace na taimaka na Kai musu ruwa,rufewa nai na d'auki jug na zuba musu ruwan na nufi dakinsa Domin yau acan suka zauna Sallama nayi na shigo na ajiye tareda yi musu sannu,sai had a gumi suke suna kaiwa ciki "Saka hannu muci Mana Dan nasan bakici ba" jabir ya fad'a ba tareda ya kalleni ba,kallon wainar nayi naga saura hud'u,wainar da na zuba musu kusan 12 "A'a na zuba ai ka tasoni,ku cinye Dan Allah kar ki bar ragowar bansan ya zaai da ita ba" Tashi nayi zan fita naga Saleh na kallona,murmushi yayi yace "Kinyi kyau fa bilkisu Ina zuwa haka?" Shiru nayi,bansan dalilin da yasa bana iya zancen sulaiman gaban Saleh ba,sai naji nauyinsa,ko Dan Yana abokin yaya na? "Zan Dan fita ne" "To saikin dawo a taho Mana da tsaraba,kyakkyawa" Ban saniba ko.hallucinating nake Amma saida naji jikina ya sauya da ya kirani kyakkyawa,cike da kunya na fita daga d'akin ba tareda na kalleshi ba Kalmomi biyun da ya fad'a kemin yawo a Raina _kinyi kyau fa....kyakkyawa_ Sai murmushi nake har na shiga Palo,Kiran wayata sulaiman yayi yace gashi yazo,sai yanzu na fara tunanin Ina zan ajiyeshi Gidanmu self-contained ne komi Yana cikin Palo Banda d'akin jabir,umma na samu na sanar Mata tace na d'au babbar darduma sai na shimfidata daga wurin d'akin yaya Shimfida nayi na Kai duk abincin na ajiye sannan naje shigo dashi Riga da wando ne a jikinsa sun,rigar karama ce duk ta d'ameshi,haka ma wandon,boot ne a kafarsa Mai matukar kyau,Wanda ni shi kadai ne ma.ya burgeni a shigarsa Murmushi nayi na gaidashi,matsowa yayi kusa Dani yasa hannunsa a kafadarta yace "Hey sexy,ya...kike?" Wani yar naji a jikina,ga hannunsa a kafadata Kuma yana kirana wani Abu marar dadin ji,kankame jikina nayi ina kokarin matsawa daga jikinsa,dariya yayi ya sakeni janyoni,hannunsa yasa a kuguna yace "Babu inda zakije,nine dai mijinki ko?so mene laifi dan ri'ke matata hakan?ai Babu ko?it's not like.....zan cinyeki ne ko wani Abu" Kansa ya sako kafadata tareda sha'kar turaren da na sanya yace "Umm,turaren so cool" Tuni idona ya ciko da kwalla,ji nayi tsikar jikina ta fara tashi,na kasa bud'e Baki ma nace ya d'auke hannunsa,idan har nayi Kuka yanzu to na bawa kaina kunya,Dan haka na saka hannuna na janye hannunsa Gyaran murya nayi nace "Bismillah" tareda yin gaba cikin sauri Dariya yake Yana Bina a baya Yana fad'in "Idan nai kissing dinki Kuma kenan mutuwa zakiyi" _aikam ba abinda zainhanani mutuwa_ Na fad'a a Raina Nuna masa wurin zama nayi na Kama wuri na zauna,dab Dani yazo zai zauna na ja baya,dariya yayi ya koma gefe Zuciyata ta fara tunzurani na fad'a Masa abinda yakeyi ba Daidai bane a addinance da aladar bahaushe,shidai ba bature bane balle yace su haka sukeyi Bude flask din yayi ba tareda yace komai ba,gyad'a Kai yakeyi ganin wainar shinkafa Daga wainar yayi tareda yamutse fuska yace "Ya ma.sunan wannan?naga NaNa nayi Amma ni Bata burgeni ban taba ci ba" "Wainar shinkafa ce" "Okay Bari nai trying" Ya fad'a tareda fincina da yatsansa yakai Baki,daga kafadarsa yayi yace "Well,ba laifi" Bance komai ba na zuba Masa Miya a bowl da wainar a plate,dangwala yayi yaci ya turomin kwanukan yace "Wannan ai yayi yaji da yawa" "Okay,sorry" na fad'a Ina matsar da kwanukan gefe,sunkuyar da kaina nayi Ina tunanin wannan bawa na Allah da ake neman li'kamin Hannu yasa ya d'ago fuskata yace "Yaya ne dai?" Sure hannunsa nayi nace "Ka Dena tabani banaso" "Why?haka ne bakyaso?" Ya shafi gefen fuskata,kallonshi nayi Domin yaga yanda na Bata rai,Amma ko a jikinsa,sauke numfashi nayi nace masa "Mu al'adar hausawa ba'a haka,ina ganin mu dinga maitaining space har Allah ya kaimu lokacin auren" "Okay okay naji,tunda na ganki Bari na tafi" Tashi yayi nace sai anjima ko?" Peck naji a goshina na daga kaina,na rasa meke damun sulayman,zama nayi a wurin ba tareda na motsa ba har ya fita Takaici yasa na janyo abincin da na zuba masa na fara ci,digon hawaye naji ya fitomin nagoge da saurin da naji alamun maganar su jabir Kallona sukayi jabir yace "Au,dama abinda ya sakaki kwalliya kenan....inyee Yar kanwata an fara girma" Kallon saleh nayi ta gefen Ido naga yanayinsa b yabo ba fallasa,a hankali nace "Yaya ka Bari banaso" Zama yayi gefena,cikin serious tone yace "Bilki,wai shi yaronnan ya yake,fadamin komai da komai nashi" Zama Saleh yayi shima suka sakani gaba,bud'e Baki nayi saidai na kasa furta komai saboda Saleh,kwarjini yakemin ne ko me?Allah masani Murmushi yayimin tareda kashe idonsa daya yace " Have Yar kanwarmu,Kar kiji komai ai Nima yayanki ne,so dai muke mu tabbatar da he is good for you or not" Hannuna nake kallo nace "Dan gidan baba habibu ne,sunansa sulaiman,ya Gama karatu a Russia Yana aiki a KEDCO" "To ya halayyarsa take?Kuma ya Miki ko kinada ja?" Kallon Yaya nayi nace "Eh to,bansan me nakeji game dashi ba,amma wasu halayen nasa basumin ba" "Kamar me da me?" Shiru nayi Yaya yace "Kanwata,Kinga tun wuri ki Fadi abinda kikeji game da yaronnan tun kafin ta ai nisa,Kar akai matakin da zaki fara Jin haushin kanki akan hukincin da kika yanke kina ganin inama a maida hannun agogo baya" Muryata ce ta fara rawa nace "Tun farkon zuwansa ya nuna yana kyankyamin aikin da nakeyi,sannan Kuma....Yana da dabiu irin na wake Yana ganin Dan ya tabani ba komai bane" "Me?ke Kuma kikayi Masa me?!" Kalmar da ta fito daga bakin Saleh kenan,kallonsa nayi cikin mamaki Domin yanayin da kalmar ta fito tamkar ransa ya baci sosai "Nace.....nace Masa mu al'adar hausawa ba'a haha kamata mu maintianing space har zuwa aurenmu" Gaba d'aya yanayin Saleh ya sauya,cikin fushi yace "Wani irin irresponsible yaro ne?a tunaninsa ke irin matan da yake gani ne a titi?ya ganki cikin kamalarki sannan yakai hannu ya taba jikinki?and ke Kuma kina me?a matsayinki na mace ai sai inda karfinki ya Kare idan wani yaso ya Kai hannunsa jikinki ama Kika zauna kina kallonsa ko?Hana bilkisu da wayonki da ilminki bazaki iya tsayawa ki kwaci yancinki yanda ya dace ba sai ki tsaya kina Kuka?why?" Kasa furta komai nayi na zuba Masa Ido,ya bala'in birgeni,abubuwa biyu ke yawo a kaina Kinyi kyau bilkisu,Ina zuwa haka?......sai kin dawo kyakkyawa..... Hakanan sai na tsinci kaina a wani yanayi na nishadi na daban,Kiran wayar Yaya akayi ya kalli Saleh yace "Man,tashi.mu tafi yarinyarnan fa Tana jirana" Hankalinsa na kaina yace "Jeka kawai,daga Nan zan wuce gida" "Okay sai gobe to" Yaya ya fad'a yayi gaba Jabir na tafiya Saleh yace "Bilkisu,kina son yaronnan?" Shir nayi na sauke kaina "D'ago ki kalleni,bilki aure ba wasa bane,ki dinga tuna cewa ke ba wai jigari jigarin Mata bane,ke macece da kowani Namiji zai burin samunki a matsayin Mata,wannan mutumin shi zai zama mijin aurenki,kin shirya katange kanki a kasan inuwarsa,shi ne Zaki Kare rayuwarki a karkashin ikonsa, kin shirya haka?to Dole sai kin nuna masa yabar abinda bakyaso yabi Wanda kikeso,kema Kuma Zaki bi abinda yakeso Wanda Zaki iya,idan aka aurar dake a haka zakisha wahala dear" A Daidai wannan lokacin na lura da na fara son Saleh,soyayyar sa nasan Babu riba a cikinta,Wanda hakan ya bani tsoro sosai.... Not only vote,comment Domin nasan me kukeso tunani akan abinda na rubuta,tnxx 5 D'auke kwanon abincin gabana yayi yace "Idan kina cin abinci saboda fushi to kin kusa yin kiba,nikuwa bazanyi kanwa da lukuta ba" Dariya nayi ba tareda nace komai ba,anan muka zauna muka sha Hira Kala kala,Yana bani labarin shagonsu na kfintanci Ina bashi labarin aikina,Ina jin dad'i sosai yanda yake nuna shaawar karatuna Har saida aka Kira magrib sannan ya tashi Domin ya tafi,rakashi nayi har gate Ina mamakin yau wani irin zance nayi? Kwashe kwanukan nayi Ina shiga d'aki umma tace "Sai yanzu?" "A'a tuntuni sulaiman ya tafi Saleh ne ya zauna mukayi Hira" "Okay" umma ta fad'a Tana tada sallah,nasan baza tayi wani tunani ba Domin Saleh kaman da take a wurinta,Domin tun secondary suka manne da jabir har yanzu Sallah nayi Ina idarwa na zuba tagumi Ina tunanin irin cakwakiyar da nake Shirin hadawa kaina,nasan idan ba wani miracle din ne zai faru ba sulaiman shine mijina,Amma meyasa zan sakawa raina son Saleh?Allah yasa attraction ne kawai,Domin idan sonshi nake nasan zansha wuya,Domin ban iya so ba Ina wannan tunanin naji sallamar su zulaihat tareda sallamar baba,fita nayi na gaidashi baba yace na d'auko masa abinci yunwa yakeji Tare da su zulaihat muka shiga kicin d'in,jingina nayi zulaihat tace "Albishirinki,baba ya kawomin wani" Flask din abincin baba na d'auka nace "Wannan zumudin naki da alamu yayi miki" Har wani tsalle tayi Cike da murna tace "Ai alhamdulillah ya had'u wallahi,xuwansa na farko bazaki ce lokacin muka fara Hira ba,ya iya Raha da barkwanci" "Kinyi sa'a,nikuwa wani Dan iska baba ya turo,Bari muje d'aki na baku labari" Daukan tray din nayi na fita dashi,samin albarka baba yayi ya kalli mama yace "Kinga kuwa munyi magana akan masu zuwa wurin yarannan,habibu yace yafiso ayi komai da wuri" Ji nayi gabana ya fad'i Colin sauri nabar wurin Ina dafe kirji,a Kan gadona na samu su zulaiha da rukayya,zama nayi na fara musu bayanin sulaiman da Kuma abinda naji baba ya fad'a yanzu,saidai na boye musu abinda nakeji game da saleh Kallon juna sukayi rukayya tace "Ni Ina ganin ruwan wajen ne bai sakeshi ba,ki fara daurashi a hanya sai kiga an Dace" Kwanciya nayi nace "Allah yasa,ke zulaiha bamu bayani,ke Kuma rukayya Babu ke ne a rabon?" Murmushi tayi tace "Harda ni,Amma ya fadamin zai Karo karatu ne sai bayan shekara biyu,Amma kullum muna waya,har video call munayi baida matsala gaskiya,Kuma sau d'aya dai yazo yacemin zai le'ko weekend,Yana can maiduguri" Allah sarki,ni kadai ce banyi Dace ba,zuba musu ido nayi suna Koda mazajen da baba yayi musu,saidai ni Saleh kawai nake gani a idona Washegari jabir da ya daukoni daga aiki ban ganshi da Saleh ba,tambayarsa nayi ya sanar dani ya tafi kotu Ana raba musu gadon mahaifinsu da ya rasu shekara daya baya Haka mukayi tafiyarnan babu wani dad'i,ko da mukaje gida sai naga gidan yayimin wayam da yawa,gizo ya faramin Ina Jin kaman sallamarsa,duk nayi sanyi tun Ina zuba Ido har na Dena Next day ma babu alamun Saleh,ji nake kaman banida lafiya sam banida kuzari,Ina aiki Ina tariyo hirar da mukayi dashi last Haka na Kare aikina ba wani walwala,ban ma jira zuwan jabir ba ina gama abinda zanyi na wuce gida Sallama nayi na shiga na samu mama da wata Mata suna hira,ga bedsheets a gabansu,gaishesu nayi na nufi d'aki,kirana mama tayi tace "Zo ki duba cikin wadannan bedsheet ki zabi Wanda kikeso tunda Allah ya kawoki" Komawa nayi na zauna na saka bedsheets din a gaba,dukkansu sunyi kyau,da kyar na samu na ware guda biyu na zuba tagumi Ina kallonsu D'aya maroon ne yayi kyau sosai dayan Kuma light purple,kallon mama nayi nace "Mama zabarmin a cikin biyunnan na kasa za'ba" Caraf matar tayi tace "Aikuwa bilki kin iya zabe,ni kaina wallahi karfin Hali nayi ban kwashe biyunnan na ajiyewa kaina ba,Amma hajiya me zai hana ki daukar mata biyun sai na Miki ragi,ki bada 75" Zare Ido nayi jin kud'in zanin gadon da yawa,da sauri nace "Kai mama kud'in akwai yawa,na d'auki purple din....ko Kuma Maroon din kamar yafi kyau ko?" Dariya mama tayi ba tareda ta kalleni ba tace da matar "65 zan Baki duka biyun,Banda abinki ma ai yanda muke dake cewa zakiyi na d'auki dayan a gudunmawa Amma kekam wurin kud'i bakya lamuni" Nikam tashi nayi na bar musu wurin sunata cinikinsu,Akan zanin gado kawai an tafi 70,to shi gadon nawa yake? Wanka nayi na fito na d'auki abincina Ina Jin suna zancen kayan kicin,Sam banaso naji Ana zancen aurena indai da sulaiman ne Bayan magrib ina kwance Ina faman Danna wayata Kiran sulaiman ya shigo, saida ya kusa yankewa na d'aga,cikin sanyin murya yace "Matata,Ina waje kiyi hanzari wucewa zanyi" Ajiye wayar nayi naja tsaki na saka hijab na fita, gaidashi nayi fuskata Babu wani annuri,dariya yayi yace "Wa ya ta'ba wifey na be?um?" Kokarin Kai hannunsa kumatunta yake na d'auke Kai tareda ture hannunsa nasa,bud'e Baki nayi zanyi magana ya katseni da cewa "Dad d'ina yamin magana cewa sun tsaida aurenmu,kema kinji ko?to shine nace bari nazo nayi proper proposal" Wani bracelet ya ciro a aljihunsa yace "Kawo hannunki na saka Miki" Kallonsa nayi na maida hannuna baya yace "Please, wannan karon kawai" Mika masa hannun nayi ya dauramin abun hannun,siriri ne golden colour sai wasu kananun stones dake zagaye dashi "Will you be my wife bilkisu?" Daga idona nayi na kalleshi,maganar da ya fad'a ji nayi tamin d'aci,ya had'e hannayensa biyu a wurin bakinsa Bata Rai yayi yace "Bakya Sona ko bilki?Baki yarda Dani ba?bazaki iya zama Dani ba? bakyaso ki zama matata?" Sauke kaina nayi nace "Ba haka bane" "To zan Kara tambayarki sau d'aya, idan Baki ce yes ba nasan Baki Sona Kuma ban Miki ba at all,will you be my wife bilkisu" "Yes" na amsa can kasan makoshina,ji nayi hawaye na neman gangaromin,Domin Saleh kawai nake hange a idona "Okay,nagode yanzu zan wuce sai mun sake haduwa ko?wannan abin na hannunki ya kasance koyaushe yana tareda dake,a wani store da naje a can Russia aka bani na siya,Mai shagon yace  dun Wanda ya bawa matar day za aura wannan to zasu rayu rayuwa Mai tsayi,Ina fatan muyi rayuwa Mai tsayi" "Nagode" na fada ina shafa abin hannun nawa Sallama mukayi na koma gida yayi tafiyarsa,wani business app dake wayata na bud'e na d'auki hoton abun nayi searching dinsa, sai ga irinsa sak,duba kud'in nayi Naga $42,converting nayi naga ya bani 15k harda wasu Yan canji,Cirewa nayi na saka a akwatin sarkokina Domin wannan ba abun yawo koyaushe bane Ina kokarin gyara shimfidata na kwanta mama ta kirani tace baba na son ganina,fita nayi na zauna a kasa wurin kafarta na sunkuyar da kaina Cikin fara'a baba yacemin "Ya sulaiman Babu wata matsala ko?" Gyad'a Kai nayi baba yace "Kidena daga min Kai kamar kadangaruwa,eh ko a'a,akwai matsala ne?" "A'a baba,Babu komai" "Kun fahimci junanku?" "Eh" na fad'a muryata can kasa Cike da murna baba yace "To Alhamdulillah,dama munyi magana da habibu Kuma an tsaida ranar aurensu Nan da wata shida idan Allah yayi muna Raye,ku Mata kune kuke shirya komai maman bilki,sai a fadamin abubuwan da ake bukata Wanda za'a fara yinsu a kusa" Ji nayi gabana yayi mugun faduwa,na ma kasa motsawa day wurin har saida baba yace "Jeki bilkisu,Allah yayi Miki albarka" Tashi nayi na tafi a sanyaye,Kiran sunana yayi yace "Nayi mantuwa,dangin Mahaifinki sun kirani dazu sunce suna bu'katar kije ki musu kwana biyu,gobe sai ki tafi idan Allah ya kaimu ko sati ne kiyi" Da kyar na amsa da to na shige d'aki da sauri,Ina zama Kan gado Kuka ya kwacemin da bansan dalilinsa ba,saida nayi Mai isata sannan nayi sallar Isha na Kuma yi salatul istihara Domin neman zabin Allah akan abinda zuciyata ke sakamin,son Saleh yayimin kamun da banyi tunani ba Washegari banje asbitin da nake zuwa ba,Ina d'aki ri'ke da carbi Ina addu'ar Allah ya ciremin Saleh gaba d'aya daga Raina na huta,ya Kuma bani ikon zama da sulaiman zaman aure Da wuri na had'a kayana Domin yaya ya kaini,ni kaina Ina son zuwa cikin dangin mahaifina Domin yanda suke nunamin soyayya da kulawa,idan naje goma ta arzi'ki suke hadomin,kowa so yake naje gidansa na kwana d'aya,sunso su karbeni daga wajen mama Amma ni nace musu nafison zama a wurin mama,zamana a tare dasu zai had a fad'a Domin kowa so yake ya rikeni daga mazansu har matansu 11:30am na fito daga d'aki ina Jan akwatina,kallona mama tayi tace "Me ya Sami idonki na gansu sun kumbura?" Murza idon nayi nace "Mama ciwo sukemin ne,jiya da dare suka yita ruwa,idan naje can zanje asbiti insha Allah" Bakin glass jabir ya bani yace "Sa'ka wannan saboda rana ko?sabo ne yau nake niyyar sakawa Ashe rabonki ne,Kar dai ki manta tsarabarki biyu Zaki kasata" "Na amince" na fad'a Ina saka glass din a idona,sallama na yiwa mama muka fita Ina shiga motar Yaya yace "Kiyi ha'kuri zamu fara biyawa mu d'auko Saleh sai mu kaiki" Okay na fad'a na gyara zamana,unguwar rijiyar Zaki muka nufa,wani iri nakejin a jikina ji nake Sam banaso Naga Saleh Horn yaya yayi a kofar gidansu Saleh,wani tangamemen gida ne masha Allah,da gani part part ne Domin Naga gidaje masu bene har uku,iya abinda nake hangowa a jikin gidajen babu banbanci,duk gidajen Ana musu fenti a lokacin "Yaya gidansu Saleh babba ne sosai Masha Allah" "Eh gaskiya gidansu nada girma,mamansu da yayyensa biyu maza duk a ciki suke gini, "Eh gaskiya gidan nada girma,Kinga benayennan,gidajen su Saleh ne da Yan uwansa maza biyu,akwai Kuma bangaren mahaifiyarsa itama Tana ciki,ai kwanannan ma insha Allah zamusha biki shiyasa kikaga Ana yiwa gidajen fenti" "Bikin wa?" Na fad'a cike da mamaki "Bikin Saleh da yayansa" Yaya na rufe Baki sai.ga Saleh ya fito,yayi matukar kyau cikin farin yadinsa,plain Babu wani aiki a jiki,agogo yake makalawa a hannunsa yana tahowa cikin sauri Shigowa motar yayi yace "Kanwata sannunki ko?kwana biyu" Murmushi na kakalo Domin har yanzi Ina cikin shock na zancen aurensa,duk yanda yaso ya Jani da Hira na dinga dojewa har suka kaini Gidan Yayar mahaifina suka ajiyeni,sallama na musu a gurguje na shige ba tareda waiwaye ba Oyoyo yara suka.fara min har suka kusa kaini kasa,fitowa yayar mahaifina tayi Cike da fara'a tace "Sannu da zuwa bilki,wato sai yau ko?" Hugging dinta nayi nace "Kiyi ha'kuri anty,wallahi karatu yasha min Kai" "Ba wani karatu,bayanta tun yaushe kukayi hutu har ya kusa karewa?kedai kice kina San kina soyayya Dan babanki ya sanar Mana an Sanya ranarki muna farin ciki Allah ya Sanya alkhairi" Murmushi kawai nayi muka.shige tare, d'akin yayanta mata ta kaini duk basa Nan,kwanciya nayi Kan gadon take na hau bacci Ina farkawa abincina na jirana,ci nayi na sake kwanciya abuna har la'asar sannan ta tasheni,haka tayita dawainiya Dani har dare Muna zaune da dare muna Hira naji Kira a wayata,dubawa nayi Naga bakuwar numba na daga ba tareda magana ba,coming muryar da tafi komi za'ki a kunnena naji ance _kanwata Saleh ne_ Sum sum nantashi daga wurin nayi d'aki ina jin dariyarsu,kwanciya nayi Ina Jin wani farin ciki a Raina nace "Yaya Saleh ya kake" _ina lafiya,nace dazu ko laifin me nayi ake shamin kamshi?ko Dan kinsan kin Had'u ne dazun?_ Shiru nayi Ina mamakin abinda ya fad'a,bai damu da shiruna ba yace _ya mutumin naki?_ "Lafiya" na fad'a a hankali _banason ganinki dashi ko kad'an bilki_ "Meyasa?" _nima ban saniba,idan na ganku tare ko naji kina zancensa Raina baci yake,ranar da Kika cemin ya tabaki ban iya baccin kirki ba_ "Meyasa?" Na sake tambaya tare da tashi na zauna _ina sonki bilkisu,Ina matukar sanki,tunda Kika taso naji raina Yana sonki,na Dade Ina adana soyayyata har lokacin da ya dace,saidai kaman ke ba rabona bace bilki,_ Zuciyata bugu take cikin sauri,take hawaye ya fara zarya a fuskata,cike da takaici nace "Haba Yaya Saleh,meyasa baka fad'a tuntuni ba,saida aka sanya ranar aurena?" _bilki....ko yayanki baisan Ina sonki ba sai kwanannan,na kasa furta hakan saboda kunyar iyayenki,gani nake kowane lokaci yayi wuri,a wurina me karamar yarinyace bilki,kanwata dukkanmu munsan bakyason sulaiman,ki fadawa iyayenki bakya sonshi kafin lokaci ya Kure maki_ Cikin shesshekar kuka nace "Yaya Saleh lokaci ya Riga ya Kure,an Sanya ranar aurena bazan iya bud'e Baki na sanarwa iyayena bana son zabinsu ba" _bilki nasan bakya Sona Nima,Amma kinsan Zaki Sami kulawar da sulaiman bazai Baki ita ba a wurna_ "Ina sonka Mana....." A tsorace na rufe bakina domin bansan na furta hakan ba _me kikace bilki?_ Da sauri na katse Kiran Ina Kara sautin kukana,meyasa wannan abun zai faru Dani a wannan lokacin,ban saniba Ashe sautin kukana ya fita parlor Kirana Saleh yake naki dagawa,shigowa anty tayi ta dafani cike da damuwa,ba tareda tace komai ba ta d'auki wayata da keta Kara ta daga ta Sanya a speaker Cike da damuwa Saleh yace _bilkisu.....hello bilkisu Dan Allah kice wani Abu Mana,nasan nayi babban kuskure da ban furta Ina sonki ba duk tsawon shekarunnan,karki hukuntani ta hanyar auren wani ba niba,kema kina Sona bilkisu ki sanarma su mama zasu fahimceki_ Cikin Kuka nace "Saleh Dan Allah mubar wannan maganar,daga ni har Kai aure zamuyi,Allah yayi ba rabon juna bane mu muyi ha'kuri mu rungumi kaddararmu Allah yasa itace Mafi alkhairi" Danne wayar nayi na kashe aunty ta kalleni tace "Me yake faruwa?" Cikin Kuka nace "Babu komai anty" Tashi tayi tace "Bari na Kira mamanki to na sanar Mata" Cikin sauri na ri'ke anty nace "Dan Allah anty karki kirata,banaso kowa yasan da wannan,an Riga an Sanya aurena da sulaiman,da ace Saleh na Sona da gaske da tuntuni ya furtamin,sama da shekara goma Yana ganina,kuma shima aure zaiyi" Fita tayi Bata kulani ba ta Kira mama,can take dawo da cookies da lemo ta ajiyemin,take na cinye cookies din tas Nasha lemon,Amma banji wani sanyi a Raina ba Dawowa anty tayi ta zauna ta nunamin cinyarta alamun na kwanta,kwanciya nayi hawaye na bin idona,kaina take shafawa cikin rarrashi tace "Kina sonshi sosai ko?" Gyad'a Kai nayi Kuka na neman kwacemin nace "Anty abin yafimin ciwo da ya furtamin shima,a tunanina Ni kadai nake abuna,anty Yaya zanyi Dole na auri sulaiman Dani da Saleh Dole mu hakura da juna" "Na Kira mamanki na Kuma sanar Mata,zamu San abinyi insha Allah,bilki ke yarmu ce,Kuma baba bazaiji dadi ba ace kin zauna da Wanda ya za'ba Miki ta Dole ne kawai,iyayenki mass fahimta ne komai zaizo da sauki" Share hawayena nayi Ina tunanin kala kala a raina,a haka har bacci ya kwasheni Da safe kuwa mama sammako tayi muna karyawa wurin 10 sai gata,fuskarta d'auke da damuwa ta zauna tana kallona Sunkuyar da kaina nayi na kasa cin abincin na Kuma kasa daga kaina,Ana gamawa kowa ya barmu daga ni sai mama sai anty Cike da damuwa mama tace "Wallahi binta bakiji damuwar da na shiga ba da Kika cemin yarinyarnan Tana Kuka,Bata taba fadamin sulaiman nada matsala ba Kuma duk tambayar da babanta zai Mata zata ce Babu komai" Bayani anty ta Mata na iya abinda ta sani suka juyo kaina,cikin lallashi mama tace "Bilkisu meyasa Baki fadamin ba?" Shiru nayi na kasa cewa komai,anty ce ta amsamin tace "Tayi zaton ita kadai take Sonsa shiyasa tayi shiru,Amma yanzu tunda sun son junansu sai a San abinyi" Ina zaune kamar kurma suka Gama.tsarinsu suka ce mama.zata tuntuni baba da maganar,sosai naji relief a Raina just nake kaman an saukemin nauyi daga zuciyata Babu Wanda ya sakemin maganar aure,Amma kullum anty tana daukana muna zuwa shagunan da ake saida kayan d'aki,tana nunamin su,sati na daya a gidanta take sanar dani zasumin kayan gado a matsayinsu na dangin uba,Amma baba yace su Bari,still dai zasu min ko da ace Babu wurin ajiyewa Godiya na dinga Kora Mata har na bar gidan na koma gidan kakannina wato iyayen mahaifina,kwana biyu nayi a can sannan na tafi gidan kanwar mahaifina itama na mata kwana biyu,saida nayi sati uku cir Ina yawo sannan na koma gida Ranar da na koma kuwa baba ya sakani a gaba,ya d'auki lokaci kafin yayimin magana Wanda hakan ya bani tabbacin ransa a bace yake,ni nasan zancen Saleh bazai ma baba Dadi ba,kallona yayi yace "Bilki,kema 'yata ce kamar yanda sai yayana suke,bana banbantashi sa yayana,yanda zan baiwa yayana zabin abinda sukeso kema zan Baki,meyasa Baki sanarmin bakyason sulaiman ba?" Kaina a kasa nace "Kayi ha'kuri baba" "Allah yayi Miki albarka,Saleh yazo ya sameni kuma har ya turo magabatansa,kamar yanda lokaci yake,Nan da watanni shida  za'a d'aura aurenku da yardar Allah" Sunkuyar da kaina nayi Ina godiya a zuciyata,sakamin albarka yayi sosai sannan y sallameni,Ina zuwa daki kuwa sai ga Kiran Saleh Cike da farin ciki na daga yace "My angel" "I'm" na amsa cike da fara'a "Hmm munso mu cutar da junanmu fa" ya fad'a yana dariya a hankali Cikin sanyin murya nace "Yaya fa yacemin ka kusa aure,ya akai haka?" "Eh to dogon labari,kamar dai or dinnan Nima li'kamin ita akayi,Yar uwata ce a gidanmu ta taso Kuma Allah ya bani ikon kuncewa na barwa tuzurun yayana ita,tare za'ayi aurenmu insha Allah,ke Kuma ya mutumin naki?" "Ban saniba wlh,Domin banji daga gareshi ba" "Har yanzu mamaki nakeyi" ya fad'a cikin daddadar muryarsa "Ni kuma.tsoro abin yake bani,na kasa gaskata abin" "Mu daiyi fatan Alkhairi" ya fad'a tareda canza hirar,tamkar wadanda suka Dade Nan muka hau zancen kalar fentin gidan da kalar kayan gado da labulaye da kujerun da ya dace a saka,har zancen kayan kicin mukayi dashi A Daren sulaiman yazo ya sameni yake sanarmin zai koma Russia ya samu aiki,dama aurena ne zai zaunar dashi Kuma Allah ya taimakeshi ya rabamu, bracelet din da ya bani na maida Masa ya karbi abinsa ya tafi Abu kamar wasa kamar baza ayi ba har watanni shida sunzo karewa,gida ya cika ma'kil da Yan biki na kusa da na nesa,no kuwa tuni na birkice,mutane gareni lungu da sa'ko,duk na susuce wajen aika katin gayyata,Katina 700 aka buga na kamu amma kaf sun Kare,na rasa Dani da mama was yafi gayya Biki biyi kawai mukayi sai gidansu ango suka shirya liyafa d'aya,an gayyaceni da Yan tawagata mutum 100 kawai Bikin nasu yayi matukar haduwa,saidai na zama bare a ciki, dukkansu Yan uwane,anan Naga Yan uwantaka,jikina Kuma yayi sanyi yanda wasu daga cikin matan wurin ke wurgomin kallon banza Anzo wurin da banaso wato li'ki,a rayuwata na tsani zubar da kud'in da ake a wurin biki,daga iyayen amarya har na ango ai sunada bukata,meyasa bazaka kunshe ka Basu ba sadai ka zubar saboda duniya ta gani? Kiran dayan angon aka fara you da amaryarsa sultana,murmushi ke saika daga fuskarta,oh,da tuni itace matar Saleh,tsayawa sukayi a fili Nan fa yan uwa suka fara musu barin kud'i, Bayan an gama asarar kud'in aka kirani,danginmu Basu damu da li'ki ba,Nan dangin saleh suka fito suka.fara zuba Masa kudade,shima nashi ya ciro ya fara li'kamin ganin nawa dangin ba Wanda yazo,MC na ta min habaici wai ko baa Sona ne nikuwa ko a jikina,saida wata take ta kar'bi Mike din tace "Jamaar dake wurinnan Babu mai taimakawa wannan amaryar ne ua fito ya fanshi danginta?da alamu baby canji a hannunsu" Daga yanda tayi maganar nasan zagina take,gashi sun'ki Dena yiwa Saleh li'ki,ta Dole dai aka Sanya Yan uwana yimin li'ki,Nima kuwa Naga gata ta wannan fannin,saida aka cikawa masu kida aljihu sannan muka bar wurin Raina a dagule,Domin harda masu kallona sumin tsaki,na taorata sosai a Raina Ina cewa wani irin Rami nake kokarin jefa kaina? An gama taro lafiya har an d'aura aure,bazaka ce Saleh suruki bane  Domin bajewa yayi a gidanmu ya cika tumbinsa sannan ya dauki hanyar gidansu,duk yanda zaiyi ya sameni naki Domin Saleh d'aura aurennan naji kamar na fita da gudu nace a kunce,tuni kewar gida ta fara kamani Nasha nasiha kala kala,na kuma sha gudunmawa,kowa yazo yace iyayena mutanen arzi'ki ne Iyayena da suka mutu basu barmin komai ba sai gidan da.suke ciki,Kuma.mahaifina yana da arzi'ki,kyauta ce dashi sosai a haka ya karar da duk abinda ya mallaka,sai gashi Naga gatan da nayi zato ba Kayan gado a aka kawomin set uku kyauta,Banda kayan kicin da bansan adadinsu ba,kud'i kuwa sai godiyar Allah Domin an rubanyamin sadakina kusan biyar Da akazo kai amarya kuwa Nan na shiga daru,da kyar aka banbareni jikin mama Tunda muka d'au hanyar gidansu Saleh gabana ke faduwa, innalillahi wa inna ilaihi raji'un naketa maimaitawa a tunanina ma accident zamuyi sai gaahi munje lafiya Part din mahaifiyarsa aka nufa Dani Domin danka mata amanata Fuskata a rufe saboda haka Banga komai ba,naji dai sallama da gaishe gaishe,bayan sun gama.bayanansu na manya Mahaifiyar Saleh tace "To mu a al'adar gidannan idan aka kawo Mana suruka,zata zauna anan har mijinta yazo ya dauketa,ni zan danka Masa amanar da kuka barmin," Ba wani ja inja suka barni anan suka fice,suna fita naji ance "Tashi ki zauna Kan kujera" Tashi nayi Babu musu na zauna, "To amarya bud'e fuskarki Mana mu ganki mu gaisa',Domin mijinki ma bazai iso ba sai nan da kusan AWA daya da rabi" Bud'e fuskata nayi kaina a sunkuye,umarni akamin na daga kaina ba musu nayi,dayar amaryar wato sultana na gani ta hard'e kafa Kan kujera Tana cin dambun shinkafa Nunani tayi da cokalin hannunta tace "Yaya maymu,Kinga fa akan abinda uncle ya kasani" Wadda aka Kira da Yaya maymu tace "Ai wallahi Namiji butulu ne,ita ba kyau ba,uban me.ma ya gani a jikinta? Sultana Bata tanka ba taci.gaba da cin dambunta,Mata hud'u ne a d'akin Banda mahaifiyarsu,d'aya daga cikinsu ce ta taso tace "Ai wallahi sale y badamu,aikin banza aikin wofi ya'ki jininsa akan wannan abar,wallahi hajiya ji nake kaman na shaketa saboda tsana" Nayi zaton mahaifiyarsu zata musu magana Amma ga mamakina sai Naga tayimin wani kallo Mai d'auke da tsantsar tsana,cikin Isa da gadara tace "Waye Mahaifinki?" Daga Nan nasan kaddarata ta zaman aure ta fara 5 Gyaran murya nayi nace "Mahaifina ya rasu" "To Wanda Kika taso a wajensa fa?" "Dan kasuwa ne" "Kasuwancin me yakeyi" "Man gyad'a" Had'a Baki sukayi suka kalleni sukace "Man gyad'a?" Ba tareda na d'auki hakan cin fuska ba nace "Eh,man gyad'a" Ri'ke ha'ba yaya maymu tayi tace "kinji fa kursum,wai man gyad'a for God's sake,ai duk danginmu Babu mai kaskantacciyar sana'a kaman shi salen,shine zai d'auko mana Yar Mai saida man gyad'a a kasuwa" Sosai naji zafi a Raina,Domin sana'ar baba tafi karfin a kirata kaskantacciya,shi yake sayen gyad'a ya bayar a Masa Mai,ya saida ga manyan dealers na man gyad'a,a Nigeria jihohi kad'an ne baya Kai man gyadansa,Kuma yana ri'ke iyalinsa Daidai gwargwado harda ni ma Yar karere,Kuma dai a kayan aurena kowa yasan Babu kaskanci Bance musu komai ba na sunkuyar da kaina,sunata sukar sana'ar baba da ta Saleh,ni kuwa alfahari nake da sana'ar mijina,abin mamaki duk maganganunsu sultana Bata tankawa saidai ta kalleni irin kallon tausayi ta kalli Yan uwanta ta girgiza Kai A hankali na lura da mutanen dake d'akin,yayan hajiya Mata uku ne a d'akin,Yaya maimu,wadda nasan dai sunanta bazai wuce maimuna ba,sai Kuma ummukursum,sai Kuma wadda take kaman ta shakeni,naji itama sunanta aymana,dayar da na lura Bata sanya baki ba Naga kaman sirika ce irinmu "Ke Kuma jumana kinyi shiru ko?" Murmushi jumana tayi tace "To ni ai sirika ce me zance?aikin Gama dai ya Gama tunda har hajiya ta Masa magana ya'ki ji saidai mu zuba Masa Ido,ni kaina kunyar idon hajiya yasa na amince da auren uncle Hashim,Kuma gashi ta sanyamin albarka yanzu son junanmu muke sosai,Banga abin 'ki a auren danginka ba,dukkanmu fa cousins ne meye abin 'ki a sultana?yarinyar da ta taso Tana masa Ladabi da biyayya,Kuma a gabansa ta girma balle ma ace wani abun,mudai ki sani bilki,bama maraba dake cikin danginmu ko kad'an " Tashi sultana tayi ta nufi wata kofa da plate din hannunta,da alamu kicin ne,fitowa tayi da plate biyu a hannunta tazo ta ajiye a gabana tace "Kunga ki barta haka.mana,daga kawo amarya zaku saka mata ciwon Kai,ba Dan ni akeyi ba?to na yafe na yau kwa d'aura gobe,amarya sauko kici dambu,ko zakici shinkafa?akwai kunun aya da zobo wanne kikeso?" Kallon dambun nayi tuni kwantacciyar yunwata ta taso,Amma ai bazan zage darena na farko a gidan surukai naci abinci ba Girgiza Kai nayi nace "Nagode,Amma na koshi" Ai Ina gama fad'in haka cikina yayi wani Kara alamun yunwa,kunya ce takamani ita kuwa sultana murmushi tayi tace "Idan kina kunyarmu ne ki ma Dena,Domin cikinmu Zaki zauna,sauko ki cika cikinki Bari na d'auko Miki lemo" "Um,taci?tun dazu take kallon kofa Tana rawar kafa ita zata shiga daki da miji taci kaza,rabu da ita taci kazar" aymana ta fad'a Tana wani.yatsine fuska Bansan lokacin da nace "Kuyi ha'kuri wallahi ba haka bane" "Kuma dai" kursum ta fad'a tana kallona,Dole na d'auki dambun na fara ci Domin fa Raina ya sosu,idan bankai Abu bakina ba za'a iya samun matsala Dambun kuwa yayi Dadi,gefena sultana ta dawo ta zauna tana cin dambunta plate na biyu,a hankali nakeci ina jin Yana kokarin shakeni Amma naki daukan zobon Nasha Ina cin dambun naji sallamar su Saleh,maza uku ne suka shigo d'akin,sune ragowar yayan hajiya kenan,kallona Saleh yayi yace "Kut,wa ya baiwa amaryata dambu?salan ta shake ko?" Dariya sultana tayi tace "Uncle nice,Kuma da bataso ai bazata ci ba" "Ni amaryata nama zata ci ba dambu ba,ke dai da bakisan dadin nama ba kick dambunki" ya fad'a cikin zolaya,dariya tayi tace "Ai naji Dadi da baba cin Naman,babu wani abun Dadi a nama nidai a wurina" "Shiyasa na siyo Miki kifi" dayan dake gefen Saleh ya fad'a,cikin say sultana ta ajiye plate din dambunta ta Masa wuri a gefenta tace "Kai,Amma kuwa na gode Yaya usman,mugani" Kallon su maymu yayi yace "Bazan bud'e su cinye mana ba,ki Bari sai mun haura" ya fad'a tareda kashe Mata ido,d'auke.kanta tayi inaga dai yanzu ta tuna ita amarya ce Domin ta dan fara nuna alamun damuwa Dukka d'akin Babu Wanda ya kula Saleh Banda sultana,tashi sultana tayi da ya Usman suka koma dayar kujerar da zata ci mutum biyu suka bawa Saleh gefena ya zauna,karashe dambun dake plate Dina nayi na ajiye Sunkuyowa yayi daidai kunnena yace "Wato bama wuce tayi ko a gaban surukai" Tamkar ban jishi ba nayi,Domin duk idonsu kaina yake,Kara matso da kansa yayi kafin yayi magana yaya maymu tace "Kunga Kar ku Mana rashin kunya anan,mama a sallamesu kafin su Mana aika aika" Gyara zama mama tayi ta fara Mana nasiha kamar gaske "Alhamdulillah,nagode Allah da ya rayamin ku ya Kuma rayani Naga wannan lokacin da na aurar daku dukkanku,bazan muku dogon bayani ba Domin dukkanku yayana ne,Usman da Hashim,ga Amana Nan na baku,dukda Hashim Kai tsoho ne a cikinsu,Amma inaso ki rikemin yayana Amana,karku cutar dasu karku Bata musu Rai,ki musu duk.abinda sukeso,Kuma sultana da jumana,ki kularmin da yayana tsakani da Allah,ki ri'ke sirrikan mazajenku ku zauna lafiya" Shiru tayi ta kallemu,daga Ni har Saleh jikinmu yayi sanyi,wato mu ba 'ya'ya bane,kallon saleh nayi ta gefen iso naga yanda fuskarsa ta sauya sosai rashin jin Dadi ya bayyana,cigaba tayi ba tareda ta kallemu ba tace "Naso ace Rayuwar yayana ta kasance yanda na tsara,ku auri jininku mu zauna Babu bare a cikinmu,Amma hakan batayi ba,Dole mun samu shigowar bare cikinmu,Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba,Allah yayi muku albarka" Ko Bata fad'a ba na jima da jin Kaina a matsayin bare,kallon da sukemin tsikar jikina tashi take,hajiya kuwa idan ta kalleni gabana yankewa yakeyi ya fad'i "Ku ku Kira mazajenku suzo su kwasheku ku Kuma ku tafi Allah yayi muku albarka" Tashi sukayi suka ja sultana d'aki,mu kuwa mun kasa motsi a wurin,hajiya ko kallo bamu isheta ba kamar ma bata san da rayuwarmu a wurin ba Kusan minti 20 suka fito da sultana,tashi usman yayi suka jera sukace "Hajiya Bari mukai Yar lelenmu dakinta ko?" "Ya kamata,Domin banason 'yata ta taka ita kadai" Ina zaune kamar marainiya,ko da yake ita din ce,tamkar ma dai an kafemu a wurin,muryarsa cikin nuna rashin Dadi yace "Mu tafi ko?" Tashi nayi cikin kasala na bishi a baya,tafiya mule duk cikin rashin dadi,shewarsu naji muna karasawa wurin gidan,duk kewar gida ta kamani,da ace sulaiman na aura da haka zamuyi muma Gidanmu shine na uku a cikin gidajen,muna shiga naji shirun yayimin yawa,kwalla ce ta zubomin na saka mayafina na goge a Raina Ina Kiran mamana Zama yayi gefena yace "Kiyi ha'kuri bilkisu,bansan zasu Miki hakan ba" Murmushin yaqe nayi nace "Bakomai,ai Yan uwanka ne,mu bar wannan a gefe" "To mu tashi muyi abubuwan da Allah ya umarcemu sai mu ci abinci ko?" Gyad'a Masa Kai nayi yayi hanyar wani lungu a babban palon da muke zaune,bene na gani muka hau,alwala nayi shima yayi muka zauna a palo,kazar da ya kawo kasa ci nayi,da kyar naci fukafiki Nasha lemo naja gefe Kokari ya dinga yi Domin nayi fara'a,saida ya tabbatar na sakin raina tukunna ya fara nunamin hanyar Disney world 😉tuni na fara ajiyar zuciya Ina Kiran mama,lalube yake a duhu na kuwa barshi yayita fama Wani Dadi naji a Raina ganin y kima gefe,na aza ya yafe ne,wayarsa Naga ya d'auka ya kunna torch light ya koma....zare Ido nayi na rasa ma takaici zanyi ko dariya, gama haske haskensa yayi ya aje wayarsa Kan bedside drawer yaci gaba da ibadarsa..... Washegari da wuri wuri na tashi,shayi na daura na fara tunanin me zance dafa,da alamu Torchlight ta haska inda ya kamata Domin ban wahalar da nake tunani ba,dariya nakeyi Ni kadai a kicin din 'kasa,Allah ya kaimu lokacin da zan fara kiransa Torchlight guy Muna Gama breakfast kuwa sai ga hayaniyar Yan uwana,cike da murna na fita Domin tarosu Shigowa sukayi Niki Niki da kayana,ko ta kan Saleh ban Kuma bi ba na rakasu sama,jera kayan mukayi muna hira sannan muka sauko A kujera muka na sameshi Yana zaune,muna sauka ya koma upstairs Abinci muka girka na Kai masa,Yana bacci na ajiye na rufe kofar na fito,wuni mukayi da sisters muna Hira sai can yamma suka tafi Washegari da safe na fito gaida hajiya,sultana na gani itama ta fito muka gaisa muka karasa tare D'ar dar nakeji Amma na dake,muna shiga hajiya ta fadada murmushinta ganin sultana,Ni kuwa da ta kalleni saida naji Yar a jikina saboda wani irin kallo da ta watsamin,zama sultana tayi a gefenta ta gaisheta,dur'kusawa nayi Nima nace "Hajiya barka da safiya kin tashi lafiya?" "Lafiya" ta amsa ba tareda ta kalleni ba,ra'bewa nayi jikin kujera kaman marar gaskiya,hura suke da sultana wadda ni kwata kwata na hankalina baya Kan maganarsu "Ke" naji hajiya ta fad'a,da sauri na d'ago cikin tsoro nace "Na'am" "Tashi ki fita mana,kin sakamu gaba" Tashi nayi na fita jikina a sanyaye,wace irin matace wannan?Ina Jin sultana na cewa "Hajiya da dai kin Mata a hankali" Wucewa part Dina nayi na d'auko system dita na fara karatu,Domin presentation gareni jibi Ajiye system din nayi Kan kujera Ina zagaye d'akin Ina yiwa kaina bayani da karfi,a hankali na fara mantawa da abinda hajiya tayimin Ina cikin bayanin Saleh ya sauko daga bene,wayarsa ya bude ya faramin video nayi kaman ban gansa ba "Wow, that's my beautiful wife" Murmushi nayi naci gaba da bayanina ya sake cewa "I love you my star shine" Kallonshi nayi cikin shagwaba nace "Kana distracting Dina" "To nadena" ya fad'a yana mele Baki wai zaizo kwaikwayeni,hannu na nuna masa alamun yayi shiru naci gaba da bayanina Maida wayarsa yayi aljihu yayi hugging Dina ta baya tareda pecking Dina a kumatu yace "Zan fita,sai na dawo star shine" "Sai ka dawo" na fad'a Ina sunkuyar da kaina "Me kikeso na kawo Miki?" Ya fad'a yana ri'ke Dani,murya qasa qasa nace "Bakomai,Allah ya dawo dakai lafiya" Kansa ya d'aura a wuyana yace "Kawai ki fad'a Mana,kice so nake ka dawomin da kanka yanda ka fita" Hannu nasa na rufe fuskata cikin Jin kunya irin ta amare,dariya yayi yaja kumatunta yace "bye bye ki kulamin da kanki" Karasa presentation. Din nawa nayi na sake dubawa na tabbatar ba gama editing sannan na daura abincin rana Washegari ma da wuri naje gaida hajiya,Ina gaidata tace na zauna tana son magana damu duka, Addu'a nake Allah ya sa abin alkhairi zata fad'a Dukkanmu da mazajenmu mun had'u a d'akin,Saleh na Kan kujerar da nake zaune a kasanta,jinsa nake tamkar kariya ne gareni Domin zaman dakinnan kaman zaman kurkuku yake a wurina,hajiya na fara magana naji tsoro ya kamani "To Alhamdulillah,da farko dai zan yiwa jumana godiya da irin kokarin da tayi min,Allah yayi Miki albarka Allah ya Baki zuri'a ta gari" "Bayan wannan kaman yanda ku Kuka sani Banda waccan,jumana tunda ta shigo gidannan take dawainiyar kawomin abincin safe,Rana har ma da dare,kusan shekara biyu kenan" Tura Baki sultana tayi tace "Hajiya Nima fa da inanan Ina Miki,ki sakamin albarka Nima" "Kema Allah yayi Miki albarka,yanzu abinda ya Sanya na taraku anan shine,a tsakaninku Zaku Raba,bazai yiwu a bar jumana ita kadai da wannan dawainiyar ba,tunda ku uku ne wata zata dinga min abincin safe,wata na rana wata na dare" Nidai bance komai ba,da sauri sultana tace "Na dau na dare" Jumana Kuma tace "Na d'auki na safe" Dago kaina nayi Naga duk hankali na kaina,kallon saleh nayi sannan nace "Zanyi na rana" Cikin sauri Saleh yace "Hajiya gobe bilkisu zata koma makaranta Kuma zata fita da wuri,sannan sai can yamma zata dawo,Ina ganin sultana ki bata na Daren ke ki d'auki na safe" Kafin sultana ta amsa hajiya tace "Idan bazatayi ba ta barshi,da mahaifiyarta ce ai zata iya ajiye makarantar Domin ta Mata girki ko?" Kirjina naji ya daure saboda ambaton mahaifiyata,baiwar Allah da ko ganin fuskata batayi ba ta koma ga mahaliccinta akan Dan karamin abunnan za'a nemi tozarta min ita Muryata kasa kasa nace "Kiyi ha'kuri hajiya zanyi" Tsaki jumana tayi tace "Meye kike wani magana kaman an maki Dole?Kinga idan baza kiyi ba ki barshi,mu da take uwarmu ya zamar Mana Dole mu Mata ai zamuyi,Amma ke ai uwar mijinki ce" Ban to daga kai na kalleta ba nace "Zanyi hajiya,insha Allah zanyi kiyi ha'kuri" A fusace hajiya ta kalleni tace "Au hakuri ma kike bani saboda nace ki ciyar Dani?kina karkashin Dana kina cin arzikinsa?abincin da zakimin shine ya Bata Miki Rai har kike wani daure fuska?ki barshi tunda bazakiyi ba,Kar ma Kimin abinda zai batamin rai" _ai a cikin garata zan dafa Miki ba wai arzikin danki zanci ba_ Na fad'a a Raina,kwalla naji na kokarin zubomin na danne nace "Hajiya ba haka bane,kema kamar uwa kike a wajena,zanyi komai Dan na kyautata Miki,ki yafemin idan nayi wani Abu da zai Bata Miki Rai" D'auke kanta tayi daga gareni tace "Naji,gobe 12 ki kawomin abinci,wainar shinkafa nakeso da miyar ganye,ki sakamin cow leg a ciki" Da kyar na amsa da to,sannan nace "Hajiya Ina neman afuwarki,gobe 12 zanyi presentation a makaranta,kiyi ha'kuri karfe biyu zan kawo Miki duk abinda kike bukata" "Tunda ba Taki uwar bace Zaki ce haka mana,ki barshi banaso" Ha'kuri na dinga Bata tayimin banza,shima Saleh ya saka Baki tayi kaman batasan inayi ba,saida sultana da usman suka saka Baki sannan tace ta ha'kura,Amma idan 12 ta wuce Bata bu'katar abincin Tashi nayi na fita,Ina sanya kafata a kofar d'akin hawaye suka fara bin fuskata,cikin sauri nayi gaba ba tareda na jira Saleh ba Ina shiga gida na goge fuskata cikin sauri,shigowa Saleh yayi damuwa karara a fuskarsa,kafin yayi magana nace "Dan Allah ka samo min cow leg yanzunnan saboda na daura yayi laushi kafin gobe" Hugging Dina yayi sosai a jikinsa Yana shafa bayani,a hankali ya furta "I'm sorry" Wasu hawayen naji na danne na kakalo murmushi nace "Laifina ne,itama uwace bai Dace Ina sa insa da ita ba,yanzu dan Allah ka samo min cow leg d'in" Amsawa yayi da toh sannan ya sakeni ya fita,zama nayi Ina tunanin yanda zanyi,Nan dabara ta fadomin Jika shinkafa nayi na fara shirya abubuwan da nake bukata na miya,na Gama hada komai Saleh y kawomin cow leg d'in na daurashi a pressure pot Kafin na kwanta bacci saida na had'a miyar wainar na sanyata a fridge sannan na Nika shinkafar a blender na hadata na rufe Da safe 10am na fara soya wainar,kafin 11 na Gama kasancewar kad'an nayi,Domin Sam waina ta fita a Raina daga jiyan Ina Gama soya wainar na bawa Saleh instruction na yanda zai dumama miyar na bashi flask din da zai zuba abincin a ciki na fice cikin sauri Na kuwa yi sa'a 12:10 na shiga class din,Daidai lokacin da malamin ya shiga, addu'a na dinga yi Domin duk na rude,cikin taimakon Allah nayi Amma ba yanda naso ba,nasan bazaifi rabin mark Zan samu ba Mun fita sallar azahar Naga text din Saleh. _idan kin tashi ki kirani zanzo na daukeki😘😘_ Ok na tura masa na zauna muna Hira Kan presentation dinmu,cikin hirar kawata Fatima take cewa "Wato yarinyarnan aure ya rud'aki ko?presentation dinnan da kyar kikasha,Kar fa aure ya fara interfering da karatunki,bakiga yanda Kika shigo ba firi firi kamar an koroki" Murmushi nayi na d'auko powder na saka na saka lip balm na gyara hijabina nace "Yanzu fa?" "Ko kefa,har kinyi kyau dake" sa'eeda ta fad'a, mu ukunnan haka muka fara karatu tun shekarar farko,gamu a ta hud'u muna jiyo kamshin gamawa Zuba tagumi fatima tayi ta kalleni tace "Yanzu fa Nan da shekara sai mu ganki da jaririya ko jariri ko?" "To me Zan jira?karatu ai yazo gangara yanzu ko da rarrafe ma.wuce da yardar Allah,Kuma kinsanni,wallahi banki wata Tara ma na haihu ba,Allah Allah bake kawai na ganni da baby Nima,na gaji da d'aukan na mutane" Sa'eeda na Danna wayarta tace "Nikuwa auren nawa ma sai mun Gama Domin bataso na haihu a school wallahi,Dame zanji?rainon yara ko na uban yaran ko kula da kaina ko Kuma karatun?bazan iya ba,da na Masa bayani yace shima yafiso idan na gama na samu nutsuwa sai ayi auren mu more soyayyarmu" Itama Fatima cewa tayi "To ai ko ni da zaai aurena next year Kinga dai muna final year,planning zanyi Kuma munyi magana ma ya amince cewa nayi,idan na Gama karatuna sai na haihu na samu lokacin kaina da na baby da na mijina,kema kiyi Mana bilkisu,haihuwa a nursing wahala ce kina ganin yanda suke fama" Nikuwa ko a jikina nace "Haihuwa rahama ce wallahi,ba abinda zanyi gara nayi na huta,ko zanyi planning sai na haifi daya,Naga kafin yayi shekara na samu wani cikin to anan ne zanyi planning,Amma for now zagewa zanyi na day ciki Nima na ji Dana ko yata a hannuna" Dariya sukayi sukace "Mayyar yara kenan,to Allah yasa 9months ki haihu dai kowa ya huta,na tabbatar ma kina haihuwa idan kikaji wuyar zakice bazaki sake ba sai bayan shekara biyar" Ban amsa musu ba na Kira Saleh nace na Gama,sanarmin. Yayi Yana cikin school din na fito,kwatantamin inda yake yayi naje Amma Banga alamun motar Yaya ko Kuma adaidaita sahu ba,waiwaye nake nace "Kana Ina ne ban ganka ba" "Ganinan kina kallona Mana" ya fad'a cikin wayar Yana dariya,sake waiwayawa nayi ban gansu ba na kalli motocin dake gabana,d'aya ce a kunne wata VIBE, "Daga Ina kake ne?" "Ina cikin motar da Kika kurawa Ido matar salihu,matso kusa ki gani" ya fad'a tareda le'ko kansa ta glass din motar,cikeda mamaki na nufi wurin motar,savuwa ce dal Domin ko ledojin kujerar baa cire ba,kallonsa nayi zanyi magana yace "Shhhhhh,kar kice komai,mota dai tawace sauran bayanin Kuma sai munje gida,shigo muje" Shiga nayi na zauna da na bud'e Baki zanyi magana sai yace "shhhhhh" Muna Isa gida ya ajiye motar muka nufi wurin hajiya,ji nayi kaman na zauna a bakin motar Amma na shiga Ina Jin darr a Raina Daga yanda Naga Saleh ya kalli flask din abincin dake palon nasan da matsala,kallon flask din nayi na gansu Babu alamun an taba,bedroom din hajiya ya nufa ya kwankwasa ta fito fuskarta da annuri,tana ganinmu ta hade rai Murmushi yayi yace "Hajiya mota ta ce dama nazo ki saka mata albarka" "Mota?yaushe kayi mota?" Sosa keyarsa yayi yace "Hajiya....yau dai na karbota Amma tun kafin biki na bada kud'inta," "Shine Kuma baka sanarwa kowa ba ko?kaje kayi gaban kanka ka sayi mota,Saleh idan kacemin kanada kud'in sayen mota zan kwace ne ko Zan hanaka?" Sunkuyar da Kai yayi yace "Ba haka bane hajiya,kawai naso na muku surprise ne,Kuma kud'in na sanar Miki da samunsu,sannan na sanar Miki cewa inaso na sayi mota a lokacin" Zama tayi tace "Yayi kyau ai,wadda ta cancanta ta sani ai tasani,jeka Allah ya tsare" ta karash maganar tana kallona Tsayawa mukayi kaman wadanda aka kafe,bansan kaikayin bakin da ya kaini magana ba nace "Hajiya kiyi ha'kuri,wallahi Nima yanzu na sani da ya daukoni daga makaranta,Dan Allah kiyi ha'kuri" Kallo ta watsomin Wanda saida naji fitsari ya kamani,nuna flask din da Saleh ya Kai Mata abinci tayi tace "Wannan shine abincin da Zaki kawowa uwar mijinki ko?saboda nace ki kawomin abinci 12 shine Kika kawomin sassanyar waina,sannan kikayi Miya da tafarnuwa, saboda karatunki yafi iyayenki ko?ko ni ban haifeki ba ai na haifi mijinki,banacin tafarnuwa d'auki abincinki ki koma dashi" Dur'kusawa nayi nace "kiyi ha'kuri hajiya,wallahi ban saka tafarnuwa ba ko kad'an," "Nayi karya to" Cikin sauri nace "Hajiya ba haka nake nufi ba kiyi ha'kuri" "To me kike nufi?nace abincinki da tafarnuwa kincemin Babu,kin karyatani gaban Dana Kuma mijinki,kinyi daidai ai,ku fice ki bani wuri,idan har kinsan Abincin da Zaki dingamin zai dinga batamin rai Kuma ki Kare da kallon tsufana ki cemin makaryaciya to ki barshi banaso" Kwalla naji ta zubomin na goge nace "Hajiya Zan kiyaye,kiyi ha'kuri Kimin afuwa,me Zan dafa Miki gobe?" "Saboda na fad'a kice na Baki wahala saboda bana sonki?ki dafamin duk abinda ranki keso tunda Naga karatunki yafi Mahaifiyar mijinki,tunda bani da girman da Zaki kawomin abinci da kanki saidai ki baiwa mijinki ya kawomin" "ku fitarmin Mana kun tsayamin a ka" Fita mukayi Ina ri'ke da flask d'aya Yana ri'ke da d'aya,ya Usman da uncle Hashim na gani tsaye gefen motar sunata yabawa,gaidasu nayi da kyar sannan na wuce cikin sauri Ina shiga tsakar gida na ajiye flask din a gaba na zuba Masa Ido nayi tagumi,bud'e miyar nayi na dandana,Ni nasan ban saka tafarnuwa a ciki ba Kuka sosai na fara Ina tuna maganganun hajiya meyasa takeson saka iyayena a ko yaushe Maimakon naji Ina bu'katar cin abinci sai naji abincin ma ya fit daga Raina,wainar da na kusa rasa maki Mai yawa a kanta gatanan hajiya ko tabawa batayi ba ta dawomin da ita Palour na koma na hau kujera na kudundune Ina kuka,yanzu haka zanci gaba da rayuwata?me Zan yiwa hajiya ta Soni ko ta Dena min wannan tsanar Qarar wayata naji Ina dubawa Naga mamana,goge fuskata nayi na saita kaina sannan na amsa Kiran,dukda haka Ina magana tace "Mura kike ne naji muryanki haka?" "Eh mama,yau da safe na tashi da ita" "To Allah ya sauke,Kisha magani,ya abokan zaman naki?" Dariya na kakalo nace "Kai mama kaman wasu kishiyoyina?duk suna lafiya na dai shiga mun gaisa dasu" "To yayi kyau,a zauna lafiya sannan cikin mutunci,ya ita Mahaifiyar tasa?" Ambato hajiya da mama tayi kadai yasa naji kwalla na neman zubomin "Itama Tana lafiya Lau,dukkansu alhamdulillah basuda wata matsala dukda Yan uwane" "To Allah ya Kara muku zaman lafiya,ga yayanki yace na gaidake" "Mama ki fad'a Masa fushi nake dashi,tunda yaki zuwa ganina" Dariya mama tayi tace "Wannan ragon?to ai yana Nan saura kiris yayi Kuka saboda Babu ke a gidan,har wani rama yayi a kwana ukunnan" Murmushi nayi inajin kewar gida na kamani nace "To mama kice shima ya fito da Mata kawai a kaishi ya cika Miki gida,ai na kusa zuwa insha Allah" Sallama Saleh yayi na amsa,mama na Jin haka itama tamin sallama ta katse Kiran Gyara zamana nayi ya zauna gefena,hannunshi ya Sanya a kafadata ya Jani jikinsa yace "Kuka kikai ko?" Shiru nayi Domin ba sai na fad'a ba daga ganin fuskata yasan Kuka nayi Shafa bayana yake cikin lallashi yace "Laifina ne da ban sanar dake hajiya Bata son tafarnuwa ba,I'm sorry,nasan hajiya nada fad'a Amma kema duk abinda zai hadaki da ita ki kauce Masa kinji?" Gyad'a Kai nayi Domin na lura ya fara goyon bayan mahaifiyarsa,hawaye ne ya sake gangaromin nace "Baka sanarmin yanayin da zan shigo ba da na shiryawa tararsa tun a waje,kaga fa duk Yan uwanka basa Sona" Dagoni yayi ya d'aura hannunsa a lips Dina yace "Karkice haka star shine,Yan uwana Ni suke Jin haushi saboda na'ki karbar zabin da hajiya ta yimin,Amma a hankali zasu karbeki na maki wannan al'kawarin,Dan yimin dariya Mana nagani" Dariyar ce ta kwacemin yaja kumatuna yace "Ko kefa Yar matata ta kaina,zanje shago yayanki ya kirani yace ya koma gida,yara ne kawai a wurin" Tashi nayi na cire hijabin jikina nace "To saika dawo Allah ya dawo dakai lafiya,Amma Dan Allah ka fita da wannan abincin ko almajirai ne ma bawa kar ya lalace" Flask din ya d'auka ya fita dasu na Masa rakiya,saida ya shiga mota ya nufi gate sannan na koma gida,Kara hutawa nayi na dan lokaci sannan nayi wanka na shirya cikin doguwar rigata Material ne Mai layin black and white,rigar Daidai jikina,tanada gajeren hannu,jollof din macaroni na daura Domin ita zan iya a wannan lokacin Ina Gama girkin na d'auki kayan kwalliya na lullube damuwar fuskata da powder na jira dawowar Saleh ************ *SALEH* D'auko flask din yayi ya nufi shagonsu,cikin girmamawa yaran shagon suka karbi flask din suna sanya Masa alkhairi a sabuwar motarsa da sabuwar amaryar da yayi Bayan ya amsa musu yace "Ga abinci Nan saidai kuyi ha'kuri Babu farantai" Cikin shagon suka shiga suna Masa godiya,kafin minti biyu sun fito da flask empty,wankewa sukayi suka saka Masa a mota Zama yayi cikinsu suna tattaunawa Kan kayan da zasuyi next,sai yamma sosai ya bar wurin a lokacin hankalinsa ya koma Kan bilkisu,tunanin yanda zai bullowa lamarin yakeyi,sake sake yake yanda zai sasanta bilki da hajiya Yana wannan tunanin ya Isa gida,hajiya ya fara zuwa ya gaida  ta,da kyar ta amsa yayi Mata sallama ya nufi gidansa Tunda ya doshi gidan yakejin kamshi na tashi,murmushi yayi na jin Dadi sannan ya kwankwasa kofar,sassanyar Kuma daddad'ar muryarta yaji tace "Ana zuwa" Bud'e kofar tayi fuskarta cikeda fara'a,kallonsa tayi ta bud'e kofar tace "Sannu da zuwa" Shiga yayi yace "Yauwa sannunki star shine,Babu welcome hug?' Gyad'a Kai tayi alamun eh Tana hade hannayenta a bayanta,hugging dinta yayi yace "Kinyi kyau" "Nagode" ta amsa ba tareda yunkurin maida Masa hug din ba,ri'ke hannunta yayi suka shiga  parlour tare Wata ni'ima ce cikin Fallon,sassanyan kamshi ke tashi irin mai kashe jiki,Wanda zakaso kayi bacci, Alwala yayi ya fita sallah sannan ya dawo,dining suka nufa tare ta Gama jera komai,a plate d'aya ta zuba abincin ta Mika masa spoon ta d'auki nata Tare suka fara cin abincin,tura abincin take kaman bataso ta,lura yayi da hakan ya ri'ke hannunta tareda karbar spoon din ya ajiye Da nasa spoon din ya fara Bata a Baki,kin kar'ba tayi ya matsar da kujerarsa dab da ita ya ri'keta a jikinsa ya bude bakinta da hannu d'aya sannan ya tura Mata abincin Ganin da gaske dura yakeso ya Mata ya Sanya ta fara karban abincin da kanta har saida takoshi taji kaman zai dawo "Wallahi na koshi,bazan iya Kara ci ba" ta fad'a Tana ri'ke cikinta" "Sai kin Fadi sunana dake on wayarki" "Um?" Tayi kaman Amsawa yayi da eh ya kura mata "Ina jinki" ya fad'a Yana turo spoon din wurin bakita "My heart desires" ta fad'a a hankali "Ban ji ba" "My heart desire" ta fad'a da karfi ba tareda ta kalleshi ba,kanta a kasa tayi murumushi tareda saka hannu ta goge lips dinta,kallonta yakeyi Yana jin bugun zuciyarsa na canzawa Hannu yakai yana shafa fuskarta Ta sauke idonta,duk soyayyar dake tsakaninta da Saleh bata iya kallonsa Ido cikin Ido,hakan Yana sawa taji nauyinsa sosai sannan idanunsa na nuna Mata abubuwa da dama da ta kasa gane ya akai take fahimtarsu Yanda yanayin wurin ya sauya jikinta ya Bata akwai abinda ke Shirin afkuwa "Look at me Mana,star shine" Dago idonta tayi ta kalleshi,ba tareda ya sake magana ba ya hade bakinsa da nata,dafe kujerar tayi tareda rufe idonta,saidai kunyar amarci ta hanata responding Kissing lips dinta yake ta duk hanyar da zai iya,hannunsa na yawo daga kafadarta zuwa bayanta,duk ya kashe Mata jiki Hannunta taji ya kasa ri'ke kujerar ta maidasu kafadarsa,mintina da dama Yana kissing dinta sannan ya saketa Domin Jan numfashi Kanta ta sunkuyar kasa cikin kunyar da ta zamar Mata ado a wurinsa, hannu ya Sanya ya shafa lips dinta da ya kumbura,kallon hannunta takeyi tana wasa da yatsunta Murmushi yayi yace "Bari naje nayi sallar Isha ko?" Toilet ya nufa har ya shige kanta na kasa,wani ajiyar zuciya ta sauke bayan ya bar wurin fa nufi kicin da kwanuka Yana tafe hanyar masallaci yana tunanin bilkisu,baiyi tunanin zatayi kunya haka ba Domin ance Mata wadanda suka fara zurfi a karatu basa kunya,saidai kunyar ta zamar Mata ado wadda a duk lokacin da ta sunkuyar da kanta cikin kunya Yana kara Mata daraja a idonsa Kafin ya koma ta canza kayanta ta saka na bacci,Riga da dogon wando ta Sanya ta yafa karamin mayafi tana gyara gadonta Da key dinsa ya bude gidan ya rufe sannan ya kashe fitilu ya nufi upstairs,tana Gama gyaran gado ya shiga d'akin Shima canza kayansa yayi zuwa na bacci ya zauna yana kallonta tana karanta kurani a hankali sautinta baya fita sosai,bata d'au lokaci ba ta rufe tayi addu'a sannan ta kalleshi tace "Saida safe" Kallanta yayi ya hade Rai yace "Haka akeyi?" Zare Ido tayi Tana kallonsa Domin bata fahimceshi ba,hannu yasa ya nuna gefensa alamun ta koma can,a hankali ta koma ta kwanta taka abun rufa Hannu takai zata kashe fitila yace "Wait" Kallonsa tayi ta.gefe Taki hannunsa na zare wandon jikinta,ba tareda ta sani ba ta ri'ke hannunsa,daga gira yayi yace "Ba ance Miki baa kwana da miji da wando ba?bakisan yana janyowa mace da mijinta.rashin jituwa ba?naji ance ma yana kashe darajar mace a wurin mijinta" Ya fad'a Yana sake kasa da wandon jikin nata,muryarta kasa kasa tace "Kayi ha'kuri ban saniba" "Bakomai,Bari na cire Miki" "A'a zan cire" ta fad'a Tana kokarin bud'e abin rufar Matso da kansa yayi wuyanta,numfashi y sauke a wuyanta Wanda ya Sanya tsikar jikinta ta tashi, "Idan Kika bud'e kunya zakiji,ki Bari na cire Miki" Ba musu ta barshi har ya zare wandon daga jikinta,sassanyan hannunsa ya Sanya yana shafa cinyarta zuwa cikinta,numfashinta take ri'kewa tana cije bakinta Domin bayanta ke facing dinsa,wuyanta ya fara kissing Yana shafa cikinta a hankali........ Ku Dan raka da wannan na gaji😫 8 Runtse idona nayi na kasa motsi,saukar numfashinsa naji a kumatuna,cikin sanyin murya yace "Bud'e Idonki" 'kin bud'e idona nayi,yaye abin rufar yayi cikin sauri na janyo kafafuwana na hadesu a kirjina,idona a rufe "Bazaki bud'e idon naki ba kenan ko?" Gyad'a Kai nayi alamar eh" "Okay" ya fad'a tareda zagayowa ta kaina ya dawo Yana facing Dina, kissing fuskata ya fara naki bud'e idona Kamo rigata yayi ya cireta ta kaina,hannu nasa na rufe jikina,abubuwa ya fara karantomin da Dole suka da na bud'e idona,sai da ya Gama kidinsa tukun na rufe idona Hannu yasa ya shafi fuskata tareda pecking lips Dina yace "Bud'e idonki Mana ai an Gama" Hannu na saka na sake rufe idona, "Dan yi murmushi Mana" Murmushi nayi ba Dan na shirya ba,tashi yayi sai kuma ya dawo yace "Zancen wandonnan....da Wasa nake Miki kawai Ni nafi son ganinki a haka ne okay?" Tafiya yayi na bishi da kallo,lallai ma mutuminnan,na d'auka da gaske yake Ashe kawai raayinsa ne (so masu cewa sun Dena kwana da wando ba a bakin mero ba😂kiyi baccinki yanda kikeso) Washegari posting gareni,gashi tun 8 ne har 4,da tunanin abincin hajiya na kwana a karshe na yanke shawarar saleh ya siyo Mata kawai,tunda ko nayi ba lallai taci ba Da asuba bayan munyi sallah na hau gyare gyare,Yana dawowa daga masallaci ba sameshi da maganar abincin "Ummmm,maganar abincin hajiya ne,kaga da wuri Zan fita Kuma sai la'asar,ko siyo Mata zakayi?Dan Allah" Tagumi ya zubayana kallona,numfashi ya aje yace "Ban taba Jin kin Kira sunana ba fa,ko dai banida suna ne a wurinki?Kinga da ki dinga cemin kaga ko umm kice Saleh kawai" "To insha Allah,yanzu ya za'ayi da abincin?" "Bakomai Zan siyo Mata d'in,Amma fa banason sayen abinci a waje" "Nima banaso ka dinga siya,break dinmu 12-2 ne,da ace hajiya zatayi ha'kuri da zan iya dawowa a wannan awa biyun na Mata abincin,to Amma bazata kar'ba ba,kaga yanzun ma tace Kar ka sake Kai Mata saidai Ni" Fuskarsa Naga ta canza alamun baiji dadin maganata ba,kallona yayi yace "Hajiya tanada ha'kuri sosai,Baki fahimceta bane sannan Kuma nayi Mata laifi na kin karbar zabinta,Amma indai zakiyi abinda takeso ai zaku zauna lafiya,tunda take ke takeso ki Kai Mata me zai Hana nazo Na daukeki kaman 11:30,ki kawo Mata abincin sai ki koma?duk abinda zai sasanta tsakanina da hajiya shi nakeso" Tofah,a yau Kam na fara fahimtar uwa ta fi Mata,dukda wasu abubuwan gaskiya ne amma banji dadin goyon bayan hajiya da yayi ba "Basa barinmu mu fito sai 12,musamman idan akwai aiki a wurin,Amma Zan duba nagani zance mahaifiyata ba lafiya zasu iya barina na fito" "Hakan yafi Kam,idan Kika Mata abinda takeso sai kiga ta sauko cikin sauki" Tashi nayi na bar masa wurin cikin takaici,breakfast na had'a na gama.duk abunda zanyi,7:00 na shirya zan fita,Saleh na bacci na ajiye masa abincinsa na fita a hankali Domin kar na tasheshi Ina wurin aiki Ina tunanin hajiya,11:00 na nufi wajen supervisor dinmu na sanar Masa mahaifiyata na asbiti yanzunnan, mutumin nada fahimta ya barni nayi signing na fita Saleh na Kira a waya yazo ya d'aukeni,tare muka siyo abincin,da flask a motar,a ciki muka siyo 12 Daidai muna cikin gidan,a waje ya tsaya na shiga da abincin Hajiya na hakimce a Palo ita da sultana suna hira,dur'kusawa nayi na gaidata ta and ba tareda ta kalleni ba A gabanta na ajiye flask din nace "Hajiya ga abincin" Kallona sultana tayi tace "Kai,bakije school bane yau?" "Naje,dawowa nayi dai Amma yanzu Zan koma" "Okay,to Dan Allah idan Kinga rake a hanya ki tahomin dashi,Bari muga me Kika dafa" Fried rice muka siyo da pepper chicken Domin shine baza'a Gane ba,bude abincin sultana tayi ta saka hannu ta dibi kad'an takai bakinta "Um,yayi Dadi kuwa" Plate ta d'auko ta zuba ta zubawa hajiya,daga Mata hannu hajiga tayi alamun ta ajiye,ko a jikinta ta ajiye na hajiya ta fara cin nata Zama nayi na takure har kusan 15mins sannan na tashi nace "Zan koma makaranta" "Saikin dawo" sultana ta fad'a tareda dagamin hannu,hajiya kuwa ko kallo ban isheta ba,wannan Abu Yana bani mamaki,yakinnan akan sultana ake yinsa Amma yarinyar tafi kowa bani muhimmanci a gidan,jumana har mantawa nake da ita a gidan Part Dina na nufa na kwanta na huta,girki na ma Saleh,sai 1 sannan na koma school Sai dare ya shigomin da flask din abincin,Banda Wanda sultana taci Babu abinda aka sake diba a abincin Kallonsa nayi nace "yanzu ya za'ayi da wannan?" "Ajiyeshi kawai" Ya fad'a tareda kwanciya akan kujera,a fridge na saka na dawo na zauna nace "Gobe weekend,me ,an dafawa hajiya Wanda takeso?" "Kiyi Mata tuwo,nasan zataci" "Ka tabbata?" Tashi yayi ya zauna yace "Haba....yanzu gobe Saturday ki fara tunanin yanda Zaki kula da mijinki kina ta abinci?zo Nan ki zauna,hajiya idan taga dama zataci abinci,gobe Nima sai 11 Zan fita Kinga zamu huta dukkanmu" Zama nayi a gefensa ya hadani da jikinsa,wani film muka fara kallo da bansan sunansa ba,a haka muka zauna har na fara bacci,daukana yayi a hannunsa ya kaini d'aki ya lullubeni Ina ji ya fita ya koma yaci gaba da kallonsa Nayi bacci sosai na huta,sai 10 na farka,Ina tashi na had'a breakfast da sauri sauri sannan na daura tuwon hajiya Tuwon alkama nayi da miyar Kuka,Domin shi Saleh yacemin tana so,zubawa nayi na nufi bangaren hajiya Jumana na gani kwance Kan kujera sultana na zaune a wurin kafarta,cikin damuwa hajiya tace "Wannan 'barin y fara damuna wallahi,shi wannan asbitin da kukaje me sukace Miki?" "Sun bani magani sannan sunce idan na Sami want akwai allura da za'a dinga min duk three weeks" "To Allah ya Kara sauki" "Hajiya Ina wuni" "Lafiya Lau kin tashi lafiya?" Ji nayi tamkar a mafarki,yau ni hajiya ta amsawa gaisuwa harda 'kari?amsa Mata nayi na gaida su jumana nace "Ya jikin?Allah ya Kara sauki" "Ameen,yanzu Yaya jumana wannan barin bazai kawo matsala ba?na hud'u fa kenan ko?" "Sunce zai kawo to ya zanyi?ai ba yina bane,yunwa ma nakeji" Ajiye flask din nayi nace "Hajiya ga abincin" Sai Yanzu hajiya ta lura da Ni a wurin,cikin Isa tacemin "Mene a ciki" A durkushen da nake na bud'e flask din nace "Tuwo ne" Kallon jumana tayi tace "Zakici tuwo?" "Zanci" Kicin hajiya ta nunamin tace na d'auko plate da cokali,plate uku na d'auko na zuba musu na mika musu,yau dai hajiya taci abincina,Dadi kaman nayi kwalla,tuwon da suka rage ma jumana tace a ajiye Mata zataci anjima Na Dan jima a dakin dukda ba wani Abu nace ba,sunata hirarsu akan jumana,Ni kaina na tausaya mata,aurenta shekara biyu kenan Amma duk lokacin da tayi ciki saidai ya zube, addu'a nayi a zuciyata Allah karya hadani da wannan wuyar Daga ranar hajiya Bata sake cin abincina ba,karshe ma tace na Dena dafawa bataso A haka dai naci gaba da rayuwa a gidan,idan abin hajiya ya motsa ta huce a kaina,kewar Yan uwana da iyayena ta kamani sosai,musamman duk ranar lahadi da yayan hajiya ke haduwa a part dinta ayi Hira,anan nakejin kaman na haka Rami na binne kaina,a wannan lokacin nake ganin amfanin auren Dan uwa ko da ace Babu soyayya a tsakaninku,wata biyu da aurenmu Amma zaman gidan duk ya isheni,Saleh Kuma saidai yace nayi ha'kuri ko.maganar ma.baiso na dinga yi Duk na rame hakan yasa Saleh yace zai kaini Naga gida,ranar tun asuba na kasa komawa zumudi duk ya cikani 9 na safe na Gama shirina, takura Masa nayi har ya gaji ya kaini a lokacin Ko da Mika Isa gida coming sauri na shige na barshi a waje,sallama na doka na fad'a Palo,jabir da baba na samu suna breakfast Cike da fara'a suka juyo gareni Saleh yace "Kanwata kece?" "Nice mana Yaya,baba barka da safiya"na gaida baba,amsawa yayi yace "Ya mutan gidan?" "Kowa lafiya lau" jabir na kalla nace "Ina mama?" "Inaga ta shige wanka,wannan zuwa haka Babu alert?Ina saleh din Kuma?" "Yana ajiyeni ya juya yace sai anjima zai zo" Zama nayi muka fara Hira dasu har mama ta fito,ficewa sukayi suka barni da mama,muna gaisawa tace "Bakida lafiya ne?duk kin zuge" "Lafiyata kalau mama,kawai zirga zirga ce da aikace aikace" "To ki rage aikace aikacennan da kikeyi,ki dinga samu kina hutawa" "To mama Zan rage,ya su adda?anjima Zan shiga na gaidasu" nayi saurin canza hirar,dukda inada abubuwa da dama a raina da nakeso na fitar Amma ba yanzu ba,wata biyu da aurena na kawo ma mama matsalata zata shiga damuwa sosai Tambayoyi Mama ta dingamin akan hajiya da su jumana,cikin dabara nake amsa Mata har ta gamsu banida wata matsala,sai dare Saleh yazo ya d'aukeni ji nake kaman nayi Kuka,har zazzabi ne ya saukarmin a hanya saboda damuwar me zai faru gobe Washegari na Gama aikace aikace na na shige gidan sultana,tazomin lokuta da dama Amma ni bnje Mata ba,yau na samu lokaci y kmata naje Sallama nakeyi amma shiru,dubawa nayi Naga Babu motar Usman alamun ya fita sannan na koma na sake sallama Amsawa sultana tayi ta fito daga d'aki da abin pregnancy test a hannunta,zama tayi tana juya abin a hannunta ta mikomin tace "Wai ya are duba wannan abun ne?na kasa ganewa" Kar'ba nayi na kalla,murmushi ne ya sauka a fuskata nace "Congrats, positive ya nuna" "Akwai kenan?" "Eh" "Oh God, ciki a wannan lokacin Dan Allah mutum ko hutawa bai Gama yi ba?tun last week nakeji jikina ba Dadi shine na karbo a wurin jumana na gwada,Allah ban shirya ciki yanzu ba sai irin nayi 6months haka" Mika Mata abin nayi nace "To ba saiki gode Allah ba?Idan kin haihu ai hutunki ne,sai kiga kin d'au lokaci Baki sake ba" "Allah yasa to,kefa?ko hutawa kikeyi" "A'a jira dai nakeyi nima,Everytime Ni a shirye nake" "U'um fa,nasan irinku masu karatunnan,yawanci kunfiso sai kin Gama ku haihu,ba saura shekara guda ba?gara ma fa ki huta abinki" "Nifa...." "Kinga banida fa da matsala da wannan,ko nice nake karatu wallahi bazan haihu ba saina Gama,yanzun ma idan Allah ya kawomin wanna sai na shekara kaman 7 kafin na Kuma wani,q tsarina yara biyu tall.sun isheni,ki Bari ki Gama karatunki tukun ki fara Tara yara" Dariya na Mata kawai nace "to" amma nikam bazan iya jira har na Kare karatu ba,ina matukar so na ganni da baby a hannu,dukda wannan magance da muka yita mu biyu,bansan cewa zata zama sanadin tasowar gagarumar matsala gareni a wannan gida ba ..... 9 Ko da na koma d'aki zama nayi na fara lissafin ciki,idan na samu yanzu yaushe Zan haihu?me Zan fara Haifa?wasu irin Kaya ya kamata na saya na baby?inata lissaafina har Saleh ya dawo Turare na fesa na goge fuskata na fita Dan tsakar gidanmu Ina tsumayin shigowarsa,da ace gidanmu ne mu biyu da fita zanyi na taro abuna,to Amma Nan babu wannan damar Tattare skirt Dina nayi kaman wadda zatayi gudu,Yana shigowa na Dane bayansa nace "Booboo!!" Cikin sauri ya saki jakar hannunsa ya rikeni ta baya,dariya yayi yace "Boo ko nauyin jikinki bakyaji?idan Kika Fadi fa?" Cakulkuli na masa a gefen kunne nace "Ai nasan zaka tareni,sannu da zuwa ya aiki?" D'aki muka nufa yayi yayi na sauka na'ki,saida ya fara juyi Dani a baya naji kaina na juyawa tukun nace ya tsaya na sauka Zama mukayi Kan kujera yace "To ya kike?" "Lafiya Lau nake, ya aiki?" "Alhamdulillah,me Kika dafa ne yunwa nakeji" Tashi nayi nace "Bari na d'auko abincin kafinnan ka rage kayan jikinka" Amsawa yayi da to ya nufi d'aki na nufi kitchen,a dining table na shirya komai na zauna a palour Ina jiran fitowarsa,fitowa yayi da jallabiya ya nufi dining din ba tareda jirana ba, kafin naje har ya zuba abincin ya fara ci Cikin murmushi nace "Da alama kana jin yunwa sosai" Dagowa yayi ya kalleni yace "Bazaki ci ba" Shafa cikina nayi nace "nope,abincin baya Raina yanzu ne" Hannuna ya kalla dake Kan cikina ya kalleni,wani murmushi Naga ya sauke ya matso kusa dani yace "Akwai abinda ake Shirin fadamin ne?Ni dama Naga yau walwalarki ta daban ce,to Yaya?" Ya kalli cikina ya kashe idonsa daya,tagumi nayi nace "Wai ta Yaya ka iya kashe Ido ni ban iya ba?" "Ai inaga ma a wurinki na koya,bakice komai ba,tun dazu Kuma hannunki na belenki" Dariya nayi nace "Kai booboo,ba ciki ne Dani ba,Amma kasan me?sultana tanada" "Ikon Allah,saura ke" D'aura kaina nayi a dining table din nace "To sai ka Kara kwazo mu haihu tare da sultana" "Karki damu,yau zamu kwana muna ibada,Babu bacci har sai kinji durum" "Haka nakeson ji my booboo" na fada tareda petting bayansa A hakan har aka Kara diban kusan wata guda,inata zuba Ido naji alamun ciki Amma shiru,nayi amfani da pt lokuta da dama har dai Saleh ya gaji yace na Bari na fiye gaggawa,aure wata uku na damu kaina,nidai ban damu ba kawai nasan d'oki ne kawai Ina zaune mun fara hutu yau,Wanda daga wannan hutun Kuma Zan shiga shekarar karshe ta karatuna Ina kwance Ina Danna wayata naji bugun gida,ba tareda na tambayi waye ba na bud'e,sultana na gani tsaye idanunta sunyi ja tana ta goge hancinta alamun Kuka Tasha ko take Kan Sha Cike da damuwa na bud'e gidan nace "Subhanallah,sultana lafiya?" Gaba tayi ta barni a tsaye,binta nayi a baya na sameta ta nad'e kafafu kan kujerata Tana cigaba da shesshekar kuka Zama nayi na dafata cike da fargabar nace "Meya faru kike Kuka haka?rasuwa akayi?" "Bakin cikin Namiji ai d'aya yake da rasuwar,haba bilki meyasa ya Usman bazai fahimceni ba,meyasa maza basuda adalci,nifa tunda na samu cikinnan yakemin wani gani gani,da nace banason yin girki abincin hajiya nakeso kullum Yana karbowa,Amma nace Zan yo girki me yakeso wai Kar na bawa kaina wahala,ko Ina ruwansa da wahalata?sannan Kuma nace banason turarensa shine sai ya fesa a daki ya rufe d'akin,Kuma ni yanzu banason ganin fuskarsa nace mu raba room wai bazai iya ba" Nidai zuba Mata ido nayi na rasa Ina ma.maganarta ta dosa,can nace "Amma kuwa bai kyauta ba" Ai kaman na kunnata ta dinga zubo laifukan ya Usman Wanda idan aka duba da kyau laifinta ne,Amma Abu na ciki baza a ce laifinta bane,hakan da take ma birgeni takeyi sosai,ji nake inama nice Ina tunanin yanda takeji a ranta,saida ta Gama min bayani Tass sannan nace "Karki damu sultana,Zan Ma ya usman magana Kuma zai fahimta kinji?kiyi ha'kuri kinsan mazannan sai a hankali" Cune fuskarta tayi tace "Ni sunansa ma tayarmin da zuciya yakeyi,kinada abin za'ki?" Baba rabo da Dan abun Zaki haka na d'auko Mata Dan cookies din da Saleh ya siyomin da chewing gum da na siyo,kaf kwalin cookies din ta cinye ta saka cingam din a bakinta Nidai binta nake da Ido Domin ita kadai sai Taki takeyi,wannan za'ayi masifaffen ciki,zobo na d'auko mata Nan ta sha ta hau Santi Tafi minti biyar tana zancen zobonnan,saida tasha jarka d'aya da rabi sai Kuma bacci Sai azahar ta farka tayi sallah ta sake komawa,tunda nasan ba girki zatayi ba ban tasheta ba,Ina shirya abincin rana naji Usman na kwankwasa gidana,hijab nasa na bud'e muka gaisa Kasa kasa yayi magana yace "Tana ciki ko?" "Eh bacci takeyi ma" Sauke ajiyar zuciya yayi yace "Alhamdulillah,dama ba wani bacci takeyi ba a gida kwana take tana mita,kema ta maki ko?" Dariya nayi nace "Eh tayi,sai kayi ha'kuri da ita ai kasan" Dafe kansa yayi yace "Ai dama sultee sai ha'kuri,abunne yayi yawa,ya zatace zata koma wurin hajiya?wai batason ganina" "Eh to haka zaka ha'kuri har ta dawo San ganin naka,ko dai Bata koma wurin hajiya ba ka Bata space haka da kanta zata sauko" "To Allah ya rabasu lafiya dai a huta,nagode ko?" "Um bakomai" Tafiya yayi na koma,Ina shiga naji muryar sultana tace "Ya Usman ne ko?" Dafe kirji nayi a tsorace nace "Kai,wallahi na d'auka bacci kike har kin tsoratani" Tsaki taja tace "Idan ma karata ya kawo Miki can ku karata,indai bazamu Raba daki ba daga Nan wurin hajiya nayi" "A'a Dole yayi abinda kikeso ai,hukuma saida lallashi" Shiru naji alamun ta koma baccinta,kitchen na koma naci gaba da hada abincina Tana tashi tace min zobo,abinci kad'an taci Tasha zobo sai dare na samu ta koma gida,shima da kyar harda kukanta wai bana kaunarta Daga Nan na d'au dawainiya da sultana,kullum sai Tasha zobonnan,kafin ya Kare ma na hada wani Domin idan tace na Bata nace aa sai Nasha mita Ta zama wata hulk,daga Ni har mijin nata ba Wanda ta Bari,Ana Dan tabota kad'an sai masifa,indai ta tambayi Abu baa Bata ba to ta dinga Kiran bamu sonta kenan har sai tayi kuka tayi bacci A haka har hutuna ya Kare na koma school,cikin sultana a lokacin watansa 6,Babu abinda ya ragu sai ma karuwa,kowa Allah Allah yake ta haihu a huta Yau lahadi muna zaune Ana meeting a palon hajiya,yau taron yafi na kullum domin yayan hajiya Mata suna Nan Hira aka fara Kan sultana da cikinta sunata lissafin haihuwa,nidai Ina rakabe a gefe banaso ma su sanyani cikin hirarsu Domin Bata karewa da dad'i "Ke Kuma bilkisu ko alamun cikin Babu,ko kina hutu ne?" Tunda naji muryar anty maimu gabana ya fad'i,bud'e Baki nayi Domin na Mata reply sultana tace "To kuwa a wani dalili bazata huta ba?shekarar karshe take idan ta Gama ba saita.haihu ba ta huta?Ni na Bata shawara ma karta haihu saita Kare karatunta,ko Ni da nasan Cikin zamani zanyi Allah planning zanyi na shekara guda tukun na haihu" Ji nayi tamkar sultana ta sakarmin bomb a tsakiyar kaina,Domin wani irin kallo su hajiya suka watsomin,shima Saleh kallona yakeyi kallon tuhuma D'akin yayi shiru kamar ance nayi kisan Kai,hajiya dawo da hankalinta kaina tayi tace "Wani irin yahudanci nakeji a Nan?Kai Saleh Kaine ka Bata damar yin wannan haramtaccen Abu?" Kallona Saleh yayi cikin rashin Dadi ya girgiza Kai yace "Hajiya bansan da wannan maganar ba sai yanzu" "Bilkisu?me hakan ke nufi kenan?kinje kin tsaida haihuwa ba tareda iznin mijinki ba?Akan karatunki na banza da wofi?mu muna nema Ido rufe Allah bai Bamu ba Amma ke kafin ma kisan matsayinki Zaki dakatar?bakida hankali ne?" Jumana ta fad'a cikin fad'a "Banyi planning ba wallahi,nasan munyi maganar da sultana Amma....." "Amma me?me zakice Mana?sultana karya take kenan kome?sultana zata zauna ta tsara zance ne ta fad'a?me ma hakan ke nufi?wato karatunki yafi zuriarki ko?Baki duba mijinki ba da yake burin samun zuri'a,Baki duba iyayenki dake jiran jikoki ba,Akan bokon banza da Zaki barta a duniya zakije ki lalata mahaifarki ko?kune kuke wayar da kan Mata Kar suyi planning kafin su haihu Yana Hana haihuwa,sai gashi ke da kike cikin field din kin aikata hakan,ai dama said muka fad'a ma Saleh,yasan irin matar da zai auro ai ga irinta nan" anty maimu ta fad'a ba tareda ta Bari an tari numfashinta ba,gaba d'aya jikina yayi sanyi,muryata tuni ta fara rawa a hankali nace "Wallahi Yaya maimu banyi planning ba,na rantse muku da Allah Babu abinda nayi,gashinan ku tambayeshi idan nay wani abun ai da saninsa" "To wa ya sani ko tun kafin a kawoki kikayi?shi Saleh zai bi diddiginki ne?" "Wallahi...." "Banason rantse rantse a wajennan,kije ko ma me kikayi ki cire ko ki Dena,bazaki kawo Mana yahudanci gidannan ba,dukka yayana Babu jahilai,kowacce da karatunta Kuma gasunan suna haihuwarsu,shekara guda Nan gaba Ina son ganin jikana" "Hajiya inaga an samu misunderstanding,nifa cewa nayi nace tayi ba wai tayi ba,Kuma tunda tace batay ba....." "Sultana bana son sake jin muryarki a wajennan,Kai Kuma Saleh kaji kunya da baka da iko da gidanka,idan ma da Kai Kuka hada ba'ki shekara guda,inason ganin jikana daga gareka,ku barmin d'aki" Ran Saleh ya baci sosai,jikina gaba daya rawa yakeyi na rasa inda zan saka kaina,muna fita sultana ta biyoni a baya Cikeda damuwa ta ri'ke hannuna tace "Wallahi bilki banyi hakan da wata manufa ba,bansan zasu d'auki abun da zafi ba,Amma Zan fahimtar dasu,kiyi ha'kuri Dan Allah" Murmushi nayi dakyar nace "Bakomai sultana banga laifinki ba Nima" Gaba nayi na barta ganin Saleh har ya shige gida,Ina shiga na sameshi ya tsaya jikin katanga ya hade hannayensa kansa a sama,daga Nan nasan akwai matsala Kallona yayi yace "Bilkisu,inaso ki fadamin gaskiya,duk abinda Kika fadamin Zan fahimceki Amma karkimin karya,menene ainahin abinda sultana ta fad'a?kinyi planning a bayan idona ko Kuma maganar kawai kukayi kina Shirin yi ba tareda sanina ba?" 10 D'auke kaina nayi daga gareshi nace "Idan baka amince Dani bane kaima mu tafi asbiti,iya zama na dakai ya kamata ace kasan abinda Zan iya da Wanda bazan iya ba,ko baka sani ba a matsayinka na mijina nauyinka ne ka goyi bayana a gaban danginka ko ma me zamuyi a bayan idonsu mayi" "Amma yanda suke nunamin rashin soyayya kaima a gabansu baka nuna ka damu Dani,ko Ni na bud'e Baki nace nayi planning zaka yarda?Kai kasan yanda Allah ya jarabceni da son 'ya'ya,da akwai yanda zanyi na d'auko ciki na saka a jikina wallahi ko wane Hali ne zanyi,Amma Allah yayi time Dina baiyi ba,muje asbiti kawai a dubani ka kauda zarginka,da na Yan uwanka Nima na samu sukuni" Takunsa naji ya matso kusa Dani,kasa juyawa nayi na kalli fuskarsa Domin Raina a bace yake sosai,cikin lallashi yace "Ba wai ban yarda dake bane boo, kawai maganar ce tazo kin bazata" "Indai zaka dinga d'aukan maganar Yan uwanka haka wataran kashe Mana aure zasuyi,nasan bakaso na fad'a Amma boo-boo Yan uwanka basa Sona hka ma mahaifiyarka,sau d'aya ka amince da hakan ka nuna gskiya na fad'a,kayi backing Dina up a gabansu,idan kana barina da wayona a cikinsu wataran bazan tsira ba,inaga ma rashin kwanciyar hankali ne ya hanani samun ciki" Hugging Dina yayi ta baya yace "Sorry dear,ya wuce kiyi ha'kuri" "Bai wuce ba boo-boo,shekara d'aya hajiyarka ta bamu saboda bata aminta Dani ba,muje asbiti Dan Allah ko ma zo Mata da result ba cewa Babu planning a jikina" Juyoni yayi ya kalli cikin idona yace "A'a boo,Babu inda zamuje,na yarda dake Ni kadai na Isa na zama shaida,wata shida kawai bai Isa ace mun fara yawon asbiti ba,nasani lafiyarki kalau lokaci be baiyi ba,sannan wannan shafaffen cikin naki dama ai bazai d'auki baby ba saboda haka ki dage da cin abinci har babynmu ya samu space ya zauna" Murmushi nayi na jin dad'i,hannuna ya ri'ke muka shiga d'aki take ya canza hirar Bayan Saleh ya fita masallaci da magrib sai ga sultana,tun kafin ta shigo Palo tace "Dan Allah bilki kiyi ha'kuri,wallahi bansan haka zai ja maki matsala ba da na kame bakina,naso na fahimtar dasu Amma sun kasa fahimta,kiyi ha'kuri kinji?INSHA Allah Zaki Basu kunya duka,dukda Yan uwana ne bana son abinda suke maki wallahi" Murmushi nayi nace "Bakomai sultana,nasan ba da niyya kikayi ba,Kuma wallahi ya wuce a wurina.kawai...." "Daga yanzu Zan iya bakina ba sai kin fadamin ba,duk abinda ya gudana tsakaninmu iya Nan zai tsaya na maki al'kawari" Murmushi nayi Amma zuciyata ta fara waswasi akan sultana,a zamana na San labarin soyayyar sultana da Saleh Sultana cousin din Saleh ce,mahaifiyarta da hajiya uwa d'aya uba d'aya tun daga yaye aka kawota wajen hajiya,tunda tazo tafi yarda da Saleh akan kowa,hatta hajiyar ma,hakan yasa ta taso cikin shakuwa da Saleh tamkar yayanta Lokacin da ta fara girma hajiya ta fara tsokanarta da amaryar saleh,tun Tana Kuka har ta fara sabawa,a haka Kuma sai ta fara Jin soyayyarsa na shigarta,ta boye Bata fad'a ba Ashe hajiya ta lura da hakan Shi Kuma gogan Yana can Yana rainona,Nima na taso ya furta Yana Sona,Mahaifiyar Saleh da ta sultana sukayi magana ba tareda saninsa ba Akan an bashi sultana,baa tashi sanar Masa ba saida suka fara shirin fidda ranar aure,da farko ya amince said yaga bazai iya ha'kura Dani ba sannan ya bijirewa umarninsu Bai bani labarin dramar da akayi Kan haka ba yace dai ran kowa ya baci Amma da maza suka shiga lamarin Dole su hajiya suka hkura,sultana har ciwo tayi daga baya hajiya tace ta hadata da Usman saboda ran mahaifiyarta ya baci,babu musu ta amince Hakan yasa na fara tunanin da gayya tamin abinda tayimin tunda ta Dade da soyayyar mijina a ranta,Kuma nasan har yanzu akwai birbishin wannan soyayyar ko da ace wani sashi ya ragu Hira muka fara kaman Babu abinda ya faru,kwata kwata ban d'auki maganar hajiya a matsayin threat ba,idan banyi cikin a shekara guda ba ta Isa ta cusamin shi?aka ce idan fitsari vanza ne kaza ma tayi,idan cikin Kai kake yiwa kanka ita ma tayiwa kanta Mana Har Saleh ya dawo Bata tafi ba,shima mijinta shigowa yayi muka d'aura hirar dashi,a wurina sukaci abincin dare ta kar'bi zobonta ta tafi Sati biyu tsakani Ina tsakar gida Ina wanki,vest ce a jikina da short kaina Babu dankwali naji bugun gidana Wanke hannuna nayi nace "Sultana ce?" Shiru naji nayi murmushi tareda girgiza Kai,ita dai sultana idan miskilancin nata ya juyo ba dama,bud'e kofar nayi na kame a wurin Hajiya na gani a tsaye a kofar,tsayawa tayi itama Tana karemin kallo na rasa Ina zan saka kaina,ji nayi kaman tsirara nake a gabanta,ban San Ina ri'ke da kofar ba saida tace "Juyawa zanyi kenan tunda Baki da niyyar bude kofar?" Matsawa nayi cikeda kunya nace "Sannu da zuwa" Bata amsamin ba ta shige cikin Palo,gashi ba fitowa nayi da zani ba,haka na shige d'akin na ratsa ta bayan kujera na shiga d'aki na d'auko zani da hijab Dur'kusawa nayi har kasa na gaidata ta amsamin ciki ciki Yayime yayime na fara Ina ajiye Mata,sannan na Kama wuri na zauna nace "Bai dade da fita ba ko na Kira Miki shi?" Bata amsamin ba ta d'auki wayarta ta Kira saleh tace "Idan bakayi nisa ba kazo Ina gidanka" Tana ajiye wayar tace "Tashi kije kiyi aikinki" Cigaba nayi da wankina ina tunanin me ya kawo matarnan? Yana shigowa yace "Hajiya na ciki?" Na amsa Masa da eh,bin bayansa nayi muka zauna a palon dukkanmu a kasa,karewa palon kallo hajiya tayi sannan tace "Part Dina ne mukayi magana da Hisham za'a fara gyaransa,tiles din d'akina sun tsufa,carpet din ya lalace,sannan toilet Dina ya samu matsala,sannan ga hihuwar sultana ta taho,so,na dawo Nan ne kafin a karasa aikin part din nawa na koma" Hasbunallahu wa niimal wakil na fara maimaitawa a Raina,aikuwa Ina cikin gagarumar matsala,hajiya a gidana? Shiru mukayi dukkanmu,Ina Jin idonsa a kaina Ni kuwa ko d'aga kaina banyi ba,numfashi hajiya ta.sauke tace "Au,ajiye Mahaifiyar taka ma a gida sai ka nemi iznin matarka?" Cikin sauri yace "Ba haka bane hajiya,sama kikeso ki zauna ko kasa?" Kallona tayi tace "Inda matarka ta zabarmin" Kallonsu nayi dukkansu na rasa Ina zance,a kaida a kasa ya dace ta zauna,Amma idan nace ta zauna a kasa zatace na wulakantata,hadiyar yawun da ya tsayamin nayi nace "Hajiya ai Nan ma.gidanki ne,ki zabi duk inda kikeso ki zauna,Amma Ina ganin saman zaifi muna tare dake" Tashi tayi tace "Muje nagani" Gaba tayi na bita a baya,duk kaina ya shiga duhu,ga d'akina ga na *uwar mijina* (by janaf😉), wani irin zama za'ayi ne hakan?yanzu Dan wasan palonnan Babu shi,idan na ma mijina kwalliya saidai na kunshe a d'aki Key d'in jikin kofar na murd'a na bud'e d'akin,fes dashi Domin duk bayan kwana biyu sai na share,bedsheet ne dai babu a gadon Kallon d'akin takeyi sama da kasa,a Raina nace 'hajiya ko master's bedroom Zan kaiki ne?' Cikin girmamawa na bud'e wardrobe din d'akin na ciro bedsheet,cherry ne a jikin bedsheet din duk kalarsa ja,sai ganyen cherry din green kad'an kad'an,har na fara shinfidawa tace "A'a,karki sakamin Jan zanin gado" "To hajiya" na fad'a tareda komawa dakinmu na d'auko  sea green bedsheet Dina da nayi niyyar shinfidawa mijina😒,kujerar mudubi na janyo Mata nace "Hajiya Ki zauna anan" Zama tayi tace "Yanzu shi wannan d'aki da shedanu aka barwa?" Shiru nayi mata,mutane da baa iya musu,da ace empty aka bar d'akin da cewa zatayi an kawoni a tsiyace Saida na Gama gyara gadon sannan ta fita,kafin ta fita tace "Kuma karku rufemin kofa kaman Kuna zaune da barayi,banaso nazo Ina bugu" ta koma part dinta,abubuwan da suka dace na Sanya a bandaki da Kan mudubinta na sakawa d'akin turare na rufe Daga ni har Saleh shiru kawai mukayi Amma kowa da magana a ransa,ga weekend gashi hajiya zata rage mana Jin Dadi,gashi mun kasa sakewa bamusan a wani yanayi zata diro ba tunda ba sanar mana tayi ba Abincin Rana nayi na ajiye Mata,na saka kayana masu mutunci saboda tsaro,lace ne Riga da zani Wurin 5pm muna zaune muna kallo kaina a kafadarsa naji motsin kofa,cikin sauri na matsa gefe tareda waiwaye,karamin tsaki yayi yace "Iska ce fa,hajiya fa inaga sai gobe zata dawo Domin Hisham ya fadamin sai gobe za'a fara aikin" "Okay" na fad'a tareda kwantar da kaina a cinyarsa,zip din gaban rigata ya ri'ke Yana wasa dashi ya bude ya rufe,kallonsa nayi nace "Karfa ka lalatamin zip" Kama zip din yayi da harshensa ya zugeshi tareda kissing Dina a wuya,lumshe ido nayi na gyara kwanciyata na had'a bayana da cikinsa Hannu nakai Domin Sosa bayana ya ri'ke hannun yace "Ina ke Miki kaikayi" Nunawa nayi tareda rub da ciki nace "Lace dinne ke min kaikayi" Zuge zip din bayan yayi Yana sosamin cikin nutsuwa Yana min tausa,gyangyadi na fara naji Yana was da bra hook Dina "U'um" na fad'a tareda d'aura hannunsa inda zai sosamin,sassanyan lebensa naji a bayana kissing Dina ya farayi hannunsa na shafa bayana Cikin sassanyar murya n d'ago kaina nace "Boo-boo yamma..." Amfani yayi da wannan damar ya hade lips dinsa da nawa,zazzafan making out muka fara kafin muje bugun kofa a fusace A tsorace na matsa daga jikin Saleh ina kici kicin zuge zip din rigata,wani irin kallo hajiya ke watsomun da saida naji kaman na lume Kan kujerar da nake...... Hajjaju ke fa kika kawo kanki😏 11 Tunda na kalli hajiya sau d'aya ban sake juyawa ba,zamewa nayi daga Kan kujerar kaina a kasa,kici kici nake na zuge zip Amma Dan sharri yaki zugewa Tsabar tashin ta Ido na Namiji naji hannunsa a bayana zai rufemin zip din,bansan lokacin da na watsa masa wani kallo ba Jingina nayi jikin kujera hajiya ta zauna ta kalli Saleh tace "Jeka daukomin kayana" Fita yayi Yana waiwayena,Ina nan inda nake Ina jiran me hajiya zata ce,Amma ga mamakina sai tayi shiru ta bawa iska ajiyata Sum sum na tashi na koma d'aki na gyara rigar jikina na dauro dankwalina na sauko Abinci na d'auko ma hajiya tayi kaman Bata ganshi ba,tv na kunna na zauna a gefe inata sake sake har Saleh ya dawo Jan akwatin da ya d'auko yayi ya nufi hanyar bene,kiransa hajiya tayi tace "Ajiyemin a dakunan dake nan kasa" Tsayawa yayi Yana kallonta,har saida tace "A hakan Zan zauna a d'aki dake kusa daku?" Ta fad'a Tana nunamu Sosa keya yayi ya dawo da akwatin ya kaishi bedroom din dake kasa,tashi nayi na gyara d'akin na d'auko abubuwan da na sanya mata a sama na dawo dasu,tunani na fara da Babu gado a kasan ya zatayi? Ba tareda na zauna ba na hau Shirin abincin dare,daga Ni har Saleh bamu damu da cin abincin dare ba,Amma na Isa na bar gyatuma da Yunwa? 7:30 na Gama komai,zuba tuwon nayi na fita na kaiwa sultana na Santa da son tuwo Kaman yanda ta Saba ko girkin Rana batayi ba,tuwon ta fara ci tace "Dan usmanu ya ce min za'a yiwa hajiya gyara tana gidanki ko?" "Um" na fada Domin banason magana irin wannan da sultana,haka Nan banajin sakewa dukda tana bani goyon bayanta "Zanje na daddagota ne ta dawo Nan,Banda abin hajiya ita da ta kayyade muku lokacin yin ciki Kuma zata zo ta sakaku a gaba?Ina laifin tazo Nan tunda nayi nauyi Kuma dukkanmu yayanta ne zata fi sakewa,balle ma Ni ba ruwana abinda naso zanyi a gaban hajiya,Amma ke bazaki iya ba" Dariya kawai naji ta tasomin da na tuna abinda ya faru dazu,gyaran murya nayi na waske Ashe ta lura "Me ya faru?" "Me Kika ga" "Kin fini sani,Allah akwai abinda ya faru,hajiya taga wani Abu ko?" Fad'a Mata abinda ya faru nayi ta dinga dariya harda tintsirewa tace "Allah sarki hajjaju karki taso Mata da tsohon gwaurancinta,zanzo na d'auke miki ita ai ko Kya sake" Cikin sauri nace "A'a Dan Allah ki barta,tunda tazo tana son karki ma fara,ki barni mu rabu lafiya karki jamin magana" "To Naji,Amma dai nasan zamanki da hajiya bazaiyi Dadi ba" "Maybe Kuma mu samu maslaha ba" "Hm bakisan wace hajiya ba" ta fad'a Tana girgiza Kai "ki gode Allah Baki had'u da mamata ba ma" Murmushi kawai na mata na tashi nayi Mata sallama na koma gidana,ban samu hajiya a Palo ba saboda haka na shiga kitchen na fara wanke wanke Bayan na gama muka zauna a palo muna kallo,Yana kujerarsa daban Ina kujera daban,Amma just muke kaman mu manne da juna,dukda hajiya Bata le'ko daga dakinta ba amma mun kasa sakewa 9:30 Daidai na tashi na leka na ma hajiya saida safe,Tana zaune kan darduma tana Jan carbi,hannu kawai ta dagamin na fice na nufi sama Kafin Saleh ya hawo na cire kayana na Sanya na bacci,tunda na lura mijina na son ganin kafafuna a waje to duk kayan da zan saka Ina tabbatar da bayyanar dasu Riga na Sanya armless Mai santsi,tsayin rigar ya wuce gwiwata,saidai tsagar dake tsakiyar kafar hagu har kusan kugu Kaina Babu kitso na saka ribbon nayi packing gashina a can keyata,na shafeshi da Mai da turare,sai sheki yake Yana kamshi Ina shafa turaren jiki Saleh ya shigo,dur'kusawa yayi gabana yace "Umm wow" "A cikin scale na 1_10 a wanne zaka sakani" na fad'a Ina dafa kafadarsa tareda sunkuya was saitin fuskarsa "Zan sakaki a....4,Dan wannan ba'indiyar fa ta had'u" Hade Raina nayi cikin wasa nace "To ai gaka ga tv,sai kaje Yar indiyan ta baka soyayya" Tashi nayi Ina rangwada na koma dayan gefen gadon na daura kafata d'aya Kan d'aya,har ga Allah Ina kishi da wannan mutanen TV din,inaga ma hanashi kallo zanyi,har wani nutsuwa yake ta daban idan Yana kallon India Yana ganin matansu dinnan pre tsirara,sai kace da hijab nake yawo Zama yayi ya Sanya hannunsa saman cikina yace "Haba my boo,ke kinsani Babu macen da zata kaimin get rayuwarnan,da wasa nake Miki please forgive me" Kallonshi nayi ta gefe tareda Masa murmushin gefen Baki,hannu na Sanya ina shafan fuskarsa,idona Yana cikin nasa,abubuwa ke yawo a idanuwanmu da mu biyun kadai ke fahimta Cikin sauri ya kwantar Dani a gadon ya haye bisa kaina,kafata dake bayyane na Sanya a bayansa hannuna na shafan wuyansa Gaba d'aya ya maida hankalinsa ga fuskata zuwa kirjina,kisses yake sakarmin masu narka zuciya,tuni na sakar Masa ragamar,da kaina na zare rigar jikina ta sama Tashi yayi ya kashe fitilar d'akin ya dawo ya cigaba ta inda ya tsaya,cije bakina nayi nace "Ko sai na d'auko maka Torchlight?" Dariya sosai yayi tareda biting Dina a wuya,wani sauti na saki da nasan zai rudashi........ Cikin kunnena yace "Idan Kika bani Torchlight hajiya zata jiyo ihunki ne,Dan haka barni nayi lalubena" Gyad'a kawai kawai nakeyi....... *********** A firgice na farka Jin karar wayata,janyo wayar nayi Naga _besty_ salati nayi tareda kai wayar kunnena,cikin damuwa tace "Besty kina inane?ba dai makara kikayi ba Domin Nan da 20_30 mins malamarnan zata iso" "Wallahi besty ke Kika tasheni Amma ganinan zuwa" Da gudu na tashi na rasa Ina Zan fara dosa,duba agogo nayi Naga 8:32,Babu girki Babu wanka Babu komai..... Ruwa na kunna na sauka da sauri na daura tea,fitowa nayi da niyyar na sanarwa Saleh ya dumama tuwo yaci Zan fita yanzun kawai mukayi kacibis da hajiya Gaba daya na manta da hajiya a gidan,dur'kusawa nayi na kasa furta komai saboda yanayin kayan jikina Bayan nayi wanka ban maida rigar da na cire ba,wata yaloluwar vest na Sanya iya cinyata,gaba dayanta shara shara ce gashi pant ne zalla a jikina sai it,kaina kuwa kaman na mahaukaciya A fusace hajiya ta kalleni tace "Wani irin wulakanci ne wannan?saboda kinyi har sau biyu ban Miki magana ba?wato saikin nunamin ke Yar zamani ce Baki taso gidan tarbiyya ba, kinaso ki nunamin saidai na fita na bar Miki gida,da gayya kike abubuwan da ko uwarki ce a gidannan bazaki yisu ba" "Meye hakan?Ina matsayin uwar mijinki ki fito kina min fareti tsirara?nayi magana ace na takura Miki na hanaki sakewa da mijinki ko?to kin kyauta kin nunamin Baki gaji tarbiyya ba,Baki d'auki uwar mijinki a mutum ba ma balle uwa,saboda haka Zan fice na bar muku gidanku tinda na lura da take takenki,bansan gaba me.zaki aikata ba Kuma" Muryata na rawa nace "Wallahi hajiya bansan kina Nan ba,da na sani......" Bata ma tsaya Jin me zan fad'a ba ta fice daga gidan,numfashi naja tareda goge kwallar da ta zubomin,Banga laifin hajiya ba sai laifina,kowace uwar mini zata d'auka da gayya nayi hakan ko da kuwa akwai soyayya a tsqkaninmu,kashe tea din da na daura nayi Domin har yayi,gashi hajiya ta cinyemin kusan minti 5 Wanka nayi cikin 5 mins na Gama na fito,ban shafa Mai ba balle turare na dauki farin kayana na Sanya a jikina na tashi Saleh Kaman zanyi Kuka nace "Dan Allah ka kaini school na makara,saura minti goma malamar tazo,duk Wanda baije ba sai ya sake jarabawarta" Cikin magagin bacci yace "Okay" tareda d'aukan rigarsa dake bedside ya Sanya,key na d'auko muka fita Gudu sosai yakeyi kafin muje nace "Munsamu matsala da hajiya,wallahi kaga na manta Tana Nan na sauko cikin sauri da wannan rigar a jikina,to hakan yasa Ranta ya bacci Bata jira na Bata ha'kuri ba ta fita tace ta bar Mana gidan,Dan Allah ka Bata ha'kuri kafin na dawo" Shafa fuskarsa yayi yace "Tab,wallahi na manta ma Tana Nan,Amma karki damu Zan Bata ha'kuri" Amsa Masa nayi da to,muna zuwa saiga Kiran besty na ya sake shigowa,Ina dagawa nace Mata ganinan na shiga school din Tare da malamar muka shiga,cikin 20mins ta Gama abj da zatayi ta fita Gaba d'aya tunanin hajiya nakeyi,me zata cewa yayanta na aikata?me Zan tarar idan na koma? "Ke lafiya?" Naji muryar hauwa bayan ta ta'boni "Lafiya Lau" "To me nace yanzu?" "Lafiya kikace" Hararata tayi tace "Seriously...muna tattaunawa yanda assignment dinmu zai kasance kina can do tunani sannan kice min kalau?me ya faru?ko sirrin ciki ciki ne?" "A'a wallahi hauwa,uwar mijina ce take Mata gyara a part dinta shine tazo wurina ta zauna....to Kinga wallahi tun jiyan da tazo nake abubuwa na rashin dacewa" Tuni suka rufe maganar assignment,duk su ukun besty,hauwa da ummusulaym suka juyo kaina "Me kikayi hakan?" Besty ta tambaya harda zuba tagumi "Jiya da ta shigo ta samemu dai ba a yanayin da ya dace ta ganmu ba as uwar miji,sannan yau da safe wallahi na manta da ita a gidan kawai na sauko half naked,shine fa tayi fushi tace fita zatayi" "Amma kuwa wannan ba uwar mijin arzi'ki bace,da wata ce ai dauke kanta zatayi ta nuna kaman ma batasan da ke wurin ba,jiyan ma da taga abinda yafi karfin eyes dinta saita sum sum ta juya,ko ni as a friend nazo gidanki na sameku getting it on Sadaf sadaf Zan koma inda na fito,Amma dukda haka ki Bata ha'kuri Kuma ki kula da abubuwa,Kar taga kaman da gayya kike hakan" Amsawa nayi da to na fara tunanin ta inda Zan tunkareta 11 Gida na fara shiga na ajiye jakata sannan na fito, part din hajiya na nufa na samu har an fara aiki. Kai tsaye sashin sultana na nufa, Hira sukeyi nayi sallama, ciki-ciki hajiya ta amsamin na dur'kusa na gaidata. Amsa min tayi da " lafiya ". " Hajiya kiyi ha'kuri da abinda ya faru, insha Allahu bazai sake faruwa ba wallahi ba da gan-gan nayi ba, Dan Allah kiyi ha'kuri ki dawo " Banza hajiya tayi dani kaman ma ba magana nake ba, alamu nayi wa sultana da ta Sanya baki, gyara zama tayi tace. "Hajiya tunda ta baki ha'kuri ki ha'kura mana, kinga ni gashi yanzu da vest nake zaune muna hira dake baki ce komai ba, to me zai hana itama ki d'an bata chance, tunda bakyaso tana zama hakan zata daina kiyi ha'kuri hajiya" Ba tare da hajiya ta kalleni ba tace, " jeki naji, zan dawo " Godiya nayi mata na koma na d'aura tuwon semo miyar kuka, Domin dumame nakeson ci da dare. Har na gama nayi wankana na zauna ina hutawa hajiya Bata dawo ba shima d'an hajiya bai dawo ba, Ina zaune a gida ni kad'ai har magrib. Saida akayi magrib tukun saleh ya dawo, sallamarsa naji na tashi cikin sauri na fita,saida na le'ka na tabbata hajiya Bata taho ba tukun na yi masa welcome, duk da haka ban sake ba ina rungume dashi ina duban 'kofa. Kafad'ata ya ri'ke yace, " Wai me kike waiwaye ne haka? " 'Daga gira nayi nace " hajiya mana,da 'kyar fa na shawo kanta da taimakon sultana tace zata dawo, bana so na sake wani abun da zai 'bata mata" Hancina ya ja cikin wasa yace, " kefa akwai matsoraciya, to ai hajiya bazata hana mu soyayya ba ko?" " Ni dai a'a " na fad'a tare da d'auke hannunsa daga kafad'ata, turo min baki yayi yace "To zamu yi magana anjima". Gaba yayi nabi bayansa, gani nayi yayi sama nayi zamana, da alamu ya d'an hau, to hajiyarnan dai gyatumarsa ce Jallabiya ya Sanya ya fita masallaci sallar isha, yana fita hajiya na shigowa. Tashi nayi cikin hanzari na dur'kusa na gaidata, zama tayi Kan kujera nace, " Hajiya a kawo miki abinci?" "Naci abinci " ta fad'a tare da gyara zamanta kan kujerar, remote na d'auka na mi'ka mata domin takai channel d'in da take so na nufi kitchen na d'aura d'umamen tuwona Fitowa nayi da man shanu na da yajin daddawa, Ina ganin idon hajiya Kan tuwon a raina nace kin ma kanki Ina fara cin tuwon hajiya ta tashi ta nufi d'aki, da alamu 'kamshin man shanu ya isheta. Kafin na 'kare Saleh ya dawo, zama yayi muka ci tare muka sake 'karowa, saida mukayi fam tukun. 9:30 nayi ma hajiya sallama na wuce na kwanta,tashin asuba nayi na hau aiki da shirin breakfast, ina gama wa na d'aura na rana domin sai yamma zan dawo. Har 10 hajiya bata fito ba, kwankwasa mata 'kofa nayi na sameta tana azkar, gaisheta nayi bata amsa ba na ajiye mata kwanon tuwonta nace " Hajiya yau sai yamma zan dawo amma nayi girkin rana, idan ya dawo zai fito miki dashi " Ficewa nayi ban jira me zata ce ba saleh ya d'aukeni ya kaini school Haka muka zauna tsawon sati biyu hajiya bata cemin komai saidai idan na gaisheta ta amsa da lafiya, girkina kuwa na lura ya fara mata dad'i, musamman idan nayi tuwo saita ci da dare taci da safe ta kuma ci da rana ,hakan yasa kullum sai nayi tuwo. Mun shiga sati na uku na tashi da ciwon mara, da 'kyar na daure na yiwa hajiya dumamenta nayi mana chips da 'kwai domin Saleh ya fara mitar tuwo. A daddafe na fito da abincin na jera duk suna d'aki na koma kujera na kwanta ina ri'ke ciki, sosai ciwon ya fara cina ban san lokacin ma da na fara kuka ba " Ya salam, me ya sameki boo?" Kasa amsa masa nayi sai nuna masa wurin ciwon nayi, zama yayi ya d'aura kaina a cinyarsa Yana min sannu, kaman nace ya tashi saboda hajiya amma ciwo ya hanani. Bansan hajiya ta fito ba sai muryarsa naji yana cewa "Hajiya bilkisu bata da lafiya,naga dai kaman tace cikinta ke ciwo " Idona a rufe sai hawaye dake zuba naji alamun hajiya a kaina, bud'e idona nayi a hankali na kalleta tace " Ciki ko dai mara?" Da 'kyar nace mata mara,ficewa tayi ta barmu sai had'a zufa nake ko motsin kirki na kasa, sannu kawai saleh ke min yana min fifita dukda fankar dake d'akin Kusan 10 mins babu sau'ki itama hajiya Bata dawo ba, cikin damuwa yace " Ko dai muje asbiti ne?" "Um" na amsa da 'kyar Tashi yayi domin d'auko key hajiya ta shigo tare da sultana da cup a hannunta , dawowa yayi ya zauna yace "Wai da asbiti ma zamu je" Zama sultana tayi da tulelen cikinta tace "Gaskiya dai ya kamata kuje asbitin,last month ma haka tasha wahala wallahi,inaga duk cycle haka take fama, Kuma ai ance idan ciwon yayi yawa da matsala ko? " Tayi tambayar tana kallon hajiya, hajiya bata amsa mata ba ta mi'komin kofin. Tunda na sha'ka naji amai na tasomin haka na daure, ina shan hulbar ina yunkurin amai har na shanye Kwanciya nayi a tsohon makwancina ina Jin amai na tasomin, "Idan akai massaging marar ma ai naji ana samun releif " sultana ta fad'a tare da tashi Saleh kaman jira yake ta fad'a naji hannunsa ya fara shafa marata,rufe idona nayi inajin ciwon na raguwa da kad'an-kad'an, tunawa nayi da hajiya cikin sauri na ture hannunsa tareda bud'e idona, babu hajiya babu sultana Ko a jikina na maida idona na rufe nace "Ka koresu kenan " "Sun dai kori kansu, kinji nace su tafi? " " To ya zaka fara shafani a gabansu dole su watse ai " "Kai boo bana son sharri, ni magani nake miki ba shafaki nake ba, yanzu kikace ina shafeki ai sai a d'auka shaaaaaaafeki nake " Gyara kwanciya ta nayi nace "indai kai ne kad'an da aikinka kayi ko ma mene a gaban hajiya " Dariya yayi yace "Sau'ki ya samu kenan an samu bakin magana, to kuwa zan baki mamaki, zan shasshafeki a gaban hajiyan tunda kince kad'an da aikina " Murmushi kawai nayi domin bacci ya fara d'aukata. Lokacin da na farka 2 ta wuce,ni kad'ai ce a gidan da alamu ya fita aiki hajiya kuma tana wurin sultana. Jikina har yanzu babu 'kwari, kwanciya nayi naci gaba da hutawa har wani baccin ya d'aukeni Sai 5 na fara shirin abinci, hajiya kuwa bata dawo ba sai bayan isha, sati d'aya kawai ta 'kara a wurina ta tattara ta koma wajen sultana, ban damu da hakan ba domin ta nunamin kawai tana son kula da sultana ne ********* Bugun gida naji bayan na idar da sallar asuba, mamaki ne ya kamani domin nasan dai saleh da key d'insa yake fita sallah Fita nayi nace "Waye" "Usman ne" ya fad'a cikin damuwa, cikin sauri na bud'e gidan domin nasan tabbas haihuwar sultana ce ta taso Takalminsa wari da wari abin tausayi d'ayan ma na sultana ne ya sanya ya fito bai sani ba, cikin tsantsar damuwa yace "Wallahi sultana ce ba lafiya kuma mota ta babu mai, shine nazo saleh ya kai mu asbitin" "Subhanallah, ya fita masallaci kuma, amma ta dad'e da fara ciwon ne" "A'a, wurin dai 4:00 ta fara, ko zaki duba ta ne?" "To muje " Ina jan gidan sai ga saleh ya dawo,bayani na masa ya shiga ya d'auko key ni Kuma na nufi cikin gidan, abin mamaki sai ga sultana da akace tana zaune tana gyangyad'i da waya a hannunta Zama nayi gefenta nace "Sultana akace baki da lafiya" "Um na warke, bacci ma nake ji amma wannan ciwon ya hanani bacci, bilki rabona da baccin kirki kwana uku kenan fa, na gaji dan Allah so nake na haihu " " Kwantar da hankalinki zaki haihu, minti nawa ne da kin fara na'kudar asali kin haihu?" "Dan Allah ni ki dubani kiga saura nawa na haihu ne? " "Kai, sultana kin fiye wutar ciki " "Dake cikin ba a jikinki yake ba ko? " Dariya nayi ina Jin tana tsaki, dubata nayi nace "Allah zaki iya kai 12 na rana ma tukun ki haihu, ki bari kaman 10 sai mu tafi asibitin ko?nayi zaton ma hajiya tana nan " "Hajiya ta koma tun last 2 weeks " "To yanzu kwanta kiyi baccinki bari na sauka na musu bayani ko sa samu su huta musamman mijinki Allah kad'ai yasan halin da ya shiga yana can yana fama da wari-warin takalma" Tana gyangyad'i tace "Dan Allah idan kinje ki dawo kar ciwo ya dawomin bakya nan, idan baki dawo ba ke da Allah" Dariya ta bani nace "to naji zan dawo " Sauka nayi nace suje gidana Usman ya huta sai kaman 11 zamu tafi asbiti ni Kuma na koma wurin sultana Ta dai samu bacci amma batayi mai nisa ba ciwo ya tada ta, gama juye juyenta tayi ta ware Kuma kaman ba ita tayi ciwo ba ta sake kwanciya bacci 10 dai-dai ta azalzaleni muka fara shirin tafiya asbiti,a lokacin aka sanarwa hajiya da jumana, sosai hajiya ta nuna 'bacin ranta saboda ni aka fara fad'awa ciwon sultana kafin ita 11:20 muna asbitin, kafin 12:30 abitin ya cika ma'kil da 'yan uwan sultana ko nace 'yan uwanmu, har kunya saida ta kamani Sai wurin 2:30 sultana ta haihu,ta haifi 'yarta mace, ni na kar'bo babyn na mi'ka musu. Sun cika asbiti da hayaniya da wuri wuri aka sallamemu domin ta haihu lafiya Alhamdulillah. Da ni da ita da hajiya da kuma anty maymu muka dawo a motar saleh, hajiya na ri'ke da babyn sai barka take yi Ko da muka isa gida ficewa sukayi daga motar suka barni da zannuwan sultana har da mahaifar. Ba tare da damuwa ba na d'auki zannuwan na nufi part d'ina na sanyasu a washing machine, cikin 'kankanin lokaci suka wanke tas nayi drying na sanyasu a shanya Farfesun kaza na d'aura ma sultana sannan na d'auko wayata, message d'inta na gani da dogon lissafi na gyaran gidanta, wai ta barshi kaca kaca tasan idan yan uwanta suka zo sai tasha fad'a Ina gama girkin usman ya kawomin key na shiga gidan na fara gyara mata, ba laifi babu inda yake a gyare a gidan, harda tilin kwanukan wanke wanke inaga ma na kwana biyu ne Kusan 3 hours ina mata gyaran gidan sannan na sanya turare na rufo gidan na nufi sashin hajiya da flask d'ina a hannu Babu wadda ta d'aga ido ta kalleni a cikinsu na ajiye flask d'in na koma na d'auko mahaifa na kawo musu,shine ma hajiya ta kar'ba Zama nayi ina jiran a bani baby suna ta passing d'inta ga junansu suna d'aukanta hotuna Fitowa sultana tayi tasha kwalliyarta tayi kyau, gwanin sha'awa bazaki ce ma ita ta haihu ba. Tana zama taja flask d'in naman da na kawo ta fara ci, gaba d'aya hankalina na kan babynnan amma sunyi min haramiya, gajiya nayi ganin ta koma hannun jumana nace "Jumana muga babyn" Banza tayi dani kaman bata ji ba saida na sake maimaitawa, Cikin Isa kursum tace "Karki bata, ita da ta tsaida haihuwa saboda kar 'ya'ya su hana ta karatu? Idan tana son ri'kon jarirai sai ta haifo nata itama " D'auke kaina nayi daga garesu,a tunanina maganar ta 'kare naji jumana tace "Zata kar'bi na wasu mana ta samu abin aibatawa, an hanaki kiyi zuciya gobe ki haifa kema, masu halin yahudawa, ai irinku Allah kashe mahaifar yake duka ya nuna muku iyakar ku " " Maganar wa ake ne? " Naji muryar wata dattijuwa daga waje, kallona sultana tayi cikin damuwa tace "Mama?" "Na'am, maganar wa nakeji kunayi haka? " " Wannan matar salen mana, wai ita tana karatu shine ta tsaida haihuwa kuma babu kunya tazo tana cewa a bata babyn sultana ta d'auka " " Matar Saleh?....." Katseta sultana tayi tace " Mama ba fa haka ne ya faru ba, magana mukayi da ita nake Bata shawarar ta dakatar da haihuwa har ta gama karatu, to ni kuma...." A fusace mama tace "Rufemin baki, ke da baki san ciwon kanki ba, har wata matar Saleh zaki tsaya kina karewa? Bayan duk abinda ya faru ta dalilinta? Wa ma ya fad'a mata muna d'aukan wannan yahudancin a gidannan, ina take matar salen? " Jikina tuni ya fara kyarma, domin yanayin maganarta kad'ai ya isa ya tsoratar dani, Nuna ni tayi da yatsa tace " Tashi ki fice mana daga nan, duk wanda baya koyi da sunnar annabi bazai Kuma d'auki umarnin Allah da muhimmanci ba bazai ta'ba zama tare damu ba, mu nan 'ya'yan sunna ne babu jinin yahudanci a tare damu, shi Kuma sale zaizo ya samemu ne, shima da baisan ciwon kansa ba, Dan Allah hanzarta ki fice ganinki ma sake 'batamin rai yake 13 Zuru zuru nayi cikin tsananin kunya da takaici na tashi nayi hanyar fita, hannuna naji an ri'ke na juya naga sultana "Ke Kuma sha-sha-sha da bakisan ciwon kanki ba, ta rabaki da saleh ta aureshi amma kina nan kina ma'kale mata, sai kace mayya,ke dai lalacewa ta tabbata a kanki wallahi, kuma kina nuna mata soyayya bakisan hakan 'kara sanya mana tsanarta yake ba " Janye hannuna nakeso nayi amma ta 'kan'kame, cikin fad'a tace " Wai meyasa kuke haka ne? Meyasa bazaku ja girmanku bane? Yanzu menene amfanin hakan da mukeyi please, na fad'a muku 'karya nake amma bari na fad'i dalilina na yin hakan" Sakin hannuna tayi tace " Ina sane na had'a wannan 'karyar domin raina na min dad'i idan naga kuna mata haka " Banyi wani mamaki ba da jin hakan, domin na dad'e ina jin rashin yarda da sultana a raina, komawa tayi ta zauna ta juya min baya tace " Bayan nayi hakan kuma na sami nutsuwa a raina sai ya usman ke nunamin bayaso ina yin hakan, kenan Ina ri'ke da soyayyar saleh bayan ina aurensa, kenan auren nasa baida amfani, idan kuna ganin ina sonta ne ni ba haka bane, kawai ni nawa hanyar hukuncin ta banbanta da naku ne, idan kunga zaku ci gaba da zubda girmanku a haka......" Fita nayi kaina na juyamin, ina shiga gida na fara hawaye, Kan kujera na kwanta ina kuka mai cike da takaici, duk halaccin da nayi wa sultana da abinda zata sakamin kenan? Alamun ana bud'e gida naji ban ko motsa daga inda nake ba, ina jinsa ya shigo ya 'kwan'kwasa 'kofa alamun naje na masa welcome Da ya tabbatar bazan fita ba da kanshi ya shigo, cikin damuwa ya ajiye ledar hannunsa yace "Me ya faru " Cikin shesshe'kar kuka nace " 'yan uwanka sunyi min gorin haihuwa, dan Allah boo-boo muje asbiti a dubani domin su tabbatar lafiyata 'kalau, sun'ki bani babyn wai naje na haifa nidai muje asbiti kawai...." Kwantar dani yayi a jikinsa yace " Haba my boo, ke kika ce kin dena damuwa da abinda 'yan uwana zasu ce miki, yanzu ko munje asbiti za'a ce munyi garaje ne aurenmu baiyi shekara guda ba fa har yanzu, sunyi hakan ne dan kiji haushi kamata yayi ki nuna musu baki damu ba, my boo ni nake aurenki ba su ba, kuma ni ban shirya gintse amarcinmu a wannan 'kan'kanin lokacin ba, sannan haihuwa ta Allah ce, su d'in su suka haifi kansu ne? ki rabu dasu karki sake zuwa gidan sai ranar suna shima karki zauna " Ban amsa masa ba yaci gaba da rarrashina "My boo nifa ban sanki da mita ba, nifa kukannan naki ban gane masa ba, ba dai kukan rashin ganin baby bane? to gata nan d'ago kanki ki kalleta " Mi'komin wayarsa yayi naga pic d'in jaririyar, mi'ka masa nayi na kwanta a 'kirjinsa ina had'iye sauran kukana, ko me sukamin ni naja tunda nakai kaina cikinsu  kaman wata tsiyar zasu min bayan nasan had'uwata dasu bata zama alkhairi, yanda saleh yace bazan sake nufarsu ba sai suna, shima bazan zauna ba zan taho Share haihuwar nayi a kwanakin na shiga harkata, saidai jaririyar ta tsayamin a raina sosai nakeso na ganta, amma tafi 'karfina. Ranar suna da wuri na shiga gidan na tafi da kayan barka na, diaper bag na Kai mata da set uku na kayan jarirai da atamfa d'aya. Sai yau na d'auki babyn, sultana ta kasa had'a ido dani nikuwa na nuna mata kaman bansan me ya faru ba, cikin fara'a nace " Ya sunanta " "Surayya, sunan hajiya ne huda ake kiranta " "Allah ya raya ta yayi Mata albarka" Mi'ka mata 'yarta nayi na fice, ina tafiya ina tunanin idan Allah ya bani haihuwa sunan da zan sanya, huda ta shiga raina kafin naje gida na tsara fara addu'ar neman haihuwa Cikin dare na tashi na fara Kai kukana ga Allah ina ro'konsa ya bani zuri'a ta gari me albarka, addu'a nake bana duban time har aka fara kiran sallar asuba Kafin lokacin sallah yayi na fara bacci, saida saleh ya dawo daga masallaci ya tasheni sannan nayi sallah na koma bacci Addu'a na maida d'abi'ata, fatana kawai Allah ya bani zuri'a me albarka nima dai na haifa na wuce gori. Sati biyu da haihuwar sultana sai gata ta shigomin, fuskata ba yabo ba fallasa na sauketa na kar'bi huda, tamkar ba'kuwa nayi treating d'inta kwata kwata na'ki bata fuska, batayi 20mins ba ta tafi ganin babu fuska Watansu biyu ta kawomin huda cikinta ya kumbura, jikin yarinyar babu kuzari gashi ta sake 'kan'kancewa. "Sultana ya na ga jikinta babu wani 'kwari ne?ko bata Jin dad'i?" "A'a lafiyarta lau banda dai kumburinnan da ya fara jiya ta hanani bacci, ni ba wannan ke damuna ba, dan Allah ki fad'amin madarar da za'a siya mata munaso mu fara had'a mata da Madara" "Okay, ki bata SMA" godiya tayimin na fad'a mata maganin kumburin cikin ta tafi, tausayin huda ne ya kamani domin nasan zata sha wuyar uwa, sultana bazata ta'ba iya rainonta yanda ya dace ba. Addu'a nake babu ji babu gani,haka itama sultana shigowa jikina take sake yi tun ina mata kora da hali har na gaji, ko me zata yimin kanta. ********* Shigowa tayi idonta a kumbure alamun rashin bacci,saura 'kiris ta jefar da huda a 'kasa na kar'beta cikin sauri, kwanciya tayi kan kujera tace "Wallahi jiya ban runtsa ba saboda kukan huda,kuma lafiyarta 'kalau kukan iskanci ne kawai, dan Allah ki ri'kemin ita idan zaki iya na samu nayi bacci kaina har sarawa yake wallahi" " Bakomai, jeki kiyi baccinki" Mutsu mutsu huda ta fara tana kuka 'kasa 'kasa, wuyanta na kalla naga datti ya had'e da powder Tambayarta nayi nace "Yaushe rabon ki mata wanka?" Shiru tayi sannan tace "Inaga kwana uku ne ko hud'u? ba ke kika cemin ba'a son yawan wanka ba yana sanya yara mura shine kawai bana mata" Raina naji ya 'baci nace "Babu wani mura da ta hanaki wankan yarinyarnan, 'kyuya ce kawai wallahi da 'kazanta, huda ta kwana da Pampers kun tashi dashi inaga tun 7, yanzu ki duba 10 ta wuce amma daga tsamin dake tashi a jikinta nasan Pampers din dare ne a jikinta, yarinya sai tsami take tana 'karni  kuma kina complain tana miki kuka, ba dole tayi kuka ba kin had'a mata wahala baki mata wanka ba kuma baki goge mata jiki ba,haka akeyi?" Bata amsamin ba ta fice ta barni da huda a hannu, takaici ya kaini bango ji nake kaman na bita na mareta, sai lokacin na kula da jakar da ta shigo da ita na bud'e. Madara ce da kayan had'i da Pampers a ciki babu wasu kaya spare sai pant 'kwaya biyu, mamaki ne ya kamani, wasu basu san ciwon 'ya'ya ba amma Allah ba ruwansa Basu yakeyi. Wanka nayi ma huda, jikinta har ya d'ad'e saboda yawan sanya pampers, pant na sanya mata na had'a mata madara tasha na goyata, cikin 'kan'kanin lokaci ta fara bacci ba tareda rigima ba, a wata uku har sultana ta gaza ina ga an kai shekara? banda tazo yanzu Allah kad'ai yasan lokacin da huda zata d'auka da datti a jikinta Har azahar huda bata farka ba taji dad'in wanka da baya, tana farkawa na kira sultana a waya naji wayarta a kashe, kayan da na cirewa huda na wanke na mayar mata jikinta na fita domin kaiwa sultana ita amma bugun duniya ta'ki bud'ewa,haka na ha'kura na koma na sake bata madara ta hau min hira Sai 3 ta fara kukan gajiya na sake kaita gidansu,naci sa'a sultana ta bud'e ta kar'beta tare da godiya. Tun ranar hankalina baya kwanciya, a kowace rana sai nayi tunanin me sultana zata mata na kulawa, kwana uku na rasa sukuni naje na dubata A Palo na samu huda tana ta tsanyara kuka wai sultana na wanka,gashi tabar gidan a bud'e, d'aukan huda nayi na fita da ita ina Shirin masifar da zan sirfawa sultana 30mins shiru bata kirani ba bata le'ko ba,har dai naga tayi 1 hour dole na koma dan naga abin nata yayi yawa A rufe na samu gidan na kirata a waya, katsewa tayu ta turomin text _please am sorry na d'an fita ne, 2 hours nayi al'kawarin dawowa key yana 'kasan wannan dutsen na gefen 'kofar, komai na fito dasu suna Kan kujera sai na dawo_ Cike da haushi naja tsaki na d'au key na shiga na d'auko mata kayanta da kayan abincinta, Allah kasan dalilin da ya sanya ka bawa sultana haihuwa amma dai kam haihuwa a wannan lokacin bata kamaceta ba Daga nan kusan rabin rayuwar huda ta dawo hannuna, hakan yasa daga huda har sultana suka samu nutsuwa, huda har wani 'bul-'bul tayi ta 'kara kyau dake tana samun kulawa, idan na kar'bota da safe wani lokacin sau biyu kawai sultana zata bata nono tace ta gama sai kuma dare,   huda har ta dena damuwa da nono idan tasha Madara ta hau baya shikenan, har banaso naje school na dad'e Domin wujiga-wujiga zan dawo na sameta. Watan huda shida sultana ta fara sabon laulayi, kuka tayi sosai na sai an zubar da cikin kafin kowa ya sani nace mata ba dani ba, ganin da gaske so take ta zubar yasa na sanarwa mijinta sun samu 'karuwa dole ta ha'kura ta rungumi 'kaddararta, amma saboda naji haushi ta yaye huda a watanni shidannan ta li'kamin ita dukda bata fara wani laulayi mai tsanani ba, ita ta sanarmin jumana ma nada ciki har ya fara bayyana. Na shiga damuwa sosai na fara tunanin idan suka haihu wani irin hali zan shiga? Yanke shawarar zuwa asbiti nayi na tabbatar da lafiyata tun kafin lokacin da za'a min dole..... _naso ace yafi haka tsayi hannuna Yana Dan ciwo ne kuyi hakuri da wannan_ 15 Na dawo ina laluben key zan bud'e gida na hango jumana tana yowa wurina, d'auke kai nayi kaman ban ganta ba na fara bud'e gidan Kiran sunana naji usman yayi na waiwaya na ganshi da huda a hannu tana kuka, tun kafin su 'karaso take mi'komin hannu ina kar'barta tayi shiru. "Ina wuni " ya gaidani tareda mi'kawa huda hannu,kwanciya tayi a jikina ta'ki ko kallansa "Lafiya lau, an mata wanka kuwa?" " Anya kuwa? da kayannan na fita na barta dai gaskiya da alamu ba'a mata wanka ba,itama sultanan a kwance take tun safe jikin ya'ki dad'i " " Sannunku da hira " jumana ta fad'a tareda Kama wuri ta tsaya, amsa mata nayi da yawwa nace " Ya kamata ka d'auketa kuje asbiti " "To shikenan nagode". Shafa kan huda yayi yace "Sarkin rigima sai anjima ko?" Tafiya yayi ya barmu na bud'e gidan nace da jumana "Bismillah" Tafiya take tana turo mitsitsin cikinta da ba wani bayyana yayi ba, amma ta 'karfi da yaji ake turoshi ko ni ake nunawa? Kama 'kugu tayi ta zauna tana kallon huda dake hannuna tace " A wajenki take wuni kenan " " A'a, bakiga yanzu aka kawota ba? Asbiti zasu je ne shiyasa " Dama nasan gulma ce ta kawota, "Amma yanda take da 'kyuya naga tazo wurinki kaman kun saba sosai " Ban amsa mata ba na ajiye huda nace "Ina wuni, munata surutu bamu gaisa ba" "Lafiya lau, ya karatu? Ai kwana biyu banji dad'i ba naga baki zo kin dubani ba nace to inaga baki sani ba" "Allah sarki, ban sani ba, amma jikin yayi sau'ki ko? Koda yake masu ciki ba'a rabaku da ciwace-ciwace" Ai kaman na kunnata ta fara zuba "Ai kedai bari, ciki akwai dad'i akwai wahala, yau wancan ciwo gobe wancan, ai ita kam sultee tana da sa'a, nufa ciki na biyar kenan sannan ya zauna, saura kuma ku 'yan hutu" " Um, hutu ai akwai dad'i dukda haka dai a taskar Allah muke nema, kema gashi bayan shekara da shekaru ana abu d'aya yanzu Allah ya kawo ba zama? Shi plan d'in Allah ai haka yake sai lokacin da yaga dama yake bayarwa, idan ka takura ka samu lokaci baiyi ba ma zubewa zaiyi tayi har sai wannan wa'adin ya kai" Shiru tayi ta kasa cewa komai, friso na had'awa huda wanda na sayo a hanya, su iyayenta na fad'a su sayo amma sun fiye wasa " Ashe kin iya raino haka? Kice idan na haihu nima na huta saidai kawai na dire making wuce, wai yaushe zaki gama karatunnan ne? " Dariya nayi nace "Ai ba kowane irin d'a nake raino ba, itama lalura ce tasa nake rainonta, karatu na kusa 'karashewa " Kafin tayi magana nace " Bari na shiga na yiwa huda wanka, zaki jira ne na fito?" "A'a tafiya zanyi dama nazo mu gaisa ne sai anjima, sai munji labari kuma " Rakiya na mata na rufe gidan na yiwa huda wanka na ciro kayanta a wardrobe na saka mata, wasa wasa huda ta zama rabin 'yata domin babu abinda babu nata a wurina Kwantar da ita nayi ina lalla'bata tayi bacci har mukayi tare, sai la'asar muka farka shima bugun gida ne ya tashemu duka Bud'e gidan nayi naga sultana a tsaye, 'kare mata kallo nayi domin ta bani tsoro, tayi masifar rama tayi haske tayi zuru-zuru Magana take a hankali banji ma abinda tace ba na rufe 'kofa ta shigo. Zama tayi ta jingina da kujera tace "Ya huda ya 'ko'kari?" "Alhamdulillah ya jikin naki" "Jiki alhamdulillah, shigowa nayi na miki godiya akan d'awainiyar da kike da huda, bilki duk 'yan uwana babu wadda zata yimin haka nagode Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biyaki " " Babu komai sultana Allah ya baki lafiya " " A'a bilki, abubuwan da suka faru ko ni aka yima indai huda take bazan kalla ba, amma ke kinada kyakkyawar zuciya kulawar da kikeyi wa huda ni bana mata, nagode sosai, akwai maganar da nakeso muyi amma ba yanzu ba, ga wannan " Ajiyemin leda tayi ta tashi ta fita tana taku a hankali, rakiya na mata huda na binta da kallo, murmushi tayi ta mi'ka Mata hannu tace "Huda baza kizo mu gaisa' ba?" No'ke wuya huda tayi tana ri'ke rigata,dariya tayi tace " Yaro shima yasan mai yimai " Ri'keta usman yayi suka 'karasa, Allah sarki sultana tana jin jiki sosai, da alamu dai yau huda a wurina zata kwana. Bud'e ledar nayi naga lace masu kyau guda biyu da kayan huda, ajiyesu nayi domin saleh ya gani. Ina girki naji sallamar Saleh, shigowa yayi kicin din tareda hugging d'ina ta baya, " Sannu da aiki maman huda " Wani dad'i naji a raina da bazan iya misaltashi ba, murmushi nayi nace "Sannu da dawowa abban huda " tareda pecking d'insa a lips, dariya yayi yace " Kin gammu zamu kwacewa mutane 'yarsu, anya muma ba hudan zamu saka ba naga sunan ya hau dake maman huda " ya fad'a tareda d'aukan huda dake wasa kan table mat da na shimfid'a na ajiyeta, hannu ta fara mi'komin ya bata key d'in motarsa ta fara wasa dashi, sunyi min kyau sosai, hangowa nayi da ace huda 'yata ce abun zaifi haka bada ma'ana. Zama mukayi muka fara cin abincin huda sai hannu take kaiwa ina d'aukewa, gajiya nayi na barta taci wanda zata iya ta 'bata jikinta Tare da saleh muka tafi yi mata wanka, tunda na kunna ruwan take murna, sanyata nayi na barta da saleh na fita d'auko mata towel, kafin na koma duk ya ji'ke itama ya ji'ka mata gashinta Ri'ke 'kugu nayi nace "Me kukayi haka " Cikin sauri ya nuna huda yace "Itace". Dariya sosai ya bani kaman wani 'karamin yaro, ganin ya nunata itama ta nunashi, cigaba tayi da facal-facal da ruwa na kar'beta na korashi, wanka na mata na wanke mata gashinta. Shiryata nayi na tufke mata gashinta, gashin baida yawa sai tsayi tubarkalla, kaman ba kan yarinyar wata bakwai ba Bawa saleh ita nayi nace " Banaso na fito naga wani abu ba dai-dai ba, kar ka bata komai a 'koshe take, ka ri'kemin ita kawai har na fito " Ma'kale murya yayi yace "To mama" Tsit na jisu ina wankan, kaman dai abin arzi'ki akeyi, dukda haka hanzartawa nayi na fito A cinyarsa na sameta ya bud'e wayata suna kallon video, ina fitowa video ya katse ta kalleshi, komawa farko yayi naga tana ta ta'ba screen d'in Kaya na sanya na kwanta ina karatu ina kallonsu har huda ta fara bacci a hannunsa, kwantar da ita yayi can gefe ya dawo wurina, ba tareda jira ba ya had'e bakina da nasa, tattaro rigata ya fara ta 'kasa naji kukan huda, Cikin sauri ya matsa na kalli inda take, dafe kaina nayi nace "Allah yasa tun yanzu tayi kukan, kaima fa ka fiye garaje " 'daga gira yayi yace "Mun dai fiye garaje" *********** "Jumana ta haihu"  saleh ya fad'a yana shigowa, cigaba nayi da wankina nace "Allah ya raya, Zan shiga na mata barka " A cike na samu gidan anata barka itama ta haifi mace, Allah dai ya taimakeni babu idon wadda  ya hau kaina har nayi barkar na fito Kwana biyar da haihuwar Saleh ya shigomin da had'ad'd'en Kati ya mi'komin wai na sunan jumana, a wani makeken wurin biki za'ayi shi, ri'ke baki nayi ina mamakin wannan sabuwar bidi'a. Watanni kad'an da haihuwarta itama sultana ta haihu, namiji ta haifa bayan doguwar na'kuda, saida tayi sati guda a asbiti ma tukun suka dawo gida Ranar da suka dawo na shiga yi mata barka kuma na kai Mata huda, tsautsayi Ina shiga na tarar hajiya da haularta maganata sukeyi. " Gata nan munafuka, shigo nan" Zama nayi da dakakkiyar zuciyata na gaidasu, babu wadda ta amsamin Yaya maimu tace " To kin dai gama karatunnan na masifa, gashinan haihuwar Kuma baki yiba me kike nufi ne? " " Yaya maimu haihuwa ai ta Allah ce, ni bance sai bayan na gama karatu zan haihu ba " " Au rashin kunya zaki min? To bari kiji idan ta'kamarki kinada goyon bayan miji ne to shi kanshi mijin naki a 'kar'kashinmu yake, wallahi kinji na rantse sai ya 'kara aure tunda ke bakida mutunci, sai kiyita zama da hutunki " Cikin 'karfi ta fincike huda, tsala ihu huda tayi maymu ta daka mata tsawa, tsorata tayi kukanta ya 'karu, kallon sultana tayi tace "Ke kuma yarinyarnan tafiya zanyi da ita kafin ki warware" " A'a babu inda za'a kaita, tuntuni mukayi magana da ya usman yacemin bayaso a kaita ko ina, da can ba ni nake kula da ita ba? A barmin abata mi'komin ita ma naji d'umin kayata " Dake hankalinta na kaina bata wani damu ba ta mi'kawa sultana huda, mi'komin hannu huda take sultana na kauda hankalinta Maman sultana ce ta shigo itama suka zauna suka sakani gaba, Babu wadda ta sake magana har ina Shirin fita sai ga saleh,nuna masa wuri akayi ya zauna , cikin gadara hajiya tace "Ke bilki, d'ayan biyu ko bakyason d'ana ko kuma ke juya ce, ki fad'amin wanne ne a ciki? Haihuwa ce bakyaso kiyi da d'ana ko kuwa haihuwar ce bakyayi " Na d'au mintina kafin na amsa saida ta sake maimaitawa nace "Hajiya soyayya ce ta Sanya na auri d'anki, kuma inaso na haihu Allah ne bai kawo ba " " Ki dena saka Allah a abinda kika tsarawa kanki, su ba gashi duk sun haihu ba? Sultana haihuwarta biyu, jumana cikinta nawa kafin ta haihu? Amma ke kina zaune saidai kici ki yiwa mutane kashi aure kusan shekara biyu" maman sultana ta karashe maganar tana jan tsaki Kallon saleh hajiya tayi tace "Kai Saleh, d'auki matarka yanzunnan kuje asbiti ayi mata gwajin haihuwa, ba Kuma Kai kad'ai zaka tafi ba, ka d'auki d'aya cikin 'kannenka ku tafi, idan har aka gano tanada wata matsala a yau zamu fitar maka da wata matar ka aura " " Cikina naji ya juya, ri'ke hannuna yayi yace " " Idan kuma batada matsala zaku kyaleta da fitintinu muci gaba da zamanmu lafiya?" " Mu muke fitintinu sale? Ni uwarka zaka kalla kace muna kawowa matarka fitina? " Shiru yayi sannan yace " Naji hajiya na amince, idan har an sameta da matsala zan amince da za'binku, idan ba'a sameta da komi ba dan Allah ku barta ta huta tunda ta shigo gidannan batada kwanciyar hankali saboda ku, sannan ni bazan d'auki kowa ba, ai wannan abin daga mata sai mijinta ake zuwa " Tasowa maman sultana tayi tayo kanmu a fusace, tsayawa tayi tana nunashi tace " Akan wannan kake kallan mahaifiyarka kana fad'a mata magana? Saboda Kai baka da kunya baka da mutunci? Akan mace? Macen banza macen wofi da ta sameka da girmanka? " Shiru yayi taci gaba da surfa masifa, dawowa kaina tayi tace " Dole yayi haka mana, ya d'auko matar da ta shanyeshi, ke wai yar boko ko? To wallahi daidai muke dake, Zaki san kin shigo cikinmu wallahi sai mun......" " Wayyo mama marata!!" Sultana ta fad'a da karfi, kallonta nayi ta kashemin ido d'aya na mata godiya a zuciyata, "Ku tashi kuje kuma ku kawo Mana sakamakon nan mu gani"   tashi mukayi muka fita kursum na binmu kaman jela Mota muka shiga ta shiga itama muka nufi asbitin da nake internship, bayani na musu zanyi fertility test ne likitan ya rubutamin muka je muka fara da blood test Wuni mukayi a asbitin a jagwalgwalani nan a jagwalgwalani can, daga 'karshe akace sai bayan sati d'aya naje na kar'ba Ko da na koma surutu suka dingayi Akan ina sane na'ki kawo result d'in, dole dai suka ha'kura suka barni. Satinnan gaba d'aya banida sukuni, mafarke mafarke nake marasa dad'i akan haihuwa abin har ya fara sani rama. Ranar da sati ya cika hajiya da kanta tazo gidana akan yau ne fa zan kar'bo result d'ina,ji nayi banason kar'bowa haka kawai. Tunda muka d'auki hanya gabana ke fad'uwa, kafin muje 'kwalla ta cika idona, rarrashina saleh yake amma kwata kwallta bana ji. Muna isa likitan yacemin "Bilkisu saki jikinki mana, ko bakyajin dad'i ne?" " Doctor menene result d'ina ya nuna " na tambaya muryata na rawa Zama doctor d'in yayi ya mi'komin takarda yace " I am sorry to say this, but bilkisu you have cervical factor of infertility " *dedicated to all infertile women on Earth, Allah kad'ai yasan yanda kukeji a zu'katanku saidai komai ya faru ga bawa alkhairi ne, fatanmu Allah ya baku ikon cin wannan jarrabawa ta rayuwa😭😭😭😭😭😭😭😭 heart you all* 15 "doctor to me hakan yake nufi?" " Yana nufin cervix d'inta yana da matsala, mucus d'in da cervix d'in ke producing yana kashe sperm ne kafin ya kai cikin mahaifarta " Kaina juyawa yakeyi ina zaune, 'kafafuna gaba d'aya sun d'auki rawa, wasu zafafan hawaye ke zuba daga idona, dafe 'kirjina nayi jin tamkar zuciyata na barazanar fita. 'ko'karin fad'uwa daga kujerar da nake zaune nayi Saleh ya ri'koni cikin sauri tareda kujerar, cikin tausayawa likitan yace "Kaita waccan kujerar ta zauna" cushion chair ce nara tsayi, zama nayi ina maida numfashi tareda zubda hawayen da bana tunanin zai tsaya nan kusa. "To doctor yanzu magani za'a bata kenan ko me?" " Eh to gaskiya matsalarta bata da magani, domin da dama daga mata masu matsalar haihuwa suna fama ne da wannan matsalar, saidai ayi mata dashe na IVF amma bazata iya d'aukan ciki da kanta ba " Cikin sauri saleh yace " To yanzu a ina ake IVF d'in muje? Nawa akeyi " " Ana IVF anan kano amma gaskiya cikin 80% ko 20 ba'a samu an dace ba, saidai kuje Dubai wanda sunfi suna a harkar IVF d'in " " Nawa akeyi a Dubai d'in? " Wata takarda ya zaro ya mi'kawa Saleh yace "Wannan asbitin da suka fi suna a Dubai d'inne wajen dashen, akwai website d'insu da zarar ka shiga zaka samu duk bayananan da kakeso sannan akwai wani abu d'aya, still dai ko da cikin bazata iya haihuwa da kanta ba saidai a Mata CS a curo abinda ke cikinta" Godiya saleh ya masa bai tambayesa dalilin da bazan iya haihuwa ba, ni kaina bazan iya sake d'aukan wani information ba bayan wannan ba'kin labari. Kwata kwata bana ganin abinda ke gabana domin hawaye ke wankemin fuskata, Allah kad'ai yasan abinda nakeji a zuciyata, babu abinda nake hange sai Huda, Yana ri'ke dani muka isa mota, bud'ewa yayi ya sanyani shima ya shiga ya zauna, a wurin ya fara browsing asbitin da aka bamu " Kai 40,000 dirham? Bari muga nawa ne" Converting yayi naji yaja wani numfashi tareda salati, can 'kasan ma'koshinsa yace " Miliyan 4?" A take anan na sake cire rai da samun haihuwa, nasan a miliyan hud'unnan babu kud'in mazauni da transport da sauransu, a 'kalla sai an samu miliyan 5 zuwa shida zamu samu haihuwa wanda nasan mijina bashida su bashida dalilinsu Tunanin abinda zan tarar a gida nakeyi, idona a rufe Ina zubda hawaye naji yayi parking ya bud'e min 'kofa tare da kamo hannuna, fito dani yayi naganni a gida. Tamkar wadda tasha ta bugu haka nake tafiya, sallama yayi ya tsaya daga waje na fad'a palo, a kujera na samu mama babu shiri na zube a cinyarta ina tsananta kukana, cike da damuwa tace " Bilkisu menene? Lafiya? Me ya faru " Sallama saleh ya sake dokawa mama ta yafa mayafinta ta masa iso, bayan sun gaisa yace mata "Mama asbiti muka je ne akai mana gwajin haihuwa, to Allah ya 'kaddara bilkisu tana da wata 'karamar matsala, na rasa ta yanda Zan rarrasheta shine na kawo miki ita " " Allah sarki babu komai, karka damu zamuyi magana da ita " Tashi yayi ya fita naci gaba da tsananta kukana, kukan da nake tamkar ma 'kara hurawa zuciyata ruwa akeyi, a ta'kaice gaskiya 'yan uwan Saleh ke fad'a ni juya ce, ko yaya rayuwata zata kasance ba tare da haihuwa ba? Gyaran murya mama tayi ta fara min nasiha: " Haba bilkisu ki kasance mai tawakkali mana, Allah ba wai baya sonki bane ya jarabceki ta wannan hanyar, Allah yana sonki ne kuma yasan a cikin dubban bayi ke kad'ai zaki iya jure wannan jarabawar shiyasa ya baki ita" " Bilki na sani rashin haihuwa bashida dad'i, domin ni kaina victim ce, shekarata 13 a gidannan kafin Allah ya bani haihuwar jabir, babu irin maganar da banji ba, duk zaman lafiyar da nake da kishiyoyina saida suka gorantamin, 'yan uwan mijina sunyimin ki godewa Allah da bakida matsala da dangin miji" Tashi nayi na zauna nace " Wallahi hajiya tamkar shed'an haka yan uwan mijina suka tsaneni, fad'a miki ne kawai banayi domin karki damu, tsangwama Babu wadda ban gani ba, tun ranar da aka kaini suka fara sanyani zubda hawaye, tunda kuwa wadda akai aurenmu tare ta samu ciki na fara fuskantar matsala akan haihuwa, sukace ina sane na dakatar wannan ya wuce, yanzu ita sultana tayi haihuwa ta biyu shine suka sakani gaba dole nayi gwajin haihuwa, mama labarin da nake d'auke dashi shine labarin da suke so, yanzu haka jirana sukeyi na koma suga sakamakona shine dalilin da ya sanya Saleh ya kawoni nan, mama shikenan bazan ga jinina ba har na mutu ko? " " A'a bilki kad'an da ikon Allah kiga kin haihu kema kamar kowa saidai idan mahaifarki ce ta lalace duka shine zaki cire rai" Bayanin matsalata nayi ma mama tayi shiru sannan tace " To shi nawane IVF d'in? Idan bai gagaremu ba ba sai mu biya maki ayi ba?" " Mama miliyan hud'u ne, banda kud'in jirgi da na abinci da mazauni da sauran kayan bu'katu " " Bazata gagara ba bilki, kinada kud'in gado da yawa sannan kinada dangi masu hali, yanzu ana fad'a cikin ikon Allah zakiga an harhad'a miki ki cire damuwa, idan zaku bi shawarata ku nunawa dangin mijinki bakida wata matsala, da zarar kud'in ya had'u sai ku 'kir'kiri tafiyar aiki daga nan ayi abunda za'a yi ki dawo da cikinki ba shikenan ba? " Nasan mama ta fad'i haka ne kawai domin ta kwantarmin da hankali, cigaba tayi da rarrashina tace " Duk lokacin da damuwa tayi miki yawa ki dinga tuna ayar 'kur'ani da Allah yace. " _waman yattaqillah yaj'al lahu makhraja, wa yarzukhu min haithu la yahtasib, waman yarawakkal alallahi fahuwa hasbuh,innallaha baligu amrih, Qad ja'alallahu likulli shai'in 'kadra_ " Tabbas wannan ayoyi waraka ne, a take naji zuciyata ta fara sararawa da mama ta tunamin da wad'annan ayoyi, Allah zai kawomin mafita ya kuma azurtani ta inda banyi zato ba, dukda haka dai wannan rad'ad'in na rashin haihuwa yana cikin raina. Bawa mama labarin irin rayuwar da nake ciki nayi, fuskarta 'karara ta nuna tausayawa gareni saidai bata furta hakan ba, tacemin " Ai kad'an kenan daga jarrabawar gidan aure, kowa da kalar tasa, wata zakiga mijin ne baya sonta amma danginsa kamar su cinyeta, wata kuma gaba d'aya da mijin da dangin basa yinta, wata Allah ya jarrabeta da haihuwa amma babu wadatar da za'a ciyar da 'ya'yan, kowa da tata jarrabawar kiyita addu'a Allah yana sane dake da matsalarki, komai watarana zai sama labari kina murmushi Zaki dinga bada labarin abunda ya faru dake a baya" Na jima a gidan mama tana bani shawarwari da adduo'in da zan lazimta, sai yamma lilis Saleh ya zo ya d'aukeni, muna shiga mota yacemin. " Banaso mu nunawa 'yan uwana kinada wata matsala, da ace inada hali da babu mai jin matsalarki, bayan wani lokaci muje ayi miki wannan dashen mu dawo, amma my boo banida halin fitar da miliyan biyar zuwa shida, da ace d'aya zuwa biyu ce zan iya tattarowa cikin watanni amma......" " Karka d'aurawa kanka my boo-boo, munyi magana da mama tace nayi maka magana, nasan 'yan uwana da zarar na sanar musu cikin 'kan'kanin lokaci zasu had'amin " " A'a bilkisu, bazan kar'bi komai daga hannun 'yan uwanki ba " Abun ya dameni nace " Meyasa bazaka kar'bi kud'i daga 'yan uwana ba? Boo-boo idan muka zauna haka kowa sai yaji kuma 'yan uwanka bazasu barni da rai ba suka san inada matsala, ka sani bazasu taimakamin da kud'insu ba ko da kuwa ace mutuwa zamuyi daga ni har kai " " Boo abinda nake nufi shine, abinda mukeso mu haifa dani dake munaso mu kirashi d'anmu ne, inaso na kasance uba ga duk abinda zamu haifa, idan har na nad'e hannuna aka taimaka miki daga danginki sun fini iko da abinda zaki haifa, kuma banida zuciyar kallon wannan abun na kirashi da d'ana, inaso nasha wahala yanda kowanne uba zaisha akan d'ansa, muyi ha'kuri bilki har na samu arzi'ki na kaina mu haifi abinda zamuyi alfahari dashi muyi tin'kaho da cewar mune iyayensa " Shiru nayi domin gaskiya ne zancensa, duk son dangina dani idan har Saleh ya nuna ya fisu iko da abinda na haifa to tabbas anan za'a fara samun matsala Yana driving gabana na fad'uwa, hasbunallahu nake maimaitawa har muka isa gidan. Ai kamar jiranmu sukeyi duk sunyi cirko cirko a 'kofar gidana, na rasa wasu irin mutane ne wad'annan, magrib na gabatowa su nufi gidan aurensu sun tsaya lalata auren wasu. Ina fita daga motar Usman ya nufoni da hudaba hannunsa, cikin kuka ta mi'komin hannu tace *"MAAMA"* Wani abu naji ya sokeni a cikin zuciyata, before na gama recovering ta sake ambatar "maama", Kar'barta nayi na sanyata a kafad'ata, d'ago kanta tayi ta kalli fuskata ta sake cewa " MAAMA" sannan ta hau gwarancinta, tana gamawa tayi luff a jikina, Bansan lokacin da Hawaye ya zubomin ba, banda huda yarinya ce zan iya cewa da gayya tayimin haka, huda bata ta'ba ambatona da wani suna ba sai yau, ban kuma ta'ba lura da cewar huda kallan uwa take min ba sai yau, ban ta'ba fahimtar cewa sha'kuwarmu da huda tayi nisa har ta wuce 'ka'ida ba sai yau, ji nake tamkar ana tsaga 'kirjina ana sake cusamin soyayyar huda bayan ta ambaceni da maama, tsananin tsoro ne ya kamani na 'kan'kameta a jikina ina hawaye. " Munafuka, sai ku fito kuyima mutane bayani, tunda kike zubar da Hawaye Allah ya toni asirinki sai ku fad'a muji, tasha 'kwayoyi sun lalata mahaifarta ko?" Kursum ta fad'a Tana bubbuga 'kafa Godiya nayi ga Allah da hankalinsu baya Kan huda da ta kirani da maama, shafa Kai saleh keyi cikin takaici da ba'kin ciki, wani irin kallo ya jefomin na kin 'bata mana aiki Kwata kwata bansan na fito da result d'ina ba saida naji an fizgeshi, gabana ne ya fara fad'uwa ganin yaya maimu ce ta kwace takardar, karantawa tayi ta bud'e wayarta alamun browsing abunda ta gani, tamkar wadda taga alkhairi ta rangad'a bud'a tareda tafa hannu ta nuna ni tace " Dama ance rana dubu ta 'barawo Rana d'aya tak ta Mai Kaya, Ramin 'karya dama asalinsa 'kurarrene, gashi dai result baya 'karya ya kuma nuna ke juya ce ba macen da zamu mora bace, dan haka kai saleh sai ka 'kara aure " Dawowa gefena saleh yayi ya ri'koni yace " Ni bazan iya zama da mata biyu ba, bilkisu ita kad'ai ce matar da Zan zauna da ita a rayuwata" " To kuwa saidai ka saketa ka auro wata, Dan bazaka ta'ba zama da macen da bata haihuwa ba, ni bana haihuwar fanko Kuma Babu d'ana da zai zauna da mace fanko, ka saketa ko ka 'kara aure " Hajiya ta fad'a tareda matsowa dab damu, turani bayansa yayi yace " Hajiya kiyi ha'kuri, da ace umarninki domin Allah ne Zan miki biyayya, amma kina tilastamin nayi aurene saboda bilkisu ta tozarta kuma iya ganina bilkisu bata miki komai bayan biyayya, hajiya kece babba ke ya kamata ki dinga tsawatarwa su maimuna idan suna muzgunawa bilkisu amma bakya yi, munyi magana da likita matata zata iya samun ciki ta haihu kamar sauran mata, saboda haka zanci gaba da zama da ita kad'ai bazan iya bin umarninki na 'kara aure ba, kuyi ha'kuri" Tafa hannu maimu keyi tana ri'ke baki, nunani tayi da yatsa tace " Babu mamaki, an maka barbad'e an shanyeka, har zaka kalli mahaifiyarka ka fad'a mata magana, saboda mace ta shanye tunaninka da hankalinka an kaika wajen boka saboda baka san ciwon kanka ba, to ka sani mune Daidai da ita kuma wallahi zaka zo ka samemu, ke kuma ko kinso ko kin'ki sai kinbar gidannan tunda ba gidan ubanki bane".. 16 Reult d'in tayi tareda tsaki ta bar wurin, saleh kusa yake a jikinsa kamar zasu cinyeni, d'aya bayan d'aya suka bar wurin. Kasa d'aga ido na kalleshi nayi cikin Kuka nace " Kayi ha'kuri " Shafa bayana yake cikin rarrashi yace " Haba kukan kuma na mene? Please banason ganin hawayenki my boo, zan iya handling 'yan uwana ki kwantar da hankalinki bazan ta'ba bari su cutar dake ba ko yaya " Kar'bar Huda yayi muka shiga cikin gida, zanina da mayafi na cire zan fad'a kitchen yace " Karki d'aura komai a 'koshe nake, nasan kema bakyajin yunwa, saidai ko Huda ". Jiki babu 'kwari nace " To bari na saka mata noodles" " A'a zauna na saka mata " Kallonshi nayi na turo baki nace " Da can kai kake dafa mata? Banason wani extra attention saboda wannan abun da ya faru, muci gaba da zama normal karka fara abinda kasan bazaka d'ore ba, ko kuwa ka ta'ba tayani girki " " Na ta'ba tayaki mana " " A'a kana dai sakani 'kona abinci " Dariya yayi yace " To naji jeki d'aura mata abincin ki dawo " Juyawa nayi na nufi kitchen, ina shiga ta 'kwala min Kira, ko sau nawa Huda zata kirani da maama bana tunanin zan saba, indai ta fad'a sai naji wani iri a raina. Shigowa sukayi kitchen d'in na korasu dan nasan hali, ban fita ba saida na gama noodles d'in na zuba mata na fita da ita Bata bari na bata ba ta saka hannunta ciki duk ta 'bata jikinta, wanka nayi mata nima nayi na shirya cikin riga da skirt. Rigima huda ta fara na goyata ganin magrib ta gabato na zauna na zuba tagumi, wani kad'aici naji ya fara shigata tunanin abinda ya faru ya dawo sabo. Anya ba mistake akayi wajen bani result d'in ba? Anya ba irin abubuwan da nake gani a film bane daga baya kuma Allah yayi ikonsa? Maganar yaya maimu ce ta fad'omin, to idan har auren zai haifamin kwanciyar hankali me zai hana yayi? Matu'kar zasu bar rayuwata ta sarara ni zan iya amincewa da auren nasa domin na gaji, furucinta ya tsorata ni da tace zan ga abinda zasu iya. Tashi nayi na d'auko result d'in na sake dubawa, sunana ne da komai nawa, ga test d'in da akamin nan a jere kowanne da abinda aka samu. Hawaye naji yana neman zubomin, dama haka mata marasa haihuwa suke ji? Duk yanda zan misalta yanda nakeji a raina bazai misaltu ba, ta'kamar mace a rayuwarta itace zuri'arta, na dad'e ina ma rayuwata plan da 'ya'ya masu yawa, na dad'e ina mafarkin ganinan cikin 'ya'yana 7-8 muna hira, na dad'e ina hasashen gani nan na fita da 'ya'yana muna tafiya, na shiryasu cikin kaya iri d'aya, ashe kana naka ne Allah na nashi. Hannu naji an sanya ana gogemin hawayen da ya zubo, d'aga kaina nayi naga sultana, cikin sauri na goge hawayen tareda ajiye takardar gefe. D'aukan takardar tayi tace " Bilkisu me arahar hawaye, kedai ki sanyawa ranki damuwa ba komai bane, yanzu shima awon cikin kuka yake sanyaki ne ko me? Ko kuma......." Dakatawa tayi ta d'ago ta kalleni ta sake kallon takardar, mi'komin tayi tace " Me takardarnan take nufi " Goge fuskata nayi nace " Su yaya maimuna basu fad'a miki ba kenan " " A'a, ba wanda ma ya shiga part d'ina a cikinsu, tunda suka cemin ke suke jira suka ga zan hanasu zuwa suka fice, amma me ya faru kinsa gabana ya fara fad'uwa " Bayanin matsalata nayi mata, dafe kanta tayi tace " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya Allah ya akai haka ta faru dake? Yanzu kenan bazaki ta'ba haihuwa ba ko me?" " Eh haka dai suka ce, indai ba dashe za'a min ba bazan ta'ba haihuwa ba " Shiru tayi ta zuba min ido, d'auke kaina nayi nace " Ki dena kallona haka bana so" " To bilki bansan me zance miki bane, wallahi kaina duk ya 'kulle bansan ya ake rarrashi a irin wannan yanayin ba, saidai nace Allah yasa hakan ya zame miki mafi alkhairi kiyi ha'kuri, nasan 'yan uwana zasu kafa miki 'kahon zu'ka akan hakan amma dan Allah karki saka hakan a ranki, nasan sunce ya 'kara aure ko? " " Eh " Tashi tayi ta dawo kusa dani tace " Bilki, dan Allah ko ta yaya karki bari yayi aurennan, wallahi idan yayi aurennan kina cikin matsala, nasan su waye 'yan uwana sarai, nasan kuma irin macen da zasu aura masa, bilkisu ba munafurci ba amma wallahi bana fatan kiyi kishi da d'aya daga cikin danginmu " Jan numfashi nayi ba tare da nace mata komai ba, mutanennan danginta ne, duk yanda zata soni matar tsohon saurayinta bazai Kai son da zata yiwa danginta ba Tashi Huda tayi na saukota na ajiyeta tareda kar'bar Ahmad, shafa 'kafarsa huda tayi ta kalleni tace " Maama " Kallonta mukayi a tare sultana ta kalleni tace " Kai, ikon Allah dama yarinyarnan tana magana? " Mamaki ne ya kamani nace " Huda tana magana mana, ko nace gwaranci,amma d'azu naji ta fara cemin maama na d'auka ma ke take kira haka " " Tabd'i, to ni huda banda ihu me take min? Idan ta kwana wajena wallahi bana iya bacci, idan kika fita school ma ta dinga kuka kenan saidai idan ta gaji tayi bacci " " Laifinki ne ai, bakya kula da huda yanda ya kamata " Sunkuyar da kanta tayi tace " Bilki wallahi ni kaina bana jin dad'in hakan kuma nasan ban yiwa huda adalci ba, kinsan Allah kwata-kwata ji nake kaman ba ni na haifi huda ba, kuma ban fahimci haka ba sai da cikin ahmad, kinga cikin huda banyi d'okinsa kaman na Ahmad ba, wallahi tunda huda ta fita daga jikina naji kaman an ciremin 'kaya, bani da sha'kuwa da huda yanda ya kamata uwa ta sha'ku da 'yarta, idan Huda tana wajenki mantawa nake da ita, ni bansan ya zanyi ba " " To ai sultana tun farko baki d'auko matakin zama uwa ga sultana ba, dukda nasan da cikin ahmad da ya sakaki gaba, amma huda fa tun tana wata biyu kika fara fita kina barmin ita, wata shida kika yayeta kuma a wannan lokacin shine yaro yake fara fahimtar uwarsa, to lokacin kika yakiceta daga jikinki, bata taso ta sameki a uwa ba, kema kuma lokacin kina fama da kanki , amma dukda haka da dai kin jata a jikinki lokacin da take bu'katar ki " Cije baki tayi tana kallon huda, tashi tayi zata tafi nace " Bazaki tafi da ita ba? " Langa'bemin wuya tayi tace " Idan ba damuwa ta kwana a wurinki kawai " Amsawa nayi da to na d'auki huda muka raka sultana. Washegari muna breakfast sai ga hajiya ta shigo, tana zama naji abincin ya fita daga raina, zuba mana ido tayi har na kwashe kwanukan na koma na zauna Kallona tayi tace " Tashi zamuyi magana da d'ana " Tashi nayi na shiga kitchen na fara wanke wanke, muryarta na jiyo tana cewa " Saleh, nazo na baka umarni ne ka 'kara aure, duk namiji me hankali bazai zauna da mace mara haihuwa ba, duk d'an adam yana so yaga zuri'arsa, kuma cutarwa ce ace bazaka yi aure ba matarka kuma tana juya, yanzu haka zaka mutu ba tare da yaga zuri'arsa ba, idan har matarka zata hanaka aure to bata sonka tsakani da Allah, aurennan idan kayi ita kanta zata amfana, ko ba komai zata ga 'ya'yan mijinta " " Hajiya nifa bilki bata hanani aure ba, ni ne naga rashin dacewar hakan, hajiya bilki zata iya haihuwa, likitan ya fad'a mana za'a iya Mata dashen haihuwa a 'kasar waje kuma zata haihu, yanzu haka ina tunanin had'a kud'in ne da za'ayi hakan, hajiya bazan iya zama da mata biyu ba saboda bazan iya adalci ba " " To saidai ka saki bilkisu, Kai kenan da d'a d'aya zaka zauna a rayuwarka? Ko kuma duk lokacin da kuke bu'katar haihuwa zaku dinga zuwa ne ana mata dashen? Kaga na gaji da halayenka akan matarnan, tunda ka aurota ka dena kallona a matsayin uwarka, ka fara manta cewa ni na haifeka, to a yau umarni nake baka wanda dole kabi, dole kayi aure ko kana so ko baka so, bazan zauna da juya a matsayin sirika ba, kaje ka sami 'yar gidan habiba munyi magana ku daidaita " Fitowa nayi zan tafi sama yace " Hajiya 'yar gidan habiba kuma? Bazan iya auren yarinyarnan ba hajiya, bata da halaye masu kyau bata ganin darajar mutane, hajiya dan Allah ki barmin aurena muna zaune da matata lafiya, hajiya ba dai jika ba? Zata haifa miki bansan meyasa bakwason bilki ba duk biyayyar da take muku " Harzu'ka hajiya tayi tace " Ubanka, akan mace kake fad'amin magana? Ita zata kalli uwarta ne ta fad'a mata haka? An cuceka an had'a ka da mace juya, na fad'a 'karara bana son matarka bana 'kaunarka, kuma duk d'a na gari zai kasance Yana son abinda iyayensa suke so yana nisantar abinda basa so, ka sani, idan har bazaka yi aure ba kuma bazaka rabu da wannan yarinyar ba to ka ficemin daga gida, banason ganinka bazan kuma zauna da d'a wanda baya bin umarnina ba bayan d'awainiyarka da nayi na shekaru sama da ashirin, ka fice ka barmin gida kaje ka zauna da matarka duk inda kaga dama, karka sake kallona a matsayin uwarka kaje ka zauna da matarka ta zamar maka uwa " Ficewa tayi na sauko na zauna gefensa, kama hannunsa nayi ina murzawa a hankali, ajiyar zuciya ya sauke nace " Kaje ka bawa hajiya ha'kuri, idan har auren zai saka ta sauko dan Allah kayi kawai, boo-boo na ba abinda yakai mahaifiyarka a rayuwarnan, ka tuna fa shekaru da dama ta d'auka tana wahala dakai, mahaifinka ya rasu ya barku a hannunta ita taci gaba da wahala daku, yanzu da kayi hankali ka kawo 'karfi ka nuna Mata kana appreciating abinda tayi maka, ta baka umarnin aure a baya ka'ki, yanzu kayi mana fushin iyaye masifa ne, boo-boo na ban taso na Sami mahaifiyata a raye ba, amma inada tabbacin tayi min umarnin rabuwa dakai zan bi, bazan so kaina nace ka bijirewa hajiya ba, ka bata ha'kuri kuma kayi auren wallahi har zuciyata na amince ko wacece ka auro " Muryarsa har rawa take saboda 'bacin rai, hannunsa biyu ya sanya ya ri'ke hannuna yace " Ban bijirewa umarnin hajiya saboda komai ba sai domin tayi hakan ne domin ki cutu, mahaifiyata ce nasani, amma ya kamata taso abinda nakeso, boo ki duba fa, kallon idona tayi tace bata sonki, boo kinsan yanda nakeji a raina da furucin da tayi na bata 'kaunar abokiyar rayuwata? " " Come on.....'bacin rai ne ya saka ta fad'i haka na sani, amma dai ka bata ha'kuri, idan muka bar nan ina zamu je? Kana ganin hankalinmu zai kwanta ne? " Numfashi yaja ya juyar da kansa, hannu na sanya na juyo fuskarsa gareni tare da sauke murmushi, shafa fuskarsa nayi nace " No matter what ina tare dakai mijina, kuma inaso kaima komi rintsi karka bijirewa mahaifiyarka, zaman lafiyarmu shine samun amincewarta, I love you boo-boo na " Hannunsa ya d'aura kan nawa dake fuskarsa ya sakarmin murmushi mai d'auke da abubuwa da dama, kwanciya nayi a kafad'arsa ina karanto masa kalamai masu kwantar da hankali " Washegari na fita asbiti tun kafin na dawo sultana ta kirani tace tana son magana dani, inata tunanin abinda zata fad'amin. Da hanzarina na shiga gida, a bud'e naga gidan na shiga inata mamaki, sakin baki nayi ganin palon cike da tarkace. Kayan Huda ne ko Ina a d'akin, ga gadon jarirai, ga baby walker, akwatuna biyu, kayan wasa cike da gadon ga kuma jakunkuna da cereals d'inta Huda kanta wata kwalliya ta daban aka mata cikin riga da wando, rigar takai gwiwarta fara 'kal sai wandon tight ne light pink, gashin kanta an mata two babies da pink ribbon, takalminta kuma fari, tana ri'ke a hannun usman sultana Kuma na zaune gefensa. " Zauna mana kin zuba mana ido, waye sabo a cikinmu hudan ko kuma mu?" Ina zama Huda ta zamo daga cinyar usman ta taho wurina, had'a Ido sukayi usman da sultana sukayi murmushi, rad'a tayi masa ya gyad'a kai Kallon saleh nayi yayimin alamun baisan menene ba, gyaran murya sultana tayi tace " Da farko dai bilki ina baki ha'kuri akan abinda ya faru dake, nasan kinada 'karfin zuciya shiyasa ma Allah ya miki wannan jarabawar, Abu na biyu ba tareda 'bata lokaci ba Zan sanar miki dashi amma kafin na fad'a akwai dokoki, bakida ikon cewa a'a, idan kinsan ba amincewa ce zata fito daga bakinki ba to kiyi shiru " " Bilkisu tunda na haifi huda Kika zamar mata uwa, kece komai nata ni kawai haihuwar Huda nayi, amma idan za'a sakamin wu'ka bansan lokacin da take bu'katar abinci ba, bansan lokacin baccinta ba bansan komai akanta ba, bilki ina jin kunyar na Kira Huda 'yata domin bamuda sha'kuwar uwa da 'ya, ranar da naji Huda ta kiraki da maama kwana nayi ina tunani a raina, anan na gane Huda aya ce gareni, ba kaina na haifawa ita ba ke na haifawa, huda bata ta'ba zuwa hannun wani a cikin ni da ya usman ko yan uwana ba tareda tayi kuka ba, ke kad'ai Huda ke amincewa ta zauna dake, saboda haka muka yanke shawara ni da ya Usman, bilki mun baki Huda halak malak, har abada na tashi daga Mahaifiyar Huda ke kin zama mahaifiyarta, idan so samu ne ko girma huda tayi banaso tasan nice mahaifiyarta, wallahi da zuciya d'aya na baki ita har abada " *😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭I don't know what to say har Raina wannan kyautar ta tabani* *NEXT UPDATE: SATURDAY INSHA ALLAH,KU TAYANI DA ADDU'A INADA TEST* 17 Zuba mata ido nayi na rasa me zanyi, ban sani ba farin ciki nake ko ba'kin ciki? Tabbas zan fi kowa farin ciki da samun Huda a matsayin 'ya, amma ta yaya dangin sultana zasu kar'bi hakan?. Runtse ido nayi tare da d'aga kaina sama, 'kwalla ce ta zubomin na goge cikin sauri ganin idon Huda a kaina. " Kar kiyi kuka ki sanya 'yarki damuwa mana " Ambaton 'yata da tayi ne ya karyar min da zuciya, kuka sosai na saki, 'kirjina naji yana d'aurewa gaba d'aya na rasa inda zan saka kaina saboda emotions, sultana tayi min ba zata. Gefena sultana ta dawo tana rarrashina, zubamin ido Huda tayi take idonta ya ciko da 'kwalla. " Ki dena dan Allah bilki karki saka Huda kuka, kinsan ba'a so kana nunawa d'anka damuwarka ". Shesshe'kar kuka nake tareda sha'kuwa nace, " Dan Allah ki bari sultana, ki dena fad'amin haka ba komai zuciyata zata iya d'auka ba ". 'Daukan Huda tayi ta ri'keta a hannunta, mi'komin hannu huda tayi ta fara kuka, d'aukanta nayi tare da danne kukana, kwanciyar da huda tayi a jikina saida na jita daban, na d'auki kusan mintina biyar kafin na dawo hayyacinta, duk hankalinsu na kaina na kalli sultana nace " Meyasa kika min wannan kyautar sultana? Kina tunanin Zan kar'beta da zuciya d'aya ba tare da gudun faruwar wani abu ba? Sultana kyautar d'a ba 'karamar kyauta bace ko 'yan uwana ba kowa ne zai iya bani ba, kuma 'yarki ta fari? Dan Allah sultana kar mu fara abinda bazamu iya 'karasawa ba, kar gaba kizo kice na baki, sultana ko kin bani danginki bazasu bari ba ". Tsaki taja tace, " Bilki idan akwai wadda zance ta haifarmin Huda kece, nasani dole zakiyi kokonto akan hakan saboda abinda 'yan uwana ke miki saboda ni, amma wallahi abinda suke yi ba dan ni bane kawai son zuciyarsu ne, na sani saleh tsohon saurayi na ne kuma na soshi kaman zan mutu ". Usman ta kalla tace, " Kayi ha'kuri yayana amma inaso na goge zargina daga zuciyar bilkisu ". Juyowa tayu gareni tace, " Bilki nasan 'kaddara na kuma yarda da ita, na amince da auren ya usman ne kawai don huce takaici, amma yanzu na godewa Allah domin dalilin auren ya usman na sami gata da soyayyar da inada tabbacin da saleh na aura bazai bani ba, wallahi bilki da zuciya d'aya nake sonki tunda na tabbatar da zuciyarki a tsarkake take, furucin da nayi kwanaki saboda kawai hankalinsu ya kau daga kanki ne, amma hakan bai samu ba, bilkisu idan ban baki Huda ba cutar da ita zanyi, wallahi kinji na rantse tunda nayi cikin huda bana son cikin, laulayin da nayi takaici ne duk ya cikani, ranar kuwa da na haifeta kamar an rabani da 'kaya, ban san isharar da Allah yake son isarmin ba, amma babu soyayyar huda a raina kaman yanda uwa zata ji ga 'ya'yanta, nayi 'ko'karin naga naso huda kamar yanda sauran iyaye ke son 'ya'yansu amma jinta nake kamar bare, ke nifa banda naji zafin haihuwarta zan iya rantsuwa ba 'yata bace, Huda 'yarki ce tunda na haifeta kike bata kulawa, Huda dake ta dace ki taimaka ki kar'beta dan Allah ko na sami nutsuwa a raina, na miki al'kawari ko zan rasa duk 'ya'yan da na haifa bazan sake kallon huda a matsayin 'yata ba, dangina kuma ki barni dasu ni nasan yanda zanyi dasu, amma naki dangin ki musu shela su fara kiranki da maman Huda, har rubutu ma munyi saboda tsaro gashi zaki sanya hannu a takardarnan ". Bugaggiyar takarda ta mi'komin a ciki an rubuta, _ Ni Usman Abubakar, tareda matata sultana jibril, mun bawa saleh abubakar da matarsa kyautar 'yarmu surayya abubakar, kyauta ta har abada, bisa ga sharad'in zata ri'keta amana, bazata cutar da ita ba_. Wurin signing na iyayen aka bari sannan aka sake rubuta. _Ni Usman abubakar tare da matata bilkisu Ibrahim munyi al'kawarin ri'ke surayya abubakar bisa amana, bazamu nuna mata banbanci ba bazamu cutar da ita ba, komai wuya komai dad'i bazamu maidata ga iyayenta ba_. Daga kai nayi na kallesu na saka hannu a takardar, kar'bar takardar tayi ta mi'kawa usman tace. " Gobe sai kayo photocopy guda biyar haka ko? A bata d'aya a kaiwa lawyan d'aya, sauran mu ajiye saboda halin 'bata ". Cikin mamaki nace, " Me ya kawo lawyer kuma? ". Murmushi tayi tace, " Saboda iyayenmu mana, dole sai mun danganta da kotu, yanda ko sun 'ki amincewa kotu zata ce musu babu halin hakan ". Shiru nayi sannan nace, " Sultana na kasa furta godiyafa gareki, bansan me zance miki ba, saidai nace Allah ya biyaki da aljanna ya 'kara miki zuri'a masu tausayi da jin 'kai, Allah ya baki zuri'ar da zasu ceceki su sakaki a aljanna ranar 'kiyama ". " Ameen nagode da wannan addu'ar ". Godiya saleh yayi suka fita shi da usman muka hau hirarmu, nan nake bata labarin yanda mukayi dasu akan rashin haihuwata da kuma zuwan hajiya, bani baki tayi hankalina ya d'an kwanta. Tana fita na kira mama na sanar mata wannan babbar kyauta, d'if naji mama tayi sai can tacemin, " Wannan maganar ba ta waya bace gobe zamu zo gidan, ki fad'a min lokacin da kike nan " Fad'a mata lokacin da zan dawo nayi na goya huda tare da d'aukan kayanta na fara kaisu d'akin sama ina jerawa, saida na yiwa komai wuri gadon nata kuma yamin nauyi na barshi saleh ya d'auka Saida na gama shirya kayanta tsaf tukun na sami nutsuwa na zauna ina tunanin sabuwar rayuwar da zan shiga da Huda, ina zaune a gadon d'akin naji sallamar Saleh a palo, sauka nayi na sami fuskarsa d'auke da murmushi Cikin sauri na sauka tareda hugging dinsa, hawayen farin ciki naji ya sauka a fuskata, ha'barsa ya d'aura a kaina yana shafa huda dake bayana. Sauke Huda nayi muka zauna ya kar'beta ya zuba mata ido, kallona yayi yace " Kinga kyautar Allah ko? Dama ance yana azurta mutum ta hanyar da baiyi zato ba, daga ni har ke bamu ta'ba zaton huda zata zama mallakinmu ba amma kalli, cikin mintina kad'an kin haifarmin 'ya, Allah mungode maka " Murmushi nayi na d'aura kaina a kafad'arsa ba tare da nace komai ba, duk kalmar da zan yiwa Allah godiya da ita gani nake tayi kad'an, azumin godiya nayi niyyar yi tare da sadaka domin sune hanyoyin da nake ganin zan fi nuna farin cikina ga Allah. Kamar ance na d'aga kaina, had'a ido mukayi muka sakarma juna murmushi, kwana biyu munyi missing juna saboda damuwarmu ta fara yawa, amma zuwan huda kaman wani sassauci yazo Hannunsa ya sanya ya tallafo fuskata tare da sumbatar goshina yace " Ina 'kaunarki bilkisu, ke kad'ai nake mafarki a rayuwata ina addu'ar Allah ya barni daga ni sai ke sai 'ya'yanmu bana so kowace mace ta sake shigowa rayuwarmu " Hannu na sanya a fuskarsa nace " Allah ya amsa addu'ar ka mijina, Allah ya barmu mu biyu har aljanna " Sunkuyo da kansa yayi tareda had'e goshinsa da nawa, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya sannan ya d'ago kansa, saida ya kawo bakinsa saitin nawa na d'auke kaina tareda cije le'bena " 'daga girarsa yayi yace " Me kenan? " " Aha, abinda nakeso kayi kenan, na dad'e banga ka d'aga girarnan ba, wow I miss it ashe haka kake kyau idan ka d'aga gira?" Kwafa yayi yace " Zan rama ne " Kujerar gefe ya kai Huda dake bacci ya nufoni, da gudu na tashi ina dariya kafin nayi nisa ya ri'ko cikina,d'age 'kafafuwana nayi domin na sakar masa nauyi amma ko a jikinsa. A tsakiyar palon ya kwantar dani tare da yimin rumfa, lumshe ido nayi ina jiran naji kiss naji cakulkuli, dariya nake sosai ina bashi ha'kuri saida nace masa zanyi fitsari tukun ya 'kyaleni Dariyar bata gama sakina ba naji bakinsa a nawa, lumshe idona nayi hannuna na bayansa, hannunsa naji yana shafa kafad'ata zuwa wuyana na tuna da huda, a hankali na bubbuga bayansa ya d'ago yace " Yaya dai " Numfashi nake maidawa na nuna masa huda, d'aga girarsa yayi yace " To ai bacci takeyi, amma kuma kinyi gaskiya, ma had'e anjima " Zumbura baki nayi tareda lan'kwashe 'kafafuwana a kwancen nace " Dama ka saba min haka, aikwa ranar da zan rama bazaka ji sweet ba " " Haba matata sarkin hanzari, kawai na fara kunnaki ne yanzu kinsan button d'in naki sai ayita dannawa ya'ki kawo wuta, amma idan aka kunna da wuri da zarar an danna saidai aga haske " Tashi nayi na kai masa dukan wasa nace " Kai ka sani dai, ba wani button Mai wuyar kunnuwa kai d'inne baka gama 'kwarewa a kunnawar ba, amma karka damu ilmi kogi ne a hankali zaka koya " " Au haka zaki ce? Yarinya tausayinki nakeyi shiyasa amma idan na kunnaki yanzu sai kinzo kina ro'kona " " Bismillah " na fad'a tareda gintse dariyata, cikin hanzari ya kaini 'kasa tareda d'age rigata, hannunsa naji ya fara shafa gefen 'kuguna cikin wani salo na daban, bakinsa ya kai ya sumbaci wurin na cije baki, cikin sauri nace, " Kayi ha'kuri dan Allah, na yarda ka sani " " Tukuna ma dai " ya fad'a tareda 'kara sama da rigata, cikin sauri na ri'ke rigar tareda girgiza kai, domin kuwa na tabbata Yana kaiwa wajennan zan manta da Huda a palon, dariya yayi ya koma kujera ya zauna kaman baiyi komai ba yace " Yunwa nake ji fa " " Sai ka jira na gama recovering " Dariya yayi sosai yace " Ba'a raina 'kwazon namiji, sai a kiyaye gaba " Wayarsa ce tayi k'ara saida ta kusa katsewa ya amsa, yana gama amsawa yace " Hajiya ce, wai gobe zan kaita unguwa " *Kuyi ha'kuri da wannan za'ayi program da ni ne, insha Allah na gobe zaifi wannan yawa* 18 "Nima Mama tace zasu zo bansan da wa zasu zo ba dai, na sanar mata zancen Huda ". " To Allah ya kawosu lafiya, sai ki shirya musu abinci mai kyau ko? Me ya kamata ayi ne? " " Sai azahar zan dawo fa, kaga ba damar na had'a musu wani Abu idan ba yamma zasu kai ba ". " Duk da haka dai ayi musu wani abun ko a siyar musu wani abun Kar tazo gidan namu babu komai ". Amsa masa nayi da to na nufi kitchen na hau girki, saida ya dawo daga masallaci muka ci abincin saidai ina ganin yanayinsa yana cikin tunani, bance masa komai ba domin nasan tunanin fitarsu da Hajiya yakeyi. Sai 8:30 Huda ta farka taci abinci ta hau yi mana hira, gajiya Saleh yayi ya kwanta ya barni da ita ina fama sai bayan 11 na samu tayi bacci. Da wuri na tashi na fara aikace aikacena, tare da Huda muka farka na goyata naci gaba da aikina. 9:30 na gama shirya ta na kaita wurin sultana, cikin sauri na ajiyeta da kayanta nace " Bata ci abinci ba sai kaman 10 haka zataci " " Dan Allah kawai ki tafi da ita Ni wallahi bazan iya had'a yara biyu ba wahala yanzu kuma na'ki kula da ita sai ace dan ba 'yata bace, nidai kinga dama baki ta'ba zuwa da ita asbitin naku ba yau dai ki kaita a saka muku albarka ". Duk yanda naso Sultana ta ri'ke Huda ta'ki sam, da na takura mata sai tace bata son abinda zai had'ata da Huda har shaid'an ya fara Mata hud'uba, dole na tafi da Huda wajen aikina inata tunanin ta yaya zanyi aiki da Huda. Tunda na shiga asbitin Huda ta bar hannuna, abin mamaki duk 'kyuyar da Huda keyi a gida bata yi a asbiti ba, a nutse nayi aikina Huda na hannun mutane har lokacin tashi yayi. Saleh ne yazo ya d'aukeni saida muka yiwa su Mama siyayya tukun muka je gida, a gidan na samesu domin na fad'a mata lokacin da na tashi. Bashi kayan nayi muka nufi sashin sultana, tar'bar mutunci tayi ma su Mama kuma ta hanasu godiya nan dai muka sha hira, Sultana akwai surutu cikin mintina ta saba da su mama da aunty. Kirana Saleh yayi a waya ya sanarmin ya tafi kai Hajiya unguwa. Bayan mun koma part d'ina nake basu labarin irin zaman da mukeyi da Sultana, cike da mamaki aunty tace "kinga ikon Allah, duk wani tashin hankali ta wajenta za'ayi tunanin zuwansa amma abin mamaki zuciyarta a tsaftace, Allah ya 'kara had'a kanku da ita kuma ya kareta daga rud'in 'yan uwanta". Tsaraba suka kawowa Huda na kayan ciye ciye da kayan sawa da 'kyar suka zauna suka yi la'asar sannan suka tafi, wai kar Saleh yazo ya same su. Sai bayan isha Saleh ya dawo, yanayinsa na kalla naga da alamu abun rashin dad'i ya faru amma ban tambaya ba, abinci na kawo ko kallon abincin baiyi ba ya 'kurawa wuri d'aya ido. "Me ya faru ne boo-boo na? Naga kamar kana cikin damuwa". Na fad'a tareda 'kura masa ido, bud'e baki yayi zaimin magana sai ga mama ta shigo da yaya maimuna, bansan me yaya maimuna keyi a darennan a gida ba ki meye matsayin mijinta da yake barinta wannan uban yawon oho, gabana naji ya fad'i na zame na koma 'kasa na zauna. Fuskokinsu babu yabo babu fallasa yaya maimuna tace "ya fad'a miki abinda ya faru ko?" "A'a yana dai shirin fad'a kuka shigo" na fad'a kaina a 'kasa. "To bilkisu ina so ki bud'e kunnunwanki da kyau ki saurareni, idan baki sani ba yau ki sani, mijinki yana cikin matsala babba, fitar da kika ga munyi wajen malami muka je dashi". A raina na ambaci 'subhanallah', tunda aka ce wajen malami nasan anzo min da gagarumar magana. " A 'yan kwanakinnan komai na mijinki yana lalacewa, shagon nasu ma basa samun aiki sosai, gashi kud'i da zarar ya shigo hannunsa kamar wuta ta cinyesu, ke kanki matsalar haihuwarki akwai sa hannu a ciki haka shima matsalarsa hannu aka sanya masa, gashinan a gabansa akayi komai kuma da bakinsa ya furta matsalolinsa". Kallon yaya Maimuna nayi nayi na sauke kaina, wani irin hannu za'a saka masa? Nasan cewa basa samun aiki sosai a shagonsu amma yanzu ai ba lokacin aure bane, kuma rufin asiri dai Saleh yana dashi tunda zamu ci mai kyau musha mai kyau, rashin kud'in da take fad'a ya sanarmin ya fara tara kud'in IVF d'ina ne. "Malam ya fad'a mana cewa akwai wani abokin cinikinsu da suke sana'a iri d'aya shine baya son ci gabansu, saboda anfi sayen kayansu akan nashi shine ya jefe kasuwancin nasu basa samu kema kuma an sanar mana jefeki akayi domin karki haihu dashi ya samu albarka, akwai magunguna da aka bayar suna hannun Hajiya, daga ke har shi zaku dinga zuwa kuna sha a can domin munsan halinki, kuma wannan abun dan amfanin kanku za'ayi ke da shi,". To kawai na bata amsa tare da godiya, bansan me zance mata ba amma maganganunta sam basu gamsheni ba, amma idan ayar 'kur'ani ce zansha domin nayi imanin ba'a cutarwa da ita. Bayan fitarsu Saleh yace "yanzu kin yarda da Maimuna?" Murmushi nayi nace "to boo-boo na ai bazasu cutar da kai ba ko? Idan zasu iya min wani abu kai bazasu iya ba dan haka karmu damu kwana kad'an ne an gama ai". Lura nayi dai hankalinsa bai kwanta ba nace "yau kaga farin jinin da Huda tayi a asbitin mu? Nayi mamaki ma da batayi 'kyuya ba amma fa tayi ciye-ciye, kaga ma abinda su Mama suka kawo mata". Bud'e kayan nayi ina nuna masa ina yaba kayan har saida naga yanayinsa ya fara dawowa tukuna. Washegari 7am sai ga kiran hajiya wai muje musha magani kafin na fita school, haka na d'auki Huda muka fita ko wanka banyi ba. Ina gaida hajiya ta mi'komin wani ruwa a cup, babu alamun magani a cikinsa ba tare da wani tunani ba nayi Bismillah na shanye, saida ta bani abubuwa kala uku duk nasha, biyun dukkansu masu kala ne kaman an zuba wani abun amma hakan nasha a raina inada 'kudurin ba abinda zai sameni sai wanda Allah ya rubuta min. Kasko ta kawo ta zuba turare ta saka a gabana, Ina sha'kar turaren na fara tari harda hawaye, a haka nayi turarennan na gama ta d'auke. Shi kuwa Saleh abu d'aya aka bashi yasha shima kuma ruwa ne fari 'kal, take zuciyata ta rayamin zallan ruwa ne a ciki babu komai, jikina yayi sanyi domin tunanina tare za'a bamu komai, zargin Hajiya ne ya shiga raina zuciyata ta fara rayamin cutar dani hajiya takeso tayi. Na samu na lalla'ba sultana ta kar'bi Huda domin zan kai yamma. Tunda na fita kaina ya fara ciwo,  magani nasha a asbiti na fara aiki amma ciwon kan ya'ki sakina sai ma 'karuwa da yake, idanuna sunyi ja duk jijiyoyin kaina sun bayyana, wajen likita naje ya dubani yace migraine ne ya kamata na samu hutu gobe ma kar nazo aiki. Kasa fita nayi na kwanta na jira zuwan Saleh, a hakan ma ni kad'ai nasan me nakeji a jikina gaba d'aya na had'a gumi. Da 'kyar na taka na fito na shiga mota muka tafi, kaina ke juyawa ji nake kamar ana bugamin guduma a cikin kaina, dafe kan nayi ina addu'ar da duk tazo bakina, bud'e idona nayi naga komai yana juyawa a idona, sunana naji Saleh yana ambata kafin komai ya zama duhu. Farkawa nayi na ganni kwance a kujerar hajiya, warin turare naji nayi saurin toshe hancina ina kallonsu cikin mamaki, d'agoni Saleh yayi yana min sannu daidai fitowar Hajiya, kallona tayi tace "ai alhamdulillahi da aka fara shawo kan abin tun yanzu ashe da matsala take zaune ba tare da ta sani ba, yanzu banda Allah ya kaimu wajen malaminnan ina zamu san tanada matsalar iska? Gashi ana mata turaren kuma ta wartsake, da ana nuna maka kana ganin cutar maka da mata za'ayi gashinan ka gani da idonka". A tsorace naja baya daga gareshi, zuciyata ke bugu cikin sauri, me nakeji Hajiya na ambata? Aljanu a kaina? Gaskiya wannan zancen ban aminta dashi ba me yake faruwa ne? Gaba d'aya na hargitse tsananin tsoro ya shigeni, tashi nayi na nufi hanyar fita hajiya tace "ka ri'kota mana kar ta fita tayi titi". Jiki a sanyaye Saleh ya nufoni, zuciyata tana fad'amin na rungumeshi ko naji sassauci a raina amma yana kusantoni na tsinci kaina da ja baya daga gareshi, murya 'kasa 'kasa yace "Bilkisu ki tsaya mana Babu abinda zan miki, ki kwantar da hankalinki okay? You are all right dear zo nan". Bud'e hannunsa yayi alamun naje yayi hugging d'ina amma kamar an kafeni a wajen, wasu zafafan hawaye naji sun zubomin domin bansan me yake damuna ba, zuciyata na muradin Saleh amma gangar jikina bata so ta kusanceshi, wani ruwa hajiya ta bashi tace ya yayyafamin ya kar'ba babu musu ya zubamin ruwannan, banji wani sassauci ko 'karin ciwo ba. "Ke bilkisu tashi kije gida kai kuma Saleh zauna anan kar kaje ka takura mata". Tashi nayi ba tareda na sake ko waiwaye ba na nufi sashina, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un nake ta ambata a bakina na rasa ma wani irin tunani zanyi. Kafin na shiga na tuna da huda dake wajen Sultana, Kar'barta nayi jikina yana ciwo na shiga gida, kwanciya nayi ina tunanin abinda ya faru, saidai na kasa tunani mai kyau akan hakan. Sai bayan isha Saleh ya shigo gidan, ina zaune ina gyarawa Huda gashinta yayi pecking kumatuna, ji nayi gaba d'aya tsikar jikina ta tashi nayi murmushi da 'kyar. Tare muka ci abinci na saka Huda tayi bacci sannan na tambayeshi me ya faru dani bayan ya d'aukoni, 'ko'karin canza maganar yayi nace "boo-boo na kar muyi haka dakai tun safiya nake fama da ciwon kai sannan kuma naji hajiya tace inada matsalar aljanu, ka fad'amin me ya faru dani". Gyaran murya yayi yace "bayan na d'aukoki naga yanayin fuskarki ya fara canzawa, idanunki sun juya, ina kiran sunanki kuma naji kin fara wani irin kuka da abubuwa, har muka zo gida kinayi sai na shiga dake wajen mama, kuma cikin ikon Allah tana fara miki turarennan kika farka". "Boo-boo na ya zanyi? Shekara ta sama da ashirin a gidanmu ba'a ta'ba samuna da matsala makamanciyar wannan ba sai yanzu? Ina ganin na sanarwa Mama domin wannan matsalar tanada illa sosai". "A'a boo, karki fad'awa Mama hankalinta ya tashi, tunda har Hajiya tana iya shawo kan matsalar alhamdulillah kuma da yardar Allah bazai zamar miki babbar matsala ba". Shiru nayi masa domin bana son jan zancen, amma har ga Allah ban aminta da Hajiya ba. "Haba boo-boo na ki dena damuwa mana, kinsan a kowane yanayi ni zan zauna dake ban damu da matsalarki ba, kai boo-boo na ko maita ce ta sameki  wallahi ni zan zauna dake ba tareda naji wani abu a raina ba, ina sonki a kowane yanayi karki damu, kuma idan ma maganin Hajiya ne baki aminta dashi ba ni dake zamuje mu nemi wani wajen banaso ki fad'awa Mama ta tada hankalinta ne". 'karashe maganar yayi yana d'agoni zuwa cinyarsa, ji nayi kaman na zauna akan 'kaya amma na daure na zauna a hakan, wani hawaye naji yana zubomin na rashin dalili, hannunsa ya sanya yana shafa bayana amma tamkar yana shafa min wuta nakeji, juye juye nake a jikinsa na rasa yanda zanyi da raina sai kuka da nakeyi. Kasa jurewa nayi na sauka nace "boo-boo na jina nake kamar a kan 'kaya". "Afuwa boo, na fahimta dama Hajiya ta fad'amin hakan kiyi ha'kuri kinji? Wataran sai labari mu dage da addu'a kawai" Zama mukayi jugum jugum, a cikin raina babu abinda nake bu'kata kamar mijina amma kuma gangar jikina ta'ki aminta da hakan, sallama nayi masa na tafi sama na kwanta ina juyi ni kad'ai har ya hawo shima Addu'a ya sanyani nayi shima yayi ya shafamin ya kwanta ya rungumeni ta baya, a hankali na janye jikina daga gareshi, can gefe ya matsa ya barni da halina. Ina jinsa ya fara bacci amma ni bacci yayi 'kaura daga idona, Huda na d'auka na rungumeta a jikina ina jin ciwon kaina na dawowa, agogo yana buga d'aya na dare na fara jin 'karan 'kofa, kuma a sanina Saleh ya rufe mana 'kofa, sannan ko da ace ta bud'e ba irin 'kofar da iska zata dinga kad'ata bace. D'ago kaina nayi a hankali naga 'kofar tana yawo ita kad'ai, wani irin 'kara 'kofar tayi lokacin da ta rufe kanta, kwanciya nayi na rufe kaina cike da tsananin tsoro ina jin 'kofar na rufewa da bud'ewa da kanta, ban samu runtsawa ba har saida aka fara kiran sallar asuba wannan 'karan ya tafi kamar ba'a yi ba. Tashi nayi na kasa aikata komai a gidan sai bin kujera, ko breakfast na kasa had'awa balle wankan Huda da nawa wankan, haka ya fita ya barni da kayan bacci a jikina. Kasancewar na tashi da period bana bu'katar na tashi nayi sallah, ina kwance wuri d'aya har Huda ta fara kukan yunwa, cornflakes na had'a Mata da 'kyar jikina har rawa yakeyi tamkar nayi aikin wahala. Komawa nayi na kwanta, kamar wasa babu abinda nakejin dad'insa kamar kwanciya, shigowa Hajiya tayi ta bani magani nasha, a yanda Saleh ya fita ya samemu haka ya dawo ya samemu daga ni har Huda. Tun abu yana 'kan'kani har ya fara zama babba, na koma 'kazama ta 'karfi da yaji cikin kwanaki kad'an, gashi ba sallah nake ba ko alwala banayi balle naji sanyi a raina. Gaba d'aya na dena girki bana wanka sai Saleh ya yimin dole, sai nayi kwana uku banyi wanka ba har wani wari ke fita a jikina, ga period ga babu tsafta, sannan na Saba na kwana hud'u sai gashi na doshi kwana goma. Saleh ko sunana ya ambata sai naji hawaye, idan yana zaune a gida na dinga 'kunci kenan amma da zarar ya fita kamar an sakani a aljanna, shi kanshi ya koma wani 'kazami na 'karfi da yaji. A wannan yanayin hajiya ta sake bijiro masa da maganar aure, ranar tazo bani magani. Kallona yayi yace "Hajiya idan nayi aure bilkisu na cikin wannan yanayin ban mata adalci ba, na zama butulu ko da ace zanyi auren sai matata ta samu lafiya bazan iya aure tana wannan halin ba". Kallona tayi tace "kai har yanzu wannan kake kallo a matsayin mace?kwanan rigarnan hud'u a jikinta babu canji, babu abinda ke tashi daga jikinta sai 'karni, dubi gidanka ka ka dubi kai kanka yanda ka koma, hatta wannan yarinyar dake zuwa ta wuni wajenku ta koma kaca kaca da ita, Saleh dole ne ka sake aure a wannan karon ko fishina ya tabbata a kanka". Dafe kansa yayi yace "Hajiya ki kalli bilkisu a matsayin 'yarki mana, idan ace kursum ce take wannan halin mijinta zai 'kara aure ya zakiji? Idan aurene zanyi ita kanta ta aminta da aurena amma sai ta sami lafiya zanyi auren dan haka kiyi ha'kuri har ta warke". 19 Shiru yayi mata suka kalleni dukkansu, nima idona na kansu kuma ko a jikina zancen aurennan nasa, indai auren zai shafamin lafiya wallahi yayi domin azabar da nakeji ta isa. Idan d'aya na dare yayi na fara jin iface-iface kenan da wata iska tana yawo a kaina har sai gari ya waye, daren jiya ma wata murya Mai matu'kar tsoratarwa naji tana cemin 'ki tashi ki fita' har asuba sannan na samu salama. Gari na wayewa kuma zan fara ciwon jiki mai tsanani wanda ko hannuna bana son motsawa, ga bleeding da nakeyi da ko ta kansa bana bi, nidai nasan rabona da sallah 13 days kenan duk a zaman period nake. Wajen aikina na aika Saleh yayi reporting banida lafiya har ma 'kawayena sunzo dubani, addu'a bata zama a bakina da zarar na kama sai na kasa 'karasawa. "Saleh, zan sake maka maganar aure a Karo na 'karshe, idan har baka amince ba wallahi tallahi kaji na rantse saidai ka fita ka barmin gidannan domin bazan zauna da d'an da baya ganin darajata ba, na d'auki cikinka wata tara, nayi na'kuda na haifeka na shayar da kai na raineka ka girma, wai har kaine zaka kalleni ina fad'a kana mayarwa, ka gyara halinka kafin na dawo ko kuma dakai da wannan majnuniyar matar taka saidai ku bar min gida". Ficewa tayi na bita da kallo hawayen takaici na bin idona, zama Saleh yayi wajen 'kafafuna yace "kiyi ha'kuri boo Allah yana tare damu yasan halin da kike ciki zai yaye maki kinji?" Gyara kwanciyata nayi yace "Boo d'an tashi mu gani" Tashi nayi da 'kyar ya nunamin stain d'in dake kan kujerar, sai yanzu na tuna pad d'in jikina tayi kwana da yini, gashinan na 'bata kujeruna masu kyau. Tashi yayi ya d'auko pant da pad da kanshi ya saka pad d'in a jiki ya bani na cire na jikina na sanya sabon, wanda na cire kuma ya nufi band'aki dashi. Dawowa yayi da tsumma da detergent ya zuba ya dinga goge kujerar har saida wajen yayi tas, zuba masa ido nayi cike da tausayawa, ji nake kamar na shige jikinsa amma da na tuna abinda zanii sai na ha'kura. Yana gamawa ya dawo ya zauna muka zubawa juna ido, muryata 'kasa-'kasa nace "Ina Huda?" "Huda tun d'azu ai tana wajen Sultana, duk lokacin da Sultana zata zo kina bacci amma tace na maki sannu". Kwanciya nayi jikina na karkarwa nace "boo-boo na dan Allah ka kaini wajen Mama na ganta, dan Allah". "Babu komai shirya muje". Tashi nayi ina taking kamar mai koyon tafiya, ganin haka ya Sanya ya d'aukeni a hannunsa ya nufi saman bene dani, had'a ruwan wankan yayi ya min wanka ya zuramin doguwar riga, ganin na dameshi naga Huda ya sanya yace idan mun fita mu kar'bota. Gidan muka samu a rufe ya kirata da wayata tace ta fita, wani abun al'ajabi ne ya faru dani ina sanya 'kafata a waje gaba d'aya ciwon da nakeji ya yaye a take tamkar ban ta'ba yi ba, kallon kaina nake na kalli Saleh, gaba d'aya ya canza ya rame ga fuskarsa alamun ya dad'e baiyi gyaran fuska da aski ba. Sultana na hango da Huda a hannunta da Ahmad a goye, mi'kawa Saleh Huda tayi tace "haihuwa akayi anan ma'kwabta na shiga, ya jikin Bilkisun". Kar'bar Huda nayi nace "Sultana na gode da d'awainiya Allah ya biyaki". Sakin baki tayi tana kallona tace "Bilki? Har kinji sau'ki?" Murmushi nayi nace "Ni kaina abin ya bani mamaki, wallahi ina fitowa daga gida naji kamar an d'auke min ciwon gaba d'aya". Can 'kasan muryarta tace "ai dama na sani" sannan ta kalli Saleh tace "Uncle shawarata shine karku dawo har sai kun sami wajen mai maganin da kuka aminta dashi kunje tukun, Allah ya 'kara lafiya". Shigewa tayi gida Saleh ya kalleni tare da kai hannunsa fuskata, murmushi nayi nace "nayi kewarka boo-boo na" Rungumeni yayi tsam a jikinsa duk ya takure Huda dake hannuna,ya d'auki mintina kafin ya sakeni ya zubamin ido, nasan shi kansa al'ajabin wannan ciwo nawa yake gani. "Boo-boo ka shiryani baka sakamin bra ba". Kallona yayi yace "to banda abinki wa zai gane, muje kawai gidan maman". "A'a tunda Allah ya bani lafiya kuma ai ya kamata naje a tsaftace na kuma a shirye, ri'ke Huda nayi sauri na sako". "A'a muje tare". Ya fad'a tareda bin bayana, ina saka 'kafata a gidan naji kaina ya sara haka na 'karasa cikin sauri, ina shiga gidana jikina ya d'auki rawa ciwon da na bari a 'kofa ya dawo sabo fil, a tsakar gida na kwanta na kasa 'karasawa ma cikin d'akin, ji nake kamar ana sara min 'kasusuwana, cikin sauri Saleh ya jani zuwa waje da 'kyar na 'karasa 'kofar gida. Saida na shiga mota sannan na wartsake, tafiya muke babu mai magana a cikinmu dukkanmu tunani d'aya ne a ranmu. Tare dashi muka shiga gida mama na kitchen tana girkin rana, ko da na shiga saida ta yimin kallo biyu sannan tace "Bilkisu? Meke damunki haka?" Murmushi nayi nace "banida lafiya Mama, amma tare da Saleh mukazo ma yanzun". Fitowa Mama tayi suka gaisa nan yake mata bayanin ciwona da maganin da hajiya take bani, godiya Mama tayi masa tace "ai kakanta ma malami me yanzunnan zamu je wajensa da yardar Allah za'a samu waraka, meyasa baku fad'a min da wuri ba?" Sunkuyar da kansa yayi yace "Mama gani nayi ana bata magani a gida kuma kar a fad'a hankalinki ya tashi shiyasa". Gyad'a kai Mama tayi tace "hakane, amman zamuje wajen kakan nata Allah ya sawwa'ke". Sallama yayi mana ya tafi, yana fita Mama ta sanyani a gaba tace "fad'amin abinda ya faru tun farko? Ya akai kika fara wannan ciwon?" Ban 'boye mata komai ba na sanar mata, girgiza kai tayi tace "Bilkisu meyasa bakya fahimta ne? Mutumin da baya sonka bazai ta'ba sonka ba, mutanennan da bakinki kike fad'in basa son rayuwarki da Saleh, idan kinada tunani ko pure water zaki iya sha a gidan ne balle wani magani? Amma zato zunubi ne bari muje wajen Alhaji baba muji me zaice, amma kiyi wanka ki gyara jikinki wallahi kamar mai ta'bin hankali". 'Daki na shiga na kalli kaina a mudubi saida na dafe 'kirjina, fuskata tayi wani ba'ki ga rama, idanuna sunyi zuru-zuru ga gashin kaina da yake tsefe babu kyan gani. Kayan jikina na cire na shiga wanka na dinga dirzar jikina har saida na gaji, ina dubawa naga jini ya tsaya nayi hamdala. Fitowa nayi na tsaya nayi sallah cikin nutsuwa sannan na d'auki 'kur'ani na fara karantawa, na samu nutsuwa sosai sannan naci abinci muka tafi gidan Alhaji Baba. Bayan na masa bayanin abinda yake damuna, ruwa ya sanya na d'ebo da kaina yace na tofa ayat kursiyyu da suratul falak da nas da ikhlas sau uku na shanye, sannan yace na karanta ayatusshifa shima na tofa a ruwa na shanye. "Ni bana ru'kiyya amma ina ganin tana bu'katar ru'kiyya, ki d'auketa kuje Dan fodio ayi mata ru'kiyya sai ku dawo". Alhaji baba ya fad'a bayan ya gama min adduo'i. Muna zuwa muka samu dandazon mutane akace sai mun bud'e file da sauran abubuwa duk mukayi, sai yamma na samu aka ganni, wani ruwa aka bani nasha mai gigita jiki, jijjiga na fara ina jin hannuwana da 'kafafuwana suna juyawa kafin duhu ya lullu'be ni. Farkawa nayi na ganni a gidan Mama tana yiwa Saleh bayani, basu san na farka ba Mama tace "zata zauna anan kamar yanda kakanta ya fad'a har sai ta warke, domin da kansu shed'anun suka ce zamanta a gidan ne basa so, zamu ci gaba da mata magani har Allah ya sanya ta warke ta koma, kai kuma zaka dinga sanya karatun 'kur'ani a gidan a kowacce rana, ya kasance ko baka gidan wannan karatun yana yi". Godiya yayi na tashi ina dafe kaina, duk hankalinsu ya dawo gareni suna min sannu. "Bilki zaki zauna anan ayi miki magani har ki warke ki koma.....". Katse mama nayi nace "duk Ina Ji Mama". Tashi tayi ta bar mana d'akin Saleh ya dawo gefena ya zauna, kwantar da kaina nayi a kafad'arsa yace "ya jikin naki". "Alhamdulillah, yanzu Kai kad'ai zaka dinga kwana kenan a gida?" Na fad'a Ina kallon fuskarsa, kalar tausayi yayi yace "ko zaki bawa Mama baki ta barni na kwana anan kawai, nifa bana jin zan iya bacci idan bakya kusa dani". Cikin kasala nace "kawo kunnenka kaji". Waiwayawa nayi naji babu motsin Mama nayi kissing d'insa a gurguje sannan na hugging d'insa ta gefe nace "d'umin jikina yana tare dakai boo-boo na, kuma ai kwana ne kawai bazamu dinga yi tare a gidan ba, idan ta kama ma ai zamu iya ke'bewa a d'akin waje". Dariya yayi tareda jan hancina yace "matarnan fa bakida dama, ana ta lafiyarki kina ta ke'bewa da miji ko?" Shafa fuskarsa nayi nace "to ni kuwa inada damuwar da tafi damuwarka ne? Ai kowane yanayi nake kaine tunanina na farko bazan so ka shiga damuwa saboda ni ba, wadda kake ciki ma ta isa dan haka karka d'auka zamana a gida zai ma soyayyarmu gi'bi, babu abinda za'a fasa sai wanda bazai yiwu ba" Murmushi yayi tareda pecking goshina yace "I love you my boo Allah ya baki lafiya". "I love you too boo-boo na". Mun jima manne da juna har saida naji sallamar baba tukun saleh ya koma gefe ya zauna. Tare da jabir baba ya shigo cike da damuwa jabir ya zauna kusa dani yace " 'kanwata ya jikin naki". " Naji sau'ki yaya, tunda Kai baka son zuwa gidana ni gani nazo naku gidan yanzu". Sosa 'keya yayi yace " 'kanwata kin gane ko? Wato shi Saleh ne baya son zuwana shiyasa". "Kar kayi masa sharri, zuwa ukun da kayi ai duk shi ya janyoka da 'kyar". Dariya yayi yace "Kar ki damu 'kanwata idan kika koma duk sati zan dinga zuwa". "Allah yasa" na fad'a cike da jin dad'i, hira mukeyi amma hankalina na kan Saleh da damuwa ke bayyane a fuskarsa kamar ance masa mun rabu har abada, yau kuma sai su hajjaju a zuba ruwa a 'kasa a sha tunda bana gidan. *Kuyi ha'kuri da wannan I have alot in my plate,sai kuma gobe da yardar Allah,comments dinku suna kayatar Dani ko da banyi reply ba kusani Kuna raina bilkisu na godiya da wannan soyayya da.kuke nuna Mata😘😘😘😘😘😘😘😘* 20 Tashi yayi ya ma Mama sallama cewa zai tafi, ina zaune kamar bansan ma yayi maganar ba, ina kallon Mama tanamin alamu da Idonta na masa rakiya ni kuwa na zum'buri baki na zauna har saida tace "tashi ki rakashi mana". Amsawa nayi da to na tashi nabi bayansa, saida muka fita harabar gidan cikin shagwa'ba nace "yanzu fa tafiya zakayi ka barni ko?" Hannunsa ya Sanya a 'kirjina yace "wa yace miki tafiya zanyi na barki? Karki damu ina Nan, da zarar kinyi kissing d'ina ki sanya hannunki a nan" ya kama hannuna ya d'aura kan nasa yace "idan kikayi haka sai ki ambaci sunana, Zan amsa miki da yanayin bugun zuciyarki". Hannuna d'ayan ba d'aura a kafad'arsa nace "dama haka ka iya soyayya boo-boo na? Banda idon Mama na kaina ai binka zanyi mu gudu sai irin 11 d'innan ka  dawo dani a sace". Dariya yayi ya sanya hannuwansa a 'kuguna ya dagani na koma daidai da fuskarsa, hannuna na sa'kala a wuyansa domin na daidaita yace "kamar wasu teenagers? Ai yanzu idan inaso na saceki kawai Kiran Mama zanyi nace zamuje unguwa". "Ni kawai neman magana nakeji ai, so nake naga ya Mama zatayi idan nakai dare ban dawo ba sannan wani ya ajiyeni". Girgiza kai yayi yace "naughty girl, kallonki kawai zatayi tace Allah ya shirya". Tura baki nayi nace "yanzu shikenan bazamu fita ba?" Ajiyeni yayi yace "yauwa....shawara tazomin yanzunnan, muje gida mana mu d'auko miki kaya". "Hakane kuma fa, amma banason shiga gidannan boo-boo kaga dai yanda nake komawa a cikin gidan, kuma gashi banzo da komai ba sai kayan jikina bansan ma dame zanyi bacci ba". Kama hannuna yayi yace "to ba sai mu siyo miki kayan baccin ba? Idan yaso gobe sai na kawo miki kayan da safe, muje kawai" ya 'karashe maganar Yana Jan hannuna yana gaba. Dariya nayi nace "dakata mana malam, banda abinka ai sai su damu ganin ban dawo ba, muje mu fad'a musu zamu fita mana ko?" Komawa mukayi na sanarwa mama zamu fita na d'auki zumbulelen hijabinta na saka, kashedi tayimin na mu dawo da wuri Kar muyi dare a waje. Wani d'an 'karamin shago kusa damu mukaje na samu kayan baccin da saura abubuwan da zan bu'kata zuwa safiya, duba agogo yayi yace "kai, dubi fa sai yanzu 8:20 tayi, ina ya kamata muje?" Tagumi nayi nace "nifa kawai so nake naga daga ni sai kai, sati nawa bamuji d'umin juna ba ya kamata mu d'an _tattauna_". Dariya yayi yace "kinyi gaskiya, ya kamata muyi meeting na musamman, amma wajen had'uwar ne fa...kinga gida dai ke baya miki dad'in zama". Kallon bayan motar nayi tareda murmushi na d'aga glass d'in motar na kunna Ac, cire hijabina nayi na kalli bayan motar nace "are you thinking what I am thinking?". Zubamin ido yayi yace "oh ni saluhu, wannan mata tawa ko 'yar kunyarnan ta mata batayi". "Nayi kunya na cuci kaina da aurena ko? Ka godewa Allah ma da ya baka mai 'ko'kari irina, idan kuma kunyar kakeso sai na koma, inace kaine ka ro'keni da Allah cewa na dena kunyarnan, nayi fushi ma maidani gida kawai". Na fad'a Ina maida hijabina. Cikin sauri ya ri'ke hijabin yace "haba my humra, my saje, kinsan dai yanda nakeson sajennan nawa, to na fiki sonshi, yanda wayewar kannan taki ke birgeni bazan iya kisaltawa ba, inaso na tsokane ki need kawai domin idan kika had'e rai kinamin matu'kar kyau". 'Daga idona nayi na kalleshi ya saka hannu yana shafa fuskata yace "idan kikayi murmushi sai naji tamkar nasha giyar aljanna mai d'ankaren sanyi, idan kuwa kikayi magana, muryaki har wani maye take sakani, amma fa mayen na giyar aljanna, Allah dai ya kaimu aljanna gani gaki, d'an yimin murmushi mana". Dukda dariyar dake cina na dake tareda turo bakina, bud'e 'kofar motar yayi ya le'ka sannan ya dawo yace "tunda bazaki min murmushin ba na ma fasa kaiki gidan, a nan zan saukeki sai da safe". Kallon fuskarsa nayi naga ya d'auke Kai babu alamar wasa, da hanzarina kuwa na bud'e motar haushi ya kawomin wuya hijabin nawa ma a hannu, bud'e 'kofarsa yayi nayi gaba da sauri, ji nayi an ri'koni ta baya na fara 'ko'karin fizgewa, a kafad'arsa ya sakani bai ajiyeni ba sai a bayan motar. "Ka 'kyaleni na tafi ko na maka ihun ka sace....." Ban 'karasa ba naji lallausan lips d'insa ya had'e da nawa, 'ko'karin tureshi nake ya'ki barina har saida na ha'kura na aminta da sa'konsa. Hannunsa yake 'ko'karin kaiwa bayana ina ri'kewa har ya gaji ya d'ago ya kalleni, hannuna na hard'e a 'kirji nace "nifa ban ha'kura ba...tam". D'auke hannayena yayi ya ri'ke cikin hannunsa yace "idan na raping d'inki karki ce nayi laifi". 'Daga kafad'ata nayi alamun ko a jikina, ganin ya fara amfani da 'karfi zai lahantamin riga yasa na  mi'ka wuya..... ******** Sallama mukayi a 'kofar gida, ina shiga na sami Mama da jabir suna hira, kallon agogo Mama tayi na sauke kaina 'kasa gani nake kamar zata rafkoni. "Yanzu ke bakida lafiya zaki biye masa ku wuce 10 a waje? Allah ya kiyaye idan wani abun ya sameki fa? Bayan ance karki yawaita fita ga kuma maganinki baki ma sha ba kin saka 'kafa kin fice ke mai miji ko?" "A'a wallahi mama, Kinga mun siyo kayan nawa ne har mun fito hajiya ta kirashi tace ya siyo mata kifi, to mun siyo kifin mun dawo na tuna na bar kayan a shagon da na siya saida muka koma aka yita dubawa sannan aka gansu". "To zo kisha magungunan naki kafin kiyi bacci, ko kuma fara yin alwala anfiso asha magani da tsarki". Amsa mata nayi da to na shige, cikin sauri nayi wanka na saka kayan baccina na Sanya hula na fito, zama nayi gefen Mama tana mi'komin maganina Ina sha. Bayan na gama sha ta mi'komin wani tace "shafa a kanki da fuskarki sannan ki sha". A hankali na cire hular kaina, gashina a tsefe yake hakan yasa ji'kashin da nayi ya ji'ke sosai, shafa maganin nayi ina kallon Mama tana sorting magungunan kamar bata san ma idona na kanta ba, sauke idona nayi na sake d'agowa saida nayi haka sau hud'u. Kallona Mama tayi tace "so kike nai magana kenan ko? Ina ruwana ba mijinki bane? Me kikeso nace?" Cije bakina nayi na sauke kaina cikin kunya ina sosa kai, ajiye magungunan tayi a gefenta tacemin "idan Zaki kwanta ki tabbatar kin kwanta da alwala, kiyi duk adduo'in da suka kamata sannan kuma karki manta da karanta suratul MULK, fa'idarta tana da yawa, ko mutuwa kikayi a wannan daren kin mutu 'yar aljanna, idan Kika karanta suratul MULK Allah zai aiko mala'iku su zagaye ki suna gadinki har sai kin farka, ko sihiri aka miki wannan sihirin idan yazo bazai ganki ba, sannan alhaji baba ya bada ganyen magarya yace ki dakashi da kanki, ki samu cooler ki cika da ruwa saiki zuba ganyen magaryar a ciki ki karanta suratul BAQARA, kullum idan zaki shiga wanka ki zuba kofi d'aya na ruwan a cikin ruwan wankanki sannan idan kin futo ki d'iba ki sha, itama ganyen magarya maganin kowane ciwone da kika sani har wanda ma baki sani ba, bilki karkiyi wasa da lafiyarki kinji ko?" Amsa mata nayi da to tareda mata godiya, hira mukayi sama sama kafin bacci ya fara d'aukata. Na jima banyi bacci mai dad'in na yau ba, baccina nayi babu gigitacciyar 'kara ko taku da nakeji, babu mafarki mara dad'i har saida na kusa makara sallar asuba. Inayin sallah na d'auko turmin 'karfe na daka ganyen magarya na zauna na fara karanta suratul BAQARA kafin 7:30 na gama, tunawa nayi da kayan da Saleh zai kawomin na masa text na abubuwan da zai d'auko kar ya mantamin wani abun. Kitchen na shiga na fara had'a mana breakfast, 'kosai na had'a mana da tea ina gamawa Saleh yazo. 'Daki na kaiwa Mama abincinta muka zauna da Saleh da jabir muka ci a palour muna hira. Kayana ya shigomin dasu Mama tace ya 'karasa dasu d'akina, binshi nayi a baya ya ajiye akwatin yana 'karewa d'akin kallo, zama yayi a bakin gado yace "ba laifi, d'akin naki dai kamar na mata". "To ai na macen ne, ya kaje gida?" "Lafiya Lau, amma dai Mama Bata gane ba ko?" Dafe kaina nayi jin ya saramin nace "ta gane, kasan ban iya faking abu ba". Runtse idona nayi jin ciwon yana sake 'karuwa, wani dumm nakeji a kaina tamkar ana buga ganga a cikinsa, sauka nayi daga gadon na zauna a 'kasa. Cikin damuwa Saleh yace "boo menene?" Nuna masa kaina nayi ina ganin wani irin haske a idona dukda idon a rufe yake, addu'a na fara ja Saleh ya fita cikin sauri yana kiran Mama. Tare suka shigo Mama ta d'auko cooler da na zuba ruwa d'azu ta bud'e ta shafamin a fuskata da kaina sannan ta bani nasha, sauran magungunan duk ta d'auko ta bani, dafe 'kirjina nayi domin ya ri'ke ji nake kamar ana fizgar zuciyata, jikina ya d'auki rawa inaji idanuwana suna juyawa. Sam bana ganin komai sai haske, wani irin haske ne da yake shiga kaina yana azabtar dani, inajin muryoyin su Mama suna tofamin adduo'i har Allah ya yayemin wannan wahala da na shiga ta d'an lokaci. Tashi nayi na zauna jikina duk a ri'ke, sannu sukemin, ruwa nake bu'kata amma na kasa bud'e bakina sai alama nayiwa mama da hannuna ina bu'katar ruwa, ha'korana sun had'e sun'ki bud'ewa harshena kuma ya juye, daga yanda suke kallona nasan kamannina sun canza domin a jikina nima inaji na canza. Ruwan ganyen magarya Mama ta bani nasha na koma na kwanta, bacci naji ya d'aukeni a hankali. Farkawa nayi na samu Mama tana Jan carbi kan darduma ni kuma ina inda nake, kallona tayi tace "Bilkisu ya jikin naki?" "Da sau'ki" na fad'a tareda tashi na d'auro alwala, sallah nayi na jingina da gado ina gyangyad'i naji kiran waya. Dubawa nayi naga hafsa ce ta kirani na d'aga tareda sallama, bata amsa sallamar ba ta fara magana  _"wayyo Bilkisu sannu ya jikin naki? Yau supervisor yake tambayarki muka fad'a masa bakida lafiya kuma anyi reporting, shi yace bai saniba saboda haka gobe kije department". Godiya na mata na kashe wayar na koma baccina, wuni nayi ina bacci marar dad'i, dukda bana mafarki ko ganin abin tsoro amma a firgice nake tashi. Washegari jikina ya d'anyi dama dama amma dukda haka maganata bata fita sosai, muryata ta koma tamkar ta bebaye idona ma ya juye, a hakan na takurawa su Mama saida mukaje makaranta. Kai tsaye wajen HOD muka nufa yana ganina ya fara tausayamin, Mama ce ta sake masa bayanin ciwona a take ya lalubo takardar da Saleh ya kai masa ya aikata wurin Dean, shima rubutu yayi yace babu matsala tunda dama saura wata biyu internship d'in namu ya 'kare, duk lokacin da na warke na koma kawai. Wajen magani muka nufa daga nan aka sake min ru'kiyya, na jigata sosai amma a jikina naji alamun shaid'anun dake cutar dani babu su. Kwana biyu tsakani sai ga aunty tazo, fad'a ta dinga yiwa Mama akan me ba'a raba auren namu an bar musu d'ansu ba? Gashinan na kusa zama mahaukaciya. Waya ta dinga yi anan tana sanarwa 'yan uwan mahaifina banida lafiya, anan naga gata duk wanda zaizo da nashi kalan maganin, bansan danginmu akwai yawan malamai ba sai yanzu. An shafe sati biyu ana zuwa dubani, wasu suzo sau uku wasu sau hud'u anty kuwa kullum sai tazo, kayan dubiya kuwa a d'aki nake tarasu lemu da ruwa dashi nake saukar ba'ki, har na warke sosai ba'a dena zuwa dubiya ba. Ranar da na cika sati uku a gida muka koma Dan fodio, ru'kiyya aka sake yimin amma cikin ikon Allah babu abinda ya faru, magunguna aka bani aka tabbatar mana na samu lafiya. Huda kuwa jefi-jefi nake ganinta, idan Saleh ya kawota ma kusan a gidan su zulaihat take wuni, da zarar tayi kwana biyu Saleh ke maidata wajen sultana wai hajiya tana tambayar ina take. Tare da aunty mukaje gaba sukayi ita da Mama inaji mama nace Mata "Dan Allah dai kar kiyi abinda yaronnan zaiji ba dad'i kinga yayi 'ko'kari". Bata amsawa Mama ba muka shiga d'aki, bayan mun zauna aunty tace "to alhamdulillah jikin bilkisu yayi sau'ki, yanzu komawa gidanka ya rage amma da sharad'in bazata koma ba sai mun tabbatar da lafiyar gidan naku, sannan abu na biyu ya kamata ka shiga tsakanin matarka da 'yan uwanka, ka sani cewa sune silar shigarta wannan hali dukda cewa kaima shaida ne na zaman dake tsakaninsu, Bilkisu bata fad'a mana meke faruwa ba saida wannan abun ya fara samunta, amma ka sani yanzu zamu sanya ido a kanta sosai, matu'kar irin wannan ya sake faruwa to kayi ha'kuri amma zamu d'auki matakin da ya dace ne". Sunkuyar da kai yayi yace "hakane kuma nagode da 'ko'karin da kukayi a kanta Allah ya saka da alkhairi, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba zan saka ido akan hakan, sannan kamar yanda Mama tamin umarni kullum da 'kur'ani nake wuni a gidan, ko bana nan Zan kunna yayi tayi sannan duk wani abu da zai jawo shaid'anu na kawar". "Hakane, amma bazamu gane lafiyar gidan ba sai munje da ita, sai zuwa gobe insha Allah zata koma sannan tare dani zamu koma zan kula da ita da zamanta a gidan, idan tayi kwana biyu babu wata matsala zamu barta anan kuci gaba da kula, amma dan Allah a kiyaye". "Insha Allah". Ya fad'a tareda godiya, sallama yayi mana ya tafi. Washegari kafin na koma saida aunty ta kimtsani da kyau, ashe da shirinta tazo, sai dare sannan muka tafi gida. Jikina duk yayi sanyi raina bayason komawa gidan, idan na tuna abinda ya faru Sai naji gidan duk ya fitarmin a raina, ina tunanin yanda zan samu gidan har muka 'karasa. A bud'e na samu gidan saida nayi adduo'i sannan na shiga, sultana na samu tana kunna turaren wuta cike da farin ciki tayi hugging d'ina. Gaida aunty tayi sannan ta jani zuwa kujera, waiwaye nake Ina neman Huda tayi dariya tacemin "Huda ta fita da abban Ahmad wai coco pops takeso tasha sun tafi siyowa, ya jikin naki ya su Mama? Wallahi kullum sai na tambayi jikinki sannan nace ya gaisheki amma ban saniba ko baya fad'a, kinsan nazo sau d'aya lokacin da nazo kina bacci an fad'a miki ko?". "Allah sarki Sultana, jiki yayi kyau alhamdulillah, kullum kuma sai ya fad'amin gaisuwarki ko bai fad'a ba zance sultana tana gaidani ko? Nagode da 'ko'karinki Allah ya saka da alkhairi, gida yayi kyau". Katsemu aunty tayi tace "Bilkisu babu dai wani abu da kikeji ko?" Girgiza kai nayi nace "aunty banajin komai" Hira mukaci gaba dayi kusan rabin hirar akan Huda da tsiyar da takewa sultana, sai bayan 9 sannan ta tafi. Aunty kuwa tun 8:40 tayi mana sallama ta shige guest room ta barni ni da Saleh. Hannunsa nayi yana wasa a bayana, ture hannun nayi nace "boo-boo aunty fa". Zuge zip din rigata yayi yace "za'a yiwa aunty sharri ko? Kima sani ko Mama ce a gidannan yau sai na biya bashina, kinsan kuwa wahalar da nasha bakyanan?" "To boo-boo naji mu tafi sama mayi zancen acan". Ina rufe bakina ya d'aukeni bridal style ya nufi stairs dani, a palon saman ya ajiyeni tareda fara kissing wuyana hannunsa na kan cikina yana shafawa, biye masa nayi muka fara raya dare tun yana farkonsa........ 21 Da 'kyar na tashi saboda jin dad'in bacci, wanka nayi na sauka na fara had'a breakfast har na gama ko muryar Aunty banji ba. 'Dakinta na nufa na sameta tana zaune kan gado da wayarta a hannu, dariya nayi nace "aunty kema an koya miki chatting d'innan ko?" "Kedai bari, zamaninnan ai saidai hamdala, yauwa zo ki nunamin yanda aka d'auko abu a utube wani video naji ana zance nima zan gwada". Zama nayi a gefenta na shiga utube na mata searching, mi'ka mata wayar nayi ta kalleni tace, "kinyi kyau fa". Murmushi nayi na sunkuyar da kaina ta sake cewa "babu dai wata matsala ko?" "Babu komai Aunty nayi bacci sosai ma Alhamdulillah" na fad'a tareda fara'a. Murmushin jin dad'i tayi tace "To alhamdulillah, haka nakeso naji, gobe insha Allahu idan na sake dubaki sai na tafi, yaushe zaki koma makaranta?" "Inaga goben zan koma insha Allah, Aunty muje palour na gama breakfast". Tashi nayi tace "a'a ki kawomin abincina nan bazan fito na takura muku ba". Cikin sauri nace "a'a Aunty wallahi ba takura ki fito muci tare". Wani kallo ta watsomin ta maida kanta kan wayar gabanta, fita nayi na had'a mata breakfast na kai mata sannan na had'a mana namu na ajiye. 'Dakinmu na koma na fara gyarawa Saleh na wanka, d'aga murya nayi nace "ka hanzarta kar ya huce!" Fitowa yayi yana goge kansa da towel 'karami, ri'ke 'kugu nayi na zuba masa ido shima kuma 'karemin kallo yakeyi, murmushi nayi tareda juyawa na fara goge mirror nace "ka hanzarta ka shirya mu sauka na fara jin yunwa". Tahowa yayi inda nake ya hugging d'ina ta baya, iska yake huramin a bayan kunnena a hankali inajin bugun zuciyarsa a gadon bayana, rocking d'ina yake kamar 'karamar yarinya faffad'an 'kirjinsa na gogar bayana. Cizar kunnena yayi tareda sanya hannunsa yana shafa kafad'ata, dawo da le'bensa wuyana yayi yana kissing tareda furtamin wasu kalmomi masu matu'kar kashe jiki. Muryata 'kasa 'kasa nace "boo-boo.....yunwa nakeji". Kamar ma tunzurashi nayi ya sanya hannunsa d'aya ya juyoni cikin 'kwarewa, shafa kumatuna yayi yace "kinada ni har kya zauna da yunwa?" "Umm..." Bai bari na furta komai ba ya had'e lips d'insa da nawa, hannuwana na sanya a bare chest d'insa yayinda hannunsa ke roaming bayana, rabuwa mukayi da juna saboda numfashi  na dafa kafad'arsa nace "boo-boo munbar Aunty fa ita kad'ai, kafin tayi suspecting abu ya kamata mu sauka". Pecking d'ina yayi a lips yace "hakane, amma kiyi gaba zan biyoki idan na shirya". Har azahar babu wanda yazo dubani daga mama har haularta, sultana ce kawai ta kirani tamin ya jiki jumana kuwa har mantawa nake tare muke rayuwa da ita. Ban damu da rashin zuwansu ba, washegari tareda aunty muka fita aka ajiyeni a wurin aikina ya wuce da ita gida, aikin ma basu barni nayi sosai ba sai kar'bar gaisuwa nake ta yaya jiki. Saida nayi kwana uku a gida tukuna hajiya da jumana suka zo dubani, ina ri'ke da Huda tana cin biscuit a hannuna, zama sukayi bayan sunyi sallama na gaidasu suka amsa da 'kyar. "Huda zo mu gaisa mana" jumana ta fad'a tareda d'aukan Huda daga cinyata, tuni idon Huda ya ciko da 'kwalla tana mi'komin hannu ni kuma nayi kamar ban ganta ba. Kuka ta saki tana zamewa tana yun'kurin ta dawo wurina amma jumana ta ri'keta, tsaki tayi tace "wallahi Huda bakida sabo, ji wani kuka kamar ana figar naman jikinta". Huda kuwa ganin ban kulata ba ya sanya ta 'kara sautin kukanta, cikin d'aga murya tace "MAAMA!!!" Tareda mi'komin hannu, kallonta Mama tayi ta kalleni taga da gaske dai ni ta Kira da maama, wani irin juyi naji cikina yayi yayin da mama tace da Jumana "saketa muga inda zataje". Wani gumi naji ya karyomin domin d'abi'ar Huda ce indai ta kira sunana ban amsa ba tayita kira kenan sai na amsa, rarrafowa tayi ta dafa 'kafata ta tsaya tana rage sautin kukanta, "maama" ta fad'a tareda mi'komin hannu, d'aukanta nayi na kwantar da ita a kirjina ina shafa kanta cikin rarrashi, "maama" ta fad'a tareda ri'ke rigata tana kallon Jumana, shiru nayi ta sake fad'a ganin dai ban amsa ba yasa ta d'ago daga jikina ta ta'boni tace "maama". "Um?" Na amsa mata da 'kyar, gwaranci ta faramin nace "to shikenan yi ha'kuri". Su hajiya kuwa sakin baki sukayi suna kallona, biscuit d'in da ta yar na d'auka ina bata a baki, kar'bar na hannuna tayi ta turamin a bakina, dariya tayi tareda d'ago kanta ta had'a bakinta da nawa, murmushi nayi idanuna na kan su hajiya, gaba d'aya jikina yayi sanyi, kallon juna sukeyi suna min kallon tuhuma ni kuma na sunkuyar da kaina. Da alamu sun manta dubiya ce ta kawosu domin cikin hanzari sukamin sallama suka fice, basu fi minti talatin da fita ba naji bugun sultana cikin sauri na bud'e da Huda a hannuna, cike da damuwa tacemin "me ya faru ne? Su hajiya sunzo suna tambayata tsakaninki da Huda". Palour muka shiga na fad'a mata duk abinda ya faru, dafe kanta tayi ta girgizashi cikeda damuwa,  ri'ke hannuna tayi tace "Bilkisu dan Allah komai rintsi kar kice kinyi giving up akan Huda, wallahi Huda taki ce Huda bazata ta'ba jin dad'in rayuwa ba idan babu ke, ina ganin lokaci yayi da ya kamata ace na sanarwa su hajiya tsakaninki da Huda". Numfashi kawai nake ja ina saukewa na rasa ma me zance, kallon Huda nayi da take kamo wuyan rigata tana mi'kewa Kan cinyata, hannunta na kama nace "Huda dan Allah ki zauna kawai". Tamkar taji abinda nace ta kwanta a jikina, kallonta nayi na shafi kanta tabbas soyayyata da Huda had'in Allah ce, wani yanayi nakeji yana tsirgawa cikin jikina a duk lokacin da na had'a jiki da Huda, zan iya rantsuwa soyayyar da nakewa Huda ta ninka wadda mahaifiyarta take mata. Lumshe idanuna nayi nace "wallahi ko ni Sultana banaso a rabani da Huda, jin Huda nake kamar 'yar da na haifa a cikina indai bazaki goyi bayan 'yan uwanki ki kar'be Huda ba, nima bazan ta'ba bayar da ita ba". Girgiza kai Sultana tayi tace "Bilkisu bana goyon bayan rasuin gaskiya ko Yaya yake, kuma ni bana magana biyu, inaso gobe ki tafi da Huda makaranta domin a gobe za'a yita ta 'kare". 'kan'kame Huda nayi a jikina nace "wallahi Sultana da zarar kin furta haka nakejin gabana ya fad'i". "Addu'a zakiyi komai zaizo mana da sau'ki, abinda nakeso dake kawai ya zamana kin ri'ke Huda kuma kin tsaya tsayin daka akanta, ko mahaifiyata bata isa ta rabaki da Huda ba, Kai ko ni ban isa na rabaki da Huda ba, yanda zakiyi ya'ki akan Yar da kika haifa ki aikata hakan akan Huda". Na rasa ma bakin yiwa sultana godiya, ranar kasa bacci nayi kwana nayi ina juyi da tunanin abinda zai faru gobe, da wuri na farka na shirya Huda muka fice saidai hankalina ya'ki kwanciya a hakan ma. Bayan na tashi daga aiki na bud'e wayata, 28 missed calls na gani da 3 messages, 2 missed calls da message d'aya daga Sultana ne sai missed call d'aya da message biyu daga hubbyna sai kuma ragowar daga numbobi daban daban, cikina naji yayi k'ara domin nasan yau akwai 'karamin ya'kin duniya a gidannan, Me zai faru Shin Sultana zata ri'ke alqawari na a barmin Huda? Zan iya cika al'kawarin Kare Huda dukda nasan zansha gori da takaici? Wane bangare Saleh zai kasance? Wasu irin maganganu za'a ya'bamin? Ina irin wadannan tunanin har nakai gida, wata irin hayaniya naji tana tasowa daga 'bangaren sultana, 'kara ri'ke Huda nayi na nufi sashina saidai kafin na 'karasa naji an nufoni cikin hanzari....... Kuyi ha'kuri da wannan kaina ya fara daukan caji, alot of tests ga exams tana gabatowa Zanin goyon Huda na ciro na goyata, kursum ce ta 'karaso tana huci kamar zata fashe tace "kizo ana nemanki". Banza nayi da ita ina bud'e gida, "wai baki jini bane? Cewa nayi fa ana nemanki hajiya ce take so ta miki magana". "To ina zuwa". Na fad'a tareda bud'e gidan na ajiye jakata da mayafina sannan na gyara goyon Huda, ina 'kokarin fita Saleh ya shigo, murmushin ya'ke nayi tareda hugging d'insa, shafa bayana yayi yace "muje ko?" Gaba nayi har na fita ya ri'ke hannuna, ina hangosu a tsaye idanunsu na kaina, murmushi yayi tareda shafar fuskata yace "boo-boo na komai zai zo da sau'ki kinji? Just believe in yourself and protect your daughter at all cost, ina tare dake komai rintsi". 'Dage nayi da 'kafafuna na waiwaya na kalli dangin mijina tukun na had'e bakina da nasa, a take yayi responding tareda sunkuyowa, wannan shine ownership sai naga a cikinsu wacece zata iya masa haka duk juyashin da suke so suyi. Breaking kiss d'in mukayi nace "mint d'in bakinka yayi min dad'i, zan so ace na sake tasting amma kuma na lura idanun surukaina na Kaina". Ri'ke hannuna yayi yana min wasa da yatsansa a tafin hannuna har muka isa, cikin ladabi na dur'kusa nace "ina wuninku?". "Yayi miki kyau tambad'add'iya, wato ke gaki mara kunya ke mai miji ke wayayyiya sha-sha-sha mara tunani zaki tsaya gaban uwar mijinki kina wani cakumar bakin mijinki ke a ganinki kin waye, banza....." Katse anty maimuna Saleh yayi yace "maimuna ya Isa haka, idan zaki zageta ni ya kamata ki zaga domin ni na nuna mata ina bu'katar hakan kuma duk mace tagari abinda mijinta keso takeyi". "Rufe min baki shanyayye, Dole ka fad'i haka Mana mace ta shanyeka tana juyaka yanda takeso, baka da aiki saidai tayi laifi ka goyi bayanta". Ri'ko kafad'ata Saleh yayi yace "yanzu menene laifin Bilkisu Dan ta sumbaci mijinta? Meye laifi a ciki? Kuma a 'kofar gidanmu ne ba wai 'kofar gidanku bane please ya isa haka muyi abinda ya kawo mu". Cikin fad'a Aunty Maimuna tace "baza a bari ba, abinda yarinyarnan tayi dole a mata magana, haka fa zaman hajiya a gidanta ta dinga fitowa rabin tsirara Kuna shashanci a gaban hajiya, sannan yanzu....." "Wai dan Allah abinda mukazo yi kenan a wajennan? Yaya maimu muyi abinda zamuyi mu tafi kafin nayi abinda yafi wanda kike fad'a muni". Sultana ta fad'a tana kallon Usman, galla mata harara Maimu tayi "Dalla malama ki mana shiru wa ya sakaki a ciki? Wawiya wadda bata san me take ba, yanzu sai ki maimaita mana abinda kika fad'a a bayan idonta". Hard'e hannu Sultana tayi tace "Ni ba munafuka bace kuma bana magana biyu, abinda nace shine nasan Bilkisu tana cikin mawuyacin hali na rashin haihuwa, kuma ita yafi cancanta ta ri'ke Huda domin tafi nuna mata soyayya a kaina, sannan nace Bilkisu tana da son yara sosai shiyasa naga ya dace na bata Huda domin bazan iya rainon yara biyu lokaci guda ba, sannan anty Maimuna abinda baku sani ba tun Huda na wata biyu na mallakawa Bilkisu ita ba tareda na sanar muku ba, nidai abinda nakeso dan Allah ku bar Bilkisu tayi rayuwarta da mijinta banida had'i da ita bayan zaman faccalata da takeyi, ku dena sako relationship d'ina da Saleh cikin rayuwata idan ba haka ba zaku kashemin aure a banza domin ya Usman ya fara si'kewa". Sai yanzu hajiya tayi magana tace "yanzu ke Sultana abinda kikayi ya dace kenan? Huda mun sani 'yarki ce ke kika haifeta kina da iko da ita, amma bakida ikon ki bayar da ita ba tareda sanin iyayenki ba, ke bakiyi tunanin cewa kema 'ya bace kamar kowa? Kinada iyayen da dole sai kin nemi izninsu zaki aiwatar da abu irin wannan amma uwarki bata sani ba balle ni, kinje kinyi gaban kanki kin bawa bare 'yarki wadda baku had'a jini da ita ba". Tura baki Sultana tayi tace "to Hajiya ai gani nayi ubanta ya amince kuma nima na amince to me muke bu'kata kuma? Idan har na sanar muku zaku amince ne? Kuma nayi imanin a cikinku babu wadda zata ri'kemin Huda yanda Bilkisu ta ri'keta, na riga na baiwa Bilkisu ita saidai kawai kuyi ha'kuri yanzu haka ma maganar nan tana wajen lawyer ko ni banida ikon na 'kwace Huda daga wajen uwarta". " 'karya kike wallahi bazai yiwu ba, uban wani ya hanata haihuwar da zaki d'auki 'yarki ki bata? Ke sauke 'yarnan" Aunty Maimuna ta fad'a tana 'ko'karin kunce goyon dake bayana, a hankali na ture hannunta nace "Aunty Maimuna bari mana kar ki tasheta a bacci". Bud'e baki tayi zata min magana Hajiya ta dakatar da ita da cewa "Bilkisu inaso a yanzunnan ki sauke yarinyarnan ki mi'komin ita hannuna" Bansan ta yaya na samu dakakkiyar zuciya ba nace "Hajiya ki min afuwa amma a yanzu kotu ce kawai keda ikon rabani da Huda domin yarjejeniya ce muka 'kulla akan hakan, Sultana tayi rantsuwar bazata kar'bi yarta daga wurina ba nima nayi rantsuwa duk rintsi bazan maido Mata 'yarta ba, bazan zama munafuka mai karya al'kawari ba ko sultana a yanzu bata da ikon kar'bar Huda a hannuna". Cikin zafin nama Anty Maimuna tayo kaina, janyeni Saleh yayi cikin sauri tazo dab dani tana kallona, hannunta ta sanya tana nunani tace " 'karya kike baki isa ba wallahi kinyi kad'an, dole sai kin bada Huda ko kinaso ko bakyaso babu ruwanmu da wata kotu". Hannunta ta sanya tana kunce goyon Huda na ri'ke hannun nace "Aunty maimuna tun ina girmamaki ki d'auke hannunki daga jikina, banaso kiyi abinda girmanki zai zube a idona, ku da mahaifiyarku kun nunamin tsana iya tsana na danne na jure, kin shiga rayuwar aurena na ha'kura, yanzu kuma so kuke duk wata hanya ta farin cikina ku toshe? Bakwa tunanin kuna cutar da d'an uwanku a haka? Muna son junanmu ku rabu damu mana, Sultana tana Sona after all the circumstances da ya faru tsakaninsu da mijina, wannan kad'ai bai isheku izna ba? Sai dole kun rabani da 'yata meyasa kukemin haka ne?" Kursum ce tayo kaina cike da tsiwa tace "kar ki sake na sake jin kin ambaci hakan a bakinki, Huda ba 'yarki bace babu abinda zai had'a jininmu dake, baki haifi  Huda ba baki shayar da ita ba, babu abinda kika sani game da ita kuma dole ne ki bada ita". Dariya nayi na shafa Huda dake bayana nace "alhamdulillah ban haifi Huda ba balle naji zafin haihuwarta, ban shayar da ita ba amma tun kafin Huda tazo duniya nake d'awainiya da ita da mahaifiyarta har Allah ya kawo ta duniya, ban haifeta ba amma na haifar mata soyayyar da duk wajennan babu wadda zata iya bata ita, Mahaifiyar Huda ta aminta dani ta bani ita dan haka babu komawa baya". Hannu kursum ta Sanya a k'ugunta tace "bazaki bayar ba kenan?" Gyara goyona nayi nace "bazan iya ba gaskiya", hannu maimuna ta mi'komin tace " idan na k'irga uku baki bani Huda ba zan miki abinda sai kinyi dana sanin ja-in-ja dani". Dariya nayi cikin takaici nace "to ni kuwa a zamana na gidannan menene ban ganiba? Tun daga day one nasan matsayina a gidannan bana tunanin akwai abinda zaku yimin na jishi a jikina, babu wadda ta isa ta rabani da Huda wallahi ko da kuwa Sultana ce" Kallon Hajiya Maimuna tayi tace "Hajiya kiyi mata magana mana" Daga inda take tsaye tace "Bilkisu, umarni nake baki idan har jin haifu ki sauke 'yar nan ki bani ita a hannuna, idan kuwa bakiyi hakan ba to tabbas bakya ganin darajar wad'anda suka haifeki". Wani abu naji ya tsayamin a raina a hankali na kunce Huda, Kar'barta Saleh yayi tana bud'e idonta ta Kira sunana tare da mi'komin hannu, dogon tunani nayi a wannan lokacin ba kalli Sultana, girgiza min Kai takeyi na rungume Huda nace. "Hajiya ni 'yar halak ce kuma ina ganin darajar mahaifana duk da banzo duniya na samesu a raye ba, amma duk d'an halak ya san girman al'kawari, bazan iya baki Huda ba har sai anje kotu mun tsaya ni da Sultana ta fad'i cewar ta canza maganarta da dalilin canzawar, sannan nima zan goge nawa al'kawarin ba baki Huda amma a yanzu Huda mallakina ce, bazan iya....." Saukar wani mari mai gigita tunani naji a fuskata, saura 'kiris na yar da huda saboda tsananin firgici da zafin marin, d'agowa nayi idanuna a take suka sauya, zuciyata ta sake 'ke'kashewa, Raina ya kai 'kololuwar 'baci nace "Maimuna wannan ya zama karo na 'karshe da zaki kai hannunki jikina, na d'auki iya abinda zan iya d'auka daga gareku, na gaji da zama daku Banda ina 'kaunar mijina babu abinda zai zaunar dani a cikin wannan gidan, Huda ce bazan bayar ba duk wadda take ganin tanada iko da ita tazo ta 'kwaceta" "Da wa kike?" Maimuna ta fad'a tana kallon tsakanin ni da Hajiya, tsaki naja nace "duk wadda take ganin girmanta ya isa ta zubar dashi tazo tana kishi da matar d'anta ko Kuma matar 'kaninta saboda matar tana samun wadatar da ita bata samu a gidan aurenta, ina magana ne da duk wadda ta gaji da zamana a gidannan, Huda tawa ce haka ma Saleh nawa ne duk duniyarnan Babu Wanda ya Isa ya rabani da wad'annan mutane biyu, idan kun rabani da Saleh kuna tunanin zaku bashi abinda nake bashi ne? Ni nake baiwa Saleh walwala na bashi farin ciki na kuma raba dare ina masa hidima, duk soyayyar da kuke masa kuna tunanin zaku iya masa hakan ne? Meyasa kuke kishi dani? Meyasa bakwa son farin cikina? Meyasa? Banida lokacin tsayawa cece kuce daku amma kusani ku tsaya ku kula da aurenku domin aure Rai gareshi, idan kana tunanin raba wani da nasa Kai baka san wa'adin da Allah ya d'ebarwa naku ba, na gama maganata anan duk wadda take da ikon kwace Huda daga gareni ta sameni a mazaunina". Cikin sauri na bar wurin na nufi sashina zuciyata tamkar zata fita saboda 'bacin rai da tsoro, tunda nake ban ta'ba tsintar kaina a irin wannan yanayi da aka Kai hakurina nesa ba, yanzu me zai faru tsakanina da Huda? Me zasu aikata next? 23 Sauri nake saboda hawayen da naji yana zubowa daga idona, kiran sunana Saleh yakeyi amma Sam na 'ki tsayawa, tura gidan nayi na shiga cikin sauri kai tsaye kujera nabi na ajiye Huda na kifa kaina ina matsanancin kuka, dukda cewa a yau na 'kwatarwa kaina 'yanci amma dukda haka rad'ad'in maganarsu yana damuna. Dur'kusawa Saleh yayi a gefena yana shafa bayana ba tare da yayi magana ba, ha'barsa ya d'aura kan kafad'ata yace "I am so sorry boo-boo na, kiyi ha'kuri kinji?" 'Dago jajayen idanuna nayi nace "meyasa hakan yake faruwa ne boo-boo, meyasa 'yan uwanka bazasu barni nayi rayuwar aure mai dad'i ba? Meyasa......" Sar'kewa magana ta tayi na sake kifa kaina, hannunsa ya sanya ya d'ago fuskata yace "babyna kalleni nan, ki fad'amin dalilin zuwanki gidannan, saboda su kike zama ko saboda ni? Soyayyarsu kike so ko tawa?". Hannuna na Sanya a kan nasa nace "komai da nake yi saboda kai ne, amma soyayyarsu tana da matu'kar muhimmanci a wajena domin zata bani damar zama kamar kowacce mace, nima naji dad'in zaman aurena amma aure anfi shekara babu abinda ya canza? Yaushe zan bar wannan 'kangin walahalar saboda bana haihuwa? Ni na d'aurawa kaina? Su suke bada haihuwar ko kuma su suka haifi Huda da zasu nunamin iko da ita? Wallahi a duk lokacin da hakan ta faru sai na tsinci kaina ina nadamar......". Bai bari na 'karasa ba ya had'e bakinsa da nawa, cikin zafin rai nake tureshi amma ya ri'ke kafad'ata sosai, wani abu naji yana min yawo a cikin raina, zuciyata ta sake raunana wasu sabbin hawayen ke zubomin. Shafa kafad'ata yakeyi zuwa wuyana zuwa saman bayana, sake deepening kiss d'in yakeyi tareda sanya hannunsa yana goge hawayen dake zuba, a hankali zuciyata ta fara rinjaya zuwa ga aikin da yakeyi saidai wani 'bangare na jikina yana fad'amin na dakata. Ban maida hankali ba na biye masa, daga yanda nake maida masa martani yasan Ina cikin tsantsar 'bacin rai, so nake kawai na samu hanyar da zan fidda zafin dake cikin raina gashi kuma Saleh yazo min da hanyar da tafi sau'ki gareni. Idanuwana sun rufe, hanya kawai nake nema da zan cike emptiness d'in da nakeji a raina, kwanciya nayi kan carpet d'in yayi rolling kansa bisana, cikin da'ki'ku kad'an komi ya fara heating up HUDA, cikin hanzari na tureshi na kalli kujerar da na ajiye Huda, tana kwance tana bacci yau dai kamar tasan me zai faru bacci take ta faman yi, ajiyar zuciya nayi nace "kwata-kwata na manta da Huda a wurinnan Allah ya taimakemu bata farka ba". Murmushi yayi ya kalleni yace "har kin huce kenan, God you are so sexy when you are angry, Zan tabbatar ina 'bata maki rai akai-akai domin wallahi I love this demanding you". Duka na kai masa cikin wasa sannan na 'karasa zuge rigata na cireta ba tare da nace masa komai ba, 'kurawa 'kirjina ido yayi yace "wannan ban Santa ba sabuwa ce ko?" Ya 'kare maganar yana nuna bra d'in jikina, kai na gyad'a masa nace "amma ai ta dad'e tun kafin na fara rashin lafiya fa, baka dai kula bane". Skirt d'in jikina na cire shima na ninke na zauna da underwear, camo bra ce a jikina saboda haka so comfortable nake jina tamkar na saka riga, ajiyar zuciya nake tayi amma abin na bani mamaki yanda lokaci guda 'bacin raina ya yaye saidai zuciyata ta fara rayamin abinda nayi ban kyauta ba. "Humm Bilkisu kenan, ki ma dena tunanin yanda wannan genie d'in mijin naki ya kawar miki da damuwa nan da nan, na sanki fiye da sanin kanki na san yanda kike da abinda kikeso when you are exhausted or angry, na sani cewa kina jin rashin dad'in abinda Kika ma 'yan uwana a gabana ko? Bilkisu na san ke wace irin mutum ce, kinada tsananin ha'kuri da kawarwa sau da dama zan miki abu nasan ranki ya 'baci, amma saidai kawai kice hmm ko ki nemi abin ci ki kai bakinki, ina sane da yanda kike d'ebo wanki ki fara saboda damuwa ko bakyaso kiyi magana akan abu, Bilkisu ina lura da yanda kike d'aura girki da zarar mun shigo gida a duk ranar da akayi taro saboda bakyaso abinda ya faru ya dameki, ina karantar yanda yanayin idanunki ke canzawa a duk lokacin da aka maki wani abu, tunda nake dake ban ta'ba ganin wannan side naki ba, kuma zan fad'a miki gaskiya a yau na sake tabbatarwa nayi sa'a da mace ta gari, ba wai fad'awa Yan uwana magana shine abinda ya dace ba a'a, amma yanda kike kauda kanki saboda ni shine abunda ya birgeni, kiyi ha'kuri bilkisu a yanzu hakan shirye shirye barin gidannan nake ko dan ki huta, saidai hankalina ya rabu zuwa haihuwarki da sama maki sabon mazauni". Cushion na d'auko daga kujera na kwanta nace "boo-boo na na matsu na haihu wallahi, ni ko cikin kara zan iya zama indai zan haihu, Kar ka takura ma kanka wajen neman wani gida na daban nidai ayi abinnan na haihu naji me akeji da akemin gori kaima ake maka gori akai". Mi'ka nayi domin jikina duk yayi tsami, hannu Saleh ya Sanya ya shafi inda Maimu ta mareni bud'e baki yayi zaiyi magana nace "Kar ka tunamin da wannan, a rayuwata 'karshen 'kas'kanci shine mutum ya mareni, amma babu komai ai rauwa ce, baka yi ba ma an maka balle kayi" Dariya yayi ya fara matsamin 'kafafuwana, rufe idona nayi nace "ya akai kasan abinda zai saukarmin da 'bacin rai? Ai nayi tunanin baka iya rarrashi ba". Pecking d'ina yayi a lips yace " 'kwarai kuwa ban iya rarrashi ba, amma nasan matata sarai itama ba kowane rarrashin take ji ba, sannan na lura a duk lokacin da kikayi full week kina zuwa makaranta kinfi zama active ban saniba ko gajiya ke 'kara maki kuzari ko kuma motsa jikin ne? So I just guess bari na baki abinda bazaki iya resisiting ba ko nima naji sau'ki a raina". Shiru nayi ina tunanin mijin da Allah ya bani, gashi dai Babu wata doguwar magana amma har na fara cire abinda ya faru a raina, wato Saleh ya karanceni fiye da tunanina, idan naga abu kuma inason abun kuma Ina Jin nauyin na  nauyin  na tambaya, saidai kawai na ganshi da wannan abun idan nace ya akayi ya san inaso sai yace zuciyata ce ta sanar masa, haka nima na karanci mijina iya yanda ya kamata na san abinda yakeso da wanda bayaso, nasan yanda zan sanyashi dariya na kuma bashi haushi in a good way, Ni nasan Allah ya haliccemu dan junanmu ne domin ba mata da miji kawai ba, mu 'kawa da aboki ne, abokan shawara ne, ya zamarmin tamkar babban yaya wajen tsawatarmin ni Kuma na zamar masa tamkar 'yar uwa wajen bashi shawara, tabbas nayi Dace da miji nagari. "tabbas nayi dace da mace ta gari, wato Bilkisu Allah kad'ai yasan 'boyayyen al'amarin dake cikin aurenmu, wallahi baby girl ni nasan halin da na shiga da kina gida ji nake tamkar an yanke 'barin jikina bana iya bacci saidai na tashi nayita sallah ina ro'kon Allah ya baki lafiya ya 'kara karemin ke daga fitintinu" Rub da ciki nayi yaci gaba da massaging bayana, bacci naji yana neman d'aukata nace "boo-boo na mu 'kara ha'kuri, babu wanda ya ta'ba dawwama a wahala ko damuwa wataran zamuyi farin ciki mai tsawo, ai duk rayuwar da babu 'kalubale a cikinta to dama ku binciki imaninku, yanzu dai mu zuba Ido muga abinda zai biyo baya". Shiru mukayi dukkanmu yaci gaba da massaging d'ina cikin 'kwarewa, hamma nayi nace "Allah ya maka albarka mijin 'yar aljanna" "Ameen matar d'an aljanna", ya fad'a Yana dariya, ganin zanyi bacci yasa ya dena yace na tashi yamma tayi nayi ko adduo'i ne. Kwana hud'u da faruwar wannan al'amari naji bugun gida, zani na d'aura akan short d'in dake jikina na fita na bud'e gida, ajiyar zuciya na ajiye ganin Hajiya, Sultana da kuma mahaifiyar sultana. Sunkuya nayi na gaidasu Mahaifiyar Sultana tace "ba wannan ya kawomu ba, ina yarinyar take fito da ita". Kallon Sultana nayi da idanunta sukayi ja alamun tayi kuka, tausayinta ne ya kamani duk wannan damuwar da take ciki ta sanadina ne, palour na nufa suka bini a baya sai ga Saleh ya sauko da Huda gashinta a cukurkud'e ya saka mata jeans da yellow shirt, mi'komin ita yayi a hankali yace "ba na fad'a miki zan iya shiryata ba? Gatanan kin gani ki dai gyara gashin nata na kasa gyarawa". Gaida su Hajiya yayi amma cikinsu babu wadda ta amsa, kallon sultana mahaifiyarta tayi tace "ke Sultana, ina baki umarni ki kar'bi yarinyarnan yanzunnan". Runtse idonta tayi tace "Mama Dan Allah Dan girman 'kur'ani, Mama dan soyayar da kikewa manzan Allah idan kina Sona da gaske ki 'kyale Huda a wajen Bilkisu, Mama bana son Huda na fad'a maki tun farko, sannan bazan iya kar'bar Huda ba idan Huda ba rabon Bilkisu bace da kanta zata dawo wajena". "Ba shawara nake nema ba Sultana, a matsayina na uwarki na baki umarni ki kar'bi huda daga hannun Bilkisu ta dawo gareki, ko kuma wallahi tallahi a yanzunnan na miki baki". Wata mummunar fad'uwar gaba naji na ambaci innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu akan wannan abun Mahaifiyar sultana ke ambatar wannan kalma marar dad'in ji? Hannu Sultana ta Sanya ta rufe fuskarta, shesshe'kar kukanta kawai ke fita, a hakan tace "Bilkisu.....dan Allah kiyi ha'kuri". Dama ko bata bani ha'kuri ba nayi niyyar bata 'yarta, bazan zama silar shiga tsakaninta da mahaifiyarta akan abu na son zuciya ba. Tana dur'kushe a 'kasa na mi'ka mata Huda, girgiza min kai tayi ta nuna min su Hajiya, a sanyaye na mi'ka musu Huda muryata na cracking nace "bari na d'auko kayanta". Danne zuciyata nayi na fara kwaso kayan Huda, Saleh bansan dalilin fitarsa ba amma a halin yanzu ina bu'katarsa a kusa dani, shikenan zaa rabani da farin cikina Huda. Kayan da hannuna zai iya d'auka na fita dasu na ajiye a gabansu,  dakewa nayi nace "duk abinda ya rage zan aika dashi part d'in sultana idan Saleh ya dawo". Kuka Huda keyi tana mi'komin hannu na kauda kaina kamar bansan tana yi ba, tashi maman sultana tayi ta kai mata Huda amma ta'ki kar'barta, tsawa tayi mata ta kar'bi Huda Wanda hakan ya sake gigita Huda ta fashe da kuka, hannu sultana ta Sanya ta ri'keta amma fizgewa takeyi tana nufo wurina da hannunta. Sakinta Huda tayi, rarrafowa tayi cikin hanzari ta nufo inda nake tsaye ta kama 'kafata ta tsaya. "Tashi ki d'auketa" hajiya ta fad'a Tana kallon Huda, ko da sultana ta ta'ba Huda wani matsanancin kuka ta saki tana 'kan'kame 'kafata, bakinta baya ambatar komai sai maama. A hakan babu tausayi babu imani Hajiya ta cire Huda daga 'kafata suka fita da ita, kukan Huda har cikin raina nake jinsa, Huda tayi wayon da ko makaranta zanje saidai na fita a 'boye da hijabina a jaka nake iya fita, sautinta nakeji Yana amsawa a kunnena tana ambatar maama, dafe 'kirjina nayi saboda yanda zucoyata tayi zafi, wasu hawaye ne suka zubomin nace "ya Allah idan har Huda rabona ce ka dawomin da ita, idan kuma Huda ba alkhairi bace a garenj Allah ka.za'bamin abu mafi alkhairi". *kuyi min afuwa da abinda Zan fad'a, Ina tunanin wannan shine last post da zanyi sai kuma nan da kusan wata guda, next week insha Allah zamu fara exams, I'm gonna miss you guys😥* 24 A wurin da nake zaune na zuba tagumi, Ina jin kiran sallah amma na kasa motsawa tunanin Huda kawai nakeyi, ki wajen mahaifiyarta taje kwana da sassafe ake dawomin da ita ta ishesu balle kuma wurin bare, tunda na dawo daga gida wata sabuwar sha'kuwa ta shiga tsakaninmu, ya zanyi babu Huda? Ya Huda zatayi idan babu ni?. Tashi nayi jikina babu 'kwari nayi sallah na had'a kaina da gwiwa kukan Huda kawai nakeji a cikin raina, har lokacin bacci na kasa aikata komai. Batun girki kuwa babu, Saleh tun yana rarrashina har ya dena domin da zarar yace nayi ha'kuri tamkar ya sake tunamin abinda ya faru ne, wace irin masifa ce wannan ta dangin miji da zasu raba uwa da 'yarta? A jikina ina ji cewa Huda na cikin damuwa. 8:30 Sultana ta shigo da food flask ta ajiye gabana, bata ce komai ba ta d'auko plate ta zuba abincin ta saka spoon ta mi'komin, kallon macaronin nayi irin dogayennan ce mai kama da taliya saidai gajeru, tayi mata jollof mai cike da kayan had'i gata ruwa-ruwa gwanin sha'awa saidai sam banida appetite da zanci abincin. Girgiza Kai nayi nace "Sultana bazan iya ci ba". A tunanina zata tursasani kawai naga taja plate d'in ta fara ci, tana ci Saleh ya shigo ta 'kara musu suka cigaba da ci ina zaune a gefensu. Saida suka cinye tukun ta sake zubawa tace "Bilkisu idan zaki kwantar da hankalinki kici abinci kici, wani irin azabtar da kai ne haka? Akan Huda zaki hana cikinki abinci tun safe? Ki dubi fuskata Mama ta har mari na tayi akan Huda, babu irin abinda basu ce ba to amma ya zanyi? Idan akwai abinda Huda zata so shine ki zauna da kuzarinki domin 'kwato mata 'yancinta, inada tabbacin Huda bazata jima ba zata dawo gareki, wallahi na dad'e ina mafarkin wata mata mai yalwataccen haske tana ri'ke da yarinya suna zagaya wani lambu mai matu'kar kyau, ina zaune daga gefe ina kallonsu dukkanmu fuskarmu cike da annuri, Bilkisu tun kafin na haifi Huda nake wannan tunanin kuma a hankali Allah ya nunamin kece uwar da ta dace da Huda, tunda Huda ta'ki zama da kowa na tabbata ba rabin kowa bace rabonki ce, kuma wallahi duk inda take sai ta dawi domin Allah ya baki babu mai ikon 'kwacewa, nifa zaman gidannan ya isheni shi kanshi ya Usman yace ya fara gajiya, dukda babu Wanda muka sanarwa sai ke amma muna tunanin barin gidannan zamuyi, domin wannan gidan baiyi ba, ban ta'ba sanin zaman family a had'e tashin hankali bane sai akan namu wallahi na gaji, da ace munada hali ma garin zamu bari duka, kaima Saleh abinda ya dace kenan, ka nema mata gida ko na haya ne ku koma ku huta, wannan mutanen zasu kashe mutum da ransa, kaga dai 'yan uwana ne amma wallahi ina takaicin kasancewarsu dangina". Shiru nayi ina kallon Sultana yanda take maganar cike da 'bacin rai, kuma tabbas gaskiya ta fad'a indai haka zaman dangi yake to baida amfani, ni bare ban huta ba itama 'yar gidan bata huta ba. "Kici abinci muga zuwa gobe da safe abinda zai faru kuma, mama ta ta tafi da Huda bansan ya zasu 'kare ba, amma dai ko mene bazan bar gidannan ba sai kin ci abinci". Abincin har ya fara hucewa haka na daddanna domin yunwa taci 'karfina sosai, saida na cinye abincin farantin duka sannan Sultana ta tafi bayan tayimin al'kawarin da kanta zata je ta gano Huda gobe ko kuma tayi waya taji lafiyarta. Ko da na kwanta bacci juyi na dinga yi, baccin ma cike da mafarkai marasa dad'i akan Huda, kusan yanda naga rana haka naga dare har daren ma yafi tashin hankali. Wasa wasa har akayi kwana biyu, takurawa kaina nake akan na cire tunanin Huda na ha'kura da ita amma na kasa, dai-dai da minti d'aya Huda bata bar cikin raina ba, saidai addu'a nake Allah yasa tana cikin 'koshin lafiya. Ranar da Huda ta cika kwana hud'u a wurin maman Sultana ina Shirin fita sai ga sultana ta shigo, yanayinta kawai na gani naji hawaye na neman zubowa. 'ko'karin 'boye damuwarta tayi tace "wai meke damunki ne dan Allah Bilki? Duk kinbi kin sakawa ranki masifa akan 'yar da ba ma ke kika haifa ba, to da haifarta kikayi mutuwa zakiyi kenan idan an kar'beta ko me?" Muryata na rawa nace "Dan Allah ki fad'amin me ya sami Huda?" Numfashi ta sauke tace "ba wani abu bane mama tace zazza'bi ne kawai yayi mata 'karfi yanzu haka suna asbitin UMC". Hango zazza'bin yara kawai nakeyi yanda ake kawo mana su wasu na farfad'iya wasu na suma wasu na fita hayyacinsu, ciwon yara yafi na manya tashin hankali balle kuma Huda 'yata. Duk yanda naso na nuna dakiya a matsayina na Nurse da ta saba fad'in tsananin ciwo, mutuwa, damuwa da duk wani abun tashin hankali sai naji na gaza, jikina rawa ya kamayi hawayen da na danne tuni ya zubo, cikin sauri na goge tareda d'auke kaina cikin Jin kunyar Sultana, ita da take Mahaifiyar yarinyar ma bata nuna damuwa ba kamar ni, murmyata a 'kasa nace "kiyi ha'kuri". "To ya zanyi dake Bilki? Ni da nasan wanda ma ya baki license da sai na bishi nace ya 'kwace, for God's sake a haka kike kulawa da 'ya'yan mutane sama da goma masu tsananin ciwo? Anya kina aikinki yanda ya kamata kuwa?" Fita nayi ta biyo ni a baya, motar Usman muka shiga saidai babu mai magana a cikinmu, waya na ciro na sanar cewa zan makara 'yata ba lafiya. Muna zuwa asbitin jikina ya fara sabon 'bari, zuru-zuru nayi kamar mara gaskiya domin na gaji da d'aukan cin mutuncinsu, kuma a yanayin da nake zuciyata zata iya bugawa matu'kar suka tozarta ni a asbitinnan. Hannuna sultana ta ri'ke muka shiga, ta waya akewa usman jagora har d'akin da aka kwantar da Huda, babu addu'ar da ban ja ba harda ta shiga band'aki duk saboda sharrin wad'annan mutane. Ko da sultana ta bud'e 'kofar ji nake kamar zuciyata zata fita saida na dafe 'Kirjina da hannuna na d'an dur'kusa domin numfashina kansa sar'kewa yake saboda tsananin tsoro. Kallonmu hajiya da Maman huda sukayi tamkar sun San da zuwanmu, ban gaidasu ba saboda bana cikin yanayi na gaisuwa ji nake zuciyata kamar zata fito, meke faruwa dani ne? Hango Huda nayi kwance kan gado hannunta da cannula, dukda ban hango fuskarta ba amma ina hango yanda jikinta ke motsawa a kowane numfashi da takeyi alamun ajiyar zuciya take saukewa. Ji nake kamar na 'karasa da gudu gareta saidai dole ne na tsaya a limit d'ina, jan hannuna Sultana tayi na tsaya a wurin na'ki motsi, d'aga murya tayi tace "kizo muje ki ganta mana tukun ki tafi? Gani dai ai ba cutarwa bane". Babu wanda ya d'ago kai ya kalleni a cikinsu hakan ya bani 'karfin gwiwar 'karasawa gareta, tausayinta sosai ya kamani yanda ta zuge cikin kwanaki hud'u, dama kuma Huda ba auki ba ta zama kamar wadda tayi cutar watanni. A hankali na sanya hannu n shafi gashin kanta da na kitse kwana biyu kafin kar'barta, ta'ba goshinta nayi tayi motsi cikin sauri na d'auke hannuna. Juyowa tayi muna had'a ido tace "Maama" sai kuma ta fara kuka, hannunta take mi'komin cikin gwaranci da kuka tace "akkeni". Ganin zata goce allurar hannunta ya sanya na d'auketa cikin dabara, muryar Hajiya naji tace "likita fa yace Kar a d'auketa ke wa ya baki damar d'aukanta". Numfashi na sauke ina jin 'kirjina na sake d'aurewa nace "Hajiya nima fa nurse ce, ya fad'i haka ne saboda ba kowane irin ri'ko za'a mata ba amma ni nasan yanda zan ri'keta ba tareda matsala ba, kuma kina gani kuka take bazai yiwu a barta kwance ba". Ta bud'e baki zatayi magana sai ga likitan ya shigo, har wani annuri ne ya bayyana a fuskarta ganin likita ya shigo wato zai min fad'a kenan, ta manta uniform ne a jikina duk inda na shiga an San practicing nurse ce. Cikin ladabi na gaida likitan na sanar masa wacece ni sannan na tambayi jikin Huda, da turanci ya fara min bayani yace " She passed out due to energy exhaustion maybe from crying, she was brought here unconscious with high fever since around 3 in the evening until 6pm, you have to be careful with her she has a weak heart, if something like this happens again we might loose her" Kallon Huda nayi na rasa ma me nakeji a raina, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un nake maimaitawa a fili, kallonta yayi yace "did she lost her mom? She called said maama the moment she wake up". Kallonsa nayi naga alamun dai yana jin hausa, dukda suma nasan suna jin turanci nace " likita ko zaka sake mana bayanin meke damunta?" Dalla-dalla ya sake bayanin ina kallon su Hajiya jikinsu yayi sanyi nace "To doctor meke sanya yara su taso da irin wannan matsalar?" " Halitta ce, wasu yaran sunada tsananin sha'kuwa da iyayensu ne ta yanda zakiga ana raba yarannan da iyayensu zasu shiga damuwa musamman yara irin wad'annan, Allah ya haliccesu da zuciya mai matu'kar rauni da abu kad'an kan iya sanyasu damuwa dukda su basusan ma mene damuwar ba, muu samu irin wannan case watanni da suka wuce amma ita babyn nata yayi worst, ko kuka tayi kad'an sai ta fara numfashi sama sama, daga 'karshe zuciyarta ta zama very weak and she couldn't make it, idan mahaifiyarta ta rasa it's better ku nemi wadda tazayi replacing d'inta ko da a kamanni ne ko a closeness da ita wannan yarinyar, and if possible please she should be always happy daga nan har lokacin da zatayi wayo sosai domin wannan shine danger stage d'in domin iyaye baku fiye gane concern na yaranku a wannan time d'in ba" . "Mun gode likita Allah ya saka da alkhairi insha Allah zamu kula, yaushe zamu tafi?". Kallonta yayi yanda ta ri'ke rigata gam kamae her life depends on it tana baccinta, murmushi yayi yace "at least ta samu bacci yanzu, da zarar ruwannan ya 'kare zaku iya tafiya, a kiyaye please". Yana fita kuwa bud'ar bakin Hajiya sai cewa tayi "to yanzu tunda yarinyarnan tanada matsala ba sai a maidata wajen uwarta ba ko? Tunda gashi dai abinda likita ya fad'a tana bu'katar kasancewa da uwarta". Take yanayin Sultana ya canza, ganin zata 'bata lamarin yasa na ri'ke hannunta da ido ina mata alamun kar ta bamu matsala. Numfashi taja ta sauke tace " Hajiya duk abubuwan da likitannan ya fad'a iya wanda kikaji kenan? Kina ji fa ya sanar cewa tana farkawa ta kira maama, wa take kira da maama bayan Bilki? Muryarta har tayi 'kasa saboda tsananin kuka da Kiran maamanta, kin kuwa tuna sanadin fad'awarta wannan halin? Saboda an rabata da maamanta ne, a wajen Huda bata da wata uwa bayan Bilkisu, ki duba yanda take ri'ke da jikin Bilkisu tamkar za'a 'kwaceta daga gareta, hajiya Huda 'yata ce kuma farin cikinta da lafiyarta yafimin komai, bari kigani". Zama tayi ta kar'bi HUDA, tana Sanya Huda a cinyarta ta farka daga baccin da takeyi, kallon fuskar sultana tayi ta ta'be baki tace "maama" idonta na kawo 'kwalla, mi'komin ita Sultana tayi take tayi shiru ta koma kwanciyarta tare da kama rigata, nuna musu ita Sultana tayi tace "Wannan kad'ai aya ce garemu, idan har muna son lafiya da rayuwar Huda mu barta ga Bilki, wannan shine kad'ai abinda zai sama mana lafiya ya kuma samawa Huda lafiya, a lokacin da Huda tayi wayo ta mallaki hankalin kanta zata nemi uwarta da kanta kamar yanda kuke cewa" dur'kusawa tayi a 'kasa tace "Mama, Hajiya na ro'keku dan Allah ku bar Huda a wajen Bilkisu inaso naga 'yata ta rayu, banaso naga ta tashi da matsalae zuciya kamar yanda bazaku so ganina da matsalar zuciya ba". Shiru sukayi dukkansu suka gyad'a kai, tashi sukayi Hajiya tace "kwa taho da ita kayanta suna wajena". Farin cikin da naji baida misali, a Raina na musu godiya domin bakina bazai bud'e ba. Gidana na tafi da Huda ina addu'ar Allah yasa wannan shine 'karshen wahalata a wannan gida, domin bana tunanin zan iya jure wani abu bayan wannan. Alhamdulillah mun samu zaman lafiya, gaba d'aya Hajiya ta fita daga harkata sun fita daga harkar Huda, tunda aka sanarmin tana da weak heart ko kuka bana bari tayi mai tsayi, dukda nasan ina sangartata amma banida wani za'bi, duk abinda Huda zata bu'kata ina tabbatar da ta samu komi wahalarsa. Na gama internship d'ina cikin ikon Allah kud'in da gwamnati take biyanmu na internship ban ta'ba komai ba, kusan miliyan d'aya da rabi na had'a a shekara target d'ina shine IVF, idan na bawa Saleh ya cika nasan lokaci kad'an ya rage ayimin na haihu nima na huta, dukda inada Huda amma idan na tuna gorin haihuwa abin na damuna, sannan sun fini iko da Huda a kowane lokaci suna iya rabani da ita yayin da ta girma. Sanye nake da Riga da wandona tight ina jiran shigowar Saleh, 'karan motarsa naji na tashi na sake gyara wurin dukda komai tsaf yake na fita taroshi. Da mursmushi muka tari juna ya kama hannuna tare da d'aukan Huda duk ya sumbacemu a kumatu, ri'ke 'kuguna yayi yace "Allah yasa dai kujerar hajji zaki biyamin kika kasa daurewa saida Kika kirani Ina aiki". Murmushi nayi nace "ka huta mana ka fara cin abinci sannan muyi". Impatiently ya buga 'kafarsa kamar wani 'karamin yaro yace "Kai dan Allah ni bazanci abinci ba sai kin fad'a min, wa ya saka ki tasoni daga aikina inata d'okin dawowa........" Cak ya tsaya yaja da baya yana 'karemin kallo, tamkar me rad'a yace "are you pregnant?" Dariya nayi na girgiza kai nace "boo-boo.....no ba ciki ne dani ba amma dai maganar zamuyi". Takura min yayi bayan mun zauna, abincin da na ajiye ko kallansu baiyi ba yace sai na fad'a masa dalilina na kiransa, gyara zama nayi nace "boo-boo na nasan kana ta fafutukar yanda zaka had'a kud'in aikina na IVF, shine naga nima ya kamata na kawo nawa, kasan dai tsakanin Mata da miji akwai taimako ko? Kuma ba wai zanyi ne saboda ka gaza ba a'a, na had'a kud'in internship d'ina ne sama da one million na shekara guda, banida wani abu da zanyi dasu yanzu shine na yanke shawarar na baka ka had'a a kud'in tafiyarnan tamu, kaga ai mun rage ko?" Shiru yayi har saida na shiga damuwa tunanina ransa ya 'baci, d'agowa yayi ya shafa fuskata tareda murmushi yace "Ina miki albishir da cewa, nan da wata shida masu zuwa da yardar Allah kema kina hanyar samun d'anki ko 'yarki na cikinki, kud'in aikin naki tuntuni na cike wani loan da ake bayarwa na miliyan biyar, har na cire rai suka sake kirana suka sanar dani naje a sake min interview nan da four to five months kud'i zai shigo". Farin cikina bashida misali, lissafi na fara at least dai nan da shekara d'aya da rabi nima na zama uwa. Saidai tunanina dangin mijina, yanzu kuma ta wacce hanyar zasu 'bullomin domin duk inda zan samu alkhairi sai sunbi sun toshe 25 Bilkisu yarinya ce da ta taso a gidan yayar mahaifiyarta, mahaifinta ya rasu tun kafin haihuwarta mahaifiyarta kuma ta rasu bayan ta haifeta, hakan bai sanya Bilkisu ta taso a maraici ba, hasalima ta taso cikin gata kasancewar yayar mahaifiyarta d'anta d'aya Namiji a duniya, jabir. Kamar yanda al'adar gidan su jabir take kowacce mace ana aurar da ita ne ta hanyar auren zumunci, lokacin da auren bilkisu ya taso baba, wato maiahifin jabir ya za'ba ma Bilkisu d'an abokinsa da ya kammala karatunsa a 'kasar Russia, saidai d'abi'ar sa da halayensa sunsha  ban-ban da yanda Bilkisu take so. Hakan ya sanyata shiga damuwa sosai, abokin yayanta SALEH shine yake rarrashinta da kalamai masu sanyaya zuciya, hakan ya sanya ta fad'a soyayyarsa ba tareda ta shirya ba, bayan wasu al'amari da suka faru Bilkisu ta bayyanarwa iyayenta Saleh takeso, babu jayayya aka aura mata shi. Tun ranar da Bilkisu ta Sanya 'kafarta a gidansu Saleh tasan cewa she's not welcomed, Mahaifiyar Saleh ta tsara Masa l auren 'yar 'kanwarta SULTANA, inda Saleh ya bijirewa umarnin hajiya saboda BILKISU, hajiya da sauran Yan uwan Saleh sun d'auki tsana sun d'aurawa bilkisu, haka alamura suka yita faruwa marasa dad'i har SULTANA ta samu ciki ta haihu ta sake samun wani, takura da natsawa sun yiwa bilkisu Yaya yayinta dangin mijinta ke zargin planning tayi domin karta haihu tana karatu. Bilkisu tayi gwajin fertility anan ta samu most shocking news of her life, cewa bazata iya samun ciki ba saidai a Mata IVF, bayan wannan abun ya faru SULTANA ta d'auki yarta da ta Haifa ta baiwa Bilkisu ba tareda sanin kowa ba sai mijinta , duk yanda dangin Saleh sukaso ya sake aure ko ya saki bilkisu ya'ki amincewa, karshe suka had'ata da shaid'anu sannan sukayi kokarin k'wace Huda daga gareta, a wannan lokaci ne aka sanar musu Huda nada matsalar zuciya takurawa zata it sanyawa a rasata, Kan Dole dangin Saleh suka barwa Bilkisu Huda domin tafi amincewa da ita Kan uwarta, Saleh ya sanarwa bilkisu cewa saura kad'an ya kammala had'a kud'in aikinta suje a artificial insemination...........anan labarinmu ya tsaya Masu nema daga farko na rage masu aiki😅😅😅😅😅 ************* "Oh come on...... komai sai kice Huda, to Huda kwakwalwarta wani ri'kon abu zatayi? Infact ba fa wani abu nace ba kawai I just want to kiss you kafin na fita". Kallonsa nayi tareda kashe ido d'aya, yayimin matu'kar kyau yanda ya turo bakinsa Yana buga 'kafarsa kamar yaro, ni kaina zanso ace yau ranar kawai tamu ce mu wuni muna ririta juna, amma dole ya fita aiki, sannan bazai yiwu na barshi ya lasamin Zuma sannan ya tafi ba, Sarai nasan mijina is a good teaser. Kwanciya nayi kan love seat dita na tan'kwashe 'kafafuna tareda d'aura 'kafa d'aya kan d'aya, cije le'bena nayi jin ya saki wani sauti tareda matsowa inda nake kwance, kallon bayansa nayi naga Huda tabi motar wasanta bayan kujera. Sunkuyowa yayi numfashinmu na gaurayuwa, bud'e bakina nayi zanyi magana naji ya hade lips d'insa da nawa, lumshe ido nayi tareda mantawa da duniyar da nake, banajin komai sai hannunsa dake zagaye 'kuguna, muryar Huda naji tana kirana a hankali na tureshi tareda tashi, wani murmushin mugunta yake yi na harareshi cikin wasa tareda bin muryar Huda, ko ya akai take guest room oho. A bakin gado na ganta tana 'ko'karin shigewa 'kasan gado, d'aukota nayi da motarta da ta shige 'kasan gadon na fito da ita, har yanzu sauke numfashi nakeyi, a tsaye na sami Saleh da jakarsa a hannu yace, "sai na dawo boo-boo na, me zan taho miki dashi?" Hugging d'insa nayi ta gefe nace " kai nakeso ka dawomin da kanka lafiya, yanda fuskarka ta tafi cikin walwala haka nakeso ka dawo, Allah ya tsaremin kai ya kautar da mugun ido daga gareka". Kissing kumatuna yayi yace "I love you". Kafin na amsa Huda ta mika masa hannu, na lura Huda ta fara kishi dani ba damar taga muna soyewa sai tayi interrupting, haka duk abinda aka min sai an mata. Saida yayi pecking dinta tukun ta dawo hannuna, iya 'kofar gidana na rakashi saboda kayan dake jikina bazan iya fita ba, d'aga masa hannu mukayi ni da Huda har ya fice da motarsa. Abubuwa sun canza sosai, Alhamdulillahi na samu kwanciyar hankali domin duk sun watsar dani,rabona da hajiya nafi wata biyu ko sallama bata had'a mu ba, Sultana ce ma muke d'an gaisawa amma itama na jima ban ganta ba, kowa harkar gabansa yakeyi. D'aki na shiga na samu wurin ajiya mai kyau, Domin Saleh yace zai fara bani ajiyar kud'insu na kafintanci, Domin an fara sata a shagunan kusa dasu sannan kud'i ne na da basaso su sanyashi a banki, 'karshen shekara zasuyi lissafi suga ribarsu sannan su siyo kaya da ragowar, a ciki ne yace idan sun raba shi nashi kason zai cika muje Dubai. Da farko na'ki amincewa da Ajiyar kud'in amma bayan doguwar magiya da kuma kirana da jabir yayi ya ro'keni na kar'ba babu yanda zanyi dole na amince, gashi yanzu duk inda na kalla sai naga kamar bai dace da ajiyar kud'i ba. Shawara ce tazo min na d'aga gadona, kasancewarsa gadon zamani a rufe yake ta ko ina, sai an d'aga katifa sannan a d'aga katako anan zakaga 'kasan gadon, an sanya katako an rarraba k'asan gadon. Bankin da Saleh ya kawomin na d'auka na Sanya a k'asan gadon, sai a yanzu na samu kwanciyar hankali nasan insha Allahu kud'insu is safe. 5:30 Saleh ya dawo, yana zama ya mi'komin kud'in, zare Ido nayi ganinsu da yawa na bud'e na 'kirga, 250,000, d'auko bankin 'karfen nayi na saka key na bud'e padlock d'in sannan na saka kud'in na rufe na maida, harkokinmu muka shiga kamar muka manta da wannan ajiyar saidai na rasa nutsuwa bana son harka da kud'in mutane sam. Washegari tare muka fita ya ajiyeni a gidan mama na jima banje mun gaisa ba,anan na na wuni sai dare tukun muka koma gida. Kujera na kama cikin sauri na Kai MBC action, ban ta'ba kallon wrestling ba sai yau abin mamaki ya shiga raina, talla nagani a gidan mama kawai naji inason kallan wrestling. Huda tayi bacci tana kujera tana kwance, zama Saleh yayi ya Sanya hannunsa a kafad'ata yace "da gaske wrestling zaki kalla?" "Eh mana, kaga wancan? To last week anyi dashi wancan me Jan gashin ya 'kwace masa trophy d'insa, shine fa yau ya dawo ya kar'bi abinsa, kuma kaga fa wannan mutum uku akan mutum biyu sannan wancan......." Dariyarsa ce ta katseni nace "menene?", "Yaushe Kika kalli wannan har kike bada labari?" " Jabir ne ya bani labari ai, yanzu  dai yi shiru Muji me suke cewa". Shiru yayi saidai Ina jin idonsa a kaina maimakon a tv, hannu ya Sanya ya shafi gefen fuskata nayi murmushi ba tareda na kalleshi ba, "side view naki kinada matu'kar kyau Bilkisu, kinga yanda bakinki ke motsawa idan kikayi murmushi? Gashin idonki gwanin sha'awa, ga lebenki a duk lokacin da kika motda bakinki.......gaskiya nayi dacen mace a duniya, Kai har lahira ma da yardar Allah". Kwanciya nayi kan kafad'arsa nace "nagode sosai". Sake matso dani jikinsa yayi muka fara kallon wrestling d'in, duk na cikwikwuye Masa riga saboda tsoro, wad'annan mutane akwai mugunta, rufe idona nayi tareda 'kan'kame Saleh ganin wani ya d'auko kujera ya Sanya kan opponent din nasa cikin kujerar had'a kan opponent d'in da garu a cikin kujerar, jini ke zuba, inada tabbacin wancan ya mutu. Jikina duk ya d'auki rawa shi kuwa Saleh dariya yakeyi, d'ago kaina yayi yace "kalli kigani, paramedics sun d'aukeshi yanzu aka rubuta cewa bai mutu ba amma an kori wancan daga wrestling d'in saboda ya karya doka, kinga zai daki wani d'an kallo". Ban bud'e idona ba kuma ban sakeshi ba, muryata a hankali nace " Dan Allah canza channel banaso na sake gani". "An gama ai yanzu ma maze runner zasuyi, d'ago ki gani". Daga kaina nayi Naga da gaske an gama, kwanciya nayi na d'aura kaina a cinyarsa na fara kallon maze runner, bansan lokacin da bacci ya d'aukeni ba. Wani mummunan mafarki nayi, inda naga Saleh cikin wani yanayi mai firgitarwa, tsayawa yayi a kaina cikin tsawa yace "bazaki fad'amin gaskiya ba!!!!" Tsoro da firgici sun hanani magana, hawaye ne kawai ke zuba daga idona gefe d'aya kuma ga hajiya da su maimu fuskarsu d'auke da walwala, murmushi hajiya tayi tace "meye ban sanar maka ba? Gashinan ai yanzu ka gani da idanunka" Kallona Saleh yayi saidai babu abind nake gani a idonsa face tsana, takaici da nadama, wata takarda ya jefomin yace "kin bani kunya". Bud'e baki nake amma babu kalmar da ta iya fitowa, numfashina ya sarqe a wuyana, ambatar sunansa nake amma babu Wanda yakeji sai ni, da kyar na  furta da wuri Wanda ya sanyashi juyowa a firgice, dawowa yake gareni da sauri saidai maimu tazo ta tsaya a gabana tareda dafa kafad'ata, ji nayi tamkar an sakar min kibiya a wurin, kallona tayi ta kalli Saleh tace "lokaci ya 'kure" tareda murmushi a fuskarta. Bansan me ya faru ba da ya sanyani tsorata, cikin firgici na tashi inaja da baya tareda fara gudu, muryar Saleh nakeji Yana kirana saidai na kasa tsayawa, zuciyata rayamin take idan har na tsaya zai cutar dani, matsowa yake dab Daniel saidai ba tareda na waiga ba nake ambatar "karka matso kusa Dani, banaso Kar ka cutar dani ka bari!!!"........ A firgice na farka tareda Jin kiran sallar asuba, fuskata ta ji'ke da gumi ga bugun zuciyta da ninka kusan sau hud'u, har saida na dafe kirjina saboda yanda nakeji bugun zuciyata, wani irin mafarki ne haka? Me yake nufi?. Kar kuce yayi kadan banajin dad'i ne, luv u all😘😘😘😘😘 26 Tashi nayi jikina babu 'kwari, mafarkin da nayi sake dawomin yakeyi tamkar da gaske ya faru, girki nake amma hankalina sam baya wannan duniyar. Tsorata nayi jin muryar Saleh a bayana, hannunsa ya zuro ya ri'ke cikina tareda juyani a hankali, "ina kwana" na fad'a cikin sanyin murya. "Kin tashi lafiya?" Ya fad'a tareda kissing kumatuna, "you look stunning as ever". 'ka'kalo murmushi nayi domin ji nake kamar hawaye zai zubomin, meyasa mafarkinnan ya razanani haka? Me ke Shirin faruwa damu ne? Tabbas mafarkin yayi min kama da zahiri, sannan naga alamin laifina ne, to me zai faru tsakaninmu domin tashin hankalin da naga mun riska a mafarkin bana bu'katar na ganshi a zahiri. "Bilkisuuuu!!" Naji Saleh ya ambaci sunana a saitin kunnena tareda d'aga muryarsa, kallonsa nayi nace "um?", Juyoni yayi ya zubamin ido yace "meke damunki? Bakida lafiya ne?". "Lafiyata lau inaga baccin ne bai isheni ba kasala kawai nakeji". Kallona yayi alamun bai yarda ba yace "kasalar ce ta sanya inata miki magana bakisan inayi ba? Me kike tunani ne haka?". Shiru nayi na d'aga kaina, had'a Ido mukayi cikin sauri na sauke kaina, hannunsa ya Sanya a kafad'ata yace "me ya faru Bilkisu? Idan akwai wata damuwa ne ki fad'amin, me aka miki? Waye yayi miki? Mama ce?". Girgiza kai nayi inajin zuciyata babu dad'i, gaba d'aya na karaya ji nake tamkar wata katanga ke gina kanta tsakanina da Saleh, meyasa bayan mun samu kwanciyar hankali zuciyata bazata huta ba? Wannan illusion d'ina ne kawai mafarkine mara ma'ana, idan har na kalleshi ta hanya mai kyau komai zaiyi daidai, idan kuma naci gaba da kallonsa ta hanya marar kyau tabbas Ina cikin matsala. Saidai zuciyata ta gama rayamin tabbas fa akwai abinda zai faru marar dad'i, mafarkina gaskiya ne ba tunani bane, ya zanyi idan wani abu ya Sami Saleh a dalilina?. "Ya Isa, ya isa babu abinda zai faru kinji? Ko ma waye ya miki laifi zanyiwa mama magana kiyi ha'kuri, banaso kina zubar da hawayenki boo-boo na wallahi" Saleh ya fad'a bayan yayi hugging d'ina, cikin sauri nace masa "babu abinda aka min boo, mafarki nayi da mahaifiyata kawai kayi ha'kuri idan na sanyaka a damuwa". Cigaba yayi da shafar bayana har saida hawayena ya tsaya sannan yace "Allah ya ji 'kan mama ya mata rahama" "Ameen" na fad'a tareda kakalo murmushi, hannu na Sanya a na shafa hannunsa nace "ganina zuwa saura kad'an na 'karasa". Ya lura so nake kawai ya barni ni kad'ai baice komai ba ya fita, 'ko'karin kauda mafarkin nayi a raina, idan ma Abu ne zai faru ai future ne, abinda ya kamata shine nayi cherishing farin cikin da nake ciki. Cikin wasa da dariya muka gama breakfast na shiga ayyukan gidana, ina gamawa na kira mama muka gaisa, mun d'auki kwana hud'u Banga alamun wata matsala ba na saki jikina Bayan sati biyu Saleh ya sake kawomin kud'in ajiya, 'kirgasu nayi nace "wasa-wasa fa boo-boo kun kusa had'a 500, indai yakai 1million inada 200 a ciki". Dariya yayi yace "duka ma zai iya kasancewa naki ne". "Asbitinnan na Dubai...." Shiru yayi ba tareda ya 'karasa maganar da zaiyi ba, murmushi nayi domin nasan dalilin da ya hanashi 'karasawa, na sanar masa banaso muna maganarnan akai akai har sai lokacin yayi, domon duk ranar da mukayi maganarnan sai yanayina ya canza, ji nake kamar ban cika mutum ba, tamkar akwai halittar da ta ragu a jikina. " D'azu na shiga website d'insu har munyi magana da wani likita, tunda kinga nan da watanni kad'an da yardar Allah kud'in zai had'u, likitan ya sanarmin mu tura picture na result d'in gwajinki recent one, kuma yacemin zamu iya zuwa a hakan, ayi miki aikin daga baya sai mu bada sauran kud'in". Shiru nayi kwakwalwata na processing abinda ya faru, na kasa had'a pieces na maganar Saleh, hakan na nufin cewa cikin satittika ko watanni kad'an zan Samu ciki?. "Kwarai kuwa boo-boo na, insha Allah nan da sati uku zamu fara shirye shiryen tafiya" Dariya nayi nace "bansan cewa da 'karfi na fad'a ba". Shirye shirye na fara na tafiya,  duk yanda naso na rufe bakina kar na fad'awa mama murna ta hanani, a 2nd week na kirata, tana amsawa ban jira mun gaisa ba nace "mama albishirkinki, farkon July dai insha Allah muna Dubai". "Masha Allah tafiyar ta taso kenan". Ta fad'a cike da farin ciki "Eh mama, tun last two weeks ya fad'amin yace zamu fara shiri nan da sati uku, dama wasu kud'i yake jira kuma a satinnan ma har sun shigo, next week ,zuwa dai July d'in mun gama shiri sai tafiya" "Masha Allah, Allah ya kaimu lafiya ya bada sa'a, kuma duk ya gama hada kud'ad'den?" "Eh kusan dai an had'a, dama tun  watannin da suka wuce ya had'a miliyan 2 da abubuwa, to kud'ina na internship na bashi ya had'a a ciki, idan ya kar'bo wannan kud'in kusan 5m kenan, zai ishemu har iya zaman da zamuyi a can". Ina rufe bakina naji alamun mutum a 'kofa, tun ban juya ba gabana ya fara fad'uwa, bansan tsautsayi da ya sanyani waya a palour ba. Juyawa nayi naga jumana a tsaye, sallama tayi min a hankali da Sam muryarta bata fitoba, "mama zan kiraki anjima" na fad'a tareda katse wayar na amsa Mata sallamar nace "ya akai". Dariya tayi ta kama kujera ta zauna tace "haka kuma kika koma saukar ba'ki bilki? Ko kuma duk canjin na an samu kud'i ne?" Ban tanka mata ba ta girgiza kanta tace "zanso naga yanda su mama zasuyi idan sunji zancennan, ana can ana fafutukar had'a kud'i Ashe ga inda kud'i suke, har an rasa abinda za'ayi dasu ana shirin tafiya yawon duniya ko?". Dukda na tsorata amma na danne nace "jumana kud'in mijina kud'insa ne, baku da damar yin iko dashi, kuma abinda zamuyi ba abinda ya shafeki bane, kud'innan ko zubar dasu zaiyi a kwata babu ruwanku a ciki". Waya jumana ta ciro, dukda zuciyata na ingizani na ro'ki jumana kar ta Kira ko ma waye take son kira amma na gaza yin hakan, lokaci yayi da ya kamata na tashi na nemi 'yancina da kaina, ha'kuri na yazo 'karshe sun Riga sun kaini bango, wannan shine kad'ai opportunity  d'ina babu Wanda ya isa ya hana wannan tafiya tamu sai mahaliccinmu. "Hello yaya ya mai jikin?..... Yauwa Allah ya 'kara sau'ki, mu had'u anjima a gidan mama akwai magana babba ma kuwa.... a'a kedai kizo mana magana ce mai muhimmanci sosai wallahi.....yauwa to sai kinzo....eh duk su zo....to Allah ya 'kara sau'ki". Tana katse wayar naji tamkar an zaremin laka, me zai faru idan jumana ta sanar musu? Me zasu aikata? Bazan ta'ba bari su sake wargaza min rayuwata ba. Tashi tayi tace "dama zuwa nayi na sanar miki d'an gidan yaya maymu bashida lafiya, ita munafukar taki nasan Bata sanar miki ba tunda tana fama da kanta itama, sai mun had'u anjima ko?". Binta nayi da kallo har ta fita, zagaye d'akin na fara na kasa yanke shawarar komai, cikin sauri na laluba number Saleh a wayata na kirashi. "Hello boo-boo na ya akayi ne? Har kin fara missing d'ina ne? Domin ni ban fara ba". "Boo akwai matsala, jumana tasan da tafiyar mu". "Kai boo-boo kefa akwai tsoro, wa zai fad'a mata? Ya akai ma Kika san ta sani? Fad'a masa komai nayi, shiru yayi na d'an lokaci sannan yace "ba matsala karki damu kinji? Zan san abin yi idan na dawo". Hankalina gaba d'aya ya tafi part d'in mama, idan suka zo me jumana zata ce musu? Me zasu yi?, Kwantarwa da kaina hankali nakeyi dukda nasan matsala dole ta faru, saidai ina fatan kar ta zama babba. Tunawa da mafarkina nayi wanda ya sake tsorata ni, me zai faru idan mafarkinnan ya zama gaske? 3:00 naji shigowar motar Saleh, jikina a sanyaye na fita, hugging d'ina yayi ta gefe yace "hajiya ce ta kirani tace na dawo yanzu-yanzu, bari naje duk yanda akayi zan sanar miki". Gyad'a kai nayi na koma na zauna ina tunanin abinda yake faruwa, ko dai hajiya cewa zatayi ya kawo kud'in, to me zai sanya maganar kud'i ta zama babbar magana? 4:10 ina idar da sallah saleh ya kirani a waya yace naje, takalmi na sanya na tafi cikin sauri ko rufe gidan banyi ba. Muryata 'kasa-'kasa na gaidasu babu wadda ta amsa, kafin na zauna hajiya tace "kud'in da kike bada labarinsu a waya na waye?" Kallon Saleh nayi ya kalleni kawai ya d'auke kai, "tambayarki nakeyi kud'in waye?". Kasa cewa komai nayi domin bansan me Saleh yace ba, saida ta sake tambaya nace "hajiya kud'ina ne". "Ina kika samu wannan kud'ad'den?" Shirya 'karyar da zanyi nake saidai naga meye amfanin hakan? Dole dai gaskiya zatayi halinta idan lokacin tafiyarmu yayi, gyara zamana nayi cikin confidence nace "mama kud'ina ne amma Saleh ne ya bani su, mun tara ne ba don muje yawon duniya ba, aiki zamuje ayi min na haihuwa". Tsaki maymu taja tace "idan Allah bai baka haihuwa ba akwai shegen da ya Isa ya baka ne? Masu bijirewa ikon Allah, haka zakuje ayi aikin kizo ki haifi d'a kamar aljani". Kallonta nayi nace "ko me na Haifa ai yafi babu ko? A tunanina abubuwan da kukemin saboda ban haihu bane, idan na haihu nima kuka tabbata mahaifata tanada lafiya sai hankalinku ya kwanta". "Wace lafiyar mahaifa? Ai lafiya kuma babu zancenta tunda babu ta yanda zaki samu ciki ki haihu saidai wani 'katon banza yayi miki cikin, abinda ma gashinan malamai na fad'a zina ce wannan dashen cikin shine zakuje ayi miki, saboda shi mijin naki bai san ciwon kansa ba". Kursum ta fad'a cike da 'bacin rai, nunata Saleh yayi yace "ki iya bakinki, Bilkisu matata ce kuma ra'ayi na ne wannan, babu ruwanku a ciki". "Ba wannan ne ya Sanya na taraku ba" hajiya ta fad'a cikin iko "yaron maimuna bashida lafiya kuma kana sane, tunda aka haifi yaronnan suke yawon asbiti akan matsalar zuciyarsa gashinan shekara hud'u Babu wani ci gaba, a asbiti an fad'a mana cewa sai an masa aiki, kuma indiya za'a kaishi aikin,babansa ka sani bashida 'karfi kuma aikinnan yakai miliyan biyar, zaka bada miliyan biyu 'yan uwanka su bada sauran tunda kai kanada kud'in a 'kasa". Kallona juna mukayi ni da Saleh, shiru yayi ya kasa cewa komai, raina yayi matu'kar 'baci a wannan lokacin, mijin jumana yafi Saleh da mijin sultana 'karfi, a cikinsu ma Saleh ne mai 'karamin 'karfi meyasa zasu mana haka? Na tabbata mijin jumana da Usman zasu iya had'a kud'innan, idan so suke ya taimaka meyasa zasu masa iko da abinda zaiyi? "To uwar Saleh, kin amince ya bayar da kud'in ko kuwa kinfi so d'an ya mutu tunda ke baki haifa kinji yanda ciwon d'an yake ba?" Maimuna ta fad'a Tana kallona cike da tsana, sai yanzu na lura da yaron dake Kan kujera da cannula a hannunsa da wani Abu a hancinsa, ya rame kana ganin 'kashin kansa da 'kirjinsa. Bansan dalilinta na yin magana ba saida mama tace "kun zauna kamar kurame, yaushe zaka kawo kud'in domin ance aikin imagency za'ayi masa a indiyan. Runtse Ido na nayi, nasan d'ayan biyu ne, idan har bamu bada kud'innan ba yaronnan ya mutu to tabbas bazan yafewa kaina ba, idan har na hana bada kud'innan to naso kaina da yawa, ko kuma mu bada miliyan d'aya in yaso ko su mama sa cika mana. "Shi...shikenan zamu kawo zuwa gobe" na fad'a muryata na rawa, tashi nayi na fice ba tareda na jira me zasu ce ba, hawaye ke bin fuskata a raina ina tunanin Anya alkhairi ne wannan abin? A duk lokacin da ya taso sai wani abun yazo ya toshe mana hanya, "Allah ka za'ba min abinda yafi alkhairi" na fad'a cikin raina. Saida na shiga gida sannan Saleh ya shigo, zama yayi gefena ya d'aura kaina a kafad'arsa Yana shafa gashina, cikin rarrashi yace "duk Wanda ya dogara ga Allah to tabbas Allah zai kawo masa mafita, ta yiwu wannan tafiyar tamu a yanzu ba alkhairi bace shiyasa hakan ya faru karki sawa kanki damuwa kinji?" Cikin shesshe'kar kuka nace "to boo-boo na, amma meyasa zasu yi mana haka? Sun k'wace mana dukiyarmu cikin iko da isa da gadara, da ace ro'ka tayi ma da sai yafi amma dole fa aka mana, idan mun hana wani abun ya samu yaron kuma shikenan zaace laifinmu ne". Baice komai ba yaci gaba da shafa bayana har na samu nutsuwa, shiru mukayi dukkanmu har lokacin sallar magrib yayi, yana fita masallaci na Kira mama na sanar mata abinda ya faru, "Babu komai Bilkisu ai taimako kukayi a hakan, idan Allah ya bashi lafiya mafi yawan kason ladan naku ne, wannan ba abun damuwa bane kawai abinda za'ayi zan baku kud'in ku cika a matsayin rance tunda yace baya son kyauta, idan anyi aikin an gama lafiya sai ku biya". "To mama Zan fad'a masa mungode Allah ya saka da alkhairi". "Bakomai bilkisu kiyi ta ha'kuri dai, insha Allahu komai mai wucewa ne, babu abinda yake dawwama a duniyarnan kinji? Wataran da kansu zasuyi nadamar abinda sukeyi su nemi yafiyarki". Shiru nayi Ina jin kalaman mama masu kwantar da hankali, muna cikin wayar Saleh ya Kira na katse Kiran mama na d'auki nashi "nayi mantuwa akwai fura da nono a booth d'in mota ki d'auko kar yayi tsami sai ki dama mana, ai akwai kwakwa ko" "Eh akwai kafin ka dawo na dama insha Allah" Fita nayi na bud'e motar na d'auko nonon, dariya naji daga bangaren jumana har nayi gaba na tsaya domin naji akan me suke magana, wajen duhu hakan yasa basa hangoni sannan da alamu hankalinsu baya kaina. "Dan Allah da gaske ko wasa?" Jumana ta tambaya "Wallahi jumana da gaske, asbitin ne sun ganemu sun kuma san amir yana Shan wuya kuma bamuda Hali, ban ma san da zancen aiki kyautan ba sai last week da kwankwaso yazo asbitin 'bangaren masu matsalar zuciya yara, anan ya zabi yara goma harda Amir ya biya musu kud'in aikin kyauta a indiya". Saura kad'an na jefar da ledar hannuna, wannan wasu irin marasa imani ne? "Lallai ma Yaya maimuna, to Hajiya ta sani?" "Ta sani mana, kursum ma ta sani, ke kowa ma ya sani ranar 23 ga wata zamu tafi, har kud'in guzuri ya bamu fa kyauta". "Lallai Yaya maimuna ke bala'i ce, to me zakuyi da miliyan biyun?". "Ni bala'i ce ko hajiya bala'i ce? Ai hajiya ce ta 'bullo da wannan maganar kar'bar kud'in, shi gashi mai Mata zasu je kasar waje su siyo 'da miliyan biyar, sai muga ta yanda zata je ai, kud'in kuma hajiya tace raba mana zatayi mu uku muja jari". "Wai duk Ina ina akayi wannan abubuwan?". "Ha jummai kenan, kina kirana na kira hajiya ta tsara min wannan abun, karki damu kema za'a baki wani abun a ciki ai tunda ke kika mana hanyar kud'in". Cikin sauri na nufi gidana cike da al'ajabin wannan magana ta maimuna, wasu irin azzaluman dangin miji na had'u dasu haka? Abu mafi wuya shine yanda zan sanarwa da Saleh wannan magana da yanda zai d'auketa, zai amince dani ko kuwa zai 'karyata ni? Ta yaya zamu bullowa wannan al'amari? 27 Bayan mun gama dinner na zauna ina tunanin yanda Zan kawowa saleh maganar da naji, nasan ya yarda dani zai amince da abinda na fad'a ko? "Bilkisu" "Na'am?" Na amsa cikin sauri, nasan baya kiran sunana sai ya kirani sau da dama ban amsa ba. "Inata tambayarki kinyi shiru". "Banji bane me kace?" "Boo-boo nasan abinda su hajiya sukayi bakiji dad'insa ba, amma bamuda wani za'bin, ALLAH zai kawo mana mafita kinji?" Gefensa na koma na zauna nace "boo-boo ba wannan ne ya sanyani tunani ba, dukda bazan boye maka ba banji dad'i ba ko kad'an, amma babu yanda zamuyi, abinda yake damuna shine maganar da naji su maimu nayi lokacin da na fita d'auko fura daga mota". "Boo...ki dena bari maganganunsu suna damunki mana please, banaso Naga damuwa a fuskarki nafiso a koyaushe na ganki cikin walwala". "Boo-boo ba ni suka fad'awa ba....kawai jiyosu nayi suna hirarsu, akan wannan aikin da za'ayi wa amir". Shiru yayi yana kallona saidai na kasa furta komai na fara wasa da yatsuna I was so nervous, ta Yaya zai d'auki maganata? Ganin hankalinsa ya dawo gareni yasa naja numfashi na fara bashi labari ba tareda na tsaya ba "maimu naji tana fad'awa jumana aikinnan kwankwaso ne ya biya musu kud'in da zaa kar'ba wai business zasu fara dashi". Gumi naji ya had'u a hannuna kamar mara gaskiya, kallonsa nayi naga yana murmushi, dariya yayi a hankali sannan yace "a'a boo bakiji dai sosai ba, haba, ko zasuyi 'karyar ai banda hajiya kuma 2million fa ba wasa ba, maybe dai bakiji maganar Daidai bane". "Baka yarda ba kenan". Na fad'a Ina jin raina ya fara 'baci, dafa kafad'ata yayi yace "no boo ba wai ban yarda bane, amma Ina tunanin wani zancen suke fad'a kikaji amma ko zasu kar'bi kud'i a hannuna 2million tayi yawa fa" A fusace na matsa nace "to boo-boo 'karya nayi maka tunda na saba". Matsowa yayi na ture hannunsa cikin lallashi yace "bilkisu ki fahimceni mana, ba cewa nayi 'karya kike ba amma shikenan zanyi magana da hajiya gobe". Girgiza kai nayi nace "a'a, kar...." Ban 'karasa ba nace "okay shikenan" na bar wajen, domin babu abinda zan fad'a ya amince indai bai amince da wannan maganar ba, gado na fara gyarawa ina tucking bedsheet d'in ya shigo, hugging d'ina yayi ta baya ya zuro kansa ta gefen wuyana yace "boo-boo fushi kikayi fa ko?". Shiru nayi ban tanka masa ba, hannunsa naji cikin rigata Yana shafa cikina nayi kamar bansan yanayi ba, cigaba yayi zuwa bayana yana 'kara sama-sama a hankali, tashi tsaye nayi na zare hannunsa nace "boo-boo am not ready for this okay?". "Boo kinyi min kyau ne sosai, yaushe rabon kiyi shigar Riga da wando haka sannan yau d'in da kikayi kina jamin class". Bud'e baki nayi domin na tanka sai kumabna rufe domin ba magana ce mai dad'i zata fito ba, drawer bedsheet d'ina na bud'e na fara ninke masu datti ina jerawa, zama yayi a bayana ya sake zura hannunsa cikin rigata yana massaging bayana, hannayensa da sanyi hakan yasa duk inda ya ta'ba a jikina sai na motsa, sam na'ki kulasho domin idan Yana tunanin wannan zai sanya na huce yayi kuskure, lokaci d'aya da ya kamata ya yarda dani amma ya'ki. Bra d'in jikina naji ya 'balle, still ban nuna nasan yanayi ba saida naji hannunsa Yana d'age bra d'in ta gaba, cikin 'karfi na zare hannunsa nace "please boo-boo ya isa ka barni nayi aikina". "Naji amma ki kulani mana, nasan kinyi fushi amma ni ban furta haka saboda kiyi fushi ba" ya fad'a Yana gyaramin bra d'in da ya 'balle, juyawa nayi na kalleshi bayan ya gama nace "na sani baka yi domin raina ya baci ba, nasan bazaka ta'ba yin abinda raina zai 'baci ba amma at least ka yarda dani mana, amma ka nuna tamkar kawai na fad'a ne domin na kawo hanyar da zata dakatar dakai ka bada kud'innan, tabbas zanbi duk wata hanya da zata sanya a fasa bada kud'innan amma boo-boo bazan maka 'karya ba na wuce haka a wurinka, na Kuma fi 'karfin haka a wajensu, ka gane ciwon da nakeji na rashin haihuwa, idan zakayi amfani da tunani duk abunnan had'i ne, da ace jumana bataji zancen kud'innan ba har zasu tambaya? Sannan ga abinda naji da kunnena amma duk baka gani ba, idan ka tambayi hajiyan ma matsala zaka janyo mana kawai a basu duk abinda zasuyi dashi suyi, wasu lokytan abubuwan dake faruwa suna sanyani nadamar shigowa cikin wannan ahalin, suna sanyani nadamar choice d'in da nayi na rayuwata, sam banyi dacen Rayuwar aure ba, domin a shekara ta uku a aurena farin cikin da nayi baifi na 'kirga da hannuna ba". Tabbas maganganuna sun daki Saleh saboda yanda yake kallona, wasu kalmomin banso na furtasu ba amma ba'a maida magana, numfashi ya sauke yace "na fahimta Bilkisu dangina basa sonki haka kema bakya 'kaunarsu, amma ki sani sunada dalilinsu na yin haka, kuma 'yan uwana ne banida kamar su, jinina ne su bazan iya rabuwa dasu ba har abada, su na fara sani a rayuwata kafin na sanki, na jima ina goyon bayanki Kuma har yanzu ina goyon bayanki amma dangina dangina ne, dole nayi ha'kuri dasu dole kuma nayi musu abunda sukeso, bilkisu a lokacin da banida komai su na sani su suka taimaka min". "But boo-boo I am your wife!! A yanzu ina bu'katar kulawarka kamar yanda suke bu'kata, ina bu'katar taimakonka fiye da yanda suke bu'kata domin a wannan duniyar taku banida kowa sai kai, boo kafin ka fara goyon bayana ni kad'ai ka barni ina ya'ki da 'kiyayyarsu". Hawayene ya gangaromin zuciyata cike da takaici, murya 'kasa-'kasa Saleh yace "bilkisu".... "No" na fad'a yayinda kuka yaci 'karfina, "ya Isa, abu na 'karshe da zanso shine fad'a dakai a rayuwata, nasan danginka sun fini kuma i understand that, nasan muhimmancin dangi tunda ni 'yar dangi ce kaima shaida ne, Banda ka shigo rayuwata auren gata za'ayi min na dangi, saboda haka na fahimceka na fahimci inda ka dosa, kayi ha'kuri idan na 'batawa danginka". Dafe kansa yayi yace "ya salam.... bilkisu me mukeyi haka?" Share hawayena nayi nace "Nima ban sani ba" Kuka sosai yaci 'karfina domin a karo na farko nayi nadamar auren Saleh dukda soyayyar dake tsakaninmu, Allah ne ya tsara wannan itace jarrabawata amma da ace Dan uwana na aura ya rayuwata zata kasance? Da tuni ina nan ko ina na juya dangina zan kalla, ace duk d'umbin gatan da nakeda shi anan na 'kare? Rayuwa kenan. Zama nayi a gefen gadon na ri'ke kaina ina 'ko'karin danne hawayena, dukkanmu babu mai 'ko'karin rarrashin wani domin duk zuciyarmu babu dad'i, kayan jikina na cire na sanya na bacci na kwanta ba tareda na kalleshi ba, nasan zuwa safiya dai ni zan 'kare da kar'bar laifin kuma nayi rarrashi. Sai bayan na kwanta da kusan minti 15 sannan naji ya kwanta, muryarsa a hankali naji ya furta "saida safe" tareda kashe side lamb d'in gadon, bacci yayi 'kaura a idona hawaye kawai nake gogewa ina tunanin rayuwata, 5years back da za'a cemin haka rayuwar aurena zata 'kare bazan ta'ba yarda ba, sam bana mafarkin auren bare balle har matsala irin wannan ta taso mana, amma kana naka Allah yana nashi. Addu'a na fara har nayi bacci, Huda ce ta tasheni da asuba nayi mata wanka ta koma bacci na fara aikace-aikace na, saidai tunanina yana kan fad'an da mukayi da Saleh, ya kamata ace na bashi ha'kuri amma ego d'ina bazai barni ba, na danne abubuwa da dama a raina, kamar yanda iyayenmu ke fad'a mana idan kin samu sa'bani da mijinki ko laifinsa ne ki danne ki bashi ha'kuri haka nima nakeyi, a shekara uku a aurenmu babu abinda nake banda ha'kuri, zaiyi laifi amma na bishi na bashi ha'kuri amma not this time. Ko da muka zauna yin breakfast babu wanda ya kula wani har muka gama cin abincin, kwashe kwanukan na nufi kitchen na fara wanke-wanke, ina wankewa naji muryarsa yace "na tafi" kafin na juyo ya fita, zubawa 'kofar ido nayi cike da damuwa, tension d'in dake tsakaninmu ya wuce yanda zan iya controlling dole na nemi shawara" Mutum d'aya ce ta fad'omin raina cikin sauri na 'karasa wanke kwanukan na d'auki Huda ko mayafi ban sanya ba na fice part d'in sultana, tana zaune gaban stand d'inta tana gogewa ta kalleni cikin fara'a tace " 'yar halak, yanzu nake tunaninki nace Bilki ta gujeni tunda na fara rashin lafiya sau d'aya kika shigo kika dubani". Sai yanzu da ta fad'a na tuna tayi fama da typhoid kwanakin baya, sam na manta banda yanzu da ta fad'a min, "kiyi ha'kuri sultana wallahi abubuwa ne sunyi min yawa, kuma ina ganin wai an fara samun mafita sai kuma abubuwa ke ta'bar'barewa". Dawowa kujera tayi ta zauna tace "me ya faru kuma? Domin ni yanzu gaba d'aya basa sakani a harkarsu bana sanin meke faruwa, sai last week ake fad'amin Amir baida lafiya ma". Numfashi na sauke nace "ni sai jiya nasan ma baida lafiyar, amma lokacin da jumana ta shigo fad'amin ta sameni ina waya da mana Ina sanar mata mun kusa tafiya a yimin aiki". "Alhamdulillah Bilki am so happy!, Allah yasa ayi a sa'a", dariya nayi na fara bata labarin duk abubuwan da suka faru har fad'an da mukayi, girgiza kai tayi tace "Bilki nasan halin su yaya Maimu wannan kad'an daga aikinsu ne, kuma kud'innan tunda suka 'kwallafa ransu wallahi sai sun kar'ba da kin nemi shawarata ma da baki sanar masa ba, ko ya yarda dake sai sun sami hanyar da zasu bullo masa ya yarda dasu, ha'kuri kawai zakiyi yanda kika saba ki bashi ha'kuri a wuce wurin, karki ma sake kawo maganar tunda mama tace zata baku kud'in ai an rage matsalar ko?" Jingina nayi jikin kujerar nace "yanzu sultana ina gani zasu rabamu da kud'innan bayan mun fisu bu'katarsa? Sannan ai shi ya kamata ya bani ha'kuri ko kuwa?". "A'a Bilki maganar gaskiya laifinki ne....." Dafe goshina nayi nace "matsalae hausawa kenan, duk abinda ya faru laifin mata ne, miji yana bin mata ace laifin matarsa ne, miji yana dukan matarsa ace laifinta ne, miji ya saki matarsa ace laifinta ne, miji zai 'kara aure ace laifin matarsa ne shi Namiji baya laifi ne?" Kallona sultana tayi da seriousness tace "Anya ba kina gab da fara period bane?" Kallonta nayi taja baya a tsorace wanda ta bani dariya, dawowa kujerar da nake tayi tace "gaskiya na fad'a miki maman Huda laifinki ne, da ace baki kawo maganarnan ba ai da haka bata faru ba, kawai man up and apologize komai ya wuce". "Shikenan mum abdallah". Hira muka wuni munayi har saida naji raina ya d'an sarara sannan na koma gida, girki na musamman nayi na cancad'a kwalliya na zauna ina maimaita abinda zan fad'a masa a raina. Ina Jin tsayuwar motarsa na fita na kama 'kofa na tsaya, a hankali ya matso fuskarsa ba yabo ba fallasa, ko da ya ganni tsayawa yayi da alamu baisan dame zai fara ba. "Sannu da zuwa" na fad'a tareda kar'bar jakar hannunsa, "kinyi kyau" ya fad'a tareda murmushi, sauke kaina nayi nace "nagode". Ajiye jakar nayi nace "yau favourite d'inka nayi". Bud'e flask d'in yayi ya sha'ki 'kamshin tareda lumshe ido, kissing goshina yayi yace "thank you". Zama mukayi muka fara cin abincin ba tareda magana ba, saida muka kammala muka koma palour sannan nace "boo-boo.....I am sorry, I am so sorry nasan abinda nayi jiya ban kyauta ba na bar 'bacin rai ya rinjayeni na fad'a maka maganganun da basu dace ba". Side hug yayimin yace "nasani boo kuma Banga laifinki ba, you have the right to be angry kuma na fahimci maganarki, da na zauna nayi nazari sai naga nima inada laifi ya kamata ace na saurareki na fahimceki na kuma yarda da abinda kikace kiyi ha'kuri kinji? Kuma na miki al'kawari bazan bada kud'innan ba sai nayi bincike". "Nagode da fahimtata da kayi amma ina ganin ba sai kayi bincike ba kayi abinda sukeso kawai, dan sun kar'bi wannan kud'in ba 'karshen duniya bane Allah zai bamu wasu". "I love you" ya fad'a tareda snuggling wuyana, dariya nayi nace "I love you boo boo na" ************** Ko da Saleh ya fita kai tsaye part d'in hajiya yayi, cikin sa'a kuwa ya samu maimuna tana nan, zama yayi suka gaisa yace "ya mai jikin". "Um, jiki gashinan jiya I yau babu wani cigaba, likita ma said yace idan bamu gaggauta kaishi aikinnan a kwana goman da ya fad'a ba za'a iya rasashi, Saleh ka taimaka ka kawo kud'innan kaga 'yan uwanka duk sun bada nasu". Maimuna ta fad'a cikin magiya Shiru yayi na d'an lokaci sannan yace "Hajiya ba wai na'ki bada kud'innan bane, labari naji ne cewa kwankwaso ya biyawa yara masu matsalar zuciya aiki kyauta a indiya sannan kuma ance a asbitin da maimuna take zuwa ne...." "Me kake nufi?" Hajiya ta katseshi. "Ina nufin...bilk..... a'a ina nufin naji ance an biya kuma nasan maimuna na yawan zuwa shine nace ko an biya da Amir?". A fusace mimuna ta kalleshi tace "wato matsiyaciyar matarka ta fad'a maka an biyawa amir aiki a indiya ko? Saboda itace mai ri'ke da asbitin? To ubanta ne ya biya? Idan shi ya biya sai ta kawo shaida, Ni dama nasan yarinyarnan Bata 'kaunarka bata 'kaunarmu, a wajenta gara Amir ya mutu saboda ita bata Haifa ba, to gashinan sai ka kai Mata, itace takardar kud'in da aka bamu na asbitin gashinan a rubuce a jiki, dama ai baka yarda da kowa sai ita, kai bakaji kunyar zuwa gaban Hajiya ka fad'i wannan maganar ba? Kana nufin hajiya zata yaudareka ko me?". Kallo d'aya Saleh ya yiwa hajiya jikinsa yayi sanyi, domin kallo ne na takaici take jifansa dashi, jiki a sanyaye ya d'auki takardar da sunan asbitin a jiki da kuma kud'in da zasu biya, dukda anbi kan kud'in an gyara da biro sannan ga sunan Amir a jiki, ri'ke takardar yayi yace  "kuyi ha'kuri Hajiya ba haka nake nufi ba, sannan babu laifin Bilkisu a ciki". "Zaka fad'i haka mana tunda tafi uwarka, Saleh idan har zaka bamu kud'innan kana 'bata mana rai ka barsu zamu fita nema a gidan rediyo ko mubi gidajen masu arzi'ki tunda kafiso muyi bara akan ka bamu" hajiya ta fad'a a fusace. "Kuyi ha'kuri Hajiya wallahi ba haka nake nufi ba, zan bada kud'in". "Ka kawosu zuwa 'karshen satinnan, sannan a hannu nakeso ka kawomin kud'in ba wai ka turo". Hajiya ta fad'a tareda barin wurin. Tashi Maimuna tayi tace "sannan idan kai me tunani ne yanda ran hajiya ya baci ita Bilkisu ya kamata ka bawa kud'in ta kawo sannan ta nemi afuwar Hajiya". Gaba d'aya tazhi sukayi suka barshi a wajen, tafiya yayi da takardar cike da tunani da nadamar wannan magana da yazo musu dashi. ************** Ina zauna Ina tunanin me yasa Saleh ya dad'e haka? Sam banaso yaje part d'in hajiya ya dad'e raina yana rayamin abinda ya faru baida kyau. Shigowa yayi babu sallama da takarda a hannunsa, yanayinsa kawai na gani nasan akwai matsala sannan nasan dalilin matsalar, zama nayi a gefensa nace "boo-boo...saida nace kar kayi magana, am so sorry". Kar'bar takardar hannunsa nayi yace " da gaskene kud'in aikin suke bu'kata....ran hajiya ya 'baci sosai". Shafa bayansa nake cikin lallashi nace "ya isa kayi ha'kuri, yaushe za'a basu kud'in?". "Tace zuwa 'karshen satinnan tunda aikin saura kwana goma". "Shikenan Allah ya kaimu". "Ameen, amma idan na ciro kud'in ke zan bawa ki kai musu sai ki bawa hajiya ha'kuri". Girgiza kai nayi nace "a'a, ka kai musu da hannunka zaifi gaskiya". "Bilkisu....ki yarda da abinda na fad'a miki kawai, hakan zai Sanya su sauko daga fushin da sukeyi kuma hakan zai nuna kin damu dasu". "To" na amsa tareda canza hirar, amma Sam banaso hannuna ya shafi kud'innan, su je su 'karata. Bayan ya fita na d'auki takardar, abin ya bani mamaki ganin flyer ce, suka rubuta sunan Amir a saman sannan suka bi Kan original kud'in suka saka biro suka 'kara, ko da na 'kura ido sai naga kud'in $3,200, da nayi converting baifi 1.5 ba, wannan wasu irin macuta ne?. Sunan asbitin na rubuta a internet naga a wannan lokacin sun bada discount ne na 40% akan aikin zuciya, maybe dalilin da yasa aka biyawa su amir kenan, nad'e takardar nayi na jefar. Ranar Friday sai gashi ya dawo da kud'in a leda, bud'ewa yayi ya nunamin na zubawa kud'ad'den ido, rashin dad'in da naji bai misaltuwa amma na danne. Mi'komin ledar yayi yace "gobe da safe sai ki Kai ko? Dan Allah duk abinda za'a ce kedai ki Basu ha'kuri banaso kuyi rigima kinji?" 'gani sarkin rigima ba' na fad'a a raina sannan na gyad'a masa Kai tareda 'ka'kalo murmushi, washegari sai wajen 12 na Rana sannan na d'auko kud'in, zuba musu ido nayi na rasa yanda zanyi, haka na zubasu a leda na fita na kai ba don raina Yana so ba. Ko da nakai musu kallo ma ban ishesu ba na basu ha'kuri na koma part d'ina, inajin dariyar kursum tana "yarinya idan kinsan wata bakisan wata ba". Bayan na koma gida na sanarwa mama a waya ta bani Baki sannan tace duk lokacin da muka shirya zata bamu cikon ayimin aikin. Saleh yana shigowa yace "kin kai musu ko?", Juya idona nayi nace "daga shigowa sai tambayar na kai? Ko kana tunanin zan boye ne? Na kai mana basu fad'a maka ba?" Tallafo fuskata yayi tareda kissing d'ina yace "I am proud of you" ya fad'a tareda shafa fuskata, kissing d'insa nayi nace "proud of you too, b wannan ba inada good news amma sai kaci abinci". Muna cin abinci yana tambayata mene good news d'in, kallonsa nayi nace "mama tace zata cika mana kud'in bayan anyi aikin sai ka biyata a hankali". "Da gaske?" "Da gaske mana, tace koyaushe mukeso kawai mu mata magana ko yanzu ne". "Yaushe zamuje?". "Eh to koyaushe, amma ai gani nake ba ma sai munje ba, magana ta waya ma ta isa". Ajiye spoon d'insa yayi yace "haba, ai dole muje wannan fa babbar magana ce sai munje munyi godiya" "Sai muje Sunday Zan fad'a mata". Washegari Saturday su hajiya basu Kira Saleh sunyi godiya ko suce sunga sa'ko ba, ko da ya fad'amin tsaki naja nace "dama sun samu abinda sukeso me zasu kiraka suyi? Kud'in kawai suke bu'kata kuma sun samu" "Bilki....." "Alright alright...fine" na fad'a tareda murmushi, washegari mun fita zamu je gidan mama said ga hajiya da maimuna da kursum sun taho, tunda na gansu nasan ba alkhairi ne ya kawosu ba, tsayawa sukayi gabanmu Hajiya ta bud'e ledar hannunta ta zaro kud'i, nunawa Saleh tayi tace "yanzu kai bakaji kunya ba? Idan bazaka bada kud'in bane sai ka fad'a mana amma zaka tuwo matarka ta kawo mana 500,000? Ba ma rabin abinda muka tambaya ba, ungo ri'ke tsiyarka Allah zai kawo masu bamu" Cillo kud'in tayi ya fad'i 'kasa, mutuwar tsaye nayi Ina kallonsu, maimuna sai zubar da Hawaye take kursum ta had'e rai, d'aukan kud'in Saleh yayi ya juyasu tare da kallona....... _clap for me tinda na fara post ban ta'ba Mai yawan wannan ba😅😅😅😅😅😅- 28 Kasa furta komai nayi yace "hajiya tun ranar juma'a na bata kud'in ta kawo". "Eh ta kawo ai ga abinda ta kawo nan a hannunka". Kallona yayi yace "Bilkisu". Muryata tuni ta fara rawa tamkar mara gaskiya nace "boo-boo wallahi na kai". Na fad'a ta yanda shi kad'ai zaiji, sunkuyowa yayi shima yace "boo idan kinkai yana ina?" "Nima ban sani ba...." Na fad'a gabana yana fad'uwa, me mutanennan suke shiryamin? Me suke Shirin aikatawa haka?. "Malama karki raina mana hankali, kina nufin hajiya 'karya zata yi masa ne? Menene zamu ribata idan munyi miki 'karya wacece ke? Me kike dashi da har zamu 'bata lokacinmu muyi miki 'karya ko sharri?" Dakewa nayi nace "nasani banida wani abu da kuke son rabani dashi bayan farin cikina, akan me zan 'boye kud'innan bayan nasan zaku fad'a idan ban bayar ba? Wannan kud'in ba komai bane a wurina cikin mintina biyar dangina zasu iya had'a min ninkin baninkin wannan kud'in tsiyarku ba komai bace a wurina". "Bilkisu ya Isa" Saleh ya fad'a tareda d'aura hannunsa a kafad'ata, kallonsa nayi cike da tsoro da firgici da takaici nace "boo kana ganin abinda take fad'a, idan na boye kud'innan me zanyi dasu? Sun fini bu'katarsu akan me zan hanasu? Ko hanasu zanyi ai bazan basu ko 'kwandala ba wannan kawai sharri sukeso su 'kullamin saboda son zuciyarsu, kuma Allah ya fisu Allah yana tare da....." Saukar mari ce ta dakatar dani daga cigaba da maganata, d'ago kaina nayi naga maimuna, nunani tayi da yatsa tace " 'karya kike ki zauna kina zaginmu da mahaifiyarmu mu 'kyaleki 'karamar 'barauniya, ba dai kinada bakin zaginmu ba? Muje gidan naki a duba, idan har akaga kud'innan duk abinda muka miki ke kika janyowa kanki, idan ba'a gani ba kinada ikon zaginmu yanda kikeso tunda mijinki ya nuna mu danginsa bamuda wata martaba da daraja a wajensa ciki kuwa harda uwar da ta haifeshi, saboda yana tareda matar da Bata san ciwon iyaye ba saboda Bata tashi taga nata ba, kuma Bata haifa taji zafin 'ya'ya ba". Kallon Saleh nayi da ya dam'ke kud'in a hannunsa da alamu ransa ya gama 'baci, sauke numfashi yayi yace "maimuna bakida ikon ta'ba jikin matata akan abinda bamuda tabbas akai, na san cewa bilkisu bazata ta'ba 'kin kawo kud'innan ba, saidai ko mistake tayi ta bar wasu a gida". "Boo-boo wallahi tallahi duka kud'innan na kawo Babu abinda na ajiye, suna dai niyyar 'kullamin wani abun ne". "Saleh, nice na haifeka ko kuma bilkisu?" Kallonta yayi yace "hajiya...." "Dakata banaso naji abinda zaka fad'a, nasan cewa zakayi bilkisu batada laifi saboda an tsaface ka an lalata maka zuciya baka ganin  kowa da gashi sai ita, ni uwarka da na tsuguna na haifeka zaka kalla kace ina 'karya matarka ce mai gaskiya ko?" Shiru yayi ya sunkuyar da kansa, 'karfin Hali nayi nace "Hajiya kiyi...." 'dagamin hannu tayi tace "banason Jin komai daga bakinki". "Wannan dramar taki da wasan kwaikwayonki ya isheni, har mu za'a yiwa kissa da yaudara? Saleh  zamuje gidanka mu bincika idan har anga kud'innan kai kasan abinda zaka yiwa matarka, idan baa ganiba mun yarda daga mu har mahaifiyarmu ma'karyata ne". Kafin Saleh yace komai nace "na amince muje, idan kunga kud'innan kuyimin duk abinda kuka ga dama". Na fad'a tareda yin gaba dukkansu suka biyo bayana, bud'e gida nayi muka shiga na tsaya ina kallonsu, wani murmushi naga kursum nayi sannan tace "saimu fara da d'akin ta domin bazai wuce anan ta 'boye ba". Zama hajiya tayi kan kujera su biyun suka bini a baya, Banbi ta kansu ba na hau bene tareda bud'e 'kofar kasancewar bana rufe gidan da key idan zan fita, Jan doors d'in kawai nakeyi wataran ma da naja main door ta gidan na saka jamlock shikenan. Bincikemin sirrina suka fara na tsaya ina kallonsu har suka je gado, zazzage pillow sukayi suka Sanya n d'aga katifa, ganin yanda gadon yake yasa sukace sai na d'aga babu musu na d'aga musu, kallon bankin da nake ajiya kursum tayi tace "meye wannan". "Ajiyar mijina ce kuma yasan da ita". D'aukan bankin kursum tayi tace "sai ki bud'e mu gani". Na gaji da magana hakan yasa na bud'e, kallon kud'in tayi tace "anan kika saka kenan ina ragowar?". "Wannan ajiya nake bata kursum bana son magana". Mayarwa tayi tace "Allah ya baka ha'kuri". Har dai aka gama binciken d'akunan sama Basu samu komai ba, 'kasa muka koma tun daga kitchen suka fara sun hargitse min komai, ganin Ina maida musu magana idan suka yadamin yasa mahaifiyarsu biyo bayanmu, bayan bincike marar amfani harda sa ido sukayi, Banda sa ido me ya kaisu bud'e freezer?. An gama muka koma guest room, daga toilet aka fara aka dawo d'akin, an gama duba ko Ina ba'a ga kud'in ba, bedside d'in d'akin kursum ta bud'e  karo na biyu cikin sauri tace "Hajiya kuzo ku gani". Ciro drawer tayi sai ga kud'in a ajiye a can 'kasan drawer, ja nayi da baya cikin tsananin tsoro yayin da duk idanuwasu ke kaina, me ya kawo kud'in cikin gidana? Ciro kud'in tayi yanda suke 500k a hade guda uku, zubesu tayi a 'kasa tace "to malama mai gaskiya yanzu me zakice?" Kallon Saleh nayi da yake kallona da wani yanayi da na bazan iya fasalta shi ba, girgiza kai nayi nace "wallahi na kawo muku kud'innan bansan ya akai suka dawo ba". "Wallahi kinji kunya bilkisu Allah wadaranki, kinso had'amu da d'an uwanmu Allah bai baki iko ba, saboda Kinga ya yarda dake ko? Yana fifitaki akan mu shine zaki 'bullo ta wannan hanyar ko?" Maimuna ta fad'a tamkar zata dakeni. Murya 'kasa-'kasa Saleh yace "bilkisu kikace kin kai kud'innan". "Boo-boo wallahi na kai ka yarda dani". "Idan kinkai me sukeyi anan Bilkisu? " Danne kukan dake neman kubcemin nayi nace "nima ban sani ba". Cikin 'bacin rai yace "kina nufin yanzu ma zakice su suka kawo kud'in cikin gidanki suka ajiye? Dama shine dalilinki na cewa Mama zata bamu kud'i har kina cewa ba sai na kirata ba? Meyasa zakiyi haka Bilkisu". "Ka yarda dani na rantse maka da girman Allah banida niyyar ajiye kud'innan a wajena". "Kina da niyyar bani kenan? Bilki nace miki ina bu'katar kud'innan ne? Tun farko kin hanani bada kud'innan ban ta'ba tunanin zaki bullo ta wannan hanyar ba". Na kasa cewa komai saboda su maimuna dake d'akin, nasan cewa idan nayi masa magana ni dashi zai fahimceni, goge 'kwallar nayi nace "boo ka nutsu muyi magana". "Babu wani boo ko me, kiyi mana bayani me kikayi haka?" Kursum ta fad'a tareda zama gefen gadon, dukkansu zama sukayi Banda ni da Saleh, wannan itace ranar da gaskiyarka bazata yi maka amfani ba, yanzu duk abinda sukayi min Ni na jawa kaina. Muryata na rawa nace "bansan ya akayi kud'innan ya dawo d'akina ba" "Me kike nufi? Karki maidamu mahaukata mana, akwai Wanda yake gidan ne bayan ke da mijinki? Wa kuma kikeso a cikinku ki la'kabawa mugun halinki na sata da zamba? Ko a tunaninki yanzun ma mijinki zai kareki bayan ya ganewa idanunsa? Bilki kin ci mana mutunci kin zagemu akan laifinki, dan Allah bakiji kunya ba?" Rintse idona nayi na rasa me zance musu, kursum ta fara kaini bango, tunanin basu ha'kuri nake saidai nasan hakan bazai canza komai ba. "Kinyi shiru ko duk borin kunyar ne? Bayan an kamaki dumu dumu tukun bakinki zai mutu? Gamunan zaune a gabanki yanzu ma kinada ikon fad'a mana bakar magana, bilkisu ki zagemu mana, Ko har yanzu kinada bakin 'karyatamu ki 'karyata uwar mijinki ki kuma kare kanki? Ashe duk rashin kunyar naki na banza ne ganin mijinki yana goya miki baya? Banda mijin naki bashida hankali me zaiyi dake? Tuntuni muke nuna masa ke ba matar aure bace ba macen kirki bace, gashinan wadda ya Yar saboda ke tana can tana hayayyafa ke gakinan bakida wani amfani banda Sanya masa damuwa da ba'kin ciki". "Ya Isa...na fad'a muku ni ba b'arauniya bace babu abinda na aikata ku 'kyaleni mana dan Allah, meyasa burinku ku 'batamin rayuwar aurena ne? Idan har zan d'auki kud'in Zan ajiyeshi a cikin gidana ne?" "Ya isa Bilkisu....ya isa haka na gaji da jin maganganunki, ki amince da laifinki ki fad'amin dalilinki na yin hakan, waye zai kawo kud'i ya ajiye a cikin gidanki? Waye yake shigowa bayan ni dake ko kinaso kice dani aka had'a baki ne aka kawo kud'in cikin gidannan? Ko kinaso kice min su maimuna ne suka baro gidan aurensu suka hauro gidanki suka saka kud'in? Bilkisu ya isa haka please, meyasa koyaushe 'yan uwana sune da laifi ko da kuwa kece mai laifin?" Ba 'karamin mamaki nayi ba jin wannan maganar daga bakin Saleh, meyasa zai za'bi wannan lokacin domin ya kunyatani? 'ko'karin kare kaina na fara nace "saboda 'yan uwanka sune masu laifi a koyaushe, tun farkon zuwana sun nuna basa sona kuma duk abinda sukeyi Yana nuna hakan, meyasa zan maka 'karya? Meyasa zan 'boye kud'in bayan inada masu bani? Tun kafin kace zaka biya kud'in aikinnan 'yan uwana sukace zasu bayar, ko sanin halin 'yan uwanka bazan fara gigin ajiye kud'innan ba meyasa bazaka yarda dani ba?" Matsowa yayi dab dani yace "saboda kinyi abinda bazan iya yarda dake ba, bilkisu tunda na aureki goyon bayanki nake akan dangina ban ta'ba 'kin amincewa dake ba ko da sau d'aya, amma a yau na fahimci mene halinki, koyaushe kuka sami matsala da Yan uwana sai kin nuna ke bakida laifi, zakibi duk wata hanya da zaki bi domin baiwa kanki gaskiya, ke koyaushe bakya laifi? Meyasa kikeson kanki da yawa haka? Meyasa son zuciyarki kawai kike bi? Me aikin yaronnan zai rageki? Ke kawai kanki kika sani? A tuninki ke kad'ai kike jin zafin rashin haihuwar? Bilkisu nima inaji, a duk lokacin da na kalli 'ya'yan 'yan uwana sai naji wani yanayi a jikina, ina biye miki ne kawai saboda tausaya miki tunda kin fini nuna damuwar akai, bansan cewa kin kai haka akan son haihuwa ba amma ki sani hakan bazai ta'ba baki haihuwa ba". "Ya Isa...ka bari dan Allah Saleh, ka Bari". Na fad'a yayinda kuka yaci 'karfina, farin ciki kuwa a fuskokinsu kamar an musu musu kyautar hajji da umra, tsayuwar ta gagareni na dur'kushe a wajen, kuka nakeyi sosai ban ta'ba tunanin Saleh zaimin haka a gaban danginsa ba, mafarkin da nayi ne ya fara dawomin cike da tsoro na d'ago na kallesu, me yake shirin faruwa ne? Ya Allah karka bari abunda ya faru a mafarki ya faru a gaske. Maganar hajiya naji tana cewa "Alhamdulillah da Allah ya nuna maka hakan ka fara fahimtar cewa mara tarbiyya ka aura wadda bata ganin mutuncinka bata ganin na iyayenka, ita tayi karatu 'yar boko tana ganin zata take kowa, ta rufe idonta bata ganin darajar kowa, ka duba abinda tayi yanzu Kai kanka bakaji kunya ba? Ace matarka tana neman kashe d'an yayarka saboda son zuciyarta? Sannan Kai a haka zakaci gaba da zama da macen da take cin amanarka take yaudararka? Allah kad'ai yasan abubuwan da ta maka bayan wannan". Shiru nayi inajin maganganunsu masu Muni suna dukan kunnena, banida bangon da zan ra'ba naji dad'i, saida suka gama zagina tas sannan na ajiye pride d'ina a gefe nace "dan Allah kuyi ha'kuri". "Kin kar'bi laifinki kenan". Maimuna ta fad'a tana kallona, idanunta cike da mugunta, share hawayena nayi nace "nayi laifin fad'a muku maganganu amma bayan wannan Banga wani laifi da nayi ba, kud'in da aka samu a d'akina Allah kad'ai zai fiddani amma ni ba b'arauniya bace ba macuciya bace ba kuma mayaidariya bace". Dariya tayi tace "Mai hali baya fasa halinsa, zamu tafi mu barku kayi maganin matarka, gobe kazo ka samemu nasan Hajiya tana bu'katar ganinka, ku kwana lafiya". Ficewa sukayi suka barni, zage d'akin Saleh yakeyi har ya gaji ya zauna bakin gado, had'e kansa yayi a hannunsa yana sauke numfashi, ina dur'kushe tamkar baiwa a inda suka fita suka barni har nayi kukan na gaji, ambatar sunana yayi a yanayin da ya sanyani na tsorata yace "Bilkisu". "Na'am". Shiru mukayi na d'an lokaci sannan yace "ki fad'amin dalilinki na yin haka please, inaso na fahimceki". Kallonsa nayi cike da 'bacin rai nace "sai yanzu zaka so fahimtata bayan cin fuskar da kayimin a gaban 'yan uwanka? Sai yanzu zaka so fahimtata bayan lokacin da nakeso ka fahimceni 'bacin rai ya rufe maka ido? Me kakeso ka fahimta yanzu? Dalilina na satar kud'inka? Ko dalilina na 'boyesu?" Had'e hannayensa yayi yace "bilkisu don't make this harder please, abu d'aya na tambayeki ki fahimtar dani and you are turning the table? Ko bakida abun fad'a ne kike neman hanyar kare kanki yanda Kika saba ko yaushe?" Tashi tsaye nayi nace "ya Isa, ka dena jifana da kalamanka masu zafi Saleh, me kakeso na fad'a maka bayan abinda danginka suka nuna maka kuma ka amince?". Tashi tsaye yayi cikin d'aga murya yace " Bilkisu meyasa a koyaushe bakida magana sai dangina? Ga abu zahiri amma bakinki ya gaza dena furta dangina? For once ki amince kinyi laifi mana, meyasa a yanzu kalmar take miki wuyar furtawa? Saboda aikatawa yafi furtawa wuya ko? Just say it, dalilinki na aikata hakan shi kawai nakeso naji". Bansan lokacin da na d'aga murya ta ba nace "bazan furta hakan ba saboda Babu abinda na aikata!! Saleh gaskiya tana gabanka amma ka rufe idonka ka kasa ganinta, ban aikata komai ba why can't you believe me!!!". Matsowa yayi inda nake ya tsaya idanunsa sunyi jajir yace " 'kwarai kuwa ga gaskiya nan na ganta wadda kike kokarin rufewa da hannayenki da halayenki, I can't believe you because I don't trust you anymore Bilkisu, kin bani mamaki I am really disappointed in you...." Ficewa yayi ya barni cikin rudani, Ina ganin farin cikina Yana wargajewa a gaban idona, kalmomin Saleh na 'karshe sunfi duk bakaken maganganun da aka fad'amin a wannan rana Muni, na rasa yardar mijina wanda zaiyi wuya na dawo da ita  a wannan situation d'in. _naso yafi haka yawa Amma abubuwa sun d'aukemin hankali tun la'asar nake typing😅😅😅enjoyyyyy....._ 29 Bansan dad'ewar da nayi a d'akin ba, kabbarar sallah naji na tashi domin bansan anyi Kiran sallah ba, na shiga zurfin tunanin yanda kud'in ya dawo gidana, duk da Saleh ya wula'kantani amma ba duka ne laifinsa ba, idan har Zan Sanya kaina a matsayinsa bazan yarda da kaina ba. Ranar da na kai musu kud'in ban bar gida ba haka ma washegari babu inda naje, a cikin kwanakinnan ban fita ba sai yau ko dai bayan sun tsaida ni suka Sami damar shigar da kud'in cikin gidana? To ta yaya? Key yana hannuna shima Saleh key d'insa na hannunsa, ko dai sunyi amfani da key d'in jumana ne tunda duk lock d'in namu iri d'aya ne? To waye zai shigo ya ajiye kud'in bayan ina tare dasu a tsaye? Ko dai Jumana suka baiwa wannan aikin? Amma sam babu alamun an shiga gidan lokacin da na shiga, su dai bazasu yi aiki da aljanu akan wannan 'karamin abun ba. Kaina ne ya fara saramin saboda yawan tunani, saidai na kasa kautar da tunanin a raina, babban abinda ke d'aga min hankali shine yanda zuciyata ke neman Kare Saleh bayan duk abubuwan da ya fad'amin, want irin so nakewa Saleh da nake neman cutar da kaina a kansa? Tunda nake ban ta'ba ganin 'bacin ransa kamar yanzu ba, sannan tunda nake a duniya ban ta'ba jin d'acin maganganu kamar wad'anda suka fita daga bakinsa ba, danginsa sun zageni sosai da maganganu masu zafi, amma Basu ta'ba min rad'ad'in da maganganun Saleh suka yimin ba, amma idan har na duba a mahangar tunani yanada ikon yin haka, iyayena ne kad'ai zasu yarda dani a irin wannan lokaci ko 'yan uwana b kowa zai yarda dani ba, saboda haka na 'kuduri sake magana da Saleh a karo na 'karshe nasan mijina yana sona duk abinda yayi cikin 'bacin rai ne. Bayan Nayi sallar azahar na d'auko wayata, missed call d'in mama na gani domin tun 11 na kirata nace mun fito, a yanzu bazan iya kiranta na fad'a mata wannan matsalar ba har sai naga tafi 'karfina Wanda bana fatan hakan ya faru. Tashi nayi saboda 'karfin hali na d'aura girki, empty nake jina ko kukan da zanyi naji sanyi a raina babu hali, girkin da nake absent mindedly nakeyi ko 'kamshin banaji a hancina. Canza kayan jikina nayi zuwa marasa nauyi na zauna jiran saleh, sa'ka nake a raina ina warwarewa har naje conclusion, d'ayan biyu ne ko dai ya fahimceni y yarda dani ko kuma ya d'auki matakin da ya dace a kaina, bazan sake bari ya zageni akan gaskiyata ba, wai nice Mai son zuciya bayan ga tsantsar son kai da son zuciya a wajen danginsa. 'karan motarsa naji alamun ya fita, tuntuni yana tareda munafukan 'yan uwansa kenan, a kujerar na kwanta har la'asar, alamun dawowarsa naji amma bai shigo gida ba, ajiye motarsa yayi ya tafi har Isha, damuwa da 'bacin rai sun had'emin sai sauke numfashi nakeyi ina runtse idona. Sai 8:40 ya shigo, Yana sallama ya nufi bene ba tareda ya kalleni ba, binsa nayi a baya yana zama ina shiga d'akin. "Boo-boo ya kamata muyi magana". "Kallona yayi idanunsa har yanzu na nuna 'bacin rai, murmushin takaici yayi yace "wace magana zamuyi kuma? Ai mun gama magana". Kujerar mirror naja na zauna nace "zamuyi magana ne irin ta masu hankali ba maganar da zamu dawo daga baya muna nadama ba" "Sunce zakiyi haka ai" ya fad'a can 'kasan ma'koshinsa da alamu baisan naji ba, controlling kaina nakeyi kafin na fashe domin Nima na fara zuwa bango, had'e hannuna nayi nace "su waye sukace zanyi haka? Bayan wannan 'kazafin kuma me sukace na aikata? Boo-boo meyasa bazaka gane intension d'insu a kaina ba? Burinsu su rabaka dani su rabaka da farin cikinka, idan har suna sonka zasu so abinda kakeso amma dubi tunda nazo suke nunamin 'kiyayya har takai ga sunyimin wannan sharrin, meyasa ba zakayi tunani irin na masu hankali ba kaga inda wannan abun ya dosa?" "Kina nufin duk abinda nayi a cikin hauka ne? For the last time Bilkisu stop dragging my family into your mess, danginka danginka, komai dangina har a yanzu da suke fafutuka da mara lafiya laifinsu kike gani, sai yaushe zaki fara hangen laifinki ki dena ganin na dangina?!!" Ya fad'i maganar cike da bacin rai saboda haka na maida masa martanin da ya dace dashi "saboda danginka sune matsalata a rayuwa!! Na taso ba uwa ba uba amma ban ta'ba jina cikin maraici ba saida nazo na zauna dakai, kuma danginka sune damuwata sune laifina, wa kakeso nayi pointing a matsayin mai laifi? A wajensu har abada kai mai laifine indai kana tare dani, Kai kasan me sukacemin farkon zuwana gidannan? Kuji tsiya wai 'yar gidan masu man gyad'a ya d'auko, bayan tsiya da son duniya ya 'kare a kansu, gata da dukiya inada su fiye da tunaninka, kud'inka sunyi kad'an na 'boye domin nafi 'karfinsu, ninkinsu za'a iya bani meyasa kake tunanin zan wula'kanta kaina akan wannan tsiyar? Menene miliyan biyu? Me akayi aka yisu?" "Me akayi aka yisu da kika 'boyesu kika kunyatani a gaban dangina ko?!! Bilkisu duk actions d'inki suna sake fito da rashin gaskiyarki ne, sannan kina min gorin dukiya ai Allah ne yake bada ita, kuma cikin ikonsa sai ya baka dukiyar ya hanaka wani abu na jin dad'in rayuwa, dukiyarku ba komai bace tunda bata yi miki maganin matsalarki ba, sannan kika sake ambato dangina a wannan maganar zan miki abinda baki ta'ba zato ba, nasan duk zaman da kikeyi a gidannan a gaban idona ki nuna you are innocent a bayan idona kina wula'kantani". Tuni 'bacin raina yayi exploding, dama ance ba'a kai mai ha'kuri bango abin baya 'karewa da kyau " me kuma sukace? 'karshen magana suce Ina kawo maza gidanka Wanda a wannan state din da kake zaka amince da komai da sukace, ka kasa ganin greediness nasu, kayimin gorin haihuwa Wanda Allah ne yake bayarwa kuma kud'in iyayena bazai ta'ba bani 'ya'ya ba, a wannan lokaci na fara nadamar shigowa ahalinka Wadanda basu san darajar mutane ba, na godewa Allah da ya hanani haihuwar ya bani iyaye da dangin da sukasan darajata da mutuncina, wad'anda Basu da son zuciya da son kansu, domin akan na zama uwa mai son zuciya irin mahaifiyarka gara na mutu ban haihu ba". Ban ta'ba tunanin wannan maganar zata fito daga bakina ba saidai babu damar canzawa, illar magana kenan ba'a maidata ciki idan ta fito ta fito kenan, kuma illar da zatayi ya ninka zafin fitarta, saidai ban ta'ba tunanin maganar da zata fito daga bakinsa zatayi muni haka ba... "Ki tafi gidanku NA SAKEKI". Tamkar ya sakar min bomb a kaina naji, ja da baya nayi cike da tsoro da fargaba, babu abind nakeso na gani a fuskarsa sai nadamar abinda ya aikata amma sam babu wannan, saidai muryarsa 'kasa-'kasa yace "bazan zauna da matar da zata dinga cin zarafina da na iyayena ba, duk abinda nayi miki ki rasa dame Zaki sakamin sai zagin mahaifiyata". Yana fita na zube a wurin, ko a mafarki ban ta'ba tunanin Saleh zai iya sakina ba ko da kuwa na mari uwarsa, Ashe nayi kuskure. Ko d'igon hawaye bai zuba daga idona ba, gaba d'aya gidan ya fitarmin a raina banaso na kwana a cikinsa dukda 9:30 ma ta gota, akwatina na janyo na fara zuba kaya saidai yanda nakeji a raina bazan iya fasaltawa ba, a lokaci d'aya ina Jin takaici, bakin ciki, nadama, da tausayin Saleh, me yake damuna ne bayan dun abinda yayimin tausayinsa nakeji? Idan har hakan zai sanya duk mu dawo hayyacinmu musamman shi....Allah yasa hakan ne yafi alkhairi". Na gama d'aukan iya kayan da zan bu'kata sannan na kira jabir, ko Dan dangantakarsu da jabir bazai ji kunyar sakina ba? Yanzu bazaiji kunyar kallon mama da baba ba da auka zamar masa tamkar iyaye? Har d'inki iyayena ke yiwa jabir da Saleh, Banda kud'in makarantar da aka taimaka Masa dashi amma Dan Adam butulu ne. Saida na kirashi sau uku a na hud'un ya katse ya kirani, sai yanzu naji kuka na tahomin amma na danne, muryarda naji cikin zolaya yace " autar mama you miss me ko? I miss you too kiyi ha'kuri na kwana biyu ban kiraki ba wallahi abubuwa sunmin yawa shi kuma Saleh bakya barinsa yayi abinda ya dace, dama inaso nazo na ja miki kunne mijinki ya fara wasa da aikinsa". Numfashi naja nace "Yaya dan Allah alfarma nake nema, ko zaka zo ka d'aukeni?" Tuni salon muryarsa ya canza yace "nazo na d'aukeki kuma bilki? Me ya faru? Bakida lafiya ne? Meyasa mijin naki bazai kawoki ba? Ko motar ta samu matsala ne?". "Yaya idan kazo duk zan maka wannan bayanin, dan Allah kayi sauri kaji". "Bani minti ashirin ganinan" yana fad'a ya katse wayar, kayan jikina na fara cirewa Wanda yayi dai-dai da shigowar Saleh, kallo d'aya yayimin ya kauda kansa Ni kaina jinsa nayi tamkar ba muharramina ba bayan ya furta kalmarnan, yanzu su mama da maimuna sai a kama efficient ayi party 'karfen 'kafa ta tafi, Domin banajin idan su mama sukaji labarina zasu bari na dawo wannan gidan ko sun bari bana sha'awar sake dawowa wannan Rayuwar. After dress na sanya na saka 'karamin hijabi, Saleh tuni y fita bansan inda yake ba ban kuma damu da inda yake ba, a cikin wuni d'aya rayuwarmu ta turning upside-down. Parlour naja akwatina snnan n d'auki wani na sake cikawa tunda d'aukana za'ayi gara na debi duk kayan da nake bu'kata. Ina rufe 'karamin akwatin sai ga kiran yayana, d'aukan 'katuwar hand luggage d'ita nayi naja akwatunana zuwa gate, abin takaici part d'in hajiya shine dab ba gate, a 'kofar d'akin na gansu kursum harda sakin gud'a, banbi ta kansu ba na fuce inajin maganganunsu na biyoni amma banida lokacin saurara...... 30 Cikin sauri jabir ya 'karaso tareda d'aukan akwatina d'aya, 'kare min kallo yayi kafin ya Sanya akwatin a mota yace "me ya faru Bilkisu". Wani azababben ciwon kai nakeji sannan banida niyyar bashi amsa, kalar tausayi nayi domin na sanshi da takura nace "Yaya idan munje gida mayi maganar yanzu dai muyi mu bar wannan wurin". Bai sake tambayata komai ba har  muka d'au hanya, saidai lokaci lokaci idanunsa na kaina yayin da nawa idon ke titi, ciwon kaina 'karuwa yake saboda tunanin da nakeyi Wanda baida amfani. Tsayawa naga Yaya yayi ya fita ba tareda yace min komai ba, dawowa yayi da ice cream da cake ya mi'komin su ta window, godiya nayi masa na bud'e ice cream d'in na fara sha, fata nake sanyinsa ya kashemin zafin da nakeji a cikin jikina, dukda ya sanyayamin raina amma zuciyata tana nan yanda take sai ma 'ko'karin kuka da ba fara, meyasa Saleh zai yanke wannan hukuncin a irin wannan lokacin? Meyasa banyi ha'kuri har ya huce ba na takura masa akan ya yarda dani har yardar ta kawo wannan ga'ba? Akan wane dalili ma nake baiwa kaina laifi? Ba laifina bane ya sakeni zuciya ce kawai ta d'ebeshi, idan har inada zuciya ya dace na cire Saleh tun yanzu daga raina. Bansan lokacin da na shanye ice cream d'in ba, jifa nayi da robar ta window na maida kaina ina kallon waje, har yanzu ganin sakinnan nake kamar 'karamin abu ne, kamar yana zuwa yana cewa nayi ha'kuri ya wuce, gani nake tamkar zai biyoni a baya yace yayi kuskure nayi ha'kuri na koma d'akina Amma nasan duk wannan ba abune Mai faruwa ba, yanda naga fuskar Saleh a yayin da ya furtamin wannan mumkunar kalma bnaso har mutuwa ta na sake ganin wannan yanayin. Muna isa gida na d'auki 'karamin akwatin na shige na bar Yaya a waje, sallama nayi sai naji tamkar an manne min 'kafafuna a waje, tsoron haduwa nake da mama na fad'a Mata wannan abun, ban sake tabbatat da saki babban Abu bane sai yanzu. Amsa sallamata mama tayi tareda ambatar sunana, Jan jikina nayi kamar wadda 'kwai ya fashewa aciki na shige kaina a 'kasa, shiru mama tayi ta zubamin ido har na zauna, tun kafin ta tambayeni nace "ya sakeni". Wasu zafafan hawaye naji sun zubomin Wanda na danne tun farkon faruwar wannan abun, sam ban shirya amsa tambayoyin da nake tunanin zasu fito daga bakin mama ba, nasan abinda zata tambayeni shine me ya faru? Meye dalili? Akan me?......saidai ga mamakina jin mama nayi a gefena tana rarrashina. Hakan na nufin ya sanyamin nutsuwa amma sai na sake karaya, Kuka nake sosai a kafad'ar mama tana bani ha'kuri, abinda ya kamata mijina yayimin lokacin da aka min sharri amma sai ya goyi bayansu, ta yiwu rabuwata da Saleh shine alkhairi. Sallamar Yaya naji shima ya shigo ya zauna, abinka da namiji yana zama yace "wai ke meke faruwa ne?" Cikin sanyin murya mama tace "jeki ki ajiye kayanki a d'aki ki huta". Tashi nayi ba tareda na kalli Yaya ba na shige d'aki, ajiye jakata nayi da akwatin da naja na kwanta kan gadona, 'karewa d'akin kallo nakeyi fatana wannan d'akin ya sanyamin nutsuwar da nake bu'kata amma Ina...tunanin gidana nake ko nace gidan Saleh, the more nayi tunanin gidan the more yake sake fita a raina, idan na tuna da Saleh kuwa tamkar zuciyata zata fito. Cire kayana nayi na shiga wanka na dinga sakarwa kaina ruwa har saida na gaji, fitowa nayi nai shafa'i da wutri da rashin nutsuwa ya hanani yi a gidana.....afuwa gidan Saleh, sai yanzu Huda ta fad'omin a Rai, ji nayi Ina matu'kar kewarta. Duk abubuwannan da suka faru Huda sun fita da ya Usman, al'kawari yayi mata cewar zai kaita ta hau lilo saboda na daketa shine suka fita yau, bansan lokacin da ya dawo ba ban kuma ga alamar Huda ba, alamun dai ya samu labarin abinda ke faruwa ya barta wajen Sultana kar taga halin da muke ciki. Wayata na d'auko na kira sultana na tambayeta lafiyar Huda, sanarmin tayi Huda nata tambayata, ban sani ba ko tasan abinda ya faru saida naji ta sanarmin zata baiwa Saleh uta ya kawomin, cikin sauri nace "a'a Dan Allah ki baiwa usman ya kawomin ita banason ganin Saleh yanzu". Shiru tayi sannan tace "kiyi ha'kuri bilkisu komai mai wucewa ne, dukda bansan duk abubuwan da suka faru ba amma bai kamata kiyi yaji ba Zaki basu abinda sukeso ne, gobe za'a kawo miki ita amma Dan Allah kiyi ha'kuri ki dawo,bansan ya zanyi rYuwa a wannan gidan Babu ke ba kinsani kowa ya tsaneni". Shiru nYi na rasa me zance mata, ha'kura tayi ta katse wayar Nima na d'auki cajata na fita, zuwa yanzu na d'an samu nutsuwa kad'an a yanayina amma cikin raina Babu wani banbanci da lokacin da na baro gidan Saleh....Saleh, synannan ya zama tamkar magani a bakina, duk lokacin da na tuna da sunan sai naji wani d'aci har cikin bakina. Fita nayi naga mma tana yiwa jabir kashedi kar ya sake ya yiwa Saleh magana ko ya nuna masa wani Abu ya faru, "Wannan abun tsakanin Mata da miji ne idan ka shiga ka zubar da girmanka ne da darajarka, sannan Kai bakasan me ya faru ba menene amfanin d'aukan hukunci akai? Mu jira muji ta bakinta Amma inaso ka sani, ko me ya faru kar ya ta'ba ala'karka da Saleh musamman ta bangaren kasuwancinku". Zamana ne ya dakatar da mama ta kalleni tace "ya kikeji yanxu?" "Dan dama-dama" na fad'a tareda 'ka'kalo murmushi, harga Allah Babu abinda nakeso nayi a yanzu kamar Kuka, sannan inaso na sanarwa mama abinda ya faru Ina Jin tsoron me zata ce?, Kamar Yaya ya karanta tunanina yace "bilki....ki fad'amin me ya faru ne wai? Meyasa Saleh yayi gaggawar sakinki ki nacw gangancin sakinki?" Har na bud'e baki mama ta katseni tace "jabir ka bar yarinyarnan ta huta tukuna, jeki d'auko abinci kici". "Banajin yunwa mama". "Yaushe rabonki da abinci?" Shiru nayi domin yau tea ne kawai a cikina shima Babu Madara, d'okin zuwa wajen mama ya hanani cin komai sannan bala'i ya hanani lunch, a takaice dai daga tea sai ice cream nasha yau kuma banajin yunwa, numfashi naja nace "nasha ice cream a hanya banajin yunwa". Tashi mama tayi tace "ice cream ba abinci bane, daga alamunki tun safe baki ci komai ba ni Bari na zubo Miki tuwo Kuma banaso ki sake min musu". "Mama Dan Allah ki bar tuwonnan bazan iya ci ba, Yaya ya siyamin cake zansha da tea". Zama tayi ba tare da tace komai ba sai kalle kalle muke, kafin kowa ya tambayeni na fara magana nace "Mama akan wannan kud'in ya sakeni". Kallona tayi cike da mamaki naci gaba, Basu labari nayi ban cire komai ba a zagin da yayimin, Wanda yan uwansa sukamin da martanin da na maida Masa, lokacin da na Gama har sha'kewa nake saboda kuka, kallonsu nayi idona dishi dishi Amma naga alamun bacin rai a tattare dasu musamman ma Yaya da yake alamin zai iya kashe mutum, dukkanmu munyi shiru sautin kukana kawai ke tashi... 31 ''Allah ya kyauta Kuma Allah yasa haka ne mafi alkhairi". Mama ta fad'a bayan min day lokaci shiru, amsawa nayi da amin ina goge hawaye na, ledar cake d'in da na shigo da ita na d'auka na bud'e na fara ci dukda Kuka nake, dariya mama da jabir sukayi Wanda ya sanyani murmushi, har na manta da wannan bilkisun mai sauke 'bacin ranta a kan abinci, wadda bata ri'ko Bata bari abu komai girmansa ya dameta, matu'kar Zan kai abu bakina zance ya 'kare. Kallona sukeyi yanda nake sauke 'bacin raina kan junk food d'in dake gabana, a duk loma idan na kai maganganu nake a zuciyata Wanda bazan iya furtasu ba, janye ledar mama tayi tace "Kar Kuma kici wanda zakiyi amai". "Amma mutane basuda halacci, duk taimakon da na yiwa Saleh baiji kunya ba ya sako 'kanwata? To mama ko dukansa takeyi ya saketa? Ai ya duba girmanku da mutuncin dake tsakanina dashi, sai ya san ya wula'kanta 'kanwata". Girgiza kai nayi cikin sauri nace "a'a Yaya Dan Allah Kar kayi haka ba girmanka bane, ko dan abotar dake tsakaninku ka rabu dashi dan Allah Kar kayi masa magana ka nuna tamkar ba abinda ya faru,wannan tsakanina dashi ne banaso ka shiga da kansa zai san yayi kuskure". Wani irin kallo jabir yayi min yace "har kin fara tunanin komawa gidansa kenan ko?" Shiru nayi na zubawa hannuna ido, banaso ko hanyar gidan Saleh na sake bi, amma tsabar rashin zuciya irin nawa akwai tiny hope na gobe da safe Saleh zaizo ya bani ha'kuri mu koma zaman lafiya, me yake damuna ne? Wannan itace soyayya? Wani irin so nake ma saleh haka? Wace irin zuciya ce dani? "Amma bilkisu kin bani mamaki bakida zuciya ko kad'an wallahi, mutumin da ya zageki ya zagi iyayenki ya sakeki ba tareda tunawa da zaman da kukayi dashi ba, ba tareda tuna zaman da nayi dashi ba har shi kike tunanin komawa gidansa? Bilkisu da nasan abinda zai faru kenan da ban goyi bayan aurensa ba, da Abdul Zaki aura ko kinaso ko bakyaso, ko ba komai d'an uwane bazai ta'ba wulakantaki ba musamman yanda yaga gatan da kike ciki". "Yaya ni ba so nake na koma ba fa, kawai banaso ne wannan abin ya shiga tsakaninka dashi banaso hakan ya ta'ba ala'karka dashi". Tashi tsaye yayi yace "idan har bakyaso hakan ya ta'ba ala'kata dashi ki barni nayi magana dashi, idan har na kauda kaina bazan ta'ba yafe Masa ba". Fita yayi ya barni a zaune, mama kuwa tunda muka fara maganar ta tashi, jikina a sanyaye na shige d'aki na shimfid'a bedsheet na kwanta, Saleh zaizo bikona kuwa? Shin zaiyi nadamar sakina? A Daren yau zai iya bacci babu ni a gefensa? Nima zan iya bacci babu Saleh a gefena? Tambayoyin da suketa yimin yawo kenan har nayi bacci. ************ *SALEH* Wani numfashi ya sauke bayan kalmar saki ta fita daga bakinsa, bai ta'ba tunanin ko da wasa zai saki Bilkisu ba amma gashi yau lokaci yayi, yasan cewa su hajiya basa sonta amma wannan karan bazai ta'ba yiwuwa ya goyi bayanta ba bayan yaga laifinta da idanunsa sannan ta d'aura laifin kan 'yan uwansa har ta kai ga zagin hajiya, tunawa yayi da maganar da hajiya ta fad'a masa wadda kusan ita ta tunzurashi ya saki bilkisu Bayan sunyi hayaniya ya fita part d'in hajiya ya nufa, Hira ya samesu sunayi akan abinda ya faru, tsayawa yayi a inda yake tunanin bazasu hangoshi ba, baisan cewa zuwansa ne ya Ssanya suka fara maganar ba, ji yayi maimuna na cewa "Wallahi nayi mamakin bilkisu, nasan Bata sonmu bata son rayuwarmu, amma me zai kaita aikata haka? Ita kenan kowa ma ya mutu idan zata samu haihuwa , bata tunanin cetar ran amir zai iya sanya Allah ya kawo mata komai cikin sau'ki, Kuma babu kunya babu tsoron Allah tace Bata san ya kud'in suka shiga gidan ba". "Hm, ai da ace ma yasan me tace mana da ta kawo kud'in da bai tsaya tantama akai ba, kin tuna kallon tsabar idon hajiya tayi tace "idan har Kina haka ne Dan ki rabani d'anki idan ya rabu Dani ya aureki sai kije kiyita haihuwar dashi, wace macece mai tarbiyya zata fad'awa uwar mijinta haka?" Kursum ta fad'a Tana murmushin mugunta domin duk motsin Saleh sunaji. "Ai kad'an kikaji ma da kinsan zagin da takewa hajiya da bakiyi mamaki ba, idan hajiya tace a fad'a masa sai nace a'a domin a wajensa Babu mai gaskiya sai ita, wataran da kansa zaiji ta zageta a gabansa ai, anan zai nuna kansa idan shi d'an halak ne". Shiga yayi tareda sallama Wanda ya dakatar da maimuna daga cigaba da zuba sharrinta, zama yayi Hajiya tace "yanxu kai Saleh haka zaka ci gaba da zama da matarnan? A gaban idonka ta zagi Yan uwanka na jini, 'karara ta nuna Bata son yan uwanka Kuma duk Wanda baya son jininka baya sonka, meyasa bazaka saketa ka auri wata ba ita kad'ai ce mace a duniya?" Jan numfashi yayi yace "Hajiya nasan bilkisu tayi kuskure amma ai bazan saketa akan wannan abin ba banyi mata adalci ba, zan bata dama ta biyu ne sannan tazo ta nemi afuwarku". A fusace Hajiya tace "tir da hali irin naka, a duk cikin 'ya'yana kaine bare, baka d'aukeni da daraja ba ko kad'an, a nan matarka zata zo ta dinga fad'amin maganganun banza haka zan danne na kyaleta bazan fad'a maka ba saboda bazaka yarda dani ba, matarka ta fini ni da na tsuguna na haifeka na shayar dakai na d'auki d'awainiyarka, bayan rasuwar mahaifinku wace irin wahala ce bansha a kanka ba? 'yan uwanka suna taimakawa kansu amma kai baka iya komai, har gyad'a na soya saboda na cika maka burinka amma baka da abinda zaka sakamin sai bijirewa umarnina, kake ka auro matar da batada abin yi sai fariya da kud'in iyayenta tana cin zarafin danginka kana zaune kana ganin laifinmu". Jikinsa yayi sanyi yayi shiru, kukan munafurci maimuna ta fara tace a gabana nan Bilki ke cewa Hajiya kishi take da ita, take cewa Hajiya Bata Isa ta raba aurenku ba saboda hajiya Bata Isa tayi maka abinda ita Bilkisu keyi ba, wace irin kalma ce ta rashin kunya bata fad'a ba? Ta kalleni ni da kursum da nana yafi sau a k'irga tana cewa idan munada iko mu aureka sai mu haifar maka abinda bazata iya ba, idan kana ganin 'karya muke maka kaje ka nuna mata kafi goyon bayanmu, zakaji da bakinka abubuwan da zata ce". Tashi yayi zai fita hajiya tace "Saleh, idan har matarka ta sake zagina a gabaka baka d'au mataki ba....Allah ya Isa". Gyad'a kai yayi ya fita, motarsa ya d'auka ya fara yawo a titi, bashida abokin da ya wuce jabir saidai wannan ba maganar da zai kaiwa jabir bace, sannan bazai iya shiga gida yanxu ba sai ya huce kar yayi abinda zaiyi Dana sani. Yawo yayi har ya gaji, a can wata unguwa magriba tayi masa yayi sallah sannan ya nufo hanyar gida, tsayawa yayi a masallacin unguwarsu yayi sallar Isha ya zauna Yana tunanin abubuwan da suka faru, saidai nothing makes sense a abubuwan da Bilki ta fad'a, bayaso tana masa 'karya dukda yasan ba halinta bane, amma wannan ba Abu bane da zai yarda cewa laifin su Hajiya ne, kud'innan a gidanta aka sameshi Kuma a bo'ye, bayan tace Mama zata basu wani me take shiryawa? Shiri take kenan da mama ta turo Mata ragowar ta had'a ko me take tunani? Meyasa Bilkisu zata aikata hakan? Meyasa? Da wannan tunanin ya nufi gida,saidai yana shiga 'bacin ransa ya dawo, meyasa Bilkisu batada magana sai danginsa? Meyasa komai zata furta sai ta had'a da danginsa da mahaifiyarsa? Meyasa Bilkisu bazata saukaka komai ta amshi laifinta ba? Wace irin mace Bilkisu ta koma saboda tsananin bu'katar haihuwa? Shiga gida yayi ya sameta tana jiransa, "ya kamata muyi magana irin ta masu hankali" itace kalmar da ta sake ingizashi, tana nufin bashida hankali kenan? Saidai kalmomin da suka biyo sunfi wannan Muni, gaba d'aya maganganun su hajiya ke dawo masa kansa, ko da ya kalli idanunta yayi da take ambatar danginsa da mahaifiyarsa babu komai cikinsu bace tsana, tabbas bilkisu Bata son mahaifiyarsa da danginsa Kuma yayi imanin zata iya aikata komai domin hadashi da su,  _idan matarka ta sake zagina baka d'auki mataki ba Allah ya Isa_. Itace kalmar da ta dawo kansa, ga Bilkisu ta rufe idonta tana ta fad'in ba'kin mahaifiyarsa baisan lokacin da 'kwa'kwalwarsa tayi processing kalmar ba har ya furtata, saidai baiji nadama ba ki kad'an. Bayan tafiyarta wata nutsuwa yaji ta shigeshi, kallon gidan yayi yaji yayi shiru,  fita yayi ya nufi part d'in Hajiya ya tarar su maimuna sun tafi saura Hajiya ita kad'ai, a k'asa ya zauna tana ganin yanayinsa taji wata walwala ta saukar Mata amma ta danne tace "Saleh me Kuma ya faru?" "Na saketa". "Alhamdulillahi barka" ta fad'a cike da murna, kallonta yayi cikin mamaki bai ta'ba tunanin zata yi hamdala ba, ai ko ba komai ta nuna cewa bataji dad'i ba ya saki matarsa, amma Kuma da gaskiyarta. "Ni dama nasan wacece matarka tun tuni saleh, sau da dama Munso nuna maka ba macen arzi'ki bace Amma ka rufe idanunka ka kasa ganin abinda muke son nuna maka, amma tunda Allah ya 'kwato mana kai daga sharrinsu sai mu godewa Allah domin shi kad'ai yasan irin mugun abun da matarnan tayi maka, amma tunda Allah ya karya mana ita saidai muyi masa godiya, yanzu abinda za'ayi idan ka huta kwana biyu sai kaje ka gano hadiyya 'yar wajen 'kanwata bata jima da kammala karatunta ba". Sunkuyar da kansa yayi ya rasa me zaice da Hajiya, a irin wannan yanayin batada tunani sai na ya sake aure tun kafin 24hrs da sakin matarsa? Ai bama a fara lissafin 24hrs ba baifi 1hr da mintina ba amma tana Masa zancen aure. "Kayi shiru bakace komai ba? Sanin kanka ne Saleh duk cikin 'ya'yana nafi sonka nafi sha'kuwa dakai, lokacin da kana yaro har fad'a kake da yayyenka saboda na Basu umarni sun'ki bi, lokacin da kazo karatu tun daga Nan ka fara sa'bawa umarnina, naso kayi likita kaima ka zama kamar d'an uwanka amma kaqi amincewa, gashinan karatin da kayi baya maka wani amfani ka 'kare da fama da katako, duk 'yan uwanka sun zama wasu abubuwa a rayuwa amma kai fa? Bayan wannan kazo yin aure shima ka sa'bawa umarnina, Saleh ji nake kamar ka dena min kallon uwa, idan har kana Sona a matsayin mahaifiyarka ka amince da wannan bu'katar tawa ka auri hadiyya, Kai ka sani jininmu Allah yana azurtamu da haihuwa, idan ka huta kaje ka sameta ku daidaita wannan shine kad'ai abinda na nema daga gareka sau d'aya Saleh ka cikamin burina ka kar'bi za'bina". "To Hajiya zanyi abinda kikace" ya fad'a yanajin ba dad'i akan abubuwan da yayi mata, tashi yayi ya fita iskar dare na dukan jikinsa, shiga gida yayi sai yanxu ya lura da flask d'in da bilkisu ta jere a dining, bud'ewa yayi yaga abincin dake ciki babu alamar an ta'ba, shin dafawa tayi tana jira ya dawo suci tare? Da sauri ya rufe ya nufi d'aki, kallon budaddiyar wardrobe d'in bilki yayi ta Debi kusan rabin kayanta, zama yayi a gadon Yana shafa wurin kad'aici ya fara damunsa, saidai Babu damar maida hannun agogo baya, wannan shine abinda suke bu'kata, dukkansu space sukeso. Band'aki ya nufa yayi abubuwan da zaiyi ya fito, 'kaida idan ya fito zaiga idon Bilki a kansa tana masa murmushi, ya kalleta yace "me kike kallo?" Tace "kyakkyawar fuskar mijina Mana, akwai Wanda ba Wanda ya Isa ya kalla sai ni ko kanada ja?" Numfashi yaja ya kwanta Yana tunanin yanda rayuwarsa zataci gaba a haka, saidai ya kawar da tunanin Bilkisu daga ransa, yanzu tunaninsa na kan Hajiya da abinda takeso ko da kuwa ransa bazai so ba. Washegari bai fita da wuri ba, kiransa hajiya taji tace yaje yayi  breakfast, dukda yunwar da yakeji ransa baya son cin abincin haka dai ya tafi, bayan ya gama breakfast ya fito suka had'u da usman da Huda a mota, gaisawa sukayi ya tambayeshi ina zaije, Yana sanar masa inda zaikai Huda hajiya ta fito cikin sauri, "Ina zakaje Kuma? Wannan yarinyar kana koya mata yawo da yawa fa". "Hajiya ba yawo zamuje ba wajen Bilkisu zan kaita ne", a fusace Hajiya ta bud'e 'kofar motar ta ciro Huda tace "babu sauran ala'ka tsakanimu da ita dan haka batada sauran ala'ka da Huda, Babu inda zaka kaita" 32 Ina tashi daga bacci na turawa sultana message akan ta shiga gidana ta tattaromin kayan Huda, ko breakfast na kasa yi ina zaune jiran zuwan Huda, jikina yana bani wani abu zai iya faruwa domin na tabbata indai hajiya taga Huda baza a kawomin ita ba, fatana Allah yasa Kar su had'u da hajiya duk laifina ne da ban tsaya na d'aukota ba. Tunda naga 11 tayi jikina yayi sanyi, kiran sultana nayi tacemin ai tun 8:30 Usman ya fita da Huda, "Anya hajiya bata gansu ba?" Na fad'a a hankali "eh to sai ta yiwu hakan amma bari na kirashi, hajiya ba tace ta fita daga harkar Huda ba? Kai Hajiya tanada matsala wallahi". Tana gama maganar ta katse kiran, bayan mintina ta kirani tace "na kirashi yace Hajiya ta kar'beta, amma Bilkisu dama sakinki Saleh yayi?" Shiru nayi na kasa amsa mata, "kai amma Saleh yayi kuskure babba, inada tabbacin Hajiya ce ta tursasa shi banda haka Saleh bazai ta'ba sakinki haka nan ba". Girgiza kai nayi nace "sultana salen da kika sani a kullum ba shine a jiya ba, babu tilas a sakin da yayi min ra'ayinsa ne, saidai kawai nace Allah yasa hakan ne yafi alkhairi". "Ameen Bilkisu, insha Allahu ma komai zai koma dai-dai ki dawo domin nasan babu macen da ta Dace da Saleh sai ke Bilkisu". Dariyar takaici nayi nace "mu dena wannan magana Sultana, yanzu shikenan ni da Huda har abada?" Wani hawaye naji ya tahomin, dama me neman kuka..... Tsaki sultana tayi tace "meye kuma na kuka? Ba dai nace na bar miki ita ba? Huda Taki ce insha Allahu zata dawo wurinki, ko bata dawo ba zata dinga zuwa miki akai akai kar nayi miki al'kawari na kasa cikawa, bari naje wajen hajiyan nagani". Sallama mukayi muka rabu na sake bin gado na kwanta na fara tunanin abubuwan da suka faru jiya, a dai-dai wannan lokacin aurena ya fara rawa gashi 24hrs kamar ba'a yi ba, Allah abin tsoro wannan duniyar ba komai take ba. Sallamar mama naji na tashi na zauna tareda amsawa, kallona tayi da ta tabbatar babu alamun kuka a idona tace "baki fito kinyi breakfast ba, yayanki ya shigo kuyi sallama bai ganki ba ya fita". "Waya muke ne da Sultana, tace za'a kawomin Huda yau kuma wai Hajiya ta hana". Tashi mama tayi tace "to tunda ta hana ai shikenan karki d'aurawa kanki damuwa akan hakan, kiji da wannan d'in kawai ya isheki yarinya kuma ki bar musu kayarsu, hakan ya nuna ita hajiyar ta fara datse duk wata ala'ka dake tsakaninku, ki fito kiyi breakfast". Tana gama fad'in haka ta fita, tashi nayi na bita a baya nasha kunun gyad'a na koma d'aki, mama Bata takura min ba bata kuma le'ko ta dubani ba ko sai d'aya, da alamu ta lura ina bu'katar space ta kuma bani, hakan kuma yayimin dad'i. Gani nake tamkar duk matan duniya babu marar zuciya kamar ni, duk wannan abun da ya faru tsimayin muryar Saleh nake, so nake ya kirani a waya ko naji sallamarsa kai ko aike ne yayi domin nasan cewa yana sane da zamana, saidai babu alamun ko d'aya daga cikin wannan zai iya faruwa. Hawaye ne ya zubomin da na tuna lokacin da na fara son Saleh ta dalilin allurar da nayi masa, tunawa nayi da kalamansa lokacin da Abdul yake wula'kantani, yanda ya nunamin Abdul bai Dace da ni ba, yace "duk Wanda zai sakaki kuka to ki sani baikai matsayin ki zubar masa da Hawaye ba, kinfi karfin haka Bilkisu" meyasa a yanzu na kasa dena zubar da hawaye akan kukan da ka sanyani Saleh? Meyasa kayi iya 'karfinka ka rabani da Abdul amma ka kasa koyamin jurewa rashinka? Kuka na fara sosai na kifa kaina a cikin pillow, tabbas Saleh bai kai matsayin na zubar masa da Hawaye ba domin ya sakani kuka, amma ta yaya zan tsaida wad'annan emotions d'in da nakeji? A lokaci guda raina na 'kunar an wula'kantani, an tozartani, an kunyatani, ba'a d'aukeni da muhimmanci ba, amma mafi ciwon hakan babu wanda nakeson gani kamar wanda ya aikatamin hakan, zama da dangin Saleh babban hatsari ne, domin a wannan lokacin banida kowa sai shi, shi ya zamemin gatana a kullum yana sake koyamin 'kaunarsa domin dashi kad'ai na dogara, lokaci guda ya janye kafad'arsa ya barni a 'kasa nasan yaya zanyi da kaina, why is love so cruel? Tambayoyi ne a kaina babu adadi da nakeso na yiwa Saleh, meyasa? Meyasa? Meyasa?....shine abubuwan da nakeso na tambayeshi amma Sam babu Hali, yana can yana celebrating rabuwa dani tareda danginsa. Saida nayi mai isata sannan na tashi nayi sallar azahar, ina sallah mama ta shigo ta ajiyemin abincina ta fita, saboda kar na 'bata mata rai yasa na tura abincin ba don raina yana so ba, kewa ke damuna yayin da nake cin abincin domin na manta rabon da naci abinci ni kad'ai, kai da hannuna ma zan iya 'kirga kwanakin da naci abinci a wannan lokacin, tamkar wani sabon honeymoon muka fara tunda na gama karatuna ashe bazan shekara da gama karatu ba za'a koroni gidanmu. Ina gama cin abincin na kwanta, 'karan wayata naji cikin sauri na janyota, wani iri naji a raina ganin message d'in sultana tace na bata address d'ina zata kawomin Huda, tura mata nayi tareda jifa da wayar ban damu da inda zata fad'a ba. ********** *SALEH* Sunkuyar da kansa yayi yana kallo hajiya ta shige da Huda d'aki, cike da mamaki Usman ya kalleshi yace " Saleh yanzu bazaka bawa hajiya baki ta bari a kaiwa Bilkisu yarinyarnan ba? Ka fa duba yanda Huda ta damu jiya saboda bataga Bilkisu ba amma kana gani hajiya ta hana kuma ka zuba mata ido?" Jingina Saleh yayi jikin motarsa yace "Usman na gaji da yiwa Hajiya musu akan Bilkisu, tunda na auro yarinyarnan kana gani bana bin maganar Hajiya, kuma a duniya babu wadda ta dace nabi kamar mahaifiyata, na bawa Bilkisu dama iya dama amma yanzu bazan sake yiwa Hajiya musu akan komai ba". Zuba masa ido Usman yayi yace "ko da kuwa ba dai-dai tayi ba? Dukda mahaifiyarmu ce amma sanin kanka ne wasu lokutan bata abinda ya kamata". Numfashi Saleh yaja yace "ko ma me Hajiya tayi mahaifiyata ce kuma itace gaba da matata, idan bataso a tafi da Huda ya zauna, Huda ba ni na haifeta ba saboda haka banida iko da ita". Dariya Usman yayi ya fita ya bar Saleh a tsaye, shima Saleh shiga motarsa yayi ya d'auki hanya tareda taraddadin had'uwa da Jabir, amma ya shirya kar'bar duk wula'kancin da Jabir zaiyi masa akan abinda ya aikata, bakin al'kalami ya riga ya bushe ko yanaso bashida ikon maida wannan kalma da ya furta. Parking yayi ya fita ya gaisa da sauran ma'aikata sannan ya nufi Jabir da yake waya, bayan ya gama wayar ya mi'ka masa hannu suka gaisa ya bar wurin, binsa Saleh yayi da kallo ya bishi a baya amma still Jabir yayi kamar bai san da rayuwarsa a wurin ba, "Jabir...." Katseshi jabir yayi yace "mun samu aiki ne a had'eja yanzu muka gama waya da matar har ta turo rabin kud'in, wata uku kawai muke da sannan kaya ne da suke bu'katar nutsuwa, saboda haka zamu fara da wuri". "Ni ba wannan ba magana ce akan...." Sake dakatar dashi Jabir yayi yace "kaga bamuda lokacin hira munada abubuwa da yawa, akwai kayan gidan da aka gama na ja'en da kai za'a kai tunda kai ka auna gidan, zanje kasuwa na siyo wasu abubuwa ne". Yana gama fad'in haka ya bar wurin, dawowa yayi yace "wad'annan kud'in na wurinka muna bu'katarsu, karka manta ka taho dasu Monday saboda ranar zan tura da kud'in a kawo mana irin yadin da zamuyi mata kujerun dasu". Binshi Saleh yayi da ido, tabbas ance shiru magana ce ga mai hankali domin wannan kaucewar da Jabir yayi masa tamkar ya sokeshi da wu'ka yakeji, yana bu'katar wanda zai nemi shawararsa game da wannan lamari sannan bashida wanda yakai jabir, bazai iya magana da 'yan uwansa ba yafi so yayi magana da bare, aiki ya faru cike da 'bacin rai yana tuna abubuwan da suka faru jiya, gashi har sun fara zama labari. La'asar ya tashi daga aiki yana komawa gida Sultana ta sameshi tace zata d'ebi kayan Huda, bud'ewa yayi suka shiga tare Yana zaune ta kwashi duk kayan Huda ta zuba a buhu ta fita, binta yayi a baya yaja gidan ba tareda ya damu da rufe ko Ina a ciki ba. *********** *BILKISU* Washegari ina d'aki a kwance naji sallamar Sultana, ban ko motsa ba domin nasan mama zata turo ta d'akin, Ina jin muryarta tace "Huda jeki kiramin Maamanki a d'akincan" amsawa Huda tayi da to inaji tana 'kwalamin kira, bud'e labulen tayi tace "maamma" "Na'am" na amsa hawaye yana d'igomin, tahowa tayi da gudu ta nufoni na d'auketa tareda hugging d'inta, murna take sosai ni kuma ina kuka, da ace hawaye yana 'karewa inada tabbacin nawa saura murfi d'aya domin daren jiya ban samu baccin cikakken awa uku ba ina sana'ar kuka, zama Huda tayi ta zubamin ido sai a yanzu na fara 'ko'karin goge hawayena ina danne damuwata, murmushi nayi nace "ke da waye kukazo". "Atti" ta fad'a tareda nunamin 'kofa, Hijabin kanta ta cire ta jefar ta d'auki wayata ta kai kunne tace "Abba" Nan ta fara zuba gwarancinta cikin waya, duk lokacin da saleh baya gida haka takeyi Wanda hakan da tayi yasa naji wani sabon ciwo a raina, Anya Huda zata iya zama a wurina ba tareda tana ganin Saleh ba? Indai inaso na manta da Saleh sai nayi nesa da Huda. Gama gwarancinta tayi ta bani wayar ta fara jan rigarta alamun a cire, cire mata rigar nayi na barta da vest ta sake dawowa jikina ta kwanta, Sultana bata shigo ba da alamu bawa mama labari takeyi, tashi nayi na wanke fuskata na d'auki Huda muka fita. "Kuma wallahi mama ko ni bazan iya ha'kurin da Bilkisu tayi ba saboda abubuwan sunyi yawa, ni kaina ba komai nasani ba amma iya wad'anda na sani bazan iya jurewa ba, kuma still.....Ah maman Huda kin fito kenan" Sultana ta fad'a lokacin da taga na fito, murmushi nayi mata nace "sannu da zuwa ina Ahmad". "Gashinan a goye". Shiru mukayi dukkanmu, wayar mama ce tayi 'kara ta d'aga, cikin sauri ta d'auki hijabi ta saka tace "Ru'kayya ke labour zanje mu kaita asbiti". Tashi nayi nace "Mama yanzu Ru'kayya na gida amma baki fad'amin ba? Inaso na biki". Kallona tayi ta kalli Sultana sannan tace "ba'kuwar kuma kiyi Yaya da ita? Ki zauna idan mun dawo sai kuje kuga babyn". Fita Mama tayi ta barmu ni da Sultana, "wacece Ru'kayya"  Sultana ta tambaya, "itace wacce akayi aurenta watanni bayan nawa, Kinga har zatayi haihuwa ta biyu". Shiru nayi sannan nace "ya akai kika fito da Huda bata sani ba". "Ta sani kawai ce mata nayi zanje gidan friend d'ita ita kuma Bata ta'ba ganin Huda ba tace naje da ita,  idan Usman ya dawo zai biyo ya kawo kayanta suna motarsa". Shiru mukayi na d'an lokaci sannan Sultana tace "Bilkisu kiyi ha'kuri kuma kisani Allah yana tareda mai gaskiya na sani an cuceki amma ki dogara ga Allah, 'kulle kanki a d'aki ba mafita bane dukda nasan rabuwa da Wanda kakeso akwai wahala" "Bilkisu na sani kuma bazanga laifinki ba, domin a duniya akan Saleh nasan menene so, tun ina 'karamar yarinya nake son Saleh, tun ina 8years nake fad'an Uncle zan aura, haka nayi secondary na tafi saadatu rimi na gama ban bari kowane namiji ya shiga rayuwata ba saboda zuciyata na adanata ga Saleh, ki duba soyayyar da na ri'ke sama da shekara ashirin ina rainonta a zuciyata na ha'kura meyasa ke bazaki ha'kura ba, shekara nawa kikayi kina son Saleh? Gaba d'aya bakifi biyar ba, amma duk yarintata ta 'kare akan Saleh, daga silly crush har takai ga ta zama soyayya, bazan miki 'kary ba har yanzu akwai soyayyar Saleh a raina amma ba yanda zata hanani rayuwa ba, soyayya ce wadda bazata ta'ba barina na aureshi ba ko da kuwa mu kad'ai muka rage a duniya, ranar da Saleh ya sanar mana ke nakeso wallahi ji nake kamar na kashe kaina a wannan ranar, nasan yanda kikeji bazan kuma hanaki damuwa ba  amma ki tuna akwai wad'anda suke sonki suke damuwa dake, bakya tunanin kin yanke musu wani 'bangare na farin cikinsu saboda son zuciyarki? Duk abinda zakiyi ya kasance ya shafeki ke kad'ai karki bari akan mutum d'aya ki saka mutane sama da goma a cikin damuwa kiyi tunani". Sunkuyar da kaina nayi nace "insha Allah zanyi 'kokari na kuma duba maganarki, amma ki duba rabuwata da taki ba iri d'aya bace, ba wai iyakacin soyayyar Saleh bace ke damuna, irin wula'kancin da zargin da yakemin ma yafi damuna bayan yasan a cikin gidan shine gatana bayan mahaliccina". "Idan Kika yimin kuka ranki zai 'baci kuma zan tafi da Huda bazan sake kawo miki ita ba, a haka kikeso ki zauna da 'yar taki bata da abin kallo sai hawayenki? Ki lura ki san me kikeyi". 33 Sai bayan la'asar Sultana ta tafi ta barmin Huda, bayan tafiyarta na zauna na fara tunani, idan har na ri'ke Huda to kenan inada hope na komawa ga Saleh? Gashi har na kwana a gida bai nemeni ba, idan har inaso na cire Saleh a rayuwata sai na rabu da duk wani abu da ya danganceshi. Huda na bacci mama ta dawo ta sanarmin Ru'kayya ta haifi mace, d'aukan Huda nayi na fice na nufi babban gida, babu kowa a gidan daga ita sai adda da Yaya dake had'a ruwan zafi ita Kuma tana d'aki tana zaune tana waya sai wani lullumshe Ido takeyi, d'aukan babyn nayi ta ajiye wayar tareda kallona tace "Bilki yaushe kika zo babu labari?" "Jiya" na fad'a ina gyara Safar babyn, zubamin ido tayi tace "bakida lafiya ne? Naga kin canza". Murmushi nayi mata na girgiza kai alamar a'a, wasa ta fara da Huda ganin banida niyyar magana, ganin shirun yayi yawa nace mata "mun rabu da Saleh jiya na dawo gida". Kallona tayi cike da tausayawa abinda banaso kenan, banaso ana tausayamin hakan ke sakawa Ina tausayawa kaina, dafa kafad'ata tayi tace "Ayya Bilki kiyi ha'kuri Allah yasa hakan ne mafi alkhairi" "Ameen nagode" na fad'a tareda 'ka'kalo murmushi, Ru'kayya ta san irin zaman da nakeyi dukda ba komai ta sani ba, ta san dai matsalar rashin haihuwa da kuma 'kiyayyar dangi, da ace ina haihuwa wani wula'kancin ba'a isa a yimin shi ba. Bansan cewa da 'karfi na furta maganar ba saida naji Ru'kayya tace "a'a ki ma dena wannan tunanin bilki, idan ba'a sonka hausawa suka ce sai ka shiga ruwa ace ka tada 'kura, ko kina haihuwar abinda Allah ya tsara sai ya faru sai ya faru, sai ace kin fiye haihuwa ko ace kin fiye haifar maza ko Mata, ko ace 'ya'yanki basuda tarbiyya ko Basu da kyau ko 'kazamai ne, d'an adam ba'a iya masa ke dai kuyita addu'a Allah yayi miki za'bin alkhairi ya kuma saka miki, amma kuma kun rabu kika taho musu da yarinya?" Kallon Huda nayi nace "gani nayi kamar idan na taho da ita zata ragemin kewa kuma..." Shiru nayi Ru'kayya tace "a'a indai gaskiya zan fad'a miki babu fa'idar tahowa da yarinyarnan, kina tunanin watarana zaki koma kenan ko? Kinada hope kwanannan zai maidake ko? Bilkisu na rasa wace irin zuciya ke gareki, ko da tilastashi akayi ya sakeki karki sakawa ranki cewar zaki koma domin mazan yanzu wallahi sun 'baci, duk son da namiji ke miki wuyarta ya furta sakinnan sai Kinga banbanci, idan kika ri'ke yarinyarnan kamar bakyaso kin ri'ke wani sashi ne na 'kaddararki mara kyau, babu ke babu kwanciyar hankali indai Zaki kalleta to zaki tuna iyayenta, ki tuna tsohon mijinki sannan ki tuna irin 'kuncin da kika shiga ta dalilin jininta, indai kece bilkisun da na sani kina dab da fara Jin haushin yarinyarnan, shawarata idan kinaso ki manta da baya to ki maidata wajen iyayenta, bakya ganin wasu idan an sakesu 'ya'yan cikinsu ma barinsu suke saboda basa son abinda zai tuna musu da rayuwar aurensu, ki maidata kya dinga ganinta a hoto zaifi miki gaskiya a ganina, amma kiyi tunani". Ko da na kwanta bacci tunanin maganar Sultana da Ru'kayya nayi, tabbas inada son kaina a wannan lamari bana hangen kowa sai kaina, ta yaya zan cirewa kaina wannan damuwar domin banaso ta shafi kowa nawa, hawaye ne ya gangaromin na goge, sallamar mama naji da sauri na rufe idona kamar bacci nakeyi, sunana ta kira nayi shiru ina jin takunta tana matsowa dab dani ta d'aura hannunta a kaina, numfashi ta sauke tace "Allah ya kyauta" sannan ta ajiyemin abu a gefen gadona ta fita, juyawa nayi naga pcm na d'auka nasha domin kaina na ciwo na koma na kwanta na rufe ido ina jiran zuwan bacci saidai kamar nasha maganin hana bacci, na san cewa ina gab da bawa kaina matsala idan har bana cikakken bacci da cin abinci, a cikin jikina ma na fara Jin na canza. Wasa-wasa har nayi kwana biyar a gida Saleh bai le'ko ba balle waya, Ina zaune a Palo na zubawa tv ido naji sallamar aunty, amsawa nayi na gyara zamana, tana shigowa ta ri'ke 'kugu ta zubamin ido take tsoro ya kamani nasan yau zuwan nawa ne na musamman, " 'kaniyarki" ta fad'a tareda yimin da'kuwa, turo baki nayi nace "ni kuma anty me nayi?" "Uwaki kikayi, yanzu ke akan d'a Namiji kika lalace haka? Amma kinji kunya wallahi dubeki, har namiji ya wula'kantaki ki zauna kina wani damuwa a kansa? Kamar wadda tayi ciwo dubi fuskarki? Wato jira kike ki mutu kawai ki bar mana gawarki saboda namiji ko?" Sunkuyar da kaina nayi na fara hawaye, tsawa tayimin tace "karki sake ki yimin kuka anan!! Ke da kinsan ciwon kanki ba kece da kuka ba shi wanda ya sakeki shine da kuka". Ai kamar ta tunzurani kuka na fara sosai, zama tayi gefena ta jani jikinta sai kuma rarrashi kamar ba itace ta shigo take shirin dukana ba "ya isa haka Bilkisu ba kuka ya kamaceki kiyi ba, na sani akwai ciwo amma kin sakamu a damuwa, Bilki zaki d'aura ma kanki ciwo ki barmu da ganin laifin kawunanmu, amanarki mahaifiyarki ta bar mana idan kika sakawa kanki ciwo ai kamar mun ci amanar mahaifiyarki ne, mun sani kina sonshi amma idan ya rabu dake kema ki rabu dashi mana, menene amfanin barinsa a zuciyarki yana haifar miki da damuwa?". Goge hawayena nayi nace "aunty kuyi ha'kuri banyi hakan dan na saka muku damuwa ba, na kasa controlling hakan ne a raina". "Tunda kin auri autan maza dole soyayya ta kasheki ko? Ke kina nan kina kuka shi kinsan me yakeyi? Bilki ki dawo hankalinki mana, na zamar miki misali shekara goma sha uku da mutuwar aurena, dai-dai da awa d'aya ban zubar da Hawaye akan sakaran mutumin da ya rabu dani ba domin asararsa ce, ke yanzu bayan zargin da yake miki da kuma sakin wula'kancin da yayi miki har kikewa soyayyarsa kuka? Kukan da bai san kinayi ba? Tunda haka ne d'auko gyalenki maidake zanyi, ai dama a shari'a bazaki bar gidan ba sai kin cika idda, ki koma kiyi iddarki sai ki dawo idan ya maidake kuma shikenan kowa ya huta". Kallonta nayi naga alamun ko da wasa take amma sam babu alamun wasa a tattare da ita, tashi tayi tace "maza d'auko gyalenki mu tafi domin babu maganin kukanki sai zaman gidan mijinki ko kuwa?" Girgiza kai nayi nace "Aunty banaso na koma" wani kallo ta watsomin tace "sai kin koma, bazaki zauna kina mana kuka muna kallonki ba, ta yiwu idan kina ganin mijinki zaki dena gaki ga dangin mijinki ga kuma mijinki da alamu wannan zaman yafi miki dad'i". Hango irin gori da wula'kancin da zasu min na fara, a 'kasa na zube na fara mata magiya ina kuka sosai, gashi mama ta'ki fitowa ta ceceni, da 'kyar da al'kawura Aunty ta barni sannan ta zauna, ba tareda ta kalleni ba tace "Abu na farko shine ki maida wannan yarinyar" babu musu nace mata "to" sannan tace "takardunki suna wurinki ko suna gidan tsohon mijin naki?" Harda kaurara tsohon mijin nawa, ban nuna mata komai ba nace "suna nan bayan an bani na kawowa baba". "Zan kar'be su na nema miki aiki ko ya rage miki wani abun sannan idan tsautsayi ya had'a ni da mijinki wallahi sai na yi masa tatas, jinin matsiyata wanda bai gaji arzi'ki ba, shi ko duniya ce dashi ya isa ki masa sata?miliyan biyun banza da wofi? Ko gadonki ba ya tattake arzi'kinsa ba? Zai san ya wula'kanta mana 'ya zai gane cewa kinfi 'karfinsa daga shi har matsiyatan danginsa, daga yanzu kin fara facaka da dukiyarki, Allah ya kaimu ki fita idda a satin zamu bar 'kasarnan, sai munyi yawon duniya dake har kin gaji, Yana can yana fama da tsiyarsa tsautsayi ma ya Sanya yace ya maidake sai na makashi a kotu wallahi". Shiru nayi da bakina aunty tayi ta banbaminta, tana cikin magana naji 'karan wayata, dubawa nayi naga *my boo* hannuna rawa ya fara aunty ta kar'bi wayar ta duba, mi'komin tayi ba tareda tace komai ba, ina kallon wayar har kiran ya katse, sake kira yayi saidai na kasa d'agawa, meyasa Saleh ya kirani? Ko dai ya fara nadama ne zai bani ha'kuri? Kafin Kiran ya sake tsinkewa na d'aga na kai kunnena "Salamu alaikum" Tsit nayi saida ya sake sallama sannan na amsa, shiru yayi shima sannan yace "ya kike?" Amsa masa nayi nace "lafiya" Ina jin saukar numfashinsa jira kawai nake naji dalilinsa na kirana kamar ya sani ya fad'a "umm....ajiyar da nake baki ce ina key d'in yake?" Kallon wayar nayi na sake maida ita kunnena, I can't believe this!!! Yanzu dalilinsa na kirana kenan ba dan duba lafiyata ba? Gaskiya ake fad'amin Saleh baya sona kamar yanda nake sonshi, 'bacin rai ya turnu'keni saidai nace masa "kazo gida ka kar'ba Yana hannuna" na katse kiran, nayi haka ne domin na jarraba shi saboda kud'in da ya bani last ban sakasu a ciki ba suna cikin jakata a can gidan, so nake naji me zaice. Zubawa wayar Ido nayi har aunty tace "akan me ya kirawo ki? Ko kud'in da kika sace yakeso ki biyashi?" Girgiza kai nayi kalamanta na dukana, har yaushe wannan kalmar satar zata dena bibiyata? Daurewa nayi nace "kud'i yake bani ajiya shine yake tambayata suna ina?". Gyara zamanta tayi tace "yanzu tunda kikazo gida bai nemeki ba sai yanzu? Shima ba don lafiyarki ba saboda bu'katarsa? Wani irin miji muka aura miki bilkisu? Wace irin rayuwa muka turaki kikayi?" Gyaran murya nayi nace "aunty ba laifinku bane laifina ne da na kasa ganin gatan da kuka yimin nabi son zuciyata na auri bare, da d'an gida na aura bazai min haka ba, gaskiya kuke fad'amin Saleh baya sona baya ganin mutuncina". "Bilkisu Saleh yana sonki amma a baya, kawai yanzu wani abun ya canzashi ne shiyasa da ki auri miji danginsa basa sonki gwara-gwara ki auri wanda baya sonki 'yan uwansa kuma kamar su cinyeki (readers ya kuke ganin wannan batu? Ina jiran raayoyinku). Yana sonki amma ya had'u da sharrin mata ne kinsan sharrin mace ki shaid'an ya sarawa mata, Allah kad'ai yasan abinda suka kitsa masa kuma dama shi karkatacce ne sun janye ra'ayinsa, amma gaskiya bata 'buya zai ganota amma lokacin da bazata amfana masa komai ba". Bamu sake wata magana ba sai ta aikin da za'a nema min da 'kasashen da nakeson zuwa, muna hirar naga kiran Saleh ba tareda na amsa ba na d'auki key ko mayafi baj yafa ba na fita, har na kai gate na koma na d'auko Huda da kayanta, Ina fita na bud'e bayan motarsa na sakata ba tareda na kalleshi ba, cire key d'in nayi na ajiyeshi a kan motar nayi gaba. "Bilkisu" cak na tsaya wannan shine Karo na farko da ya kira sunana bayan kwana biyar, gabana fad'uwa ya fara yi jikina gaba d'aya ya d'au rawa, ba tareda na juya ba na fad'a gida tareda doko 'kofar, idan aunty taji wannan labari zata iya bani kyautar kujerar maka, domin a yau babu sunan da bata Kira Saleh ba, tun ina jin haushi har ta fara bani dariya, bayan na gama saita kaina naji tafiyarsa sannan na koma gida na fara jiran kiransa akan ragowar kud'in da basa cikin akwatin, abun mamaki har dare bai kirani ba maimakon hakan ya birgeni sai ya bani takaici, wato ma bazai tambaya ba saboda halina ne cinye kud'insa, takaici yasa nayi yun'kurin deleting numbersa sai kuma nayi tunani, idan nayi deleting number dake kaina ai 'bata lokaci ne, editing number nayi nasa EX SALE, daga yau bazan sake grieving rashin Saleh ba zan fara tsarawa kaina sabuwar rayuwa. ************* *SALEH* A kwanaki biyar d'in da yayi babu Bilkisu gaba d'aya ya canza, har mantawa yayi da wankin underwear nashi saboda ya saba tana wanke masa, 'bangaren abinci kuwa ya ma dena cin na gida saboda Hajiya batada abinci sai tuwo, idan ba tuwo ba shinkafa da miya ko lettuce babu, a hakan ma shi yake bada kud'in cefane domin da gayya Hajiya zata yi miya babu nama sai yazo ci ya gani, a nan zai bada kud'in naman domin tace baisan kan cefane ba Bilkisu ta lalatashi da cefanen almubazzaranci. Tafiya yake hankalinsa na kan rayuwar da ya koma, gashi Jabir ko sallamarsa a ciki yake amsawa, baya bashi fuskar da zai masa wata magana, cikin takaici ya daki steering d'insa ga kukan Huda ya isheshi ga damuwar me zai tarar yau a gida, tsorata ta yayi ta sake fashewa da ihu har suka je gida tana kuka, saida ya kaita wajen sultana sannan ya shiga ya gaida Hajiya. Tana zaune tana cin tuwon dawa da miyar kuka, dan kyau abinci yayi kyau domin Hajiya bata tuwon banza, saidai shi tuwo bai dameshi ba Bilki ce kawai ta san cikinsa, "matso muci mana sai na 'karo mana", "Hajiya naci abinci ai" ya fad'a tareda gyara zamansa, kallonsa tayi tace "yanzu Saleh fisabilillahi ka d'auki mummunar d'abi'ar cin abinci a waje ko? Wato wannan tsohuwar matar taka me halin yahudawa abinda ta koya maka kenan yawon cin abinci? Wa ya sani ko wanda take baka kullum siyowa takeyi shiyasa bakinka ya saba" Shiru yayi bai tanka mata ba, ganin haka yasa ta sauya zancen tace "ya maganar hadiyya? Tunda mukayi maganar kai bakace komai ba yaushe zakaje ka ganta ne? Yarinyarnan fa Allah ya bata farin jini shiyasa ma uwarta takeso ka aureta su huta, kullum akwai wanda zaizo wajenta Allah yaso ma mai hankali ce tunda akayi maganarka duk wanda yaje wajenta sai tace an mata miji, yanzu ka saka rana kaga yau lahadi ko? To banaso wannan rana ta zagayo baka je kaga yarinyarnan ba". Tashi yayi yace "to Hajiya insha Allah za'ayi hakan, aiki ne ya hanani amma zan fidda lokaci naje". Fita yayi ya nufi gidansa, bud'ewa yayi ya kalli uwar 'kurar da TV stand yayi, wucewa yayi stairs ya zauna bakin gado, tun bedsheet d'in da ta bari bai canza wani ba, kwanciya yayi ta baya ya tuna lokacin da suke rige-rigen hawa gadon idan sun fita musamman fitar dare, kawar da tunanin yayi ya d'aga gadon ya d'auko akwatin ajiyar bilki ya bud'e ya ciro kud'in, 'kirgasu yayi yaga babu 140,000, tunawa yayi ta fada masa ya tuna mata ta ajiye kud'in a Jakarta, d'auko jakar yayi ya had'a kud'in ya sanya a jakar fitarsa ya cire kayansa ya nufi toilet, shi kansa toilet d'in ya fita a hayyacinsa haka yayi abinda zaiyi ya fito ya kwanta. Wayarsa ya bud'e ya shiga WhatsApp, har zai fita yaga wani link yaga an turo *yara goma da kwankwaso ya biyawa aikin zuciya a india* Cikin sauri ya danna link d'in cikin sa'a kuwa yaga hotunan yaran, tunawa yayi da maganar Bilkisu da sauri ya tashi ya zauna ya fara karanta labarin, bin sunan yaran yake d'aya bayan d'aya yakeyi har yaga suna mai kama da na Amir ZAYYANU ISA, hannunsa har rawa yakeyi ya shiga hoton zayyanu, hoton amir ya gani ga maimuna na ri'ke dashi a 'kasa an rubuta *Babu abinda zamuce sai godiya ubangiji ya 'kara arzi'ki, inji Mahaifiyar zayyanu MAIMUNA ABUBAKA*...... I 'Kurawa hoton kallo yayi ya kasa ko 'kifta idonsa...... 34 Tashi yayi cikin hanzari ya fita, a 'kofa ya tsaya ya runtse idonsa idan ya kaiwa hajiya wannan magana ranshi ne zai 'baci bayaso tace ta san wannan zance saidai bayaso ya gaskata hakan, idan har gwamnati ta biya musu kud'in aiki meyasa suka kar'bi kud'insa? 'ko'karin danne gaskiyar yakeyi a bayan ransa saidai gaskiya a bayyane take 'karara, sai yanzu ya fara komawa hayyacinsa, shin me ya aikata cikin fushi? Me su hajiya suka aikata masa? Komawa yayi ya kwanta yana sake duba labarin domin ya gaskata, kwanciya yayi kan kujera ya fara tunanin yanda zai tunkari hajiya da wannan bayani, dalili d'aya yake son ji, meyasa suka kar'bi kud'in? Me zasuyi dashi? Da wannan tunanin ya kwanta ********* *BILKISU* Banyi tunanin za'a samar min aiki da wuri ba, amma abin mamaki ina zaune sai ga kiran aunty tace na shirya naje gidan ta zata kaini interview na aiki, dama ana bu'katar interview a nursing? Ina shiryawa ta sake kirana, cikin d'aga murya tace "saura kizo min da jajayen idanu sau na saka a kwantar dake a asbitin na wata hud'u", dariya nayi nace "to aunty" abinda bata sani ba tuni na dena wa mutuwar aurena kuka, dama nasan igiyar aurena bazata zauna ba tun ranar da na saka 'kafafuna a gidan. Bazan ce Saleh ya fita daga raina ba amma na kaishi can wani wuri a zuciyata, koyaushe yana raina amma bana tunaninsa, bansan ko akwai wanda ya fahimci maganata ba. Na san halin aunty ko gumi ta gani a fuskata sai ta 'karewa Saleh zagi nima na sami rabona, saboda haka na d'an b'ata lokaci wajen makeup, abinda banyi ba kusan sati biyu kenan. Powder na shafa na sanya purple d'in jambaki nayi highlighting da  jagira, saida na 'karewa kaina kallo sannan na yafa mayafi, i can't believe it, wai ni ke iddar Saleh ya sakeni, Allah yasa ma ba fara wuri. Ina zuwa gidanta na sameta tana zaune a palour da jakarta da mayafi a gefe, kallona tayi ta saki murmushi tace "haba ko kefa, har kin fito a mace da kina kwance bakida aiki sai kuka akan wancan me......" "Dan Allah aunty karki 'karasa ki barshi haka, ni ina mamakin ma yanda kalamannan basu 'kare a bakinki ba duk zaginsa da kikeyi a barshi haka". Na 'kare maganar ina dariya, harara ta tayi cikin wasa tace "da kansa kamar banana". Dariya nayi sosai, har mantawa nakeyi aunty ta kai mahaifiyata saboda yanda take abubuwanta, ta iya tafiya da mutane ko Yaya mutum yayi socializing da aunty sai ya sota, idan akayi hutu gidan cika yake da yara, dukda ban ta'ba ganin mahaifina ido da Ido ba amma idan na kalleta tana tuna min dashi, mama tana yawan fad'amin halinsu d'aya da mahaifina, irin mutanennan ne da basa nuna fushinsu, idan kana tunanin basu haushi saidai ma ranka ya 'baci. "Tashi muje kar mu makara" tashi nayi muka fita a motarta, baifi tafiyar minti 15 ba sai gamu a asbitin, kallon wurin tayi tace "ya kamata a saya miki mota saboda fita", bance komai ba domin zanso nima na fara tu'ka motar kaina, ina yawan driving ta Saleh musamman zuwa makaranta kuma fita a motarka yafi mutunci musamman a wannan zamani na cudanya da 'katti a abin hawa. Asbitin nada girma ba laifi sannan ya matu'kar had'uwa, tun daga wajensa har ciki, secretary ta wurin naji ta tambaya wani mutumi nan tace mata yana office, babu wani jira taja hannuna muka zagaye secretary d'in muka wuce, 'kwan'kwasa 'kofa tayi kafin ace mu shiga ta bud'e tareda turani sannan ta shiga. A fusace mutumin ya juyo zai fara fad'a yana ganinta yanayinsa ya sauya, bansan waye wannan ba amma dai naji yanayin wurin ya canza, "ko kujera baza'a bamu ba Abban shaheed?" Kallona yayi da alamun kunya sannan yace "kuyi ha'kuri ga wuri ku zauna", d'aura 'kafa d'aya kan d'aya aunty tayi sannan tace "sai naga kana nuna kamar baka san da zuwanmu ba bayan dai kai ka kirani ko har tsufa yasa ka fara mantuwa haka, ko kuma kyakkyawar 'yar tawa ce tayi maka?" Dariya yayi yace "a'a babu ko d'aya, Hafsa banda abinki ina ni ina 'yarki bayan na aureki? Kawai zuwan naku ne....." Katse maganarsa yayi ya kalleni yace "itace Bilkisu ko?" "Eh 'yar wajen marigayi ba" kallona yayi cikin tausayawa sannan ya janyo file, sunkuyar da kaina nayi domin na tsani wannan kallon, Allah yayimin gata da bana cikin maraici bansan meyasa mutane ke son dawomin da kewar iyayena a koyaushe ba. Gaba d'aya hankalinsa ya dawo kaina yace "Bilkisu takardunki sunyi kyau, na duba komai naki, amma meyasa kika 'ki amincewa asbitin da kikayi internship bayan sun d'aukeki aiki?" Shiru nayi na rasa me zance, a lokacin bana so na fara aiki saboda Shirin d'aukan ciki, sannan ban dad'e da warkewa daga ciwon da nayi mai kama da hauka ba wanda har mutuwata bazan manta dashi ba,amma ta yaya zan fad'a masa wannan? Sannan asbitin bana 'kaunarsa dama dai koyan aiki ne ya kaini kuma na aikatu, na kar'bi haihuwa tafi 500 a shekara d'aya da nayi banda aikin emergency da sauransu. "Nayi rashin lafiya ne a lokacin bazan iya aiki ba sannan basu barmin offer d'in ba bayan sunga yanayin rashin lafiyata sai suka janye offer" "Wani irin rashin lafiya kikayi?" Aunty ce ta tari numfashinsa tace "aljanu ne suka kamata a lokacin amma cikin ikon Allah da taimakon su alhaji baba ta warke kamar batayi ba, baban shaheed haka ake interview d'in aikin? 'yata ce fa ka yiwa Allah ka dena mata tambayar ya uwarta ta haifeta ka bata aikinnan". Dariya yayi, wani abu dana lura shine duk tambayoyin da yakemin hankalinsa na kan Aunty, waye wannan ko dai?..... Kunya naji da tunanin yazo raina, duk girman anty ace wannan saurayinta ne? Au bazawari? Dariya naji ta 'kwacemin na danne, ina kallonta tana min wani irin kallo. Tambayoyi yayimin akan aiki, tambayoyi ne da sai ka amsa a dabara har tambayata yayi wani 'bangare ne banaso nayi dealing da nace babu, bayan kusan awa guda ya d'aukeni aiki, takura masa Aunty tayi akan sai ya fad'a mata salary na ya'ki yace idan naga alert sai na fad'a mata idan naga dama Har mun fita ta bud'e 'kofa tace "ka gaida maman shaheed kace mata tsohuwar natarnan taka me naci tana gaidata". Girgiza kai nayi tareda murmushi, amma nayi mamaki da tunda na taso ban ta'ba ganinsa ba, ina yawan zuwa gidan Aunty amma bana ganinsa. Kamar ta karanta tunanina tace "gaba d'aya aurena baifi a 'kirga ba yake zaman gida lokacin yana aiki a England sannan ya'ki tafiya dani, a shekara baifi yazo sau biyu ba, zuwansa na 'karshe yazo min da maman shaheed da shaheed ya dad'e da auren ban saniba abubuwa da dama suka faru bayan haka da sukayi sanadin mutuwar aurenmu, wannan asbitin nashi ne yanzu idan ya miki abu komi 'kan'kantarsa ki fad'amin kinji? Allah ya kaimu first salary d'inki ya shigo idan ya sake ya baki 'kasa da d'ari dai ya ciko miki". Ta fad'a tareda had'e girar sama da ta 'kasa, numfashi ta sauke tace "ni ya kamata inci wannan kud'in amma ya zanyi? Yanzu ke zaki ciyo min su kin jini ko?" Gyad'a kai kawai nayi ta canza hirar, kafin muje gida na sayi yadin uniform sai yanzu na tuna da million d'ita dake wurin Saleh, dole kuwa na kar'bo kud'ina. Bayan mun sayi yadin muka wuce gidan aunty a can na wuni sai dare ta Kira Jabir ya d'aukeni, a hanya nake ce masa "Yaya akwai kud'ina fa a hannun abokinka, almost a million". "Meyasa kika bashi kud'inki haka? A ina ma kika samu wannan kud'in?" "Kud'in internship ne da gwamnati ke biyanmu duk wata lokacin da mukeyi, ana bani 135,000 duk wata, ina d'an siyayya shiyasa ma kud'in baikai million ba sannan ya ari wasu". Murmushi yayi yace "Zan sa ya turo miki kud'inki sai ki kiyaye nan gaba kisan wa zaki bawa kud'i, tunda ya manta da amince masa da kikayi kika bashi ajiyar ma'kudan kud'i yake zarginki da sata". Jingina nayi a kujerata nace "Yaya dan Allah mu bar wannan maganar kaji?" Amsamin yayi da to mukayi shiru, fruit muka saya sannan muka tafi gida. ************ *SALEH* Yanke shawarar fad'awa Hajiya yayi, bayan sun gaisa ya d'auko wayarsa yace "hajiya...." Katseshi Hajiya tayi tace "na gaji da kar'bar uzurinka akan zuwa wajen hadiyya, yau bayan Isha zakaje ka sameta na sanar da iyayenta kuma banaso a sami sa'bani". Maida wayarsa aljihu yayi yace "Hajiya ya jikin Amir" cikin sauri tace "Amir dai to gashinan idan Allah ya yarda wannan asabar d'in zasu tashi zuwa indiya, Allah ya saka maka da alkhairi ka taimaka wa 'yar uwarka". "Kenan jirgi d'aya zasu hau da yaran da gwamnati ta biyawa aiki". "Eh..." Shiru tayi ta zuba masa ido tace "me kake nufi? Wannan tsinanniyar bayan ta tafi ma sai ta dinga jan ra'ayinka? Me kake nufi da abinda ka fad'a? Zargina kake da 'karya ko me?" Tashi yayi tsaye yace "hajiya ba 'karya nake nufi kinyi ba, tambaya kawai nayi saboda naji ance suma asabar zasu tashi na yarda da abinda kika fad'a" fita yayi ba tareda yace komai ba yana jin tana tuna masa da zuwa ganin hadiyya. Kamar kullum suna gaisawa da jabir suka fara aiki, ya gaji da silent treatment d'in da Jabir ke masa saboda haka ya nufeshi kafin Jabir ya koreshi yace "Jabir kayi ha'kuri da abubuwan da suka faru ka saurareni, nasan nayi kus......" Dakatar dashi Jabir yayi yace "lokacin da Bilkisu ke ro'kon'ka ka saurareta ka saurareta? Lokacin da take bu'katar ka fahimceta ka fahimceta? Ka saki 'kanwata tsawon sati biyu amma baka tambayi Yaya lafiyarta ba, baka kirata ko sau d'aya ba sannan kace kana so na saurareka kayi kuskure bazan ta'ba sauraronka ba, akwai aikin kitchen da muka kar'ba daga yobe zaka tafi ranar lahadi zan had'aka da mutum biyu saboda ayyukanmu na nan sunada yawa" Yana gama maganarsa ya bar wurin, cikin 'bacin rai Saleh ya daki katakon dake gefensa dariya  jabir yayi yace "Kar ka karya mana katako zaka biya". Har Jabir ya gama aikinsa ya tafi Saleh na wurin, sai gab da magrib ya tafi gida, ko abinci baici ba ya fita ya nufi gidansu hadiyya, kwatancen da Hajiya ta masa saida ya sake tambaya aka kaishi gidan, kallon unguwar yayi yanda yara keta shige da fice kamar ba dare ba, yaro ya tura aka kirata ta kusa 30mins sannan ta fito. Sanye take da hijabinta kanta a 'kasa, dur'kusawa tayi ta gaidashi  ya amsa, shiru sukayi tana dur'kushe yana tsaye hakan yayi masa wani daban shima ya dur'kusa a 'kasan, 'kwala mata kira akayi daga gida ta tafi da sauri, dawowa tayi da tabarma da fitila ta shimfid'a ta zauna a can gefe, zama sukayi ta had'e kanta da gwiwa tana kallon gefe, haka suka 'kare zaman nasu shine ma ya d'an mata tambayoyi   wanda ta bashi amsa da kalma dai-dai, gajiya yayi ya tashi ya tafi. Ranar asabar baije aiki ba kasancewar lahadi zaiyi tafiya Jabir ya bashi day off ya kintsa, yayi tunanin za'a shirya Amir a part d'in hajiya amma sai yaga hajiyan ma bata nan lokacin da yaje gaidata, gidan maimuna yana zuwa yayi sa'a sun fito, a tsorace duk suka kalleshi ga Amir yasha farar shadda da jar hula, hajiya ce ta dake tace masa "me kakeyi anan?" Murmushi yayi yace "nazo yi musu sallama ne Hajiya kuma naso mu taho tare naga kin rigani zuwa, muje na kaiku airport d'in". Gaba yayi da amir a hannunsa ba tareda ya jira me zasu ce ba, haka suka bishi a baya suna jan 'kafafu, babu wanda ke magana a motar sai shi har suka isa, Takarda maimuna ta nuna aka tafi da ita da Amir inda sauran yaran suke da iyayensu a tsaye, hotuna aka fara sannan suka shige jikin su Hajiya gaba d'aya yayi sanyi domin ba haka suka yi zato ba, tunaninta zaije aiki kafin ya dawo saidai tace masa maimuna ta tafi amma yanzu bata san ma me zata ce masa ba. Bayan sun shige Saleh yace da kursum "muje na kaiki gida ko? Ko kuma gidanmu kika nufa?" Gyad'a masa kai kawai tayi kamar 'kadangaruwa suka nufi mota, suna shiga Hajiya ta fara kuka, kallonta Saleh yayi yace "Hajiya kiyi ha'kuri Allah zai bashi lafiya su dawo, bakiga wasu daga cikin yaran ba sun fishi jin jiki?" Goge hawayenta tayi tace " 'yan uwanka suna cikin matsala wanda ni banida yanda zanyi na taimaka musu, ka duba ka gani ace inada 'ya'ya maza masu arzi'ki kamar ku amma 'ya'yana mata suna shan wahala? Daga maimuna har kursum babu wacce take auren mai arzi'ki, ni nawa 'ya'yan suna Shan wahala amma 'ya'yan wasu na cinye arzi'kinku, yanzu Amir har sai gwamnati ta biya masa aiki saboda talaucin mahaifinsa? Kun isa ai ku biya masa shiyasa da jumana tace min taji zancen kud'innan nace to 'ya'yana sunfi matarka bu'kata, na kar'bi kud'in ne Dan na tallafa musu na raba musu suyi jari tunda nasan idan nace ka bayar bazaka bayar ba". Dam'ke steering yayi yace "Amma Hajiya kinsan me zanyi da kud'in meyasa kika kar'beshi a lokacin? Idan har jari kikeso ni mai basu ne amma Hajiya dalilin wannan kud'in.....na rasa matata". Cikin 'bacin rai hajiya tace "dama ba matar arzi'ki bace, lokacin da zaka bada kud'in ba hanaka tayi ba?" Ya kusa dukan mai mashin cikin sauri ya kauce yace "hajiya ba hanani bayarwa tayi ba, gaskiya ta fad'amin cewar gwamnati ta biyawa Amir kud'in aikin, kuma ta fiku bu'kata, tana cikin damuwa na rashin haihuwa sannan ga takurar ku abinda tafi bukata shine ta haihu, nima ina bu'katar naga jinina, hajiya kinsan me zanyi da kud'innan amma kika kar'be?" Cikin d'aga murya hajiya ke magana tace "dakeni nace tunda na lura dukana kakeso kayi, idan haihuwar kakeso meyasa baka auro wadda zata haihu a kyauta ba sai wadda zata sayi d'a 'kwaya d'aya a miliyan hud'u? Banda hauka irin naka duk matan duniya masu haihuwa kyauta bazaka aura ba sai ita? Kud'i ne na kar'ba idan kanada hali sai ka 'kwata". Idanunsa tuni suka ciko da 'kwalla nadama ta dirar masa, muryarsa 'kasa-'kasa yace " Hajiya ya akai kud'innan suka koma gidana?" Saukar mari yaji a fuskarsa saidai rad'ad'in da yakeji a ransa yafi zafin marin, a fusace Hajiya tace "zargina kake ni na kai kenan? Uwarka ce ni idan ka manta ni na haifeka Dan ubanka!! Kuma matarka ta tafi kenan ka dawomin da ita gidana Allah ya Isa ban yafe maka ba, shashasha kawai". Saleh bai sake cewa komai ba har Allah ya kaisu gida domin tafiya kawai yake baisan inda yake bi ba, a waje su hajiya suka fita ta doka masa 'kofa, jingina kansa yayi a jikin steering Yana dukan sterrin, meyasa ya aikata wannan kuskuren? Anya Bilkisu zata yafe masa idan ya koma? Yasan halin bilkisu da sau'kin kanta zata saurareshi. Gida ya shiga ya zauna kan kujera, karo na farko a lokaci mai tsayi ya zubar da Hawaye, haka ya zauna Yana tunanin abubuwan da yayi messing, idan har ba sa'a yayi ba ya rasa matarsa har abada....bazai yiwu ba bazai iya zama da kowacce mace idan ba Bilkisu ba. Yana sallar magrib ya d'auki wayarsa ya fara Kiran number Biliisu saidai gaba d'aya ma kiran ya'ki shiga, Jabir ya kira saida ya kirashi sau hud'u tukun ya amsa, cikin sauri yace "dan Allah ka had'ani da Bilkisu". Shiru jabir yayi masa ya dinga masa magiya, Jin yanda yake magiya yasa jabir yasan an samu matsala, murmushin mugunta yayi tareda gyaran murya yace. "Saleh Bilki fa bata garinnan tun shekaran jiya suka tafi Kaduna saidai idan zaka bita". 35 "Dan Allah Jabir kar ka yimin haka ka taimakamin na ganta jo da na minti biyu ne". Jingina Jabir yayi a bango yana kallon Saleh, hannunsa yasa a aljihu yace "yanda na fad'a maka a waya Bilkisu bata nan tana tana KD, Idan wani sa'ko ne ka fad'amin idan ta dawo na sanar da ita". "Yaushe zata dawo?" "Friday" jabir ya fad'a Yana kallon wayarsa, cikin rawar murya Saleh yace "Dan Allah Jabir a d'aga min tafiyarnan zuwa wata Sunday d'in inaso nayi magana da Bilkisu kuma na kirata numberta bata shiga". "Tayi blocking number d'inka ne saboda tace batason wani abu da zai had'ata da kai, sannan tafiya idan har muka d'aga munyi asarar kud'inmu gaba d'aya kenan saboda sati uku ya bamu mu gama masa aikin, tunda kayi aure ban ta'ba bari kaje aiki a wani gari ba shekara uku kenan, yanzu akwai adalci ace tafiya d'aya da zakayi kana dodging? Idan bazaka je bane ka fad'amin nasan abun yi". Kallon agogon hannunsa yayi dukkansu sukayi shiru, kallo d'aya ya yiwa Saleh yaga alamun damuwa sosai a tattare dashi, amma basjida niyyar bashi abinda yakeso, indai Bilkisu ce sai ya sha wahala kafin ya sameta...idan ma ya sameta d'in kenan. "Idan ta dawo zan had'ata da kai a waya kuyi magana, saida safe ko? Allah y kiyaye hanya" Jabir na gama fad'in haka ya shige gida ya bar Saleh a tsaye, sake kiran Bilkisu yayi yaji bata shiga ba ya ha'kura ya tafi. Washegari 6:00 Jabir yaje ya d'auko Saleh domin ya kaishi tasha, ko sallama Saleh baiyiwa Hajiya ba ya fita ya shiga motar Jabir. "Dan Allah Jabir da gaske Bilkisu batanan?" Saleh ya fad'a yana kallon wayarsa, shiru Jabir yayi masa har sukaje tasha saida ya shiga mota sannan ya Janir ya juya ya koma gida. A kujera ya sami Bilkisu tana bacci da uniform a jikinta domin night tayi,wayarta ya d'auko ya bud'e ya duba number Saleh ya ganta a blocked, bud'e Ido tayi tareda mi'ka tace "Yaya ina kaje ne da sassafe haka na dawo bakanan?" Gefe ta matsa ya zauna yace "naje kai Saleh tasha ne zai tafi yobe aiki, nace idan kin tashi ki dinga kirana meyasa zaki dawo? Gari fa bai gama wayewa ba nasan kika fito haka last week kika taho da dare, Bilki yanayin garinnan sai a hankali karki sake tahowa da safe ko dare sai kin kirani kinji?" ************ *BILKISU* Tura baki nayi nace "to baba" kallo yayimin alamun na tashi ki gudu, aikwa cikin sauri na tashi, ri'ko hijabina yayi ya kama kunnena yace "me kikace?" Dariya nake sosai da kyar nace "yi ha'kuri yayana bazan sake dawowa ba tareda na kiraka ba, dan Allah sakeni". Sakin kunnena yayi na cire hijabin nace "ai Aunty ma tace za'a siyamin mota bansan dai yaushe bane". Dafe kansa yayi yace "au, aikuwa tayimin maganar tace tanaso ki fito gari kema ki shiga cikin 'ya'yan wane da wance, tace na bincika mota mai kyau ta mata me tsada, batason kamfanin motar Saleh komai kyantq". Had'e 'kafafuna nayi a kan kujera nace "Aunty dai is so obsessed with Saleh, bansan yaushe zai fita daga bakinta ba, naga anyo beetle sabuwar yayi shape d'in mata, tayimin kyau sosai motar". "To waye bazai so ki fita daga sahun su Saleh ba bayan wannan wula'kancin da yayi miki? Miliyan biyun banza? Ai motar da za'a siya miki sai tafi miliyan biyu domin ya gane kurensa, ke fa sai kinfi 'karfin Saleh a 'yan kwanakinnan". Dafe kaina nayi nace "Dan Allah yaya muyi wata maganar da babu saleh a cikinta" Jingina kansa yayi a kujera yace "ni da nake Shirin fad'a miki a daren jiya yazo nemanki amma nace masa bakyanan". Wani iri naji a raina amma na daure nace "me yazo nema a wurina? Ko wani kud'in ya nema ya rasa?" Murmushi Yaya yayi yace "ba kince bakyason maganarsa ba? A barta kawai". Banyi musu ba nace "okay" na d'auki mayafina da jakata nayi hanyar d'akina. "Cewa yayi yazo ya baki ha'kuri ne...ya kiraki baya samunki, na fad'a masa kina Kaduna idan kinaso ku had'u zan masa magana idan ya dawo". Ban waiwaya ba na shige d'akina na rufo 'kofar, zama nayi bakin gado na zuba tagumi, da ace a weeks d'in da suka wuce ne tsalle zanyi saboda murna, amma a yanzu wani irin takaici ya 'karamin, bai zo bani ha'kurin ba sai yanzu? Ya fara gano gaskiya kenan ko kuwa ya gaji da zaman kad'aici? Kwanciya nayi ina kallon ceiling, inaso na had'u da Saleh? Sadly yes inaso na had'u da Saleh, inaso naji dalilinsa na zuwa nemana bayan sati uku da sakina, inaso na kalli fuskarsa nace "gashinan abinda na fad'a maka ka 'ki amincewa dani" inaso naga Saleh amma duk yanda naso ganinsa nasan ba abu ne da ya dace ba, bazan amincewa zuciyata naga Saleh ba domin kalma d'aya zai fad'amin ya juyar da ra'ayina na koma gareshi wanda a yanzu shine last thing da nake bu'kata, inaso na zauna a gida na 'kara sanin kaina na san muhimmancin kaina, nayi tunani na kuma yanke hukunci ba tareda soyayya ta rufemin Ido ba, Ya Allah katka had'a ni da Saleh a wannan lokacin kar kuma ka bashi ikon maidani har sai na samu nutsuwa. Bacci ne ya d'ebeni na gajiyar aiki, 'karan wayata ne ya tasheni na duba naga number Aunty, danne wayar nayi na maidata silent naja abun rufa kafin na koma bacci naji muryar mama "tunda kin tashi sai ki fito kiyi breakfast ko?" "Ummm mama sai anjima har yanzu da bacci a kaina" na fad'a cikin shagwa'ba, matsowa mama tayi ta yaye abun rufar tace "tashi ki karya 11 ta kusa kina kwance, idan kinci abincin kya koma baccin, na rasa meke hanaki cin abinci jiya haka Kika fita bakici komai ba". Saida ta fad'a na tuna daren jiya banci komai ba, tashi nayi na nufi toilet nayi brush na fito na canza kayana sannan na fita parlour, breakfast nayi ina tunanin me zanyi tunda inada day off yau, hakanan naji I want to have some fun amma babu hali dan bansan ma me zanyi ba. Wayata na bud'e na hau Wattpad na fara duba litattafai, d'auko books nayi da dama na zauna na fara karantawa, Ina karantawa mama ta fito ta zauna. "Wani film ne wannan akeyi?" Ta tambaya tareda d'aukan remote, kallon tv d'in nayi naga 'mission impossible 2' da sauri na zauna nace "aikwa film d'innan yayi kyau". Kallo mukeyi muna dariya mama tace "Babu dai abinda yake damunki ko?" Girgiza Kai nayi domin banason wannan maganar da mama ta d'auko, indai za'ayi maganar Saleh sai naji yanayina ya canza wanda banason hakan, nayi tunanin Mama zata bar maganar amma sai naji tace "kinaso ki koma Bilkisu?" Jan numfashi nayi na zubawa tv ido, kasa bata amsa nayi domin a yanzu bansan me nakeso ba "Na fahimta idan kinaso ki koma Bilkisu, amma ya kamata kiyi tunani akan abinda ya faru sannan ki shiryawa duk wani abu da zai iya faruwa, bazan bo'ye miki ba amma banji dad'in rashin zuwansa ba, idan aka saki mace ko kai miji baka zo ba 'yan uwanka maza na zuwa su bada ha'kuri, amma anci sati uku babu wanda ya le'ko, shi bai kira yaji lafiyarki ba dukda har yanzu baki fita daga matarsa ba, nasan kina son mijinki amma....." Katse mama nayi nace "Mama ni a yanzu bansan abinda nakeso ba, ban saniba inason zama da Saleh? Banason zama dashi? Gaba d'aya a yanzu bansan me nakeso ba amma bana fata na koma wannan gidan ko dan wahalar da nasha a cikinsa". Inajin idon Mama a kaina amma na'ki juyawa, shiru tayi sannan tace "to idan zai maidake kenan wani gidan zai kama miki?" "Bana tunanin zai maidani bayan abinda ya faru, ko yanaso ya maidani Hajiya bazata ta'ba bari ba nima bana sa ran komawa, ina fata Allah yayimin za'bin da yafi alkhairi". "Alkhairi shine barin gidan Saleh har gaban abada" juyawa mukayi ni da mama muga mai maganar, Aunty na gani na cine bakina, wai ita bata gajiya da yawo ne? Gashi tazo ana maganarnan na shiga uku. Zama tayi bayan sun gaisa da mama tace "wannan sha-sha-shar ta zauna tana karanta miki irin son da takewa sale ko?" Dariya Mama tayi tace "a'a muna dai magana ne a kansa tunda ya saketa shiru shi baizo ba danginsa ma babu wanda yazo" Hard'e 'kafafu Aunty tayi tace "yo wa zaizo? Ai idan kikaga ana zuwa to dama an d'auki dangin mata da daraja itama matar an d'auketa da daraja, ko kuma dangin mijin ba matsiyata bane, amma wannan matsiyatan ina zasu iya zuwa? Ai wallahi na 'kagu ta gama iddar wannan talakan banzan na nuna mata inda rayuwa take, wannan Saleh yake ko wa d'in sai ya raina kansa domin bazai ganta a hanya ya ganeta ba ma, ko ya ganeta saidai yaja da baya domin tafi 'karfin ya kulata tsoro ma zaiji". "Auntyna ya batun motar tawa?" Na fad'a domin na kauda hankalinta daga kan maganar Saleh, take walwala ta bayyana a fuskarta ta ciro wayarta ta mi'komin tace "gasunan ki za'bi wadda kikeso ki fad'amin". Duba motocin nayi naga wata fara, tayi matu'kar had'uwa motar, nuna mata nayi ta kalla tace "yauwa 'yar gari, wannan kamar 3 ko 4 yacemin kud'inta". Zare Ido nayi nace "Aunty miliyan uku?" Hararata tayi tace "idan an cire miliyan uku an siya miki mota me akayi to? Macece miliyan uku? Shiyasa ma za'a 'kala miki sharrin sata kina nuna kamar kin taso a cikin tsiya, bilki dukiyarki dan an cire miliyan uku an siya miki mota wallahi ba'a fad'i ba, kefa Allah ya cetoki ne kawai daga wuta zuwa aljanna, wani dad'in ma sai kin gama idda". Zuba mata ido nayi nace "wai ni aunty wannan dukiyar tawa da kike fad'a nawa take ne? Meyasa ban fara cinta ba sai yanzu?" Yanayinta ne ya koma serious one tace "dukiyarki bazan fad'a miki adadinta ba saboda nima ban sani ba, bayan mahaifiyarki ta rasu Mama ta d'auko ki anso a bawa baba Kabiru gadonki, amma ya'ki kar'ba sai aka dan'ka duk dukiyar a hannun 'kanin mahaifiyarki, Allah ya bashi albarka da baiwa idan har kud'i kakeso ka juya ka samu riba Mai yawa da albarka to kabi ta hannunsa, Kar kice ya akai na sani domin a wajen mahaifiyarki yake zaune, tun iyayenki na raye yake juya kud'in mahaifinki har ya rasu, bayan Mama ta d'aukeki babu wani abu da suke bu'kata ba dawainiya dake dukiyar taci gaba da zama a hannun Khalid yana juyawa, lokacin da mukaji shiru babu labarinsa mun d'auka har ga Allah ya cinye dukiyar ne ashe Yana ta juyawa, a takaice dai yanzu kinada hannun jari babba a wani kamfanin mayafi dake Dubai, iya abinda na sani kenan,  kuma bamu san da hakan ba sai bayan kinyi aure, yanzu haka yana shirin zuwa ya ganki yanda yace mana sannan za'ayi lissafin kud'inki na yanzu, motar ma shine zai taho miki da ita". Gyad'a kai kawai nayi domin ban gama fahimtar abinda take so ta sanar dani ba, wani tunani ne yazomin nace "aunty to ya akeyi da zakka ko baya fitarwa?" "Idan yazo ki tambayeshi, next week zai iso Nigeria da motarki shine kawai abinda zan iya fad'a miki" Anan muka bar zancen dai amma duk hankalina ya tafi wani wurin daban, hira su mama suka fara akan iyayena na zuba kunne Ina sauraronsu, irin zaman da ummina tayi da Khalid, irin zaman auren da tayi abubuwa da dama dai, tunani na fara ina hango rayuwata tare dasu da yanzu ina tare dasu ya rayuwata zata kasance? "Waye yayi miki wannan d'inkin?" Kallon aunty nayi cikin sauri domin ta katsemin tunani ban kuma ji me tace sosai ba, maimaitawa tayi nace "wani tailor ne Saleh yake kaimin yana min d'inki". Tashi tayi ta shiga d'akina na bita, kayana ta fara cirowa daga wardrobe sai ta bud'e taja tsaki ta cillar a gefe, saida ta gama hargitsemin kaya sannan tace "Allah Bilkisu ke abin tausayi ce, dama baki tsaya kin waye ba sannan shima mijin naki ba'kauye, yanzu wannan sune kayan da zaki saka ki shiga cikin mutane ki fita kunya? Kinada kayan da baki d'inka ba?" Raina ya sosu da maganarta amma na share na zauna ina ninke kayana nace "inada kusan turmi 20 a gida da laces wad'anda ban d'inka ba". "To shikenan da sau'ki ai, ni sai nake ga kamar ma duk kayan lefe ne", kallonta nayi dukda auntyna ce ita kuma babba ce ta fara wuce 'kaida, numfashi naja nace "Aunty dukda Saleh talaka ne a wurinki amma ya wadata ni da sutura yanda ya kamata, a cikin kayan lefena baifi goma sha biyu na d'inka ba a shekara uku domin duk abinda za'ayi na taro sabbin d'inki yake min". Bansan meyasa nayi defending Saleh ba amma gaskiya na fad'a, dukda shine talaka a cikin 'yan uwansa amma suturar da nake sawa zatayi dai-dai da tasu har ma ta wuce. Aunty batace komai ba ta fita, bayan na gama gyara kayana nayi zamana a d'aki ina danna waya, le'kowa tayi tamin sallama sannan ta tafi. Haka naci gaba da tafiya da rayuwata, a kowacce rana aurena na sake fita a raina ina kuma sake jin haushin Saleh, na 'kagu na cire Saleh daga rayuwata na samu sau'ki, idan naga 'yammatan da basuyi aure ba sai naji Ina ma ina cikinsu, dukda banyi auren wuri ba nayi aure a 21 amma ji nake inama na sake jira, kamar yanda ake fad'a da kayi auren wuri babu kwanciyar hankali gara kayi zamanka a gidanku, gashi dai ni naje na fito Allah yayi 'kaddarar tawa sai na sake jera kafad'a da wad'anda na tafi na bari. Ranar da Khalid ya dawo tana d'aya daga cikin ranakun da suka sanyani farin ciki a rayuwata, ba wai jin adadin dukiyata ba a'a, sai domin yazomin da labarai na iyayena wanda babu wanda ya ta'ba bani su, dad'in dad'awa ya kawomin kyakkyawar mota ta kamfanin KIA, bayan ya dan'ka min motar sannan ya dan'kamin account da ya bud'e da sunana wanda riba ce kawai zata dinga shigomin nayi abinda naga dama dasu, zakka da sauran juya kud'ad'den duk yana hannunsa, saida idanuna suka kusa fitowa da ya lissafamin kud'in, da alamu dai Aunty ta kusa juyamin rayuwata na koma ajebota. Har naci wata biyu a gida ban sanya Saleh a idona ba, zuwa yanzu na gama samun nutsuwar da zan iya yanke hukunci, kud'ad'de shigomin sukeyi sosai ga salary na, abin mamaki aunty ta shareni ta manta da rayuwata hakan yayimin dad'i, domin ban shirya tashi daga Bilkisun da nake ba banaso aunty ta cusamin ra'ayin kud'i na zama wata ta daban, rayuwata a haka tana min dad'i banaso na shiga wata rayuwar. *********** *SALEH* Aikin da ya kamata ya gama a wata d'aya ko sati uku a sati biyu da kwanaki Saleh ya gama ya juyo, duk yanda yayi Jabir ya had'ashi da Bilkisu ya'ki, yace masa ta koma wajen kakarta a had'eja dukda haka bai 'kyaleshi ba yace ya bashi address d'inta. 'kin bashi address d'in da Saleh yayi ya sanyashi fara gadin gidansu Bilkisu, amma cikin rashin sa'a baya ta'ba ganin shigarta ko fitarta, gashi ayyukansu sun fara yawa. Saida aka ci wata biyu bai samu ganawa da Bilkisu ba, a watanni biyunnan har an fara kwashe kayan Bilkisu hakan ya d'aga masa hankali sosai, yanke shawarar neman mafita ta 'karshe yayi wato ya samu mahaifin Bilkisu. Kwalliya yayi ta ganin surukai sannan ya d'auki hanyar fita, kafin ya kai 'kofa ya had'u da Hajiya ta fito, washe baki tayi tace "a'a Saleh dan Hajiya gidansu hadiyya zaka je ne a wannan daren?" Girgiza kai yayi tareda gyara tsayuwar sa babu amfanin yiwa Hajiya 'karya saboda haka ya sanar mata da gaskiyar al'amari yace "Hajiya zanje na dawo da Bilkisu ne, a yanzu na Gane kuskurena da na saketa kuma nayi nadama, banida matar da ta wuce Bilkisu kuma bana fatan rabuwa da Bilkisu, kiyi ha'kuri ki zauna da ita lafiya Bilkisu batada matsala". "Waye me matsalar kenan?" Ta fad'a tana kallansa a wula'kance, "Hajiya bance ga Mai matsala ba amma nasan cewa bakyason Bilkisu, amma ina sonta idan kina Sona zakiso abinda nakeso, Hajiya Bilkisu itace farin cikina bazan iya rayuwa babu ita ba". "Zaka mutu kuwa domin indai cikin gidannan zaka kawo Bilkisu bazan zauna da ita ba". "Sai na kama gida na sakata, nidai ki amincemin na zauna da ita". Numfashi taja tace "hadiyyan fa?" "Hajiya banason auren wata bayan bilkisu kiyi ha'kuri zan dawo da ita". Hanya ya d'auka zai fita tace "karka fita Saleh". Juyowa yayi yace "hajiya bazan miki biyayya akan wannan ba, bayan duk abubuwan da Kika yiwa Bilkisu neman yafiyarta kad'ai ya kamata kiyi". Numfarsa tayi a fusace tace "bani mu'kullin gidanka" kallonta yayi cikin mamaki, maimaitawa tayi cikin d'aga murya babu musu ya ciro wallet d'insa, kafin ya ciro key d'in ta wafce wallet d'in gaba d'aya sannan ta kar'bi wayarsa tace "kaje gidansu Bilkisu, idan kaje ka zauna acan, indai ka Sanya 'kafarka ka fita daga gidannan saboda wata Bilkisu to ka fita kenan". Tana gama fad'in haka ta juya ta nufi cikin gida, tsayawa yayi ya bita da kallo ya rasa yanda zaiyi da ransa, yana tsaye ta dawo ta shige d'akinta ta rufe, ganin tsayuwar batada amfani ya sanyashi ya juya ya nufi gidansa saidai ya sameshi a rufe, a fusace ya daki 'kofar ya jingina kansa numfashi yake ja yana saukewa har ya d'an sami nutsuwa tukun ya nufi part d'in Hajiya. A rufe ya samu 'kofar saida yayita bugu sannan ta bud'e "shigo" ta fad'a tareda zama Kan kujera, zama yayi a 'kasa tace masa "me kakeso" "Mu'kulli nazo kar'ba". Sunkuyowa tayi tace "bazan baka duk abubuwan dake hannuna ba Sai akan sharudda, zaka auri Hadiyya cikin wata biyu sannan babu kai babu Bilkisu" Ya gaji da yi mata musu yace "to" Kashe murya tayi tace "Saleh na gaji da  musu dakai kamar ba ni na haifeka ba". Sunkuyar da kansa yayi yace "hajiya nima banaso na dinga miki musu". Tashi tsaye tayi tace "zan barka ka dawo da Bilkisu" cikin sauri ya d'aga kanshi ya kalleta, murmushi tayi tace "amma ka yimin al'kawari zaka amince da duk abinda na nema daga gareka ko menene". Cikin sauri yace "zanyi Hajiya ko menene". "Zakayi duk abinda nakeso?" Shiru yayi ya kalleta, Anya ba kuskure bane amincewa da sharad'inta? Still dai yace "eh", ajiye masa abubuwansa tayi tace "gobe da safe kazo ka sameni". 36 Kwana yayi yana tunanin abinda hajiya zata nema daga gareshi, bazai wuce auren hadiyya ba amma indai akan ya dawo da Bilkisu ne zai amince da ko mene, yasan Bilkisu ma zata amince da hakan. 9:00am a part d'in Hajiya tayi masa saida yayi breakfast sannan Hajiya tace masa "Zan cika maka al'kawarinka da na d'auka na amince ka dawo da Bilkisu" Ajiyar zuciya ya sauke tare da godiya, girgiza kai tayi tace "sharad'in shine...bazaka dawo da ita ba sai ka auri Hadiyya ta sami ciki tukuna ka dawo da ita". Sunkuyar da kansa yayi yana auna maganar Hajiya, idan har zai dawo da Bilkisu sai bayan watanni kusan biyar kenan zuwa bakwai, d'agowa yayi yace "Hajiya kiyi ha'kuri na amince zan auri Hadiyya amma ki barni na dawo da Bilkisu, lokaci zai 'kuremin". "Bazai yiwu ba kayi abinda nace kawai, idan bazaka iya ba sai ka ha'kura da matarka". Sauke murya yayi yace "Hajiya har yanzu da aurena akan Bilkisu kiyi ha'kuri na dawo da ita sai na auri Hadiyya daga baya". Dariya tayi tace "Haba Saleh kar ka yimin wayo mana, nasan idan matarka ta dawo bazaka ta'ba auren wata matar ba, sai kayi aure zaka dawo da ita". Tashi tayi ta shige d'akinta, fitowa tayi tace "ban kuma lamince maka kaje gidansu ba indai ba kayanta zaka ce su zo d'iba ba". Zama yayi ya zuba tagumi a palon hajiya, wace masifa ce haka ta sanyashi sakin Bilkisu gashi tun kafin aje ko ina ya fara nadama, Banda sharrin zuciya ta yaya zai saki Bilkisu? Bilkisu tayi ha'kuri fiye da wanda shi zai iya, ta zauna dashi cikin biyayya ba tareda matsala ba ko rigima sukayi sai tasan yanda ta shawo kansa bata bari ya kwanta da 'bacin rai ko da kuwa laifinsa ne, meyasa bai kwatanta hakan ba a lokacin da zuciyarsa ke kusa? Ko dan darajar iyayenta bai dace ya saketa ba da wani ido zai kalli iyayenta bayan halaccin da suka masa? Fita yayi duk da maganar Hajiya amma ya toshe kunnuwansa ya d'auki hanyar gidansu, a hanya ya tsaya yana tunanin dame zai tunkareta take jikinsa yayi sanyi ya juya ya nufi aiki. ********** *BILKISU* "Mama yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo?" Na fad'a tareda rungume pillow d'in kujera, 'kauye mama zata je bikin wata 'yar 'kanwar mijin waye waye ni bana gane wannan lissafin nata, gashi aiki bazai barni ba ko da ace banida aiki bana son zuwa 'kauye kwata-kwata musamman irin wannan. "Zanyi kwana biyar". Kwanciya nayi a kafad'arta nace "ya zakiyi da babyn taki". Dariya tayi tace "tunda bazaki 'kauye ba sai kije gidan Aunty, nayi mata magana". "Nifa Mama ba wai 'kauyen ne matsala ba, kikace fa 'kauye cikin 'kauye za'aje a lokacin bikin kuma ko band'aki na kirki babu, haka kawai ka tu'be kana wanka wani 'kato yana le'koka". Dariya Mama tayi tace "shikenan naji, ki had'a kayanki jibi zan tafi, gobe saiki tafi da yamma saboda fitar sassafe zanyi, idan akwai wani abu da kike bu'kata sai ki fad'amin". Master card d'ina na nuna mata nace "karki damu mama ko shekara zakiyi bana bu'katar komai kuma Aunty ai batada matsala Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya har na fara missing d'inki" na fad'a tareda hugging d'inta ta gefe, zare hannuna tayi tace "banason shirme tashi ki fara had'a kayanki". D'aki na nufa na d'auko akwatina na fara jera kaya a ciki, sati biyu zuwa uku suka rage na gama idda shikenan na fita daga matar Saleh...bansan Yaya nakeji game da hakan ba, dukda nayi blocking numbersa amma raina yana 'baci saboda rashin zuwansa ko zuwan waninsa, duk mutanen arzi'ki basa haka. 'karan wayata naji na d'auko naga aunty, nasan yanzu zata fara jero min kayan da ya kamata na d'auko, amsawa nayi tana sallama tace "Bilkisu yaushe zaki taho?". "Gobe insha Allah da dare" "Alhamdulillah, 'ya'yan sister na zasu zo suma gobe hutu daga Abuja dan Allah kizo da wuri". "Allah ya kaimu amma gobe morning gareni idan na taso sai nazo". Tun safe na yiwa mama sallama na saka kayana a mota na nufi aiki, wa'ka nakeji 'kasa-'kasa a motar ina buga steering hakanan duniyar naji tayimin dad'i ga motar na kasa sabawa da ita kullum na hau sai naji ta sakemin sabinta. Babu wani aiki sosai azahar na gama abuna na nufi gidan Aunty, hayaniya nake jiyowa na shiga fa akwatina a hannu. "Oyoyo" naji yarinya tayi hugging 'kafafuna, murmushi nayi tareda d'aukanta sai yanzu hankalinsu ya yo kaina, murmushi nayi nace "sannunku da zuwa" na kama kujera na zauna suna kan carpet suna zaune, kallo d'aya zaka musu kasan gata da jin dad'i ya ratsa su. 'yammata ne uku dukkansu sanye da atamfa amma d'inkin dake jikinsu ya matu'kar had'uwa off shoulder ne, jikinsu so smooth da ka kallesu kasan ba irin mai namu na ya ku bayi suke shafawa ba, mayafan jikinsu da jakunkunan gefensu ma abin kallo ne, sai yanzu na tuna ban kalli takalmansu ba. Cikin murmushi d'aya daga cikinsu ta kalleni tace "Aunty Bilki ko? Maama tana ta kod'a mana ke". Huda, ita kad'ai ta fad'omin rai da tace maama, kawar da wannan tunanin nayi nace "Allah yasa dai abubuwa masu kyau ta fad'a a kaina". "Sosai, anyway ni sunana raudah nice babbarsu sai 'kannena twins amal da nawal, we are technically...your cousins" ta 'kare maganar tana dariya. "Sannunku da zuwa kun zo lafiya?" "Lafiya lau" ta fad'a tareda ta'bo amal da nawal da suketa musu akan wani abu a waya, kallona sukayi suka saki murmushi tareda cewa "sannu anty Bilki". "Ina Aunty?" Na tambayesu, kitchen suka nunamin suka koma bickering d'insu, kaman abu sukeso su saya sun kasa tsaida same colour, sun bani sha'awa sosai inama Allah zai bani haihuwar twins da nafi kowa murna. Shiga kitchen d'in nayi da sallama aunty tana d'and'ana miya "sannu da aiki Aunty akwai wani abu ne?" "Yauwa Alhamdulillah Allah ya kawoki, zo'bo ne gashinan na tace ki had'a abubuwan da ya kamata a ciki". Amsa mata nayi da na zauna na fara had'a zo'bo nace "Aunty su raudah cousins d'ina ne amma ban sansu ba". "Amfanin zuwanki kenan ai, da mahaifinki da mahaifiyarsu da ni uwarmu d'aya ubanmu d'aya, gasunan rainon cornflakes ne zuwansu na biyu kenan garinnan  sai yawon duniya, zuwansu na farko ma suna yara yanzun ma banda Aliyu ya takura bazasu zo ba, ai kun gaisa dashi ko?" "A'a su hud'u dai na gani, raudah, twins da wata yarinya". Waya ta d'auko tace "ina kuma yayi shi da baisan kowa ba?" Kiran wayarsa tayi sukayi magana tacemin "yana d'akinsa ashe yana can boys quarters, wannan yaran bazasu barshi ya huta ba ai musamman twins". Shiru mukayi har muka 'karasa had'a abincin na fara fita dasu, kamar kaji suka nufi kan tray d'in da na ajiye suka fara bud'ewa, hannu suka saka su ukun suka dangwali miya tareda lasa, wani lumshe ido sukayi suka kalli juna nidai ina tsaye ina kallon ikon Allah, alkubus da sinasir Aunty tayi musu babu wani jiran plate suka fara dangwala a cikin miyar ga miyar da zafi har wani 'karamin tsalle sukeyi. "Me kukeyi haka? Haka ake cin abinci a garinku babu manners kawai kun duma hannu a flask". Juyawa nayi domin kallon me maganar nayi arba da wani had'add'en gaye, fad'in had'uwarsa is an understatement, yana kama da 'yan uwansa sosai saidai yanayinsa yafi fitowa a buzu-bafillatani, murmushi yayi yayinda dimples d'insa suka bayyana ga gashin kansa ya kwanta anyi masa aski sama-sama, sajensa yabi fuskarsa gwanin sha'awa.....cikin sauri na sunkuyar da kaina, me nakeyi haka bayan da ragowar aure a kaina? Astagfirullah amma gayennan duk macen da ta kalleshi dole ta sake kallonsa, kyawunsa ba 'boyayye bane. Matsowa yayi dab dani saida bugun zuciyata ya sauya amma na dake, mi'komin hannu yayi yace "Bilkisu ko? Your cousins....AALI". Kasancewarsa cousin d'ina nayi shaking hannunsa, wow fatar hannunsa soo smooth ga gashin hannunsa ya kwanta.... 'kifta idona nayi tareda d'aga idona muka had'a ido, wani killer smile ya sakarmin yace "it's okay you can watch and drool, na saba da wannan kallon daga wajen ladies" ya 'kare maganar tareda winking, oh my God this guy will be my death, janye hannuna nayi da yake ri'ke da nasa nace "sannu da zuwa". Gyaran murya naji daga bayana na juya, ashe duk sun bar cin abincin suna kallona, tafawa twins sukayi raudah ta juya idanunta tace "stop flirting in front of us guys, kar ku hanamu cin abinci". Kunya naji na nufi kitchen da sauri, saidai ba 'karamin 'ko'kari nayi ba na 'kin waigawa na kalli Aali, d'auko tray d'in plates da drinks nayi na fito duk sunyi circle gaban flask suna cin abincinsu hankali kwance, ina fitowa naga duk sun kalleni alamun maganata sukeyi, rad'a twins sukayi raudah ta zare musu ido, babyn cikinsu naga tanata fama ko ta kanta basa bi tana 'ko'karin cin abinci, plate na d'auka na d'auketa a hannuna na koma kitchen na zubo nawa abincin na fito na zauna na fara bata ina ci, "ya sunanki" ya tambayeta Ina goge mata baki, duk loma sai an goge mata baki da tussue na rasa wannan fele'ke, "jannah" ta fad'a tareda bud'e bakinta, ban sake magana ba saida na gama bata abincin, lokacin sun gama cin nasu abincin har sunyi kyan kai sun kai kwanukan kitchen sun dawo. Wanke ma Jannah hannu nayi na tambayi Aunty inda zan kai akwatina, itama tana palour suna hira dake sun 'koshi duk sun kama wuri sun kwanta "Kayan su raudah na wannan d'akin ban saniba ko zaki saka a wancan...." Kallona raudah tayi tace "a'a aunty Bilki kai kayanki d'akinmu we are sharing the same room saidai idan kece bakyaso ki zauna damu". Shiga nayi da kayana na ajiye akwatina a gefen nasu, cire kayana nayi na shiga wanka, ina wanka aka fara kiran sallar la'asar, fitowa nayi na samesu kan gado suna kwance da alamu sallah suka shigo. Juyowa twins d'in sukayi suna kallona d'aya daga cikinsu tace "aunty Bilki mama tace mana ke nurse ce ko?" Gyad'a kai nayi tareda murmushi "kin ta'ba ganin mutane sun mutu ko?" Nan ma na gyad'a kai sannan nace "mata biyu sun mutu gaban idona bayan haihuwa, biyar kuma saida na fita na dawo na samesu sun rasu, sannan dai akwai wasu a bangaren emergency haka....kawai dai mutuwar zata 'kara maka imani". Girgiza kai mai tambayar tayi tace "na fasa karantar nursing wallahi, gara na zama dentist ai a ha'kori ba'a mutuwa". D'ayar twins d'in ce ta harareta tace "ke fa nawal kin fiye tsoro, nidai bazan iya dentist ba wallahi kayita fama da mouth odour na mutane". Kallonsu nakeyi ina tunanin ta yanda zan ganesu amma babu alama, twins ne masu matu'kar kama hatta kwalliyarsu babu banbanci". Kwanciya wadda nake tunanin amal ce tayi ta kalli ceiling tace "I am bored, aunty Bilki me kukeyi na fun anan?" Shiru nayi domin ni bansan wani sha'katawa ba banda naje aiki na koma na zubawa tv ido idan dare ya tsala nayi bacci, a da dai jabir na d'aukana muje muyi ciye-ciye amma banda yanzu saboda haka nace mata "ban saniba, ba wani fita nake ba". Tashi tayi ta 'kwalawa Aali kira tace "sweet Aali" har cikin raina naji sunan yayi matu'kar hawa, cije le'bena nayi tareda runtse ido, ba dai har na fara missing Namiji ba.....kawar da wannan tunanin nayi na canza kayana zuwa marasa nauyi nayi sallah, ina jiyo magiyarsu daga palo bayan na idar naji ance "to naji ku kiramin cousin". Da gudu amal ko nawal ta shigo tace "Aunty B ya Aali na kiranki". Samun sa nayi sun cukwuikuyeshi suna dur'kushe gabansa harda su jannah, dariya abin ya bani yace "taimaka ki fad'amin inda zasu je su d'anyi loosing up ko nayi numfashi da kyau" stupid me is just staring at his mouth, yanda yake motsa bakinsa kad'ai is a sight, bansan me yasa nakejin haka game dashi ba, but it's not my fault, I wasn't laid like in....2 and a half month. Sosa kaina nayi nace "ban san me suke so ba ai, saidai ko zuwa dare muje 'bangaren nassarawa maybe suga inda ya birgesu". Hankalinsu dawowa yayi gareni raudah tace "anan ana shawarma me azabar dad'i irin tamu?" Zama nayi nace "eh to shawarmar 10-4-10 tanada dad'i sosai amma ban sani ba ko zata kai taku". Tashi raudah tayi tace "zamuyi sallah mu huta, 8:30 kazo ka kaimu duk inda tace please kaji big bro?" Rufe idonsa yayi tareda jingina kansa a kan kujera yace "oh Lord take me" dariya mukayi gaba d'aya saboda yanayin yanda yayi maganar, hannunsa ya d'aga yace "okay naji 8:30 amma gobe babu inda zamuje hutawa zamuyi". D'aki suka shige dukkansu na zauna tareda binsu da kallo, tasowa Aali yayi ya dawo kujerar da nake kawai naji hannunsa a kafad'ata, kallonsa nayi naga ko a jikinsa shi tv ma yake kallo, saida na gama 'kare masa kallo ta side view sannan ya juyo ya kalleni yace "Aunty tacemin ke nurse ce". "Um, na fad'a tareda matsawa daga gareshi domin har d'umin jikinsa Ina ji ta gefen jikina, d'auke hannunsa yayi daga kafad'ata yace "sorry, na saba haka da sisters d'ina ne kuma ganin kema you're my cousin sister ai ba laifi bane ko?" Bance masa komai ba naga dai kaman yaji haushi saboda haka na sauya yanayin nace "haka suke maka kowane lokaci?" Dafe kansa yayi tare da weening kamar yaro yace "ki bari kawai fiye da haka ma sai su yimin, duk d'an asusun nawa idan mukayi tafiya sai sun cinyemin shi, dan Allah idan mun fita bayan wannan wurin karki nuna musu wani kinji?" Zuba masa ido nayi yanda yayi kalan tausayi kaman "karamin yaro harda turo baki ya had'e hannayensa, wani involuntary murmushi na saki nace "okay". "Promise?" Ya fad'a tareda washe  fararen ha'koransa, gyad'a masa kai nayi ya mi'komin 'karamin yatsan sa, kallon yatsan nayi na kalleshi ya d'aga kafad'a tareda cewa "zama cikin mata kuma yara duk sun koyamin dabi'unsu". Maida hannun yayi ya kalli tv yace "bani labari a kanki mana ko irin minor abubuwa ne saboda mu kashe time, nima zan baki nawa". Lumshe idanuna nayi, wai shin ina wannan al'amari yake nufa ne? Me ke Shirin faruwa 37 Ina zaune na zubawa akwatina ido na rasa kayan da zan sanya domin ban zo da shirin fita ba kayana casual ne wad'anda zan fita aiki dasu, idan naje na cure na saka uniform idan na tashi na maidasu jikina na taho babu wani kayan kwalliya. Kallonsu nayi sun gama shiryawa sai naji kamar nace na fasa zuwa, sunyi matu'kar kyau cikin lace sun yafa mayafansu a kafad'a d'aya suna d'aura d'ankwali, kallona Raudah tayi tace "anty Bilki Yaya Aali bayason jira fa gara kiyi ki shirya da wuri, naji maama na cewa bataso mu wuce 9:30 a waje". Zuba tagumi nayi nace "bansan me zan saka ba", zama tayi ta fara zaro kayana tana kallo tana ajiyewa, wata doguwar rigata ta ciro milk colour ta bud'eta tace "wannan tayi kyau sosai, I am telling you yayanmu bazai iya d'auke idonsa daga kanki ba". Ban kulata ba na kar'bi kayan na zura kan vest d'in jikina, kafin na d'au mayafi taja hannuna muka nufi mirror d'in d'akin ta zaunar dani tace "twins ku fito min da ita". Kit d'in make-up naga sun d'auko cikin sauri nace "no!", Dariya sukayi gaba d'aya Raudah tace "dan Allah Bilki ki daure kiyi kwalliya ko yaya ne ki dan fito Kinga dare ne, kuma there is no way zamu fita dake a haka mu kallemu, ai it's not fair". Kallon hannuna nayi na d'ago nace "Aunty Raudah ba wai bana son make-up bane, kawai it's inappropriate nayi at this time". D'aga girarta tayi tace "saboda me? Idan kina tsoron kar wasu maza suyo kanmu ne karki damu munada ya Aalee, bayan haka ba yawo zamuyi ba, muna cin shawarmannan muka d'an zagaya dawowa zamuyi, ba lallai ma 10 tayi mana a waje ba". "Ba tsoron wani abu nake ba, nidai mu fita kawai ba sai nayi wani make-up ba please". "No" ta fad'a tareda hard'e hannunta a 'kirji". Murmushi nayi nace "Aunty Raudah da aure a kaina bazan fita da kwalliya haka ba zunubi ne zai hau kaina". Shiru tayi ta zubamin ido ina ganin tambayoyi kala kala a fuskarta amma ta kore tace "okay, amma ai ko powder da d'an light janbaki kya saka ko kuwa hakanan zaki fita?" Komawa nayi na zauna na d'auki powder, kar'ba d'aya daga cikin twins tayi, ko yaushe zan fara ganesu? Shafamin tayi ta d'auko janbaki red ta shafamin sannan tayi contouring yanda kalarsa zata ragu, d'ayar twin d'in kuma ta kama gashina tana tajewa, sun juyar da fuskata daga madubin saboda haka bansan me suke aikatawa ba, mayafin rigar tawa suka d'auko naga sun had'a Ido, yarannan sun iya magana ta ido sosai, ajiye mayafin mai tajemin gashi tayi ta d'auko wani silver kalar kwalliyar rigar ta fara min rolling d'insa saida suka gama sannan suka ce na kalli kaina a mudubi, ni kaina nasan nayi kyau ga mayafin ya sauka yanda zai rufe jikina dukda rigar bata bayyana jikina ba, duk da haka ji nake kamar na karya dokar shari'a, kafin na gama tunani Raudah tace "selfie" kafin na ankara ta d'aukemu, ina kallon kaina a mirror twins kuma na kallona ta gefe, pic d'in yayi kyau amma dukda haka saida twins sukayi kanta ta d'aukesu basu shirya ba. 8:20 mun gama komai mun fita, suna ri'ke da jakunkuna ina ri'ke da purse, gaba twins sukayi zasu kira Aliyu suka barni da Raudah a palour, d'inkin jikinta na kalla nace "d'inkin ku yayi min kyau". "Tailor d'in namu kuwa anan yake idan kinaso sai na had'a ki dashi". Ta fad'a tareda d'aukan jannat ta d'aurata a cinyarta, sai yanzu na lura suna kama sosai da jannat twins kuma sunfi kama da Aliyu sannan sha'kuwar jannat da Raudah tafi yawa, rufe idona nayi nace "Allah sarki Huda".  "Wacece Huda? Ur baby?" Kallonta nayi domin bansan taji maganar da nayi ba nace "sort of". 'daga gira tayi tana jira naci gaba twins suka shigo, kallonmu Aliyu yayi yace " 'yammata na kunyi kyau fa, yau zansha fama da mazaje kenan don hanasu kallonku" ya fad'a tareda d'aukan jannat ya fara kissing fuskarta tana dariya, kallona yayi yace "Aunty Bilki zaki ara mana motarki da ita zamu fita". Amsa masa nayi da okay na koma na d'auko key na mi'ka masa, fitowa Aunty tayi ta kallemu tace "haba, ko kefa Bilki kema kya fara ganin duniya da haske ki yaye duhun wannan ba'kin......" Girgiza Kai nayi tare da katseta nace "Aunty dan Allah bar maganarnan sai mun dawo". "Allah ya kiyaye, kuma goma ta muku a cikin gidannan ko kuma gobe na hanaku fita". Cikin sauri muka fice Raudah na ganin mota ta ta dafe 'kirji tace "wow!" Murmushi nayi jin kaina ya 'kara girma tace "ya Aalee irin wannan nakeso". Ba tareda ya kalleta ba yace "bazan sake baki mota ba Raudah ki ma dena tambaya". Buga 'kafarta tayi tace "ya Aalee na fad'a maka bazan sake ba fa meyasa bazaka yarda dani ba, accident ne kuma tunda Allah ya rubuta zai faru ko a hannunka take sai tayi hakan". Juyowa yayi naga yanayinsa ya sauya amma dukda haka yayi maganar cikin nutsuwa yace "Raudah, bazan sake baki mota ba for your own safety, last time da kikai driving you almost kill your sisters idan ma akwai accident da gangancin ki, motoci uku Kika kashe a 2years". Hard'e hannunta tayi a 'kirji tace "sai me? Tunda Allah yasa wajen saida motoci ne da kai mene na damuwa ko nawa na kashe? And for the last time wannan motar ita ta bugemu ba ni na bigeta ba". "I am not giving you another car until you learn to stop driving like a drunk teenager!!! Idan kina tunanin wajen mota ne dani zan dinga cirewa ina baki kin yaudari kanki tunda ba daga sama suke zubowa ba kud'i nake sakawa nake siya, ki shige mu tafi". Juyawa tayi a fusace tace "na fasa zuwa". Cirko-cirko muka tsaya muka zuba musu ido, da sauri yabi bayanta ya ri'ko hannunta ta juyo idonta cike da hawaye, numfashi ya sauke yace "I am not sorry Raudah, saboda kin san laifinki ne kuma mum and dad su suka ce kar na sake baki mota sai kin 'kara hankali". Kallona tayi tace "why would you embarrass me in front of her? Tsawa fa kayimin a gabanta". Kallon juna twins sukayi amal tace "ya zamuyi dasu ne? Wannan rarrashin sai su kai 9 sunayi wallahi, inaga ma an fasa fitarnan". Nidai ina jikin mota ji nake kamar na koma, wannan 'bacin ran saboda sunyi fad'a a gabana ne? Ni fad'an nasu ma ya tasar min abinda na dad'e ina dannewa a raina, ya Aalee da Raudah wa da 'kanwa ne amma yanda yake rarrashinta gwanin sha'awa, meyasa Saleh bai yimin haka ba? Sai ma 'karewa da yayi da fad'amin maganganu da sakin wula'kanci, dariyar Raudah naji na kallesu sun taho tare tana dukan hannunsa ta gefe cikin wasa, runtse ido nayi ina jin wani iri a raina, da ace inada choice komawa gida zanyi nabi gado nasha kukana, once upon a Time haka muke ni da Saleh dukda takurar da nake ciki, amma lokaci d'aya komai yayi blowing gashi cikin kwanaki kad'an zan dena kiransa da mijina. Dukda ina jin haushin Saleh sosai amma ina matu'kar missing d'insa, yanda yake hugging d'ina idan ya dawo gida ina jiransa, yanda yake hugging d'ina ta baya a kitchen da safe, yanda d'umin jikinsa yake calming d'ina a duk lokacin da na kasa bacci, yanda nake d'aukan lokaci ina sauraran bugun zuciyarsa a lokacin da nake bu'katar nutsuwa, how his hands feel on my body, ta yanda yake sakani na manta duk wani bacin rai da gajiya by his single touch..... "Earth to Bilkisu!!!  Tunanin me kikeyi haka?" Cikin sauri na kalli Raudah da tayi tafi saboda ta dawo dani daga tunanin da na tafi, tunanin da na jima da turashi can 'kasan zuciyata domin banason tunawa da wad'annan abubuwan, murmushi na 'ka'kalo nace "babu komai". Motata muka bud'e ni da twins da jannat muka shiga baya ya Aalee da Raudah a gaba, twins na hirarsu su Raudah ma na hirarsu ni kad'ai ce babu abokin hira, kan jannat na cinyata 'kafafunta na cinyar amal, na ganesu ne saboda mayafansu yau ba kala d'aya bane. Zubawa window Ido nayi ina kallon fitilun titi, ba sai na nunawa Aalee hanya ba domin ya bud'e GPS yayi searching wurin tafiya kawai muke muna bin hanya. "Aunty Bilki ba dai bacci kikeji ba ko?" Aalee ya fad'a tareda juyowa ya kalleni, murmushi nayi nace "a'a kaina ne ya d'an fara ciwo". Cike da kulawa yace "oh, I am sorry mun d'auko ki bayan kinsha aiki". "Bakomai ya Aalee" na fad'a tareda kallonsa nayi murmushi, bansan meyasa yanzu yake tunamin da Saleh ba, domin akwai banbanci sosai tsakanin su, Saleh mutum ne mai saurin fushi kuma sai nayi da gaske yake saukowa, amma abinda na lura d'azu da Aalee yanada sau'kin kai ko da kuwa a kan 'kannensa ne, sannan yanada fahimta domin tunda muka zauna yanayin hirarsa da Raudah akan wani sukeyi amma yanda yake Bata reply cikin tunani da basira ya matu'kar birgeni, meyasa Saleh bai zama haka ba, da ace ya yarda dani yanda na yarda dashi ya kuma fahimceni yanda na fahimceshi bazai ta'ba sakina ba ko da kuwa laifin da nayi yayi muni, yardar da na yiwa Saleh gani nake ko da namiji ya kamani da idonsa zai ce "na yarda dake Boo-boo na amma kiyimin bayani ya akai hakan ta faru, nasan ba laifinki bane" sai gashi abinda bai taka kara ya karya ba ya sanya ya sakeni, _boo-boo_. Abinda ke ta min yawo a kaina kenan, tunawa nayi da lokacin da na fara kiransa boo-boo, yana kirana babyna lokacin ban ta'ba ambatar sunansa ba saidai nace "umm kaga" Bazan manta ba ina amarya ya d'auki wayata yaga nayi saving numbersa da boo-boo ni kuma kunya ta hanani fara fad'a masa, pinning d'ina yayi kan kujera ga tsoro a raina lokacin ga alamun munyi ba'ki yace bazai d'aga ni ba sai na fad'i sunan da bakina..... Memories ke zuwarmin na zamana da Saleh, hawaye naji ya zubomin na goge da sauri, idon Raudah na gani a kaina tana kallona ta gefen kujerarta, a hankali tace "are you okay?" Gyad'a mata Kai nayi na koma kallon window, ko wace rayuwa Saleh keyi yanzu? Yana nan yana rayuwarsa free 'barauniyar matarsa ta tafi ya huta, hannuna na Sanya a 'kirjina jin ya d'aura, duk lokacin da kalmar 'barauniya taso Raina sai naji 'kirjina yayi tightening, ba abinda nakeso a yanzu kamar na koma gida na 'kudundune a gado nasha kukana na zazzage Saleh da danginsa a raina sannan nayi bacci. "Yauwa mun iso, Bilki nan ne ko?" Kallon wurin nayi nace "eh nan ne, fita mukayi muka nufi cikin wurin muka kama table, da mutane sosai yawancinsu maza ne wasu kuma da 'yammatansu, lemo mai sanyi aka fara kawo mana da ruwa a take na shanye ruwan tas, idonsu na gani a kaina sai naji duk nayi wani iri, ba dai kunya na basu ba saboda d'aga ruwan da nayi ba ko? Sunkuyar da kaina nayi na kasa kallonsu har aka kaso shawarma da ships d'in da twins suka ce suna so, fara cin abincinmu mukayi ko nace sukayi domin ni kusan wasa kawai nake da fork da spoon d'ina, wata 'katuwar shawarma sukeyi a wurin da bazaka iya kaita baki ba saidai ka dinga yanka da wu'ka kana ci da fork. Kallona sukeyi dukkansu cikin damuwa, bayan wani lokaci nawal ta ajiye fork d'inta tace "Aunty Bilki ko cin abinci ne bakyaso kiyi damu? Muma fa mutane ne bazamuyi judging d'inki akan yanda kike cin abinci ba idan wannan ne damuwarki, idan zakiga yanda muke cin abinci kaman kaji a gida bazaki 'ki cin abinci damu ba". Wani kallo dukkansu suka wurga mata Raudah tace "ina ruwanki?, Sorry Bilki". Murmushi nayi nace "bakomai Raudah, ba wai banason cin abinci daku bane kawai banajin dad'i sannan wannan ba shine first time da na fara cin abinci a waje ba kuma wajennan na zo almost three times". "Ya kuka ji shawarman tayi muku?" Aalee ya fad'a tareda kauwa bakinsa, hakan ya d'auke hankalinsu daga kaina suka hau hirar abubuwan da suka ci a waje, irin abincin da suka ci a 'kasashe daban-daban da yanda taste d'in yayi a bakinsu, hira sukeyi suna dariyarsu abinsu, a haka dai na samu naci abinda zan iya ci na bar ragowar nasan ma shara zaibi. Ko da muka shiga mota wayarsa ya jona da Bluetooth ya fara kunna mana wa'koki, bin wa'kokin sukeyi suna yi suna tsallensu a mota harda shi Aalee, har wani rawa yakeyi da motar idan mun tsaya a haka har mukaje gida. Ina zuwa d'aki na shige na nufi toilet na wanke kwalliyata na canza kayana sannan na fito, ina fitowa Aunty ta yi min wani kallo tace "Ina son magana dake" tashi sukayi duk suka bar wurin na zauna ina jiran fad'an Aunty. "Me yake damunki Bilkisu?" Ta fad'a cike da kulawa, wasa nake da yatsuna nace "bakomai aunty". Kallona tayi tace "kinmin al'kawari kin dena barin tunanin Saleh yana shiga raguwarki, meyasa yau kika sanya 'yan uwanki a damuwa suna shigowa suka fara fad'amin akwai abinda ke damunki". Sunkuyar da kaina nayi nace "Aunty kiyi ha'kuri ni kaina bansan ya akai hakan ta faru ba, yanda na miki al'kawari na cireshi a rayuwata kuma insha Allah zanci gaba da nisantashi da rayuwata, bansan me yasa...." Kasa 'karasawa nayi tace "Na fahimta Bilkisu Allah ya yaye miki son wannan mutumin domin indai kina sonshi ko kasheki zaiyi ki dawo komawa aurensa zakiyi". Girgiza kai nayi nace "Aunty bana fatan komawa gidan Saleh a yanzu" cije baki nayi jin marata ta d'aure, a dai-dai lokacin da naji d'umi a 'kasan 'kafata, murmushi nayi nace "a kwanakinnan iddata zata 'kare Aunty". Tashi nayi na gyara jikina sannan na fito na nemi ruwan d'umi nasha na kwanta, flo app d'ina na duba a 'ka'ida period d'ina saura kwana 5 ma amma Allah yayimin gata da alamu dai aurena da Saleh ba mai komawa bane. Du'kun'kunewa nayi a gadon da zamuyi sharing ni da Raudah twins kuma a katifa a 'kasa, dafani Raudah tayi bayan ta saka pyjamas d'inta, ji nayi kaman ta jona min shocking na ture hannunta, cikin damuwa tace "Bilkisu meke damunki?" "Cramps" na fad'a tareda rufe idona ina fatan ciwon ya tafi, bansan dalilin da yasa har bayan aurena nake ciwon Mara ba maybe Yana relating da infertility d'ina, pills Raudah ta bani tace "pain releiver ne kisha". Karbat nayi ba musu ta mi'komin ruwa nasha na koma na kwanta, dariya naji tayi tace "shiyasa muka ganki kamar a yanayin damuwa kenan ashe hormonal crash kika samu". Rashin dad'i naji akan yanda nayi musu a waje nace "kuyi ha'kuri Raudah banso na sakaku a damuwa ba" Shafa kaina tayi tace "bakomai" mi'ka nayi Jin duk ga'bo'bina sun ri'ke sannan na tashi na zauna, kallon wayarta takeyi tace "kikace kinada aure amma maama tace mana mamanki ce zatayi tafiya shine Zaki zo ki zauna anan, ko kwalliyar ce kawai bakyaso kika bamu wannan excuse d'in?". Girgiza kai nayi nace "ba cewa nayi inada aure ba cewa nayi da aure a kaina, min rabu da mijina ko idda ban gama ba shiyasa nace haka". 38 "oh" ta fad'a tareda maida hankalinta kan waya, bayan ta gama dannawa ta ajiye ta kalleni tace "ya kikaji?" " me fa?" Na tambaya tareda tashi na zauna, "mutuwar aure, how does it feel?" Shiru nayi ina tunanin yanda zan bata amsa, tunda aurena ya mutu babu wanda ya ta'ba min wannan tambayar dukda mama da aunty sun kula dani sosai, amma ba sa'annina bane da zasu tambayeni yanda mutuwar aure take, abinda suke tambayata shine kina lafiya? Saboda kar damuwa tayimin yawa. Zama nayi na had'e hannayena a gwiwata nace "umm to naji abubuwa da yawa ban ma san yanda zan fasalta su ba". Idanunta na kaina tace "baki ta'ba fad'awa kowa ba kenan". Gyad'a kai nayi alamun eh ta juyo gaba d'aya ta maido hankalinta kaina tace "nima nan da kike ganina bazawara ce na miki ta hausawa, amma bansan zafin mutuwar aure ba saboda ni da aurena ma ya mutu bansan ya mutu ba sai bayan almost 6months, shiyasa nake tambayarki i can see how hurt you are Bilkisu". Numfashi naja na sauke sannan nace "a wajena it was the worst feeling ever, I feel sad, hurt, rejected, guilty,...I feel so many things at the same time gaba d'aya 'kwa'kwalwata kamar an dakatar da ita daga aiki, ko processing abinda ya faru na kasa yi a kaina kalmar ce kawai ke min yawo, sai bayan na koma gida Mama ta tasomin da maganar sannan na fara jin zafin abinda ya faru, Raudah muna matu'kar son junanmu, mun yarda da juna,idan muna tare gaba d'aya mantawa muke da kowa da komai, abinda ya girgiza ni shine yanda a cikin mintina kad'an shekarun da mukayi suka tashi a banza". Saurarona takeyi yayin da na bata labarin abinda ya faru itama take sanarmin dalilin nata mutuwar auren, rayuwarta abin tausayi dukda ta tsayawa kanta ta kuma kare , tayi fighting ma right d'inta har 'karshe, kuma ita dangin mijinta na sonta sosai unlike me. Har 12 muna hira kuma naji dad'i sosai, domin da iddata ta matso 'karewa kullum tunanin Saleh nakeyi, a cikin fargaba nake idan na gama idda wacce irin rayuwa zan fara, ya zanji idan Saleh ya dawo rayuwata bayan na gama tsarata na cireshi daga lissafi na? Hannun Raudah naji a kafad'ata tacemin "Bilkisu ba laifi bane ka so mutumin da ya cutar da kai, kuma yanda kika bani labarin zamanku zaiyi wuya ace baya missing d'inki fiye ma da yanda kike missing d'insa tunda ke mace ce shi Namiji ne, na sani zai nemeki ko kusa ko nesa, kawai kiyi preparing kanki yanda Zaki kar'beshi, kina son ya koma rayuwarki ko kinaso ki canza rayuwa it's up to you, balle ma kwanaki kad'an suka rage da zarar igiyar aurensa ta sauka daga kanki ke a jikinki sai kinji sauyi, yanzu ragowar hormones d'insa da ke jikinki su ke sanyaki wannan damuwar amma trust me da kin gama idda zaki samu sau'ki insha Allah". "Thank you" na fad'a tareda share 'kwallar da ta zubomin, banason tunanin rabuwa da Saleh amma abinda Allah yayi baka da ikon canzawa. Washegari babu wani abu da muka yi, a kwance na wuni saidai nayi bacci na farka na gyara kwanciyata na sake komawa bacci, breakfast ma a d'aki nayi zazza'bi ne sosai a jikina. Muna parlour muna hira Aunty ta le'ko tace min "ya kamata yau muyi celebration fa". Juyawa mukayi duk muna kallonta Raudah tace "au Aunty sai yau zakiyi celebrating zuwanmu? Har munyi kwana biyar?" Zama Aunty tayi a gefena tace "celebrating 'yata ta zama sakakkiyar tsuntsuwa mana ni ina ruwana da ku, celebration zamuyi na fitar Bilkisu daga idda". Hannu biyu na saka na rufe fuskata nace "Aunty dan Allah ki bari mana". "Da gaskiyar aunty, yau ranar taki ce dan haka ki fad'a mana abinda kikeso". Raudah ta fad'a tareda zama a kusa dani, twins kuwa har sun fara rige-rigen shiga wanka Aalee kuma idonsa na kaina duk jira suke suji me zance, nasan basa son zaman gida sannan nima akwai abinda nakeso na siya, jingina nayi a bango nace "shikenan ku shirya mu fita". Bayan sun shige d'aki nace da Aunty "aunty ya batun kayan d'akina? Yaushe za'a dauko min su Kinga bani da jaka ko d'aya ban taho da jaka ba". "Zamu san abinda za'ayi, ko zuwa 'karshen satinnan ne sai a san yaushe za'a d'auko da inda za'a saka su, jakunkuna kuma dama ai an gama yayinsu, idan kin fita sai ki siyo na zamani". "To Aunty" na fad'a domin banaso na mata musu, dole ne na fara canza rayuwata a wannan lokacin. ********** *SALEH* Maida maganar da sukayi da hajiya baya yayi ya maida hankalinsa ga Bilkisu, idan baiyi wani abu ba yana gab da rasa Bilkisu har abada. Komawa gida yayi ya samu Hajiya ta siyo kayayyaki da dama, kallon kayan yayi yace "Hajiya mene wannan?" "Kayan lefenka aka fara had'awa". Kallonta yayi cike da mamaki yana tunanin inda ta samu kud'in, kamar ta karanta zuciyarsa tace "kud'in da yake wajena miliyan biyu, na bawa maimuna wasu dai lokacin da zata tafi to saura su muka fara had'a kayan dasu, ka duba kaga sunyi?" Ko sake kallon kayan baiyi ba ya tashi ya bar d'akin, Hajiya bata damu da fitarsa ba ta kalli Maimuna tace "wannan atamfofin na dubu talatin kina ganin biyun sun isa?" "Eh to da dai a 'kara mata d'aya, tunda matsiyaciyar can ma hud'u ya saka mata kuma ni ban ta'ba ganin ta saka su ba, shegiya kullum cikin saka kayan da basa cikin lefe takeyi maybe ma a gidansu ake saya mata". "Ko ma dai mene ai yanzu ya 'kare, iddar tata ma ai ta kusa cika kowa ya huta, tunda nace masa sai yayi aure matar tayi ciki sannan zai dawo da ita ai shi ma yasan zamansu ya 'kare". "To Hajiya yanzu ga wad'annan laces d'in da akace za'a tahomin dasu daga legas, a 32,000 zasu zo amma gaskiya a 40 zan baki su". Jere kayan a leda Hajiya tayi tace "ko ma menene ni dai ayi aurennan komai ya dawo yanda mukeso, a kawo guda biyu". Abun duniya ya taru yayi wa Saleh yawa gaba d'aya zaman gidan baya masa dad'i, tashi yayi ya nufi gidan su Bilkisu yana nocking Jabir ya bud'e, jingina a jikin 'kofar jabir yayi yace "me kakeso Saleh?" "Bilkisu nake son gani dan girman Allah Jabir". Bud'e 'kofar Jabir yayi yace shigo to". Palo suka nufa ya saka key ya bud'e sannan yace masa "idan nace maka bata nan bazaka yarda ba, gashi ka gani da idonka bata nan kuma bansan inda suka je ba". Dur'kusawa Saleh yayi a gaban Jabir yace "dan Allah Jabir ka taimakamin wallahi bana son rabuwa da Bilkisu nasan nayi kuskure kuma inaso na gyara dan Allah ka fad'amin inda take". Tausayinsa sosai Jabir yaji ganin yanda duk ya susuce, alamu yayi masa na ya tashi tsaye sannan yace masa "me kakeso ka fad'awa Bilkisu?" "So nake kawai na ganta Jabir, nasan idan na ganta zata fahimci abinda nazo mata dashi". Shiru jabir yayi sannan yace "kana nufin ka shirya maidata ne ko me?" "Eh" "Hmm lokaci ya 'kure maka Saleh, a lokacin da Bilkisu take jiran zuwanka kana ina? Sai yanzu zaka dawo gareta? In fad'a maka gaskiya har iyayenmu fushi suke da kai ba ma Bilkisu ba, sannan baba zaka samu da wannan maganar ba ita ba". "Zan ga baba amma inaso na ganta". Numfashi Jabir yaja yace "tana gidan Aunty Salma?" Cikin sauri Saleh ya gyad'a kai alamun eh, "tana can amma ka bari sai zuwa Thursday kaje ka sameta, ta fad'amin tanada day off" Godiya sosai Saleh yayi ya koma gida gani yake kaman Thursday bazata zo ba, ranar Thursday kuwa da wuri ya bar aiki domin yaje ganin Bilkisu, shin Bilkisu zata kar'beshi? Da wane hannu Bilkisu zata amince dashi? Shin Bilkisu zata amince da komawa rayuwarsa? Da wannan tunanin ya d'auki hanyar gidan Aunty. *********** "Dan Allah ku barni haka idan ba aljana kukeso na koma ba" na fad'a ina dariya, ina jin dad'in kulawar da suke nunamin a yau jina nake wata special. Tashi nayi nace "na fad'a muku kayannan sun kamani bazan iya saka su da wannan mayafin ba yayi 'karami, idan kuma ba tallan jikina zan yi ba". D'aukan mayafin nawal tayi ta yafamin shi a kafad'ata ta yanda bayan zai sauka sosai,ta gaba kuma yayi dai-dai yanda jikina zai rufe. Kallon fuskata nayi a mirror tare da jin wani confidence na daban, ban sani ba ko kwalliyar da aka min ce ta sanyani Jin hakan ko kuma yanke hukuncin cire Saleh daga rayuwata ne? "Ya kikaga kanki?" Raudah ta fad'a tareda tsayawa a gefena mayafinta na ninke a kafad'arta, "kamar ba ni ba" na fad'a tareda juyi a gaban mudubin, kallonta nayi nace "I feel sooo good". "Muje muji me ya Aalee zai ce" ta fad'a tareda jan hannuna, yana tsaye 'kofar kitchen suna hira da aunty yana hangoni ya matso da sauri, tsayawa yayi dab dani ya matso da kansa sosai har inajin numfashinsa, ja nayi da baya yace "you look great". Ya fad'a tareda min thumbs up "Nagode?" Na fad'a kamar a tambaya, dariya yayi tareda girgiza kansa yace "ina zamu je free Bird?" Murmushi nayi nace "kaima kabi sahun Aunty ko? Ku dena min tsiya fa dama can free nake". "Amma yanzu kin zama more free, zakiyi abinda kikeso ba tareda tunanin nauyin kowa a kanki ba, kowane namiji zai kulaki ba tareda kina jin dar ba". Murmushi nayi na d'auke kaina, saidai maganarsa ta sanyani saurin juyowa na kalleshi lokacjn da ya furta "dukda aurenku ya rabu amma da alamu zuciyarki tana tare dashi". Bansan me ya kawo maganarnan ba saboda bamuyi wannan sabon da Aalee ba sannan hakan da ya fito daga bakinsa sai naji ya 'batamin rai, d'auke kaina nayi nace "babu abinda ya shafeka da rayuwata sannan matsalar aurena ba abinda ya shafeka bane, so please ka san abinda zaka dinga furtawa". Hannuna ya kama fuskarsa dauke da murmushi ya d'an sunkuya yace "am sorry Aunty B tsokanarki kawai nake". Janye hannuna nayi lokacin da su  Raudah suka fito, key d'ina na mi'ka ma Aalee ko nace na cilla masa domin haushinsa nakeji, shi kuwa ko a jikinsa abinda ya 'kara bani takaici kenan. Takalmina mai tsini ne hakan yasa gaba d'aya yanayin tafiyata ya canza ga kuma skirt d'in ya kamani, fita nayi can waje kafin su fito saidai idona yayi tozali da Sam ban shiryawa ganinsa ba, Saleh na gani yana 'ko'karin aiko yaro gidan Aunty. Tsayawa nayi na zuba masa ido yayin da shima yake kallona, bud'e bakinsa yayi yace "Bilkisu?" A tunaninku Yaya Bilkisu zatayi responding? Idan Kece Bilkisu ta Yaya Zaki fuskanci Saleh?.....sai naji daga gareku?😉😉😉😉 39 Matsowa ya fara yi dai-dai lokacin da Aalee ya fito, dafa kafad'ata Aalee yayi yace "haba sweet B yanzu fushi kikayi sosai? Am sorry kema kinsan da wasa nakeyi bansan cewa har yanzu wannan is a sensitive topic to you ba". Gaba d'aya hankalina na kan Saleh, Aalee ganin ban kalleshi ya sanya ya saka hannunsa biyu ya tallafo fuskata tareda juyota gareshi, murmushi yayimin wanda ya bayyanar da kyawawan dimples d'insa yace "look into my eyes and say you forgive me baby, bazan kuma ba kinji?" Ya Kare maganar yana turo baki, kallon Saleh na sakeyi da idanunsa a take suka sauya da alamin kishi, wani irin kallo yake ma Aalee wanda baisan ma yanayi ba hakanan naji wannan lokaci yayimin dai-dai. Cire hannun Aalee nayi daga fuskata nace "na yafe maka, idan kuma ka kuma...." Jan kunnensa nayi ya saki wani 'kara had'e da murmushi, kama hannunsa nayi na nufi 'kofa cikin sauri Saleh ya matso tareda kama 'kofar, a fusace ya kalli hannuna dake ri'ke da na Aalee sannan yace "me kikeyi haka Bilkisu?" Shigewa gabana Aalee yayi yace "easy man, no one talks to my girl without my permission". Tamkar Saleh zai daki Aalee yace "malam matsa da matata nake magana". Bansan lokacin da dariya ta 'kwacemin ba na girgiza kai tareda jan Aalee nace "mu tafi kar mu makara". Shigewa gida nayi na doka 'kofar saida Aliyu ha d'an tsorata, knocking Saleh keyi yayin da nake jingine jikin 'kofar yanda zuciyata ke bugawa abun har tsoro ya bani, ban ta'ba tunanin ganin Saleh a wannan lokacin ba kuma banda Allah ya kawo Aalee bansan ta yaya zan fuskanci sale ba, hannuna na Sanya a 'kirjina tareda sauke numfashi ina jin bugun Saleh har cikin kaina. Fitowa su Raudah sukayi tareda Aunty tace "waye yake mana bugu a gida?" "Ba kowa" "Tsohon mijin Aunty B ne" mukayi maganar a lokaci d'aya, cikin sauri aunty ta nufo 'kofar take yanayinta ya canza, bansan lokacin da na ri'ke hannunta ba. Girgiza mata kai nayi a hankali nace "dan Allah Aunty a'a". Hard'e hannunta tayi a 'kirji tace "a yanzun ma kareshi kikeyi?" Muryata tana rawa amma a haka na dake nace "a'a Aunty ba kareshi nake ba, amma bashida matsayin da zaki saurareshi a wurinnan jannat ce kawai dai-dai dashi, ki kyaleshi dan Allah bansan ma da rayuwarsa a wurin ba". Dafa kafad'ata tayi tareda murmushi sannan ta juya ta koma gida, runtse ido nayi tareda maida numfashina na bar 'kofar gate d'in da murmushi a fuskata, bud'e gate d'in mai gadi yayi duk muka shiga mota bansan yanda na 'kare a passenger seat ba au Raudah kuma suna baya dukkansu, a tsaye naga Saleh ko kallo bai isheni ba muka wuce. Mun kusa 10mins babu wanda yayi magana, jannat ce tayi breaking silence d'in tace "ya Aalee Ina zamuje wai". Kallona yayi yace "Aunty B zaki tambaya". Kaina na window nace "inaso na sayi kayan makeup, takalma da jakunkuna". Bansan inda zan samu abubuwan da nake bu'kata ba saboda haka muka yita yawo a gari har na samu wurin jakunkuna masu matu'kar kyau, guda biyar na siya su Raudah suka sayi d'ai-d'ai, muna zuwa wajen biya Aalee ya mi'ka katinsa, wurga masa harara nayi na kar'bi katin na mi'ka nawa. Raudah dake bayana ce ta kar'bi katin ta mi'ka tace "kin ta'ba ganin inda aka fita da namiji mace tayi siyayya?" Cashier d'in har mun fara b'ata rai, kallon Raudah nayi nace "tunda nace zan biya ki barni kawai dan Allah, na dad'e da kud'innan bansan me zanyi dasu ba kuma abin kashewa yazo sai ace bazan kashe ba?" Ja tayi da baya ta barni na biya, a kusa da shagon na sayi takalma su Raudah suka 'ki saya saboda basaso na biya, da kyar suka amince suka d'auki d'ai-d'ai shima saida nace zamuyi splitting kud'in da Aalee. Wasu dogayen riguna na hango a shop d'in kusa da su again nan ma muka shiga, kallon kayan muke munata yabawa naji Aalee yace "wannan kuma a 'kafa ake rufawa ko shima belt ne na ciki?" Juyowa mukayi dukkanmu kawai muka ganshi ri'ke da bra yana jujjuyawa, a tare muka ja tsaki wanda dukkanmu ya bamu dariya babu wanda ya kula shi nan ma dai bamu fita ba saida muka sayi riguna 2pcs kowa jannat kuma 4, wannan karon Aalee ne ya biya, inaso na sayi panties amma idon Aalee ya hanani. Saida muka gama siyayyarmu sannan nace da Raudah "inaso na sai undie amma wannan yayan naku sai ya kwana Yana min tsiya idan ya gani". Dariya tayi sannan tace "ba dai tun na lefe baki canza ba". Harararta nayi nace "haba dai, ai an samu matsala kenan". "Ah to nasani? Dan wannan matsolon mijin naki da na gani a waje ba alamun zai iya siyan panties". Bata jira na bata amsa ba ta nufi Aalee tareda bashi kayanmu tace gamunan zuwa ya jiramu, kusan gaskiya ta fad'a tunda mukayi aure Saleh bai ta'ba siyamin panties ba ko ya bani kud'in siya wannan aikina ne kuma Banga hakan a laifi ba ko kuwa laifi ne? Indai zai gani a jikina ya yaba ni yafimin komai, too bad ba sake gani zaiyi ba. Aalee na fita na d'auko wanda suka min kyau, twins na gani suma suka ce sai an siya musu siyayyar lingerie dai harda su jannat, mun sake sosai kasancewar shagon Mata ne a cikinsa, maimakon muna gamawa mu fita sai ga amal ta hango wata bra a lallai tana so, peach colour ce itama nawal tace tanaso Kuma sai peach, haka aka dinga neman peach d'in babu kuma suka 'ki ha'kura. Dawowa Aalee yayi alamun ya gaji da jira ya samesu suna musu da Raudah, tace ko dai su canza color d'in ko kowacce ta d'auki different colour, na rasa wannan iyayin na twins har undies ma sai kala d'aya?. Ina zaune a gefe Aalee ya zauna a kusa dani, an samu sun ha'kura sun d'auki light purple, ta'boni Aalee yayi tareda mi'komin bra yace "wannan zata miki kyau fa". Kallonsa nayi na rasa daga wani baki wannan maganar ta fito? Tashi yayi ya fice ya barni baki a sake na dubata kuwa naga tayimin na siya. Mun gama kashe kud'i sannan muka nufi inda zamu sayi abinci, Aunty tace bazata mana girki ba gashi mun gaji balle muyi tunanin yin girki, takeaway mukayi muka nufi gida. Kallon 'kofar gidan nakeyi wani bangare na zuciyata na son ganin Saleh, wani iri naji a raina da ban sameshi ba, "karki damu gobe ma zai dawo" Aalee ya fad'a tareda fita daga motar, wannan yaron da alamu duka yakeso ya fiye shiya rayuwata. Waya mukayi da Mama ta sanar dani sai bayan 2 days zata dawo, naji dad'in 'karin kwanakin nasu domin zaman gidan aunty Yana min dad'i, sannan kuma 2weeks su Raudah zasuyi kafin su koma. Bayan mun huta suka ciro kayansu da suka zo dasu zasu kai  d'inki, tagumi nayi nace "nima da ace zan iya debo kayana ai da na kaisu d'inki tareda naku". Tunani ne ya fad'omin na kira Sultana "sai yau kika tuna damu ko Bilki? Wallahi baki ri'ke amana ba Bilkisu ai ko lafiyar yarinyarki kya kira kiji". Shiru nayi na d'an lokaci tareda Jin rashin dad'i na kiran sultana da banyi ba, tun ranar da na maida Huda ban sake kiranta ba itama bata sake kirana ba, ko babu aure tsakanina da Saleh ya dace nayi zuminci da sultana domin mutum ce, har tafi Saleh a wurina domin ta tsayamin fiye da yanda ya tsayamin. "Kiyi ha'kuri Sultana abubuwa ne sukamin yawa wallahi sannan banason duk wani abu da zai shafi Saleh....amma yanzu insha Allahu zamuyi zumunci alfarma nakeso daga gareki". "Wacce irin alfarma Bilki?" "Umm dan Allah gidana..." Wani banbarakwai naji da nace gidana amma na 'karasa maganata nace "kinga har yanzu ba'a zo an fara kwasar kayana ba, dan Allah so nake ki shiga akwai kayana da ban d'inka ba suka cikin akwati, ki d'aukomin su". "Okay gida za'a kawo miki su?" Tunani nayi sannan nace"a'a bana gida, amma...yauwa shikenan ma ki bawa Saleh ya kawomin yasan inda nake". Dariya tayi tace "kai Masha Allahu, Allah yasa a jone a haka". "Haba sultana kya min wannan fatan? Ai ni da sake zama da hajiya har abada, kin lahira banaso na tsaya kusa da ita ko haularta". "Bakyaso ba wallahi, yanzu ma tananan tana had'a kayan auren....". Shiru tayi ba tareda ta 'karasa ba, "kayan auren wa ake had'awa Sultana?" Shiru tayi nace "MAMAN DEEDAT". "Kiyi ha'kuri wallahi bansan 'kai'kayin bakin da ya sani fad'a miki ba, kayan auren Saleh take had'awa, shima hira naji sunayi da Saleh Yana neman shawararsa wai tace bazai maidoki ba sai ya auri wata matar itama matar sai tayi ciki tukuna, kiyi ha'kuri bilkisu". Dariya nayi dariya kuma sosai, hankalin su Raudah duk yana kaina har Aunty ma, saida na gama dariyata sannan nace "lallai Saleh namijin duniya, shi kuma ya amince ko?" "To Bilki ya zaiyi? Inaga ya gano duk abubuwan da suka faru sharrinsu ne yace zai maidoki shine ta kafa wannan sharad'in, kuma kinsan ba yanda zaiyi wallahi yana son ya dawo dake sosai shiyasa ya amince". Murmushi nayi ina lissafa maganar, saboda ni banida zuciya a 'kirjina zan zauna jiransa har yayi aure yayita kwanciya da matar har sai tayi ciki, to ciki abin Allah akwai Wanda ya isa ya kawo shi lokacinsa baiyi ba? Wato duk sai anyi wannan budirin sannan a dawo ga Bilkisu wadda ta yar da zuciyarta dangin mijinta sun take da takalmansu, ace na koma kuma na koma, ina Nan a juya ita kuma tayita ciki tana haihuwa na zauna banida maraba da hoto, domin ko shi indai ya fara samun 'ya"ya nasan Dole soyayyata sai ta canza a wurinsa, to kin Haifa ma miji ya raba son da yake miki ya maidawa abinda kika haifa rabi balle ke da ba zaki Haifa ba? Da alamu dai zamana da Saleh har abada, dole ne na fuskanceshi muyi magana mu samu closure kowa yayi hanyarsa. "Sultana bakin al'kalami ai ya riga ya bushe, idan kikayi tunani a abinda hajiya ta tsara kawai plan ne a wula'kantani har 'karshen rayuwata, kina tunanin idan ya fara samun haihuwa zai kashemin miliyan hud'u domin na haifi d'a d'aya tal bayan yana samunsu a kyauta? Na gama fahimtar plan d'in hajiya da alamu dai ni da Saleh saidai a bada labari". Muryarta gaba d'aya ta canza kamar zatayi kuka tace "Bilkisu dan Allah ki taimaka masa wallahi Saleh yana bukatarki fiye da yanda kike tunani kuma yana sonki, bakiga yanda ya lalace ba a tafiyarnan taki, ni kaina wahala nakesha saboda rashinki a gidannan ga Huda ga Ahmad wataran na rasa yanda zanyi dasu saidai na sasu a gaba na zuba tagumi. ni abinda nace ma yayi shine ya maida ke ko wani wurin ne ya kaiki ya ajiye kafin iddarki ta 'kare, idan yaso ko me za'ayi dai kina matsayin matarsa". Dariya nayi nace "Sultana yau na fita daga idda ai, na tashi daga matar Saleh na zama matar...." Kafin na 'karasa Raudah tace "Aalee!!" Rankwashinta nayi nace "na zama matar mai rabo, saidai ya shiga jerin zawarana". Da alamu kuka ta fara saboda yanda muryarta ta sauya, a hankali tace "shikenan Bilkisu bazan sake ganinki ba?" "Zaki ganni mana Sultana zamu dinga zumunci dukda bazan iya zuwa inda kike ba saidai ki dinga ha'kuri kina zuwa inda nake" "Dukda haka zumuncinmu bazai kai yanda nake so ba, dan Allah Bilkisu ko Huda ki kar'ba nasan cewa muna nan a "yan uwa". "Sultana ina kewar Huda sosai wallahi, amma a yanzu ne ma lokacin da ya kamata Huda ta zauna dake, dama auren Saleh ne ya sanya kika bani ita yanzu babu wata dangantaka tsakanina daku, ri'kon Huda zai zamarmin damuwa musamman da su Hajiya basa so, zan dinga ganinta dai akai-akai nagode da kulawarku sultana, kece kad'ai farin cikin da bazan manta dashi ba a zamana a gidanku". Kuka take a yanzu sosai har ta sanyani hawaye nima, cikin kuka tace "na dad'e ina kishi dake Bilkisu na dad'e ina sha'awar zaman da kikeyi da Saleh, idan na zauna sai nayita tunanin meyasa ni da usman bama wannan zaman? Soyayyarku nake kwaikwaya Bilki har na 'kware nima, yanzu duk wannan zaman kin manta dasu?" Murmushi nayi nace "Sultana abu marar Dad'i d'aya yana kore duk wani Dadi da kaji a duniya, ban manta dasu ba amma bana tuna lokutannan kamar yanda nake tuna ranakuna na 'karshe a gidan Saleh, amma wataran sai labari ki shafamin kan Huda". Ban jira me zata ce ba na katse kiran tareda share hawayena, duk jikinsu yayi sanyi banda mutum d'aya, kunsan waye ba sai na ambaceshi ba, dawowa yayi hannun kujerar da nake yace "yanzu salele yana number one kenan a zawarawanki, please make me number two". Galla masa harara nayi ya d'aga gira tare da cewa "I am serious, zan Kara dashi naga a cikinmu wa zaici wannan game d'in?" "Ya Aalee yanzu Aunty B d'in ce game?" Raudah ta fad'a tana kallon yanda naji ba dad'i da ya kirani game, murmushi yayi yace " 'kwarai kuwa, duk macen da tayi aure ta fiti ta zama game a wurin mazaje, musamman mata irin su Sweet B, tamkar gwal ne, mutum yayi amfani dashi ya yar aka dasashi a tsakiyar ruwa kowa yana kallonsa kuma wannan gold d'in na attracting attention na duk wanda ya wuce, saidai a 'karshe ansan dole mutum d'aya ne zai zama mamallakinsa, mai shi bazai gane tsadarsa da kyawunsa ba sai yaga yanda mutane ke rububin d'aukansa, wannan shi ya maidashi game, wa zaka kayar wa zai kada kai? Ke kinsani bazawara tafi budurwa white blood domin har wani shining takeyi". Duka muka kai masa da ni da aunty da Raudah, dariya yayi yace "oh my God ashe gidan zawarawan nake, nidai sweet B ki sakani a list". Tashi nayi nace "ai ba ni zan sanyaka a list ba, kai zakayi proving kanka ka isa shiga list d'in ma ko kuwa". "Game on wifey, na miki al'kawari a 'karshe ni zan d'auki wannan gold d'in, ba zanyi swimming kamar yanda kowa keyi ba, zan bi ta sama ne na d'aukeshi kowa yana kallo". Juyowa nayi na kalleshi nace "ai ba d'aukan gold d'in bane wahalar, zaman gold d'in a hannunka shine abinda yafi wuya, karka maida hankali wajen samun abinda ka 'kwallafa Rai ka fara duba wannan abun ya dace da kai ko kuwa? Idan har ka d'auki gold din hanyarka ta fita kayi tuntube da diamond, zaka d'auki diamond d'in ne ka had'ashi da gold d'in ko kuwa zaka yar da gold d'in ne saboda diamond ya fishi daraja? Kuma daga kallonka nasan zakayi amfani da maganata ta biyu ne". Ni kaina bansan ma'anar maganar da nayi ba saida na shige d'aki, sam ban amincewa Aalee ba na farko saboda yana da kyau, ba wai mummunan namiji nakeso ba amma maza irin su Aalee bakada kwanciyar hankali, namiji ne kamar balarabe  komai nasa sai ya d'auki hankalin mace, a fitar da mukeyi ina kallon idanuwan mata da dama a kansa amma ko ta kansu baya bi, sharrin matan zamaninnan wata ta dora Ido kansa kin gama yawo, kuma ni ba aurene ma yanzu a gabana ba, namiji ya bani lesson d'in da Zan dad'e ban amincewa wani namijin ba, wanda ka dad'e dashi ya maka haka balle kuma wanda ka gani a titi? Tun ina secondary nake hulda da Saleh amma yayimin haka, Ina ga wanda zamu had'u a titi? Sallar Isha nayi kafin na fita na jiyo maganar su "Gaskiya ya Aalee baka kyauta ba" Raudah ta fad'a cikin 'bacin rai. "Me nayi?" "Kai baka San me kayi ba? Ta yaya zaka fara wani zancen game a wannan yanayin? Kwana nawa da mutuwar auren nata zaka fara mata wasa, ba sonta kake ba bai kamata ka fad'i abinda ka fad'a ba". Dariya yayi yace nifa "banga laifi a abunda na fad'a ba". "Wai ta Yaya zaka ce baka yi laifi ba? Ita Bilkisun abar wasa ce a wajenka? Ta yaya zaka fara tempering da emotion d'inta bayan halin da ta shiga? Ita ba irin wad'annan sha-sha-shan 'yammatan dake binka bane kana yarfa su, Ka sameta ka bata ha'kuri kar kuma ka sake mata magana irin wannan, idan kanada interest a kanta ne ka biyo ta hanyar da ta kamata mana". "I mean what I say Raudah, babu na ha'kuri da zan bata" alamun fitarsa naji na koma na kwanta, banaso ma na saka Aliyu a lissafina shirme kawai yakeyi. Bud'e wayata nayi tareda unblocking number Saleh, pics d'in da mukayi na fara kallo naji sallamar Raudah. "Me kikeyi?" Ta fad'a bayan na amsa mata sallama, nuna mata pics d'in da nake kallo nayi ta kar'ba tana kallo, twins ne suka shigo suma suka zauna gefenta, kallon hotuna suke wasu su nunamin suce waye wannan na fad'a musu, yawancin pics d'in duk na Huda ne, ji nayi na sake missing d'inta. Rufe ido naga twins sunyi Raudah kuma ta juyomin wayar tana dariya, wani pic ne nawa da Saleh...wanda dai bazan so kowa ya gani ba, "gogeshi dan Allah" amsamin tayi da to ta goge, saidai fa irin pics d'in ne suka yita bayyana kansu, tun ina cewa ta goge har dai na kar'bi wayar tawa na fara gogesu da kaina, duk hotunan akwai memory d'in da suke holding, tun ina gogesu babu wani emotion har saida zuciyata ta fara karaya hannuna ya gagara danna delete, fita nayi na ajiye wayar a gefe tareda nufar toilet nayi kuka na mai isata sannan na fito, duk yanda zan yaudari kaina nace na cire Saleh a rayuwata nasan cewa wani gurbi na zuciyata har abada yana tareda Saleh. 40 A gajiye na shaso kwanar gidan Aunty, yau munsha aiki fatana kawai na samu na huta, mayafin abaya na yafa kasancewar na fito abokiyar aikina na sallah da hijabina kuma bazan iya jira ba, Saleh na hango a tsaye yana juya key a hannunsa sai raba ido yakeyi. Mamaki nayi ganin Huda a hannunsa, ya kamata ace yana wurin aiki yanzu meyasa jabir ya barshi ya taho? Me yazo yimin ma in the first place? Idanunsa na kaina har nayi parking, dukda nayi farin cikin ganin Huda amma ban wani nuna ba kar yayi tunanin shi nake farin cikin gani, domin ina ganinsa maganar sultana ce ta fad'omin ta auren da zaiyi. Cikin 'karfi na daki murfin motar ina kallon idonsa a kan motar tawa, domin yasan tafi tashi tsada da kyau. Murmushi ne ya bayyana a fuskata jin Huda ta kirani da maama, nayi tunanin ta mantani a wannan lokacin da muka d'auka bama tare amma abin mamaki ta ganeni, kar'bar ta nayi na rungumeta a 'kirjina. "Motarki tayi kyau" ya fad'a yana kallon jikina babu ko kunya, doguwar riga ce a jikina mayafin ne dai a 'kirjina ya tsaya, murmushin takaici nayi nace "too bad ba da kud'in da na sata a gidanka na siya ba, da kud'ina na siya". Yanayinsa ne ya canza kunya da nadama suka kamashi, "boo-boo am....." Dakatar dashi nayi nace "me ya kawoka? Me kuma ka nema ka rasa da kazo wajen 'barauniyar tsohuwar matarka?" Ri'ke keys d'in hannunsa yayi cikin 'karfi, saidai bai amsamin ba yace "kayanki Sultana ta bani na kawo". Bud'e booth d'in motar yayi ya janyo akwatina, ajiyeshi yayi nace "thanks". Har zan juya gida na tuna da Huda dake hannuna, haka nan banso ba na mi'ka masa ita, ri'ke wuyana tayi tareda d'aura kanta a kafad'ata alamun bazata je ba, ya Allah Huda dai so take da dad'e da mutuminnan saidai dad'ewata tare dashi yana nufin dawo da duk abubuwan da suka faru baya wanda bana son hakan ya faru, ina jin 'bacin raina Yana tasowa ga gajiya ga yunwa. "Huda kije wajen uncle kinji? Gobe sai a kawomin ke ki kwana a wajena". Girgiza kai tayi ba tareda ta d'ago ta kalleni ba hakan ya bawa Saleh damar fara magana "Boo...." "Bilkisu" nayi saurin gyara masa, baisan rad'ad'in da yake sakawa zuciyata ba idan ya ambaci wannan kalmar, sunkuyar da kai yayi sannan yaci gaba "wallahi na Gane kuskurena Bilkisu kuma nayi nadama sosai, bansan me ya faru dani a wannan lokacin ba har na aikata hakan, Bilkisu wallahi na yarda dake kema kinsan haka amma nasan na tafka kuskure mai girma a wurinki, dan Allah ki daure ki dawo Bilkisu wallahi na miki al'kawarin makamancin haka bazai sake faruwa ba, ina bu'katarki a rayuwata Bilkisu". Shiru nayi na zuba masa ido, bansan me zan furta masa ba saboda maganganunsa a wurina are bullshit, tambayoyi da dama sunzo kaina kamar me yasa sai yanzu zaka nemeni? Idan da gaske kana sona meyasa ko ta hanyar sultana bazaka ji lafiyata ba? Meyasa a duk danginka babu wanda yazo ya bani baki akan kayi kuskure? Saidai wad'annan tambayoyin ina tsoron jin amsarsu, numfashi naja nace "me kakeso yanzu Saleh?" Shiru yayi na seconds sannan yace "inaso ki dawo gareni Bilkisu, tunda da aurena a kanki". Dariya ce ta 'kwacemin nace "are you stupid? Wani aurenka ne a kaina?" Zare ido yayi sannan a hankali yace "har yanzu wata uku bai cika ba...". Wata dariyar na sake yi nace "idda ba watanni uku bane gareni karka manta ni ba 'karamar yarinya bace, jini uku ne kuma nayi na gama". Sosai Saleh ya firgita da maganata, muryarsa har rawa take yace "dan Allah Bilkisu ki bani dama ta biyu". "Gyara ri'kon Huda nayi nace "meyasa ka sakeni? Meyasa ka wula'kantani Saleh bayan kasan ban ta'ba son wani namiji a duniya ba bayan kai, a kanka nasan mene so, kuma nayi rashin sa'a na aureka, meyasa a lokacin da nake bu'katar fahimtarka ka juyamin baya? Bayan ka sakeni ka kasa nemana saida bu'katarka ta kawoka gareni, a danginka babu wanda yazo wajena, kayi ignoring d'ina na tsawon watanni biyu da satittika sai yanzu rana d'aya kazo kana so na koma? Why are you so selfish? Me ya dawo dakai gareni? Ka gaji da cin abinci ba irin nawa ba? Ka gaji da kwanciya a gado kai kad'ai? Ka kasa handling desire d'inka kuma ni kad'ai ce option d'inka? Nasan wad'annan sune dalilanka ba wai don kana sona ka dawo gareni ba, ka dawo ne kawai saboda bakada wani escape sai ni, kacemin ba haka bane Saleh". Da alamu maganganuna gaskiya ce domin Saleh ya kasa furta komai idanunsa na kallon 'kasa, ni kad'ai nasan rad'ad'in da nakeji a zuciyata, Allah ya sani naso ya 'karyata maganata, naso ace ya furtamin yazo gareni ne saboda ya gane kuskurensa saboda 'kaunar da yakemin, guess kawai yazo ne saboda selfish interest d'insa. Dire Huda nayi na juya jikina har rawa yakeyi saboda 'bacin rai, hannuna ya ri'ko na juya na kalleshi, yanda ya kalleni nasan idanuna sun saya domin ya kalleni a tsorace. "Bilkisu I really miss you and...I love you bazan iya zama da wata mace ba bayan ke" maganganunsa tamkar wu'ka ne a jikina musamman da na tuna da maganar sultana, murmushi nayi na danne hawayen dake neman zubowa nace, "Matar da zaka aura kuma fa? Ita ba zama zakayi da ita ba?" Nasan yayi mamakin yanda nasan hakan amma ba abin mamaki bane, girgiza kai yayi yace "Bilkisu na rantse miki da Allah ba ni na nemo Hadiyya ba Hajiya ce ta tilasta min sai na auri Hadiyya, tacemin idan ina so na dawo dake sai na auri Hadiyya, a wajena ita ba komai bace ko na aure babu abinda......" D'aga masa hannu nayi na dakatar dashi nace "Kar ka fara min maganar banza, ni ba 'karamar yarinya bace kuma ni da kai munsan dalilin mahaifiyarka na aikata hakan, zata aura maka macen da take haihuwa, ita ta haihu ni na zama shara, do you think I am still that low? Da zan zauna jiranka na koma a mace ta biyu gidanka? Bakasan cewa nasan sharad'in Hajiya akan aurena ba? Saleh ka sani daga lokacin da kayi aure tunanin dawowata ma ya fita a ranka, wallahi kaji na rantse bazan zauna da wata mace ba a matsayin kishiya, ko a gidanka ko ba a gidanka ba, bazan ta'ba zama da kowacce mace ba, kaje kayi aurenka Allah ya Sanya alkhairi and please leave me alone!!" Ina juyawa na fara hawaye, ina jin muryar Saleh yana kirana amma na'ki juyawa, kaina a 'kasa, fad'awa nayi jikin wani wanda babu makawa aliyu ne, cikin sauri naja baya jin 'kirjinmu ya had'u da juna, ja da baya da nayi ya sa na kusa fad'uwa cikin sauri ya taroni, hannunsa d'aya yana bayana d'ayan ya ri'ko hannuna, maimakon ya d'agoni ina kallon idonsa ya kalli Saleh, wani murmushin mugunta yayi ya sunkuyo da fuskarsa dai-dai tawa yace "kinsan idan a film ne rawa kawai ya kamata mu fara". 'ko'kari nake kar ya sakeni na fad'i, 'kafata har ta ri'ke kasancewar ta gurd'e, kula yayi da hakan ya gyara min tsayuwata, sai yanzu damuwa ta bayyana a fuskarsa, hannu ya saka ya goge hawayena tare da cewa are you okay?  _ya Allah this is so wrong_  na fad'a a raina, dukda shi muharramina ne amma bai dace yana ta'bani haka ba musamman yanzu da ya furta sai yayi conquering d'ina. Janyewa nayi daga gareshi nace "I am fine". Juyawa nayi kad'an na hango Saleh a tsaye yana kallonmu, da ace kallo yana kisa ni da Aliyu da mun fad'i matattu saboda irin kallon da Saleh yake mana, bansan lokacin da na kama hannun Aliyu na jashi gida ba. Tsayawa mukayi a harabar gidan yace "ki bari ki d'an kimtsa kafin ki shiga ciki ko?" Gyad'a masa kai nayi alamar eh, murmushi na gani a fuskarsa amma hankalina na wani wurin daban, cikin zolaya yace "da alamu hannuna yana taimaka miki ki nutsu". Cikin sauri na saki hannunsa da na manta ina ri'ke dashi, har ga Allah tunanina na wani wajen bana ma jin hannunsa a hannuna, amma da ya furta saida naji d'umin hannunsa a cikin hannuna, tunawa nayi da yanda na fad'a 'kirjinsa, yanda shi bai motsa ba sai ma ni naja da baya, t-shirt ce a jikinsa wanda hakan yasa.....oh my God what am I thinking? Ya kamata ace ina tunanin abinda ya faru tsakanina da tsohon mijina ba wai yanda naji 'kirjin Aliyu ba. "Key d'inki yana cikin motarki ko?" Ya tambaya bayan munyi mintina uku a tsaye, gyad'a masa kai nayi alamar eh ya fita ya barni a tsaye, mai gadi na sanarwa ya bud'e masa gate na wanke fuskata na shiga gida, saidai kallon da Raudah tamin yasa nasan ban wanke kukan nawa da kyau ba. D'aki na shiga ta biyoni twins na kan katifarsu, akwatina na bud'e na cire kayan da zan saka, zama Raudah tayi gefena tareda zugemin zip d'in rigar, a hankali nace "nagode". "Me ya faru?" Ta tambaya bayan na cire rigar ina 'ko'karin saka marar nauyi, shiru nayi tace "I understand idan bakyaso ki fad'amin, kawai ina fatan it's not something bad". "Ex d'ina ne yazo" cigaba nayi na fad'a mata duk abinda ya faru, ina gama fad'a mata tayi hugging d'ina tareda cewa "wallahi naji dad'in hakan da kikayi sosai, kin tsayawa 'yancinki, idan har yana sonki da gaske bazai ta'ba amincewa yayi auren ba, idan kuwa yayi to an fi 'karfinsa kuma duk namijin da mata suka fi 'karfinsa sorry to say ko mahaifiyarsa ce to akwai matsala, balle a condition d'inki kawai ta d'auko step ne na wula'kantaki, bazaki gane hakan ba sai kin koma gidansa yayi aure, matar ta samu ciki anan zaki fara ciwon zuciya, za'a yi ta cewa tana son abu kaza, sai an cinye kud'insa tas kina zaune, idan kikayi magana ace kina ba'kin ciki ke bakya haihuwa, idan ta haihu 20hours zai dinga yi a wajenta ke kuma 4hrs, bazance karki koma wa mijinki ba amma ki nemi za'bin Allah gaskiya in my POV zamanku ba mai alkhairi banez you will end up getting hurt more than you imagine, rayuwarki zata 'kare ne a bautawa soyayya da bautar 'ya'yan da bazasu ta'ba daukan ki da muhimmanci ba". Numfashi naja nace "Raudah na yarda da maganarki, nima ba wai so nake na koma ba musamman a yanzu, abinda na gani shine Saleh yayi ha'kuri dani akan rashin haihuwa, kina tunanin zan samu mijin da zai aureni a haka bana haihuwa ya zauna dani tsakani da Allah ba tareda na fuskanci tsangwama ba? Raudah...wallahi ina matu'kar son haihuwa fiye da tunaninki, na dad'e ina mafarkin 'ya'yan da zan haifa, idan na kar'bi haihuwar mace ji nake kamar na tura babyn cikina na haifoshi a matsayin nawa, tun kafin nayi aure nake craving 'ya'ya yanzu da nasan matsayina abin worsening yakeyi, gani nake Saleh da ya fahimci halin da nake ciki shi kad'ai ne zai iya bani abinda nakeso ba tareda gori ba". 'kare maganar nayi cikin hawaye sannan nace, "a duk lokacin da nayi maganar haihuwa sai nayi zuciyata ta d'aure, na dad'e ina pretending everything is alright akan rashin haihuwata amma it's eating me up every single day, banaso nayi sa'bo amma nakan tsinci kaina ina tambayar kaina, meyasa Allah ya jarabceni da jarrabawar da take da wuyar cinyewa a gareni? Allah ya rabani da iyayena tun ina tsumma, ya rabani fa burin duk wata mace, wato samun zuri'a, sannan ya rabani da mijina da nake tunanin shine gatana". Hugging d'ina Raudah tayi a yanzu hankalin twins na kanmu, nawal ma share 'kwalla takeyi tana tausayamin Banga laifinta ba domin rayuwata abin tausayi ce, a duk lokacin da na samu farin ciki sai Allah ya d'aukemin shi, fatana Allah ya musanya min wannan rayuwar da na rasa da wadda ta fita. "Bilkisu you are a strong person shine abinda zan fad'a miki, ban ta'ba ganin mace mai jarumtarki ba a rayuwata, ki sani Allah yana sane dake kuma yana jarrabaki ne saboda imaninki yanada yawan da idan aka rabawa mutane da dama a duniyarnan zasu amfana, shiyasa Allah yake jarrabaki, ke ta daban ce a cikin halittunsa kuma zaici gaba da jarrabarki har zuwa mutuwarki, Amma kinsan me? Inaji a jikina kina gab da samun soyayyar da kika dad'e kina nema, Allah zai baki rayuwa da mutumin da zai soki ya rufa miki asiri, karki manta fa akwai mazan da suka fi Saleh imani da tausayi, sorry to say amma Saleh yana da son kansa, yana son zama dake ne saboda kece kariyarsa, nasan yana sonki babu musu akan wannan amma baya miki so enough da zai kareki daga danginsa, pray, pray hard akan za'bin Allah, kinsan Allah bazai kuma ta'ba mantawa dake ba, stay stronger and be happy". "Nagode Raudah" shine abinda na fad'a tareda kwanciya a katifar, fatana kawai wannan ya zama karo na 'karshe da zanyi kuka akan Saleh da kuma rayuwata, ni kaina na gaji. Bamu fita ba sai bayan munyi magrib, Aunty muka samu da Aliyu suna hira a kaina, bansan ko tambaya yake mata ba tace "eh bazata iya haihuwa ba yanda dai suka ce saidai a mata IVF". Hankalinsa duk yana kan Aunty yace "maama kuma an tabbatar da tanada matsalar ba wani had'i bane na wad'anda basa sonta?" Kallona Aunty tayi tace "eh to da farko nima ban yarda ba amma asbitin da take internship taje aka dubata sannan likitan ba irin 'kananunnan bane, sannan bayan sunyi magana da asbitin da zasuje na Dubai saida aka sake mata exam d'in, sannan shekara uku babu labari wannan duk shi ya tabbatar". Kallona yayi cikin tsokana yace "maama ya kamata to a sake mata saboda inaso na tabbatar kafin na d'auketa, kinga ana aurenmu sai muje Dubai d'in honeymoon anan a dasa mana babies d'inmu triplets ko ya kikace?" Ya Kare maganar tareda winking, dukda nasan da wasa yake amma har zuciyata saida naji maganar sosai ta sosamin rai, at least someone is willing to help me ko da a wasa ne, share maganar nayi nace "in your dreams yaro ba wani aurenka da zanyi". Kallona yayi wannan karon da seriousness yace "hey am 31 sannan ni da gaske nake aurenki zanyi". Zuba masa ido nayi nace "dan Allah ka bari banaso". Gaba d'aya hankalinsa ya dawo kaina yace "ba wasa nake ba, idan ba ni d'in ba wa ya dace ya aureki baby? Na farko dai babu mai auren juya, na biyu kuma babu yanda za'ayi a sake bada ke ga bare tunda auren waje baya haifar mana da komai sai fitina, Raudah ta auri bare gatanan ta fito, kema kin auri bare ga abinda ya faru, so better be ready domin kina gab da fara kirana husbyyy". Dukda cewa ya saka wasa a cikin maganar tasa amma sosai yana nufin abinda ya fad'a, girgiza kaina nayi nace "meyasa? Meyasa kakeda matsala Aliyu? To ni bazan aureka ba domin nasan ba dan so kakeso ka aureni ba tausayina kakeji, kuma bazan iya auren namiji irinka ba". Kallon Aunty nayi amma ta d'auke hankalinta daga kaina, su Raudah ma duk sun koma kallon wayoyinsu amma nasan hankalinsu na kaina, dariya yayi a hankali yace "okay, zamu gani ni dake waye zaiyi winning, better stop being stubborn". Tsaki naja nace "ni ba yarinya bace ba kuma auren farko bane da za'a min dole, idan kana ganin kuma kanada wani iko a kaina da ni banida Bismillah show me". Ina gama fad'in haka na nufi d'aki, jinsa nayi yace "ko dan na rage miki stubbornness sai na aureki". 41 *SALEH* Driving yake maganganun Bilkisu na dawo masa, tabbas yaso kansa farin cikinsa kawai yake dubawa baya duba nata, idan har aurensu ya koma a yanzu zata shiga cikin 'kunci da 'bacin rai fiye da na baya, amma yana jin a rayuwarsa bazai iya rayuwa babu Bilkisu ba, zaiyi duk abinda zaiyi ya janyo hankalin danginsa su sota sannan yayi 'ko'karin dawo da ra'ayinta kansa, ya gama tsara musu rayuwa meyasa wannan 'kaddarar zata shigo? Yana isa gida ya tarar da mutane suna kwashe kayan Bilkisu, tsayawa yayi jikin motarsa ya kasa motsawa ji yake tamkar gidan ya kama da wuta, kayan dake cikin gidan su ke rage masa kewar Bilki yanzu an kwasheshi, tabbas Bilkisu da gaske take batada niyyar dawowa gareshi, amma yasan akwai soyayyarsa a zuciyarta saboda haka sai yayi iya yinsa a kanta. Barin wajen yayi zuciyarsa na 'kuna, kafin ya fita Hajiya ta kirashi, shiga palonta yayi yaga akwatina set 2 kowanne set 6pcs, "zauna" Hajiya ta fad'a tana fad'ad'a murmushinta, shi kuwa ganin akwatinan kad'ai ya bala'in tayar masa da hankali, Bilkisu ta tabbatar masa bazata dawo ba matu'kar yayi aure, ga Hajiya tace bazai dawo da Bilkisu ba sai yayi aure, wani irin masifa ce wannan ya shiga? Zama yayi Hajiya ta fara yiwa kursum da jumana order su bud'e masa kayan ya gani, har Sultana yau tana d'akin, kallon kayan tayi yanda aka had'a atamfofi da laces masu matu'kar tsada, 'karamar atamfa a lefen itace 6k, tagumi ta zuba tace "oh ai lefen Bilkisu baifi rabin wannan ba". Harara kursum ta wurga mata tace "wannan kuma ai harda ke aka ce baza'a mata mai yawa ba kuma zamaninta da wannan ai daban". Tashi Sultana tayi yace "lokacin bansan wacece ita ba, amma a yanzu na fahimceta kuma wallahi ta cancanci kaya fiye da wad'annan ma, kuma da ace zaku zauna ku fahimceta da yafi, kaya kuma tunaninku Saleh zaikai wula'kantattun kayan da kuka bayar ne?" "Shegiya munafuka kedai kinji kunya wallahi, kin za'bi matar da ta 'kwace miki miji, idan bazaki Mana m magana me amfani ba fice ki bamu wuri mara zuciya" Maimuna ta fad'a kamar ta daki Sultana, hanyar fita Sultana tayi ta kallesu tace "da zamanku kuke a gidan aurenku da yafi yawon zuwa cin shinkafa a gida, gidan miji babu". Bata jira me zasu ce ba ta fice abinta ta nufi part d'inta, tana fita Saleh yace "Hajiya, nifa gaskiya ba wani aure da zanyi banida niyyar aure yanzu, ko da zanyi aure Bilkisu Zan aura". "Zaka ciko kud'i 100k, sannan nan da farkon wata me kamawa za'a kai kayan". Tashi Hajiya tayi ta bar wurin shima ya fita ba tareda ya sake kallon kayan ba, har ya nufi part d'insa ya sauya hanya ya fita. Gidan Kawunsa wanda yake wakilinsa ya nufa, a tsakar gida ya sameshi da matanrsa suna hira. "Saleh kai nake gani haka?" Matar ta fad'a, sunkuyar da kai yayi cikin jin kunya, rabonsa da gidan ya kusa shekara, tashi tayi ta bar musu wurin kawun nasa yace, "Sannu Saleh ya mutanen gidan?" "Lafiya Lau baba kowa lafiya". "Ya iyalin naka?" Shiru Saleh yayi sannan yace "matsalar da ta kawo ni kenan Baba". Murmushi kawun nasa yayi yace "ni nasan banza bata kai zomo kasuwa, nasan haka kawai bazaka zo wajena ba saida bu'katarka, ina jinka ya akai". Saleh bai bar komai ba ya sanarwa kawunsa tun daga dalilin sakin har zuwa sharad'in Hajiya da kuma na Bilkisu, bayan ya gama kawun nasa yace "yanzu me kakeso nayi?" "Baba so nake ka taimaka ka yiwa Hajiya magana a dakatar da aurennan saboda wallahi banaso na sake aure". Shiru yayi alamar yana tunani sannan yace "to Saleh zan kwatanta Amma kai kasan halin mahaifiyarka idan ta kafe akan abu kamar kafiran farko, a idonka dai ta cimin mutunci gaban mutane ta zazzageni akan na wakilci aurenka, zanyi iya 'ko'karina dukda nasan a banza, gobe zanzo na gani". Tashi Saleh yayi tareda godiya ya bar gidan, baya son ma komawa gidansa hakan yasa ya d'auki hanya yayita tafiya ba tareda yasan inda zai nufa ba, sai 9 na dare ya koma gida, gidan empty babu komai haka ya zauna kan sassanyan tiles d'in ya jingina kansa jikin bango yana tunani, mota ya koma ya kwanta a ciki yayi bacci. Washegari kiran jabir yayi yace masa bazai shigo da wuri ba saboda zuwan kawunsa, kafin azahar kuwa kawun nasa yazo, Hajiya na ganinsa ta had'e rai tace "me kuma ya kawo ka?" "Maganar d'ana ce ta kawoni, haba surayya Saleh fa ba yaro bane ba kuma saurayi bane, Saleh ya wuce ace za'a tursasashi yayi abu, ki fita daga harkarshi da harkar iyalinsa ki dena masa dole akan aure, ba'a yiwa namiji dole a aure ko kuwa ki 'kare da kunya". "Bazan ta'ba jin kunya ba saidai kai kaji kunya, saboda ya'ki auren 'yarka shine kake haka? Bakasan ina sane da suwaiba da kakeso ka bashi ba? Saboda kaga ni da d'ana muna zaune lafiya shine zaka fara mana mummunana fata ko? To Saleh d'ana ne daga jikina ya fito dan haka abinda nace dole ne yayi shi, aure babu fashi kuma ni ban hanashi dawo da matarsa ba, idan har ya amince ya auri wannan yarinyar wallahi tallahi zan barshi ya dawo da matarsa, fa'kat, kai ayuba ka dena shiga abinda babu ruwanka, idan ka sake shiga harkata wallahi sai na maka wula'kancin da ban ta'ba maka irinsa ba, tashi ka ficemin daga gida, ko kuwa yanda kuka cinye gadon 'ya'yana haka kazo ka 'kwace gidan da ya rage mana eh?" Tashi yayi yana girgiza kai yace "Allah ya kyauta" ficewa yayi Saleh ya bishi a baya yana bashi ha'kuri, murmushi yayi yace "babu komai Saleh na saba da wannan cin fuskar tun kafin haihuwarku, bakuyi sa'ar uwa ba  Saleh domin tun tana amarya take cin mutuncinmu da mahaifinku, shiyasa zakaga duk bama shiga harkarta a hakan ma tace mun cinye gadon ku, babu komai dai amma shawarar da zan baka shine kabi mahaifiyarka, dukda tana da taurin kai da kafiya akan abinda takeso amma batada sa'ba al'kawari, idan kayi auren shine mafitarka na dawo da matarka, ita kuma matar taka zaka iya lalla'bata ko wani gidan ka kama mata ta zauna idan zata amince, nidai a nawa ganin kenan dukda mahaifiyarka bata kyautawa amma bijire mata zai iyabshafar rayuwarka". Sunkuyar da kai Saleh yayi sannan ya sake bawa kawu Ayuba ha'kuri ya rakashi har waje, yasan cewa maganar kawu Ayuba kad'ai zai iya d'auka a wannan lokacin ya tsira, daga Hajiya har Bilkisu fushi suke dashi kuma Bilkisu babu abinda zai dawo da ita gareshi yanzu, gara ya rage zafin yabi umarnin Hajiya idan an d'auki lokaci Bilkisu ta sauko yasan yanda zaiyi ya rarrasheta. ************ Na dena bari ma wani wasa yana shiga tsakanina da Aalee tun maganar da yayi na zai saukemin girman kaina ta hanyar aurena, ranar da mama ta dawo ranar muka shirya kai d'inki. Kwasar kayanmu mukayi muka nufi gidanmu gaba d'aya domin su gaida Mama, Aalee ba yanda baiyi ba akan na bashi yayi driving nace ba zamuje dashi ba suma kuma basumin musu ba, nayi tunanin Aunty ko Raudah zasu min magana akan halayyar da na canza towards Aliyu amma babu wanda yayimin, Saleh kuma...well ya shareni kuma hakan yayimin dai-dai yaje can ya fara shirin taresa da amaryarsa tunda an kwasomin kayana, tunda naga kayana an kaisu boys quarters na Aunty nasan cewa labari fa yazo 'karshe. Mun jima muna hira da Mama aka auren da taje, irin yanayin bikinsu a can, dariya muke sosai lokacin da take bada labarin amarya zata hau mashin ta bud'e saman rigarta tana rawa ana zubata mata kud'i a rigar. Bayan mun gama hira muka fita muka barta ta huta, d'inki muka kai ya bamu 10ays mu kar'bi duka kasancewar 2weeks zasuyi gashi har munci kusan 8days, dole suka 'kara kwanakin tafiyar tasu. Sunso na bisu gidan Aunty amma na'ki, a gidan mama muka zauna sai dare sannan Jabir ya maidasu gida, ina kallonsa yana shisshigewa Raudah, zan masa magana ne domin ita ba irin yammatan da yake bi bane. Haka muka ci gaba da zumuncinmu idan na dawo aiki naje gidan aunty na wuni sai dare sannan na koma gida har dai aunty ta fara gajiya ana magrib take korani. Ranar da zamu kar'bo d'inki ranar mahaifiyarsu zata zo su tafi tare, mota na bawa Aliyu ya d'aukota na tafi aikina, tunda ta sauka Raudah ke kirana ga Mum tazo tana so ta ganni, ina tashi daga aiki ko uniform ban cire ba na fita neman adaidaita sahu. Aliyu na gani da motata yazo d'aukana, sallama nayi na shiga ba tareda nace masa komai ba, munyi tafiya me nisa babu mai magana har muka tsaya a traffic light, kallona yayi sannan ya sauke idonsa 'kasa yace "I am sorry Bilkisu". Juyawa nayi ina kallon window ba tareda na amsa masa ba, cigaba yayi yace "nasan abinda na fad'a ban kyauta ba bai dace ace nayi miki wasa da maganar aure ba, inaso ki sani nayi hakan ne kawai saboda wasa amma ba da gaske nake ba, ke macece independent, kina tsaye da 'kafafunki, kina iya tsayawa kanki a kowane condition, yanda kikayi coping da mutuwar aurenki kin birgeni hakan ya nunamin you are stronger than I thought, kina son mijinki hakan ya bayyana 'karara a yanayinki, amma still you are pushing him away, babu wanda yake fahimtar halin da kike ciki amma still you are not broken kina masking real feelings naki saboda farin cikin family d'inki, you are fighting for your right and that's good, idan har gidan mijinki shine alkhairi a gareki Allah ya maidake, nasan bakida niyyar aurena saboda haka nima banida, kawai inaso mu zama friends ne saboda you are my role model and my sister's". Kasa furta komai nayi domin ban ta'ba tunanin Aalee ya fahimceni haka ba, na zaci yana sahun su Aunty masu ganin rashin zuciyata, for the first time ko nace 2nd ko kuma third, Aliyu ya birgeni ya kuma sanya naji dad'i, apart from Raudah shine mutum na farko da ya fahimci halin da nake ciki, Raudah ma gani take ina takurawa kaina. Kallonshi nayi nace "thanks for understanding me". Winking yayi yace "anytime.... friend, gobe zamu tafi banaso na tafi kina fushi dani nasan zakiyi missing wannan kyakkyawar fuskar tawa". Ya kare maganar yana shafa sumarsa, juya idona nayi tare da dariya nace "Banda hasken fata ai ko kallonka bazan iya ba, kana kallon mudubi kuwa? Kasan yawan munin dake fuskarka?" Dukan wasa ya kawomin naja gefe ina dariya yayin da aka sakemu, indai babu maganar aure Aliyu kam aboki ne na arzi'ki,nasan zanyi missing d'insu duka musamman ma shi. KUYI HA'KURI RASHIN WUTA YASA BANYI TYPING JIYA BA, BANSANI BA KO GOBE ZAN SAMU DAMAR YI. 42 Hira ke tasowa yayin Danna doshi palon, shiga nayi tareda sallama na tsaya cikin mamaki nace "Aunty Aisha?" "Oyoyo 'yata sannunki da dawowa" Aunty Aisha ta fad'a tareda hugging d'ina, kallona su Raudah sukayi amal tace "wai dama aunty B kinsan Mum?" "Ta sanni mana, rashin zumunci yasa baku san juna ba, Bilkisu ya kike ya aiki?" "Lafiya lau Aunty Aisha" na fad'a ina kallon Aunty, meyasa bata cemin su Raudah yayan Aunty Aisha bane? Dukda banida zumunci ta 'bangaren dangin mahaifina, ko taron sallah da akeyi ban fiye zuwa ba haka nan nake jina out of place duk da suna nunamin gata ba laifi, amma ban ta'ba ganin su Raudah ba a d'an zuwan da nakeyi sannan Aunty Aisha ma zan iya 'kirga sau nawa na ganta, kusan dai duk bamuda zumuncin. Mun gaisa sosai anan na san aikinta ita babbar likita ce wanda kasancewata mai aikin lafiya ya sake birgeta, kamar bata gajiya da surutu hakanan muka zauna muka yita yi tsakaninmu. Sai bayan magrib muka nufi kar'bo d'inkin mu, gidan Mama muka nufa anan muka bud'e kayan muka duddubasu, d'inkin yayi kyau sosai dukda ansha kud'i, 5000 zuwa 6000 a kan kowane set d'aya. Washegari ji nake kamar zanyi kuka saboda kewarsu, zuwansu ba 'karamin d'ebe min kewa tayi ba yanzu zasu tafi su barni da kad'aici. D'aga musu hannu nake ina danne hawayena yayin da suka shige departure, kiran Raudah na gani na d'aga tace "we will miss you too Bilkisu, amma tunda kinyi al'kawarin zakizo mana dan Allah karki karya al'kawari muna nan muna jiran ki". "INSHA ALLAH zanzo Raudah Allah ya kaiku lafiya". Jiki a sanyaye na juya, tun kafin na bar airport d'in naji wani emptiness na dibana, ni ba wata 'kawa ba a yanzu da zanyi shawara da ita, tunda nayi aure dalilin matsalar gidan Saleh tasa na dena Jan 'kawaye a jiki ina tsoron abinda zasu zo su gani, a haka har na yanke ala'ka ta da duk wata 'kawa tunda friends d'ina na makaranta sukazo Hajiya ta bani kunya a gabansu, ga sa'annina sunyi aure, haka dai zanci gaba da danne damuwata har Allah ya kawomin mafita. ************ *SALEH* Saleh ya saukar da kansa ga Hajiya, matu'kar dai hakan zai bashi abinda yakeso to zaiyi komai da tace, sati biyu kafin kai lefe ta takura masa yaje ya sake ganin Hadiyya, wannan karon da rana yaje. Zuba mata ido yayi cikin mamaki, meyasa Hajiya zata masa haka? Yaya zata had'ashi da wannan 'karamar yarinyar? Hadiyya yarinya ce da bazata wuce 17 ba, dan kyau tanada kyau irin black beauty d'innan idanunta farare ne 'kal gasu manya, d'auke kansa yayi yayin da ya kalli idanunta. Dukkansu sunshi shiru tana tsugune tana wasa da 'kasa da tsine shi kuma yana tsaye, dur'kusawa yayi taja gefe yace "kin gama makaranta kenan ko?" Gyad'a kai tayi yace "wacce?" "GGSS goron dutse" cije le'bensa yayi cikin bacin rai, meyasa Hajiya zata ce masa yarinyar ta gama FCE alhali secondary kawai ta gama, sannan kud'in da take fad'a shi bai ganshi ba dukda wannan ba damuwarsa bane, amma meyasa bazata nema masa yarinya me hankali ba? Tambayoyi yaci gaba da mata tana amsa masa, shekarunta kamar yanda ya canka 17, saura 5 months tayi 18, su bakwai ne a gidansu itace auta, aurensu kuma ita bata ma san mene so ba balle tace tana sonshi ko bata sonshi, lallai Hajiya ta had'a masa aiki, yaushe zai gama rainon yarinyarnan balle har yayi tunanin had'a ta da Bilkisu? Haka dai ya kare mata kallo ya tattara ya koma. Part d'in Hajiya ya nufa bayan sun gaisa yace "Hajiya naje na ganta amma 'karamar yarinya ce fa". "Eh to amma ai ta isa aure, tunda iyayenta sun baka ita ai shikenan ko? Nasan zaka iya ri'keta shiyasa na nema maka aurenta Kuma su iyayensu a haka suke aurar dasu 'kanana abunsu". Shiru yayi domin yasan bashida wani choice, har ya fita ta.kirashi tace "karka mata, saurin.yin aurennan shine saurin dawowar matarka". Shiru yayi mata ya fita domin a yanzu kam baisan ma direction d'in da rayuwarsa take bi ba. Bai fasa zuwa wajen Bilkisu ba ita kuma Bata fasa wula'kantashi ba, a haka har lokacin aurensa yayi, yayi komai kamar ango saboda al'kawarin da Hajiya ta d'auka na ta janye sai Hadiyya ta samu ciki, matu'kar ya kuka da ita kamar matarsa cikin so da kulawa to a wata uku zata barshi ya dawo da Bilkisu sannan tsyi al'kawarin bazata sake shiga harkar Bilkisu ba idan yaga dama ma ya nema mata gida a waje ta zauna, amma kar yayi tunanin zata so Bilkisu, hakan ya amince saboda yanda soyayyar Bilkisu ke dawowa sabuwa fil a kowacce rana, yayi missing d'inta sosai har abin ya fara affecting rayuwarsa. An kawo amarya amma ko kallon inda take baiyi ba, kwanciya yayi yana kallon ceiling tareda tunanin Bilkisu a first night nasu, da second da duk sauran rayuwar da sukayi takaici da nadama sunyi masa yawa, Hawaye ne suka zubo masa meyasa ya saki Bilkisu? Meyasa ya aikata babban kuskure a rayuwarsa wanda bai ta'ba aikata irinsa ba kuma yasan zai dad'e yana nadama, idan ma Bilkisu bata dawo gareshi ba to zai 'kare rayuwarsa yana nadama akan hakan. Kuka yaji a gefensa ya juya cikin mamaki, baiyi tunanin har yanzu batayi bacci ba, zama yayi itama ta tashi ta zauna kafin ya bud'e baki tace " saboda baka sona shine zaka kwanta kana kuka? Ai ba haka aka cemin anayi ba idan bazaka min abinda miji yakewa matarsa ba kawai ni ka sakeni na koma gidanmu". Dafe kansa yayi, matsalar auren yara kenan ita a karatun auren abu d'aya aka sanar mata?, Sauke numfashi yayi tareda goge fuskarsa yace "ki kwanta kiyi bacci banajin dad'i kema kuma nasan a gajiye kike". hard'e hannayenta tayi a 'kirji tareda turo baki batada niyyar kwanciya, wata harara take wurga masa, dafe kansa yayi domin ta fara Sanya masa ciwon kai yace "Hajiya kuma da wata matsalar ta had'a ni?" "Da matsalar mata mana, au nice ma matsalar bayan na taimaka na aureka? Hajiyarnan taka fa zuwa tayi ta dinga ro'kon umma akan a baka aurena banda haka ai kai ba sa'an aurena bane ko? Inaga ma bakada lafiya shiyasa babarka ta had'a aurena dakai gashinan kazo ka zubamin ido kamar ba namiji ba". *dedicated to FEENAT JAAFAR NOVELS GROUP, you are the best among the bests😉😉😉😉😉* 43 Ganin bazai iya jure yarintarta ba ya tashi, binsa tayi har ya fita ya koma palour, a kujerar da ya zauna itama ta kama gefe ta zauna, kallonta yayi tace "mene? Ance na bika sau da 'kafa sannan darena na farko bazan bari ka fita ba, wa ya sani ma ko wajen wasu matan zaka je?" Zare ido tayi tareda rufe bakinta tace "kai? Abinda nake gani a littafi zakayi ko? Zaka yimin tsawa ka d'auki key d'in motarka ka fita ka tafi wajen tsohuwar matarka kuyi iskancinku, sai gari ya waye ka dawo ka sameni ina kuka ko? To ni ba matan littafi bace wallahi ba kukan da zan maka kuma ba inda zakaje". Ji yayi tamkar ya d'aga hannu ya tsinka mata mari, numfashi yake saukewa cike da 'bacin rai yace "ki ficemin daga gani". "Babu inda zanje, bazaka wula'kantani ba kawai ranar da aka kawoni zaka fita isk......" "GET OUT!!!" Ya fad'a cikin 'kara, a firgice ta tashi daga kujerar cikeda tsoro, amma hakan bai rufe bakinta ba, kafin ta wuce d'aki saida tace "wallahi saida fad'awa Hajiyarka duk abinda kayimin, kuma Allah ya isa ka shiga ha'kkina". Ranshi yayi 'kololuwar 'baci, banda Hajiya ta janyo masa raini har wannan jaririyar ta isa ta kalleshi ta gaya masa magana? Ita Hajiya a duk matan dake dangi bataga wata kamilalliya ba mai hankali sai wannan yarinyar mai tsinannen surutu da bud'add'en ido? Idan har bataga girmansa ba a mijinta girman wa zata gani? Agogo ya duba yaga 1:30, 'kur'ani ga d'auko yana karantawa sautin Bilkisu na zuwa masa kai yana tuna lokutan da take za tayita karatun 'kur'ani musamman idan ta kasa bacci, yayi karatu sosai sannan yayi nafilfilu, bacci ya fara kan dardumar har lokacin sallar asuba yayi. Sallah yaje yayi sannan ya shiga d'aki, tashin Hadiyya yayi domin tayi sallah amma yana juya bayansa ta koma bacci, ya tashe ta kusan sau biyar sannan ta tashi shima tanata gunaguni, tana gyangyad'i tayi sallar da ka kalleta kasan cikin gaggawa take sallar, tana idarwa ta haye gado babu wani addu'a. Girgiza kai Saleh yayi yana kallonta, wannan wace irin macece? 'karara dai tarbiyya tayi 'karanci anan. 7:30 ta farka tana farkawa ta fara kiran waya, wanka tayi ta saka riga da zani na atamfa taci kwalliyarta, tayi kyau sosai banda hura hancin da take tana masa kallon banza. Hajiya ce tazo da kanta kawo musu abinci, "inata kiran wayark a kazo ka kar'bar muku abinci amma baka amsa ba shiyasa nazo da kaina" ta fad'a kafin ma a tambayeta, kallon Hadiyya tayi tareda fad'ad'a murmushinta tace " 'yata kin tashi lafiya". "Lafiya lau" ta fad'a tareda turo baki tana kallon Saleh, juyawa Hajiya tayi ga saleh tace "me ka mata". "Hajiya ban mata komai ba". "Ka fad'i gaskiya mana" Hadiyya ta fad'a tana harararsa, "Hadiyya fad'a min me ya faru?" "Hajiya har kusan dukana yayi jiyannan bakiga irin zagin da yayimin ba, wata tsawa da ya dakamin Allah na kusa fitsari". Had'e rai Hajiya tayi tace "abinda aka kawo ta kayi mata kenan? Kai ko kunya bakaji zaka dinga yiwa wannan yarinyar tsawa? Wallahi kar na sake ji ko kuwa ranka yayi mummunan 'baci". Juyawa tayi ga Hadiyya ta fara rarrashinta, suna haka kuwa sai ga sallamar mutane, tashi Saleh yayi ba tareda yayiwa kowannensu sallama ba ya fita, a 'kofa ya had'u da yammata fuskokinnan nasu kamar anyi 'barin hoda da jambaki, gaisuwa suka fara yi masa ya amsa da "lafiya" ya fita. Kai tsaye suka danna kai cikin d'akin, wata shewa suka saki kafin su ankara da Hajiya su zube su gaidata, sai washe baki take tana saka musu albarka, fita tayi suna tabbatar da ta fita d'aya daga cikinsu tace "wannan ba uwar mijinki bace? Dama har yanzu iyayen miji na zuwa d'akin matan 'ya'yansu washegarin kaisu?" Hakimcewa Hadiyya tayi kan kujera tace "abinci tazo kawomin wai ta kirashi ya kar'ba bai d'aga ba". "Ko dai tazo tabbatar da 'barnar da d'anta yayi ba" wata daga cikinsu ta fad'a, shewa suka saki tareda tafawa, tsaki Hadiyya tayi tace "kai nifa ba abinda ya faru". Zayyane musu abubuwan da suka faru jiya tayi tsaf, d'aya daga cikinsu tace "babu mamaki tausayinki yake dan ya ganki yarinya". Kwanciya tayi kan kujerar tayi supporting kanta da hannunta tace "amma tunda aka aura masa ni ai yasan cewa zan iya d'aukan nauyin namiji ko kuwa? Nidai banga alamun tausayi ba kawai wula'kanci ne" "Eh to dukda haka ki bashi lokaci nan da sati d'aya idan kikaga ba abinda ya faru wallahi ki tada balli" d'aya daga cikinsu ta fad'a kana kallonta kaga rigimammiya, tashi Hadiyya tayi ta zauna tareda dafe kanta tace "nifa na dad'e ina fasalta abinnan, na karanta naji labari kawai so nake naji da gaskene amma d'an rainin hankalinnan...mtsewww". "Kedai ki 'kara ha'kuri dan wallahi kika takura ma zaice ke 'yar iska ce, dan haka sati d'ayan ki jira ki gani". *********** *BILKISU* Kamar wasa ranaku gudu sukeyi, zuwa yanzu kam soyayyar Saleh ta zama tarihi a zuciyata dukda bazance babu ba amma nadena tunanin wai soyayyarmu zata dawo. Wata na shida kenan nake ciki zuwa yanzu mutane biyu sunyi approaching d'ina, saidai babu wani dogon bayani kai tsaye na sanar musu ni juya ce, babu bata lokaci duk suka kama hanyarsu, wannan shine abinda nake gudu domin idan za'a tara maza d'ari a cikinsu baifi biyar bane zasu iya aurena bana haihuwa saboda haka ma bansa tunanin aure a gabana ba. Ana gab da fara azumi gari ko ina a cike da mutane, idan Allah ya yarda cikin kwanaki biyu za'a d'auki azumi, naje kar'bo wa Mama sako a wata unguwa, bayan na fito naga wani mutumi a tsaye, da murmushinsa ya nufo ni. Sallama yayi na amsa yace "na dawo da yarana daga makaranta ne na hangoki kuma naga kamewarki...." Haka ya gama zuba surutunsa, su maza wai basuda lines ne kowa abu d'aya yake fad'a?, Bayan ya gama kod'a ni yace "dan Allah ko zan sami numberki?" Bashi numberta nayi mukayi sallama, ana gobe azumi kuwa sai ga kiransa yana neman address d'ina, tura masa nayi cikin 'kan'kanin lokaci sai gashi yazo. Bai 'bata lokaci ba ya sanarmin sunansa sa'ad maganar aure ce ta kawoshi kuma shi da gaske yake sannan bayaso mu 'bata lokaci, ya sanarmin yanada mata d'aya da 'ya'ya biyar, bayan ya gama bayani nace masa "To bansani ba ko zaka iya aurena gaskiya, saboda nidai bana haihuwa". Shiru yayi ina jira yayimin sallama yace "nidai a wajena wannan ba matsala bace saboda kusan dalilin da yasa zan 'kara auren ma kenan". "Kamar yaya? Ana aure dan a samu 'karuwa kai kana cewa haihuwar ce zata sanyaka aure?" "Matata ce gaskiya tana shan wahala wajen haihuwa sosai sannan ni kaina ina shan wuya, ba 'karamin kud'i nake kashewa ba idan zata haihu duk haihuwar biyar d'innan babu sau'ki, to nace tayi tsarin iyali...tacemin ita bataso shiyasa naga gara nayi aure". Kallonsa kawai nakeyi na ma rasa me zance, meyasa wasu mazan rashin imaninsu ya tsananta ne? Dan matarka tana shan wahalar haihuwa shine zaka 'kara aure? Idan kayi auren kuma sai ka dena kusantarta dan kar tayi ciki ko me? Wato nidai kawai advantage zai d'auka dani tunda bana haihuwa kawai naje na zamar masa abin wasa, ranar da matar tasa ta amince zatayi planning shikenan na gama yawo. "Kinyi shiru". Kallonsa nayi da niyyar nace masa 'ina tunanin rashin imani da son zuciya ne irin naka' amma na canza ra'ayi nace "tunani nake da ace kuma ina haihuwa me zakayi?" Sosa kansa yayi yace "sai nabi wata hanyar da zaki amince ki aureni ba tareda haihuwa a gidana ba, amma tunda an samu hakan ai kinga komai yazo da sau'ki". Sunkuyar da kaina nayi yace "to yanzu akan wacce magana muke" Banaso nace masa a'a saboda tsoron halin mazan yanzu saboda haka nace masa "Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi". Da wannan muka rabu, nan ya fara damuna da kira, babban abinda ke bani takaici shine bashida hira sai complain akan matarsa, bayan haihuwar da take yawan yi kusan duk shekara, haihuwa biyar, sannan bata kula da yaran yanda ya kamata, wai idan ya aureni ma kwaso su zaiyi ya kawomin. A hankali nake ja baya dashi, a azumin ma 'ko'karin hanani ibada yake ana shan ruwa zai kirani sai yakai awa ki fiye da haka, daga baya nadena d'agawa sai nayi sallah, nan ma sai mukai 12, duk yabi ya isheni. Kamar wasa anyi azumi goma, ana shan ruwa Aliyu ya kirani muka gaisa, a speaker ya sanya wayar muka fara hira dasu Raudah, bayan komawarsu naje nayi kwana biyu saidai lokacin Aliyu yayi tafiya bamu had'u ba. "Dan Allah Aunty B kizo mana Shan ruwa sai kiyi sati d'aya" amal ta fad'a cikin shagwa'ba, dariya nayi nace "amal ai ba'a tafiya da azumi ki bari dai da sallah nazo". "A'a mu zamu zo da sallah ai, dan Allah kizo kiyi mana sati wallahi muna missing d'inki". "A'a nawal bazan zo ba sai bayan sallah insha Allah". Shiru nayi inaji suna rad'a wa jannat tace dan Allah nazo, muryar Aunty Aisha naji kafin mu gaisa suka fara ro'kon ta, kar'bar wayar tayi tace "Bilkisu ya kamata kizo mana yaushe Zaki zo?" "Aunty Aisha bayan sallah...." "A'a Bilkisu a cikin satinnan ki fitar da rana, zan miki booking flight". "To Aunty Aisha 44 Samun Jabir nayi baba yana masa fad'a, sunkuyar da kaina nayi ina 'ko'karin shigewa d'aki Mama ta kirani tare da min alamar na zauna, zama nayi na kasa kunnuwa baba yana ma Jabir fad'a. "Sha'kiyancin naka ya kai har ka nemi 'ya'yan abokaina biyu? Yau ina kasuwa dukkansu suka zo lokaci d'aya domin su min maganar ya kamata a tsaida magana, ka sani naji kunya na rasa ma me zance maka, wannan shine karo na 'karshe da zance ka fito da mata kuma a yanzu nakeso ka fad'amin yarinyar da kakeso da aure". Murmushi nakeyi domin ni kaina halin jabir ya isheni, numbobin 'yammata a wayarsa sunfi talatin, duk garin da yaje sai yayi 'yammata uku zuwa sama anan garin namu kuwa sai hamdala, a friends d'ina ma ya nuna yanason biyu a cikinsu. Kanshi a 'kasa yace "Baba kayi ha'kuri ka bani ko da sati biyu ne nayi al'kawarin zan fito da mata". "Na baka sati biyu yakai sau uku, na baka wata guda sau biyu, a yanzu nakeso ka fito da matar aure gobe gobe ni da kaina zanje na samu iyayenta, idan kuma baka da ni inada wadda zan baka". Cikin sauri Jabir yace "akwai Baba". "Wacece?" "Um, wata ce a can sokkoto lokacin da mukaje....." Dakatar dashi Baba yayi yace "zancen banza zancen wofi, na lura kai baka da girma sai na jikinka saboda haka ni na fitar maka da mata da kaina, idan ka tashi aiki kake gidan Habibu abokina". "Baba zanje had'eja aiki gobe" Jabir ya fad'a kamar zaiyi kuka, ya tsani auren zumunci shi a wajensa duk matan danginmu munana ne sannan yafi ajinsu, gashinan Allah ya kamashi. "Idan ka dawo sai kaje wajen nasa yana jiranka, zan masa magana shi zai had'aka da yarinyar da ta dace, Bilkisu ya aiki?" "Lafiya lau Baba ya kasuwa?" "Alhamdulillah, Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya dafa miki sannan Allah yasa wannan abu da za'ayi ya zamo miki alkhairi". "Amin Baba" na amsa cike da mamaki, me baba yake nufi ne?, Kallon Jabir yayi yace "kana gani dai 'kanwarka yanda tayi mana biyayya akan maganarnan, ya kamata ka fara koyi da ita, Allah yayi muku albarka amma Jabir ya kamata ka yiwa kanka fad'a". Fita Baba yayi Jabir shima ya fice, komawa gefen Mama nayi na zauna nace "Mama maganar me Baba yakeyi?" "Dama nace miki zamuyi magana idan kin dawo ko? To magana ce dai ta aure maman Raudah ta kirani ta fad'amin duk abubuwan da suka faru tsakaninki da wad'anda ke zuwa wajenki wanda ni kika 'boyemin, ta sanarmin bazai yiwu a barki kici gaba da fuskantar wula'kanci ba zasu had'a aurenki da Aliyu d'anta". Shiru nayi na zubawa hannuna ido, banyi wani mamaki ba akan had'a aurena da Aliyu domin a jikina na jima ina jin alamun faruwar hakan tun dawowata daga Abuja saidai bana shirin aure yanzu musamman auren Aliyu, a wannan 'kan'kanin lokacin ta yaya zai samu soyayya ta da yardata? "Mama kuma me kikace musu" na fad'a ina kallonta, murmushi tayi tace "to Bilkisu dangin mahaifinki ne fa, bar mana ke da sukayi sunyi namijin 'ko'karin da ba kowane dangin uba ne zasuyi ba, banida ikon hanasu iko dake a yanzu musamman da wannan abun ya faru, idan kuma bakyaso tacemin zasu zo ya kamata ma ace sun iso idan sunzo saiki sanar mata". Mama na rufe baki kuwa sai ga sallamarsu "Aunty B!!' shine abinda na fara jiyowa, kaina amal da nawal sukayo saida Mama taja gefe karsu fad'a kanta. "We miss you" suka fad'a a tare, tsaki Raudah tayi tace "jiya fa kun ganta wani missing kuma?" "Haka ake gaisuwa?" Naji muryar Aunty Aisha, da sauri suka zube a 'kasa tareda gaida Mama, tashi mama tayi ta bar mana kujerar suka fara bani labarin sunje kallon wata kilisa, muna cikin hirar Aunty Aisha ta kirani tareda nufar d'akina, da alamu duk sunsan maganar da zaayi. A bakin gado na samu Aunty Aisha na zauna a 'kasa, murmushi tayi tace " 'yata dawo kusa dani mana". Zama nayi gefe ta matso yanda space d'in dake tsakaninmu baida yawa, kaina a 'kasa tace "Mama ta miki bayanin komai ko?" Gyad'a kai nayi alamar eh tace "Bilkisu kar kiji tsoro idan har wannan had'in da mukayi bai miki ba ki fad'amin, dukda cewa I want the best for you amma banaso nayi abinda zaki takura ko kiga an miki dole, na duba wannan lamarin ne ta fuska mai kyau, zaki ci gaba da fuskantar irin wannan wula'kancin ne Bilkisu har tsawon lokaci, yanzu unguwarnan har sun fara sanin bakya haihuwa, da zarar anzo bincike suke fad'in haka, muna zaune da Allah ya rufa mana asiri bazai yiwu muna kallonki ana miki wannan tonon asirin ba, idan har za'bin da nayi miki na d'ana ya miki ki fad'amin idan bai miki ba kar kiji nauyin sanar min nima uwace a gareki bazan so abinda zai cutar dake ba". Ko da na duba maganganun ta naga gaskiya a cikinsu, tabbas sai duniya ta gama sanin ni juya ce kafin a samu wanda zai aureni, ko ba komai auren Aliyu sutura ne da rufin asiri, amma zai iya zama dani a haka? Kallon Aunty Aisha nayi nace "Aunty Aisha shi ya amince da aurena? Kuma zai iya zama dani a hakan?" Dafa kafad'ata tayi tace "mun gama wannan maganar ya amince kuma he's more than happy da wannan had'in, domin ya jima yana cewa bayason ya auro bare ya kawota cikinmu saboda haka mu za'ba masa mata a dangi, sai kuma gaki, Aliyu bashida matsala ke nake tunani zaki iya zama dashi? Ban sani ba ko saboda tsohon mij......" Katseta nayi cikin sauri nace "Aunty Aisha na amince da za'bin da kuka min nasan bazaku ta'ba min za'bin da zai cutar dani ba, zan zauna da Aliyu indai zai iya zama dani". Farin ciki sosai ya bayyana a fuskarta tace "Allah yayi miki albarka 'yata Allah ya sanya alkhairi da albarka a rayuwarki, daga yanzu zuwa sallar layya ku fahimci junanku bayan sallah kuma sai a fara maganar aure ko?" Nidai bance mata komai ba ta sake sanyamin albarka ta fita, na kai mintina biyu a zaune ina processing komai kafin nima na fita, da alamu dai ni da Saleh sai tarihi dukda naso naga yanda 'karshen labarinmu zai kasance saidai wannan kamar hutu ne Allah ya kawomin, ko yaya kuma rayuwata da Aliyu zata kasance? Sai 10 sannan Aunty tace su tashi su tafi, gaba d'aya 'kin binta sukayi bata sani ba ma har kaya suka sako a mota. Jabir ne ya maidata gida na shiga d'akina domin gyara mana wajen kwanciya, gaba d'aya twins sun'ki barina nayi komai wai su basu so Auntynsu ta wahala, shimfida nayi kan carpet saboda gadon bazai ishemu ba amma suka ce su matar yaya fa bazata kwana a 'kasa ba, dariya suka bani kawai na bisu da ido. Tun kafin su farka na farka, a hankali na fita na nufi kitchen taya Mama breakfast, sanar mata nayi na amince da auren Aliyu ta sanyamin albarka sosai itama, so far dai alkhairi nake gani Allah yasa ko bayan auren ma haka zai kasance, Allah ka bani soyayyar dangin mijin da na rasa a baya. Bamu had'u da Aliyu ba sai ranar da zasu koma, shima gaisawa mukayi sama-sama yace idan suka isa gida zai kirani. Bayan awanni biyu kuwa sai ga kiransa, amsawa nayi tare da yin shiru, bayan mun gaisa yace. "Bilkisu kiyi ha'kuri, nasan bakya sona kuma nasan kin amince ne kawai saboda nauyin Mum, amma idan kina ganin zaki cutu ni zan sanarwa Mum da kaina a soke wannan had'in, banaso ne ace kin aureni kina kuma tunanin tso....." Na gaji da jin ana ambaton Tsohon mijina saboda haka na dakatar da Aliyu nace "Kar ma ka sake ambaton wani tsohon mijina, Aalee wannan ra'ayina ne nasan za'bin gata suka min kuma na amince, tsohon mijina tsohuwar rayuwata ne yanzu sabuwar rayuwa zan fara". Dariya yayi 'kasa-'kasa sannan yace " yanzu fa soyayya zamu fara ko?" Hakan ya bani dariya nace "eh to ga alamu nan". Gyaran murya yayi yace "nifa in fad'a miki gaskiya? Banida 'kwa'kwalwa ta fannin soyayya duk 'yammatan da nakeyi tsorata su nake suna guduwa saboda tsabar rashin iya soyayya ta". "Eh to amma ai ka iya mu'amala da mutane wannan shine step na farko a soyayya ko? " "Hakane amma zan 'ko'karin nuna miki soyayya iya iyawa ta, banaso ki d'aukeni a mijin had'i inaso muyi zama real ba fake one ba, Kinga kuwa dole na koyi iya nuna love". Girgiza kai nayi tamkar yana kallona sannan nace "Aalee no need to rush, nima banaso kayi treating d'ina da tausayi muyi working komai a hankali har mu fahimci juna, ko da bamu gama fahimtar juna ba idan munyi aure munada lokaci, for now Kar mu d'aurawa kanmu abinda bazamu iya ba, duk abinda zuciyarma bataso ko bata shirya ba kar kayi bazanga laifinka ba". "To shikenan Aunty B" ya fad'a cikin zolaya, murmushi nayi nace  "ina twins?" "Suna gida, ni ina office ne na kiraki tunda muka koma suke takuramin akan na kiraki ni kuma banaso suna saka matata aikin wahala". "Aikin wahala kuma?" "Eh mana, suyi ta saka ki magana har ki gaji saboda haka nace baza'a kiraki ba sai dare". "Amma kai gashi kana sanyani maganar ai". Ina gama fad'an maganar kuwa sai ga hamma, dariyar Aliyu naji sannan yace "da alamu nima ina saki gajiyar ko? Bye take care duk wanda ya kulaki a titi kice ke matar commissioner of police ce". "Shikenan zan fad'a sir". Shiru ya d'anyi sannan yace "bye motocinmu sun" kiss yayi cikin wayar sannan ya sake cewa "bye take care". *** Rana akace bata 'karya to fa yau ranar tawa ce, a yau ne zan zama Mrs Aliyu shamsuddeen, ba wani taro akayi ba family ne kawai amma sun cika gidan ma'kil, wannan karon a gidan kakannina na 'bangaren uba aka d'aura aurena, a yau dai naga mahaifin Aliyu balarabe ne sosai domin har harshensa a karye yake, irin 'yan Lebanon d'innan ne da talauci ke korosu daga 'kasashensu suzo nan su fimu iya neman kud'i su Tara arzi'ki yayin da hausawanmu ke tunanin Allah ya baku mu samu. Inaji a kunnena aka d'aura aurena da Aliyu kan sadaki 50,000, jikina ya mutu domin wannan karon zan bar garin gaba d'aya nabi mijina Abuja, shikenan ni da Mama sai lokaci-lokaci. Hawaye naji na neman zubomin na danne yanzu ina fara kuka za'a samu masu tunzurani, kwana biyu zanyi anan jibi zan wuce Abuja a can zan tare, duk lokacin da na kawo maganar rashin haihuwata sai Aliyu ya canza maganar, hakan yasa na damu ina ganin kamar bayason rashin haihuwar tawa ne. A ranar su Raudah da Aliyu duk suka koma gida, kafin su tafi suka kaini gida. Saleh na samu da Jabir suna magana akan kasuwancinsu, cikin 'bacin rai naji yace "wannan ba excuse bane Saleh, akan wannan matsalar da ka raina zaka jawo mana asarar kusan miliyan guda ko nace ma ka janyo mana, menene amfanin baka ajiyar takardarnan idan har zata wula'kanta?" Kallon Saleh nayi naga ya rame sosai har ramar tasa ta bayyana, idanunsa kamar ya kwana uku ba bacci sannan fuskarsa 'karara damuwa ta bayyana, jingina yayi a bango yace "idan nasan zata 'kona takardun zan kar'ba ne? Allah yayi ba alkhairi bane muyi aikin nan banga abin tada hankali akai ba". Sallama nayi musu tareda gaisuwa, kallona Saleh yayi sannan ya juyar da kansa ba tareda ya amsamin ba, shima Jabir yauwa yacemin ya juya suka ci gaba da hirarsu, ko wace irin mace Saleh ya aura kuma Allah masani amma ga dukkan alamu baya samun farin ciki, ko da yake meye ruwana a ciki?" Ranar da zan tafi Abuja rakiya sosai akamin airport, duk matan baba saida suka rakani har su zulaihat sunzo min rakiya, nasha kukana sosai kafin na tafi na barsu a tsaye, a zuciyata ina fatan Allah yasa zuwan da zan musu na farko suka murmushi da walwala a fuskata *Inaso na gama book d'innan kafin shekarannan ta 'kare😫 amma kuma labari sai jana yakeyi, ina fatan Allah ya bani ikon kammalawa before 31st December, tnx guys* 45 Wata lafiyayyar dinner aka had'a a can Abuja, sai 12:30 sannan muka bar wurin muka wuce gidan Aunty Aisha. Bacci ne sosai a kaina amma su babu alamun bacci a tare dasu, tashi nayi idona na rufewa nace "to saida safenku bacci nakeji". D'akin Raudah na nufa Aliyu ya kira sunana, juyawa nayi yace "Ina zakije? Ai gida zamu wuce". Kallon Raudah nayi na kalli Aunty Aisha, tashi yayi tareda mi'komin hannu alamun na taho mu tafi, no'kewa nayi na 'kara sauri domin na shiga d'akin, takunsa nakeji a bayana cikin sauri, ban ankara ba naji ya ri'ko cikina ya raba 'kafafuwana da 'kasa, kunya ce ta kamani na fara wutsil-wutsil da 'kafa su Raudah kuwa ba abinda sukeyi sai dariya, maganarsa naji a bayana yace "da ace inada 'karfi a kafad'a zan saka ki". A hakan ma naga 'ko'karinsa domin ya ri'keni kamar wata 'karamar yarinya, ture hannunsa nayi da 'karfina nace "Dan Allah ka sakeni su Raudah fa na kallona kar Aunty ta fito". "Mum!!", Bata amsa ba ya sake kiranta, fitowa tayi tace menene? "Wai matata bazata bini gidanmu ba". "Ka ajiyeta, ai dama anyi sai gone za'a kaita". Ajiyeni yayi da sauri kuwa na shige d'aki ba tareda na juya ba, ni idan tawa za'a bi nayita zamana a nan. "To Aunty na bita d'akin kenan?" Na jiyo maganar Aliyu, shiru naji Aunty Aisha tayi masa Raudah ce ta amsa masa tace "kar ka shigar mana d'aki ko kuwa mu barta anan sai tayi sati". Toilet na shige na d'aura alwala, su fa maza basusan kunya ba, gado na haye cikin 'kan'kanin lokaci bacci ya d'aukeni. Wani 'karamin wuni akayi yau inda 'kawayen Aunty Aisha suka zo, Raudah da twins ma sun kira friends d'insu, nayi shigata cikin lace riga da skirt na d'anyi kwalliya, nunawa mutane Aunty ni takeyi yawancinsu suna sa min albarka yayin da wasu saidai kawai su kalleni su gyad'a kai, ko kud'i ne ya musu.yawa har ya danne walwalarsu oho. Abu d'aya na lura dashi wanda ya sake bani tsoro da auren Aliyu, ba 'karamin arzi'ki Allah yayi musu ba nayi zaton motocin da yake saidawa irin ka siyo ka sayar d'innan ne amma inaa, kamfani guda ne dashi motoci harda na had'a titi yake saidawa. Mahaifinsa ya bar masa business d'in motar a hannunsa tun bayan ya kammala karatunsa, kuma Allah ya sanya masa albarka har wata plaza ya bud'e a can Abuja, duk shagunan dake ciki an kama kuma yanda nakejin labarin suna kar'bar hayar kusan 200k ko fiye da haka a duk shekara, duk wannan labari a yau na sameshi saboda 'kawayen Aunty Aisha basuda abun yi sai bragging akan arzi'kinsu, itama kuma ba'a barta a baya ba. Tsabar gulma duk matan suka zauna har bayan la'asar lokacin da za'a kaini, gida kam da na ganshi saida na hadiyi miyau domin kyawun gidan da girmansa ya isa ta waje, wani irin gate ne daga waje gaba d'aya baifi tsayin mutum ba, daga nan zaa wuce makeken compound sannan a shiga main house, gabana fad'uwa yakeyi saboda bansan kayan d'akin da aka min ba, Allah yasa ba tsofaffina aka kawo ba domin zanji kunya gaban 'kawayen Aunty Aisha, maybe ma su fara gorantamin ko su fara mata habaici, ugh kad'an daga illar auren me kud'i dukda nima alhamdulillahi ba talaka bace amma maganar gaskiya kaf abinda na mallaka baifi kud'in mota d'aya a kamfanin Aliyu ba. Ko da muka shiga palour kasa barin lullubin kaina nayi, palour d'in sai ka taka stairs zakayi 'kasa  sannan ga kujeruna a wurin, roynd ne shape d'in palour d'in haka kujerun nawa ma round ne sunyi matu'kar kyau, ga wata tafkekiyar tv ta cika bango, d'aga kaina nayi naga wata chandelier wadda tayi yanayi da ta frozen, da sauri na sauke kaina jin Raudah ta makeni a kaina, ban gama kallo ba aka shiga dani d'aki, saida na d'auke numfashina ganin had'uwar d'akin, ni Bilkisu anya  zan iya zama a wannan gado? Bedsheet ne fari 'kal a kan gadon sai wasu red flowers a jiki basufi 6 ba, a hankali na zauna naji katifar ta wani lotsa, hmm yau akwai bacci me dad'i. An gama ganin gida kowa sai zazzare ido yake domin gidan Aliyu ya matu'kar had'uwa, gaba d'aya tsarin gidan na 'kasashen waje ne ga girma ga kyau. Bayan 'kafa ta d'auke daga Ni sai sisters d'in Aliyu na cire mayafina, hannuna Raudah taja tace "zo kiga" Wani labule ta bud'e sai ga glass babba ya bayyana, sakin baki nayi ganin wani had'add'en garden ga kujeru irin na gini da akeyi sannan ga flowers masu matu'kar kyau wajen an shimfideshi da grass carpet. Gefena Raudah ta tsaya tace "anfi shekara goma ana ginin gidannan tun farkon dawowar Ya Aalee daga karatu, shi ya fara bayyana yanda yakeso gidan ya kasance sannan idan har yayi tafiya yaga wani abu da ya birgeshi sai yazo yace ayishi, ai bakiga komai ba ma a gidan da kanshi gobe zai nuna miki sauran wuraren, sai ma Kinga kitchen d'inki wallahi kamar a can, daga kitchen kana hango palour......" Kafin ta 'karasa mukaji maganar Aliyu yace "au ke aka bari ki mata hudubar? Oya oya a ficemin daga gida yanzu tunda nayi mata banason sake ganin kowaccenku a wannan d'akin". Shigowa twins sukayi da saurinsu sukace "Aunty B toulet d'inki fa...." Katsesu Aliyu yayi tareda kama hannunsu ya fita dasu yana cewa "oya oya a tafi gida sai watarana saura naga 'kafar wata a gidannan gobe". Babu sallama haka ya korasu, Allah yasa gidan babu nisa zuwa gidansu da 'kafa suka tafi ina hamgosu ta glass d'in dake d'akin. Bayan ya fitar dasu ya dawo, mayafina na yafa na zauna sai yanzu gabana ya fara fad'uwa, yana sallama ya dafe kai yace "shit!!" Na bar abincinmu a office wallahi". Bance masa komai ba yace "na aika a siyo mana 'yar kazarnan ta zamani da ake kaiwa kowacce amarya to aiki yayimin yawa gashi ina d'okin ganinki na manta, sorry bari naje na sake siyowa, amma da nisa wurin ko na kaiki gida idan na dawo sai na d'aukeki?" Girgiza kai nayi nace "ba sai ka siyo ba naci abinci kafin na taho". Ri'ke 'kugu yayi kamar wata mace yace "tabd'i, so kike ace aurena dake baiyi ba sai an sake? Gaskiya bazamu wayi gari ba a gidannan sai kinci kaza". Lissafi nayi naga nidai bazan iya zama a wannan gidan aljanun ni kad'ai ba, sannan banaso na koma gidan Aunty Aisha sannan na dawo, sake girgiza masa kai nayi nace "wallahi ka barshi banaso na yafe". Zama yayi gefena tareda dafa kafad'ata yace "da gaske? Dama ana yafe kazar amarci ai na d'auka har biyan bashi akeyi". Sunkuyar da kaina nayi nace "sai ka biya bashin ai". "Shikenan amma dukda haka bari na duba mana kitchen ko akwai d'an abin motsa baki". Bai jima ba ya dawo da champagne da fruit, ajiyewa yayi yace na sauka muci ba musu na sauka, muna Shan fruit d'in yakemin bayanin yanda aka Gina gidan da hanyoyin da yake samun ideas d'insa, yayi yawo 'kasashe da dama har yake cewa nima zai tafi dani wasu 'kasashen idan zaije. Bayan mun gama cin abinci ya fita, hakan ya bani damar sauya kayana zuwa na bacci, doguwar riga na saka wadda zan kwanta comfortable sannan na haye gado, wata ajiyar zuciya na ajiye jin yanda katifar da bedsheet d'in keda wani laushi na daban, lumshe idona nayi take naji bacci yana neman d'iba na. "Ba dai kinyi bacci ba" naji maganar Aliyu, bud'e Ido nayi nace "banyi ba". Ya sauya kayansa shima zuwa kayan bacci riga da wando. Kwanciya yayi ya jani jikinsa ya kwantar da kaina a 'kirjinsa, ban janye ba dukda zuciyata ta fara bugawa da sauri, bayan ya kwanta comfortably yace min "idan zaki had'a aurenki na baya da wannan a ranar da aka kaiki wanne yafi miki?" Shiru na d'anyi sannan nace "to bansan meyasa kakeson yawan ambato aurena na baya ba amma  babu had'i, wannan an kawoni gida na alfarma wanda har na fara tsoron ranar da za'a min gori wancan kuma an kaini family house, mintina na na farko na fara sanin matsayina a gidan gaskiya idan za'bi zanyi zan za'bi wannan dukda Ina jin tsoro". Tallafo ha'bata yayi muka had'a Ido yace "me yake baki tsoro?" Tashi nayi daga jikinsa na kishingid'a a gefe, har ga Allah har yanzu ban fara jin Aliyu a matsayin miji ba, nace "Naga irin mutanen da family d'inka suke mu'amala dasu, mutane ne masu bala'in arzi'ki da wula'kanta mutane, a dinner da akayi I feel so out of place, kayan da na sanya mahaifiyarka ce tayimin su, abokananka sun bani tsoro sannan kud'in da aka zubar a wajen ya bani tsoro, duk ranar da abokananka, 'kawayen Mum, ko ma : kawayen su Raudah sukaga daga inda na fito sai na fuskanci matsalar gori dukda babu talauci a tattare damu muma, sannan irin 'yammatan dake wajen nayi mamakin da baka auri d'aya daga cikinsu ba, ka tabbata kana son aurena bayan duk wad'annan had'add'un matan da kake gani? Sune irinka ni daban ce". Maimakon ya amsa min sai ganin fuskarsa nayi dab da tawa, kallon lips d'ina yayi sannan ya kalli idona, kasa motsawa nayi take hannuwana suka fara gumi, murmushi yayi kafin ya d'ora lallausan lips d'insa a kan nawa, hannayensa shafar bayana sukeyi a hankali yake isarmin da sa'konni, hannunsa cigaba yayi da shafar bayana a hankali tamkar massage. Bayan 'yan da'ki'ku ya janye tareda had'e goshinsa da nawa, d'ago fuskata yayi yace "na za'beki saboda dukkansu irina ne ke kuwa daban kike, kowa yanason canji a rayuwarsa ko? Kema ya kamata ki d'auki aurena a matsayin gwada wata rayuwa ta daban". "Okay" na fad'a tareda sauke numfashi, hannunsa ya sanya ya shafi lips d'ina yace "u smell amazing". Murmushi nayi zuciyata tana dukan uku-uku, "can I try again" ya tambaya tareda turo baki kamar 'karamin yaro, wow he look so cute, murmushi nayi na gyad'a masa kai alamun eh, had'e gira yayi yace "this time kiss me back otherwise you will break my heart". Cije le'bena nayi cikin rashin sani, kafin na ankara yayi straddling d'ina yayin da lips d'inmu ke bada wani sauti na daban, hannayensa take suka fara isar da sa'konni daban daban, da alamu dai Aalee so yake ya goge Aliyu daga 'kwa'kwalwata a wannan lokaci kuwa tabbas yayi nasara....... ********* *SALEH* Yana kai jollof din shinkafar bakinsa 'karnin kifi ya daki hancinsa, cikin sauri ya maida abincin cikin plate tareda ture abincin gefe, ita kuwa Hadiyya sai cin abincinta takeyi, ganin ya tashi daga dining d'in ya sanyata d'ago kanta daga farantin tace "Ban gane ba, wai yau ma bazaka ci abincina ba?" " 'karnin kifi ke tashi a ciki". Dukan dining table d'in tayi a fusace tace "wannan wani irin wula'kanci ne? Kwanana goma kenan a gidannan amma kullum nayi girki sai kace baiyi ba, nayi miya kace tayi d'anya, na maka farfesu kace 'karni, nayi tuwo kace d'anye, sannan har yanzu baka bani ha'kkina na aure ba wallahi na gaji wajen Hajiyarka zan kai 'kararka". Kafin ya bud'e baki ta fice da gudu, zama yayi ya dafe kansa dake masa ciwo sosai ga yunwa, da safe chips tayi masa da kwai, 'kwan bai soyu ba ga 'karni, sannan chips d'in ya kusan 'konewa har wani d'aci yake masa a baki, haka ya fita ya wuni yana aiki sai wajen azahar yaci gurasa, sannan yanzu ga wannan pre d'anyar shinkafar da uban 'karnin kifi a ciki. Hadiyya shiga d'akin Hajiya tayi tana kuka wiwi, a tsorace Hajiya ta fito daga bedroom tace "Hadiyya me ya faru kike kuka haka?" Zama Hajiya tayi Hadiyya ta zauna a gefenta tareda d'aura kanta a cinyar Hajiya, Cikin kuka tace "Hajiya na gaji da halin Saleh, ba abinda yakeyi sai wula'kantani, duk abinda nayi yace baiyi ba, baya cin abincina". Cikin rarrashi Hajiya tace "kiyi ha'kuri bari na kirashi". Tashi tayi ta zauna ta chone baki tace "kuma Hajiya har yanzu bai bani ha'kkina ba". Hajiya Bata fahimta ba tace "Zan masa magana ai bazai yiwu ya zauna dake yana 'kin cin abincinki ba". "Nifa Hajiya ba wannan ne yafi damuna ba, ki ta'bani fa bai ta'ba yi ba balle ya sanni a mace, nidai ayi masa magana wallahi ai wannan cin zarafin ne ko?" Tsit Hajiya tayi ta zubawa Hadiyya ido, wace irin suruka ce zatazo da irin wannan magana kwana goma kacal da aure? Ko a jikinta Hadiyya taci gaba tace "dukda kwana uku da suka wuce ina fashin sallah har ma yanzu, amma ai ya kamata ace ma tun ranar da aka kawoni ya kwanta dani ya sanni a mace amma dan Allah mutum yayita kallon miji kamar hoto? Yanzu idan na nemeshi Sai ace nayi rashin kunya". 46 Zubawa Hadiyya ido Hajiya tayi domin bata ta'ba tunanin jin haka daga bakin Hadiyya ba, ba ma matsayinta na suruka ba ko dan yarintarta. Hajiya dai tsit tayi kafin ta d'au waya ta kira Saleh sai gashi ya shigo da sallamarsa, zama yayi a 'kasa ya gaida Hajiya kafin tayi magana ya mi'ka mata plate cile da jollof d'in Hadiyya yace "Hajiya nasan akan na'ki cin abinci ne ta kawo 'karata, ki ci abincin kiji ya yake". Spoon d'in da ya sako a plate d'in ta d'auka tana kai bakinta ta yamitse fuska a haka dai ta tura abinci, 'kayar kifi ce ta fara mata sallama a bakinta, da 'kyar ta tauna abincin ta had'iye sannan tace "to ai ba wula'kanta abincin ya kamata kayi ba gyara zaka mata". "Hajiya na gyara mata tun ba yanzu ba amma babu wani canji". Kafin Hajiya tayi magana Hadiyya tace "kai nifa Hajiya rabu dashi idan bazaici abincina ba yayita zama da yunwa damuwarsa ce, akwai restaurant kala kala a titi idan yunwar ta isheshi yaje can ya ci abinsa ko a jikina, ni matsalata shine rashin bani ha'kkina". Cikin mamaki ya kalli Hadiyya sannan ya kalli Hajiya, gaba d'aya Hajiya ta ma rasa ta inda zata fara, ganin sunyi shiru yasa Hadiyya dafe 'kirji tace "na shiga uku, kardai ba lafiyayye bane kika had'ani dashi, aikwa bazan iya zama ba wallahi, tabd'i jan". Jikin Hajiya yayi sanyi shi kuwa ko a jikinsa, maganinta kenan da ta'ki Bilkisu yarinya mai kunya, har take mata sharrin tana yawo tsirara a cikin gidanta, yau gashinan ta samu sirika me kawo mata manyan maganganu. Da 'kyar ta daure tace "Saleh ya kamata kaji tsoron Allah kayi adalci a kan kanka da iyalinka, idan ka tauye matarka Allah bazai barka ba kuma ha'kkinta zai iya kaika wuta". "U'hum ko kefa, kaji magana daga wad'anda suka san Allah, to kaji dai kuma wallahi kaci gaba da tauyeni addu'a zan maka balbalin bala'i ya sauka akan 'kannenka suma...." Shiru yayi sannan ta canza maganar tace "Shikenan dai Hajiya ni Zan koma, na tafi da abincin ne ko na bar miki ki 'karashe?". "A'a jeki dashi". Bayan ta fita Saleh ya tashi shima, kiransa Hajiya tayi tace ya zauna ta tashi, dawowa tayi da tray da shinkafa akai da miyar kifi sai 'kamshi take ga lettuce ga kuma lemon za'ki me sanyi. Ajiye masa tayi tace "kaci kafin ka fita, zan sa jumana ta koya mata girki Amma maganar ha'kkinta kaji tsoron Allah ka dena tauye mata, idan matarka kake tunanin zata dawo to tayi aure kuma har abada bazata dawo maka ba". Tana gama fad'in haka ta bar wurin. Zama yayi ya dinga cin shikafarnan kamar yau ya fara ganinta, saida yaci plate guda da rabi sannan ya kora kunun za'ki ya yiwa Hajiya godiya ya fita, rabonsa da cin abinci mai dad'in na yau kwana takwas kenan, tunda Hajiya ta dena kai musu abinci, gashi ya sayi kayan abinci ya jibge babu abinda babu amma sarrafawa ya zama aiki. Hadiyya na komawa gidanta ta kira mahaifiyarta "hello ammy" "Na'am 'yar leleta kina lafiya? Yanzu nake shirin kiranki kuwa yayyenki zasu zo gobe". "Dan Allah da gaske? Aikuwa nima gobe zanzo". "To Allah ya kawoki 'yar lelen ammynta, bani labari me dame kikayi?" "Ammy dan kiji nayi farfesun nama ranar nan sannan kinga yanda nake miya da nama zu'ku-zu'ku? Inanan nayi 'bul-'bul dani ina cin nama ina shan madara". "Kai lallai 'yar lele kina jin dad'inki, Amma dai bakya mantawa da ammynki ko?" "Eh mana komai naci sai na tunaki, ai goben ma zan taho miki da abubuwa". "To ki bo'ye dai kar ya gani yace daga aure kin fara yiwa uwarki guzuri banason haka". "Kai ammy sai ya fita fa sannan zanzo". "To shikenan, oh kina ta Shan Madara abinki ni rabona da shayi me madara tun kafin aurenki". "Karki damu Ammy ai naga ma ba sha yake sosai ba zan d'auko a ta gara ta na kawo miki". "To Allah yayi miki albarka". Saleh na yin sallama ta tashi zumbur ta tafi gabansa ta tsaya tace "gobe zanje gidanmu". "To Allah ya kaimu" ya fad'a tareda nufar d'aki ya ajiye jakarsa, babu sannu da zuwa babu ya aiki babu komai sai gobe zanje gidanmu, inama ace idan taje tayita zama a can, shine abinda ke ran Saleh. Bata ma yi gigin bashi abincin dare ba indomie ta dafa ta soya kwai taci abarta ita kad'ai. Washegari ma tea kawai ta had'a masa, ruwa ne zalla sai Lipton da ta jefa a ciki ko rabin cup baisha ba ya tashi ya fita, har ya fita ta bishi da gudu tana 'kwala masa kira, tsayawa yayi tace "nace maka zanje gidanmu baka bani kud'in mota ba balle kud'in tsarabar da zanyi musu". 3000 ya ciro ya bata yace ta musu tsaraba sannan ya bata 1000 kud'in mota, godiya ta masa ta koma gida da gudu. Shiga yayi gaida Hajiya ta bashi kunun alkama yasha yaci d'umamen shinkafar jiya ya fita. Saida ta bari ya fita sannan ta d'auko 'karamin buhu, store ta nufa ta d'auki Madara biyu a ta gararta da milo da sugar da Lipton kwali biyu, sannan ta d'auki jarkar mai 'karama. Fridge ta bud'e tace "tunda ka kawo kai bazaka ci ba akwai masu ci" raba nama da kifin dake fridge d'in tayi gida biyu-biyu ta sakawa Ammynta rabi ta ajiye rabi, kallon kayan tayi tace "yauwa, nasan sai nafi kowa kai abin arzi'ki". Babu kunya haka ta fita da buhunta Allah ya taimaketa babu  wanda ya gani a cikin gidan, adaidaita ta d'auka har 'kofar gida. "Salamu alaikum!" Ta fad'a cike da murna, amsa mata sukayi ta fara shiga da jarkar mai ta ajiye sannan ta koma ta d'auko buhun sauran kayan. "Kai kai kai.....me muka samu haka? Wai wai wai...'yar lelena wannan irin gara haka? Kai harda nama? La harda kifi".kallon Hadiyya tayi tace "ba dai kwasowa kikayi duka ba saboda shirme ko?" "Kai Ammy ya za'ayi na kwaso duka? Akwai da yawa a firiji wannan kad'an na d'ebo ai". "Dama ga yayarki ta kawomin kayan miya fal bari azo ayi abinci me dad'i kai nagodewa Allah 'ya'ya mata jari, kai 'yar lelena zo nan na rungumeki kinji?". Rungumar Hadiyya tayi tace "Allah yayi muku albarka yanzu bari nazo nayi miya da abinci dama akwai kabeji sai aci dashi, duk ku zauna ku huta". "A'a Ammy tsaya kiga" kud'in da Saleh ya bata ta ciro ta mi'kawa Mahaifiyar tasu tace "wannan ya bani yace na siyo miki abu kawai naga gara na kawo Miki". Kar'bar kud'in Ammy tayi tace "har dubu uku? Kai yau dole na taka rawa na rangada gud'a, ayyiririiii, Allah nagode maka da ka bani farar haihuwa, yo a hankali ai zan maida kud'ad'den da na ranta na aurenki". Kitchen ta nufa tana rawa abinta su kuwa sai ya'ke baki sukeyi sun farantawa mahaifiyarsu, zama Hadiyya tayi kan tabarmar dake shimfid'e ta kalli yayarta tace "sakina ta kawo kayan miya ke kuma me kika kawo?" "Ni ce masa nayi adda batada lafiya ai, anjima zaizo dubiya zai taho da abubuwa". Bayan d'an lokaci Ammy ta fito da bokitin markad'e a hannunta tace "bari na mi'ka wannan ku zauna ku huta". Cikin sauri Hadiyya tace "a'a Ammy kawo na kai". Mi'ka mata botikin ammy tayi ta bata hamsin tace "ga kud'in markad'e". "A'a Ammy ki barshi akwai canji a hannuna". "To shikenan Allah yayi muku albarka". Bayan sunci abincinsu suka fara hira, dad'in hira ya sanya Hadiyya ta fad'a musu bayacin abinci sannan har yanzu fa ita ba amarya bace, shawarwari suka bata na yanda zata ja hankalinsa. ********* "Seriously I am okay ka bani towel d'in kawai" na fad'a a karo na boyar tareda matsawa daga gareshi, tunda yayi wanka ya fito ya dameni dole sai ya nad'eni a towel kamar wata yarinya. "To shikenan ungo". Kar'bar towel d'in nayi na d'aura sannan na sauko daga gadon, gaba d'aya towel d'in bai wuce rabin cinyoyina ba, zubawa 'kafafuna ido yayi babu 'kiftawa, ba tareda na waiwayo ba na shiga bathroom a take gajiyar da nakeji na nema na rasa, jina nayi kamar nabar 'kasarnan wani had'add'en d'aki na gani na glass sai ka bud'e 'kofar zaka shiga shower, a ciki akwao sitting jacuzzi. Ruwa na cika na shiga na zauna tuni na fara gyangyad'i, har na manta ma dare ne domin hasken wurin ma na daban ne, na jima ina gasa jikina sannan na d'aura towel d'in na fito, Aliyu na kwance idanunsa na kaina. 'karamin towel na saka a gashina na bud'e wardrobe na d'auko kayan bacci, gefensa na nufa na kwanta ya matso dab dani, hannunsa ya sanya a cikina yace "goodnight". Da safe bayan munyi breakfast muka fara zagaya gidan yana nunamin wurare, d'akuna uku ne kawai a main house sai kuma boys quarters sai kuma 'bangaren masu aiki da nidai a wurina baida amfani, akwain'karamin gym sai study nashi wanda yake ajiye takardunsa da suk wasu abubuwa da suka shafi aikinsa, bayan mun gama ganin wad'annan sannan ya nunamin kitchen na daban a waje yacemin anan chefs zasu dinga girki, garden ya nunamin yace "da naso ayi mana swimming pool daga can to sai kuma naga akwai wahala sai na barshi". Zama mukayi sanyin ciyayin wurin na dukanmu nace "naji kace akwao wajen masu aiki da kuma chefs ai Ina ganin babu amfanin hakan ko?" Girgiza kai yayi yace "a'a wannan gidan nasan bazaki iya gyaransa ba ko zaki iya bazan barki ba, sannan kaman yanda kika gani a gidanmu chefs ke mana girki kema anan bazan barki kina girki ba, ki zauna ki huta idan kinaso kiyi girkin ga kitchen d'inki nan d'an abun kwad'ayi dai idan kinaso sai kiyi da kanki". "Okay" na fad'a tareda mi'ka domin bayana ya ri'ke, hannuna ya kama yace "muje wancan zaifi miki dad'in zama". Kujera ce gatanan dai half gado half kujera, kishingid'a nayi akai shima ya kwanta a gefena, idona a rufe inajin wata ni'ima na ratsani, idan kana irin wannan wurin ai ko wula'kancin dangin miji ma ba jinsa zakayi ba. Hular kaina ya cire yace "twins d'inmu fa akwai rashin ji". Murmushi nayi nace "nikuma sai nake ganin kamar basuda matsala". Kansa naji a 'kirjina yanda yana magana inajin vibration na muryarsa na shiga jikina yace "da suna 'kanana so adorable, amma da suka fara girma duk suka ishi kowa, ita dai Mum tace sunfi bata wuya da suna babies amma mukam sunfi bamu wuya da suka fara takawa, duk saida suka bi glass d'in gidan suka farfasa". Dariya nayi ina hango amal da nawal suna toddlers nace "nikuma twins na birgeni sosai fa, gani nake kamar ba wani wuya, saboda kana kallansu kana Jin dad'i". D'ago kansa yayi yace "da twins Mata da maza wanne kikafi so?" Dariya nayi yayin da naji wani abu a 'kirjina nace "Ni da bazan samu ko d'aya ba mene nawa na za'bi?" 'bata rai yayi yace "am sorry idan tambayar tawa ta 'bata miki kawai na tambaya ne". "A'a baka 'batamin ba kayi ha'kuri, gaskiya dai....to duk inaso saboda kowannensu akwai abin sha'awa, amma dai zanso na fara da maza". "Nima nafison twins maza, yauwa na tuna kinada passport ne?" "Eh inada amma yayi expiring". "Okay za'ayi renewing d'insa kin taho dashi ko? Inaso mu tafi honeymoon amma sai mun biya Saudi sai muje wata 'kasar ko?" Wani dad'i naji nace "Allah ya kaimu" a take na fara d'okin zuwa saudiyya, tunda akamin passport d'in baiyi amfanin komai ba, tashi nayi da sauri nace "bari naje na duba". Tare muka tashi Aliyu yayi 'ko'karin d'agani, a lallai sai ya sakani a kafad'a shi kuma ba wani 'karfi ba, a tsorace nake 'ko'karin dukansa aikwa Yana d'agani muka zube tare kan grass carpet d'in, dariya nake sosai shi kuma ya had'e rai, cikin gunaguni yace "Shikenan zaki d'aukeni rago". Tashi nayi ina rigata har tayi danshi saboda ra'ba ce kan ciyayin nace "karka damu nasan ba rago bane kai ni d'in ce mai nauyi". Hannu ya mi'komin alamun na kamashi ya tashi, maimakon ya tashi sai ya jani na fad'a kansa, Ina fad'awa ya had'e lips d'insa, intense kiss ne amma bai wani dad'e ba ya janye, d'aga gira yayi yace "wato ni jarumi ne ko?" Tashi nayi daga kansa na juya, dariya yayi yace "au sai yanzu kika fara kunyata after you spend minutes moa....." Kunnena na toshe na bar wurin da gudu, biyoni yayi yana cewa "tsaya mana na 'karasa fad'a miki abubuwan da kikayi a daren jiya" Ban tsaya ba na shige d'aki da sauri na kifa kaina a kan gado saidai fuskata d'auke da murmushi, bansan meyasa na yada kunyata jiya ba gashi ya samu abin tsokanata. 47 Tashi Hadiyya tayi tace "nidai zan tafi unguwarnan tamu yamma nayi zakiga duhu ya shiga ga wahalar abin hawa, yanzu ma tunani nake yanda sai naje titi zan hau". Janyota yayarta tayi tace "ke dalla ai shi ya kamata yazo ya d'aukeki, ya za'a yi zuwanki na farko gida zaki tafi da kanki ai ba'a haka". "Ai bamuyi zaizo ya d'aukeni ba kuma kinga ya bani kud'in mota". "Dalla malama zauna, ki bari idan anyi magriba sai ki kirashi kice kin fita baki samu abin hawa ba kuma kinga lokacin sallah yayi kin koma gida, idan babu abinda yakeyi ko zai iya zuwa ya d'aukeki? Haka akeyi ai dabara ake kinga kud'inki ma ya huta". Haka kuwa akayi tana idar da sallar magriba ta d'auki waya ta kirashi, yana d'agawa tace "ina wuni? Umm nace kaga na fita ban samu abin hawa ba har akayi sallah, nakoma gida nayi sallah kuma dare yayi ko zaka zo ka d'aukeni idan ka gama abinda kake?" "Okay idan anyi sallar Isha zanzo". "To sai kazo" ta kashe wayar, wani uban dundu taji an mata saida ta gantasare ta saki ihu, kama kunnenta yayarta tayi tace "Uban waye yace miki haka ake magana da miji? Shegiya me kan dutse kamar bakya ja? Komai  a gabanki mukeyi saboda ki koya amma a banza?, Meye wani kaga? Ba wani sweety, darlin, honey, baby da sauransu se wani kaga? Babu kashe murya kice dan Allah baby alfarma zakamin akwai matsala fa? Wallahi kaga na fita kaza kaza amma kina magana kamar gayan tuwo? Inaga ma kagan da kike sakawa basa bayyanar da jikinki ta ina miji zaiyi sha'awa? Ke ki gyara wallahi idan ba haka ba kafin ya kwanta dake yayo miki kishiya, shawara ma ta canza yanzu nasan me zakiyi". Hud'uba akewa Hadiyya har zuwan Saleh, saida yazo sannan tayi sallah ta shafa powder da janbaki ta saka turare ta fita. Cikin sauri ta bud'e motar ta zauna, kissing kumatunsa tayi tace "yi ha'kuri honey na barka da jira sallah nayi ne sannan na taho maka da abinci". Kallonta yayi tareda hadiyar yawu yace "okay" yasan yau zaisha rigima tunda ta samu tsarki. Hira taketa zuba masa yana binta da uhm har sukaje gida, suna zuwa tace ga abinci dan Allah kaci, nasan baka son girkina amma wannan wallahi ammyna ce tayi da kanta, bari nayi wanka". Guest room ta shiga ta cire kayanta ta fad'a toilet, jika jikinta tayi sannan ta shafa turare, fitowa tayi ta kurma ihu sannan ta sake, a firgice Saleh ya shiga yana shiga ta d'afeshi tace "tsaka!! Duba ka gani nazo fitowa na ganta wayyo Allah na!!". Ganin zata fad'ar dasu yasa ya tallafo bayanta ta kuwa sake 'kan'kamseshi, 'kamshin turaren da ta shafa ya Sha'ka 'kamshi mai matu'kar dad'i sannan gata naked ga ruwan dake jikinta. Ajiyeta yayi ta sake kama hannunsa da alamun tsoro, gyaran murya yayi yana d'auke kansa yace "to nemi abu ki d'aura. Dukda kunyar da takeji na tsayuwa a gabansa babu kaya amma ta danne tace "meyasa baka sona ne? Ko kallona baka son yi saboda baka sona? Naji bamuyi soyayya dakai ba amma ai ko a matsayin matarka ta aure ka kalleni, ba fa zaman gadi nazo ba zaman aure nazo". Ja tayi baya ta nufi kayanta dake ajiye ta d'auki d'ankwali ta d'aura a jikinta tace "tunda banida amfani a wajenka zan tafi wajen Hajiyarka na kwana gobe zan tafi gidanmu bazan sake zama a gidanka ba, haba dan Allah dan cuta kwana goma da kawoni amma bansan kaina a matsayin amarya ba? Ya isheni na tafi na bar maka gidanka sai ka biyoni da takardar saki". Kwasar ragowar kayan tayi ta nufi 'kofa, binta yayi da sauri ya ri'kota ta sake sakin d'ankwalin daga d'aura. Hannunta ya janyo ta fad'a 'kirjinsa ta saki kuka, tausayinta ne ya kamashi dukda dai akwai rashin ha'kuri da kunya amma gaskiya ta fad'a ya kamata ya bata ha'kkinta domin yanzu ya lura ba yarinya bace sannan shi kanshi yana da bu'katar hakan". 'Dankwalin ya d'auka ya d'aura mata sannan ya d'auketa bridal style, ta kasa 'boye murnarta tayi ta cusa kanta a 'kirjinsa tana murmushi. A kan gadonsu ya ajiyeta sannan ya bud'e wardrobe d'inta ya d'auko doguwar riga, wanni kallo ta masa yace "ki saka muyi sallah". Zura rigar tayi ta d'auro alwala suka gabatar da sallah, bayan sun idar ta zauna kan dardumar hannunta na kan cinyarta tana jiransa. Zama yayi a bakin gado sannan yace tazo ta zauna, a cikin zuciyarta murna take kamar ta zuba ruwa a 'kasa tasha amma a bayyane ta nutsu sosai, d'aga kanta tayi ta kalleshi a hankali ya janyo fuskarta, gani yake duk yanda ya ta'bata zai iya cutar da ita. Ai kafin ma ya gama matsowa ta rufe ido tareda turo le'benta, murmushi yayi yana tausayin yarintarta, Bilkisu ce ta fad'o masa rai amma ya kawar, indai ta cigaba da rayuwarta shima ya kamata yaci gaba. Kissing d'inta yayi ta tsaya cak tateda bud'e idonta, ganin nashi idon a rufe ya sanya ta rufe nata idon itama, hannunta taji yana dago rigarta a hankali itama ta tayashi tareda jan rigar zuwa cinyarta, hannunsa ya sanya a cinyarta yana shafawa take ta fara mutsu mutsu. Tunda kuwa rigar ta rabu da jikinta ta fara shan jinin jikinta, kwantar da ita yayi tareda shiga tsakanin 'kafafunta, take bugun zuciyarta ya canza ta zazzare ido, abubuwa da dama da taji labari ke zuwar mata, ganin ta tsorata ya sanyashi sake kissing d'inta, tashi yayi ya fara cire kayansa tun tana zuba ido tana kallonshi har abin yafi 'karfin jaririyar 'kwa'kwalwarta ta juyar da kanta. Dakewa tayi saboda kar ya Gane tsoronta amma ta gama.tsorata da ganin wannan 'katon mutumin a kanta, bata gane barno gabas take ba saida ayar Allah ta tabbata a kanta, tun tana cije baki har ta gaji ta saki kukanta mai isarta. ********** Muna zaune kan couch d'in dake bedroom d'inmu, kallon tv d'in dake d'akin nayi ina tunanin rashin amfaninta, meyasa za'a sanya Tv a bedroom a sanya a sitting room tsabar kud'in yayi yawa? Netflix ya kai a cikin tv d'in ya fara scrolling yana karantomin sunayen films d'in dake wurin ina girgiza kai, ya fad'i kusan 10 duk ina cewa sunan baiyi min ba, ajiye remote d'in yayi ya kalleni yace "Anya kina kallon American film?" "Ina kallo amma ba sosai ba". "Okay to yanzu zan za'ba mana mai kyau mu kalla tare". Wani film ya kai mana 'golden intelligence', kallo muka farayi film d'in kuwa yayimin kyau, muna kallo naji 'karan wayata, dubawa nayi naga Raudah cikin sauri na amsa, dad'in gida ya sanya na manta ma dasu domin jina nake a wata duniya ta daban, banda gidana na aljanna yafi wannan ai da sai nace a aljanna nace, ga farin fentin d'akin da kujerar da muke kai ya sake haska d'akin. "Lallai Bilkisu har ya fara hure miki kunne ko? Bazaki neme mu ba to ai gamu mu mun kawo kanmu, malamai ku bud'e mana 'kofa". Dariya Aliyu yayi ya tashi ya fita nabi bayansa, wani wuri naga ya danna gefen 'kofar palon sai ga camera ta bayyana, kallonsa nayi na zubawa hoton su Raudah Ido suna tsaye a bakin 'kofa, dariya yayi yace "me kukazo min gida?" "Ka bud'e mana". "A'a ku koma". "Workers d'inku muka kawo idan kuma bazaka bud'e ba shikenan sai mu koma dasu tasha aikinta". Jikin cameran ya dannan naji alamun lock ya fita daga 'kofar, turo 'kofar sukayi twins suka kama waje suka zauna Raudah ta tsaya mana bayanin ma'aikatan da suka kawo. Mutum biyu ne zasu dinga gyara cikin gidan sai gardener sai kuma sharar compound kace maigadi yace a bashi zai dinga yi ko?" "Eh, chefs d'in fa?" Shigewa tayi ta zauna tace "zasu zo anjima tunda sai gobe zasu fara aiki, kaje waje suna jiranka". Fita yayi na koma wurin twins muka fara d'an hira, kirana Aalee yayi na kar'bi mayafin Raudah na yafa na fita. Yana tsaye da wasu mata biyu 'yan dattijawa dasu, sai namiji d'aya, kafad'ata ya dafa yace "wannan itace matata Bilkisu, zatayi muku bayanin yanda aikin yake kai kuma muje da kai". Gaisheni sukayi har 'kasa duk kunya ta kamani sannan muka shiga cikin gidan dasu nayi na nuna musu wuraren da zasu dinga gyarawa sannan na kaisu part d'insu domin damu zasu dinga zama, komi ni kallon sabo nake masa amma dole na saba indai zaman aure zanyi. Zuwan su Raudah ya sanya Aalee fita, basu koma gida ba saida ya dawo, kama wuri sukayi su fa a lallai yau anan zasu kwana harda Raudah. Kama hannun amal da nawal yayi ya fara jansu suna da'kirewa nikuwa ba abinda nake banda dariya, kashe murya nawal tayi tace "Dan Allah Aunty B kice ya barmu mu kwana Allah ni gani nake ma yau bazan iya kwana a d'akinmu ba yayi 'karami". "A'a ku godewa Allah twins d'akinku yanada girma fa tunda kowacce nada gado a cikinku a ciki sannan ga space dukda haka, amma idan zai yarda ku kwana ga d'aki nan". Na fad'a ina dariya. Girgiza kai yayi yace "muje na siyo muku burger da pizza, indai kwanan gidannan ne har sai kun gaji bari na koma aikina". Anyi sa'a sun ha'kura yace na shirya mu fita tare, wani pizza joint mukaje ya siya mana family  size, gidansu Aliyu muka nufa a can muka ci sannan muka tafi gida. Washegari da safe bayan mun gama shiryawa sai ga kira ta land line, d'agawa yayi yace "okay, yeah right now.... thanks". Hannuna ya kama yace "breakfast is ready" muka nufi dining, bansan cewar mutane zasu shigo ba saboda haka ban fito da mayafi ba, wani iri naji ganin maza biyu sun shigo d'auke da tray, jere plates sukayi sannan suka dur'kusa suka bar wurin, suna fita nace masa "Amma baka cemin mutane zasu shigo ba". "Sorry, next time zance su kawo kafin mu fito za'a kawo abincin hakan yafi ko?" Gyad'a masa kai nayi alamar eh sannan na fara kallon abincin, abincin kad'an-kad'an ne a plate, kallon Aliyu nayi ya d'auki fork da hannun hagu ya d'auki knife da hannun dama, a hankali nace "babu kyau cin abinci da hannun hagu fa". Murmushi yayi yace "bakiga na ri'ke knife d'in da hannun dama ba? Hakanan akecin wannan abincin". "A'a wannan d'abi'ar yahudawa ce annabi bayaso, ko tea da bread ba'aso a ri'ke cup da hagu saidai ka d'auki bread kaci ka ajiye ka d'auki cup". "Yeah well yanzu zamani yazo da abu na daban? Indai zakiyi yawon duniya dole ki fara cin abinci haka, ko ina hakanan akeyi zamu je 'kasashe da dama zaki ganewa idonki". Ajiye maganar nayi saboda batada amfani na saka hannu na fara cin abincina, kallona yayi tareda cire hannuna ya ri'ke yasa tissue ya goge hannun tare da mi'komin fork da knife yace "ki kalli yanda nakeyi sai kiyi". Raina ya sosu kad'an, me yake nufi da hakan? Daga 'kauye ya d'aukoni ko me?, Danne fushina nayi nace "nasan yanda akeyi kawai banida ra'ayin hakan ne, sannan shaid'an ke cin abinci da hagu banaso naci da shaid'an". "Ni inaci da shaid'an kenan?" "Ni bance haka ba kayi ha'kuri" na fad'a tareda sunkuyar da kaina, take abincin ya fita daga raina dukda nasan wayewa ke sanya hakan amma wannan ba d'abi'a ce me kyau ba, indai sai nayi hakan zan waye nayita zama da 'kidahumancina. Abincin na fara ci da fork d'in, abinda sai na yanka sai na yanka sannan na ajiye wu'kar naci, a haka mukaci abincin shiru, sunyimin dad'i sosai saboda haka ban bar komai ba, ina gama ci fara 'ko'karin had'a kwanuka? Ri'ke hannuna yayi tareda girgiza kai yace "ki barsu za'a kwashe". Gaba nayi inajin jikina ba dad'i, ta yaya mutum zai iya rayuwa babu aikin komai? D'an aikin da nake zuwa ma ya ragemin zaman banza babu shi sannan gashi tun yanzu mun fara samun sa'banin halaye da Aliyu. Ganin banida abinyi ya sanyani fara goge gogen d'akin dukda babu wani datti, ina goge gogen ya shigo, amsa masa sallamarsa nayi ya 'karaso inda nake sannan yayi wrapping hannunsa a kan cikina, rad'amin yayi a kunne yace "kiyi ha'kuri". "Nima kayi ha'kuri ina ganin na wuce boundary d'ina, idan haka dabi'unka suke banida ikon canza maka". Juyoni yayi na kalleshi yace "kinada ikon canzani mana saboda ke matata ce amma ba yanzu ba, mu fara fahimtar juna tukun sannan zanyi duba akan abinda kika fad'a". Anan muka ajiye maganar, mun sake fahimtar juna kafin ya fita ya barni ni kad'ai, part d'in ma'aikata na nufa, suna waje suna girki su biyun ina musu sallama cikin sauri suka nufo inda nake tareda dur'kusawa. Bayan mun gaisa d'aya daga cikinsu wadda naji d'ayar ta kira da inna kulu tace "Hajiya alfarma nake nema daga gareki, Kinga jikata ita kad'ai gareni uwarta ta rasu an barmin ita, to na taho na barta wajen kishiyar uwa gashi azabtar da ita takeyi, Hajiya ko zaki iya barina na d'aukota ta zauna dani anan?" "Babu matsala ki kawota, Allah ya jikan mahaifiyar tasu" "Ameen Hajiya nagode Allah ya 'kara arzi'ki Allah ya ji'kan mahaifa". "Ameen, akwai wani abu da kuke bu'kata?" "Babu, Alhaji ya saka an kawo mana kayan abinci dan Allah ki 'kara masa godiya, babu wani abu da muke bu'kata". "To shikenan idan akwai wani abun Sai ku fad'amin". Bayan dawowar Aliyu na sanar masa da abinda ya faru, kissing d'ina yayi yace "to ai kece me gidan duk abinda kikayi daidai ne Hajiya". Zama nayi jikina duk ba dad'i nace "wallahi nayi missing aikina sosai, yanzu haka zanyi ta zama ba wani aikin gida babu aikin waje?" Hannunsa biyu ya saka yaja kumatuna yace "idan munyi tafiyar da zamuyi mun dawo sai ki yanke shawara, idan kinaso ki koma aiki sai mi sanarwa Mum ta samar miki a asbitinsu amma nasan da wuya ma ki amince ki koma". Nikuwa me zai hanani komawa aiki? *** A cikin two weeks da nayi a gidan har anyi renewing passport d'ina a yau muke shirin tafiya Saudi da yardar Allah, su Raudah ke tayani had'a kayana. "Haba Raudah kamar zan bar 'kasar har abada wannan uban kayan?". Cigaba tayi da loda kayan tace "bakiji yace daga nan zaku tafi wata 'kasar ba? Kika san dad'ewar da zakuyi? Shiyasa nake saka muku kayan da zasu isheki har ku dawo". "Dukda haka ki barsu dan Allah, wannan ai sai ace abu na sako a akwatin musamman zuwa saudiyya, sai ace goro ne kisa ayita cajeni". "Hakan ma bazai faru ba" "Ko a yagamin jakar kayan su zube kowa ya gani na rasa a ina zan sa...." "Shutup, na barsu haka shikenan?" Gyad'a mata kai nayi alamar eh sannan muka daddanna akwatin muka rufe, twins suna parlour da 'kawayensu na kalli agogo, saura three hours mu fita, kallona raudah tayi tace "Bilkisu kina son ya Aalee?" "Meyasa kika tambayeni? Na fad'a ina kallonta. "Umm saboda wannan maganar tanada muhimmanci kafin ku tafi, har yanzu kina tunanin komawa tsohon mijinki?" "A'a bana wannan tunanin, sannan na fad'a miki gaskiya Ya Aalee yana burgeni, sannan yana kyautatamin ina kuma 'ko'kari wajen cusawa Raina sonshi, amma dukkanmu bamu fara son junanmu ba, we are taking it slow". "Zamuga zuwa yaushe hakan zai tabbata, indai kin amince da zama dashi har 'karshen rayuwarki shine kawai abinda nakeso naji". "Na amince Raudah zan zauna dashi har abada indai zai zauna dani a yanda nake". Dariya tayi tace "me zai hana kuwa?" Cigaba nayi da abubuwan da suka kamata har lokacin tafiyarmu airport, bayan mun musu sallama amal tace "ya Aalee amma dai ka bar key d'inka a gida ko?" "Eh me ya faru?" Tsalle sukayi tare nawal tace "bakomai, sai ka dawo, gadi kawai zamu yi maka kafin ka dawo". Munyi umrarmu cikin kwanciyar hankali, Aliyu shi ya dinga nunamin wurare sannan nayo tsaraba mai yawa, domin na shirya da mun dawo zanje naga gida. Sati biyu mukayi sannan muka wuce Dubai, a cikin raina ko sunan 'kasar banason ji saboda abinda ya faru a baya, har yanzu asbitin suna turomin notification ta email d'ina wanda hakan na tasomin da abubuwa da dama, fatana Allah yasa ba dad'ewa zamuyi ba. Muna shiga 'kasar na fara kalle-kalle kamar ba'kauyiya, babban abin farin cikin shine mun sauka a best hotel in the world, burujul arab, suite ya kama mana Allah kad'ai yasan kud'in da ya biya, dukda ba VIP bane amma ai shiga hotel d'in kansa abin kallo ne. "Bakinki ya'ki rufuwa fa tunda muka shigo". "Ta yaya bakina zai rufu man, ka kuwa kalli garinnan da kyau? Babban birnin 'kasar fa muka sauka kamar dai Abujanmu, wayyo Allah kamar kar na koma gida". "Hm wani abun ma sai munje skating da bowling". Tsalle nayi cikin murna shi kuwa dariya yake ta min, le'kowa nayi ta glass d'in da ya kewaye d'akin, kana ganin rufin garin, dan ma rana ce da dare ne nasan sai yafi haka. Ahmad ne ha fad'o raina a take na kirashi na sanar masa gani a Dubai, cikin murna yace zai hau jirgin 'kasa yazo ya sameni idan aiki ya ragu. Ranar ban wani huta ba sam banajin gajiya, na dad'e banyi farin ciki irin wannan ba ban saniba ko Allah ne ya albarkaci 'kasar da sanyawa mutum nishad'i? Ko da muka je ice skating ri'ke hannuna Aliyu yayi shi ya dinga min jagora, sai dare sannan muka koma bayan naga had'add'en ruwannan, Aliyu kuwa ko a jikinsa shi ni yake kallo ma. Muna kallon ruwan naji kansa a kafad'ata yace "ban ta'ba ganinki kina farin ciki kamar yau ba". Hugging d'insa nayi sosai ban damu da mutanen dake wurin ba nace "all thanks to you ka sanyani farin ciki, ka bani abinda a rayuwata ban ta'ba tunanin samu ba Allah ya biyaka". "Hmm to idan wannan kinyi farin ciki haka next surprise da zan miki ai zaki iya suma". Da sauri nace "Dan Allah mene ne shi". "It's a surprise" "Please" "No" "Pleeeeaseeeee" "Noooooooo".. "Pretty please?" "Yes you are pretty, mu koma n fara jin bacci". Duk yanda naso ya fad'amin surprise d'ina ya'ki yace sai na kissing d'insa nayi, yace na Masa massage wanda yayi leading zuwa wani abu daban.....a haka na ha'kura, nifa inada matsalar surprises na tsani ace za'ayi surprising d'ina. Abin takaicin ma washegari ya'ki fad'amin sannan yace bazamu fita ba sai dare, tuni na yanke shawarar.maybe wani cinema zai kaini ko dai taro haka, lokacin da zamu fita rufemin Ido yayi da 'kyalle ya kama hannuna ya shigar dani mota, kasa kunne nayi naji ya bawa direba address d'in inda zamuje amma naji yayi shiru, nidai inajin mota na tafiya,  ko da na fara 'ko'karin bud'e idona sai ya had'a hannayena a kan cinyarsa. Bayan motar ta tsaya muka fita yace "yi a hankali dai". Baifi taku goma mukayi ba ya tsaya tareda kuncemin idona, kallon glass doors d'in dake wajen nayi take na lura da asbiti ne, saman asbitin na kalla naga an rubuta IVF CLINIC...... Wani mugun fad'uwar gaba naji yayin da Hawaye suka fara zuba daga idona, wannan shine surprise d'in da ban ta'ba zato ba ... 48 Kuka sosai nakeyi har saida na gagara tsayawa kan 'kafafuna, dur'kusawa nayi shima ya dur'kusa, hannunsa ya saka a kafad'ata ba tareda yace min komai ba, ban ta'ba kawo yin IVCF a gidan Aliyu ba dukda nasan wataran zai nemi haihuwa, amma ban ta'ba tunanin dani zai haihu ba. Mun d'auki mintina a haka sannan ya bani handkerchief na goge fuskata muka shiga ciki, hankalina sam baya kan abinda yake fad'i har yaja hannuna muka nufi wani office, anan naji yana bayanin appointment da akayi na Bilkisu mustapha, wato shi ya gama shirinsa duk ban sani ba. Wata takarda aka bamu ya kira nurse yace ta rakamu za'a min gwaji, gabana sai fad'uwa yakeyi na kama hannun Aliyu na 'kan'kame, Saleh ne ya fad'omin rai, da ace dashi mukazo wajennan zanji nervousness haka ko kuwa murna zan dinga yi? Ba wai na tuna bane saboda soyyaya, a'a na tuna ne saboda shine mutumin da nasan bana haihuwa a wurinsa sannan dashi muka fara wannan magana, Allah yayi ba dashi zanzo ba. Muna shiga ya mi'ka ma ma'aikaciyar wurin takardar, gado ta nunamin tace na kwanta sannan Aliyu ya zauna a kujerar gefena, bayanin test d'in da za'a min takemin, HSG wanda za'a hasko can cikin mahaifata ina kallo a screen, saida aka saka wani abu kamar syringe da ruwan allura tace min sunanshi contrast media, injecting d'insa akayi zuwa uterus d'ina, bayan wani lokaci aka d'auko HSG tool d'in shima ta saka, hannuna Aliyu ya kama yana murzawa a hankali, wani hawayen ne ya zubomin kafin na goge yasa hannunsa ya goge, muka zubawa screen d'in Ido. Sai ga mahaifata ina gani dukda ba wai komai da komai ba, bayani take mana a hakan dai aka tabbatar inada cervical infertility, komawa wajen likitan mukayi har yanzu ban furta ko kalma d'aya ba, bayan likitan ya gani yace za'a fara aiki next ovulation d'ina, wanda almost 13 days kenan, sannan a d'auki eggs d'inmu a saka a kwalba sai yayi six weeks sannan a maidashi jikina, bayan wasu six weeks sannan a yimin US scan a tabbatar akwai cikin sannan bayan 2 weeks a sakeyi bayan an tabbatar baby na lafiya lau sai a barmu mu tafi. Godiya Aliyu ya musu sannan doctor d'in yace da zarar na gama period naje za'a min ovulation test, oh ni Bilki naga ta kaina. Bayan mun fita Aliyu yace "kinyi shiru baki ce komai ba har kin fara bani tsoro". "Bansan me zance bane...." Wani kukan na fara yace "Allah ya baki ha'kuri ba sai kince komai ba". "Amma inaso nayi magana" na fad'a ina goge hawayena, murmushi yayi yace "munada sauran lokacin wannan maganar yanzu dai muyi wata maganar". "Zamu dad'e anan yanzu ya zamuyi da aikinka?" "Dad ya hau kai, dama shine a kai ya d'aurani, sauran kuma da na fara zan 'karasa anan kafin mu koma". Shiru na sakeyi har yanzu gani nake abin wasa ne, ranar kamar kurma na koma da zarar Aliyu yayimin magana sai hawaye, kamata yayi ace tsalle nake da murna amma tsananin murna yasa na kasa hakan, farin ciki yasa washegari na tashi da azumin godiya ga Allah. Kamar wasa har ranar da za'a fara mana aiki tazo, a tare aka d'auki sample d'inmu aka saka a wata kwalba, da yawa suka d'iba wanda bayan 6 weeks d'in wad'anda suka rayu za'a d'auki biyu a ciki a sakamin, sunce zasu yi 'ko'karinsu su tabbatar maza ne tunda munce duk mazan mukeso. Muna fita nayi hugging d'insa a bakin titi nace "nagode sosai, abinda ka bani Allah ya ninka maka ya baka". Dariya yayi ya d'agoni kad'an sannan ya ajiyeni, turo baki yayi yace "ya kamata ki rage nauyi fa". "Kai ya Aalee nawa nake? 58 fa". "Aikwa kinyi nauyi da yawa sosai, nafiso na d'aukeki cak ya sa'ba a kafad'ata nayita yawo dake a haka". Dariya nayi yayin da muka tsaida taxi nace "Banda abinka ai jannat ce kawai zaka iya d'aukanta haka laifi daga kai ne ya kamata ka 'kara 'kiba". "A'a ke ya kamata ki rame tunda fa kin kusa samun babies, ba ma d'aya ba biyu kinga ya kamata ki musu mazauni". Murmushi ne ya bayyana a fuskata ba tareda nace komai ba, wai ni Bilkisu nice zan haifi 'ya'yana, abinda nayi shekaru uku Ina shan gori akai, dama ance wani hanin ga Allah baiwa ce. Takura masa nayi muka bar burujil arab domin kud'in da ake kashewa dukda bai fad'amin ba kuma nasan baya damunsa amma ni yana damuna, banaso naji ana lissafin an kashe miliyoyi a kaina. Six weeks muka koma aka dasa min babies d'ina, tunda muka baro asbitin nake shafa cikina gani nake kamar za'a ce sun lalace kafin lokaci yayi. Ko da muka isa gida kama hannuna Aliyu yayi, a hankali yake tafiya ina yin sauri kad'an ya tsaidani yace "ki tafi a hankali kar babies d'inmu su samu matsala". Kallonshi nayi shi kanshi yana cikin farin ciki domin idanunsa sun nuna, jingina kaina nayi a hannunsa ya ri'ko gefen cikina a hankali har muka 'karasa d'akinmu, saida ya zaunar dani kan gado ya d'auko min kayan baccina ya bani sannan ya fita yace "zanyi aiki kar na dameki da 'karan keyboard, duk abinda kike bu'kata ki kirani kar fa ki tashi indai ba sallah zakiyi ba". Rigar jikina na fara cirewa nace "nifa banji doctor ya bani bedrest ba, dan nayi tafiya cikina bazai samu matsala ba insha Allah, aikin nauyi ne bazanyi ba har sai an tabbatar da zamansa". "Ke da aikin nauyi sai bayan kin haihu, ya zaki dinga d'aukan nauyi da baby a jikinki salon su gaji? A'a banason haka". Murmushi nayi cikin jin dad'i na zura rigar baccina, kafin na kai rigar 'kasa ya ri'keta tareda bud'e cikina, hannu yasa ya shafa sannan yace "good night my babies, kar ku takurawa mummy". Kashe murya nayi nace "goodnight Daddy". Kissing d'ina yayi yace "kiyi sallah ki huta kin sha jagwalgwalo yau". Banyi masa musu ba na tashi na nufi toilet, saida yaga shigata sannan yace "take care karki fitsararmin da babies!!". Dariya nayi yanzu kam farin ciki ya yalwata a cikin zuciyata, kullum cikin murmushi nakeyi ga son Aliyu shigata yakeyi, kai ba so kad'ai ba 'kaunarsa nakeyi sosai da sosai. A six weeks d'in da mukayi wani riritani yakeyi kamar 'kwai, abinda ke damuna shine ban fara laulayi ba gashi a lissafi dai 12weeks idan aka had'a da wancan 6weeks da yayi a kwalbar bature, gani nake ma kamar dai cikinnan babu shi dukda ina shan magungunan da aka bani. Ranar da mukaje gabana sai fad'uwa yake ina dam'ke da hannun Aliyu, a yau ne zamuji heartbeat na babies d'inmu gaba d'aya hankalinmu na kan na'urar da aka kunna, bayan ta shafa min jell d'in ta fara aikinta, shiru shiru zuciya ta'ki bugawa, murmushi tayi tace "I think your baby is playing hide and seek with us". Sake shafawa tayi sai wani shuuuu mukeji ta cikin na'urar, bansan lokacin da na fara hawaye ba Aliyu shi kansa yanayinsa ya canza, ya Allah kar kasa wannan cikin ya lalace this is my last hope. Yanayin ri'kon da Aliyu yayimin shi ya sanya nasan cewa yana cikin damuwa shima, kuka sosai na fara yayin da mukaji bugun zuciyar ya fara fitowa, tare muka sauke ajiyar zuciya Aliyu ya kwantar da kansa a 'kirjina, share hawayena nayi yayin da na farin ciki suka fara zuba, I can't believe this is real, ni Bilkisu da aka yiwa gorin haihuwa nice da 'ya'ya har biyu a cikina, inama Hajiya zataga wannan ni'imar da Allah yayimin tasan cewa ba d'anta ne kawai zai iya bani haihuwa ba, Allah ne yake bayarwa ta hanyoyi da dama. Mun jima muna sauraron heartbeat d'in babies d'inmu sannan ta nuna mana kan babies wanda shine abinda dai yafi bayyana a yanzu, gender dai da saura amma gasunan twins gwanin sha'awa dukda ba wani ganewa mukeyi sosai ba. Ri'ke takardar Aliyu yayi kamar ransa ne a jiki muka fita, wasu masoya muka gani suna tafe suna Shan ice cream, kallon ice cream d'in nayi naji amai ya tasomin da gudu na nufi gefen titi, amai na dingayi kamar zan amayar da kayan cikina kafin na gama Aliyu ya Kira emeegency.... 49 Bayan zuwan ambulance na sanar musu ba wani abu bane, banda ma shirmen Aliyu kawai daga fara amai zai kira min asbiti? Bayan sun dubani sun tabbatar babu wata matsala suka bani magani a cikin motar sannan suka sallamemu muka tafi. Muna zuwa gida zazza'bi ya rufeni gaba d'aya hankalinsa Aliyu ya tashi, da alamun bai ta'ba ganin marar lafiya ni kuwa baisan dad'in hakan nakeji ba nima na fara jina a mutum. Kashe AC d'in d'akin yayi ya kunna min heater tare da lullu'bata, dafa kaina yayi yace "sannu Bilkisu ya kikeji?" "Dad'i" na fad'a tareda 'kudundune jikina, wani kallo yayimin yace "lafiyarki kuwa? Ya mutum yana ciwo zaice yana jin dad'i? Wai kinsha maganin da aka baki ma kuwa?" Tashi nayi na zauna na jingina a kafad'arsa nace "ya Aalee ba dole naji dad'i ba? Wannan wahalar da zan sha itace zata sanyawa 'ya'yana tausayina, ba wannan ba ma wannan shine first and last time da zanyi laulayi this is so important to me, indai maganin zai hanani ciwon ne to bazan sha ba, wannan shine stage na farko a motherhood kuma banaso nayi skipping". Shafa kaina yayi yace "Bilkisu bansan ya kikeji ba amma cuta ko ya take batada dad'i idan ciwon yayi yawa zaiyi affecting babies d'inmu ko kuwa? Banaso a samu matsala". "Babu matsalar da zamu samu da yardar Allah, mata da yawa suna shan wahalar da tafi tawa wata sai an kwantar da ita a asbiti, wata tsabar ciwo fita hayyacinta takeyi, nawa me sau'ki ne fa". Maganin ya d'auko daga kan bedside drawer yace "to ki daure kisha ba lallai maganin ciwon zai miki ba amma zai rage miki ko da zazza'bin ne, tunda muka dawo ko ruwa baki sha ba gashi abinda kika ci ya dawo kisha magani sai kici abinci yanda suka ce". Kar'bar maganin nayi nace "okay zansha to d'aukomin ruwa please". Yana tashi na ciro maganin, bayan na duba naga vitamin ne na yanke shawarar sha, d'ayan kuwa 'boyewa nayi. Bayan nasha ya fara tambayata me zanci, sunayen abincin da yake lissafowa ne suka sanyani amai da gudu na tashi na nufi toilet. Ko sunan abinci banason naji ga yunwa tana addabata amma ko zakici yacemin sai naji zuciyata na tashi, malt na samu nasha kafin na kwanta, itama ina bacci ta tasomin na tafi na amayar. Washegari da safe mukayi waya da Mama, ban sanar mata ba so nake na bata mamaki idan na koma gida naje saidai ta ganni da abuna, Mum ma yacemin kar na sanar mata domin basu san za'ayi min aikin ba. Bayan two weeks muka koma aka duba babies suna lafiya lau, a ranar muka baro Dubai domin 'kasar ta isheni, cikina har ya fara fitowa amma kayan da na saka basu bayyanar dashi ba Ko da muka shiga jirgi hannun Aliyu na kan cikina, shi gani yake laulayin da nakeyi zaiyi affecting cikina saida na sanar masa yanda abun yake lafiyarsu ce ta sanyani hakan tukuna ya barni na huta. Muna isowa gida naji wani annushuwa, twins na hango suna d'ago mana hannu muka 'karasa wurinsu, a tare sukayi hugging d'ina suna tsalle na cije baki domin sun danne min babies d'ina amma ban nuna ba, Aliyu yayi 'ko'karin janyesu nace masa a'a. Bayan sun sakeni muka gaisa da Raudah, itama hugging d'ina tayi tace "lallai Dubai ta kar'beki kinga yanda kikayi fresh kuwa?" Murmushi na mata ba tareda nace komai ba na nufi Mum, dur'kusawa nayi ya d'agoni tareda hugging d'ina tace "welcome home". Turarenta ne ya daki hancina naji amai na tasomin, 'ko'karin dannewa nakeyi amma na kasa da sauri na bar jikinta na nufi wurin da zanyi. Gaba d'aya wurina suka yo cikin damuwa Mum ta dafani tace "sannu Bilkisu dama...." Tsayawa tayi da maganarta ta fara 'karemin kallo, wani faffad'an murmushi ta saki na sunkuyar da kaina, Raudah ganin yanayin mum yasa ta zare ido tace "OH...MY...GOD!!" Da alamu twins ne kawai a duhu domin sai kallonmu sukeyi, dukkanmu fuskokinmu d'auke da murmushi. "Muje ko? Ya kamata ku samu ku huta saboda gajiyar tafiya" Mum ta fad'a tareda yiwa Aliyu alamun tana son magana dashi, gaba sukayi nayi hamdala domin turarenta ya dameni, jan hannuna tayi mukayi gaba tace "how many weeks?" "14" na fad'a ina murmushi, hannu ta saka ta dafa cikina tace "haba, ni naji abu ya tokareni nayi tunanin d'inki ne, I am so happy Bilkisu wallahi bazan iya fasalta miki farin cikin da nakeji a yanzu ba, nasan munyi maganar da ya Aalee yace zai duba ya gani, ashe shammatarmu yayi". Kawunan twins ne suka le'komu a tare sukace "wai dama ciki ne da Aunty B?" Tsalle sukayi tare amal tace "Allah yasa twins ne irinmu". "Ba amin ba wannan rashin jin naku ina zata kai shi? Ku jira ma ya Aalee yasan abinda kukayi sai jikinku ya gaya muku". Gaba sukayi cikin sauri suna dariya nace "me sukayi?" "Hm kibar yarannan ai bana fatan ki haifi twins, wallahi shegen neman magana amma zaiyi maganinsu ne, mota suka d'auka ba'a saniba ita kuma Mum bataso ta musu fad'a kinsan sune auta". Ko da muka je gida jansu Mum tayi tace "ku barsu su huta anjima sai kuje". "Mummy dan Allah labarin Dubai kawai zata bamu". "Saboda baku ta'ba zuwa ba? Ku wuce mu tafi gida" Mum ta fad'a tareda jan hannayensu, gidanmu muka nufa muna zuwa Aliyu ya shiga wanka, kwanciya nayi kafin ya fito na fara bacci. Tashina yayi na shiga wanka saidai gaba d'aya 'kamshin toilet d'in baimin ba, sabulun da na d'auka ma sai naji yana neman sani amai, wankan gaba d'aya banason yi haka na watsa ruwa a fuskata na fito na zura kayana na koma bacci. ********* *SALEH* Bacci ne ya d'ebeta bayan ta gama koke kokenta taga Saleh yayi mata banza, tunda yayi mata sannu sau d'aya yayi kwanciyarsa sai bacci, takaici ya mata katutu domin ita fa ba haka taji ana yi ba, kamata yayi ya rungumeta yayi ta rarrashinta bazaiyi bacci ba ma har sai tayi, yana shafa ta Yana I love you thank you, amma dan wula'kanci ya kama wuri ya kwanta sai baccinsa yakeyi. Kafin tayi baccin ya juyo sai d'aya ya dubata, bayan ya tabbatar ba wani matsala dake bu'katar kulawa ya koma baccinsa, tunaninsa idan ya ta'bata zata tsorata ne shiyasa ma ya barta baisan hakan haushi ya bata ba. Da safe shi ya shirya musu breakfast sannan ya tasheta yace zai fita ta tashi tayi breakfast, amsa masa tayi da to ta koma baccinta ya fita. Haka yayita hidima da ita kusan kwana uku har saida ya gaji ya rabu da ita, zamansu ya canza sun fara treating juna a matsayin mata da miji amma babu wata soyayya ko sha'kuwa. Saleh ba shirin fita taje ta sameshi tace "honey zan fita zanje asbiti". Kallonta yayi gata dai lafiyarta 'kalau yace "meke damunki zakije asbiti". "Jikina ne nakejin ba dad'i sosai kamar dai ciki ne dani shiyasa nakeso naje asbiti a dubani". Tashi yayi cikin sauri yace "muje na kaiki". Suna tafe Bilkisu ce kawai a ransa yana tuna irin gwagwarmayar da sukayi a kan samun ciki, ji yake ina ma Bilkisu ce ta kawo masa wannan labarin, hango murmushinta yake yayin da take sanar mana wannan magana, hango kansa yakeyi suna celebrating tare, meyasa 'kaddara zata masa haka? Bayan an dubata aka samu positive, dukda cewa Saleh yayi farin ciki amma ba kamar dai ace Bilkisu bace. Suna biyo hanya ta fara nuna abubuwa tana cewa ya siya mata, a 'kofar gida ya ajiyeta ya juya. Shiga tayi da ledarta cike da kayan kwad'ayi suka had'u da Hajiya, fara'a Hajiya tayi ita kuwa Hadiyya ta sha kunu. "A'a ina kukaje haka da safiya?" Ta fad'a tana kallon ledar hannun Hadiyya, matsar da ledar Hadiyya tayi tace "asbiti mukaje ance inada ciki". Yage baki Hajiya tayi tace kai masha Allah alhamdulillah, ga inda ake abun arzi'ki yaje ya mannewa juya gara ma da na rabashi da ita gashi kafin aje ko ina Allah ya bashi arzi'ki, akwai wani abu da kikeso ne na miki?". "Bakomai amma idan inaso zan miki magana". Tana gama maganar tayi gaba, ledar hannunta ce ta yage rake da d'ata da gyad'ar da aka siya mata suka zube, tana ganin Hajiya na kallon d'atar ta kau da kanta ta kwashe abinta a mayafi tayi gida. Part d'in Sultana ta shiga ta sameta tana yiwa Huda kitso, gaisawa sukayi ba sakin fuska dukda haka ta zauna har aka gama yiwa Huda kitso. Sultana na 'ko'karin tashi ta fara aikace aikacenta Hadiyya tace "um maman Ahmad tambayarki nazo yi". "Akan me?" "Akan tsohuwar matar Saleh, ina son nasan komai a kanta". Dariya Sultana tayi tace "nidai abu d'aya zan fad'a miki, matar Saleh macece mai ha'kuri da kirkin da ban ta'ba ganin wata mace dashi ba tunda nake, a gidannan nice aminiyarta sauran kuma kije ki tambayi jumana ko Hajiya da kanta inada abin yi". Shigewa Sultana tayi ta barta a zaune, tashi tayi ta nufi part d'in jumana itama dai bata sakar mata fuska ba domin bata son raini, bazata tsaya tana kula wannan 'karamar yarinyar ba. Ganin dai babu biyan bu'kata ya sanya ta nufi wajen me gayya me aiki wato Hajiya, tayi sa'a kuwa kursum tazo. Bayan sun gaisa ta tambayi Kursum wacece Bilkisu, gyara zama tayi tace "wannan munafukar? Ai Allah ne yayi mana maganinta tazo ta nemi ta mallake Saleh saida muka nuna mata muma fa ba a zaune muke ba, ga masifar naci duk abinda ake mata saboda ta fita da kanta ta ki saida ya saketa dan dole....." Babu pull stop ba comma Kursum ta dinga zayyano ba'kin Bilkisu, duk wannan labarin abubuwa biyu Hadiyya ta fahimta, irin tsananin soyayyar da Saleh ke yiwa Bilkisu da kuma tsanar da Hajiya tayi mata, hakan na nufin yanzu ita ce 'yar gaban goshin Hajiya, sannan ta lura da yanda Saleh ke jin maganar mahaifiyarsa wanda ta d'auki hakan a abinda ya Sanya baya sonta yanda ya kamata, zata san yanda zatayi ta janyo Saleh gareta ita kad'ai ba tareda ta hadashi da wata ba ko da kuwa mahaifiyarsa ce. 50 Ranar a wurin Hajiya Hadiyya ta wuni, saida taci abincin rana tayi takeaway na dare sannan ta koma part d'inta. Washegari da wuri ta tashi ta zauna ta saka tv a gaba har Saleh ya tashi, saida taji tashinsa sannan ta nufi toilet ta fara kakarin amai kamar da gaske. Fitowa tayi cikin kalar tausayi tace "Honey bazan iya girki ba, ina saka 'kafata a kitchen nake jin amai ko zaka kar'bo mana a wurin Hajiya? Gaba d'aya banason ganin kitchen d'in ma dan Allah". Rufe kitchen d'in yayi ya fita kar'bo musu abinci a wurin Hajiya, dawowa yayi da d'umamen tuwo ta kalla a yamutse tace "wayyo Allah na d'aukeshi daga gabana banason gani". Kallonta yayi shi dai baiga wani alamun ciwo a tattare da ita ba saidai maybe haka masu cikin suke, duk 'ko'karinta na yin kalar ciwo ta kasa. D'aukan tuwon yayi yaci yace "me kikeso?" "Koko nakeso da 'kosai". "Shikenan bari na duba waje idan akwai sai na siyo miki". Tashi yayi zai fita tace "a'a dan Allah banason na waje na Hajiya nakeso, na waje amai zai sakani". Kallonta yayi yace "Hadiyya aikin 'kosai aiki ne mai yawa sannan kinga gari ya jima da wayewa, ki bari na siyo miki gobe sai na fad'a mata da wuri idan kinaso". Hard'e hannayenta tayi ta turo baki tace "barshi banaso". Komawa gefenta yayi ya zauna yace "kar kiyi fushi mana, naga Hajiya ta tashi da shirin funkaso ne kar na sake had'ata da wani aikin". "Shikenan naci funkason kaje kayi wanka saboda lokaci ko?" Yana tafiya wanka ta fita harda saurinta, tana shiga part d'in Hajiya ta fashe da kuka. "A'a Hadiyya me kuma ya faru kike kuka?". Cikin kuka tace "Hajiya Saleh baya sona ko kad'an, na fad'a masa 'kosai nakeso kuma na gida amma wai saidai ya siyomin, kuma ni banason na waje, a 'karshe ma cewa yayi saidai naci kaina bazai ro'ke ki kimin ba yayi tafiyarsa ya barni gashi yunwa nakeji". "Kai Saleh me yake damunsa ne? Anya asirin da yarinyarnan ta masa kuwa ya sakeshi? Kiyi ha'kuri zan masa magana kuma indai 'kosai ne kin samu yanzunnan zan wanke waken dama an 'barzo min shi, zauna anan zaizo ya sameni, ace amanar Allah mutum ya kasa ri'keta? Ko ba dan ke ba ko dan wannan juna biyun ai ya tausaya miki, zaizo ya sameni ne". Hajiya ta fad'a tana nufar kitchen, kwanciya Hadiyya tayi akan kujera tace "To Hajiya tun yanzu ya fara nunamin haka ina ga ciki ya tsufa? Idan na haihu ma zai iya kashe jaririn tunda ya nunamin shi baya son cikinnan". Dawowa Hajiya tayi a fusace tace "shi yace bayaso?" "A'a Hajiya kawai naga yanayinsa, amma dan Allah Kar ki fad'a masa sai ya 'kara jin haushina". "Shikenan zauna ki huta zanyi magana dashi". Tana zaune hajiya ta wanke waken ta markad'a a blender duk 'yar lele na kwance, ta gama markad'awa Saleh ya shigo. Yana sallama Hajiya ta balbaleshi da masifa "Allah ya wadaran halinka, shekara nawa kayi kana neman haihuwa Allah ya hanaka yanzu da ka samu shine zaka fara wasa da damarka ko? Saboda kaga yarinya mai ha'kuri kake wula'kantata, me yarinyarnan ta tsare maka? Meyasa kakeson azabtar da rayuwarta, kai kenan daga wannan sai wancan ko imani baka dashi? Ka duba juna biyun dake jikinta ki dan shi ai ka tausaya mata, daga yau yarinyarnan tace tana son abu ka hanata wallahi sai na 'bata maka". Shiru yayi har Hajiya ta gama banbanminta sannan ya fita yana tunanin me yayi da za'a masa fad'a haka? Ko dai 'kosan da tace tana so ne ya janyo haka? Hadiyya dai bata rabuwa da drama. Yana fita Hadiyya tace "Hajiya wannan bilkisun da ya aura a baya anya ba 'yar shed'anu bace? Nifa gani nake ita ta mallakeshi wallahi ta hanashi sakat, wani lokacin yana bacci saidai kiji yana ambatarta na rasa dalilin hakan, ko kuma idan zai kira sunana ya ambaceta, ni fa gani nake sallah ma ba dai-dai yake ba saboda sai inji kamar yana fad'an sunanta a sallah, anya baza'a nema Masa magani ba? Indai ya zauna a haka zaiyi ta wula'kantani ne". Kafin Hajiya ta amsa maimuna ta shigo a gigice, a firgice suka kalleta Hajiya tace "menene hakan? Lafiya kuwa?". Wayarta ta ciro daga jaka hannunta na rawa ta danna ta nuna musu, zubawa wayar ido Hadiyya tayi tace "nifa banga komai ba". "Hajiya wai tsabar wula'kanci sa'idu aure zai 'kara? Ashe duk wahalar da nasha akan Amir yana cemin baida kud'i kud'in aure yake tarawa, jiya na d'auki wayarsa ina bincike kawai naga hoton wata a take ya sanarmin ita zai aura kuma ba wanda ya isa ya hana auren". zama Hajiya tayi tace "to meye abin tashin hankalin?". "Hajiya ga tashin hankalin nan kina gani? Kishiya bala'i ce masifa ce wallahi, mutumin da watarana yake fita ya barmu babu abinda zamu ci shine yake zancen sake aure? Rashin lafiyar Amir gaba d'aya dubu biyar ya kashe duk sauran ku kuka biyamin a hakan zaiyi aure? Wallahi Hajiya a san abin yi bazan bari yayi aureba, kuma wadda zai aura da gani tangararriyar 'yar iska ce". Tashi Hadiyya tayi ta nufi kitchen tana 'ko'karin fara suyar 'kosai, maganar Hajiya taji ta fara faking amai tare da fita daga kitchen d'in, zama tayi gefen Maimuna da ke ta sambatu ita kad'ai amma batace mata komai ba. Bayan d'an lokaci Hajiya ta dawo da 'kosai a faranti, zama Hadiyya tayi ko a jikinta ta fara cin 'kosan yayin da suka ci gaba da maganarsu, cikin 'kaguwa Maimuna tace "Hajiya wannan mutumin da mukaje wajensa yayi mana maganinta mayyar can da farko wajensa nakeso naje, amma banida kud'i shiyasa nazo ki bani". Shiru Hajiya tayi tace "to ai nima d'an kud'in dake hannuna a aurennan duk ya 'kare, amma anya zaki koma wajensa? Kina gani dai itama aikin nata babu wata riba tunda bayan cutar da tayi saida ta dawo". "Hajiya shiyasa nace miki mayya ce amma yanzu ba ta fita dan kanta ba? Kuma bazata ta'ba dawowa ba? Nidai ko wajen su usman ko zayyad ki tambayarmin su bani dan Allah". "A'a usman Usman shekaran jiya ya kawomin kayan abinci sannan shima zayyad d'in ya kashe kud'i sosai, kuma sun bada gudunmawa 150k dukkansu a aurennan, bazai yiwu na tambayesu kud'i yanzu ba kuma zayyad yayi tafiya usman kuma aikin nasa sai a hankali, bari Saleh yazo mu gani". Wani takaici Hadiyya taji jin ance minjnta ne zai bada kud'in, duk yanda zatayi ta hana a basu kud'innan sai tayi, ko da kuwa hakan zai janyo rasa abinda ke cikinta ne sai tayi, zama tayi ta fara tsara 'karairayi a ranta har ta samu shawara tsayayyiya, tashi tayi ta nufi band'aki ta fito tace da Hajiya  "Hajiya zanje asbiti banajin dad'in jikina, marata ciwo kuma yanzunnan ya fara". "Subhanallah to bari na d'auko mayafina muje Allah yasa dai lafiya". "A'a Hajiya kiyi zamanki wallahi yanzunnan zan dawo nasan ba wani abu bane babba, sannan ga Maimuna ya kamata ki zauna da ita". Bata jira me Hajiya zata ce ba ta fita, part d'inta ta nufa ta zari mayafi ta d'auki kud'i a ma'ajiyar Saleh ta nufi gidansu, da uwarta suka gama tsara abunsu. Wani 'karamin asbiti suka nufa wanda suka san za'a musu abinda sukeso, asbiti ne da ya shahara da zubar ma da mata ciki, bayan sun gama yiwa likitan bayanin abinda sukeso yayi da kuma kud'in da zasu bashi Hadiyya ta kira Saleh, likitan ne ya kar'ba yace. "Good afternoon sir, matarka ce Hadiyya Bello tazo asbiti tayi complain ciwon mara, da na duba sai naga tana critical condition babynta a bayan mahaifa yake yanzu haka tana tsananin zubar da jini, mun shiga da ita theatre za'ayi aiki saboda muna gab da rasata idan ba'a yi aiki an maida babyn cikin mahaifa ba, ana bu'katar 110,000 naira, mahaifiyarta tayi signing kawai ana bu'katar amincewarka ne". Cikin tashin hankali saleh yace "wani asbiti ne? Ganinan zuwa". Kafin ya masa kwatancen asbitin ya kashe wayar gaba d'aya, kira Saleh yakeyi amma ta'ki shiga hankalinsa yayi matu'kar tashi, kiran Hajiya yayi itama tace bata san ina taje ba, kiran number Ammy yayi itama not reachable babu.ahir. Sai bayan awa d'aya sannan Hadiyya ta kunna wayarta ta sanar masa tana gidansu har an mata aikin ta koma gida. Cike da damuwa yaje ya sameta tana kwance a lullu'be, zama Ammy tayi ta dinga shirga masa 'karya sannan tace ya kamata da sun fita su wuce gida domin Hadiyya ta jigata, kud'in kuma ga account number d'in likitan ya tura masa. Haka kuwa akayi a take ya tura kud'in sannan ya d'auki Hadiyya suka tafi gida sai dafe ciki takeyi, saboda abin nasu yayi dai-dai saida aka d'an yanka cikinta kad'an aka nad'e da bandeji duk dan ya yarda, murna Hadiyya keyi a cikinta domin burinta ya cika, yanzu sai ta gani idan Hajiya nada rashin imanin da zata kar'bi kud'i a hannunsa. ********** Da'kirewa nakeyi yana 'ko'karin jana zuwa bathroom, tuni idona ya ciko da 'kwalla amma yau Aliyu bai ko tausayamin ba, kwanana hud'u kenan babu wanka kafin kuce 'kazama ba laifina bane, na tsani 'kamshin sabulu, man shafawa, turare kai hatta towel d'in wankan na dena d'aurawa, saboda haka idan na shiga sai an d'anyi kwaskwarima da ruwa na fito, yau dai dubuna ta cika Aliyu ya kamani. Tattaro 'karfinsa yayi sai gani a kafad'arsa for the first first time, tsoro ne ya kamani yace "kina motsi zamu fad'i fa". "Dan Allah ka bar wankannan yau Allah gobe nayi al'kawari zanyi kaji? Wallahi gaba d'aya 'kamshin bathroom d'innan bana sonshi ka fahimceni mana". Ajiyeni yayi ya rufe 'kofar da key sannan ya zubamin ido, hard'e hannunsa yayi a 'kirjinsa yace "haba Bilkisu kwana uku ba wanka bai isheki ba sai kin 'kara da na hud'u? Wato shiyasa kika koma wanka da hijab saboda ki wanke fuskarki ki fito ban ganeba, sorry to say amma a kwana biyunnan naji jikinki ya d'an fara canzawa, look idan kikayi wankannan yau gobe na amince kiyi fashi sai kiyi jibi, amma ko d'an deoderant kina shafawa mana". Wani kallo na wurga masa, a ta'kaice dai so yake ya cemin ina wari amma ni ba abinda nakeji, dukda daud'ar na damuna amma sam banajin wani odour a jikina. Had'e rai nayi nace "ka fito kace min wari nake kawai". "Kai Bilkisu you are making this hard, ko ma mene dai idan kinyi wanka sai muyi idan ma rufeni da duka zakiyi sai kiyi amma bazaki fita daga bathroom d'innan ba sai kinyi wanka". Hawaye ne ya fara bin fuskata abinka da hormones d'in me ciki, kuka na fara nace "duk zamana dakai baka tsiri cewa ina wari ba sai yanzu, sai yanzu ka tsiri ka fara wula'kantani ka kirani da 'kazama". Dur'kusawa yayi a gabana ya saka hannunsa ya goge hawayen yace "bance ke 'kazama bace Bilkisu kinada matu'kar tsafta, kawai cewa nayi ya kamata kiyi wanka ko dan kiji dad'in jikinki". "Ni inajin dad'in jikina a haka meyasa kakeso dole sai nayi wanka? Wallahi na tsani sabulunnan da man da nake shafawa da turaren da komai ma me 'kamshi". "Duk yau zan canza miki su dake zamu fita ki za'bi wanda kikeso, for now kiyi wankan tukuna please". Towel ya mi'komin nayi cilli dashi domin banason 'kamashinsa, shiga yayi ya kunna shower ba fara kici kici da 'kofar fita, kamoni yayi ya turani a cikin shower d'in ya janyo 'kofar, ruwan dukana yake ina dukan glass door d'in har na ha'kura na tsaya ruwan na dukana tun daga kaina banyi yun'kurin d'aukan sabulu ko sponge ba. Idona a rufe naji alamun ya bud'e 'kofa, ban bud'e idona ba naji yayi wrapping hannunsa a cikina yana shafawa a hankali, kansa na wuyana, kissing wuyana ya fara tareda shafa cikina zuwa 'kirjina, ajiyar zuciya na sauke na sake manne bayana da jikinsa, abinda ya kamata yayi kenan ba wai ya cicci'boni ya kawoni ba. Hannunsa ke descending zuwa 'kasa-'kasa, cikin kunnena yace "sorry baby" sai jin soso nayi a jikina, struggling na fara na gudu amma ina, ya kamani ram. Saida ya wankeni tas har round uku, ji nake kamar bazan iya numfashi ba domin sabulun ya gama shiga kaina, ganin haka yasa ya ha'kura da wankan a hankalin nace "mugu". "That's me" ya fad'a tareda fito dani daga shower d'in, towel ya yafamin na cire na yar na d'auki zanina na d'aura, shi kansa zanin rabonsa da wanki.....Kar dai a tona domin 'kamshin omo da sabulun wankin ma matsala ne a gareni. Bai ma yi gangancin cewa na shafa mai ba, wardrobe na nufa na fara laluben kayan da zan saka wanda suke sababbi, jikina har wani sakayau yayimin gaskiya Ina d'auko kayan ya kar'ba ya ajiye a gefe, kallonsa nayi ina 'ko'karin fara mita ya had'e lips d'insa da nawa, zanin ya kunce ya ri'ke gefe da gefen a hannunsa yace "ko baki so na 'karasa abinda na fara a can?" Amsarsa itace pushing d'insa da nayi zuwa gadon, dariya yayi yace "I love this side of you". "Ba wai na huce bane ba, I will deal with you later". Na 'karashe maganar ina attacking lups d'insa....... Washegari da kewar gida na tashi sosai na kira Mama muka sha hirarmu, har yanzu ban sanar mata inada ciki na so nake saidai ta gani kawai, Allah yasa ranar da zanje naga Saleh, I will rub it on his face domin a yanzu cikin ya fito sosai bazaka ta'ba cewa four and a half months yake ba, har ya fara min nauyi babu mai cewa 5 months nake, dukda saura sati d'aya yayi 5 d'in. Muna gama wayar na nufi mirror na duba fuskata, duk 'kin wankannan nawa banaso naga abu ya ta'ba jikina, sai nayi 20mins a gaban mirror abinda a da bai dameni ba amma yanzu idan naga 'kurji a fuskata kamar nayi kuka nakeji, ban saniba ko dan jikina ya 'kara kyau ne nakejin haka. Abincin da nake ci yanzu ya banbanta, wasu had'i chefs d'in ke min na masu ciki, nidai ci nakeyi kawai amma tabbas a jikina naga banbanci, babu abinda ya canza a fuskata ko irin nayi muninnan na masu ciki sai ma wani haske da nake 'karawa ga gashina ya ninka yanda yake a tsayi, ina ma zai zauna a haka. Bayan na 'karewa kaina kallo na d'auki mayafi na nufi part d'in masu aiki, tuwon gero na samu sunayi ya bani sha'awa, sa'a nayi lokacin da naje ana kwashewa na zauna. Gaba d'aya sun rud'e ganin zanci abinci a wajensu, plate jikar Inna kulu ta d'auko dukda a wanke yake ta sake wankewa sannan ta mi'ka aka zubamin tuwon, nama naga ana tsamowa daga miyar ana sakamin nace "Inna kulu Naman d'aya ya isheni fa". "A'a Hajiya ai ko duka muka saka miki bazai isheki ba nawa yake?". "A'a Kar ya wuce d'aya fa inna kulu da gaske ya isheni". Kar'bar tuwon nayi naga ta sanyamin nama hud'u, tukunyar miyar na nufa na rage naman sannan na fita bayan na musu godiya. Ina komawa naga Aliyu ya dawo yana nemana, garden na nufa tareda yi masa alamar ya biyoni na zauna a kujera me table, kafin ya 'karaso na fara ci. Yana zuwa ya sunkuya ya kalli tuwon yace "meye wannan kuma?" "Tuwon gero, ci kaji wallahi su inna kulu sun iya girki, miyar tayi dad'i sosai". 'ko'karin janye tuwon daga gabana yayi na ri'ke plate d'in nace "please, dan Allah kar muyi haka da kai, ka barni naci abinda nakeso". "Haba Bilkisu wannan wani kalan tuwo ne kike ci haka? Ai sai ya cutar da yarana". "Idan har abu zai cutar da yaranka a tunaninka zanci ne? Duk abinda zaka ga na saka a cikina a yanzu babies d'inka keso ba ni ba, sannan abinci be babu abinda zai musu, stop worrying about stupid things instead kazo kaci kaji yanda yake". Bai cemin komai ba ya zauna ya kar'bi spoon d'in hannuna, loma d'aya yayi ya mi'komin saida na tashi da tuwonnan, rabona da tuwo har na manta yanzu kuwa zaryar wajen su inna kulu ta kamani. Bayan an gama ci na jingina na fara rocking kujerar nace "yaushe zanje gida? Ina kewar gida sosai". "Indai kikayi wanka duka satinnan babu fashi Monday zaki je gida". Kallonshi nayi zan masa jayayua yace "anjima zaku je da Raudah ki za'bi sabulu da man da kikeso ki dinga amfani dasu zan kwashe wad'ancan na zubar kafin ki dawo". Wani kallo na masa, wace irin asara ce wannan? Set d'in sabulun da man da na gashi harda wasu abubuwa 40,000 ya siyamin shi, amma yace zai zubar? Girgiza kai nayi nace "akwai masu bu'kata zan kai musu ba sai ka zubar ba, akwai mabu'kata da dama a duniya, wasu rabonsu da wanka sunfi sati saboda rashin sabulun naira 50, amma kai kana neman zubar da na 40,000 ya kamata ka yawaita taimakawa mabu'kata, ka sani saboda kana da arzi'ki hakan ba yana nufin kowa yana da shi ba". "Duk shekara muna fitar da zakka, sannan every month muna bada contribution ga wata 'kungiya dake tallafawa matasa marasa aikin yi". Gyara zamana nayi nace "matsalar zakkar da kuke fitarwa shine, kuna bayarwa ne ga mutanen da suka wadata, zaka fidda zakka ka dan'kawa wani mutum kace ya bawa wad'anda suka kamata, a tunaninka zata kai inda akeso taje? Idan ka fitar da zakka ka samu magidanta masu iyali wad'anda ke cikin talauci da wahala ka basu 100k kowannensu, wani shikennan ka azurtashi har abada, amma ka dan'kawa wani mutum ya saka a gaba ya ciri nashi kason, ya d'auka ya rabawa 'yan uwansa da abokanansa, saboda tsananin rashin imani sai yabi talakawa da 1000 ko yabi 'kananun yara da 20 20, ko yabi mabarata da 200 naira, wannan wula'kanta zakka ne, shiyasa 'kasarmu bata ci gaba, ayita cewa masu kud'i basu fidda zakka saidai yawancinsu suna fitar da ita ne ta mummunan hannu". Hugging d'ina yayi ta gefe yace "na godewa Allah da ya had'ani dake Bilkisu, zan duba wannan maganar da Dad gida kuma ki shirya Monday wannan time d'in insha Allah kina gida, Amma fa sai kinyi wankannan". Ko da mukaje wajen sayen sabulun kasa za'ba nayi gaba d'aya wurin ma hawarmin kai yayi, yanke shawarar komawa shafa coconut oil ko man zaitun nayi, sabulu kuma...wannan sai wani ji'kon. Ranar da zan tafi gida inata tattara kayana, tsarabar da nayi daga saudiyya tana nan haka na hada da kayan sawa ta, rakiya suka min sannan na tafi gida wannan karon ni kad'ai babu d'an rakiya...... 51 *SALEH* Ko da suka isa gida da 'kyar Hadiyya ke takawa, part d'in Hajiya suka fara shiga Maimuna tana nan, kwanciya Hadiyya tayi tana wash Hajiya tace "sannu wai garin yaya haka ta faru? Anan fa lafiya lau muke zaune". "Wallahi Hajiya ni kaina nayi mamaki, kawai ina zuwa Asbiti ba sai jini ya fara malala ba? Aikuwa a take ake shiga tiyata dani, dake ma likitan d'an aljanna ne da yaga halin da nake ciki bai tsaya sai an bashi kud'i ba, da wani ne akan 110,000 wallahi bazai ta'bani ba saidai na mutu amma haka akamin aikinnan". "Ikon Allah, ai na d'auka idan akayi aikin ba sai an kwana biyu allura ta sakeki ba za'a dawo?" Maimuna ta fad'a cikin mamaki "A'a yace ba matsala ai aikin ba wani babba bane ba shiyasa ya sallamoni". "To ai naga ma'kwabciyata da aka mata irin wannan aikin kwananta uku a asbiti sannan aka sallamota". "Ta yiwu tanada 'kan jiki ne ko kuma na gwamnati taje, amma aikin sama da dubu d'ari ai baza'a ri'ke mutum a asbiti ba". Ganin Maimuna na neman 'kureta yasa ta danne cikinta tace "washh, bari naje na sha magani sai da safenku". Tashi tayi Saleh na ri'ke da ita suka fita suka nufi gida, suna fita Maimuna tace "wannan wace irin masifa ce, yanzu ba yanda za'ayi ya bani kud'innan". "Kinga tashi ki tafi gida kafin dare yayi, ki d'an laluba ki gani ko zaki samu ko bashi ne daga baya sai na kar'ba a wajensu na biyaki". "Zan tambaya na gani bari naje gida na bar yara, yanzu bani kud'in mota". Kud'in motar Hajiya ta bata ta fita, kafin taje gida saida ta tsaya neman bashi da 'kyar ta samu 10,000. Hadiyya kuwa tana zuwa gida ta narke a kan kujera, kayan jikinta ma saida Saleh ya tayata cirewa ya bata ruwa tasha domin tace ance kar taci abinci. Yana tafiya d'auko ruwan tace "indai inanan kai da kashewa danginka kud'i har abada". Kafin ta warke taci kud'ad'den magani a hannunsa sosai, gaba d'aya ta ajiye girki Hajiya keyi tana kawo mata, hakan yasa cefane ya koma hannun Hajiya hakan bai mata dad'i ba. Jinsu tayi da Hajiya suna zancen kayan abinci saida ta bari ya shigo ta tafi cikin d'aki sanya wayarta a kunne, da 'karfi tace "Ammy kiyi ha'kuri insha Allahu ji aro zanyi na kawo miki ki sayi kayan abincin. Zan tambayeshi ya aramin...... a'a ammy bazance masa haka ba". Fitowa tayi ta sameshi saida.suka fara hira sannan tace "umm Honey dan Allah aron kud'i nakeso ko 10,000 ne, yaya zuwaira ce ta tambayeni ni kuma na hannuna bai kai ba ...kai bazan iya maka 'karya ba kayan abincin Ammy ne ya 'kare mukeso mu harhad'a mu bata ta siya bataso ka sani da ace da kud'i ma a hannuna bazan tambayeka ba". Sunkuyar da kai tayi tace "Ammy tana shan wahala sosai, da inada hali wallahi bazan ta'ba bari ta rasa komai ba, 'yan mazan gidanmu basuda imani basa mata komai, matan ne ma ke d'an taimaka mata sai ni da nake nan lokacin take bani abubuwa ina kaiwa makwabta ana d'an saya, to yanzu yayyen nawa ma sai a hankali da inada hali ko, jari zan bata ta huta". Matse hawaye ta farayi yace "karki damu zan baki ki kai mata". "To nagode inada 500 sai na bata tayi cefane dashi". "Ki barshi zan bayar gaba d'aya". Godiya ta dinga masa har 'kasa, tausayinta yaji sosai ya tuna lokacin da Hajiya take irin wannan halin, irin wahalar da tasha wajen rainonsu da irin wahalhalun da suka sha suma, ji yayi a ransa Yana so ya taimakawa Mahaifiyar Hadiyya. 30,000 ya bata yace ta kaiwa ammynta, Hadiyya baki ya bud'e haka ta dinga zuba masa 'karairayi na wahalar da Ammy kesha. Maimuna kuwa duka hankalinta ya tashi akan kishiya, washegari da wuri ta nufi wajen malamin ta zauna ta fara masa bayani. "Malam taimako zaka min kamar yanda ka saba min a baya, wallahi ina cikin matsala duk aikinnan da ake akan ya saki aljihu na huta babu wani cigaba, ya matse komai ya hanani komai har abinci wataran sai nake gida na anso, to yanzu ya tsiro da maganar aure, bai wadata ni ba balle ya 'karo aure, so nake a hana aurennan ko ta wane hali ne". Sur'kullensa yayi ya buga 'kasa ya shafe yace mata "gaskiya hana aurennan zaiyi wahala amma za'a iya idan anbi ta wata hanya, saidai hanyar mai wuya ce". "Mecece ita? Ko menene zanyi wallahi". "Gashin kan matar da zai aura zaki samo min, da shi za'ayi amfani a cusa mata ba'kin jinin da ba shi ba ma duk namijin da yaso aurenta da kansa zai gudu". Ri'ke baki tayi domin wannan aiki ba 'karamin wuya ce dashi ba amma zata san yanda zatayi. Komawa gida tayi ta sami sa'idu ya dawo yana shirya yara zuwa islamiyya, tunda ta shiryasu fita boko ta fice sai yanzu ta dawo. "Sannu da zuwa" ya fad'a ba tareda ya kalleta ba. "Yauwa, kunci abinci kuwa amir?" Gyad'a mata kai yayi alamar eh sannan 'karamar tace "baba ne ya siya mana gurasa da nama a hanya". Jan hannunsu yayi ba tareda ya kalleta ba ya fita, saida ya kaisu makaranta ya dawo ya sameta tana sallah, zama yayi ya jira ta idar sannan yace "Maimuna meyasa kike haka? Har sai yaushe zaki canza ki dawo hankalinki? 'kananun yara kamar wad'annan ki fita ki barsu su kad'ai a gida, haka jiya nazo na samesu sun dawo daga islamiyya sunyi cirko cirko ga yunwa, cikin wannan rashin kulawar zakice kar na 'kara aure?" A fusace ta tashi tsaye tace "Kaga sa'idu banason wasu 'kananun maganganu, laifin waye da nake fita nake barin 'ya'yan a gida? Haka zaka fita ka barni babu ko sisi a gidannan wataran kayan abinci babu sai naje gida na kar'bo, a hakan adalci kakemin zaka ce zaka 'karo aure?" Cikin nutsuwa yace "menene bana ajiye miki a gidannan? Duk abinda kike bu'kata ina ajiye miki, a baya bana bari kayan abinci su 'kare amma me hakan ya haifar? 'Diba kika farayi kina sayarwa ba tareda sanina ba, nasan bana baki kud'i wadatattu amma ina baki wanda zakiyi bu'katunki dasu amma mene bana ajiye miki? Daga 'karshe zagi kika fara janyomin ana cewa ina zaluntarki har takai kina saida kayan abinci shiyasa na dena ajiyewa". "Kana kare kanka ne a kan zaluntata da kakeyi kawai!!". Ta fad'a cikin d'aga murya, girgiza kai yayi cikin takaici yace "Idan na zalunceki akan wannan fitar da kikeyi babu iznina fa? Barin 'ya'yan da kikeyi a gida da 'karancin shekaru bakya tunanin a cutar dasu ko a sacesu fa? Shima laifina ne?" "Laifinka ne mana da ace kana min abinda nakeso har na fita? To ka sani wallahi aurennan indai kaga an yishi saidai bana raye, wallahi tallahi bazan zauna da kowacce mace ba, bazakayi aurennan ba na fad'a maka, wannan ba shine Karo na farko da na hana aurenka ba kuma bazan dena hanawa ba sai ranar da na dena numfashi, kai bari kaji wallahi har mutuwa bazaka ta'ba aure ba bayan ni". Kallonta yayi cikin mamaki yace "au haka kikace, da yardar Allah sai nayi aurennan". "Wallahi bazaka yi ba" Murmushin takaici yayi yace "Allah ya shiryeki". "Dama ubanka ne yake shiryani? Sai kayi auren na gani, kai mu zuba ni da kai mu gani sai aga wanda ya haifu a ciminu ni da kai". Dawowa yayi yace "Maimuna na gaji da halayenki, ki tafi gidanku sai na nemeki". "Idan kaga na saka 'kafa na bar gidannan to da takardar saki na fita, idan ka cika isasshe ka sakeni kawai ka huta tunda ka gaji dani". Babu musu ya shiga d'aki ya fito da takarda a hannunsa, dan'ka mata yayi yace "Allah ya sani na fita ha'kkinki na miki duk abinda zan iya, zan d'auki 'ya'yana na kaisu inda ya dace". *********** Gyara zamana nayi kan kujerar jirgin wanda yayi dai-dai da jin wani naushi a cikina, murmushi ne ya bayyana a fuskata na dafe cikina, motsin naci gaba daji, Ina ma Aliyu y tare dani zanso ganin yanayinsa idan na sanar masa hakan. Jabir ne yazo d'aukana bayan na sauka, shiru yayi na d'an lokaci sannan yace "lallai Abuja tayi miki dad'i, Banda mama ta kiraki niyyarki sai kin haihu tukun kizo ko?" "A'a Yaya, inason zuwa wallahi sosai, satina biyu mukayi tafiya saida mukayi wata hud'u sannan muka dawo tunda muka dawo kuma banajin dad'i, amma yanzu ai sai nayi wata a gida zan koma". "Da gaske?" "Da gaske". "To Allah yasa, ya zaman abujan da dad'i?". "Da dad'i dukda dai ba kamar gida ba, Amma ba laifi gaskiya, na d'auko pics na gidana zan nuna maka su ka gani". Muna Isa gida day saurina na shiga, dariya jabir yayi yace "yi a hankali indai Mama ce ba guduwa zatayi ba, yanzu ma b ta taki take ba ta samu sabbin 'ya'ya". Ban bashi amsa ba na shige, 'kwala kira nayi nace "Mama!! Mama!!". "Na'am Bilkisu ina zuwa". Fitowa Mama tayi ri'ke da hannun yara biyu mace sa namiji, kallonsu nayi sosai nace "kamar 'ya'yan kawu badamasi Allah ya ji'kansa". "Eh sune mahaifiyarsu ce zatayi aure shine ta dawo dasu, Ni kuma tunda ni kad'ai ce shiyasa na d'aukesu". "Aikuwa naji dad'i wallahi, dama ina ta tunanin kina nan ke kad'ai". "Kina tunanina zakiyi wata bakwai baki ganni ba ko?" "Ooo mamana kinsan fa I miss you". Na fad'a tareda hugging Mama, murmushi tayi tace "Nima nayi kewarki, amma mamaki ma ya hanani magana wannan fa?" Ta 'karasa tana nuna cikina, murmushi nayi nace "Nima tashi nayi na ganshi a haka kawai". "Banason shashanci fa, da gaske nake ya akayi haka? Ko dai 'karya likitocin nan suka mana? Ko ma dai Yaya ne mun gode Allah, amma sai kin haihuwa zaki koma ko?" Dariya nayi nace "mama a kwanakinnan fa ya cika 5months, da saura kawai dai twins ne shiyasa yayi girma haka". 52 Bayani nake yiwa Mama yanda akayi min IVF, saurarona take kamar irin ina kora mata karatu saida na gama tace "Tabd'i lallai zamani yaci gaba, wato idan da kud'inka babu abinda bazaka samu ba a duniyarnan saidai Aljanna wannan sai kayi aikin alkhairi, amma an kashe kud'i sosai ko?" Kwantar da kaina nayi a cinyar Mama nace "wallahi Mama a zamanmu a can Dubai an kashe yafi 10million, ina wannan Hotel d'in burujul arab da akace duk duniya a yanzu babu mai kyansa? Anan fa muka zauna mukayi sati kusan uku, saida nace mu canza, gaskiya an kashe kud'i". "Wai, haka suke 'barnar kud'i?" "Hm Mama 'barna ma sai Kinga gidana bari na nuna miki". Wayata na d'auko na fara nunawa Mama yanayin gidan, girgiza kai takeyi kawai har muka gama, kallona tayi tsoro ya bayyana a fuskarta tace "Allah yasa dai kud'innan ta hanyar halaliya suke samunsu kar a dinga d'oraki akan haramun". "Mama ta halal ake samunsu a iya ganina, kinga fa kamfanin saida motoci ne dasu harda manyan motoci sosai, akwai motar da ya nunamin yace ita kad'ai kusan miliyan 150, sannan ga 'katuwar plaza mai hawa hud'u kowanne hawa shaguna ne kusan 10, hayar shagunan kansa kud'i ne, gaskiya dai Allah ya azurtasu". "To Allah ya kauda wula'kanci da gori nifa tunda akayi aurennan addu'a nakeyi Allah ya tsareki da gori da wula'kanci domin ni bajintarsu ta bani tsoro". Dariya nayi nace "Mama sunsan nima ba 'yar kananan mutane bace sannan ni fa 'yarta ce tunda mahaifina 'kaninta ne, sannan suna sona wallahi sosai ai kingani a lokacin da suka zo". "Hakane, yanzu dai zauna ki huta sai kije ki gaida su Adda sunata tambayarki". Zama nayi nace "to amma da so nake sai na kunce tsarabarnan sai na tafar musu da ita". "To hakan ma yayi amma ki huta tukun 'kafafuwan naki su saki, ko zakici abinci?" Girgiza kai nayi nace "saidai ko anjima yanzu bari na d'an tattaka naje". Tashi nayi na zari mayafina na fita, fitar da nayi Saleh da jabir suna shigowa, kallona Saleh yayi daga sama har 'kasa sannan ya zubawa cikina ido fuskarsa d'auke da mamaki, murmushi nayi nace "Sannunku". "Yauwa 'kanwata ina zuwa haka?" "Zanje na gaida su yaya ne". "Okay to saikin dawo". Ban sake kallon inda Saleh yake ba har na fita, ina jin alamun idonsa a kaina ban waiwaya ba, yayi wasa da damarsa gashinan tun kafin aje ko ina ya fara gani, kallon da na masa naga canji sosai a tattare dashi wanda banida lokacin zayyanosu. A gidan Yaya na samesu duka su ukun, sunyi murnar ganina sosai na kuma ci danwake, da alamu dai sai na biya bashin abincin gargajiyar da bana ci a Abuja. Da wuri na nufi d'aki na kwanta sannan na lalubi habibyna, sai yanzu na fara missing d'insa. _sai yanzu Kika fara missing d'ina?_ Dariya nayi nace "tunda na baro gida nake missing d'inka uban 'ya'yana, kawai banaso na takura maka ne nasan akwai ayyuka sosai a gabanka". _duk ayyukan dake gabana zan iya ajiyewa saboda nayi magana da uwar 'ya'yana, ya babies d'ina suna missing d'ina ko?"_ "Sosai ma amma fa sun maka laifi, yau sun fara motsi". "Da gaske? Oh my God!! I can't believe this meyasa zasumin haka? Ki d'aukomin a video". Murmushi nayi na shafa cikina nace "yanzu haka ma motsi sukeyi amma  bazan iya d'aukowa ba yanzu breech yake sai an kwana biyu". "Oh God I miss you so much, this bed is cold without you". "I miss you too, I miss your smile, your touch your warmth, I miss the whole of you anya  zan iya month ban ganka ba? I need you right now...." "Elaborate". Ya 'kare maganar cikin dariya. I miss your kiss, how your soft lips feels on mine, how wet you.....". "Ya Isa na fahimta yaushe zaki dawo?" "Ai ban gama maka elaboration d'in ba, sannan sai na haihu zan dawo". Alamun ya tashi ya zauna naji sannan yace "yauwa dama inaso na tambayeki, wace 'kasa kikeso ki haihu?" "Nigeria mana". "A'a Banda Nigeria ki za'bi wata". "No dear banaso naje ko ina na haihu anan Nigeria nakeso na haihu gaban 'yan uwa da dangi, banaso naje wurin da zan haihu daga ni sai kai". "Da gaske nake Bilkisu bazaki haihu anan ba, kinsan irin wahalar da matan Nigeria kesha wajen haihuwa? A cikin lokitoci 10 a wannan lokacin bazaki samu 6 da suke yin aiki tsakani da Allah ba, ni hospitals d'in nan yanzu tsoro suke bani gara muje can wata 'kasar, Australia ma nake tunani". "To Allah ya kaimu lokacin" na fad'a ina hamma, hira mukaci gaba dayi har ya sanyani bacci. Da 'kyar Mama ta barni nayi sati biyu a gida ta korani bayan naje na gaida Aunty. Tunda akayi scan aka ce babies d'ina maza ne shikenan family d'in Aliyu suka zama wasu daban, duk wanda ya fita sai ya shigo da kayan babies, har twins idan suka fita sai sun taho da kayan babies, kusan ma sunfi kowa murna za'a samu twins kamar su. Shigowa Aliyu yayi da leda ni'ki-ni'ki, kafin ma na kalli kayan nace "yau ma kayan baby ka siyo?" "Eh mana, idan naga kayan ne bana iya wucewa ban d'auka ba duba kigani rigunan sunyi kyau ko?" 'dagamin su yayi na kalla nace "sunyi kyau, amma ya kamata ki barsu haka fa, Mum tana nata ga Raudah da twins suma, sannan gaka ina zamu kai wannan kayan? Duk inda akayi 3months yara sun fara girma sai an canza su". Maida kayan cikin leda yayi yace "sai a bada su a siyo wasu, ki duba fa ni kad'ai ne namiji a gidanmu, yanzu da za'a samu maza har biyu ki duba farin cikin da family na zasuyi, kar kiga laifinmu". Daga ranar ma idan ya siyo kaya saidai ya kai wajen Mum, Allah kad'ai yasan yawan kayan a wannan lokacin domin wad'anda ke wajena ma sun cika akwati. Lokacin da na kai 8months tuni an gama d'inkin suna, kayan ma ba'a bani na gani ba wai na fiye complain ni kuma gani nake asarar kud'i akeyi. Fita mukayi tare dashi yiwa Dad barka da zuwa yaje umra ya dawo, twins muka samu suna hanashi sakewa Mum tana gefe tana murmushi, Raudah ce ma take yi musu magana. 'ko'karin dur'kusawa na gaisheshi nake ya d'aga min hannu tare da cewa "it's okay my daughter zauna". Gefensan Aliyu ya nufa ya d'aga amal cak ya ajiyeta a gefe sannan ya zauna dab da mahaifinsa yace "welcome Dad". Shafa kansa yayi yace "son". Maganar business suka fara har na gaji da zama, kafin mu tafi Dad ya bani tsarabata akwati guda, shima dai harda kayan baby, kai wannan family are obsessed with my babies. Tashi nayi da ciwon 'mara da baya, ina sanarwa Aliyu ya kira Mum, kafin wani lokaci sai ga mum, twins, Raudah, jannat harda Dad sunzo, gaba d'aya muka tattara muka tafi asbiti tun  ma ban fara wani labour sosai ba. Asbitin da nake zuwa anti-natal muka nufa, asbiti me mai matu'kar kyau da tsada, ko da aka dubani akaga da saura amma hakanan suka ri'keni, bayanin painless delivery suka min nace banaso. Kamar dai ba haihuwa nazo ba haka muka 'kare da 'karamin picnic, mukaci muka sha ko nace suka ci suka sha domin ni abincin ma na kasa ci ciwo yana cina kad'an kad'an Gajiya nayi muka koma gida, gidan Mum muka nufa inata safa da marwa suna baccinsu, Mum da Aliyu ne idonsu biyu har cikin dare lokacin da labour ya taso sosai. Muna zuwa muka shiga tare da Aliyu aka bashi kujera a gefena, shafa kaina yakeyi yana min sannu, kamo hannunsa nayi na dam'ke tareda sakin 'kara a hankali, gumi ke ketomin dukda sanyin Ac d'in dake d'akin. Aliyu kam dashi muke labour d'in indai nayi 'kara sai yayi, ji nake kamar na nausheshi saboda takaici. Gogemin gumin fuskata yayi da handkerchief yace "well done baby, keep pushing saura kad'an". Hannu nakai na makeshi ya dafe hannun yace "owww!! Ya da duka kuma". Ban kulashi ba naci gaba da fama na, bansan adadin da na d'auka ina labour ba na haihu, na farko kenan, gaba d'aya na gama gajiya ji nake tamkar 'kasusuwan jikina sun dena amfani. Aliyu ne ya tashi ya le'ka ya gano, wani farin ciki ne ya bayyana a fuskarsa ya dawo ya zauna, kissing d'ina yayi yace "we did it baby saura d'aya". "I did it, na gaji ya Aalee bayan iya ba". Ina gama fad'in haka sabon labour ya tasomin, cikin 18mins na haihu ya Aalee harda tsalle saboda murna, murmushi nayi ina kallon 'ya'yana idona cike da 'kwalla, na rasa da kalmomin da zan godewa mahaliccina. Lokacin da aka mi'komin su kasa danne hawayena nayi na fara kuka sosai, Mum ce tayi hugging d'ina ta gefe tana rarrashina. Sam na kasa samun hutu saboda ina haihuwa aka fara dandazon zuwa, yawanci friends d'in mum ne da Raudah, harda abokanan Aliyu. Dauriya kawai nakeyi ina murmushi amma ji nake kaina yana juyawa, hayaniya ke tashi a d'akin sosai, maida kaina baya nayi jin yana rinjayata na fara ganin mutane biyu-biyu, bud'e bakina nayi da niyyar na kira sunan Mum sai ganin wasu taurari nayi suna yawo a idona Kafin na fad'a duh I ************ *SALEH* Shiga gida Maimu tayi fuskarta kamar a d'aure, Hadiyya na zaune tana jiran Hajiya ta gama abincin dare ta d'auka ta tafi. Sallama tayi Hajiya ta fito da sauri tace "kin samu kud'in? Kinje wajen malamin ne ko yanzu zaki tafi?" Zama tayi tace "Hajiya ya sakeni fa!!" Ta 'kare maganar tana cillar da takardar gefe, d'aukan takardar Hadiyya tayi ta karanta da 'karfi *Ni sa'idu Adamu, na saki matata Maimuna saki biyu sakamakon rashin kwanciyar hankali da nake samu daga gareta* Nad'e takardar tayi tace "uhm, Allah ya kyauta". Zama Hajiya tayi cikin tashin hankali ta d'auki takardar hannunta har rawa yakeyi tace "me ya faru kuma maimuna?" Maimuna bata bo'ye komai ba ta sanarwa Hajiya abinda ya faru, shiru Hajiya tayi sannan tace "ni bansan abinda zance ba wannan 'kaddara ce". "Hajiya abincin baiyi bane yunwa nakeji fa" Hadiyya ta fad'a tana turo baki. Galla mata harara Maimuna tayi tace "abincin uban me? Ke ta abinci ma kikeyi a wannan tashin hankalin ko?" Tsaki Hadiyya taja tace "to tame zanyi? Tashin hankali kaina ya hau? Ni ta cikina nakeyi aure dai kin kasheshi me kuma ya rage?" Kallonta Hajiya tayi tace "wace irin magana kikeyi haka Hadiyya?" "Maganar gaskiya nakeyi, ai suk wanda yace d'an wani bazai huta ba shima Allah sai ya Hana nashi hutawa, duk wanda yace auren wani bazai zauna ba sai Allah ya hana nashi zama haka kuma aure rai ne dashi, ki godewa Allah ma da ba mutuwa kikayi yayi auren ba". "Kutumar ubancan, ke yarinyarnan ni kike fad'awa haka?" Maimuna ta fad'a a fusace Tashi tsaye Hadiyya tayi ta nuna Maimuna tace "an fad'a miki maganar kuma karki sake kirana yarinya domin ina shirin aje yarinya kwanannan, gaskiya ce daga 'kinta sai 'bata auren da kuka had'u kuka kashe shi Allah ya fara hukuntaku tun yanzu, ai hukunci ma da saura sai kin zauna kin rasa mijin aure". Tasowa Maimuna tayi tayo kan Hadiyya zata daketa, ri'keta Hajiya tayi sannan tace "Ke Hadiyya kar ki 'kara fad'an irin wannan maganar". "Barta Hajiya, dan ubanki banda an kashe auren ke kin isa ki shigo har kici arzi'kinmu? Ki sani aurennan mu muka so ayi yanzu idan muka so ya sakeki sai ya sakeki". Dariya Hadiyya tayi tace "da farko dai karki ta'bani ki shafamin gumin zawarci ki kashemin kasuwa a wajen mijina, sannan abu na biyu karki sake zagin ubana zan zage uwarki ne tas kuma ko a jikina, abu na 'karshe aure baki isa ki saka ayi ko a fasa ba, itama wadda kuka kora d'in wa'adinta ne ya cika, nikuwa nan na samu wajen zama, a tunaninki boka da malam su suke zaunar da aure? Ashe girman naki duk na asara ne wawiya ce ke? Da kissa ake siye miji, idan 'yan neman tayin zawarci kike nema sai ki kama ta gefenki gatanan, aure kuma da kike cewa Zaki kashe Bismillah idan baki kashe ba kafira ce ke". Sakin maimuna Hajiya tayi tace "Hadiyya, zagina kikeyi?" "A'a Hajjaju na isa na zageki? Uwar miji ai uwace idan akwai so da 'kauna, 'yarki ce dai ya kamata ki sake mata sabuwar tarbiyya inaga ta baya ta zube, sannan ta kiyayi kanta ta dena sako aurena a harkarta domin nafi 'karfinta wallahi, idan Kinga aurena ya mutu to Ni na mutu ko shi". "Ke Hadiyya Ashe bakida mutunci bakida kunya? Ni kike kallo kike fad'awa wannan maganar?" "Ai d'a me kuka shi ke janyowa uwarsa zagi, da Maimuna bata ta'bani ba da Babu yanda za'ayi abun ya shafeki, sannan da ace bansan wace irin uwar miji bace ke da bazan fad'i haka ba, sannan da bata ta'bo mijina da aurena ba bazan kulata ba domin babu abinda yakai mijina yanzu a wajena kuma ko ke uwarsa baki isa ki rabani dashi ba wallahi". Cikin zubewar girma Hajiya ta kalli Hadiyya tace "abinda zai fito daga bakinki kenan? Bayan na taimaka muku na baki auren d'ana saboda na rage muku wahalar da kuke ciki shine zakizo kina fad'an haka? Zamu gani salen zaizo ya sameni, idan kikayi wasa Zaki rasa aurenki ki koma cikin talaucinki na baya". Dariya Hadiyya tayi tace "talauci ai ya 'kare Hajiya tunda kika nunamin hanyar arzi'ki, yanzu kam mijina ya yanke mana wahala dukda ba a talauci nake ba munada wadatarmu daidai misali sannan aure ai ya gama mutuwa akan 'yarki, kuje kuji da abinda yake damunku ni nan zama daram, shi kanshi d'an naki yanzu zaisan ya auri mace sannan yanzu zan fara mulki a gidannan, idan kina ganin kina juya d'anki to daga yau wannan ya 'kare zaki san wa kika aurawa d'anki, ki zuba Ido ki gani zan gyara miki zama ke da wannan shekararriyar bazawarar domin Idan wannan halin zaki ci gaba ke da aure saidai kiga anayi". Fita tayi ta barsu cirko cirko, tana fita ta ciro wayarta daga zaninta ta kira Saleh, fashewa tayi da kuka tace "honey ka dawo gida ba lafiya ina cikin matsala, honey na shiga uku mutuwa zanyi shikenan zasu kasheni". "Meya faru?" Ya fad'a cike da damuwa, kukan 'karya takeyi tace, "Honey Hajiya ce da Maimuna suke neman kashemin aure, Maimuna ce aurenta ya mutu sai naji suna maganar abinda suka yisa Bilkisu tsohuwar matarka suk turo mata aljanu saboda ta bar gidanka shine nace sai na fad'a maka sai Hajiya tace wallahi yanda ta kori Bilkisu cikin ruwan sanyi haka zata koreni nima sai ta saka ka sakeni ka wula'kantani ni da cikina, honey kayimin rai ko dan cikina ka taimakeni karka sakeni, nasan Hajiya zata fad'a maka abu daban kuma nasan zaka amince da ita saboda mahaifiyarka ce, amma ka sani nima uwa ce a gareni banida riba idan nayi mata wani abun, dan Allah karka sakeni Honey kaji?" Shiru yayi sannan yace "shikenan ina zuwa gidan yanzu kashe zan d'aga waya". Cikin 'kan'kanin lokaci sai gashi ya dawo, zuwa yayi ya d'aukota tana zuwa ta dur'kusa kamar mutuniyar arzi'ki, kallonta Hajiya tayi tace "a yanzu zan nemi ka tsawatarwa matarka ne, ace yarinyarnan ta kalli tsabar idona ta zageni? Yarinyar da na haifa ta kalleni ta zageni saboda ka d'aure mata gindi ko? To ka ja mata kunne wallahi ta sake zan d'auki tsattsauran mataki a kanta". "Hajiya kiyi ha'kuri amma ni Banga abinda Hadiyya tayi ba, Hajiya kiyi ha'kuri ki dinga yi mata uzuri". Mamaki Hajiya tayi tace "wani sharri da 'karyar ta fad'a maka? Nan tazo tana nunani da yatsa tana cewa ban isaba, ta kalli Maimuna a gabana ta zageta ta fad'amin ban isaba a matsayina na uwarka sannan kace na mata uzuri? Saboda bance ka saketa ba ko? Ka sani ni na aura maka Hadiyya Kuma a yanzu zan iya cewa ka saketa kuma dole ka saketa". Girgiza kai yayi yace "Hajiya saki masifa ne a al'umma, banaso na Saba da saki sannan Hajiya kiyi ha'kuri da abinda zan fad'a, na auri Bilkisu za'bina kince Bata miki ba na miki biyayya na rabu da ita, kin bani Hadiyya na kar'ba saboda biyayya, dukda Hadiyya ba za'bina bace bazan saketa saboda umarninki ba, idan har Hadiyya tana miki ba dai-dai bane zan nema mata gida na rabaki da ita inaga hakan zaifi". Cikin fusata Hajiya tace "au laifina ma kake gani ko Saleh? Wato duk abinda ya faru laifina ne, ita Bilkisun da tana haihuwa zan rabaka da ita ne? Sannan babu inda zakaje da Hadiyya anan zata zauna". Shiru yayi Hadiyya kuwa tunda ta zauna ta sunkuyar da kai ko d'agowa batayi ba, Hajiya ce ta gama banbanminta suka tashi suka fita, suna fita Hadiyya ta 'kan'kame Saleh tace "honey tsoro nakeji, yanzu haka zanci gaba da zama da Hajiya? Honey zata saka ka sakeni ko kusa ko nesa, nawa nake da zan zama bazawara? Honey na ta'ba 'bata maka? Na ta'ba maka abinda zai saka kaji kana son sakina meyasa  Hajiya bata sonka? A tunanina tunda tace na aureka zata soni amma a kunnena naji tana cewa ta tsani taga wata mace tana cin dukiyarka, Honey ma taimakamin ka samamin mafita kar sumin abinda suka yiwa Bilkisu banaso na haukace". Kuka take wiwi tana ri'ke da Saleh dafata yayi Yana tausaya mata, ga yarinta ga ciki sannan ga matsalar family d'insa, tabbas dole ya nema masu mafita kafin su sanya mata ciwo domin ya amince da duk abinda ta fad'a masa tunda yasan abinda suka aikata ko me aka fad'a amincewa zaiyi. Rarrashinta yakeyi da kalamai masu dad'i, dukda har yanzu bai fara sonta ba amma tunda tana d'auke da cikinsa dole ya bita a hankali, sannan Idan ya biyema mahaifiyarsa yasan cewa bazai ta'ba zaman aure ba. Washegari bayan sunyi breakfast da kansa ya samu sultana ya ro'keta ta bawa Hadiyya abinci saboda bata iya girki sannan sun samu matsala da hajiya, tsabar son gulma yasa Sultana yin girki da wuri ta kaiwa Hadiyya, bayan ta zauna ta tambayeta abinda ya faru aikwa Hadiyya bata bo'ye komai ba ta sanar mata, dad'i ne ya kama Sultana tace "inama Bilkisu na nan wannan abu ya faru?" 53 Salati nakeji a kaina ba tare da naga komai ba, idanuna a bud'e suke amma bana ganin komai sai duhu, da 'karfi na furta "Mum!!" "Bilkisu ganinan". "Mum bana gani!!" "La'iaha illallahu..." "Muhammadur-rasulullahi!!" Na 'karasa domin ni duk a tunanina mutuwa zanyi ake la'kaba min shahada, har yanzu bana ganin komai a idona sai wani shuuuuuuu da nakeji a cikin kaina, ga salati dake tashi a d'akin sannan ga kukan babies d'ina, hankalina 'kara tashi yake wanda hakan ke 'karamin ciwon kan da nakeji, a hankali na fara ganin mutane a dusashe yayin da naji maganar likita tana fad'in a barni ni kad'ai. Allura aka yimin wadda ta d'an fara dawo dani hayyacina, bayan na d'an warware naga d'akin yanzu daga ni sai Aliyu da Mum. "Doctor post eclamsia ne ko?" "I think so amma bari mu gani". Bp d'ina ya duba naga Mum ta zare Ido tace "Oh God". "160/90, post eclamsia ne zamu bata magani kafin kuma ayi urine test, for now ta samu hutu sosai saboda zata iya sake samun seizure". Ni gaba d'aya hankalina ba a kan post eclamsia d'in yake ba yana kan babies d'ina dake ta canyara kuka, dannewa kawai nayi amma ji nake kamar nayi tsalle daga gadon na d'aukosu. Aliyu ne ya lura da hakan bayan mun da doctor sun fita ya d'aukomin d'aya ya mi'komin sannan ya ri'ke d'ayan Yana jijjigashi a hankali, nayi mamaki da ya iya ri'ke yaro domin yawancin maza basa iyawa. Jingina nayi saboda yanda kaina yayimin nauyi ji nake kamar zai fashe, matso da babyna nayi 'kirjina na fara bashi nono, bai wani jima ba ya fara kuka na cireshi na ajiye a gefe saboda kukansa 'karamin ciwon kai. Dafe kaina nayi na cije baki ji nake kamar na fasa ihu, ga ciwon kai ga kukan yara ga babu nono Ina zan saka kaina? Dawowa Mum tayita d'auki babyn dake kuka a gefena sannan tace "feed them mana Bilkisu". Muryata a hankali saboda banason magana nace "babu ruwan nono Mum". "Okay bari a samo musu madara kema ya kamata kici abinci sai kisha magani". "Mum ya naga fuskarta ta 'kafarta sun kumbura?" Aliyu ya fad'a cikin damuwa, idanuna a rufe suke kuma banida niyyar bud'ewa Mum tace, "Eh duk alamu ne na post eclamsia, yanzu jeka ka samowa yarannan Madara, SMA zaka kar'bo musu idan ka fita daga nan akwai wani pharmacy zaka samu a ciki". Yana fita Mum ta had'amin tea, wato murna da farin ciki yasa suka manta ma ya kamata naci abinci, ni kaina farin ciki yasa na manta da yunwar da nakeji, rabona da abinci yanzu nayi 24 hours. Alamun zamanta naji a gefena ta tallafo kaina ta d'aura a 'kirjinta, a baki ta dinga bani tea d'in saida na shanye duka sannan ta 'karamin pillow na jingina, magani ta bani nasha na dafe kaina nace "Wai Mum yarannan bazasu dena kuka bane?" "Ta yaya zasu dena kuka suna jin yunwa? Da zaran sunsha madara zasuyi bacci". "Nima inajin yunwar amma banyi kuka ba". Dariya Mum tayi tace "ko kinyi ba mai ganin laifinki". A hankali na fara 'ko'karin sauka daga gadon, kamoni Mum tayi tace "ina zakije kuma?" "Fitsari nakeji". "To muje taka a hankali". A hankali na taka Mum na ri'ke dani, da alamu maganinnan yana da kyau domin har na fara jin dad'in jikina. Stiches d'innan ba dai azaba ba fitsarin ma saida dabara, bayan na gama da wayyo wayyo na fito na tako da kaina na koma gado, Mum na samu da Aliyu kowannensu na bawa baby d'aya Madara gwanin sha'awa murmushi nayi na kwanta ina kallonsu, ko ina jama'ar da suka zo suke? Su Raudah ma babu su amma naji dad'in hakan. Doctor ne ya shigo yayimin allura sannan yace sai washe-gari za'ayi discharging d'ina. Babu wanda ke yimin magana a cikinsu zuwa yanzu kaina yayi sau'ki, twins ne suka fad'o d'akin babu sallama Mum ta daka musu tsawa tace "bakwa ganin batada lafiya zaku shigo kuna hayaniya?" Tsayawa sukayi suna kallon Mum da baby a hannunta, wani iri naji a raina domin tunda nake ban ta'ba jin Mum ta d'aga musu murya ba banaso ace saboda ni ko abinda na haifa ta fara, murmushi nayi na bud'e hannuna nace "my babies come and hug me". Ajiye flask d'in hannunsu sukayi suka nufo ni tareda hugging d'ina, turo baki nawal tayi tace "kinga Mum tayi mana tsawa saboda anyi sabbin babies ko?" Kumatunta naja nace "nawal ai ko babies nawa za'ayi Mum a wajenta ku kad'ai ne babies, kawai taga banajin dad'i ne sannan ga twins sun ishemu da kuka shiyasa amma ai da mace ake auta kune auta". Ta'be baki suka yi su a lallai an 'bata musu sannan amal ta d'auko plate ta zubamin abinci, mi'komin tayi naga tuwo, wani farin ciki naji domin a yanzu shi kad'ai zan iya ci. Mi'komin tayi tace "Inna ce tazo da akace za'a miki farfesu sai cewa tayi 'karku kaiwa 'dan jikana 'kazanta baku iya komai ba" amal ta 'kare maganar tana kwaikwayon kakar tasu, dariya mukayi Mum tayi murmushi har yanzu baby na hannunta ta'ki ajiyeshi, na lura family d'innan na son yara maza. Ina cikin cin tuwon na fara jin bacci da 'kyar na samu na cinye kafin na fara bacci. Na samu sau'kin ciwon kan sosai domin babu wanda ya sake zuwa wurina a ranar har washe-gari, bayan an duba Bp d'ina anga ya sauka akayi discharging d'ina. Muna isa gida gida muka samu twins suna 'ko'karin karya 'yat tsohuwa sun hau kanta wai sai ta goyasu, mi'komin baby Aliyu yayi ya nufi inda suke ya kamo kunnensu, 'kara sukayi ya janyo kunnensu yace "kuka sake takurawa Inna had'aku zanyi ta tafi daku sai kunyi shekara a wajenta". Gyad'a kai kawai sukayi suna 'ko'karin cire hannunsa a kunnensu, sakin kunnen yayi yazo ya kar'bi babyn hannuna muka 'karasa kujera muka zauna, gaida inna nayi tace, "Sannu ummm Bilkisu ko?" "Eh Inna". "Kin sauka lafiya". "Lafiya lau Inna". "To barka Allah ya 'kara lafiya". Kallon Mum tayi tace "na saka an d'aura ruwan zafi kafin ku huta nasan yayi". "Inna jininta ya hau fa baza'a mata wanka ba sai ya sauka". Tafa hannu Inna tayi ta ri'ke 'kugu tace "lallai ni larai naga sha'kiyancin 'yan zamani, wato dabarar ma ba yara kawai ba harda ku manya, banda wad'annan turawan sun juya muku tunani ai wankan ma zai rage mata hawan jinin yake ko menene? Sai anyi wankannan yau". "Dan Allah Inna a bari sai gobe dai ko? Ance fa ruwan zafi zai iya ta'ba mata kai zata iya suma, idan tasha magani jinin ya sauka sai ayi wankan". Saleh ya fad'a cikin lallashi, shiru tayi sannan tace "to naji, amma ruwan da aka d'aura baza'a yi asararsa ba, dashi zatayi idan ya huce". Hakanan aka barta, zama tayi ta kar'bi babyn hannun Mum nidai uwar yara na zama 'yar kallo, kara da kawaici kawai nakeyi amma so nake naji d'umin 'ya'yana. Yanzun ma banida wani hope domin bud'ar bakin Mum sai cewa tayi "jeki d'akin Raudah ki kwanta ki huta, sai mu ri'ke su kar su dameki da kuka" kallon twins tayi tace "duk wanda yazo kuce masa tana bacci ance kar a tasheta ko da bananan, ga babies d'innan su gansu". Murmushi nayi na amsa ma Mum sannan na nufi d'aki, gani nake kamar sun fini son yarannan domin har Inna kallonsu take cike da sha'awa, yanzu ma biyun na hannunta ta hana kowa. Da kewar 'yayana na samu nayi bacci ban tashi ba sai la'asar, ruwan wanka Inna ta kawo min sannan ta yimin wankan, mita take ruwan babu zafi nikuwa dai cije baki nake, har wani tiriri ke tashi a jikina, idan wannan babu zafi na jegon ya yake? Bayan na fito Mum ta kawomin twins nayi feeding d'insu sannan ta dawo ta d'aukesu, yau naga inda akewa uwa iko da 'ya'yanta. Kwalliya nayi sannan na nufi parlour, mamaki nayi ganin akwatina a parlour ga twins na ta shan jagwalgwalo. " 'yata ta kaina" naji muryar Aunty, tasowa tayi da sauri tayi hugging d'ina tace "barka barka 'yata, wallahi naji dad'i sosai". Murmushi nayi nace "nagode Aunty, amma dai bazaki koma ba sai bayan suna ko?" "Kwarai kuwa, 'yata ta haifi twins maza ina naga ta zuwa?" Bayan na gaida sauran mutum biyu dake d'akin muka koma gefe da Aunty, kallona tayi sosai tace "lallai Bilki ciki ya kar'beki, dubi yanda kika 'kara fresh da alamu ma haihuwar bata miki wuya ba". "Tabd'i Aunty wallahi da wuya, labour biyu fa". Na karasa maganar ina kallon twins. Dafa kafad'ata Aunty tayi tace " 'ya'yanki sun miki wuya ko? Ha'kuri zakiyi da zaran anyi suna shikenan". Sosa kaina nayi cikin Jin kunya sannan tace "danginmu Allah ya bamu son 'ya'ya maza sosai kuma Allah da ikonsa bama haifar mazan sosai, dukkanmu matanmu da mazanmu 'ya'yansu maza d'ai-d'ai, mutum d'aya ce mai maza biyu, shiyasa da akace kin haifi twins maza kowa yake farin ciki, ki jira zuwan sauran sisters d'inmu ganin fuskar babies d'in ma sai ta miki wahala, kayan barka kuwa sai kin rasa wajen ajiya". ************ Washegari kafin Saleh ya fita saida yayiwa Hadiyya cefane, yana fita ta nufi part d'in sultana ta ro'keta ta koya mata girki ta tafi da kayan cefanenta. Miya sukayi tare Sultana ta nuna mata yanda ake tsaftace kayan miya da nama wanda shine abinda ke fara 'bata girki, sannan ta nuna mata yanda ake had'a miya, bayanin dahuwar shinkfa tayi mata tace taje gidanta ta dafa. Godiya Hadoyya tayi ta tafi da miyarta ta zauna ta dinga maimaita abubuwan da Sultana ta koya mata, a 'karshe ma littafi ta nema ta rubuta domin yanzu da gaske so take ta mallake Saleh ko dan uwarsa. Sultana kuwa dukda Hadiyya Bata birgeta amma tafi sakewa da ita akan Jumana, ko ba komai dukkansu basa son halin hajiya, kuma musamman yanzu da Hadiyya ke son gyarawa Hajiya zama hakan yayiwa sultana dad'i, a yanzu zasu gane amfanin Bilkisu sai sunyi nadamar rashinta a gidan. Saleh yana dawowa ta d'auko abincin ta jere masa sannan ta tsuguna a wurin, addu'a take silently Allah yasa abincin yayi masa dad'i. Shima tunanin ci yake amma ganin yanda ta damu ya sanya ya daure ya kai abincin bakinsa, a hankali tace "yayi dad'i dan Allah?" "Yayi sosai ma". Tashi tayi tareda hamdala ta fara rawa, dariya yayi yaci gaba da cin abincinsa, zama tayi gefensa itama ta fara ci sannan tace "Ammyna tana gaida ka, tace gobe zata zo ma tayi maka godiya". Girgiza kai Saleh yayi yace "a'a ba sai tazo ba godiyar da kika yimin ta isa, itama kamar uwa take a wurina ai". 'ka'kalo hawaye takeyi sannan tace "gani nake koyaushe kamar banyi maka godiya yanda ya kamata ba, ka ceci mahaifiyata saidai nace Allah ya biyaka, samun miji irinka a wannan lokacin akwai wahala". Shiru yayi baice mata komai ba suka ci gaba da cin abinci, ya lura da canji sosai a tattare da ita fatansa Allah yasa canjin na alkhairi ne. Anyi kwana biyu babu wata hatsaniya tsakanin su Hadiyya da Hajiya, hakan yasa hankalin Saleh ya d'an kwanta. Zuwa mahaifiyar Hadiyya tayi domin ganin lafiyarta ta tahowa da Saleh takalmi, hira sukeyi Hadiyya tace "aikwa zaiji dad'in takalminnan dama ina ta raya me zan masa a raina saboda alkhairin da yake miki". Maida takalmin kwalinsa Ammy tayi tace "gaskiya yaronnan yaron kirki ne, kinga Hadiyya kar kiyi wasa dashi, banaso sha-shancinki yasa ki janyowa kanki matsala". "Kai Ammy inada hankali ma, kuma abinda nayi laifinsu ne ba nawa ba basuda imani wallahi, nasan dai banda Allah yasa ya saki Bilkisu d'innan ba yanda za'ayi ya aureni amma Ammy asiri fa sukayi mata wai har hauka ta kusa yi, ni tsoro nakeji ma wallahi kar suyimin asirin nima". Murmushi Ammy tayi tace "mutum me baki ai ana wuyar cutarsa, kiyi taka tsan-tsan dasu sannan ki dage da addu'a, amma kuma duk wadda tayi miki a cikinsu karki raga mata saidai kiyi takunki cikin tunani da basira indai zaki bi hanyoyin da na dad'e ina nuna miki zaki mallakeshi babu boka babu malam da addu'a da dabara sannan kiyi maganinsu idan sun takura miki kenan, idan basu takura miki ba ki fita daga harkarsu". Ammy na gamawa sai ga Maimuna ta fad'o d'akin kamar mahaukaciya, tsayawa tayi ta ri'ke 'kugu tace "naji duk maganganun da kukeyi munafukai Allah ya kama ku, wato a mallakeshi a raba mu dashi ko? An kawo ki cin arzi'ki zaki fara za'kewa ke kuma uwar banza mai goyawa 'yarta baya ta ya'ki dangin miji, ai wallahi nayi nadamar ma amincewa da aurenki". "Saboda bakisan cewa naki auren zai mutu ba ko? Maimuna dan Allah na ro'ke ki ki fita daga harka ta ba ni na kashe miki aure ba, ba ni nace kiyi sharri Allah ya kamaki ba, kije kiji da zawarcinki na illa nadiran ki barni naci aurena a kwanciyar hankali". Kafin su ankara sai ga Maimuna a gaban Hadiyya, kamo wuyan rigar Hadiyya tayi tace "Dan ubanki sai kin bar gidannan, wallahi tallahi sai kin fita tunda ba gidan ubanki bane". A fusace Hadiyya ta tsinka mata mari sannan ta tureta daga jikinta, dama ji take da 'karfi da cikinnan yau Allah ya kawo abinda zata huce, nuna Maimuna tayi tace "ke idan kina cin 'kasa ki kiyayi ta shuri, ba gidan ubana bane amma zama daram, bakisan wacece Hadiyya ba ko? To kije ki tambayi wacece ni, shegiya mai ba'kin hali 'yar muguwar mace, bakisan wacece". Ammy Hana Hadiyya magana takeyi amma tuni idon Hadiyya ya rufe saboda 'bacin rai, ji take hannunta har rawa yakeyi duka kawai takeso tayi, maimakon maimuna tayo kanta sai ta nufi Ammy, tsayawa tayi dab da ammy tace. "Kinji kunya wallahi, a gabanki 'yarki tana nuna bata koyi tarbiyya ba, babu mamaki a jininku yake tunda kema tsabar rashin tarbiyya cikin shege kikayi kika gudu kikayi aure". A fusace Hadiyya ta kaiwa Maimuna naushi, baya-baya Maimuna tayi Hadiyya ta sake naushinta a ciki saida ta fad'i, ko nauyin cikin jikinta bataji haka ta haye kan Maimuna ta dinga kai mata duka da mari, tuni ta fasa mata baki jini na fita daga hancinta, a tsorace mahaifiyar Hadiyya ke janta amma ta kasa d'ageta daga kan Maimuna, salati kawai takeyi domin dama tasan halin Hadiyya musamman idan aka ta'ba Ammynta. Saida Maimuna ta kusa suma sannan Hadiyya ta tashi daga kan ruwan cikinta ta 'kudunduma mata ashar tace "idan baki fita daga gidana ba wallahi sai na illataki yanda bazaki sake son kallan kanki a mudubi ba 'yar gidan jakai kawai". _din din ....to fah ayimin afuwa zanyi tafiya kuma zanyi kwanaki, amma idan na samu rara ki Yaya ne zanyi posting, thanks_ Banyi updating ba saboda I'm broke, nayi typing tun tuni kunsan Dan School da hutu😅😅😅😅but here it is fatan bakuyi fushi ba Share Vote Comment Follow 54 Kwanaki biyu suka rage kafin suna wanda a lokacinnan duk wasu family d'in Mum na nesa sunzo Abuja. Shirin suna akeyi yayin da mai jego ta zama 'yar kallo, an rad'a ma babies Abdul-malik da Abdul-hakim, saidai anata musu akan nickname da za'a yi musu nidai na bar musu wu'ka da nama tunda yaran ma na zama 'yar kallo. A cikin kwanakinnan kullum sai na sanya sabon kaya wanda duk bansan an d'inka su ba, saidai kawai na bud'e wardrobe d'in Raudah na d'auka, ko gida ban bud'e ba tunda na dawo su Raudah dai na zuwa. Kayan barka kuwa tun ina mamaki har na dena, ranar farko wata friend d'in Mum wadda mijinta abokin Dad ne tazo da baby Walker guda biyu. Daga nan fa aka fara bajinta kowa yanayi iya yinsa, da masu yi dan Allah da kuma masu yi saboda ace sunyi, da masu yi saboda su kere wasu. Kud'in barka mafi 'kankanta da na samu shine 20k, daga 50 zuwa sama ake bani banda kayan yara da nawa, kafin suna na samu zannuwa 16pcs, banda masu janyo trolley cike da kayan babies, kai talaka yana shan wuya, wata ma baiwar Allah haka za'a dinga binta da omo 'kullin 10naira da 50 naira, wadda ta fini bu'kata, amma gasunan ana kawomin ko godiyar kirki banayi domin na lura haka tsarin yake, ka nuna cewa kafi 'karfin abin shine girma, tun abubuwan na min wani iri har sun zamarmin jiki. Gida ya cika da ma'aikata a daren ranar suna, tunani kawai nakeyi me gobe zatayi holding domin kullum Mum na kan waya tana fad'in haihuwar da nayi. A family d'ina part d'in su Mama basu wani zo ba, domin yanda suka ce sai anyi suna nasu a can, saboda haka 3 days bayan sunan nan zan tafi kano ayi wani sunan na daban, sai ni 'yar gata. Kwalliya aka yimin kaman wata sabuwar amarya, a bayan gidan akayi decorations tamkar aurena za'a sake yi, ga katifa 'katuwa da zan zauna saidai banbancinsa da aure akwai gadon babies a gefena. Yau dai na samu na d'auki babies d'ina saboda hoto amma da zaran anyi nake maidasu gadonsu domin sunyi kyau sosai a gadon. Gado ne guda d'aya amma ta ciki an raba biyu, light blue ne kalan gadon haka ma kayan jikinsu, bedsheet d'in kuma da kayan jikin nasu yazo. Sai yau na 'kare musu kallo, kamanninsu sak na mahaifinsu saidai kalar ta banbanta, maimakon farin mahaifinsu sai sukayi wata kala mai 'kyau kamar jariran black Americans yawancin mutane idan suka kallesu sai sun sake kallona, seriously munin nawa ya kai haka? Ni abun ma ya fara bani haushi. Aliyu ne ya matso tareda wani abokinsa ina shirin tashi, zama nayi muka gaisa abokin ya le'ka gadon sannan ya kalleni ya kalli Aliyu, murmushi yayi yace "wow Masha Allah, kayi gaskiya". "Ah to, ba na fad'a maka ba? Idan kaje ka auri kalarka aljanu zaku haifa dubi fa ka fini haske sannan ka auri irinka? Sorry man". Dariya nayi na kallesu, kafin su tafi Raudah ma tazo da friend d'inta tana ri'ke da babynta mace, zama sukayi Raudah tace "sannu da zama me jego". "Yauwa Auntu Raudah sai niyyar tashi nakeyi amma mutane sun hanani, ko zaki zauna a madadina naje bathroom?" "Babu matsala amma ku fara gaisawa da intisar". Gaisawa mukayi na kar'bi babynta, da alamu itama bata wani dad'e da haihuwa ba yarinyar fara 'kal, dariya nayi da na tuna wata magana da wata ke cewa kyakkyawa ya auri kyakkyawa su haifi aljanu mu kuma munanan mu haifi me? Domin wannan yarinyar tubarkalla, lips d'inta ja ga kuma gashin kanta ba'ki sosai, dukda nasan basu fi 40 ba amma an gyara mata kanta yayi kyau tana ta baccinta. Abdul-hakim ta d'auka ta "Masha Allah....Raudah seriously yayanki ya iya breeding" kallona tayi harda marairaicewa tace "dan Allah aunty Bilki miyi exchange ki bani d'aya na baki wannan tsohuwar". Dariya nayi nace "bakomai, ga mamansu nan Raudah duk abinda tace ya zauna, ki za'bi wanda kikeso". Shafa fuskar Abdul-hakim takeyi tace "wallahi yaran sun bani sha'awa sosai, haba naji mamma na ta kod'a kalan yaran ashe tubarkallah kalar 'kwai ce dasu, abinka da mun saba ganin farare, ya kamata dai a family a fara samar mana da wannan kalar kai ni na bawa khadija d'aya ma". Tashi nayi ina murmushi naga wasu sun doso mu, da sauri nabi ta baya na nufi gida domin tun kusan 1hour back nakeso naje gida. Na fito daga toilet naji wasu na hira a parlour, ma'kalewa nayi Jin an ambaci matar Aliyu na kasa kunne. "Nifa nayi mamaki da suka ce wai 'yar gidan uncle Ibrahim da ya rasu ce, nasan dai tayi aure a baya amma ban san yaushe ta fito ba har Aliyu ya aureta". D'aya daga cikinsu ce tace "ni naji labarin ta fito tunda ina yawan zuwa Kano, sannan akwai Aunt d'inta friend d'ina ce, nidai kamar ce min tayi rashin haihuwa ne yasa aurenta ya mutu, amma ba ma wannan ba, yanzu Aliyu duk ruwan idon nasa ya rasa wa zai aura sai bazawara? Ya gama kumfar bakin shi family zai aura amma ya auro wannan, na farko ba class d'insa bace wajen kud'i ji nake inda ake ri'kon ta baifi boys quarters na gidannan ba? Kuma ma ya akayi ta haihu bayan ance bata haihuwa? Sannan maza wallahi duk zatona idan zata haihu ma mata zatam Haifa tunda kinga Dad shi kad'ai ne namiji sannan mu ma Namiji d'aya ne damu, haka aunty batul ma d'ayan ta haifa" Tsaki wata taja tace "wai ku meye naku? Tunda yana sonta Aunty batul na sonta, su Raudah suna sonta harda Dad yana sonta, ta haihu kuma ta Haifa musu abinda suke so ko nace abinda muke so har biyu ma, maimakon kuyi murna sai ku dinga gulmarta? Haihuwa ta Allah ce ai kuma Allah ya 'karo musu mazan tayita haifarsu kuma nuna bakuji dad'i ba bazai saka ta dena Haifa ba, idan Aunty Batul taji kunsan abinda zata muku, kamar ba 'kannenta ba? Haba sisters". Fitowa nayi da murmushina na gaidasu na fice, ni wannan d'in ma dad'i yayimin domin ba kowa ne zai soka ba, idan har dukkan mutane zasu nuna suna sonka to tabbas ka binciki halayyarka ba dai-dai take ba. Ina komawa na samu Mum tana gadin jikokinta, friends d'inta suna zaune suna hira, gaidasu nayi suka min wuri na zauna tsakiyarsu aka mana hoto sannan suka bani abin barka, bazan iya 'kirga kud'in da na samu a yau ba domin na baya ma nafila ne, banda kud'i ga kuma kaya a gefen katifar da nake zaune, kayan da twins suka samu zasu iya shekara ba tare da na sake sayen tsinke ba, abu d'aya ne babu a taronnan dangina na 'bangaren uwa, Mama ce kawai tazo itama a yau zata koma har na 'kagu a gama taron nan na koma Kano, sai nayi 40 tukun zan dawo domin rayuwar gidannan ta fara isa ta musamman bayan na haihu. Dukda ina 'ko'karin zama d'aya dasu amma abun akwai wahala, dole tasa na zama fake, banaso nayi saboda a san inada shi, banaso nayi saboda ace nayi sannan a kowane lokaci tsoron kuskure nakeyi domin ido na kaina, 'wannan talakar matar bari mu ga me ta iya?' shine kallon da nake samu daga wasu daga cikinsu. Idan har zan zauna daga ni sai dangin mijina banida matsala domin sun san wacece ni kuma suna respecting d'ina a yanda nake, duk abinda nayi sa'banin nasu birgesu yake amma wad'annan sabbin mutanen tsoro suke bani. Suna bai tashi ba sai 9:30, tun a ranar na fara shirin tafiya kano, I can't wait to meet some real people. ************* *SALEH* Zubawa Hadiyya ido Saleh yayi ya rasa ma me zaice mata, ita ma kanta a 'kasa tana turo baki gaba d'aya yau tsiwar ce a kanta. "Kayi shiru bayan gashi ta tabbatar da ita ta daketa, ka d'auki mataki mana 'kanwarka ta daka fa". Hajiya ta fad'a a fusace. Had'e hannayensa yayi yace "Hadiyya me yasa kika aikata haka? Meyasa zaki daketa ko me tayi maki bazaki jira na dawo ba sannan ki fad'a min?" "Kayi ha'kuri amma abinda tayi min ko kai aka yiwa bazaka jira ba, sannan nasan ko na fad'a maka ba abinda zaka iya, uwa fa ba abin wasa bace ba, kuma idan zagi ne kawai ai da sau'ki ta Yaya zata yiwa uwata 'kazafi a gabana? Tana magana tana nuna mata yatsa tana goranta mata akan aurena, sannan ko kotu aka je ba wanda zai bata gaskiya tunda gidana ta shigo ina zaune, kuma inata tabbacin Banda na daketa da niyyar duka tazo min". Juyawa yayi ga Maimuna yace "ke Maimuna meyasa zakije gidanta? Me tayi miki?" "Ban sani ba, ko ma menene ai ni aka cuta, wallahi idan baka d'auki mataki ba wallahi zan d'auka da kaina, matarnan banda mun baka ita ina zaka ganta ka aureta? Ke kuma wallahi sai kin bar gidannan domin ba gidan ubanki bane shegiya me gadon rashin kunya". Tsit Hadiyya tayi bata ce mata komai ba shima Saleh yayi shiru, abin takaici Hajiya na zaune itama Shirin tayi, kallon Saleh Hadiyya tayi tace "Honey idan na bata ha'kuri shikenan ya wuce?" Marairaicewa tayi dole yace "eh ya wuce bata ha'kuri". "Allah ya baki ha'kuri Aunty Maimuna kinji? Insha Allahu indai baki shiga gonata ba bazan sake miki komai ba, ko gaisuwa bazata sake had'ani dake ba". Tamkar an sake zuga Maimuna taci gaba da zazzaga bala'i da masifa tana rantse-rantse kan sai Hadiyya ta bar gidan, ga Hajiya tana mara mata baya a fakaice, cike da kunya ya d'auki matarsa suka fita. Suna zuwa gida Hadiyya bata sake d'auko zancen ba ta ciro takalmin da Ammy ta kawo masa, ta lura abinda sukayi bai masa dad'i ba. A cinyarsa ta zauna tace "wayyo gyara 'kafarka ka takura mana baby". Murmushi yayi ya gyara ta zauna sosai tare da tallafo cikinta, kwantar da kanta tayi a 'kirjinsa sannan ta kama hannunsa tana shafa cikinta dashi tace "na 'kara nauyi ko?" "Sosai ma" ya fad'a a hankali, tunda aka fara hatsaniya tsakaninta da su Hajiya kuma sai yaji tana shiga ransa, tana yawan tuna masa da Bilkisu yanda ta kasa defending kanta, shima ya kasa bata tsaron da take so har ta kai ga sun rabu, yanda take tsayawa kanta yasa take birgeshi dukda kuwa a kan danginsa ne. Takalmin da Ammy ta bayar ta d'auka ta bashi tace "dukda nasan kafi 'karfin wannan takalmin amma dai gashi Ammyna ce ta kawo maka tace "ayi maka godiya yanda kake mata sutura kaima Allah ya suturtaka duniya da lahira". Kar'bar ledar yayi ya ciro takalmin, juyashi yayi tace "idan baiyi maka ba wallahi ba matsala nasan kafi 'karfin wannan, ai inaga baifi 1500 ba ko? Domin iya 'karfin Ammy kenan na sani, kuma saida nace kar ta kawo ba lallai kaso ba, idan baiyi ba......" Rufe bakinta yayi da hannunsa ya sanya takalmin a 'kafarsa sannan yace "wannan takalmin yafi kud'in da kika fad'a kuma ni a wurina ko bai kai ba ban damu ba domin kyautar da baka ta'ba zato ba tafi shigar maka rai, yayi kyau sosai zan mata godiya idan Allah ya kaimu gobe ma da shi zan fita". "Naji dad'i sosai, wallahi nayi zaton zaka dai yi godiya ne kawai amma bazaka so ba". Tashi tayi ta zauna a gefensa yace "akwai wani labari da mahaifinmu ke bamu lokacin da Yana raye yace wani bawan Allah irin masu kud'innan ne sosai zaiyi auren d'ansa sai mai aikinsa ta kawo masa atamfa wadda tasan ko zanin goyo baza'a yi da ita ba, mutumin yace tunda ake masa kyauta ba'a ta'ba masa irin wannan da ta shiga ransa ba, tsabar dad'i a shekarar saida ya biya mata makka sannan yace atamfarnan sai an saka a lefe, labarinnan fa ya bada shi ne bayan ta rasu kusan shekara ashirin baya, yawanci abinda ke hana mu Alkhairi kenan nuna tunanin wanda zamu yiwa zai raina abinda aka yi masa , indai zakiyi kyauta ki yita domin Allah kawai". Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace "aikuwa na dad'e ina irin wannan tunanin kafin nayi kyauta, amma yau ka canzamin ra'ayi, dukda banason yin maganarnan amma kayi ha'kuri da abinda nayi bazan sake ba da yardar Allah". "Shikenan amma ko gaba duk abinda ta miki karki sake dukanta kinji? Ki sanarmin da kaina zan d'auki mataki". **** Had'a kaya Hadiyya keyi na tafiya gida domin haihuwarta ta matso, tana fito da kayanta taji sallamar Hajiya a parlour. Ko amsa mata bata yi ba domin tun fad'ansu da Maimuna bata sake kallon part d'in Hajiya ba, gaba d'aya ta manta da rayuwarsu a gidan dukda lokaci zuwa lokaci suna takura mata amma bata damuwa domin ta samu mijinta yana goyon bayanta. "Ina mai tabbatar miki idan kika tafi gida bazaki dawo ba, tunda ke raina mutane kika sanya a gaba sai kije kiyi a gidanku amma gidannan insha Allahu kina fitarsa kin fita kenan". Dariya Hadiyya tayi tace " Hajjaju ki kama girmanki kinji? Indai kuwa so kike na bar gidannan Ina nan ba inda zanje, tunani na zan rage miki takaicin ganin kayan da mijina zai shigo dasu na haihuwa amma tunda kince haka na fasa fita, a idonki za'a yi komai kuma baki da ikon cewa komai". _ku raka da wannan gajiyar hanya bata sakeni ba_ 55 Na gama cire kayana na suna kenan Aliyu ya shigo, hugging d'ina yayi ta baya tare da sha'kar jikina yace " 'kamshin jego na daban ne, ina ma koyaushe zakiyi ta wannan 'kamshin". Juyowa nayi na kalleshi daga underwear jikina sai bra nace "baka san masu jego 'karni suke ba? Kaima angon 'karni ne kuma ni nafi son 'kamshin jikina lokacin da bana jego". Hannu na sanya na sa'kalo wuyansa ya matso da fuskarsa dab da tawa, numfashinsa na dukan fuskata yace "ya gajiyar suna?" 'kurawa lips d'insa ido nayi nace "ai na manta da gajiyar ma". Murmushi yayi ya matso tamkar zai kissing d'ina sannan yace "dole ki manta da gajiya mana tunda kina kallon kyawawan lips d'ina". Ya 'kare maganar yana cizar lips d'insa, ban bashi amsa ba nayi pecking lips d'in nasa kafin yayi kissing d'ina naji gyaran murya. Juyawa nayi naga twins sun rufe idonsu da hannunsu suna dariya da sauri na sakeshi yace "ku bud'e". Ido d'aya suka bud'e Nawal tace "bamu ga komai ba". Zama nayi kan gado ya zauna gefena yace "to meye ma dan kunga komai" ya sanya hannunsa daga bayana ya ri'ko 'kuguna, ture hannunsa nayi ya sake matsowa, 'ko'karin tashi nakeyi domin na fara jiyo muryar Mum da Inna idan suka ganmu a haka ai naji kunya. Ko a jikinsa ya sake matsowa twins kuwa sun tsaya suna kallon live show, sallamar Mum naji yayin da na tashi ya rikoni, girgiza kai tayi tace "kun saka min babiesa gaba zaku 'bata su ko?, amal nawal kuzo mu tafi". Jan hannun jariranta tayi ta fita tana murmushi Inna kuwa shigowa tayi ta zabga masa ran'kwashi tace " 'kaniyarka, ba nace kar na sake ganinka a wajen yarinyarnan ba sai tayi arba'in? Shine ko bi'kin bata gama ba ka fara cakumarta ko? Ki barshi ya sake d'irka miki wani cikin kece da wahala". Turo baki nayi nace "Inna ban fa gayyato shi ba kawai ina shiryawa ya shigo". Mun riga mun saba haka sam Inna ta hana Aliyu zuwa wajena mu d'anyi love d'innan, da zarar yazo zata koreshi tace kar ya d'irka min wani cikin ko kuma ta zauna har ya gaji ya fita. Ri'ke 'kugu tayi tace "ayyo, wato shiryawa kikeyi shine yana shigowa kika tu'be ko?" Sum-sum ya fice ya barni a wajen na bishi da kallo, zaka yi bayani ne. Zama tayi tace "nemi riga ki saka ni kin tsaya kina turo min nono". Riga ta na zura nace "to Inna meye baki gani ba? Ai yanzu har zana ni zaki iya domin kin kalleni tsaf" Duka ta kawomin na kauce muka yi dariya sannan tace "Bilkisu sai fa kin kula, Kar kiga ina korar mijinki kiji haushi saboda ke nake yi, namiji fa bashi da saiti a yanzu kika mi'ka masa kai hayewa zaiyi ya barki da wuya, kwainuka idan d'aya ne da sau'ki amma biyu akwai wuya". "To Inna zan kiyaye amma ai nayi tazarar haihuwa". Tagumi ta zuba tace " Ni Indo yaran zamani ana nuna muku annabi kuna rintse ido, to ai shikenan Allah ya kyauta, wato kinyi tazarar haihuwa saboda bazaki iya jurewa har kiyi arba'in ba ko? 'ya'yan zamani ina zaku kai zumud'i? Shiyasa mazan zamaninnan ke muku kallon banza". Sunkuyar da kaina nayi nace "Inna ba haka fa nake nufi ba". Abdul-malik ne ya fara kuka na d'aukeshi ina d'aukansa Abdul-hakim shima ya fara, suna fara kukan twins suna zo da gudu suna kokawar had'a madara,  amal na mi'kawa yaron hannuna na nufi toilet ina jiyo Inna na musu jaraba, kullum dai haka akeyi a kwana bakwai d'innan. 'Dokin tafiya ta Kano kawai nake yi, Mum har ta lura da hakan tace "ina ganin kwana uku zuwanmu kano yayi nisa, gobe sai mu tafi". Bance komai ba amma a ciki ji nake kamar nayi tsalle, ban raina abinda suka yimin ba domin naga iyakacin gata a wannan sunan, saidai ni ba haka na saba ganin hidimar suna ba, babu irin cika gidannan da akeyi ana aikin kayan miya da sauransu, babu haya'kin itace babu masu sabbin riguna da tsofaffin zani sun kama gaban tukunya suna tu'kin tuwo, babu kunun aya da zo'bo na leda, babu plates d'in roba ko irin shige da fice da yara keyi suna a basu abinci babu, komai anyishi silently  cikin gayu, bazaka ta'ba cewa ana suna ba sai kaje inda akayi decoration, ina zaune ake kawomin gaisuwa maimakon na dinga bin mutane ina gaidasu, nayi kewar rayuwar middle class d'in da nakeyi sosai. A daren na tattara kayana har gidana naje na d'ebo wasu, abun mamaki duk kayan da na sanya 15 sets akwai wasu daban na sunan gidanmu, washegari da wuri na farka na kasa komawa bacci, 7:30 Inna ta yiwa twins wanka ta bamu su mu shiryasu. Dukda nayi rainon Huda tun tana 'karama amma sai na kasa komai, ko saka Pampers na kasa sai zuba ma Raudah ido nayi tana shiryasu da taimakon twins, ba laifina bane tunda na haihu nursing d'insu kawai nakeyi bana komai sai zuba ido. 10am jirginmu ya tashi, kasancewar VIP muka d'auka yasa duk muka sake, twins d'in Mum har bacci suka fara ni kuwa gani nake kamar anqi zuwa. Muna isa kuwa na fito da sauri, da gudu na nufi Mama nayi hugging d'inta shima Yaya ya bud'e hannu cikin zolaya, gwalo nayi masa na mi'ka masa hannu muka gaisa sannan na dur'kusa na gaida Baba, nayi mamakin zuwansa d'auka na saida Jabir ya fad'amin akwai inda zasu wuce ne, tunawa nayi da mota ta nasan  tana nan tasha 'kura. Ina zuwa gida na tarar duk 'ya'yan Baba kabiru mata suna gidan Mama sai wad'anda ke nesa, bud'a aka saki Zulaihat tayi hugging d'ina, nan aka fara min congrats gani nake kamar d'akin cike yake da jama'a saidai dukkansu su 8 ne sai 'ya'yansu. Su Aliyu kuwa kawai kallona sukeyi, na saki murya muna zuba hira da 'yan uwana sai yanzu na jini normal tunda na haihu, domin ko magana da 'karfi ban isa nayi ba a can magana suke kamar an saka su dole haka nan na kwaikwaya nima. "Lokacin da na haifi Abdul-hakim ji nayi kawai bazan iya ba, na dinga nadamar 'kin amincewa Mum da tace nayi painless delivery har na fara tunanin ayi min aiki kawai, da na haifi Abdul-hakim fa labour d'in tafiya yayi na Abdul-malik saida aka d'aura Abdul-hakim a kan cikina tukun labour ya dawo, ai daga wannan na gama twins wallahi dan nasha wuya ga eclamsia da nayi bayan na haihu...." Labari nake basu yayin da Mama ke entertaining su Aliyu, bayan mun wuni muna hira sun nuna min tsantsar farin cikinsu da wannan haihuwa da nayi suka tafi, sai lokacin na samu na gana da su Aliyu. Kwana biyar nayi a Kano sannan aka yi suna, ranar suna da Asuba Mama ta nufi babban gida suka fara aiki, anyi suna irin namu na gargajiya wanda ke nuna tsantsar soyayya. Zama nayi nace sai nayi arba'in tukuna zan koma gida duk yanda Mama ta juyani na'ki da suka ga na fara kuka suka barni saidai 2 weeks aka barni nayi. ********** *SALEH*. Shiga gida yayi da sallama yaji shiru d'aki ya duba ya sami Hadiyya tana bacci ya duba baiga akwati ba. D'ayan d'akin ya duba yaga akwatin a Ajiye ya janyoshi ya fito sannan ya koma tashinta domin saboda ita ya dawo ya kaita gida ya koma aikinsa. Juyi tayi ta sake 'kudundune jikinta yayin da ya tasheta, da 'kyar ya samu ta tashi da alamu baccin ya mata nauyi. "Na same ki kina bacci 3:00 fa, tashi muje na kaiki gida saboda akwai aikin da zamuyi yau". Hamma tayi ta jingina da gadon tace "ina sallar azahar na kwanta so nake sai gab da la'asar na farka, jiya ban samu nayi bacci ba sosai, sannan gida na fasa zuwa a nan zan zauna Ammy tace zata turo wadda zata kula dani". "To saboda me?" Ya tambayeta cikin mamaki, kwanciya tayi sannan tace "zan yi maka bayani idan ka dawo amma babban dalili shine bazan iya tafiya na barka kai kad'ai ba bayan nasan Hajiya ba shiri take sosai da kai ba, wani abun zai iya faruwa bayan bana nan". "To shikenan bari na koma". Kallonsa tayi idonta na rufewa tace "na gama girki fa amma, dan Allah kaci kafin ka koma kar ya huce". Fita yayi ya barta taci gaba da baccinta domin har tausayi take bashi a kwanakinnan bata iya baccin dare na kirki. Abincin yaci sannan ya koma aikinsa yana ta tunanin dalilinta na 'kin zuwa gida, tunda cikinta ya kai 6 months take fad'in idan ta koma gida, komai zatayi sai tace idan taje gida haihuwa ko kuma bayan ta dawo. Yana gama aikinsa ya koma gida ya sameta tana tuwo tana yiwa kanta bayani, jingina yayi yana kallonta yana murmushi. "Yauwa yanzu na gama sai na barshi ya sulala, sai kuma miya idan ta dahu sosai...." "Sai a kad'a ta sannan sai a rufe ta dahu" ya 'karasa yana dariya, yanzu kam girkin Hadiyya babu laifi ta fara 'kwarewa, haka idan tayi mistake d'aya bazata sake maimaitawa ba domin dai ta rubuta ma a littafin girkinta. Tayata zuba tuwon a leda yayi sannan ya taya ta wanke kwanukan, zuwa yanzu ya mi'ka lamuransa ga Allah tunda Bilkisu bazata dawo gareshi ba gwara ya rungumi Hadiyyan ta yiwu itace matarsa ba Bilkisu ba. Suna komawa parlour yace "nayi mamakin fasa tafiyarki yanda kika jima kina zumud'i akan zuwa gida lokaci guda kice kin fasa". Sosa kanta tayi tace "in fad'a maka gaskiya bazaka ji haushi ba?" "Fad'i mana". "Ummm.... d'azu ne ina had'a kayana Hajiya ta shigo". Shiru tayi ta kalleshi taga duk ya tattaro hankalinsa kan ta, gyaran  murya tayi tace "da ta shigo sai tace min tana mai tabbatarmin idan na tafi gida wanka to na tafi kenan bazan dawo ba, sai tayi iya yinta ta tabbatar da cewa ban dawo ba domin ita kashe aurenka a wajenta shan ruwa ma ya fishi, yanda ta kori Bilki haka zata koreni kuma sai ta tabbatar na wula'kanta a duniya, zata yad'a cewa cikin jikina ba naka bane rufamin asiri kakeyi har Allah ya Toni asirina aka gane, tacemin kuma kowa yarda zaiyi tunda uwata ma ana rad'e-rad'in da shegiya ta dawo bayan ta gudu daga gaban iyayenta, ni kuma naji tsoro Honey dukda Allah ya sani kaima ka sani cikinnan naka ne kai ne shaidata a budurwa nazo, idan na haihu ma na amince aje ayi gwajin jini, shiyasa na'ki tafiya gida banaso na fita na jawa kaina matsala na zama abar nunawa a duniya". Goge hawaye tayi tana bashi ha'kuri, ji yayi kansa ya masa nauyi 'kirjinsa ya d'aure, tunda ya bijirewa auren Sultana Hajiya ke nuna masa banbanci yake fama da 'bacin rai har wannan lokacin, ta rabashi da farin cikinsa ta rabashi da Bilkisu, yanzu kuma da yaks gab da mallakar d'ansa na cikinsa take neman sake wargaza maza, ya rasa wacce irin uwa ce dashi a yanzu baya tuna gatan da tayi masa sai damuwar da ta d'ora masa. Katse masa tunani Hadiyya tayi tace "Honey anya kuwa Hajiya ce ta haifeka? Gani nake babu uwar da zata yiwa d'anta haka". "Ita ta haifeni kawai dai tana wareni ne cikin 'ya'yanta, lokacin da nake 'karami babu wanda ke da gata kamar ni duk abinda ta samu ni take bawa kasancewar yayyena suna 'kananun sana'o'i". Baisan dalilin da yasa yake fad'a mata haka ba dukda yana ganin yarintarta amma matarsa ce. Gyara zama tayi saboda jin gulma tace "to naga duk sun fika kud'i ai ko? Shi dama mijin jumana ba mazauni bane amma cikinku duk yafi kud'i, itama mijin sultana ya fika kud'i aikin gwamnati yakeyi fa, meyasa bazata takura musu ba sai kai kafinta?" "Ban sani ba, amma abin yana damuna" ya fad'a yana jin ransa ya sosu, shiru tayi na d'an lokaci sannan tace "ina ganin na san dalili, dukkansu 'yan uwa suka aura ko?" "Eh 'ya'yan yayyenta duk suka aura, farko ni taso na auri Sultana nace nafi son Bilkisu, banason auren dangi musamman na danginta, hakan ne ya 'bata mata rai tace usman ya aureta ya amince". "Honey nasan dalilin da yasa Hajiya take maka haka, dukda cewa Kai ne talaka a cikinsu amma duk ka fisu yi mata alheri, sannan lokacin da kana 'karami ka fisu morarta, ban sani ba ko abinda zan fad'a bazai maka dad'i ba amma Hajiya na takaicin wata bare tazo taci abinda ka tara ne saboda ita ce silar hakan, tafi so danginta suci hakan yasa ta takurawa Bilkisu har kuka rabu, sannan kuma ta aura maka ni ne saboda mahaifiyata abokiyar shawararta ce, dukkansu mazaje sun mutu sun barsu da 'ya'ya suna wahala, sun San sirrin juna amma Ammy bata ta'ba fad'amin komai a kan Hajiya ba saidai gashi Hajiya tana 'kulla mata abinda batayi ba". "Ina ganin mafita d'aya ce gareni,  bayan haihuwarki da yardar Allah zamu bar gidannan, idan har Hajiya na tare damu bana tunanin zamu samu kwanciyar hankali". *56* akiya na musu zuwa airport hannuna na cikin na Aliyu. Kallona yayi ya kalli hanyar tafiyarsa yace "yanzu bazaki tausaya min ba ki taho tare dani? Su Mama kya dawo daga baya ki gansu". Murmushi nayi nace "a'a na fa dad'e banga gida ba, tunda akayi aurena sau biyu nazo nan, sati biyu dai ai ba yawa ni da naso nayi arba'in?" "Tabd'i da wallahi sai na biyo ki, watannin da nayi babu ke fa jurewa kawai nakeyi but I really miss you". 'karashe maganar yayi tare da hugging d'ina, banyi hugging d'insa back ba da farko saboda Mum tana kallona, daga baya dai nayi hugging d'insa nace "I'll miss you too". 'ko'karin kissing d'ina yayi na d'auke kaina, iya kunyar da zanji gaban Mum na jita banaso na 'kara wata. Saida muka ga tashinsu sannan Jabir ya d'aukeni muka koma gida. A gidan ma bata sauya zani ba, domin Yaya ke min wanka sannan ta wuni tana kula da Abduls, da dare kuma ni da Mama muyi fama domin kukan dare garesu. Tunda naga sun wuni suna bacci na san yau akwai hirar dare, saboda haka na samu nima nayi baccin rana. . 12am dai-dai suka farka saidai Basu tashi da rigima ba, 1:30 suka fara kuka gaba d'ayan su, 'ko'karin had'a musu madara na fara saidai gaba d'aya na rikice, yau ne rana ta farko da zan had'a musu madara. Karanta instructions d'in na fara saidai kukansu gaba d'aya ya gigita ni, ga Mama yau tana wurin mijinta. Ruwan zafin na zuba bansan lokacin da na cika feeder da shi ba, ragewa nayi yayin da ruwan ya zuba a hannuna da 'kyar na samu na had'a musu madara ba yanda ma ya kamata ba, ina fara Basu suka 'ki sha suka fara sabon kuka, Abdul-malik nayi Abdul-hakim na amsawa, rasa yanda zanyi dasu nayi na saka su a gaba na fara hawaye, daga hawaye sai kuka sosai dama haka raino yake? Meyasa na kasa controlling 'ya'yan da na haifa a cikina? Yanda nake da son yara gani nake zan iya kula da 'yan biyar ma, saidai gashi tun kafin ayi nisa na fara gazawa. "Wai yaya nake jin kuka ne ko bacci kikeyi?" Zubamin ido tayi ganin na saka yara a gaba ina kuka, matsowa tayi kusa dani tace "Bilkisu lafiya?" "Mama bansan ya zanyi ba". Kuka sosai ya 'kwacemin tace "to ki basu nono mana". "Tun 12 nike basu har na gaji, kuma na basu madara sun 'ki sha". 'Daukan madarar Mama tayi ta kalla tace "ruwa yayi yawa ta yaya zasu sha? Saidai a zubar a had'a musu wata". Abdul-hakim ta d'auka ta goyashi sannan ta nufi toilet ta zubar da madarar, dawowa tayi ta fara had'a musu madara tana min bayanin yanda ake had'awa. Abdul-malik na d'auka na fara feeding d'insa haka yasa kukan ya ragu, tana jijjiga Abdul-hakim ta gama had'a madarar sannan ta saukeshi ta fara bashi Madara, bayan d'an lokaci ya kar'ba muka samu d'akin yayi shiru. Goge hawayena nayi tare da sanya ma Abdul-malik feeder shima, bacci suka fara mama ta kalleni tace "yanzu ke bakiji kunyar kuka ba?" "Mama na rasa ya zanyi ne, tuj 12 nake fama dasu sama da awa kenan fa sannan suna kuka sosai a tare, sun rikita ni gaba d'aya na rasa me zanyi". D'aura yaron hannunta tayi a kafad'a tace "Raino nutsuwa yake bu'kata Bilkisu, idan kina freaking out bazaki iya komai ba, tsaida hankalinki zakiyi wuri d'aya kar kiyi focusing a kan kukansu, kiyi focusing akan yanda zaki sama wa kanki nutsuwa ki sama musu". Kwantar da shi tayi ta tashi tace "saida safe". Ta fita ta barni, na jima ina tunanin yanda zanci gaba da kula da su har bacci ya d'aukeni. Kwanaki sunyi gudu sosai kamar yau nazo wai har sati biyu sun cika. Aunty naje yiwa sallama a gidanta na wuni, muna zaune Aliyu ya kirata bayan sun gaisa ta tashi, hakanan naji yau ina son yin gulma saboda haka na kasa kunne domin jin abinda zasu ce. "Ita ta fad'a maka hakan? A'a Aliyu kar ka yanke hukunci babu bincike, kowace 'ya tana son ganin gidansu ba Bilkisu kawai ba, sannan na tabbata rayuwarku na birgeta kawai sakewa da hakan ne bazata iya ba........ a'a kar ka sake ka mata wannan zancen wannan tsakanina da kai ne, tunda yanzu kana sonta wannan batu a barshi dan Allah saidai idan har ita tace bata sonka, idan har ka lura bata sonka sai muyi yanda muka ce amma idan har kaga akasin hakan to wannan magana ta zama tsakanina da kai, mu binneta har abada babu wanda zaiji ta, na tabbata hakan bazai wa Bilkisu dad'i ba dukda saboda 'karuwarta akayi". Gabana naji yana fad'uwa, me Aunty da Aliyu suka aikata da basa so kowa ya sani? Shin hakan ya danganci aurena ko kuma haihuwata? Zuciyata bugawa take cikin sauri yayin da abubuwa marasa dad'i ke min yawo a raina, Aliyu ne kawai mutumin da ya dace nayi wannan maganar dashi fata na bazai 'boyemin komai ba. ************* *SALEH* Hajiya da Maimuna na ta zuba ido su ga fitar Hadiyya suka ji shiru, gashi Saleh ya dawo tun kafin lokacin dawowarsa shima ya shige yayi zamansa. "Hajiya ko na'kuda shegiyar nan ta fara ne? Tunda ya kamata ace ta d'auki hanyar tafiya gida". "Da na'kuda take ai zai fito ya fad'a mana, kawai dai wani munafurcin take sa'kawa kanta amma zata gani ne, matu'kar ta Sanya 'kafa ta bar gidannan ta tafi kenan domin na gaji da ita". Sai magrib Saleh ya fito tafiya masallaci, tareshi Hajiya tayi tace "Yaya dai har yanzu baku fita kaita gidan ba? Dare fa zaiyi muku a hanya". "Ai Hajiya ta fasa tafiya gidan Mahaifiyar tata tace ta zauna anan sai ta kawo mata wadda zata zauna da ita". Takaici ne ya ishi Hajiya tace "akan me zata zauna? Kowace mace tana son haihuwa a gidan iyayenta domin anfi samun kulawa, ita tsabar rashin sanin ciwon kai ya sanya tace zata zauna? Wannan ai shashanci ne". "Hajiya ni nace ta zauna fa, amma idan na dawo zan miki bayani". Bai jira me zata ce ba ya fita, ko da ya dawo duk yanda taso ta juya ra'ayinsa akan ya tura Hadiyya gida ya'ki har ta ha'kura. A gida ta zauna Ammy ta kan ziyarceta tayi mata kwana d'aya zuwa biyu sannan ta samo yayarta take zama da Hadiyya kullum. Hakan ya bawa 'yan uwanta damar zuwa cin rice, yau wannan tazo kwana yau waccan tazo Saleh kuwa baya gajiya da yi musu hidima dake Allah yayi musu baki, basu da zance sai nashi kullum cikin saka masa albarka suke yi, shi kuma namiji da son ganin an yaba duk abinda yakeyi musu ko a jikinsa. Haihuwar Hadiyya tazo da sau'ki domin a gida ta haihu sai bayan haihuwarta sannan suka tafi asbiti, ta haifi 'yarta kyakkyawa kamar ita, a nan fa hankalin su Hajiya ya sake tashi. Kullum Saleh sai ya shigo da gara leda-leda ga gida kullum cike da mutane, ranar 'kauri ma rago Saleh ya yanka musu. Kiransa Hajiya tayi ta zaunar dashi tace "wai kai me kakeyi haka ne? Kud'innan kamar ha'kosu kakeyi kullum sai ka kashe kamar baka san ciwonsu ba? Ban ce kar ka yiwa matarka hidima ba amma ya kamata ka san me kakeyi, idan ka biyewa matarnan taka sai sun tatseka tas su barka babu ko sisi na san Halin mahaifiyarta sarai domin na zauna da ita, babu abinda take koyawa 'ya'yanta sai yanda zasu yaudari samari su ci kud'insu, Bata da aiki sai koyawa 'ya'yanta kissa yanda zasu cinye kud'in mazajensu, ka rage abinda kakeyi". Mamaki sosai Hajiya ta bashi yace "Hajiya a tunanina kin fini murna da samun haihuwarnan kuma duk abinda nakeyi bana yin sama da kima, na yanka rago ne saboda miyar suna da sauransu sannan ga mutane a gidan bazai yiwu a barsu haka ba". "Mutanen kai ka kawo su!! Banason maganar banza kaji ko?!! Ta tara 'yan uwanta ciyar da su da kake yi ma ai 'ko'kari ne har sai ka 'kara da wata d'awainiya ta daban? To bari kaji idan kai bazaka koresu ba ni zan koresu tunda ba gidan ubansu bane, sai sun talauta min kai sannan ka dawo kana dur'kushe min a gaba? Bazai yiwu ba wallahi". Da 'kyar Saleh ya shawo kan Hajiya ta amince bazata kori dangin Hadiyya ba, saidai a zuciyarta ta 'kuduri niyyar sai tayi maganin wad'annan mayun. Ranar suna Hajiya taci kwalliyarta ta sanya shaddarta Ash ta nufi gidan Hadiyya, hidima ake ta yi mutane kad'an ne suka gaisa da ita kowa kai ya shiga caji. Tabbas Aliyu ya wadata su da kayan cefane abinci kala-kala akayi, waina, funkaso, sinasir, alkubus, tuwo, gurasa, snacks, drinks. Kasancewar Hadiyya me surutu ce hatta makwabta ta saba da su, mutane sosai sun halarci sunan nata. Bin abincin Hajiya keyi da kallo tana yatsine fuska, fitowa Hadiyya tayi tayi shigar lace yayi mata kyau. Da murmushi ta nufi Hajiya tace "sannu uwar mijina" . "A tunaninki wannan 'karamar 'kwa'kwalwar taki da jahilin tunaninki da wanda uwarki ke nuna miki ya isa ya saka ki rabani da d'ana? Baki isa ba wallahi..." Katseta Hadiyya tayi cikin walwala tace "Hajiya muna magana a gaban mutane mu d'an shiga ciki mana" Kafin Hajiya tace wani abu Hadiyya taja hannunta, duk inda tayi sai tace "ga Mamansa ku gaisa ko tace ga uwar mijina ku gaisa". Saida ta samu inda babu mutane sannan ta kar'bi plate d'in abinci da miya tace "Hajiya kina magana, ko kuma sai kin fara cin abinci ne?" "Wannan 'kazantar taku zan ci? Na fi 'karfin naci abincinki". Tuntu'ben 'karya Hadiyya tayi ta juye kaf miyar da ke hannunta a jikin Hajiya, kama baki tayi tace "na shiga uku". Tsumma ta janyo mai daud'a da alamu ma tsane ruwan dattin girki aka yi dashi ta ya'ba shi tun daga fuskar Hajiya har rigarta da zimmar goge miyar da ta zuba, murmushin mugunta tayi tace "kad'an kika gani Hajiya matu'kar baki fita daga gonata ba sai na kwantar dake wallahi". Tana gama fad'in haka ta shiga gida tana ihun a taimako mata tayi 'barin miya a jikin surukarta. *57* Ina goye da Abdul-malik yayin da nake ri'ke da Abdul-hakim, tunani nake tunda na hau jirgin har na sauka gani nake tamkar minti biyu nayi a hanya. Ina fita Raudah ta kar'bi yaron hannuna twins kuma suka fara kokawar kwance na bayana, bansan dalilin da ya sanya ma Aliyu ya taho dasu ba kaman wadda nayi shekara a gida? Mum tana aiki hakan yasa kai tsaye muka nufi gidanmu tare da bar musu twins, naji dad'i da basu biyo mu ba domin yanzu kam lokaci nake so daga ni sai Aliyu. Muna shiga Aliyu yayi attacking d'ina da kisses, dariya nake ina tureshi amma sam ya'ki tsayawa, kissing fuskata yake ta kowane 'bangare sannan ya gangaro wuyana saidai a hankali yake kissing wuyana, kowanne kiss yana d'aukan lokaci kafin ya tafi wani, kashemin jiki ya fara yi yayin da hannunsa ke bin sassan jikina. "Ya Aalee" na fad'a da dasasshiyar murya, turani yakeyi a hankali yana ri'ke da hips d'ina har na fad'a kan kujera duk da maganar Aunty na raina amma na barta sai next time. Straddling d'ina yayi tare da had'a lips d'insa da nawa, rigata ya d'aga ya fara shafa cikina cikin wani salo na daban, wani sauti na saki da bansan lokacin da ya fito ba, janyewa yayi tare da sake pecking d'ina yace "I miss you more". Kissing wuyana yaci gaba dayi zuwa 'kirjina yayin da hannuna ke shafa gashin kansa zuwa bayansa, slowly yake shafa marata na lumshe ido tare da barinsa yaci gaba da hakan. Cikina ne yayi 'kara alamun yunwa, dariya Aliyi yayi tare da barin abinda yake yace "ya kamata kici abinci". Waya yayi cikin minti goma aka kawo mana abinci, muna manne da juna muka ci abincin muna gamawa muka gudanar da natural excercise..... Sai da na nutsu sannan aka kawomin twins wai sun ishe su da kuka, ganin twins ne ya tuna min da maganar Aunty. Washegari hankalina ya gaza kwanciya saboda haka na yanke shawarar yi masa magana. Muna 'kare breakfast ya fita, gashi twins da Raudah duk suna school haka na wuni ina rainon twins har saida na gaji na mi'ka su wajen su inna kulu. Sai yamma sosai Aliyu ya dawo, bayan fitarsa sallah na wanke 'karnin twins daga jikina na saka riga 'karama na shafa powder da lip gloss na zauna jiransa, na samu twins sunyi bacci gara naci lokaci na kafin su farka domin tsabar raino wankan ma sai yanzu nayi, har na fara tunanin samun mai tayin raino. Shigowar Aliyu ce ta tasheni daga zaman da nayi na nufeshi domin yi masa sannu da zuwa, d'agani yayi cak tare da juyani wanda ya bani tsoro da mamaki a lokaci guda, bansan yaushe yayi 'karfi haka ba ko kuma nice na rame? Ajiyeni yayi tare da saka hannayensa bit 'kuguna, sama yayo da hannayen nasa zuwa 'kirjina sannan yace "kin rame sosai fa Bilkisu ko baki da lafiya ne?" Kallon jikina nayi nace "lafiya ta 'kalau kuma ni banji ramar da nayi ba, ko kuma kai dai ka 'kara 'kiba". "Bari mu gani muje mu gwada". Gym d'in cikin gidan muka nufa na kalla nace "da alamu kana shigowa wurinnan sosai ko?" "Tunda kika tafi da zaran na dawo daga aiki nan nake shigowa, babu machine d'in da ban hau ba". "Ai naga alamun haka last night". Na fad'a ina rufe idona, dariya yayi ya cire hannuna daga fuskata yace "ke kuma na lura kin rage kuzari, oya hau mu gani". Saida naji fad'uwar gaba ganin nauyi na 49kg ni da nake 55-56, sai yanzu na yarda na rame cikowar da boobs d'ina yayi yasa na kasa ganewa. Kallona Aliyu yayi cikin damuwa yace "Bilkisu ki fad'amin abinda yake damunki". "Babu abinda yake damuna Ya Aalee kawai Nursing d'in da nakke". "Please don't lie to me, kinyi lossing weight da yawa sannan kice nursing kawai". "I'm not lying" na fad'a tare da kallon idonsa, murmushi nayi nace "da gaske nake babu abinda yake damuna saidai idan akwai wani abu da ban sani ba". "ki sanya skirt muje wurin Mum tabbas akwai abinda yake damunki 7kg fa da yawa, ta yaya zakiyi losing 7kg a 'kan'kanin lokaci?" Hannuna yaja muka fita ina ta rantse masa babu abinda yake damuna, bai amince ba saida ya kira Mum ya sanar mata gamunan zuwa bani da lafiya. Yaranmu muka d'auka muka nufi gidan Mum, waya take tana bayanin wani patient saida ta gama sannan ta juyo gareni, cikin damuwa tace "Bilkisu me yake damunki?" "Mum na fad'a masa babu komai amma ya'ki yarda wai akwai abinda yake damuna saboda nayi loosing 7kg". "7kg da yawa kin tabbatar ba abinda yake damunki?" "Mum bana jin ciwo a jikina ko kad'an, ko ciwon kan da nayi tuni na dena nace masa nursing ne ya sani rama ya'ki yarda". "Gaskiya kam rainon twins akwai wahala, ni da na raini mata ma saida naji a jikina ga 'yan raino ina da balle ke da baki da mai tayi gasu maza, suna shan madarar sosai?" "Ba sosai ba dai jiya sau biyu suka sha yau ko sau d'aya basu sha ba, ko na had'a basa sha maybe har yanzu ban iya had'awa ba". D'aukan Abdul-hakim tayi tace "Masha Allah dukda haka da nauyinsu, ko da yake zasuyi 'kiba tunda suna tsotse min ke, ya kamata ki dinga cin abinci sosai....." Haka taci gaba da bani shawarwari harda maganin da tace zata bani nace mata ta barshi, dukda na rame amma naji dad'in jikina a haka saboda dalilai da dama, kuzari na kawai ya kamata na 'kara. A hanyarmu ta komawa gida shiru nayi ina tunani, ta yaya zan 'bullo masa da maganar da ke damuna a raina? Wace amsa zan samu? "Bilkisu". "Na'am" na fad'a tareda kallonsa, hannuna ya had'a da nasa yace "naga kinyi shiru tabbas akwai abinda yake damunki". "Hakane, idan munje gida sai muyi magana". Yana ri'ke da hannuna yaci gaba da driving har muka shiga gida, muna zama yace "ina sauraronki". Bud'e bakina nayi na rufe, na sake bud'ewa na rufe, cije le'bena nayi ya sunkuya a gabana yace "Babyna please say something mana na fara damuwa". Abubuwa da dama ne suka fara zuwa kaina, meyasa kake tausayina da yawa? Meyasa ni da kai bamu ta'ba fad'a ba? Meyasa duk abinda nayi dai-dai ne a wurinka? Meyasa baka ta'ba ganin laifina? Meyasa kake d'aukana da muhimmanci foye da yanda ya dace? Kai kake aurena amma meyasa ni nake iko da kai? Wad'annan sune tambayoyin da suke kaina amma na danne nace "Meyasa ka aureni". Kallona yayi tareda murmushi, zama yayi kan kujerar da nake yace "yanzu wannan tambaya ce?" "Na sani ni da kai auren had'i ne baka sona lokacin da aka aura maka ni, nasan tausayina yasa ka aureni da kuma biyayya ga iyayenka, nasan dole aka maka..." Yanke maganata yayi ta hanyar kissing d'ina, rashin responding da nayi yasa ya janye tare da turo baki yace "Bilkisu ni bana kallonki a matsayin auren dole, tun ranar da na ganki kike birgeni dukda ban fara miki kallo a matsayin macen da zan aura ba, saidai a duk lokacin da na zolayeki nakan ji hakan a raina kamar da gaske nake ban ta'ba nuna miki bane". Girgiza kai nayi tare da tashi na nufi bedroom, bayan na canza kayana zuwa na bacci Aliyu ya shigo da damuwa a fuskarsa yace "Bilkisu wani abu nayi miki ne? Idan laifi na miki ki fad'amin na baki hakuri ban fahimci tambayoyin da kike min ba me suke nufi?" Kallonshi nayi nace "saboda maganganunka ba gaskiya bane, Ya Aalee naji maganar da kukayi da Aunty so nake ka fad'amin dalilin ka na aurena banda wanda na sani". "Me kikaji? Ni bansan wani abu ba bayan had'amu da akayi saboda ganin mun dace, bansan maganar da kika ji ba". Dur'kusawa nayi a gabansa nace "dan Allah ka fad'amin gaskiya wallahi na san cewa akwai wani dalili na daban, naji abubuwan da Aunty ta fad'a ka fad'amin menene real dalilinka na aurena?" Hawaye na matso ina kallonsa da kalar tausayi, d'agoni yayi yace "ki min al'kawari bazaki gujeni ba idan na fad'a miki gaskiya". Nasan maganar babba ce amma banida wani za'bi nace "na maka al'kawari, babu inda zani". "Bilkisu.....am sorry to say this Aunty ta bani aurenki ne a matsayin contract". Zare ido nayi nace "ban gane ba". Tashi yayi tsaye tareda sanya hannunsa cikin lallausan gashinsa, cije le'bensa yakeyi saidai gaba d'aya kaina ya 'kulle, contract? Wani irin contract? Me Aliyu yake nufi da hakan? "Ka yimin bayani mana dan Allah". Zama yayi saidai da ganinsa ya shiga damuwa sosai, kansa a 'kasa yace, "Daga ni sai maama mukayi maganarnan babu wanda ya sani sai Allah sai mu, ta sanarmin tana so a d'auki fansa akan abinda Mijinki na baya yayi miki, ta san cewa bakya sha'awar rayuwa irin tamu wanda hakan yasa ta had'ani dake akan sharad'in zan taimaka miki ki haihu daga baya na rabu dake kiyi wa kanki za'bi, ganin yanda kika sha'ku da dangina da kuma yanda Mum ke son twins yasa tace kar mu taso da wannan maganar, saidai na lura bakyason rayuwa irin tamu, kinfi  sha'awar rayuwar da kike ciki wanda munga hakan 'karara a komawar da kikayi, na san kina cikin takura a zamanmu dake shine dalilina na kiran maama na sanar mata tace min zata miki magana da kanta cikin dabara". Runtse idona nayi tare da dun'kule hannuwana, 'bacin ran da nakeni a wannan lokacin ban ta'ba jin irinsa ba, meyasa Aunty zata yimin haka? Meyasa aunty zatayi wasa da farin cikina akan d'aukan fansa? A tunaninta hakan zai sakani farin ciki? Ina tunanin nayi auren gata ashe ni ba komai bace face mai zaman cin dukiya, babu soyayyata a zuciyarsa face tausayi da kallona a 'kas'kantacciya mai barar haihuwa wadda zai d'auki kud'insa ya bani sadaka domin na samu haihuwa, shin bu'katar haihuwar tawa har ta.kai na sayar da dignity d'ina? Idan har Aunty tana tunanin ta sama min farin ciki tayi kuskure domin ta jefani a tsaka mai wuya, bazan iya cigaba da zama da Aliyu ba bayan wannan sirrin da ya bud'e min 58 A fusace Hajiya ta shiga gidan tana magana cikin d'aga murya, Hadiyya kuwa tsabar iya acting gaba d'aya ta rud'e kamar da gaske kuskure tayi. "Sai kin tafi gidan ubanki tunda bakinda mutunci, wallahi tallahi a yau zaki bar gidannan sai na saka ya sakeki mara kunya 'yar marasa mutunci, har ni zaki watsawa miya a jikina? Kina auren d'ana ni zaki wula'kanta? Zanga uban da ya tsaya miki daga yau babu ke babu d'ana, ki tattara kayanki ki fice min daga gida takardarki zata biyoki 'yar iska shed'aniya". Har 'kasa Hadiyya ta zube ta kama 'kafara Hajiya tace "Hajiya ke fa kamar uwa kike a wajena ta yaya zan watsa miki miya ina sane? Dan Allah ki min rai bazan sake ba, jama'a ku tayani bata ha'kuri dan Allah". "Hajiya kiyi ha'kuri mana tunda kuskure ne tayi ba ganganci ba". "To ki gangancin ne wannan yarinyar nawa take? Me ta sani ma a auren?" "Wannan kam rashin kyautawa ne, saboda kinada iko da d'anki sai ki sanya ya saki matarsa kawai saboda tayi tuntu'be miya ta zuba a jikinki? Meyasa iyayen mijin yanzu bakuda imani ne? A saki 'yar wani ke taki 'yar ta zauna a gidan aurenta? Wannan son zuciya ne wallahi". Tuni reshe ya juye da mujiya dukda miyar dake zayyane a rigar hajiya da dattin da ya biyo miyar amma kowa rashin kyautawarta yake gani, Hadiyya dai tana dur'kushe tana kiran "ku bari dan Allah kar ku sake janyomin matsala amma abu na mata baki ya'ki rufewa. Fita Hajiya tayi bayan tace da Hadiyya "Zaki ga abinda zai biyo baya sai kinyi nadamar haihuwarki da uwarki tayi". Hajiya ta sha zagi kuwa haka Hadiyya taji dad'i, dukda haka ta tsorata dole ne ta sake shiri kafin ta samu matsala, dukda 85% na mutanen dake wurin laifin Hajiya suke gani, Suma ragowar kawai suna tunanin sharrin yaran zamani ne amma basu tabbatar ba. Hadiyya na dur'kushe a gaban Hajiya babu abinda take sai kuka, kwalliyarta duk ta 'baci da hawaye, bayan an fara watsewa ta tattaro jama'a aka tafi baiwa Hajiya ha'kuri. Ammynta na gefenta da sauran 'yan uwanta, har ma da 'kawayenta da makwabtan arzi'ki na unguwa da na mahaifiyarta. Tana dur'kushe sauran suna zaune ta rantse bazata tafi ba sai Hajiya ta yafe mata ko kuma Saleh yazo anyi abinda za'ayi. Tana jin sallamar Saleh ta sake fashewa da wani sabon kukan, 'kafarta har ta kumbura saboda tsuguno bayanta ya ri'ke amma fatanta kawai kwalliya ta buya kud'in sabulu. Hajiya ce ta kirashi da kanta saidai yana shigowa ya nufi Hadiyya, dafata yayi yace "Hadiyya". Ri'ke hannunsa tayi tare da cije bakinta sannan ta samu ta zauna,  zama yayi gefenta wanda hakan ya sake tunzura Hajiya. "Hajiya me ya...." "Saketa" ta katse masa magana "wallahi sai ka saki wannan 'yar marasa mutuncin". Mamaki yayi domin Hajiya bata sanar masa me ya faru ba ta dai ce masa yazo Babu lafiya. Kallon jama'ar dake d'akin yayi  yaga Mahaifiyar Hadiyya fuskarta d'auke da damuwa yace "mama me ya faru". "Um wallahi tsautsayi, Hadiyya ce tana ri'ke da miya ka san sha'anin jego sannan mahaifiyarka ta barta a tsaye kawai jiri ya kwasheta cikin tsautsayi miyar ta zuba a jikin Surayya, shine take ta bala'i gaban mutane take kiran sai ka saki Hadiyya, bazan so 'yata taci gaba da wannan wahalar ba ga yarinta ga d'anyen jego sannan ga damuwa, sannan batada cikakkiyar lafiya ina ganin kayi abinda ya dace wanda zaka ceci 'yata ka kuma yiwa mahaifiyarka biyayya". Wani kallo Hajiya ta mata tace "lallai kuma kin cika uwar banza, mai daurewa 'yarta gindi tayi abinda taga dama kina sane da abinda 'yarki tayi amma babu kunya kina wa d'an cikinki 'karya, lalacewar taki har ta kai haka? Kinji kunya kin bani mamaki". Babu wanda ya tankawa Hajiya a cikinsu ita kanta Ammy murmushi tayi ta girgiza kanta kawai, hakan ba 'karamin ciwo yayiwa Hajiya ba ta sake kallon Saleh tace "ka saketa yanzunnan na baka umarni". Cikin biyayya Saleh yace "Hajiya nake ganin Ammy bazata mana 'karya ba, kuma Hadiyya bazata zuba miki miya da gangancin ba musamman cikin taro, kiyi ha'kuri". Kallon sauran mutanen dake wurin yayi cikin jin kunyar abinda uwarsa keyi, tambayarsu ya fara yi abinda ya faru kowa ya shaida cewa kuskure ne, wad'anda ke kusa da wurin ma sunga tuntu'ben da tayi. Sallamarsu yayi d'aki ya rage daga shi sai Hajiya, Ammy da kuma Hadiyya wadda ji take kamar tayi ihu duk jikinta ciwo yake saboda yanda take zaune, kasa jurewa tayi tace Ammy ta taimaka mata ta zauna kan kujera bayan ta nemi afuwar Hajiya akan hakan. Bayan an nutsu yace "Hajiya kiyi min afuwa da abinda zance miki, amma matakin da kike nema na d'auka ba mai kyau bane, na saki mace karo na farko da umarninki, idan har na sake sakin mace to tabbas na barwa zuri'a ta gado marar kyau, 'ya'yana mata bazasu yi zaman aure ba haka 'ya'yana maza bazasu ri'ke aure ba, malaman ilmi sube suka fad'a Hajiya kinaso rayuwata ta zama ta lalace?" Tashi tayi tsaye tace "to malam, yimin waazi kaji, mara kunya fitsararre wanda bai san darajar iyayensa ba nice zan 'bata maka rayuwar ma ko? To ka fita ka bani waje kar na sake ganin fuskarsa matu'kar baka saki wannan yarinyar ba". D'aki ta shige ta barsu a nan, a fusace Maimuna ta nufi Hadiyya ta tsinka mata mari tace "la'ananniya matsiyaciya, kina neman lalata mana zuri'a to ta Allah ba taki ba wallahi sai munga bayanki". Ba tare da ta damu da Saleh ba tace "ganin bayana sai na juya wallahi, kuma kece la'ananniya wadda bata san darajar farin cikin d'an uwanta ba, kin ta'ba jikin ki sani wallahi kinci bashin da zaki biya ninkinsa, baniyi muku laifin komai ba kun d'auki tsana kun d'aura mun, kisani duk wanda yake yiwa wani fatan sharri kansa zai koma, iya tsawon lokacin da zaki d'auka kina neman kashemin aure iya tsawon lokacin da zaki kai a gidannan babu aure". Tashi tayi a hankali ta nufi 'kofa ita ma, Hajiya ta kaita bango amma daga yau ta gama dur'kusawa Hajiya, ta gama bata girmanta na uwar miji zata fito mata a sak mutum d'inta sai ta koya mata hankali ita da 'ya'yanta, ganin Saleh ma sai ya gagareta. A gidan Ammy ta kwana saidai sun kasa bacci sa'kawa suke suna warwarewa, fata kawai sukeyi kar Saleh yayi biyayya ga mahaifiyarsa. Washegari da Saleh yaje part d'in Hajiya sai ya sameshi a rufe,  haka ma da yamma har dare. Kwana uku sukayi a wannan halin Hajiya na rufe da 'kofarta yayin da kullum zai buga yana ro'konta ta bud'e amma bata sauraronsa, yasan cewa fushin mahaifiyarsa masifa ne a gareshi amma Allah yana gani bashida laifi. A rana ta biyar yana wajen aiki saidai hankalinsa na gida yana tunanin halin da Hajiya da Hadiyya ke ciki, har yafi damuwa  akan lafiyar Hadiyya domin yanda yaga tsantsar tsana a fuskar Maimuna tunaninsa kawai kar su cutar da ita. "Saleh!" Jabir ya 'kwala masa kira tare da masa alamar yazo, nufar jabir yayi ya sameshi da wani mutum, gaisawa sukayi jabir yace "wad'annan kayan yakeso ayi masa saidai yace a cikin gidan nasa yakeso ayi kamar yanda mukayi na kwanaki". "Okay ba matsala". "Amma fa a Had'eja ne". Kallon Jabir yayi sannan yayi shiru, jabir sabon ango ne sannan ga tafiya mai tsayi ta tashi, shi kuma gashi an masa haihuwa, hakanan d'ayansu zai sacrificing ya tafi. Tunani ne yazo kan Saleh yace "babu matsala ni zanje, saidai zan de'bi yara da yawa saboda muyi abinda zamuyi akan lokaci". Walwala ce ta bayyana a fuskar mutumin yace "alhamdulillahi hakan yayi ai, sabon gida ne zamu koma sannan yanzu yanayin fita da kaya wahala ne, sannan akwai idanuwan da bamuso su ga kayan namu, zamu baku mazauni a can har lokacin da zaku gama ku dawo da yardar Allah". "To Alhaji mun gode amma ina ganin a barshi kawai, yaran namu zasu dinga kwana a gidan ni kuma da iyalina zan je zan nemi masaukin da ya dace". Murmushi mutumin yayi yace "harkar gidaje da filaye nakeyi kar kaji komai, zan baka gida kai da iyalin naka ka zauna su kuma yaran sai a gyara musu wani 'bangare a cikin gidan su zauna, abinci ma na d'auke muku har ku gama mana aikinmu, fatanmu kuyi aiki mai kyau". Kallon Saleh matar tayi tace "yanzu aikin zai kai yaushe?" "Ya danganta, d'akuna nawa ne? "d'akuna hud'u ne da kitchen da dining". "Idan har munyi sauri zamuyi wata uku zuwa hud'u". B'ata rai tayi tace "baza'a iya gamawa kafin hakan ba?" "Hajiya munaso mu muku kaya mai inganci ne sosai, hakan dai za'ayi ha'kuri zamuyi iya bakin 'ko'karinmu muga mun gama kafin hakan ko dai-dai hakan". Dafa kafad'ar matar mutumin yayi yace "Maman Abba kiyi ha'kuri kamar yau ne". Cikin nuna gajiyawa tace "Alhaji ba gajen ha'kuri nake ba kawai ina tsoro sake kwana da Mama ne gida d'aya, baka ganin mu Kama haya kafin lokacin?" Hannunta ya ri'ke dukda a matsayin rad'a suke maganar amma saleh na jin komai sannan yace "Maman Abba hakurin da kikayi a baya ki 'kara kad'an a kai ba wai ina fad'in haka saboda mahaifiyata bace, amma tunda mukayo wannan tattakin saboda kayan gidannan ai komai yazo 'karshe a iznin Allah, idan mun tafi masaukinmu mayi maganar". Murmushi tayi Aliyu ya kalleta, 'karara zaka san cewar tasha wuyar rayuwa yanayin kayan jikinta da ma jikin nata, bazaka ta'ba cewa matarsa bace domin kayan jikinta 'kas'kantattu ne". Murmushin takaici tayi tace "shekaru goma sha biyu a 'kunci dole nayi d'okin samun walwala mana". A take Saleh ya fahimci halin da ake ciki, 'mahaifiyata' d kuma 'halin 'kunci ya had'a ya tada abinda ke faruwa garesu, tabbas Mahaifiyar mutumin itace matsala, ya kamata ya watsawa tasa matsalar ruwa kafin tayi yawa. Sati biyu mutumin ya basu su had'a kayan aiki sannan suje Had'eja su fara aiki. A lokacin ya sanarwa jabir 'kudurinsa ya goya masa baya, yana zuwa gida ya sanarwa da Hadiyya yace mata "naga yanda matsalar mahaifiyata ke sake yawa, saboda haka na yanke hukuncin tafiya dake jigawa aikin da zamuyi nan da sati biyu, banaso ki fad'awa kowa, kafin kwanakin suzo zamuyi faking munyi fad'a dake ki had'a kayanki ki tafi gida, ni kuma ranar da zamu tafi zanzo na d'aukeki mu tafi, zamu kai a 'kalla watanni hud'u". Tsabar murna harda tsalle sannan tayi al'kawarin kama bakinta, yanda suka tsara kuwa sukayi fad'an 'karya har gate ta fita tana sirfa Allah ya isa bata yafe ba, tana fita kuwa Hajiya kamar ta rungume Saleh wanda hakan ya Sosa masa ransa, a haka take fad'in tana son farin cikinsa? Ko da zuwan Hadiyya sa'ka surkullenta tayi ta kira 'yan uwanta, bayan ta kira saleh ta tabbatar yana aiki suka d'auki zugarsu da bulala a hannu suka nufi gidan su Saleh. Babu sallama Hadiyya da yayyenta suka danna kai, d'amara tayi ganin Hajiya da Maimuna suna shewa tace "kin rabani da d'anki, ke kuma kin rabani da d'an uwanki, to ku sani wallahi ba'a ta'ba hadiyyatullahi a zauna lafiya kutumar uban mutum nake ci duk girmansa". Tasowa Maimuna tayi kafin ta bud'e baki Hadiyya ta fara mata sallama da mari, kafin ta dawo hayyacinta ta sake sakar mata wani saida ta kai Maimuna 'kasa da mari sannan ta zazzabga mata dorinar, ihu Maimuna takeyi Hajiya na kawo mata d'auki amma a banza, saida Hadiyya ta yiwa Maimuna likis sannan tace da Hajiya "saura ke uwar banza". Kallon sisters d'inta tayi suka yi kan Hajiya suka danneta a kife, hayewa kanta Hadiyya tayi ta shiga zabga mata dorinar nan a duwawu, tun Hajiya na masifa da zagin Hadiyya har saida ta fara kuka wiwi tana ro'kon tayi ha'kuri, d'aga ta Hadiyya tayi tace "idan d'anki yazo sai ki kwaye masa duwawu ki nuna masa shaidar na dakeki kinji? Kema 'yar gidan najadu zaki iya d'aga masa yaga dukan domin nasan wuraren da na daka a jikinku, ke Hajiya tunda ya rabu dani inaso dan Allah ki aureshi, ki zauna dashi ki bashi ha'kkin auren da ni zan bashi tunda kina kishi da ni, ko kuma ki bashi wannan salamatun". Ficewa tayi ta barsu suna ta juyi a 'kasa, gwara ma Maimuna Hajiya ko zama ta kasa ba abinda take furtawa sai "wannan anyi tsinanniyar yarinya". Yau na cika burinku sai ku bani tukwuici😂😂😂 59            Na kasa furta komai haka shima Aliyu ya kifa kansa a hannayensa fuskarsa tayi. Muryata na rawa nace "aurena ne contract d'in ko kuma twins? Tun kafin ka aureni kana sane da abinda zan haifa kenan?" "Eh". "Aliyu......meyasa ka amince?" Hawayen da na ri'ke ne suka fara zuba, kunya da takaici nakeji a raina domin ni ba komai bace face mai kwad'ayin abin duniya da nazo nuna tsantsar son kaina a biyamin bu'kata na fita, meyasa Aunty batayi tunanin yanda wannan abun zai cutar dani ba a lokacin da ta shirya wannan had'i? Da wane ido zanci gaba da kallon Aliyu? Na zauna na sake ni da sunan matarsa Ashe ba komai bace ni sai contract. Bai amsa min tambayata ba saida na sake tamhayarsa yace "Bilkisu baza mu bar maganarnan ba?" "Yinta yafi barinta alkhairi, Ya Aalee ina son nasan komai dan Allah". "Bilkisu na amince ne saboda....saboda ina  tausayinki a wannan lokaci Bilkisu, kowa ya damu da halin da kike ciki 'yan uwanki na tunanin zaki iya fad'awa wani hali marar kyau, da farko na aureki ne saboda na taimaka miki amma komai ya canza daga baya". Cije le'bena nayi cikin takaici, ya aureni saboda ya taimaka min, wannan ba shine irin auren da naso nayi ba naso nayi aure ne na aminci da soyayya. "Bilkisu daga baya komai ya canza, lokacin da mukayi tafiya dake a lokacin na fahimci wacece ke da halayenki, na sanarwa maama Ina son na baiwa aurenmu chance amma idan har bakya sona zan barshi a matsayin contract d'in ta kuma amince, bayan kin haihu muka yanke shawarar bazamu sake maganar contract d'innan ba amma na lura da yanda kike a cikin family na, da zaran wani ya 'karu apart from Mom and my siblings bakya sakewa kina shiga takura duk na lura da wannan a lokacin haihuwarki da ranar suna amma da muka je gidanku ba haka kikayi ba, na sanarwa Maama cewar na lura bakya Sona ba kya sakewa da family na idan har kika dawo zan nemi za'binki akan aurenmu....shine maganar da kikaji but Bilkisu I really admire you bazan miki 'karya ba nasan bana miki irin son da kikeso amma dan Allah inaso kici gaba da kasancewa matata bazan iya rabuwa da ke ba". Ban bashi amsa ba domin maganganunsa basu gamsheni ba, kwanciya nayi na 'kudundune har twins suka farka na d'aukesu na fita dasu. Yanda suka saba sai 2am suka yi bacci har lokacin idanuna babu alamar bacci, sallah na fara gabatarwa har saida gwiwoyina suka fara gazawa, it's now or never dole ne na yanke hukuncin da ya dace dani. Da safe babu wanda ya yiwa wani magana a cikinmu har mukayi breakfast ya fita, haka ma da ya dawo gaisawa kawai mukayi ya wuce d'aki, binsa nayi da kallo ina jin rashin dad'i, ya taimaka min amma na sanyashi a damuwa, da bai aureni ba na tabbata a wannan lokacin ciwon zuciya zai iya kamani, Saleh yayi aure zuwa yanzu nasan yana nan da 'ya ko d'a yayin da zanyi ta zama a gida maza na zuwa suna taya ni a wula'kance tamkar gwanjo, amma yayi min sutura ya aureni dukda nakasar da nake da sannan yayimin maganin damuwata, godiya ya kamata na masa ba fushi ba Aunty ya dace na nunawa kuskurenta. Kiran Aunty nayi bayan mun gaisa na sanar mata da na san dalilin aurena da kuma rashin dad'in da naji, lokaci mai tsayi ta d'auka tana bani ha'kuri tare da nunamin manufarta hakanan na ha'kura tunda banida damar yin fushi da ita. Washegari kafin na tashi ma Aliyu ya fita, banji dad'in hakan ba domin na tashi da niyyar na bashi ha'kuri. 12pm ina shirya twins Mum ta shigo, muna gaisawa tace "Aliyu ya fad'amin komai....". Sunkuyar da kaina nayi banyi zaton zai kai wannan maganar gaban Mum ba. *********** "Baki da hankali ko Hadiyya? Me kika aikata haka saboda ke shashasha ce? Wannan karon kin wuce gona da iri bazan ta'ba goyon bayanki ba". Jikin Hadiyya yayi sanyi domin sai yanzu ta San cewa ta tafka kuskure, dukda ta shirya yanda zata tsara Saleh kar yaga lafinta amma fushin Ammynta ya razana ta sosai. "Ammy dan Allah kiyi ha'kuri bansan laifin nawa zaikai haka ba". Hadiyya ta fad'a tana marairaicewa, tasan idan ka kashe murya Ammynta zata yafe mata amma yau babu wannan, tamkar sake fusata Ammy tayi tace, "Ba ni ya dace ki bawa ha'kuri ba surayya da Saleh ya dace ki bawa ha'kuri, wannan tsantsar rashin tarbiyya ne ban d'ora ki akan wannan ba, Hadiyya Mahaifiyar wasu kika daka bakya tunanin wani zaiyi min hakan nima? Duk wanda ya raina uwar wani hausawa sunce bai d'auki tashi da muhimmanci ba, kin bani kunya Hadiyya". Kuka Hadiyya ta fashe dashi zuwa yanzu hankalinta ya tashi, dur'kusawa tayi tace "Ammy dan Allah ki yafemin banyi haka saboda na baki kunya ba dan Allah kiyi ha'kuri". "Zanyi ha'kuri ne kawai idan kika amince da laifinki kika sanarwa da Saleh, ki kuma kar'bi duk hukuncin da zai miki, karki manta ke fa uwace kin haifa, ki duba ciwon da zakiji idan uwar mijin tasleem ta dakeki ta dalilin 'yarki, ki kar'bi laifinki da hukuncinki". Fita Ammy tayi ta barta tana ta share hawaye, sai yanzu ta san cewar ta wuce gona da iri kuma gaskiyar Ammynta ne, uwa uwace ko da mahaukaciya ce bazata so a ta'ba lafiyar Ammynta ba meyasa ta aikata hakan? Ta san saki kawai zai rabata da Saleh shikenan tayiwa aurenta, nadama sosai takeyi tana kuka yayin da ta d'auki waya ta kira Saleh. Yana d'agawa tace "Honey, dan Allah kazo gida yanzu inada magana dakai ta gaggawa". "Hadiyya me ya faru?" Bata amsa masa ba ta katse kiran ta zauna ta fara preparing kanta for the worst. Yana tashi daga aiki kuwa ya biya, tana zaune bakin katifa yayin da yake zaune a kujerar dake dakin. "An sanar maka abinda ya faru a gida ko?" "Maimuna ta sanar dani, amma inaso naji ta bakinki". Hawaye ke zuba daga idanunta tace "duk abinda suka fad'a gaskiya ne, naje har gidanku na daki Hajiya da Maimuna.....da dorina" ta 'kare maganar tana shesshe'kar kuka "ka yankemin hukuncin da ya dace domin na fahimci laifina na kuma kar'beshi duk abinda ka yanke zan kar'ba Saleh, abinda nayi babu mai hankalin da zai aikata, na wula'kanta mahaifiyarka bana tunanin ni za'a yiwa tawa haka". "Hadiyya meyasa kikayi haka?" "Honey banida dalilin da zan kare kaina, dalilina mara amfani ne shine kawai yanda Hajiya ke son rabani dakai, bayan wannan dalilin bani da wani abu sai son zuciya da raina na gaba dani, kayi ha'kuri dan Allah". Tashi tsaye yayi tareda dun'kule hannunsa yace "bazan sakeki ba Hadiyya banaso na Saba da saki, amma naji rashin dad'in abinda kika aikata, mahaifiyata ce fa wannan sannan kuma surukarki, aminiya ga mahaifiyarki, ina ganin tafiyarmu tare bazata yiwu tare ba zan tafi ni kad'ai, ki zauna kiyi tunani akan abinda kika aikata sannan ki bawa mahaifiyata ha'kuri, zuwa lokacin da na dawo idan har baku samu fahimta da mahaifiyata ba, ina ganin zan d'auki matakin da takeso domin uwata tafi min kowa a duniyarnan, kin bani kunya Hadiyya banyi zaton haka daga gareki ba". Ficewa yayi ba tareda ya sake kallon inda take ba, fashewa tayi da kukan nadama tana tunanin yanda zatayi wata hud'u wannan laifin yana cinta, mahaifiyarta na fushi da ita shima Saleh Yana fushi da ita, ya zamar mata dole ta canza halayyarta domin samo soyayyar mutum biyu, Hajiya da Saleh. "kiyi ha'kuri kinji Bilkisu?" "Mum komai ya wuce nayi tunani naga hakan da sukayi ba dan su cutar dani bane, sannan kuma ta dalilin haka na had'u dake, twins, Raudah da kuma Dad. Ko wannan ya isa nayi alfahari da auren I think I overreacted back then banso na nuna masa hakan ba". "Banga laifinki ba idan kinyi fushi domin an miki yawo da hankali amma is it true you are not comfortable around us?" Sunkuyar da kaina nayi nace "sometimes, amma Mum a cikinku banajin komai, kawai idan wasu suka zo ne nakanji am out of place". Dafa kafad'ata Mum tayi tace "bai kamata ki dinga Jin haka ba Bilkisu, you are one of us, da ace mahaifinki yana raye yana nan kamar mu, ke mutum ce haka muma mutane ne karki bari wani abu namu ya canza miki d'abi'arki, muna sonki ne a yanda kika ba wai yanda zaki koma ba". "Nagode Mum amma gani nake kamar ina tauye Aliyu, ya aureni ne saboda yana tausayi na kuma hakanan yake treating d'ina tunda mukayi aure, zaman mu zaici gaba da kasancewa haka Mum?". "Bilkisu dukda ke abinda kike gani kenan amma bayan tausayi Aliyu ya damu dake, kuma ko da bai nuna miki ba yana sonki kai ko baya sonki mu muna sonki, zanyi iya 'ko'karina dan ganin kin zauna tare damu ko da bakyaso, Bilkisu idan kin rabu da Aliyu ina zaki koma? Destiny ya nuna ke da mijinki na baya bakuda 'kaddarar kasancewa ma'aurata na tsawon lokaci just accept it like that, zamu baki duk wata kulawa da kike bu'kata kuma ni a matsayina na uwa a wurinki bazan ta'ba bari wani abu ya cutar dake ba ko da jinina ne, kiyi tunani" Ina Shirin tada sallar magrib naji sallamar Aliyu, amsa masa nayi sannan na tada salla yayin da ya nufi twins. Har na idar da sallah banji kukan twins ba abin ya bani mamaki, bayan na idar da addu'a na juya na kallesu, cikin sauri naga Aliyu ya 'boye abu a bayansa na tashi na nufeshi, twins na samu sai tand'ar baki sukeyi na kalleshi nace "me ka Basu?" "Ni? Bakomai yunwa dai kawai naga kaman suna ji". Ya fad'a yana sake 'boye abinda ke hannunsa, rabuwa nayi dashi na juya ina 'ko'karin cire Hijabina, da sauri na juyo na kuwa kamashi dumu-dumu yana lasawa yarana lollipop, seriously yaushe maza zasu girma? "Ya Aalee!" Na fad'a da 'karfi tareda buga 'kafata a 'kasa, 'boye alawar yayi harda zare ido yace "menene?" Ji nake kamar na makeshi amma na danne nace "baka san ma me kayi ba ko? Ya zaka basu sweet?" "Kallo naga sunayi am sure Abdul-malik har zubda yawu yayi, ai Kinga nayi rashin adalcu idan ban Basu ba ko?" Dafe kaina nayi na kalleshi, ya had'e hannunsa biyu da lollipop d'in a ciki ya turo le'bensa, kasa ce masa komai nayi na kar'bi lollipop d'in na saka a baki na juya. Saida na ninke hijabina sannan na zauna nace "ka kaini 'kara wajen Mum ko?" Kansa ya d'aura a kafad'ata yace "more like na kai kaina 'kara wajen Mum, ki yarda dani Bilkisu ina sonki kwanakin da kikayi bakya kulani na shiga takura sosai, please stay with me Bilkisu kinji?" "Indai zaka dinga treating d'ina kamar matarka ba kamar abin tausayi ba zan zauna da kai". "Nagode nagode nagode Allah ya barmu tare" ya fad'a tareda tura ni kan gadon, tickling d'ina ya fara ina dariya a haka Dan hatsaniyar namu ta wuce. Madara na had'awa twins muka d'aukesu muna basu a tare, waya ya ciro yayi mana pic ba tareda na lura ba, ture wayar nayi ya bo'ye yana min gwalo, bansan yaushe Aliyu zai girma ba. "Hashtag feeding my babies" ya furta yana danna wayarsa, kafad'arsa na ture a hankali nace "Dan Allah ya Aalee kar ka tura wa kowa pic d'innan kalli fa kayan dake jikina". Maida wayar tashi aljihu yayi yace "dama babu wanda zan turawa tsokanarki nakeyi amma bakiga yanda kikayi kyau ba fa, yanzu dai me ya kamata mu yiwa wannan wajen ya cika?" Ya fad'a yana shafa 'kasusuwan wuyana da suka bayyana, hannuna na saka na shafa nace, "Inajin dad'in jikina a hakan banaso na 'kara 'kiba a yanzu, idan lokacin 'kibar yayi sai ka nemi yanda za'ayi na ragu". Sannu-sannu muke bin relationship d'inmu kamar sabbin couples, mun zama friends sosai ta yanda yake fad'amin sirrinsa nima nake sanar masa da nawa saidai ba duka ba wani sirrin yafi a barshi a 'boye, kamar zamansa a turai wanda banaso ko ambata ayi. Munada differences sosai tsakaninmu wanda ban fahimta ba sai yanzu, a baya danne komai yake yi saboda ni amma yanzu yana bayyana min komai. "Ina twins" ya tambaya yayin da na shiga gida, bayansa na haye nace "relax mana beb, twins suna wajen su inna kulu". 'bata rai yayi kafin yayi magana nace "na San cewa baka son ina kaisu amma banida wani choice, banaso na shiga wanka na barsu su kad'ai it's not healthy". "Zamansu a wannan wurin ma is not healthy, ki duba haya'kin dake tashi a wurin sannan su kansu mutanen.....". Hannu nasa na rufe masa baki nace "su Inna kulu suna da tsafta fiye da yanda kake zato, sannan da shinfidarsu na kaisu dan Allah ka dena damuwa". Dukda Aliyu baya 'kyamar talaka amma baya so 'ya'yansa suna ra'bar su inna kulu, ta 'bangarena kuwa tamakamon sukeyi sosai. Twins na 6 months Mum ta tambayeni ko inason na koma aiki zata nema min nace a'a, domin aikina bashida amfani a wannan lokacin, bu'katuna kafin na fad'a an biya min ga kud'in dake shigomin lokaci-lokaci. Lokacin da na Tara kud'ad'de na da dama na nufi sansanin 'yan gudun hijra na Abuja, na bawa mazansu da matansu jari sannan na siya musu abin sarrafawa na rayuwa. *5 YEARS LATER* "Mace da namiji". "No baby Mace zallah kawai nakeso". "To namiji da mace". Kallonshi nayi na koma aikina, kusan 2months kenan yana takuramin akan muje mu sake IVF wai twins sun tsufa tunda har sun shiga school sannan gidan ya fara rashin dad'i, kaicewa maganar nakeyi saidai ya ma'kale kullum sai yayi nace masa mace nakeso yace shi namiji yakeso, ni kuma na rantse bazan sake haifar twins ba wad'annan har yanzu suna bani headache. "Babyyyy......nifa ba babyn ne banaso ba nima inaso kawai banason na sake twins ne wancan sun bani wahala, sannan kuma idan har zaka amince.... adopting baby nakeso nayi". Wani kallo yayimin yace "adopting kuma? Kamar yaya? Bilkisu kinsan bakida matsalar bu'katu ko wani abun IVF d'innan minti nawa ne an gama?" "Ba wai banason aikin bane kawai ladan nake dubawa, instead of mu 'bata kud'inmu wajen neman 'ya ko d'a gasu suna neman taimakonmu, please reconsider this". Numfashi y sauke yace "Bilkisu ina tsoron halin mutane sannan da halin rayuwa da kuma bakin mutane, ance tsintacciyar mage.....". "Itace kuwa take mage domin ka tambayi gidajen da maguna suka tsufa a cikinsu zasu sanar maka asalin magennan tsintuwa ce, baby mu muke lalata komai da tunani marar kyau, ka tsarkake zuciyarka na tabbatar idan muka bawa 'yar da zamu d'auko kulawa tsakaninmu da Allah bazata tashi da mummunar manufa a ranta ba". Wa'azi na dinga yi ma Aliyu har ya amince da murna ta muka nufi orphanage home na Abuja, baiyi min musu ba akan baby girl da nace inaso. Tunda muka je na lura jikinsa yayi sanyi, bin yaran yake da kallo amma bai ta'ba ko d'aya ba, wata baby nagani da bazata wuce wata biyu ba tana bacci cikin shinfidarta instantly ta shiga raina na d'auketa. Muna fita na mi'ka ma Aliyu ita ya'ki kar'barta saidai da kansa ya kaimu wajen kayan yara na siya mata wad'anda zasu isheta. A gidansu Aliyu ma Mum batayi approving completely ba saboda bamu sanar mata ba sannan bata tunanin it's a good idea, a hankali na shawo kansu suka amince da yarinyar da na d'auko mai suna Aisha. ************ Saleh yana shiga gida Hajiya tayi masa magana tace "ka 'karashe mata saki ukun ko?" "Hajiya.....". "Karka yimin wata maganar banza marar amfani, yarinya tazo har gida ta daki uwarka bazaka mata saki uku ba?" "Hajiya bazan iya sakinta da 'yata a hannunta ba, ban san bayan wannan mata nawa zaki sanya na saka ba sannan na tsani kalmar saki, da ace kinada ikon sakin Hadiyya da na baki kin saketa amma bazan iya sakinta ba". Kuka Hajiya ta fara tace "wato har wata mace tafi uwarka ko? Tazo ta sameka na gama kiwata maka ita sannan tace zata rabani dakai, ta wula'kantani ta cimin mutunci sannan kace bazaka rabu da ita ba? Me ka d'aukeni Saleh?" Runtse ido yayi domin a wannan karon ya fara karaya, bai san yaushe Hajiya zata dena masa gorin kulawar da ta bashi ba". Dur'kusa gwiwoyinsa yayi a 'kasa ya dago idanunsa d'auke da hawaye, karo na farko da Hajiyarsa taga hawayr a fuskarsa tun bayan sakin Bilkisu da yayi, muryarsa so weak yace, "Hajiya wace irin biyayya zan miki ki amince dani a matsayin d'anki? Tunda na bujirewa umarninki sau d'aya rayuwata gaba d'aya ta canza, kin tashi daga uwar da nake zuwa wajenta a duk lokacin da nakeda damuwa, kin tashi daga uwar da nake zuwa gareta a duk lokacin da farin ciki ya sameni ko nake bu'katar walwala, har ta kai ga idan na ganki gabana fad'uwa yakeyi, dan Allah Hajiya ki fad'amin me zanyi na gyara tsakanina dake? Na gaji wallahi, na gama sarewa da samun farin ciki a rayuwata shekara hud'u da d'ori kenan kina nunamin banbanci a cikin sauran 'ya'yanki, meyasa Hajiya meyasa? Idan har auren Sultana zai sauya tsakaninmu ki umarci usman ya saketa walalhi na miki al'kawarin zan aureta indai hakan kikeso". Jikin Hajiya yayi sanyi kunya ta rufeta, a dalilin son zuciyarta ta sanya Saleh damuwa ta tsawon shekaru, kallonsa tayi taga gaba d'aya ya tashi daga d'an da ta sani, ya tashi daga salenta mai barkwanci mai yawan walwala a fuskarsa, tsufa ya fara bayyana a fuskarsa dukda bai cika koda shekaru arba'in ba, abunda yafi Mata ciwo shine kukan da yake sanadiyyarta, idan har ciwon da yakeji ya kai ga yayi kuka da girmansa a gaban mahaifiyarsa wani irin ciwo yakeji a ransa haka? Dafashi tayi tace "Saleh tabbas nayi kuskure na kuma so kaina da yawa, gaskiya ka fad'a na tashi daga uwa mafi soyuwa a wajenka na koma wata iri daban, bana haifa maka komai sai damuwa, amma da yardar Allah komai ya canza, na sani cewa na kasance mai sanya ido a duk abinda zaka yiwa iyalinka saboda wahalar da nayi a kanka, na zama mai son zuciya da son kaina amma ka yafemin d'ana, Ina ganin mafita d'aya ce garemu, ka d'auki iyalinka ka nemi wani gidan ka zauna ni zaifi min kwanciyar hankali kaima haka". "Amma Hajiya banaso nayi nesa dake, inaso mu zauna a matsayin zuri'a d'aya ni da 'yan uwana". Murmushi Hajiya tayi tace "na sani amma zamanka a waje zaifi alkhairi, ko da na wani lokaci ne kaje ka huta da matarka a wani waje daban nesa daga gareni idan lokaci yayi sai ku dawo ku zauna tare damu, Allah yayi maka albarka". Baiyi mata musu ba sannan ya kasa d'ago kansa ya kalleta, yanda hawaye ke zuba daga idanunsa haka suke zuba daga idanunta tabbas ta lalata farin cikin d'anta na tsawon lokaci saboda son zuciyarta, amma Hadiyya ta koya mata hankali. "Kayi ha'kuri da rabaka da Bilkisu da nayi, a yanzu na tabbatar nayi babban kuskure kuma wallahi nayi nadamar aikata hakan, inama Bilkisu tana tare dakai a yanzu da na nemi yafiyarta, Dan Allah Saleh idan akwai yanda zakayi ka dawo da Bilkisu gidannan wallahi zan fi son hakan, son zuciyata yasa na aura maka Hadiyya gashi a kaina 'bacin ran ya 'kare, tazo tayimin dukan da mahaifana basu yimin shi ba a 'kuruciyata". "Hajiya Bilkisu tayi aure Allah yayi ba matata bace, kiyi min addu'a Allah ya sanya albarka a cikin aurena na yanzu ya bani farin ciki, Hadiyya tayi kuskure mai girma amma ta nuna min tsantsar nadamarta". Shiru Hajiya tayi alamun batason maganar Hadiyya shima ya ajiye maganar, idan har da Hadiyya Allah ya tsara zaiyi zaman aurensa dole ya rungumi wannan 'kaddarar, amma zaiyi tafiya ya bata dama idan bata canza ba saidai ya rabu da ita. Washegari da sassafe Maimuna ta tashi tana Shirin fita, kallonta Hajiya tayi tace "ke Kuma ina zaki je da sassafe haka? Ba na hanaki zuwa gidan mijinnan naki ba saboda rashin zuciyas shine zaki koma?" "Hajiya ba fa gidan mijina zanje ba, wajen malam zanje ayi mana maganin tsinanniyar yarinyarnan kowa ya huta, sannan daren jiya kwana nayi ina mugayen mafarkai na tabbatar jifana akayi ake rabani da samari, daga idddata zusa yanzu maza nawa ne suka zo suka gudu? Na tabbata baban su amir ne yake rabani dasu dan haka nayi magana da malam a waya yace nazo da sassafe a maida masa mugayen abubuwansa kansa da 'ya'yansa". Zama Hajiya tayi tace "yanzu ke Maimuna bazaki yi hankali ba ki zauna ki nutsu? Tabbas asiri gaskiya ne amma ba kowa ne zai miki asiri ba, idan ma anyi ki zauna kiyi addu'a ya karye, da ace aikin malaminnan yana ci ba da tuni kin koma gidan aurenki ba? Yanzu gaki nan kina zaune saidai wannan yazo ya tafi wancan yazo ya tafi, sannan banaso ki saka Hadiyya a wannan abin, ba sai da asiri ba zamuyi maganinta tunda yasan me ta aikata shikenan". Ko kallon Hajiya bata sake yi ba ta fice, tana zuwa wajen malamin ta fara zayyana masa mafarkin da tayi marar dad'i, buga 'kasa yayi yace "tabbas abinda kike tunani gaskiya ne ba'ka'ken aljanu aka turo miki domin su hanaki aure, amma zamuyi maganin abin ga wannan ki shafa bayan sallar Isha sannan kiyi wannan turaren, ki tabbatar shine abinda zakiyi 'karshe kafin ki kwanta, zakiga abin mamaki cikin baccinki Allah zai nuna miki duk wanda yake nufarki da sharri, zakiga shaid'anun dake kanki suna fita da kansu kuma ina tabbatar miki babu makawa a zancena kina gama turarennan mazaje zasu fara zuwa gareki har sai kinyi ruwan ido". Cikin murna Maimuna ta d'auki sa'kon ta fita. 'bangaren Hadiyya kuwa kwana tayi tana kuka, da safe ta shirya ta nufi gidan Hajiya. Tana sallama Hajiya ta d'auke mata kai, ta kai 30mins tana baiwa Hajiya ha'kuri amma ta'ki ko kallonta haka ta tashi ta tafi da al'kawarin zata dawo gobe, zata ci gaba da zuwa har lokacin da Hajiya zata ha'kura. Saida Maimuna tayi sallah ta sanya kayan baccinta sannan ta d'auko turaren malam ta fara yi, cikin 'kan'kanin lokaci d'akin ya turnu'ke da haya'kin amma bata damu ba, saida ta tabbatar ya ratsa jikinta sosai sannan tabi gado ta kwanta. Mummunar fad'uwar gaba ta fara ji tare da wani wari a d'akin, kanta ne yayi mata nauyi yayin da takeji wani motsi a d'akin, runtse idonta tayi jikinta ya fara karkarwa, meyasa malam bai fad'a mata hakan zai faru ba? Idanunta a rufe taji an fizge abinda ta rufa dashi, a ckin 'kan'kanin lokaci taji hannu ya Sha'ke mata wuya, a firgice ta bud'e idanunta tayi arba da wata mummunar halitta da bata ta'ba ganin irinta ba, cikin tsananin firgici ta saki gigitaccen 'kara. A d'imauce Hajiya ta nufi d'akin Maimuna jin 'karan da ta saki, samunta tayi idaninta a 'kafe tana kallon gefe bakinta a bud'e bata motsi. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Maimuna" Hajiya ta fad'a tana jijjigata amma ko motsawa batayi ba, ruwa Hajiya ta d'ebo ta fara yayyafa mata tana shafa mata a fuska tareda tofa mata addu'o'i, ta kai awa tana yiwa Maimuna addu'a sannan ta farfad'o, da wani 'karajin ta farka tana zabura da 'kyar Hajiya ta ri'keta tana tofa mata addu'a har ta samu ta lafa. A haka suka kwana Hajiya na tofawa Maimuna addu'a Maimuna na tashi tana 'kara, kafin safiya ta zama tamkar mahaukaciya duk inda ta kalla ta saki ihu tana fizge fizge, sai rufeta a d'aki Hajiya tayi ta kira taimako. Ki da Hadiyya tazo bada hakuri komawa tayi babu shiri domin samun Maimuna tayi ana Mata ru'kiyya, ihun da takeyi ya samu sau'ki saidai kuma bakinta ya'ki bud'ewa, kallon mutane takeyi kamar wasu halittu daban cikin kwana d'aya ta zama abin tausayi. A wannan hali Saleh ya tafi ya barsu wanda hakan ya 'karawa Hajiya nauyi, sauran 'ya'yanta dama basu damu da su dubata yanda Saleh keyi ba, saidai su bata kud'i suyi tafiyarsu suyi watanni. Daga Hajiya har Maimuna sun koma abin tausayi kowa tsoron Maimuna yakeyi banda Hajiya, Jumana ma tsabar tsoro mijinta tabi sukayi tafiyarsu can wajen aikinsa, Sultana ma le'kowa takeyi tana musu sannu har 'kannenta basa iya shiga d'akin Hajiya. Tuni Hajiya ma ta manta da batun Hadiyya, saidai Hadiyya bata yi 'kasa a gwiwa ba takan je ta d'ebewa Hajiya kewa har suka sha'ku sosai, Hajiya batada zance sai na Maimuna ita kuma Hadiyya tana zama ta saurareta ta kuma bata baki. Ana yiwa Maimuna magani kuma cikin ikon Allah ta fara samun lafiya, yanzu ciwon lomaci lokaci yake tashi saidai ta canza sosai. Hajiya da kanta taje ta d'auko Hadiyua ta dawo da ita domin ta dinga d'ebe mata kewa. A wannan hali Bilki tazo ganin gida, waya tayi da Sultana ta sanar mata tazo ganin gida. "Dan Allah Bilki kizo na ganki ke da yaranki Saleh baya nan sai Hajiya, ki yiwa Allah kizo ki nuna mata yaranki". Amincewa Bilkisu tayi ta d'auki yaranta ta nufi gidansu Saleh, mamaki tayi ganin gidan a rufe tayi knocking. "Waye?" Taji muryar Hajiya, saida taja numfashi sannan tace "nice, ba'kuwa ce". Binta Hajiya tayi da kallo daga sama zuwa 'kasa, ta kasa amincewa Bilkisu take gani a gabanta "Bilkisu?" "Na'am Hajiya ina wuni, sultana tana nan ko?" Kasa amsa mata Hajiya tayi tana bin yaron hannu ta kallo ga d'aya a goye a bayanta, kaucewa tayi Bill ta shige har yanzu Hajiya ta kasa furta koda kalma d'aya, tabbas ta cuci kanta da yanzu yarannan a gidannan za'a haifesu, gaba d'aya Bilkisu ta canza jin dad'i ya bayyana a tattare da ita, taso ganin Bilkisu cikin mawuyacin hali bayan aurensu amma saidai Allah ba azzalumin bawansa bane, ga Bilkisu tayi aure ta sake kyau kwanciyar hankali ta bayyana a gareta ga kuma 'ya'yanta har biyu, yayin da ita tata 'yar take kwance bata cikin hayyacinta. Tsabar murna Sultana harda 'kwalla tana kallon twins, godiya take ga Allah da ya musanyawa Bilkisu da miji wanda yafi Saleh ya Kuma azurtata da haihuwa. Fitowarta daga gidan sultana tayi arba da Hajiya, murya na rawa Hajiya tace "Bilkisu dan Allah ki yafemin duk abubuwan da nayi miki". "Na yafe muku gaba d'aya Hajiya, Allah ya yafe mana". Tana hanyar fita taga Maimuna a 'kofar d'akin Hajiya, riguna biyu ne a jikinta da zani sannan ga wando dogo ga dankwalinta a du'kun'kune, 'kuda ke binta amma ta kifawa waje d'aya ido tana kallo bata damu da 'kudan dake binta ba, addu'a Bilkisu tayi mata a zuciyarta tana neman mata waraka daga Allah. Watanni kad'an bayan dawowar saleht Hajiya ta tafi d Maimuna 'kauyensu nema mata magani, gida ya kasance babu Hajiya suna rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, saida sukayi wata shida sannan suka dawo a wannan lokaci Maimuna ta samu waraka sosai. Dukkansu sun hankalta akan ajiga sabgogin surukansu, Hajiya taso su barta ta koma wani gidan suka 'ki amincewa domin zamanta tare dasu ya fiye musu, a haka ta zauna ita da Maimuna da har wannan lokaci babu aure babu maganar aure a kanta....... *END* *ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO 'KARSHE WANNAN BOOK NAWA ME DOOOOGON ZANGO😅😅😅INA SAKE BAKU HA'KURI GAME DA JA MUKU LOKACI SA NAYI AMMA ALHAMDULILLAH ITS FINALLY THE END* *DAMA NA SANAR MUKU I SUCKS AT ENDINGS😂😂😂KAWAI KU RUFE IDO KU KARANTA DUK ABINDA KUKA GANI, INA GODIYA GA MASOYANA A DUK INDA KUKE ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI* *MY WATTPAD READERS BANI DA KAMARKU, SOYAYYARKU TA DABAN CE* *SPARKLING SONSORIANS* *NAYI DACE FANS* *MARYAM NOVELS* *MUSHA KARATU 2* *FEENAT JAAFAR NOVELS* *DA MA DUK INDA BOOK D'INA YAKAI INA MUKU GODIYA FOR BEARING WITH ME, SAI WATARANA KUMA LOVE YOU ALL*