Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/H9AHhhPcNlNGjHMI4bGhsl *ZAINAZAIN..*! _(Is a love Story and Betrayal)_ *The story of  Patriotic,optimistic,joygiver and a Simple gal..* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira❤️* *Bismillahir Rahamanir Rahim,in The Name of Allah the Most beneficient the most mercefull praise be to Allah loard of the words..Assalamu Alaikum my Follows Fans am Starting my new book i ask Allah Subhanahu Wata'ala to guide me,Throught and Make it Sussefull till the end* *BOOK 1*          0️⃣1️⃣ *BAUCHI NIGERIA..* Tun Daga Yanayin Girman Asibitin da yanayin Tsarin Gininsa zaka Fahimci Wanda ya Mallaki asibitin ba karamin Mutum bane,Asibitin ba mallakin gwannati bane,Asibiti SPECIALIST HOSPITAL ne,ya bambamta da Sauran asibitocin da muka sani. *SAULAWA SPECIALIST HOSPITAL ADDRESS 144Box ALAWA BAUCHI NIGERIA* Asibiti ne Daya samu Tunani kuma Hangen kwakwaran Likitan kwakwalwa Wanda Yayi gwagwarmaayan karatu Tundaga nan gida Nageria Har Zuwa Kasashen Ketare Shekaru talatin da wani Abu da Suka gabata. *Dr Abubakar Bashir Saulawa* Shine ma mallakin Asibitin Saulawa Specialist Hosp wanda ya Budeshi Ba Domin komai ba Sai Domin Taimakon Takala da kuma Burinsa na Ganin ya Gina Asibiti na kashin kansa,Duk da Asibitin bana Gwannati bane kuma Babu Hadin Gwiwan Wasu yan kasuwaci aciki Hakan Wani Sauki ne ga Takalawa kuma marasa karfin Garin na Bauchi Sosai ake Rubibin asibitin Tunda Cikin kashi 100% na Kudin Abunda zaka kashe ana Cire kashe 50% kashi Hamsin ake Karba Shiyasa Asibitin ya zama Wajen zuwan Takalawa da marasa karfin da masu Rufin Asiri Harda masu Kudin Duka Saboda Ingancin Likitocinsu da kuma Kama da Nurses din Dake aiki asibitin da masu Kiwon lafiya,zuwa masu kula da Tsaftan Asibitin Har zuwa kan Security Din Cikin Asibitin da kuma masu Gadin Dake kula da Shige da Fice na asibitin Duka Tsararru ne kuma kwararru ne.. Duk da Dr.Abubakar Bashir Saulawa ya kasance likitan kwakwalwa,Tun a zamanin baya Yanzu ma da Girma ya kamashi Karfinsa ya kare,Yana da ya"ya da kuma Jikoki Wanda Yaso Tun yana da karfinsa an samu Mai gadonsa Cikin Ya"yansa Biyar da Allah ya bashi a Duniya sai dai Hakan bai samu ba Ammh Allah bai barsa Haka ba Biyu Daga Cikin manyan Jikokinsa Mafi Soyuwa acikin Ransa Sun kasance Duka likitoci ne,Daya Likitan yara ne Daya kuma Likitan Fannin mata ne,Shekaru Biyu da suka Gabata asibitin gabadaya ya koma Hannunsu Domin Dr.Abubakar Bashir Saulawa Karfinsa ya kare ga Tsufa ga Shekaru don ma an samu Jin Dadin Rayuwa da kuma Nagartan Tsufa Da ba Haka ba Yana zaune agidansa Tare da matarsa Yana Fama da Ciwon kafa sai dai Duk Sati Jikokinsa Dayake alfahari dasu Suna Zuwa Dubasa da Sanda ma yake Tafiya Ta kowani Bangare Buri da kuma Muradin ALHAJI TSOHO yagama Cika. **** *Monday* *8:54pm* "Fitowa yayi Daga Cikin wani makeken Office din Dake cikin babban Asibitin,Hannunsa Dake Daure da Rantsntsan agogon Kamfanin Gucci ya Tura Cikin aljihun wandon Suit dinsa mai kalan Baki da Fari, Dake jikinsa yayi Lokaci Daya yana Fitowa da Wayarsa Kiran Samsumg ce. Yana Kokarin Amsa Kiran Daya Shigomai da Mirmishi Bisa Fuskarsa kenan Wata Matashiyar Yarinya Da bazata wuce Shekaru Ashirin da hudu ba duniya ba ta Sheko Da Gudu Jikinta Sanye da Fararan kayan Both Riga wando sai karamin Hijabin Dake Jikinta wanda ya Rufe kanta da Wuyanta kawai Cikin Haki Ta Dakata Tana Fadin "Sir..." Kafin ma ta Samu Sauke Numfashin mganarta ya Dago A Zafafe lokaci Daya yana Daga mata Hannu yana Fadin"No..ke  im Going Home...Juz koma miye go to Dr peter or Dr Hisham or Dr Haddir..."Daga Haka kawai ya Wuceta Batare ma Data samu kyakyawan kallo Daga Garesa ba Lokaci Daya wayarsa na Kara Daukan Tsuwa Cikin Muradi da  kuma doki ya Daga Kiran yana Fadin. "FIRSTLOVE...." Da kallon Haushi da kishi Hade kuma da Soyayyah Ta Bishi dashi har ya kulema ganinta. Ingarman Namiji ne kuma mai Cikar Zati Dogon Namiji ne, Fari ne ammh Farinsa ba Sosai bane yadai Hadu ne da Jin Dadi da Tsabar Hutawa,Doguwar Fuska garesa mai Dauke da matsaikatan Idanuwa da Gashin Ido da gira Daidai gwargwardo Bakin Gashi kai garesa wanda yayi wani nadewa irin na Fulanin asali Bakin Sajensa Shi ke karamai kwarjini da Cikar zati akallon Farkon in kaimai zaka mai Shaidan Dattako da Nagarta da kuma kamewa a Fuska *DR.ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA* Yana da kamewa da kuma Basarwa ba kasafai mutun ke iya gano Wani Abu game dashi ba in Dai bashi ya Furta maka ba Kwararran Likita ne afannin mata wato gyneacologist Doctor Wanda ya Shafi Shekaru wajen Takwas a Oxford University London Kafin ya Wuce Mumbai Medicine School ya bata Shekaru Biyu achan kafin ya Dawo kasarsa ta Haihu bayan Dawowarsa ne ya Fara aiki a Asibitin Daya kasaance Mallakin Kakansa ne Alhaji Tsoho Wato Dr.Abubakar Bashir Saulawa. Ajiyar Zuciya mai karfi Ta Sauke kafin ta Yamutsa Fuska Tana Fadin"Dama ai na sani..Komai Firstlove sai anyi mgana Ya kama Masifa Ammh an Tabashi sai ya wani karya Murya yana Firstlove A"a Third Love ne ba Firstlove ba..Tafada Cikin wani irin Haushi Daga kasan Ranta Domin a Hakikanin gaskiya Tun Lokacin da aka Dauketa aiki awannan Asibitin Da Haduwarta da DR.ZAIN,taji Duk Duniya ba Namijin Datake so kamar sa Eh Tana matukar sonsa Domin ya Chanchanta kuma yakai matsayin Asoshi Da Farko ta Fara kokarin Tusa kanta Garesa Sai dai Bata samu Fuska ba Tunda shi bamai Sakin Fuska bane koda yaushe zaka ga Fuskarsa ta Gintse ne,yana da Tarin kwarjini da Haiba Dan Babban Gida ne mai Dattako,Ba Ruwansa da Mata mazan ma ba kasafai yake sakar musu Fuska ba Mace Dayace ke da Wannan Darajan Itace Matarsa Wacce akayi Bikinsu Wata Takwas da Suka Gabata. Bazata ce ga Ainihin Sunanta ba Ammh FIRSTLOVE dai kowa ya sani Duk ba bata taba ganinta a Fuska ba Ta Tabbata Duk wanda yake aiki acikin Asibitin ya san Sunan Firstlove abakin Dr Zain "Daga Haka ta saki Wani Dogon Tsaki kamar bakinta zai Fado ta wuce Fuu kamar Tatashi sama Zuwa Office din Dr peter Domin gwarashi Sau Dubu akan Taje wajen Dr Imran Shima Yan Uban Masifan ne da Rashin bama aikinsa muhmmanci,Da kuma Tsinanan Son mata kamar Bunsuru,Dr Haddir kuma Taga Fitanshi Tun Dazu Baya Cikin Asibitin. **** Tana Jin Sanyin Zazzakar muryansa ta Daki Dodon kunnuwanta ta saki Wani marayan Azuciyar Zuciya mai Hade da Samun Sukuni da Salama Cikin Wata irin Murya mai Cike da kulawa da Soyayyah Take Fadin"Firstlove Ina ka Shiga ne..? Tun dazu ina ta Kiranka u did pick my Call..." Tafada Cikin Wani Irin Sangarta da Shagwaba Har tana Buga kafa Jin muryanta Cikin wannan Shagwaban yasa ya kara Susucewa Cikin Kwaso mgana yake Fadin"Innalillahi FIRSTLOVE...U WANN KILL ME KO.. ? jin Abunda yace ne yasata sakin Wata Siririyar Dariya kafin Tayi wani luu da manyan Idannuwanta kamar yana Ganinta ta Fara Dira kafa tana Fadin"Umh..! Inn....Umh...Ahhhh...Ni Wlh ban yarda ba ina ka ijiye wayarka naji ka shuru almost 3hour Rabon da naji ka fa.." Tafada tana wani Tande baki irin na Mata wadanda suka san kansu,Dafe Kirji DR. ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA yayi kafin ya wani Fesar da Numfashi Yana Fadin"Ohh....Firstlove..HALIMATA my Zainah nayi Attending Din Wata patient da aka kawo Kuma Wayar tawa tana Silent ne am Really Sorry..! Cikin Muryan yarda da Amana ta Furta Daga Bangaranta.."Appolgy Accepted Firstlove kafi kowa sanin ko kana Laifi Wajen kowa ni awajena bazaka Taba Zama mai Laifi ba,kafin ka kuskuremin nake maka afuwa Zain dina.."Tafada Cikin wata murya ta Soyayyah da Sadaukarwa. Tafiya yake yana Waya ammh in kaga yadda Gabadaya Hakoransa ke kyalli awaje zaka Fahimci Irin Farinciki da Nishadin Dayake Ciki da kuma yadda Wayar take mai Dadi Cikin Kasa da Murya yace"Na yarda Dake Firstlove...Na fi kowa Sonki anan Duniyan Hatta kuwa Umman Zarena Allah na Fita Sonki Firstlove.."Yafada Daga karshe Cikin Tura baki yana Tuna irin yadda Umman Zareena ke nuna Tafi kowa Son Zainar Tasa. Dariyar Jin Dadi da Nishadi ta saki Kafin tace"Kai Firstlove Umman tawa ce kafi ta Sona..? Cikin Bata Fuska yace"Eh kina Musu ne..? Da sauri Tace"Haba Firstlove Soyayyah Uwa da yarta Na musamman ne Daga Allah fa.."Cikin kunkuni yace"Alrigt TUnda ni Soyayyata Dake ba Daga Allah bane...Ki koma Wajenta sai ta baki Abunda nake baki mai Dadin nan Every Night.."Yafada Cikin Zolaya da Dariya. Jin Abunda yace ne yasa Ta saka Siririn Hannunta Dayaji Bakin Kunshi da ja Ta Rufe bakinta Tana Fadin"La....La.la...Firstlove ya Fadi Abunda mallam ya Hana Fada.."Ta Fada Cikin Dariya Shima Dariyan yake yana Fadin"Ai ke kika ja..Taya zaki ce Umman Zareena Tafi ni Sonki Ni ai bazance Neneta Tafi ki Sona ba Cos i Know kin Fini yarda Dani Firstlove Duk Duniya Bayan Iyayena da Suka Sanni ta Fannin Rayuwa Kece Wacce kikafi Sani na,Completely kuma kika Yarda Dani 100%..." Cikin Son Tabbatarwa tace"A"a Na fi yarda Dakai Fiye da kaina Firstlove i Trusth u More Dan i Truth my Self..."Tafada Cikin yarda Da kalaman Wadanda Suka Fito Daga kasan Ranta Runtse Ido yayi yana Tuna Wani Abu Jikinsa sai yayi sanyi Yana Tunanin anya yana yi ma Firstlove adalci kuwa..? Ta bashi Dukkan yardanta Shi kuma Batare da saninta ba yana Cin Amananta Duk da ba Laifinsa bane ko yana so ya yakice Abun sai ya kasa ammh Har acikin Ransa baya jin Dadin Abunda yake aikatawa yana Taoron Faruwan wani Abu Watarana.." "When zaka Dawo gida...? Yaji Sanssanyan Muryanta ta katsemai Tunanin Daya Shiga kansa ya shafa Lokaci Daya yana Fadin"Yanzu zan Dawo Firstlove kin ganni ma na Fito Daga Office dina Zuwa Haraban Asibitin Anytin Special for me..? Dan Fuska ta Gimtse kafin tace"Yes...Oh...No..."Tafada Tana Dariya Cikin mamaki yace"Wht..? Da sauri Tace"No is a Suprise For u.."Yana Cijan lebensa na kasa yace"Umh..Ai Ba wani Suprise Da Special dana fi Bukata irinki Firstlove ur know Dadinki Ya kusa Haukatar dani in D morning plz in nazo zan kara Ko Daya Befere nayi Takin Bath muyi Dinner.."Yafada yana marairaice mata. Dariya Take mai Shi kuwa Fadi yake"Plz..plz Firstlove Don"t Say NO...! Cikin Girmamashi Tace"It Ok..Am Waiting For u Come Back Soon Am Here For u Forever Firstlove.."Tafada Lokaci Daya tana Sakamar kiss Din Tare da Huramai iskar ta Cikin Wayan wanda Sai da yaji Tsirgawansa Har tsakiyan kansa. Daga Haka ta katse Kiran Sauke Wayar yayi Daga kunnansa yana Fitar da Huci mai Zafi Daga bakinsa lokaci Daya yana Shafa Kirjinsa,Yana jin yadda Gabadaya yanayinsa ya Chanza Jikinsa na wani Shaking waje Daya na Tsabar Sha"awace yana Jinsa kamar yana yawo Cikin gajimare ne. Sauri Sauri Gudu gudu ya Fito Daga Cikin Asibitin Duk wanda ya ganshi sai ya Bisa da kallon Mamaki,Duk yadda ake ta Kiransa Sir..!Sir..!Banza yayi Ba wanda ya Tankamawa Ya Fito Haraban Makeken Asibitin kai Tsaye parking Space ya nufa jikinsa na Rawa Burinsa kawai ya Bude ido ya gansa gaban Firstlove dinsa Tun Daga Nesa ya Ciro makullin Motansa kirar Toyota 320, Lokaci Daya yana Zare Coat din Jikinsa Daga nesa ya latsa wani Abu Jikin Key din Motar Tayi wani kuka ta saki Light ta gaba da baya,Ya karisa Cikin Motan kenan yana kokarin Budewa ya Shiga yaji karan Bude Get kamar wanda akace ya waiwaya Da Sauri ya waiwaya yana kallon mai Shigowa.    Da Bala"in Gudun Data saba Shigowa ta Shigo Cikin Haraban Asibitin,Bata Tsaya ko"ina ba sai Gabda inda Dr Zain ke Tsaye yana kallonta Cikin mamaki,Cikin Abunda bai fi Sakwan goma ba ta gama Daidaitan Motan nata ta Bude Murfin Motan ta Sako Kafarta Waje. Wata Farar Kaface ta Fara Fitowa mai Dauke da Wani Ubansu Takalmi na kamfanin Gucci,baki Mai Tsini Wanda yake Dauke da igiyoyi,Ta Daursu Cikin kafarta Wacce Taji Karin Kumba,kuma Shafe da penti mai kalar pink,sai kafar ta kara kyau da ban Sha"awa barin ma Sarkan Gold din Dake Daure a Tsitsiyan kafanta na Hagu,Hannunta ne ya Fara Bayyana ana Biyu mai Dauke da Wata Waya mai Kalan Pink a Hannunta sai key din Motarta Shima mai Sakale da Key Holder kalan pink Daga gani dai ma mallakiyar motar mai son Abu pink ne Domin Data Bayyana Waje ma Wata Doguwar Riga ce mai Roba kalan pink ajikinta Ta kamfanin Armani sai Farar Rigar Likitanci Wacce ta Dora asaman Rigar ammh sakamakon Roba ce sai tabi Rigar ta lafe kowani Motsi na Jikinta ana iya gani Daga kusa. Farar mace ce Tas Ita bamai Tsawo ba kuma itama ba Gajera bace,Manyan Idanuwa gareta masu Dauke da gashin Ido Zara zara,Tana da Cikar gashin kai Domin ya Bayyana ta kasan Gyalen Rigarta Datayi Rolling Bisa kanta,Matsakaicin Bakinta mai Ban Sha"awa wanda yaji pinck Din Jam baki. *DR.DINA GADDAFI SHEERIF...* Kenan Farar mace alkyabban mata,Mace ce mai kyau da ilimi A kallan Farko in kayi mata zaka Fahimci Half cast ce Domim Mahaifiyarta Balarabiya ce,Ta gaji arziki gaba da Baya Domin Diya Take ga kwamishinan kudi na Jihar Kanon Dabon Alhaji Gaddafi Sheerif,Daga Fatarta zaka Fahimci Tana Cikin Jin Dadin Rayuwa,Daga yanayin Takunta Zaka Fahimci Idanuwanta Suna Budewa Tana da Tarin Wayewa Sosai Tunda tayi yawon kashashen Duniya Sosai Bayan Karatun Datayi a London achan ne ma Sanadin Haduwarta da Dr. Zain wanda Dalilinsa ne yasa ta Baro Gaban Iyayenta tazo Tana aiki Dashi a asibitin Dayake mallakin kakansa ba wai Domin bata da wajen da zatayi aiki ba,No Zata iya yin aiki adukkan Asibitin Kasar  Nageria a inda taga Dama sai dai kash Soyayyar Zain Acikin Jininta Take tagama Bashi Duka Rayuwarta Bata Jin Koda da Minti goma Rayuwarta da Numfashinta Yayi nesa Da nashi Tana son Ta kasance Dashi Har karshen Rayuwarta. Fara wani irin Taku tayi zuwa Gabansa Lokaci Daya Albarkatun Kirjinta Suna wani Girgiza Cikin karamar Rigar Likitocin Dake Jikinta Dayake wata Arniyar Dogowar Riga mai Roba ce ajikinta tabi ta kama ko"ina ta manne Shiyasa ta lafeta in Tana Tafiya ko"ina na Jikinta na Nunawa. Kafeta da ido yayi kamar yadda Itama ta kafeshi da idanuwanta Masu Cike da wani manadigido da da wani Sha"awa da Bariki yadda Kirjinta ke Shaking ne yasa Hankalinsa ya Tashi Ya kasa Dauke idanuwansa akai,sai da ta kariso gabansa ta saka key din Motarta ta kada mai akan Fuskarsa Tana Fadin'"HI....' Sai Lokacin ya Dawo Cikin Hayyacinsa ya wani yi Baya kamar zai Fadi da Sauri ta saka Hannu ta Riko Hannunshi Tana Fadin"Are u okey..?Tafada tana mai wani irin kallo bayan ta Sunkuyi mai Sosai kamshin Turaranta ya Daki Hancinsa Wanda ya kara Rikitashi ya Fita Daga Hayyacinsa Dama kuma Abunda Take muradi kenan Ya Fita Daga Hayyacinsa Wanda zai saka ya manta da kowa da komai sai ita kwara Daya Tak. Runtse Ido yayi kafin ya Bude Saurin Mikewa yayi yana Rabuwa da Hannunta Daga Rikon Datayi mai ganin mutane na Zirga zirga a Haraban Asibitin Jefi jefi Dukka suna parking Space baya so wani ya gansu ahaka yana da kima a idanuwan Mutane baya so wannan kimar ta Zube Gyara tsayuwa yayi yana kokuwa da Numfashinsa ganin yana Barazanan Daukewa Cikin wata Dashashiyar Murya yace"Am going Home Dina.U can meet Tomorrow Morning Firstlove is waiting For me.."! Yana Gama Fadar haka ya Juya Cikin Sassafar ya isa ga Motarsa ya saka Hannu ya Bude ya Shiga Ya zauna Da kallo Ta Bisa Galala Cikin Wani Irin Bakinciki da Kishi Tana kokarin Danne Abunda Taji yana Taso mata Daga kasan Ranta Jin Sunan Daya ambata FIRSTLOVE,wai da miye wannan yarinyar ta Fita ne..?me take bama Zain wanda bata bashi Da tafita matsayi awajensa...? Ganin yana neman Tada Motar nashi ne yasa ta Farga gudu Gudu Sauri sauri ta Nufi Motar nashi kamar walikiya ta Zagaya bangaran mai zaman banza ta Bude ta Shiga ta zauna Lokaci Daya tana Maida Kofar ta Rufe Cikin mamaki ya Dago Daga key din Dayake ma Motar nashi yana kallonta Baki Bude Cikin mamaki yace"What is dis Dina..! ? I tell u gida zani ko..? Cikin Daure Fuska Tana kallonsa Tace"Yes I want to Tok wit u Zain...! Tafada kai Tsaye tana Sakarmai Bayan idanuwanta masu kashe mai Jiki Saurin kauda kai yayi zai yi mgana ta katseshi da Fadin"Juz 10minite plz..Dr..! Tafada Cikin karya Wuya Lokaci Daya Tana Dafa Hannunsa Dake kan Cinyarsa wani Iri yaji yayi Saurin Janye Hannunsa yana Fadin"Ok..Go ahead..!. Yafada Yana Kokarin kauda kai Bayaso Taci galaba akanshi kamar yadda ta saba gashi kuma yayi ma kansa alkawarin bazai kara aikata Laifinsa na Baya ba Wato ZINA da Auransa ba. Ganin yadda ya kauda kai ne ya sakata Dariya ta Murmusa Tana Fadin"Why kake neman gujema Dina Dr Zain..? Ta fada Cikin Wata Murya mai Cike da Sha"'awa juyowa yayi yana kallonta Cikin Ido Itama Shi Take kallo Lokaci Daya tana Wani Bude baki Tana Rufewa kamar wata sakarya Miyau ya Hadiye yana Jin reaction Dinsa na Mikewa Cikin Wandonsa ammh sai yayi Saurin Dannenta idanuwansa ya kauda akanta yana Fadin"No..Dina plz ki bar wannan mganar na Fada miki Firs...! Bata Bari ya karisa ba tayi Caraf ta Hade bakinsu Waje Daya Tana Kissing Dinsa in a Romantic Way,Kansa Ta Rike da Hade keyansa Tana kara manne Bakinsa Cikin nata Lokaci Daya kuma tana mai Sosa acikin Gashin kansa nan da nan ya Rasa Natsuwarsa Duk kokarinsa na Son kauce ma Daina ya kasa Shima Hannun yasa ya Dafo kanta,Da Dayan Hannunsa Dayan Hannun kuma ya Dafe bayanta wanda ya bata iko yin Tsalle Daga kujeran Datake Zuwa Kan Cinyar Zain Bakinsu na Hade suna Cigaban da Kissing Din Juna kamar zasu Cinye kansu hankalinsu kwance Tinda Motar Tintek ne ko"ina yana Lullube ne. Sun Shafe wajen Minti goma Acikin Wannan Halin kafin Dina ta Fara Janye bakinta Tana sakin Numfashi sama sama Shi kanshi Zain Baya yayi da kansa ya Jingina da kujeran Motan yana Sauke Numfashi Idanuwansa sun kala Sunyi Jajir saboda Jaraba Cikin Wani irin yanayin kallo yake jifan Dina ita kuwa ganin Haka sai ta Saka Hannu Tana Shafa Kirjinsa Lokaci Daya Tana Fadin"I NEED U ON BED ZAIN...! Tafada kai Tsaye tana Sakarmai Idanuwanta Da Suka kankance Kokarin yunkurawa yake ta kara Danne Kugunta Wajen Sandar Girmansa,jin Tana kunnosa yasa ya Furta"Stop it Dina..Gida zani Firstlove tana Jira...n."Shiii...! Bata bari ya karisa ba,ta sakamai Yatsanta a baki Tana yawo Dashi Lokaci Daya Tana Fadin"Plz Don"t Say No Zain...Is not going to Take long Time Juz 20m...! Tafada tana Wani Shafa Sajensa Cikin Wani Salo. Kallonta yake cikin Wani yanayin ganin yana kokarin mgana yasa ta kwantomai Nonuwanta suka Daki Kirjinsa Tana Fadin"Plz...Please...!Take Fada tana gaba da baya akan Cinyarsa kamar wacce take Kokarin Tashi ta kasan nan kuwa tasan Abunda take yi,Shi kuwa Zain Jin Sha"awarsa takai Kololuwar tashi ga Sandar girmansa Ta tashi kamar zata Fasa Wando Ita Dina kema wannan Gaba da baya,Domin Tafi kowacce mace Sanin Lagon Zain Din Har kuwa da wacce yabani matsayi Fiye da ita Wato Firstlove din nasa. Cikin Shakakkiyar murya yace"Ok..Ammh ba amotan nan ba ko..? Muje Office dina.."Cikim Kiss tace"Why..? Plz u can do it here Zain..Zai fi Dadi da Romantic.."Hararanta yayi yana Mikewa da Karfi Tayi Saurin Kwatomai ajiki Tana Fadin"Ohhwayyo.."Cikin Wani Salo,Tureta yayi Gefe yana gyara Zaman Rigansa Data yamutse Coat dinsa kuma Dama abayan Mota ya Wurgata Kallonta yayi yana Fadin"Meet me in my Office Now..! Daga haka ya Bude Murfin Motan ya Fice Da Sauri yana Gyara Wandonsa lokaci Daya kuma yana kai Duba ga Haraban aaibitin Domin yana Son Mutumta Mutumtakansa Baya so yayi Abunda kimar Gidansu data iyayensa Zata Zube ganin ba wanda yake ankare dashi yasa ya Fito Daga parking Space Din ya Nufi Cikin Asibitin da Sassarfa. Mirmishim Keta ta saki kafin ta Rarumi key din Motar da wayarta Ta Daya Fadi kasa,Bakinta ta Duba amudubin Mota Taga Duka Zain ya Shanyen Jan Bakin Data saka wani Munafukin Mirmishi takarayi kafin ta Bude murfin Motan ta Fito Lokaci Daya tana Rike aKugunta Tana Fadin"Choooo...So So Sorry HALIMATU DIYAR MEGADI YAR MAI AIKATAU....yau ma Dr Zain is Under my Control Sai kiciga da Jiransa.."Daga haka ta saki Wata Irin Siririyar Dariya kafin ta Kada key din Motarta tabi Bayansa Cikin wani irin Takun Gogaggun mata wadanda suka san kan Duniya. Bata tsaya bata Lokaci ba Sama sama take Dagama Ma"aikatan Asibitin da Nurse din Dake gaisheta Hannu Allah Allah take ta karisa Office din Dr. Zain Kada wannan Dan Anacen ya Fito ya ganta sai dai Addu"arta bata Ciba Kamar Daga sama Taji muryansa"Dr.Dina..." Cak taTsaya Cikin wani Takaichi ammh bata waigo ba Cikin Sauri ya kariso gareta Lokaci Daya Yana Fadin"Yana ga kin Dawo... .?Bayan Dazu kince min zaki Fita..? Ya Fada yana son leken Fuskarta Cikin Jin Haushi ta Waigo Tana Fadin"Why Dr.Imran...? Fitata da kuma Shigowata Cikin Asibitinnan Duk akan idonka ne Am i Ur Wife..? Haba Takuran naka Is Over me Wlh Ban so Wlh.."Tafada tana wani yarfa Hannu. Kyakyawan Fuskarta yake kallo Yana Jin wani iri acikin Ransa Meyasa Dina take mai Wulakanci ne... ? Ita kuwa Karamin Tsski Taja tana Juyawa Lokaci Daya ta kadamai Manyan mazaunanta Ta wuce ta barshi nan da kallo ya Bita yana Wani Hadiyan yawu Harda Lashe baki kamar wani maye ya kada kai yana Fadin"Allah yakai Damo ga harawa ko bai ci ba yayi Birgima akai.."Daga Haka ya Juya yana Juyawa suka Hada Ido Hudu da Dr.peter Wanda yake ta Dariya yana ganin haka ya Hade rai ya wuce yana Fadin"Wai Su cin Danko Harda su kaza..Sa"ido ma Harda Arna Mtseww Allah ya kyauta.." Ya wuce Fuu kamar Shima zai Tashi sama Nurses din Dake Zirga Zirga awajen kowacce Taitayinta Ta Shiga sanin Halin Dr.Imran Masifaffan ne na Bala"i Asibiti ba Asibitin Ubansa ba sai iko Daga Cin Arziki Har gwarama Dr.Zain in yayi wannan da Hujja tunda Asibitin a Sali na Kakansa ne ammh Shi fa,sai Iskanci shi ba kowan kowa ba,Ammh fa iya masifar ya tsaya in yaga Wata Nurse tamai yakan Taya in ta bada Hadin kai ana Hutawa Sosai ba Ruwansa ko Bunsuru ya shafamai lafiya wajen cin mata. Knooking ta Farayi Cikin Muryansa wacce tayi kasa Taji ance "Come in plz.."Saboda yasan Itace Domin adaidai Wannan Lokaci Doka ne bamai Shigomai Office kai Tsaye sai Mutum Daya Abokinsa kuma Amininsa Kuma Dan"uwansa wato DR HADDIR ALIYU ABUBAKAR SAULAWA. Cikin Wani Taku ta Tura Kofar ta Shiga yana Tsaye ko zama ya kasa tana Shigowa ya Dago da Idanuwansa da suka Zama Jajir saboda Jaraba Cikin Laushi da kuma Muradi yace"Plz Key d Door.."Ya fada yana Wucewa Dircet Cikin Wani Daki dake Cikin makeken Office Dinsa da Sauri Tabi Umarninsa ta saka Makulli ta Rufe Office din ta Bar key din Ajiki itama ta Rufamai Baya tana Shiga ta ganshi ya Juyamata Baya yana Tsaye ganin Haka yasa Tundaga nan ta Fara Cire Farar lapcoat Din Dake Jikinta kana ta Tube Karamin Vail din Data Yane kanta,Kamar al'amara ta Sabule Doguwar Rigar Jikinta sai gata Naked dinta Haihuwar Uwarta Tana Tsaye tana wani munafukin Mirmishi. Nufarsa Tayi sai dai yaji ta Rumgumeshi ta Baya Tana Shafa Kirjinsa Cikin wani Shauki Runtse ido yayi yana Jinta ta Zagayo ta gabansa Tana Balle mai Botorin Farar Rigar Dake Jikinsa Sai da ta Ciremai kana ya Bude Idanuwansa akanta yana kallonta,Nonuwanta ne da Suke Tsaye Cur Cur suna wani kadawa,saboda yadda Take kokarin Rabashi da wandon Jikinsa,Ta ciremai Dogon wandom Ta Cillar gefe Tana kokarin Sabule mai Boxers din Jikinsa ya Damke Hannunta Da Sauri Ta kalleshi Tana Fadin"Why..? Kauda Kai yayi batare da yayi mata mgana ba kawai Ya Dagata sama sai kan wani karamin Gadon Dake Dakin,wamda na Duba marasa Lafiyane,Akwai guda Daya Daga Chan Falon,wannan na yan Family ne in Laluran kwantarwa ta kama, Yana Sauketa kan gadon ya Bita ya Danne Lokaci Daya yana Hade bakinsu waje Daya Cikin wani Irin Shauki itama Ta Damke Kansa Suna Kissing Din Juna kamar zasu Cinye bakin juna,lokaci Daya Hannayensu na kara kaina ajikin Juna. ***** *Area: Federal lowcost* Agogon Bangon Dake Falon nata takai Duba Taga karfe 10:30pm na Dare,karamin Tsaki Taja sau ba Adadi Tana Cigaba da Kiran Layin Firstlove,Ammh kuma Still Wayar nata Ringing Ba"a Daga ba Ranta ya kara Baci kamar ta saki kuka. Falon tabi da kallo Tana ganin irin yadda ta kawatashi Dinning Table din Data kawatashi da Abinci kala kala da kuma wani katon Cake takai ma kallo Yau gabadaya wuni Tayi Wajen ganin ta Shirya First Birthday Din Zain, ko Sch ta kasa Shiga Duk da kuwa Suna da lectures,Bayan Sunyi Aure wannan ne First Birthday  dnsa suna matsayin ma'aurata Tana so Tayi Supresing dinsa,ammh kuma Ta rasa meyasa Wani Lokacin Firstlove yake kaiwa Dare acikin Asibiti,Duk da Tasan Yanayin aikinsa ammh ai alkwai Tarin likitoci acikin Asibitin kuma in ba wani Emergency ba bai Cika kwanan Asibiti ba. Zagaye Madaidaicin Falon nata ta Dinga yi Rigar Jikinta tana jan kasa Irin gown din nan ne mara Hannu wacce sama Take da Raga Raga,Rigar ta Dameta Sosai Tayi mata kyau kanta yasha Gyara Gashinta ta Daureshi a Tsakiyar kanta tayi wani Tufka Fuskarta tasha kwalliya Duk da bamai yawa bane. Doguwar mace ce mai madaidaicin Jiki,Tana da Manyan Idanuwa da matsakaicin Hancinta dirarriyar mace ce Ta gabanta da Bayanta ba Fara bace Chaculate Colour ce ko kuma mu kirata da Bakar mace Jin Dadi da kuma Hutu suka saka Fatar ta Murje tayi kyau sosai Matashiyar ce yar kimanin Shekaru Ashirin a Duniya. *HALIMATU ABDULLAHI GADA* Wacce Aka fi Sani Da _ZAINA.._ Wasu kuma suna Kiranta da *ZAINAZAIN..*!Kenan mace ce wacce takai mace kuma Wacce Namiji zai yi alfaharin mallakarta amatsayin matarsa ta Aure akallon Farko in kayi mata zaka Hangi Tsantsan Natsuwarta da Hankalinta Tana da Tarin baiwa,Tana da Cika ido da kwarjini,Halima tana da Rauni Gata da Saurin yarda Tana da Rikon Amana uwa uba Ladabi da Biyayyah Tana da Sadaukarwa ga wanda Suke tare,gata da Tarin Bama kowa yarda arayuwarta Domin Tataso Tun Tana Karamarta marainiya ta Bangaran Uwa da Uba,Bata tashi Gaban Duka Ahalinta na Both Uwa da Uba ba,Ammh Tatashi Hannun Uwar Rikonta Hajiya Aisha Wato Umman Zareena da kuma Uban Rikonta Alhaji Usman Abubakar Saulawa shiyasa Duk Duniya bayan su Da Alhaji Tsoho Ko Dangin iyayenta bata yarda dasu ba kamar yadda Taayarda Ta bama Zain Ragamar rayuwarta gabadaya. Komawa Tayi ta Zauna kawai Saman Daya Daga Cikin Royal Chairs Din da sukayi ma Falon kwanya Ganin bata da wata mafita ammh Idanuwanta na kan agogo Hankalinta kuma na kan wayarta Rabi kuma yana Haraban Gidan tana Sauraran Hon da kuma Shigowar Mota,Ammh Shuru har 11pm ta Buga tana Zaune Bashi da Dalilinsa Idanuwanta Suka kawo kwallah meyasa Duk sadda Ta Shirya wani Abu Special ga Mijinta sai komai ya Lalace Wayarta ta kara Daukowa ta Cigaba da Kiransa ammh bai Daga ba. Hawayen Data ke kokarin Dannewa ne suka Zubomata Bata yi Yunkurin Sharesu ba ta barsu Suna Zuba,Wata Zuciyar tana Cema ta"Easy Halima Kila Wani Emergency ne ya Taso...! Jin Haka yasa Ta Saki ajiyar Zuciya kafin ta Dauki Wayarta Ta Fara Neman Layin Umma Har ta yi Dialing Sai Wata Zuciyar ta Hanata da Sauri ta katse afili ta Furta"11 na Dare nasan yanzu Umma ta kwanta zan Tayar musu da Hankali toh ko na Kira Nene ce..? Sai kuma ta Girgiza kai Tana Fadin"A"a baya Gida Domin Abba bazai barshi yakai Har uwar haka achan ba..! To ko yana Gidan Alhaji Tsoho ne..? Tsai da Rai Tayi tana wani Tunani kafin ta Girgiza kanta Tana Fadin"Me zai sa ya Dade haka in ba wani abu bane ya Faru..! Kuma ya gayamim ya Fito Daga asibiti zai Taho gida kodai accident yayi..'"Fadin Haka yasa gabanta ya yanke ya Fadi nan da nan Jikinta ya Fara Rawa Cikin Tashin Hankali Take Fadin"No...No He is Fine...InshaaAllahu Babu Abunda zai sameka Firstlove.."Take Fada ita kadai kamar Wata zararriya. Tunanin Kiran yaya Haddir ne Ya Fado mata acikin arai da Sauri Ta Fara neman layinsa Tana Fadin"Am Sure yasan inda Firstlove yake.."Lambarsa ta nemo Tayi Dailing Ta Fara Ringing ta kara kunni kowani Di..! Di! Yana Tafiya ne da Bugun zuciyarta. "ZAINA Lafiya kuwa..? Taji Haddir  Yafada bayan ya Daga Kiran nata Datake gab da katsewa yana Hamma Cikin Sauri Halimatu tace"Ya Haddir Am sorry na Tasheka ko... ? Dama zan tambayeka ne Kana asibiti ne..? Munyi waya da Ya Zain Tundazu zai zo gida naji Shuru Har yanzu kuma ina Kiran wayarsa Baya Dauka.."? Cikin Yanayin Barci yace"Halimatu ki kwanta kiyi Barci kila wani Emergency ya Tsaidashi Ni yanzu ina Gida Tun Around 6pm  na yammah na Baro Asibiti naje Gidan Alhaji Tsoho na Dubashi Jiya yace min ya kwana da Mura.."Cikin karaya Halimatu tace"Ayyah..Allah Sarki Alhaji Tsoho how is he Doing now..? Hop da Sauki ko..? Daga Chan Bangaran Haddir yace"Yes ..he is Feeling much Bette now..Na barosu Shi da Tsohuwar matarsa Hajiya mama Tana Jinyarsa Zata Dafamai kaza Queen.."Yafada yana yar Dariya Mirmishi ta saki kafin tace"May Allah Shifa Him.Ameen gobe in na tashi Daga Sch zan Biya na Dubashi.."Haddir yace"Ameen..Ok Allah ya kaimu karki Damu zai dawo kila Wani Abun ne ya Tsaidashi kinsan yanayin aikin namu.."Cikin Dauriya tace' Shikenan Gud Nigt Yaya Haddir.."Night kawai yace mata ya Datse kiran Lokaci Daya yana Komawa ya kwanta ammh acikin Zuciyarsa yana Tur da Hali irin Halin Zain Ya Tabbata ba kowa ya Tsaidashi ba sai Wannan Karuwar yarinyar nan Dr.Dina duk da yana Musanta Zargin Dayake yi akansu ammh He is Very Sure Akalar Dake tsskaninsu bata alheri bane Tun Suna karatu a London Da kuma Gayyatar da Zain din ya aika mata Natazo Suyi aiki a asibitin Kakansa tare, kuma ba Musu tazo Duk da kuwa Zata iya yin aiki a ako"ina  a kuma Duk inda take so kuma tun ba yanzu ba yasan Dinar son Zain take shine dai yake wani pretending ammh kallonsu kawai yake yana Fatan Allah yasa ba Abunda Zain yayi mai alkawarin ya Daina bane na Neman matan Daya koyo Daga kasashen Turawa yake koma Sunayi da Dina ba Domin in Hakan ta Faru Kokarin sa na Rufama Dan"uwansa kuma abokinsa Asiri zai iya Fasuwa Har wadanda bai kamata su ji ba, zasu Ji Abubuwa su zo su Rikice Yadda kowa ke kallonsa da Kima Harda kuwa iyayensu Uwa uba kuma Alhaji Tsoho Daya bama Zain Din Dukkan Ammana Da yarda Da kuma Marainiya Data Kwashi Yardanta da Duka Amanarta ta mikama Zain din. _Ya kuka ji Salon Labarin..? Wannan karon Tafiyar mai Dogon Zango ne Ni kaina zan iya Rantse muku Wlh Tun bayan Littafin Uwar Mijina ban kara Yin wani labari kamar wannan ba,Labari ne Daya Tsaru kuma ya Sarrafu,Labari ne Da zai Tabo bangaran Tsantsan kauna da Soyayyah,yarda da juna,cin Amana Rauni Tsausayi,Halin kaka kani,Gararin Rayuwa Dama Abubuwa Dadama Labarin zai zo Kashi1 da kuma Kashi 2 Fata zaku yi jimarin Bina Tundaga Farko Har karshensa Ku ijiye Comment din ku da Like din ku,Vote kuma kuyi Sharing dinsa ya kai inda ya kamata Ni kuma Kusan ni kun gwada kun gani bazam Taba baku kunya ba Wajen yi muku Upadate akai akai insha Allahu Nagode Allah ya jikan iyayanmu..._ *Intelligent Writer"s asso..* *Janafty...* *04/06/2021* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Jum2f8sNNmx9HXBUvqPmsl *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1* _In mutum yasan yana Band1 plz kada ya shiga Band2 na Budeshi ne saboda wadanda Basu samu Shiga Band1 ba,And kuma in kinsan zaki shiga ki Fita ne U better stay where u are Hajiya Allah ya gafartama iyayenmu Ameen._            0️⃣2️⃣ "Duk kokarinta so Take sai sun koma Around 4 kamar a mafarki yaji Ringing Din wayarsa Duk yadda Dina Take kokarin Daukemai Hankali wannan karon bata Ci nasara ba,tana samansa ne ya Birkitata gefe ya Dira Daga kan Gadon Lokaci Daya ya Dauki Gajeren wandonsa ya Saka ya Isa wajen Wandonsa Dake yashe a kasa ya Dauko ya Zira Hannu Cikin aljihun ya Fiddo da Wayarsa ya Danna Waro Ido Yayi Lokaci Daya yana Fadin. "Innalillahi...30missedcall From Firstlove.."Yafada yana Dafe kansa Lokaci Daya kuma yana kokarin Zira Wandonsa Cikin Hanzari kamar kuma wani wanda ya Rasa Natsuwarsa yana gama  sakawa ya Waigo yana Kallon Dina yana Fadin"Ke park ur Self..."ya fada yana kallonta ido Cikin ido kafin ya kauda kai ganin yadda take binsa da wani irin kallo Lokaci Daya Tana Shafa Nipple dinta Da Hannunta guda Daya. Daga haka ya Shige Toilet Din Dake Dakin,lokaci Daya yana kara Duba wayarsa Da kallo Ta bishi Har ya Shige kafin ta saki karamin Tsaki Tana Fadin"Firstlove Dai...Firstlove dai...I hate dat Name...I Hate u Halima I Hate u Zainah..Kina Tarayya Dani kan Abunda nafi so Duk Duniya Dalilinki Zain yakasa zama nawa Har yau har gobe yake bani Wahala na Tsaneki.."Tafada da karfi kamar wata mahaukaciya. Da Hanzari ya Fito Daga Tiolet din Bayan Shudewar wasu mintuna da basu gaza Goma ba, Kansa Duk Ruwa alamun Dai wanka yayi ko Ta kanta bai bi ya Jawo Rigarsa ya saka Lokaci Daya kuma yana Tsane kansa da karamin Towel din Dake Hannunsa ita kuma mikewa tayi ta Fara Zira rigarta Domin tasan Ko Giwan wake tasha bazai barta ta Shigarmai Bayi Tayi wanka ba. "Wai duk wannan Rawan Jikin  Daka keyi kan Haliman kake yi..?.Tafada kai Tsaye tana kallonshi bayan tagama saka Duka kayanta yana Saka Botirin Rigarsa yace"Ba Ruwanki Dina Tom.."Yafada Cikin muryan Natsuwa.. Cikin Jin Haushi Tace "Da Ruwana Zain..Kullim mganar ka Dayane Firstlove..Zainah..Halimatu Wai Shin Miye Halimar ke baka wanda bana bakashi anan Duniyan..? Me ta ke Dashi wanda bani  Dashi..?kudi..! Ilimi..?Dukiya ko asali mai kyau..? Ina ce na Fita komai infact ma ai bazaka Hadani da Diyar MEGADI YAR MAI AIKATAU KUMAJ JIKAR MEGAD..." "Enough DINA...! Ya katseta Cikin Wani Tsawa Dakawata Tayi Tana Sauke Numfashin Kishi da Bacin Rai Cikin Nunata da yatsa yace"kar ki Kara kuskura  Fadin Irin wadanan mganganun kan Firstlove dita...Bata Fiko komai ba Dina Abu Daya ta Fiki ta kuma yi miki Zarra NIKKA..HalimaTU matatace ta Sunna Wacce Mala"iku Allah ya saka Suka Daurama Aure Tun Ranar Datazo Duniya Am Her Firstlove itama She is my Firstlove Kuma I Love her So much Domin da wannan Hannayen nawa ni na Fara Tarban Halima Bayan tazo Duniya kinga kuwa kuna da Tazara mai yawa.."baki Bude kawai Take kallonsa Bata samu Zarafin mgana ya nuna ta da yatsa yana Fadin"So u better Be Carefully ki daina Hada kanki da Matata in kina son Cigaba da alaqa dani.." "Ammh Zain u Know i Love u ko...?kai tsaye yace mata,"Yes i know..Ke kuma kin Riga kin sani Tun Ranar da muka Fara Haduwa na Fada miki anan Duniya mace Daya kawai nake so kuma Itace HALIMATU my Zainah...Zainah zaina Sauran mata kawai kwadayinsu nake ji bawai so ba.."Cikin Hargagi tace"Kana kwadayinsu kuma baka son su..?Karya kake Zain Sai dai indon Ita Haliman Fanko ce Salam ce Rijiya ce baka Jin Dadin.." "ke are u mad....?Ina Ruwanki da ina Jin Dadinta ko ba na ji..? Dis is Stupit karki kara sako matata Cikin iskancinki Halimatu is Special ,unique wanda Samunta Cikin mata Sai Antona ki daina mganar Dadi Ita Tana sani Ihu To The Top Tundaga Farkon Dare Har karshensa kefa..? U Only Sex me ammh Ko Groming bana yi Cos baki iya komai ba sai Jarab...! "YA ISA ZAIN..!Ta fada Cikin Bakinciki Lokaci Daya kuka na kwace mata Cikin kukan Take Fadin"In bani da Dadi kamar Halima meyasa Baka tsaya mata ita kadai ba..?Karka manta koda muka Hadu daman chan kana Harka da mata in ka manta bari na Tuna maka da bakinka ka Fadamin ba nice mace ta Farko da ka fara Sex dani ba Kayi Hulda da matan Turawa sosai kafin ni..! Cikin kular da ita yace "Yes Of course...Aurena da Halima Wannan kuma bai Shafeki ba Tarayyana da mata Ma bai Shafeki ba,i know abaya nayi Harka da mata ammh by now ke kanki kinsan bana Harka da kowacce mace sai ke..Ke din ma ina iya bakin kokarin yakice Bansan Dalili ba sai kina Maidani Ruwa.. Mganar Matata kuma ba Ruwanki da ita Dole Duk inda Dr.Zain yake ya ambaci Halimatu,Firstlove  So in kinga Bazaki iya juran ji  ba Dina d Door is open Dama kawai Manegi nake yi Dake Har ga Allah nagaji da alaqa da ke ke kanki kin sani.! Yafada Kallonta ido Cikin Ido Hawayenta suka Zubo Daga Cikin Idanuwanta Cikin yanayin karaya da Muradi mai Girma take Fadin"Ni kaina nagaji da wannan Shashancin da muke yi a waje Juz Marry me Zain zamu fi samun Natsuwa..! Ido ya kwalalo waje yana Fadin"M...Merry me fa kika ce Dina..? Yafada yana kallonta kafin ya saki wata karamar Dariya yana Fadin"U are not Serious?...Ni na taba ce miki zan Aure ki ne Dina..? Ya tambayeta yana kallonta Kai ta Girgiza kafin tace"Baka Ce ba..Ammh ka hanani kula kowa ko..? Kuma infact ma kai ka amshi Virgin dina Kana nufin zan je ma wani ahaka ne bayan komai kai ka karba..? Kai ma kasan bazai sabu ba Zain Dole ka Aureni ko kana so baka So..."Dariya ma ta bashi ya Murmusa yana Fadin"Ji wata mganar Banza..! Yes ban musa ba ni na karbi Virgin dinki ammh Do i Force u..? Ta karfi nayi miki..? Ko Fyade nayi miki..? Dafa karfarki kika kawo kanki na Taya ba Gardama ki kayi accpted Shine nayi laifi..? U Better Wakeup Daga wannan mafarkin naki Dina Am Not Going To marry u Dazs is d Truth...! Kai Tsaye ta kalleshi Tana Fadin"Karya kake Zain...Ina Sonka ina Matukar kaunar...Kuma am Very Sure sai ka Aure ni ko Ta lalama ko ta Tsiya Ban damu da Duk Abunda zai Faru ba Nidai Burina ka kasance nawa na Har Abada..! Baki bude yace"Really..? Dina me kike shirin yi..? Kinsan Allah karki sake kice zaki Fasa wannan alaqan tamu ga wani ahali...! Bai karisa ba ta barmai Dakin Fuu tana Tsiyayan kwallah da kallon Dariyan Tura Haushi ya Bita kafin ya Dauki Key Din Motansa ta yabi bayanta. Yana Fitowa Daga Office Dinsa Suka Ci Karo Da Dr Peter wanda yayi mai wani kallo Domin yaga Fitiwar Dina ba Tun yanzu ba Yasha Zargin akwai wani Abun da ke gudana Tsakanin Dr Zain da Dr.Dina Ammh bai Taba Fadama kowa ba Yana kokarin yi ma Dr.Zain din mgana kawai ya Wuceshi batare da ko Sannu yace mai kuma ya Tabbata ya ganshi da kallo ya bishi kafin ya Kada kai yana Barin wajen Yana kawowa Haraban Asibitim Yaga Ficewar Motar Dina Da Gudu ko Ta kanta bai bi ba ya Fada Motarsa ya Bata Wuta yayi Kwana Tare da Zuba Hon aka wangalemai get ya Sulale ya Fice Daidai Lokacin Daya Duba agogon wayarsa 12:00am na Dare,adaidai na Ranar Laraba kuma Lokacin Sako Ya Shigo wayarsa Daga Firstlove. Da Sauri ya koma Driving da Hannu Daya ya Bude Sakon.. *HAPPY BIRTHDAY FIRSTLOVE...* Waro ido yayi sai alokacin ya Tuna da Birthday Dinsa na Cika Shekara Talatin aduniya Allah Sarki Halimatu baiwar Allah Zainahzain kenan Bata iya manta Duk wani Abu Daya Shafeshi Tana sonshi da Duk Zuciyarta da Ruhinta ta gama yarda Dashi 100%ammh shi kuma yana nan yana cin Amanarta Sau Tari yana kokarin yakice wannan neman mantan  ya samu ya yakice Neman Sauran wasu matan Tun bayan Haduwarasu da Dina ya Rasa Wani irin Abu ne ke Tsakaninsa da  Dina koda yayi alkawari wa kansa Da bazai kara kusantanta ba  sai matarsa ba Baya iyawa Jikinsa Har rawa yake musamman in yaga Dina,Kamar Tuwo Haka yake mata Ko Halima baya mata Cingam Din Dayake ma Dina kuma yana da yakinim Garau garau kawai yake Ci Jan Miya mai Dadi sai Wajen Halima,Yayi kokarin Rabuwa da Dina sau ba Adadi ammh kuma Abun ya Faskara Saboda tana Barazan da zata Fasa alaqarsu ga Ahalinsa da matarsa Abunda kuma baya Fatan ya Faru kenan Ya Tuna Nasihan Dan"uwansa Haddir kullum itace Zain ka Daina kusantan kanka da Zina,Ita Din Haramin ce kuma tana Cinye Duka ayyukan Alheri..Allah Sarki yasan yana Nenan mata ammh bai taba Fadama kowa Daga Cikin Ahalinsu ba sai ma Kokarin Dayayi ya Rufamai asiri yana so ya Daina yana son yakice Dina ammh kuma Tana neman ta zama Wata Bakar kaddara gareshi...! ******* Motar ya saki Sosai yana Sharara Gudu Bisa Titin Garin na Bauchi sakamakon Dare yayi Kafafu da kuma Zirga Zirgan Abun Hawa yaja baya sai ya bashi Daman Zuba Gudunsa Sosai Yadda yake so Cikin lokaci kalilan sai gashi ya iso Federal Lowcost. Bakin wani Tagamemen Gida ya Tsaya yana Zuba Hon Get din Gidan kalan Golden ne,Hakama Fentin Gidan kalansa kenan yana Tashin kyalli Dayake akwai Wuta kuma Akwai Wadatar manya kwayayan Wuta awajen sai Wajen ya kasance Cikin Haske ba Duhu ba. Hon yake ta saki ammh Shuru Tanimu megadi bai zo ya Bude mai Get ba karamin Tsaki yaja afili ya Furta.."Yanzu haka Tanimu na chan yana Shegen Barcinsa na Fama.."Yafada Lokaci Daya yana kokarin Bude Murfin Motan ya Fito sai ga Tanimu ya Bude karamar Kofa ya Leko yana Mitsike ido kamar mara Gaskiya Ganin Motar Zain yasa Ya washe baki ya koma da Sauri ya Wangalemai get Din Kara Sakin Saki Zain yayi kafin ya Sulala da Motarsa Zuwa Cikin Gidan. Aparking Space ya Adana Tashi Motar Gefen motar Halima Kirar piagion 607,kashe Motar yayi ya Fito Lokaci Daya yana Bude bangaran baya ya Dauko Caot Dinsa Hannunsa Rike da Wayarsa ya Latsa wani Abu jikin Key din Motar tashi Sai gashi Lokaci Daya Motar ta kulle kanta Hanyar da zai Sadashi da Falon Gidan ya Nufa Cikin Takunsa na Natsuwa da Cikar kamala in ka ganshi alokaci aka gayamaka Yana aikata Wani Zunubi mai girma zaka Rantse kace karya ne Domin afuska Zain yana da Baiwar Cikar kamala da Mutuntaka.. Tanimu megadi ne ya Tareshi Wanda ya zo da Sauri yana Fadin"Allah ya Taimaki Likitan Bokan Turai..An Buga Dakai an Barka..Gaban ka Arziki bayan ka Arziki kai dan na Gada ne ba Dan na Haya ba Kakan Ma Likita ne,Ka gaji Abun ne ba Haya kayi ba Kaga Dogon Likita Angon Gimbiya Halimatu barka da Dawowa Ranka ya Dade..! Yake Fada yana Jinjina mai Hannu mirmishi ya saki kawai Sanin Halin Tanimu maigadi mutun ne mai barkwanci ba wani Babba bane Domin ko zai Girmi Zain Din da kadan ne Kallonsa yayi yana Fadin"Kai dai baka Baro da Shirme Tanimu.Anya zaka iya gadin nan kuwa Ace kana gadi ammh baka da aiki sai barci.? Yafada yana kallonsa Sosa kai Tanimu megadi ya Fara yana Fadin"Allah ya Taimaki Dakta Wlh Kaga chan kan wanchan karamar kujeran kai nake Zaune ina Sauraran Radio na Shuru Shuru ban ji Dawowarka nace kila yau Dakta dai aiki ya Rikeshi kasan aikin jama"a Nidai Tun ina Sauraran Dawowarka Har barci ya Fara Dibana ban sani ba Chan sama sama naji Hon Dinka Yallabai kamun afuwa..! Ya Karishe Fada yana Sunne kai kai kawai Zain ya kada yana Fadin"Allah ya kyauta...Koma ka kulle get din kaje ka Kwanta Kada gobe ma nazo Fita kaje ka Tsaya Jirana Daganan barci ya kwasheka..'Kasa Tanimu yayi Dakai yana Fadin"Wani kaya sai amale..Wane ni Dakta Allah ya Tashemu lafiya a gaida Gimbiya Halimatus Sa"adiya.."Daga Haka Kawai Zain ya Cigaba da Tafiya yana Dan Mirmishi Tanimu megadi kuma ya Rakashi da Kirarin Dayake mai kowani Lokaci Wanda Har ya zame ma Daktan Jiki. Da Sallama Lokaci Daya kuma ya Tura Kofar Falon ya Shiga,Cak ya Tsaya yana Bin Ko"ina na Falon da kallo ganin yadda Halima ta kawata komai da Baloons,Dinning Area ya kai Duba yaga yadda ta kawatashi Barin ma katon Cake din Dake wajen bai yi mamaki ba Sanin Tun Suna Gida Ita da Zafeera Sunyi Catering And Snaks School Lokacin yana London Sunsha yin Vidoe call Da Halima in tana Chan kayan Docaration kuma ya Tuna Shekaranjiya Ta kirashi yana Office tace Daga School zata Shiga kasuwa Kamar ya Tambayeta me zata Siyo sai kuma ya Fasa Daya Dawo kuma ya manta Shiyasa bai mata Tadin ba. Kallonsa ya Sauke kanta Wacce Barci ya Bingiran da ita saman Kujeran Data ke kai ga Waya ta Damke a Hannunta Cikin Takunsa na Natsuwa ya Fara Taku Zuwa gareta Lokaci Daya kuma yana Kafeta da ido Har sai da ya karisa kusa da ita Kallonta yake daga sama Har kasa Wani Tsausayinta na Cikamai Zuciya Allah Sarki Ashe Duk kiran Datamai na ya Dawo Gida,Saboda Birthday Dinsa ne,Tayi komai saboda shi Tayi kwalliya Saboda shi ammh Har tayi barci bai Dawo ba anya yana yima Halima Adalci kuwa..? Coat Din Hannunsa ya ijiye Hade da Wayarsa da makullin Motarsa,Ya isa ga Halima ya Zauna agefenta Lokaci Daya yana Shafa Fuskarta Har Zuwa Lebenta Cikin Wani yanayi kamar acikim Barci Taji kamshin Turaransa Ta Bude ido da Sauri Sai ta Saukeshi akansa Kura mai ido Tayi Tana kallonsa Shima kallonsa yake yi ganin Haka yasa ya Damke Hannuuwanta yana Fadin"Am Really Sorry Firstlove...Wlh..." "Shiiii...."Tace Lokaci Daya tana Saka yatsanta ta Danne bakinsa Kafin ta yunkura ta mike Hannunta Guda Daya yana Cikin Nashi Cikin Muryan Barci da kulawa tace"No need to say Sorry Firstlove...Nagode ma Allah Tunda ka Dawo lafiya Wannan kadai ya isheni Farinciki.." Tafada tana Sakarmai Mirmishi Wani Irin Sanyi yaji acikin Jikinsa kawai sai ya Sulale ajikinta ya Rumgumeta Itama Rumgumensa Tayi suka kamkame Juna,Bayanta yake Shafawa Zuwa Wuyanta Lokaci Daya yana Fadin"Tanque my Zaina...Tanque For been Their For me...And Tanqur For d Birthday Wishes Firstlove..!. Mirmishi Ta saki kafin tace"Firstlove ka manta yau ne Birthday dinka ko..? Dagota yayi yana kallon Cikin kwayan Idanuwanta yake Fadin"Wlh na Manta Firstlove kinsa ko da ina London sai naga Massages Dinki na Happy Birthday nake iya Tuna Ranar ne Birthday dina Haka yau ma sai da naga Sakon ki kana na Tuna.." Hanci ta Lakace mai Tana fadin"Karka Damu miye amfanina...Ni ina Sane ka manta pin dina na Atm da Password Dina na wayata Duk Key Code din Birthday dinka ne..? Taya kake Tunanin Halima zata manta da Abu mafi muhimmanci arayuwata..? Kai kawai yake kadawa ya kasa Mgana Mikewa tayi Lokaci Daya Ta mikamai Hannunsa Tana Fadin"Oya taso muje..Kafin komai sai ka Fara yanka Cake din Dana Hada maka Da kaina Firstlove.."Hannunsa ya mika mata yana Fadin"As u Wish Firstlove.." Yafada yana Mikewa Mirmishi ta sakarmai Shima ya Sakarmata Lokaci Daya yana Sumbatan Goshinta Suna Rike da Hannayen juna Suka Karisa Saman Dinning Din Tajamai kujera ya Zauna kana ta Duka ta kunna Kiddle din Dake wajen suka kama da Wuta Kana ta mike ta kara mikamai Hannu ya kama ya mike Tana Kallonsa Tace"Oya Off D Fire Bofere Cutting d Cake..! Ba musu ya Duka ya Fara Hure Candle din Ita kuma tana mai Tafi sai da ya gama kana ya kama Hannunta Suka Rike Wukar Suka yanka Cake din Suna Gama yankawa Halima ta Saki Tafi raf! Raf!Tana Waka tana Fadin" "_HAPPY BIRTHDAY TO U...HAPPY BIRTHDAY HAPPY BIRTHDAY TO U.....FIRSTLOVE...!_ Take Fada tana Sakin Dariya Shima Dariyan yake kafin ya Yanko Katon Cake din ya Tusa mata abaki,Itama ta ballo Wani katon Cake ta Tusamai abaki har Wajen gefen bakinsa Dariya ta kama mai Shima sai ya Biye mata Harshenta ta saka Tana Lashe Ragowan Cake din Shima Harshensa ya saka ya lashe mata Ragowan Cake din Daya bata mata gefen baki,Kafin ya Zarce da Sumbarta Sumbata mai Tsawo na Tsawon mitina Biyar kafin ya Saketa yana kallon Kwayan Idanuwanta yace"Tanque...Tanque Firstlove t Relli Appricent it Allah yayi miki albarka...! Tana Rike da Duka Hannuwansa Take Fadin" *Wishing u an Amarzing Day And Many Great Things to Come To a Wonderfull Person Dr. Zainullahi Usman Saulawa HAPPY BIRTHDAY FIRSTLOVE...!* Ta Fada tana Kallonsa Ido Cikin Ido Shima kallonta yake Cikin Wani yanayi kafin ya kamata ya Rumgume,Rumguma mai Tsawo, sukayi ma Juna kafin su Saki Juna Suna kallon Juna Cikin Mirmishi Kana ganin Soyayyah da kaunar junansu Cikin Kwayan Idanuwansu,matsar da Cake din Halima tayi,Gefe ta jawo Manyan kololin Data Zuba Delicous Din Datayi aciki ta Bubbude. Frefesun Kaza ne Sai Fride rice,Sai Ferfesun Kayan Ciki,Sosai Zain yaci Shinkafar ya Hada da Ferfesun naman kazan ya Dora da Kunun ayan da Haliman ta Hadamai mai Dadi da gardi Wanda Daman mutuminsa ne,Sosai Tare suka ci Sukasha Su kuma Cinyar da juna Duk Tana kan Cinyarsa Cake din Ta maidsshi Cikin kwalinsa sai Gobe In zata Tafi makaranta zata Tafi Dashi Gida Wajensu Umma su Taru Dasu Zainab su Yanka Cake din Tunda Sun Riga sun gama Celebreting din su ita da Firstlove. Duk yadda taso ya barta ta Tattara kololin Zuwa Kitchen Hanawa yayi ya Sunkuceta Sai makeken Bedroom Dinsu Wanda yaji Shimfidun alfarma Bai Direta ko"ina ba sai kan Gadonsu Tana Shirin mgana ya Saka Hannu ya Danne mata baki Yana Fadin"Shiii...! BirThday gift Dina zan karba Firstlove..! Lum Tayi mai da ido kafin ta Fara Kokarin Cire Gown Din Dake Jikinta yana Gefe ya kafeta da Ido Har ta Sabuleta Daga Zaunen Daga ita sai Farin pant da Bra Ta Dago Tana kallonshi Bra Din ta Ture gefe tayi kasa tana mai Wani kallo Take Fadin"Here is ur Birthday Gift  Firstlove...Do Wht ever u want All is Urs.." Take Fada tana Jifanshi da wani kallo Cikin Rawan Jiki ya Chakumota Yana Fadin"Kafin gobe in kika Kasheni Firstlove na yafe miki...In Abba da Su Nene suka Tuhumeki ni nace ki Fada musu Dadinki ne ya Zautar dani na Mutu Shikenan.."Saurin Hade bakinsu Tayi Lokaci Daya tana Kokarin Sabulai mai Rigar Dake Jikinsa Shi kuma Hannunsa na kan Kirjinta yana wasa dasu Domin Aduk Duniya yafi kaunar Kirjin Halima da ko"ina ajikinta Domim Su kadai kawai su kan Sakashi Natsuwa ne. ******* *Washegari..* Tsaye Suke Dukkansu agaban Makelen Dressing Mirror Din Dake Cikin Bedroom Dinsu,Kokarin Dauramai Neaktie Take yana Sanye da Ubansu American Suit na Kamfanin Armani ne Kalan Ash Colour ne. Hannunsa na Sanye Cikin agogon Fata na Fatar Damisa sai kafarsa sanye Cikin Takalmi Baki Sawu Ciki,Ita kuma Halima tana Sanye Cikin Wata Bakar Doguwar Riga itama Din Kirar Armanin din ce Sai ta nannade kanta da Vail Din Rigar,Ba kwalliya afuska ta Daga Hoda sai Liptick. Rike yake da Kugunta yana mata Dage Har sai da ta gama Sakamai kana ya Sauketa Cikin Sauri ta Juya ta Dauki Karamar Jakarta Tana Fadin"Firstlove na makara 8 nake da Class fa..! Wayarsa ya Dauka Daga kan Gadon yana Fadin"Ok muje ko ai nagama.."Wani littafi ta Daukan Saman Side Drower din Gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Ina key din Motata Ba fa zan Bika ba Zaka sani nayi latti kai ma kayi..Da Motata zani Saboda ina so in na Tashi Daga Sch na Biya na gaida Alhaji Tsoho Yaya Haddir yace min Baya Jin dadi Daganan zan karisa na gaida su Umma kwana Biyu ban leka su ba..! Yana Tsaye yana kallonta har ta gama Kafin yace"Hmm  Kedai kawai kina so kice zaki je Kiga Umman Zareena kawai malama.."Tana Dariya Lokaci Daya Tana Daukan key Din Motarta Take Fadin"Eh mana ai ban yi karya ba nayi kewar Uwata...Allah Sarki yar"uwata Zafeera Firstlove yaushe zamu Kano ne gidan Inna Rukayyah Rabona da zuwa Tun kafin Auranmu." Yana Shirin Barin Dakin Lokaci Daya Yake Fadin'"Ba Rana bq wata....ki Fito mu Tafi ko na barki ne ni na Tafi na Makara nima.."?Yafada yana Duba agogon Fatan Dayake Hannunsa. Wani bakin Flat din Takalmi ta Dauko ta saka Tana Fadin"Mu je na gama..Plz Firstlove Fara Daukan mun Cake din chan muje..."Kada kawai kawai yayi ya Fita Itama ta biyo bayansa,Gidan Bedroom Uku ne sai Falo sai kitchen,Saman Dining yaga Cake din ya Dauka ya Fice itama ta biyo bayansa. Aharaban Gidan ta ganshi Suna gaisawa da Tanimu maigadi yana Ganinta ya Hau washe baki Tana Fadin'Barka da Fitowa Matar Dakta..Gimbiya Tauraruwa agidan Dakta..Allah yaja zamaninkk Dade kiyi karko Irin na Dabino Bari nayi addu"an dana Saba Allah ya Tsare gabanki da bayanki Gimbiya agidan Dakta...Allah ya albarkaci Rayuwarki Allah kuma yasa kada Dakta yayi miki Kishiya Ku zauna ahaka Mutu ka Raba.."yafada yana yar Dariya karamin Tsaki kawai Zain yaja yana Fadin"In ka gama Surutun naka Sai ka Bude mana Get zamu Fita ne..! Daga Haka ya wuce Halima ce ta Tsaya Suna gaisawa Lokaci Daya Tana Fadin"Tanimu kenan Kai da baka gajiya..? Ameen ya Allah.Nagode.."Take fada tana Zaro 1k Daga Cikin Jakarta ta mikamai Tana Fadin"Gashi Tanimu ka Siya wani Abu kaci yau Bazan dawo Gida da Wuri ba.."Har Kasa ya Duka ya karba yana Fadin"Allah ya Kareki..Allah ya Daga Darajanki..Allah yayi Riko da Hannayenki Allah ya Tsone idanuwan Matan Bariki akan Dakta Domin kinsan Yan matan wannan zamanin sai addu"a kada wata ta Makalema Dakta mu Shiga uku.."Dariya ta kama Halima Ta Murmusa tana Fadin"Toh nagode Tanimu ka kula..Sai mun Dawo.." Ya Bisu da Allah ya kiyaye Hanya kamar yayi mata Sujjuda Saboda Godiya Zain ne Dake chan Gefe Jikin Motan Halima ya Daga Murya yana Fadin"Don Allah Tanimu ka Bude mana Get Haba..Chai Chai bakinka baya gajiya Sai kace Zafeeran Umman da Take kama da parrot wajen mgana.."Yafada Daidai sanda Halima ta Kariso Kusa Dashi Mikata Cake dinta yayi yana Fadin"Kinga karbi Abunki..Zan makara Tunda ke kin Tsaya biyema Shirmen Tanimu..". Karba Tayi Lokaci Daya Tana Fadin"Afuwan Firstlove...Kasan Halin Tanimu baya gajiya..Ka wuce kawai Allah ya bada Sa"a sai munyi waya..".Tafada Lokaci Daya tana Rumgumeshi Shima Rumgumeta yayi na Dan Wani Lokaci kafin su saki Juna Kallonta yayi yana Fadin"Take Care For u Self for me kinji ko..? Kai ta kada tana Fadin"U too..."Ita ta Budemai Motar ya Shiga Ta Rufemai Ya Tada Motan kenan tana Tsaye tana kallonsa ya leko bayan ya Sauke Glasa yana Fadin"Nima zan Fara Biyawa ta Gaida Nagaida Neneta Kafin wata ta Rigamu zuwa Ehe..."Yafada Har da Murdamata baki Kansa ta Tallafa Bayan ta Zura Hannunta Cikin Motan Tana Fadin"Kai ko..? Zaka sani ne Jealousing Firstlove ko..? Dariya yake mata kafin ya Daga mata Hannu itama ta Daga mai Kaucewa tayi yayi Riverse ya Danna Hon Da Sauri Tanimu ya wangalemai Get ya Fice da Sauri Halima na Dagamai Hannu Tanimu na Faman mai addu"an Dawowa lafiya. Yana Fita itama ta Bude bayan Motanta ta saka Cake din Ta koma Bagaran mai zaman Banza ta Ijiye Jakarta da Littafinta kana ta koma Bangaran Direba ta Bude ta Shiga Ta Zauna ta saka Site Belt Lokaci Daya tana karanto addu"an Matafiya kafin tayi ma Motar key tayi Riverse Ta Danna Hon Dama Tanimu bai kulle Get din ba,Ta Sulala ta Fice Tanimun na Faman Fadin Adawo Lafiya Gimbiyan Dakta tana Mirmishi Take Fadin.. "Ameen Ya Allah Tanimu...Ina Jin Dadin Sunanan Gimbiyar Dakta.."Ta fada Lokaci Daya Tana Mirmishi kafin ta Daidaita Motarta Saman kwalta ta Saki Gudu Sai ATBU BAUCHI inda take Karatunta na B.SC. Mathemathics...! *Masha Alhamdulillah...Hakika Naga yadda kuka karbi wannan Labarin ina matukar Godiya Yanzu aka Fara wasan bama muce komai ba a kafcen sai mun Shiga Labarin Sosai Allah ya Taimakemu Ameen* *Comment* *Share* *Vote* *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira* *BOOK 1* *ina ta samun kiran Waya Da DM cewa wasu basu iya Pronaucing din sunan Littafin nan,wasu ma sun Dauka wani yare ne..?ZAIN sunan Zainullahi ne ZAINA kuma Sunan Halima ne sai na Hadasu Waje Daya suka Bada ZAINAZAIN....*           0️⃣3️⃣ *Area:GRA..* A bakin kofar wani Tamgamemen Get ya Tsaya yana Zuba Hon Cikin Abunda bai Fi Minti Goma ba aka Wangalemai Get din Lokaci Daya ya Sulala Ciki Zuwa parking Space. Tun kafin ya Gama Daidaita Zaman Motar Nashi Daga chan Haraban Gidan ta Gefe ya Hangi Saudart da Junior Suna Buga Ball,mamaki ganinsu agida ya kamashi,Tunda yau Ranar School ce Kashe Motar yayi ya Fito Yana Gyara zaman Caot Din Jikinsa Lokaci Daya yana Duba agogon Fatan Dake Hannunsa Pass 8. Da Baba Megadi suka Fara gaisawa kafin kai Tsaye ya Fara Taku Zuwa Kofar da zai sadashi da ainihin Babban Falon Gidansu Motar Abba yagani da Direbansa yana Tsaye yana Jiransa alamun Shima yau bai Fita da Wuri ba,Barayin su Saudart ya kallah bama su Lura dashi ba ganin Haka yasa ya Dakata ya kwalama Junior kira. Waigowa Sukayi Duka Atare Jin Muryansa da Sauri suka kwashi Gudu Zuwa Wajensa Atare suka Hada Baki Suna Fadin"Sannu da zuwa Yaya Dacta..And Happy Birthday.." Suka Fada Suna Mirmishi Yara ne Masu kama da Zain kamar an Tsaga kara Barin ma mace Saudart yar Shekara Goma Sha Uku a Duniya yayinda Junoir yake dan Shekara Tara aduniya Cikin mamaki da Mirmishi yake kallonsu Kafin ya Dafa kawunansu,yana Fadin"Kai...Waya gayamuku yau Birthday Dina..? And kuma meys Hanaku zuwa School yau .? Saudart ce tayi Saurin Cewa"Yaya Dacta Jiya aka bamu Hutun Meadteam Break Sai Monday zamu koma.."Kumatunta ya Shafa yana Fadin"Daz Gud Anty Kumatu kamar Nene na baki Madaran yara sai kiba ki ke Karawa Saudatu.."Dariya Junior ya Kwashe Dashi Ita kuma sai ta bata Rai kamar zatayi kuka Tana Hararanshi,Ganin Haka yasa Zain ya Riko Hannun Junior yana Fadin"Kai karka kara mata Dariya ok..? Kai ya gyadamai Yana Kokarin Danne Dariyansa kafin yace"Yaya Dacta Nene ce ta gayamana yau ce Ranar Zagayowar Haihuwarka..."Kai ya Jinjina yana Fadin"Dama nasan Itace Kadai agidan bata Manta Ranar Haihuwarta ba..." Yafada kai Tsaye yana Rike Hannayensu Dukkansu Suka Nufi Cikin Gidan Suna Tafe Suna mai Hira Suna Dariya da Haka sukayi Sallama a Babban Falon Gidan Zainab ce Kadai ke Zaune Tana kallo Gefe Daya kuma Tana Danna Wayarta Dake Hannunta tana Jin Sallamarsa ta mike tana Ihu Tana Fadin"Happy Birthday To U...Happy Birthday Happy birthday To u Yaya Dacta..Nene Fito ga Yaya Dacta yazo..!. Take Fada gabadaya Fararan Hakoranta Suna Waje Jin Haka yasa Wacce aka kira Da Nene ta Fito Daga Cikin Bedroom Dinta Tana Fadin"Maraba da Da" irin na Nene Dan albarka.."Take Fada cikin Tsantsan Farinciki,Wata Gajeruwar mata na gani mai Kiba kadan Ashekaru bazata wuce 48 aduniya ba Fara ce Tas Tana da Zanen Biyu Biyu agefen Fuskarta Akallon Farko in kayi nata Zaka Fahimci Tana da Saukin kai da Wayewar Zamani. Zain da Farinciki ya Cika Ransa ya Saki Hannun Su Saudart ya Tafi ga Nene ya Ramkwafa zai Gaisheta da Sauri ta Dagosa Tana Fadin"A"a kul Dan albarka Babban Mutum Mun Tashi lafiya...? Barka da Zagayowar Ranar Haihuwa Son..Allah karama Rayuwa albarka Dama yau muke Shirin in baka zo ba zamu kwasa muje chan Gidan naku muyi Shagali Wasu sai jin Haushi Suke Suna Fadin Shirmen Banza.." Tafada Tana Nuna Umman Zareena da baki Wacce ta Fito Daga Kitchen,Dauke da Mug din Ruwa a Hannunta Doguwar Mace Ba Fara ba Chan tana da Haske,A kallan Farko in kayi mata Zaka Shaida Mahaifiyar Zain ce Saboda yanayin kamarsu da Juna Ashekaru itama Bazata gaza 49 ba Aduniya Tabe baki Tayi bayan Ta kallesu Tana Fadin"Kwa ji Dashi dai..'. Yana Dariya ya Juya yana Fadin"Umman Zareena ina kwana.."Tana kallonsa Tace"Lafiya lau Dacta...Ina Kwanan Diyata..? Yana Sosa kansa yace"Tana lafiya Umma..Tare muka Fito ta Shiga School ammh Tace In ta gama abunda take Daga Gidan Alhaji Tsoho nan zata zo gaida ke.."Yafada yana yar Dariya Mirmishi Umma ta saki Tana Fadin"Na sani...Allah ya kawomin Ita Lafiya ina kewarta Daga Ita Har Zafeera ban ji su ba kwana Biyu,Jiya dai mun yi mgana da Zareena..! Nene Tayi karaf tace"Wannan dai ya"yan naki Sai dai nace kinyi Sa'an Haihuwa Ya"ya Suna Mantawa da Uwarsu Abu dai Baiyi Dadi ba.."Tafada tana Dariya Umma tace"Au ke saboda naki Yaron na gabanki..? Allah kawomin Halimatuna lafiya..! Tafada Tana Juya zuwa Shashen Megidan Wato Alhaji Usman Abubakar Saulawa,Zain ya saka Baki ya Kirata.."Umma baki ji ba..!ta waigo tana kallonsa Cikin Shakiyanci yace"Umma baki min Happy Birthday ba yau fa nake Cika Shekara Dai Dai Har Talatin aduniya fa Umma.."Wani Dogon Tsaki Taja Kawai Tana Fadin"Rabani da Saka kaina Cikin Shirmenka kai da Uwarka.."Daga Haka ta wuce su Nene suka Rakata da Dariya Harda Yaran Itama da Mirmishin ta Shige Akan Fuskarta. Tana Wucewa Nene ta Jashi ya Zauna kan kujera Tana Fadin"Ina Zuwa Yarona.."Tafada Lokaci Daya ta wucewa Kitchen Zainab ta kariso Tana Fadin"Yaya Dacta Don Allah yau ka bari a Shirya kayattacen party for u agida nan plz..! Kallonta yayi yana Fadin"Kefa yarinyar nan na Lura yar son Bidi"a ne fa.."Yafada yana Hararanta Dariya ta Saki Tana kokarin mgana Nene ta Fito da wani katon Cake a Hannunta Su Junior suka Saka Ihu mamaki bai Kama Zain ba Domin Duk Shekara Sai Nene ta Shiryamai Ranar Haihuwa koda baya Gari zata yi Shagalinta agida su Kirashi Vidoe call Suna Tayashi Murna. Kan Center Table Din Dake Tsakiyar Falon taja ta Daura Cake din,su kuma su Zainab da Saudart suka je suka kwaso kananan Baloon din da suka Hadashi Tun Jiya suka zo suka watsa Afalon Lokaci Daya Suna Sakin Wannan Abun mai kamshi da kuma Farfatsi asama yana Sauka Bisa kan Zain Din Lokaci Daya Suna mai wakar Happy Birthday bakinsa yaki Rufuwa da Farinciki Haka bakin Nene Sai da suka gama Tace su Dakata Zain ya yanka Cake. Har gaban Cake din Taja Hannunsa Takai Ta mikamai karamar Wukar Hannunta ya karba yana mata Dariya Duka Hannuwan Kannensa yahada da Na Nene zai yanka Cake din Yaji Dagachan Abaya Ana Fadin"Yaron Nene wannan Son kai yayi yawa Shikenan Haka akeyi sai ka yanka Cake ba Umma zareena ba Abba kuma ba Ita Firstlove din Taka..? Dukkansu suka waiga Jin muryan ABBA,farin Karkkafan Namiji ne mai Cikar kamala da Zati kenan,In ka gansa zaka Fahimci nan Zain ya Debe Tarin Dattako da kamalan Fuska Harda Haiba da kwarjini,afizge Suna kama na jini,Da Duka Ahalin nashi yana ashekaru ba zai gaza 58 ba Sanye da Riga da wandon Shadda Harda Babban Riga kansa Sanye da Hula Umma na Gefensa Rike da Karamar Jakarsa na Briefcase Tana Mirmishi. Ganinsa yasa Zain ya Washe baki yana Fadin"Sabahul khair Abba.."Fara takowa sukayi gabansu Lokaci Daya Yana Fadin"Lafiya Likitan Mata na Nene Kuma angon Halimatu ko..? Yafada Cikin Zolaya Lokaci Daya Yana kallon Nene kafin ta samu Zarafin mgana ya Rigata da Fadin"Kin kyauta..Munga Son kai Hajiya Nene masu D"a...Kawai Sai ku yanka Cake dinku ku kadai Salon Rowa kada muma ayanko a saka mana Baki Toh Wlh baku isa ba gamu munzo Dale ajiramu ayanka Damu kuma aci Damu badai Fadi kawai ake Happy Birthday ba muma mun iya.."Ya karishe Fada Cikin Barkawanci da Zolaya. Gabadayansu Suka sakamai Dariya yana Kallon Junior yace "Ko ba Haka Ba Basiru..'Baki ya Tura yana Fadin"Ni fa Abba ba Basiru bane Sunana Am Bashir Usman Abubakar Saulawa by Name.."Abba yace"Kai Don Allah..? Maimaita me kace Sunanka.."Yafada yana karkatamai Kunni Cikin Haushi Junior yace"Bashir Usman Abubakar Saulawa Abba.."Gabadayansu suka kara Sakamai Dariya Ganin Idanuwansa ya kawo kwallah ne yasa Umma ta Jawo sa Jikinsa Tana Fadin"Kyalesu Junior na Abba ke son Taba min kai ko? Kowa ya sani Sunanka Bashir ne ba Basiru...! Sai da suka gama Dariyan Nasu kana Abba ya karkace kai yana Fadin"To mu yanka Cake din mana Sauri nake Meeting gareni 10 fa.."Nene tace"Taci albarkacin ka ABBa...Da naso Sai Yar nata tazo sai su yanka nasu mugani.."Zain na Mirmishi yace"Kamar kin sani Nene..Ragowan data Hadamim Jiya yana nan zata Zo Dashi..Su yanka ita da Mamanta.." Nene tace"Kaji ko Abba..? Gaskiya bamu so Leken Asiri.."Tafada Tana Dariya Umma tace"Mugani..? Wannan cake din ba bai kai kyan na Diyata ba na sani..? tafada tana Leke Cikin Barkwanci Bata Rai Nene Tayi zatayi Mgana Abba yace"Meye na Fushi..? Bar ta ta yanka taci Itama in yarta Tazo Dashi ataru ayanka aci sai a Tantance Tsskanin na Uwar Da na matarsa wanne yafi Dadi.."Abba yafada yana Dariya Zainab ta kada baki Tana Fadin"Gud Idea Abba.." Dole ba Yadda Nene Zatayi suka Hadu suka yanka Cake Zain ya Dinga Dauka Daya Bayan Daya Yana Basu Nene aka fara Bamawa Itama ta bashi Tana Fadin"Allah ya albaeci Rayuwarka da Farinciki yarona..Zunubanka na Baya Allah ya yafe maka Allah yasa wannan Shekaran Daka Tunkara Alherin Allah ya Lullubeka.."Gabadayansu suka amsa da Ameen Daga Ita ya bama Umma itama ta bashi Tana Fadin"Duk da Mamanka ta Riga ta gama cewa Komai..Ammh Nima zan ce..Allah yayi maka albarka Likita.."Tafada tana Shafa kanshi Mirmishi yayi yana Jin Wani Farinciki kafin ya Furta..'Nagode Umma..! Daga Ita sai Abba ya Bamawa Daya Dauko karami kin karba Abba yayi yana Fadin"Nene ji Son kan D'anki.? Wanda ya baki katon Gaske yama Fi karfin bakinki ammh ni kalli nawa Wani karami Wanda iyakarsa bakin Saudatu.."Yafada yana kauda kai Dariya suka sakamai Kafin ZAIN ya yanko wani kato kana Abba ya Karba ya Turamai baki Har sai ya Fi karfinsa Ya batamai Gefen baki me yaran zasuyi in ba Dariya ba Zainab na Gefe Tana Daukan Vidoe tana Fadin"Dole su Anty Zareena susha Takaichi in suka ga Wannan Show din..' Haka ya bi kannen nashi Duka ya basu suma suka Bashi,Suna yi Suna Barkwanci Suna Dariya Suna gamawa Abba yace"To angama..? Ni bari na Tafi office saura na anjuma in Firstlove tazo da nata.."Yafada yana yar Dariya Umma tace"Kwarai..Bazamu yanka ba sai ka Dawo Abban Saudat..' Nene tace"Oho dai Sauran yarona ne..Tunda Jiya sai da ya Fara yanka Abunsa kuma yaci..'Umma tace'Naji ba komai..Ai ni na Koyar da ita kyautatama yaron naki..' Nene tace"Nima ai na Koyar dashi Rike Diyar naki..Ke kanki kinsani Samun irin mai Nagartan Dana sai an Tona.."Umma tace'Nima fa..Ai ya sani Diyata Badaga Baya ba.." Abba ya mika Hannu yana Fadin"Nidai bani Jakata Nagode..Bari na Tafi in kuka Fara wannan Jayayyan naku kan ya"yan naku ba kwaji bakwa gani..na Tafi sai na Dawo.."Gabadayansu suka Rakashi da Adawo lafiya Zain ya Biyosa yana Fadin"Abba gidan Tsohon nan zaka Fara biyawa kafin ka wuce ko..? Abba yace'Eh Zaka ne..? Yafada bai Tsaya ba Da Sauri Zain yace"Eh Abba..Dazu Firstlove ke Fadamin Haddir ya Fadamata yana Fama da Mura.." Bai samu bashi amsa ba Sai da Suka Fito Daga Falon kana Yace mai.."Yanzu sai karfe nawa zaka Tafi asibitin kenan..? Yaron Nene adaina Wasa da aiki fa..! Yana Sosa kai yake Fadin"Ba Haka bane Abba...Akwai Likitoci asibitin kaima ka sani..Kuma ina zuwa zan Fara addenting din Patient.."! Abba na Mikama Direbansa Jakarsa yana Fadin"kardai abarsu Jira..Kakanka na alfahari Dakai ya kamata ka daina Shiriritarka.."Da Sauri Zain ya Budemai Murfin Motan yana Fadin"Insha Allahu Abba..! Sai da Yaga Fitar Motan Abba kana ya Shiga Tashi yabi Bayansa Tsakanin Gidan Iyayen nashi da Gidan Alhaji Tsohon ba Nisa Duka Anguwa Daya ne ko a kafa zaka iya zuwa..Kusan Tare suka isa da Abba Tare suka kuma Jera suka Shiga Babban Falon na Alhaji Tsoho kana ganin yanayin Gidan zaka Fahimci ma mallakin Gidan Yana da Tarin Ilimi. Suna Shiga Suka iske Haddir yagama Dubashi yana Shirin Tafiya ne Suna Shigowa da Sallama Alhaji Tsoho ya Dago yana Kallonsu Lokaci Daya yana Gyara Zaman Siririn gilashin Dake karamai karfin gani Farin Dattajo mai Yalwar Fara"a Da Dattako,yana Zaune Bisa Wata kujeran alfarman Daga Tsakiyar Falon,Sanye yake da Wata Farar Jallabiya Rantsatsiya mai kyau irin ta Saudiya,Gefe daya kuma Yana Rike da Wata karamar Sanda kamar ta Axurfa wacce ke karamai karfin Takawa,Akallan Farko in kayi mai zaka Fahimci Tsantsan Haibansa da Zatinsa Uwa Uba Nasabansa da Nagartansa,Dr Abubakar Bashir Saulawa kenan a Shekarunsa na Haihuwa Kimanin 93 kenan a Dunya Farin Gemu Duk ya Lullube kansa da Sajensa Gabadaya Ammh Fatarsa bata Yamutse ba kamar na Wasu Tsoffin Saboda Tana Samun Jin Dadi da kulawa Daga ya"yansa Uwa Uba kuma Tsantsan Ilimin Dake Tare Dashi Both Boko da Arabi. Da Mirmishi Bisa Fuskarsa ya amsa Sallaman nasu yana Fadin"A"a Muryoyin wa nake ji kamar ta Usmanu Bin Fodiyo da Babban Likitan Mata Iyayenmu Dr.Zainullahi Usman Abubakar Saulawa Mijin Halimatu Sa"adiya..."Yake Fada Gabadaya Hakoransa Suna Waje Domin Babu Hakoransa ko Daya Daya Fita. Haddir Dake gefensa Sanye da Suit Black and White sai Rigar Likitancinsa Lapcoat Daya Dora asama yace"Kaji Tsohon nan Da wani Dogon Sharhi..Kana Nufin baka gani ne sai Daukan Murya..? Lalle ka Fara Tafiya Tsoho..! Ya Fada yana Dariya Dakuwa Abba yamai yana karisowa Cikin Falon Lokaci Daya Tana Fadin"Kaga Naka nan Hadiru mu kam Tsohon mu sai ya Bar Duniya da Idanuwansa Insha Allah.."Yake Fada yana Zama Kusa da Alhaji Tsohon Cikin Girmamawa ya Shiga gaisheshi Haddir da Zain suka Sarke Hannun Juna Suna Dariya Mirmishi Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Kyalesa Usmanu Bin Fodiyo Haushi yake ji Domin nace in ya wuce wannan Ramadhan Din bai kawomin Matar Aure ba sai na Bugamai Kidan Gauro ka ganshi nan Shine yake ta wani kunci Toh ba wasa nake ba Jira nake Karshen Satina nan yayi Ubanninka Su Taru zan Musu bayani in ma Baka lafiya ne Gwara Tun Wuri ka Fada anema maka mgani..! Da Sauri Haddir yace'Waye bai da lafiya..? Ni wlh Lafiyata kalau.."Yafada yana wani Bata Fuska Zain da Alhaji Tsoho Suka Fashe da Dariya Lokaci Daya Abba na Tayasu Duka Haddir yakai ma Zain Abaya yana Fadin"Ameobo..."Shidai Zain Dariya kawai yake ya Duka ya bama Alhaji Tsoho hannu Sukayi musabaha Yana Fadin"Likitan kwakwalwa ya Mura..? Jiya Firstlove ke Fadamin Baka ji Dadi ba..? Alhaji Tsoho yace"Wlh...Naji Dama yanzu Muran ma Tayi Sauki Uwargida da Amaryata Suna Kula Dani..'Yafada yana Mirmishi kafin ya Cigaba da Fadin"Wato Iyayen naka Zainullahi sai dai nayi musu Fatan Gamawa da Duniya lafiya kawai Jiya nan suke Har Dare da Kayan Dubiyarsu Tare da Feefesun kazan su Wanda yaji Citta namu na masu Mura..Lalle ban yi Nadamar Aurama Usmanu Su Arana Guda ba Aisha da Fatima Allah yayi musu albarka Allah kuma ya albarkaci Zuru"arsu.."Gabadayansu suka amsa da Ameen kafin Zain yace"Wai ina Matas ne ban ji Motsinta ba.." Alhaji Tsoho zai yi mgana kenan Sai ga Wata Farar Dattijuwa ta Fito Daga Cikin Kitchen Dauke da Silba Cike da Damammiyar Fura,Kallo Daya zaka mata ka Shaida ita ta Haifi Alhaji Usman Saboda yadda Yake kama da Ita,Itama Ashekaru bazata wuce 70 ba,Ammh bazaka Fahimci haka ba sai ka Kura mata ido saboda jin Dadi Hajiya Amina Kenan Wacce Ya"ya da Jikokinta ke Kiranta da HAJIYA MAMA..! Tana Karisowa Cikin Falon Tana Fadin"Ga ni nan Ango na ina chan ina Dama ma wannan Tazurun abokin naka Fura ne ina Tsausayamai kada yaje aiki Bai ci komai ba.."Tafada tana Dire silban Gaban Haddir Tana Fadin"Gashi nan...Megida ba Cefene na gaji da maka Bauta..Ka nemi mata kayi Aure kafin na Dauke maka kafa Atoh..'Jan Silban yayi yana Fadin"Ke kuma shikenan sai kimin Tonin Silili gaban wannan Tsohon Mijin naki me Tafiya da Sanda ko..? Alhaji Tsoho yace"Kwarai..Kuma yafi wani mai kafan amfani Tunda ni Har yau ina Cefane.."Hajiya Tayi Dariya Suna gaisawa da Abba da Zain kafin Haddir yace"Au haka kika ce ko..? Bari na koma Wajen Baba Tabawa Ita zata yi Mijin Dani.."Hajiya mama tace"Eh Jeka tana Kitchen ka sameta ita kam zatayi Kayan Megida ba Cefane sai Wahala."Zain sai Dariya yake Haddir na Hararansa ya Dauki Furansa zai bar Falon kenan Alhaji Tsoho yasa baki ya Kirashi Ya Dawo kallon Abba yayi yana Fadin"Tayani Gayamai Usmanu..Kila kai yaji mganarka ace yau Dan Aliyu Yana Garinan ga Gidanka ga Gidana Ammh bazai zauna ako Daya ba Sai yaje ya kama Haya Shi gashi ba Mata ba..? Kaniyarsa yake achan Usmanu..? Maza ka gayamai komai yake Ciki ya Tattaro ya Dawo Gidanka ko Nan Gidan da Zama ban lamunci Zamansa awannan Gidan ba Tunda ba mata gareshi ba..! Yafada Cikin Alamun ba Wasa yake ba Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Hakane Alhaji Tsoho..Kai Haddir maza ka Tattaro kayanka Ka zabi Gidana ko Nan Gidan ka Dawo ka Zauna Zamanka achan baida wani amfani Tunda Kana da Wajen da zaka Zauna.."Hajiya Mama ta karbe da Fadin"In yana so ya samu sakewa..Yayi Aure..! Fuska ba Walwala Haddir yace"Toh Abba Dama Abunda yasa na kama Chan Gidan naga yafi kusa da asibiti ne.."Alhaji Tsoho yace"Wannan Ba Hujja bace..Da zai saka ka Zauna kai kadai..Sai Mutane surika Munana maka Zato Tunda ina da Tabbacin ansan kana da Mu anan garin Zamanka achan bai Dace ba kayi yarda muka ce kawai ."Kai ya kada yana Fadin"Shikenan Weekend zan yi parking..Zan dawo nan daman Wannan Tsohon matar naka Tana So tana kaiwa kasuwa..! Yafada yana Hararan Hajiya Mama Shewa ta saki Tana Fadin"Ja chan Me zan Dakai..? Kaga Sabon Megida nan,Megidana akwai Cefane.."Tafada Tana Dafa Zain Dake gefenta Shima ya Dafata Harda Ma Haddir gwalo Abba yace"Hajiya mama Ayi ma Tsohon mu haka..? Hajiya Mama tace"Me za"a Fasa..? Shima Tawaye yake neman yayi min da Halimatu Kullum sai tazo Gidan nan kaga Sun Hada kai suna ta kus kus in kuma bata zo Zata kirashi a waya ko Aikomai da wannan kawomai wannan Kaga fa in batazo ba ya Dinga Damuna da Fadin Oho Aminatu yau Halimatu Shuru ko lafiya..? Bari na Kirata..! Abba na Dariya yace"Au Ramawa kikayi kenan kema kika kwace mata miji kenan..? Hajiya mama Tace"Eh mana Taji In Da Dadi itama.."Alhaji Tsoho yace"Hoho Aminatu...Ina Laifin Halimatu kinsan Bakin Tsoho sai da Gishiri Gishiri kuma Kus kus Din Da kikace munayi labarin Iyayenta nake bata Ina gayamata kyawawan Halayansu da na sani Lokacin da muka Zauna dasu Suna Raye..." Allah ya Jikan Umaru da Abdullahi da Duka Musulmab da Suka Rigamu gidan Gaskiya.."Gabadayansu suka amsa da Ameen sai kuma Jikinsu yayi sanyi Alhaji ya Cigaba da Fadin"Haske da Rahma yakai musu..Bayin Allah ne masu Zuciyar Zinare Na Sha Gayama Halimatu Ta Debo Wasu Daga Cikin Hallayan Mahaifiyarta Maryama.."Hajiya Mama tace"Ba Shakka...Allah ya Hadamu a Aljannah Dasu.."Gabadayansu suka amsa da Ameen Ameen kafin su Cigaba da Hiransu Jefi Jefi Abba bai Jima ba yayi musu sallama ya Tafi Zain kuma sai da ya Tsaya Suka Sha Furan da Hajiya Mama ta Damama Haddir Duk da yadda ya Dage kan bazai Sha ba Bayan sun gama suka Tafi Kitchen suka gaisa da Baba Tabawa Wata Yar Dattijuwa ne aiki take Gidan Alhaji Tsoho Tun Tana Matashiyarta Har Girma ya kamata an Riga da an zama Daya Dayake Baba Tabawa irin yan gudun Hijiran ne ba wasu Dangi ne Alhaji Tsoho ya Zame mata Tamkar Uba Duka su Zain Agabanta suka Taso Ita tayi Wahala dasu In Aka kawosu Hutu Gidan na Alhaji Tsoho. Bayan sun Fito ne sukama Su Hajiya Mama Sallama suka Fito Atare Haddir na Kokarin Shiga Motarsa yana Fadin"Wai ina ka Tsaya Jiya Zainarka ta kirani Tana Tambayana ko muna Tare..? Yana Sosa Gemunsa da Key din Motarsa yace"Na tsaya Cikin Asibiti ne Kuma Wayar tawa Tana Silent Shiyasa ban ji kiranta ba.."Kallon Sama da kasa Haddir yayi mai kafin ya Cije baki Cikin Tsarguwa Zain yace"Lafiya kake min wannan kallon..? Ko zan maka karya ne alkali Hadiru..! Yafada Lokaci Daya yana Dauke kai Mirmishi Haddir yayi kafin yace"Kai dai ka sani..Ka kama kanka ne ammh ni wani kallo nake maka..? A koda yaushe bazan gaji da Fadamaka ba kaji Tsoron Allah..Ka kuma guji Ranar da Wata baraka zata Faru wacce Zata Zubar maka da kimarka Harda ta iyayenmu.."Yana Gama Fadar haka ya Bude Motarsa kiran Jeep ya bar Zain nan Tsaye yana Binsa da kallo Mganar Haddir din namai yawo a saman kansa yana Tsaye ya Fice Daga Haraban Gidan ya barsa ajiyar Zuciya ya Sauke kafin Shima ya Nufi Motarsa ya shiga ya Tasheta Shima da Gudu yabi bayan Haddir din. Kusan Tare suka Shiga Cikin Asibitin..Kowa Bangaran Office Dinsa ya Nufa Saboda sun makara Sun san Fayels Din patient na chan na Jiransu da Uban Layi,illai Haddir yana Shiga Office ko zama bai gama yi ba yace First ya Shigo Shi kuwa Zain yana Gabda Shiga Office Dinsa Suka Hade da Dina ta Fito Daga Office Dinta kallo Kallo Sukayi ma Juna kafin Shi yayi Saurin Dauke kai ganin Tana Jifanshi da Irin kallon Data saba kashemai Jiki Dashi Fuska ya Hade kawai ya Tura kofar Office dinsa ya Shige yana Kiran Wata Nurse da Hannu Alaman ta Biyoshi. Sai da ya Shige kana Dr.Dina ta Kada kai ta Murmusa tana Fadin"Kayi kuskure Dr.Zain in kana Tunanin zaka iya gujema Dina..Har Abada bazaka iya ba..Ban Fara sonka don na Daina ba kuma Ban Fara mu"amala Dakai don na Daina ba..Yanzu ma aka fara Wasan...! Tafada tana wani Sakin Wani Shu"umin Mirmishi ta kada kai ta Wuce so take ta bar Cikin Asibitin Tunda Ta Duba patient 10 yau da Safe tace abarshi haka Sauran aturama Dr Imran Ita ZATA fita Ma"aikatan su Zakiya take son zuwa su Tattauna wasu Abubuwa sun kwana Biyu Basu hadu ba..! ***** Fitowarsu kenan Daga Lecture Suna Gangarawa zasu Shiga Lap Duba wani Calculaton da aka basu Tafe suke suna Hira Sama sama Har suka Isa Libary Din Sai da suka samu Waje suka Zauna kana Halima ta Fito da Wayarta Tana Fadin"Kinga Laila kafin mu Fara Duba Assigment din nan Let me Call Firstlove Tukunnah na gayamai na Fito..! Mirmishi Wacce aka Kira da Lailah Tayi,Itama Dim kamar Sa"ar Haliman ce sai dai Ita Fara ce Tas kuma kyakyawa ce,Kai ta kada Tana Fadin"Hmm kirashi Dama waya isa ya Hanaki Kiran Firstlove..'Halima bata Jita ba Domin tayi nesa da Ita Suna mgana da Dr.Zain tana mai Shagwaban Ta gaji,shi kuma yana Lallashinta Daga karshe yace in tagaji ta koma Gida Shima da wuri yau zai Tashi aiki nan dai suka Shiririce Suna Mgana Sai da Taji Shigowar Haddir da mganarsa kana Suka Datse kiran Ta koma Wajen Laila Tana Fadin. "kawas afuwan..Na bata miki Lokaci.."Laila tayi Mirmishi Tana Fadin"Bakomai..ai na Saba Daukan Bata Lokaci indai akan Firstlove ne.."Dariya kawai Halima Tayi  Batayi mgana ba Laila ta kalleta Tana Fadin"Ni kuwa Halima in bazaki Damu ba zan so na baki Wata yar Shawara..! Halima na Fito da Note Book Dinta Da Handout Lokaci Daya Tana Fadin"Wata Shawara..? Ina Sauraranki Lailah..'Tafada Tana kallonta..'Laila ta gyara Zama Tana Fadin"Tunda muka Fara karatu a wannan makarantar muka Hadu Dake Halima muka kulla kawance Saboda Duka Abu Daya ya kawomu..Duk da Banta Aure ba ammh ina da Labaran Zamantakewar Aurarranki Da Dama Halima..Na Tabbata a Haduwata Dake zuwa yau zan Shaida Girman matsayin Soyayyah da Kauna Hade da yarda Da kike ma Mijinki Halima Kuma Hakan yana matukar Burgeni..ina jin Dama ace Nima na samu miji kamar naki Wanda zamu Dinga Gudanar da Rayuwarmu kamar yadda kuke gudanar da naku keda Firstlove dinki..! Mirmishi Halima ta Saki kafin Tace"Bake kadai ba..Mutane Dadama Suna Fadin Irin Soyayyar Dake Tsakanina da Firstlove Tana Burgesu."Laila tace"Dole ne..Ammh Duk da Burgenin Datake Ina da yar Shawara gareki Halima..Kinga Da" Namiji Buhun kaya ne kuma Dan Hankaka ne gabansa Baki bayanshi Fari ina Tsoron yadda Kika gama Bashi Yardanki kada Watarana yaci Amanarki Zuciyarki ta kasa Dauka Har Abun yazo yayi affecting Dinki Halima..! Tun kafin Ta karisa Halima ke Jefenta da wani kallo kafin tace"Bangane ba Laila..What Do U mean..!? Kai tsaye Laila tace"Ina Nufin ki Rage Wannan Zafin so da yardan da kika bama Mijinki ban ce ki Daina yarda Dashi ba Duka No ki Rage karki manta Namiji ne kuma Likita Likitan ma na Mata Yana Harka da mata kala kala kinsan Zuciya bata da kashi Ina Tsoron kada Wani abu ya Faru kika sa Jurewa Zuciyarki Zata iya Tabuwa a yadda na Sanki da Komai kankanta Abu Damunki ya...! "Don Allah Dakata Lailah..! Bata karisa ba Halima ta Tareta a Fusace Shuru Laila Tayi Tana kallonta Ita kuma Halima ta Fara Mgana Cikin Bacin Rai Tana Fadin"Kin bani mamaki laila Wlh Ban Taba Zaton keda bakinki zaki zo da irin wannan Zargin ga Firstlove ba na Dauka kowani Kikaji yana Fada sai inda Karfinki ya kare adai yadda muke Dake ammh sai gashi keda kanki ki ke Fadan Haka..Toh bari na gayamiki Abunda baki sani ba Firstlove Bazai Taba Cin Amana ta ba Domin na Yarda Dashi Fiye da kaina Banda Uwa Bani da Uba..Iyayensa Sune iyayen Goyona Sun Rikeni Tamkar yar da suka Haifa Tun Ranar da na Zo Duniya Firstlove Shi ya Fara Daukana kafin Innata da Babana Goggo Halima da Bakinta Take Fadamin Taga Soyayyata a kwayan Idanuwan Firstlove Tun Ranar dana Zo Duniya..Laila inda Firstlove zai iya Cin Amanata da Tun Tuni yayi..Domin tun ina da Shekara 9 a Duniya ya Tafi London karatu Cikim Jajayen Fata da Turawa masu al"adu da Dabam Dabam...Ammh bai Sauyani ba Ya Jirani Har na Girma Shima Lokacin ya gama karatunsa Auran mu Ya Tabbata Baki Tunanin wanda ya Tsallake zukan Zukan mata Harda Turawa ya Dawo gareni baki kyautatamai zato laila..? Tafada tana kallonta Ido Cikin Ido Ajiyar Zuciya Laaila ta saki kafin tace"Nifa Baki gane mganata ba Ha...'! Nagane Duka Inda kika Dosa..So kike na Cire yardan da nayi ma Firstlove..Toh bari kiji na Yarda da Firstlove Aduk Duniya Shi na Fara yarda Dashi Tunda Ban yi Wayon sanin iyayena ba..Kuma ki sani Firstlove dina Bazai Taba Cin Amanata ba Har gaban Abada Saboda yafi kowa Sona da Sanin Raunina..! Tana Gama Fadar Haka ta tashi ta Fara Tattara Takardunta Laila ta Mike tana Rikota ta Fizge Hannunta Tana Fadin"Stay Away From me Laila..Alaqata Dake bata yiyuba...Juz Leave me..! Daga Haka ta kwashi Littafanta ta bar mata Wajen Laila ta Bita da Kallo Kafin ta kadai afili ta Furta..'Allah yasa Haka Halima..Rauninki na sani Shiyasa nake Tsausayinki Har acikin Raina ban kuma san Dalili ba ina Jin Wani abu acikin Raina mai kama da Tsoro..! *Comments* Share and Vote* *Intelligent Writer"s asso* *Janaftyshakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             0️⃣4️⃣ *#SHEKARUN BAYA..*!   "A kowani Fanni na Rayuwa akwai Cigaba akwai akasinsa Haka Zalika kamar yadda akwai Samu akwai Rashi akwai Nasara akwai Faduwa,kuma Duk Allah Subuhanahu Wata"ala yake Tsara Abunshi kuma ya Tafi yadda ya Tsarashin.   In mukayi Duba da wannan Rayuwar Tamu ta yau da kullum,Allah ya Hallicemu Dabam Dabam ne kuma Rukuni Rukuni Akwai Kasa kasa a Duniya akwai mu kuma Jaha Jaha,Kana kuma sai yazo yayi mu al"adu da kuma Harsuna Dabam Dabam..Sai kuma ya bama wasu Daga Cikinmu ikon Tashi Cikin Addinin musulunci wasu kuma Daga Baya ya basu ikon Zamowa Musulmai akwai kuma Wadanda Yake son ganinsu Haka kuma ahaka ya barsu Tunda Shi din mai Fitar da matacce ne acikin Rayayye kuma mai Fitar da Rayayye acikin matattu. Kamar yadda muka gani ko yatsun Hannunmu ba Daidai Suke ba Wasu sun Dara wasu Toh Haka Abun yake in mukayi Duba da Rayuwarmu ta yau da kullum,Acikin mu akwai masu Tarin Dukiya wadanda bazamu iya Gogan Kafada dasu ba kama Daga wasu yan Siyasa ne wasu kuma yan kasuwa ne masu Tarin Arziki wasu kuma Suna Kasansu ne ma"ana masu Rufin asiri Daidai Gwargwardo Wadanda Suke fin karfin Gidansu Har da Nauyin wasu akansu Wasu kuma iya Nauyin kansu ma Suke iya Dauka yayinda da wasu kuma ko Nauyin kan nasu bazasu iya Dauka ba saboda Halin yau da kullum Ammh Duk da Haka basu Gaza ba ba kuma Suce Allah baya sane dasu ba akowani Hali na Rayuwa Sai dai Su Furta kalmar Godiya Ga Allah ALHAMDULILLAH..! *Dr.Abubakar Bashir Saulawa* Haifaffan Garin Katsina ta Dikko Dakin kara ne,Kuma Haifaffan anguwan nan ta Cikin katsina mai Suna Saulawa,Abubakar ya Taso Dan Gata Cikin Dangi Duk da Tun yana karami ya Tsinci kansa amatsayin maraya ta Bangaran uwa da Uba sakamakon Hadarin Mota sai Rikonsa ya koma Hannun Baffansa Ma"ana Yaya Wajen Mahaifinsa. Shi ya Daukeshi ya Hadashi Cikin ya"yansa Ya inganta Rayuwarsa Tunda alokacin Yana da Halin yin Haka Tunda ma"aikacin gwannati kuma yana Cin Lokacinsa Sosai Abubakar Tun yana karaminsa yake da Burin Zama Likitan kwalkwalwa Sakamakon Labarin Daya samu Kakarsa wacce ta Haifi mahaifiyarsa da Ciwon Hauka Ta Rasu Sai Abun ya Shiga Ransa ya Saki Tasiri Tun Daga Lokacin Yayi ma kanshi alkawarin sai ya zama Likita Ta Bangaran kwakwalwa kodomin Taimakama Talakawa Maraasa karfi Wadanda Suke karewa a Hauka Har su mutu basu samu mai Tallafamusu. Alokacin ba wanda ya Dakatar Dashi kan kudirinsa sai ma Goyon Baya Daya samu Ana Cikin Haka yagama Secondry School Dinsa anan garin na Katsina Lokaci kalilan Baffansa yayi masa Cuku Cukun Samun Gurbi Karatu Awata Medicine School Inda ya Shafi karatun Likitan Kwakwalwa Wato Psychiatric kenan Dake Birnin Delhi India Chan ya Tattara ya Tafi Inda ya Kwashe Shekara Goma achan kafin ya Dawo kasar sa ta Haihu Shima Din Rasuwar Baffansa ne ya Dawo Dashi Tunda Shekara Daya kenan Da kamallah karatunsa  da kuma kananun Cosa cosan Dayai ta Hallata Saboda Cikar Burinsa ya Fara aiki da wani Asibitin kwakwalwa Dake Bangcof  a matsayin Psychiatric Doctor,duk da bashi da Burin aiki a ko"ina sai a kasar sa ta Haihu bai Hanashi Fara aiki Dasu ba Ba domin komai ba Sai Domin yana Bukatar Tsayuwa da Kafafunsa kafin ya koma kasar sa ta Haihu yaga kuma ta ina Zai Bullo Domin Cikar Burinsa na Taimakawa Talakawa ya Tabbata. Ana yin Sadakan Bakwai ya Tattara ya koma Dama Bashi da gado Tunda Da iyayensa Suka Rasu da Abunda ya Gada aka Dinga mai Hidima koda ma Ragowa bai Damu Daya Nema ba alokacin Hankalinshi ya Karkata kan neman Halas Dinsa da kuma yadda Burinsa zai Cika. Yayi gwargwarmaya Sosai kafin Cikar Burin nashi Tunda Sai da ya kara kwashe Shekaru wajen uku achan Bangcof kana ya Dawo Gida Nigeria ya yada Zango a Lagos inda ya Fara da Wani asibitin a Bangaran Masu Laluran kwalkwalwa,bayan nan yayi Tafiye Tafiye zuwa kashashen ketare da bai san iyaka ba Wajen kara sanin kam Abunda ya Shafi masu Laluran kwakwalwa yana Da Shekara 28 a Duniya komai na Bukatar Rayuwa ya mallaka Motar Hawa da Gidan kansa da kuma Wasu kadarori gefe Daya kuma yana Kokarin Taimakama yan"uwan da Dangi. Sai da ya Shekara Talatin   Yan"uwa suka Taso mai kan Mganar Aure Alokacin Shima bai kiba sai ya amince ya Fara Neman Aure sai dai Dayake Tun Farko ba"anan Hankalinsa ya karkata ba Sai ya kasa kawai Daga karshe sai ya basu Zabi Su kuma Suka Zabamai Aminatu Diyar Baffansa Wanda ya Rikesa bai yi gaddama ba ya karba,Duk da Amina itace auta Bai wani Wayeta sosai ba,Saboda Tana karama ya Daga Zuwa Delhi ammh bazai Taba kinta ba ba"a saka Lokacin Bikin da Tsawo ba Tunda Itana Aminar ta gama Secondry School Dinta kenan Mganar Tataso kuma bata ki Dan"uwanta ba Duk da Lokacin ana Ta so a Hure mata kunne ganin Abubakar din ya Riga ya Tazurance bai yi Aure ba ammh Taki Jin kowa Tunda dai Mahaifiyarta ta yarda da mganar kuma yan"uwanta Sun bata Goyon baya Sanin Dr Saulawan Samun kamarsa a wannan Marran sai an Tona. Wata Biyu Tsakani aka Daura Auran Amina da Dr.Abubakar Saulawa,Direct kuma Gidansa Dake Lagos ya wuce da matarsa Tunda ba wani Sha"ani akayi ba Ta Samu Rakiyan yan"uwa da basu gaza Biyar ba,sukaje suka ga Inda Take suka kwana Biyu suka Dawo Suna Musu Fatan zama Lafiya na Har Abada. Alhamdulillah Zamansu na Gudana Cikin kwanciyar Hankali Amina nada matukar Hankali da Natsuwa Shi ma Haka sai suke kokarin Sauke Nauyin Juna Dake kansu,Watansu Biyar da Aure ya Sakata a makaranta Tayi Diploma Dinta Shikuma alokacin yana taCikun Cikun Dawowa Arewa da zama Gabadaya Hakan bai samu ba sai da Suka Shekara Biyu kana Ya samu Babban matsayi a Asibitinn General Hospital Bauchi Ya Tattaro Amina Suka Dawo Garin Bauchi da zama Wanda ya zama kamar garinsu Ciki yayi ya"ya da Jikoki har kuma Babban Burinsa na mallakan Asibitin kansa ya Tabbata. Suna Dawowa Amina ta Fara Laulayin Shigar Ciki Murna Wajen Dr.Saulawa Ba"a mgana yan"uwaa Suna Ta Murna Sosai Dama Ta gama Diplomanta Dayayi mata mganar Cigaban karatunta sai tace ya bari sai ta Haihu Shikuma sai ya kyaleta ganin Tana Fama da Lailayi. Watan Cikin Amina na Shiga Wata Tara ta Haifo Santalelen yaronta Sak mai kama da Dr.Saulawa,Ranar Suna ya Ci Sunan Mahaifin Abubakar Wato BASHIR kuma basu mai wata alkunya da Bashir dinsa Suke Kiransa,Haihuwan Bashir kamar Tazo da wani Budi ne Tuni Sunan Dr Saulawa yayi Fice agarin Bauchi Da kewaye Duk inda ake nenan Likitan kwakwalwa Wanda ya kware a aikinsa Shi ake nema kuma yana Taimakawa gwargwardon ikonsa Ya Hallaci Seminar Seminar ba adadi,Kuma Sunansa yayi Fice Tunda Har ya goggayan Da manyan Likitoci,Tarruka na mussaman na karama Juna sani Duk yana Hallata Saboda Sanin irin gwazonsa da kuma irin yadda yake aikinsa da Jarjircya Hatta Asibitin na General ta san da zaman Dr.Saulawa Wanda Abubakar din ya bace sai dai kaji Ana Kiran Dr.Saulawa. Bashir Nada Shekara Uku Duniya Amina ta kara samun Wani Cikin Lokacin ma Dr.Saulawa na Shirin nema mata makaranta ne sai kuma ga wani Cikin bai nuna komai ba Sai Jin Dadin Domin yace yafi son Haka yadda ya Dade bai yi Aure ba yana so kafin karfinsa ya kare ya"yansa Su more Lokacinsa Kamar kuwa ya amsa gaban yan Ameen Bayan Bashir Sai Kuma aka samu USMAN,Daganan Haihuwa ta Bude ma Amina ba Daga Kafa Daga Usman Sai Tayi ALIYU sai kuma ta Sirka ma Mata Tayi HANNATU sai kuma Tayi Autarta Ta karshe Wacce Daga Ita bata kara Haihuwa ba RUKAYYAHTU. Da wadanan Ya"ya Biyar din Dr.Saulawa ya Godema Allah Suka Cigaba da Rayuwarsu Suna Tarbiyantan da ya"yansu Zuwa Lokacin Allah Duk Ya Dauki Sauran iyayen nasu Mata Sai suka Rumgumi maraicinsu Su da Amina Suna Cigaba da Rayuwarsu gefe daya kuma suna Bama ya"yansu Duka kulawansu. ***** *Shekaru Talatin da suka Shude..* Zuwa Lokacin Zan iya cewa Duka Buri da kuma Fata na Dr Saulawa ya Cika Domin ya Kamallah Ginin Kayattacen asibitinsa mai Suna SAULAWA SPECIALIST HOSPITAL BAUCHI...! ya kuma Gina wani katafaren Gida a GRA gida ne Ginin zamani mai kyau da Tsari Tunda Duka yayansa Sun Girma Bashir Shine Babba Chemical engneering  yayi sai Usman Wanda ya karanci Fannin Na"ura sai Aliyu Wanda Karanci karantun Lauya,,Hannatu da Rukkaya kuma kowace Tayi Aurenta Tana Cigaba da karatunta a Dakim Mijinta. Rukayyah Tayi Aure agarin Kanon Ta Dabo ne,Tana Auran wani Dan Siyasa ne sai Hannatu Wacce ta Lula garin lagos Tana Auran wani Dan Canji ne Dukkansu sun gama Degree dinsu Basa dai aiki ammh kowacce Tana Kasuwancinta ta Tsaya da Kafafunta. Dr.Saulawa yaso Dayan Burin nashi ya Cika Na samun Daya Daga Cikin ya"yansa wani ya gajeshi ya zama Likita koda ta wani Bangaren ne ba Bangaransa ba Ammh kana naka Allah na nashi ne,Hakan bai samu Tunda Duka ya"yansa Nashi basu da wannan Ra"ayin sai ya kyalesu ya Binne abun Aransa yana Tunanin inda da Rai da Rabo Allah zai cikamai Burinsa ko ba akan ya"yansa ba akan Jikokinsa da zai samu ta Tsatsansu Tunda shi karfinsa karewa yake bawai Raguwa ba. Asibitin Daya Gina ya samu karbuwa Domin ya samu Shawara da kuma Taimakon manyan Likitocin Duniya musamman Likitocin kwakwalwa Shashi Guda aka Bude acikin Asibitin Saboda masu Wannan Fanni Dr. Saulawa da kansa yake Attending Din patient dinsa Sauran Bangarorin kuma ya kawo Likitoci Masu kwarewa Da Taimakon Abokan aikinsa da Abokan karatunsa da kuma yan"uwansa Harda Taimakon ya"yansa Dana Matarsa Tunda Da Farko yana ganin kamar bazai iya ba Sai kuma gashi Da Taimakon Allah da kuma ganin Niyyarsa komai ya zama Sai Tarihi. Dr.Saulawa Mutam ne nagari kuma Mai Daraja acikin Idanun Mutane da suka sansu su kuma San Labarinsa,Game da ma"aikatan Gidansa Shi mai Kirki game da Likitocin Dake aiki Dashi asibiti Mai kirki ne kama Daga ma"ikatan lafiya zuwa masu matsayin Aikin Share Share da goge goge da kuma Masu kula da Shige Da Fice Duka Sun Shaida Dr Saulawa mai Kima ne Haka game da patient dinsa zakayi mamakin ganin yadda yake Tafiyar dasu ba kyama ba wani Girman kai Zai koma Kamrsu Suma Ya Shiga Cikinsu Domin mema musu lafiya Shiyasa Lokacin kalilan indai Haukan naka bq Tuburan bane Dr Saulawa zai Taimaka wajen Dawowa Dakai Cikin Hayyacinsa awannan Fanni Shi kwararre ne kuma Haziki ne. Dr.Saulawa yana da Wani Megadi Wanda yake gadin Gidansa Mai Suna Mallam Umar  Gada Wanda Dan asalinsa Haifaffan Garin Gada ne Dake Jahar ta Sokkoton Shehu,Talauci da kuma neman kudi ya barosa da Garinsa da ya"yansa zuwa Garin Bauchi yayi gadi a gidajen masu kudi Dadama da yan Siyasa bai ji Dadi ba Sai da Allah ya Hadashi da Likitan kwarai likitan Takalawa Wato Dr.Abubakar Bashir Saulawa Ya Bugeshi da Mota Lokacin yana Kokarin Komawa garinsu ne wajen iyalansa Abun ya Faru,Dr Saulawa ya Dinga Kula da Mallam Umar a asibitinsa Duk da bai wani ji Rauni ba Karaya ce da Gocewar kashi,Dashi da matarsa Hajiya Amina Wacce Mijinta da ya"yanta ke Kiranta Hajiya Mama Sunsha Dawainiya Dashi Bayan an sallameshi Dr.Saulawa da Matarsa Suka Dauki Mallam Umar har garin gada suka sadashi da Danginsa da Iyalansa. Wannan Abun Da yayi ma Mallam Umar Shi ya karamai kima adanuwansa da kuma na Danginsa dana iyalansa Bakinsa ya Dinga Fadin Alherin Dakta Garesu,domin Da suka maidosa Gida bai barsu Haka ba sai da yayi musu Sha Tara na arziki balle ganinsu Cikin Halin Talauci da Wahalan Rayuwa Abun bai Tssya nan ba kowani Lokaci in Dr Saulawa ya samu lokaci zai zo ya Duba Jikin Mallam Umar kuma baya zuwa Hannu Rabbana kafin Mallam Umar ya warke yaga karammawa da kuma Karancin Irin na Likitan Mai Hangen nesa da Taimakon Takalawa ba Shi kadai ba yan"uwansa ma Suna yaban Hallin kirki irin na Dr Saulawa da matarsa. Bayan Mallam Umar ya Warke sai Dr.Saulawa yazo ya zauna Dashi anan ne ya Fahimci ba wata kwakwaran Sa"ana da kuma Dalilin Daya kaishi Garin Bauchi Jin Haka yasa sai Dr Saulawa yace in bazai Damu ba yazo Gidansa ya Zauna Shida iyalansa Da matarsa Allah barshi sai ya Dinga Mishi gadi matarsa kuma ta Rika Shiga Tana Taimakama Amina Tunda Bai yi karatun Boko ba Ballatana ya Taimakamai ta wani Fannin. Wannan Albishir din yafi komai yima Mallam Umar Dadi Yan"uwansa ma Sun Tayashi Murna,cikin Abunda bai fi Sati Daya ba Dr.Saulawa ya Turo Mota aka kwasheshi Shida Matarsa Atine da kuma Dansa kwara Daya Daya mallaka Abdullahi Zuwa Bauchi Gidan Dr.Saulawa aka kuma Saukesu a Shashin Boysquaters Inda Aka Jikasu da komai na Bukatan Rayuwa Mallam Umar da Matarsa Atine suna kuka suna ma Dr Saulawa Godiya na Irin karamcinsu garesu shi kuma yana Fadin karsu Damu. Mallam Umar shi ya Cigaba da gadin Gidan Dr.Saulawa awanchan Lokacin bayan ya sallami megadinsa Dama Buzu ne, zai koma garinsu,Cikin Jin Dadi da kuma Cigaban Rayuwa ita kuma Atine ta zama yar gida Tunda Ta zama yar Dakin Hajiya Amina kusan a Shashensu Take wuni Abdullahi kuma anyi anyk a sakashi makaranta Boko yaki wai karatun allo yake so ganin Haka yasa mallam Umar ya Tattarasa ya maida gada inda chan aka kaishi argungu yana Makarantar allon Dayace Ita yake so. ******** *Bayan Shekaru Biyar..!* Abubuwa Dadama sun Faru Cikin Gudun wannan Shekarun Ciki kuwa Harda kamallah Duka karatun Ya"yan Dr.Saulawa Duka Zaratan mazan nasu Wadanda Dukkansu suke da Qualification din Masters dinsu  Wato Bashir ne Babba wanda ya Samu aiki agarin kaduna A Refenaring,sai Usman Wanda Ke Bimasa Wanda Shi ya samu aiki a anan garin Bauchi a wata ma"ikata Inda Suke Wallafa Littafan karatun na makarantu Dabam Dabam a matsayin Manajansu sai Karamin su Aliyu Wanda Shine Lauya Mai zaman kansa. Dukkansu sun yi Aure Sai Dai Aliyu ya Rigasu yin Aure da Matarsa Safiya,suna Zaune agarin Abuja,Sai Usman Wanda Dr.Saulawa ya Aurama Mata Biyu arana Daya Wato Fatima da Aisha kuma Dukkansu yan garin Bauchi ne Wadanda Dr.Saulawa yayi zaman Amana da iyayensu,kuma yaji yana Sha"awar Hada zumunci da ya"yansa da Farko Fatima ce ta Usman Aisha Ta Bashir ce wanda ko kafin Dr.Saulawa ya gabatar da ita ya Riga ya gabatar da matar da zai Aura Iklima Wacce itama yar Kaduna garin gwammace Koda Dr.Saulawa ya Kawo maganar Aisha sai Bashir din ya Nuna Ita Iklima din yake so sai ya kyaleshi Ganin ya Riga kuma ya Furtamai iyayen Ita Aisha sai ya Nemi Usman din Daya Hadasu Duka Biyun ya aura bai yi gaddama ba ya amince Dr.Saulawa ya Aura masa Fatima da Aisha Arana Daya Bashir kuma sai bayan Shakara Daya da wani Abu da Auran Usman kana yayi Auransa Tunda Daman Shi Duk yafi su akidan Boko ita kanta Ikliman yar Boko ce Tunda itama ma"ikaciyar gwamnatice. Usman yana Zaune nan GRA inda ya Gina Gidansa kusa da iyayensa Tunda Shi kadai ne ke Zaune garin Bauchi sai yaga gwara ya zauna kusa da iyayensa Tunda Shi kanshi babu wasu Dangi Duk Sun kare ammh Har yau bai manta da garin katsina ba yana zuwa kuma Hannunsa na kaiwa nan yake Zaune Shi da Matansa Tamkar Tagwaye Wato Fatima da Aisha. Ayayinda Bashir ke garim kaduna Shima ya mallaki gidan Kansa da Motar Hawa haka ma Matarsa nada Motarta Sai Aliyu Barrister kenan yana Zaune agarin Abuja Shida matarsa Safiya Suna Zaune a Maitama Abuja Shima Din ya mallaki gidan kanshi Da Motar Hawa Rayuwa Dai ta inga Su Rukayyah kuwa da Hannatu kowacce Tana Gidan Mijinta ta Haiyayyafa Suna kuma Cikin Jin Dadi sai wanda ya gani. Dr.Abubakar Saulawa ya Samu Duka Cikar Burinsa Shiyasa Shekara na Zagayowa ya Tattara Duka iyalansa da matansu sukaje kasa mai Tsarki suka Sauke Farali,Shi dai Dr Saulawa da Hajiya mama Gida suka Dawo Ammh Su Bashir Kowanne kasar Dayake Muradi ya Wuce Shi da iyalansa Haka ma Su Rukayyah kowacce da Mijinta da ya"yanta Tun a Saudiya sukayi sallama da Junansu kowanne ya yada Zango a Inda ya Tsara zashi Su dai su Rukayyah da Hannatu da Mazajensu sun koma Gida da Wuri ammh Su Usman kam sai da Dr.Saulawa ya Dinga Musu waya yana Fadin Sun bar ayyukansu sun je wani kasa Sun Tare,Maza su Tarkato su Dawo wannan Dalilin yasa suka Tattaro Suka Dawo Kasar su ta Haihuwa kowanne na amsa Sunan Alhaji matansu ma na amsa Sunan Hajiya. Duk acikinsu Matan Usman ne suka Fara samun Ciki Wato Fatima da Aisha kuma duk atare,Murnan wajen wannan Ahali ba"a mgana barin ma Dr.Saulawa Farinciki ya Cikashi zai Fara samun Jikoki,samuwar Cikinsu da Wata Biyar sai ga Wani albishir din Safiya ma Matar Barrister Aliyu itama ta Harbu Sai Farincikin ya ninku,Bashir dai Shuru Dama Shi yace Tsarin iyali zasu yi ba yanzu zasu Fara Haihuwa ba sai zuwa gaba koma sun Fara 3 Childeeen ya Ishesu. Samuwar Cikin Fatima da Aisha Sai kuma Lalura ta karu gasu dama su kadai agidan ba yar aiki Tunda Tun Farko sun Nuna basu bukatar Wata yar aiki su Zasu Dinga aikinsu da kansu,sai kuma ga Samuwar Cikinsu Lokaci Daya kuma Dukkansu Suna Fama da lailayi sai Hankali Alhaji Usman ya Tashi kwarai yaje ma da Hajiya mama da Batun Samun mai Taimaka ma su Fatima kafin komai ya Daidaita ita kuma sai ta gayama Dr.Saulawa Batun Shi kuma sai yace Abun bana gaggawa bane gwara a tsaya a samu mai amana Tunda zata zauna da iyalansa ne. Da wannan Mganar Alhaji Usman ya bar komai a Hannun Dr.Saulawa Da Hajiya Mama kwatsam Atine taji Hajiya Maman na Zencen sai tayi karaf tace In suna so ga Matar Dansu Abdullahi wanda yayi Aure Shekaru Uku da suka gabata ya Gaba Karatun allo ya koma Gada ya Fara Sa"anan sai da kayan Dinki Wanda Dr.Saulawan ne ya Tankamai Jali Tunda yaki Karatu kuma Har yau har gobe akwai amana Tsakaninsa da Mallam Umar da iyalansa Atine kuma ta zama kamar yar gida. Wannan Mganar ta Atine Hajiya Mama ta kaima Dr.Saulawa Shi kuma yayi Na"am acewar Iyalan Mallam Umar Abun so ne Takalawa ne masu Wadatar Zucci da Dr.Saulawa ya Tuntubi Mallam Umar gada da mganar sai yaso yamusa saboda yace Kada Maryama Tayi Nesa da Mijinta Jin haka yasa Dr.Saulawa yace kada ya Damu Duka da Maryama da Abdullahin Zasu dawo nan gidan Usman da zama kamar yadda shi da atine suke zaume agidansa Dama yaji Usman Din na neman mai kula mai da Kifayen Dayake Kiwo Faduwa tazo Daidai da zama Mallam Umar Bai iya mgana ba,sai Godiya kamar yayi kuka na Karamcin Dr.Saulawa agaresu. Koda Dr.Saulawa ya Tuntubi Usman da mganar bai yi gaddama ba Saboda Baba Atine kamar Wata Babba yaya Suka Dauketa Shi kanshi Mallam Umar ba"a Matsayin Megadi suke kallonsa ba Suna Kallonsa ne Kamar kanin Mahaifinsu Baba Umaru ma Suke Kiranshi Batare da bata Lokaci ba Dr Saulawa ya Saka Mallam Umar ya Kiramai Abdullahi sukayi mgana Dayaji labari murna ta Cikashi Dama Tun bayan da yagama Almajirancinsa ya Dawo Bayan yayi Sauka ya Dinga Nadamar kin karatun Boko da yayi Tunda ya Fahimci yanzu Rayuwat bata Tafiya sai da Duka Fuka fukan Biyu gashi kuma Lokaci ya kuremai Dole dai Kanwar naki ya zauna chan Babban Gidansu a Gada ya Auri Wata yar"uwansa Maryama Bayan Dr.Saulawa ya Tankamai Jali ya Fara Sana"an kayan Miyan Jin wannan Rokon alfarman ta Dr Saulawa Sai Abdullahi yaji kamar an sakashi a aljannah ko kwana Uku basu yi ba ya Tattaro maryama Zuwa Bauchi bayan yayi sallama da Yan"uwansa ita kuma maryama Tayi sallama da yar"uwanta kwara Daya Tal aduniya wato Halima wacce ke Aure a nan garin Gada. Direct Gidan Alhaji Usman aka yi musu masauki,awani Shashe Dake gefe wanda bama Boysquaters bane Flat mai kyau aka kuma ingantasu da komai na More Rayuwa,Babu Abunda zasu iya cema Iyalan Dr.Saulawa sai Fatan gamawa da Duniya Lafiya,Cikin ikon Allah Maryama ta zama mai Taimakama Fatima da Aisha Duk da kasancewarta yarinya Domin Lokacin bata wuce Shekara 19 ba ammh akwai kwazo na matan kauye da kuma Biyayyah gata Shuru Shuru ba Ruwanta ga kwaici ga kunya,Anty Fatima Anty Aisha Sama Shi kuma Alhaji Usman Daga ita Har Abdullahi Yaya Suke Kiranshi yayinda Suke Kiran Dr Saulawa da Alhaji Dr. Ayayinda Gefe Daya kuma Abdullahi na Cigaba da kula da Kifayen da Alhaji Usman ke kiwo aikinsa kenan,Gidan Dr.Saulawa kuwa kowani Lokaci Suna Zuwa Shida Maryama Domin ganawa da iyayensa Danginsu na chan gada kan kawo musu Ziyara Lokaci Bayan Lokaci Ita ma Maryama Yayarta Halima tazo Taga inda take ta Dinga murna da Fatan alheri Ganin Maryama ta samu iyayen Daki na Gari Tunda Daga Fatima Har Aisha Suna matukar Tsausayin Fatima Shiyasa komai suka samu itace Shi kanshi Alhaji Usman din kallonta yake kamar Hannatu ko Rukayyah Shiyasa suka Rikesu Hannun Bibbiyu tun Bale ma Dr.Saulawa wanda akullun Usman yaje gaisheshi sai yayi Fadan Kula da Hakkokin mutanen Dake kansa Tunda Tamkar Amanace gareshi. Sannu Sannu Bata Hana zuwa sai dai Adade ba"a je ba Cikin Hajiya Fatima da Hajiya Aisha na kara Girma suna kuma samun Dukkan kulawa Domin Likita guda Dr.Saulawa Ya samu Daga asibitinsa tana Zuwa Duk bayan 4 weekes Tana Dubasu Tana musu awo Hankalinsu kwance Har Cikinsu ya Shiga Watan Haihuwa Wata Ranar Jumma"a Babba Rana Allah ya Saukeki Hajiya Fatima Lafiya inda ta Haifi santalelen Danta mai kama da Dr Saulawa,ko Mintuna Talatin ba"ayi ba itama yar"uwanta Hajiya Aisha ta Haifi Santaleliyar yarta mace mai kama da Alhaji Usman acikin asibitin Daya ke mallakin Surukinsu Wato Saulawa Speacialist Hosp Bauchi. Dama Hajiya Fatima na Fara mukurkusun naguda Abu kamar wasa Maryama ta Kira Hajiya mama ta gayamata Tunda Alhaji Usman baya Gida Ita tazo Da Direba ita da Atine Bayan ta Kira Dr.Saulawa yace ta kawosu nan asibitin yanzu,kamar wasa fa Harda Hajiya Aishan da Maryama Suka Shiga Motar zuwa asibiti sai dai kafin su kai asibitin Itama Hajiya Aishan Ta Fara Nagudan maimakon Hajiya Fatima Sai Dr Saulawa yaga Duka Surukan nashi ne ke kan gwiwa ganin haka yasa aka Shiga Dasu Bangaransu masu Haihuwa Domin basu Taimakon gaggawa. Haihuwan batayi Tambari ba Sai da aka gama Shirya masu Jego da yaran kana Hajiya mama ta Shiga kiran Waya tana Fadan Haihuwa murna ba"a mgana Alhaji Usman haka yazo asibitin kamar bakinsa zai Yage saboda Murna Maryama ita ke Tare da masu jegon a Dakin Hutu kuma Duka Jariran na Hannunta itama bakinta yaki Rufuwa iyayen Dakinta sun Haihu... Atare da Dr.Saulawa da D'ansa Alhaji Usman Suka Shigo Dakin na musamman da aka Kai su Hajiya Fatima,Hajiya mama da Atine na Binsu abaya suna Shiga bayan sannu da Barka daya Biyo baya sai Dr.Saulawa ya kalli Maryama yana Fadin"Maryama Mikominsu nan naji Dumin Jikokina..Allah yakai Raina.! Tana Mirmishintaa na kunya ta Tashi Ta mikamai Su Duka ya Hada ya Dauka Har Hajiya Mama namai Tsiyan bai bari Uban Yara ya Dauka ba yayi mirmishi yana Fadin"Nima Uba nake garesu Amina..Ko ba Haka ba Usman Bin Fodiyo..? Dariya yayi yana Fadin"Kwarai Abba..Tabbatas kai Uba kake garesu kai zaka musu Hudubu yanzu yanzu ka Sa ka musu Sunan da kaga yayi maka..Ai Dani da Matana Da ya"yan Dana Haifa duk ikon ka ne..! Kowa Mirmishi yake adakin Dr.Saulawa ya kalleshi yana Fadin"Allah yayi maka albarka kaida Matanka Usman Fodiyo..! Duka suka amsa da Ameen kujera Usman ya bashi ya Zauna ya Fara Daga macen ya mata Huduba aduka kunnuwanta kana ya Matsamata Dabino a baki kana ya mikama Usman yana Fadin"Allah ya Raya ZAREENA USMAN ABUBAKAR SAULAWA..! Ya karbeta yana Fadin"Masha Allah Ameen Ameen Abba.."Namijin ya Daga Shima yayi mai Huduba kuma ya Bashi Dabino Shi harda Ruwan zamzam ya mikama Alhaji Usman yana Fadin"Wannan yaron Magaji na ne..Tun a Suna na sakamai DR.ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA..Allah ya Rayamana Shi.." Gabadayansu suka amsa da Ameen kafin ya mike Alhaji Usman ya mikama Hajiya mama Jaririan ta Dauka kana ta mikama Atine itama ta Dauka ta saka Albarka kana ta mikama Maryama su Wanda Ta Nufi Hajiya Fatima Ta mika mata Zainullahi sai taki karba sai kawai ta saka Hannu Ta karbi Zareena Tana Fadin"Nifa ga yata nan..Mikama Aisha yaronta..! Kowa sai ya saki baki yana kallonta Jin Haka yasa Hajiya Aisha Tace"Naji bakomai..Maryama Mikomin Da'na..Dama mun Riga mun gama mgana nayi miki alkawarin in mace na Haifa taki ce Har Abada ke kuma in kika Haifi Namiji nawa ne Har Abada..Allah ya cikamana Burinmu sai dai muyi Fatan Allah ya tayamu Tarbiya..! Maryama Tana Mirmishi Tace"Nice Shaida..Ni kuma nayi alkawarin Tayaku kula dasu Tankamar ya"yan da zan Haifa da Cikina..! Gabadaya Dakin suka amsa da Ameen Mirmishin Farinciki da kuma Annushuwa ya wanzu a zuciyar Dr.Saulawa hakama Hajiya Mama da Atine Shi kuwa Alhaji Usman mamaki ya kamashi na yarda har suka Tsaida wannan alkawarin bai sani Hadin kan matanshi na Burgeshi kuma yana jin Duk Duniya ba wanda yakai shi Dace.. *Comments* *Share and vote* *Shakira...* *Intelligent writer"s asso...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             0️⃣5️⃣ "Dr.Abubakar Saulawa yafi kowa Murna da wannan Sabon Hadin kai Tare da alkawarin Dake Tsakanin Hajiya Fatima da Hajiya Aisha,sai dai kuma ya katse musu Hanzari Wajen basu Umarnin kowacce ta Shayar da Abunda ta Haifa da kanta Ammh alkawarinsu na nan bai Tashi ba Da Suka nemi sanin Dalili sai yace musu Saboda Halin Rayuwa Ko bakomai Tunda Dukkansu Suna Raye ya Zama Dole kowacce ta Shayar da Abunda ta Haifa da wannan matsayar aka Tsaya Inda aka Mikama Fatima Zainullahi ta Shayar dashi Ita kuma Aisha aka Mika mata Zareena ta bata Nono kuma Dukkansu suka kama Bayan Sun gama ba Jaririnansu Nono ne bayan sun Samu Natsuwa aka Sallamesu suka Dunguma Zuwa Gida Cikin Tsantsan Farincikin da baki bazai iya Furta shi ba. Kafin kace kwabo Haihuwan Tagama Karade Dangi kafin Suna ta Zagayo yan"uwa na Nesa Dana Kusa Sun iso kamar su Hannatu da Rukayyah Bashir da iyalansa Hakama Aliyu Shima Da nashi Iyalin Wacce Itama Cikinta Dan Kimanin Wata Shida ya bayyyana Dukkansu Sun Taru Domin Taya Dan"uwansu Murna samun karuwar ya"ya a karo na Biyu bayan Matansa Daya Aura Rana Daya. Ranar suna ansha Shagali Abunda sai wanda ya gani bayan Raguna Harda sa Dr.Saulawa ya sa aka Kada Saboda Haihuwan Jikokinsa aka Rabama Takalawa kowa fa ya Shaida wannan Haihun matuka kuma kowa ya Fahimci yadda Dr Saulawa ya Dauki Haihuwan da matukar Muhimmanci Shi da Hajiya Mama. Bayan Suna Baki da yan'uwa kowa ya koma Gidajensa aka bar masu Jego Maryama na Tare Dasu na Kula da yara Sai kuma Atine Dake zuwa Tana yima Su Hajiya Fatima wankan Tare da Umarnin Hajiya Mama ganin Maryam bawata Babbace bace Sai aka bar mata kula da yaran Wanda ko yake Kiransu da yan Biyu ganin Rana Daya suka Zo Duniya Kuma Duk da kowa Uwarsa ke Shayar dashi Ammh Da Zarar Kowacce ta gama Shayar da nata Hajiya Fatima Zata Karbe Zareena Itama Hajiya Aisha Zata karbi Zainullahi Har suna Rige Rige Wani Lokacin Maryama Ke ganin Dirarmar nasu Tayi ta bama Alhaji Usman in ya Dawo Labari Shi kuwa yana Jin Labari Nishadi da kaunar matan nashi na Kara Wutar Ruruwa acikin Ranshi... Wata Hudu da Haihuwan su Zareena Safiya Matar Aliyu ta Sauka achan Abuja Ta Haifi Santalelen Danta Jajir mai kama da Ubansa Wannan karon ma Dr.Saulawa ya Saka mai Suna Wato HADDIR ALIYU ABUBAKAR SAULAWA..! Tun Daga sannan kuma Babu Wata karuwa da aka Kara samu Sai Duka Suka maida Hankulansu Wajen kula da yaran da Allah ya basu,Bangaran su Zareena da Zainullahi kuwa Maryama ce keda alhakin kula dasu Har ma Sun Saba da ita,domin itace komai nasu Wankansu Saka musu kaya kula da Cin Abincinsu da kuma Cire Musu pampers in sun bata Duka itace Lokaci kadan Yaran suka Shaku da ita Bama Ita kadai Harda Abdullahi mijinta Sun Shaku Dashi Domin In Tagama aikinta Sassan su Hajiya Fatima kwasan Yaran take su koma Barayinsu Su tayi ta kula Dasu Ita da Abdullahi Tunda Shima ba wani aikin yake ba kula da Kifaye ne,da basu abinci Safe da Yammah Da ka gansu zaka Fahimci Suna Cikin Farinciki da Jin Dadin Rayuwa. Bashir Bai Haihu ba Sai da su Zareeena Suka Shekara Biyar a Duniya Yayinda Haddir keda Hudu da wani Abun Sun Girma Babu Inda kafarsu bata takawa Har an sakasu a Makaranta,Lokacin da Iklima ta Haihu Tasha Wuya Sai kuma Jaririn ya Fito bashi da lafiya haka akayi Suna yaro yaci Sunan Dr Saulawa Wato Abubakar bai kai Wata Biyar ba Allah yamai Rasuwa Tun kuma Daga Lokacin sai ya koma in ta Samu Ciki Sai ta Dinga Barinsa Ko kuma Sai yakai Wata bakwai ta Haifeshi Ba Rai,Sakamakon Ita Ikliman Binciken Likitoci Sun gano Tana da Raunin Mahaifa Sosai Gashi kuma ta Fara Palanning kafin Ta Haihu Shi ya jawo mata matsalan Bashir ya Damu Sosai Domin a Lokacin yana Bukatar Haihuwar ammh kuma Sai Allah ya Nuna ikonsa Dole babu yadda Suka iya suka koma Suka Rungumi Junansu Tunda bai isa ya Gujema Ikliman ba Koma meya Faru Shine Silan komai. Su Zareena Da Zain nada Shekara Bakwai Aduniya Zain kamar yadda Zareena Take Kiranshi Tunda bakinta bai iya furta Zainullahi din Sosai ba,sai Sunan Gabadaya yabi bakin iyayen nasu kowa da Zain yake Kiransa Ita kuma Hajiya Aisha Zain ne Tunda ya Fara koyon mgana ya Fara Kiranta da NENE shikenan kuma Sunan ya Bita ayayinda Zareena ke kiran Hajiya Fatima da UMMAN ZAREENA,saboda yadda Duk Duniya Hajiya Fatima Bata da Abun kauna da Tattali Irin Zareena Shiyasa Dr Salauwa Ya sakamata Umman Zareena sai kuma ya Bita har ya"yan suka kama Maryama kuma Mama maryama Abdullahi kuma Suna Kiranshi da Baba ne ayayinda Suke Kiran Alhaji Usman da Abba Tun Suna yara. Duk da kowa ya Fahimci mahaifiyarsa ammh yarintarsu bai Hana Sun Fahimci inda suka Fi Samun kulawa ba,Kowanne sai ya fi Nuna Doki ga inda akafi Jansa ajiki,Zain yafi Son Nene Saboda itace komai nashi Sai ko Mama Maryama Umma Zareena kuwa komai ta samu yarta ce Zareena Ko ta kan Zain bata Bi Tana mai alkunyar dan Fari da kuma Kawaicin Nuna ita Zareena ce yarta Da Farko Zain Din ya Fara nuna Damuwarsa Sai kuma Daga Baya da Nene itama Ta Tare komai nashi Sai Shima ya koma Tamkar itace ta Haifesa ba Umma ba. Mama maryama kuwa Tamkar Uwa Haka Suka Dauketa Domin Itace Komai nasu Sun Taso Sun ganta ne Ita da Baba Abdullahi sai suke kallonsu kamar wasu iyayensu kuma na Dabam Tunda Watarana ma nan Shashen Maryama Suke kwana In Tatashi aikinta Daga Cikin Gidansu zata Shashenta sai su makale mata Sai Sun Bita su kuma iyayen suce Tatafi Dasu Haka zasu Bita suje chan suyi ta Kirniya Abdullahi na Biye Musu Har barci ya Daukesu Maryama ta kwashesu zuwa kan gado ta kwantar Dasu bayan tayi musu addu"an Barci Cikin so da kulawa. Gidan Dr Saulawa kuwa Suna yawan Zuwa Musu Weekend ko Hutu Duk su nasu baya Wani Dadewa Suna kusa da gidan iyayensu Haddir ne kulafunci Zuwa Hutu Bauchi Saboda Su Zain Wadanda Tun Suna Yara mafarin Abotansu ta Fara Su ukun Haka mafarin Rayuwarsu Ta Fara Da Shakuwa da kaunar Juna Barin Ma Zain da Zareena Tamkar yan Biyu haka suke wanu bai isa ya Taba Wani ba acikinsu Hakama Haddir sunfi Shakuwa da Zain sosai kan Zareena,ita Suna yawan Fada Tunda Tana ganin yana so ya nuna yafita son zain sai suyi ta Fada Sai Maryama ta Raba Fadan ko kuma Chan Gidan Hajiya Mama ko Atine su Raba Tsiyan Da karfi da yaji Haddir ya Dawo Bauchi yaki Abuja Dr.Saulawa yace su kyaleshi cikin yan"uwansa Dole suka barshi Alhaji Usman ya Dauki Haddir ya sakashi makarantar da  su zain suke zuwa mai Suna International School Bauchi,Iyayensa basu wani Damu ba Tunda Lokacin Safiya Tana Goyon yarta mace Da Ta sake Haihuwa mai Suna Hamdiya. Kwatsam Megadin Gidan Alhaji Usman yazo ya sameshi kan Zai ijiye aikinsa yana so ya koma Garinsu Mahaifinsa bai da lafiya karfi ya karemai zai koma yayi Jinyarsa Hakika Alhaji Usman Yaji ba Dadi Saboda Sun Saba Da Yusha"u megadi ammh Uba ya wuce wasa Hakanan yayi mishi Fatan samun Lafiya ga Mahaifinsa kuma ya Hadamai Sha Tara na arziki Suka Rabu Faruwar haka sai Alhaji Usman ya Fara Tunanin Samun wani Megadin Jin haka yasa Maryama ta Shawarci Mijinta kan me zai Hana Shi ya karbi Gadin Yayi Tunda dai ba wani aiki yake yi ba karamcin Su Alhaji Garesu yasa Ya amince mata kuma ya samu Alhaji Usman din da mganar da Farko yaso yaki Tunda ya Nuna Tamkar kani ya Dauke Abdullahi Shi kuma ya Dake sai yayi mgana dai Har ta kai ga Dr.Saulawa Da Mallam Umar Shi Mallam Umar shi ya kashe mganar inda yace Sai dai In Usman bai yarda da Abdullahi ba Ammh in ya yarda Dashi ya barshi yayi mai gadin Tunda Ba wani Abu yake ba Dole Alhaji Usman ya Amince ammh Har Cikin Zuciyarsa baya Kallon Abdullahi Da maryama wasu Bare yana kallonsu nr amatsayin Wasu Shakikan yan"uwansa.. Faruwar  Haka da wasu Wattani Ciwon Daji mai Tsanani ya kwantar da Mallan Umar da Farko Abun kamar Ba Ciwon Daji ba Sai da Dr.Saulawa yayi ta Shige Da Fice dashi a asibiti kana aka Fahinci Ciwon nashi Duk da kokarin da Dr Saulawa ya Dinga yi Bai Hana Mallam Umar Rokon alfarman Su barshi ya koma ga Ahalinsa yayi Jinyar achan ba,Yana Tunanin Ciwonsa bana Tashi bane Da Farko yaki Sauraransa ammh ganin yadda ya dinga Rokonsa sai bai ki ba Lokacin da Mallam Umar da Atine zasu koma Gada da Zama Gabadaya Ahalin Dr.Saulawa Sun Girgiza Sakamakon Sabo Ammh ba yadda zasu yi Tunda Mallam Umar ya nuna musu ko basu ga Abdullahi da Maryama nan Tare dasu kuma in da Rai ba"a Rabu ba. Suna ji suna gani Haka zamansu ya yanke a garin Bauchi Ashe kuma ta Har Abada ne,Da komawarsu Garin Gada da Rasuwar mallam Umar Kwana Ashirin ne yace ga garinku ne hakika ba Yan"uwan Mallam Umar kadai sukai Rashi ba Hadda Dr.Saulawa da Duka iyalansa,domin dasu akayi zaman gaisuwar har akayi bakwai Saboda Atine wacce Tunda Taji Mutuwar Mijinta ta yanke jiki ta Fadi ko da ta Farfado ba Baki Ance Jininta ne yayi bala"in Hawa. Bayan addu"ar Bakwai su Hajiya Mama suka Dawo Bauchi Harda Abdullahi da Maryama Saboda Yara,Wanda Suna Gida Tare da iyayensu sai dai suna Ta Kuka da kiran sunan maryama din Da Abdullahi,Allah mai Gagara Misali Rasuwar mallam Umar da Wata Biyu itama Atine ta Bisa kuma ta Rasu ne Akarkashin Kulawan Likitocin asibitin na Dr Saulawa Tunda yaje garin yaga Halin Datake Ciki ya Daukota ashe bazatayi Tsawon Rai ba Duka Duka kwanta Biyu a asibitin tace ga garinsu nan. Duka Chan suka Tafi Gada Tunda Dangin nata sun Nuna Chan suke so ayi mata Sutura Hakika Hajiya mama tafi kowa jin Mutuwar Atine awannan karon sai kuwa Abdullahi Daya Dawo Maraya Sadakar uku kawai Sukayi suka Dawo ammh Sun bar Abdullahi da Maryama achan sai da akayi bakwai suka koma Cike da alhinin Rasa Iyayen nasu Domin Ita kanta Maryama Bayan yayarta Halima bata da kowa sai iyayen Mijinta Abdullahi. Bayan Dawowarsu ne kuma Umma Zareena ta Fara Laulayin Ciki wannan karon ita kadai ce Sai kuma Matar Bashir itama Iklima da ta Fara Nata laulayin Cikin,Kwanci Tashi ba wuya a wajen Allah Umman Zareena ta Haihu Da kwana Uku iklima ta Haihu kuma Duka maza Suka Samu Bashir sai ya maida ma Dansa Sunan Dansa na Farko Daya Rasu Abubakar hakama Abba Usman Shima Abubakar din ya saka ma nashi Suna Kiranshi Sadiiq Babba Yaron Wajen iklima kuma Suna Kiranshi Sadiq karami. Wannan karon ma Nene tayi Ruwa Tayi Tsaki kan Abata Sadiq Babba Har Dr.Saulawa da Jikokinsa ke kira Alhaji Tsoho yayi mata Lakabi da Nene Uwar Maza Domin Allah ya Doramata Son Haihuwan ya"ya Maza Sai dai kuma Allah bai bata ba Shiyasa,Zain da Sadiq babba Suka koma Tamkar sune ya"yanta Ita kuma Umman Zareena Dama Uwar matace Domin Itama Tafi son ya"ya mata Sai aka Raba kowa yaja Nashi Cikin zaman lafiya da kwanciyar Hankali. Sadiq Babba nada Shekara Daya da wani Abu Ciki ya Bulla ajikin Maryama Murna Wajen Nene da Umman Zareena Ba"a mgana kamar su Za"ayi ma Haihuwan,Ita kanta Maryaman Tana Farinciki Domin Sosai Take son ganin kwan ta adunya koda Kwara Daya ne,Duk da Su Zareena Sun Debe mata wannan kewan komai Mama Maryama kinga Haddir ko.? Mama maryama Kinga Zain ko..? Mama maryama kin ga Xareena ko..? Aikinta kenan Cikin Rabon Fada da alkalanci. Tunda Cikinta ya Fito yaran suka Fahimci Tana da Ciki suka kama Murna Kada ma zain yaji labari Domin Tun Sanda yaga Cikin Mama maryama yayi Girma ya Tambayeta ya yaga Cikinta yayi kato ko Bata da lafiya ne..? Lokacin Tana Shashen Su Umman zareena ne Nene ce Ta bashi amsa da Cewa kani za"ayi musu ko kanwa Yana jin Haka ya Bata Rai yace Shi Gaskiya Mata yake so Mama maryama ta Haifamai Kowa sai da yayi mamakin kalaman yaro Dan Shekara Takwas da Wani Abu sai dai Ba Abun mamaki bane sanin Halin manyance irin ta Zain kamar wani Babba Kowa ya Bude Baki Yana kallonsa Sai Mama Maryama Taja Jikinta Tana Fadin"Karka Damu D'ana zain...Nayi maka alkawarin in mace na Haifa Na baka Ita matsayin mata Ko da bana Raye in kuma Namiji ne zan baka shi a matsayin Karamin kani Wanda zai iya ma Yayansa Biyayyah Har karshen Nunfashimsa..! Kowa ya Dauka kalaman Maryama da Zain amatsayin Wasa ne Har da Alhaji Usman ya Dawo Matansa ke gayamai yana ta Dariya,Ashe a Bangaran Maryama Da Zain ba Haka bane Shi da Gaske yake Cikin yarinta ita kuma Da gaske take Cikin Son Cikamai alkawarin Tana jin Babu Abunda zata mallaka wanda ba zata iya mallaka ma Iyalan Dr.Abubakar Saulawa ba. Tunda ga Lokacin Komai Zain ya samu sai yace na Matar sane wanda Mama Maryama Zata Haifamai ko makaranta yaje baya kashe kudi wai yana Tarawa zai Siyama Matarsa Babyn Wasa,Komai dai ya Samu ko naci ne sai ya Tsakura yace na Matarsa Wacce Mama maryama Zata Haifamai ne,Tun ana Daukan Abun Wasa Har dai aka Fahimci Zain Da gaske yake Labarin kuma yakai ma Kowa,kowa kuma sai Dariyan Kuruciyar Zain yake da Shirmensa Lokacin da Cikin Maryama ke Wata na Shida Umman Zareena itama ta samu Ciki kuma kusan Lokaci Daya Suka Fara laulayi da Nene Wannan karon ma. Cikin kwanciyar Hankali Duka Suka Cigaba da Rainon Cikinsu Har Cikin maryama ya Shiga Watan Haihuwarta sai Yayarta Halima tazo akan Tana son Tafiya Da maryama Chan Gida taje ta Haihu ammh Sai Alhaji Usman ya Hana yace Maryama Tamkar kanwa take garesa Saboda Haka anan zata Haihu Karamci Irin nasu yasa Halima Batayi Gaddama ba Ta Tsaya ta kwana Biyu Ranar Datayi Shirin komawa aranar Maryama Tatashi Da naguda aka kwasheta Zuwa asibitin Mallakin Dr Abubakar Saulawa. Suna zuwa aka karbeta Sai Dakin Haihuwa Duka Gidan aka Tafi Umman Zareena da Nene,Sai Halima da Baba Abdullahi Da Direba Hajiya mama Tana Gida bata Taho ba Sai Dr.Saulawa Wanda Dama yana Cikin asibitin Alhaji Usman Daga baya Yazo Asibitin ganin Har Wajen Yammah Maryama Bata Haihu ba Sai Aka yanke Shawaran yimata aiki Zuwa Lokacin Hajiya Mama ta iso Ita dasu Zain Wadanda Tunda suka Dawo makaranta aka kaisu Wajenta Suke mata kuka Suna ta Kiran Sunayen iyayensu Dana Mama maryama ganin Haka yasa Ta lallashesu Ta Fada musu suyi ma Mama maryama addu"a Tana asibiti zata Haifa musu kani ko kanwa Jin Haka yasa Zareena da Haddir suka Fara Murna Shi kuma Zain sai ya Fara kuka yana Fadin Shi ba kanwa za'a Haifamai ba Mata da kuma kukan sai an kaisa yaga Mama Maryam Dole Hajiya Mama ta Tarkato su suka Taho Tare Duk da Dr.Saulawa Nata Fada ammh ganin yadda Yaran suka Sha kuka ne sai suka bashi Tsausayi. Cikin Ikon Allah ana Kokarin Saka ahannu akan Takardan da za"ayi ma Maryama aiki Allah ya Sauketa Lafiya Inda ta Samu Haihuwar yarta Mace mai kama da Ita sak,sai Kuma Duhun mahaifinta Data Debo Saboda Maryama Faraace Sosai Sabani  Abdullahi Dayake bakin Fata Sai da aka gama gyarata ita da Abunda ta Haifa kana Nurse Ta Fito da Jinjiran a Hannunta Da Halima ta Faracin karo Zata mikamata Zain yayi azamar Mika Mata Hannu yana Fadin Ta bashi matarshi Tsaye Tayi tana kallonsa Cikin Mirmishi Dr.Saulawa yace ta mikamai Tako mikamai ya karba kamar zai Fadi Halima ta tareshi suka koma Suka Zauna kowa ya Kura mishi ido ana kallon yadda ya kurama Jinjiran ido yana kallonta da wani Mirmishi Kafin ya Dago yana kallon Abbansa Cikin Yarinya yace"Abba me sunanta...? Kafin Alhaji Usman ya bada Amsa Abdullahi ya bashi amsa da Fadin"Maryama Ta gayamin in ta Haifi mace Sunan Yaya Halima Take son asakamata Saboda Haka Alhaji Dakta kayi mata Huduba da HALIMATUS SA"ADIYA..! Gabadaya Murna Ta kama Halima wacce ya"yanta ke Kiranta Goggo Halima Cikin Jin Dadi Take fadin"Masha Allah..Allah ya Raya Halimatu.."Zain kawai akaji yace"Ba Sunanta Halima ba Abba..Ni Matata irin Sunana gareta..!? Cikin mamaki Nene tace"Irin Sunanka Da'n Nene..? Wani Suna kenan..? Cikin Kura ma Jinjiran ido yace"Tunda Sunana ZAIN ita kuma Sunanta ZAINAH daga yau ba Halima ba...Kunga Zainazain kenan..!gabadaya al"ajabi da Mamaki ya kama kowa Dr.Saulawa yana kallon Zain da wani Farinciki acikin Ransa kafin ya Dafa kansa yana Fadin"Allah ya maka albarka...Karka Damu Sunanta Halima ammh Kai mijinta me kuma ka zaba mata Suna ai Shikenan kowa ya Shaida Sunan Matar Zain Zainah ko..? Yafada yana kallonshi Washe baki yayi yana Daga sai Abun ya basu Dariya Dakyar Dr.Saulawa ya iya karbanta Suka Dunguma Dakin da aka maida Maryama Suka Iske ta Farfado agabanta yayi ma Jinjiran Huduba da Halima ya Dago Yana Fadin"Allah ya Raya Halimatus Sa"adiya..! Karaf Zain yace"Ba Sunanta Halima ba Sunanta Zainah nace muku..!Maryama ke neman karin Bayani Nene ta Koramata yadda akayi Dariya Tayi Tana Fadin"Gaskiya ne Yarona..Sunan da aka Zabamata yayi Daidai da..Sunanka ina Fatan ko bayan Raina zaku Tabbatar da Halima amatsayin matar Zain..? Tafada Tana Tsare Duka yan Dakin da Ido Kowa sai yaji Abun Wani iri Baba Abdullahi ne yayi Mirmishi yana Fadin"Kema yarintar Zain din zaki mana..? Kai ta girgiza Tana Fadin"Ba yarinya bace..Ku kalli Idanuwansa Tsabar gaskiyansa yake Fada..Nidai Nayi alkawarin Tun Kafin Ta Fito Duniya na Bama Zain ita amatsayim Mata Har Abada Ko Bayan Raina Abdullahi ka Tayani Sauke nauyin Dana Dauka..! Kowa adakin Sai da Jikinsa yayi Sanyi Dr.Saulawa ne yace"Karki Damu Maryama...Insha Allahu da kanki zaki Hada Hannun Zain da Halima amatsayin ma"aurata."Wani Sanssayar Miemishi Tayi kafin tace"Allah yasa Ina Fatan Haka.."Daga Haka bata kara cewa komai Suma ba wanda ya kara mgana sai aka koma Raba Rigima Tsakanin Zain da Zareena Inda Take Rigiman sai ta Dauki Halima karama ammh Zain ya Dafe gadon da Maryama ke kai yace bamai Taba mai Mata Tun Abun nashi na basu Dariya Har suka zo suka Tabbatar ma kansu zain Da gaske Acikin Ran Dr.Saulawa kuma yana Ta auna Abubuwa afili ya Furta Haka Allah ke al"amarinshi Daman. Kwana Daya Maryama Tayi a asibiti Aka sallamota ta koma Gida aka cigaba da karban yan Barka Gabadaya Kulawanta ya koma Karkashin Nene da Umman zareena Duk da suma Suna Fama da kansu Goggo Halima Sai dai kallo Domin ko Tace su barshi Sai suce sai sunyi ai maryama Tamkar kanwa Take garesu Hakama Hajiya Mama Tana iya bakin Kokarinta,Zain kuwa ansha Fama Dashi Domin Tunda akayi Haihuwan sai Ansha Fama Dashi yake zuwa makaranta sai ya Fara kukan Sai dai ya Tafi da ita da Dubara yake Tafiya yana Dawowa kuwa Shashen Maryama yake yada Zango Daga ma Karshe chan ya koma da kwana Saboda Zaina Ba Wanda ya Damu da Hakan Domin Kowa yana ganin Maryama da Mijinta yanzu Suna Cikin Ahalin Dr.Saulawa Tsudum. Dr.Saulawa da ya"yansa sun ma Maryama kara Sosai Da Abun arziki Sai wanda ya gani Musamman ma Alhaji Usman da Matansa Sunfi kowa Rawan gani Haka da yan Gada suka zo Suna suka koma da Fadan Irin Dimbin karamci da Dattako irin na Iyalan Dr.Saulawa Goggo Halima ma Bayan Suna Ta koma Itama da Sha Tara na arziki Tana Ta Godiya Aka bar Maryama da yarta Halimatu Sa'adiya wacce Taji Tudu Biyu Sunan Goggo Halima kuma Sunan Baba Atine na gaskiya. Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah Zaina nada Wata Shida Aduniya Nene ta Haifi Yarta mace Wacce taci sunan ZAFEERA bayan Haihuwanta da Kwana Hamsin Ita kuma Umman Zareena ta Sauka Wannan karon ma Namiji ta samu Yaci Sunan Mallam Umar suna Kiransa Faruq,kamar dai yadda Tsarin yake Nene uwar Maza Taja Nata itama Umman zareena Uwar mata taja nata Tunda Lokacin Zareena ta Girma Suna Cikin Shekaru na Goma da Haihuwa sai Tattalin ya koma kan Zafeera Yadda kukasan kwai haka Umman Zareena ke ji da Zafira kamar Tsoka Daya amiya Zain kuwa da karfi Da yaji ya zama Dan Shashen Maryama Saboda zainarsa Reno kuwa Tare sukeyi da Maryama Tun baya Iya Daukanta Har sai da ya iya Haka zai zauna yana ta mata wasa Tun Kafin ta isa Cin Abinci Zain ya Fara bata kayan zaki Ko Iyayen nashi na Fada Maryama Ta kanyi Mirmishi Tace su kyaleshi Mutum da matarsa Saboda Hakama Ta Riga ta ganeshi Da Taji muryansa zata Fara wuntsila kafa Tana Babban Dariya irin na Jarirai yana Daukanta kuma Shikenan Haka zasu yi ta Rigima da Zareena kan sai ya bata ta Dauketa In Kuma akaci Sa"a ya bata Zareena na Daukanta sai ta Fara kuka Sai Zain ya Fara Dariya Haddir dai yana Gefe Shi baima Cika cewa zai Dauka ba Ganin yadda Zain din ya mamaye komai Sai dai yayi tama Zareena Dariya ita kuma Taji Haushi Ta Fara kuka Maryama Ce mai Raba Fada ta kuma Shiga Ciki Tayi alkalanci. Shekaran Halima Daya da Wattani Maryama ta kara samun Ciki Sai dai kuma yazo da matsala Tunda Tayi ta Ciwo sai da akaje asibiti nan aka gano Tana da Cancer Mahaifa Hankakula Suka Tashi barin ma Abdullahi,Ammh Dr.Saulawa da Alhaji Bashir sukayi Tsaye sai da akayi mata aiki taji Sauki Bayan an Fitar da wanchan Cikin,Dalilin wannan Ciwon sai Dawainiyar Halima Ya koma Hannun Umman Zareena Tunda Allah ya Doramata kaunar Yarinya Ta Hadasu ita da Zafeera Tana Rainonsu Tare Zain na Tayata Domin Dakyar ma ya bari Umman Zareenan ke Daukan Halimar har ta goyata Ganin Mama Maryaman Bata da Lafiya ne Shiyasa. Bayan Taji Sauki ma Hakan bata Chanza Zani ba sai dai in Tana kuka akaita Maryama Ta bata Nono a maida mata Ita,Cikin ikon Allah ba Dadewa Maryama ta Sake samun Wani Cikin Wannan karon Da Sauki Abun Sun dai koma asibitin anyi Gwaje gwaje aka Tabbatar da Maryama zata iya Haihuwa ba Matsala Da haka tacigaba da Rainon Cikinta Gefe Daya kuma Dawainiyar Halima yana Hannun Umman zareena Cikinta na Shiga wata na Shida Ta Yayeta Ta Damkama Umman Zareena Ita,wacce ake ma Lakabi da mai Rainon Yan Biyu Sakamakon Zafeera akwai Girman Jiki Har ta kamo Zaina a Girma Ita har ta Fara Takawa Halima din ce Take Ta Rarrafe. Acikin Wannan yanayin ne Wani al"amari ya Faru wanda iyalan Dr.Saulawa suka kasa mantawa Dashi Shine Wata Ranar Asabar da Misalin karfe 2:00pm na Dare yan Fashi Suka Shigo Gidan Alhaji Bashir da Manyan makamai Lokacin da Suka shigo Gidan Abdullahi ya Tashi gaban get ya Shiga Gidan Wajen Maryama Dama Hakan yake yi sai asuba kuma yake Dawowa,Duka ya Kulle get Din Haurowa sukayi suka Shigo kamar Wasa Dama Tunda ya Shiga Ciki bai kwanta ba,Alwala ya Dauro ya Fara Sallar Nafila yakai Raka"a na Biyu yaji motsin Takun Kafafu Da Sauri ya Sallame ya Dauki Fitilansa da Sandansa zai Fita Sai maryama ta Farka ganin zai Fita yasa Ta Tambayeshi sai yace mata yana Zuwa ya Fita da Sauri Yana Fita kawai yaci karo da Wani katon Mutim Cikin bakaken kaya ya Haskeshi da Fitila yana Tambayan waye Kafin ma yaji wani Abu Daga Bayansa yaji an sakarmai Harshashi aciki nan Take ya Fadi matattace Jin wannan karan Harbin Shi ya Rikita Maryama Ta Fito Da Gudu Ga Ciki Tana kuka Itama nan Take wani ya sakarmata Harshashi aciki Itama Ta Fadi ba Rai. Innalillahi Wa"inna illairaju"un wannan ahali Sun ga Tashin Hankali kwarai yan Fashi Sun Shiga Har Shashen Alhaji Usman basu dai kashe kowa ba ammh Sun Karbi kudaden Daya Dawo Dasu Daga Tafiya yana Shirin Washegari zai kai Banki,sai kuma Dan kunnayen Zinaren su Nene da wasu kudaden Dake Hannunsu Sukayi ma Alhaji Usman Dukan Tsiya sai da ya Suma kana suka Tafi Su Nene suka Rude sai kuka Ga su Zain Suma kukan suke Zaina da Zafeera kuwa sai kuka Suke na Tashin Hankali Umman Zareena ita Tayi Hausan Kiran Wayar Dr.Saulawa ta Na kuka Tana gayamai Halin daSuke Ciki Cikin Tashin Hankali Shida Hajiya Mama suka Nufo Gidan Domin Daman Kaf an anguwan ba wanda bai ji karan Harbi Biyun Da sukayi ba. Abun Tsausayi Suna Zuwa Gidan suka ga Get a wangale Hankalinsu ya Tashi ai basu Rude ba sai da suka ga gawan Maryama da Abdullahi kwance afarfajiyan Gidan cikin Jini Sai Zuciyoyi Suka Raunana Idanuwa Suka Zubda Kwallah Su Nene sun Rude matuka ga Halin da Suke Ciki ga mutuwar Maryama da Mijinta Sun Rasa Ina zasu Tare Hawayensu ne,Wanda ke zuba ba kama Hannun Yaro ganin Alhaji Usman baya Cikin Hankalinsa ne yasa aka Tattarashi Zuwa asibiti Dr.Saulauwa ya Kira yan Sanda suka zo Suna Ta Binciken gawan su Maryama Abun gwanin Ban Tsausayi Hajiya mama Kuwa Ta Rude sai kuka Take tsakanin ita dasu Nene an Rasa mai bama wani Hakuri. Sai da yan Sanda suka gama Bincikensu kana suka Tafi da Cewar Insha Allahu za"a kama Yan Fashin da sukayi wannan aikin Sai alokacin Dr.Saulawa ya iya Kiran Chan Gada suma ya Sanar dasu wannan Mugun labari Fadar irin Tashin Hankali da Suka Shiga bata baki ne Mota Guda sukayo suka zo Goggo Halima da Hajiya Mama suka Yi ma Maryama Sallan gawa yayinda Wasu mazan Daga Gada sukayi ma Abdullahi wankan gawa aka Sallacesu Zuwa Gidansu na Gaskiya Allahu akbar. Duka da su Bashir akayi Sallar gawan Domin Duk sunzo Hannatu ne kadai bata zo ba Ammh Rukayyah itama ta iso Tuni Zukata suka Raunana Sai ma in ka Tuna da Ciki Maryama ta koma ga Allah ga Yarta Karama wacce ko Shekara Biyu bata gama kaiwa ba Sai kaga yadda Zain da zareena da Haddir suke kuka Kamar Ransu zai Fita Duk da Suna Yara sun Fahimci Mama Maryama da Abdullahi Sun Tafi Tunda Hajiya Mama Ta gayamusu sun Tafi inda ba Dawowa Umman Zareena Goye da Zafira Zain kuma ya kama Halima ya kamkame yana kuka Abun gwanin ban Tsausayi. Anan Gidan Alhaji Usman aka yi Karban gaisuwa Duk da Shi yana asibiti sai da akayi uku ya Dawo Gida Domin ba Laifi Ya Daku Allah yasa ba karaya sai Gocewar Kashi,Shi kanshi Yayi kuka Zuciyarsa ta Raunana da Wannan Mummunar kaddaran Data Fada musu,Sai da akayi bakwai kana yan Gada sukayi Shirin komawa nan Goggo Halima tace abata Halima ta tafi da ita ta Riketa,Tana ta kukan Bayan Maryama Bata da kowa Duka iyayensu Sun Rasu Su bata ita ko In ta ganta zata Dinga Tunawa da ita Da Farko Dr.Saulawa ya karbi Rokonta yace Umman Zareena ta Hadoma Halima kayanta ta bama Goggonta Tatafi da ita Umma Sai ta Fara kuka Tana Rokon Itama abar mata Ashe Zain yalura Da Sanda Goggo Halima Ta karbi Zainarsa Sai ya Fara kuka yana Kokarin son Karbanta Duk yadda akayi Tunanin Abun ya Wuce wasa Dr.Saulawa yabama Umman Zareena Hakuri yace Ta barma Goggo Halima Rikon Halima Tunda Ita ga Zafeera ma Tana Raina Hakanan ta Hakura Tana ji Tana gani Ta Hado kayanta tabama Goggo Halima Dakyar Aka Rike zain wanda ke kuka yana Birgima kan ba"a Tafi da Zainarsa ba Ganin Har Goggo Halima ta Shiga Mota sai Numfasa ya Fara Daukewa kafin kace kwabo ya Suma Wannan Dalilin Shi Ya Hana Goggo Halima ta Fasa Tafiya da Halima ta Sauko Ta Damkama Umman Zareena ita tana kuka Tana Fadin'Naga Soyayya da kaunar Halima I idanuwan wannan yaron Tun Ranar datazo Duniya..Bazan so na Raba wannan kaunar ba..Gata Hajiya Fatima Allah ya baki ikon Riketa da Amana..! Ba wanda Baiyi kuka ba awajen Zain kuwa yana Farfadowa Daya ga Zainarsa sai ya Karbeta ya Rumgumeta yana ta kuka Zareena da Haddir ma suka Taru Kusa Dashi Suma Suna kuka ahaka yan Gada suka koma Chan garinsu daDacin Mutuwar Maryama da Abdullahi. *Comments *Share and vote* *Janafty...* *Intelligent writer"s asso..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*            0️⃣6️⃣ "Haka Halima Zaina Tatashi Ta ganta a Hannun Iyayan Rikonta,Musamman Alhaji Usman Daya kasance Kamar Uba Gareta Umman Zareena Ta zama Tamkar Uwar Data Haifeta Da Cikinta Saboda yadda Take Nuna mata kauna. Alokaci Daya Suka Taso Su Uku Halima,Zafeera da Umar Faruq Duk da Ta Girme musu da Wasu Wattani Sun kawo Ta Girma Tunda Ita Haka Allah yayi ta mai karamin Jiki ce,Tunda Halima ta Fara Wayau Ta Fara Cin karo da matsancin Kauna Da Soyayyah da Zain ke Nuna mata Tun yana Lokacin kuruciya Shiyasa Ta Fara Bude Ido Dashi Duk Gidan Bayan Umman Zareena Halima Bata yarda da kowa ba Sai Zain Ko Makaranta Da karfi Da Yaji aka Sakasu Suna da Shekara Biyu da wani Abu basu Cika uku ba Saboda kukan da take yi Duk Sanda Zain zai Tafi makaranta ya Barta Wannan Dalilin yasa Alhaji Usman ya Saka su Nursing Section Saboda dai Halima da Zain su kasance Waje Daya Hakan kuma ba karamin yima Zain Dadi yayi ba ko achan makaranta Da ya samu Faraga sai ya Leka ajinsu Halima Lokaci kalilan Su kansu yan Makarantar suka Shaida Halima zaina yar gatace kuma Ta gaban Goshi a Wajen Zain Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah...Yau da gobe bata bar komai ba Gashi Har Su Zain Sun kamallah Secondary School Dinsu Lokacin Zain nada Shekara 19 aduniya shi da Zareena da Haddir,ayayinda da ita kuma Zainarsa Take Cikin Shekara na Tara aduniya ita dasu zafeera Zuwa Lokacim kuma Abubuwan Duk Sun karu an samu Cigaba Sosai Ta Bangaran Haihuwa Nene Ta kara Haihu Yarta Mace mai Suna Zainab Wacce Tsakaninta Dasu Halima ba Nisa,sai Umman Zareena ta kara yin Bashir Wanda Suke Kira Junoir sai na Karshen Allah ya bata Ya mace Wacce Tacii Sunan Saudart. Ayayinda kuma Bashir Wanda Suke Kira Da Baban kaduna Bayan Sadiq karami Sai Kuma Amina Wacce suke Kira Hajiya,sai Karaminsu Muhammed Amin,suna Kiransa Amin Kawai,Aliyu kuma Wanda Suke Kira Dadyn Abuja kuma Bayan Hamdiya,Ta kara Haifan Waleeda da Kuma Lauratu,yayan Su Inna Rukayya Ta kano da na Inna Hannatu dai ba Wacce Tayi Aure Dayake ya"yan nasu suna karatu mai Zurfi ne. Zuwa Lokacin kuma Girma ya Fara kama Dr.Abubakar Saulawa,sai ya Damka Ragamar komai a Hannun ya"yansa  Asibitinsa kuwa ba koda yaushe yake samun zuwa ba sai dai ya Damka Amanar komai Hannun Amintattun Likitocin Dake Asibitin Suna aiki..sai kuma Burinsa kan Jikikinsa Guda Biyu Haddir da Zain Wadanda suka ce zasu Karanci aikin Likitanci ammh kuma Bangare Dabam Dabam Wannan Abun yafi komai Mai Dadi Farincikinsa sai da ya kasa Boyuwa,Yana ji acikin Ransa ko ayau ya Fadi ya bar Gidan Duniya Allah ya Cikamai Burinsa. Halima Tataso ba Hannun iyayenta ba ammh Babu Abunda Ta nema na Rayuwa ta Rasa,Umman Zareena,Nene, Zain,Da Alhaji Usman Kowa Sonta yake Kada Hajiya Mama Taji Labari da Dr.Saulawa Wanda Jikokinsa Ke Kiransa Alhaji Tsoho Har Duka ya"yan sa Suma sun kama ganin Girma ya kamashi Har ya Fara Farin gashi. Ashekarun Halima Tara aduniya Ta Fahimci Tsanatsanin Son da Zain yake mata,Domin Tun kafin takai Haka Komai nata Zain ne,Tun Tana yar Shekara Biyu Tare suke kwana Shi ke bata abinci abaki Yayi mata wanka komai Shi yake mata ko Su Nene sun ce ya bari sai ya saka kuka Dole suka Kyaleshi Itama ta Bude ido da Wannan Kaunar Nashi ne Da Allah ya sakamai Tun Tana Cikin Mahaifiyarta. Tun Tana yar Shekara 5 aduniya Zain yake kiranta da Firstlove Dinsa,itama kuma Sai Take Kiransa da Hakan,Duk wanda yake Cikin Wannan Ahalin ya Shaida wannan Kaunar Dake tsakanin Halima da Zain,Sai da Zain din ya Fara mallakan Hankalinsa ya kai Matakin Shekara Sha Hudu Umman Zareena ta Hanashi kwana Daki Daya da ita Saboda Halin Rayuwa Da Farko ya Nuna Fushinsa Sai da Mganata takai kunnan Alhaji Tsoho ya Kirashi yamai mgana kana ya Hakura Zainarsa Ta Daina kwana Dashi Shakuwa ce Wacce Bata da Karshe ta Shiga Tsakaninsu in Daya bai Ga Daya ba,ba kwanciyar Hankali In Daya na kuka Daya zai Fara ne komai nasu dai Daya ne in Daya ya samu Abu Toh bazai iya ci ba sai da Daya Suna Kara Girma Tsananin kaunarsu ga Juna na kara Tasiri acikin Ransu kuma Duk Wanda ke Tare da Zain Dole yasan Labarin Halima matarsa ko da Mutum bai Taba ganinta Ba ba"a zaman Minti Biyar Dashi bai ambaceta ba Haka Islamiyansu da Suke Zuwa Sai da Hukumar Makaranta ta kawo karar Zain kan yana Zuwa ajinsu Halima yana Daukanta zuwa ajinsu Baya barinta Tayi karatu Dalilin Haka Umman Zareena ta Saka aka Cire Zain din da Haddir da Zareena aka Sauya musu islamiya Saboda Zain ya samu kwanciyar Hankalin yin karatu Shima Din sai da aka Sha Fama Dashi kana ya Hakura ammh da yace Bazai bar makaranta ba Sai dai in inda aka maidasu Din Su koma Tare da Zainarsa. In Homework aka bata Amakaranta Shi ke koyamata Komai in bata gane ba kafin Ta Fara Ma Umma mgana Shi zata Fara nema,Dama gashi da kwalkwalwa Zain irin yaran nan ne masu kaifin kwalkwalwa da Kokari Ita kadai yake koyama Karatu,Zareena Tayi ta Jin Haushi Shi kuwa Haddir Baya Damuwa,Tunda bamashi ba kaf abokansu na makaranta Sun san da Zaman Halima amatsayin matar Da Zain zai Aura in ya Girma ya gama karatu,Saboda koda yaushe ko kuma a ina ya zauna Bai da Labari sai nata Allah ya Riga ya Dasa wannan kaunar junan a Tsskaninsu. Lokacin da sukayi Candy Zain yana Gida Tunda Batare da Saninsu ba akayi musu Cukun Cukun Fita Aborad Su Dora karatunsu Zareena kuma Alhaji Tsoho ya Hana yace ta zauna agida Nageria Tayi karatunta,Zain ya gama Sakankancewa ATBU bauchi zai yi Saboda Bayason Nisa da Zainarsa sai dai kuma Yaga Sabanin Hankalinsa Domin sai da komai ya kamallah Suna gabda Tafiya Shida Haddir suka Tsinci Labarin. Haddir Kadai yake ta Murna Banda Zain wanda ya Fara cewa Shi ba Inda zashi Saboda Zainarsa Tun ana Dauka Wasa ne Har aka ga Da gaske yake Ganin Yaki ce shi bazashi ba yasa Baban Kaduna yazo Har Gida yana ta yimai Fada Daga baya kuma ya koma Lallashi ammh Sai da akayi mai alkawarim Daya Dawo Bayan ya gama Karatunsa Za"a Daura musu Aure da Zainarsa kana ya yarda akwanakin da suka Rage musu na Tafiya duk batasu yayi wajen Sallama da Zaina da kuma Daukan ma Juna alkwarinka da kuma Sharadai Sharadai masu Dama Da ba wanda ya sani sai shi sai ita Duk da Tana da karancin Shekaru ammh Ai tasan mai Sonta Ta kuma Shaku Dashi Tayi kuka Sosai Lokacin da zasu Tafi Ammh sai ya Lallasheta da Fadin Ta tsaya Tayi karatu Dakyau In ya Dawo Zai Tafi da ita Bayan An Daura musu Aure suje chan su zauna Allah Sarki Rayuwa Suna Makarantar Ranar Wata Talata Jirginsu Zain da Haddir ya Daga zuwa London Ta Abuja ya Tashi In da suka samu Rakiyan Dadyn Abuja da Mommy Iklima Sai Zareena Wacce tasha kukan Rabuwa Da yan"uwanta wannan Shine karo na Farko da zasu Rabu da juna Tun Bayan Haihuwansu.... Itama Din Tafiyarsu ba Dadewa Ta Tatattara zuwa Zaria Inda Ta Fara Karatunta na Aikin Jarida Wato Mass Com,a nan cikin ABU zaria Cike da kewar yan"uwanta Wanda suka Riga suka zama Jikin jikin Juna,Hakuri kawai Take Tinda Daman ko ba Karatu akwai Aure wanda Dole zai Rabasu. Sai bayan Tafiyarsu Su Umma Da Nene suka Fahimci Yadda Shakuwa tayi mugun Shiga Jikin Halima Domin kwana Take kuka Tana Kiran Sunan zain Dalilin Haka sai da tayi zazzabi Harda kwanciya a asibiti Da aka Sallamota Sai ta koma Shuru Shuru bata Mgana sai dai ka ganta ta zauna Tayi Tagumi Kawai Chan kuma sai ta Fara kuka Sai a Hankali a Hankali Ganin Zafeera da Faruq suna Kokarin Janta ajiki Saboda ta Saki Jikinta da Ita kanta Umma da Abba Wadanda basa Son ganin Damuwarta Da akayi Hutun Makarantar Wannan Shine karo na Farko Da taje Gada Tayi musu Sati biyu ta Dawo,Domin Lokacin da Zain yana nan Baya barinta Taje ko"ina in ma Abba ya matsa Dakyar yake yarda Suje da ita tayi kwana Daya Su Dawo Goggo Halima Ta gaji da Mitan ta Zura ido Ammh Bayan Tafiyar Zain sai Alhaji Tsoho yace Taje chan Tayi musu Hutu Saboda yan"uwa su ganta Koda Taje Din bata wani Sake ba Duk da tasan Sune Dangin Mahaifanta ammh kuma Rashin Zain a gareta Tamkar wani Gibi ne na Rayuwarta. ****** Rayuwar Haddir da Zain a Jami"ar Oxford Universty London Tasha Bambam Domin Dama ko Ahalayya da na yau da kullum Suna da Bambamci Haddir Mutum ne mai Mugun Zuciya Kuma So Silent gashi bai Cika Shiga Shirgin mutane ba,In ka ganshi ya Sake to da Dan"uwansa Zain ne,Duk da ba Abu Daya Suke karanta ba,Shi Zain yana Bangaran Gyneacologist ne,ayayinda Haddir yake Bangaran Paediatric ne,ammh yanzu Suna Hade ne sai Tafiya Tayi Tafiya ne kowane Bangare zai Ware kanshi. Tun Zuwansu Makarantar Basu Dade ba Sunan Zain Usman Abubakar Saulawa yayi Fice Saboda Zamowarsa Guru a bangaran Kokari Shi kanshi Haddir ya sani bai kama kafarsa ba Dalilin Haka sai ya Sanu Tarin Masoya da abokai kana kuma gashi Handome Matashin yaro mai Kokari,nan da nan ya Shiga Ran maza da mata kafin kace me Zain ya Shiga Click na mata da Maza ba Adadi Tunda Gaskiya Haddir yafishi irin wannan kamewar Ammh Shi Zain yana son Rayuwa da Jin Dadi. Tun Farko Sai da Haddir yamai mgana kan ya maida Hankali ga Abunda yakai su Ammh Zain bai Ji ba,sai ma yayi Biris da Mganar Haddir din yana Ganin ai yana ganin Karatunsa bazai Hanashi Jin Dadin Rayuwa ba,Ganin Haka yasa Haddir ya Fita Batunshi Saboda karatunsu ba Koda yaushe suke samun Kiran Gida ba Sai bayan Wasu Satittuka Dama Shi Zain Ba da wanda yake waya sai Halima Waya Dakeki..? kina cin kaza..? Kin yi kuka..? Umma na baki madara..? Tambayoyi Dai gasunan sai Ta Rasa wanda zata amsa mai ma aciki Dama Shi yana Kiran Gida ne saboda ita Domin Duk Duniya bayan Iyayensa Itace agabansa kuma aransa. Ko achan London zaku yi mamakin yadda Sunan Halima yayi Fice Sau Tarin Abokan Zain Turawan Suna mai lakabi da ZAINAZAIN ne kuma yana Jin Dadi Baya jin kunyar yace musu matarsa ce da zai Aura da zarar ya gama karatu ya koma Gida Shi Ba mutum bane mai ijiye Sirri A"a indai ya Hadu da kai ko na Wuni Daya ne Dole ka Shaida Wacece Firstlove a Wajen Zain. Ba Dina Bace Sanadiyar Fara Lalacewar Zain ba Ita Dina Daga Baya tazo makarantar Domin Zain na gabanta da Shekara Daya sai akaci Sa"a kuma Duka Course Daya zasu karanta,Zain yana da Sakewa da Mutane Both Mata da Maza Sabanin Haddir Dake da kamewa da kuma Daraja Mutumtanka Gidansu da kuma Tarin Nasihun Iyayansu har ma Gargadin Alhaji Tsoho Garesu na su Tsarkake Zuciyarsu Suji Tsoron Allah Suyi Abunda ya kaisu ammh Zain ya watsar da Wannan Farkon Abun da ya Fara kaishi ga Kusanta ZINA shine Biye ma Matan Turawa Wadanda muke da Bambamcin al"ada dasu da kuma addini. Tun Zuwan Zain makarantan Yayi yanmata da Kawaye mata Wadanda bai san iyakarsu ba In suka ce Suna sonsa baya Taka musu Burki Saboda Shedan ya saka Mishi Sha"awarsu Banda Son su Saboda So Daya ne Tak kuma Zainarsa yake ma Wannan Son Da wannan Abun yasa ya kan kyale su Tabashi Har ma Suyi Hugging Dinshi Su kuma yi Kissing Dinsa baya Damuwa Tunda ya gani a nan Duk Normal ne. Dalilin Fara aikata Zinarsa Ta Farko Suna Shekara Na Biyu a Landon ne Wata Kawarsa Gloria,Baturiyace yar kasan London din ce itama karatu ya kawota makaranta Tun ganin Farko Da Tayi ma Zain ya Shiga Ranta Ta Dinga Neman kusanci Dashi Dayake bashi da Wuyar Sakewa Nan da nan ya Saki Jiki Da Ita suka Shaku suka zama kawaye suna Fita yawo Tare da Zuwa Wurare Dadama Kwatsam Ranar ta gayyaceshi Gidanta Cin Abincin Dare Wato Dinner Daya nemi Haddir yazo suje yace bazashi ba sai yayi Fushi ya Tafi shi kadai Ashe ta Shiryama Ranar Mganin karfin Sha"awa ta sakama Zain a Alemi yasha Domin ya Biya mata Bukatunta Tunda Tayi kokarin Hakan ta kasance ammh kuma Shi Zain din yana kwace ma Hakan. Ranar Zain yayi Zina da Gloria kuma Abun Takaichi ma Bashi ne ya Fara saninta ba Ranar agidanta ya kwana Bayan komai ya Lafa yashiga Nadaman Abunda ya Faru yana kuka yayi mata Kaca kaca suka Rabu koda ya koma Gidan da iyayensu suka kama Musu Shida Haddir baya Cikin Natsuwar,Dama bai da Rike Abun Aranshi yana komawa ya kwashe komai ya Gayama Haddir Suka zauna sukaci kukansu Tare ammh Haddir yayi ta ma Zain Fada kuma yayi mai alkawarin Rufe wannan Sirrin ba Wanda zai Ji Bayan Shi Zain din yamai alkawarin zai Guji Faruwan haka. Kamar Gaske Zain ya Fitar da kansa Cikin Wani Shashancin makaranta ya koma ya maida Hankalinsa kan karatunsa sai dai kuma Waasa Farin Girki Tunda Gloria ta Dandanamai kamar ta Jona mai Bala'i sai ya kasa Sukuni yayi yayi ya Danne Abun ya kasa Bayan Faruwar Haka da wattani kadan Zain ya Koma Ruwa Harka da Mata kaca Kaca Duk wacce ta saki kanta zai Taya kuma yayi Abunda yaga Dama da ita Tun Yana Boyema Haddir har Abun ya Bayyana ya sani Ranar ya kwana Cikin Bakincikin Halin da Dan"uwansa ya saka kansa Yayi mai Fadan da Nasihan ammh Duk Abanza Sai ya koma mai addu"an Shariya Abu Daya ne yamai Dadi ganin bai wasa da karatunsa ba kusan yana Jerin masu Tafiya da manyan point aset dinsu. Addu"an da Haddir ya keta mai da kuma Nasihan Dayake ta mai a kullum yasa Kuma Abun yayi sauki Zain din ya Rage Neman matansa Ba kamar baya ba Duk da yana yi ammh ba Sosai Haddir nata jin Dadin sai dai kwatsam Suna Shekara ta uku a London har kuma Lokacin basu je gida ba Sai da Abba yazo Dubasu Shida Alhaji Tsoho da Dadyn Abuja Wanda suka Rako Alhaji Tsohon wani Asibitin aka Dubashi bayan Tafiyarsu ya Fara Fama da Kafa Da sukazo Haka Zain ya Dinga Rokon Kar Haddir ya Fada musu Halin Da yake ciki Shi kuwa mai zai kaishi Fadan wannan Abun..? Ya gwammace koma me zai Faru ya Faru ammh Zai Rufama Amininsa Kuma Dan"uwansa asiri Ahaka suka zo suka gansu suka koma Batare da sun Fahimci Zain din ya Chanza Daga yadda suka Shanshi ba. A Daidai Tsskanin ne kuma Dina Gaddafi Sheerif ta Shigo Rayuwar Zain wanda ta kara Tabarbara komai Daga Tarbiyansa Gabadaya. Dina Gaddafi Sheerif Haifaffiyar Garin Jahar Kanon Dabo ce Mahaifinta Gaddafi Shareef Dan garin Bama ne Dake Maidugurin Nageria,Mahaifiyarta kuma Sarah Balarabiyar Sudan ce Auran Soyayyah suka yi da mahaifinta Wanda ya kasance Dan Siyasa ne,Tun bayan Auransa da Sarah suka Fara samun Matsala kan Rashin Kulawa ga iyalansa Yafi maida Hankali kan Harkokinsa na Siyasa Suna Haka har Allah ya basu Dina Ita kadai kwara Daya Allah ya basu Shiyasa ta tashi Cikin Gatan Duniya ta kowani Bangare. Abunda yasa Ta kara Sangarce Shine Rasuwa Mahaifiyarta Sara Tana da Shekara goma aduniya Dangin Mahaifiyarta Sun so su Dauketa Su maidata Sudan su Riketa Tunda Rikon Diya Mace sai mace ammh Alhaji Gaddadi Shaeerif ya Hana Adauketa Saboda yadda Gabadaya ya maida Soyayyar Sarah ga Dina din Dole suka Bar mai Ita Ba Domin Ransu yaso ba Sai Domin Tsausayinshi na Ganin Rasuwar Sarah din Ta Tabashi Sosai. Da farko kamar zai iya kula da Ita sai kuma ya gaza Saboda ya kara Shiga Harkan Siyansa Sosai,Sai ya Dauko mata mai Reno ya kawo Gidan Tana kula da ita Tunda Wani Lokacin Tafiya Tana Kamashi Wannan Dalilin Shine Dalilin Dayasa Dina Tatashi bata Da Tarbiya Ga kuma Sangarta Datayi mata yawa Tatashi ba"a gaban Uwa ba Ba kwaba Uba kuma bai da Cikakken Lokacinta Ballatana ya Tsaya Tsayin Daka Wajen bata Tarbiya Sai Rayuwarta Tatashi Sai Abunda Dina Taga Dama Take yi kuma Duk Abunda Tayi Niyya Shi take aikatawa bamai ce mata Domin komai Ko Chan Sudan bata Cika zuwa ba sai dai su suzo su ganta Ko su Suna Cikin Takaichi da bakincikin Yarda Dina Ta sangarce Ta kuma Tashi ba Wata Tarbiya Tare da ita. Duka Karatunta Har zuwa matakin secondary a Frine Collage Tayi Dake garin kano Sai kuma alokacin Alhaji gaddafi ya kara Aure,da Wata Mata Itama Ta taba Aure Mijinta ya Rasu Sai dai bata Taba Haihuwa ba mai Suna Hajiya Batula,itama yar nan garin kanom ce kanwar Wani abokin Siyarsa ne ya bashi ita ya Aura Saboda Suna samun suka Wajen abokan Siyarsasu kan Rashin Auren na Alhaji Gaddafi. Bayan kamallah karatun Dina amatakin Secondary University of Lagos Dina ta Fara ammh ganin Kokarinta da Hazakarta Yasa Mahaifinta ya Dauketa Daga nan ya kaita London Domin Tayi Karatunta achan Ita kuma da Kanta Dinar Ta zabi Bangaran Likitan mata a fanni da zata karanta Duk wanda ya ganta Sai ya san cewa Dina yar gatace ta gaba da Baya Domin Gida sunan gida Mahaifinta ya Siyamata ya Zube mata ababen Jin Dadin Rayuwa Gata kyakyawa Son kowa kin Wanda ya Rasa Da wannan kyan nata Take jan Hankalin da yawan Maza da mata zuwa gareta Duk da Iya Rumguman Namiji da kissing Abunda dai ba"a Rassa ba Ammh bata Taba jin zata iya bama Wani Martabanta ba sai Haduwarta da zain wanda Taji zata iya Bashi komai saboda Son shi da Allah ya Dora mata. Tun Shigowarta makaranta ta Fara Sanin Labarin kwazon zain da kuma Kokarinsa sai dai bata maida kai akansa Ba Tunda Itama Tana Ji da kanta ammh Sai kuma ta kasa Saboda kowa Tadinsa yake Duk da yana Gabanta Sai da ta Shekara a makarantar kana Tataba ganin Zain Ranar da Ta Fara ganinsa Wajen Buga Table Tinnes ta Raina kanta Domin akaron Farko,Ta Raina kanta Saboda ganin Haduwar Zain da kuma yadda komai nashi ya Tafi da Imaninta Bata Tunkareshi ba Saboda Itama Tana ji da kanta sai dai kuma ta kasa Sukuni da Tunaninsa Abu kamar wasa ya Zama gaske karfi da yaji Zain ya kaasa bace ma Dina acikin Zuciyarta da Haka ta Fara Neman saninsa Dayake Tana da kudi Cikin Lokaci kalan Ta samu Labarinsa Garinsa da kuma Abunda yake karanta da kuma Wasu Daga Cikin Hallayarsa ta Hannun Wani Saifkhan wani abokinsa Dan Indiya ne Wanda Yake ta Shigema Dina Saboda yana Sonta ita kuma sai Tayi amfani da wannan Damar tasan komai game da Zain din Harda Neman matansa Hatta da Labarin Haddir ta samu. Jin Labarin yana Harkan Mata sai Ranta ya baci kishi ya kamata Da Farko Taso ta kyaleshi Sai kuma ta kasa Dole ta Nemi yadda suka Fara Haduwa da Zain din Ta Hanyar abokinsa Saifkhan,wanda Taje da Niyyar wani karatu ya Shige mata Duhu ya koyamata Ganin Farko da Zain yayi ma Dina yaji Kyanta da komai nata ya Burgesa Cikin Lokaci ya Saki Jiki Da Ita Har ta Fara sanin Wasu Sirrinkan nashi Ciki kuwa Harda Labarin Zainarsa Wanda Tun alokacin Dina Taji ta Tsaneta Saboda Ko karatunsa Zain baima Maimaici kamar Mganar Wannan yarinyar. Haddir Rana Tsaka yaga Kawance da Wata Shakuwa ta Sarke Tsakanin Zain da Dina Wanda Tun ganin Farko da yayi ma Dina tazo gidan da Suke zaune yaji batamai ba Domin Daga ganinta Bata da Wani Cikakken Tarbiya Da yayima Zain mgana akan ya Rabu da ita sai da sukayi Wani gagarumin Fada da suka kusa Sati basa mgana Sai Daga baya suka Shirya Ganin baya son Ana mai mganar kan Dina sai Haddir din ya Tattarasu kawai ya Watsar Ita kanta Dina Tasan Haddir baya yinta Domin ko Gaisheshi Take Dakyar yake amsawa yana wani Cin mgani Har Zain din Tataba mq mgana kan Shi Dan"uwanshi bai son Wayewa bane..? Ya takura kansa Shi kadai Dariya yayi mata yana Fadin Haka yake Tun muna Yara Haka yake baida Hayaniya Bazaki iya Chanzashi ba Daga haka Itama ta Fita Batunsa ta Dinga Jan Zain din ajiki Domin Ta Rabashi da Hulda Da Sauran mata. Zain Shi ya Fara sanin Dina a Ya mace,Kuma Bashi ya Roketa ba Ita da kanta Ta bashi Saboda ta kamashi da Wata Budurwann Shashancinsa Ta koreta Bayan Tatafi sai ya Fara mata Fadan Bayason Haka Data koreta zata Bashi Abunda wanchan zata Bashi ne,Ita kuma saboda Lokacin Tagama mutuwan a kansa Tana Jin zata iya komai akansa kawai batare da wani Nadama ba ta bashi kanta Tun kuma daga wannan Lokacin su ka koma suka kulle kamar mata da Miji,Dayake shi Zain yasan kanshi Da Condom yake amfani Da Dina Tamai mgana sai yace Mata Tana so ya kwasan ma Firstlove dinsa Cuta ne..? Ita kadai ce Yake so Duk Duniya Shiyasa bayason yayi Abunda Zai Bata mata Rayuwa Ranar sai da sukayi Kaca kaca da Zain a Kan Zainarsa Ta Shareshi shima ya Shareta Ammh Daga Baya ita Ta Nemeshi kana Suka Shirya Domin Bazata iya Jurewa ba Kalaman Zain sun fi komai kona mata Rai Dayace mata Halima ce kadai yake ma Sona Na Hakika Sauran matan kuma Da Taga yana Harka dasu Sha"awarsu kawai yake Da Tace mai Harda ita Kai Tsaye yace Kwarai Tana Cikinsu Wannan Dalilin yasa Ta kara Tsanar Zaimah Din Tun ma bata Taba ganinta ba,ta kuma gane in Tana Son Zama da Zain Dole ta Daina Nuna bata kaunar Halima in kuma ba Haka zai iya Rabuwa da ita akanta.   Koda Haddir ya Farga da irin Kullewan Zain da Dina yaji Takaichi Yayi ta ma Zain Fadan meyasa yake Kokarin Sauya kansa,ya manta da iyayensu da Abunda suka Turosu suyi..? Yaya Halimar tashi zataji in Tasan Abunda yakai aikatawa zata yadda ta Aureshi kuwa..? Wannan kalaman na Haddir sunsa Zain ya Dawo Daga Hayyacinsa har yayi kokarin yakice komai Hatta ko da Dinan yace Rabuwarsu tazo Saboda Halimarsa Bayaso ta Samu Raunin Zuciya in Taji Abunda yake aikata mata na cin Amana Anyi Haka ba Dadewa suka samu Dogon Hutu suka Dawo Nageria wanda ko Sallama bai iya ma Dinar ba Sai Bayan Tafiyarsu Taji Labari alokacin Idanuwanta ya Rufe Basu samu Hutu ba su itama Ta Tattaro ta Dawo Gida Saboda Tayi Shiri Sosai kan Zain Domin bata Fara Sonshi Domin Ta Daina ba alokacin Daya Nuna baya son Harka da ita,ita alokacin Take Kara Jin Dadin Harka. Tana Komawa Gida Babanta bai Tsaya Tambayanta meya Dawo da Ita ba Itama bata Tsaya mai Bayani ba Tunda Alokacin Siyasa Tayi zabi Har yana matsayin House af Rep na kano alokacin ba Zama Tana Dawowa Taje ta Nemi Wata kawarta Zakiya Nuhu Wacce sukayi Makaranta Tare a Frine Collage Kawancensu ya samu asali ne Tunda kaf Hallayansu yazo Daya na Rashin ji da kuma Rashin ishashiyar Tarbiya Itama Zakiya Bata da Uwa Hannun Muguwar Kishiyar uwa Tatashi Shiyasa batajin Mgana Ita Taje har Chan Zaria inda Zakiyan take chan Tana karatunta,Ta sameta ta Zayyane mata komai ita kuma ta Dauketa Ta kaita Hanyar kaduna Wajen wani malami Dayake mata aiki kan Samarinta Tana Juyasu yayi mata aiki kan Zain akan komai Runtsi bazai Taba Rabuwa da ita kuma Kuma Tana so ya Daina Son kowacce mace da Sha"awarta sai Ita Malamin ya gayamusu zasu yi Nasara ammh Akwai Wani Taurari Dake Tare da Taurarin Shi zain din Yana da Karfi kuma yaga Aurattaya Tsakaninsu Toh Ita din bazai Taba Daina sonta ba kuma Ita Din Tana Daga Cikin kaddaransa Ko bai Fadi Suna ba Tasan kowacece Halima ce Zainarsa. Malamin ya gayamusu zatayi Nasaran Rabashi da Sha"awar kowacce mace,zai Dawo nata ita kadai kuma Bazai iya Rabuwa da Ita sai dai kuma a Tarrayansu yaga Duhu Sosai,Kuma Zasu yi Aure da Juna bayan ya Auri Wacce yake so Sai dai yaga Tashin Hankali Soaai da Turniki acikin lamarin Dina ta yadda da komai Da malamin yace daga Haka suka Zubemai kudi suka Tafi akan cewa Zain din da kansa zai Nemeta Su sasanta. Dawowarsu Zain Lokacin Halima Tana Cikin Shekaranta na Sha uku ne Ta Fara zama Budurwa Tunda Har ta Fara Kirgan Dangi,Zain yayi matukar murna ganin yadda Zainarsa ta kara Girma sai dai yayi ma Su Umma Korafin Zafeera tafi Zainarsa Kiba ita sai Tsaho Yana ta Kunci wai basa kula mai da Ita,Sudai sai Dariya suke mai Ita kuma alokacin Ta Fara Fahimtar komai sai ta koma Jin kunyar Zain din Duk da Tafi kowa Dokin Dawowarsa . Lura Da hakan da yayi sai ya Fara Janta ajiki Sosai yana kara nuna mata Salon Soyayyarsa Wanda Daman itama Dashi ta Bude ido Tsaraba kuwa Rabi da kwata nata ne kantin London sun Shaida Haka Domin Tun Farkon zuwansu Duk Abunda ya gani sai yace zai ma Zainarsa kyau sai ya Siyamata Zafira nata Jin Haushi ita kayanta kadan ne Ita kuwa Halima sai murna Take tana musu gwalo Ita da Faruq. Sun Dawowa ba Dadewa Zareena ta Dawo Gida Hutu da kuma zata Tsaya tayi Wata Shiga agidan Radiom Bauchi Saboda koyon makaman aiki Murna Wajensu ba'a mgana sai Gida ya Sake Rudewa Duk da Tunda Suka Dawo Gidan Alhaji Tsoho Suke yada Zango Kafa Tayi Dadi yanzu baya zuwa Ko"ina Kafafun sun gaza Don ma Hutu da Jin Dadin Suna Tare dashi Zareena ta Dawo ba Dadewa Zain yabi Haddir suka Tafi Abuja kwamansu uku da Zuwa zain ya kasa Jurewa ya Nemi Dina sai da taga mai Wulaknci kana Tace mai Tana kano Haddir bai san ina Zain yake Saurin zuwa ba Suda sukayi Niyyar yin Sati kafin su Tafi ammh Zain yaki zama Yace zai Fara Tafiya Haddir din yazo Daga Baya Da Haka ya Barsa a Abuja yaje Kano wajen Dina Chan ya karishe mata Kwana Hudun acikn gidansu da Hajiya batula ta Yi mgana sai tace abokinta ne bata Damu ba nan sukayi ta Shedancinsu Babu Wanda ya Damu Dasu,har kuma ya Tafi Basu Hadu da Mahaifin Dina ba wai yana Abuja. Koda ya koma Bauchi ya iske Haddir ya Dawo Daya Turkeshi yana Tambayansa Bai iya karya ba ballantana Rike Sirri ba,sai kawai ya gayamai Wajen Dina yaje..Ranar Sai da Suka kusa Dambe da Haddir Daga Karshe akayi Rabuwan Baram Baram Washegari kuma Haddir din ya Hada kayanshi ya koma Abuja Wajen iyayensa Bakuma wanda yasan Abunda ya Faru Tunda Haddir din bai gayama kowa ba Shi ma Zain din Ammh Su Umma sunyi mamakin Abunda yasa Daga Dawowan Haddir Jiya Jiya kuma Gari na Wayewa yace musu zai koma Zareena Tayi Tambayan Duniyan Yaki gayamata komai saboda ya Riga yayi alkawarin zai Cigaba da Rufama Zain wannan Sirrin Har Abada ba wanda zai ji Sai dai yana Fatan ya Daina Abubuwan Dayake yi kada Bacin Rana tazo Ranar da kuma zai yi Nadaman Abubuwan da yake yi. Sun Samu Hutu mai Tsawo Wajen Watansu Hudu agida kana suka koma Wannan karon ba Dawowa sai sun kamallah karatunsu,Wannan karon ma Halima Tasha kuka ammh ya Lallasheta Tare da mata alkawarin Daya Dawo za"a Daura musu Aure Duk inda zashi Sai Su Rika Tafiya,Sun koma da kwana Biyu Itama Dina ta Dawo Domin Taki yarda Ta koma Saboda Zain bai koma ba Kuma ahakan ma yana Zare jiki ya bita chan kano su lalacewarsu sai yayi karyan yana gidan Baban Kaduna ko Gidansu Haddir wanda Har suka koma basu samu wani Fahimtar juna ba sama sama. Tunda suka koma Suka maida Hankali ga karatunsu ganin Abun yazo ganganra,Bamgaran Halima kuwa suna mgana Lokaci bayan Lokaci Game da Birthday Dinsa Ita da Nenensa basa manta Wannan Ranar ko bai kunna Wayarsa ba zai zo ya Samu Sakonninsu na Tayashi Murna Achan Gida kuma su Taru Su Tayashi Murna Suna Cikin Shekara na Shida a London ne Halima da Zafeera suka Shiga Catering School and Snack kuma Shima sai da ta gayamai ya amince kana ta Shiga Na wata uku ne suka gama aka yayesu Bayan an Basu Takardan gamawa. Sai da suka Shekara Bakwai a London kana Suka Tattaro suka Dawo bayan sun kamallah karatunsu Duka Iyayen nasu Sunje musu Murnan gamawa Alhaji Tsoho me kadai da Hajiya mama Basu zamu zuwa ba ammh Baban Kaduna da Mommy iklima Sai Dadyn Abuja da Mama Safiya Umma ce kadai batazo ba Tana Gida Nene ce Gaba Gaba da Abba sai Zareena Wacce Har ta gama karatunta Tayi Bautar kasa ta samu aiki a Gidan Radion Bauchi Sai Zafeera da Halima da Umar Faruq,sai Sadiq babba bai zo ba yana Makarantar Chan Univesrty of Ibadan,Hatta Da Inma Hannatu Taje London Inna Rukayyah ce bata samu Zuwa ba. Wannan Shine karo na Farko Da Dina Taga Zaina ido Ido ta kuma Shaida Irin kaunar da zain yake Fadin yana mata ta ganin ma Idamuwanta Tun da ya samu Tarin kyauttukan kan Hazakarsa da Kokarinsa Duk inda ya saka kafa Zainarsa tana Gefensa baya Yarda Hannunta ya Rabu da Hannunshi Gabadaya kyauttukansa Ita ke Rikemai kowa kuma ya ga Zainar Zain wanda suka Dade suna Jin Labarinta Dina Tayi Bakinciki ganin aranar Zain yama manta da ita ganin yan"uwansa da Halima Wacce ta kara Ninka Tsanan Data ke mata,Zain bai Tuna da Dina ba Sai bayan komai ya kamallah Da Daddare kana ya Saci Jiki yaje Gidanta Bata barshi ya Fito ba Sai da ta Hillaceshi suka aikata Haramun kana ta barshi ya Dawo Sunyi sallama Tunda gobe da Safe zasu koma Gida da Iyayensu,tayi tayi Zain yayi mata alkawarin zai Aureta ammh yaki Kalma Daya yake gayamata Bata ga Matarsa bace Shi Daman bai Taba Cewa yana Sonta ba wannan Harkan ce ta Hadasu kuma Ita ta Nuna tana Ra"ayi Shiyasa Har suka kawo iwar Haka,sallam nasu dai ba wani Dadi Tana kuka tana komai ya Tafi ya barta koda ya Dawo Iyayensa da Ita kanta zainar nashi Tana Ta Nemansa Ba"a ganshi ba sai yayi karya Dayaje sallaman Wasu abokansa ne,Kowa ya  yarda banda Haddir wanda ya kalleshi kawai Shi kuma ya Banka mai Harara nan ya Ja Hannun Zaina suka Kebe Gefe suna ta Hiransu Cikin So da kaunar junansu. *Comments* *Share and Vote..* *Shakira...* *Intelligent writer"s asso..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*              0️⃣7️⃣ "Shekara Daya Zain da Haddir suka yi a Bauchi Suna housemanship Dinsu a asibitin Dr.Saulawa Wanda Dama Dole alhakin komai na asibitin kansu zai koma,Gaskiya sun yi kokari Sosai sai yabama Kokarinsu yake ashekara Dayan da sukayi Sun bada gudummuwa Sosai Wanda ya kara Farantama Alhaji Tsoho rai Wanda Yaji ko Cikinsu ba"a samu Wanda ya Karancin Bangaran kwakwalwa ba akallah ya samu Wadanda Suka karancin Bangarorin da zasu Taimaki Talakawa Wato Yara da kuma Mata. Bayan sunyi Shekara Daya Suna Internship Dinsu Sai kowannensu ya Tafi Yin Course akan Abunda ya karanta na Shekaru Biyu Zain Wata Medicine School ya Tafi Dake Garin Mumbai Shi kuma Haddir ya Tafi Cyprus,wanman karon Iyayensu sunyi mamakin Yadda Suka Raba Wajen karatun nasu ammh Dalilin bamai jin kansu ba Wanda ya Matsa sai yaji Dalili ko Zamansu na Shekara Daya ba wata Jituwa suka samu ba Duk da Tun Suna London Suna Gabda gamawa Zain yayi ma Haddir alkawarin Insha Allahu in suka koma Gida ya Daina Duka Abubuwan da yakeyi Shi kuma Haddir din yana Fatan Haka toh koda suka Dawo Kunsan Bambamcin Ra"ayi Da kuma Yadda Shi Haddir din ko Fita zain yayi sai ya Dora Zargin wajen Wata yaje sukayi Shashancinsu sai Suna yawan Fada da Samun Matsala Dalilin Dayaasa Haddir ya bar Zama Gidan Abba Usman kenan ya Koma Gidan Alhaji Tsoho da kwana Sai dai su Hadu da Zain a Asibiti kowa ya kalli Juna Su Dauke kai kamar ba Aminan Juna Ba Wadanda suka Tashi Tare Koda Abba Usman ya Farga da Barin Haddir Gidansa Har Gidan Alhaji Tsoho ya Bisa ga Shi ga Hajiya Mama ga Alhaji Tsohon Ga Haddir din ya Tambayeshi ko anyi mai Wani Abu ne..? Domin Tun yana Yaro Shi ya Rikesa har ya kawo Girmansa Bai Taba ganin Sun Raba Wajen kwana da Zain ba sai yanzu da Girma ya kamasu ko Sun samu matsala ne Tun da yasan Halin Zain din da saurin Fusata,Ammh sai Haddir din yaki yarda yace komai Ya nuna ma Iyayansa kawai yana Sha"awar zama agidan Alhaji Tsohon Tunda ko da Zain Da Zareena Tun Suna yara nan Gidan Alhaji Tsohon kamar gidansu ne sai Hajiya Mama Ta gaji da Kirniyansu ta Kadasu Gida da Haka ya Kashe bakin kowa ammh bawai Domin sun yarba ba Sai Domin Daga Zain din Har Haddir din sunki basu Damar Fahimtar wani yasa suka Fita Batunsu Suna Tunanin koma Miye Chan Tsakaninsu ne. Dan zaman da Zain Yayi agida kafin Tafiyarsa Mumbai ya Tada Tsiyan sai an Daura mai Aure da Zainarsa Domin alokacin Da Ita da Zafeera Suna Cikin Shekarunsu na Sha bakwai kenan a Duniya Har da Umar Faruq,Duk da Zafeera tafini Girman Jiki ni na Fita Tsawo Da kuma Cikar Hallitan Ya Mace,Kuguna da Kirjina Tun ban kai Haka ba Kuguna da Kirjina yake aciki in ka kalleni zaka Fahimci Allah yayi Mace anan Wajen Allah ya sani ni Ba Fara bace kuma ba wata Chan mai kyau ba ammh kuma in da Tsarina Fuskata Daidai Misali ,Zafeera ce Fara ni kuma Bakin Fatar Mahaifina na Dauko Inji Goggo Halima Wanda Bansansu ba sai dai a Hoto Tabbas dana Biyo Hasken Fatan Mahaifiyata ko Zafeera bazata Nuna min Haske ba. Ina da Sanyin Hali da kunya da kwaici Wanda Umman ke Fadamin Duka Hallayan Mahaifiya tace na Dauko,Zaman Zain agida yasa ganin yadda na koma sai ya Fara Kafa min Dokokin Rashin Fita Saka Hijabi da dai Sauransu Daga makarantar Boko sai Islamiya kadai yake yarda naje sai Kuwa Gidan Alhaji Tsoho,Da muka samu Hutun makaranta naje Abba Ya barni Tafiya Gaga Wajen Dangin iyayena Musamman ma Goggo Halima Wacce koda wani Lokaci Tana Zuwa Dubani ita nake gani kamar Uwa gareni Dakyar Zain ya yarda yabarni naje Da yace na Jira Weekend yakai ni ya Dawo Dani sai da Umma ta Hadashi da Abba yamai Fata Fata kana ya yarda ya barni na Tafi ammh Ko Sallama bai yarda Munyi dashi ba yana Fushi ya Fita Zuwa asibiti kuma nayi ta Kiransa awayar Nene Tunda ya Dauka Yaji muryata ya kashe Nayi ta Kira bai Daga ba Zafeera tace Zata Rakani Tare muka Tafi Da ita. Kwanamu Goma agarin gada a gidan Goggo Halima muna Shan na kauye,Mu zazzaga Gidajen yan"uwa da abokan arziki Sai mamakin Girmama Suke da yarda na Zama Cikin Hakane Wani Abokin Wasa na ya ganni yace yana Sona Hisham Wanda Yake karatu a Usman Dan Fodiyo University Sokoto yana Shekaran Karshe Lokacin Daya Tunkare ni da Mganar na Nuna mai Ni ina da Mijina yaki yarda Har Sai da ya Danganta da Goggo Halima yana mata magiya kan Shifa Da gaske sona yake Goggo Halima batayi kasa a Gwiwa ba ta gayamai Gaskiyan Cewa Ina da Mijin da Zan Aura Tunkafin na Fito Duniya kuma yana nan yana Jirana Da wannan mganar Goggo Ta Sahalemin Hisham Bayan Shi ma na samu Haren Haren Wasu Samarin Da Dama Nida Zafeera wannan Dalilin yasa muka Dawo kawai ba Shiri Saboda Sanin Halin Zain da Kishi,gashi ma yana Fushi da ita bai nemeta ko ta Wayar Goggo Halima ba Tunda suka zo Har suka koma. Bayan mun koma Zafeera ta Rariyan Baki Taje tana Ba Su Umma da Nene labarin Abunda ya Faru a Gada karaf ya Fada kunnan Zain Ranar kuwa Yayi ta Bala"in ya kuma Tafi Gidan Alhaji Tsoho ya zauna mai kan Shifa Sai an Daura mai Aure da Matarsa,Dakyar Alhaji Tsoho ya Lallashe da Cewa ya bari Yaga Duka Iyayen nashi Suyi mgana Abunda suka yanke Shikenan Da Haka ya Hakura ya bar mganar,Bayan kwana Biyu Alhaji Tsoho ya Tara Duka Ya"yansa Dama suna Taruwa Duk bayan Wata Biyu Domin Tattauna Abunda ya Shafesu ya sako Mganar Zain da Bukatarsa Tun kafin ma Kowa yace komai Baban Kaduna yace bazai yuyuba Duka Duka nawa Zain din yake Shekarunsa fa 27 ne Karatunsa ma bai gama ba meya Tara mai ya ajiye..? Nan fa ya Fara Fadan Yace zai samu Zain din Maza ya bar wannan mganar Karatu zasu koma Dukkansu Shida Haddir din su kara Daukan Cos kan Abunda kowannensu ya karanta Jin haka yasa kowa yayi Na"am da mganarsa Shi da kanshi ya samu Zain din yamai Fata Fata kana ya Shiga Taitayinsa ya kuma ce in yasa Tsiya bazai Auri Halimar ba sai ta Gama Digree jin haka yasa ya bar mganar sanin Halin Baba kaduna kaifi Daya ne,Zareena da Haddir sai Dariya suke ganin yadda Zain din yazama Abun Tsausayi Sai Laifin ya Shafi Harda ita Zainar nasa Wajen Sati ya Dauka baya mata mgana ko Tayi mai mgana sai ya Dauke kanta wai Takan yace ta samu Abba tace itama Tana son ayi musu Aure yanzu Tace bazata iya ba Shikenan Fushin ya Shafeta Dakyar ta Lallasoshi ya Hakura aka wuce Wajen. Bayan Haka sun Taba zuwa Biki Kano Bikin Babbar Diyar Inna Rukayyah mai Suna Asma"u Abunda yasa ma Taje harda Zain din yaje Daurin Auran Shiyasa ya barta Taje ammh sai da yayi Nadama da Wani Abokin ango ya makalema Halima awajen Lonching Ranar kuwa kowa yaga Kaunar da Zain yake ma Halima ko kayanta bata Daukaba ya kwasheta Suka koma Bauchi sai dai Su Zafeera bayan an gama Biki suka Dawo mata Dashi,Ko Tafiyarsa ma Mumbai Sai da aka Sha Daka da kuma Tarin alkwarin da Nene ta Daukan mai na Kula da Duk wani Motsin Zainar nasa kada wani yazo Daga baya ya Batamai Shirinsa,Da kuma Tabbacin da Alhaji Tsoho ya bashi kan ko Bayan Ransa yasan Ya"yansa zasu so su Cika Wasiyyan Maryama kan Auransa da Halima Dalilin Dayasa Hankalinsa ya kwanta kenan ya Tafi ya bar Zainar Nashi Zuwa Lokacin da zai Dawo Ta kamallah Secondry Sch Dinta sai mganar Auran. Da Farko bayan Sun Dawo Nageria Baya mgana da Dina,Duka Hanyar da yasan zata Sameshi ya Dakileshi Saboda yana son Cikama Haddir Alkawarin Daya Daukan mai Sai dai me,Yayi kokarin ya Jure ya kasa Ya Rasa Dalilin Dayasa yake Kasa Rabuwa Da Dina Tun Yana Bauchi ya Fara Nemanta Suna Mgana Sama sama sai konawar sa Mumbai ta Sauya komai Domin Dina Tana kai mai Ziyara har chan su Sheke ayarsu son Rai ba Wanda ya sani Dama Haddir ne ke gayamai gaskiya kuma Basa Tare sai kawai Zain ya koma Ruwa Tsumdum Duk da wani Lokacin yana so ya Daina ko Domin Zainarsa ammh Kuma sai ya Kasa Gashi dai ya Daina Hulda da kowacce mace sai Dina Dinar ma yana iya bakin kokarinsa Wajen yakiceta ammh Ina tana kara Shiga Jikinsa ne Wanda ya Rasa gano Dalilin Haka. Suna Shekara Daya Da Tafiya akayi Bikin Zareena,Wanda ta Auri Wani Bakatsine mai Suna Jawaad,Ma"aikacin kamfanin Shinfida Titina kuma Babba ne awajen,Allah Sarki Daga Haddir Har Zain ba wanda ya Hallaci Bikinta Har acikin Zuciyar Zareena Taji wani iri ammh ya zatayi Tunda ba Hali da sun zi bikinta ta sani Da Farko Katsina suka Fara zama bayan Wata Uku kuma Approving letter Dinsa ta fito ya samu aiki a Babban Birnin U.S America Da Wani Babban Kamfanin Shinfida Kwalti na kasar Da Farko Shi kadai ya Fara Tafiya bayan Wata Daya kuma ya Dawo ya kwashi Zareena suka Tafi Zama na Dindin Tunda Sun mai Takardan zama dan kasar Sun bashi Gida da Mota da komai na Bukatar Rayuwa,Dukkansu sukayi Sallama da Ahalinsu suka koma Chan da Zama,bayan komawarsu da wani Lokaci Zareena Ta kira waya tace ta samu aiki a gidan Radion Dake Shiyarsu Iyayenta suka Tayata Murna ainun. Su Zain suna gabda Dawowa mukayi Candy Nida Zafeera da Umar Faruq,Lokacin Ya Saddiq Babba yana Abu Zaria inda ya Fara Masters Dinsa,Muna kamallah makarantar iyayanmu suka Fara Shirya Shiryan Aure na da Zain,kamar yadda sukayi mai alkawarin Tuni Sun kai Chan Gada da Sakon Lokacin yayi da zasu cika Wasiyan Maryama Goggo Halima Tafi kowa Murna da Haka Zain yana Mumbai aka saka Lokacin Bikin mu nan da Shekara Daya bayan ya Dawo Ya Fara aiki ya samu Muhallinsa Duk da wannan ba Matsala bane ammh Iyayansa sunfi son ya zauna da Kafafunsa Dagani Har Zain an Raasa wanda yafi kowa Murna wannan Auran Sai dai ni nawa na Boyeshi Saboda kunya Ammh Shi kam Daga chan kamar yayi Tsuntsuwa ya Dawo har yana ma Nenen korafin an saka Lokacin Bikin da Tsawo Tace karya Damu kamar Gobe ne. Anyi Haka da Wata Biyar Haddir ya Fara Dawowa Tsskaninsa da Zain kwana Goma ne Shima ya Diro Abunda zai ba kowa mamaki da Hadin kayan Lefensa ya Dawo akwatunasa 12 yayi ma zainarsa da yan Kudaden da ake Ta Biyansu Tun Suna London To Dayake baya komai dasu Tunda komai Iyayansu sun Daukemusu wannan Nauyin sai ya Rika Tarasu Domin irin Haka kowa ya Jinjina ma Kokarinsa Sosai Nene sai Murna Take Yaronta yakara Hankali Umma kuwa Sai Shirin Aurar dani kawai Take Abunda kowa na Tututiya da Zai Aurar da Nashi. Suna Dawowa ba Bata Lokaci suka Fara aiki na Dindin da asibitin Dayake zaman Jiransu Duk da sun samu Gayyace gayyace Daga asibitoci Dadama ammh Suka Ture wannan Bukatar sukace sun Yi karatun Likitanci Saboda su Cikama Kakansu Burinsa sun yarda sun kuma amince zasu aiki Tukuri a asibitin Dayake mallakin wanda yayi Sanadiyar kawo iyayansu Duniya ne koda bazasu samu komai ba Zasu yi Hakuri da Dan Albashin da asibiti zata Dinga Basu. Dalilim Fara aikinsu yasa Suka Gayyato Likitoci abokan Karatunsu Domin suzo ayi Tafiyan Tare dasu Dr Imran abokin Karatun Haddir ne,Dr Peter kuma acikin asibitin suka zo suka Sameshi,Lokacin da Suka Fara aiki sai Haddir ya kama Wani Flat House nan kusa da asibitin Saboda Jeka ka Dawo Alhaji Tsoho yayi ta Ciwon bakin Haddir ya Dawo Wajensa ko Wajen Abba Usman ya zauna ammh yayi Biris da mganar. Sun Fara aiki da Wata Biyar Bikin Zain da Zainarsa ya Taso aka Fara Shirye Shirye Sai ana Gabda Bikin ne Abba Usman ya Damkama Zain makullin Katon Gidan Daya gina mai a Federal Lowcost,Wanda zasu zauna Shida Halima Farinciki Wajensa Ba"a mgana su kuma su Umma suka Dauki masu Tsara Gidaje suka kai suka ga yanayin Gidan suka Saki kudi zuwa kawai sukayi Suka Tsara komai Duka Iyayen nasu suka Hadu suna Gudanar da duka Shiryen Shiryen yan Gada ma Abba Usman yace karsu Damu Daga Halimar Har zain Duka ya"yans kuma zai yi Abunda kowani Uba Nagari kema ya"yansa Dole suka Zuba ido suna ganin inda Tsananin karamci da Dattako ke aiki. Anyi Auran Zain da Halima Tana Da Shekara 20 cif aduniya Shi kuma yana Cikin na 29wannan Bikin Ya Tara Dimbin Tarihi,Hatta Zareena Dake U.s Tazo Sadiq babba ma yazo Daga makaranta kaf Duka iyalan Baban kaduna da na Dadyn Abuja Inna Hannatu da nata Iyalan Haka ma Inna Rukayyah itama da nata Ahalin yan Gada ma Sunyi bajinta Mota Biyu Mota Daya na mata Mota Daya na Maza yan Daurin Auran da aka Daurashi a Gidan Alhaji Tsoho wanda Abba Usman ya zama Wakilin Amarya Yayinda Baban kaduna ya zama Wakilin zain kuma ya Biyamai Sadaki. Ansha Shagalin Biki Haddir ne Babban Abokin ango yayinda da Zafeera ta kasance ta Hannun Damar Amarya sunyi Lonching Da Dinner wanda Hotunan Dinner ne suka dinga Yawo Har Zakiya Nuhu kawar Dina taci karo Dashi Wacce ta samu aiki a Hukunar Layin Mtn Anan Bauchi Take da Office,nan take Zaune Tunda Har ta Siya gida Da Mota,Dina bata da Labari Domin Duk Rashin Rike Sirrin Zain bai iya gayamata Zencen Auransa ba sai da Zakiya ta gayamata ta kuma Tura mata Hotunan Dinner Da taga yan"uwa sun Dora akafafan yada Zumunta Lokacin da Dina Ta Gama karatunta ta Dawo Kano Har ta Fara aiki a Mallam Aminu kano a matsayin Cikakkiyar Likitan mata. Lokacin Dataci karo da Hotunan Zain da Halima Hauka ne kadai Dina Batayi ba Sai da Zakiya ta Baro Bauchi tazo Tana lallashinta da bata baki,Washegari Suka koma Wajen malaminsu,Nan yake kara Tabbatar musu da cewa Daman ya gaya musu Tsakaninsu akwai Aure da Zuru"a Sosai,Itama Tsakaninta Dashi akwai Aure sai dai bai san yaushe ne ba bai kuna san Wani Turniku da Duhun daya gani acikin Lamarin ba,Hakuri ya Bata da cewa Taje ta Jira Lokaci ammh ya gayamata In dai Tana son mallakan Zain Har Abada Toh sai dai Ta daina Sukan Matarsa Wacce Duk Duniya ba wacce yake so bayan Iyayensa sai ita. Da Haka Suka Tattaro suka Dawo Bauchin Ta koma Gidan Zakiya Tana Jinyar zuciyata Ita take ta aikin Lallashinta da bata baki karta Damu Zain bazai barta ba Tunda malamin ya Riga ya Tabbatar mata,da wannan Mganar yasa Hankalin Dina ya Kwantar Har ta Tattara ta koma Kano Saboda aikinta Lokacin Tuni Babanta ya zama kwamishan kudi na Jihar kanon Dabo. Fadar irin gyaran da Nasha Wajen Umma ba"a mgana Tamin Abunda Ko aya"yanta bata Musu bata bama Tuna wai Danta zan Aura kawai ita Ni yarta ce zan Auri wani ne chan Dabam Wato Babban yaron Nene Itama Nene Tayi Rawar gani Sosai da Bajinta an kai Amarya Gidanta na Aure Tare da Nasihan duka Iyayan Rikonta da kuma Ahalin iyayenta na Gada Goggo Halima Tayi mata Nasihan Zaman lafiya da Hakuri da kuma yadda zata gyara zamantakewarta. Anyi Biki lafiya yan"uwa Da Abokan arzuka sun Koma Gidajensu da Fatan zaman Lafiya ga Ma"aurata Fadar irin Daran Farkon Daya Gudana Tsakanin Zain da Halima Bata baki ne,Domim Shekara ashirin yayi Yana Dankon Jiran Ganin Wannan Ranar bai Tsausayamata Sai da ya Famshe wadannan kwanakin Yaji Halima Dabam acikin Sauran mata kamar yadda Take Dabam acikin Zuciyarsa wata irin Soyayyah da Zaman Amana da yarda Dakai suke ma juna,Zain ya Riga yagama Sangarta Halima da Salon Soyayyarsu Ita kuma Tagama yardan ma kanta Bata da wani Wanda zata yarda Dashi bayan ZAIN shine Duka Sirrinta Ganinta da Jinta Ta gama Bashi Duka yardanta ta ganin Shine abokin Sirrinta Shima Haka tana ganin Shine kadai yasan Rauninta Tana ganin Bayan Iyayenta ba wanda zai kai adadin kaunar da ZAIN yake mata Shiyasa itama Ta Sadaukarmai Da Duka kanta da komai nata Domin Biyansa bashin Dimbin kaunar Daya ke mata Bata Taba kawo ma kanta Watarana Zain zai iya Cin Amanarta ba Shiyasa Zuciyarta da Ruhinta suka gama Bashi Dukkan Wata yarda. Bayan Auransu da Wata Biyu Duk Yadda Zain yaso kada ya Neme Dina sai ya Nemeta,Saboda su kasance Tare yasa yayi mata Tayin aiki a asibitinsu Ba gardama ko Neman Shawara kawai ta amince kuma Da ta gayama Mahaifinta ga Ra'ayinta bai Tsaya Son Jin Dalilinta ba ya amince mata,Saboda yana Sonta kuma ya Riga ya bata Damar yin Abunda Taga Dama Haddir sai dai kawai Rana Tsaka yaga Dina acikin Asibitinsu Da Sunan Sabuwar ma"akaciya mamaki ya kamashi bai iya Shuru ba sai da yayi ma Zain mgana kan Meyasa ya gayyato Dina..? Ya barta Chan kano Inda ta Fara aikinta mana..? Ko ya Dawo Da Ita kusa Dashi Ne saboda su Cigaba daga inda suka Tsaya..? Nan sukayi ta ba Dadi Zain din ya Musa ma Haddir Zarginsa akaro na Farko yayi mai karya Ba Saboda komai ba Zain yana jin kunyar Haddir ya kara kamashi da laifin da yayi mai alkawarin ya Daina Uwa uba kuma ga Halima Wacce bata inda ta Rageshi,Auransu Duka Duka Wata Biyu ammh kuma Har ya Fara cin Amanarta..? Koshi yana son ya yakice Dina acikin Rayuwarsa Tunda ba Sonta yake ba ya Dade da gayamata bazai iya Auranta ba,Su Rabu ammh Abu kamar Zanen kaddara Tunda ta Shigo Rayuwarsa ya kasa yakiceta. Tun Zuwan Dina asibitin Dr.Imran ya kyalla ido ya ganta Ransa ya Biya Dama mayen mata ne,Tuni yake taya Nurses Din nan Wacce ta bata kai Shikenan Yayi Kokarin Tusa kansa ammh Dina Taki bashi Fuska Har Fitomata yayi da Maitarsa ammh ta Watsa mai kasa acikin Ido,Daya gane Zain take so Shi kuma sai yana Zugata da Cewa Zain baya sonta kowa ya Shaida Mace Daya yake so Itace Firstlove in yana Fadamata Haka ji Take kamar ta Mangareshi Ya gaji da Maitarsa bata kulashi ammh Duk da Haka bai Hakura ba Tsakaninta kuwa da Haddir gaisuwan Sama sama ne kawai na Wadanda suke aiki awaaje Daya ammh Ta Riga ta sani Tun Farko Bata Burge Haddir Wani Lokacin Zain yana kaucema Haduwarsu da Dina ammh Ita ke Hillatansa Zuwa Gidanta Chan su lalace,Ko a Office Dinsa baiso suka Fara wannan Mu"amalan ba Ammh Dina Tayi ma Zain Farin sanin Da tasan Hanyoyin Datake kunnosa,Shiyasa baya iya kaucema Tarkonta Sunsha yin Fada kaca kaca kan Firstlove dinsa Daga baya kuma su koma Su Dinke Likitoci Dadama su Na Dora Musu Zargi ammh Rashin Shaida yasa kowa ya kauda kansa Tunda Zain din kwata kwata bai da Sakewa Saboda nan ba Wata kasa bace Gida ne kuma Duk Abunda zai yi Mara kyau zai iya Taba Mutumtakansa Data Gidansu Shiyasa yake Kokarin Kiyayewa Bayan Auransu ne Halima Tayi Jamb Taci ita Da Zafeera suka Rubutu kuma Dukkansu sunci,Dukkansu ABU samaru Zaria suka samu ammh Zain yace Zainarsa bazata ba,Dole Zafera kadai Tatafi itama Din An Sauya mata BUK kano Tatafi Tana zaune gidan Inna Rukayyah Tare suka Fara karatu da yar Autatanta mai Suna Shema"u, Shi kuma Faruq Ya Tafi Kasar Ketare Wato Chicago inda ya Fara karatun Digree dinsa achan Ayayinda Shi kuma Zain ya Sauyama Halima makaranta Zuwa ATBU BAUCHI ta Fara karantar B.SC Mathematics Tana Shekaran Farko ne,Lokacin ya Siya Motar Hawa Ita kuma Abba Usman ya Siyar mata NATA Saboda Zirga zirgan Tafiya makaranta Tunda Zain yana zuwa Wajen AIKI bai zama ba lalle Tafiyansu tazo Daya ba,Shidai Zain ya bata Gudummuwar Siya mata Tsaleliyar Waya sai ta bama Zainab Tsohowar Tata wacce Abba Ya siya musu ita da Zafeera tun suna gida Tun Zuwanta makaranta Suka Hadu da Laila Adam,Course Dinsu Daya,Kuma Sai Halinsu yazo Daya Tunda itama Lailan akwai kokari anan garin Bauchin take da zama ita da iyayenta Duk ba masu Hali bane Suna Da Rufin asiri,Bayan Zafeera Laila ce kadai Halima ta yarda Ta sake kawa da ita Tunda Zafeera Tana makaranta sai dai in sunyi Waya,Duk wanda ya zauna da Halima Dole yasan Waye Firstlove agereta,Laila Taje har gidan Halima Tasan Zain Shima yasanta Tunda Yana zuwa Daukanta Wani Lokacin in bata je da Motarta ba,Har gidan su Umma Taje,Tasha kuma Raka Halima Gidan Alhaji Tsohi suje su gaishesu Yarinyar tana Da Hankali Shiyasa Har Zain ya yarda Halimar Tayi kawance da Ita. Halima Bata Taba ganin Dina ba Sai sau Daya Da Zain zai kaita makaranta Ranar Motarta ba Lafiya tana Wajen gyara sun Fito sai ya samu Kiran gaggawa Daga asibitin sai ya Fara Biyawa da Ita asibitin Har Cikin Office Dinsa awannan Ranar ne wasu Suga Firstlove dib Dr.Zain,Aranar zaina taga Dina Ta ganta Ido Cikin Ido Tunda batasan da zuwanta ba Ta Shiga Office din Zain din ne Ta ganta ganin Ta Tsaya Tana kallonta ne yasa Shi Zain din ya Gabatar da Halima ga Dina Itama Dinar ya gabatar da ita akan cewa abokiyar aikinsu ce Dr.Dina gaddafi Sherrif. Hannu Dina Tabama Halima sukayi musabaha kowanne na Kallon kowa da Wani Tunani Dabam Ita Halima aganin Farko Taji Zuciyarta ta Fara rawa Akan Dina Haka kurum taji Matar bata kwantamata ba Duk Kokarinta na tayi mata Dariya kasawa Tayi sai yake,Shima Zain din bai yarda Zainar Tasa ta gano wani Abu ba,Ya Tattarata suka bar asibitin a Hanya da zai kaita Makaranta sai da Halimar tace ita Kuwa Taji Zuciyarta bai kwanta mata da Wannan Dinar ba,Da ta Fadi Haka yaji mamaki ammh sai ya Shanye mamakinsa yace mata Dama Haka Allah ke Abunsa ba kowa bane zakaji ya kwantamaka ba Ammh Dina Bata da matsala Daganan bai kara mgana ba itama Bata kara mai Zencen Wata Dina ba ammh Abun ya Tsaya mata arai Har Haddir ta Tambaya yace mata Karta Damu Juz kawai abokiyar aiki ne Shi ina zai yarda aji mutuwar sarki abakinsa ba Domin Har ga Allah Tsausayin Halimar yake ji Yana Tsoron Faruwar wani abu indai Sirrin Boye ya Fito Fili. ******* Fitowa Tayi Daga Library Ranta a matukar bace da kalaman Laila agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin Gucci takai Duba Taga har pass 10 kuma sai 11am zasu Shiga Lectures Din Dr.Tafida ne Baya son Wasa ammh da ba Haka da gidan Umma zata wuce kawai. Departement Dinsu ta koma ta Samu Waje ta zauna Ta Fito da Wayarta Tana latsawa Zafeera take son Ta kira sun kwana Biyu Basu yi mgana ba,gabadaya Walwalarta Ta Ragu akowani Dakika kalaman Laila gareta Suna Dawowa mata kuma Suna sanya mata Faduwar gaba da Wani Rauni wanda Ta Rasa Daga Ina yake Fitowa. Ta kira Zafeera 2missedcalls bata Daga ba sai ta kyaleta Tana Tunanin kila itama Tana Class ne Tana kokarim maida Wayarta Cikin karamar Jakarta Laila ta kariso Wajenta bayan Ta gaji da nemanta Kafin ma Ta samu Zama Halima tayi Saurin Dagowa Lokaci Daya Tana Dakatar da ita Hannu. "Wai bana ce miki ki kyaleni ba Laila..? Don Allah ki barni Dazu najure kin Fadi maganganu Son Ranki Buh by now Zuciyata bazata iya Jure waba gwara ki Kyaleni kamar yadda nace Simple...! Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Bacin Rai da Sauri Laila Tasha Gabanta Tana Fadin"Naji zan kyaleki Halima..Ammh plz ya kamata Ko Sau Daya ne kima mganata kyakyawan Fahimta ba Nufi...! "Ya isa Laila..Sai yanzu na gano Inda kika Dosa Wato Kina son mijina,Shiyasa kika Fito da wannan Hanyar da Rashin Jituwa zai Fara Shiga Tsakaninmu saboda ki samu Wata Dama ko..? Tafada tana Watsa mata wani kallo Waro Ido Laila Tayi kafin Tace"Wa...? Innalillahi Wlh banzata ba Halima Banzata zaki min Wannan kallon ba..Ammh komai ya Faru ba laifinki bane ni naja..Allah ya baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba kuma ina so ki sani yau ko Mutuwa kikayi bazan iya Cin Amanarki ba Ballatana Kina Raye Halima..! Ta karishe Fada Idanuwanta na kawo kwallah kafin ta Juya Ta Fara Tafiya Halima da kalaman Laila suka kashe ma Jiki ta Daga Kafa Tana Tafiya ga Lailan Tana Fadin"Haka zalika kamar yadda Ko Da bana Raye bazaki iya Cin Amanata Haka ma Firstlove Ko Gawata bazai iya Cin Amana ba Laila Ballatana Da Rai na da lafiyata Bazan Taba yarda Dake ba..Domin Firstlove ya Fara Min Kauna ta gaskiya Tun ina Cikin Mahaifiyata..! Cak Laila Ta tsaya ammh bata Waigo ba sai Halima ce Tasha Gabanta Tana Fadin"Nima am Sorry In mgana ta bata miki Rai I did Mean to hurt u..! Tafada Tana Riko Hannuwanta Mirmishi Laila Ta saki kafin tace'Na Fahimceki Kawata..Samun Wannan kaunar ta Firstlove dinki gareki sai An Tona Irin Labaran da muka Sha karantawa ne English Novels Da Hausa Banta Tsammanin akwai Ira iransa a xahiri ba..! " Halima Ta saki wani kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Gashi kin gani Wajen ZAINAZAIN..! laila ta Jinjina kai Tana Fadin"Kwarai kuwa na Shaida wannan kaunar Daga Allah ce.."Dariya suka Saki Lokaci daya kafin su Fara Tafiya Tare Hannayensu na Cikin na juna suna mgana Sama sama Wanda duk wanda ya gansu zai Fahimci Suna da kyakyawan alaqa akwancensu. Cafteria suka je suka Sha Lemo da Snacks kafin su Wuce Class sai 1pm suka Fito Daga lectures Daganan Halima tayi ma Laila Tayi Zuwa Gidan Umma bata yi musu ba Ta Bita ammh Bayan ta Kira mamarta Ta gayamata Suna zuwa Gidan Umma su Saudart suka Fara Ihun Murnan ga Anty Halima ga Anty Halima Tun kafin ma Tagama Daidaita parking Dayake suna Haraban Gidan ne sai ga Zainab ta Fito suka Rumgume juna cikin Ladabi Take gaida Laila wacce Darajan Halima yasa Duka yaran ke Kiranta Anty Laila. Bude Bayan Mota tayi ta Dauko Cake din suka Dunguma Cikin Gida Da Umma suka Fara cin karo Halima Tatafi gareta ta Rumgumeta Tana Fadin Tayi Kewarta Itama Rumgumetan Tayi Tana Fadin Itama Tayi kewarta Nene na gefe Tana Fadin Ayi dai mugani Umma tace anyi kuma Sun gani Laila na gefe Tana Dariya Cike da Sha"awan wannan ahalin Kafin Halima ta saki Umma Taje ta Rumgume Nene tana gaisheta ta Shafa kanta tana saka mata albarka Laila ta gaishesu suka amsa Cikin Sakin Fuska Suna Tambayanta karatu Daganan zainab Ta Shiga nuna ma Halima da Laila Vidio da sukayi ma Su Umma da Safe Lokacin da Zain yake yanka Cake sai da suka gama gani Halima tace kowa yazo suyi nasu Shagali Yanka Cake din akayi kowa yaci Halima Ta Diba Dayawa tace Na Alhaji Tsoho ne da Hajiya Mama su Umma nata Dariya Sallah sukayi sukaci Abinci kana Laila Tayi musu Sallama Tatafi Gida Saboda Mamarta zata Fita tace ta Dawo Da wuri Tunda kannenta Duk kanana ne suna Makaranta Gidan ba kowa. Sai da Halima Tayi La"asar kana Ta bar gidan Shima Firstlove ya Kirata yace ta koma Gida Hakanan Daganan Gidan Alhaji Tsoho ta Biya ta gaishesu Shi da Hajiya Mama da Tabawa ta kuma basu nasu Cake din Hajiya Mama naci Tana Fadin"Shidai Zanullahi dan gata ne..Kowacce Shekara sai munci wannan Abun mai Dan karen Dadi da Sunan wai Bazday dinsa..! Gabadaya Halima da Alhaji Tsoho suka sakamata Dariya Halima na Fadin karta Damu zata Shiryama Alhaji Tsoho ammh sai ya Cika Shekara 100 aduniya kana Zata Shiryamai Suna Ta Firansu suna Dariya Bata Jima ba tayi musu sallama Tatafi Alhaji Tsoho na kara Jadaddamata ta kula ta Dinga Tuki a Hankali tace Insha Allahu akoda yaushe tana Alhafari da Alhaji Tsoho Domin Tana kallonsa kamar kakanta ne ya Kure mata Dukkan Rashin kakanni Shi da Hajiya Mama. Daganan Motarta Ta Shiga Ta koma Gida ta Fara Tunanin me zata Dafa musu na Dinner ita da Firstlove gefe Daya kuma Lokaci bayan Lokaci kalaman Laila na Dawo mata Ganin ta saka Abun Aranta zai Dameta sai ta Watsar da wannan Tunanin ta kwabe kaya ta Shiga tayi wanka ta Saka Saukakkun kaya na Zaman Gida Riga da Wando ta Fada Kitchen. *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             0️⃣8️⃣ "Dina na Fita Daga Cikin asibitin bata Zarce ko"ina ba sai Dan madaidaicin Gidanta wanda mahaifinta ya Siya mata take zaune aciki Daura da asibitin yake ba Nisa Wanka Tayi ta Sauya kaya zuwa Wata Doguwar Rigan Abaya baka tayi Rolling din Vail Din gyalen Bisa kanta kana ta Dauki Wayarta Ta kira Zakiya tace mata Tana Office ne ko Tana gida..? Nan tace mata Tana Office,kawai sai ta yanke Kiran Wani Hill din Takalmi ta sakamai mai Tsawo Ta zari key dim motarta Wanda ke Hade Dana gidanta ta Fito ta Kulle kana Ta Fada Motarta ta Bata Wuta kai Tsaye Babban Ofishin Kamfanin Sadarwa Ta MTN ta Nufa Zuciyarta Cike da Tunanin Yadda zatayi Da Zain Domin bata Jin zata yi Sanyi kamar yadda yake Bukata agaresa. Tana zuwa ba wani Neman izini Domin Duk wanda yasan Zakiya acikin ma"aikatan Dole yasan Dina Saboda kawaye ne na Sosai koda ba Bangaran karatu Daya suka karanta ba aikansu ya kawosu gari Daya kuma Halayyansu da Dabi"ansu tazo Daya Shiyasa Bond Din kawance su har yanzu yana nan Zakiya Babba ce awajen tana matsayin Matakiyar Md kenan Wato Manaja Shiyasa Tunda Dina ta Shigo ma"aikatar take ta samun gaisuwa yake kawai Take Tana Daga Hannu Domin bata Cikin Hayyacinta Gudu Gudu Sauri Sauri ta karisa ga Babban Office din zakiyan wanda ya zama Tamkar gidanta Wajen Zarya kamar yadda Shima Office din Dina na asibiti ya zama Dandalin Zakiya din. Tana Shiga ta isketa Hakimce kan Kujeran ta mai Juyawa da Mutum din nan katon Office ne wanda bayan katon Tuberin aiki da kujerun karban baki akwai Kujeran gida wadanda Suka karama Ofishin kwanya sai karamin Firaza sai Kofar Tiolet inda Mutum zai Shiga in Lalura ta kamashi. Dina na Shigowa ta Watsar da Key din Hannunta da wayarta Saman Daya Daga Cikin Kujerun wajen ta Nufi Fridge din ta Bude Ta Dauko Ruwa Swan mai Sanyi akwai kananan Kofuna a kife saman Fridge din ta zari Daya ta Tsiyaya ta kafa kai Tana Sha Cikij gaggawa Duk zakiya Dake Hakimce Tana Waya idanuwanta na kanta,Sai da Ta kusa Shanye Rabin Ruwa kana ta Dakata tana Sauke Numfashi Lokaci Daya kuma ta maida komai Cikin muhallinsa ta Baro Wajen zuwa Kujeran Dake Fuskantan Zakiya ta Zauna Tana maida Wani karamim Numfashi. Ita kuwa Zakiya kai ta Cigaba Da kadawa Tana kuma Wayarta Lokaci Daya Kusan Mintina goma da Shigowar Dina Office din ammh bata gama ba sai wani narkema wanda Take wayar Dashi Take tana Tsarashi Da kalamansu na yan Duniya Ran Dina ya Fara baci Ta kai Duba Zuwa ga Agogon Guccin Dake Tsitsiyan Hannunta Lokaci Daya Ta saki Tsaki Tana Fadin"Ko in koma Inda na Fito ne..? Tafada Tana Sakarma Zakiya manyan Idanuwanta Mirmishi ta Saki Tana Girgiza mata kai Kafin Tayi Saurin sallaman wanda Suke wayan Lokaci Daya Tana kallon Dina Cikin Shakiyanci Take Fadin"Dr Dina Gaddafi Sheerif...' Karamin Tsaki Dina Taja kafin Tace"Karki Batamin Rai..wai don Allah zakiya yaushe zaki Daina Harka da yan Barikin nan Tsoffin Banzan nan ne..? Me kike nema Kudi..? Suna..?matsayi..? Duka fa Allah ya baki Zakiya Wannan Rayuwar Da kikeyi sam Bata Dace da mace mai aji kamar ki ba..! Wani Shu"umin Mirmishi Zakiya Tayi kafin tace"Allah ko.? Ke bari ni nayi Tsoffin Banza Da kike mgana Duk fa yan Siyasan munr mu Dina gwara na karbe kudaden Tunda Duka kudin aikinmu da"aka basu suke Shashancin Dasu,gwara na karbi Rabona Domin ko Dangote na zama a kudi Wlh bazan hakura Da Nema ba Dina Kudi Sune Rayuwa Kinji..! Tafada Tana wani Rausayar Dakai Dina ta gyara zama Tana Fadin"Yan Siyasa fa kikace Zakiya..? Zakiya tace"Yes Sufa nace..Ai sune yan Harka ke bari nayi Miki gwari Gwari Wlh Duk yan Siyasan kasan nan namu Kadan ne na Allah Sauran duk yan Bushashe ne.."Da sauri Dina Tace"Ammh banda Ubana ko..? Wata Shegiyar Dariya Zakiya ta Saki Harda Buga Tebur kafin ta Dakata Tana kallon Dina Cikin Iya bariki ta Daga mata Gira Tana Fadin"Ammh ai kema kinsan Barewa batai gudu Danta yayi Rarrafe ba ko.? Cikin wani irin kallo Dina Tace"Bangane ba..! Zakiya ta kara wani Sakin Dariya kamar Wata Shashasha Tana Fadim"Dina kin sanni na sanki...Zan tsage miki gaskiyata kema zaki Tsagemin ita koda bazatamin Dadi ba ki Rantse da Allah me mahaifinki ki zuwa garuruwa yanayi da Sunan Taron Siyasa..? Shifa ba Dutse bane Tun muna yara sai ya Shafe sati Bashi agida to yana ina..? Ke Namiji fa sunansa Namiji Tawajena ni kin ganni nan Ko Ubana ban yarda Dashi ba Ballatana Uban Wata..! Ta karishe Fada Tana sakin Wata karamar Dariya Tsaki Dina Ta saki Kai ta Dauke tana Fadin"Zakiya bana som iskanci..Ni Dad dina ba irin Kazaman Da kika saba bi bane...Na yarda dashi Taron Siyasa yake zuwa Fakat..! Zakiya na Dariya tace"Yes Shima ya yarda Dake..Aiki kika zo Bauchi ba Sheke ayarki kikeyi keda Dr Zain ba ko...? Tafada Tana kallonta ido kawai Dina ta sakarmata ta kasa Mgana Ganin Haka yasa Zakiya ta kara saka Dariya Kafin ta Tsagaita Tana Fadin"Is Ok....Tuba nake Tawan Babanmu ba Dan isk..! Bata karisa ba Dina Ta Wawuri Wani Littafi ta wargeta Dashi kaucewa Tayi Tana karamar Dariya Tana Fadin"Ahh..Meyayi zafi haka..? Toh Allah baki hakuri ban karawa Tawajena..! Tafada Tana kokarin Hadiye Dariyarta Cikin Kufuluwa Dina ke Fadin"Ammh dai kinsan ance mu Nemi Duniya kamar bazamu barta ba ko..? Zakiya TaDaga kira Tana Fadin"Yes haka kuma muke Neman lahira itama kamar bazamu Risketa ba.."Hararanta Dina Tayi Tana Fadim"Toh ke Ai Duniyar kadai kike Nema kin manta da zaki Lahiran Wata Rana..! Zakiya Tace"Duniyan Dai muke Nema Ba nake nema ba..Duk wani Zunubi Danake aikatawa kema kina aikatashi Dina Kinga kuwa miye maraban Dambe da Fada ai Duka Sunansu Fada..! Dina Takadai kai Tana Fadin"A"a muna da Bambamcin Ni Tunda Nake wa Zain kadai na yarjema Gonata Zakiya kinsani ina Son komai nawa ya kasance Specail ne ke kuwa nayi nayi na Raba ki da Rabama kowa ni Jig and Jag Jikinki kinki jina Zakiya in ma Kina so ne kiyi irin nawa ki Zabi Wani Daga cikinsu kawai kice ya Fito kiyi auranki yafi Wannan Rashin Madafan..! Zakiya Ta Daga kanta Sama na wani Lokaci kafin Tace"Ai Duka Zina Zina ce Dina..Da wanda yasha Giya ta Dubu Daya da wanda yasha ta Dubu Dari Duka Dai sunanta giya sukasha.Dake da kike Harka da Mutum Daya Dani Da nake baza Hajata Duka A mizanin sunan Zunubai Daya ne Dina ko ki yarda karki yarda Tare zamu gyara Halinmu im ma Haka kikeso kice..mganar kuma na samu wani na Aura nifa ba wanda yamin ne..Dama zaki mim Hanya na samu wannan Cute and Handome Dan"uwan Farkan ki dinan Allah zan Tuba na Bishi muyi Aure na Tabbata yadda Zain yake Cika ki tsaf nima na Tabbata zai Cikani Har ya kure Kwadayina..! Tafada Tana yar Dariya Hararanta Dina Tayi Tana Fadin"Karma ki saka ma Ranki..Domin wannan Haddir din sai yafi Zain Taurin kai...Kullum.Fuskarsa ba Fara"a ba Ke ba,nikaina ya Tsanane kamar ya Fahimci da wani Abu Tsakanina da Dan"uwansa in ya ganmu Tare ya Dinga Hararata kenan Kamar na Tsaremai wani abu.! Zakiya Ta Tabe baki Tana Fadin"Kinga Abunda yasa naki yarda da Shawaranki kenan..Ka tsayama Namiji Daya ya zame maka Ciwon ido gwara ki barni Ahaka gida goma mganin kashe Gobara."Kai Dina ta Jinjina kafin Tace"Allah ko ya kyauta..! Zakiya Tace"Nagaba..Domim wannan ya Riga da ya Faru..Lafiya na ganki a Hanzarce..? Tafada Tana Tsareta da ido kai Dina Ta Dafe kawai batare da Tayi mgana ba Cikim Mirmishi Zakiya Tace"ZAIN again..? Kai Dina ta gyada mata Cikim Rauni Tace"Zakiya kin sani Kaf Duniya Ba Namijin Da nike so kamar Zain..Ammh kuma Shi yana Bani ciwon kai kullum Kalaman bakinsa bai Taba sona ba kuma bazai Taba Aurena ba Mace Daya yake so kuma itace Kadai matarsa Firstlove Halima Zakiya na Tsani jin Wadandan Sunayen zuciyata na kuna Jiya nan mukayi Fada dashi wai kamar ni Zaim zai kalla yace Bayajin Dadina Halimarsa na Sakashi Kuka Tundaga Farkon Dare Juz Imaging fa Zakiya Ni Wai Zaim ke Fadama haka Nida maza Dadama suke son na basu irin Damarshi ban basu ba ammh Shi ya samu yana min Wulakanci yana Hadani da wannan Banzar matar Tashi Wacce Daga ganinta Jikinta ba Ruwan da yake isanta ma Ballatana ta jika wani Dashi..! Tafada Cikin Jin Haushi da Kishi Dariya Zakiya ta saki Har tana Mikewa Tsaye Galala Dina Tayi Tana kallonta ganin Yarda Take Dariya kamar wani Abun Dariya ta gayamata Cikin Takaichi ta kauda kai sanin Halin Zakiya na Dariyan mugunta Tana Cikin dariyan ne ta kware Ta Fara Tari Cikin Kufuluwa Dina tace"Allah ya kara.! Da karfi Fridge Zakiya ta Nufa ta Bude ta Ciro Ruwa ta kafa kao Tasha sai da ya isheta kana ta Sauke Goran Ruwan Tana Sakin Ajiyar rai Cikin Mirmishi Dina Tace"Gud...Dama ai mganin mai Dariyan mugunta kenan..Nakawo miki matsalata ammh Sai kika Fara min wannan Banzar Dariyan Taki..! Zakiya ta murmusa kafin ta kariso Ta zauna Kujeran Dake fuskantan Dina gab Da gab Cikim Danne Dariyanta Take Fadin"Ya zanyi..? Wlh Nakasa Danne Dariyata ce Wai Shi Zain din yace ke baki sakashi kuka Daga Farkon Dare sai Matarsa..? Tafada Cikin som karta Saki Dariyanta Cikn Jin Haushi Dina Tace"Wlh..Jiyan nan ya Fadamun wai ya gaji da Tararrayanmu..Dama na gaya miki koda yaushe Cikin Fadin haka yake so yake na Rabu da Dashi yaci Bulus Zakiya ni kuma Kinsani Duk Duniya Zain kadai nake so kuma Shi nake mafarkin ya zama Mijina ko Ta Halin kaka...! Zakiya Tace"Ikon Allah ai bai Kamata ki Damu ba Sanin Dama Aikin Boka ne ke Tafe dashi. ammh ba Domin Haka ba da Tuni ya Rabu Dake..."Dina ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Duk nasan wannan Zakiya plz ki gayamin ya zanyi..? Wlh bazan iya Rabuwa da ZAIN ba Shine kadai Namijin Dake gamsar dani..! Zakiya Tace"Dama ai bazaki Rabu Dashi ba sai mun kai ga Nasara.."Ido Dina Ta sakarmata kafim Tace"Taya..ya..? Help me kaina ya Dunkule waje Daya baya wani Motsi...! Mikewa Zakiya Tayi Ta kariso Kusa Da ita Lokaci Daya Ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Alluran planning din da kikayi na How many Month ne..! ? Kai Tsaye Dina Tace"Harkin mata..? Tare fa mukayi na Six Six Month ne..! Zakiya Tace,"Ban manta ba So nake na kara Tabbatarwa..In ban manta munci Almost 4 month kenan Tana mana aiki ko..? Kai kawai Dina Ta Dagamata alaman eh Cikin Sauri Zakiya Tace"So ina so Indan Ta gama aikinta ajikinta karki sakeyi mujira mugani...! Da mamaki Dina ta Dago Tana kallonta Cikin som karin Bayani Lokaci Daya Tana Fadin"Kar na sakeyi kuma.? Kinsan me Hakan ke Nufi..? Zakiya Tace"Yes naasani..Ba Ciki kike Tsoro ba..? Kai Dina ta gyada mata Tana Fadin"Eh mana..Kinsan Zain ya gargadeni akan Hakan Tun Farko...! Wani Mirmishin Mugunta Zakiya Ta saki kafin tace"Toh ai da Cikin zamu Amfani mu Razani shi..Tunda na Lura yana Tsoron Danginsa Da Matarsa Wacce yafi so baya so Taji Labarin yana Tarraya da wata mace awaje..Duk Shaidar da zamu Tanada Bata kai Shedar ki Mallaki Kwan Haihuwarsa a maranki ba Dina Kuma Dole in Mgana ta kai kunin Manyansa su Zauna su sassanta mganar Domin na Tabbata baza su so wannan mganar ta Fita ko Domin kada kimarsu da Darajansu ta Zube akan Idanuwan Duniya ba..! Ta karishe Fada Lokaci Daya ta Juyo Tana kallon Dina Wacce tayi Shuru Tana kallon Zakiya kafin Zakiya tace"Ya kika ga wannan Salon..? In yasan wata bai san wata ba Tawan..Kuma kin manta Boka daman ya gayamana kafin Auranku yaga Turniku da Duhu..? Toh ai wannan yakin da zai Faru Shine Duhun Tabbas za"a kai Ruwa Rana Rayukan wasu zasu baci..Wasu zasu Raasa kimarsu Dayawa ammh mu bamu damu ba Koda mun Rasa namu kimar Daman chan ba wata kimar garemu Wajen Allah ba Indai Burinki zai Cika na mallakan Zain na yarda Duniya ta Shaida bamu da Wata Cikakkiyar kima Kura ce Lullube Daman da Fatar akuya..! Tafafa Tana wani kada mata Hannunta Ajiyar rai Dina Ta Sauke kafin tace"Hakan kina ganin bazai Taba Siyasar Mahaifina da kujeransa ba..? Zakiya Tace"In Macijin yayi mana Taurin kai ne Mganar zata Fasu saboda bamu da Zabi..Ammh in ya nuna yana son Sulhu zaku Sulhu iya ku Biyu ammh kuma ki Tuna Hakan bamai yuyuwa bace Dole ne Shima yarasa kimar Dayake Takama Dashi in ko Hakan ta Faru Dole ne Labari ya Fasu...indai kin Zabi Kujeran mahaifinki To ya zama Dole ki Yi Hakuri Da Cikar Burinki Dina..! Shuru Dina Tayi tana wani Tunani kafin ta Sauke Tagwayen Numfashi Tana Fadim"ammh kada muyi Saurin Datse ma Macijin kai Zakiya..Gwara mu Fara Datsan ganganar Jikinsa koda mu Rabasa da Kansa ne batare da Mun kashesa ba.' ! Zakiya Ta saki Dariya Tana Fadin"Wato Dai mu Fara Sare Macijin kafin mu Sare kansa kenan.? Kai Dina ta Gyada mata Kafin Tace"Haka nake Nufi..!kai kawai Zakiya Ta Jinjina kafin Tace"Shikenan komai na Hannunki..' Daga haka suka Cigaba da Tattauna mganar sun Jima Kafin Dukkansu su Shirya su Fita Tare Dina cikin asibiti Ta koma Ita kuma Zakiya Gida ta wuce Zatayi wanka Ta Shirya Tana da Bako. ***** Gabda Kiran Sallar mangariba Halima Tagama Komai Zobo Take Hadawa Taji Kiran wayanta Daga Falo Mirmishi Ta saki Sanin Firstlove ne ke kiranta Zobon Tagama Hadawa kana ta Dauka ta saka Cikin Fridge yayi sanyi Abincin Datayi kuma Farar Shinkafa Miyar ganye Mai kifi sai Ferfesun Pepe Kitchen wanda Tayi Saboda Firstlove nan Kitchen din ta bar komai Saboda Tana so Sai ta koma Daki Tayi wanka Tayi sallah kana sai Tazo Ta jera komai kan Dinning ta goge Kitchen Din Inda ta bata. Da Sauri ta Fita Daga kitchen Din Zuwa Falo Katon Talabijin Din Dake kafe Shi yake ta aiki Shi kadai kan Center Table Din Dake Tsakiyar Dakin Ta Hango Wayarta Da Sauri ta karisa ta Dauka kenan wani Kiran ya kara Shigowa Fuska Ta bata ganin Sunan mai kiran *UKTI ZAFEERA..*! Cikin Tura baki Ta Daga Kiran Tana Fadin"Dillah ji yarinyar nan ta sakani gudu nifa da naji Kiranki na Zata Firstlove ne....!Tafada Tana wani Tura baki kamar Wata karamar yarinya Dariya Dagachan Bangaran Zafeera Ta saka kafin Tace"Ehhe..Kaji masu Firatlove...Mu da bamu Dashi Allah ya bamu Ukti..! Halima ta saki Dariya Tana Fadin"Ameen Ukti kefa kikayi sanya Ina Barrister Ahmed yake..?Meyasa baki bashi Dama ba yana Sonki Wanchan Satin Alhaji Tsoho ke Fadamin yaje ya gaisheshi Da wani aiki ya Shigo Dashi Garin..'! Tabe Baki Zafeera Tayi Dagachan Bangaran Tana gyara Zaman System din Dake gabanta Cikin Basarwa tace"Yayi kokari..Ukti ya gida..? Ya kuma Yaya Dakta yake..? Naga Kiranki Dazu ina Cikin makaranta ne Shiyasa na bari sai na Dawo Gida na Kiraki..! Halima Tace"Komai lafiya Ukti to ya karatun.? Ya su Inna Rukayyah Ina Shema..? Zafeera Tace"Shema ta Shiga wanka..Nima yanzu na Fito Dayake ko Mintoi Ashirn bamu yi da Shigowa Gida ba.."Halima Tace"Allah ya Taimaka Ukti nayi kewarka yaushe zaku samu Hutu..? Zafeera Tace"Nima ina matukar Kewarki Ukti..Wlh sai nan da 2 Month inaga domim ko Test bamu Fara ba.."Halima Tace"Muma bamu Fara ba..Kuma ina ta ma Firstlove nacin yakai ni kano Wajenki yaki Maida kai akan mganar..! Zafeera Tace"Dama ai bazai barki ba Ukti..Kim manta Tun muna Gabansu Umma Sai inda ya Zabar Miki..? Dariya Suka saka atare kafin Zafeera Tace"Ahki Faruq na gaisheki Ukti Dazu ina School ya Kirani mukayi Vd call.."Tsalle ta Buga Tana Fadin"Don Allah..? Kice kinga Mutanen Chicago..! Zafeera Tace"Wlh..Kinga yadda ya zama ya kara Kiba da Fari.."Halima Tace"Allah Sarki Shine ni bai kirani ba.."Ta fada Cikin Shagwaba Zafeera Ta Saki Dariya Tana Fadin"Ho..Ni kuma Kishiyarki ba..Toh Yace ya Kirani bai sameki ba ya Kira Yaya Dakta kuma yace kina Gida Shi yana asibiti..! Halima Tace"Shikenan ya Fita...Nima zan Kirashi mu gaisa Wajen wata Biyu Rabon da muyi mgana Dashi.."Zafeera Tace"Nima kinsan yanayin karatunsu na lauyoyi Tunda ya Dage sai yagaji Dadyn Abuja.'Dariya Halima ta saki Kawai Lokaci Daya kuma suka Sarke Hiran Jin ana Kiran Sallar mangariba ne yasa Halima tace"ke wai hala baki Sallah ne..? Dariya Zafeera ta Sheke Dashi Tana Fadin"Au da kin zauna ne..? Nifa Shehi yayi min Tawa.."Halima tace"Banza Allah ya isana.."Dariya Zafeera ta kara sawa Tana Fadin"Dama Ai chan Allah ya Isa mana.."Halima Tace"Naji ni ba wannan ba Ukti Dama ina Son ganinki mgana nake so nayi Miki.." Zafeera Ta natsu Tana Fadin"Ko..? Toh ina jinki ko sai kinyi Sallah ne..? Halima Tace"Bari mu Fara mganar Tunda naji yanzu Wasu masallatan suke kira...! Jin Haka yasa Zafeera ta Ture Laptop Din gabanta ta mike Tsam Ta Fice ganin Shema"u ta Fito Daga Tiolet,ita kuma Zafeera macece mai Zurfin Ciki bata yarda kowa yasan Cikinta in ba Umma ko Halima ko Faruq ba,Koda Shema ta kasance Diyar Inna Rukayyah bakomai nata ta sani ba Fita tayi zuwa Falon ganin Duka yaran Mazan sun Tafi massallaci Matan kuma sum Shiga Dakumansu yin Alwala Inna Rukayyah ma Tana Dakinta kan Daya Daga Cikim kujeran Falon Ta zauna Tana Fadin"Ina Jinki Ukti..Na Fito Falo ne..! Mirmishi Halima Tayi kafin tace"Kan mganar Barrister Ahmed ne meyasa bazaki Bashi Dama ba Zafeera..! Naga yana sonki kuma Naga Dadyn Abuja da Alhaji Tsoho suna yabonsa Sunce Dan Gidan mutumci ne kuyi Auranki Ukti na Tabbata zai barki ki Cigaba da karatunki..! Numfashi Zafeera Ta saki Kafin Tace"Uhm..Ukti Nifa ba wai ina kin Ahmed bane..Kawai dai Mazan wannan zamanin ne baka gane kansuu baka san abunda ke cikinsu ba kuma Abun ke ransu dabam Abunda bakinsu ke Furtawa Dabam.."Da Sauri Halima Tace"Bangane ba..? Zafeera Ta gyara zama Tana Fadin"ina Nufin Acikinsu Dai dai ku ne keda Amana..Sai mace Ta gama yarda dasu Daga baya su Ci Amananta Ukti zuwana Kanon nan naga Casess na mazan da sukaci Amanar Matansu Daga Karshe suka bar matansu da Ciwon Zuciya Da Damuwa Shiyasa Maza suka Fita kaina na ke musu kallon Duka Halinsu Daya..! Da Sauri Halima Tace"Ammh banda Firstlove dina ko? Na Tabba Kin Shaida Bazai taba Cin Amanata ba.."Zafeera Tace"Ba zan iya sani ba Ukti bar ganin Yaya Dakta na yayana kema yar"uwata ce ta Jini Dole na gaya miki Gaskiya bansani ba Tunda Nidai Zahiransa nake gani ba Badini ba..Ammh dai karki saka komai acikin Ranki Ki kyautatamai Zato..' Jikin Halima yayi Sanyi Cikim Rauni Tace"Yanzu kina so ki gayamin kema kina Tunanin Wata Rana Firstlove zai iya yin wani Abu nacin Amana agareni Ukti..? Da sauri Zafeera Tace"A"a Ni wlh bance ba Ba kuma Haka nake Nufi ba..Nace bansani ba..Ammh Mu kyautamai Zato Ukti ni na Shaida Kaunar Yaya Dakta agareki Insha Allahu makamanciyar cin Amana bazai Taba gitwa tsakaninku ba.." Jin Tayi Shuru yasa Tace"kinji Ukti Don Allah karki Damu plz..! Ajiyar Rai ta Sauke kafin Tace"Shikenan...Zan kiraki zuwa gobe mu karisa mganar bari naje nayi wanka da Sallah Firstlove na Kan Hanyar Dawowa.."Kai Zafeera Ta gyada kafin tace"IS ok..Akulamin da Yayana Dakyau.."Dariya kawai Tayi ta katse Kiran Tsaye kawai Tayi Tana Tattara maganganun Zafeera gefe Daya kuma tana gamashi Dana Laila sai take ganin Kamar Abu Daya suke Nufi gabadaya Jikinta sai yayi sanyi Dakyar ta karisa Cikin Bedroom Dinsu ta Fada wanka bata Fito wanka ba sai da Ta Dauro alwala tazo Ta shafa Lotion Dinta Ta Zura Doguwar Riga ta Tada Sallah bayan ta Idar ne ta karisa gaban Wardrope Ta bude ta Dauko Riga da Sikat dinta na wani Atamfa mai kalan Ja ta saka ta karisa gaban madubi ta kashe Dauri ba wata kwalliya tayi ba sai dai kayan sun kamata kwarai sun Fitar mata da Sirrin kyanta,Turare ta saka a ko"ina na Jikinta kana ta Fito Daga Bedroom din. Karo suka kusa Yi da Zain wanda ya Sawo kanshi Cikin Bedroom dinsa Dauke da Suit dinsa a Hannun Dayan kuma yana Rike da wayarsa da Key din Motarsa Baya Taja Tana kallonsa Shima kallonta yake Cikin mamaki bai samu Zarafin mgana ba tace"Yaushe ka Shigo..? Kai Tsaye yace mata"Yanzu na Shigo..! Ido ta Rausayar Tana Fadin"Kwata kwata banji Bude get ba da Shigowarka ba."Cikin mamaki ya sakamata Ido kafin ya Fara taku zuwa gareta Cikin Tsare ta ido yace"Meke Damunki ne Firstlove..? Kai Ta Dago Tana kallonsa Tace"Me ka gani...? Cikin Sauri yace"U look so Silent Ba yadda nasan ZAINA ta ba.In taji Dirin Motatana zata Fito da Gudu ta kamkameni Abunda tasan yafi komai Sakani Farinciki kenan Fara Tozali da kyakyawan Fuskarta da kuma jinta acikin Jikina."Sai da ya Fada Taji Tayi wani Gibi Daga Abunda ta saba Cikin Sanyi Jiki kawai Ta Fada Jikinsa Batare da tace komai ba Shima azuciyar Zuciya ya saki kafin ya Saka Hannu Daya ya Rumgumeta yana Fadin"I Love u Firstlove In kika Bar Rayuwata Wlh zan lalace ne..! Tana Jinsa Saboda Jikinta a sanyaye yake bata iya cemai komai ba Sun Dade haka kafin ta Dago Daga Jikinsa Rigar Hannunshi ta  Karba Tana Fadin"Muje kayi wanka..Daman ban gama Jera abincin saman Dining ba..' Tayi gaba yana Binta abaya Cikin mamakin ganin yanayinta ayau kuma da Safe lafiya Kalau suka Rabu Har Tailet ta Shiga Ta Hadamai Ruwan wanka kana Ta Fito Ta Tayashi Ciro kayan Jikinsa Ta Daura mai Towel ta Rakashi Har Cikin bayin kana ta Fito Shidai da kallo yake Bita yana so ya karanci meke Damunta taki bashi Dama,tana Dawowa ta Tattara kayan Daya Cire Zuwa Cikim Wardrope dinta Bangaran inda Take Tara kayan wankinsa,Ta Rufe ta Fice Daga Bedroom Dim kichen ta koma ta Dauko komai ta Jera Bisa Dining kana ta koma ta Gyara Kirchen din ta Fito kenan sai gashi ya Fito da wata Bakar Jallabiya mai Gajeren Hannu Mirmishi ya sakar mata Itama ta maida mai Kafin ta karisa ta Riko Hannunsa Zuwa Saman Dinning Din Taja mai Dayan Daga Cikin kujeran ya zauna Ita Tayi Sarving Dinshi Har sai da yace Ta barshi haka kana ta koma Kujeran Dake kallonsa ta zauna itama Taja Filet ta zuba Daidai Cikinta. Cikin mamaki yakura mata ido Ganin Haka yasa ta Lamgwabe kai Tana Fadin"Bai yi Dadi bane abincin Firstlove..? Kai yaGirgiza kafin yace"Ko Daya....Kawai naga wani Chanji Tare Dake ne Firstlove wanda Banta gani ba..! Ido kawai ta sakamar Batare da Tayi mgana ba Shi kuma ya cigaba Da Fadin"Na Dawo ba"asan na dawo ba..Na biyu kuma Tunda mukayi Aure indai ina Gida baki da wajen zama sai kan Cinyata ni nake Ciyar dake Da Hannayena Firstlove ammh yau sai naga kin samu Kujera kin zauna kin kuma Dibi naki abinci ke kadai zaki ci..Sai na Fara Tunanin wani irin laifi ne mai Girma na aikata miki..? Wanda ni acikin Raina ina jin da na Bata miki gwara ke kin batamin Firstlove..! Ya karishe Fada yana Tsareta da mayun idanuwansa kai ta Kauda gefe bata iya Juran kallonsa Kanta na kasa ta Dago Tana Fadin"Allah bakomai Firstlove karka Damu..! Cikin Mamaki ya ijiye cokalin Hannunsa yana Fadin"Kinga bana son gaddama ban gane kada na Damu ba.? Ya bazan damu ba alhalin ga damuwa nan ta bayyana atare dake..?ki gayamin Abunda ke Damunki Firstlove in har kin Daukeni Abokin Rayuwarki..! Yafada Cikin Nuna Ransa ya baci Kai ta Rausayar kafin Tace"Babu Abunda ke Damuna Firstlove Belive me..! Fuska ba walwala yace"Na yarda Dake Fiye da yarda na yadda Dakaina..Ammh Damuwar Dake Fuskarki ta macece..? Ido Cikin Ido Ta Dago Tana kallonsa ba Zato ba Tsammani yaji tace"Firstlove don Allah zaka iya cin Amanata watarana..? Zaka iya barina Watarana saboda Wata.? Karishe Fada kai Tsaye Tana kallonsa wani irin Dam! Dum! Yaji gabansa ya amsa Cikin Waro Ido yake kallonta Tuni kuma yaji zuciyarsa ta sake Ta fara Tunanin kodai Tasan wani Abu Dake tsakaninsa Da Dina ne..? Daya shiga goma bama uku ba...! *Yan group din ZAINAZAIN BAND1&2 Bakwa sharhi kalilan ne masu Comments kuma gashi Kun cika Groups din duka ko ku gyara ko kuma Duka na kakkabe ku nayi Sabbin Zubi...* *Shakira...* . *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*           0️⃣9️⃣ Cikin In ina da Tsoro da kuma Fargaba Hade da Faduwar gaba Zain ya Tattaro mganar da take Kan Harshen Bakinsa yace"Wa...n..wannan Wata irin Mganace ko nace Tambaya kuma Firatlove..? Waya gaya miki Watarana Ni Zainullahi zan Guje ki saboda wata...? Yafada kai Tsaye yana kara Tsareta da manyan idanuwansa Itama Shi take kallo Cikin Son karantar yanayinsa Ganin yadda mganar ta Dakesa ne sai yasa Ta saki Wani Kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Kaima kaji Dukan Zuciya ko..! Kaji ka Razana da mganar ko...? Nima Haka naji Firstlove Lokacin da Laila Take Fadamin na Rage Sonka na Rage yarda Dakai saboda kai Namiji ne Watarana Duk Yadda ka kai da Rashin Son ganin Raunina zakayi Sanadiyar bayyanarsa..! Ta Fada Manyan Idanuwanta na kawo Cikar kwallah mamaki ya kama Zain da maganganun Zainarsa Cikim Mutuwar Jiki yace"Laila kuma..? Dama ita ta gaya miki Watarana Zan iya barinki Saboda Wata..? Ya karishe Fada yana wani Hade Rai Cikin Karaya da Rauni Tace"Bata ce bane....Misali Ta bani Da kuma jin Tsausayina kada Hakan ya Faru dani Watarana..! Cikin zafin Nama ya Daga mata Hannu yana Fadin"Kaji min Yarinya da Gulma..? Da ina kallonta yarinya mai Hankali Shiyasa na barki kike kawance da Ita Banta Zatonta Zatayi Sanadiyar Tsarwatsamin yardanan Danayi Shekaru ina gina ta ba Firatlove..! Ya karishe Fada yana wani karya mata Wuya Cikin Wasa da Spoon Din Hannunta Tace"Ba ita kadai Ta gayamin Haka ba..Ukti Ma na Tambayeta kan tana ganin zaka iya Cin amanata Watarana..? Kasan wata amsa ta bani..? Zuwa Lokacin maganganun Zainar Tasa Sun Fara Bashi Tsoro Cikin Tsoro da jarumta Duka Lokaci Daya ya Girgiza mata kai alaman bai sani ba Cikin Mutuwar Jiki ta Cigaba Da Fadin"Wai itama cemin Tayi bata sani ba..Zahirinka ta sani ba Badini ba ammh Tana da kyakyawan Shaida akan ka..Firstlove kalaman Laila dana Zafeera suna min amsa kuwwa acikin kunnina sun sakamin Raunina ina Ji ajikina in Hakan Ta Faru wani Hali zan Shiga..? Wlh zan iya kashe kaina indai na Wayi Gari Zaka barni Saboda Wata Firslove..! Ta karishe Fada Cikin kuka kamar Wata karamar yarinya kana ganin yadda Take kukan zaka san Daga karkashin Zuciyarta yake Fitowa Da Sauri Zain ya mike Daga Inda yake ya Isa gareta ya saka Hannu ya Dagota Tsaye Cikin Wani Sanyi Jiki dana Zuciya yake Fadin"Kinga Firstlove..Stop Craying..Kinga Mganar Zafira Data Laila Hasashe ne kawai Zainata Bazai Taba Faruwa ba..! Yafada yana Dauke mata Hawayenta Da Tafin Hannunsa Cikin Tsuramai ido Tace"In Hasashensu ya zama gaskiya fa Firstlove..? Tafada Cikin Kuremai Idanuwanta masu Cike da wani Rauni da neman Tallafi Jikinsa ne ya kara Mutuwa Sai kawai ya kauda Kansa Lokaci Daya Ya Jawota jikinsa ya Rumgume ya kamkameta yana Sakin Zuciya kamar wani karamin yaro Itama Jinta acikin Jikinsa yasa kawai ta Kara sakin kukan Dake Cin Ranta Tuni Shi kuma sai aukin Shafa bayanta yake Cikin Sigan lallashi kafin ya Dagota ya Share mata Hawaye yana Fadin"Kin yarda Dani..? Kai Tsaye Tana kallonsa Tace"Sosai ma Fiye da yadda na yarda Dakaima ma kuwa Firstlove..! Cikin wata murya yace mata"To indai kin Yarda Dani ki saka Ranki Har Abada ni Zainullahi bazan Taba barinki saboda wata ba..Duk Duniya mace Daya nake so kuma kece..Bayan ke ba Wata Firstlove mganar Laila da Zafeera kuma Suna Dora mizanin Haka kila sun ga Wani Abu ya Faru achan wani waje da Nisa wanda bamu da alaqa da Hakan Ki daina Kokwanto akaina Kinji Insha Allahu ko Mutuwa Tare zata Daukemu..! Ya karishe Fada yana Sakar mata manyan Idanuwansa Sun Dade suna kallon Juna kafin ta kada kai Tana Fadin"Na yarda Dakai Firstlove...Ina Sonka Abun alfaharina..! Rumguma ya kaima ta Cikin Wani yanayi yake Fadin"nima ina Kaunarki Zainata...! Yake fada yana Shinshinar wuyanta itama makaleshi Tayi Sun Dade ahaka kafin ya Dagota yana Fadin"Kuka ya kare ko..? Kai ta gyada mai bai yi Wata Wata ba ya Dagata Cak yana Fadin"Muje muci Abinci....nagode ma Allah dana iya Shawo kan wannan Matsalan da Zafeera da Kawarki Laila suka so su kunnomin acikin gidana..! Yafada yana yar Dariya itama Dariyan Take kan Cinyarsa ya zaunar da ita bayan ya zauna ya Jawo Filet din Abincin da Cokali ya Fara bata tana karba Har sai da tace ta Koshi kana ya bata Zobo da Ruwa Tasha kafin Shima ta Ciyar Dashi Har sai da ya Koshi suna kamallawa ya Tashi ya Tayata suka kwashe komai suka maida Kitchen jin ana Kiran Sallar Isha'i yasa ya Tafi Bedroom yayi alwala Ita kuma ya Barta Tana kara gyara Kitchen din. Minti Talatin ya kwashe sai gashi ya Dawo Lokacin Har ta sake wanka ta Chanza kaya Zuwa Wata karamar Riga ta Shan a Iska Falo,Suka Yada Zango Ta Nannade ajikinsa Tana Shagwaba Shi kuma yana Biye mata Wayarsa na Gefe Yana ganin Dina nata Kiransa Allah ya Taimakeasa Wayar Tana Silent ne Da bai da kuma amsan da Zai bama Halima in ta Fahimci wani Abu Dama Dayan Layin da suke yawan mgana da Dina Dr.Dogara ya sakamata Saboda in yana Gida tana yawan Kiransa Dayan layinta ne ya Sakamata Dr.Dina kuma ya Tabbata Kiran ta bana alheri bane Halima na kan Jikinsa ya Jawo Wayar ya Kasheta Gabadaya,ya Biye mata Basu wani Dau Lokaci ba Ya Tattarata Zuwa Cikin Bedroom dinsu,chan suka kwakwame Juna Cikin so da kauna Cikin Lokaci kalilan Ya mantar da ita Duka wasu manganun Laila da Zafeera ta saki Jiki kan Duk Duniya ko kowa zai iya Juya mata baya Toh Banda Zain aciki. ***** Washegari Tun Karfe 7:45am na Safe Zain ya Fice,A gida ya bar Halima ita sai 9 take da Lactures,Gida ya Fara Biyawa ya kaida Umma da Nene Koda yaje Abba ya Fita Tun 7 shima yana da Meeting bai jima ba yayi musu sallama ya Fice Daganan Gidan Alhaji Tsoho ya Biya suka Gaisa Bayan sunyi Wasan Jika da kaka Dashi da kuma Hajiya Mama Baba Tabawa tazo Suka gaisa Bai jima ba yayi musu sallama Yana Sauri zai Shiga Cikin Asibitin Kusan Tare suka Shigo Cikin Haraban asibitin da Haddir kusan kuma Waje Daya kowanne ya Faka Motarsa Suka Fito Dukkansu a Tare,Sakamakon yau jumma"a Dukkansu Shigan Manyan kaya ne ajikinsu,na Shadda Fara kowanne kuma ya Daura Hular zanna Bukar Bisa kansa kafafunsu kuma Kamar hadin Baki Duka Suna sanye da Rufaffan takalma ne na Fatar Damisa,Kallo Daya zaka musu kaasan Sudin Jini Daya ne Saboda yadda Suke Diban kama Sai dai Haske kawai da Zain ya Dara Haddir ammh har yanayin Tswonsu da kuma Sumar kansu da kuma Sajen Fuskarsu iri Daya ce Komai nasu Cikin Tsari ne Shiyasa Mata da yawa Suke Zencensu Suna kuma Jinjina ma Tarin baiwar da Allah yayi ma wadanan Zaratan samarin. Da Farko Dauke kai Zain yayi Daya ga Haddir zai wuceshi yana Tusa key din Motarsa Cikin aljihun wandonsa Da Haddir yaga Haka sai ya Murmusa ya Bishi Suka Jera Tare Lokaci Daya yana Mika mai Hannu da Fadin"Assalamu alaika...! Cikin Basarwa ya Dakata da tafiyar dayake yi ya Bashi Hannu yana amsa Sallamanshi Fuska ba Fara"a Haddir bai Damu ba Sukayi Musabaha yana Fadin"Ya gida..? Ya kwanan Halima..? Cikin Son kauda mganar yace"Komai Normal....! Daga Haka ya sa kai zai Wuce Haddir yace"Zareena Tace Tana ta Neman wayarka Bata samu...In ka samu Lokaci ka Kirata..! Waigowa yayi zai yi Mgana kenan Daidai Lokacin Motar Dina ta Shigo Cikin Asibitin Dukkansu da kallo Suka Bi Motar har ta karisa Parking Space ta samu waje ta Tsaya Bata Jima ba ta Bude Murfin Motan Ta Fito Cikin Shigar alfarman na Riga da Sikat na Wani lees mai kyau da Tsari,Dinkin ya kamata Sosai sai karamin mayafin Data yane kanta Dashi karamar Jakarta ce a Hannunta Da wayarta sai key din Motarta Kwalliya ta Chaba Sosai kuma Yayi mata kyau Sosai Sai Tashin kamshi Take kafarta Sanye Cikin Takalmi mai Tsini Ta Fara Taku Daya bayan Daya kowani Sassa na Jikinta na Motsawa Kai Tsaye kuma Inda su Zain ke Tsaye Suna kallonta Haddir Dai Kai ya kauda Daga kasan Ransa yana Jinjina Shedancin Dina Zain kuwa ya kasa Dauke ido Daga kanta Haka kurum yaji kamar wani manadigosu na Jansa Zuwa ga kallonta. Har sai da Ta kariso kusa Dasu yana kallonta ganin yadda Haddir ya kafeshi da ido ne yasa ya kauda kai Lokaci Daya yana Sakin karamin Tsaki Haddir ya kallah yana Fadin'Ok zan kirata..Ok..! Daga haka kawai ya Wuce Cikin Asibitin da Sassafar Dukkansu da kallo Suka Bisa,Shi Haddir kallon Takaichi yake Bin Zain Dashi Ita kuma Dina kallon Soyayyah da kauna Tana jin kamar ta Bishi ta Rumgomsa Saboda yadda yayi mata kyau kwarai yau din da Shigar Jikinsa. Maida Dubanta tayi kan Haddir Wanda ke Kokarin Fiddo wayarsa Daga Gaban aljihun Rigansa Cikin Kissa Tace"Mrning Sir...! Bai kalleta ba ya Juya zuwa Cikin aasibitin Lokaci Daya Yana Fadin"Mrning How are u..? Daga Haka ya Dora Wayarsa a kunni ya Fara mgana kuma yana Tafiya Cije bakinta Tayi Tana kallonsa har ya bace ma ganinta kafin Ta Murmusa Tana Fadin"Hmm baka da yarda Zakayi Watarana Haka zaka ganni agidan ku a matssyin Matar Zain..! Daga Haka itama ta Nufi Cikin Asibitin Cikin Takunta na Goggun mata Tana Shiga Da Dr Imran ta Fara cin karo ya Fito Daga Office din Dr Peter,Da wasu Folder a Hannunsa yana ganinta ya Washe baki Lokaci Daya yana Sakarmata manyan Idanuwansa kamar zai Cinyeta Danya,Ganin haka yasa Ta Zabgamai Harara maimakon Ta Nufi Hanyar Office dinta kawai sai ta Fada Office din Dr Aisha Saboda Gujema Haduwa da Bakin Maye Dr Imran. Shi kuwa Zain yana Shiga Office Dinsa Daman da Folders Din Mutane yaci karo Wata Nurse ta Shigo Tana gaisheshi Cikin Daure Fuska ya Zauna kan kujeransa yana Jawo Folders Din gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Wadanan Folders din fa..?cikin girmamawa tace"Na Patient ne masu ganin Likita Sir...Dr Imran yace na Tara maka Su Kafin ka iso..! Karamin Tsaki kawai yaja kafin ya zari Biron Dake kan Teburinsa ya Bude Folder Din Farko yana Fadin"Hannatu Bashir Call her.." daga haka ya Juya yana kallon Folder din matar yana Nazarin Abunda ke Damun matar yar Shekara 41 da wani Abu a Duniya,Da Sauri ta Fice Zuwa Gaban Office din nashi Inda Masu Jiran ganin Likita ke Taruwa takira Sunan Hannatu Bashir wani yaro Dan kimanin Shekara 20 ya Mike Lokaci Daya yana Tada wata mata Dake gefensa Cikin Kulawa Nurse din tace"Itace ko..? Yaron ya Daga mata kai da Sauri Tace"Ok ku Shiga da Sauri Dr.Zain ne bayason Jira..Ku kuma ku Tsaya ayadda na Tsaraku Daga na Daya zuwa na Goma,In wannan ya Fito wannan ya Shiga ku kuma Sauran ku taso muje Nakai Folders din ku Office din Dr Imran ne..! Daga Haka tayi gaba Sauran Majiyanta Suka Bita abaya,Yaron nan kuma ya Shiga da Mamansa office din Dr Zain ya zaunar da ita Shima ya zauna Zain ko Dago kansa bai yi ba ya Fara Fadin"Hawan Jini ke Damunki Mama..! Yaron ne ya bashi amsa da Fadin"Eh likita.." sai Lokacin ya Dago kansa ya Sauke kan yaro na Dan Lokaci kafin ya kada kai yana Fadin"Sannu Mama bari na gwada Bp ki..! Yafada ganin Tana ta Numfashi Sama sama. Cikin kwarewa ya Fara aikinsa ya Gwada Bp Dinta Bayanan kuma yana ta mata Wasu Tambayoyi Tana Bashi amsa,Rubuta mata mganguna Yayi ya basu,yace su dawo nan da 4weeks bayan ya dan bata Wasu Shawarwarin na Rage Tunani Tayi ta mai Godiya Tana Sakamai albarka Cikin Mirmishi yake Fadin"Bakomai Mama Aikinmu ne..! Suna Kokarin Fita ta Sawo kanta Cikin Office Din,Kallo Kallo akayi Tsakanin Matar nan da Danta da Dr.Dina Tabe baki kawai Tayi ta wucesu suma suka Fice suna mamakinta,bai ma san ta Shigo ba ya Dukufa Duba Dayan Folder Dake gabansa Na wata mace ne kamar kuma Zuwanta na Farko kenan,jinjina kai yake Dazu matar da ta Fita bashi ya kamata ya Dubata ba Dr Imran ne,ammh Tunda Fayels dinta ya Fado gabansa kuma ganinta Babba Tayi Sa"ar Nene yasa ya Dubata ammh Shi yafi Duba Wadanda suka Shafi Ciwon mata kamar su Ciki haihuwa,Mtsalan Bari,sanyi Da Sauransu. Azatonsa Itace kai Tsaye yace"Aisha Jarma meke Damunki..? Zan iya Taimakonki..? Yafada kai Tsaye Yana Dora Bironsa Bisa Folder Din zai Fara Rubutu wani Mirmishi Dina ta saki ganin bai Fahimci ita bace Siririyar Dariya ta saki mai kara wacce Har Zain ya Jita da Sauri ya Dago Suka Hado 4eyes yana kallonta Lokaci Daya kuma kamshin mayen Turaranta ya Shigemai Hanci. Cikin Hade Rai ya ijiye Biron Hannunsa yana Fadin"What..? Baki ganin ina kan Duba patient ne Dina..?meke damunki..? Yafada yana Tsare ta da idanuwansa Cikin Kayattacen Mirmishi Tace"Nima Patient din ne Dubani zakayi..! Tafada Tana Kafeshi da mayen kallonta Wani karamin Tsaki yaja kafin ya maida kansa baya bai samu zarafin mgana ba aka Bude Office din aka Shigo Ganin su Su biyu yasa Ta Juya zata Fita da karfi Zain yace"Aisha Jarma..? Bafullatanan ta Daga kanta Tana Fadin"Eh Dakta...! Kai Tsaye yace mata'"Shigo Ciki mana..! Yafada yana maida kallonsa kan Dina Lokaci Daya Yana Fadin"Plz Dina Get out...In ke baki san Darajan aikin ki ba Ni na sani ki Fitarmin daga Office Tun kafin Raina ya Baci..! Mamaki ya Cikata tayi Galala Tana kallonsa Cikin Taushin Murya tace'Buh Zain mgana...! I said get Lost....Ke Dakikiyar ina ce da baki gane mgana..? Ya Katseta Cikin Wata Gigitaciyar Kara wacce ba ita kadai Ta Razana ba Har Bafullatanan Dake tsaye sai da Taja Baya,Daskarewa Dina Tayi Tana Bin Zain da kallo Idanuwanta Sun Cika da kwallah ganin Taki Tashi ne yasa ya Mike ya Nuna mata Kofa yana Fadin"Fita..Fita Tun ina ganin Mutumcinki kafin Sauran Mutumcinki Dake Idona su Zube..Wlh zan saka ayi Miki Wulakancin da in har kika bar cikin asibitinan bazaki so ki Dawo ba Ki Fita nace..! Yafada Cikin Bayyana Bacin Ransa Lokaci Daya Jijiyoyin kansa na Mikewa Ganin haka yasa Dina Ta Mike tana Kallonsa Gefe Daya kuma tana Kokarin maida Hawayen Idanuwanta kafin tayi wani Mirmishi kawai ta Juya da Sassarfa ta Fice da wani katon Tsaki ya Rakata yana Fadin"Shedaniya kawai..Allah yamin Tsari Daga Shedancinki.."! Batulatanan Dake Tsaye ta amsa da Ameen Ameen Saboda ita kanta Dinar bata mata kalan Mata masu kima ba,Komawa yayi ya zauna yana Dafe kanshi kafin yace"Zauna Hajiya..!kai tsaye yana Janyo Fayel Dinta Zama tayi Shi kuma Cikin Zafin Numfashi yace"Meke damunki.? Bayani ta Faramai Shi kuma yana Rubutawa Lokaci Daya yana Jifanta da Wasu Tambayoyi Tana Bashi amsa. Dr.Dina kuwa na Fita Daga Office Din Zain Hanyar barin Cikin aaibitin Ta Nufa Tana Tafe Tana Sharban Hawayen da ta kaasa Hanasu Zubowa,Allah ya Taimaketa bata Hadu da wani Likita ba sai dai Nurses da Metro wadanda ke mata kallon Ko lafiya wasu kuma suka Fara Gulman cewa Dama ai ita ke Bin Dr zain ammh Shi kallo bata Isheshi ba,Ahaka dai ta kai kanta Haraban Ajiyan Motoci Ta Bude Motarta ta Shiga Tayi mata Key idanuwanta Har Rufewa suka Farayi saboda kuka da Bacin Rai Da gudu ta yi Riverse ta Saki Hon aka Wangalemata Get tafice da Gudu Daga Cikin asibitin kamar azata Tashi sama Kai Tsaye Hanyar kano ta Dauka Domin Haka Kurum taji Tana Bukatar Zuwa Gida ko Zataji Sanyi Ko taje wajen zakiya mganar Duk Dayane Wlh zain yana so yayi mata Wulakanci kuma Wlh karyansa,Tana Tsausayamai bataso komai ya kwacemai ammh zai Fusata tayi Abunda batayi Niyyah ba,Haka tayi ta Sharara gudu kamar zata tashi sama. ***** Yau da Halima Tatashi Daga School Sun gama Lecture da Wuri Wajen 12pm ta Fito Daga Cikim makaranta Sai da ta Shiga Motarta ta Kira Zain Bayan ya Dauka sun yi gaisuwan da suka saba da Tambayan lafiya juna ta tambayeshi Tana so Taje Gidansu Laila Ta Duba Mamarta Bata da lafiya Dazu sukayi mgana da Lailar ganin batazo School ba yasa ta Kirata nan take Shaida mata Mamarta bata ji Dadi ba Batare da wani Tunani ba Zain yace Taje ammh Ta Tuka kanta a Hankali ta kuma kula da Kanta ta kuma Dawo da Wuri Domin Shima Bayan Sallar Jumma"a zai Dawo Gida Da Haka suka Rabu. Laila Suna zaune a anguwan yakubu Wanka ne,Koda Taje Jikim Mamar na Laila da Sauki Tunda Har an Cire mata karin Ruwan Da aka saka mata nan Halima Ta gaisheta da Jiki ta amsa Cikin Sakin Fuska Tana Tambayanta megidanta Daganan Dakin Laila suka Shigo Suna Hira Halima na Fadama Laila Karatun da sukayi a makaranta yau bata wani Jima ba ta mata Sallama ta Tafi da alkawarin gobe zata Dawo ganin yau din Bata Riko ma Mamar Lailan komai ba. Har Wajen Mota Laila ta Rakata Sukayi sallama Daganan Gida ta Koma Tayi wanka ta Shiga Kitchen Tayi Tuwon Shinkafa Miyar agun da Tok Fish Saboda Alhaji Tsoho da Kuma Abba ta Riga ta saba Tunda sukayi Aure Da Zain Duk Jumma"a bata Fashi Sai tayi musu wannan Tuwon Takai musu,Tana kamallahwa ta Saka a kololi guda Biyu Daya na Gidan Alhaji Tsoho Daya na Gida ne,na Abba kenan Sauran kuma ta Zuba ma Tanimu megadi nashi Sauran kuma ta Saka Cikin Wata karamar kula nata Dana Zain kenan Dama Tun Da Tadawo Zobo Ta Fara Hadawa ta saka a Fridge saboda yayi sanyi. Sai dai ta Gyara Kitchen din kana ta Koma Cikin Bedroom Ta Shiga Dama bayan ta Dawo Sai Taga Jinin al"ada yazo mata Tana Cikin Toilet tana Wanka Zain ya Shigo Gidan Bayan ya Shigo Dakin Jinta Tana wanka yasa Shima ya kwabe yabi ta Chan Bayi sai ta ganshi kawai ya Shigo Bata damu ba sanin Dama Yawanci Tare suke wanka nan suka Hadu sukayi wanka bayan an Sha Shafe Shafen Juna kafin su Fito Tare suka Shirya kansu Ita Shigar abaya Tayi Domin Halima Tana son Abaya Sosai Shiyasa Zain ya Cikamata Wardrope dinta dasu Shi kuma wani yadi ya saka mai Santsi Falo Suka Fita suka baje sukayi Dinner kana sukayi Shirin Fita Zain shi ya Dauki Duka Kololin Tuwon Ita kuma ta Dauko na Miya Sai Wani katon Jug da Zobo na Abba ne Alhaji Tsoho baya Chan Zobo,sai da suka kai komai Cikin Booth din Motar Halimar kana ta Koma ta Daukoma Tanimu megadi nashi haka ya Duka Har kasa yana mata Godiya da Kirarin Gimbiya agidan Dakta. Shidai Zain gabam Motar ya kame Saboda yace mata a Motarta Zasu Fita ita zata Tukasu ganin ta Biyema Surutun Tanimu ne yasa ya Fara latsa mata Hon da Sauri ta Sallameshi bayan tace ya Bude mata get da Gudu ya wuce Yana Fadin"Angama Uwargidan Dakta..Amaryama kuma Insha Allahu Daga ke ba kari gimbiya agidan Dakta..! Yafada yana yar Dariya Mirmishi kawai ta saki ta Juya ta Shiga Motar kallonta ZAIN yayi yana Fadin"Meyasa kike Biyema Shirmen Tanimu ne..? Shifa baya gajiya ko kwana zaku yi kuna Mgana..! Mirmishi ta Saki Lokaci Daya Tana ma Motar key Ta tasheta tayi Kwana ta Saki Hon kafin ta Sulala ta Fice Daga Gidan Tanimu na Faman Daga mushi Hannu Shi kuwa Fadi yake"Kai Tirr...Ga Gimbiyar Dakta..Tana Tuka Daktan da kanshi Allah bar kauna Kaji..! Sai da ta Daidata Tafiya kan Titi kana ta Saki yar Dariya Tana Fadin"Allah Tanimu na Tuna min da wani Idi akusa da gidan Goggo Halima Dake gada..Surutunsu da komai nasu Iri Daya ne.."Zain na Latsa wayarsa yace"Kidaina dai Biyemai Zainata..Karki manta ke Matar Dr.Zain ce..! Mirmishi Ta Saki kafin tace"Insha Allahi Zain Dina..! Hannunta Datake Driving yakai ma Kiss Yana Fadin"Nagode zainata..! Hira suka Fara sama sama Cikin Hiran ne Halima ta Kalli Zain Tana Fadin"Firstlove wai yaushe Zamu je Gada ne..? Ina son ganin Goggo Halima bansani ba ko lafiya kwana Biyu ina ta Kiran Layinta bana samu..! Kansa ya Shafa yana Fadin"Ki bari ku samu Hutu mana..Nima Kinga bani da Lokaci ko Weekend ne ina Shiga asibiti.." bata som mai musu yasa Tace"Shikenan Allah ya kaimu.." shi kuma ganin kamar ta Damu yasa yace"Karki damu ba komai..Tunda baki sameta ba ki kira Layin Isuhu mana kiji ko Lafiya..? Da Sauri tace"Kash nako manta da Kiran Ya Isuhu bari mu Daawo zan Kirasa naji ko lafiya..? Kai kawai ya gyada mata yana Cigaba da Latsa wayarsa ahaka har suka kai Gra Gidan Abba suka Fara Zuwa Sun ci sa"a kuma yana Gida Tana Shigowa da Kololi Bayanta kuma zain ne da kulan miya da Jug Din Zobo Nene Tace"Mungode Allah Da zuwanki Halima Domin ga Abbanki nan Duk Abincin da muka gama Jeramai yaki Taba komai yana Jiran Tuwonki..! Zain da Halima suka saki Mirmishi Abba kuwa yana Zaune kan Daya Cikin Kujerun Falon ya Sauko kasa yana Fadin"Allah yayi miki Albarka Diyata..Bani nan Kigani Hannuna Dama Tun dazu na wankeshi ke nake jira..'Gabadaya suka sakamai Dariya Har Umma data Fito Daga Kitchen nan Halima ta Baje komai Bayan Taje Kitchen ta Dauko Filet da Cokali ta Zubama Abba Kin karban Cokalin yayi yana Fadin"Bar ni na saka Hannuna Dashi Annabin Rahma ke Cin Abinci..! Umma na Gefe Tace"Ba Tayi ne Abba..? Kai ya girgiza mata yana kai Lomar Tuwo yana Fadin"A"a fa kuci Abincin ku yau na yafe..Wannan Tuwon Har Dumamen Gobe..'" Su zain Suna ta Dariya nan aka zauna ana ta Hira Halima ta Tambayi su Saudarta Nene tace suna gidan Alhaji Tsoho. Basu bar Gidan ba sai Bayan Sallar La"asar suka isa Gidan Alhaji Tsoho Shima chan Hajiya Mama Nata Fama Dashi yakin Cin komai yana Jiran Tuwon Halima Suna zuwa Hajiya mama tace"Nikam Halima wani Boka kika kai Sunan Mijina ya kamashi haka..? Aka saka Dariya Alhaji Tsoho nacin Tuwonsa yana Fadin"Ba Boka ba Mallam..Yin Allah ne Ko Hali Dubu..? Halima ta Daga kai Tana Fadin"Gayamata dai Tsoho..Kyaleta Kishi Take dani..! Hajiya Mama tace"Nima ai na Rama Domin Zainullahi yanzu Nawa ne.."Halima na Dariya Tace"Wane ke..?Mata ma Dadama sun gwada sun kasa ai Ba wacce ta Isa ne Ni da Firatlove Takalmin kaza kenan.."Zain yace"Kin Fadi gaskiya Zainata.." hararansa Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"Au bayanta kabi.." yana Dariya Yace"Toh yana iya Hajja mama..? Ki dau na Annabawa kawai..! Gabadayansu Dariya suka saka Nan suka kai Dare har sallar mangariba nan sukayi suna Shirin Tafiya ne sai ga Haddir da kaya yayo parking din kayansa ya dawo gidan Alhaji Tsoho Zain sai Dariya yakai mai yana Fadin"Wanda Yaja da Likitan kwakwalwa zai ga ba Daidai ba..! Alhaji Tsoho na Zaune yana Sakacen Hakorinsa Daya gama Cin Nama yana Fadin"Kwarai Matukar ina Raye Idanuwana na kan Jikokina Musamman ma Kai da Hadiru...'Haddir bai Tankashi ba Fuskarsa ba Walwala ganin Haka yasa Hajiya Mama da Tabawa suka Rika Tayashi kwasan kayansa Zuwa Bedroom Din Dake kusa dana Alhaji Tsoho Tana Fadin ta Sauya Miji ga Hadiru Yaro Sammari ga kyau ga Kudi me zatayi Da Ragowan Halima. Sai Dariya ake Zuwan Haddir yasa suka Kara Shantakewa sai Wajen karfe 9pm suka koma Gida,Zain yana Cike da Bukatarta Ganin Tana Fashin Sallah yasa ta Lallabashi ta mai Dubarin Datake mai in Tana Cikin Jinin Al"ada har ya samu ya gamsu suka kamkame juna Har Barci mai Nauyi mai Dadi ya kwashesu. *Shakira..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             1️⃣0️⃣ *KANO...* _Area:Sabuwar kofa..!_    "Kwance Take Kan mamaken Royal Bed wanda yaji Shinfudun Alfarman,Misalin karfe 10:46am na safe na Ranar Lahadin karshen mako. Motsawa Tayi Ta leko Da kanta cikin katon bargon Datake ciki Lokacin Da Taji Karar Wayarta Dake saman Side Drower din Gadon,Hannu ta zira tana wani yamutsa Fuska Lokaci Daya Ta Jawo Wayar nata ganin Sunan Zakiya Ya bayyana baro baro saman Sreen Din Wayar nata yasa Ta Daga Cikim kasala Tana Fadin "Zakiya yane...! Dagachan Bangaran Zakiya Tace"Kina ina ne nazo naga gidanki a kulle..? Ko kina Cikin asibitin ne..? Wani Hamma Dina Ta tattaro ta sakarma Zakiya Tana gyara zaman Blanket din Data Rufu Dashi Take Fadin"Ina anguwar Sabuwar Kofa...! Cikin Mamaki Zakiya Tace"Kano..? Dakai Dina Ta mata amfani Wajen bata amsa Kafin Tace"Eh ina Kano..Tun Ranar Friday na Taho.." Zakiya Ta gyara Tsayuwarta Jikin Bakar Motar kirar prado Tace"Ke kuwa me kika je yi kano Haka da gaggawa ba Labari..? Karamin Tsaki Dina Taja Lokaci Daya Tana yamutsa Fuska Kafin ta Yunkura ta Mike zaune ta Jinkina Bayanta da Jikin Gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Hmm Bari kawai Zakiya Wai ni Zain ya kora Daga Office Dinsa..." Cikin Zaro Ido Zakiya Tace"Kora kuma..? cikin Takaichi Dina Tace"Wlh Korar kare yayi min Ranar friday Dana Shiga Cikin Asibiti,Abunda ya bani Tsoro Shine wani kallon Tsana Danaga Yana Bina Dashi Abun ya bani Tsoro Sosai...! Zakiya Ta saki Tsaki Tana Fadin"Hmm lalle..Ai Indai baki kama kanki ba kina Tare da Wahala Dina...Karki manta Boka Yace Sihirin Dayayi masa fa na Dan anace ne Ko Baki Bishi ba zai Biki Dolensa ammh sai kiyi ta Binsa yana Miki Wulakanci Kuma ahaka ke ki kiran kanki mai aji Mtswwss Wlh,Wannan dai Abunda kike yi Shine Rashin aji mu kuma Abunda muke yi kina ganin Rashin Aji ne Shine ajin Tunda ko Yayane Namiji bai isa ya Wulakantani ba Sai na Juya akalata Tunda bashi kadai bane Namiji agidan Duniya ba.." Cikin Zafi da Takaichin Kalaman Zakiya Dina Tace"Zakiya kin fa sani Ba iya Sha"awar Zain kadai nake ba Ina Tsananin Sonsa Wanda bana iya Jure Rashinsa,Ina so Koda Yaushe ya kasance yana Tare Dani Nima ina Tare Dashi Ina so Na zama wata Bangaran Rayuwarshi Gabadaya zakiya ya zanyi..? Wlh ina Son Zain So kuma mai Tsanani Wanda Domin Son na mallakeshi ban Damu da kowa waye zai Rasa Kimarsa ba, indai Zain zai zama Nawa na har Abada.." Tafada Cikin Fidda Wasu Zafafan Siraran Hawayen Da suka Cika mata Idanuwanta gyara Tsayuwa Zakiya Tayi Tana Fadin"Shawarata kawai zaki Dauka Dina Cikin kankani Lokaci Burinki zai Cika zaki mallaki Zain Insha Allahu..."Kai Dina Ta gyada tana Share Hawayenta Take Fadin"Shikenan Hakan za"ayi Na yarda mu Sare macijin Da Kansa Lokaci Daya Tunda bayajin Roko ballatana ban baki..Zan Dawo Gobe in Allah ya kaimu Asibiti sun Kirani.." Zakiya ta Kada kai Tana Fadin"Ok..Sai mun sake mgana.."Daga haka suka yanke Kiran Dagachan Bangaran kuma Zakiya ta Shige Motarta Ta bata Wuta ta bar Kofar Gidan Dina Ranta Cike da Sake Sake da kuma Hanyar da zasu bi komai ya Daidaita Ita kuwa Bangaran Dina Ture Bargon Tayi ta Sauko Daga kan Gadon Daga ita sai Wata Doguwar Rigar barci mai Igiyoyi Gashin kanta Ta tattara ta saka aBand,Silafas dinta ta saka Ta Nufi Hanyar Kofa tana wani Taku Cikin Son Nuna ita din Watace. Saukowa Take Daga kan Steps din Tana wani Lumshe idanuwanta Kamar mai Jin Barci nan kuwa Tunani Take Gata agidan Zain a matsayin Matarsa Shiyasa Take saukowa Cikin wani Rangaji da Karairaiya,Har ta Sauko Gabadaya Falon Inda kannenta Waleeda da Waleed ke zaune suna Buga game ganinta yasa Dukkansu Suna Hada bakin Wajen gaisheta"Gud Mrning Anty Dina.." Kallo Daya Tayi Musu Ta kauda kai kafin Tace"Mrning Kids How are u..? Tare suka amsa da "We are Fine.."Daga haka ta jinjina kai ta Wuce kai Tsaye Dinning aRea Mai kama da alkarya guda,Kujera ta ja ta zauna Ta Fara Bubbude Kololin Gabanta tana Wani yamutsa baki kafin Ta Daga baki Tana Fadin"Zulai...Zulai.." Da dan karfinta Da Sauri Wacce aka Kira Da Zalai ta Fito Da Gudu Daga ciki jikinta na Bari,Gabanta ta Durkusa Tana Fadin"Gani Hajiya ina Kitchen Ne Lokacin da kike Kirana.."Tafada Cikin Ladabi kanta na kasa ko Kallonta batayi ba Tace cikin yanga da Yauki."Soyamin kwai 3 karki saka Gishiri kana ki Soyamin Buredi da kwai.." Da Sauri Zulai ta mike Tana Gyada kanta Cikin gamsuwa Tace"Angama Hajiya Bari naje na soyo.."Da sauri ta Juya ta koma Kicthen ita kuma Sai ta Kada kai ta jawo Fulas Din Ruwan Zafi ta samu karamin Kofi ta Tsiyaya Ruwan Citta da Na"a Na'a,ta Fara kurba sannu a Hankali Cikin kwanciyar Hankali. Tana Cikin Kurban Tea din Taji Kamshin Wani Turare mai Dadin Shaka ya Ziyarci Hancinta Lumshe ido Tayi Kana ta Budesu kan Inda Take Jiyo kamshin Fes ta Sauke su kan Matar Mahaifinta Anty Batula Farar mace alkayabban mata Cikin Shiga ta alfarma. Kai ta kauda ta wani Tabe baki Tana Jinta Tana mgana Dasu Waleed kafin ta Kariso Dinnig din Taja Kujera Ta zauna Tana kallon Dina Wacce ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Gud Mrning Uwata.."Tafada cikin Wani Izgili Duk da Batula ta san da Tsageranci Dina ke Kiranta Uwarta,ammh Nuna mata take taFita iya Duniyanci Cikin Sakin Fuska da Fara"a Tace"Mrning Dota..? How was ur Nite..? Cikin Basarwa Dina Tace"Cool..."Daga Haka ta Dauke kai Cikin Mirmishin Leben baki Hajiya Batula tace"Yayi kyau..? Yaushe zaki koma Bakin aiki ne..? Sarai Taji Tambayar nata sai kawai ta Basar da mgana Cikin Kallon Ido Cikin Ido Take ma Hajiya Batula sanda itama Take Tsiyayan Ruwan Na"a Na"an Tana wani Sakin Annurin Dake Fuskarta. Cikin Dakiya Dina Tace"Uwata yaushe Daddyna zai Dawo ne..? Sai da ta Kurbi Tea din kana Ta kalleta Tana Fadin"bansani ba Kila dai Cikin Satinan...Kinsan in suka Tafi Abuja Tarurrukan nasu Yakan yi sati bai Shigo Gida ba.."Wani irin kallo Dina ta Jefata Dashi Tana Tunanin kalaman zakiya akan Yawan Tafiye Tafiyen Da Daddynta keyi Saurin kauda wannan Tunanin Tayi Zuwan Zulai da Filet din kwai,Sai Dayan Filet mai Dauke da Soyayyan Buredi Da kwai kan Dinning Din ta ijiye mata Tana Fadin"Gashi Hajiya.." Shuru Dina Bata ce mata komai ba Kuma Idanuwanta na kallon Wani Gefe bata ma kalli Abunda Zulai din Ta kawo mata ba Hajiya Batula ne ta kalli Zulai Tana Fadin"Tafiyarki Zulai..Je ki cigaba da aikin ki.." Cike da Girmamawa Zulai ta Rankwafa Tana Fadin"Toh Ranki ya Dade..."Daga haka ta Wuce Da Sauri Dina ta Bita da kallo mai kama da Harara Kafin ta saki Wani karamin Ajiyar Zuciya ta ja Filet din kwai ta Saka Fork ta Fara ci Cikin yanga Kamar Tana Tauna Madaci Hajiya Batula Ta Sauke Kofin Hannunta Tana Fadin"Wai yaushe zaki leka chan Sudan ne..? Naji ko kwanaki Babanki na Basu Hakurin kina Tafe Aiki ne yayi miki yawa.." Kur Kawai Dina Take kallonta Kamar bazata Tanka ba Sai Chan Ta Nisa Tana Fadin"Uhm...Zanje Insha Allahu Nima Suna ta Kirana kan Bikin Diyar Anty Jiddo da za"ayi.." jinjina kai Hajiya Batula Tayi kafin Tace"Gaskiya kam ya kamata..Allah bada iko.." Daga Haka ta Tsuke bakinta Ganin Dinar ta Mike ko Soyayyan Buredin bata ci ba ta dai Ci kwan Shima bada yawa ba,Batare da tayi mata mgana ba kawai ta Wuce zuwa sama Tana wani Taku Daya bayan Daya Kowani Gabanta na Girgizawa Cikin Kallon Tara saura Kwata Hajiya Batula ta Bita Dashi har sai da ta kule ma Ganinta kafin Ta Tabe baki a Fili  ta Furta"Allah ya Shirya.." Domin Duk Macen Da Taga Dina Da yanayinta zata mata Zargin Tasan Namiji,sai dai ita bata Shaidanta da Iskanci ammh kam wasu al"muran na Dina Suna Bata mamaki kara Tabe baki Tayi kawai Ta mike Daga Dinning Din ta Nufi Falon Inda Yaranta gefe Daya na Zuciyarta na Watsar da Sha"anin Dina ganin Mahaifinta ma bai damu da Bincikan Halin data ke Ciki ba,Ballatana ita da bai bata wannan Damar ba Ballatana ita kanta Dinar da bata mata kallon Uwa sai ma wani kallon Raini da Kaskasacin Data saba yi mata akoda yaushe. ****** Kamar yadda Dina ta Tsara Washegari ta koma Bauchi Kuma aranar ta Shiga Cikin Asibitin ta iske an kawo wata patient zata Haihu ita da Dr Aisha Sukayi Attempting Din Patient din ta Sauka Lafiya Gabd Mganariba Dina ta bar Cikin Asibitin Zuwa Gidanta a Hanya sukayi Clashing Da Zain Kila ya Fita ya Dawo ne,Tana ganinsa yayi mata Double Signa Zuciyarta kamar ta Fashe saboda Farinciki Bata Bi ta kansa ba Ta Take Motarta Tana ji ajikinta Dole zai nemeta Dolensa. Kamar kuwa ta sani Tana komawa Gidanta tayi wanka tayi Sallah ta Sauya kaya zuwa Wasu Riga da wando iyakar Wandon Gwiwanta,rigar kuma Cibiyarta Bude Take,Kitchen ta Shiga Ta Soya kwai ta Dafa Ruwan Zafi ta Fito Falo Ta zauna kenan Sako ya Shigo Wayarta ganin Lambar Zain da tayi ma Saving da *LIFELINE..* Yasa ta Ja Saman wayarta da Sauri Cikin Rawan Jiki Ta Duba Sakon Nashi Inda yace Mata" kina gida ne..? Kawai yace Cikin Sakon nashi,Wani kayattacen Mirmishi Tayi kafin Ta Maida wayarta ta ijiye,Tana wani kada kai kamar wata Sakarya,Zata Bi mganar Zakiya Dole me ta Koyama Zain Hankali Ko zai gane Darajarta. Ba"a jima ba, Taji Tsayuwar Motarsa Tashi Tayi da Sauri Ta Bude Labulen Window ta Leka Daidai Lokacin ya Bude Murfin Motan ya Fito yana gyara zaman Tek tie din Wuyansa Cikin Wani irin kallo Take Binshi Dashi kamar ta Jawoshi Ta kwakwameshi Ganin ya Fara Taku Zuwa kofar Mashiga Flat din Nata yasa ta koma Ta zauna ta Harde kafa Daya kan Daya,Tana Kurban Tea din Hannunta Taji yana Knoking din Kofarta Sai da ta Sha iskanta tana Wani Hura Hanci Tatashi Bayan Ta Ijiye kofin Hannunta Saman Center Table Din Dake Tsakiyar Dakin Ta Fara Taku Cikin Wani Iya Bariki Ta isa Jikim Kofan Ta Bude Fuskar Zain Ta bayanna wacce baka isa ka gane yanayin Dayake Ciki ba. Kallon Kallo Sukayi ma Juna Cikin Wani Yanayin kafin kowa ya Janye Idanuwansa yana Mganar Zucci Ita Dina Farinciki ne ya Cika ta kamar an sakata a Aljannah Ganin Zain ya Biyota Shi kuma wani Takaichi ne ya kumeshi yana kallonta yana Tunanin me Tafi Zainarsa..? Me Dina Take Jiyar dashi Da In ya kwana Biyu zuwa uku bai Kusanceta zai jishi kamar ba Daidai ba Baya Samun Kowani Natsuwa sai yazo Gareta..? Amsan Daya Gaza samun amsanta kenan Kuma Tuni Take yawo acikin Ransa. Baya ta Koma Batare da tamai Mgana ba ta Bashi Hanya,Cikin Takun Jaruman Maza ya Taka ya Shiga Falon ita kuma ta maida Kofa ta Rufe ta Biyo Bayansa Tsakiyar Falon ya Tsaya yana Nazarin Falon kamar yau ya Taba Shigowa Ita kuma kai Tsaye wajen zamanta ta koma Ta zauna Tana Daura Kafa Daya kan Daya Cikin Wani irin yauki Ta Sunkuya Har sai da Nonowanta Ta sama Suka Bayyana Filet din Da ta saka kwan ta Dauko Zuwa kan Jikinta ta saka Fork din Dake saman Wajen ta Fara Tsakura Gefe Daya kuma na Zuciyarta Najin Kaifin Idanuwan Zain akanta. Shi kuwa kallonta yake Cikin Mamakin Shareshin Datayi Cikim karfin Hali yace"Baki ga Sakona bane..? Sai da ta Tauna Kwan Dake Cikin Bakinta Kana ta Dago Dararan Idonta ta saka Cikin Nashi kafin tace"Nagani mana." Tafada Cikin Wani lum da idanuwanta Cikin Kissa cikin mamaki yake Fadin"Kingani.? Kai Tsaye Tace mishi"Eh nagani.." Cikin Kufuluwa Yace mata"Me hakan ke Nufi Dina..?kinga Sakona kinyi banza Dani Nazo kuma kin kalleni kin watsar kamar baki ganni ba.."Dina ta saki Mirmishi Cikin Farinciki acikin Ranta Tace"me zan yi maka..? Dama ina da Sauran wani amfani ne awajenka ka manta kai ne ka Koreni Daga Office Dinka Ranar..? Ina Zainar naka..? Na Dauka zata Share maka Gurbin Dina acikin Zuciyarka kamar yadda kake ikirarin Ta Share ta kowacce mace.! Wani Taku ya Fara Zuwa Gareta Ido Cikin Ido yake kallonta kafin ya saka Hannu ya Fizgota ta Mike Tsaye Filet din Dake Hannunta yayi Gefe Cikin Tsoro Take kallonsa Idanuwanta ta Zaro ganin Yadda Fararan Idanuwansa Suka Sauya launi Cikin Wata Irin murya yace"Dina baki da amfani awajena...Ba ki kuma da wani Kima acikin Zuciyata..Haduwata Dake Kaddara ne Haka ma Tarayyana Dake Tsakaninmu ma Kaddara ne Sai dai ina so Ki sani ba iya Kamarki Zaina ta Koremin acikin Rayuwata ba Irinki Dubu ma Ta Sharemin Su Tas..Ita Tauraruwa ce kuma Zahra ce Cikin Wata." Ya karishe Fada ya Wani Mata wani Munafukin Mirmishi Cikin Takaichi Ta Juya Labbanta zatayi mgana ya Dakatar da ita Bayan ya Dora bakinsa kan Labban nata yayi mata wani Light kiss din Daya Sumar da ita Bata Dawo Daga Cikim Hayyacinta ba ya Radamata Cikim kunnuwanta. "Kada ki Hada kanki da ita..Ita Ta Dabamce Awajen Zain..Ina mata Kaunar da Bayan Ahalina babu kamarta Ki kiyayi Harshenki Wajen Ambaton Abunda Zain yafi kauna Da Darajawa sai Ki Tsira da Matarbanki.."Cike da Izza da Dariyan keta yake gayamata Haka kuma bai bata zarafin mgana ba ya Hade bakinsu yana Bata wani Hot kiss wanda ya Rikita ta saki ajikinsa Lokaci Daya Tana karban Sakonshi Fin Minti Goma kafin ya saki Bakinta ganin yadda tayi Laishi ne yasa ya saki Mirmishi kafin ya Shafa Kumatunta bai Tare da yayi mgana ba ya Ciccibeta zuwa Jikinsa ita kuma ta kara lafemai Wutar kaunarsa da Kishin Halima na Cika mata Zuciya Da Kafa ya Daki Kofar Bedroom Din ta Bude ya saka kai Cikin Kan Gadon ya Wurgata Kafin ya Bita ya Danne yana Sumbatarta ta ko"ina Cikin Mugunta Cikin Ranshi Kuwa yana Tunanin Gwara yau yayi ma Dina Cin Kacha kila In yayi mata Ci mai kyau Bazai kara Jin son kasancewa Da ita ba. Ita Kuwa Dina Farimciki ne ya Cikata da Sassafar take Rabashi da kayan Jikinsa,shima Cikin Saurin yake Rabata da kayan Jikinta,Achan gefe kuma sai Kiraya Kirayan Sallar Isha"i akeyi ayayinda wasu Mutanen ke kokarin yin alwala Domin Tafiya Masallaci Wasu suna chan Suna aikata Sabon Allah Wa"izubillah. ***** Shudewar Awa Daya da Wani Abu Zain yana Caccakan Dina Kamar Allah ya aikoshi So yake yaji Kwadayinta da Sha"awarta Sun Kare acikin Ransa Ita kuwa Dina Duk da Yadda Jikinta ya gaji da Sabon Mu"amalanta da Zain bai sa ta Nuna gajiyawarta ba sai ma kara Daurewa Da tayi Tana Kokarin Bashi Hadin kai Akallah ya Juye mata Abunda ke Maransa yafi Sau Uku kafin ya Sarara mata,ya koma Gefe yana Maida Numfashi Sama sama,Itama Dina Numfashin Take Maidawa Lokaci Daya kuma Tana Mirginowa Tana Rungume Zain din Ta Baya Ta Cikin Blanket din Da Zain ya Rufa musu Saboda Shi mutum ne Da baya son Ganin Tsaraicin Juna Gaskiya Tunda ta Fara Tarayyah Dashi baya yarda ya kalleta Ido Cikin Ido Ba komai ajikinta. Tsawon Mintina goma Kafin ya yunkura ya Ture Dina Daga Jikinsa,Daga kwancen ya Jawo Boxers Dinsa Dake gefe ya Zura Duk da kyamar kansa ya kamashi ammh bai zai iya Shiga  Toilet din Dina ba Yana Da Tsantsane da Tsabta da kyankyani,Abunda yasa ma yake Mu'amala da ita batare da kariya ba saboda yasani shi ne kadai Namiji kwara Daya da Dina Take Mu"amala Dashi Shi yasa ya bata yardansa a wannan Fannin. Saukowa yayi Daga kan Gadon Sauri Sauri ya Maida kayan Jikinsa,Dina Data Dago kanta Cikin Blanket din Take Bin Zain da wani irin kallo na Tsantsan Farinciki,Tana kallonsa Ya Zura Hannu Cikin aljihun Wandonsa ya Fito da Wayarsa,Missed calls yagani Rututu Na Firstlove Dana Nene sai na Haddir Karamin Tsaki kawai yaja Lokaci Daya yana Daura Tek Tie dinsa,Cikin Hanzari ya maida Coat din Dake Jikinsa Batare Daya kalleta ba ya Juya ya Fice Daga Dakin Ko Waiwayota baiyi ba Karamin Dariya ta saki Cikin Wani Shauki Tace"Hmm Yanzu aka Fara wasan..! Sai da ya Shiga Cikin Mota ya Daidaita zamansa kana ya Kunna Motar ya Fice Daga Kofar Gidan Dina da Gudu Daidai Lokacin da agogon Fatan Dake Hannunsa ya Nuna Karfe 9:20pm na Dare karamin Tsaki Yaja Yana Tunanin Dole zai koma Cikin asibiti Yayi wanka bazai iya zuwa gida ahaka ba In ya yi Wanka Firstlove zata Dora ayan Tambaya akansa Wanda kuma Faruwar Hakan kamar Faruwan wani Abu ne. Cikin Asibiti ya koma Office Dinsa ya Shiga yayi wanka bai Fito ba sai da ya Tsaya ya Tsane Ruwan kansa da Karamin Towel Din Dake Toilet kana ya Fito Sauri Sauri ya kara Shiga Motarsa ya Fice Daga asibitin ya Nufi Hanyar Gida Daidai Lokacin Wayarsa ta kara Daukan Tsuwa Tana Gefensa ne ya Waiga yaga Firstlove ke Kiransa Da Sauri yayi amfani da Hannu Daya ya Dauki Wayar nasa ya Daga Kiran yana Fadin "Hello Firstlove...!" Dagachan Bangaran Halima ta Buga Tsalle Tana Fadin"Heyy Firstlove...Zuwa America Ya Tashi...Anty Zareena ta Haihu Yanzu Ummana ke Fadamin.." Tafada Cikin Bayyana Farincikin Datake Ciki,Bakinsa ya Washe yana Fadin"Masha Allah...Me aka samu.? Cikin Murna da Farinciki Halima tace'"An samu Baby Girl Firstlove.."Zain ya Kada kai yana Fadin"Allah ya Raya ya amfana Jalal ya samu kanwa kenan..? Halima Tace"Jalal Kuwa ya samu kanwa Firstlove yaushe zan Tafi ni..? Ko Tare da Umma zamu Tafi..? Fuska ya yamutsa kamar Tana kallonsa yana Fadin"A"a Firstlove ina kuma Zaki kin manta kun kusa Fara Test ne a makaranta..."Tura baki Halima Tayi Tana Fadin"Kai Firstlove...Kaifa kamun alkwari Sanda Umma zata maida Anty Zareena Lokacin kace na bari zamu je Tare dakai,yanzu kuma sai kace A"a bazani ba.." Tafada Kamar Tayi kuka Mirmishi ya saki kafin yace"Naji..Ki bar wannan Tura Turan bakin sai na dawo sai muyi mgana.."Cikin Bata rai Tace"Yaushe zaka dawo Toh...? Da Sauri yace"Yanzu ina kan Hanya ne.."Batare da tayi mgana ba Ta katse Kiran alamun Ranta yana bace ne Wayar ya Sauke yana Mirmishi kafin ya Furta afili"Zaina Rigima.! Sun Gama wayar kenan sai ga Kiran Zareena Da Lambar Waje Da Sauri ya samu Gefen Hanya ya Faka kafin ya Daga Kiran Nata yana Fadin"Abokiya Zareena Barka da Arziki..." Dagachan Bangaran Zareena Dake Kwamce kan gadon Marasa Lafiya awani Daki na Musamman Cikin Wani kayattacen Asibitin kudi Dage U.S Babban Birnin America,Fara mace ce Wacce Ba inda ta Baro Nene a kama Sai dai afizge Tana Diban Kama da Zain,Rumgume da Jaririyarta sai Megidanta Dake Gefenta Jawaad da Yaronsu Dan Shekaru Uku da wani Abu Jalal. Cikin Farinciki Da Jin Muryan Dan"uwanta Tace"Aboki Zainullahi Yauwa..Ashe ka samu Labari..? Yana Shafa Sumar kansa yace"Eh yanzu Mukayi Mgana da Firstlove Take Fadamun Ta Fara Rigiman sai Taje nace ta bari na koma Gida sai Muyi mganar.."Zareena na Dariya Tace"Wlh da gaskiyanta ita da Zafira ba wanda ya Taba zuwarmin gwamma kai da Haddir kun Rakoni Lokacin da Umma zata maidani Wannan Karon Tunda ba Gida na Haihu ba Ina Bukatar ganin Duka Ahalina.." Zain yace"Insha Allahu karki Damu Abokiya Zareena ga Ummamki zata yi Kokari Taga Ta isa kan Lokaci.."Ya karishe Fada yana Dariya Zareena tace"Fadi ka kara Gobe Abba yace Min Umma zata tafi Lagos yama Mijin Inna Hannatu mgana zai nema mata Flight din da zai Tashi Da Daddare da Safiyar jibi zata iso nan din..' Zain yace"Uhm kaji masu Umma...."Zareena Tace"Kwarai wanda Bai da Umma kuma Sai Jin Haushi.."Zain yace"A"a Fadi ma wanda bai Dashi Ni ina Da Neneta.."Dariya Ta saka kafin Tace"Yanzu muka gama mgana da Aboki Haddir yace min ya kiraka ka Baka Daga sai nace bari na gwada kiranka nagani sai gashi kuma ta Shiga..Gamu asibiti ammh yanzu za"a bamu sallama mu koma Gida.." Zain yace"Eh naga Kiransa Ban Kusa da wayar ne..Allah Sarki Abokiya Zareena Allah ya Raya Jalal yayi kanwa kenan Ina angon Karni mijin Zareena.."Tana Dariya Take kallon Mijinta Lokaci Daya Take Fadin"Gashi a gefena..Ga Jalal mana yana gaida Uncle Zain,nidai Har kai da Aboki Haddir ku Taho Don Allah Kila sai ya samu Wata Yar Baturiya anan su Daidaita Tun Da naga alaman ya Fara zama Tazuru ba Aure.." Zain ya Saka Dariya Yana Fadin"Wlh ai yama zama Tazuru kawai ya jira in Wannan Jaririyar ta Girma Sai ki bashi Ita ya Aura..."Zareena ta saka Dariya Harda Jawaad Dake gefensa Tunda Wayar a amsa Kuwawa aka sakata Zareena Tace"Kai mugu ne Aboki Zain Sai na gayamai.."Zain yace"Gayamai ko yaji Haushi nan da Wata Biyar musha Biki..Haddir fa ina jin Ko Budurwa bai da ita.."Zareena ta kada kai Tana Fadin"Zai yi ne in Lokacinsa yayi da yardan Allah.." Zain yace"Allah ya yarda..Ba Angon karni Wayar mu gaisa..Nan ta mikama Jawaad wayar ya karba suka gaisa da Zain ya yi mishi Barka Daganan sukayi Sallama Bayan sun gama wayar ne Sai ya Kira Nene nan take Shaidamai Haihuwar zareenan yace sunyi mgana Daganan ya tada Motarsa ya Nufi Gida,Koda yaje chan Rigimar Zainarsa ya tashi kan ya barta Taje sunan Zareena ba yadda ya iya Dole ya amince Sai da ya koma Gida sukayi mgana da Haddir inda yace Daman Zareena ce tace ta nemi Wayarsa bata samu ba,Cikin Dakile Zencen Yace mai Sunyi mgana Daga Haka ya katse Kiran Saboda Bayaso Haddir din ya Jefomai Tambayan Ina yaje har ya Kirashi bai Daga ba. Washegari da Safe kan ya Tafi aiki ya Biya Gida Ya gaida su Nene nan yaji Tafiyar Umma yau zata Bi Jirgi zuwa Lagos,Bai sani ba kawai Umma tace mai Tare da Zainarsa zata tafi mamaki ya kamashi Yace ma Umma"Umma na Dauka sai Zuwa Suna Sauran kwana Biyu Lokacin Jirgin da wadanda zasu Tafi Sunan ya samu..? Umma Ta kalleshi Tana Fadin"A" a Tare Da ya'yana zan Tafi...Ta kano zamu Tashi Zuwa Lagos Zafeera nachan na Jiranmu."Mamaki ya kama zain kawai sai ya Fara Tura baki yana Fadin"Nifa Umma ban amince Tatafi yau ba gaskiya.."Umma bata kulashi ba Ta kalli Nene Tana Fadin"Nene Gayama D'anki Da yata zan Tafi Yaji da wai ma.."Daga Haka Tayi Shigewar Daki Ta barsu nan Nene ta Lallabashi ya yarda,Dole ya Kira Zaina yace ta Shirya zata Bi Umma Ta Fara Murna tana Tsalle Ta Fara Shirya kayanta ta Kira Laila ta gayamata Ta kuma ce ta Dinga saka mata Atendence kafin ta Dawo Da haka sukayi Sallama,Saboda Zumudi Ko Ta Jira Zain din ya Dawo batayi ba ta Hado kayanta zuwa Gida,Sai da tazo Taji Labarin Harda Zafira zasu Tafi ta fara Murna Nene da Umma na Musu Dariya Zain yana asibiti Halima ta Kirashi kan zasu Tafi Suna Gidan Alhaji Tsoho baro asibitin yayi yazo Sukayi sallama Daga Halima sai Umma Direba ya Tafi Dasu kano,Wajen La"asar suka isa,Salloli kawai sukayi suka Nufi Airport Dama sun ci Sa"a sun samu Jirgin Azman wanda zai yada Zango a Birnin Ikko Suka Shiga Bayan Inna Rukayyah ta Rakasu har Airport din Tana musu Fatan Dawowa lafiya Domin bazata samu zuwa ba Inna Hannatu ce Zata tafi. Jirginsu ya yada Zango A Murtala Muhammed International Airport Dake Birnin Ikko,da Misalin 7pm na yammah Direban Gidansu Inna Hannatu yazo ya Daukesu Zuwa Gidanta Dake Victoria island,Nan sukaci Abinci sukayi Sallah Ba zencen zama Domin Jirgin Karfe 11:30pm na Dare zasu bi Zuwa U.s Babban Birnin America. Koda 11pm Tayi a Airport Tayi Musu Daman Mijin Inna Hannatun ya Riga yayi musu Bucking Tunda Tafiyar Harda Ita Lokaci nayi kuwa Jirginsu ya Daga Basu isa ba sai Washegari da Hantsi Dama Tun Suna Lagos Sunyi waya Da Zareena sun gayamata Lokacin Hawan Jirginsu ita kuma sai ta Kin Taci Lokacin Saukarsu Suna Sauka suka ga Jawaad da Dansa Jalal Sunzo Daukansu a Filin Jirgin nan suka Rankaya sai Jerin Estate din da Ma"akatarsu su Jawaad ta basu Umma ce kadai Ta Taba Zuwa Lokacin Da Zata maida Zareenar Bayan Jawaad din ya kawota Gida Ta Haifi Jalal Lokacin ya samu Hutun Karshen Shekara ne sai suka Tattaro Gabadayansu Zuwa Mahaifarsu Sai bayan Ta Haihu Tayi Arba"in kana suka Dawo Da Rakiyar Umma da na Mama Safiya Matar Dadyn Abuja,Tunda Daman Tun Dawowarsu kasar ba wanda ya Taba Zuwar mata sai wannan Zuwan Wanda Bakin Zareena yaki Rufuwa Saboda Murnan ganin Ahalinta. *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*                  1️⃣1️⃣ "Sai da su Halima suka kwashe Wajen kwana Goma a kasar ta U.S kafin su Dawo,Kwanansu Hudu da zuwa akayi Suna Yarinya taci Sunan Umma Wato Fatima,Suna Kiranta little Umma Washegarin Suna sai ga Baban Kaduna da Mom Ikilima Sun Biyo Sun ga Zareena da Bby kwana Daya sukayi suka Wuce Cyprus Wajen Sadiq karami Chan Yake Degree dinsa Yana Shekara ta uku achan. Tafiyar Halima Ta saka Dina Tayi amfani Da Wannan damar Kusanci ya kara Shiga Tsakaninta da Zain wanda take iya bakin kokarinta Koda yaushe suna tare acikin asibiti ne gidanta ne,Ita take Dauke mai Kishiruwan Zainarsa,Duk da baya Jin Dadin Hakan dayake yi Ammh kuma bashi da wani Zabi,Haddir kuwa Ransa ba karamin kuna yake ba in yaga Zain da Dina suna Tare Saboda ya sani Shedaniya ce Kuma bawai ya yarda da kalaman Zain Din bane bama Shi kadai ba Mutane Da Dama suna Dora musu Zargi,Ganin Abun nasu yayi yawa ne yasa ya yanke Shawaran zai yi ma Zain din mgana Tunda yanzu har Fita Suna Tare da Dinar Wani Lokacin da Motarta wani Lokacin da Motarsa Cin Abinci kuma Tun Farkon Tafiyarsu Umma yake zuwa Wajen Nene yana Ci ammh yanzu sai dai Dina Ta jashi Zuwa Waje Su je chan suci Abinci ko kuma ta Jashi Gidanta Su je chan suyi Watsewarsu in Sun gama ta Sulala musu Ko Indomie ne Suci Su Dawo Cikin asibiti Abubuwa dai gasunan ba Tsari Wanda Haddir din yake Tsoron Faruwar waani abu. Ranar sun Dawo Daga Resutarant Cin Abinci Bayan sun Faka Motarsu a parking Space,Sun Fito Motar Dina ce ita ke Driving Din Motar Dukkansu Sun Fito Suna Dariya Fuskarsu na Bayyanar da Annurin Da Suke Ciko karo Suka ci Da Haddir ya Fito Daga Cikin asibitin zai Fita da kallon Mamaki ya Bisu Dashi Daga Zain Din Har Dina,Zain kuma kallon kallo Sukama Juna kafin Zain din ya kauda kai Dina kuwa Data gaida Haddir Kin amsata yayi sai ma kallon Tsana Daya watsa mata yana kallon Zain Lokaci Daya Yana Fadin"Zain ina son mgana Dakai..! Yafada Cikin Kakkausan Murya Juyowa Zain yayi yana kallonsa Kafin ya kada kai ya kalli Dina yana Fadin"Shiga ciki gani nan Tafe.."Daga haka ya Juya ya Bi bayan Haddir wanda ya karisa Wajen Motarsa yana Bin Dina da wani kallon Tara saura kwata Ita kuma kai kawai ta gyada kafin ta wuce zuwa Cikin asibitin Tana wani Takun Isa. Zain na karisowa Kusa da Haddir ya karkace Kai yana Fadin"gani Lafiya ka ke son ganina..? Ido Cikin Ido Haddir yace'"Meka yi kenan Zain..? Kasan Ma"nar haka kuwa..? Gyara Tsayuwa Zain yayi yana Fadin"Me kenan..?bangane inda ka Dosa ba Mallam.."Haddir ya Murmusa yana Fadin"Karka Raina ma kanka Hankali Zain..Kagane inda na Dosa ina mgana ne kan Wanchan yarinyar Dina,miye yake Hadaka Da ita..? Muharamanka ce..?na lura dakai kwana Biyun nan kun wani kulle ne wanda kuma Nake zargin Ba ta alheri bace..! Zain ya wani Cije baki kafin ya fara mgana"Bangane Kaga mun kulle ba..?wannan wata irin mgana ce Karfa ka manta Dina Bayan Abokiyar aikina Abokiyar karatuna ce kuma Kawata ce akwai illah ne Don kaganmu Tare..? Kuma wani irin Ba alheri bane kake Fadi Me kake son Fadi...? Kai Tsaye Haddir yace"Kafini sani..Ina Zargin kun koma Ruwa Kaida Ita kuma Faruwar hakan kamar Barazana ne ga Zubewar mutumcinmu Da naka gabadaya.."Da sauri Zain ya Tareshi Yana Fadin"Tsaya mallam kasan kuwa Zaton Zina... ? Ko kutu akaje Sai ka kawo Sheda Hudu suma sai sun ganin ma Idanuwansu Turmi da Tabarya kana da wannan Shedar ne..?Mganarka kawai kake wanda kuma Ra"ayinka ka Fada mallam Ni babu komai Tsakanina da ita sai na abokiyar aikina ce Fakat.." Ya karishe Fada Cikin Son Nuna Bakomai Haddir yace"Hmm koma miye kai ka sani Nidai ina Fadamaka nan ba London bane Bauchi ne Wlh Zain ina Jiye maka wani Tsoro ka dawo Cikin Hayyacinka Nidai nagaya maka Tuni nace ka sallami yarinyar nan Ta kama gabanta Ammh kaki In banda kana da Manufa miye na gayyato ta nan Tayi aiki Damu..? In gaya maka ina jiye maka Mtsala Ne..' Karamin Tsaki Zain yaja yana Fadin"Zato Zunubi Dai koda ya kasance Gaskiya ne..Kuma Hadisi ne guda Ka Rika kyautatama Dan"uwanka Musulmi Zato.."Daga haka ya wuce Ya bar Haddir nan Tsaye yana Binsa da kallon Tsausayi kuma Har acikin Ransa ya yarda da Zarginsa akan Zain ganin yadda yayi wani Wiki Wiki Dashi kada kai kawai yayi ya Bude Murfin Motansa ya Shiga acikin Ransa yana yima Zain Fatan Shiriya Zain kuwa har ya isa Office dinsa yana Juya Mganar Haddir Tabbas yasan gaskiya yake Fadamai ammh Taya zai iya yakice Dina..? Yayi iya bakin Kokarinsa wajen ganin ta bar Rayuwarsa ammh Abu ya gagara Shi kanshi yana Tsoron Wani abu ya Faru ya Tabbata Cikin Ahalinsa ba wanda zai mai Uzuri uwa uba kuma Zainarsa da wani ido zai Kalleta..? Haka ya wuni Sukuku kamar mara lafiya La"asar ya bar Cikin asibitin zuwa Gida Yaje yayi wanka ya kwanta yana ganin Kiran Dina yaki Dagawa sai ma ya Lalubi Zareena yace ta bama Umma wayar,bayan an bata sun gaisa ya Fara Complain din cewa Matarsa yaushe zata Dawo Umma tace suna Tafe Dole ya Hakura ya maida Wukar ammh Shi kanshi yasan yana Bukatar Matarsa ta Dawo Hakan nan Tunda Sukayi aure Bai Taba bari Taje wani Waje ta kwana Fiye da Biyu ba Shiyasa yake Jinsa Wani Iri. Ranar asabar su Umma suka Dawo Ta lagos suka Sauka nan Suka kara kwana Washegari Umma da Halima suka Bi Jirgi zuwa Bauchi Ita kuma Zafeera ta Hau Jirgi zuwa kano Taso Binsu Umma zuwa Bauchi Gabatowar Test dinsu yasa ta hakura ta koma kano sai sun samu Hutu,Zain bai ma san Ranar zasu dawo ba sai da ya Dawo Daga asibiti yaji Gida na Tashin kamshi,sai ga Zainarsa tazo ta Rumgumeshi Tana Murnan ganinsa Shima kamkameta yayi Yana Bayyana mata yadda yayi kewarta Ranar dai kwana sukayi Suna Bayyana ma Juna yadda Sukayi kewar Juna. Washegari kuma Monday ta koma makaranta Ranar kuma suka Fara Test ba zama Sai Hankalinta Duk ya koma kan karatunta Tunda Suna Tun karar Exams Din Second Semister ne,Don ma Allah ya Taimaketa Laila tayi mata Wasu Assigment din Da Data samu Gibi da yawa ba kadan ba. ***** Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai adade ba"a je ba Gashi Har Su Halima Sun kamallah Test dinsu na makranta Haka ma Su Zafeera,Shiryen Shiryen Fara Jarabawa suke yi nan da Sati Daya Gabadaya Hankalin Halima ya koma kan Makaranta da karatu bata ma samun Lokacin kanta hatta Gidan Umma da Gidan Alhaji tsoho Sai Ranar Sati Take samun Zuwa Saboda karatun Jarabawa bata da wata Natsuwa. In Ta Shiga Cikin makaranta sai yammah Take Dawowa Suna Chan Libarary ita da Laila da Sauran mates Dinsu Suna karatu,Hakama in ta Dawo Gida Zata Dukufa Sallah kadai ke Tashinta,Sai kuma wani aikin Daya Shafi Mijinta Shi kanshi Zain Din Tsausayamata yake yanzu ganin Ta saka Karatu acikin Ranta Sosai Shiyasa Girki ma sai Weekend take yi Musu Sai Breakfast kafin su Fita daSafe Da Rana kowa Wani Abu yake nema yaci Da Daddare kuma Kafin Zain ya Shigo Gida yake Biyawa wani Restaurant yayo musu Takeway suci Su kwanta Wani Lokacin Har sai ya kwanta ita bata kwanta ba Tana Falo Tana karatu Har sai ya Farka ne in ya Laluba yaga bata sai ya Fito Falo ya Tattara ta zuwa Ciki Toilet yake Turata Yayi mata wanka Wani Lokacin ma abinci sai ya Zaunar da ita ya bata take iya ci Ta Riga ta saba Da Abinci Shi yake Ciyar da ita da kansa Shiyasa Dagashi Har ita In Kowanne ya Tafi Laluransa Da Rana ba wani Abincin Kirki Suke zama su Ciki ba Saboda sun Riga sun Saba Da Ciyar da junansu. Bangaran Dina kuwa Ta Yarda da plan din Da Zakiya ta kawo mata Duk da Tana Tsoron Zubewar Mutuncin Mahaifinta ammh Zakiya ta Nuna mata Daga Mahaifinta har iyayen Shi Zain din bazasu zo mganar ta Fasu Waje Ba Tunda Dukkansu Suna da kima a idon Mutane zasuyi Abunda zai zama Rufun Asirinsu ne kuma Shine Aure Tsakaninta da Zain,Ta yarda da Shawaranta Sosai Shiyasa Ta Kudura acikin Ranta Six Month Din Datayi Alluran Planing Din Datayi yana karewa Bazata karayi ba In Allah ya Taimaketa Tsarinsu ya Tafi Daidai kamar yadda Suka Tsara,Acikin Zuciyarta Batason Faruwar hakan ammh ya zama Dole ne Tunda Tana son Son Zain kuma Tana Son Kasancewa Tare Dashi Har Abada Har yau har gobe In Tayi mai mganar Aure sai ya kara Maimaita mata bazai Taba Auranta ba Tunda bai Taba Cewa yana Sonta ba ya gayamata ba tun yau ba Mace Dayace Matarsa itace Zaina bazai iya Auran wata mace ba bayan Ita da irin Wadanan kalaman yasa Ran Dina ya kara Baci Batare da wani Dogon Tunani ba ta amince da Shawaran Zakiya ammh Bayan ta sun kara zuwa Wajen Bokan Zakiya na Hanyar kaduna Daman Zakiya ta kaita wajensa Shi yake mata aiki kan Alhazanta ta samu alheri akansu Yake kuma mata aiki in Taga wani Alhaji mai kudi a Tsaida mata Shi ta wanki Rabonta Da suka je mai da Bukatarsu ya Buga kasa yace musu in Sukayi Haka Auran nasu zai Tabbata sai dai yaga Duhu sosai acikin al"amarin Kamar yadda yagaya musu a Farko Suka ce bakomai Kowani Duhu suna Maraba Dashi Sun karamai Zubemai kudi kan ya kara Sakama Zain Din Fitinaniyar Sha"awar Dina Wanda bazai iya kwana bai Kusanceta ba Ko zasu samu Hakkansu ya cimma Ruwa yace karsu Damu anyi an gaba su Jira sakamako kawai Sai Dina tana Koran Zain ammh yana manne mata kamar wani Tsohon Maye mara Zuciya. Cikin Ikon Allah su Halima suka Fara Zana Jarabawar Karshen Zangon karatunsu na aji Daya,Chan ma Kano Zafeera suma sun Fara,Duk wani Masoyansu yana Tayasu ga Addu"an Fatan Nasara da Sa"a,Sannu sannu kamar yau suka Fara sai gashi Sun kamallah Zafeera sun Riga Halima gamawa a kuma Ranar bata kwana agarin Kano ba Sai Bauchi sai dai su Umma suka ganta Kwatsam Murna wajen su Zainab ba"a mgana Ita Tana gida Ta Rubuta jamb sai Farkon zango karatu Zata Fara zuwa makaranta itama Din ATBU bauchi Abba yace Zatayi bayason Tayi Nisa da Gida,Su Halima kuwa sai Da su Zafeera suka gama da kwana Uku kana suna Suka gama Farinciki Kamar me bakinta yaki Rufuwa,Sai da ta kai Laila Gida kana ta Wuto Gidan Umma Direct Daman Tunda Zafeera ta Dawo basu Hadu ba aikuwa tana Zuwa Suka Rumgume Juna Suna Murna kamar Wasu yara kananan Umma na Dariyan Farinciki Tana Fadin suyi a Hankali Nene kuma na Fadin Yaranki Umma basu Girma sai na Jikinsu. Bayan gaishe gaishe Dakin su Tun na yamatanci Suka Kule Ciki Inda yake matsayin nasu Har yanzu Tunda Zafeera batayi Aure ba,In tazo Hutu nan take Sauka Itama Halimar nan take wasu Abubuwan nata in tazo Ko Dakin Umma ko Dakin Nene Duka Basu da Shamaki da Dakunan Iyayen nasu. Hira ce ta Barke Tsakaninsu Cikin Hiran ne Zafeera ta kalli Halima Tana Fadin"Wai Ukti ba wani Bayani ne..?kusan fa Shekara kadan bashi a auranku keda Yaya Dakta..! Halima Ta gyara zama Tana Fadin"Bayanin me kuma Ukti..? Zafeera tace"Dillah na Haihuwa nake mgana Tun ina kano nake so nayi Miki Tadin munji Shuru ba wani Bayani me Dadi ko matar Likita Tana planing ne..? Halima Ta Daka mata Duka a Cinya Tana Fadin"Uwar planning Din kema kin zama Hajiya mama ko..? Haka wanchan Satin da muke je gaishesu ni da Firstlove take mana Fadan wai ko muna Tsarin Iyali ne Sa"o"in Auran mu Duk sun Haihu Har fa Tsohon can yana mana Nasihan Muji Tsoron Allah.."Zafeera tace"Wlh da gaskiyansu...Yadda Alhaji Tsoho ke Bala"in kaunarku keda Yaya Dakta Zai zo Ganin Ya"yanku kafin ya bar Duniya..' Tagumi Halima Tayi Tana Fadin"Wlh Nima ina so Ukti...Allah ne bai kawo ba Kinsan Allah ban taba Shan kowani kwaya ba kuma ban Taba Allura ba Firstlove ma baazai bari ba kinsani.."Zafeera Tace"To wani Taimako kuka nema..? Ta Sauke Tagumin ta Tana Fadin"Wani Taimako kuwa Kwanaki Dana Fara mai mganar sai ya Fara min Fada yaushe Duka Duka mukayi Auran Ballatana ace bamu Haihu ba..shi bayason Irin Haka Haihuwa Lokaci ne, in Lokacinta yayi Komai zai Wuce Daga Lokacin yace na bar mganar Babu Komai Dukkanmu lafiyanmu Lau Tunda Daga kowani Bangaran mun gaji Haihuwa.." Zafeera Na Dariya tace"Kuma fa Hakane mganarsa...In Lokacinta yayi Burum zamu ji Ukti na Faman Laulayin Ciki ana Tsirtar da yawu.."Ta fada tana wani yamutsa Fuska Duka Halima ta kaimata Ta Goce Tana Fadin"Kefa Ukti Saurin Hannu ne Dake ga Zafin Hannu Wani Lokacin.."Dariya Halima Tayi Tana Fadin"Kema din kwana nawa ne..? Alhaji Tsoho zan Zuga nace ya Aura miki Barrister Ahmed ko baki sonshi Kina Kano Sai da kiji Sakon kin zama Amarya.."Ta karishe Fada Tana Dariya Fuska Zafeera ta bata Tana Fadin"Allah da ban Yafe Miki ba kuwa Ukti..Kinsan yadda Na Tsani Ahmed din nam kuwa..?Ko Sunansa aka ambata sai Raina ya baci.." Ta karishe Fada Tana Bayyana Bacin Ranta ga Mganar,Dafata Halima Tayi Tana Fadin"To wai Duk meyasa Ukti..? Yana da wata mtsala ce..? Zafeera tace"Ko Daya wlh in nace yana da Mtsala na Dauki Hakkinsa..Kawai dai bana Sonshi ne Shi kuma ya cika Takura Rayuwar nan fa ba"a Dole Ukti Tun Farkon Haduwata Dashi na gayamai ba yanzu Zanyi Aure ba sso na gama karatuna Ni Ra"ayina kenan da Farko kamar ya Rabu dani sai kuma ya Dawomin Tunda yayi Bincike ya gano Ni Diya nake Wajen Dadyn Abuja Shikenanan ya kama Bina Abunda yafi Bani Haushi Har da kawo kanshi Wajen Alhaji Tsoho Dan Shishhigi ko Uban wa ya aikoshi Bansani ba.." Ta karishe Fada tana wani Murguda baki Halima ta Saki Mirmishi Tana Fadin"Shikenan Tunda baki sonshi ammh ai Aure baya Hana Karatu Ukti..Bagashi ni nayi Auran ba kuma ina karatun nawa ba..? Zafeera tace"Ke Dabam ce..Daman Tun Tasowarki ke yar Gatace Miji gareki fa ahannu Tun kafin kizo Duniya Ukti Miji kuma na nuna ma Duniya Nima danasamu gatanki ai Tare zamu Shige Daga Cikn nan nima naji Abunda ake Ji.."Tafada Tana Daga mata Gira Irin Kin gane din nan Dariya Halima ta saka Tana Fadin"Allah Nima ina son Kiji Mazan nan Ukti Shiyasa nake so kiyi Auranki Tun yanzu ki Mori Kuruciyarki.." Zafeera tace"Allah ko Ukti..? Gira taDaga mata Tana Fadin"Ba"a Fadin Dayan Abun Ukti..."Hannu Ta bata suka kashe Lokaci Daya Suna saka Dariya,Nene ce ta Shigo Dakin Nasu Tana Fadin"Ku kuma yayan Umma me kuka samu ne kuke ta Dariya Harda Buga Shewa.." Zafeera ce tace"Nene Sirri ne.."Nene tace"Eh Sirrin a Fadamin naji.."Da Sauri Halima Tace"Kaji Nenen nan keda kike Shigewa Daki kina Kuskus da ya"yanki Kina gayamana ne..? Nene Tayi Dariya Tana Fadin"Abun na gori ne..Kwa ji Dashi Dai nasan Dai Tatsuniyar Gizo bata Wuce ta Koki..Muna zaune za"a zo agayamana.."Dariya suka saka mata ta Fice Tana Kiran Umma Tana Fadin Yayanta Sai Shewa suke Suna Dariya Duniya tayi Musu Dadi Umma tace Eh karfa a Takura ma Ya'yanta abarsu su Shakata Suna Daga Cikin Dakin su suna Jinsu sunayi Suna Dariya Hakika Rayuwar Gidan Abba Usman Rayuwace Abun Koyi ga Kowa baka isa ka Bambamce ya"yan Nene da ya"yan Umma ba sai wanda Daman yasan Komai Tun Fari. Nan Halima ta Kai yammah Da Taso Takai Dare Abba ya Dawo ya Kadata Gida Daman sunyi mgana Da Firstlove Lokacin yana asibiti yace in ya Tashi Daga asibiti zai Biyo sai su koma Tare Ta Share kafa kenan sai ga Abba ya Dawo ya Fattaketa Zafeera ma taso ta Bita Gidanta ta kwana Duka Abban ya Hana Yace zasu Shiririta ta bari zuwa Gobe sai Taje,Sai da ta koma Gida ta Kira ZAIN ta fadamai ta koma Gida Yaji Dadin hakan Domin yana Son ya Fara Biyawa ta Gidan Dina kafin ya Dawo Gida Domin yanzu Abun ya koma mai kamar wani Tsafi Duk da Tsafin ne,Baya iya Hakura da Kusantar Dina Kusan kowani Dare sai ya Biya ta Gidanta Sunyi watsewarsu kana yake komawa Gida Abun ya Fara Damunshi Saboda Ko Zainarsa yakan Daga mata kafa na kwana Daya ammh Dina yana jin a kullum in bai kusanceta ba kamar zai Mutu wani Lokaci Alokaci Daya sai suyi mayawa yafi Biyar Domin daya gama Kusantarta zai ji Sabuwar Sha"awarta ya kamashi,Da yasan Ba Haka yake ba ammh ya kasa gano Dalilin Hakan yayi Callaging Din Dina Ko mganin Mata take sha Tamai Rantsuwan bata shan komai,Ya yarda da ita,abunda yafi bashi Tsoro bayajin Haka akan Matarsa ta Sunna sai akam wata Karuwa Yana kuma da yakinin Wahala kawai yake bawai Don yana samun Wata gamsuwa ba Gamsuwa da Natsuwa awajen Zainarsa kadai yake samu Tuni yasan wannan Duk Nema neman matan Da yayi Lokacin suna London ba macen Datakai Dadin Zainarsa Ita Zainarsa Dabam kawai take,Abun yana Damunshi ammh Yarasa Wazai Fadama Matsalansa Ballatana ya Bashi Shawara Haddir ne kuma saboda Dina yanzu basu da wani Fahimta a tsakaninsu,Sakacin Zain Ya kasa ya gano Wani Abu Ballatana ya iya kai kukansa ga Allah Dina kuwa kakartace ta yanke Saka Wani Farinciki Take Fama Dashi na ganin Zain ya Fara zama nata Har Abada,Sau tari har Gwadashi Take in yazo ta nuna ita ta gaji ya tafi Wajen Zainarsa mana Tasan da abaya ne Bazai kara bi Ta kanta ba sai bayan wani Lokaci ammh Abun mamaki Haka zai zauna yana mata magiya kamar yayi Kuka Haka ta Kira Zakiya Tana bata labari suna Dariya Zakiya na kara gayamata aikin Bokan bana Wasa bane Sun Dade Tare kuma yana mata aiki Tana ganin Cigabansa nan da nan Dina ta yarda dashi 100%Alhalin da Da farko Bata yarda Da Harkan Bokaye ba Zakiya ma Fada suke kan hakan sai Gashi Dalilin Zain Komai nata yakara Tarbabarewa. Washegari kuwa Tun Safe Zafeera ta Shirya tatafi Gidan Yaya Dakta wajen Halima,Saboda Sammako ma Zain yana gida bai Fita ba Tazo Daya Fito ya ganta baki kawai ya Hangame kafin yace"Ikon Allah Wannan wani irin Sammako me kamar yaki..? Dariya Suka sakamai gabadaya Kafin Zafeeran ta gaisheshi Tare sukayi Breakfast suna Hira Sama sama kafin yayi wanka ya Shirya ya Fice zuwa asibiti,Bayan Fitarsa suka koma Falo Suna Hira cikin Hirar ne ma Halima ke gayama Zafeera sati mai Zuwa Zataje gada Tayi Sati Daya Saboda Bikin Dan Wajen Goggo Halima,Dakuma Duba Dangi Zafeera na jin Haka Ta Daka Tsalle tace sai Taje Halima tace Shikenan Daman Duk Zuwan Datake Tare da Zafeeran suke zuwa nan suka Wuni Tare Zafeeran ta Tayata tayi ma Abba da Alhaji Tsoho Tuwonsu Da Takwana Biyu Batayi musu ba saboda Makaranta Da suka gama komai suka sake wanka suka Shirya Halima ta Tukasu a Motarta Gidan Alhaji Tsoho suka Fara Zuwa suka kai mai Nashi yana ta ma Zafeera Tsiyam n Ta Dawo bata zo ta gaisheshi ba Hajiya Mama tace"Tana tsoron ka Tare ta Da Sakon ka mata Miji.." Zafeera najin Haka ta Hade Rai Tana Hararan Hajiya mama Alhaji Tsoho kuwa cewa yayi"Bam ma ya"yana Dole ba Amina itama Bazan mata Dole ba ammh In ta zabi Ahmed a matsayin Mijinta zanfi kowa Farinciki.."Zafeera najin Haka ta Sulale ta Gudu Gida sai da Zaina tasameta Gidan Umma tana mata Dariya nan takai Dare Sai Wajen 10 Zain yazo suka koma Tare Motarta agida ta Barta Daman wani Lokacin Tana barinta agida In takai Dare Saboda Zain ya hanata Driving Din Dare. Da kanta ta gayamai Tare da Zafeera zata tafi Gada yaji Dadin Haka Daman Da Farko yaso Su Tafi Tare ne ana gama baki ya Tattarata su dawo Sai kuma ga wannan Halin Dayake Ciki Ta yaya zai Tafi wani gari Batare da Dina ba..? Wanda Nisa da ita kamar barazan Rasa Numfashinsa ne a koma wani Hali ne Shidai sai ya Rab'i da Dina yake jin Dadi Daman yana Cikin Tunanin mafita sai gashi Tace da Zafeera zasu Tafi sai yaji Dadin Haka yace zai kaisu ya Dawo Allah barshi in an gama Biki Taga Dangi tayi Sati Daya sai yaje ya Daukosu ita kanta Haliman Tayi mamaki Zain bai taba barinta zuwa wani Waje Tunkafin suyi Aure ta wuce kwana Uku zai ce ta Dawo Gida ammh sai gashi bai Nuna wata Damuwa ba da Farko Kamar zatayi mai mgana sai kuma ta watsar da Tunanin da Cewa Kila ganin Tare da Zafeera zata tafi Shiyasa. Shi yayi musu Dukan wani Shirun Tafiya da Tsaraba da komai Duk da Abba ma dasu Umma sunyi iya nasu Kokarin,Tun Ranar alhamis Suka Tafi Zain din yakai su Umma da Nene da Abba sai Ranar Daurin Aure zasu Taho,Tun Safe suka Fita Wajen Azahar suna Gada Abinci kawai Zain yaci yayi sallah yadau Hanyar Komawa bayan ya Cika Goggo Halima da Kudi Gudumuwa Na wajen Abba kuma Su Halima suka bata harda na Wajen Alhaji Tsoho da Hajiya Mama Goggo Halima sai da tayi kuka Ta Tuna da yar"uwanta Maryama da Dalilinta ne take ci Har yanzu Tana ta kwaromusu Addu"a Tare da Addu"an Allah yajikan Maryama da Abdullahi sai da ta saka Halima da Zafeera kuka. Cikin kankanin Lokaci Su Zafeera suka saki jiki aka Shiga Sha"anin Biki,Daman su yan Gida ne Kowa yaga Halima sai ya kara kallonta tayi kiba ta Cika Ta kara kyau da Fari Dangin Babanta Dana Mamanta kuma Sam Barka suke da Ahalin Alhji Abubakar Saulawa Domin Bazasu manta Alherinshi Garesu ba. Ranar Asabar Daurin Aure Abba yazo Shi da Dadyn Abuja da Mama Safiya da Umma da Nene Umarnin Alhaji Tsoho kena  yace Shima ba Domin Laluran kafa sai yazo,Basu kwana ba Suka Jiya,Goggo Halima Taji Dadi kwarai Har bakim Mota ta Rakasu Tana ta Godiya Su Zafeera kuma sai da sukayi Sati Cur kana suka dawo Bayan Ta Raka Halima ta Zaga Gidajen Dangi da yan"uwa ko"ina taje sai anyi mganar Rashin Samun Cikita ayi ta cewa ko suna Tsarin Iyali ne, Tunda sune Abun Sai ta Rantse da Babu Abunda Sukeyi Direban Abba yazo ya Daukesu da zasu koma Abun yabama Halima mamaki Alhalin Jiya da Daddare sunyi mgana da Firstlove ya Tabbatar mata Shi zai zo ya maidosu ammh Kuma sai taga bashi bane kuma Tun Suna Hanya Take ta Kiran Wayarsa Baya Dagawa Tuni hankalinta ya Tashi Zuciyarta ta Fara Tsinkewa zafeera ma ne ke ta bata Baki Har suka iso Bauchi. *Sannunku da kokari ZAINAZAIN BAND 1&2...naga Sharhin ku Allah ya bar Zumunci..Yan Janaf Novella 1&2 ku kuma Kun kyauta Tabbas kun kusa daina ganin Update kan Zainazaina sai dai ku karantashi Chan Waje...* *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*            1️⃣2️⃣ "A lokacin da Zaina ke ta Kiran Zain yana gidan Dina suna ta Lalacewarsu da suka saba,Dama Tun safe yayi Shirin Tafiya Chan Gada ya Daukosu sai kuma ya samu Kiran gaggawa Daga asibiti an kawo Wata patient zata Haihu ammh kuma Kafar jaririn ne ke Turo kai Dr Aisha tayi iya bakin Kokarinta Abun ya Faskara sai anyi mata C.S Dinar ce ma ta Kirashi Ta gayamai wannan Dalilin ne yasa ya bar Tafiya Daganan shirya ya Tafi asibiti,Bayan yayi ma Matar C.s An Fitar da Abunda ke Cikinta ba Rai sai kuma ga Wani Case din makamanciyar irin Haka sai dai ita Biyu ne acikinta Daya ya Danne Daya ganin Zasu sake Shiga Theater Room ne yasa ya Daga waya ya Kira Nene yace Ta Tura Direban Abba ya Daukosu yana Busy ne Bayan Haka ma Asibitin Ranar ta Rikice Saboda akwai wasu yan Daurin Aure da zasu shigo Bauchi Suka samu Hatsari Yawanci Duk asibitin Aka Yo da masu Raunin,Su Dr Imran ke kula da wannan Barayin Bayan sun Fito Daga Tiyatar ne Dina ta Ribaceshi Ta Jashi Gidanta,Da Farko gida yaso ya koma yayi wanka ammh Ta Hillaceshi ya bar Motarsa Cikin asibiti ta Tukashi Zuwa Gidanta Chan suka Tube Ta Hillaceshi da Salonta suka Gama Tambadewarsu a Tiolet kafin Suyi Wanka su Fito Bayan sun Fito Tayi musu Girki Sukaci Ta kara Hillatanshi Suka koma Ruwa Tana Dariyan keta Domin Ita ta Saka wayarsa a Silent Saboda Bata so wani Abu ya Katse mata Jin Dadinta Abun Takaichi Dukkansu ba Wanda yayi Sallar azahar ita batayi ba kuma bata barsa yayi ba Shiyasa Halima keta Kiran Wayar nashi Baya Dagawa. Wajen Biyu na Rana Suka Iso Gidan Umma suka yada Zango da Tsaraban Gada Sukayi Sallah suka ci Abinci,Shuru Firstlove bai Kirata ba Hankalinta ya kara Tashi Tayi wani Sukuku da ita Zafeera ce ta Lura da Halin Data ke Ciki Ta Kalleta ganin ta da waya a Hannu Cikin Sigar Tambaya tace"Wai har yanzu bai Daga wayar ba...? Tafada Tana kallonta Kai ta gyada mata kafin Ta zabga Tagumi Tace"Wlh Ukti Hankalina ya Fara Tashi Anya Lafiya..? Zafeera bata samu Zarafin mgana ba sai ga Umma ta Fito Daga Dakinta ganin yadda Halima Tayi ne yasa ta zauna Gefenta Tana Fadin"Ya"yana meke faruwa ne..?nga kamar kuna cikin Damuwa ne..? Zafeera ce Tace"Ukti ne ke ta Kiran Ya Dakta Tun muna Hanya bai Daga ba yanzu ma Ta kara Kira Still bai Daga ba kuma bai Kira ba.."Takarishe Fada Cikin Sigar Damuwa tana kallon Zaina wacce ta Yi kamar ta Fashe da kuka,Kallonta Umma Tayi kafin Tace"Inaga aiki ne yamai yawa..Domin Shi ya Kira Nene da safe yace atura Direban Abbanku ya Taho Daku aiki yayi mai yawa a asibiti.."Da Sauri Zafeera Tace"Kinji ko Ukti Don Allah ki kwantar da Hankalinki Insha Allahu Komai Lafiya.." Umma ta Dafa kanta Tana Fadin"Karki Damu Ya'ta..yaron Nene yana lafiya kinji ko..? Kai ta Dagama Umma Lokaci Daya da Kwakulo Mirmishi Wanda iya Saman Fuskarta ne bai kai Zucci Domin Haka kurum Take jin Wani Tsinkewan Zuciya Hira suka Fara sama sama da Umma Sai kawai ta Fara Hamman karya Umma ta kalleta Tana Fadin"Barci.? Maza jeki kwanta kafin an juma ki wuce gida.."Daman Abunda Take so kenan Tatashi ta Shige Dakinsu ta Fada kan Gado Tana jin Zuciyarta na Rawa Wani iri Taji ba yadda ta saba ji In Firstlove ya Tafi asibiti ba. Lambar Ya Haddir ta Lalubo Ta Kirashi Shima sai da Ta katse kana ya Kirata bayan sun gaisa ta Tambayeshi Zain yace mata Bai sani ba gaskiya ammh Yana Tunanin bashi acikin Asibiti kamar ya Fita,Gabanta Taji ya Fadi ammh Bata bari ya gane ba Tamai sallama ta kashe Wayarta Tana Tunanin Ina Firstlove yaje Daya kasa Daga wayarta Ta Tabbata ko Duba Marasa lafiya yake in ta Kirashi yana Daga Wayarta In ya Shiga Tiyata ne kadai bata samunshi kamar Wasa wata Zuciyar tace mata toh in yana Tare da Wata ne fa..?kuma watan tafiki Matsayi da kima awajensa fa..? Wannan Tunanin yasa Taji ta Fara jin Jiri Tana Daga kwance,Kwallah ya Cika mata kwarmin Idanuwanta Cikin Wannan Halin Zafeera ta Shigo Ta sameta Ganinta a Haka yasa ta Zauna Gefenta Tana Fadin"Ukti Damuwar ne..? Ko zaki Shirya muje cikin asibitin ne muga ko lafiya..? Tashi Zaune Tayi Cikin Wata kasallaliyar murya tace"Ba bukata yanzu muka gama mgana da Ya Haddir ya Tambatarmin Firstlove baya Cikin asibiti ya fita.."Kallonta Zafeera Tayi kafin tace"Ikon Allah ina yaje .? Ko gida ya koma ne...? Zaina Ta Kada kai tana Fadin"Bansani ba Ukti..Bansani ba.." Tafada Lokaci Daya Hawaye na wanke mata Fuska Cikin Mamaki Zafeera tace"Lafiya..? Haba Ukti miye Abun kuka..? Kai   kawai ta yada Saman Cinyar Zafeera Tana Fadin"Bansani ba Ukti..Haka kurum naji Zuciyata na Zafi Wata kuma na Fadamin kila yana Tare da wata ne Ukti..! In ba wata ba taya Firstlove yake kin Daga wayata Ukti..? Tafada Hawaye suna Kara Kwaranyomata. Cikin Tsausayawa Zafeera ke Shafa Kanta Tana Fadin"Kina Tsammanin akwai wata mace Datafiki Daraja awajen Ya Dakta ne..?babu Ukti ke kadai ce ba baki da Na biyu Wlh kowa ma Shaida ce.."Tafada Tana Share mata Hawaye Mikewa Zaina tayi Tana Fadin"Hakane kila Ya tafi Waje ne Da ba'a san Daga waya ko.? Da sauri Zafeera Tace"Eh hakane mu barsa ahaka Ukti..zai kiraki da Zarar ya samu Sarari.." Da haka Zafeera tayi ta Lallashin Zaina tana bata baki har ta Sauko Hankalinta ya kwanta ta saki Jiki suka Cigaba da Hiransu,Har barci ya Dauketa Kana Zafeera ta Fita ta barta acikin Ranta kawai Tana Jin Tsausayin Zaina Ranar da Yaya Dakta yace zai kara Aure akwai Daru. Shi kuwa Zain sai wajen 3pm na Rana suka Dawo Cikin Asibiti suna Shigowa Suka Hade da Haddir wanda yamai kallo Daya ya kauda kai Shima Zain din Kai ya Daga sama yana wani Cin mgani,har sun Gotashi ya Daga murya yana Fadin"In ka gama Shashancin naka ka Kira Matarka ta Kirani tana Tambayarka tace Tayi ta Kiran wayarka baka Daga ba..' Daga haka ya wuce ya barsa nan jin Haka yasa gabansa ya Fadi Dina Dake gefensa ta kalleshi bata samu zarafin mgana ba ya wuceta da Sauri kamar zai Tashi Sama ya Shige Office dinsa ya Rufe kofa sai da yazauna kana ya Lalubo Wayarsa Missedcalls din Firstlove Wajen 14 Ido ya Zaro yana Rawan Jiki ya Bi bayan Kiran Nata sai da yayi kira wajen uku kafin yaji Zafeera ta Daga wayar nan take cemai Zaina tana barci,Zafeera ce Tace"Ina ka Shiga ne Yaya Dakta..? Ukti Da kuka ta kwanta Duk ta Damu..? Kai ya Dafe yana Fadin"Oh my God..Kuna gidan Umma ne..? Tace"Eh Tun dazu muka Dawo.."Daga haka kawai ya katse Kiran Ya tashi Da Sauri ya Lalubi key din Motarsa ya Fice Office Din Dr Aisha ya Shiga yace mata ta Duba Tiyata petient dinsu in basu Farka ba nan da 1hr ta kirashi Ta amsa da To Yana kokarin Fita Dina na Sawo kai Bai tsaya ma Kallonta ba ya wuce da Sauri kamar zai Tashi Sama Da kallon mamaki Hade Dana Kishi Ta bishi Dashi Domin Tana da Tabbancin Wajen Tsinanniyar matarsa Zashi In yaji Sunants yana Rawan Jiki kamar wata Uwarsa da Katon Tsaki ta rakashi kafin tace acikin Ranta"Lokacin ya kusa Zuwa..! Yana Fita Kai Tsaye Motarsa ya Shiga Sai GRA,koda ya Shigo Falon Da Umma yaci karo Sama sama ya gaisheta ta kalleshi Cikin mamakin ganin Hanzarinsa tace"Kai kuma lafiya.? Yana Tafiya zuwa Dakinsu Zafeera yace'Lafiya lau Umma Firstlove naciki ko..? Bata ma samu zarafin mgana ba ya tura kofa ya Shige Dakin,Umma ta Rakashi da wani kallo kamar baya Cikin Natsuwarsa Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin Ta gyara zamanta Daman Tashar Sunna Tv take kallo Kawai sai ta Cigaba da kallonta Nene kuma Tana Dakinta ta Dan kwanta Zainab kuma Bata nan Tana Kaduna Da Baban kaduna yazo Ta bishi Suka Tafi Tare su Saudart kuma suna Makaranta basu Dawo ba. Yana Turo Kofar Zafeera Ta Dago Tana kallonsa wacce ke Zaune gefen gado Tana Latse Latse Bisa Laptop dinta ganinsa yasa Ta Mike Tana gaisheshi Yana amsawa Hankalinsa na kan Zainarsa ganin Tana Barcinta cikin Salama Da Hannu yayi ma Zafeera alama da ta Fita ta bashi waje Mirmishin gefen baki tayi kawai ta Fice Dauke da System dinta aranta Tana Fadin ko bakace ba Dama Fita zanyi..' Tana Fita ta turomusu Kofar Shi kuma yana ganin Fitarta ya Duka ya Sabule Takalmin kafarsa ya hawo kan gadon ya Ciccibota ya Daurata kan Jikinsa ya Rumgumeta kam yana Sakin ajiyar Zuciya Gefe Daya kuma na Zuciyarsa Tayi wani Rauni Yana Tunanin Abunda yake yi baya Ma kansa da Zainarsa adalci,Ya rasa ya zai yi ya yakice Dina arayuwarsa Idanuwansa sun Sauya launi Kamar ya Fashe da kuka. Cikin Barci Take jin kamar an Rumgumeta Sama sama ta Fara Bude idanuwanta ta Saukeshi a kansa Yana Rumgume da ita kamar zai Tsaga Jikinsa ya maidata Cikin Muryan Barci Tace"Firstlove...' Jin Ta Kira Sunansa yasa ya Dagota Suna kallon Juna,Cikin Sanyin murya Zaina tace"Ina ka Shiga ka kyaleni ina ta Kiranka... ? Kara rumgumeta yayi yana Fadin"Bako ina Firstlove...ina asibiti ne Yau Mutane Biyu nayi Ma Fida Firstlove kema kinsan Haka kurum bazan kyaleki ba.."Ido ta Rausayar Tana Fadin"Na kira Ya Haddir yace min ka Fita Baka cikin asibiti..? Fuska ya Hade yana Fadin"Ki daina ma Kiransa in kin kirani baki Jini ba..Ba Bangaran mu Daya ba Kowa da Barayinsa Kinji ko..? Bazai san na Fita ba ko Ina nan ba,kawai zai yanke Hukunaci ne batare Daya sani ba..Ni ina Cikin asibiti ba inda naje.."Kokarin mikewa take zaune Yayi Saurin Rikota ya Zaunar da ita kan Ciyarsa yana Shafa Fuskarta kafin yace"Kun Dawo lafiya..? Ya kuka baro su Goggo halima..? Kai ta Lamgwabe saman Kirjinsa kafin tace"Duk suna lafiya..Kowa yace agaisheka."Kanta ya Shafa Lokaci Daya yana Zame mata Dan kwalin kanta Ya ci karo da Kitson shukun Da akayi mata achan Shafawa ya Farayi yana Fadin"Wow...Yayi kyau sosai Firstlove waya yi miki..? Kanta ta Dago Tana Fadin'Matar Junaidun Goggo Halima taminshi Jiya.."Kiss ya sakarma kan yana Fadin"Yayi kyau Dole zan Biya wannann kitson.."Ya Fada yana Kure ta ido Kirjinsa ta Shafa Tana Fadin"Miye naga ka Kureni da ido..? Kai Tsaye yace"Idanuwanki sun Tasa..kin yi kuka ko... ? Kara lafemai tayi Bisa Kirji Tana Fadin"ba kai bane..? Kuka nayi saboda Zuciyata tana ta Rayamin kana Tare da wata ne Shiyaasa ka Shareni.."Dam! Yaji mganar nata Cikin Rawan Jiki ya kara kamkameta yana Fadin"A"a Bana son wannan Tunanin Firstlove Taya ya Kike Tssmmanin zain dinki Wanda yafara Sonki Tun kina Cikin mahaifiyarki Taya kike Tsamanin zai kalli Wata mace Da sunan so..? A"a wannan ba Tunani bane karki kara Kinji Zainata.." Ya Fada yana Shafa bayanta Zuwa Kugunta,ita kuma Tana Shafa Kirjinsa Cikin wata irin murya tace"bazan kara ba..Haka Ukti ma tace...Na Tsorata ne ganin ina ta Kiranka baka Daga ba.."Dago kanta yayi yana Fadin"Kin manta Mijinki Likita ne..? Akwai Ceton Rayuwanka Jama"a awuyansa Wani Lokacin Zaki rika Jin haka Firstlove plz kimin afuwa kinji ko..? Na saka Zainata kuka.." Yafada yana Kokarin Hade bakinsu Waje Daya bata Mai gaddama ba ta Dago kanta suka Hade Lebensu Waje Daya Keyarta ya Riko ita kuma ta Riko Bayan Kansa tana Shafawa Cikin Wani Salo sun Dauki Dogon Lokaci suna Sumbatar juna kafin su saki bakin Juna kan Kirjinsa ta koma ta lafe tana Sakin ajiyar zuciya Lokaci Daya Tana Fadin"Firslove lalle nayi kewarka Har ina jin kamshin Bakinka ya Chanzamin..'" Yana jinta Tana Fadin Haka saboda ya kauda mata wannan Tunanin yasa ya Fara mata Wasu Abubuwan da bazata iya Jurrewa ba kawai sai ta bar mganar ta biyemai suna Farantama juna Rai da kuma nuna ma Juna yadda sukayi kewar Juna Ammh Tabbas yasani kamshin Man bakin Da Dina Ke yawan amfani Dashi ne,Domin ya Tuna koda suke Mota sai da ta kwakumeshi Ta sha Bakinsa tana Bala"in son Ta Tsotsi Bakinsa Shiyasa Zainarsa taji Kamshin Bakinsa nashi ya Sauya. Kan Kirjinta ya Yada kansa yana Sauke Numfashi,sama sama ita ma Numfashin take Saukewa Chan Cikin Shakakkiyar murya yake fadin"Firstlove muje gidanmu.Nan gidan yamin kadan na Nuna miki yadda nayi kewarki ba.."Yana Fada ya mikewa ya Fara Daura mata Dankwali ya Sauko Daga kan gadon ya mika mata Hannu ta kama ta Sauko,Gyalenta ya mika mata ta Yafa Shi kuma ya Dauki karamar akwatinta yana Fadin"Ina karamar Jakarki...?cikin Sanyin Murya tace"Yana Dakin Umma..' Gaba ya wuce yana Fadin"Muje Ki Dauka mu wuce gida ai nayi Kokari Sati Daya nayi ina Maraicin Rashinki Fistlove.."Tare suke Fita Falo ita ta wuce Dakin Umma ta Dauko Jakarta ta Fito Koda ta Fito har ma yakai Haraban Gidan Umma da Kalleta Tana Fadin"Sai anjuma Dota.Allah huta gajiya.." Ta amsa da Ameen,Zafeera kuma Harara ta watsa mata Tana Fadin"Naga wariyan launin Fata Cewa fa kikayi ni zan Rakaki gida ammh yanzu kinga Yaya Dakta kin juyamin baya.."Dariya Zaina Tayi Kafin Tayi mgana Umma ta Rigata da Fadin"Kinga yi Tafiyarki yana waje yana Jiranki kinsan Halin Yaron Nene Wutar Ciki..."Jin haka yasa ta Fice tana Fadin agaida Nene in ta tashi Zafeera ta Bita da kallon mamaki ganin ta saki kamar ba ita ba. Koda suka koma Gida Zain bai iya Daga ma Zaina kafa ba Sai ya ta Tabbatar da ya samu Natsuwa kana suka Shiga wanka Bayan sun Fito ne ya Shirya ya koma asibiti saboda ya samu Kiran Dr Aisha Ita kuma ta Zage ta Shiga Kitchen Domin Farantamana Mijinta Abun alfaharinta. ****** Kwanci Tashi babu Wuya awajen Allah gashi Har Su zaina sun cinye Hutunsu Dayake Hutun bamai yawa bane sosai iyaka Sati Hudu ne Ma"ana One Month kenan,Zafeera ma Tana ta Shirin komawa Ana gobe zata koma Tazo Gidan Zaina ta mata Wuni Tazo kenan ba Dadewa sai ga Laila itama ta iso Daman Tana Jin Labarin Ukti Zafeera wajen Zaina ammh bata Taba ganinta  ido da ido ba sai dai ahoto Itama Zafeera Tana Jin Labarin kawar Zaina ta makaranta Laila sai Ranar suka Hade nan fa sukayi ta shan Hira Suna Dariya Dukkansu Ukun Tare suka Shiga Kitchen sukayi Girki Sukaci,Zain bai dawo Da Wuri ba,sai wajen biyar na yammh Lokacin Laila ma na Shirin Tafiya ne,Yayi mamakin ganinsu bayan sun gaisa yana ta Musu Tsiyan ashe sune suka zo suka saka Firstlove dinsa yau kwata kwata ta manta Dashi,Laila na karewa Zafeera dai Sai Mirmishi Sanin Ko da suka Taso Kai da kai Tare da Zaina Yaya Dakta bai Cika sakar mata Fuska ba Shiyasa itama Take jan kankantar ta da matsayinta awajen Matarsa. Ciki ya Shiga Zainar ta Bishi Ta Taimakamai yayi wanka ya Sauya kaya Ta zubo mai abinci yaci kana ya sake Fita zuwa gidan Alhaji Tsoho,Domin yace ya kwana Biyu bai lekasa ba Daganan zai biya ya gaida Matan Abba Nene da Umma Bayan Fitansa ne laila Tayi ta ma Zaina Tsiyar ko sun samu karuwa ne Taga tayi wani Kiba ne Ta kara Cika kamar ba Ita ba Zafeera kuma Tana gefe Tana kare ma Zainar kallo Itama Tana Shaida Kibar Dataga Tayi ammh Tasan koma miye In Ta fasu zasuji. Kusan Tare da Laila da Zafeera suka Fita Zafeera da Motar Umma tazo sai ta Rage ma Laila Hanya Ta kaita Har gida kana ta Wuce Gida,Tana zuwa gida taci karo da Ya Haddir ya kawo Zainab Daga Kaduna yake ya je Gaida Maman Wani Abokinsa sai ya Biya shine Baban kaduna ya Hadosa da Zainab sama Sama suka gaisa da zafeera daman Ita bata cika sakarmai Fuska ba tace ya cika Girman kai yaya Dakta ya fishi Sakin Fuska shima kallon Wata mai Girma kai yake mata Shi kuma bata sanshi ba Haka yake yafi Zain Miskilanci da Shariya. ***** Misalin karfe 8:30pm na Dare Zakiya ne zaune kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Da suka yi Ma Falon Dina kwanya itama Dina Tana zaune kan kujeran Dake kallon Wacce Zakiyan ke kai Dukkansu kananan kofuna ne a Hannunsu cike da madaran Hollandian suna Sha Suna Taba Hira,Yau din zakiya ce takawo ma Dina Ziyara Shima din ba Dadewa zatayi ba wani Alhajinta take Jira zai zo Gidan Dina ya Dauketa. Sai da ta Hadiye Abunda ta kurba kana ta Tsurama Dina ido Tana Nazarartanta Ganin haka yasa Dina tace"Yane..?irin wannan kallo sai kace kin ga wani Tsohom kwartonki.."Dariya Zakiya ta saka kafin tace"Tsohon Kwarto ai ya gama aiki Dina...Rabani bana Harka da Duk Abunda ya zama Tsoho nafison Harkan da Abunda yake sabo ko banza zan Mori Quality dinsa kafin ya Tsufa.."Dukkansu Dariyar suka saka Cikin Nishadi kafin su Tsaigata Zakiya ce ta ijiye Kofin Dake Hannunta kan Center Table Din Dake Tsakiyar Falon Tana Fadin. "In lissafina ya cika Daidai mun Riga mun Dana Tarkonmu Tun 3weeks da suka gabata.."Tafada Tana kallon Dina Mikewa Dina Tayi Dauke da Kofin Hannunta Tana Fadin"Eh mana..Kin manta ke ma ai sabuwar alluran taki Satinta uku dana Rakaki akayi miki ko..? Zakiya tace"Hakane..Toh sai ki Dage ba Daga Kafa mu samu Zomon mu ya Shiga Tarko..In ya Shiga Duka Burikanki zasu zama gaskiya ayayinda Zaki mallaki Zain mallaka na Har Abada..' Kai Tsaye Dina Tace"in kuma plan din mu ya Kuskure fa..? Wani munafukin Mirmishi Zakiya ta saki kafin tace"Kin Rasa Zain har Abada Dina..In nace Har Abada ina Nufin har Abada bazaki Taba mallakansa a matsayin Miji ba kuma kila nan da Lokaci kadan ma Tarayyar Dake tsakaninku ta Wargaje gabadaya kedashi sai dai Hange Daga Nesa.."Ta karishe Fada Tana kallon Dina Ido Cikin Ido. "Bai isa ba..Bazai Taba yuyuba ya zama Dole na mallakesa ko yana so ko baya so.."ta fada Cikin zafin Rai dana zuciya Zakiya Ta mike tana Taku Daya Bayan Daya Zuwa ga Dina Lokaci Daya tana Dafa kadarta Tana Fadin"Shiyasa nace in baki son Hakan ta kasance sai kin dage sosai Kin kuma Danne wannan bakin Kishin acikin Ranki in ba Haka ba Duk sanda kikace zaki Rika bayyana Abunda ke Ranki Game da matarsa zaki lalatamana plan ne Domin zai gujeki kuma ni bana son Haka nafison ku kasance Tare har sai Hakanmu ya cimma Ruwa.." Tafada Tana kallon Dina wacce ta sadda kansa Tana wani Tunani kafin ta Dago Tana Sakin ajiyar rai lokaci Daya Tana Fadin"zan yi kokarina..Ammh Wlh baki ji yadda na Tsani Diyar megadin nan ba in ya ambaci Firstlove ji nake kamar naje gidanta na Burma mata wuka in kuma ya ambaci Zainarsa din nan kamar na Kashe kaina nake ji.."Zakiya ta Kara Dora Hannunta saman kafadarta ta Hannun Hagu ta Girgiza da karfi Tana Fadin"Ki Daure kada ki lalatamana plan Dina na gayamiki.." Dina tace"Insha Allahu muke da Nasara..."Zakiya tace"Ina saka Ran haka..."Ta fada tana wani Mele baki Kallonta Dina Tayi Tana Fadin"in plan din mu ya Tafi Daidai me kike ganin zai Biyo Baya..? Sakin Kafadunta Zakiya tayi kafin Ta Sheke da wata Dariya irin na mugunta sai da tayi ya isheta kana ta Dakata Tana Fadin"Ke yanzu baki Hasoso mezai Faru gaba ba..? Ta fada Tana kallon Dina wacce ta sakar mata ido Tana kallonta lokaci Daya Tana girgixa mata kai alaman Bata sani ba Cikin Tafa Hannu Zakiya take Fadin"Ya kamata ki Hasaso wani Abu mana Dina Har kin manta Tare Dani DaKe muka biya kudi muka samu Labarin Tarihin Zain Tundaga Tushe..?ashe har kin manta..? Da Sauri Dina Tace"Ban manta wannan ba meyasa kika ce haka awannan gabar..? Zakiya tace"Dalilai Da Dama mana..Bala"i ne zai Faru Lokacin da muka Fasa kwan...Za"ayi Kitimurmura fa,Ahali zasu Girgiza fa Kimarsu zata Raunana ba kadan ba,kinga wannan Matar nashi Dayake ji da ita kamar ransa..?hmm wannan Firstlove din da Zaina na zain ko.? Duka zasu kare Plan din mu zai saka Soyayyarasa ta Rikide ta koma Tsantasan Tsanarsa acikin Ranta Yan"uwansa da iyayensa zasu Daina yarda dashi kilama har Iyayensa Su kama Fushi Dashi Fushi mai Muni ma kuwa,..!" Ta karishe Fada tana wani kallon Sama kamar tana ganin Abun na Faruwa agabanta ne. Dina ta saki Mirmishi Tana Fadin"Naji Duk wannan ta ina nawa Burin zai cika..? Zakiya ta Dago kanta Tana kallon Dina Ido Cikin Ido kafin tace"Ta wannan Hanyar...Karki manta Sunan Kakansa Dr.Abubakar Bashir Usman Saulawa ya zaga garin Bauchi dama kewayanta Wajen Kimarsa da Dattakonsa da Son Talakawansa Na Biyu kuma Mutum ne mai Daraja wanda Al"umma ke ganin Darajansa Karki manta mai bamu labarin ya gayamana Duk Cikin Jikokinsa yafi son Zain da Haddir kuma yana kimantasu acikin Idanuwansa ya kike ganin in wannan Labarin ya Sameshi Da Shaida mai karfi..? Zai so wannan kimar nashi ta Zube..? Bazai Taba yarda ya Rasa Dattakonsa ba Dole mafita Daya ne Zasu bi koda Zain din yana so ko baya so Saboda Lokacin ba Mganarsa za"a Tsaya Saurara ba Domin bashi da wata Kima alokacin..' Kai tsaye Dina Tace"Wata mafita ce..? Ta fada tana Kallon Zakiya da neman karin Bayani ta Bude baki zata yi mgana kenan Wayarta dake Cikin karamar Jakarta ta Dauki Kiran Neman agaji Hannu ta kada mata Tana Fadin"Kin cinye lokacinki Alhajina ya iso.."Tafada tana Karisawa kusa da Jakar nata ta Dauka ta Zageta ta Dauko Wayar nata Har Kiran ya katse Tana ganin mai Kiran Ta Dago Tana kallon Dina Wacce ta Sakar mata Ido Tana Jiran amsanta Dariya ta saka Tana Fadin"Sorry kawata Lokacinki ya kare...Ammh ki bani Bashi zan baki amsa in muka Hadu.." Bata bari Dina ta samu Zarafin mgana ba ta kama Hanyar barin Falon Daidai Lokacin Da wayarta ta Sake daukan Neman agaji Ta Daga Ta kara akunne lokaci Daya ta waigo Tana kallon Dina Tana Fadin"Zan bar Motata awajenki Zan dawo na Dauka..." Daga haka ta Bude kofa ta Fice Cikin yanga da Takun Yanmatan Zamani Wadanda suka san kan Duniya Dina Ta rakata da kallo mai kama da Takaichi kafin ta koma kan kujera ta zauna Tana Dafe kanta. ****** Washegari iyalan Dr.Saulawa suka Tashi da alhinin Rashin Lafiya Alhaji Tsoho Wanda Mura da Zazzabi ya Sarkeshi Cikin Dare Numfashinsa ma baya Fita sama sama kamar zai Sheka Dalilin haka yasa Haddir Da Hajiya Mama suka Rankaya Dashi Zuwa Asibitin Dayake mallakinsa Wato Saulawa specialist Hop,wajen Misalin uku na Dare,Dr.Imran Haddir ya Kira Tunda Shi ke kusa da asibitin Kafin su iso ya iso Cikin asibitin Tare dashi Da Dr.Peter suka bashi Taimakon gaggawa Har Numfashinsa ya Dawo ya Daidaita ashe majina ce ta Tushemai Kirji yasa baya iya Numfashi,Duk da Dare ne alokacin ammmh akwai Nurses masu Duty din Dare suna ta kai da kawo ganin Dr.Saulawa da kansa aka kawo ba lafiya. Daki na Mussaman aka kaishi Wanda Dama Dakunan na Family ne in wata mtasala ta Faru,Sai wajen asuba kana Haddir ya samu natsuwa ganin Alhaji ya samu Barci Hajiya mama Tasha kuka Haddir nata Mata Tsiyan Shima kanshi ya Shiga Rudu nan ya barta ta Shiga Toilet ta Dauro alwala Domin ana ta Kiran Sallar asuba Shima Fita yayi zuwa masallacin Cikin asibitin Yayi alwala yayi Sallah sai da aka idar kana ya Tuna da Abba da Sauri ya Fito da waya ya Kirashi ya gayamai Abunda ke Faruwa Hankalinsa ya Tashi Dama lokacin Dawowarsa masalaci kenan Su Nene suna tsaye Sun Firfito Jin Salatinsa sai da Ya gama wayar kana yake gaya musu Suma Duk Sun Rude sanin sudai Basu Taba ganin Alhaji Tsoho yayi ciwon Daya kwantar Dashi Haka ba. Kafin wayewar gari Labarin Ciwon Alhaji Tsoho yakai kunnan Duka ya"yansa Dalilin Dayasa Zafeera ta Fasa Tafiya kenan Zain ma yana Gida Nene ta Kirashi ta Shaidamai Hankali Tashe Shida Zainarsa suka Nufi asibitin,Hakama Abba Da su Umma da Nene da Zainab da Zafeera su Saudat suna makaranta Kafin karfe goman Safe Hatta Baban Kaduna da Dadyn Abuja sun iso Inna Rukayyah ce ta Kira tace tana Hanya Inna Hannatu kuma ta biyo Jirgi Itama Duka Hankalinsu ya Tashi Lokaci Daya Hatta su Zareena Dake Kasar U.S Haddir ya Kira Jawaad ya Fadamai sai Kira Zareena take tana Tambayan Jikin na Alhaji Tsoho. Dina Bata sani ba sai da Ta Shigo Cikin Asibitin Taga yadda Asibitin ya Cika ga yalwar Motoci a parking Space,Ta faka Motarta kenan tana Shirin Fitowa Misalin 12pm na Rana sai ga Motar Haddir ta Shigo Cikin Asibitin Inda ya Dauko Inma Hannatu Daga Filin Jirgi ita da Autarta Maryama,Agaban idon Dina suka Firfito Daga Motan zuwa Cikin asibitin Gabanta ya Fadi Domin Taga Tsantsan kama da Zain din akan Fuskar matar sai ta Fara Tunanim ko mahaifiyarsa ne..? Cikin asibitin ta Shiga sai kuwa suka ci karo da Dr Aisha ita ta Tambaya take Fadamata Mai asibitin aka kawo ba lafiya Kakan Zain da Haddir Dr Saulawa Ido Dina ta kwalalo Tana Fadin"Kai don Allah Tun yaushe..? Dr Aisha tace"Tun Cikin Dare..Su Dr Imran sukayi Attempting Dinsa ammh yanzu da Sauki Tun safe Jikokinsa da ya"yansa suka Cika asbitin nan.."Dina tace"Allah sarki Allah bashi lafiya.."Dr Aisha tace Ameen harzata wuce Dr Aisha tace Mata"Ki shiga ki Dubashi mana Yana Family Side Dinsu.."Kai kawai Dina ta kada mata Jikinta asanyaye ta wuce Office dinta tana Jin wani Sanyin Jiki Taya zata Hadu da Ahalin Zain bayan kuma suna kam Shirya wani Abu..? Haka ta isa office dinta sukuku har ta zauna bata da Natsuwa patient din ma sama sama take Dubasu Duka duka goma ta Duba ta kira wata Nurse tace ta kwashe Sauran Folder din ta kaima Dr Aisha batajin Dadin Jikinta ita kuma ta maida kanta ta jingina da kujera ta Dauko Wayarta ta Doka ma Zakiya Kira Don Ta bata mafita. *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*              1️⃣3️⃣ "Koda ta Kira Zakiya ta gayamata Abunda ke Faruwa karamar Dariya Zakiya tayi kafin Tace"Sai me..? Kema Dangin ki ne nan da Lokaci kadan zaki zama Daya Daga Cikinsu So ya kamata ku Hadu Duk yana Cikin plan dinmu ne..! Dina Ta saki Numfashi Tana Fadin"Zan iya kuwa Zakiya..?ina jin wani iri zuciyata tana Rawa Taya zan Fara Tunkararsu yanzu..? Zakiya tace"Karki Damu ki Jira zuwa nan da 3pm zan tashi Daga office zan biyo nan asibitin zan Rakaki sai muje mu gaida inlaws dinki.."Ta karishe Fada Cikin Dariyan Shakiyanci kashe wayarta kawai Dina tayi tana maida Numfashi Har acikin Ranta tana jin Wani iri bayan Haddir da Zaina adagin Zain bata taba Haduwa da kowa ba Zuciyarta na Rawa Tun yanzu kafin ma su san Ita din Wacece a wajen Zain. Haka kuwa akayi Misalin 3pm na Rana sai ga Zakiya tazo Cikin Asibitin Lokacin Har Dina ta koma Gida tayi wanka ta Sauya Shiga Zuwa Wata Abaya mai Ruwan Coffea,Ta yane kanta da Vail din Abayan wacce ta Bayyana Suran Jikinta,Kafarta sanye Cikin Wani Damdamalin Takalmi Fuskarta ba kwalliya ammh Sanin Dina mai kyau ce ko Batayi kwalliya ba kyanta yana Haskawa Ita kuma Zakiya Doguwar Atamfa ce ke jikinta wacce ta kamata sosai Daga mazaunanta,Kanta ba Dankwali Sai da ta yafa wani Vail a Kanta zuwa Saman Kafadarta Takalmin kafarta ma mai Tsini Ne sai wani Glass Data Toshe Fuskarta,Hannunta Dauke Da karamar Jaka lokaci Daya kuma Tana Kada key din Motarta akallon Farko in kayi musu sai ka kara Domin Sun amsa Sunansu na Mata masu aji da Baiwar iya Taku da isa da kuma Haiba Iya Sarrafa Jikinsu. Zakiya Tayi ta kara ma Dina karfin Gwiwa Tunda ita ta Sare,kuma ganin Kowa nata zuwa gaishe da Alhaji Tsohon zakiya ta nuna mata in bataje Ba, Zain bazai ji Dadi ba Da wadanan kalaman Ta kara jan Ra"ayinta Ta jata suka Nufi Family Side na Cikin Asibitin. Duk wanda ke asibitin Dr.Saulawa ya san da wannan Shashin,Shashi ne wanda Dr.Saulawa tun yana da karfinsa yasa aka samar Dashi Saboda iyalansa da yan"uwa da abokan arzuka nan ake Attempting Dinsu har su samu lafiya Shashi ne mai matukar Girma da kawatuwa,Koda yaushe Cikin Gyarashi ake da Sauyamai Fasali,Duka iyalansa ba Wanda bai da Fayel acikin asibitin Saboda Halin Rayuwa Dr.Saulawa da kansa yayi ma Shashin Lakabi da Fanmiy Side. Daki na Mussmman Mai dan Girma ne Alhaji Tsohon ke Ciki Kofar tana Rufe ne ammh Kana jin Hayaniyar mutane kadan Kadan Daga Ciki Zakiya ce tayi Knooking Din kofar kafin ta Tura ta Fara Shiga da karamar Sallama Hannunta jaye da Hannun Dina Wacce Take jin Wani irin Faduwar gaba kamar ta arce ta gudu,Suna Shigowa Dakin Gabadaya kallo ya Dawo Garesu Sai da suka kariso Tsakiyar Dakin zakiya Taja ta Tsaya Itama Dinar sai ta Tsaya cak,wanda yaji kayan alfarma kamar ba asibiti ba kama Daga Cafet,Kayan kallo kujeru Da kuma Abun Sanyaya Daki A.C,Fridge, Sai gadon Mara lafiya Dake gefe chan Shima din Wani Tsararra ne,Wanda ba Daya yake da Sauran gadajen Dake Cikin Asibitin ba Daga gani na Musamman ne kamar yadda Barayin Ko Shashin yake na Musamman. Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba Usman Suna zaune kan kujeran Dake Gefe,Yayinda mai kallonsu kuma Mom Iklima da Mama Safiya sai Nene ke zaune akai,Daga gefe kuma kan Wata Farar kujera Inna Rukayyah ce zaune,Daga Saman Cafet din kuma Umma ce da Inna Hannatu,Daga saman Gadon da Alhaji Tsoho ke Kishigide Bayan an karamai Filo abayansa kuma Hajiya Mama ce ke zaune gefensa Itama Daga gefenta Zain ne zaune ya yada Kafadarsa Bisa Kafadarta Suna mgana kasa Kasa Daga Tsaye kuma Haddir ne Wanda ya coge Hankalinsa kaco kan yana kan Wayarsa ne,Daga tsakarwajen kuma ga manya manya kololi nan Baje na Abinci sai manya manya Ledoji na kayan Marmari,Daga yanayinsi zaka Fahimci Tabbas Ahalin ya Cika Ahali kuma Ahali ne na Girma Da Dattako. Da yin Sallamarsu Dama Wajen yayi Tsit duk da Farko Hira na Tashi Sama sama,Gabadaya ido Suka zuba musu suna kallonsu Sama sama da kasa Duk da Baki sun Ta shigowa wasu ba saninsu sukayi ba wasu Likitoci Asibitin ne wasu kuma Nurses ne da Sauran Harda ma"aikatan Asibitin Ba"a barsu abaya ba,ganin Sun Coke ne sun kasa karisowa yasa Inna Hannatu ta Washe bakinta mai Dauke da Hakorin makka Tana Musu Maraba sai Lokacin Dina ta iya Dago kanta ta Kare ma Jama"ar Dakin Kallo Daidai Lokacin da Zain ya Dago kansa Daga Kafadar Hajiya Mama suka Hada Ido Hudu Da Dina. Wani irin yanke gabansa yayi ya Fadi Lokaci Daya ya zaro Ido yana kallonta ita kuma sai ta lamgwabe mai kai ta wani Rausayar da idanuwanta,Zakiya ce ta Damke hannunta Lokaci Daya tana Sakin Mirmishi ganin Gabadaya idanuwansu yana kansu ne,Zain kuma da Sauri ya kauda kai yana kokarin Daidaita  Natsuwarsa Haddir ne ya Dago kansa ya Sauke su kan Su Dina da mamaki yake kare musu kallo bai samu Zarafin mgana ba Yaji Alhaji Tsoho Dake Kishingide Cikin Wata Farar Jallabiya Muryansa ta Dan Shake alamun Mura yace"Maraba sannunku da zuwa..Ke Hannatu ku basu Wajen zama mana.." Yafada yana kallon Inna Hannatu dake Zaune kasa,Bata mike ba illah kafanta Data jaye Tana Fadin"Ai maraban nake musu Alhaji Tsoho Sannun ku da zuwa ga waje ku zauna Duka iyayan naku sun zaune kujerun.." Tafada Tana yar Dariya Da Sauri Zakiya Tace"La bakomai..Dama munzo Duba mai Jiki ne.."Tafada tana jan Dina zuwa Gaban Gadon Alhaji Tsoho Cikin ladabi Ta Rankwafa ta gaisheshi da Alhaji Tsoho da Jiki ya amsa Ganin haka yasa itama Dina Tayi hakan ya amsa Cikin Sakin Fuska yana ta saka musu albarka Zain dai Gabadaya bai da Natsuwa Hajiya Mama dake gefensa Tace"Kai kuma lafiyarka sai Hada Zufa kake Kamar wanda yake jin kashi..! Tafada Tana kallonsa Dariya ta Kubcema Haddir ya saketa har yana Dukawa yana kallon Zain wanda ya Hade rai yana wani Hura Hanci Cikin Son Basarwa yace"Ina Ruwanki kedai ji da wannan Tsohon Mijin naki gawa taki Rami kawai.."Haddir sai Dariya yake Hajiya Mama na Tayashi Dina kuwa sai nacin kallonsa Take yaki yarda su Hada Ido Zakiya kuwa kowa awajen take karema kallo su Baban kaduna dai suna ma Hirnsu ne haka ma su Nene Gwara ma Inna Hannatu da Umma hankalinsu na kansu Suna Nazaratansu. Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Yau kuma Aminatu Keda Megidan naki ake jin kanku..? Haddir yayi Saurin Fadin"Tsoho Daman ai Megidan na Bugi ne..Nine kadai Megidan gaskiya.."Hararansa Hajiya mama tayi Lokaci Daya Tana maida Hankalinta kan Zain wanda ya Fito da wayarsa yana Dannawa ji yake kamar Ahalinsa sun san Abunda yake aikatawa Shiyasa ya kasa Sukuni Sai Hada Zufa yakeDafoshi Tayi Tana Fadin"Kaji Juyo gareni Megidana Zainullahi kyale Hadiru ni kam Bani son Shi baya Cefene."Saurin Ture hannunta yayi yana Fadin"Jeki na Sakeki..Ko ki koma wajen Tsohon Mijinki ko kuma ki koma Ma Haddir din."kwabe baki Tayi Tana Fadin"Au ni zaka watsa ma kasa a ido..? Fuska ya Hade yana Fadin"An watsan wa ya ja.."Yafada yana matsawa kusa da ita nesa kadan Haddir da Alhaji Tsoho suna ta musu Dariya Dina dai da Zakiya suna Tsaye suna kallon Tsabar Shakuwa Tsskanin Jikoki da kakaninsu,Alhaji Tsoho ne ya an kare dasu,Dasauri ya kallesu yana Fadin"Af..Kunga mun Sha"afa da Baki..Sannunnku an gode ko..? Ammh Daga ina kuke ne...? Yafada Cikin Muryan Tsufa Lokaci Daya yana gyara zaman Farin Gilashin Idonsa Zakiya ce ta Murmusa bata samu Zarafin mgana ba Haddir yace"Wannan  anan asibitin Take aiki...Wannan kuma ina jin kawarta ce Domin ba'anan take aiki ba"Yafada yana kallonsu Zakiya Tayi yake kafin Tace"Eh ni Kawarta ce.."Tafada tana wani kallon Haddir din Kasa kasa yana Lura da ita ammh sai ya basar da ita,Alhaji Tsoho yace"Allah Sarki Sannunku fa Nagode Allah yayi albarka.."Sukace Ameen Cikin Dattakonsa ya kallesu yana Fadin"Duk wanda yazo gaisheni Ko daga ina ne baya Tafiya sai na san Sunanshi ko Sunanta.! Zakiya ta Murmusa kafin Tace"ni Sunana Zakiya Nuhu Daga Jahar kano.."Tafada tana kallon Dina Wacce take nacin kallon Zain Shi kuma yaki kallonta Cikin Sadda kai Tace"Dina Gaddafi Sheerif Nima Daga Kano.."Alhaji Tsoho ya kalleta Sosai bama Shi kadai ba Hatta su Baban kaduna sai da suka Dago Suna kallonta kafin Alhaji Tsoho ya samu Zarafin mgana Baban Kaduna yace"Gaddafi Sheerif Dai da muka sani kwamishinan kudi na Jahar kano.." Haddir ne ya gyada kai yana Fadin"Shifa Baba..Diyarsa ce.."Baban kaduna da Daddyn Abuja suka Hada baki wajen Fadin "Ikon Allah.."Shiko Alhaji Tsoho Mirmishi yayi yana Fadin"Masha Allah..Sannunki naji Dadin yadda kika Dogara ga kanki ba wa mukamin Babanki ba kika Tsaya kikayi karatu Domin Taimakon Al"ummah Allah yayi albarka.."Kansu na kasa Suna amsawa Da Ameen Alhaji Tsoho ya sake kallon Dina yana Fadin"Ammh yata Baki da wani Suna ne..? Naji kince Sunanki Dina kuma a sanina Sunan Kiristoci ne wannan Sunan domin in bazan manta akwai wata wacce mukayi aiki da ita a asibitin Dana Fara aiki a Bongcuf,Itama Likitar kwakwalwa ce Sunanta Dr Dina itama.."Dariya ta kama su Umma da Inna Hannatu Hajiya Mama tayi karaf tace"Yo in ban da Abunka Alhaji Yanzu yandda zamanin nan ya lalace Sunan ma Da zakaji an saka bashi da wani Ma"ana ayi ta kwaikwayon Arna wajen saka Sunaye Allah dai ya kyauta kawai.."Haddir da Alhaji Tsoho Suka ce Ameen Dina kuwa sai Taji ta Muzanta Kallonsu Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Nagode kwarai Allah yayi albarka..! Zakiya ta Rankwafa Tana Fadin"Allah kara lafiya da Nisan kwana.."su Inna Hannatu suka amsa da Ameen Ameen juyawa sukayi suna ma su Nene sallama Mama Safiya ce kadai ta amsa Mom Ikilima kallon TaraSaura kwata tayi musu Tana Fadin"Kai Nene wadanan yan mata basu da kamun kai kalli Shigarsu.."Nene ta Tabe baki Tana Binsu da wani kallo Haka Kurum Taji basu Burgeta ba,Suna Gabda Fita Daga Dakin aka Turo Kofa aka Shigo Zainab ce kan gaba ita da Maryama Din Inna Hannatu,Dauke da manyan Kololi a Hannunsu,Sai Zafeera da Zaina da suka Shigo Daga Baya Zafeera na Rike da Filet da cokali ita kuma Zaina na Rike da Katon Jug,Dukkansu basu ma Lura dasu ba Zafeera har Tana bangazan kafadan Zakiya kuma ko ta waigo Saboda Hankalinta ya tafi kan iyayenta Dake Dakin ne,Zakiya ta Juyo Tana kare ma Zafeera kallo Cikin baki isa ba ita kuma Dina Zaina ta kura ma ido ganin ta ta kara Kiba da Haske Alhaji Tsoho ne ke ta Fadin"Maraba da Amaryata Halimatu Sa'adiya mai Hali Dubu...Maraba da Zafeeratu Farar mace alkyabban Mata maraba da Zainabu Abu mai Tagwayen Suna Maraba da Maryama Allahu Akbar Allah yasa Ki yi koyi da Hali Irin Maryama Uwar Rikon Haddir da Zanullahi da Zareena uwa Shakikaya wajen Halimatu Sa"adiya Allah ya mata Rahma Ita da Abdullahi Da Mallam Umaru da Atine Allah ya Hadamu a Aljannah Firdausi.."Ya karishe Fada Cikin Alhini Duka Dakin suka Hada baki Wajem Fadin "Ameen Ameen ya Allah...Allah ya Haskaka kabarinsu.! Gaban su Umma suka yada Kololin Gabansu suna gaida Iyayen Nasu Daddyn Abuja ne yace"Sa"adiya me kika Dafo ma Tsohon naki ne?ya fada yana kallon zaina dama Sa"adiya yake Kiranta da Shi,Baban Kaduna ne kan kirata Halimatu su Mom Iklima kuma Dukkansu Zaina ne,Tana Dariya Tace"La..Daddy Tuwon Semo nayi muku miyar Kubewa Bushashiya Dukkanku Domin nasan Duka iyayen nawa sun yi Gado Wajen Tsohon nan na kwance.."Ta karishe Fada Tana Dariya Suma Dariyan Suka saka Mama Safiya tace"kwarai..Duka gidajenmu Gidan Daura Tuwo ne..Allah dai ya karama Alhaji Tsoho Lafiya..! Suka amsa da Ameen gabadaya Alhaji Tsoho yace"Dama ai kyan ya"ya su gaji Tsohonsu...Kunga wannan Tuwon Shi ke kara Muku Lafiya da karfin gani ba Ciyen Ciyen kayan Turawan nan ba.."Zain yace."Hakane Tsoho...Ina mamakin zamowarka Likitan kwakwalwa Ba Likitan Sanin Mutum har hanji ba.."Dariya suka sakamai Gabadaya kafin Hajiya Mama tace"Ke ta kwacen Miji zuboma mijina Tuwon yaci yasha mgani Tun Dazu yaki cin komai yana Jiranki.."Tafada Tana Hararanta Dariya kawai tayi ta Duka ta Fara zubamai Tuwon Zafeera na Tayata Zain na Daga gefe ya Dago kansa yana Fadin"Kinga Firstlove Da kin Sakama Tsohon nan Zubomin Ina jin yunwa.."Haddir ya kallesa yana Fadin"Lalle ne ma.Su Abban fa..? Harara ya Zabgamai zai yi mgana kenan suka Hada ido Da Dina Dake tsaye har yanzu basu Tafi ba Ido yazaro yana kallonta ganin Haka yasa Zakiya Taja Hannun Dina suka Fice su kansu basu san meya Tsaidasu ba ammh Ahalin na Gidan Saulawa Abun kallo ne Suna Da Fahimta Da kuma Kaunar Juna basu samu Zarafin mgana ba sai da suka Dangana da Office din Dina Zakiya kafin ta zauna sai da taKwankwadi Ruwa kana ta koma tazauna Tana maida Numfashi Dina kuma Takaichi ne Fal acikin Ranta da kuma Kishin Zaina Daya yi mata katutu. Dina kuwa zama Tayi kan kujeran Dake kallon na Zakiya Tana Fadin"Tsohon nan ya Cika Tambaye Tambayen Tsiya..'Zakiya tayi Mirmishi Tana Fadin"Likitan kwakwalwa ne fa...Tsohon Daga gani Lokacin Da yake kan ganiyar kuruciyarsa anyi Jajirtattace.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya kafin ta Dora da Fadin"Baki mamakin yadda Shekarunsa sukaja Haka ba ammh kallesa Hutu da Jin Dadi Sun Boye tsufansa..? Dina Ta Tabe baki Tana Fadin"Ke ni bama Wannan ba..Wai kiji fa Cemin yayi Sunana irin na Kiristoci ne..? Da gaske ne sunana ba na Musulmai bane.'? Ta fada Tana kallon Zakiya Ido Cikin Ido Wacce ta saka Dariya Tana Fadin"ina zan sani.? Ammh Tunda kikaji ya Fada gaskiya ne..Sai kiyi Hakuri Tunda Babanki ya Riga Da ya saka miiki baki da yarda zakiyi kuma..! Baki Dina Ta Bude Tana Fadin"Bangane ba.? Zakiya Tace"dama ai bazaki gane ba....Ke wai wata yarinyan ce ta Bangajeni Da zata Shigo Din nan.? Baki Dina Ta Tabe Tana Fadin"Ina zamnsanta..Banga Fuskarta ba  Matarsa kadai na iya Ganewa Sai Haddir sai Shi kanshi zain din gabadaya Cikin Dakin Banda su ban son kowa ba..! Zakiya tace"Soon zaki sansu Kawata...Nadai san na kan gadon nan Kakanininsu ne,Sai kuma Mazan Dake gefe sukuma iyayansu ne,Kin manta an gayamana Ya"yansa Biyar uku Maza Biyu mata,Kana ina kyautata zaton bayan Matan ya"yansa akwai ya"yansa mata Biyu a wajen."Dina tayi Tagumi Tana Fadin"Hmmm..Kina Nufin Harda iyayen Zain awajen..!? Zakiya tace"eh mana Surukan ki na Wajen..Kilama sune Wadanda da zamu Tafi mukayi musu Sallama sukabi da kallon Wulakanci.."Dina ta waro Ido Tana Fadin"Topha..Kada fa hakan ya bata mana Shiri fa..? Mikewa Zakiya Tayi Tana Rataya Jakarta Lokaci Daya Tana Fadin"Basu isa ba....Ki kwantar da Hankali Wlh bazan Taba Natsuwa ba sai naga wannan aikin namu ya tafi Sussufull ba wata matsala.."Dina ta sakar mata ido kafin tace"Kin Tabbata..? Taku Zakiya ta Farayi gabanta Lokaci Daya Tana Dafa Kafadarta Tana Fadin"Kin manta da kudinki kika Biyamin nayi Rigisteration na Shiga Jami"a Lokacin da Babana ya nuna Aurar Dani zai yi..?ni kuma nace karatu zanyi na Tssayu ga Kafafuna..? Ko kin manta Kina London kin Sha Turomin da kudin Abinci Dana Makaranta Har sai da na Shiga Aji Uku na Fara Raba ma maza Jikina Suna Bani kudi..? Ta fada Tana kallon Dinar wacce tayi Mirmishi Tana Fadin"Ni na manta...Bakuma nasan kina Tuna Baya.."Dariya Zakiya Tayi Tana Fadin"Zaki iya mantawa ammh ni bazan Taba Manta wannan Alherin naki gareni ba Dina..Shiyasa nayi Miki alkawarin bazan Runtsa ba sai naga Kin mallaki Zain kamar yadda kike Buri..! Ke baki Hango Yadda Fuskokin wasu zai sauya Daga Farinciki Zuwa Bakin Ciki ba..? Na Tabbata zasu Girgiza in sukaji labarin Abunda Dansu mafi Soyuwa garesu yake aikatawa Wlh inda ace Nasan inda zan samo Wasu Daga Cikin yanmatan Dayayi Hulda Dasu Har dasu zamu Saka Cikin plan din mu sai dai Kash..Bai yarda yayi Hulda da Ira iranmu bane Shiyasa Daya gane baida wayau..' Dina ta Saki Numfashi Tana Fadin"Na samu Natsuwa yanzu..Yaushe plan dinmu zai Tabbata kuma Wa zamu Fara. Tunkara.? Zakiya tace"Karki Damu...Komai na Tsarashi Daki Daki zan zo Gidanki Da Daddare akwai aikin da zan sakaki kiyi mana Shima yana Daga Cikin plan dinmu...Ni na Wuce sai nazo.."Da kai Dina ta amsa Kafin Tace"Shikenan sai mun Hadu.'Juyawa kawai Zakiya tayi ta Fice Daga Office din Tana wani Takun Daya Bayan Daya Dina ta Bita da kallon Tabbatar da mganarta. Bangaran Su Zain kuwa Duka nan suka wuni Cikin asibitin sai Dare kana suka Watse Hajiya Mama aka bari da Haddir zasu kwana da Alhaji Tsoho,Inna Hamnatu da Inna Rukayyah da su Baban Kaduna da Matansu Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Daman nan suke sauka Iyalan Abba kuma suka Wuce Gida Zaina kuma da Zain suka ce Gidansu sai da safe kana suka Dawo yau ma Zaina ta Dafo Abinci Farar Shinkafa da Miyar Ganye mai Kifi,da aranar Alhaji Tsoho ya matsa zai koma gida Dakyar su Abba suka Lallabashi ya kara kwana Tun Safe kuma yace sai Gida Dole aka bashi Sallama suka Tattara Zuwa Gida Tunda yaji Sauki Muran ma Tayi Sauki Ta Sakeshi. Washegari Kuma Inna Rukayyah Ta koma ita da Zafeera Inna Hannatu dai sai da ta kara kwana ta Jira Megidanta yazo ya Duba Jikin Alhaji Tsoho suka koma Tare nan dai suka bar Maryama Gidan Abba Tunda Sa"anin suke da Zainab itama sai wannan Shekarar zata Shiga Jami"a suma su Baban kaduna Duk Aranar suka koma Gidajensu su da iyalansu ganin Jikin na Alhaji Tsoho yaji Sauki kuma ga Zain da Haddir suna Kokaron Kula dashi Shi da kanshi ma yace Kowannensu ya Dauki Iyalansa ya koma Bakin aikinsa Shi ya samu Lafiya da wannan suka samu Natsuwan Tafiya su ma Su Nene sai Ranar suka samu Natsuwa agida. ******** *Bayan wata Biyu..* Bayan Wata Biyu da kwanaki Tuni Zaina sun Dade da Komawa makaranta sun Fara karatu ba kama Hannun yaro Tunda yanzu Suna aji Biyu ne,Zafeera ma Tana kano Tana Cigaba da Karatunta sai dai suna Waya Lokaci bayan Lokaci da Zainar. Bangaran Dina da Zain kuwa Tana iya bakin Kokarinta Wajen bata ga wani Baraka ya Shiga Tsakaninsu ba,Duk domin don plan dinsu ya Tabbata ammh Har Zuwa wannan Lokacin Shuru ba wani Bayani mai Karfi Zakiya Ta kagara kullum Cikin Zuwa Take ko Kiran Waya Tana Tambayan Dina bataji Wani Chanji Daga jikinta ba Tace Mata ita dai bataji Komai ba Har ta Fara Tunanin ko Zain yana amfani da wani matakin kare kai ne Daga barayinsa Ita Dina Tace bata sani ba ammh kusan kullum Suna Tare da Juna ya cita ya kuma Koma yaci Matarsa kamar wani Bunsuru. Har zakiya ta Fara sarewa da al"amarin ta Fara Tunanin nemo Wata Hanyar ita Aranta Take Tunanin kila Zain yana amfani da wani Abu agabansa na Tsikan Sparm kafin ya Shiga Mahaifar Dina ya Lalace,Ta riga ta gama Sanyi da Al"amarin ta kuma Fara Nema musu Wata Hanyar ganin wannan Taki Bullewa har yanzu. Yau din Dina ce takai Ziyara gidan  Zakiya suna zaune Suna cin Abinci A Saman Cafet din Dake Falon zakiya Indomie ne da kwai suke ci,ita Zakiya Dafa nata tayi Na Dina kuma Ta Soya mata sanin bata son Cin Dafaffen kwai Ammh Abunda yafi bata mamaki ganin yau Dinar tace bata ma son warin Soyayyah Dafaffen taci Ta barma Zakiya taci Soyayyah,Ita dai Zakiya sai kallon Dina Take Tunda Ga samam kanta Har zuwa kafarta ammh bata ga wani Chanji ba sai ta watsar da Lamarin kawai suka gama cin Abinci suka koma samam kujera suna Cigaba da Hiransu Ranar ma Gidan Zakiya Dina ta kwana sai da Safe ta koma Gidanta. Sakamakon yadda aiki yayi ma Zakiyar Yawa a office sai Suka kwana Biyu basu Hadu da Dinar ba,Sai da suka kwana Wajen Biyar kana Dina ta Kira zakiya Da wajen Misalin 3pm na Rana tace Tazo ta sameta agida tun Jiya bataje ko"ina bata jin Dadi Da Zakiya Taji Haka bata kawo komai ba Tana Tashi Daga Wajen aiki Ta wuce gidan Dina,Kwance Ta ganta Cikin Bargo Lokacin da suka Hada ido sai da ta zaro ido ganin yadda Dinan tayi wani Fari kamar mai Hadawa da mai jikinta Duk ya Saki da Sauri zakiya ta yarda Jaka da Takalmi ta Hau kan gadon ta Cicccibo Dina Tana Fadin"Dina lafiyanki kuwa..? Kinga yadda kika Dawo..?. Take Fada Lokaci Daya Tana yaye mata Bargon Data Rufu dashi Daga ita sai Rigar Barci Haka take kare ma Jikinta kallo kafin ta Fizgi Tafin Hannun Dinar tana kallo Cikin Zaro Ido Zakiya tace"Dina yaushe kika ga period Dinki Last..? Yamutsa Fuska Dina Tayi Tana Fadin"Kinji ki da wata mgana Sau nawa zaki Tambayeni na gayamiki dis Month ne kadai ban yi ba ammh Last 2 month da suka wuce Duk nayi..! Kura mata ido Zakiya Tayi kamar mai son gano Wani Abu kafin Tace"Meke Damunki..?Dina ta wani Dafe kai kafin tace"Kaina ne ke Ciwo..Tun Jiya da Zazzabi na kwana ga Kasala da Dacin Baki komai naci bayamin Dadi.."Cikin Farinciki Zakiya Tace"Zain yazo Gidanan ne... ? Dina Tace"Yazo jiya..Wlh wani Abu yabani mamaki sam naji bana Sha"awar Sex Dakyar na bashi Hadin kai Bayan mungama Haka na Shiga bayi ina ta kwarara amai kamar zan amayar da ya"yan Hanji.."Bata bari Dina ta karisa ba Ta Fada Jikinta ta Rumgumeta Tana Fadin"Allah nagode maka our plan Was Sussefully Dina..! Cikin mamaki Dina Tace"Bangane ba..? Sakinta Zakiya Tayi ta Mike Da sauko Daga kan gadon Tana Fadin"Tashi zakiyi zama bai ganmu ba...Ina zargin Kina da Ciki Dina.."Ido Dina ta Waro Cikin Farinciki Tana Fadin"Da gaske Ina da Ciki Zakiya..? Tafada Cikin Sigar Tambaya Kai Zakiya ta Gyada mata Tana Fadin"Haka nake Fata kuma nake Zargin ya kasnce.."Aikuwa da Sauri Dina ta Diro Daga kan gado Suka Rumgume juna Suna Murna Kafin su saki Juna Zakiya tace"Tashi ki Rarrafa Ki Shiga wanka sanyi Jiiki ba namu bane..Zamu Shiga plan B din mu.."Dina najin Haka ta Daka Tsalle Tana Fadin"Yanzu kuwa.." Da gudu Ta Fada tiolet zakiya ta Bita da Dariya Ita ta Fito da kayan da zata saka a gurguje Dina tayi wankan ta Fito Ta Shirya Suka Fita amotar zakiyar basu zarce ko"ina ba sai wani Private Hop,baban Likitan Dake asibitin Saurayin Zakiya ne sunyi Soyayah Holewarsu Daga Baya Ta Rabu Dashi Shi kuma har yau har gobe yana Binta da nacin in ta yarda zai Aureta ya Killaceta ita kuma tace ba yanzu zatyi Aure ba Bata gama Bariki ba Shi kuma har yanzu bai Hakura ba acewarta In Tagama Barikinta Saurayi Uztas zata samu Tayi Wuf Dashi ba irinshi Da Suka Hadu a Bariki ba. Yana ganinsu ya Fara Rawan Jiki nan da nan Zakiya ta gayamai Abunda ke Tafe Dasu,Shi kuma ya kira wata Nurse Daga Lab tazo Ta Dibi Jinin Dina yace ta kaishi Lap yanzu yake son sakamakon Da Hanzari ta wuce Cikin Sassarfa Ita ko Dina sai Bin Zakiya Take da kallo Domin bata mata wani Bayanin Dalilin Zuwansu wannan asibitin ba Tana chan Suna Hira da Likitan Dagajin yadda suke mgana zaka Fahimci anyi kyakyawan zama tare. Shudewar Mintina Arba"in kana aka kawo sakamakon Sai da ya Bude ya Duba ya gani kana ya Mikama zakiya yana Fadin"Kawar naki tayi Aure ne..? Yafada yana Nuna Dina Fuska Zakiya Ta Hade kai Tsaye tace"Ina Ruwanka..? Mallam bamu Sakamako muna kan Hanya ne.."Dariya yayi kafin ya Mika mata yana Fadin"Congarulation Kawarki Tana Dauke da 5weeks and 2dys Pregant...! Wani Farinciki ya Cika Zukatan Zakiya da Dina wanda sai da suka Rumgume Juna Cikin mamaki yake Binsu da kallo Sai yayi Tunanin kila tayi Aure ne ba kamar yadda yake Zargi Da Farko ba,Sai da suka gama Murnan kana Dina ta Juya Tana kallonsa Tace"Dacta Last Month fa nayi Mesis wannan Watan ne kadai ban yi ba Hakan ba matsala bane.? Yana yar Dariya yace"Likita Tana Tambayan Likita game da Abunda ta sani ko Duk Murnan ne..?karki damu Normal ne Mata Wasu Daga Ciki kuna Haka kila ki Dakata daga haka kila kuma Bayan kowani Wata Daya ki Rika ganinsa yadai Danganta Daga yanayinki ne.."Zakiya ta ja Jakarta Lokaci Daya da Hannun Dina Tana Fadin"Docta sai munyi mgana.." Daga Haka suka Fice Daga Office din Zakiya Dauke da Resuilt Din Cikin na Dina,Basu samu mgana ba sai da suka Shiga Mota Zakiya ta Ja suka Fice Daga asibitin Sai da suka Daidaita Tukin Bisa kwalta kana Dina ta waigo Tana kallon Zakiya Tana Fadin"Yanzu ina muka Nufa..? Hankalin Zakiya na wajen Tuki Tace"Saulawa Specialist Hop..."Ido Dina ta waro Tana Fadin"Bangane ba..? Wajen Zain zamu je..? Kai ta Girgiza mata kafin Tace"Ba yanzu ba...Wajen Saurayin naki zamu wama yake da Suna..? Wannan Bunsurun matan nake Nufi..? Cikin mamaki Dina tace"Wai Dr Imran kike Nufi..? Da Sauri Zakiya tace"Yauwa Shi nake Nufi.."Dina tace"Bangane ba..Miye Aikin Dr Imran awannan Plan din namu kuma.."? Zakiya tace"Bashi da wani amfani sai waje  Daya....Zamu je ne kan Baki da lafiya zaki ce ya Dauki Jininki a gwada ki kina Tunanin Maleria na Damunki.... Kinga In Sakamako ya Fito Irin na Dr.Yusuf ne,munhada Sakamako Biyu kenan Daga Mabambamta Asibitoci Ciki Harda Asibitin Dayake mallakinsu Koda zasu karyata Dr Imran zai iya zama Shadarmu.."Kai kawai Dina take gyadawa kafin tace"Daganan kuma sai yaya..,? Zakiya ta Bushe da Dariya ta saki Sitiyarin Motarta Tana Fadin"Daganan sai Ki kira Zain ki Gayamai kina Dauke da Cikinsa..! Dina tace"Sai kuma..!Zakiya tace"Daganan sai na Daukeki na kai ki Kano Sabuwar kofa.." Gaban Dina ya Fadi ta kwalalo Ido Tana Fadin"Gidanmu kuma... ? Tafada Da Sigar Tambaya Zakiya ta gyda kai Tana Fadin"Eh insha Allahu..! Dina Ta Dafe kai Tana Fadin"Miye manufar hakan..? Zakiya tana Zuba Hon abakin get din Asibitin Saulawa Ta Dago Tana kallon Dina lokaci Daya Tana Fadin"Manufa Shine Zan kai ki nace baki da lafiya..In Hajiya Batula ta Kirashi Ta gayamai Abunda ke Faru nasan zai ce akira Family Doctor dinku ya Dubaki..." Dina Tace"Kin kasheni Zakiya zai Fada musu ina da ciki fa..? Zakiya tace"Plan C din mu zai Fara Daga Lokacin.." Dina tace"Wani irin plan c kuma..ya zanyi in Daddy yaji Labarin ina da Ciki Zakiya..? Zakiya na Faka Motarta a parking space Tace"Zai ji ba Dadi mana Dina ai Duk Uba na kwarai ba zai so Gurbacewar Yarsa ba balle keda yake matukar so..Matakin da kowani Uba zai Dauka Shi zai Dauka Dina karki Damu..! Dina na Sakin Numfashi Sama sama Tace"Nidai Don Allah ki Fitar dani Duhu Zakiya Wani irin mataki zai Dauka..? Hakan yana da alaqa da Cikar Burina ne..? Zakiya tayi wani Mirmishin Kin Cika matsala afili sai ta Furta"Naso ki bari mu bi komai Daki Daki ne ammh Tunda kin matsa Shikenan..Matakin da zai Dauka Shine Zai Fara Tambayanki wayayi miki ciki..? Ke kuma sai ki Bashi amsa da ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA,Ki kara da cemai ya Ribace ya yaudareki da kalmar zai Aureki ya Lalatamiki Rayuwa Tun kuna London Yanzu kuma Daga karshe ya Nuna bazai Taba Auranki ba.." Dina ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Naji sai kuma yaya..? Ta ina zamu Fara tunkarar Ahalin Zain..? Zakiya tace"Daddy da kansa zai Dauko ki ya kawoki har garin Bauchi A gaban Iyayen Zain zai Zayyane musu Dan"su yayi ma yarsa Ciki kuma bazai yarda ba yana Neman Hakkin Yarsa.." Dina ta Saki baki kafin tace"Kai...! Zakiya ta Bude Murfin Mota Tana Fadin"Naki wasa ne..Komai na Shiryamai..Kinga Haka na Faruwa plan D zai Fara aiki..Yayinda Duka Zuru"arsu zasu Tattaru waje Daya Domin Yima Abun Tufkan Hanci.."ta fada Tana Dariya Jinjina kai kawai Dina keyi itama ta Bude Murfin Mota Ta Fito Tana Fadin"Burina fa Yaushe zai cika..? Zakiya tace"Acikin plan D zai cika..Domim Daddy zai ce bai yarda ba..Zai kai kara Kotu Su kuma iyayensa zasu nemi Sulhu..Daganan kuma Za"a ce Dole zain sai ya Aureki Saboda Rufuwar Abun kar ya Hadu a Duniya..Ammh Shi kanshi Daddy Barazana zai yi musu Domin Shima ba zai so Wannan labarin ya Fita ba ko Domin Siyasarsa...! Hannu kaawai Dina ta bama Zakiya suka Tafa Lokaci Daya Tana Fadin"Aikin ki na kyau Tawan..! Jinjina Zakiya tayi ma Dina kawai kafin su Fara Takawa atare zuwa Cikin asibitin Zakiya na kara Gayamata Yadda Tsarin Plan dinsu zai Tafi har zuwa matakin Nasara. *Ina Godiya da Sharhin ku kan wannan Labarin Keep it up...* *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*              1️⃣4️⃣ "Shigarsu asibitin basu Hadu da kowa ba sai Dr.Aisha da Dr.Peter suma din sama sama suka gaisa Dr.Aisha ce ma ke Tambayarta Lafiya Jiya bata Shigo Asibiti ba yau ma Haka Fuska a Tamke tace mata bata Jin Dadi ne sannu kawai Tayi mata sukayi sallama su suka Wuce Office din Dr Imran ita kuma ta Wuce Femele Word Kila zata yi Dubawar yammah ne. Dr.Imran na Tsaye acikin Office Dinsa ya gama Abubuwan Dayake Shirin Tashi ma yake,sai ga Dina da Zakiya sun Shigo mamaki ya Kamashi Da ganinsu ,Ya Riga yasan Wacece Zakiya awajen Dina Tunda kamar yadda Kowa ya san Dina a Ma"aikatan Da Zakiya take aiki Haka zalika kowa yasan Zakiya kawar Dina ce Acikin Asibitin. Bai iya cewa komai ba har suka samu Waje suka zauna Zakiya ce Ta kalli Dina itama ta kalleta sai ta kada mata kai,Ganin haka yasa Ta Juya Ta kalli Dr.Imran wanda ya sakar mata Bunsuran Idanuwansa Cikin Wani kallon Bariki da kwarewa Cikin Basarwa tace"ah..Zauna mana..?Ko baka Maraba da zuwan namu ne..? Cikin yake ya zauna yana Fadin"Haba..? Wane Imran yace Baya Maraba da zuwan Baki kamar Dina da kawarta...U are Higly Wlcm..."Ya karishe Fada yana wani Shafa gemunsa na yan Duniya wani kayattacen Mirmishi Dina tayi kafin Tace"Zuwa nayi yau ka dubani Dr Imran..! Tafada Cikin Son Tabbatar da Abunda Ta Fada kura mata ido yayi yana Fadin"Topha..Meke damunki kuma.? Don naga alaman Idanuwanki sun Fada Sosai..! Yafada yana Jifanta da wani kallo kafin Dina ta samu Zarafin Mgana Zakiya ta Rigata da Cewa"Zazzabi take Fama dashi da Ciwon kai ga kasala da Mutuwar Jiki Amai da Rashin Dadin Baki,mutuwar Jiki da tsinkewar yawun Baki.."Ta karishe Fada tana kallonsa kafin ta maida kallonta kan Dina Wacce ta zaro ido Tana kallonta kai ta gyada mata alamun karta Damu. Maida Hankalinta Tayi kan Dr.Imran wanda ya zura ma Dina Ido kawai yana karantar wani Abu Daga bayanan Zakiya kawarta Kafin ya samu Bakin Mgana Zakiya tace"Wani gwaji kake ganin ya kamata kayi mata Dr Imran..? Sai da ya wani Gyara zama kafin yace"Pregancy Test ya Dace da ita..Domin ina da Tabbacin Dina ciki gareki.."Yafada yana so yaga wani Reaction zata nuna sai yaga bata damu ba illah Zakiya Data kura ma ido Ita kuma kawai sai ta kada kai Tana Fadin"Zamu jira ka yanzu ka bamu Tabbaci..! Tafada tana wani Laso Harshenta Waje,Mirmishi Dr.Imran yayi kafin ya Jawo Wata Takarda yayi Rubutu asamanta Lokaci Daya ya Mike yana Fadin"Ku jira bari naje na kira Wata Nurse ta Debi Jininta..! Da Hannu Zakiya ta Dakatar Dashi Tana Fadin"A"a bama bukatar wani cikin wannan aikin.Kai zaka Dibi Jininta kuma Muna bukatar a Sirrinta Sirrinmu Saboda gudun ajikama aikinmu.."Tafada tana kada mai Hannunta wanda yaji jan Lalle. Kai Tsaye yake kallonta kafin yace'"Na yarda zan Sirrinta Abun.Ammh ni miye Tukwaicina akan Hakan..? Kai Tsaye Zakiya tamike Tsaye ta Fara Taku zuwa gaban Dr.Imran batare da Tunanin komai ba ta Saka Hannu ta Shafa gemunsa zuwa Fuskarsa Tana Fadin'"In komai ya Tafi Daidai..Nice Tukwaicinka Tun Daga Farkon Dare Har karshensa naka ne.."Tafada tana wani kashe mai ido Wata Dariyan yan Bariki ya saki kafin ya kada kai yana Fadin"An gama." Daga Haka ya fice Daga Office Din Jikinsa na Rawa da Sauri Dina Ta Mike tana Fadin"What me kikayi haka Zakiya..?. Hannu Zakiya ta Daga mata Kafin Tace"Shiii..Ba yanzu zaki Tambayeni ba..Ki bari sai mun Fita..'Dole Dina ta koma ta zauna tana maida Numfashi Itama zakiyan zaman tayi,Cikin Lokaci sai ga Dr.Imran ya Dawo Da Sirinji da Allura a Hannunsa nan Take ya Dauki jinin Dina ya sake Fita Shudewar Mintina Hamsin Biyar suna zaman jiransa sai gashi ya Dawo Da Farar Takarda ya mikama Zakiya yana Fadin"Ga Tabbaci nan Saura nawa Tukwaicin yaushe zan karba...? Karba zakiya tayi ta Bude Ta karanta ta gani Mirmishi ta saki ganin Sunan Dina maimakon Dina Gaddafi Sheerif sai aka Saka Dina G Sheerif kuma Sakamakon Iri Daya ne Dana Dr Yusuf Cikin Sati5 da kwana Biyu,Dagowa tayi Tana kallon Dr.Imran kafin ta mikama Dina Takardan Tana Fadin"Sai nan da kwana Biyar ko Shida zan nemeka da kaina..! Zai yi mgana ta Dakatar Dashi Lokaci Daya da mikamai wayarta Tana Fadin"Sakamin Lambarka In baka sabamana alkawari ba nima bazan saba maka ba.."Karba yayi ya saka mata lambarsa ya mikamata yana Kallon Dina a karkace bata Bashi Fuska ba ta Mike kawai Tayi gaba Zakiya tabi bayanta tana kada ma Dr.Imran Yatsunta Har suka Fice yana Binsu da Kallo,komawa yayi ya zauna yana wani Tunanin ya sani ba Tun yau ba Dina na Harka da maza ammh bai zata Haka ta zama wawiya da wayanta da Iliminta Itafa Likita ce Taya zata zauna ta bari Har tayi Ciki..? Ya fara Tunanin anya ba wata aksa ganin Daga ita har kawar tata basu nuna wani Damuwa ba kamar ma sun san da Ciki ya Dade yana Saka Abubuwa ganin bai gano komai ba yasa ya watsar da komai Murnansa Daya zai More da zakiya Gefe Daya na zuciyarsa na kara kwaidaita masa Dina Domin Har ga Allah yana Sha"awarta kuma yana da Burun ya kauda wannan Sha"awar koda na Dare Daya ne. Zakiya bata ma Dina mgana ba sai da Takaita Kofar gidanta kana ta Dauki Result din Da Dr.Yusuf ya basu ta mikama Dina Tana Fadin"Wannan zaki nuna ma Zain bayan kin kirashi yazo kin gayamai kina Dauke da Cikinsa..! Dina Ta kalleta Tana Fadin"Miye Manufar hakan.? Zakiya tace"Manufofi da yawa ne Dina..Yanzu ki Sauka kije gida kiyi wanka ki Sauya kaya Sai Ki kira Zain kice yazo Kina son mgana Dashi Da Daddare in ya nuna Bazai zo ba ki Turamai Sakon ko yazo ko kuma ke ki biyoshi Gidansa na Tabbata Dayaji Haka zai zo,Sai ki nuna mai wannan sakamakon Zai Firgita kuma zai yi Challaging dinki kan kin Shirya wani Abu ke kuma sai ki nuna mai baki Shirya komai ba in ya gama Rudewansa zai nemi ki yarda azubar da Cikin,karki gaddama Ki yarda da cewa zaki Zubar da Cikin.! Dina Tace"Na yarda fa kika ce..? Kai ta kada mata Tana Fadin"Eh ki yarda mana..Ammh na iya baki bai kai Zucci ba.Nasan zai ce ki bari da safe zai koma gida yana Tunanin mafita kuma Tabbas da Safe zai dawo yace ku Tafi wani asibiti azubar da Cikin.."Ta Dakata Tana kallon Dina kafin Ta Cigaba"Kafin yazo mu kuma mun Tsufa a kano zaki kashe Duka wayoyinki yadda bazai Taba samumki ba..Ke kuma Yau Da kinga Zain ya Shigo Gidanki ki Kirani awaya ni kuma zanyi Sauri na Daga Wayar na sakata cikin Recording Zan ji Abunda yake Fada Gefe Daya kuma ina Nadanshi a matsayin Hujja kin gane..? Kai Dina Ta Jinjina Tana Fadin"nagane ammh baki Tunani  yaji wayata akashe bazai yi wani Tunani ba..? Zakiya tace"Zai yi mana Lokacin yana Rudene..zai yi Tunanin wani Abu ammh kafin Tunaninsa yaje mai kan plan dinmu komai ya kamallah Sai dai kawai Bom din ya Fashe Bumm...! Tafada tana Dariya Dinar na Tayata sun Dade Tana kara Fada mata mganganun da sata gayama Zain indan yazo kafin su Rabu Ta sauka ta Bude Gidanta ta Shige ita kuma ta Sakar ma Motanta Wuta ta Fice Daga Wajen da Gudu. ****** Zaune yake akan kujera mai zaman Mutum Biyu,Zaina kwance Gefensa Tayi Matashi da Cinyarsa Tana sanye Cikin Wasu Riga da wando na Barci Masu Taushi Sun lafe ajikinta,shi kuma Dagashi Sai Boxers wasa yake da gashin kanta Suna Hira Cikin so da kauna. Lokacin Dare ne Domin Wajen 9 pm na Dare ne har ma ta wuce,Bai Dade Da dawowa Daga asibiti ba yayi wanka sukaci Abinci kana suka yada Zango a Falo suna Hiran Ma"aurata mai Dadi. Juyo da kanta yayi Yana kallonta Ido Cikin ido yace"Firstlove kin kara Haske fa..? Mirmishi Tayi Tana Fadin"Haka kowa ke Fadi...Umma Dazu haka tacemin Dana Biya bayan na Dawo makaranta.."Kumatunta Yaja yana Fadin"Har da kiba ma kin kara kalli kumatunki kin zama Zaina bombom yanzu fa..'. Yafada yana Dariya Itama Dariyan Take Tana Fadin"Haka Ukti tace Jiya da mukayi VD call da ita.."Kiss ya sakarmata agoshi yana Fadin"Naji Dadi..Abba Da su Umma zasu gane yanzu nafisu iya kiwo Tunda Gashi kinyi kiba.."Yar Dariya Tayi Tana Damke Hannunshi Cikin Kura mai Ido Tace"Firstlove..! Asama yaji Sunan ya kalleta yana Fadin"Umh menene Zainazain.."Ajiyar rai ta Sauke kafin tace"Kwanakin nan ina yawan Fama da Faduwan gaba..Sai ina ji ajikina kamar zan Rasa wani Abu Daya zama mai matukar amfani agareni.! Ido kawai ya sakarmata yana kallonta har tagama mgana kafin ya Saka Hannu ya Tadata ita Kan Cinyarsa ya Sauketa Lokaci Daya ya saka Hannuwansa ya Zagaye Kugunta Dashi yana Fadin"wa zaki Rasa Firstlove..?Nine nafi komai Muhimmanci gareki kuma Bazan Taba barinki ba Har Abada..". Tana kallon kwanyan Idanuwansa Tace"Mutuwa fa..In mutuwa ce fa ya zakayi..? Fadin Haka yasa sai Jikinsa ya mutu,Kawai sai ya lafe Ajikinta yana Fadin"Ki daina wannan mganar Firstlove ko mutuwa ce Insha Allahu Tare zataDaukemu Wani baazai mutu ya bar wani Cikin Tashin Hankali ba Kinji ko..? In kin kara Jin Faduwar ba kiyi ta Maimaita Hasbunallahu Wani'imal wakil.."Tana Daga Jikinsa ta gyada mai kai Tana Fadin"To Firstlove na Daina kuma zan Dinga yi insha Allahu..! Matseta yayi yana Fadin"Nagode My Wife...Allah ya barni Dake har Mudin Rai ta amsa da Ameen,Sun Dade ahaka kafin Ringing din wayarsa ta katsesu,Saussauta Rumgumar da yayi mata yayi Lokaci Daya yana jawo wayarsa Dake gefensa Sunan Dina Daya gani Tana Kira sai da gabansa ya Fadi Sororo yayi kawai ya kasa Daga Kiran ganin haka yasa Zaina ta waigo Tana Fadin"Ba kiranka ake ba..? Yake yayi yana Fadin"Sharesu Daga asibiti ne..' Da Sauri tace"A"a bazai ayi haka ba in wani Abun gaggawa ne fa..?ka Daga ni bari naje Kitchen nayi kaye kaye na Dawo.." Tana gama Fadar haka tatashi Daga kan Jikinsa ta wuce Kitchen sai da yaga ta Shige kana ya Tashi da Sauri Dauke da wayarsa ya Shige Bedroom dinsu ya Turo Kofa yana Kokarin Kiran Dinar sai gata ta sake Kira da Hanzari ya Daga yana Fadin"Why Dina..? Baki san ina gida bane so kike Firstlove ta Zargi wani Abu..? Dagachan Bangaran Dina Tace"Kiran yana da Muhimmanci ne...Ina son ganinka ne yanzu yanzu..! Cikim mamaki yace"Yanzu yanzu kuma..? Kan wani Dalili Kuma kinsan na dawo Gida.."Yafada yana waige waige na Marasa gaskiya. Dina tace"Eh mgana nake so muyi mai muhimmanci..."Kai tsaye yace mata,"Ki Barta sai gobe da Safe..Gaskiya yanzu ba zan iya Fitowa ba Basan wani karya zan yi ma Firstlove ba gaskiya.." Mirmishi Dina Tayi Tana Fadin"Allah ko..? To ka zauna ni sai na Taho gidanka yanzu na Sameka.." ido ya zaro Waje kamar yana ganinta yace"What.? Kizo ina..?Kai tsaye Tace"Gidanka mana in yaso sai kama Firstlove din Taka bayanin in Taganni adaidai wannan Lokacin.."Da Sauri yace"baki da Hankali ne..? Dina tace"Ina dashi..Kazo gida ka sameni yanzu ko kuma Wlh ni nataho yanzu.." Jin Haka yasa yace mata"Is Ok karki zo ganinan zuwa.."Mirmishi Ta saki kafin tace"Gud.."Daga haka ta katse Kiran Tana Dariyan Mugunta Zain kuwa Zufa ce ta Shiga ketomai Ya Fara safa da marwa Cikin Bedroom din ya Rasa mafita kawai sai ya hau Saka kaya Wata Milk din Jallabiya kawai ya saka ya Dau key Din Mota ya Fito yana Fito suka Hade Da Zaina ganinsa a gaggauce yasa Taja ta Tsaya Tana kallonsa Cikin mamaki tace"Lafiya..? Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Baza abar mutum ya Huta ba Dai...Bana ce bazan Daga wayata ba..Kikace na Daga Kira ne Daga asibiti An kawo Emegency wata mata ce zata Haihu sai Bleeding take.."Ya karishe Fada yana Kauda kai Domin yana Jin kunyar karyan Daya Shararamata ita kuwa Cikin Tsausayawa tace"Wayyo Allah sarki har na Tsausayamata..Bakomai Firstlove kaje zan Jiraka Ina Alfahari dakai..' Rumgumeta yayi tare da mata Kiss a goshi ya wuce tana Binsa da addu"an dawowa lafiya baya Cikin Natsuwarsa yana Fita ya Rika kwalama Tanimu maigadi Kira cikin Tsawa yace ya Bude mai Get Tanimu jiki na Rawa ganin Dakta Rai bace ya Budemai get din ya Fice da Gudu kamar zai Tashi sama Kai Tanimu ya girgiza yana Fadin"Allah Huci Zuciyar Gwarzom maza.." Lokaci Daya yana Maida get din Ya Rufe ya koma kan kujeransa ya zauna ya Dauki Radionsa ya kara Sauti Abunsa Ransa fes babu Abunda ya Dameshi. Shi ko Zain yana Fita ya Dinga Tsula Gudu Bisa Titi kamar zai Tashi Sama,Cikin Lokaci kadan sai gashi kofar apartment din Dina Ita kuwa Dama Tana Jirace Dashi Tana Jin Dirin Mota ta leka ta Window falo Tana ganin Shine ta Dauki Waya da Sauri ta Kira Zakiya,Tana Dauka Ta gayamata isowarsa ita kuma tace Ta bar waya akunne,Saman Center Table din Dake Tsakiyar Dakin ta ijiye wayar Da Sauri Ta Shiga Cikin Bedroom Dinta ta Dauko Result din Da Zakiya ta bata tazo ta ijiyeshi Saman Kujera,Daidai Lokacin Taji Zain na Knooking din Kofar nata Bedroom din ta ta koma ta Samu Robe ta shafa kasan Idanuwanta nan da nan Hawaye suka Fara zubo mata ba kama Hannun yaro Idanuwan kuma suka kumbura luhu luhu kamar wacce Tasha kuka gashi Sun sauya Launi. Jin yana ta knookig ne yasa ta Fito Da Sauri Zuwa Falon ta isa ga Kofar ta Budemai Suka kalli juna Cikin mamaki yake kallonta ganin yadda Hawayen Idanuwanta suka Kasa Tsayuwa Cikin Mamaki yake Fadin"Lafiya kuwa..? Hannu Dina ta saka Tana Sharban Hawaye batare da Tayi mgana ba ta Juya kawai zuwa Cikin Falon Ganin haka yasa ya Rufa mata baya,bayan ya saka Hannu ya maida Kofar ya kulle Zama Tayi kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon tana matsar kwallah karya kamar yadda Zakiya ta Tsara mata,Cikin Fargaba Zain Dake tsaye kanta ya kalleta ya sake Fadin"Wai lafiyarki..? Nazo kuma kin Tasani kina kuka..? Kara Fashewa da kuka Dina Tayi kamar wata karamar yarinya Cikin Faduwar gaba da Ta samu Zain Lokaci Daya ya zauna Kusa da ita yana Fadin"Look Dina...Ki Saussauta kukan nan ki Fadamin Abunda ya Faru plz..,? Batare da Ta Dago ba ta Mika Hannu Ta Dauko Takardan Dake saman Center Table din Ta mika mai kin karba yayi iillah Zura mata ido Da yayi Lokaci Daya yana Fadin"Wannan fa..? Takardan menene..? Cikin Shakewar Murya Dina Tace"Taka ce..Ka duba ka gani.."Baiyi gaddama ba ya karba ya Bude ya Fara karantawa Tunda Abunda Takardan Ta kunsa Zain ya Fara Jin Wani irin Jiri jiri da kuma kafewar Miyan baki bai ji Tashin Hankali Wanda Tunda yazo Duniya bai Taba samun kansa Ciki ba sai da yagama Fahimtar Takardan da Abunda ta Kunsa Cikin Wani irin Sauri da Firgita Hade da Rawan Jiki ya Mike yana Rike da Takardan Gabadaya Idanuwansa suna Waje Hannunsa da Jikinsa da Bakinsa suna Rawa Lokaci Daya Dakyar ya iya Fizgo kalmar "Innalillahi Wa'inna Illaihiraju"u....Hasbunallahi Wani"imal wakil kalu inna lillahi Wa"inna Illaihirraju"un...Haka Zain ke ta maimaitawa bakinsa da Ko"ina na Jikinsa yana Ta bari kamar wanda Wutar lantarki ke ja Dina Dake zaune gefe Tana kallonsa ta Wutsiyar ido Kamar ta saki Dariya ganin Irin Tashin Hankalin da Zain ya Shiga. Cikin Fitan Hayyaci ya Zube kan Dina yana Fadin"D...Ddina Ban gane ba..? Me wannan Takardan Take Nufi..? Cikin kukan makirci Dina Tace'Nima haka na Shiga wannan Tashin Hankali Zain...Dama ai jiya ka barni bana Jin Dadi Toh Shine Zuwa yammah na Rarrafa na Tafi Asibiti ana gwadani aka bani wannan sakamakon.." Cikin wani karaji ya Rike Kafafun Dina yana Fadin"Wani Sakamako..? Ki fadamin da bakin ki Domin ina Tunanin idona ne bai gani Daidai ba..? Cikin karfin Hali tace"Ina da Ci..Ciki na sati Biyar da kwana..."Bata gama Rufe baki Ba kamar kiftawan Abu Taga Zain ya Mike ya Cafki Wuyanta ya Shake da Hannu Daya ya Dagata sama kafafunta na Wutsul Wutsil Daga sama Cikin Lokaci Daya ya Makata Jikin Bango ya Shake mata Wuya Sosai Idanuwan Dina suka Firfito Ta fara kakarin Mutuwa Lokaci Daya tana Saka Duka Hannayenta Jikin Na Zain tana neman kwatan kanta. Cikin Wani irin Murya mai Cike da Amon Tashin Hankali da Firgici Yace"Me kike Shiryawa Dina..? Meyasa zaki min Haka..? Na Taba gayamiki a Tarayyah na Dake babu Ciki kika kuma amince meyasa sai yanzu zaki Saba alkawari kizomin da Abunda zai zama Baraza gareni Ehe..? Yafada ya Zaro mata Jajayen Idanuwansa yayinda Da Jijiyoyin kansa suka mike Radau Cikin Son kwatan kanta Dina ke Fadin"Sakeni Zain..Zaka kasheni Ka sakeni nayi maka bayani..' Ganin Tana neman Suma ne yasa ya watsar da ita gefe ya koma ya Zube saman kujera yana maida Numfashi Dina kuwa Data samu ya saketa Gefe Taja Tana Tattaba Wuyanta inda ya Shaketa Cikin Kakkausar murya taji ya kara Fadin"Me kike Shiryawa Dina..? Bana gargadeki kada ki kuskura ki Sako Ahalina awannan Mganar tamu ba..? Meyasa zakimin Haka ehe..? Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Tace"Nima bansani ba..kuma Babu Abunda nake Shiryawa ka yarda dani..".. Ido ya sakarmata yana kallonta Cike da wani Tashin Hankali kafin yace"Karya kike kin Sani..Ina Alluran Da kike saboda haka..?Da Sauri tace"Allah ina nayi yanzu hakama nayi na Wata 6 bansan ya akayi haka ba Ka yarda dani.."Tafada tana Fashewa da Kukan makirci Kai kawai Zain ya Dafe yana Fadin"Kin kashe ni Dina..Kim kasheni yanzu ya kike so nyi..? Cikin Shege fa..Cikin Shege Fa Ni Zain da wani Ido zan kalli Mutane in mganar nan ta Fasu..? Da sauri Dina Ta kallesa Tana Fadin"Ba wanda zai ji wannan mganar..Mganar Ciki kuma muyi Abortion dinsa in ka yarda.."Kamar an Tsaida shi haka ya kafeta da ido kafin ya Mike Zumbur ya Rarumi Sakamakon yana kara Dubawa kafin ya kalleta yana Fadin"Kin Tabbatar wannan asibitin kadai kika je aka Dubaki..? Kai ta gyada mai Tana kallonshi Baki ya Cije kawai Taga ya saka Hannu ya yayyaga Takardan yayi mata Gutu Gutu ya watsar da ita anan Tsakar dakin Yana Fadin"Hakane mganarki Dole ne zamu san hanyar da zamu bi mu Zubar da Cikin nan Dina Dole ne Shine kadai Rufin Asirina..! Jinjina kai Dina Tayi Tana Fadin"In har ka amince nima na yarda da Hakan wani asibiti zamu a zubar da Cikin..? Shuru yayi yana wani Tunani gabadaya kansa ya kulle sai Zufa yake yi kafin yace"Ba anan garin za"ayi aikin ba..Saboda Sunana ya Fita In Mukaje Watarana mgana zata Fasu zamu nesa da Garin nan Muje Gombe ko Kaduna Cikin Biyu Zamu Zabi gari Daya Inda zai sama Sirri garemu har muje azubar da Cikin mu Dawo ba wanda ya sani...Yes Haka ma za"ayi Gombe zamu Tafi Gobe da Sassafe saboda bamu da Lokaci.." Cike da mamaki Dina Take kallon Zain Kafin tace"Gobe kuma..? Cikin sakarmata Jajayen Idanuwansa yace"Eh gobe goben nan ba Lokaci Dina..Ya zama Dole a zubar da Cikin nan gobe Bana so ya kara kwana kada ya zamemin mtsala sannan ina Fata baki sanar da kowa Zencen Cikin nan ba sai Ni..? Gyada kai tayi tana Fadin"Ban Sanar da kowa ba..! Da Sauri yace"Gud...yanzu Abunda za"ayi Gobe ki Shiya da Wuri ki Dauki kayanki kamar Set uku haka Zan dauki Hutu a asibiti agida kuma zance Wata Tafiya ce ta kamani zuwa Gombe,Ki Jira anan Karfe 7am na Safe zan zo na Daukeki mu Tafi Ina so in muka je chan zamu Sauya Sunayenmu Saboda koda Watarana kin gane..? Ita dai kai kawai take gyada mai Gefe Daya na Ranta na Jinjina Son kai irin na ZAIN gefe Daya kuma na Zuciyarta na Fadin sai Kafi haka Razana Lokacin da mganar takai kunnin Iyayenka Zain Lokacin zaka Shiga kugin Nadama. Bai wani Jima ba ya Fice da Sassafar bayan ya gama Jadaddamata yadda ya Tsara komai,Yana Tafiya ta Tashi da Sauri ta Dauki wayarta Dake kan Layi har yanzu Tana Fadin"Zakiya na Shiga uku..? Zain ya kusa Kasheni fa yau..? Zakiya Dagachan Bangaran ta Saki Wata Dariya kafin tace"Daman ai nasan haka zai Faru..Saboda Abun bai zata bane ya Faru...Karki Damu Normal ne Tsarin na Tafiya Dai Dai yadda muka Tsara.."Dina Tana Sauke Numfashi Tana Fadin"Kinji Abunda yace..Ya zamu yi namu Tsarin Goben..? Zakiya tace"Karfe 7am na Safe yace...Mu kuma zamu Tafi karfe 6am ne na safe in Juransa Sammako mu Atafe muka kwana..Karki manta ki zama Cikin Shirin In kika batamana Lokaci zai iya Riskanmu kuma kinga Faruwar hakan kamar Batamana Shirin mu ne.."Da Sauri Dina Tace"Karki Damu zan yi kamar yadda kika ce..! Daga haka suka yanke Kiran Dariya kawai Zakiya ke kwasa Lokacin Data ke maimaita Mgangamun Zain Data gama Nada cikin wayarta Cikin Kada kafa ta Furta"Waya gaya Maka Borno Gabas Take Zain...Wlh sai na Tabbata kaji kunyar Duniya gaban Duka Ahalinka Sakarai kawai.." ****** Zain Allah ne kadai yakai Shi Gida Lafiya Domin yana Cikin Tashin Hankali da Dimuwa da Firgita Haka yaje gida ba Cikin Natsuwarasa ba Da Zaina ta ganshi ahaka sai da ta Tsorata Ta Fara Tambayanshi Lafiya yama kasa mata mgana ganin Hankalinta ya tashi ne yasa yamata karyan cewa Sun Rasa Patient din Dayaje Dubawa ne Allah Sarki Baiwar Allah harda kukanta Shi kuwa Zain Abunda ke Damunsa Dabam yana Tunanin yadda komai zai Tafi ne Batare da wani matsala ba. Tun adaran ya Fadama Zaina tafiya ta kamashi Zuwa Gombe kuma zata Dauki Tsawon kwana Uku zuwa Hudu bata kawo komai acikin Ranta ba tamai Addu"an Fatan alheri Harda Hadamai kayan Tafiya Shi kuwa yana zaune ya Zafga Tagumi kawai yana Ta Zufa,Natsuwa kwata kwata bai da ita Duk zaina ta Damu ganinsa Cikin wannan Halin,Ammh sAbun da ya bata mamaki ansha Samun irin wannan Case din a asibiti bata taba ganin Firstlove ya Shiga irin wannan Halin ba sai yau ammh sai ta Danganta da kila yau Matar ta bashi Tsausayi ne Haka Dai Ta gama Hadamai kayan Dakyar ta lallasheshi ya Shiga wamka ita kuma Barci yaci Idonta koda ya Fito Tayi Barci sai yaji Dadin haka,Zama Dirshan Zain yayi barci ko Barawo ya kasa Saceshi Zaina kawai yake kallo yana jin kwallah na Cika kwarmin Idanuwansa lokaci Daya yana mai Kaico da Rayuwarsa daya Kasa Barin Abunda Allah ya Haneshi gashi yau Dalilin Bijirema Allah ya saka kanshi Cikin Wani Bala"i wanda Fitar dashi sai Allah Da Zaina taso ta Farka sai ya kwanta ya Rufe ido kamar yana Barci,sai kuma yaga ta koma Farkawanta na uku ne ta tashi ta Bude ido ganin Wuta kau ga kuma Shi Zain din ya kwanta Ko Towel din daya fito wanka Dashi bai Cire ba saboda Zullumi da Fargaba,Ganin haka yasa ta Sauko Daga kan gadom tana Fadin"Allah Sarki Fistlove Daga gani ya gaji..Ji ko Towel bai Cire ballatana ya saka kayan Barci.." Wardrope ta Bude ta Daukomai Boxers dinsa tazo a Hankali ta Warware Towel din ta Zuramai wando Tana yi tana Lura kada ta Tadashi,Har tagama sakamai ta gyaramai kwanciya ta Rufeshi da Blanket ta sakarmai Kiss a goshi Lokaci Daya tana Shafa Fuskarsa kafin ta Dauki Towel din ta Bude Tiolet ta Shiga Idanuwansa da suka Kala sukayi ja ya Bude ya bita da kallo Sai ya kara jin Nadamar Abubuwan da yayi ta aikatawa Tun Suna London sai kuma yau ya kara yarda Da kalaman Haddir ya kuma yarda Masoyinshi ne Ace bai yi ma Matarsa ta Sunna Ciki ba sai karuwa..? Dama haka Allah ke lamarinsa Kodomin yanu mana mana Ishara mu Bayinsa,Yana Jin Motsin zata Fito ya sake lambo kamar mai barci yana Jinta ta kashe Wutar dakin ta kunna Dumlight,Ta hayo Gadon kan Kirjinsa ta yada Zango Ta Ja bargo Ta Rufesu Gabadaya Shi kuwa Zain kasa Rungumeta yayi Domin haka kurum yau yaji yana jin kunyar Tabata Haka kurum zuciyarsa ke wani Rawa ga Zunubun aikata Zina ga kuma Girman Zunubin Kashe Rai Lalle yana Cikin Bala'i Yadda yaga Safe haka yaga Dare,Sai gabda Asuba ne barci ya Kwaaheshi,Sai dai yaji ana sallame Salla Ita kanta Zainar ta makara Haka ya tashi Jikinsa Duk ya Mutu,Agurguje yayi wanka yayi sallah kana ya Shirya yana yi yana Duba agogo Fatan Dake Hannunsa Zaina na Kitchen Tana Hadamai Breakfast ya Bitachan yace mata zai Wuce Duk iya Kokarinta na Ya tsaya ya karya kasawa yayi ganin 7 din Daya ce ta Kusa haka ta Rakashi har Bakin Mota Har Motarsa Ta gama Ficewa Daga gidan Tana Tsaye Tana kallonsa Haka kurum Take jin wani Sanyi Jiki da Faduwar gaba haka kuma Take ganin yau kamar Firstlove din nata baya cikin Natsuwarsa Haka dai ta koma Cikin Gida Sukuku ta karisa aikinta ta Fada wanka Domin itama tana Da Shiga Sch 8am na safe. Koda zain ya fita Daga Gida kai Tsaye Gidan Dina ya tsaya Ammh Abun mamaki har ya kusa Mintina goma yana Mata Knooking Shuru bata zo ta Budemai ba ganin haka yasa ya koma Mota ya Dauko wayarsa ya Shiga Kiranta Abun Da yakara saka Zuciyarsa Bugawa Fat Fat Shine wayarnata Tana Kasheni,kamar zararrare haka ya Fito Daga Mota ya koma Jikin Kofar yana Bugawa Lokaci Daya da Kiran sunan Dina yayinda kuma Hannu Daya yake ta Gwada Layinta. Neagbours dinta ne wani Namiji Dama Gidajen irin ajere suke Kamar Estate ne yaji Bugun kofan yayi yawa ya Fito yana Tambayan Zain ko lafiya Shine ya karisa suka gaisa yana Tambayarsa Dina Shi kuma ya bashi amsa da Bata nan Domin yana Dawowa Daga sallar Asuba Yaci karo da ita ta Fito Daga gidanta da akwati a Hannunta wata Mota ta Dauketa Sun Fita da Gudu,kafin ma ya gama Zain bayani Numfashinsa ya tsaya Cak kamar wanda aka Dauke ma ji da gani Shidai yana gama gayamai ya wuce ya koma cikin Gidansa ya maida kofa. Zain kuwa wani Irin Juyawa ce ta Daukesa sai gashi a kasa yana Haki,Idanuwansa sum koma Jajir cikin wani yanayi yake Tunanin toh ina Dina Taje..? Wata zuciyar tace gidanku mana zataje ta Tona maka asiri..? Wani irin Rugurugu yaji a tsakar kansa kamar Rugugin Hadari Kamar an Tsikareshi haka ya Tashi yana Layi ya nufi Mota yana Fadin"Bazan bari ki Tozartani ba Dina..Bazan barki ba." Haka yake Fada kamar wani Zararre haka ya Tashi Motar ya Fita Daga Haraban wajen kamar zai Tashi Sama shi kadai kawai yake Fadin"Karki mun haka Dina..A"a don Allah karki Mim haka..! Haka yake ta Fada kamar wani Wanda yayi gamo ko ya zauce..! *Tanque so much Dearests..Allah ya bar kauna da Zumunci ZAINAZAIN BAND 1&2* *Shakira..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1* _Budaddiyar wasika Daga Zainullahi Usman Abubakar Saulawa Mijin Halimatu Abdullahi Gada zuwa ga Tarin Masoyansa da makiyansa,yace na Fada muku Mussaman yan Group din ZAINAZAIN BAND 1&2, da kuma yan Group din Janaf Novella 1&2,da Sauran Group din da suke masa One love Rokon alfarma yake Don Allah don Annabi ku Taimakamai ku Koma bayansa ko zai samu wannan Bala"in Dake Tunkaroshi Da sauki a samu masu Rokar masa Firstlove Da kuma masu bama su Alhaji Tsoho baki Domin adaidai wannan Gabar dai ya Sare Ya riga ya Shiga kogin Nadama..Yace na gaya muku yana Godiya ga masu Zaginsa da Tsine masa albarka da wadanda ke Jin Dadin Faruwar haka da kuma Fans dinsa masu Jin ba Badi Dukkanku yace na ce muku yana Muku One love.._❤️😍🤣              1️⃣5️⃣ "Zain yana Fita Daga Gidan Dina GRA ya wuce kai Tsaye yana Tafe yana manganganu Shi Kadai kamar wanda ya Fita Daga Cikin Hayyacinsa. Hon ya Dinga Zubama Megadi agigice kafin ya wangalemai get ya Sulalo da Motarsa Cikin Gidansu ko gama parking bai yi ba ya Bude Murfin Mota ya Fice da Sauri Gudu Gudu Sauri Sauri Zuwa Kofar da zata sadashi Da asalin Cikin Babban Falon Gidansu. Abba na Tsaye a tsakar Falo yana gyara zaman Hulan kansa Nene na gefensa Dauke da karamar Jakar briefcase Dinsa Umma ma na Tsaye Dayan gefen,ayayinda suka sakashi a Tsakiya kenan Sai Zainab Dake gefe Itama Cikin Shirinta na kamala Domin har ta samu Gurbin Karatu a Jami"ar ATBU bauchi Ta Fara zuwa Aji Daya 7:30am na safe Take da aji Shiyasa Abba zai kaita tunda Ma"aikatansu na Gaban Jam"ar ne,Tunda har yanzu Motar da Abba ya Siya mata bata iso ba. Sallama Abba yake da su Umma ya mika Hannu zai karbi Jakarsa Zain ya Fado Falo kamar Daga sama Gefe Daya kuma yana ta waige waige kamar wani mara gaskiya Gabadaya iyayan nashi Suka sakarmai Ido Suna kallonsa Cikin mamakin ganinsa Bashi da Natsuwa kwata kwata atare Dashi. Cikin Mamaki Abba ya kalleshi yana Fadin"Kai Zain lafiyar ka kuwa..? Ka Shigo gida kamar a Firgice..? Yafada yana sake karantarsa Shi kuwa Sai da yagama Dube Dubensa bai ga alaman Dina Tazo Gidan ba kana ya Saki Ajiyar Zuciya ya kalli Su Abba yana Fadin'Bakomai Abba...Dama...Dama..! Nene ta katseshi Da Fadin"Dama me..? Yarona Lafiya kuwa..? Ko wani abu ya Faru Da Zaina ne... ? Da sauri ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Nene....Dama Dama zan Wuce asibiti ne shine nace Bari na biyo na gaisheku Komai lafiya Da yardan Allah.."Ya karishe Fada yana Faman goge Zufar Dake Tsatsafomai Daga saman Goshinsa Gabadayansa in ka kalleshi baida wata Natsuwa. Ido Suka zubamai suna kallonsa kawai Cikin mamakinsa kafin Abba yace"Kai zain yaka nan..Daga ganinka baka Cikin Natsuwarka Meya faru..? Kada kai kawai yayi yana Fadin"Bakomai Abba Allah kuwa..Na Wuce asibiti.."Daga Haka bai basu Zarafin mgana ba kawai ya juya ya Fita a gaggauce kamar zai Tashi sama Dukkansu suka Bisa da kallon Mamaki har ya Fice Umma ta kalli Nene Tana Fadin'"Nene yaronki ba lafiya fa..? Zainab ma tace"Allah Abba kamar yaya yana Firgice ne fa.."Abba ya jinjina kai yana Fadin"Nima Haka nagani..Ammh Tunda yace Bakomai mu barsa abakomai din Allah ya kyauta.."Nene tayi Shuru kafin ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Naji Jikina Duk yayi Sanyi..Tunda Nake da Zain ban Taba ganinsa Cikin wannan yanayin Ba.." Hanyar Fita Abba yayi yana Fadin"Komai miye Allah ya Saukakamai...Ni na wuce.."Dukkansu suka Bishi da Fatan Allah kiyaye Hanya Zainab Tabi Bayanshi Suka Fice Daga Falon Abun mamaki Zain yana Cikin Motarsa bai Tafi ba ya kasa Tuka Motar ma Gabadaya kansa ya Kulle Kiran Layin Dina yake yi kamar Mahaukaci Yana ayyana Faruwan Wasu Abubuwa Dadama Indai Dina ta Rusa plan Dinsa. Abba ne ya kalli Motar Zain kafin ya Juya ya kalli Zainab yana Fadin"Dubamin Zain din yana Ciki ne.."?jin haka yasa ta karisa Jikin Motan ta Fara Knooking din Glass din Bai ma Jita ba sai chan yaji kana ya Waiwayo ya Sauke gilashin Motar Lokaci Daya yana Sakarmata Jajayen Idanuwansa,Cikin Tsoro tace"Abba ne yace na Dubaka ko kana Ciki..? Sai da tace Hakane ya Juya yaga Abba Tsaye yana kallonsu Cikin Shakakiyar Murya yace"Kice mai yanzu zan tafi na Tsaya ina Waya ne.."Daga haka ya maida glass din Motar ya Rufe yayi ma Motar Wuta yaFice Daga Gidan Abba ya Rakashi da kallon Mamaki Lokaci Daya yana Nazarinsa Zainab ma Duk Jikinta yayi sanyi,Kada kai kawai Abba yayi Direba ya Budemai Bayan Mota ya Shiga Zainab ta Shiga gaba suka Bi bayan Zain Shi kudu yayi su kuma sukayi yammah Ammh agefen Zuciyar Abba yana Tunanin koma miye yake Damun Zain ba mai Sauki bane Tunda bai Taba ganinsa Cikin Irin wannan Rudewan ba. ***** *Kano..* Sabuwar kofa..! Koda Karfe 10am na safe Tayi Su Zakiya suna Falon Gidansu Dina,Koda suka isa Dina Tun a Mota ta galabaita sun Fito basu karya ba,Sai suka tsaya Bisa Hanya Zakiya ta siya musu Dankali da kwai Ta faraci sai kuma Amai kafin su iso Duk Jikinta ya Saki haka Zakiya ta Shiga da Dina a Rirrike da Ita kamar wacce ta Shekara Tana Jinya. Hajiya Batula tayi mamakin ganinsu ahaka,tayi ta Tambayan Zakiya meke Damun Dinar ammh sai taki Cewa komai,Daman ai Tasan Zakiya sosai,Nan Falon ta kwantar da Dina wacce ke kara Murkukusun karya Mahaifin Dina yana gari Ya tafi Office ne Cikin Hikima Hajiya Batula ta Kirashi a waya ta Fadamai Ga Zakiya kawar Dina Ta kawota Bata da lafiya yana Jin haka sai Hankalinsa ya Tashi yace tayi Maza ta Kira Family Doctor dinsu Gashi nan zuwa Zasu Shiga Meeting in sun Fito zai kariso Gida. Haka kuwa akayi Ta Kira Likitansu Dr.Bala Ta gayamai Cikin Abunda bai gaza Mintina Ashirin ba sai gashi Daga yanayin Tambayoyin Dayake ma Dinar tana Bashi amsa yasa Jikin Hajiya Batula ya saki Tayi Jagale Tana Bin Dinar da wani kallon Kurulliya bata dai ce komai ba Jininta ya Diba ya Tafi Dashi Lap dinsu na Asibiti yace Nan da Lokaci kadan zai Dawo da Sakamakon. Faruwar Haka yasa Zakiya ta kama Dina ta Haura da ita saman Dakinta ta kwantar da ita kan Gado sai ga Hajiya Batula ta Shigo Gegen Dinar ta Zauna Tana Fadin'"Sannu Dota..? Allah kara afuwa..' Dina ta amsa Tana yamutsa Fuska Zakiya na gefe Tayi Tagumi kamar ta Allah kallonta Hajiya Batula tayi Tana Fadin"Kinsan Abunda ke Damunta ne..? Tafada tana Kafe ta ido Domin haka kurum Taji bata yarda da ita ba,Shuru Zakiya Tayi bayan sun Hada Ido da Dina sai taSunkuyar dakai Tana Fadin'"Anty Mu jira Dawowar Doctor...! Tana Gama Fadin haka ta kauda kai Domin bataso ta Fara mgana yanzu sai Likita ya iso da Sakamako Uwa uba kuma Daddy ya Dawo anan ne Zata Bude Baki Tayi mgana Sosai,Hajiya Batula Numfashi ta Sauke kawai ta mike tana Fadin"Allah yasa muga alheri."Basu amsa mata ba Har ta Fice Tana Fita Dina tace"Meyasa baki gayamata komai ba..? Zakiya tace"Ba yanzu ba...Sai Likita ya kawo Sakamako in Tagani ita zata Kira Daddy ta gayamai Shi kuma zai Dawo Gida a Rude Daganan ni kuma zanyi Mgana..'Kai kaawi Dina ta kada Ta maida kanta Bisa Filo ta kwantar Tanajin wani Fargaba Na Abunda zai Faru in Daddy yaji Labarin Abunda ya Faru. Dr.Bala sai da yayi wajen Awa Daya kana ya Dawo Hajiya Batula kadai ya gani afalo Ita ya Mikama Takardan Ta karba ta Bude Tana Fadin"Nifa ba gane wannan yaren naku na Likitoci nake ba Yimin Bayani Dr Bala..? Kallonta yayi Cikin Wani yanayi kafin yace"Am sorry to Say Hajiya..Dina is Taking 5weeks Pregancy..! Ido Hajiya Batula ta Zaro Tana kallon Dr.Bala kafin ta saki Takardan HannuntaTana Fadin"Ciki Kake mgana..? Kai ya Gyada mata yana Fadin"Eh kwarai..Tana da Ciki na Tsawon Sati Biyar Harda kwanaki..! Kirji Hajiya Batula ta Dafe Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna Illaihirraju"un...Munshi uku wannan Wani irin Bata suna ne Dina ta Jawo mana..? Tafada lokaci Daya Taji kanta na Sarawa Dr.Bala dai kawai Jinjina kai yake yana Fadin"Sai Hakuri Hajiya.."Numfashi ta Sauke Tana Fadin"Biri yayi kama da Mutum..Dr Bala plz Wannan mganar ya zama Sirri Kar naji ta Fita waje..? Mirmishi yayi yana Fadin"Haba Hajiya ai Famiy Doctor...Ba iya Likita ba ne Abokin Sirri ne Karki Damu a aikin mu Ba"a yarje maka ka bayyana Sirrin wani ba.."Cikin Gamsuwa tace"Naji Dadin haka...Mungode.."Daga haka taSallameshi ya fice ita kuma Kai Tsaye ta Rarumi Takardan zuwa Dakinta Wayarta ta Jawo ta Kira Kwamishina Alhaji Gaddafi Sheerif,Lokacin suna Meeting bai Daga Kiranta ba sai ta Turamai sakon ya Dawo Gida Ba Lafiya Daganan ta Fito a gaggauce sai Dakin Dina tana Shiga ta watsa mata Farar Takardan kan Jikinta Tana Fadin"Yanzu Fisabillahi Da Kuruciyarki baki Debomana Abun kunya ba Dina sai da girma ya kamaki..? Tafada Tana kallonta Cikin Wani Takaichi da Bakinciki Domin koda Dina ba yarta bace Taji Hankalinta ya Tashi da jin Wannan Labarin,Dina ta Dago kanta Tana kallon Hajiya Batula kafin ta waiga Tana kallon Zakiya wacce ta gyada mai kawai sai Dina ta Fara matsan kwallah Tana Fadin"Ba laifina bane Anty..Yaudarata yayi..! Hajiya Batula ta saki baki kawai Tana kallonta kafin tace"Daman kinsan da Cikin kenan..? Da Sauri Zakiya tace"Eh..Jiya ne ta Kira Bata da lafiya sai nazo na Rakata asibitin Datake aiki aka Dibi Jininta aka auta,Shine yake sanar damu Tana Da Shigar Ciki na Sati5 da wasu kwanaki.."Tafada Cikin Nuna alhininta cikin Kufuluwa Hajiya Batula tace"Lalle...Shine kuma sai kika kwasio ta ita da Abun kunyar zuwa nan ko..?ina laifin ku Tsaya chan anemi Uban Cikin..Tunda nasan ta sanshi ko nace ko sun sanshi.." Ta Karishe Fada Cikin Bacin Rai Zakiya ta Dukar da kai Tana Fadin"Ita ta matsa sai na kawota Gida...Kuma nayi Tambayar Duniyanan taki Fadamin ko waye yayi mata wannan aiki sai dai tayi ta kuka Tana Fadin Yaudaranta akayi.."Wani Dogon Tsaki Hajiya Batula Tayi kafin tace"Ita dai ta Yaudari kanta..Irin Abunda nayi ta Guda kenan,Da naga Alhaji ya sake ma Rayuwar yarinyar nan Dama na sani ita Mace ba"a sakar mata sai tazo da Abunda zai Bata Zuru"a gabadaya.."Daga Dina har Zakiya ba wanda ya kara mgana Ficewa Daga Dakin Hajiya Batula Tayi Tana Fadin"Sai mu Jira Dawowar Mahaifinki kila Shi in ya Tambayeki zaki mai bayani inda kika Samo Cikin Jiki ki..Aikin Banza kawai..! Sai da ta Fice ne Dina Ta mike zaune Tana Fadin"Nifa ina Jin Tsoro Zakiya..? Ina Tsoron Faruwan waniAbu.."Zakiya ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Dole daman Wani Abu zai Faru mana..Ammh ba yadda kike Tunani ba..Ki kwantar da hankalinki ina Tare dake.."Ita dai Dina Hankalinta yaki kwanciya komawa kawai Tayi ta kwanta Tana Tunanin wannan Abunda sukeyi ba wata Hanya bace ta Rusa Rayuwarta data iyayenta ba kuwa..? Da wani ido zata iya Kallon Daddy da Dan Shege...? Wannan Shine Sakamakon Irin Gata Da kaunar da ya nuna mata kenan...? **** Zain Da ya bar gidansu Gidan Dina yasake Komawa yana Ta Bugawa kamar wani Mahaukaci Sabon kamu,Yakira Lambar Dina Sau Shurun matsaki Bai san Adadi ba,Ganin ba mafita yasa ya Shiga Motarsa kawai ya Dinga yawo acikin gari bai san ina zashi ba Idanuwansa sun kala sunyi Jajir so yake yayi kuka ammh ya gagara haka kurum yaje wani irin Faduwar gaba yana jin akwai wani gagarumin Mtsala Dake Tunkararsa. Yayi ta Tunanin meyasa Dina tayi mai haka..?meyasa ta saba alkawari..!? Tuni wata Zuciyar ta an karar dashi Tayi hakan ne Domin Bayyana komai,baya Raba Daya Biyu Dina Kano Ta Tafi..? Tuna haka yasa sai da yaji wani Gigitaccen Faduwar gaba mai Dauke da wasu Rugajewar Abubuwa ajikinsa,Gabadaya ya Fita Hayyacinsa,yana ji yana gani ana ta Kiran wayarsa yaki Dagawa Firstlove tana ta Kiranshi Yana kallo Zata Tsinke ammh ya Kasa Daga Kiranta..? Da wata kalmar zai  mata mgana..? Me zai ce mata..? Ayanzu bai da wani irin Kalma ko Mgana da zai iya kare kansa komai kuma ya kare mai..! Yana ganin Kiran Sadiq Babba,Shima ya kasa Daga Kiransa,Kansa ke Ciwo kamar ya Cire ya yar haka yaje ji Ganin zama ba nashi bane yasa kawai ya yanke Shawaran zuwa kano ya Nemi Dina,Har ya Juya kan Mota sai kuma wata zuciyar tace"wannan karon wannan yakin bazai yuyu kai Kadai ba zain..Koma Miye Shirin Dina na Tozartakane ko kaje kano ka sameta ba Lalle bane ta Saurareka..Ya zama Dole ka nemi Taimako ko agaji. ! Sitiyarin Motarsa ya Buga Cikin Muryan kuka yace"Wayyo kaichona...Yanzu Wa zan Tunkara da wannan mganar..? Wazan iya Tara na gayamai nayi ma Wata Ciki watan ma karuwa ba Matar Auransa na Sunna ba.."Yake Fada yana kuka Kamar karamin yaro ammh kuma ba Digon Hawaye saboda Tsabar Halin Dayake ciki. Kamar amafarki ya Dakata da kukan Da yake yi Lokaci Daya yana Fadin"Haddir...! Yes Haddir ne kadai ya Chanchanta naje ma da kukana Shi kadai ne zai iya samamin mafita.."Da sauri ya karya kan Mota sai Asibiti kamar wanda ya Zare,yana Tafe yana Kiran Layin Haddir wanda Tana gabda Zata Katse Haddir ya Daga Kiran yana Fadin"Zain ya akayi ne..? Cikin Shakewar Murya yake Fadin"Kana cikin Asibiti ne..? Cikin Mamaki Haddir yace"Eh lafiya naji muryanka wani iri..? Batare da Zain ya kara mgana ba ya Katse Kiran Daga bangaran Haddir kuwa wayar yabi da kallo yana mamakin Jin muryan Zain din Cikin Damuwa Da Dimuwa ba yadda yake ba ganin baida wanda zai bashi amsa ne yasa ya ijiye wayar ya Cigaba da Duba patient dinsa yana yi yana Dubaa gogon domin Jirgin da ya Dauko Inna Hannatu karfe 12:30pm zai sauka ta Kirashi Tun jiya ta gayamai zai zo Filin Jirgi ya Dauketa. Haka ya Shiga Cikin asibitin kamar wani mahaukaci Sabon kamu Wayarsa ma amotar ya barsa,Haka Ma"ikatan asibitin keta mai sannu da zuwa suna gaisheshi ko tan kowa bai bi ba,Kai Tsaye Office din Haddir ya isa Bude Kofar ma Da yayi ba Cikin Hayyacinsa yayi ba Haddir Dake Zaune ya gama Duba patient din karshe Domin zai Fita ne Sai ga Zain ya Shigo. Cikin mamaki Haddir ya Dago yana kallon Zain Wanda ya kariso Gabansa batare da Tunanin komai ba ya Zube gaban Haddir Lokaci Daya da kama Kafarsa yana Fadin"Na Shiga uku Haddir...Haddir na kashe kaina..Naki jin mganarka najin Shawaranka Dan"uwana yau gashi Dalilin Rashin Jin mganarsa yakai ni ga Fadawa wani Bala"i wanda nake jin kunyar kaina da Abunda na aikata.."Yake fada yana sakin Muryansa gabadaya cikin kukan da ba Hawaye. Mamaki da al"ajabi ya Sandarar da Haddir Dake zaune da Sauri ya Janye kafarsa yana kallon Zain Cikin Tarin Tamboyoyi ya mike yana Fadin"Subhanallah Zain lafiya..? Meya kefaruwa..? Yafada yana Dago Kafadun Zain Daga Zaune zuwa Tsaye kawai sai ji yayi Zain ya Fado Jikinsa yana wani makyarkayata kamar wanda Shooking ke jansa Cikin Wani irin Faduwar gaba Haddir ya Rikesa yana Fadin"Zain meya faru.?Kasani Cikin Rudu ka gayamin Abunda ya Faru don Allah..! Sakinsa Zain yayi kafin ya Riko Hannayensa Duka Biyun yana Fadin"Haddir na jawo ma Zuru"armu Abun kunya Abunda kake gujemin ne ya Faru Dani...Ni zain yau aka wayi gari nayi mata Ciki...Ciki fa Haddir Ciki na Haihuwa nayi ma karuwa ba Matata ba.."Ya karishe Fada yana wanin Kamar ya Kwanta akasa yayi ta Birgima yana kuka. Ido Haddir ya kwalalo Waje yana Fadin"Ciki...? Wa kuma kayi ma Ciki Zain..?ya fada yana Girgiza kafadansa Cikin Fitan Hayyaci Zain yace"Eh Ciki dai Daka sani na Haihuwa..Ciki nayi ma Dina Haddir ni da kaina..Kaichona.."Baya kawai Haddir kawai ya fara ja yana kallon Zain Lokaci Daya yana Nunashi da Yatsa yama kasa mgana Ganin haka yasa Zain ya Duke kansa yana Sakin Kuka kawai Kamar wani karamin yaro. Haddir kuwa sai da ya Dangana Da Bango ya Dafa  kana ya iya Tsayuwa,Kansa ya Dafe lokaci Daya yana Maimaita"Hasbunallahi Wani"imal wakil...Allahuman Ajirni musibatihi...! Yake ta maimatawa yana Dafe da kansa Cikin Fitan Hayyaci ya Dago yana kallon Zain lokaci Daya yana Fadin"Dina..? Daman baka Rabu da Shedaniyar yarinyar nan ba Zain..? Innalillahi Shiyasa nake gaya maka Ka Rabu da ita ka rabu da wannan Shashanci Saboda gudun irin wannan Ranar Zain yanzu wa gari ya waya..? Ya fada yana kallon Zain Shima Hawayensa sun cikamai ido kamar ya saki kukan Zain dake Zaune Dirshan a kasa ya Dago Yana kallon Haddir yana Fadin"Bansan Dalili ba..Ban kuma san ya akayi haka ba..Ko ina son Rabuwa da Dina sai naji na saka Wlh Har ga Allah ba"a son Raina nake Tarraya da ita ba Haddir ba"a son Raina bane ka yarda Dani..! Haddir ya kalleshi Cikin Bakonciki Da Takaichi yace"Komai ya Faru kai ne Sila Zain...Tun farko Addininka ya Hanaka Kusantar ZINA kai kuma ka Kusanceta..Tunda ka Fara ta kaji Dadinta baxaka iya bari ba nasha Fada maka ka kori yarinyar nan Daga asibitinan ta bar garin ta koma garinsu kakijin mgana ne Abunda nayi ta Gujemaka ne ya Faru dakai..Yanzu ta ina zamu Tunkari wannan Mummunar kaddaran Data Fadomana..? Da wani ido Zamu kalli Danginmu da iyayenmu da wannan Labarin Mara Dadin Ji..? Yafada yana Share Kwallar da Suka zubomai,Zain kuwa kansa ya Dafe yana Ta Jijjigawa yana Fadin"Kaichona na Cucu kaina..Na Biyema Rudin Abokai da kuma Shedan na Fada ga Halaka Hakika Duk wanda ya maida Zina Abun kawansa ya Jira Ranar da Zata Zama Silan Shigansa wani Bala"in da bazai iya Fita ba..Ya zanyi Haddir..? bani da kowa sai kai kai ne kadai Hop dina yanzu ka Fadamin Taya zan Tunkarin wannan matsalan Data Tunkaroni..? Yafada jijiyoyin kansa Sun Bayyyana Muryansa taDisashe saboda Tashin Hankali. Batare da Haddir yamai mgana ba ya Juya ya Tunkari Kofa ya Murza Makulli ya Kulleta kana ya Dawo ya Dago Zain Daga kasa zuwa kan kujera ya zaunar Dashi kana ya zauna gefensa yana Fadin"Kaddaran ta Riga ta Faru Zain...yanzu sai dai muyi Kokarin Rufa wannan mganar Yanzu ina ita Dinar.? Cikin Jujjuya kai Zain yake Fadin"Bansani ba Haddir..Bansan ina Take ba.."Cike da Mamaki Haddir yake kallonsa yana Fadin"Bangane baka sani ba..? Cikin Damuwa da Nadama Zain ya Fara bama Haddir Labarin Abunda ya Faru Daran Jiya Har zuwa wayewar gari yau ya kara Da Fadin"Nayi ta Kiran wayarta a kashe...Gidanta kuma makotanta sun Tabbatarmin tayi sammakon Fita Haddir Ji yadda Zuciyata take Bugawa ina jin Kamar wani Abu Dina take Shiryawa akaina..'" ya fada yana Dora Hannun Haddir a saman Kirjinsa yana jin yadda kowani Dakika take Bugawa Haddir ya janye hannunshi Yana Fadin"Ba kamar kana ji ba..Tabbas ta Shirya wani Abune..Abu kuma da bazai mana Dadi ba Dukkanmu."Zain ya Dago Araunane yana Fadin"Kamar wani Abu kenan..? Haddir yace"Bansani ba..Ammh ina Zargin Da gangan ta bari komai ya Faru..Ta Shirya Fasalla mganar Cikin nan ga Su Abba ne nifa atunanina.."Zain ya Mike Zumbur yana Fadin"Ina..? Bazai sabu ba Haddir..Bazan bari Dina Tayi min Wannan Illar ba..! Yake Fada Kamar wani Zautattace,Haddir ya mike ya Rikosa yana Fadin"Wannan Surutan duk ba mafita bane...Ka zauna mu samu mafita.."Da wannan kalaman ya samu Zain ya koma ya zauna Shima sai ya koma ya zauna yana Fadin"Kasan Gidan kawarta din nan..? Kuri Zain yayi mai da ido kamar mai Tunani  kafin Da Sauri yace"Kana Nufin Zakiya..? Da sauri Haddir yace"Bansani ba..Wannan dai kawar nata dai Da suke Tare I think Zakiya din ne Sunanta.."Da Sauri Zain yace"Kssh...Sai yanzu na Tuna da ita...Ammh bansan gidanta ba sai dai Nasan a inda Take aiki.." Da Sauri Haddir yace"Ina ne..? Zain yace"Kamfanin Sadarwa ta Layin Mtn...Office dinta na Babban Heaquater dinsu ta nan garin.."Batare da wani Tunani ba Haddir ya mike yana Fadin"Tashi muje..Na Tabbata ko kowa bai san inda Dina Take ba Ita ta sani.."Ba Gaddama Zain yabi bayan Haddir suka Fita Tare Sauri Sauri Gudu gudu suka isa Haraban Asibitin amotan Haddir suka Tafi Mintina ashirin da wani Abu yakai su Ma"akatan su Zakiya sai dai suna Shiga ciki suka Tambayeta aka Tabbatar musu da yau batazo aiki ba ta Dauki Excuse zata tafi Ganin Gida kano Sai Monday zata dawo ana Fada musu Haka Zain ya Rike Haddir yana Fadin"Na gayamaka..Sun Shirya wani Abu.." yake fada kamar zai Fadi Saboda Tashin Hankali Haka Haddir ya Rikosa zuwa Mota sai da suka Fara Tafiya kana Zain ya Dago Daga Kansa yana Fadin"Menene Abunyi Haddir..? Im mukayi Jinkiri Asirina zai iya Tonuwa..? Haddir ya Sauke Numfashi yana Fadin"Tabbas...Ita da kawar nata suka Shirya komai ni Tsorona Daya bansan Ma"nar Abunda Suka aikata ba kuma ina Jin Tsoron wani tsari ne Tsarinsu na Gaba.."Zain dai ba baki sai Numfashinsa Dake kokuwa kafin yace"Mu Tafi kano kawai Haddir...Mu Je chan mu samesu sai ayi wacce za"ayi..' Cikin Jinjina kai Haddir yace"A ina zamu sameta..? Zain yace"Gidansu mana..?Haddir yace"Zata je gida awannan Halin kake gani..? Shuru Zain yayi kafin yace"Muje dai...Gidan kwamishina ba boyayye bane..In bata nan sai mu samu Wata Hanyar ammh ina kyautata Zaton Tana chan.."Kada kai kawai Haddir yayi Daidai Lokacin da Wayarsa ta Dauki Tsuwa yana Fito Da ita Daga Aljihu ya waro ido yana Fadin"Kai...Abokiya Zareena Ta zo Nageria..! Da sauri Zain ya kallesa yana Fadin"In jiwa..? Wayarsa ya nuna mai yana Fadin"Gashi ta Kirani da Lambarta na Gida ba na chan U.s ba.."Dakyar zain ya iya Hadiye wani Miyau mai Daci Shi kuma Haddir ya Daga Kiran yana Fadin"Abokiya me zan gani haka..?badai kin Diro Ba Labari ba..? Dagachan Bangaran Zafeera Dake Falon Gidansu Su Saudat  sun Zagayeta,Umma na Zaune kusa da ita rike da Takwaranta Jalal kuma na Kan Cinyar Nene Bakinta Har kunne tace"Eh mana So nake na baku mamaki..Gani afalon su Umma gasu ma kusa dani Dana Sauka nayi ta Kiran Lambar Aboki Zain Tana Ringing bai Daga ba Kawai sai na Kira Abba ya Turo Direba ya Daukeni Daga Katsina nake Tun Shekaranjiya muka sauka Nida Abba Jalal yana chan sai an kwana Biyu zai Bullo..' Haddir yace"Masha Allah..Sannu dazuwa..Zain kuma Muna tare dashi Wayarsa ya barta amota gamu nan zuwa muyi Sannu da zuwa dakyau asha Hirar yaushe gamo.."Tana Dariya tace"Yauwa Abokaina na Hakika ina Jiranku.."Daga haka suka katse Kiran Zain yana kallon Haddir bai samu Zarafin mgana ba yace mai"Zuwan mu kano yau baazai yuyu ba sai dai Mu Jira gobe..? Cike da Tashin Hankali Zain yace"Saboda..?ammh kasa."Bai ida mgana ba wayar Haddir ta Kara Daukan Tsuwa Cikin Dafe kai yace"Innalillahi ai na Sha"afa.."Zain yace"Mun Shiga uku menene kuma..?Haddir yace"Wlh Inna Hannatu ta Kirani Tun safe tace min gata zata Hawo Jirgi nan da 12:30pm nazo Filin Jirgi in dauketa..' Ido Zain ya kwalalo waje yana Fadin"kuma..? Me hakan ke Nufi Zafeena tazo ga Inna Hannatu ma zata zo Haddir..?Haddir na Shafa kansa yana Fadin"Bama ita kadai ba..Kowa dakowa zai zo Zain..Akwai Gagaruman mtasala kuwa indai Hasheshena ya zama gaskiya.." Cikin Fitan Hayyaci Zain yace"Bangane kowa da kowa zai zo ba..?kai tsaye Haddir yace"Ina Tunanin gobe Asabar din Karshen wata..In lissafina yayi daidai wannan watan Shine Watan Taronmu na Family kuma kasan wanchan watan ya Kamata ayi ba"a samu yi ba ina Kyautata zaton Gobe ne za"ayi Zaman.."Dafe kai kawai Zain yayi yana Fadin"Qalu inna Lillahi..Haddir na Mutu Shikenan Asirina zai Tonu Wlh.." Shima Haddir Yana Cikin Tashin Hankali ya kalli Zain yana Fadin "Bari muje mu Dauko Inna Hannatu Daga Filin Jirgi Allah zai kawo mana mafita.."Daga haka  Haddir yaja Mota Suka Nufi Mallam Aminu International Airport. Suna Zuwa suka iske Har Inna Hannatun tasauka sai Fada take tana Fadin Tana Kiran wayar Haddir bai Daga ba Haka ma Zain,Saboda Tana Fadan ne yasa Bata Fahimci basa cikin Natsuwarsu ba har gwara ma Haddir ya Tattaro Natsuwar Zain kuwa Zaro ido kawai yake yana kifta idanuwa Jira kawai yake ace kyf ya zura da Gudu. Gidan Alhaji Tsoho suka kaita Suna Shirin kara Zillewa tace sai sun Shigar mata da kaya Domin kaf a Ya"yan Alhaji Tsoho da ita da Baban kaduna ne mafadata,Suna Shiga Zain yaci karo da Zainarsa Cike da mamaki take kallonsa tana Tambayansa bai Tafi Gomben bane..? Ganin Baya Cikin Natsuwarsa ne yasa Haddir ya Bata amsa da bai samu Tafiyar ba Abun ya bata mamaki ganin Firstlove baya ma iya Hada ido Da ita kamar Alhaji Tsoho ya sann Suna Cikin Uzurin son Tafiya ya Hanasu ya Zaunar dasu yana gaya musu Gobe akwai Taron Family Duka iyayan nasu suna Tafe Inna Rukayyah ma Tana Tafe Daga kano Haka ma Baban kaduna da Mom Iklima Da Daddyn Abuja da Mama Safiya Da Hamdiya zasu zauna kan mganar Auran Hamdiyan daya Taso watan Gobe ne,Zain bai kara Jin Sagewar Gwiwa ba sai da yaga Sadiq babba ya shigo nan yake gaishesu tare da Shaida musu Dazu shima ya Shigo garin yazo gida yayi Hutun Sati Biyu ya koma Alhaji Tsoho nata Murna ganin Jikansa Haddir da zain sai dai suka kalli Juna kawai Kowa da Abunda yake sakawa Sai da Alhaji Tsoho ya gama Jawabinsa kana ya barsu suka Fita suna Fita basu koma ko"ina ba sai Cikin asibitin Office din Haddir din suka sake komawa Suna Kulla yadda zasu Bulloma wannan al"amarin Dake Tunkaransu Dirshan zain ya zauna yana kukan Haddir ya Taimakamai kada Asirinsa ya Tuni Ya bashi Tsausayi matuka kuma Har ga Allah baya Fatan wannan mganar ta fasu a kunnuwan iyayensu ko bakomai ya zama Silan Rufama Dan"uwansa asiri. **** Dina kuwa Da Fara Nadaman Biye ma Shawaran Zakiya Domin  Lokacin da Kwamishina ya Dawo Gida yaci karo da wannan Labarin sai da ya Kusa Fadi haka ya Zube gaban gadon Dina yana Jijjigata yana Fadin"Dina..?me kika nema kika Raasa..? Wani irin gata ne ban baki ba..? Wata irin Soyayya Uba ce ban baki ba..? Harda ta uwa na Baki Dina na Hana Dangin mahaifiyarki Daukanki Saboda ina sonki Ina son na baki Dukkan gatan Duniya..? Yanzu da Kanwar mahaifiyarki Maimunatu zata Zo sati mai zuwa Da wani baki zan mata wannan bayanin..? Na baki ilimi Na ingantan Rayuwarki saboda kada kice na zama mai Takura gareki ashe wannan sakewar har yakai ki kwasomin wannan Abun kunyar dina.? Nifa Dan Siyasa ne da wani ido kuke so na kalli mutane in wannan mganar ta Fita waje..? Ya karishe Fada Cikin zubar Hawaye Ita kanta Dinar kukan take Hajiya Batula ma sai da ta Share kwallah Zakiya ce kadai batayi kuka ba Cikin kuka Take Fadin"Kayi Hakuri Daddy..Plz Forgive me.Ba laifina bane Wlh Yaudarata yayi da Kalmar zai Aure ni ya lalatamin Rayuwa Shine kuma Daga baya yace sai dai azubar da Cikin bazai Aureni ba Shine na Gudo Gida.." Ta fada Cikin gunjin kuka Gefe Daya na Zuciyarta Tayi Rauni ganin Daddynta nakuka Hajiya Batula tace"Dama wani Namijin arziki ne zai yi Lalata da mace kuma ya aureta..? Ai Shima macen kwarai yake nema kinyi Kuskure Dina.."Kwamishina ya mike Tsaye yana Share Hawayensa ya kalli Zakiya yana Fadin"Wani asibiti kika kaita Kafin kuzo nan..? Cikin Ladabi Ta saka Hannu Cikin Jakarta Ta Dauko Farar Takarda Ta mikamai Tana Fadin"Asibitin Da take aiki ne Daddy....Gama sakamakon awajena.."Karba yayi ya Duba na wani Lokaci kafin ya Hada da wanda Dr.Bala ya Bada ya Tusa Cikin aljihunsa yana Fadin"Taga yamiki wanda yayi mata wannan Zaluncin..? Cikin Makirci Zakiya tace"Nayi nayi da ita Taki gayamin Daddy.."Tafada kanta na kasa Cikin Tsawa Kwamishina ya Kalli Dina ya Daka mata tsawa yana Fadin"Kimin Shuru anan wajen ki Fadamin wanda yayi miki wannan Abun kunyar..? Tsorata Tayi Tafara ja da baya zuwa Wajen zakiya Ita kuma Zakiya Fadi Take"Dina ki Fadama Daddy ko waye..Na Tabbata zai kwato miki yancinki na Zalunci da yaudaranki da yayi da kalmar zai Aureki yayi Miki Ciki kuma yake neman ya sake Jefaki ga Halaka.."Tafada Har tana matso kwallah Jin Haka yasa ta Fara Shesshekan kuka Tana Fadin"Likitan ne asibitin Dana ke aiki..! Kwamishina yace"Waye sunansa..? Waye kuma Ubansa a kasar nan..? Kan Dina na kasa tace"Sunansa DR ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA...! Tafada tana Rufe bakinta Waro Ido Zakiya tayi Tana Fadin"La Dr.Zain kike nufi..?Kai Dina ta Daga mata sai ta Fara Tafa Hannu Hajiya Batula tace"Kinsan shi ne..? Kodai wannan Saurayin da Dina take matukar so ne..? Da sauri Zakiya tace"Shine Wlh Anty...Tun suna London suke Soyayyah Tunda makaranta Daya Sukayi nasha cema Dina Ta Rabu Dashi ba Auranta zai yi ba sai tace Yace zai Aureta asibitin ma Datake aiki shi ya bata aikin fa asibitin mallakin Kakansa ne Dr Saulawa dake Garin Bauchi..' Hajiya Batula tace"Nifa banga laifinsa ba laifinta ne..Don Namiji yayi ma mace alkawarin Aure sai akace ta bashi Jikinta yayi yarda yaga Dama..?kwamishina ya Dago yana kallon Hajiya Batula kafin yace"Batula koma Miye Bai isa yaci Bulus ba...Na yarda Dina nada laifi Shima yana Dashi Saboda Haka Tunda ya Riga ya bari Haka Ta Faru..Wlh Tallahi ko Zan rasa Mikamina sai na kwatan mata yanci..Ke Zakiya kunsan gidan yaron..? Da Sauri Zakiya tace"Eh Daddy ai gidansu ba Boyayyen Gida bane agarin Bauchi kakansa Dr.Abubakar Saulawa yayi suna sosai.."Kai tsaye ya kada kai yana Fadin"Ku Shirya gobe daSafe zamu tafi Chan Bauchi zan je na gaya musu Abunda D'ansu yayi ma yata in ma basu sani ba gobe zasu sani..Batula kema ki Shirya dake zamu tafi sai Excort dina guda Biyu saboda Sirri yau ma Domin Anjima ina da ganawa da gwamma ne da a Daran nan zamu Tafi garin Bauchin..' Yana gama Fadar haka ya Fice Daga Dakin Kamar zai Tashi sama Hajiya Batula ta mara mai baya Suna Fita zakiya tatashi ta Rufe Kofar tazo ta Rumgume Dina Tana Fadin"Ina Tayaki Murna kin kusa samun Cikar Burunki..!. Wata Dariyan Farinciki Da Nishadi Dina tayi kafin tace"Da farko na Karaya..Ammh yanzu naji Kamshin na zami matar Zain..ammh kuma wani Fargaban Zakiya Shegiyar Firstlove din nan nashi zata yardada mganganunmu kuwa balle har ta Rabu Dashi..? Ta fada Tana kallon zakiya wacce ta Mike tana gyara zaman mayafin Kanta Lokaci Daya Tana Fadin"Karki damu da ita Tuni nagama da ita..Zatazama Comfuse mana Na wanda ka yarda dashi Fiye da kowa aduniya yaci Amanarka..Ammh Zan aika mata da Abunda Dole zata nemi karin bayani ni kuma zan gayyato inda zata ji gaskiyan komai kinga Daga Lokacin Zata ji Zain din yagama Fita Daga kanta Indai ita macece wacce ta amsa Sunanta..." Dina tace"Bangane Nufinki ba..? Zakiya ta Dauki Jakarta Tana Fadin"Ai Ba zasu zo Taji wannan mganar ba..Zasu yi Kokarin Rufa mganar kada Taji..Ammh ni zan gayyatota har zuwa Gidan kakan nasu da suke ji Dashi nayi Miki alkawarin aagaban Idonta zamu Fallasa Komai...Kin manta kin samo min Lambarta Awayar zain..?Hade kuma da aikin da na sakaki..? Kai Dina ta Daga mata Cike da mamaki Dariyan Mugunta Zakiya ta saki Tana Fadin"Ai Duka Shirin nata ne..Domin Ba lalle bane in wanchan Bomb din ya Fashe ba"a gabanta ba Mganar Daga bakin wasu Tayi mata Tasiri..Zata yi Tasiri ne Daga bakinki Da kuma Shaidunmu.."hannu kawai Dina ta Bata suka Tafa Tana Fadin"Aikin SS ya dace Dake Zakiya ba aikim kamfanin Sardawa ta Layi ba..". Dariya kawai Zakiya tayi mata kafin tace"Zan tafi Gida na kwana Dina..Saboda kinsan komai lalacewar gida gidanku ne kuma Tunda Tsoho nada Rai Bari na Leka Duk da wanchan Watan na Lekosu.."Dina ta kada kai Tana Fadin"Da safe kenan zaki Dawo..? Zakiya tace"Da yardan Allah.."Sallama sukayi Kana Zakiya ta Fice Koda ta sauka Kasa bata ga kowa kawai sai ta Fice Daga Gidan Security suna ganinta suka Bude mata get ta Fice Da Motarta Motar Dina kuma Tana kano Gidan Wata kawarta Teema suka kai Motar Dina Ajiya Tun Jiya Saboda kada Barinta ya bata musu plan dinsu. *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             1️⃣6️⃣ "Zakiya iyayenta suna zaune a anguwar gadon kaya ne,Mahaifinta Mallam Nuhu Talaka ne mai Rufin asiri Tunda Sana"ar Dinkin Surfani na Hannu yake Da Saida Zaren Dinkin kala kala Tun yana da Samartkansa. Shago garesa a kofar gidansa Inda yake gudanar da Sana"arsa,Bayan Rasuwar Mahaifiyar Zakiya Adama Ya kara Auran Wata Samira yar garin Danbatta ne,Bayan ita ma ya kara Auran wata Lubabatu suna Kiranta Luba ita yar nan garin Kano ne, a kofar wambai. Mahaifiyar Zakiya yar asalin Kauyen Minjibir Dake kano ne,iyayenta ma ba masu Hali bane Kuma Dukkansu yan kauye ne Shiyasa bayan Rasuwarta da Mallam Nuhu ya hanasu Su Dauki Zakiya su maidata chan Minjibir din sai sukayi Fushi suka Fita Batun Zakiyar basu kara waiwayarta ba itama bata Damu ba Tunda ba wani Abun hannu garesu ba Uwa uba kuma Tana ganin ci baya ne ta koma Kauye da Zama. Sai ta tashi Hannun Kishiyar Uwa Samira irin mugayen Matanan nan ne da basu Dauki Ya"yan Kishiya ya"ya ba Dalilin ta shi yasa Zakiya ta Fara kangarewa,Da kuma Shigarta prine Collage da Haduwarta Da Dina lokacin Mallam Nuhu na Zamaninsa da Dinkin Surfani Shiyasa Zakiya tafi Sauran ya"yansa samun Ingancin Rayuwa mai kyau. Mtslanta Da Mahaifinta ya samo asali ne da Samarin da Zakiya ta Fara mu"amala dasu na Banza,Wannan Motan tazo ta Dauketa wannan ta Sauke sai manganganu suka Fara yawo kan Yana ganin Zakiya zata lalace bazai Dau mataki ba Da Zugan Samira yayi amfani yace In Zakiya ta gama Babban Sakandiri zai mata Aure ita kuma tace Bata so karatu zatayi,Rigima tayi Tsanani Har ya sako Dangin Mahaifiyarta Adama aciki Har zuwa sukayi suka samu Zakiyan suka mata Fada ammh Tace ita karatu zatayi ba Aure ba Ran Mallam Nuhu ya baci yace Taje duk inda zata ammh bada gwabonsa ba da wannan Dalilin Taje ta samu Dinar da kukanta itakuma ta Share mata Hawayenta ita ta Taimakamata ta Biya Jamb ta zana kuma taci Dayake duk Iskancinsu basu wasa da karatu Barin ma Zakiya Da take ganin Bayan karatu bata da komai Bariki bai sa ta sakar ma karatu ba Taana da Burin ta tsaya ga kafafunta wata Rana ABU zaria Tana daga Cikin Inda Ta nema kuma ssi gashi ta samu Bata Nemo kowa ba sai Dina Ita Tayi mata komai sai dai ita ta Rigata Tafiya Lagos inda ta Fara karatu kafin ta Wuce lagos,Ita kuma Zakiya sai Daga baya ta wuce Zaria Bayan ta gama Hada Abubuwan da zata Bukata wajen abokan Shashancinta Domin Zakiya Tun tana SS2 ta san Tabama Namiji Jikinta ya Biyata kaso mai Tsoka Gidan ma Datake Zaune azaria Cikin Samarinta wani ya kamata Zuwanta Zaria da Shigarta Jami"a Shiya Kara Sauya Zakiya Idanuwanta suka Bude tayi kawaye na Banza Dana arziki anan ne Takara sanin Rayuwa sanari kuwa ba adadi Tayi na Arxikin kuma Tayi na Banzan Kawayenta na nan Zaria suka Fara koya mata Harka da malamai kuma Tunda ta Fara take jin Dadin Haka zakiya ta kama kudi Sosai Wajen Abokan Shashancinta Shiyasa Har ta gama karatunta Sisin Mallam Nuhu bata Taba nema ba Shi kuma ya kawo ido ya saka mata. Zakiya Tana da kanne mata Sunfi Shida,kuma dukkansu sun yi Aure Tunda ba karatun suke ba,Bayan Tagama karatu ta Samu aiki a Bauchi Shima da Taimakon Mahaifin Dina kwamishina Gaddafi Sheerif,Ta tattara ta koma chan da zama bayan ta mallaki gidan zama da Motar Hawa In taje gidansu sai dai Tayi awa Daya zuwa Biyu,ta koma Bayan ta kawo musu kayan Abinci da kudi Mallam Nuhu baya karba sai ya kalleta yace"Zakiya ina Fatan wannan kudin bana Shanshancin kibane kika kawomin ba ko..? Yau ma Data iso Gidan Hakan ce ta Faru Tsskaninsu Bayan Ta Shiga Dakinsa sun gaisa Da zata Tashi Ta ijiye mai kudi a gabansa Tana fadin"Gashi Baba ku kara acefene..! Sai Tayi Dariya Tana Fadin"Ko Daya Baba..Daga cikin Albashina ne..."Sai kawai ya kada kai yana kallonta yana Fadin"Zakiya yanzu ina amfani ga wannan Rayuwar da kika Daukan ma kanki..? Kinga ma karatunki kin samu aiki me zai Hana ki nemi ko Cikin Abokan Shashancin naki ne kuyi Aure .? Mirmishi Tayi ta sadda kai Yana Fadin"Haba Baba meyasa kake Damuwa ne..?Aure fa wani Lokacin in baka yi sa"a ba Duk Wahala ce baga su Sahura ba Sunyi Auran ammh Suna Cikin Wahalan Rayuwa ba, yanzu da karatunsu sukayi irin nawa da Suna Tsaye ga kafafunsu Baba...! Carbinsa kadai ya Cigaba da ja yana Fadin"Ban taba la"antanki ba Zakiya kuma bazan Taba ba..Akullum Tsakanina Dake addu"an Shiriya ne Allah ya Shiryeki Zakiya.."Cikin Mirmishi Tace"Shiyasa nake sonka Babana..Ameen ya Allah..Bari na Koma ciki.."Dakai kawai ya yi mata mgana Har tatashi ta Fice ya bita da kallo yana mata Fatan Shiriya Tun zakiya na zuwa ana Gulmar ta zama karuwa Taje chan wani gari da Sunan aiki Tana iskanci tayi kudi ta sai Mota Har akazo aka Daina Domin Mallam Nuhu ya Toshe kunnansa ne Fatansa Allah ya Shiryeta yasa Ta gane Rayuwar da Takeyi ba Rayuwa bace. Tana komawa Cikin Gida Dakin Luba ta sauka Daman nan take Sauka Tunda ita take Rawan Jiki da ita Saboda Kwadayi ita kuma Samira Daman basa Shiri da Zakiya Tun baya ballatana yanzu da Girma ya kamata,Samiran ma ya"yanta Biyu an sakosu suna gabanta Zakiya bata Damu ba,Haka ta saki kudi Luba tayi lafiyayen Girki sukaci Ita dai Zakiya bata ci ba, tea ta Hada tasha ta kwanta kan Katifar da Luba ta mata Shinfida. ******* Haddir da Zain sun gama Tsaida mgana kan sai gobe da Safe zasu Tafi kano,Gidan Abba Suka koma Tunda Zafeera nata Kiran waya tana Korafin Bata gansu ba Duk wanda yaga Zain sai yasan wani Abu na Damunshi baya Cikin Natsuwarsa chan suka kara ganin Zaina dama Ta gayama Zain Zata wuce gidan Umma,Yace mata Toh. Ita kanta Zareena Ta Fahimci Wani Abu Haddir ta kalla Tana Fadin"Aboki Haddir meya ke Fauwa da Aboki Zain ne..? Naga ya Zama wani Shuru Shuru ne wani Abu ya Faru ne...?Haddir ya Juya yana kallon Zain wanda ya kura ma waje Daya ido kawai Daga ganinsa Baya Cikin Natsuwarsa. Yake yayi mata Lokaci Daya yana Dafa Zain din yana Fadin"Bakomai...Strees ne na asibiti.."Jin haka yaasa Zain ya Fahinci Abunda ke Faruwa Shima yake yayi wanda bai kai Zucci ba,Zareena dai bawai don ta yarda ba sai don Taga Basu san gayamata,Zain kuwa duk iya Kokarinsa na Kada agane yana Cikin Wani hali sai da aka gane Haka Nene ta Tusashi Cikin Daki Tana Tambayanshi meke Damunsa..! Ammh ya kasa Furta komai ba amsa Dayan ce Bakomai nan suka kai Dare Har Abba ya Dawo Daga Gidan Alhaji Tsoho Shida Baban kaduna Suka Shigo da Mom iklima Da Mama Safiya da suka Biyoshi zasu kwana gidan su Umma. Nan fa su Umma suka Fara maraba Da baki,Zain fa Hankalinsa ya Tashi Komai ma ya Riga ya kwacemai Haddir ne ke Zugurinsa in gaya yayi Tagumi ya Shiga Dogon Tunani,Sai wajen 10pm na Dare suka Rabu da Haddir Shi kuma Ya Dauki Zaina zuwa Gida,bayan sun yi Dinner agidan Umma wanda Zaina tana Lura da zain abinci ma Tsakura kawai yake yi batare ma Dayaci ba. Suna Cikin Tafiya Zaina sai kallonsa Take ganin sai Sakin Numfashi yake sama sama Tunda Suka Shiga Mota bai iya cemata komai ba Driving kadai Yake ammh Rabin Hankalinsa Baya Jikinsa Gefe Daya kuma yana ta gwada Kiran Layin Dina da Koda yaushe ake cewa akashe,Mamaki ya Cikata ganin kamar Baya cikin Natsuwarsa ne yasa  a sanyaye tace"Firstlove..! Waigowa yayi yana kallonta Batare da yayi mgana ba gyara zama Tayi Tana Fadin"Firstlove meke faruwa ne... ? U Look so silent.."Maida kansa yayi Ga Tukin Dayake yi kafin ya Sauke Numfashi kawai batare da yayi mata mgana ba Har ta Fidda rai Taga ya Riko Dayan Hannunta ya Damke Dayan kuma yana Tuki Dashi Cikin wata karyayiyar Murya ya Kira Sunanta..! "Halima..."Abunda ya bata mamaki Ita Tunda Take dashi Baza tace Tataba jin ya kira Sunanta na Gaskiya Halima ba Sai dai Firstlove ko Zaina,Ammh jin yau ya Kira sunanta da wannan Murya yasa Jikinta yayi Sanyi Cikin Damuwa da Faduwar Gaba tace"Na"am Firstlove mene..? Tafada Idanuwanta na Cikowa da kwallah Sai da ya juyo ya kalleta kana ya maida Hankalinsa kan Tukinsa ya Fara mgana Cikin Raunin murya"Halima wani Alfarma nake Roko awajanki Don Allah.! Cikin mamaki tace"Wata alfarma ne Firstlove..Na Dauka Tsakanina Dakai ba alfarma.."Cikin Dakiya yace mata"Akwai ta mana..Akwai Alfarma Zainata..! Yake Fada yana waniCije baki kamar ya Fashe da kuka yaje ji wata Zuciyar na ingizashi ya gayamata wata kuma na Hanashi kawai sai ya Bige da cemata"Don Allah kimin alfarman kowani Laifi zan aikata miki komai Muninsa kada Kice zaki barni...Wlh Tallah Na Rantse miki Da Allah ke kadai nake so kuma nake kauna..Kada ki barni Saboda wani kuskure nawa..In kika Barni Rayuwata zata Tagayyara kuma Bazan Taba Gafartama kaina ba.." Ya karishe Fada yana jin wani iri Rauni acikin Zuciyarsa Tun kafin yagama mganarsa ta Fashemai da kuka Cikin Rawan Jiki yake kallonta yana Fadin"Don Allah ki bar kukan nan Firstlove kukanki na sakani naji kamar zan Rasaki ne.." Dagowa Tayi Tana kallonsa Cikin Hawaye da kuka tace"Nima Haka nakeji..Zuciyata tana rawa Firstlove...Nakasa gane wani Hali nake ciki.."Take Fada Cikin kuka Daidai Lokacin da suka iso Gida Hon yayi Tanimu maigadi yazo ya Bude musu suka Sulala Ciki ya iso wajen Motan yana ta Barkwancinsa Daya saba sai dai wannan karon Ko ita Zainar bata kalleshi ba Tana Bude Mota ta Nufi Cikin Gida Tana hada Hanya,Shima Zain din ya Rufa mata Baya Abun sai ya Daure ma Tanimu maigadi mamaki ya Rike baki yana Fadin"Komai miye Allah ya Saukakashi..! Da gudu yabi bayanta Atare suka Shiga Falon suna Shiga ya Fizgota ta Fado Jikinsa Sai kawai ta kara sakarmai kuka ta kamkameshi tana Fadin"Nima bazan iya Juran rasaka ba Firstlove...Da kai kadai Zuciyata da gangan Jikina ta saba Rasaka Tamkar rasa wani Shashi na Jikina ne..Wanda kuma in bashi bazan iya Rayuwa ba.."Yana jinta in Tana mgana sai yaji kamar ya Duka gabanta ya gayamata komai ammh kuma sai yaji ya kasa Idanuwansa sun kala sunyi jajir yana Cikin Babban Tashin Hankalin da bai Taba Riskan kansa aciki ba. Ranar kwana sukayi suna gwadama Juna wata irin Soyayyah mai wuyar rubutawa,Ranar Zain bai ji ya gaji ba,ita kanta Salon da yake mata ya bata mamaki kamar irin wanda zai barta na wasu Shekaru,ga yagamata kalaman yana Sonta ba adadi ya kuma gayamata Duk duniya ita kadai ce yafi yarda da ita Fiye da kowa Daga karshe ma kuka ya saka mata yana Fadin bazai Taba iya cin Amanarta da gangan ba ta Tsorata Ta Fara Tunanin wani abu ya Faru ko kuma yana Shirin Faruwa,Sai Wajen 3 na Dare dukkansu suka samu Barci Sallar asuba ma agida yayi ta domin Haka kurun yau din ya Tashi yana jin kamar bashi ba Ita kanta Zainar Jikinta yana Sanyaye ne ga wani Faduwar gaba Dake damunta Tun kwana Biyu da suka Gabata. Karfe 7am na safe Zain ya samu Kiran Alhaji Tsoho inda yake gayamai ya Tabbatar da Shi da Halima sun zo Taron da zai Gudana agidanshi Cikin Hadiyan Miyau yace zasu zo ammh Zaina sai Ta Shiga makaranta zata kai Assigment ne kuma lacran yace Individual yake Bukata Shi kuma sai yayi mai karyar zai Shiga Cikin Asibiti Ya Duba patient ya gama Dasu zai zo Shidai Alhaji Jadaddamai yake ya gansu awajen kana suka yanke Kiran Tunda lokacin komai nashi yake Sukuku Zaina ta taimakamai yayi wanka ya Shirya itama ta Shirya Tunda Shi zata Bi Motarta ta lalace tana wajen gyara,Breakfast ma Dakyar ya yarda Ta Turamai Fadama yake bayajin Cin komai har ta Fara Tunanin ko Bashi da lafiya ne yace mata Kada ta Damu Lafiyansa kalau. Suna Mota zai kaita makaranta Kiran Haddir ya Shigo Wayarsa Dama ajiyan sun Rabu kan kada Zain ya Kirashi shi zai kirashi Da kanshi da Sauri ya Daga Kiran Shi kuma Haddir yace mai yana Cikin asibiti yazo ya Sameshi da Rawan Jiki ya amsa mai gudu gudu ya karisa da ita Cikin Makaranta ya ijiyeta Abunda ya bata mamaki ganinsa a gaggauce yau ko bakin Department dinsu bai kaita ba ya ijiyeta wai yana Sauri ne har ya bace ma ganinta Tana Binsa da kallo Haka kurun Take jin Tsinkewar Zuciya Jakarta ta saba ta Fara Takawa da Kafa Zuwa Department dinsu ammh Cikin Zuciyarta sam ba Natsuwa Tana Jinta kamar ba ita ba. Aguje ya Shiga Cikin asibitin yana Faka Motarsa sai ga Haddir ya Fito Daga Cikin Asibitin yana gyara zaman Suit din Dake Jikinsa Motarsa kawai ya Nufa yana Fadin"Shiga muje...Ya kamata muje mu dawo kan Lokaci Kafin Alhaji Tsoho ya Farga Damu.."Zain najin haka yaDauko wayarsa Ya zare key din Motarsa ya Rufeta kana ya Zagayo ya Shiga ta Haddir wanda yana Shiga ya Tasheta suka Bar Cikin asibitin Hanyar kano Suka Dauka Lokaci Daya Haddir na Fadin"Ka sameta..? Zain na Dafe kansa yace"Ban sameta ba..Tun da muka Rabu nake Kiran wayarta..Amsan Daya ne akashe take.."Haddir yayi karamin Tsaki yana Fadin"Kashe wayar ma wani Tsarinta ne..Nidai Fatana Allah yasa in mun isa kanon mu sameta agida Komai zai zo da Sauki In muka sameta.."Jin jina kai kawai Zain yake yama kasa Mgana Daka ganshi zaka Fahinci ya Riga yayi Laushi da Rauni. ****** Abunda su Zain basu sani ba Lokacin da suka Dauki Hanyar kano Lokacin Tuni Babban Jeep din Kwamishina Ta Tsufa kan Hanyar zuwa Bauchi Tun safe,Dagashi Sai Hajiya Batula sai Dina Su Waleed Da Waleeda agida aka barsu Tare da Zulai,Sai a Gaba Direbansa da Escort dinsa Guda Daya Sai Zakiya Dake Motarta ita ke gaban Bisa Tsarin ita zata musu Jagora zuwa Gidansu Zain din *10:00am...* *Falom Alhaji Tsoho..* Falon Alhaji Tsoho cike yake da ya"yansa da Matansu da Kuma Wasu Daga Cikin Jikokinsu irin su Hamdiya da kuma Sadiq babba,Baban Kaduna,Dadyn Abuja,Abba suna zaune waje Daya asaman Cafet din Daya mamaye Falon na Alhaji Tsoho Gefe kuma chan Umma ce da Mama Safiya sai Mom Iklima da Nene Daga yammah kuma Inna Rukayya ce da Inna Hannatu Chan kuma Daga Farko Sadiq ne Zaune Sai Zareena Dake gefensa Ita Da Jaririyarta Jalal yana gida Wajen Zainab suna ta wasa dasu Junior,Daga gefen Alhaji Tsoho kuwa Hajiya Mama ce da Hamdiya Dukkansu suma zaune saman Cafet din Sai Alhaji Tsoho kadai Dake saman kujeransa yadan Mike kafa saboda Ciwo Sandar sa na Gefensa yana Bin kowa da Kallo. Kafin afara Taron sai da yace a Kiramai Zain da Haddir sai dai kuma anyi Rashin Sa"a Suna Daji Lokacin Motarsu ta lalace musu Shiyasa akayi ta Kiransu ba"a samu ba,Ran Alhaji Tsoho ya baci Domin Dukkansu sai da ya Sheda musu Duk Taron da suke Gudanawa basa samun Hallata wannan kuma yana Sha"awarsu a wajen ko bakomai Su din Ababen alfaharinsu ne. Ganin yadda ya Damu ne Baban Kaduna yace"Alhaji Tsoho kayi Hakuri...Kila suna Cikin asibiti ne Wani Uzuri ya Rikesa ammh ka kwantar da Hankalinka kafin mu Tashi zaka gansu.."Da wannan kalaman Zuciyar Alhaji Tsoho Tayi sanyi ya Umarci Dadyn Abuja ya Bude Taro da Addu"a Haka kuwa akayi bayan ya Bude Taro da addu"an Alhaji Tsoho ya Fara Jawabinsa kamar ko yaushe Nasiha ne da kuma Tunatarwa kan su Hada kansu kana ya gangaro kan su Rike aman junansu dana Matansu su kuma yi Adalci A tsakaninsu Ya"yansu kana ya Gangaro Riko Da Zumuncin Dake tsakaninsu su zama Tsintsiya Daya madaurinsu Daya ko Da watarana Baya Raye Wata Baraka bazata Bullo a tsakaninsu ba,sai ya gangaro kan mganar Auran Hamdiya ya kuma Yi mgana da Kakkausan Murya kan Zafeera game da Mai sonta Barrister Ahmed yace tunda asan Nagartan yaro bai kamata azauna ana Biye mata Kamata yayi iyayenta Maza Baban Kaduna da Daddyn Abuja suyi wani Abu akai shi in yayi wata mgana ya"yansu zasu ga kamar yana matsa musu ne,Sai kuma yayi mgana kan Haddir da zamansa Har yanzu bai yi Aure ba kuma sun saka Ido Sunki cewa komai. Baban Kaduna ne ya Fara mgana Bayan Alhaji Tsoho ya gama Jawabinsa ya Dora da mai Alkawarin zasu kiyaye wannan zumunci kana Daga karshe yace"Game da mganar Zafeera Da Haddir...Ka bamu Lokaci Alhaji Tsoho kafin Taro nagama zakaci Labari mai Dadi.."Daddyn Abuja yace"Insha Allahu.."Shima Abba ya Tofa albarkacin Bakinsa haka ma su Inna Hannatu Daganan kuma sai suka karkata kan Bikin Hamdiya Dake gabansu sun yanke Shawaran anan Bauchi Za"a Daura Dauran da Bikin Gabadaya Tunda Kaduna Hamdiya zata zauna wani Navy zata Aura,Inna Hannatu ce ta Fara kawo mganar azo nan ayi Bikin Sai Baban Kaduna yace Shu bai ga Fa"idar haka ba gwara atsaya chan ayi wannan mganar tajawo cuceku cikin Falon Matansu dai sunyi Shuru Tunda wannan ba Fagensu bane,Alhaji Tsoho na zaune yana kallonsu bai kuma katsesu ba. Ana Cikin Haka ne sai ga Sallamar Megadi Daga bakin Falon Sadiq ne ma yaji Sallaman ya amsa ya tashi ya Leka nan Megadin ke Shaidamai agayama Alhaji Tsoho Yana da Bako yace ace mai kwamishinan Ilimi ne Alhaji Gaddafi Sheerif. Mamaki ya kama Sadiq sai dai kuma Bai yi mamaki ba sanin Kakansa ai ba Boyayyan Mutum bane,Komawa yayi Cikin Falon Har Gaban Alhaji Tsoho ya Duka ya gayamai Shuru Alhaji Tsoho yayi yana Nanata Sunan kwamishina Kafin ya kada kai yace yamai Jagora ya Shigo,yana Fita Alhaji Tsoho ya yi gyaran Murya yana kallon ya"yansa Lokaci Daya yana Fadin"Ku Saurara..Yanzu Abubakar yazo ya gayamin ina da Bako awaje..Kwamishinan kudi na Jahar kano.." Gabadayansu Da mamaki a Fuskarsu Suke kallon Mahaifin Nasu kai ya Jinjina musu yana Fadin"nace amai iso...Ku Mata ku Tashi ku Shiga ciki har muji damai yazo.."Ba gaddama suka mimmike zuwa Cikin Falon Hajiya Mama,Suna Shiga ba Dadewa Sai ga Sadiq ya Shigo da Sallama Bayansa Kwamishina Alhaji Gaddafi Sheerif ne Yaci Riga da wando na Shadda Harda Babban Riga Bayansa kuma Hajiya Batula ne Cikin Shigar alfarma sai Excort Dinsa wanda Kwamishina yabama Izinin Komawa waje Gabadaya su Abba mikewa sukayi na alamun Girmamawa Kafin suma gama mamaki sai ga Zakiya ta sawo kanta Falon Dina na Binta Abaya Cikin Shigar Abaya ta Nannade mayafin Bisa kanta. Gabadaya kallo kallo kawai ake ma Juna Alhaji Tsoho ya yanke Shurun da yima Kwamishina Maraba Har gabansa ya karisa ya mikama sa Hannu sukayi musabaha Lokaci Daya da gaisaawa Gefensa nan kasa Kwamishina ya zauna ayayinda Hajiya Batula dasu Zakiya suka yada Zamansu kan Kujerun Dake Falon suna kallon Ko"ina suma su Abba komawa sukayi suka zauna Sadiq ma bai Fita Shima ya samu Waje ya zauna. Alhaji Tsoho ne ya kalli Kwamishina yana Fadin'Naji mamaki da aka sanar dani Kai ne Bako ne..Ina Fatan lafiya.? Kwamishina ya gyara zama yana Fadin"Eh Toh Lafiya ba lafiya ba..Kamar yadda ka sani Sunana Alhaji Gaddafi Sheerif Wannan kuma Matata ce Hajiya Batula sai Yata Dina da kawarta Zakiya.."Yafada Yana nuna Kowa da Hannunsa Alhaji Tsoho Dasu Abba suma suka Bisu da kallo. Gyada kai Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Masha Allah...Sannunku da zuwa.."Hajiya Batula ce kadai ta amsa Dina da Zakiya kansu suka maida kasa,kara gaisuwa akayi Suma su Abba Suka yi Hannu Da Kwamishina aka gaisa Cikin Girmamawa. Alhaji Tsoho ya Kalli Sadiq yana Fadin"Abubakar Shiga ciki kace Tabawa Ta kawo kayan Motsa Baki da Ruwa.."Da Sauri kwamishina yace"A"a Akoshe miki Mungode.."Alhaji Tsoho yace"Ayi haka..? Annabi ya koyamana Girmama Bakon mu..". Kwamishina yace"Hakane..Ammh kafin nan bari mu fara gabatar da Abunda keTafe Damu..Dina Dago kanki.."Yafada yana kallon Dina Wacce kanta ke kasa da Sauri ta Dago Kanta Tana Fadin"Na"am Daddy..."Kai Tsaye ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Ka ganeta..? Alhaji Tsoho ya kalli Dina da Zakiya Sosai Gashi yana so kamar ya ganesu ammh kuma sai ya rasa ina ya sansu Su Abba ma kallonsu suke sudai Tabbas sun Shaidasu,Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina Lokaci Daya yana Fadin"Kayi Hakuri..Kasan Jikin Tsufa Kila ko na Taba ganinsu yanzu na mantasu gaskiya.." Kafin kwamishina yace Wani Abu Baban Kaduna ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Alhaji Tsoho Ka manta ne,Sune wadanda suka zo gaida kai Lokacin da ka kwanta asibiti,Har Haddir yake Fada maka Ita wannan Din Tana aiki a asibitinmu Dayan kuma Kawarta ce..." Ya karishe Fada yana Nuna su Mirmishi Alhaji Tsoho yayi yana Fadin"Anyi Haka kuwa...Na Sha"afa kwarai har ma suka Fadamin Sunayensu,Gashi Har sunayen nasu ma ya Shigemun.."Yafada yana Yar Dariya Kwamishina ya Kalleshi yana Fadin"Wannan ce Yar Tawa Sunanta Dina...Sai kawarta Zakiya..' Alhaji Tsoho yace"Ba Shakka Sun Fadamin Sunayensu..Masha Allah Sannunku da zuwa..."Suka amsa da yauwa kafin Alhaji Tsoho ya maida Hankalinsa kan Kwamishina wanda ya gyara zama yana Fadin"Dama Abunda ke Tafe dani Abu ne mai muhimmanci Ganin Dukkanmu ba yara bane Naga kafin Komai ya Biyo baya yakamata nazo na sameku mu Tattauna na Sanar Daku Abunda Dan'ku ya aikata ma yata in ma kunsani Toh ku kara sani in ma baku sani ba Na sanar daku..! Yafada yana kallon Fuskokin su Abba da su Baban Kaduna,Suma Kallonsa suke Cikin Rashin Fahimta Baban Kaduna ne ya Bude baki yana Fadin"Wani irin Abunda Dan'mu ya aikata..? Wani.." "Bashir..."Yaji Alhaji Tsoho ya Kira sunansa ya Dago yana kallonsa Cikin Umarni yace"Karka kara mgana sai na baka Umarni.."Kai ya Jinjina yana Fadin"Shikenan.! Juyawa Alhaji Tsoho yayi ga kwamishina yana Fadin"Ina Jinka..Wani aiki Daya Daga Cikin ya"yan nawa suka aikata maka..? Kwamishina ya karkace ya saka Hannu a aljihu ya zaro Takardu guda Biyu,Daya sakamakon Cikin da Dr Bala ya basu ne Daya kuma wanda Dr.Imran ya basu Zakiya ne ya Mikama Alhaji Tsoho Karba yayi Yana kallonsa Cike da karin Bayani bai samu zarafin mgana ba Kwamishina yace"Daya Daga Cikin Ya"yanka ko Jikan kane yayi ma Yata Ciki gata nan Zaune..! Da sauri Zakiya tace"Jikansa ne ba Dan"sa ba Daddy..!. Kwamishina ya gyada kai yana Fadin"Duka dai zakiya Daya ne..! Dam...Dam! Haka gaban su Abba ya Fadi Alhaji Tsoho kuwa Gilashin Idanuwansa ya gyara yana kallon Kwamishina Lokaci Daya kuma ya maida Hankalinsa kan Takardun Dake Hannunsa yana Nazarinsu Daddyn Abuja ne ya Mike afusace yana Fadin"Ji wata mganar Banza..? Wani irin Ciki kuma sai kace wasan yara Haka kurum kazo da wata mganar ai Daga Ahalinmu anyi ma yarka ciki yar naka Yar Tsana ce da za"aJata amata ciki..! Ya karishe Fada Cikin Kumfar Baki Zakiya da Dina suka kalli Juna Hajiya Batula kuwa acikin Ranta tace"Kuma kwa gani.."Alhaji Tsoho ne ya Dagama Daddyn Abuja Hannun yana Fadin'"Koma ka Zauna Aliyu.." Ba musu ya koma ya zauna Shuru Falon ya Dauka na wani Lokaci Kafin Alhaji Tsoho ya Dago Daga Nazarin Dayake ma Takardun Hannunshi Lokaci Daya yana Fadin'Wanne Daga Cikin Jikokin nawa..!? Kasan suna da yawa..? Kai Tsaye Kwamishina Ya kalli Dina yana Fadin"Ke Gaya mishi Sunanshi.."Dina ta Dago kanta Lokaci Daya tana kallonsu Fuskar su Abba wanda suka Hade Fuska Tamau suna kallonta kafin ta Dirr kan na Alhaji Tsoho wanda Ba"a gane yanayin Dayake Ciki. Cikin Sanyin Murya Ta maida kanta Kasa Tana Fadin"Dr.Z...Zain ne..! Dum! Dum gaban Abba Usman ya Fadi Hakama na Baban Kaduna Tare Dana Daddyn Abuja,Tare kuma da Bugawar Zuciyar Alhaji Tsoho Daidai Kuma da Bugawan Zuciyoyinsu Umma domin Tun Lokacin da Daddyn Abuja ya tashi ya Fada fada sukaji Hayaniya suka Firfito suka Tsaya Daga Bakin Falon Hajiya Mama,Dukkansu Ido Suka zaro waje Cikin mamakin Abunda suke ji yana Shirin Faruwa. Nene ce ta Fizgo kanta Ta Fito Daga Cikin Falon Tana Fadin"Karya ne..Wannan Sharri ne ake so ayi ma Yarona..Zainullahi bazai taba iya ma Wata ciki ba karya ne.." Baban Kaduna ma ya mike Cikim Bacin Rai yana Fadin"Wannan ai ma wata mganar Banza ce wacce Hankali bazai Dauka ba.."Alhaji Tsoho Dai na kallonsu yama Kasa mgana Kwamishina ne yayi Mirmishi yana Fadin"Meyasa kuke gaddama..?ga Shaida nan kuma ku kira yaron naku mana sai ya karya ta gashi gamu da Dinar ko..? Dadyn Abuja ne ya mike yana Fadin"Ba wani mu Kira Dan"mu...Mu mun Riga munsan irin Tarbiyan da muka bama ya"yanmu bama Ya"yanmu bs,Wlh ko Karen gidan nan baazai Taba aikata irin wannan aikin ba..! Hajiya mama kuwa kuka ta Fashe Dashi Tana Fadin"mun shiga uku..? Me Jikana ya Tsare musu suka Biyoshi da wannan Sharrin..? Su Mama Safiya Mom Iklima tuni sun Fada Falon suna Fadin Karya ne wannan mganar ba Abun yarda bane  Barin ma Inna Hannatu da take Fada Tsaye tayi gaban Alhaji Tsoho Tana Fadin''Kwamishan me Alhaji Tsoho..? Mu za" a nuna ma Siyasa me ake jira da ba'a Fattake su ba Har ma sai azauna ana Jinsu suna Fadin karya da Abunda Tunda muke bamu Tabagani cikin Zuru"an mu..! Sadiq ma Ransa ya baci Huci kawai yake yana Fadin"Wannan ai bata suna ne..,Wlh zan iya Rantsuwa Ya zain bazai Taba aikata haka ba.."Umma kuwa da Zaneera da Hamdiya suna Kofar Falon Sun kasa gaba sun kasa Baya Umma wani Jiri Taji yana Dibanta Zareena kuwa sai da Ta Dafa bango TanaJin wani Sabon Tashin Hankali Ita Da Hamdiya haka suka Damke Hannun Juna Suna Sallalami. Hayaniya ta kaure afalon Irin su Inna Hannatu da Baban kaduna Masu Zuciya Kokarin cewa Suke Su Dina su Tashi su bar musu gids ko su kira musu Hukuma Ganin Haka yasa Alhaji Tsoho da Miyan bakinsa ya kafe yayi gyaran Murya yana Fadin"Bashir...Hannatu,Aliyu..Da kowa ma kowa ya samu waje ya zauna..! Jin Haka yasa suka kalleshi da Mamaki kai ya gyada musu Yana Fadin"Eh ku samu waje ku zauna...Mganar da suka zo da ita akwai kamshin Gaskiya aciki..'jin haka yasa Zuciyoyi Da Dama suka Buga Gabbai ya sanyaya sai ki ka ga Daya bayan Daya Suna Zama Umma dai sai da Hamdiya ta Rikota Ta iya zama Nene kuwa da Hajiya kuka suke suna Fadin Sharri ne karya ne. Mirmishin Karfin Hali kwamishina yayi yana Fadin"Ni da fari Yadda kukayi haka nayi..Sai da"a ace ban Nemo Hankalina ba Da Tuni nakai mganar gaban Hukuma ammh Sai Banyi haka ba nacegwara na Fara zuwa na sameku Na sanar daku Kila kuma baku da Masaniyar komai.." Kai Alhaji Tsoho ya Jinjina yana Fadin"Hakane..Kwarai kuma kayi Hikima da Baka sako Hukuma Cikin Lamarin ba Hakan yasa na kara ganin Kimarka Sosai.."Yafada yana Kokarin Boye Halin Dayake Ciki Kafin ya Dago yana kallon Baban Kaduna Ido Cikin Ido yace. "kiramin Zainullahi a wayarka Bashir...! *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*            1️⃣7️⃣ "Gabadayansu ido suka sakarma Alhaji Tsoho Suna kallonsa cike da mamaki Baban Kaduna ne ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Nakira Zain fa kace Alhaji Tsoho..? Gyada mai kai Alhaji Tsoho yayi yana gyara Siririn Gilashin Dake Idanuwansa yace"Eh haka nace ka Kiramin Zainullahi awaya yanzu..Ka sanar dashi Duk inda yake yazo ina son ganinshi.."Yafada Cikin Dattako da kamala Dina da Zakiya suka Rike Hannun Juna alamun Nasara. Daddyn Abuja ne ya Mike yana Fadin"Haba Alhaji Tsoho..Ai bai ma Kamata ka Biye ma wannan Shirmanmiyar mganar ba wacce bata da Tushe ballatana makama ba.Miye Abun Kiran Yaronnmu Mu Tsitsiyeshi kan Abunda zan Iya Rantsuwa bai aikata ba wanman karya ce Tsagwaronta da Bita da kulli kawai ake so azomana Dashi Cikin Zuru"a Domin abata mana Suna.." Yafada yana Kumfar baki Cike da Bacin Rai Baban kaduna da su Inna Hannatu kuwa Jinjina kai Suke alamun Gamsuwa da Zencen Daddyn Abuja,Abba kuwa Zaune yake kawai kansa na kasa yana Kiran Sunan Allah yama Rasa wani Tunani zai yi ko kuma ya Zai Dora Abun akan Mizani. Alhaji Tsoho ya Dade yana kallon Daddyn Abuja kafin ya Saki Mirmishinsu na Manya kawai ya Juya yana kallon Baban Kaduna yana Fadin"Bashir kiramin Zainullahi nace ko..? Umarni nake baka ba Shawaranka nake nema ba..". Yafada cikin Kakkausan Murya Inna Rukkaya Ta Bude baki zatayi mgana ya Daga mata Hannu yana Fadin"In har na isa Daku kada wanda ya kara mgana..Bana so ku zage da yawa Daga baya kuzo kusha Kunya..,Daga yar wajensa Har Zainullahin Duka namu ne Domin Da na kowa ne Mugu sai Mai Shi..Kuma In ba Rami me zai kawo maganar Rami..?bawai Ina da yakinin Gaskiyan Abunda suka Fada bane ammh In babu Gaskiya meyasa sai nan Gidan zasu zo..? Bauchi Tana da Fadi da sai su nemi Gidan Daya fi Namu suna da Asali,ammh kuma Kai Tsayen nan suka zo..Kuma karku manta yarinyar tana aiki Tare dasu Zainullahi a asibiti baku Hango Wani Abu Acikin Wannan Zencen..? Ya karishe Fada yana Binsu Da kallo Daya Bayan Daya,Yana karantar yanayin Fuskokinsu Sai kuma daya Fada sai kowa Jikinsa yayi sanyi,Daddyn Abuja ya koma ya zauna kaawai yana Salati acikin Ransa,Hajiya Batula na gefe Tana kallon Komai Su kuwa Dina da Zakiya Farinciki ya cika Ransu kwamishina kuwa Nadama ce Mai Tsanani ta Shigeshi na yarda ya sake ma Rayuwarsa Da yawa haka in ba Domin haka mai zai kawosa nan da Kimarsa yana Fadar mgana ana karyatasa Kwarai yana Cikin Nadama mai Tsanani. Baban Kaduna ya Fito da waya ya Nemo Lambar Zain ya Kira sai kuma,sai tayi kamar zata Shiga sai ta Dauke Cikin Tararradi Ya Dago yana Fadin"Alhaji Tsoho Layin Zain baya Tafi fa.."Kai tsaye yace"Kira na Hadiru kaji..ko basa Tare shi ya Nema mana shi..' Ba musu ya juya akalan Kiran Zuwa ga Haddir wanda ana Kira wayar ta Shiga ammh har ta katse bai Daga ba Baban kaduna ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho yana Fadin,"Na Kirasa bai Daga ba.."Nan ma kai Tsayen yace"Sake Kiranshi Bashir..Insha Allahu zai Daga Jin Haka yasa ya sake Kiranshi Haddir kuwa Lokacin da Kiran Baban Kaduna na Farko ya Shiga wayarsa yana kan Mashin Ya Shigo garin Bauchi Suna Tafiya Sun Fita Bauchi kenan sun Dau Hanyar kano Wani karfe na Jikin Taya ya Fita Daga Motarsu. Hankalinsu ya Tashi gashi ba Garejin Akusa sai ya bar Zain nan Wajen Motan ya Samu wani mai Mashin Ya Daukosa zuwa Cikin Gari ya Sauka adaidai Garejin da yake kawo Motarsa gyara,Ya Dauko Walet dinsa yabama mai mashin Din kudinsa kenan ya sallameshi Sai yaji Wayarsa na Ringing yana Daukota Sai da Gabansa ya Fadi Daya ga Sunan Baban Kaduna Cikin Girmamawa ya Daga Kiran. Sallama yayi Baban Kaduna ya amsa yana Fadin"Ina ka shiga ne in kiranka baka Daga ba..?cikin Girmamawa Haddir yace"Wayar tana Aljihu ne ban ji kiran Ba Baba.." Baban Kaduna ya Numfasa yana Fadin"Kuna Tare da Zain ne..? Na kira wayarsa bata Shiga..? Wani Rugurugu Haddir yaji Dakyar ya Fizgi mganar yana Fadin"Ehm...Ehm..Muna Tare munzo Cikin gari Daurin Aure...!ya karishe Fada yana Goge wani Zufa Dake ketomai Duk da Iskan Dake kadawa awajen Kai Tsaye Baban Kaduna yace'"Ok Toh kuyi maza ku Dawo Gida yanzu yanzu..Alhaji Tsoho keson  ganinku.."Yafada Daidai Lokacin Da Haddir yaji Muryan Alhaji Tsohon yana kara Jadadda suyi Sauri fa ai Haddir Bai san sadda ya samu Jikin Garu ya Lafe ba yana maida Numfashi Baya Duba ammh Tabbas Ranar Daya ke ta Gujema Zain ce Tazo baya Raba Dayan Biyu Dina ta Fallasa mganar Cikin ga Alhalinsu. Har Baban Kaduna ya gama Hello Hello Dinsa yaji Shuru ya katse Kiran Haddir bai sani ba Zufa kawai ke ketomai Tuni yaji na Maransa ya Daure maimaita Salati kawai yake acikin Ransa yasan kuma ba wata Dubara sai ta Allah Dakyar ya iya Karisawa Cikin Garejin sukayi magana da Mai Garejin Dayake sun saba Yana kawo gyara wajen bayan ya gayamai Matsalan Nan ya bashi Cikin Yaransa guda biyu Daya yana Da Mashin ya Dauki Haddir su biyun suka koma Wajen Motar. Suna zuwa Haddir ya kalli Zain wanda ke jingine Jikin motan Kallo Daya zakamai ka Fahimci baya Cikin Natsuwarsa,Cikin Tsausayawa yace"Bakaniken nan zamu bari anan..Zan bashi Key din Motar in ya gama gyaran motar zai Tukata zuwa Garejinsu Daga baya zan zo na karba.."Cikin Rashin Fahimta Zain yace"Bangane ba..?motar haya zamu samu Zuwa kanon..? Bazai iya kallonsa ba Shiyasa ya Juya baya yana Fadin"Gida zamu koma..Na samu wayar Baban Kaduna kan cewa Alhaji Tsoho na neman mu dagaggawa.."Gum Zain yaji kamar an Bugamai Guduma asaman kansa Cikin Rashin Fahimta ya isa ga Haddir ya Juyo Da Fuskansa yana Fadin"Me kake son Fada Haddir..? Cikin karaya Haddir yace"Banda...Tabbas ammh ina Bakincikin Sanar dakai Dina ta Rigamu...Ina Zargin mganar Cikin nan takai ga iyayenmu..! Girgiza kai Zain ya Farayi kamar wani Zararre yana Fadin"Kai ina..? Karya ne Wlh bata isa ba...Kila dai Kiran na Taron nan ne,kasan Alhaji Tsoho ya matsa fa.."Yafada Cike da kwarin Gwiwa,Cikin son yarda da Mganarsa Haddir ya Gyada kai yana Fadin"Allah yasa hakan.."Zain cikin karaya da Rauni yace'Ameen Daga haka Haddir ya Fara Taran musu Mota sai dai basu samu ba Wajen Minti goma sai bakaniken yace su Jira gyaran bai da yawa yanzu zai gama,sai gashi Cikin Ikon Allah ko Minti Talatin baiyi ba ya gama gyaran Haddir ya Hau ya Bata wuta yaga Komai Daidai 5k ya bashi yace yakai ma ogansu su kuma ya basu 2k,Daganan suka Hau Mashin dinsu Su kuma su Haddir suka Hau tasu Motar suka Juya zuwa Gida Zuciyoyinsu Kowanne yana Saka Abubuwa Dadama. Gudu Haddir yayi sosai Cikin Lokaci sai gasu sun iso Haraban Gidan Alhaji Tsoho Suna Fitowa Daga Motan su da Jeep din da su Kwamishina suka zo da ita suka ci karo Sai kuma Excort dinshi Guda Daya da Mamaki Haddir da Zain suka kalli Juna cikin alamun Tambaya,ganin basu da masaniya Dukkansu yasa suka Nufi Hanyar da zata Sadasu da Babban Falon Gidan na Alhaji Tsoho. Haddir ne agaban Gaba Zain na Biye Dashi abaya cike da karfin Gwiwa koda suka ga Takalma akofar Falon Basu Tsinke ba sanin Duka iyayensu yau suna gidan na Alhaji Tsoho Shiyasa suka Shiga da karfin Gwiwansu Musamman ma Zain,gwara ma Haddir Tsoro ya Shiga Zuciyarsa. Akusan Tare suka yi sallama akuma Tare Duka Jama"ar Falon suka Daga suna kallonsu Lokaci Daya suna Amsa Sallaman nasu Atare yadda Duka iyayen nasu suka Zuba musu ido ne yasa Jikin Haddir kawai yayi sanyi sai kaawai ya samu kansa da kwarema yan Falon kallo Daya bayan Daya zuciyarsa ta Tsaya Cak ne sanda yaci karo da kwamishina da Hajiya batula bai gama Mamaki ba sai da ya sauke ganinsa kan Dina da kawarta Zakiya suna kallonsa Cikin Wani yanayi ai sai Haddir yaji kamar an Dasashi lokaci Daya kuma Yaji kansa ya Sara wanda yasa ya Dafe kansa Lokaci Daya yana Kiran sunan Allah Cikin Rawan Zuciya da Rawan kafa Zain kuwa Da zuciya Daya bai Fahimci Halin da Haddir ya Shiga Ko domin Shima bashi da Natsuwar ne,Wucesa yayi ganin ya Tsaya bai ma Lura da Su Dina ba Idanuwansa kawai iyayensa kadai suke nunamai acikin Falon kai Tsaye Alhaji Tsoho ya Nufa yana zuwa ya Zauna agefensa yana Fadin"Kai Tsohon Likitan nan ka cika Takura Miye kake ta kiranmu baka ya"......! Sauran Kalaman Bakin nashi Sun makale ne sanda ya Dago zai Nuna su Baban kaduna kawai karaf Suka Hada ido Hudu Da Dina Wacce Daman Tunda ya Shigo Take nacin kallonsa Taga in ya ganta ya zaiyi aikuwa yana ganinta sai ya Fara Tunanin Gizon ta ne ya gane da Fari kafeta da ido yayi yana kallonta Cikin Bushewar Miyan Baki kafin ya waiga yana kallon Alhaji Tsoho irin kana kallon Abunda nake gani Sai dai kuma..? Kawarta Zakiya Dake gefenta Dukkamsu suna Jifansa da wani manufukin Mirmishi Kamar wani wanda Wutar Lamtarki taja Haka ya Mike Jikinsa Ko"ina ba inda baya Rawa Idanuwansa ya Rufe Cikin Nuna ta yatsa yake Fadin"Dina..! Kallonsa Tayi Ido Cikin Ido Kafin Tace"Na"am Zain..."Tafada tana wani karkatamai kai Idanuwansa gabadaya sun Rufe ya manta da Wadanda ke Falon ya fara Taku zuwa Gareta Kowani Taku kuma Kirjinsa na wani lugude kamar amafarki Yaji Muryan Alhaji Tsoho yana Fadin"Kai Zainullahi ina zaka..? Maza dawo nan ka zauna..! Yafada Cikin Kakkausan Murya,Cak ya Tsaya sai Lokacin kuma Ya Fara dawowa Cikin Hayyacinsa ya Lumshe Idanuwansa ya kara Budewa yana Bin Kowa Dake falon da kallo So yake ya Gani Da gaske ne Dina ya gani ko Gizon ta ne..? Yakuwa kara ganin Gaskiyan Harda karin Kwamishina da Hajiya Batula,Gabadaya Falon Shi aka zuba ido ana kallonsa Idanuwansa ya Sauke kan Dina kyam kamar an Dasashi Wani Irin Hajijiya ce da wani Taurin Abu yake taso mai kamar zai kadashi Rufe ido yayi ya sake Budewa Still Dai gaskiya ne Tuni yaji Numfashinsa ya Tsaya Cak ya Daina aiki. Cikin Bacin Rai Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fada'Ko baka jina ne..? Cewa nayi ka Dawo nan ka zauna.."zuwa Lokacin Tuni Jikin Su Umma ya gama yin Sanyi da Abunda zain yayi wannan ya nuna akwai wata akasa atsakaninsa,,Nene kuwa kai kawai ta Sadda Tana jin Duk Wata gabarta na Saki Haddir ne Daya ga Ran Alhaji Tsoho ya baci ga Zain kamar baya Cikin Hayyacinsa yasa ya Daga kafarsa Da yayi masa Nauyi ya isa ga Zain din ya Rikosa yana Fadin"Muje Alhaji Tsoho na Kira..! Kamar wani karamin yaro ya Juya yana kallon Haddir lokaci Daya Yana Fadin"Kaga Abunda Idanuwana suke ganemin kuwa afalon nan Haddir..? Cikin Wani irin kunya da Nadama Hade Tsausayi Haddir ya gyada mai kai yana Fadin"Eh nagani Zain..Yanzu ba Lokacin mgana bane muje ka amsa Kiran Alhaji Tsoho.." Karyansa kuma ta karse yau..Haka Zain yake Fadi acikin Ransa Har suka isa Gaban Alhaji Tsoho wanda ke Binsu da kallo Cike da Nazari Cikin Dakiya Haddir ya Zaunar da Zain Kusa da kafafun Alhaji Tsoho Shima ya koma ya zauna Gefensa kansu suka maida kasa Haddir Nata Kiran Sunayen Allah ayayinda Zuciyar Zain Tana Daina ma Bugawa bakinsa kuwa Motsi yake ammh kuma baisan me yake Fada ba. Gyaran Murya Alhaji Tsoho yayi kafin ya Daga Dayan Takardan Dake Hannunsa yana Fadin"Wani Likita ne ya baku wannan Shedar acikin asibitin Saulawa Spealist..?ya fada yana Kallon Dina Wacce Cikin Ladabi ba alamun Damuwa tace"Dr.Imran ne Ranka ya Dade.."Atare gaban Haddir da zain ya kara Bugawa kuma atare suka Dago suna bin Takardan Dake Hannun Alhaji Taoho Da kallo Sai dai Daga nan Basa Fahimtar komai Zain Dai kafe Dina kawai yayi da ido yana kallonta da Tambayar ni zaki ma Haka Don Kutumar Ubanki..? Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Kai Hadiru kasan wani Dr.Imran a asibitinku..? Cikin Sanyin murya ya Daga kai ba mgana Alhaji Tsoho yace"Toh Tashi..Kayi maza ka Dauki Mota kaje asibitin ka Taho min Dashi nan yanzu.."Daga shi Har zain sai da suka kara kallon Alhaji Tsoho aammh ganin yanayinsa yasa Basu kara marmarin kallonsa ba Da Sauri Haddir ya mike yana Fadin"Toh Insha Allahu. ! Da Hanzari ya Fice Daga Falon Har yana Hada Hanya yana Fita Baban kaduna ya Kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Alhaji Tsoho zaman me meke haka ne..? In zain ne gashi ya iso ka Tambayeshi ya gayamaka gaskiyan mgana Atashi wannan Taron mara amfani kowa ya kama gabashi.."Wani Mirmishi Takaichi kawai Alhaji Tsoho yayi kafin yace"Yaro Yaro ne...Yaro man kaza ne.." Yana Fadin Haka ya koma ya Gintse Ransa kawai yana Bin Zain da kallo Cikin Takaichi Da Bakinciki Wanda ke Fitowa Daga kasan Ransa Duk da bai da Wani Sheda kan Zain bai aikata wannan Fasadin ba ammh kuma alamun Rashin Gaskiya da Kamshin Gaskiya sun bayyana Garesa sai dai kuma Koda Hakan ta kasance yayi alkawarin kamanta gaskiya ga Duka Shashen Insha Allahu. Har Haddir yaje asibiti ya Dauko Dr Imran Alhaji Tsoho bai kara mgana su Inna Rukayya ne ma ke Cecekuce,Dina kuwa da Zakiya Zukatansu kamar Farar takarda Saboda Fari,Zaim kuwa Tunda Haddir ya Tafi yana nan zaune inda yake Motsi mai karfi ma Bayayi kansa na kasa Baya ma Marmarin Dagowa saboda yadda Kowa na Falon ke jifansa da Wani irin kallo wanda ke kara Tsinkamai ya"yan Hanji. Shigowar Haddir da Dr.Imran ne yasa Falon ya Dau Shuru gaban Alhaji Tsoho Suka Rusuna Dr Imran ya gaisheshi ya amsa Cikin kulawa kafin Dr.Imran yace"Ina cikin Office Dina Sai ga Dr.Haddir yazo ya sameni da cewa Ka umarceshi Dayazo ya Daukoni kana Nemana..Allah yasa Lafiya Ranka ya Dade..? Alhaji Tsoho Ya muskuta yana Fadin"Eh hakane...Karbi nan.'ya fada yana Mikamai Takardan Dake Hannunsa wanda keda Tambarin asibitinsu wanda kuma Dr Imran din ya basu Sakamakon Cikin Dina ajiki Da Sauri ya Gani na wasu sakwanni kafin ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho bai samu Zarafin mgana Alhaji Tsoho ya katseshi da Cewa"Ka gane wannan Takardan..?. Dr Imran Dagowa yayi yana Bin Mutanen Falon da kallo sai alokacin Yaga Dina da Zakiya Cikin mamaki ya ke kallonsu da Neman karin Bayani Ido Kawai zakiya Ta kadamai Cikin Takaichi Inna Hannatu tayi Tsulum Tace"Kai Shashasha...Tambyarka akayi bawai an ce ka juya kana kallon wasu ba..! Tafada Cike da Takaichi Cikin Wayancewa ya waiwayo yana kallon Alhaji Tsoho Lokaci Daya ya gyada kai yana Fadin"Eh Tabbas..Ni da kaina na bada ta  ta Shekaranjiya da yammah..' Alhaji Tsoho yace"Kai kayi Test din..? Nan ma kai ya Girgiza yana Fadin"A"a Bani keda alhakin wannan ba nidai Dina da kawarta Zakiya  gasunan sunzo sun Sameni kan Dina Bata da lafiya na Duba Toh Bisa Tambayoyin da nayi mata ne sai na Fahinci kamar Gwajin Ciki ne ya Dace da ita nan kuma take na Dibi Jininta na kai Lap dinmu na Basu suka Gwada kuma suka Fitar da wannan sakamakon.." Yafada Cikin Fargaba da kuma Tunanin meyake faruwa..? Kowa yaji Abunda ya Fada Cikin Hikima Alhaji Tsoho yace"Ka Tabbata wannan sakamakon na gaskiya ne..? Kai Tsaye Dr.Imran yace"Wlh Allah kenan..Wannan Sakamakon Gaskiya ne..In ma baku yarda ba sai akoma asibitin akara gwadawa a gani"Alhaji Tsoho ya Dagamai Hannu yana Fadin"A'a Ba Bukata ai ka Rantse..In ma karya ka Fada kai da Allah..Mungode..Kai Hadiru bama Abubakar Key din Motarka ya maidashi..' Ajiyar rai ya Sauke yana Fadin"Nagode Ranka ya Dade.."Daga haka ya mike yana Tafiya yana waiwayansu su Dina kamar zai Fadi Dina kai t kauda zakiya kuma Fari kawai ta mai ido alamun zamu gamu,Yana Fita Sadiq Daya karbi Key din Mota hannun Hadir yabi bayansa Ya Daukesa ya maidasa Har suka isa Dr.Imran kansa na Kulle ya Tufka ya warware ammh yakasa gano Bakin zare yaso ya Tambayi Sadiq  sai dai Rashin Samun Fuska yasa Ya kama Bakinsa.. Dr Imran na Fita zakiya ta Fito da wayarta Tana ma Dina Rada Tana Fadin"Yanzu Wasan zai Fara Daukan Dadi..Bari na Karisa Dayan aikimn."Mirmishi Tayi mata Cikim Kwarewa Ta Shiga Wsop dinta bayan ta Bude Data Ta Lalubo Lambar Zaina wacce Dina Ta Sato mata awayar Zain Tunda Wayarsa bata da matakan Tsaro,wasu Bad pics Take Turamata wanda Dina ta Daukesu ita da Zain cikin yanayi mara Dadin kallo Wajen guda Goma ta Tura mata Sai da Ta Tabbatar daya Shiga kana ta Fita Taje Bangaran Sakoninta ta Lalubo lambarta ta Tura mata sako Kamar haka...! *Kina Bukatar sanin wani Abu game da wanda kika bama Amanarki Da Duka yardanki..? Toh in dai kin Ci karo da Sakon nan ki Bude Data dinki ki Shiga Wsop zaki ga na Tura Miki da sako..!* Na Farko kenan na Biyu kuma sai Tace *Nasan zaki Shiga Rudu da Dimautuwa ko..?Kina kuma neman Karin Bayani..? Toh zaki sameshi Cikakke Harda ma wadanda baki sani ba..Kiyi Hanzari Kizo gidan Kakanin Mijinki zaki samu Duka Amsoshinki yanzu yanzu...* Tana Gama Tura mata da Ta Tabbatar da ya shiga sai ta Kashe wayar Dama Sabon Layi ta Siya Kuma saboda wannan amfanin Tana gamawa ta Taka Kafar Dina Tana Fadin"All D Plan Done..Sai Abu Daya kawai ya Rage Tabbatar da Auranki da zain.."Tafada tana wani Juya ido Dina batayi mgana ba ammh Ranta kamar Farar Takardan Saboda murna bangaran Alhaji Tsoho kuwa Dr Imran na Fita Alhaji Tsoho ya Juya yana kallon Kwamishina yana Fadin"Kayi Hakuri fa...Bawai don ban yarda da Abunda Kazo min Dashi bane..A"a ko Daya sai Domim kada mu zama Wasu Mutanen da Marabansu da Dabbobi kadan ne..Ko miye ya Tunkaromu mu Maida Hankalinmu mu Bincika in mun Gano Gaskiya kada mu Fusata..Mu Natsu mu yanke Hukunci Yadda ya Dace.."Kwamishina na jinjina kai yake Fadin"Hakane...Tabbas na yaba da Hikimarka.."Yafada yana jinjina ma Kaifin Basiran Alhaji Tsoho. Kai Tsaye Alhaji Tsoho ya kalli Dina yana Fadin"Diyata...Wani Shaida gareki da zai Tabbatar mana Da cewa Zainullahi ne Uban Cikin Jikinki..? Yafada yana kallonta kai ta Dukar kasa ganin Falon kallo ya Dawo kanta Zain kuwa Tunda Yaji Abunda Alhaji Tsoho yace kansa ya kara kasa kamar wanda zai Kifa Saboda Tashin Hankali,Zakiya ce ta Rike Hannun Dina tana Daga mata kai Shiya Bata kwarin Gwiwan Dagowa ta Fara mgana"Saboda Shine kadai Saurayina..Kuma Tunda Nake Shine kadai Namijin Danake irin wannan Mu"amalan Dashi.." Dam...Gaban Kowa ya Fadi,Kowa sai ya saki baki yana kallon Dina Alhaji Tsoho ya Cije Abunda yake ji acikin Ransa yana Fadin"Ai bamu san haka ba Diyata..? Cikin Dakiya da Rawan Murya Dina Tace"Shi ya sani..Shi yasan komai...Yafi Kowa sanin Bayanshi bana Mu"amala da kowani Namiji..Tabbas Zain yasan wannan Cikin Dake Jikina ba Shakka Shine Ubansa..! Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Gabadaya sai Falon ya koma Shuru Alhaji Tsoho ya Kalli Zain Cikin Kakkausan Murya yace"ZAinullahi...Kai Zainullahi..'Yafada yana Zungurinsa da Sandan Hannunsa Firgigit Zain ya Dago kansa Idanuwansa da suka Kada suka yi Jajir ya juyema Alhaji Tsoho Cikin Bacin Rai da kuma Lalama yace"Kaji Abunda Ta Fada..? Kallonsa ya maida kan Dina Sukayi Kallon kallo na wasu Mintina kafin ya Janye idanuwansa Cikin Rawan Murya da Datsewar Harshe yace"Ehhh...Amm..."Hannu kawai Alhaji Tsoho ya Dagamai yana Fadin"Ba Ammh na Tambayeka ba..So nake nace Gaskiya ne Abunda Ta Fada da wanda na gani arubuce Cikin Dake Jikinta Na ka ne..? Yafada yana Tsaresa da ido kamar yadda Kowa ya Tsareshi Da Ido Zuciyoyi na Bugawa,Kowa na Jiran yaji mai Zain zai ce shi kuma Ji yayi kamar kasa ya Bude ya Shige Ciki Wata irin Nadama da Danasani ne suka Lullubeshi,Jikinsa ya kama Rawa Zuciyarsa ta Fara Bugawa haka Yake kallon Duka iyayensa suna kallonsa Cikin son kada wannan Zaton ya Tabbata ammh Ina Bakin alkami ya Riga ya Bushe Haddir ya Kallah wanda ya Gyada mai kai alamun ka Fada kawai zain yau din Ranar Da nake Juyemaka ne Tazo. Kansa ya maida kasa yana Jin Tahowar kwallah ganin Irin yadda Abba ke kallonsa da Alhaji Tsoho Cikin Nuna mishi Mun fa baka yarda Cikin Rawan Murya Dana Zuciya ya Bude Baki Cikin Kuka yace"Ehhjhhh...!Alhaji Tsoho Ba Shakka Cikin Dake Jikin Dina nawa ne..Ni nayi mata Shiii...Ta Fadi gaskiya Dani kadai take Mu"amala Gaskiya ne..! Yafada yana Rufe Fuskansa da Tafukan Hannayensa yana sakin wani marayan kuka Kamar karamin yaro,Gabdaya Falon sai ya Rude da Salati da Salallami da kalaman Zain Dina da Zakiya kuwa Hannu suka Damke suna Sakin Numfashi Umma da Nene kuwa sai kuka Haka Zareena dasu Hamdiya Hajiya Mama da Inna Rukkaya Fadi Suke Hasbunallahi wani"imal wakil. Baban Kaduna da Daddyn Abuja Hulunan kansu suka Cire suna Fifita cikin wani yanayi Abba kuwa kansa na kasa yana jiin Jikinsa Gabadaya yayi sanyi Alhaji Tsoho kuwa Sunan Allah kawai yake ta Kira,Duk da ya Zargi hakan zata Faru ammh Ya bama Zain Duka yardansa. Daga Chan Bakin Falon sukaji Kara Da kuka Lokaci Daya da Fadin "Innalillahi Wa'inna Illaihiraju"un....Lahaula walakuwatu Illahbilahi..."Zaina Take Fada Tana Daafe da Kirjinta Wanda yake Barazan nan Fashewa da jin kalaman Mijinta Abun kaunarta wanda tafi Kowa yarda Dashi Duk Duniya. Hannu ta Daga Tana Nuna Zain Cikin Wani Fargici Shi kuma Tunda yaji kara da Mganarta ya Dago kansa Lokaci Daya ya Mike Zumbur Duka idanuwansa suna Waje Laila Ke Riketa da Ita Itama kanta Cikin Rudin Take da Jin wannan mganar kafin Tayi wani Yunkuri Zaina ta Sulale kasa asume Bakinta na wani karkafa kamar Wata mai aljanu. Ai Da wani Gudu kamar walkiya Zain ya Taka ya Nufi Zaina,Gabadaya Su Inna Rukayyah da su Umma suka mike afirgice suka nufeta. Cikin Wata irin Murya mai amo Cike da kuka Zain yake fadin. "FIRSTLOVE....". *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*              1️⃣8️⃣ "Shi ya Fara isa gareta da wani Gudu kamar zai kifa,Laila ce Ta tareta sanda zata Fadi Sakamakon Ta Rinjayeta sai Dukkansu suka Zube kasa Tare,Laila kuka ta Fashe dashi Tana Jijjiga zaina Lokaci Daya da Kiran sunanta kafin Zain ya kariso wajen gwiwa Biyu ya Duka agaban Zaina ya Ciccibi kanta ya aza Bisa Cinyarsa yana Kiran sunanta Cikin wani yanayi haka ma su Umma da suka Karisowa kowa ya Shiga mamakin ganinta da Abunda ya Faru Tunda basu san sadda tazo Gidan ba Balle har taji wannan al"amarin da kowa yasan Bazai mata Dadi ba. Laila ce ke kuka Tana Jijjiga Hannun Zainar Tana Fadin"Na Shiga uku Halima ki Tashi Don Allah..Wlh da nasan Abunda zai Faru kenan da ban yarda na kawo ki nan da kika ce ba..Allah na Tuba.."Take Fada Tana kuka kamar An Tambayeta ta Cigaba Da Fadin'"Ni bansan me ya sameta ba Tun Dazu muka gama Abunda zamuyi muka samu Waje muka Zauna muna Hira Tana ta cewa na Tashi mu Tafi nace mata mu kara Zama na wani Lokaci Ni bansan meyafaru sai dai kawai naga kamar An Turo mata sako a wayarta ta Ciro wayarta Ta Duba Daganan ne sai ta Rikice ta Fara kuka Tana Dafe Kirjinta Nayi Ta Tambayanta Ko wani abu ya Faru ne taki min mgana,Sai cewa kawai Da Tayi na Rakota nan Gidan bata ma iya Tafiya na Rikota muka Fito Daga Cikin Makaranta muka Hau adaidaita zuwa nan..". Ta Karishe Fada Cikin kuka Kamar wata karamar yarinya ba wanda ma yabi ta kanta ganin sun Rude ne sun Rasa yadda zasuyi yasa Haddir ya Shiga Kitchen da Sauri ya Dauko Ruwa mai sanyi yana Zuwa Ya sheka ma Zaina afuska Lokaci Daya ta saki Ajiyar rai Numfashinta ya Fara Tafiya Da Sauri Sauri,Zain Rumgumeta yayi yana Sauke Numfashi Lokaci Daya yake Fadin Alhamdulillah. Dina kuwa da ZAkiya Juna suka kallah kafin Dina ta Dagama Zakiya Hannu Alamun Jinjina ita kuma Sai ta Daga mata kai Cikin Jin Dadin yabonta,Ganin Numfashin zaina ya Dawo yasa sai kowa ya fara komawa Wajen zamansa Aka bar Umma da Nene da Zareena kan Zaina wacce ke Rumgume Jikin zain,Sai Laila Dake gefe Rakube Cikin Alhini Da Damuwar Wannan Al"amarin Dayake Shirin Faruwa da kawarta ko ma Tace yake kan Faruwa. Ahankali Take Bude Lumsansun Idanuwanta,Kafin Ta Fara Gani Dishi Dishi ahankali kuma ganin nata ya washe,Fes ta Saukesu kan Zain wanda ke Rike da ita Kura mai ido Tayi na wani Lokaci kamar kiftawan Ido Abubuwa suka Dinga dawo mata Tun Daga Hotunan da aka Turomata na Mijinta da wata karuwa Suna Halin Sirrarantan Juna Har zuwa Tambayar Alhaji Tsoho da kalaman Zain Tuni Idanuwanta suka Rufe Zuciyarta Ta fara wani Tsalle tana Bugawa Da karfin Bala"i ta Saki kawai ta Fashe da kuka Lokaci Daya tana Jaye Jikinta Daga na Zain Shima cikin Raunin Zuciya ya kara matsota yana Mika mata Hannu zai kamata Da wani Karfi Zaina ta Tattaro Jarumtar ta Tashi Tsaye Duk da Jirin Datake gani Idanuwanta na Zubda kwallah Tana kallon Zain ammh Ta kasa Furta ko kalma Daya. Shima Mikewan yayi Yana Kokarin Nufarta Da Sauri Ta Fada Jikin Umma tana Sakin Wani marayan kuka wanda Duk wanda yaji wannan kukan zai san kukan ne Dayake Fitowa Daga karkashin Zuciyarta Rumgumeta Umma Tayi Itama Tana Kukan mai Hawaye,Gabadaya Falon Jikin kowa yayi sanyi Kowa kaga Fuskar ba Annuri kuma Cikin Tashin Hankali Masu kuka kuma natayi... Alhaji Tsoho ne Da Tsausayin Halima ya gama Cikamai Zuciya ya Dago yana Fadin"Fatima kama ta Kuzo ku zauna.."Yafada yana kallon Umma ba Musu Umma ta Rikota suka zauna kusa Da Nene wacce Kanta ke kasa Tana Sharan kwallah Haddir ne ya Riko Zain ganin yana Neman zama Kusa da Umma Da Sauri ya Rikesa yana Fadin"A"a...Muje chan ne Zain..! Yafada yana kallonsa ganin kamar Baya Cikin Hayyacinsa Dole yabi Haddir ganin Daga Umman Har Firstlove din Nashi Da wani Mugun kallo suke jifansa Dashi Wanda yake jin kamar ya kwanta a gabansu yayi ta kuka Gaban Alhaji Tsoho suka kara Komawa suka zazzauna Kafin Alhaji Tsoho ya Fara mgana da cewa,"Innalillahi Wa'inna illaihiraju"un..Hakika Gareka muke kuma gareka zamu koma Mu musulmai ne..Mun yarda Kaddara mai kyau da Mara kyau...Tabbas wannan Itace Jarabawa Wanda Allah ya Jarbacemu Sai dai muyi Fatan Allah ya bamu ikon Cinyeta kuma Allah ya karemu da Zuru"ar mu Gabadaya..! Aka amsa Gabadaya da Ameen kafin Cikin wani irin Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fadin"Ka Bani kunya Zainullahi....Ka Barar da yarda da Amanan da na baka acikin Zuciyata..Bantaba Zaton a matsayinka namai Hankali zaka iya aikata Laifi irin wannan ba..Wlh ina da yakini mai kyau akanka Zainullahi Ayadda na san Irin Tarbiyan da muka Baku Banta Zaton Watarana za"a samu wani Daga Cikin Zuru"ata da wannan aikin assha din ba...Naji matukar kunya..Kuma ka Bani kunya ka watsar da Kimarka Idanuwan Danginka da Iyayenka Da Matarka Zainullahi Bayan haka kuma ka kwashe kayanka Gaban Allah...Domin Zina Babban Zunubi ne Allah da kanshi yace kada mu kusanceta kai kuma sai ka Kusanceta..Dama kuma Wanda ya kusanceta zai Raba kansa da Kunya da Dattako Da kima Uwa uba kuma ya saka Rayuwarsa Cikin Wani Hali na Tabewa da kaskanci Kuma Daman Ko ba ji ma Asirinka sai ya Tonu Domin Ita Gaskiya Sunanta Gaskiya Karya ma Sunanta karya..Zainullahi ka Bama yardanmu da Tarbiyan da mukayi maka kunya..Naji Nauyin Mutane guda Biyu..Na Farkon Nauyin Ubangijina Na Biyu kuma Ina jin Nauyin kallon Idanuwan Matarka wacce Tunda tazo Duniya ka Fara Koya mata Sonka da yardanka Dashi Ta tashi ta Girma Ina Matukar Jin Tsausayin yadda zata Girmama wannan Shashancin naka Zaunullahi..! Ya karishe Kamar ya Fashe da kuka Saboda yarda Muryansa ta Sauya Kowa afalon sai da Jikinsa ya karayin Sanyin Zaina kuwa Kuka kawai take ta ma kasa Mgana Haka kurum Takejin Zuciyarta na Fat Fat..kanta na Sarawa,Laila ma Dake gefe Hawaye Take Sharewa na Tsausayin Kawarta Gefe Daya na Zuciyarta na Fata da Addu"an Allah ya bama Zaina Ikon Jure wannan Jarabawan Rayuwan Daya Tunkareta. Zain kuwa Hawaye ne suke Diga Bisa Cafet din Falon Alhaji Tsoho kalaman Alhaji Tsoho sun Kara sakashi Cikin wani irin Nadama da Danasani Shi yanzu Bayama jin ta kowa yafi Jin ta Firstlove wani irin Mataki ko kuma Hali zata Shiga Dalilin wannan Al"amarin Da son Zuciyarsa ya Jawo..? Kamar amafarki yaji Alhaji Tsoho na Fadin"Zainullahi ka Dago kanka Ka Bude baki gabana gaban Sauran iyayenka ka Fadamana Tunyaushe ka Fara wannan Shashancin bamu sani ba..?.. Yaji Tambayar atsakar kansa Kunya ta sa ya kasa Dagowa Toh yace me..? Yace Tun Tafiyarsa London..? Yace kafin Dina yayi Tarayyah da mata da yawa da baisan iyaka ba..? Ko iya Kunyar da yasha ta wannan mganar ta Isheshi baya Fatan ya kara Fuskanta wani kunyan Da Tonin asiri,Haddir ma Wuri Wuri ya Farayi da ido Jikinsa na Rawa Zufa na Ketomai Domin ya Tabbatar Da in aka Bi salsala Shima bazai Fita ba,Tunda yaasan komai Tunda Fari yana ta addu"an Allah sa kada Zain yayi mgana addu"ansa ta karbu Domin ko Dago kansa baiyi ba, ballatana yasa Ran zai yi mgana Yana Sauke ajiyar zuciya yaji Muryan Dina Tana Fadin"Alhaji ai Baxai iya Fada maka ba..Ni zan Fada maka komai tun Daga Farko Har karshe..' Tafada Cikin Raunin Murya Lokaci Daya Tana Mikewa Kowa ita ya sakama Ido Haddir yaji Wani Zuu kamar ya kurmance Yana Bin Da Dina da kallon mamaki Zain kuwa Tsabar Gagara ma bai iya Dago kansa ba ya gama sama Ransa yau itace Ranar Tonon asirinsa. Kai Alhaji Tsoho ya Daga yana kallon Dina Lokaci Daya yana Fadin"Muna Sauraranki..Ki Fadamana gaskiya Hakan zai sa Mu yanke hukuncin Daya Dace akan Lamarin.."Ya Fada acikin Zuciyarsa yana Tir da irin Tarbiyan Dina na Rashin kunya da Fitsara in Banda Fitsari ta na Cikin Wannan Halin har taga ta mgana Ko Dayake yana Tunanin Koda Laifin Zainullahi itama da nata Domin da bata bada Halin kai ba da haka Bata Faru ba..". Cikin Wani yanayi na Takaichin zain Dina ta Fara mgana"Ni da Zain mun Hadu Ne a london Oxford Uni Tun Shekaru 7 da suka Gabata.."ai sai kowa ya saki baki kawai cike da mamaki Cikin Ajiyar zuciya ta Cigaba da Fadin"Kuma alaqar mu ta Faro asali ne Tun Farkon Haduwarmu..Allah ne Shaidana Duk da na taso Cikin Gata kuma ban Tashi gaban Tarbiya Uwa ba sai na Uba na Tsare kaina Har naje London ban yarda na Watsar da kaina ba..Sai dai komai ya Sauya Daga Haduwata da Zain..Wanda Allah ya Doramin makauniyar Soyayyarsa..Alokacin Zain bai Dauki mata abakin komai ba sai ababen Jin Dadi da Kore Sha"awa..Kafin ni Zain yayi Hulda da yanmata Kala kala kama Daga Musulmai zuwa Mabanbanta addinai." Da Karfi Alhaji Tsoho ya Furta"Wa"izubillah.."Yafada Cikin karaya da wani Bakinciki Haka su Baban kaduna suke jifan Zain da wani kallon Kaskanci da Takaichi Dina bata Damu ba Ta Cigaba da Fadin"Da Farko dana samu wannan Labarin game dashi naso na Fita Batunshi sai dai kuma na kasa Son gaskiya nake ma Zain Dalilin Dayasa na kasa Rabuwa Dashi kenan Dalilin Takaichin Yanmatan Dayake Tarayyah Dasu yasa Na mallaka mishi kaina Yayi yarda yaga Dama Dashi..Na Rantse da Allah Shi ya Fara sanina a ya mace ban mai karya ba..Bayan nan kyakyawan alaqa ta Cigaba da wakana tsakanimu wanda Dakyar nayi Nasaran Rabashi Da Bin Sauran mata kuma wannan yakin Nasan bani kadai nayi ba Dan"uwansa ma Dr.Haddir gashi nan zaune Shima yayi Kokari sosai wajen Daidaita Rayuwar zain ammh Abu yaci Tura ni kaina ina gajiya Da wannan Abunda da muke aikatawa nakan ce mai Ya kamata mu Daina mu Tuba muzo muyi aure ammh Duk sadda namai irin wannan mganar da Fada muke Rabuwa Sai yace bazai Aureni ba saboda Shi yana Da matarsa...Ni kuma ina sonshi Shiyasa na kasa Rabuwa Dashi Har Barinsa London da Zuwansa Mumbai muna Tare nakan kaimai ziyara Lokaci Dayan Lokaci hakama Bayan Sun kamallah sun Fara aiki da asibitin su Shi ya gayyaceni Domin muyi aiki Tare da wannan muka samu Damar Cigaba Da alaqanmu aboye Acikin asibiti ne ko kuma agida Da Rana Ni Kamar matarsa nake Haka Da Daddare ne Zaina Take Matarsa Wlh Har araina bana Jin dadin Rayuwar da muke Gudanarwa ammh ba Laifina bane Laifin Zuciyata ce da kuma Zain wanda yake nuna Bazai aureni ba ammh zai Cigaba da Shashanci Dani..'. Ta karishe Fada Wani kukan Kamar alokacin ne Zain ke Fadamata bazai aureta ba Tana kuka ne na Kishi Da kuma Soyayyar Datake ma Zain,Kamar yadda Take wannan kukan Haka zaina keyin Nata su Umma nayin nasu acikin Zuciya Kwamishina kuwa Sai da ya Share kwallah yana kallon Dina yace"Ba laifinki bane Dota..In ma kina da laifi Wlh naki kadan ne nawa yafi yawa..Allah na Tuba Allah ka yafemim..Wlh Sara in yau ta Dawo duniya bazatayi alfahari Dani ba...Na baki gatan Da Sanadinsa wannan Kaddaran ta Fadamiki Allah Mun Tuba.."Yake Fada yana Saddan kansa kasa Hajiya Batula na Bashi baki kasa kasa Lokaci Daya tana kara Nusar Dashi Kuskuran da yayi akan Rayuwar Dina. Alhaji Tsoho Daya gama jin wannan labarin mai kama da alma"ara ya kada kai yana Fadin"Allah Sarki..Allah ka Rabamu da makauniyar Soyayyah...Meyasa kika Zabi ki Fallasa mganar Cikin Jikinki Tunda Naga ga Duk alamun kema kin Biyemai wajen Sabon Allh da Zunubin Da kuke aikatawa. ? Yafada yana kallon Dina wacce ke Share Hawaye kafin Tace"Saboda Bana so na sake aikata Laifi kan laifi..Ni da Zain daman mun yi ijiye magar bazan bari nayi Ciki ba..Dalilin Haka yasa nake karban allura Duk Bayan Wata Shida na planning,Wannan karon bansa ya akayi ba kawai sai gashi Ciki ya Bulla gareni wanda arude na Kira Zain gidana na gayamai komai ammh sai ya Rude da Tsoron kada Mganar ta kai kunnen Iyayensa Har nema yayi ya Illatani saboda yana zargin da gangan na bari nayi Ciki..Ina da Racoard din Abunda ya Faru Tsakanina Dashi Ranar zakiya kunna musu suji Da kunnuwansu.."Ta Fada tana kallon Zakiya wacce kamar Jira Take ta ciro Dayar wayarta Dake Cikin Jaka ta lalubo Recording Din Datayi na Zain da Dina ta kunna Ta kara Volume Saboda ma Kowa yaji Mp Ta Fito Dashi Dama saboda Haka tazo Da ita tayi Connecting sai ga Muryan Zain Radau ta karade Falon Tiryan Tiryan Komai yake bayyana Kowa naji Tun kafin agama Saurara Zaina ta Mike da wani Irin kara tana Toshe kunnuwanta Cikin Wata irin Murya Take Fadin.. "Ya isa...Ya isa....Ya isa....! Take Fada tana wani Barin Jiki,Hannuwanta Dafe da kannuwanta kafin ta kwashi Gudu Zuwa Dakin Hajiya Mama kamar wata zararriya Zain Daya Dago kansa yana kallonta yana Hawaye ya mike zai Bita Umma Ta Daka mai Tsawa da karfi Tana Fadin"Karka sake ka Bita Zainullahi...! Tafada Cikin Kakkausan Murya Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Zafin Nama ta isa Gabansa Tana kallonsa Sau Daya ya kalleta ya maida kanshi kasa Idanuwansa na Zubda kwallah Cikin Mintina Goma Ta gama Kallonsa Cikin Wani Bakinciki Da Takaichi irin na Uwa da Danta Kawai sai Ta Cira Hannu Yau Rana ta Farko Ta zabga Mai Maruka guda Biyu Da sai da ya Durkushe Cikin Kuka Ta Nunashi da yatsa Tana Fadin"Me zaka Fadamata..? Babu..Kada ka kara kokarin zuwa Kusa da Zuciyar da Ka Riga ka Bata Rauni Zainullahi...Ka kiyaye Fushina akanka."Daga haka kawai ta Wuce Cikin kuka ta Rufama Zaina Baya,Haka zain ya Duke kawai yana kuka Hawaye na Zuba Alhaji Tsoho na kallo yama kasa mgana Baban kaduna ne ya mike afusace ya isa ga Haddir ya Mikar Dashi Tsaye Sai ji kayi Shima ya bashi Fayau Fayau har guda Biyu Sai da Shima ya Duka Cikin kunar rai yace"Kaima ka bada Gudummuwa wajen Faruwan komai..Meya hana Tun Farkon Wannan Lalacewar ta zain baka Kirani Ko Ni Ko Aliyu ka sanar mana ba In bazaka iya Fadama Usman ba..Don Ubanka ...? Dagajin yadda yake mgana zaka Fahimci Yadda Ransa ya baci Hajiya Mama na Sharban Hawaye Tana Fadin"Bafa Hadiru bane Abun Duka ga Abun Duka chan...Kai Zainullahi Ka cucemu ka cucu kanka Wlh.."Waje ya Fara Daukan mgana Inna Hannatu da Idanuwanta suka kala sukayi Jajir ta kalli zain Tana Fadin"Baka Fara kuka ba Zain yanzu zaka Fara Tunda kasa iyayenka kuka da Bakincikinka..'Sadiq kuwa Tuni ya Fice yana kuka ganin yayansa Cikin Wannan Halin Zareenaa ma kuka take kamar Ranta zai Fita Haddir kuwa Kasa ya Duka yana kuka yana Fadin"Don Allah kumin aikin Gafara..Nasan zaka ga laifina ammh ban Boye wannan mganar Saboda komai ba sai saboda Rufamana Dan"uwana asiri..Kuma Har ga Allah bansan Har Dawowarmi suna Tare da Dina ba Tunda Tun muna London yayi min alkawrin Dainawa kwata kwata..Ku yarda Dani Wlh Allah bansan komai ba yadda kukaji komai nima Haka naji.."Ya karishe Fada yana Rike Kafafuwan Baban Kaduna wanda ya Fizge yana Fadin"Rufemin baki Shashenshan banza..Ai gashi nan garin Rufamai asiri ka barshi ya saka kansa Cikin Bala'i da mu kanmu iyayanku Dukkansu sai kunci Ubanku kunjima na Rantse..". Ganin Abun na neman yayi yawa ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakatar yana Fadin"Bashir koma ka zauma..Yanzu ba Lokacin wannan bane...Mu zauna mu samu mafita Tunda mai aukuwa ta auku..'Da haka kowa ya koma ya zauna Alhaji Tsoho ya gyara zama yana Fadin"duba da Duka Abubuwan da suka Fara Da Shaidan gani da ido dana ji da kuma amsan ZAIN na cewa ya yarda Cikin nan nashi ne..Toh zanyi ma Abun Duban Fahimta na Farko bazamu bari mu kara aikata wani kuskuran ba..Mganar azubar da ciki bata Taso ba Dole Yarinyar nan zata Haifi Abunda ke Cikinta..! Baban Kaduna yace"Ta haifa fa kace Alhaji Tsoho..? Ammh dai ba"ana  ba ko..? Ina zamu kai wannan Abun kunyar..? Cikin Mirmishin Takaichi Alhaji Tsoho yace"Anan kuwa..Kuma agidan Iyayen Zainullahi zata Haifa Abunda ke Cikinta.."Kowa Alhaji Tsoho ya zubama Ido Harda Dina da Zakiya Cikin Dattako ya kalli kwamishina yana Fadin"Kwamishina kamin afuwa zanyi maka wani karambani..Abun nan ya Riga ya Faru bamu da yarda zamu sai dai Fatan Allah ya kyauta na gaba..Naji Dadin yadda ka nuna min kai Mutumin kwarai ne wajen Dauko wannan yarinyar ka kawota nan naji Dadi..Nima zan yi amfani da wannan Damar Mu Taru mu Rufama Juna asiri kai dan Siyasa ne Fasuwan wannan mganar matsala ne ga Kimarka,Saboda Haka na yanke Shawaran Yarinyar Wajen naka zata Dawo Nan Bauchi da zama agidan Mahaifin Zainullahi karkashin Kulawa iyayansa Mata Nene da Umman Zareena zasu kula da ita Har ta sauka Lafiya Daganan ta samu tsarki da zasu iya yin auree Bayan haka ni Dakaina in ina Raye zan Daura Auran yarinyar nan da Zainullahi in kuma bana Raye ga ya"yana nan insha Allahu zasu Cikamin wannar Wasiyar Tawa.."Gabadaya Falon sai D'au Shuru Dina kuwa Tun sadda Alhaji Tsoro ya Furta kalmar Aureta Runtse ido tayi Tana jin kamar tatashi Ta Taka Rawa ita bata ma Damu da Cikin jikinta da akace sai ta Haife ba,Domin Soyayyar Zain yasa Take matukar son Cikin Jikinta,ita kuwa zakiya a kunne ta mata rada. "Finale MRS ZAINULLAHI USMAN SAULAWA.! Mirmishi Dina ta mata Tana kallon Zakiya kamar ta Goyata su Baban kaduna kuwa basu ma iya mgana ba sanin In Alhaji Tsoho ya yanke Hukunci Shikenan Zain kuwa Kallon Alhaji Tsoho yake cikin Wani yanayin ya zakamin Haka Abba kuwa Kansa na kasa Ko Dagowa bai yi ba,Ballatana ma agane wani Hali yakeciki. Kwamishina kuwa saboda Murna Har kasa ya Duka yana ma Alhaji Tsoho Godiya Alhaji Tsoho yace"Bakomai..Kada ka Damu..Abunda ya Hadamu bamai Dadi bane..Ammh da yardan Allah zai zama mai Dadi Watarana Ina kuma Fatan Allah ya Shiryama Zuru"a Gabadaya.."Yadinga amsawa da Ameen kafin yace"Ina so zan koma da ita zuwa Sati mai zuwa Sboda zuwan kanwar mahaifiyarta Daga sudan..Zan zaunar da ita na gayamata komai Tunda ya zama Dole tasani kamar uwa Take gareta..Allah barshi bayan Haka ni Dakaina zan kawota wajenka Ranka ya Dade.."Alhaji Tsoho yace"bakomai..Allah ya nuna mana.." Agogo Fatan Dake hannunsa Kwamishina ya Duba 3pm na Rana ta wuce da Sauri ya Mike yana Fadin"Subhanallah munja Lokaci..Ko Sallar azahar bamu yi ba..Zamu wuce yanzu Alhaji..Nagode kwarai Daka Fahimceni Allah ya kara Kiyayewa.."Alhaji Tsoho ya amsa da Ameen yana Fadin"Dukkamu  mun Shiga Rudani bamu san Lokaci ya Tafi haka ba..Allah ya Tsare yakai ku gida lafiya..! Da Ameen ya amsa Bayan ya Bashi Hanmu sunyi Musabaha Haka yabi su Baban kaduna suma yayi musu musabaha suka karba Fuska ba Fara Abba ne ba"agane wani yanayi yake Ciki Mikewa Hajiya Batula tayi Dasu zakiya,Hajiya batula nayi musu sallama suka amsa Fuska ba Walwala Mama Safiya ce ma ta Amsa da Allah bamu alheri su Nene kuwa ko kallo Kowacce da Abunda Take Sakawa. Dina kuwa Zuciyarta Kamar Farar Takarda Saboda Haske Ta gaban Zain tazo ta wuce Tana Fadin.."Ka bar kuka..In ka Rasa Wata matarka..Ga wata nan kuma Uwar ya"yanka ce Insha Allahu.."Tafada a Hankali kasa kasa ba wanda zai jita sai Zain din Wanda ya Dago yana kallonta Cikin Wani irin Tsana da Bakinciki yake Jifanta da wani matsiyancin kallo Mirmishi ta sakamar Lokaci Daya Da gamai Gira kafin ta wuce Zakiya ta mara mai Baya Tana mai kallon Sorry For u Self Dr Zain. Sai da suka gama Fita kafin Alhaji Tsoho ya yunkura ya mike yana Dogara sandanshi yace"Sallar azahar ta Kubucemana Kowa yaje ya gabatar..Mu Dawo aci Abinci Ayi addu"a kowa yaje ya Huta.."Daga haka ya Fara Dingisawa zuwa Dakinsa Su Baban Kaduna suka Bishi da kallo Har ya Shige,Baban kaduna ne ya Mike Tsaye sai Daddyn Abuja wanda ya saka Hannu ya Mikar da Abba suka fice Batare da sun ma kowa mgana ba Suna Fita Haddir ya mike yabi Bayansu Sai Hajiya mama Tabi bayan Mijinta,Sai Zaneera da Hamdiya suka Shige Dakin Hajiya Mama Daganan sai Inna Rukayyah da Inna Hamnatu da su Mama safiya suka Mike suka Nufi ciki Ko kallon Zain dake zaune Dirshan ba wacce Tayi Laila kuwa kawar Zaina Tun Saddan Zaina ta Shiga ciki Tana kuka ta mike ta Fice Daga Gidan Ta Nufi Gida Tana kuka da mamakin Halin Namiji Damam Abunda Take jiyema zaina kenan Tuni. Nene ce kadai Ta Rage afalon sai Share kwallah Take ganin haka yasa zain ya Rarrafa gareta Zai Tabata Tayi Saurin Janye kafarta ta mike Tana Juyamai Baya cikin Fitan Hayyaci Da Muryan kuka Yace"Nenee...! Bata ma Jira cewarsa ba ta wuce Ciki Itama Tana Sharan kwallah Da kallo ya Bita Yana Jin Tsiyayan Hawaye lalle kuwa yau yayi Nadamar aikata Zina gashi Dalilinta Mutane Biyun da basu Taba gujemai ba Sun gujeshi yau wato Fitstlove da Nenensa Duniya Abun Tsoro ne. Nan ya Durkushe yana kuka Shikadai kamar zai Shide Yana cikin kukan yaji an Dafa kafadansa yana waigowa zatonsa Nene sai gaya Tabawa ce bai san sadda ya Rike hannunta ba ya kara saka kuka yana Fadin"Tabawa na Cucu kaina...Dalilin Biyema zuciya da Shedan yau Firstlove taki Dubana Nene ma haka Umma kuma Ta Daga Hannu ta mareni Wanda Tunda ta Haifeni bata Taba Koda Dungurina ba sai yau.."... Yafada yana kuka Kansa Take Shafawa Tana kuka Lokaci Daya Tana Fadin"Kayi Hakuri...Jarabawa ce..Allah ya baka Ikon Binta..Zasu sauko Dukkansu kuma zasu yafe maka Bacin Rai ne yanzu.."Kuka kawai yake Kamar karamin Yaro kafin ya mike Zumbur yana Fadin"Ina jin kunya..Ina Jin kunyar kara Haduwa da wani Ahalina ayanzu Tabawa..". Daga haka kawai ya saki Hannunta ya Fice kamar walkiya yana zuwa Haraban Gidan yaga su Abba na Sallah sunyi Jami"i ne Dadyn Abuja ke Bada Sallar Haddir ma na Cikin Sahu Hango Key din Motar Haddir yayi agabansa yasa ya karisa da Sauri ya Dauka Duka suna kallonsa ba Halin mgana Tunda suna sallah suna Ji ya shiga Motar Haddir ya Fice Daga Gidan da Gudun Kamar zai Tashi sama. *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*            1️⃣9️⃣ "Zain na Fita Daga Gidan Alhaji Tsoho Sai ya rasa Duka Natsuwarsa Tuki yake ammh ba  Cikin Hayyacinsa ba Kuka yake kukan Nadama da Danasanin Abunda ya aikata yau gashi ya Girbi Abunda ya Shuka. Iyayensa Da Duka Danginsa yau ba wanda ya kalleshi Matarsa yau Ta shiga wani Hali Saboda Shi Daman irin wannan Ranar yake ta Tsoron gashi yau tazo mai acikin yanayin da bai kamata ba, Tafe yake yama Rasa ina Zashi ayau ya Tabbatar da kansa Duk Abunda zaka aikata kada ka kaucema Umranin Allah In baka Kauce ba kowani Hali zaka Shiga zakaga Allah ya baka Mafita in kuma ka Kauce ma Umarnin Allah Zaka Dade kana Yadda kaga Dama Ranar da Allah yayi Niyar kamaka bazakaji Da Dadi ba Kashima sai yafika Daraja kuma Haka Rayuwarka zata Shiga kilaWakalan Bakinciki Da Damuwa na Har Abada. Yana Tafe yana kuka Lokaci Daya kuma yana Tuki Haka ya Dinga Zagaye Titunan garin Bauchi Yarasa Ina zashi..? Wajen wa zai Nufa.? Allah kawai ke Tsarewa ammh Wajen Sau Biyu yana Buga ma Mutane Mota Saboda baya Cikin Natsuwarsa,Daya gaji ne yasa ya samu Wani masallaci ya shiga yayi sallar Azahar da La"asar nam ya zauna Cikin Masallacin yana ta Rokon Allah Gafara ga Cikinsa na Jin yunwa ammh kwata kwata Bakinsa bayajin Zai iya saka wani Abu. Ya Dau Tsawon Lokaci Cikin Masallacin kafin ya Mike ya Fita Mota ya Shiga ya Tadata Rasa Wajen zuwa yasa yayi Tunanin zuwa Cikin asibiti Sai kuma yayi Tunanin Kila suma Labari yaje musu yanzu baida wata Sauran Kima Dole yasa ya Maida akalan Motan nashi Zuwa Gidansu dake Lowcost. ***** Bangaran su Kwamishina kuwa Suna Fita Zakiya Daman bata koma Kano ba Gidanta ta wuce saboda Zata koma bakin aiki Daganan Tayi musu sallama ta Hau Motarta ta Nufi Cikin Gari Su kuma suka Hau Hanyar Komawa kano Cike da Damuwa Wanda kaso Kadan Daga Cikin Damuwan Ta Ragu Tunda komai yazo da Sauki. Suna Tafe Ahanya Hajiya Batula na yabon Ahalin Dr.Saulawa Musamman ma Shi kanshi Cikin Mganarta Take Fadin"Gaskiya Dattijon arziki ne...Naji ba Dadi Danaga Daya Daga cikin Ahalinsa ne ya aikata Haka...Daga gani Suna da kyakyawan Hadin kai...Yayi Adalci Sosai Domin in har yaronsu nada laifi kaso mai yawa Daga ciki laifin Dina ne.."Tafada kai Tsaye Tana kallon Dina wacce ke Tura baki Tana Hararan Hajiya Batula kasa kasa Cikin Takaichi Ta kalli Dina Tana Fadin"Eh na Fada laifinki yafi yawa..Domin ai ba"a Shege sai da aka Farayin Shegiya..Babu mutumci Ba kuma So bane mace ta watsar da kimarta yanzu wa gari ya waya..? Ko banza zaki Haifi Abunda ke Cikinki bata Hanyar Aure ba..Don Allah ya Tarfama Garinki Nono Wlh Haka Zaki Haifi Cikin arasa Ubanshi..' Kwamishina ne ya katse Hajiya Batula ganin Dinar Ta Dago Tana kallonta kamar zata yi mgana Cikin Damuwa yace"Ya isa Haka Batula..Don Allah ki bar wannan mganar...Naji da laifin Dina nima da laifina kuma kema da naki..Tunda matsayin Uwa kike gareta in kin sakama Tarbiyanta ido baki laifi ba.."Kai Tsaye ta bashi Amsa da Fadin"Baka bani wannan Damar haka ba..Kaida kake mahaifinta ka bata damar Rayuwar sakewa waye ni da zan Hanata..? Kuma kai yafi Chanchanta ka fara Bincikan Halin Da yarka ke ciki ammh kayi wannan..? Baka yi ba sai Siyasa sar ka kawai ka saka agaba Ta wannan Gabar Kada ma ka Doramin wani Laifi..! Daga Dina har kwamishina Sun San Gaskiya Hajiya Batula Ta Fada Shiyasa ba wanda ya kara mgana Daga Cikinsu Ita Dina Bata Damu ba Lumshe ido Tayi Tana Mafarkin gatachan Ta Ganta agidan Zain a matsayin Matarsa Farinciki ya cikata Shi kuma kwamishina Nadama da kunyar in yau ya Mutu me zai Fadama Allah..? Hakika Barewa bazai Gudu Danta ya Rarrafa ba wannan Abunda ya Faru Da Dina kamar Dawowamai Yayi Domin bayan Rasuwar Sarah mahaifiyar Dina ya Fada Harkan Neman mata sosai Sai Daga baya ya Rage bayan ya Auri Batula,Ya bar Harkan ne Tun Watarana da wani Abokinsa Shima Dan Siyasan ne,yanzu ma Haka sanata ne aawani yankin Yake bashi labarin Wata yarinya mai zafi Daya samu,Tun yana Bashi Labari Har watarana Da sukaje Abuja wani Taro Sai Sanatan ya gayyaceta Tazo mai Sai ya nemi ya Hadasu da kwamishina yaji Matukar kunya Lokacin da yaga Zakiya kawar Dina amatsayin Karuwan Sanata Abun yayi matukar Bashi kunya yaji ya Tsani Harkan Bariki Yaji Neman mata ya fita kansa,Abun da yafi bashi kunya shine Zakiyan tasan komai Domin har Sanatan na Fadi zai bashi Fagen shima ya Dana Ammh Dayake yar Duniya ce sai bata nuna komai ba ta Basar kawai,Yaji kunya Sosai ace yau Kawar yarka ta kamaka Da Dabi"ar kwartanci Abun ba Riba Tundaga Ranar ya daina Harkan Banza da Biyema Shawaran abokai yan Siyasa,Da kuma wannan Dalilin ya Fara Fargaban Kar yazo Itama Dina Halin Datake ciki kenan yaso ya Fara saka ido da Bincike kan Dinar sai kuma wani abu ya Daukemai Hankali ya watsar da Komai,Ammh Yayi Tuban Gaskiya Domin Tundaga Lokacin bai kara Bin yar wani Ba Tsoron Allah ya Shigesa ashe an Gudu ne ba"a tsira ba Shi yana chan yana Bin Diyan wasu Shima wani na bin bashi yar,Nadama ta kara Shiganshi Yaji Komai ya Fita kansa yana jin Da zai iya Daga murya Daya Daga ya gayama Maza masu Bin Ya"yan wasu da su Daina In ba Haka ba zasu gani Domin Sharri kamar Dan Sako ne zaka aikashi kuma zai Dawo maka. Wannan Dalilin yasa Zakiya Take Sakama Dina mgana in ta ambaci Wasu Daga cikin yan Siyansa sai a hankali,Sai ta nemi kare Mahaifinta ita kuma Zakiya Sai ta gayamata Barewa bazai Tayi Gudu Danta yayi Rarrafe ba ammh ita kam ta sani Allah ya Fitar da ita cikin Ya'yan Babanta Domin Tana da Tabbacin bai aikata makamcin Abunda take aikatawa ba yanxu..Ammh Tabbas Abunda Uban Dina yake aikatawa ne yarsa ke aikatawa Shiyasa bata ganin Laifin Dinar,Bata Taba gayama Dina Wani labarin daya Danganci Dadynta Domin Tsakani Ga Allah take zaune da ita Kawa ta Dauke sosai Abokiyar Sirrinta alokacin ma koda Ita da Daddy suka Hada Farka Cikin Rashin Sani bazata Taba Yarda Tayi wani Mu"amala Dashi ba Inda Amana Ruwa bazai Dafa Kifi Ta sani Batajin mgana kuma Tana Bariki ammh Barikin ta bai kai Tayi Harka da Uban kawarta ba Balle kawa ma irin Dina ta wace komai awajenta. Da wanman Tunanen Suka Isa Gida Kwamishina da Hajiya Batula suka Nufi Barayinsu Dina kuma ta Haura Sama Ta Shiga Wanka saboda Gajiya Bayan ta Fito ne ta Hada Salollolin Da suka Kubcemata, Ta koma Tabi lafiyan gado Ranta Fes Wayarta Ta jawo Tana Laluban Zakiya Tana jin Hayaniyar su Waleed a Falo da Tashin Mganar Daddy da Hajiya Batula..! ***** Salolli suka Gabatar kamar yadda Alhaji Tsoho ya Umarcesu,Ita kam Sallah ya zama Dole ammh mganar Abinci Ba kowa ya iya ci ba...Mom Iklima ce Da Mama Safiya suka Tsakura abincin sai Inna Rukayyah Inna Hannatu dai Bata ci ba Tagama sallah Tan kan Sallaya Tana Jan Carbi Ta Zab Tagumi Umma kuwa da Nene Suna zaune waje Daya Umma ce Tayi Sallah Nene na hutu Sai Zaneera Dake Gefe Zaune Tana Shayar da yarta Itama Bayan ta Idar da Sallar Idanuwanta sun kala sun ji Jajir Saboda kuma Sai Hamdiya Dake kan Sallayan Tana Sallah Dukkansu Suna Daki Daya ne Dakin Hajiya Mama Sai Zaina Dake Kwance kan gado Wacce Kuka da Damuwa ya sakarmata Zazzabi,Umma ce ta karbo panadol Wajen Tabawa ta bata Tasha Shine Allah ya Taimaka Ta samu Barci Sai Dai Daga ganin yadda Take Sakin Numfashi zaka Fahimci a Wahale take. Duk yawansu acikin Dakin Babu Wanda ke mgana da Dan"uwansa kowa da Abunda yake sakawa acikin Ransa,Shi kanshi Alhaji Tsoho Tunda ya Shiga Ciki bai iya Fitowa ba Tunda ya Idar da sallah yake zaune kan kujeran yana Ta Can Casbaha yana istigifari,Domin Hakikanin Gaskiya Abun ya Tabashi Yanzu ace acikin Zuru"ansa asamu wanda zai kawo Irin wannan Tunaninsa ya Tsaya ne ta gano Inda suka Kuskure. Yana nan zaune har akayi La"asar ya tashi ya koma kan Sallayansa ya zauna Yayi Sallar La"asar ya idar kenan sai ga Hajiya Mama ta Shigomai da Abinci ta Iskeshi ya kurama Waje Daya ido yana kallon Hotonsa Lokacin Dayake Matashinsa,Har Hajiya Mama Tayi mai mgana ga Abinci bai Jita ba sai da Ta zauna kusa Dashi Ta Dafa kafadansa kana ya Dago yana kallonta Cikin Damuwa tace"Ka daina Saka kanka Cikin wannan Dogon Tunanin ba Ishashiyar lafiya Gareka ba..! Gyada kai kawai yayi yana Fadin"Damuwa ta zama Dole Amina..Sai dai Zamuyi Kokarin Mu ki bata Muhallin Zama acikin Zuciyoyimmu.."Jinjina kai Kawai Tayi kafin tace'Ga abincin ka..! Kallonta yayi kafin yace"Anya zan iya cin Abincin nan Amina..? Barshi Dai zuwa anjuma..' Batayi Musu ba Sanin Halinsa Tunda yace haka Tasan bazai ci ba,Sai ta kauda Farantin Abincin Gefe Ta Daawo Ta zauna Tana Fadin"Anya Alhaji Hukuncin Daka yanke Kan Wannan al"amarin nan Daidai ne..? Nifa Wlh gani nake Yarinyar nan Tana Sane bafa Dole Zainullahi yayi mata ba Da Amincewarta Suka Fara wannan Shanshancin.."Alhaji Tsoho na Jinta bai mata mgana ba Shuru kawai yayi mata yana Cigaba da Jan Carbinsa. Sallamansu Baban Kaduna da Daddyn Abuja sai Abba ne ya Dago da Alhaji Tsoho yana amsawa Cikin son kare musu kallo Dukkansu Waje suka samu suka zauna Dukkansu Sannu Da Gida sukayi musu Hajiya Mama kadai ta amsa Shi kuwa Alhaji Tsoho Abba yake ta kallo ganin Irin yadda Lokaci Daya ya zama Wani Iri Cikin Muryan Sanyi da Salama Alhaji Tsoho ya Kira Sunan Abba.. "Usmanu Bin Fodiyo.."Dagowa Abba yayi Araunane yana kallon Alhaji Tsoho Cikin Rauni Da Hannu ya yafitoshi alamun yazo ba Musu ya Tashi ya isa Kusa Dashi,Ya zauna Kansa na Kasa Hannu Daya Alhaji Tsoho ya saka ya Dafa kanshi yana Fadin"kayi Hakuri Usmana...Nasani Abun akwai zafi da Ciwo samun Wannan Abun kunyar Daga Abunda ka Haifa kuma kake alfahari Dashi..Sai dai ina so ka sani Fushi ba namu bane..Mai Faruwa ta Faru sai dai Kuma Mu nemi Hanyar da zamu gyara kar hakan ta kara Faruwa.."Kansa na kasa yana jin Shigar wata natsuwa da kalaman Alhaji Tsoho Cikin Girmamawa ya Dago kansa yana Fadin"Insha Allahu Alhaji...Da farko ina cikin Bakinciki da wannan Abun da zain ya aikata ammh kuma zuciyata tayi Fari da kalaman Uba nagari..Hakuri ya zama Dole ammh kuma Don Allah  Karka Hanani nuna mai Fushina Domin ya Ruguje yardan Dake tsakanina Dashi.." Alhaji Tsoho yace"Bazan Hanaka ba Usmana..Domin kai Uba ne Nuna Fushin kuma Tamkar Hore ne...Ammh kada yayi yawa kaji ko..? Dakai ya amsa yana Fadin"Insha Allahu.."Mirmishi Alhaji Tsoho yayi kafin ya Dago yana Yafito Su Baban Kaduna da Hannu suma suka Taso zuwa gareshi Dukkansu suka zauna agabansa Kallonsu yayi yana Fadin"Ina Shi Zainullahin da Hadiru..? Baban Kaduna yace"Muna sallah Zain ya Fita da Mota...Haddir kuma yana Haraban Gida Shi da Sadiq.."Jinjina kai Alhaji Tsoho yayi kafin ya kalli Hajiya Mama yana Fadin"Aminatu Kiramin su Rukayyah da Hannatu.."ba musu Hajiya Mama ta Mike zuwa Dakinta nan ta iskesu Jugum Jugum Gaisheta suka Farayi Ta amsa Tana kallon Zaina Dake kwance Tana Sauke Numfashi Ahankali Cikin Tsausayawa Ta kalli Umma Tana Fadin"Fatima ya Jikin Haliman..? Tana ta barcin ne Har yanzu..? Umma Ta Dago Kanta Idanuwanta Har sun kumbura Tace"Eh Hajiya Mama bata Tashi ba Har yanzu..Saukin mata na Taba Jikinta zazzabin ya Sauka.."Kada kai Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"uhmm..Allah kara afuwa..Rukayyah da Hannatu ku Taho Alhaji na Kira..Ku kuma ku saki Ranku kuci Abinci Haka Allah ya Tsara..Bamu isa mu Gujema Kaddaranmu ba..! Mama Safiya tace"Hakane kam Hajiya Mama..Bawa bai isa yaGujema Kaddaran Allah ba,..Allah ya kara Shiryamana Zuru"a Nima yanzu Da kika Shigo Su Nene nake ta ba Baki kan suyi Hakuri kada Fushinsu yayi yawa in yayi yawa Zasu saka Zain din ya kara Shiga Wani Hali Uwa uba ga Yarinyar nan Abun Tsausayi Wlh.." Hajiya Mama Ta jinjina kai Tana Fadin"Allah Miki albarka Safiya...Naji Dadin mganarki Fatima da Aisha Don Allah ku bar wannan kukan..Ke kuma Zareena Ji da yarinyar nan Sai kukanta nake ji Tun dazu ku kuma kuzo mu tafi yana Jiranku.."Daga haka ta Fice Daga Dakin Inna Rukayyah da Inna Hannatu suka Rufa mata Bayan Sun iske Alhaji Tsoho nata Lallashin Ya"yansa da Nasihu Sai gashi Lokaci Daya Sun Warware sun kuma ji Damuwarsu ta Ragu Suma Su Inna Rukayyah suka nemi Waje suka zauna suna Sauraransu Cikin Mganar Alhaji Tsoho ya kallesu Yana Fadin"Kun gano Inda muka Kuskure kan wannan Al"amarin..? Gabadayansu kai suka Girgizamai alaman A'a Cikin Hikima Yacigaba da Fadin"Kuskuran mu kadan ne .Bazan ce Saboda mun kai ya"yanmu kasashen Ketare karatu ne ya Jawo mana wannan Abun ba A"a Abun ba Haka yake ba Duk da wasu Dalilin Haka Suna Lalacewar ammh Hakan ba zai zama Hujja ba Tunda Nima nayi wayon Kashashen Ketaren kuma Wlh Allah ban yi wannan Lalacewar ba Kuma gaku kunyi kuma har yau wani Abu mai kama Da haka bai Faru ba..Nayi Tunanin Sakacinmu da kuma Rashin Bibiyar ya"yanmu akan lokaci Ko kuma nace Rashin Saka Ido Inda ace muna Kokarin Saka ido Sosai koda basa gabanmu Achan Kasar da suke mu Samu wani mai amana wanda zai Dinga Kula da Shige da Ficen ya"yanmu na Tabbata in da Muna Haka zamu samu labarin wani Abun kafin ya Girmama kun gane Abunda nake nufi..? Gabadayansu suka ce'Hakane Tabbas..Alhaji Tsoho.."Mirmishi yayi Cikin Jin Dadi yana Fadin"Yauwa..Tunda mun gano haka Sai muyi Kokarin Kiyayewa Yanzu akwai Ragowan Yaranmu da Basa gabanmu Bana jin Ta zafeera Tana Gaban Rukayyah ne kuma nasan ita da Shitu bazasuyi Sakaci Da Tarbiyansu ba.." Da Sauri Inna Rukayyah Tace"Insha Allahu Alhaji Tsoho muna iya bakin Kokarinmu.."Alhaji Tsoho yace"Yauwa sai Abubakar karami ko..? Yana ma wata kasa ce .?Da Sauri Daddyn Abuja yace"Shi yana Cyprus ne Alhaji ammh ya kusa kamallawa.."Alhaji Tsoho ya gyada kai yana Fadin"Masha Allah...Sai mai sunan Manya Umaru Faruq shima yana Chicago ko..? Baban Kaduna ya gyada kai yana Fadin"Hakane..! Alhaji Tsoho yace"Allah ya tsare su..Dukkansu zamu saka musu ido.."Baban kaduna ya Jinjina kai yana Fadin"Insha Allahu Alhaji Tsoho.."Kallonsu yayi Dukkansu yana Fadin'"Mganar Hamdiya kuma inda yafi Sauki za"a Daura auran.." Daddyn Abuja ya Kada baki yace"Nan za"a Daura Alhaji Tsoho.."Jin haka yasa Kowa yayi Na"ama Da mganar,Alhaji Tsoho yace"Sai Mganar Zafeera Zan bata Lokaci Zuwa bayan Bikin Hamdiya in bata kawo wani ba zan bama yaro nan Ahmed Dama.."Kowa yayi Na"am Da mganar nan sukaci ba Da Tattaunawa,Kafin Alhaji Tsoho ya Hada kan ya"yansa sukaci Abinci Suka koshi suka Sha Ruwa Su Inna Rukayyah kuma suka koma Dakin Hajiya Mama Kowacce Tana hada Kayanta Gobe zasu wuce. Sai Gabda Mangariba Zaina ta Farka Daga Barci Tana kuma Tashi Da kuka ta tashi kamar yadda Ta kwanta Dashi,Mganar Duniyan bata Tanka kowa ssi Umma da ita kadai Take mgana Dakyar ta Lallasheta Ta Rakata Tiolet tayi alwala tazo Tayi Sallolin Dake kanta azaune Tana Sallah Tana kuka Domin kamar Magiji Haka Abun ke Dawo mata. Abunci kuma Umma Tayi Tayi ammh Taki ci Zareena Ta kalli Zaina Tana Fadin"Kici Abinci Zaina..Don Allah.."Tana kallon Cikin Idanuwan Zareena Sai Hawaye ta kasa Mgana ganin Haka yasa Handiya Taje ta Kira Hajiya Mama tazo Tana ta Fada kan Zaina Taci Abinci ammh Sai Taki ci sai da Tayi mata jan Ido kana Ta yarda Ta karbi Abincin Daga Hannun Umma ta Tusa Ko Loma Goms Batayi ba Zuciyarta Ta Fara Tashi sai Amai Tun Tanayi da karfinta Har ta kasa Umma da Mama safiya suka Riketa ganin Bata da karfin Jiki yadda Take kuka ne Tana Hawaye yasa Tsausayinta ya kara Shiga Ransu Ruwa aka kawo Umma ta wanke mata baki Hamdiya kuma ta Tsaftace Wajen kafin kace me Jikinta ya Sake Daukan zafi Ta kwanta Jikin Umma Tana Rawan Sanyi. Abba ne ya aiko kan su Umma su Fito su Tafi Gida,Dole Nene da Umma suka Mike Kowacce Fuska akode,Hajiya Mama Tace Umma ta Kwantar da Zaina kan Gadonta su Tafi sai dai me Tana Mikar da ita ta makalkaleta Cikin kuka da Rauni Karo na Farko Datayi mgana.. "Umma...Zan...Zan biki..! Tafada Cikin Fitar kwallah gabadayansu da kallo suka Bita Lokaci Daya Ta maida kanta Jikin Umma Tana Sauke Numfashi Ganin haka yasa Hajiya Mama taje ta gayama Alhaji Tsoho Halin Da Ake ciki Cikin Nazari yace"Barta su Tafi da ita..Taje gidan ta Huta na wani Lokaci Shima ai zainullahin baya cikin Natsuwarsa yanzu haka zuwa gaba in komai ya Daidaita za"a samu Masahala.."Da haka Taje tace Umma su Tafi da Zainar gida Inji Alhaji Tsoho. su Mama Safiya da Mom Iklima suka Taya Umma Kama zaina suka Rakasu har Haraban Gidan Inda Direban Abba ke jiransu,Zareena ma Ta Goya yarta Tabi su Umma,Su Baban Kaduna Duk suna Waje nan sukayi sallama Kowane ba Farinciki ammh Da Sauki ba kamar Dazu ba,Abba ya kalli Umma yana Fadin"Fatima Har yanzu Jikin Halimar..? Kai Umma Ta Dagamai Tana Jin Taruwan kwallah Saman Goshinta ya Taba wanda yasa Ta Bude Kodaddin Idanuwanta Tana kallonsa Cikin Tsausayawa Yake Fadin"Sannu Halima..Sannu kinji ko..? Nima Hakurin zan baki Allah ya kiyaye kawai.."Yake Fada haka su Baban Kaduna Sallama sukayi Suka Shiga Mota Nene dai ba Baki sai dai kaga Tayi Shuru Kawai Tana kallon Mutane Abun ya Daketa Sosai.. Koda su Umma suka Koma Gida sun iske Sadiq ya koma Labari kuma Tuni yakaima Zainab Tunda Sadiq daya Dawo yake Fadamata itama taci kuka bata ma Kara Jin Wani kukam ba sai Da Taga Shigowarsu Umma haka Tazo ta Rumgume Nene Tana kuka Gefe Daya kuma Tana kallon Umma Dake Rike da Zaina wacce ke Kuka kasa kasa..... Dakinsu Ita da Zafeera Umma ta kaita ita da Zafeera da Nene Abba kuma ya wuce Dakinsa,Kwantar da ita sukayi suna Mata sannu Jin Jikinta yayi zafi Zareena ce ta Dago Tana Fadin"Umma ko zan kira Aboki Haddir ne yazo ya Dubata..? Wannan zazzabin yayi yawa ajikinta..! Numfashi Umma ta Sauke Tana Fadin"Kirashi in zaki sameshi.."Tafada Tana kallon zaina wacce ke kara Shiga Cikin Bargo Tana Kudundune kanta Jin za"a Kira Haddir yasa ta Dago kanta da Idanuwanta da suka Kumbura Tace"A"a Umma..Kada ki kira kowa..Ki bani panadol kawai .Domin wannan Ciwon Da nake ji acikin Kirjina Bashi da mgani Har Abada..! Tafada wasu Tagwayen Hawaye na Zubomata kafin ta koma ta kwanta Tana maida Numfashi Umma Ta Dade Tana kallonta Batayi mgana ba Nene ta kada kai Tana Fadin"Dole azo adubaki Sa"adiya Dare muke gudu..Dama ba mganin Damuwarki zai baki ba, na lafiyarki ce Domin Damuwa ko Mu bamu da mganin Tamu sai Hakuri kawai.." Zareena Ta Ijiye Jakar Zaina Wacce Ta tattaro mata Daga Gidan Alhaji Tsoho nan Gefen Gado Jakarta ta Dauko Tana Laluban wayarta Cikin karamar Jakarta Take fadin"Kuma Nene Zazzabin yayi yawa fa..! Hannu Umma Ta Dagama Zareena Tana Fadin"Kyaleta Zareena Ayi mata Abunda take so..Ina Jin Tsausayinta Fiye da yarda nake jin Tsausayin kaina Bari nayi sallahr Mangariba nazo na Taimaka mata tayi sallah Tayi wanka sai na Bata mganin Ta kwanta.."Ba suyi mata gaddama ba Suka Fice Daga Dakin Umma dai Kofar Tiolet ta Tura ta Shiga ta Dauro alwala Tayi sallah Ta Tada Zaina wacce Zazzabin ya karayin zafi Ta kaita Tiolet Ta Taimaka mata tayi wanka Tazo Ta Taimaka mata ta zura mata wata Doguwar Riga Umma Ta kasa Daina Jin wani iri game da Kukan da zaina keyi ta kasa ma Lallashinta,Dakyar ta sakata Tayi sallah azaunr kamar ta Kife Fita Tayi zuwa Kitchen ta Iske Zainab na Hada Fruit Salad shi ta Diba Ta kai ma zaina Dakyar ta iya Bata tayi Cokali Biyar ta kauda kai Allah yasa batayi Aman ba wannan karon Ta Balla mata panadol Ta bata tasha Ta koma ta kwanta Fadi Take"Umma Rufamin Bargo..Sanyi..Sanyi.."Hakoranta na Haduwa Rufamata Tayi Tana Tofa mata addu"a bata barta ba sai Da taga kamar makyarkyatan ya Ragu kamar zatayi Barci kana ta Fita Zuwa nata Dakin Tayi wanka Lokacin ana Kiran Sallar Isha"i Tayi Kan sallayar ta zauna kawai Domin Gabadaya Gidan yau ba Dadi Nene ma na Dakinta Haka ma Abba Zareena ma Tana Dakin Datake sauka ita da Jalal Zainab Kuma dasu Saudat suna Falo duk da su Yara ne basusan Komai ba Sun Fahinci gidan Ba kamar yadda yake ba Sadiq ma yana Dakinsa bakajin Motsin kowa. Babu Wanda ma ya Nemi Wani Abu Zainab ce Tayi Tunanin Hada Fruit salat Saboda Ruwa Ruwa ne zai yi Dadin sha Toh banda Wanda Umma ta bama zaina Ko Kitchen din ba wanda ya kallah Zareena ko Tana Dakin Datake sauka Bayan tayi Wanka Tayi sallah Ta Kira Haddir Sai da tayi mai Kira Biyu ya Dauka Sama sama suka gaisa Take Tambayanshi yana ina..? Yace mata yana cikin asibiti..Cikin Jimami tace ina zain Ya bata amsa da bai sani ba Tunda ya Fita da Mota Dazu bai kara ganinsa ba,Kuka ne yaci karfinta ta yanke kiran Shi kanshi Haddir kukan yake Tun Dazu yazo cikin asibitin ya kulle kanshi Cikin Office dinsa yana ta kuka Kukan Tsausayin Iyayensu da Zain din Shi kansa da kuma Uwa Uba Zaina wacce Yake Tunanin wani Hali Take ciki yanzu..? Shi kanshi yayi kuka kan wannan lamarin Ballatana ita. *Shakira..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️    *BOOK 1*              2️⃣0️⃣ "Zain kuwa Tunda ya koma Gida ya Shiga Cikin Bedroom dinsu ya kulle kansa ya zauna akasa ya Hade kai da gwiwa ya Dinga Rafzan kuka Kukan Daya Dade baiyi kamarsa ba bama zai iya Tuna Rabonsa Daya Zubar da Hawaye ba Duk da ya kasance mai Taurin zuciya BA Abu bane karami bane zai saka kaga yana kuka ko Lokacin Suna yara Haddir yafishi Rauni ko Rashin Lafiya Zareena Take ya Shiga Tashin Hankali kenan Har kuka yana yi ammh bandashi iya wutar Rauninsa Sai dai idanuwansa su kada suyi Jajir Jijiyoyin kansa Su Tashi Radau kamar mai wani Cuta yau gashi Rana tazo Daya zauna Yana ta kuka Kukan Tsausayin kansa Dana kunyar Iyayensa uwa uba kuma kunyar Zainarsa da wani ido zai kalli Firstlove ya gayamata Duk wadananan Abubuwan sun Faru..?ya sani yanzu Lokaci ya Kuremai Karyansa kuma Tagama karewa. Haka ya kwana cikin wannan Halin bai iya cin komai acikinsa ba Wayarsa kuma Rashin Chaji yasa Ta mutu,Ruwa Kadai yake sakama Cikinsa,Kafin safe wani Mugun zazzabi ya Rufeshi Ga Ciwon kai Dakyar ya iya Tashi yayi sallar asuba ya koma ya Kudundune kan gado yana Rawar Sanyi. **** Dina na kwance kan Makeken Gadonta,Misalin karfe 9:30am na Safe Tun barcin Jiya bata Tashi ba Sallah ba sai Wajen 7am Tatashi Tayi ta itama Din Domin Hajiya Batula tazo ta matsa mata ne,Kasala Take ji da kuma Tsinkewar miyau Don ma Allah ya Taimaketa Cikin bai Mata Laulayi Sosai ba ballatana ta Wahala ko amai ba sosai Take yi ba sai Taji yunwa in Taci Abincin sai ta Dawo Dashi.. Hankalinta kwance Take Barcinta Ringing din wayarta Ya Tada ita Daga Barcin salama da Farincikin Datake yi Dagowa Tayi Lokaci Daya da karamin Tsaki Kafin ta Jawo wayar Dake gefenta Domin Dazu da asuba sunyi mgana da Ummi maimuna,Tana ganin Zakiya ce ke Kiran Ta Daga da Sauri Tana Fadin"Yanzu fa nake cewa in na Tashi zan kiraki..! Dagachan Bangaran zakiya ta saki Dariyan Nishadi Tana Fadin"Kaga manya manyan mganin kanana...Mrs Zain Usman Abubakar saulawa Barka da safiya.."Mirmishin Jin Dadi Dina ta saki kafin tace"Barkanmu..Ya gajiyan Jiya... ? Zakiya tace"Gajiya Tabi Jiki..ya Karfin Jikinki..? Ki Dinga kula da kanki Dina Kinsan Ayanzu wannan cikin Shine fa makamin mu..' Dina Ta yamutsa Fuska Tana Fadin"Wai yanzu haihuwansa zanyi..? Allah ban Shirya Haihu yanzu ba zakiya.."Zakiya tace"Ya zama Dole kuwa Hajiya..Kina ganin ba Domin Cikin nan ba akwai wani uzurin da Danginsa zasu karba ne ballatana Har su Dubeki..? Kima Dawo cikin Hayyacinki.."Dina Ta Kauda zencen da Fadin"Hmmm kawai..! Zakiya Tace"Na kiraki ne na Gaya miki na cikama Dr.Imran alkawarinsa Daran Jiya Duka nashi ne Bai ma jima da Tafiya ba..Gaskiya zan Dan Raka da Gayen ya san Harka yafi Wadanan Tsoffanfin da Dama chan Basir da girma ya gama Cutar dasu.."Baki Dina ta saki Tana Fadin"Kai zakiya Don Allah ki bar wannan mganar...Ni da nake so kema ki Fidda wani ki aura Duka mu bar Rayuwa barikin nan.."Zakiya Tace"Wa zai yi Aure..? Wai ni..? A'a Wlh ko Baba yagaji da mganarsa ya kyaleni Ba yanzu zanyi Aure ba Dina Domin har yanzu ban samu Wanda yayi Daidai Dani ba nafi son na Auri Ustaz Wanda bai san komai ba na Auresa muyi ta Shan Soyayyarmu.."Dina ta Rike baki Tana Fadin"A ina zaki samu..? Zakiya Tace"Acikin gari mana..Kina mamaki ne..?karki manta Bawa baya cire rai da Rahmar Ubangijinsa.."Dina Tace"Tsiya na Dake Sani..Ammh kina Take sanin naki.."Zakiya Tace"Mutane nawa ne acikin Duniyanan Suna sani kan Abu kuma Suke Takewa... ? Ke duniyar nan fa cike da Mutane Dabam Dabam masu aikata Laifin ma sun fi kowa sani Ni kyale ni Nafi jin Dadin Rayuwata ahaka kin ganni nan Kedai Da kika ga zaki iya Auran Shikenan.." Dina Tace"Allah ya Shirya.."Zakiya Tace"Ameen..."Har zakiyan Zata kashe wayarta Dina Tace"Wai ni ya matsayin Matarsa ne yanzu..? Nifa tafi Tsayamin arai kuma Tayaya zan koma Gidansu da zama kina ganin ba mtsala..? Zakiya Tace"Ai yanzu bai da Wata mata bayan ke..Agaban idanuwanki Kika ga Abunda ya Faru..Na Tabbata ko Waye zai saka baki bazata Saurareshi ba..wannan Firstlove din ya kare Daga Jiya Ina gayamiki..Mganar zuwa Gidansu kuma yayi Daidai..Kinga kin samu Hanyar kusanci da Zain kenan da Duka Ahalinsa Kuma Bashi da wani Ikon Wulakantaki Tunda kina Gaban Iyayensa ne Uwa uba kuma Alhaji Tsoho bazai bari wani ya Tozartaki ba..' Dina Tace"Hakane....Da Farko ina Jin Tsoron Haduwa da Zain..Gabana nata Faduwa.."Zakiya Tace"Babu Abunda ya isa yayi miki..Yanzu ma Bata ke yake ba..Yana ta kansa ne ki Sharesa karma ki Kirashi In kin koma Gidansu Dole ku Hadu kuma Lokacin bashi da wata mafita.."Dina Ta gyada kai alamun gamsuwa Da sauri Zakiya tace"Sai mun sake mgana..!. Daganan suka yanke Kiran Mika Dina Tayi kafin ta yaya Bargon Dake Jikinta ta Zuro Kafarta Waje Silafis Din Dake bakin Gadon Ta zura Ta Fada Tiolet Da Farko Tana Ciikin Damuwar Taya zata iya Rayuwa awani gidan da ba nasu ba..? Ammh Mganganun Zakiya yasa Duk wani Fargaba ya Gushe mata. ***** Zuwa Safiya sai zazzabin Jikin Zaina ya Ragu Taji Sauki Sosai Har Tatashi Da kanta Tayi wanka Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Umma adakin Ta kwana Tare da ita Dukkansu Suna Jere kan Darduma Bayan sun Idar da sallah Kowanne acikin Ransa Abubuwa Dadama yake sakawa. Umma Azkar takeyi ammh Rabin Hankalinta baya Jikinta Tatafi Duniyar Tunani in Ta Tuna Abubuwan da suka Faru Jiya sai Taji Tsinkewar Zuciya da kuma Raunin Rai,gabadaya Abun ya Faru ne wanda basu Taba tsammani ba,Tunda Take bata Taba kawo ma Zain wannan Lalacewar ba Ta sani ita Ta Haifi Zain Kuma Soyayyar Uwa Da Danta na musamman ne Ammh ko afili Bata Taba Nuna wata alaman da za"a Fahimci Zain Danta bane bata Taba Damuwa da Sha"aninsa ba komai nashi Nene ne,Ita Halima itace yarta Domin Ita ta Riketa Tun tana karamarta har zuwa yau Tana Jin Dacin Damuwar Datake ciki Domin Wata Shakuwa ce tsakaninsu Kamar ta Uwar Data Haifi yarta da Cikinta ayanzu Tafi Dora Duka Laifin kan Zain ne ayayinda Gefe Daya kuma Take matukar Tsausayin Zaina,ayanzu ma Haka Ita Take Tunani Tana Tunanin wani Hali kuma zata Shiga agaba..? Tana Tsausayinta Domin Tafi kowa sanin yadda zaina Tafi yarda da Zain Fiye da kowa aduniya Ta soshi Tun bata san kanta ba Tana Fatan Allah yasa Zuciyarta Tayi Juriya wajen Daukan wannan al"amarin. Kallonta Ta maida kan Zainah Wacce ta Kurama Gabanta ido Ga Carbi a Hannunta Tana ja ammh bawai Tasan Abunda Take Fada bane Hawaye ne wasu na Koran wasu suke zubomata gani Take kamar a mafarki Abubuwan suka Faru in ta Runtse ido Da ta Bude kuma sai Ta Gasgasta Abunda ya Faru yau wai Firstlove ne yayi ma Wata Mace ciki ba Ita ba macen ma ba Wata mai Daraja ba karuwa wacce ya ijiye sunan zaman Dadiro Wannan Abun yafi komai yimata Ciwo da Nauyi akirjinta Ji Take kamar Zuciyarta Zata Fashe Tana Jin wani Zafi Zafi yana Fitowa Daga kasan Ranta,Tana jin aduniya kuma wa zata kara bama yardanta..? Tunda wanda tafi kowa yarda dashi yau yaci amanarta Wanda yafi kowa saninta da sanin Rauninta yau yayi sanadiyar da Rauninta ya bayyanata Tanajin kamar ta Mutu ta Huta da wannan Bacikin Daya Ziyarceta Daga Jiya zuwa yau. Umma ce ta Dafa Kafadarta Lokaci Daya Tana Fadin"Zaina..."Cikin wani yanayi na karaya da Tsausauyi Juyowa Tayi Tana kallonta Idanuwanta na Zubar da kwallah ganin Umma yasa Rauninta ya Karu kawai sai ta Fada Jikinta Tana sakin kukanta Umma ta Riketa Tana Lallashinta Itama kukan Zuccin Take ammh Tana Kokarin Dannesa Saboda kada Ta kara Raunamama Zainar zuciya. Sai Da Tayi kukanta ya isheta kana ta Dakata,Umma ta Dago ta Tana Share mata Hawaye Cikin Sigar Lallashi Take fadin"Kinga baki da lafiya ki Daina wannan kukan kinji ko..? Jikin ki da zazzabi har yanzu kada ya kara Daukan zafi.."Tana kallon Umma da Rinannun Idanuwanta Tace"Umma Don Allah a zamana da ya zain akwai Abunda na Rageshi Dashi ne..?Ko kuwa akwai wani Abunda nake mai wanda baya Burgeshi ne..?ko kuwa Daman chan Baya sona ne Umma alfarman na Tashi agabanki yasa ya Aureni..?meyasa Firstlove zai min Haka..?Umma Meyasa bai ce min yana son ya kara Aure ba..? Wlh bazan Hanashi ba Zan barshi ya kara aure indai zai Cigaba da zama Dani a matsayin matarsa,Da kuma Kare kansa da aikata zina...! Ta karishe Fada Cikin wani Gunjin kuka Tana Sulalewa Jikin Umma ita kanta Umman kukan Take Cikin Zuciyarta dago da Fuskarta Umma Tayi Tana Girgiza mata kai Lokaci Daya Tana Fadin"A' a Diyata ki Daina kuka..Bari kuka.."Take Fada Tana Share mata Hawaye Cikin Wani irin Dacin Zuciya Zaina Tacigaba da Fadin"Umma Dadiro fa Firstlove...Dadiro ya ijiye har yayi mata ciki..? Zuciyata Tana zafi kamar zan mutu Ina jin kamar bazan kara Rayuwa ba..Bani da kowa Umma mahaifana Duka sun Rasu wazan Tunkara wa zai Tsayamin ga wannan Jarabawan Rayuwan Data Fadamin Umma bani da kowa.." Take Fada Tana kuka kamar Ranta zai Fita,Umma Tayi mata Kuri Tana kallonta,Cikin bayyana Bacin Ranta ta saka Duka Hannuwanta Ta Tallabi Fuskar Zaina Tana Fadin"Dago ki kalleni nan Halima..! Tafada Cikim kakkausan Murya jin Umma ta ambaci Sunanta yasa Zaina Ta Dago da Jajayen Idanuwanta da suka kumbura Tana Binta da kallo Cikin Nuna kauna da Tsausayi Take fadin"Tunda kika taso na Taba nuna miki wani bambamcin Da zaki ji cewa bani na Haifeki ba..? Ta Fada Tana kallonta Girgiza kai Zaina Tayi Hawaye suna kwararan mata Umma ta Cije baki Kafin ta Cigaba da Fadin"Toh meyasa kike Tunanin baki da kowa..? Kalleni nan Halima kina da kowa ni Fatima nice Uwarki Abban su kuma Shine Ubanki Har gobe,Kidaina Tunanin baki da wanda zai Shiga Lamarinki Ni nan zan iya Shige miki gaba akomai Wlh Na Daukeki Tun baki Cika Shekara Biyu ba aduniya Halima Na Rike Tamkar Diyar Data tsaga Jinina ta Fito Keda Zafeera da zareena Ban Taba Jin bani na Haifeku ba ina muku kallon Shakikan ya"ya ne Saboda Haka ki Sani Bazan Taba bari Acuci Rayuwarki ba..Zan Tsaya miki Tsayin Daka Har sai Zainullahi YA SAKE KI..! "DAM! gaban Zaina ya Buga da Sauri Ta kara ware idanuwanta kan Umma kafin ta zaro Ido Cikin Dishashiyar murya Tana Fadin"Ya Sake ni kuma Umma..? Sakin Fuskarta Umma Tayi Ta Mike Tana Fadin"Tabbas sai ya Sake ki..Bazan yarda kiciga da zama da Mayaudari mazinaci irinsa ba..Ya baki Takardanki Bayan kin gama idda kina karatunki Allah zai kawo miki Wani Mijin Mai Nagarta kiyi Auranki..Ammh ban Zan Juyar da kai Ina gani ki ciga da zama da Wanda bai san Darajan Kansa ba Ballatana yasan Darajan ki ba.."Baki Hamgame kawai Zaina kebin Umma da kallo da wani bugawar Numfashi Hade dana Zuciya Lokaci Daya kuma da wani kaunar Umma da Kimarta Suka karu acikin Idanuwanta Tana Tunanin Aduniyan nan akwai masu Hali irin na Umma..? Masu maida Dan wani nasu Su Ki nasu..?masu bayyana Laifin nasu saboda wani bare..? Bata Taba Jin Irin Mai Halin Umma ba Bata Taba ji ba. Cikin mamakinta ta kara Bude baki Tana Fadin"Umma Saki fa kika ce..? Firstlove bazai Taba sakina ba Nasani.."Da sauri Umma Ta waigo Tana Fadin"Dolensa ya sake ki ko yana so ko baya so.."Kuka kawai Zaina ta kara saki Kamar wacce Aka Daka Umma ta Cije baki Tana Fadin"Gwara kiyi kukan Rabuwa Dashi..Da ki zauna Dashi Ki Cigaba da kuka Har karshen Rayuwarki ba Halima..! Daga Haka ta Fice Daga Dakin Ta bar zaina na wannan kukan,Kukan wani Hali zata Shiga in aka Rabata da Firstlove..? Wata zuciyar tace mata ke kuma sai ki zauna Dashi..Kina kallon Dadirosa Ta Haihu Kuma ya aureta ya Hadaku Gida Daya Tare in Hakan ta Faru ya zakiyi..? tuna Haka yasa sai Da Taji kamar Numfashinta zai Dauke Cikin ganin Jiri Jiri Ta mike Ta Fada Bisa Gado Tana Fadin"Bazan iya Jurewa ba...Allah gani gareka...Hasbunallahu Wani"imal wakil.." Take Fada Tana wani Gunjin kuka mai cin rai da kuma Saka Tsausayi ga zuciyar mai Sauraro. ****** Haddir gida ya koma ya kwana Cikin Halin Damuwa kamar yadda Ta kasance ta Bangaran Kowa da kowa Gari na waye Tun Safe ko tsayawa Karyawa bai yi ba Duk kuwa nacin da Hajiya mama Ta Dinga mai kan ya Tsaya ya karya bai tsaya ba ya Wuce asibiti,Adaidaita ya Hau Zuwa asibitin Tunda Motarsa na Wajen zain kuma Tun Jiya Daya Dawo yayi ta Kiran Layinsa Tun Tana Ringing baya Dauka Daga karshe sai ma yajita a kashe ya Shiga Tashin Hankali Dakyar yaga Safiya Saboda Zullumi Yana Tunanin Kila Zai samu Zain din acikin Asibitin sai kuma yaje bai sameshi ba Kuma Dr Peter ya Tabbatar mai Tun jiya bai saka Dr.Zain acikin idanuwansa,ba Kuma gama Motarsa nan a Haraban asibitin Tun Jiyan nan Daya barta bai Dawo ya Dauka ba, Hakan ya Tabbatar da cewa Zain Bashi a kusa Zuciyarsa ta Fara Rawa Yana Tunanin to yana ina..? Tunanin zuwa Gidansa ya Shigeshi Ko patient ko Daya bai Tsaya Dubawa ba ya samu Mai adaidaita ya Hau zuwa Lowcost Gidan Zain Yana zuwa Bayan ya sallami mai adaidata ya Fara Buga Kofar get Din Tanimu maigadi yazo ya Budemai ganin Shine Yasa ya Fara Washe baki yana mai Kirari bai ma Tsaya Sauraransa ba,Ganin Motarsa A Haraban Adana motoci ya Tabbatar mai da Zain yana Cikin Gidan ko Takan Tanimu maigadi bai bi ba,ya Nufi Kofar da zata Sadashi Da Falon Gidan Har yana cin Tuntube Tanimu megadi Abun ya Dauremai kai ganin irin wannnan Saurin da Haddir yake yi Da kuma yanayin Dawowar da Zain yayi Jiya ya Tabbatar mai da Cewa ba Lafiya. Haddir yana Shiga Falon gidan yaji Shuru Tun Daga nan yake Kiran Sunan Zain ammh sai yaji Shuru Hankalinsa ya kara Tashi,Shi kuwa Zain yana Cikin Bedroom dinsa kwance Cikin Wani Hali yana jin Kiran sa da Haddir yake ammh kuma bazai iya Tashi ba Ballatana Har yayi mgana,Ammh yana Fatan Allah ya bashi Ikon Shigowa ciki Domin yana Bukatar Taimako. Allah ya karbi addu"arsa Domin kai Tsaye Bedroom din ya nufa yana Fatan Allah yasa Zain yana Ciki,Da Farko Knooking Din Kofar ya Farayi jin Shuru yasa ya Turata ta Bude ya Shiga yana Wurga Idanuwansa zuwa Cikin Dakin Cikin Ikon Allah sai Idanuwamsa suka Hango Masa Zaim kwance cikin Bargo ba yarda  yake ya Dunkule atsakiyar gado acikin Bargo Hankalin Haddir ya Tashi Da Gudu ya karisa Kan gado ya Dago zain yana Kiran sunansa Cikin Tashin Hankali,Ammh Zain baya iya mgana Jikinsa yayi zafi Hakoransa suna Haduwa Waje Daya Hawaye kawai suke Zubomai ta Gefen Kunnuwansa,Hankalin Haddir ya Gama Tashi Ganin Halin da Dan"uwansa kuma Amininsa Yake Ciki,Cikin Tashin Hankali Ya Dagosa ya sakamai Filo ya Jingina yana Binsa da sannu Toilet ya Shiga ya Debo Ruwan sanyi a karamin Baho ya sako karamin Towel yazo yana Goge ma Zain Jikinsa Daga kansa Zuwa Kirjinsa Bayan ya Sabule Vest Din Dake Jikinsa Bai barsa ba sai da yaga Jikinsa ya Rage zafi kana Zain kuwa kansa kawai yake Dafewa Cikin azaban Ciwon da Radadi Lokaci Daya Yana Zubar da Hawaye masu Zafi Haddir na Faman Sharemai Shima kamar yayi kukan yake Fadin"Kagani ko Zain..? Dama irin wannan Lokacin nake jiye maka..! Yake Fada Shima yana Share kwallar Kwantar Dashi yayi ya Maida Komai cikin Tiolet Key Din Motarsa ya gani nan saman gadon ya Dauka ya Fice Da Gudu Yana zuwa ya kunna Motar ya Budeta ya Shiga ya Bata Wuta Cikin Gaggawa yayi ma Tanimu megadi Hon ya Bude mai Get ya Fice Daga Gidan,Wani Phamarcy Dake kusa Da Gidan yaje ya Siyo Mganguna da allurai Da kuma Drip Cikin gaggawa ya Dawo yazo ya Sakama Zain Ruwan bayan yayi Mishi alluran Ruwan Sai da ya sakamai masu Sinadaran Abinci Guda2 Kanana Bayan sun kare ya sakamai Babba Guda Daya Harda alluran Barci yayi mai kafin Lokaci Kadan Barci ya kwashesa Sai Lokacin Haddir ya Numfasa Gefen gadon ya koma ya zauna yana Kallon Zain yadda Zufa ta Fara Ketomai alamun zazzabi ya Fara sauka Remot ya Dauka ya Kunna mai A.C saboda Iska ya koma Kasan Cafet din Bedroom Din ya Zabga Tagumi Yana Bin Dakin da kallo Madubin Dakin ya kalla Shake da kayan Kawa na mata,Ga Jakunkuna da Takalman Zaina,Kan gadon ma Kayan Barcinta ne yana Tunanin kila zain ya Daukosu,Yanzu ina amfanin Haka..? Wa gari ya waya..? Da aace Zain yabi Shawaransa da Duk haka bai Faru ba.. Yana nan zaune har 1pm na Rana Tayi,Ya tashi ya Shiga Tiolet din yayi alwala yayi sallah bayan ya idar Lokacin Ruwan Daya sakama Zain din ya Kare sai yaCiremai ya sakaamai Dayan Har yanzu yana Ta barci alluran barcin bata Sakeshi ba,Fita ya sake yi Wani Restaurant yaje yayo Takeawaya Guda Biyu yazo yaci Daya bawai Domin yana Jin Ci ba sai Domin kada Shima yunwa tamai illah sai kuma Zain Wamda ya Dinga zama Dashi ba bai Farka ba sai Gabda La"asar,Kuma alhamdulillah Zazzabin ya sauka Ciwon kanma Babu Shi ya Taimakamai yayi wanka ya Dauro alwala yazo ya Rama Salolin Da suka Subucemai Kafin Haddir ya gabatar mai da abinci jalop din Shinkafa ce kadan yaci sai Madaran Yoghourt,sai Rabin kaza matsamai Haddir yayi yaci Sosai ya bashi mganguna yasha Ya koma ya kwanta Ya Lumshe Ido kawai yana Tunanin Rayuwa sai chan ya Bude yana kallon Haddir Dake gefensa yana Duba wayarsa Cikin Muryan Ciwo da Kasala yace"Firstlove Bata Dawo Gida bane..? Kallonsa Kai Tsaye Haddir yayi kafin yace"Tana Gidan Abba..Domin Bata agidan Alhaji Tsoho.."Daga haka ya Tsuke bakinsa Shima Zain din kai ya Rausaya yana Fadin"Nasani Daman bazata zo ba...Itama zata Gujeni Allah na Tuba.."Yake Fada yana Sharan kwallah Haddir na kallonsa bai yi mgana ba Domin bashi da Abun cewa. Suna nan Zaune Har barci ya Fara Fizgan Zain din sai ga Kiran Mama Safiya ta wayar Haddir Tana Fadin yana ina ne..? Gasu Gidan Abba Usman zasu wuce Jin haka yasa yace ma Zain bari yaje ya Dawo Daganan Daya Fita Bai zame ko"ina ba sai Gidan Abba Yana zuwa ya Iskesu Duka aharaban Gidan,Daddyn Abuja da Mama Safiya sai Hamdiya,Dasu Umma sai Abba Da Zareena wacce ke Rike da yarta Su Baban kaduna sun Dade da Tafiya Inna Rukayyah ma Ta wuce Inna Hannatu ne kadai sai Gobe Zata bi Jirgi ta koma Kowa kagani Fuska ba Walwala Dadyn Abuja da Abba sun kebe sai bashi baki yake Hakama Mama Safiya sai bama Su Umma Hakuri suke da kuma Nuna musu Yadda Da kaddara ya zama Dole ga Dan Musulmai,Umma Dai Tana Jin Mama Safiya ne kawai Nene ce ma ke Fadin bakomai Haka Allah ya kaddara Ita kanta zaina Mama safiya Tayi Ta bata Hakuri Tana chan suka barta Tana kuka wanda Ta wuni yinshi inda Hawaye suna karewa da Tuni Hawayen Zaina Sun Dade da karewa. Zuwan Haddir yasa suka Dakata ya Rankwafa yana gaida Iyayen nashi mata kafin ya karisa wajensu Abba ya Duka yana Gaishesu Abba ya amsa Cikin Sanyi,Daddyn Abuja ne ya kalleshi yana Fadin"Kai ina Ka Shiga ne Tun dazu Alhaji Tsoho na nemanka bai ganka ba..? Ko ka Shiga asibiti ne.? Kansa na Kasa yace"A"a Daddy nadai Shiga da safe na Fita...Zain ne naje na samu agida Yana kwance ba lafiya.."Daddyn Abuja yace"Ashha Subhanallahi..Meya Sameshi..? Haddir yace"Wlh Daddy Zazzabi ne mai zafi da Cowin kai sai yunwa kuma ammh yanzu da Sauki nayi Attemping Dinsa ya samu sauki na Barshi ma yana ta barci.."Daddyn Abuja ya Jinjina kai yana Fadin"Allah ya bashi lafiya..Ka Zauna ka kula Dashi..Sai Hakuri..' Abba yace"Dom me zai zauna ya kula da wanda bai san Darajan kansa ba Aliyu..?Kawai saboda Shashasha irin na Zain sai Haddir ya ijiye zuwa aikinsa saboda kula Dashi..ya kyaleshi In ma Mutuwa Zai yi ya mutu..Wanda Yaja Ruwa Shi Ruwa kan Duka.."Abba ya Fada Cikin Bacin Rai,Daddyn Abuja yace"Assh..Abu baiyi Dadi ba..Haba Ya Usman Hannunka fa baya Rubewa ka yankeshi ka yar..Har yau har gobe Zain Danmu ne domin wannan Kaddaran Ta Faru babu Abunda zai Sauya Yana nan a matsayin Namu ne.."Cikin Fusata Abba yaja wani Dogon Tsaki yana Fadin"In ka Ga Hannunn Naka ya Rube baka yankeshi ba Aliyu bai Dame ka bane..Ni kam wannan Rubabban Hannun nawa na yankeshi na Yardashi..Kuma na samu salama kai Hadiru ka wuce suwa sabgoginka ka kyaleshi koma miye ya Faru shi ya Jawo..! Daddyn Abuja zai kara mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Allah ya kiyaye Hanya Aliyu..Ammh awannan Karon Ko Alhaji Tsoho bai isa ya Hanani Nuna ma Zain yaci Amanar yardan Da nayi mai ba.."Daga Haka bai kara mgana ba ya Rabashi ya wuce cikin Gida Fuu Su Umma suka Bishi da kallo Kamar yadda Haddir da Daddyn Abuja suka Bishi da kallo Har ya Shige Cikin Gida. Numfashi Daddyn Abuja ya Saulke kafin ya Dafa Haddir yana Fadin"Take gud Care of Him Son..."Kai ya gyada mai yana Fadin"Insha Allahu Daddy.."Kai ya Jinjina yana Fadin"Allah yayi muku albarka..'Ya amsa da Ameen kafin yace"Yima Mamanka Mgana tazo mu tafi.."Daga Haka ya Shiga Gidan Baya Dama Direbansa ne ya kawosu Haddir ne ya karisa Gabansu Umma yace ma Mama Safiya tazo Daddy Na Jiranta Hamdiya ma Zareena ta yi ma sallama dasu Umma Ta wuce ta Shiga Gaban Mota Mama Safiya Tayi musu sallama tazo ta Shiga Mota Direba yaja Suka Fita Daga Haraban Gidan Bayan megadi ya wangale musu get suka Fice. Daga Umma Har Nene ba wacce Tayi ma Haddir mgana suka Juya Zuwa Cikin Gida,Zareena ma Bata tsaya ba, Ta juya ta koma Cikin Gida ajiyar zuciya Haddir ya Sauke kafin ya Fada Motarsa ya Fice Daga Cikin Gidan. Su Umma na Shiga Falon Suka Iske Abba na kai da kawo acikin Falon Hanayensa Goye abayansa yana ganin Shigowarsu ya Dago Cikin Bacin Rai yana Fadin"Fatima Da Aisha..! Gabadayansu suka Zubamai Ido Suna kallonsu Zainab ma Dake Daki Tare da Zaina sai da ta Fito Jin yau kai tsaye Abba ya Kira Sunan Umma da Nene wanda basu Taba jiba da wayansu ba sai yau Haka ma Zareena Gabanta sai Fadi yake Allah yaasa Jalal yabi su Saudart zuwa Islamiya. Cikin kakkausan Murya da zallar Bacin Rai yace"Ban amince ba kuma ban yar jema Daya Daga cikin ku Zain yazo Gidan nan Ta Daga ido ta kalleshi ba.."Yafada yana nuna su da yatsa Umma dai batayi Yunkurin yin mgana ba Nene ce Ta marairai ce Tana Fadin"Saboda me Abba..? Zain yana da wasu iyaye ne bayan mu..? Cikin Tsawa yace mata"Eh mana yana Dashi..In ba ya maidamu wasu Shashashu ba Taya Taya Zai aikata irin wannan Dabi"ar bamu sani ba Karuwa fa ya ijiye Dadirowa fa Aisha Ahakan kuma muke zaman iyayensa..!? Ina Ban Amunce ba Ko yazo Gidan nan kada wacce ta mai mgana ku Rabu Dashi...Tunda ya Riga ya gama Cutar da Zuciyoyin da suka yarda Dashi..Yaci Amanarmu Mu iyayensa kuma yaci amanar amatarsa,Ku kyaleshi ni da kaima zan mai iyaka Da Shigomin Gida Tunda ba Da kudinsa na ginashi ba..! Nene Taji Hawaye sun kawo mata Cikin Sagewar Numfashi Ta Bude baki zatayi mgana Abba ya Dakatar da ita da Fadin"Karki kara cewa komai...Umarni ne na baku ba Shawara ba..Har ke Zareena ban Yarje miki ki Saurareshi ba.."Daga Haka kawai ya wuce Fuu zuwa Dakinsa Umma ta Cije baki wani Abu na Suyanta acikin Ranta Ta mara mai Baya Nene ce ta Sulale nan Tana kuka Zareena ma Haka Zainab ma Tana Tsaye Tana Hawaye,Sadiq kuwa da Shigowarsa kenan Dakinsa kawai ya wuce yana jin Tsausayin Yayan nashi Har Cikin Ransa. Zaina kuwa Tana Tsaye Daga Bayan Zainab Daga Cikin Dakin Bata Fito ba Taji Duka Abunda Abba yace sai ta kara Rudewa da Shiga Tashin Hankali Taya Ya Abba zai yanke wannan hukuncin..? In yace haka ina Ya zain zashi..? Tasan Duk Harda Saboda Ita Abba ya Dauki wannan matakin Sai Taji kamar Jiri na Dibanta zata Fadi baya Tayi ta koma Kan gado Ta zauna Tana Sharan Kwallah Tana Jin Zuciyarta na Bada wani Sauti Mara Dadi Fat! Fat..! *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*                     2️⃣1️⃣ "Da Sauri Nene ta mike kamar Zata Tashi sama ta Wuce Dakin Umma Zareena da Zainab suka Bita da kallon mamaki,Kada kai kawai Zareena Tayi ta mike Tana Rangaji ta wuce Dakin Datake sauka in tazo Ganin Gida Zainab ma Baya Taja ta koma Cikin Dakin Tana Sharan kwallah Turus Tayi ganin Zaina Kwance kan gado tana Kuka mai cin Rai Da kuma Raunana Zuciyar mai Sauraro. Itama nan Kasan Cafet din Zainab Ta Sulale ta Maida Hannayenta ta Tallabi kanta Tana Cigaba da Tsiyayan Hawaye,Domin bata da wani karfin Gwiwan Hana Anty Zaina kuka Domin Abun kuka ne ya sameta Dole abarta ta koka ko Zataji Saukin Abunda ke Damunta acikinn Ranta ita Fa kenan Data ke kanwarsa Taji Zafi Abun ya Raunana mata Zuciya Ballatana ita Matarsa Da ta kasance abokiyar Sirrinasa gabadaya. Umma na Shiga Cikin Dakinta Ta maida kofa ta Rufe Lokaci Daya Tana sakin wani Siririn kukan Daya ke neman kwace mata Tuntuni Tana Boyewa,Shi ta saki yanzu Domin Abun yana Fito mata Daga kasan Zuciyarta ne kukan Bakinciki da kuma Tsausayin Zaina Gefe Daya kuma Tana jin wani Daci acikin Ranta In ta Tuna Abunda Zain ya aikata a matsayinta ta uwa Dole ne Tafi kowa Shiga Tashin Hankali game da wannan lamarin Duk da Tana Boyewa bata son Kowa ya Fahimci Ta Damu da Abunda ya Danganci Zainullahi din. Nene Ta Dade tsaye kanta Tana kallonta Bata sani ba,Har Shigowarta Bata sani ba ballatana wamzuwarta acikin Dakinta Tana ganin Tana kuka Tasaki Mirmishin Takaichi kawai Domin ko Umma Taso Boye Damuwarta ita awajenta bazai Taba Boyuwa ba ba Tun yau ba tasan Cewa Duk Cikin Ya"yan da Umma ta Haifi Tafi Son Zainullahi kara ce kawai da kawaicin Dan Fari Da kuma Tasowar Da yayi ba ahannunta Ba yasa bata Shiga lamarinasa ammh Tabbas Soyayya Uwa da Da'nta Ko Uwa taso ta Boyeshi baya Boyuwa Allah zai bayannashi Wannan kukan Datakeyi bana komai Bane nashi ne Da kuma Bakincikin Matakin da Abba ya Dauka game da lamarin. Ganin Batama san da Tsayuwarta ba yasa tayi gyaran Murya Wanda  ya karkato da Hankalin Umma Zuwa Fahimtar ba ita kadai bace acikin Dakin Kafin ta waigo sai da Tayi Saurin Share Hawayenta saboda Bataso wani ya ganta Tana kuka kana ta Juyo Cikin Sanyi Jiki ta Sauke kallonta kan Nene wacce ta kura mata ido Tana kallonta Cikin Tsausayi da wani irin Girmanta Da Nene take gani acikin Idanuwanta. Yake Umma Tayi Tana Fadin"Ya akayi ne Hajiya Nene..? Tafada Cikin Zolaya Dama wani Lokacin Haka Take Kiranta Nene bata saki Fuskarta ba tace"Meyasa kika yin mgana kan Hukuncin da Alhaji ya yanke kan Zain..? Wani kallo Umma Tayi mata Tana Kokarin Boye Abunda ke Ranta Tana Fadin"Meyasa ni kuma zanyi mgana Nene..?Yana da Damar da zai iya yanke ko wani Hukunci Tunda Dagamu har shi muna Karkashin Ikonsa ne..Kuma Banga Illah kan Abunda ya yanke din ba Nene..Yana da gaskiya bai kamata ka kara Sauraran Wanda ka bama yarda ba ya Cutar dakai ba..." Ta Fada Tana kokarin maida kwallar cikin Idanuwanta Nene tayi Dariyan Takaichi kafin tace"Naji Hukuncin yayi miki Dadi Ammh Umman Zareena Meyasa kike kuka..? Umma Tayi Saurin Cewa"Ina kukan Tsausayin Halin Da Yata Halima Take ciki ne Nene...Ina Matukar Tsausayamata Tana da kananan Shekaru ayanzu haka Tayi kankanta da Daukan wannan Abun ko ni Da nake Babbar Mace in zan auna kaina a mizaninta yanzu haka Na Tabbata Raunina zai bayyana Soasai Ko ke baki Tsausayinta..? Nene Tace"Ina Matukar Tsausayamata mana..Ammh Shima Yarona Abun a Tsausayamai ne Umma ya kamata muyi wani Abu karki manta Zainullahi Danki ne da kika Haifa da Cikinki Taya zaki Shuru Rayuwarsa ta kara Lalacewa Da Hukuncin da Alhaji ya yanke ina zashi..? Wa yake Dashi bayan mu..? Da Sauri Umma Ta Juya Ma Nene Baya Tana Kokarin Shanye kukanta Lokaci Daya Tana Fadin'A'a Ni ba D'ana bane...Zainullahi Har Abada Dan'ki ne Aisha,Mganar kuma Shima Abun Tsausayi ne ban yarda ba..Karya yake Shi ba Abun Tsausayi bane..Mu  iyayensa da Danginsa da matarsa Daya Cutar da zuciyarmu Mune Abun Tsausayi  ba wanda bai ji Tsoron Allansa ba ya Dinga aikata Laifin da Allah ya Hana Sai Daga baya da komai ya Kwace mai sai ya Fara kuka Saboda a tsausayamai..? A'a Nene Kada ki Shiga Hurumin Alhaji a wannan Lokacin Shi kanshi yana Bukatar mai Lallashinsa Domin Abun akwai Ciwo wanda ka bashi Dukkan wani yarda ka karar da Lokacinka wajen bashi Tarbiya da kafashi Rana Tsaka Ya zo maka da Sakamakon Bacin Suna Haba Nene Zain fa Mata yadinga bi Hakan bai ishesa ba ya Dawo kasar sa ta Haihuwa ya Ijiye karuwa ko nace Dadironsa suna Shanshancinsu Har sai da yayi mata Ciki kana mu Danginsa aka zo aka Bamu shi a matsayin Sakamakon Abunda Da'nmu ya aikata Taya kike Tunanin inda Karfin Gwiwan kallon Alhaji nace Abunda ya yanke bai yi Daidai ba..? Ko saboda Halima Bana Son zain ya  kara Tunkaran Gidannan ina so Ta manta Dashi da komai nashi ammh In Tana ganinsa Tabon Da yayi mata bazai Taba gogewa acikin Zuciyarta ba..! Ta karishe Fada Tana Danne Abunda ke Taso mata Daga kasan Ranta Bata Jira Cewar Nene ba Ta Tura Kofar Tailet ta Shige Domim kaucema Nene Da ganin Halin Data ke Ciki Ita kuwa Nene Duk da Tasan maganganun Umma gaskiya ne ammh Kaunar da Take tsakaninta da Zain ta uwa da Danta ne ko Kowa bai goya masa Baya Ita zata Tsayamai ta Tallafeshi kada wannan Abun ya kara Jefa Rayuwarshi Cikin wani Hali ajiyar rai ta ijiye kafin ta Juya Ta Fita Daga Dakin,Ita kuwa Umma najin Fitan Nene Ta Sulale nan Kofar Tiolet ta Fashe da wani marayan kuka Kamar wata karamar yarinya Kirjinta Ta Dafe wanda ke Bugawa Tana Fadin'"Astagafurullah..Allah mun Tuba..Nidai bam kasance mazinaciya ba Haka mahaifinka na Tabbata bai yi wannan Shanshancin ba meyasa kai ka aikata..? Ka cutaar damu zain ka Cutar da zuciyar Uwa Wacce ta Sadaukar da komai saboda Kai kuma ka Cutar da zuciyar da Uwar data fi kowa sonka" Haka Take ta Fada Tana kuka Wurjajam kukan Daya Dade aranta Bata samu Fitar Dashi ba,Ta Dade tana wannan kukan kafin ta Share Hawayenta,wanka Tayi kana ta Dauro alwala Jin ana Kiran sallar Mangariba Bayan ta Fito ta Sauya kaya Tayi Sallah,Sai ta Fita Zuwa Dakin Zaina ta Sameta Tana sallah Tana kuka Zainab Bata Dakin Fita kawai Tayi Daga Dakin Ta Leka Dakin Zareena nan Taga su Junior da Saudart da Jalal suka taso suna mata oyoyo kansu Ta Shafa Tana Dan sakin Mirmishi Saboda su yasa ta Shiga Cikin Dakin Tana kallon Zareena wacce ke Sanya ma Umma karama kaya Inaga wanka Tayi mata Zareenan ne ta Dago Tana gaida Umma ta amsa Cikin sanyin Murya kafin tace"Yaushe zaku koma ne..? Itama Zareenan Cikin sanyinta Tace"Umma wata Daya zamu yi...Ammh Sati mai zuwa zan Je katsina Bikin Diyar kanwar Baban Jalal..Shima din ma yanzu muka gama waya Ranar Jumma"a zai zo ya Daukemu sai an gama Biki sai mu dawo kafin mu Wuce..''Kai Umma ta kada Tana Fadin"Ah akwai ma Sauran Lokaci Allah ya kaimu da rai da lafiya..,"Tafada Lokaci Daya Tana Dukawa tana ma Umma karama waasa da kallon Tsausayi Zareena tabi Umma Dashi Domin Taga alaman Tayi kuka ga Idanuwanta nan sun kumbura Kafin ta samu Zarafin mgana Umma Ta Dago Tana Fadin"Ki daina Saka mata kayan Sanyin nan Haka zareena garin akwai zafi zafi kuma ki Rage wannan A.C kar ya Cutar da ita.."Mirmishi Zareena Tayi kafin Tace"Umma ai ta saba..Tun muna U.S Da A.C muke kwana Da Farko ma na Fara Fada Abbanta yace gwara na barta ta saba Tunda dashi zata Rayu..Da Farko ni ban saba ba Har nazo na saba Hakama Jalal Babansa Daman ya saba ya  kwana Cikin sanyi ya Tashi Cikin Sanyi..'Umma tace"Ni Daman Baku nake ji ba..Takwarata nake ji kar Sanyi ya kamata atoh.." Zareena Tace"Itama ta saba Umma."Umma tace"Ta sabi me..? Kudai yaran zamani masu Jegon yan gayu kawai.."Sai ga Zareena na Dariya itama Umman Dariyan Tayi Nene ce ta Dago Labulen Dakin Ta Shigo Tana Fadin"Dariyan me nake ta Jiyowa..?Umma ta kai Dubanta ga Nene Tana Fadin"Ni da Diyata ce..Kuma sai kowa yaji..? Nene ta Tabe baki Tana Fadin"Naje Dakin ki ne Daman baki Ciki...Alhaji ne baya Jin Dadi Sai da yasha panadol.."Atare Umma da Zareena suka ce"Subhanallah..Allah ya sauwake..!Bari naje na Dubashi..' Umma ta Nufi Hanyar Fita Zareena ta Dauki Umma karama ta mika ma Saudart Tana Fadin"Umma bari na biki na Duba Abba.."Umma batace komai ba Suka Rankaya suka Fita Harda Nene bayan ta tsaya ta gyara ma Saudart Rikon Umma karama sun Fito Falon kenan Sai ga Sadiq ya Fito Daga Dakinsa Kallonsa Nene Tayi ganin baida Walwala tace"Kaci Abinci..? Kai kawai ya Girgiza mata yana Zama daya Daga Cikin kujerun Falon,Umma ta kalleshi ganin bai da wani walwala tace"Akwai abincin agidan ne..? Nene tace"Eh Nace Zainab Ta shiga Kitchen ta Girka ko Macaroni Da kifi ne.."Kai kawai Umma Ta kada ta wuce zuwa Dakin Abba Nene ta mara mata Baya Zareena ce ta Tsaya Tana gayama Sadiq Abba baya jin Dadin Jin haka yasa ya mike Shima ya mara musu baya Shi da Zareena. Ko da suka Shiga Sun iske Umma da Nene duk sun sakashi a Tsakiya,Suna Faman mai sannu Da kai kawai yake amsawa Domin Shi kadai yasan Halin da Zuciyarsa ke Ciki Shigowar Zareena da Sadiq ne yasa ya Bude Idanuwansa yana Kallonsu Gabansa suka Karisa Dukkansu suka Rankwafa suka gaisheshi suna mai Sannu Mirmishi Abba yayi yana Riko Hannun Sadiq lokaci Daya yana Fadin"Babana yaushe zaka koma ne..?ko dogon Hutu ka samu ne..? Cikin Ladabi Sadiq yace"Gobe zan koma Abba..Dama na samu Break ne na leko ku sauran wattani kadan ne na kammallah sai Defence.."Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Allah ya Taimaka..Allah ya tsaremin ku aduk inda kuke.."Ya fada Cikim karaya Dukkansu suka amsa da Ameen Harda Iyayen Kallonsa ya maida kan Zareena yana Fadin"Diyar fatima ina Amaryata na ganki ke Kadai..? Zareena Tace"Tana Daki waje su Saudart Abba..Zan kawo maka ita sai ka ji sauki.."Kai ya kada yana Fadin"ki yi sauri ki koma kada Su Kada ita...Ina abokina Jalal ban ji Duriyansa ba..? Zareena Tace"Duk suna chan Tare dasu Junior.."Abba yace"Ok..Ina megidanki..? Kunsamu DogonHutu kenan..? Kafin Zarreena Tayi mgana Umma tayi saurin cewa"Eh wajen Wata daya zasu yi..Sati dai mai zuwa tace Jawaad din zai zo ya Dauketa Su Tafi katsina Bikin Diyar yayar shi Mijin nata..'Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Yayi kyau..Dukkanku Allah ya yi muku albarka Ina Zainab ina Halimatu har yanzu bata bar kukan ba ko..? Cikin Tsausayawa Zareena Tace"Ameen Abba...Bata bari ba Abun dai yayi sauki ammh bata mgana Sai dai in ita da Umma ne.."Abba ya koma ya kwanta Yana Fadin"Fatima ki kula da ita..In Zazzabin nata yaki sauka kuje asibiti adubata..! Umma tace"Taji sauki..Sai dai yawan kukan ne..Yanzu hakama Tana Sallah na sameta Tana kuka Zainab kuma Tana Kitchen.."Lumshe ido Abba yayi yana Fadin"Ina Tsoron wani Abu..Ina Tsoron Yarinyar nan takamu da wani Ciwo sanadin Yaron nan Basan da wani ido zan kalli ahalinta ba..! Nene ta kada kai Tana Fadin"Sai Hakuri..Insha Allahu babu Abunda zai Faru....Zata warware Insha Allahu.."Mirmishin Takaichi Abba ya saki kafin yace"Allah yasa..Ku barni zan kwanta ko Ciwon kan zai sauka..! Dukkansu suka mike suna mai Sannu Ya"yan ne kan gaba sai iyayen Sai da suka Fita kana Abba ya Juya yana Share kwallar Data Silalo mai ta Bayan Kunnuwansa,Dama Dalilin Daya sa yace su bashi waje kenan kar suga Rauninsa ammh Tabbas wannan Al"amarin ya Girgiza shi Shi Usman Ne za"a samu Daga Cikin ya"yansa wanda ya ijiye karuwa Har da Sakamakon Cikin Shege..? Wannan Abun in ya Tuna sai yaji kunyar Duniya ta kamashi Ko Yan"uwansa ma Baya son Hada Ido da su saboda wannan Abun kunyar da ZAIN ya aikata. Ya samu Barci sai Wajen 10pm na Dare ya Tashi yayi wanka Ciwin kan ya sauka sai dai Nauyin Kirjin Bayan yayi wanka yayi sallar Isha"i Umma ta kawomai abinci yaci Ita kuma Nene ta gyaramai Shinfidar,Mganin ya kara Sha ya koma ya kwanta Umma Ta Tafi Dakin zaina ta bar Nene zata kwana da Abba. Dakyar da Lallashi Umma ta Lallashi Zaina taci macaronin nan Shima ba wani mai yawa ba ba Dadewa ta amayar Dashi Umma ta Fara Shiga Damuwa ganin kwana Daya Rak zaina Duk ta Fada kamar ba ita ba Idanuwana sun kumbura sun yi Luhu Luhu Sun kuma Fada Gabadaya Jikinta ba karfi saboda Rashin Cin Abinci,Ko Taci sai ta amayar dashi kuma taki yarda azo adubata ko kuma suje asibiti kada wata Cutar ta kamata. Kamata Tayi suka Shiga Tiolet ta wanke mata baki kana ta Dawo da ita kan gado ta kwantar da ita Ta koma ta gyara Wajen Da tayi aman kana ta koma Kitchen ta Tsiyayo Ruwa a Fulas na zafi Ta Hada mata Tea Shima Din Sai da Tayi mata jan Ido kana Tasha kadan Kafin ta kauda kai Cikin Bacin Rai Umma ke kallonta Tana Fadin"Meyasa kike son kashe kanki Saboda wanda bai damu Dake ba..? Ke sakaryan ina ne..? Kalli yadda kika Rame Cikin kwana Daya..? Kina so ki kashe kanki ne..? Girgiza ma Umma kawai takeyi takasa mgana sai Hawaye Dakyar Tace"Umma Bazan iya cin komai bane..Ko naci sai nayi amai,Umma kirjina da Zuciyata Ko"ina Ciwo suke ni nafi son ma na Mutu Umma da in zauna wannan Dacin Da nake ji acikin Zuciyata yayii ajalina"Gam! Umma ta make mata Baki Cikin Fushi Take fadin"Shi bai mutu saboda Abunda ya aikata ba ke zaki Mutu..? Kul kar nakara jin wannan mganar Ki Fitar da Abunda ke Ranki ki Maida komai ba komai hakan bashi ne Karshen Rayuwarki ba Indai ina Numfashi sai Zain ya sake ki ki samu wani mai Nagartan ki aura Kicigaba da Rayuwarki Shi kuma yaje chan ya karata da Dadiron tasa da kuma Dan Shegen Da zata Haifa masa Tunda Haka ya zaba..! Cikin Rauni da kuma wani Tsausayi Zaina tace"Umma kema baki yafe ma Firstlove ba..? Hararanta Umma Tayi tana mika Kofin Shayin Take fadin"Bana son na kara jin wata mgana Daya Dangance sa..Karbi ki Shanyeshi Duka ki bani Kofin kafin na Saba miki.."Umma ta Fada Fuskarta ba alamun wasa Dole Zaina ta karba ta kafa kai Duk da Bakinta kamar Madaci Haka Takeji ammh Saboda Ran Umma ya baci yasa ta shanye ta mika ma Umma Kofin Ta karba Tana Fadin"Ko ke fa..? Karki kwanta Tashi kisha Mgani naji kamar zazzabin ya Dawo..? Da Toh kawai ta amsa Umma ta ballo mata panadol Ta mikamata Hade da Ruwa tasha Ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi,Umma ta gyara mata kwanciya kana ta Fice zuwa Kitchen ta maida komai,Zareena ta kwanta Zainab ma Haka suna gama cin Abinci kowa ya nemi makwanci,Shiyasa ta koma Dakin Zaina din Ta Shimfida Bargo nan kasa Ta kwanta Bayan ta Rage Hasken Dakin Duk Zaina na kallonta Wacce ke ta Sharan kwallah bata so Kukanta ya Fito Umma Taji ta. Washegari kuma Kafin Inna Hannatu ta wuce tazo ta Duba Abba Tunda Nene ta Kira Alhaji Tsoho Ta gayamai Abba bayajin Dadi yau ma bai fita aiki ba,Sai da Sadiq yaje yazo da Dr Imran Ya Dubashi Jininsa ne ya Hau yamai alluran barci Da kuma mganguna,Tunda Sadiq din yana ta Kiran Haddir bai Daga ba Sai daga baya ya Kirashi yace mai yana Gidan zain ne achan ya kwana Cikin Tsausayawa Sadiq yace"Ya Haddir ya Jikin Ya zain din..? Haddir ya Sauke Numfashi yana kallon Zain dake kwance yana Barci yace"Da sauki zamu ce Sadiq gashi kwance yana Barci.."  yanzu ya gama amayar da Tea din Da Haddir ya Hadamai yasha..Alluran barci ya sake mai ya kara Doramai Drip,Zazzabin da Ciwon kan ya sauka Jiya ammh Zuwa safiya kuma Sai ya Dawo,ba Domin Haddir gidan ya kwana ba baisan wani Hali zain zai Shiga ba yama ki yarda suje asibiti ne da Chan zai kaisa abashi gado adinga Kula Dashi Tunani yake Allah yasa wannan Damuwar da zain ya saka ma Ranshi bazai haifarmai da Hawan Jini ba Cikin Tsauyawa Sadiq yace"Allah ya bashi lafiya..In zan wuce zan Biyo na Dubasa Daman kiran da nayi maka Don kazo ka Duba Abba Shima ya kwana Jikin ba Dadi ganin ban sameka ba sai Alhaji Tsoho yace naje asibiti na Dauko Dr Imran har ma yazo ya Dubashi yamai alluran Barci ya samu barci.."Cikin Damuwa Haddir yace"Innalillah meke damunsa..? Cikim Damuwa Sadiq dake Haraban gidansu bayan ya rako Su Inna Hannatu ne Direban Abba ya Dauketa zuwa Filin Jirgi Dagachan zai wuce da Zainab makaranta Tare da ita suka Tafi yace"Yace Jininsa ne ya Hau sosai ya Haddir..! Cikin Salati Haddir yace"Subnallah yanzu ya Jikin nashi..? Sadiq ya numfasa yana Fadin"Da sauki har ya samu barci ma.."Haddir yace"Allah kara lafiya zan shigo zuwa anjuma na Dubashi in Jikin nashi yayi sauki Ina Halima..? Sadiq yace"Itama fa Tana kwance ba Lafiya ya Haddir.."Haddir kansa kawai ya Shafa yana Fadin"shikenan Allah ya bata lafiya.."Daga haka suka yanke Kiran Dafe kai kawai Haddir yayi yana kallon Zain Wani Irin Abu yake ji a kaasan Ransa zai iya Rantsuwa cewa Zain ne sanadin Hawan Jinin Abba Kaicho Dama irin wannan Abun yake ta Jiyema Zain Tun Suna makaranta ammh yayi kunun Uwar Shegu Da mganarsa sai yanzu da komai ya baci ne zai koma yana Nadama Gashi ya saka kowa Cikin Damuwa Iyayensa na Fushi Dashi haka Zakalika ma Matarsa Kuma Tana cikin wani Hali Saboda shi Yana Fatan Allah ya yayyafa ma Abun Ruwan Sanyi. Yana Tare da Zain ko"ina Baya zuwa ko Salla agidan yake yinta Daya Farka Shi zai Taimakamai yayi alwala yayi sallah yaci Abinci wanda Haddir din ke Fita ya Siyomai,Har zuwa Wajen bayan La"asar dai jikin na Zain yayi sauki Zuwan Sadiq ne wanda zai koma zaria Jikin ya kara Rikicewa Domin ya Fadamai Zaina na chan kwance kwana Take kuka Bata ci bata Sha Umma kadai take ma mgana,In ba ita ba sai dai ka gaji Dayi mata mgana bazata Tanka ka ba sai kuka Shima da zai Tafi ya Shiga inda Take ya Duka Har kan gadon Da take kwance Yana Mata mgana Tare da kalaman Lallashi gareta ammh Zaina sai kuka kawai take,Yayi kokarin yaga Tayi mgana ammh Taki cemai komai Umma tace ya Tashi ya Tafi kawai bazata mai mgana ba ya Fita da Tsausayin Zaina acikin Ranshi Zain yaji Hankalinsa ya Tashi Kwarai ya Fara Kokarin Tashi Dama Haddir ya Ciremai karin Ruwan Da cewa zai je GRA ya Duba Firstlove dinsa. Haddir na Kokarin Hanasa Da cewa"Ina zaka kana Cikin wannan Halin..? Shima Abba ba lafiya gareshi ba yau sai da Dr Imran yaje ya Dubashi Jininsa ne ya Hau.."Cak Zain ya Dakata Daga Sanya kayan dayake kokarin yi ya waiwayo yana kallon Haddir Lokaci Daya yana Fadin"Jininsa ne ya hau..? Ya Fada da Sigar Tambaya Cikin Muryan Ciwo da mamaki Kai Haddir ya kada yana Fadin"Kwarai da gaske...Na sani kuma kaima ka sani Kana da Nasaba da Hawan Jinin Abba In haka ne kuwa zuwan Ka gida yanzu ba alheri bane..Wlh Zain ko Alhaji Tsoho Dake matukar kaunar ka bai zo so ganinka yanzu ba Gwara ka Jira zuwa nan da Kwanaki kadan in Abun ya sake su sai ka Tunkaresu ammh yanzu akwai matsala Domin Sai Ciwon Abba ya kara Tashi in ya ganka..! Ya Fada yana kauda kai Saboda Bayason kallon Zain din balle har ya Fahinmci wani Hali yake Ciki Kuma baya so ya Furta masa Abunda ya Faru tsakanin Dadyn Abuja da Abba Jiya Shi kuwa Zain gabadaya Jikinsa sai ya kama Rawa wani Jiri na neman Gadashi ya Rike Jikin Wardrope yana Fadin"Firstlove fa Haddir..? Bazani naga Halin Data ke Ciki ba..? Nafi kowa sanin Halin Zaina bazata ci Komai ba Kuka zatayi Tayi har wani Cuta ta kamata Tana da Rauni indai akaina ne sosai...Ya kamata naje na lallasheta.." Ya Fada kamar yayi kuka Haddir ya kalleshi Cikin Jin Haushi yana Fadin"U are not Serious..Kana Tsammanin akwai Wata mgana da zaka gayamata ne ayanzu ta Saurareka..? Ka riga ka gama Zubar da Duka Kimarka da Soyayya da yardan dake tsakaninku..Da kake Fadin Kasanta Tana da Rauni akan ka Meyasa kasan da Haka Tun Farko baka Daina Abunda watarana In Taji Raunin nata zai bayyana ba..? Yafada Cikin Bakinciki Da Takaichin Zain din Wanda kawai ya Sunkuyar dakai bai kara mgana ba Rigar hannunsa ya Zura na wani Farin yadi ko hula bai saka ba Duk yayi wani Busu Busu dashi ya Nufi Haddir yana Fadin"Aramin key din Motarka..? Haddir ya nuna mai Gaban Dressing Mirror din Dakin yana Fadin"Ga Key din Taka Motar chan yau da Safe dana Shiga Cikin asibiti na Taho maka da ita.."Da sauri ya nufi wajen ya Dauka Yana Sauri kamar baya Cikin Natsuwarsa yana Shirin Barin Bedroom din yaji Muryan Sadiq yana Fadin"Kar kaje gida ayanzu Yaya Zain..! Ya Fada yana mikewa Haddir na Gefe yana kallonsa Zain ya Juyo Cikin Cije baki Da alamun Rashin lafiya yace"Kai Sadiq meka sani..? Baka san komai game da Dacin Da nake ji acikin Raina ba Dole zan je na Roki Abba dasu Umma gafara na kuma Dauko matata mu Dawo Gida na Tabbata ita mai yafiya ne gareni.." Daga Haka ya Juya zai Fita Sai kawai yaji Sadiq yace"Ko kaje Ba wanda zai maka mgana Ballatana ya Saurareka..In ma Abba ya bari ka Shiga Gidan kenan..! Yafada Cikin Wani yanayi Atare Zuciyar Zain Data Haddir ta amsa da Dam! Haddir ya Waro Ido yana kallon Sadiq shi kuma Zain da wani Sauri ya waigo yana kallon Sadiq Cikin Rashin Hayyaci kafin yace"Ban...Ga...ne ba..! Ya Fada muryansa na Rawa... Kada kai Sadiq yayi yana Fadin"Eh...Jiya nan Abba ya gama Tara su Umma da Nene yace bai yarje musu In kazo Gidan suyi maka mgana ba ballatana Har su Saurarekaba Daga karshe yace harta Anty Zareena na bai yarje mata ba kuma Umarni ne ba Shawara ba Daga Karshe yace Shi da kanshi zai gayamaka kada ka karo Tako mai Gida Tunda ba Da kudinka ya Siya Gidan ba..! *Shakira..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*               2️⃣2️⃣ "Ba Zain kadai ya kad'u da jin Mganar Sadiq ba Hatta Haddir Shima sai da ya nuna Kad'uwarsa a Zahiri,Zain kuwa K'asa kasa Daukansa Tayi Domin Wani irin Jiri ne ya kwasheshi ya Tafi luu zai Fadi Atare Dukkansu Sadiq da ya watsar da Jakar Hannunsa ya Nufeshi Sai dai Haddir ya Rigashi isa Gareshi Tunda Shi yafi kusa Dashi Cikin Ikon Allah ya Tallafeshi ya Fado Jikinsa Cikin Fitan Hayyaci yake Fadin"Abba...Ne Abba ne yace kada na kara Shigomai gida .? Yafada wasu zafafan Hawaye suna Biyo Duka kuncinsa Atare Sadiq da Haddir suka Rikosa Zuwa Bakin gado ganin yadda Duka Jikinsa ke Rawa suna Zaunar Dashi Haddir ya kalli Sadiq yana Fadin"Jeka Kitchen ka Dauko Goron Ruwa mai sanyi a cikin Fridge..ka Hado da karamin kofi plz.." Jin Haka yasa ya Fita Da Sauri ba"a dau wani Lokaci ba ya Dawo da Ruwa a Hannunsa Da karamin Kofi ya mikama Haddir Shi kuma ya karba ya Tsiyaya Ruwan Fin Rabi acikin Kofin ya Mikama Zain yana Fadin"Karbi kasha..Zuciyarka Zatayi sanyi ta kuma Daina Bugawa Da Sauri Da Sauri.."Idanuwansa da Suka Sauya kala ya Watsama Haddir Dake mikamai Kofin Ruwan Cikin Bugun Zuciya da wata murya Cikin yanke Tsammani yake Fadin"Taya kake Tunanin zan iya Shan Ruwa ya Tsirgamin Haddir..?Kanaji fa Abba Da kanshi yace kada kowa ya Saurareni kuma Shima zai Fadamin kada na kara Takamai zuwa Gida..? Kaichona Haddir Wlh ban Taba jin na Tsani kaina ba Irin Jiya yau kuma kalaman Abba Gareni sun kara karyamin Duk wani Sauran kwarin Gwiwata yanzu ina zan saka kaina Duka iyayena da yan"uwana Suna Fushi Dani kuma suna kallona a mutumin da bai da wata kima..? taya zan kara samun Damar da Duka Ahalina zasu yarda dani..?Ga Firstlove itama Zata barni saboda wannan Bakin Fentin da na Saka ma kaina Allah na Tuba Allah ka yafemin Astagafurullah...! Yake Fada Cikin Kuka Lokaci Daya yana saka Fuskarsa Cikin Tafukan Hannayensa yana wani kuka mai cin rai Harda Sheshsheka kamar zai Shida,Sadiq baya ya koma Shima yana Sharan kwallah Domin Zuciyarsa bazata iya Juran ganin Jajirtatacen Yayansa na irin wannan kukan,ba Haddir kuwa kansa kawai ya Dukar yana Sauraran Duka maganganun Zain din Shima Ya gaji da kukan zuccin Da yake yine,Dagowa yayi yana kallon ZAIN Din kafin ya sake mikamai Kofin Ruwan yana Fadin'"Duk naji...Karbi dai kasha Ruwan ko bakomai zai Saka ka Natsuwa..! Bai yi gaddama ba ya karba ya kafa kai Domin gabadaya makoshinsa ya Bushe ne kamar bai Taba Shan Ruwa ba sai da ya Shanye Duka Haddir ya karamai kana yaji Bushewar makogwaransa ya Ragu Da Kofin da Ruwan Haddir ya mika ma Sadiq yana Fadin"Fita dashi Sadiq.." Ba Gaddama Sadiq ya maida Komai Kitchen din kana ya Dawo ya Iske Haddir ya zauna Kusa Da zain yana Fadin"Zain Dago kanka ka Saurareni..'Dole Zain ya Dago kansa daya maida kasa yana Sharan kwallah Cikin Sanyin Murya Haddir ya Dafashi yana Fadin"Abunda Muke Gudun fa ya Riga ya Faru..Fake gaba kawai zamu yi sai Abu na gaba yadda zaka Shawo kam iyayenmu su yafe maka da kuma yadda zaka Gyara Mu'amalanka da Matarka Domin fa mai afkuwa ta Riga ta afku bamu da yarda da zamu yi wannan koke koken naka bazai kaika ko"ina ba Wlh Gwara Tun Wuri ka Ijiye wannan gefe Tunda komai ya Faru kai ne Sila Tun Muna London nasha Fada Maka kabar wannan Muguwar Dabi"an Bata Dace da Dan Musulam kwarai ba Zain kaki jina Na Dauka Da muka Dawo Gida zaka Daina Abunda kakeyi Ko Domin Tsoron Allah da kuma Darajan Mutumtakan iyauyenmu ammh baka Daina ba ka Biyema Yarinyar nan Dina Wacce Tun ganin Farko Dana yi mata na gayamaka ka Rabu da ita Shedaniya ce kaki jin mganata,Wlh na Tabbata ba sai nayi kaffara ba Da gangan ta bari Ciki ya Shigeta Saboda ta Fallasaa ka Aureta Tun Farko sai da na gayamaka in Sonta kake ka Aureta mana ka Hadasu ita da Zaina da kabi Shawarata Hakan zata Faru..? Kamar karamin yaro Haka Zain ya Girgiza ma Haddir kai alaman A"a,Haddir yaci gaba da Fadin"Toh ka gani ka kijin mganata Lokacin ma Saboda ina Gaya maka gaskiya gaba ka Farayi Dani Da auranta kayi Da Duk Abunda ya Farunan bazai Faru ba Gashi yanzu Dalilin Son Zuciyarka da kuma Shedan din Daya Dinga kawata Maka aikata zina yasa ka Cikin wani Halin Ka samu mumaa Damu da Duka Yan"uwanka da makusantanka Don Allah ina Dadinsa..? Ni babban Damuwa ta ma Fushin iyaye akan ya"yansu Bala"i ne Uwa uba ayanzu bamai Shiga mganar nan Tunda kowa ma yana Cikin Bakincikin Abunda ka aikata ga Zaina Ka saka yarinya karama Dandanan Dacin Bakincikin Cin Amanar Da Namiji ni kaina ina Jin kunyar mu Hada ido da ita bansan me zan ce mata ga Ga Babban ma Tashin Hankalin Cikin Da ke Jikin Dina kuma Alhaji Tsoho yace sai ta Haifeshi yanzu haka Acikin Zuru"armu zamu samu Dan gaba da Fatiha..?Kai son Zuciya bai yi ba sam Wlh.." Ya karishe Fada yana Dafe kansa Sadiq Dake gefe kai yake Jinjinawa alamun gamsuwa da kalaman Haddir din Shi kuwa Zain Kansa kawai ya Tusa Cikin Gwiwoyinsa Yana Kuka kamar wani karamin yaro Mikewa Haddir yayi yana Fadin"Nasan Damuwa ta zama Dole Gareka ammh u Hv To become Very Strong Tunda daman kasan Duk Abunda kake aikatawa watarana asirinka sai ya Tonu kuma Wannann Lokaci zai zo,ina Jiyemaka Hawan jini Ko Ciwon Zuciya yazo ya kamaka Domin Duk wanda zai ji wannan mganar kukan ka bazai Taba bashi Tssusayi ba Illah ma ya karama da kalmar Allah kara kai ka jawo ma kanka komai miye yake Faruwa Dakai." Ya karishe Fada yana Sakin Numfashi kafin yace"Zan je Gidan Na Duba Abba da Jiki Daganan zan Biya Gidan Alhaji Tsoho na gayamai nagani ko zai iya Saka baki Abba ya sauko ammh Shima din ba yanzu ba saboda Kaga Halin Daya ke Ciki Yanzu ba"a son yasa ka wani Damuwa aransa kaima ka sani.."Da Sauri Zain ya Dago yana Fadin"'Don Allah Haddir ka Tayani Lallashin Firstlove kace mata Tazo ta ganni muyi bankwana na Roki gafaranta kada na Mutu ka Shaidamata Wallahi Summa Tallahi Duk Duniya Ita ce macen da nake so Kuma Itace in ta barni Rayuwata zata Lalace ka Fadamata Ta Dawo Gareni Don Allah ka Tahomin da Firstlove na Rumgumeta akirjina Nayi kukan da Haryanzu ya kasa Fitowa Daga Cikin Kirjina.." Yafada yana Runtse Ido Saboda yadda yakejin Zuciyarsa na Bugawa Daga Sadiq har Haddir sai da suka kusa mai kwallah Cikin Muryan Lallashi Haddir ya Dafashi yana Fadin"Karka Damu I Will Try my Best Insha Allahu naga komai ya Daidaita..Yanzu ka kwanta ka Huta ka Cire komai aranka da Izinin Lahi Tunda kayi Tuban gaskiya Komai zai zo ya wuce kamar ba"ayi ba zan je nyi mgana Dasu Umma itama Zaina zan yi mgana da ita komai zai Daidaita kaji ko..? Kamar Haddir yamai Gafara Haka yakeji Cikin Gyada kai yace"I Trust u...Kuma Wlh da Gaske na Tuba...Nama Dade da Tubam ma Allah Dina ita ce Ke maidani Ruwa Shiyasa na Tsani Jin Sunanta ma na Tsaneta na Tsani mai kaunarta Tayi sanadiyar Jefani Cikin Bala"i Tsakanina da ita sai Allah ya isa kawai zence Shegiya macuciya..'Haka kawai Zain yake Sambatu yana Zagin Dina Haddir ya gyada kai yana Fadin"Koma miye ya Faru da Taimakon wannan Shedaniyar kawar nata...Shiyasa akomai kada kayi mu'amala da Mutumin Banza Domin Aiyukansa Watarana zasu iya Shafanka..Bari Naje ka kula Da kanka kafin na Dawo in Tabawa Tayi Tuwo nazo maka Dashi..? Da Sauri ya gyada kai yana Fadin"Allah yasa ta bada in Taji ance ni za"a kawo mawa.."ya fada kamar yayi kuka Mirmishi Haddir yayi yana Fadin"Zata baka mana...Har yau har Gobe kanan nan amatsayinka na Zain Usman Abubakar Saulawa Babu Abunda ya Sauya wannan kuma Abunda ya Faru Jarabta ce kuma Allah ya bamu ikon Cinyeta Watarana zata zama sai Labari Insha Allahu.."Cikim Karfin Hali Zain yace"Allah yasa.." Fara Tafiya Haddir yayi yana Fadin"Da yardan Allah...Kai Sadiq in ka Tashi muje na ijiye ka Tasha naga ma kamar kayi yammah.."Sadiq ya Fara Tafiya Wajen Jakarsa ya Dauka ya Rataya yana Fadin"Yauwa Ya Haddir nako gode....Banyi ba ko agida Abba yagaji Da Fada ya kyaleni nafi son Tafiyar Dare.." Haddir na Barin Bedroom din yana Fadin"Tab lalle...Yarinta ke Damunka Allah ya Shiryeka muje.."Daga haka ya Fice Shi kuma Sadiq ya Tsaya gaban Zain yana Fadin"Ya Dakta Allah kara Lafiya zan koma Zaria sai an kwana Biyu kuma.."Cikin Rinannun Idanuwansa ya Kallesa kafin ya mike ya Riko Hannayensa Duka Biyu yana Fadin"Sadiq kai kanina ne Ka ga Dai Abunda ya Faru dani ko..? Ina baka Shawara karka yarda ka Kusanci aikata Badala Kai ko mata ma kadaina sakar musu Fuska Da yawansu Shedanu ne sai sun kai ka sun baro su kyaleka Cikin Bala"i ka Tsare Kanka Don Allah.."Yafada Cikin Fitan Hayyaci Tsausayinsa ya kama Sadiq ya murmusa yana Fadin"Insha Allahu Ya Dakta..Ni Bana Shiga Harkan mata Mazan ma ni ba Shiga Harkansu nake ba Allah ya Tsaremu Daga aikata Abunda zamu zo muna Dana sani Daga baya.." Da Sauri Zain yace"Ameen Ameen Nagode..Allah ya kiyaye Hanya.."Ya amsa da Ameen Har Falon ya Rakosa kafin ya koma Shi kuma ya Fita Zuwa Haraban Gidan Inda Haddir ke Jiransa bai ma kai ga Shiga Motar ba Tanimu maigadi ya Tsareshi Da Tambayan ina Gimbiyar Dakta ko Tayi Tafiya ne bata Dawo Gida ba..? Shidai Haddir cemai kawai yayi bata lahiya Tana Gra Shine fa ya Fara kwararo Addu"o'i wata addu"ar ma baisan me yake Fadi ba Mirmishi kawai Haddir yayi ya zaro 1k ya bashi yana ta Godiya kana ya Bude mota ya Shiga Sadiq ma ya Shiga Gidan Gaba Yayi Hon Tanimu ya Bude Get suka Fice Daga Gidan. Sai da yakai Sadiq Tasha kana ya Wuce Gidan Abba Sadiq din kuwa yayi Sa"a yana zuwa Motar Zaria Ta kusa Cika Saura mutum Biyu yana Shiga sai ga wani Shima ya Zo Basu Dade ba Suka Tashi Haddir kuwa Koda ya isa Gidan Abba  ya iske Har Abba yaji Sauki ma ya Farka yana Cin Abinci Bayan ya Gaisheshi da Jiki Su Umma da Nene Duk suna Dakin Abba ya Kallesa yana Fadin"Ka koma bakim aikib ka ko..? Cikin Ladabi Haddir yace"A"a sai zuwa gobe Abba..Jikin Zain din Har yanzu ba Dadi.."Zaro Ido Nene Tayi Lokaci Daya Tana Dafe Kirji Cikin kaduwa Tace"Na Shiga uku me ya sami Zain din..? Kafin Haddir ya Bata amsa Abba ya maka mata Harara yana Fadin"Na manta ban Fada muku ba ko Sunansa na Kashe ambatonsa acikin Gidan nan..! Wannan Karon Har Umma sai da Ta kalli Abba kamar zatayi mgana sai kuma ta Fasa,Nene kuwa Idanuwanta Ne suka cika da kwallah ammh batayi mgana ba Abba ya kalli Haddir Fuskarnan nashi ba Annuri yace"Ka koma wajen aikinka ka Rabu Dashi..Babu jin kai ga wanda baya jin kunyar aikata Abunda yaso..! Kan Haddir na kasa yace"Kayi Hakuri Abba...Nasan Zain yayi Laifi matuka ammh.."Ammh me..? Me zaka Fadamin wanda ban ji ba kuma ban Fahimta ba..? Abba ya katse Haddir Lokaci Daya Da Dagamai Hannu sai Haddir yaji Gwiwansa Tayi sanyi Cikin Dauriya ya Dago kansa yana Fadin"Nasani Abba ammh In ka Lura da komai yadda ya Faru Zain ya Hadu da Shedaniyar mace ce ita ke Ribantanshi koda ya Tuba kan Abunda yake aikatawa.." Abba ya Dade yana kallon Haddir kamar bazai yi mgana sai kuma ya Murmusa kafin yace"Kaji wata mgana..? Ai Shine Babban Shedan din Hadiru.."Haddir ya Bude baki zai yi mgana Abba ya Dagamai Hannu yana Fadin"Kaga Hadiru Tashi kaje sabgoginka nagode..Ammh Matukar mganar Zainullahi zai kara kawo ka kaima na Yanke maka zuwa Gidan nan Allah bada lada.." Daga Haka ya Mike Daga kan gadon Bayan ya Ture Filet Din Abincin Daya gama ci Ya Taka ahankali ya wuce Tiolet,Dukkansu suka Bishi da kallo Cikin Tsausayawa ganin Duk ya Rame ya Fada Kada kai kawai Umma Tayi Tana Fadin"Komai ya Faru Zuciyarsa Data Rinjayensa itace Silan komai.."Daga haka ta Fice tana Kokarin Boye Damuwarta Dakin zaina ta Wuce Domin ta Dubata sai ta Iske ta samu Barci Hamdala Tayi ma Allah Domin Jiya Tana Jinta kwana Tayi bata yi Barciba Tana kuka Yanzu ko Hakkin Yarinyar nan Allah ya kama Zain Dashi zai ga Daidai arayuwarsa..? Nene kuwa Umma na Fita ta kalli Haddir Tana Fadin"Hadiru ya Jikin Zainullahi din..? Fata dai da sauki ko..? Bai mata mgana ba Jin kamar Abba na Shirin Fitowa Daga Tiolet Da Sauri Nene ta wuce Gaba Tana Fadin"Biyo  ni muje Dakina Hadiru..Alhaji ya Riga yayi Fushi Da Zain kuma Fushin da bamu Taba ganin yayi kamarsa da wani ba.." Ba Musu ya mara mata Baya zuwa Dakinta suna Shiga Ta Rufo Kofar Tana Fadin"Hadiru ba dai wani Cutar ne ta kama min D"ana bako..? Haddir ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Bata kamashi ba ammh in ya Cigaba da saka Damuwa zata iya kamashi Har tamai illah.." Salallami Nene ta Fara kafin ta zauna Gefen gado Tana Fadin"Oh ni Aisha..Ina zan saka Raina Wlh Hadiru Tun Shekaran Jiya Rabona da samun Barci mai Dadi agidanam Hankalina na wajen yaron nan babu Kowa awajensa bamai Sauraransa sai kai Ba Domin Alhaji yana mana iyaka ba Da Tuni naje naga Halin Dayake Ciki.." Haddir ya gyara Tsayuwa yana Fadin"Haka sadiq ke Fadamana yanzu Daya Biya kafin yanzu mu Fito Tare nakai shi Tasha ya Hau Motan Zaria,Zain din ne ma ya matsa bayan yaji Sauki kan zai zo gida da na Hanashi yaki Hanuwa Shine Sadiq yake Fadin Abunda Abba yace..Abun bai yi Dadi ba Nene Kinsan Fushin Iyaye kan ya"yansu fa Ba kyau sam.."Nene na Sharan kwallah Take fadin "Na sani Hadiru ya zanyi..? Wlh ni kam bana Fushi da zain sai dai in na ganshi zan mai Fata fata na Nuna mai Bacin raina kan Daukan Tarbiyan da ban Taba mai Shi ba..Ya na iya Alhaji yayi Fushi sosai wanda kuma sauko Dashi kan wannan Fushin sai Alhaji Tsoho kuma Shi din na Tabbata ba zai saka baki yanzu ba kuma Fushin Alhaji Duk da Yarinyar nan Halima ita ke kara Sakashi Jin Takaichin Zain Wlh Domin Kuka fa Take kwana yi Ta Wuni Yi Tunda Abun nan ya Faru.." Haddir yace"Ai da wuya ma Alhaji Tsoho yace wani Abu yanzu..Mganar ma Zainar  Duk da ita ta kawoni Nene,Ku saka Baki ta koma Gidan Mijinta Wlh Zain yana Bukatarta Sosai kuma Abu ya Riga ya Faru ai sai Hakuri Bawa bai isa ya kaucema Kaddaransa ba.." Nene tace"Hakane...ammh kam banajin Hakan zai yuyu gaskiya..'Haddir yace"Saboda mene Nene..? Nene tace"Saboda Ba wanda zai ce Dole Sai Halima ta koma Gidanta..Alhaji kuma bazai yi mgana ba Alhaji Tsoho kuma yasan Tana nan gidan ammh bai ce komai ba Uwarta ce kuma Bazata Yarda Ta baka ita ba.." Cikin Sauri yace"Wai Umma..? Nene tace"Eh..."Haddir ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"Bari naje nayi mata mgana in tayarda ta bani ita shikenan Abba da Alhaji Tsohi basu da yarda Zasu yi indai sukaji Ta koma Wajen Mijinta ai ba wanda ya isa ya Raba Tsakaninsu sai Allah Nene.." Nene Ta Mike Tana Fadin"Kwarai mganarka Haka Take muje Dakin Halimar Umman Tata tana Chan Tunda Ita ke kwana da ita.."Daga haka ya Fita itama tabi Bayansa Sun Fito Falo kenan suka ci karo da Zareena Tana Zaune afalo Tana bama Takwaran Umma Nono Jalal na Gefenta yana Game acikin Tap dinsa,Ganin Haddir yasa Ta saki baki Tana Fadin"Aboki Hadiru Tazuru kuma kanina Yaushe kazo gidanan..? Tafada Tana yar dariya Ba laifi Itama Ta Fara sakewa ba kamar Jiya ba Tunda Har tayi wanka Zataje gidan Alhaji Tsoho ne Hararanta yayi yana Fadin"Ni sa"anki ne wai Abokiya Zareena..? Kin Raina ni ko..? Cikin Shakiyanci Tace"ji wannan yaron..? Ban girmeka bane nifa yayarka ce ko kaki ko kaso.."Haddir yace"Wata Hudun da kika bani Shine kin Girmeni..?Ki sake Tunani yarinya akwai malaman da suka ce komai kankantar Namiji shine Shugaba akan mace saboda Haka ki Dawo Cikin Hayyacinki Maza Bisa kanki yarinya.."Yafada yana Kashe mata Ido Daya Bata rai Zafeera Tayi Tana Fadin"Da aurena da ya"yana kake cemin yarinya..? Yace"Au Ai harta wanda ya ijiyeki Engnear Jawaad din yaro ne..."Duka Zafeera Takaima ya kauce yana Dariya Nene ta Tayasu Sai ga Jalal ya Saka Dariya ashe Tun dazu yana Kallonsu kumatunsa Haddir ya Kama yana Fadin"Ai gaskiya na Fada ko Son..? Da sauri yace"Is Truth Uncle.."Dariya ta kama Haddir har Sai da ya Bashi Hannu yana Fadin"Dat my Son Plz Give a Five.."Yako bashi Hannu suka Kashe Zareena tacika kamar ta Fashe Nene sai Dariya Takeyi Haddir da Jalal na Tayasu. Kukan Little Umma ne ya katse Zareena ta koma ta zauna Ta Cigaba da Bata Nono Tana Fadin"Ka samu sa"a ne Aboki Zaim baya nan Da shi zai Taremun Tunda kafini baki.."Ambaton sunan Zain Da Tayi ya Dauke duka walwalansu Cikin Damuwa Haddir yace"Yana Gida ba Lafiya Abokiya Zareena.." Cikin Damuwa Itama Zareenan tace"Ayyah..Allah ya bashi lafiya..Zan je na Dubashi ammh Nene Kada Abba yaji labari.."Nene tace"Wa..? Ba wanda zai ji kinji na Rantse Miki anjuma kije ki Dubamanashi Don Allah kice ya kwantar da Hankalinsa Nenensa na Tare dashi komai zai Wuce.." Zareena Tace"Insha Allahu...Zan Tafi Gidan Alhaji Tsoho na kai mai mai Sunan Umma Shi da Hajiya Mama da Tabawa Daganan sai na Biya na Dubashi..Allah sarki wannan Kaddaran bata kyauta mana ba sam Nene..'"Haddir yace"Uhm...Bari dai na ga Umma kam mganar Zaina.." Zareena Ta kalleshi Tana Fadin"Tab...Anya kuwa..? Da kun bari zuwa akwana Biyu Lokacin Abun ya saketa.."Haddir ya kama Tafiya Zuwa Dakin Su Zaina yana Fadin"A"a Barin zuwa Wani Lokacin ta wannan bangaran abun kara Tabarbarewa zai yi..Zain na Bukatarta ahalin Dayake Ciki.."Zareena Tace"Allah yasa ku dace..' Nene Tace"Ameen Ameen..."Daganan Itama ta mara ma Haddir Baya zuwa Dakin Da zaina Take,Haddir ne kan Gaba ya Tura Kofar ya Shiga Nene na Binsa abaya Da Umma suka ci karo ta Riko Zaina sun Fito daga Tiolet kamar Wanka Ta Taimaka mata Tayi da alwala Tunda dai Wasu masallatan Har sun Fara Kiran Sallar mngariba. Atare Umma da Zaina suka kai Dubansu kan Haddir da Nene Cikin mamaki Umma ke binsu da kallo har suka kariso Cikin Dakin,Haddir ne ya Fara gaisheta Cikin ladabinsa Lokaci Daya yana karema Zaina kallo ganin Tayi wani Fari fayaut kamar bata da jini ajiki kuma Ta Rame bakinta ya Bushe akallon Farko sai yaga kamar Tayi wani Danye Danye kamar wata mai Shigar Sabon Ciki Ita kuma Sau Daya Ta kalleshi kawai ta kauda kai kan Gado Umma ta zaunar da Ita Tana Fadin"Zauna ki Huta kafin ki shafa mai ki saka kaya sai kiyi sallah kici Abinci ko..? Kallon Umma kawai Tayi batare Da Tayimgana ba Umma ta maida Hankalinta kan Haddir tana amsa gaisuwansa Nene ta kalli Zaina Tana Fadin"Sannu Halima Ya Karjin Jikin..? Bata amsa ba illah kanta Data maida kasa Daman bata saka Rai zata amsata ba Domin Tunda Abun nan ya Faru Bazata ce taji mganar Zaina ba ko sau Daya ba sai dai in da Ummanta,Umma ce ta kalli Nene Tana Fadin"jikin nata da Sauki ba zazzabi sai dai Rashin karfin Jiki Shi kuma wannan Rashin Cin Abinci ne Tunda ko Taci sai ta amayar dashi..? Nene tace"Toh yanaga Idanuwanta sun kumbura ne bata bar kukan bane..? Umma ta Rausayar Dakai Tana Kokarin Daukan man Vaseline saman Madubin Dake dakin Tace"Bata bari ba..Kuma Harda ma da Rashin barci Da Rana tana samu tayi kadan ammh Da Daddare bata barci Kwana Take kuka.." Umma Ta Fada Fuskarta na Sauyawa Haddir ne ya sauke Numfashi yana Fadin"Allah ya Sauwake ya kamata Taga Likita Gaskiya.."Umma tace"Bata so..Bazata asibiti ba tace..Ni kuma bana som matsamata Na kyaleta Ko Taje asibiti Basu da mganin Damuwarta Hadiru.." Haddir yace"Hakane Umma..Ammh Kuka ma da Amai Da Rashin barci ai Wata Cutan ne na Dabam ko..?Umma batayi mgana ba illah mika ma Zaina Man Data Dauko mata Datayi wacce ke sanye da Hijabi Dogo na wajen zainab ne Umma ta Dauko mata Karba Tayi Ita kuma Umma tace"Ki shafa.." Haddir ne yaga Umma na Shirin Shiga Tiolet yace da Sauri"Umma wajenki fa nazo.."Dakatawa Umma Tayi Ta waigo Tana kallonshi kafin tace"Wajena kuma..? Allah sa lafiya..? Haddir yana kallon Zaina wacce Ta Dago Tana kallonsa da Rinannun Idanuwanta yace"Lafiya lau..Dama mganar Zaina ce Umma" Umma Ta Juyowa Gabadaya Tana Fadin"Ina Jinka.."Tafada Tana kallon Nene wacce ta marairaice mata Tun Daganan Ta gano Inda suka Dosa Sai dai bara Ta katse musu Hanzari ba gwara Taji Daga bakinsu lalle zasu ga Fushinta nan take kuwa. Idanuwan Umma sun ma Haddir kaifi ya kasa mgana sai da ya Sunkuyar dakai kana ya iya Fadin"Dama..Dama..Umma mganar Komawar Zaina Gidan Mijinta ne kinga Zain yanachan kwance ba lafiya kuma Yana Bukatarta ayanzu gaskiya.." Har ya gama mganarsa Umma na Jifansa da wani kallo na lalle nema kun Raina mutane Zaina kuwa Tun mganar Haddir Taji Dan Jinin Jikinta ya Daina Gudu Bata Sha"awar kara ganin Ya zain ma Ita acikin Idanuwanta ammh akasan Ranta Tsausayinsa Sonsa Sun Hanata Sukuni Kamar Daga sama Taji Umma na Fadin"Ok Shi ya aiko ka kenan...? Shine kuma Da zaka zo Fada ka Dauko Uwarsa kuka zo Tare ko..? Nene tace"Eh yazo yagamin komai..Nace yazo muje mu Taru mu Roke ki Umman Zareena Hannunka fa baya Taba Zama Cuta gareka,Bamu da yarda zamu yi da wannan kaddaran kuma Hana Zain matarsa kamar kara Tabarbara komai ne,ki barta ta koma Gidan Mijinta Suyi Jinyan Juna Ya bata Hakuri sai Kiga komai ya Daidaita.." Umma Ta Tsuke Fuska Tana Fadin"lalle nema..Wato yanzu ne Take da kima da Daraja acikin Idanuwansa ko..? To kaje ka Fadamai Wlh Tallahi kunji Rantsuwan Musulmai yata bazata Je ko"ina ba.." Daga Haddir Har Nene kasa Mgana sukayi jin Umma ta Rantse,Cikin Jan karamin Tsaki Umma tace"Ina Dadiron nashi ko nace karuwan nashi Da bai Kirata tazo Tayi Jinyarsa ba Ko nace Uwar Shegen nashi..? Sai yata Zata Dinga Wahala kansa ko..? Hadiru ka Fita idona karka kara Zuwarmin da wannan mganar Banzan Daga kai har Uwarsa Wacce bazata ga Illah Da Abun Tir din da D'anta ya aikata ba.." Tafada Cikin Bacin rai Da Sauri Haddir ya Rankwafa yana Fadin"Don Allah Umma..Ko Sau Daya ki bani Dama nayi mgana Da zaina kila ita ta Fahimceni.."Kamar Umma zata mareshi Haka ta taso mai Tana Fadin"Anki abaka Daman..? Nace an ki abaka daman..? Ba inda Zata ka wuce ka bamu waje kafin Raina ya baci Na Tsinke ka da mari Hadiru.." Jin Haka yasa bai yi gaddama ba ya Juya yana Fadin"Allah Huci Zuciyarki Ummah.."Da Sauri Tace"Ameen.."Nene bata ma yi mgana ba ta kada kai ta Juya Tabi Bayan Haddir kawai Umma Ta Rakasu da Harara Tana Fadin"Kaji min iskancin banza iskancin Wofi..Wani wai Ta koma Gidan Mijinta..? wato ta koma Taje Chan ta Cigaba da zama Dashi karshenta ya Auri Karuwarsa Tasa tazo Tana Tayasu Renon Shegen nasu Rayuwarta Ta kare Cikin Bakinciki Wlh bazata sabu ba indai ina Numfashi Halima Ta bar Auran Zain har Abada.." Zaina Dake zaune bata san Sadda Karshen kalmar Umma ta saka Kukanta Fitowa ba Cikin wani Takaichi Umma ta Isa Gareta Tana Fadin"Rufemin baki Sakara mara wayau...Ana Neman yadda Zaki Rayu Cikin salama kina ma wanda ya ci Amanar zaman tare da irin Soyayyar da kika nuna mai kuka..? Ki Min Shuru yanzu ko na Kikkifa miki Mari yanzu yanzu nan.." Jin yadda Umma ke Sababi ne yasa Zaina Tayi gum da bakinta bata kara Bari kukanta ya Fito ba ma Ta Dinga Hadiyeshi Tana Sauke ajiyar Zuciya kamar wata karamar yarinyar da Uwarta Ta Tsigeta Tana Cikin Shan Nono Tsaki Umma Taja ta Nufi Hanyar Tiolet tana Fadin"Kafin na Fito ki Saka kaya ki Tada Sallah in kina so mu Shirya.." Da Sauri tace"Toh Umma."Tana Kokarin Goge Hawayenta da Danne kukanta Sai Lokacin Umma Taji Tsausayinta ammh kuma Dole ne tayi mata haka In ba Haka ba Haka Zatayi ta zama Cikim Kuncin zuciya har wani Cutan ta kamata Kofar bayin ta Bude ta Shiga Ta bar zaina na Kokarin Mikewa Lokaci Daya tana saka Hannu tana Danne bakinta kada kukanta ya Fito Umma Taji ta Fito taci kaniyarta. _Godiya Ta musamman ga Dimbin Masoyan ZAINAZAIN,Ina ganin Tarin Sharhinku da Comments Dinku Musamman yan Group din ZAINAZAIN 1&2 ,da Gidajen Janafty Shakira,Duka ina gani Kuma ina Jin Dadi Sosai kuke sakani Nishadi Kuyi hakuri bana samun Lokacin Maida muku martani Abubuwan ne sai a Hankali ammh ina gani kuma ina Godiya Da ku da yan Wattpadians Fans dina suma Ina ganin Sharhinsu Alhamdullahi kawai Zance Allah ya bar Zumunci Ameen..!_ *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*               2️⃣3️⃣ "Haddir ne kan gaba Nene na Biye Dashi Zuwa Falo,Zareena na ganinsu Fuska ba walwala Tasan ba"a Dace ba Domin Taga Umma Ta Dauki Fushi Sosai kuma Bata ma da Niyar Barin Zaina Ta koma Gidan Mijinta a Take takenta Datake gani. Cikin Kallonsu Tace"Ba"a Dace ba ko..? Nene ce ta zauna Gefenta Tana Fadin"taki ma Sauraranmu...Naga Bacin rai naga Tsausayi na Soyayyah da Jinkai duka acikin Idanuwanta na Farko Tana Tsausayin Zain Tana kuma Tsausayin Halima Tana kuma Jinta kamar yarta Data Haifa Da Cikinta,Wannan Dalilin yasa Ta nuna bacin Ranta Sosai wanda ban Taba gani ba.." Nene Ta Fada Cikin karaya,Zareena Tace"Hm...Allah ya kyauta nagaba.."Haddir ya amsa da Ameen yana Fadin"Bari naje na samu Alhaji Tsoho muyi mgana in anci Sa"a ya saka Baki mgana Ta kare.."Nene tace"Shima din bana Jin zai ce wani Abu awannan Lokacin Hadiru.."Haddir yace"Zan Jaraba Dai na gani yadda mukayi Dashi ko ban Daawo ba zan Kiraki awaya na Shaida Miki.." Nene tace"Shikenan..Sai na Jika.."Zareena kuma tace"Ka gaida Zain din sai nazo.."ya waiwayo yana Fadin''Ke ina zaki da Daddaran nan..? Baki bari sai gobe..? Nene tace"Nima Abunda na gayamata kenan.."Jin Haka yasa Zareena tace,"Shikenan bari na Bari sai goben Dama zan Jira in Zainab Ta Dawo Daga makaranta Direban Abba ya kaimu ne ammh Bari dai na bari sai gobe da safen.."Haddir ya wuce yana Fadin"Yadai kamata kam...Ni na wuce.."Suka Rakashi da Allah kiyaye Hanya. Yana Fita Haraban Gidan yaci karo da Zainab Ta Dawo Daga Makaranta Cikin Ladabi Ta Ramkwafa Tana gaisheshi ya amsa Sama sama ya Fada Motarsa ya Fice Daga Gidan Ta Bishi Da kallo Bata samu Fuska bane Taso Ta Tambayeshi Ya Ya Dakta yake ne..? Sai dai baima saki Fuskan ba Ballatana ta Tambayeshi Tana Shirin Shiga Cikin Gida ne sai ga Motan Abba ta Dawo Daga Dauko su Saudart Daga Islamiya bata ba Tsaya ba Taja Jakarta Ta Nufi Cikin Gida Domin yau din agajiye ta Dawo Wuni Tayi Cikin Makaranta Suna Kokarin Fara Test din Zangon Karatunsu na Farko ne. Haddir kafin ya isa gidan Alhaji Tsoho sai da ya Tsaya masallacin Kusa da Gidan yayi Sallar mangariba kana ya karisa,Alhaji Tsoho Na cikin Dakinsa saman Kujeransa yana Karatun wani katon Littafi da Siririn Gilashinshi mai kara mai karfin gani,Gabansa Haddir ya Zube bayan sun gaisa Ya Shiga Rarrafomai Abunda ke Tafe Dashi na game da Fushin da su Abba suke da Zain da kuma Halin Da yake ciki da kuma Yadda sukayi da Umma yau din.. Har ya kamallah maganganunsa Alhaji Tsoho na kallonsa bai ce komai ba,Ganin Alhaji Tsoho yayi Shuru ne yasa Haddir yace"Nazo na gayamaka ne Tsoho Saboda ka saka baki Abba ya Janye wannan Fushin Da yakeyi Ko Zain zai ga Daidai Arayuwarsa..Umma kuma ka mata Mgana Ta bashi matarsa Tunda dai mai afkuwa ta Riga ta afku Sai dai muyi kokarin kada Hakan ya kara Faruwa..! Mirmishi Alhaji Tsoho ya saki kafin ya Ijiye littafin Hannunsa Saman wani karamin Tebur Dake gabansa Lokaci Daya Yana Fadin"Toh ni yanzu da kazo kana Gayamin me kake so nayi maka..? Cikin Mamaki Haddir yace"me nake so..?kaifa Tsohon nan ka iya Nuna ma Mutane Boko fa..? Ai nayi maka Bayanin komai.."Dariya Ta kama Alhaji Tsoho wanda Tun Faruwar Al"amarin nan bai yi Dariya Haka ba baki Sake Haddir ke kallonsa kafin ya koma kawaai ya Hade Ransa sai da Alhaji Tsoho yayi Dariyansa Son Ransa kana yace"Yaro yaro ne...Yaro Man kaza bai san Wuta ba sai ya Taka.." Cikin Haushi Haddir yace'"Ammh dai bani  kake Nufin yaro man kazan ba ko..?Alhaji Tsoho yace"A"a Ba da kai nake ba...Karin mganace tamu ta Hausawa.."Yafada yana Dariya Lokaci Daya yana Daga Hannu Alaman yayi saranda Mirmishin Lebe kawai ya saki Yana kallon Alhaji Tsoho Daman ya sani Alhaji Tsoho so yake ya Hukuntashi Shida Zain alokaci Daya. Ganin yadda Haddir din yasha Kunu ne yasa Alhaji Tsoho ya Dakata da Dariyan Dayake ya Fuskanci Haddir yana Fadin"Kasan abunda kai baka Fahimta ba Hadiru..!? Bai bashi Zarafin mgana ba yacigaba da Fadin"Duk Cikin ya"yana Usmanu Yafi kowa Hakuri da kawaici Sai Mahaifinka Aliyu..Sai Rukayytu..Dama masu Zafin Da Zuciya Sai Babana da Hannatu uwata Daman kuma so Gado sukayi wajen Uwarsu Amina ka gantanan nayi Fama da Ita Tun Lokacin muna da Kuruciya.."Yafada Cikin Zolaya Murmusa kawai Haddir yayi batare Da yayi mgana ba Shima bai Damu Daya Tanka din ba ya Cigaba Da Fadin. "Tunda kaga Usmanu yayi irin wannan Fushi Ka Tabbata Babban Abu ne...Mutun ne mai kawaici da Boye damuwa Naji matukar Tsoro Lokacin Danaji Labarin Damuwar da Zainullahi Ya sakashi Ta kaishi Har kwance bai iya zuwa aiki Daganan nasan Zainullahi ya Gama Raunana Zuciyar Usmanu na Wanda banta gani ba Tunda na Haifeshi Saboda Hakurinsa da Kawaicinsa..! Ya fada Idanuwansa na kan Haddir wanda ya natsu yana Sauraransa Cikin Takaichi Alhaji Tsoho ya Cigaba Da Fadin"Me kake so nayi akai Hadiru..? Karka manta Usmanu Shine Mahaifin Zainullahi Shine Babban D'a Namiji cikin ya"yansa Wanda ya Dorama Son Duniya da kuma Burin Watarana In Bashi Shi zai Gejesa ya Rike Iyayensa da kanninsa..? Ya bashi yarda yana ganin Ya Sauke Nauyin Dake kanshi Wajen Bashi Dukkan Tarbiya da Ilimi na Arabi da na Zamani Saboda Watarana ya Tsaya Da Kafafunsa bayan Gama Dukkan wananan bai ga Sakamakon komai ba sai wannan aikin da Zainullahi ya aikata na Ijiye karuwa suna zaman Haramci Harda Tsaraban Ciki,Ni na isa na Hanashi Nuna Fushinsa da Damuwarsa akan Abunda ya Haifa..? Ya Fada yana kallon Haddir Wanda kalaman Alhaji Tsoho suka Sanyayamai Jiki Kai ya Girgiza Cikin Mutuwar Jiki Kafin Alhaji Tsoho ya Cigaba da Fadin"Toh ka gani bani da wani Abunda zan iya yi kan wannan Lamarin Hadiru Zainullahi ya gama Bamu kunya gabadayanmu..Na Riga nayi iya Abunda zanyi sauran kuma sai mu bar ma Ubangiji mganar ita yarinyar ma Mahaifinta ya Kirani yace nayi Hakuri Dayake ya karbi Lambata Ranar kafin su Wuce kan Gobe ne Suke sa Ran Zuwan ita Uwar yarinyar Daga Sudan in tazo yayi mata Bayani Insha Allahu zasu zo da mai Dakinsa su kawo ta Wajena kamar yadda nace..Sai godiya yake min abun gwanin ban Tsausayi..! Haddir bai samu Damar mgana ba yaji Muryan Hajiya Mama Dake Kokarin Shigowa Dauke da Farantin Kololin Abincin Alhaji Tsoho tace"Nifa wannan Hukuncin naka baimin ba Sam Taya za"a ce kuma tazo ta zauna Cikin mu Har ta Haihu ai sai in muna ganinta Bakinciki watarana ya Nemi kashemu daka sani Ta tsaya chan gaban Uban nata ta Haife Shegeen..' Tafada Cikin bayyana Takaichinta Da Sauri Haddir ya mike ya karbi kayan Hannunta yana Fadin"Kamar kin Shiga Raina Hajiya Mama..Wlh nima Haka nace..! Yafada yana Sauke Farantin Gaban Alhaji Tsoho wanda ya murmusa yana Fadin"Mata mata..Sai abarku..Nan din Shine mafita ai Aminatu..Mahaifinta Dan Siyasa ne zamanta gabansa akwai mtsala Gwara tazo nan ta Haihu sai a Daura musu Aure suje chan su Cigaba da Renon Abunda Suka Hadu suka samar baShikenan ba.." Hajiya Mama na zama Gefen Haddir Tana Fadin"Bafa Shikenan ba Mallam..Su mun Rufa musu asiri mu kuma mun Tona namu kana Tunanin mganar nan bazata Fita bane in Har yarinyar ta Dawo gabanmu da wannan Abun kunyar..? Alhaji Tsoho yace"Zai fita mana...Alheri ke Buya banda Sharri Aminatu..Kuma Wanda ya rufama wani asiri Allah Shima zai Rufamai Duniya da Lahira,Muma ai ya Rufamana Tunda bai kai mu kara Kotun musulunci ba Inda chan yakai Allah Jikanki jefasa za"ayi har ya Mutu Tunda da Auransa yake Zina.." Hajiya Mama tace"Ita fa sai a kyaleta..? Alhaji Tsoho yace"In ta Haihu ita kuma Bulala 80 za"ayi mata Tunda ita batayi Aure ba.."Hajiya mama Tayi Tagumi Tana Fadin"Ba wacce nake jin Tssusayinta Har Raina sai Yarinyarnan Halima Dazu mukayi mgana da Fatima Take Fadamin komai taci sai Ta Dawo dashi kwana Take kuka Ga Rashin Barci..' Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Nima Wlh Aminatu..Kamar kin Shiga Raina da Yarinyar nan marainiyar Allah nake kwana ina Tashi..Ina Fatan Allah yasa ya zame mata kaffara.."Gabadayansu suka amsa da Ameen,Kafin Alhaji Tsoho yace"Mganar da Hadiru yazo min da ita kenan kam in saka Baki Takoma Gidan Mijinta Shima yana chan kwance ba lafiya Hadirun ma ke Kwana chan yana Kula Dashi..". Hajiya Mama tace"Oh ni Amina...Allah ya kyauta na gaba..Me kace kan mganar..? Alhaji Tsoho ya sauke Numfashi yana Fadin"Me kuwa zan ce..? Bazai yuyu Ta koma yanzu ba saboda Halin Datake Ciki Gwara ta zauna anan Uwarta na Kula da ita  Zuwa akara kwana Biyu ni dakaina zan saka Fatimar tazo Da ita nan na kara mata Nasiha Da Lallashinta Mganar Usman kuma Shima sai zuwa bayan an kwana Biyu zan mai Mgana kan ya Sausssauta Fushinsa Hakan bai da wani amfani Kai kuma Hadiru in ka koma Wajen Zainullahin in Jikinsa yayi sauki gobe ka kawomin shi nan ina son mgana Dashi.." Haddir yace"Allah ya kaimu.."Daga Haka ya kalli Hajiya Mama yana Fadin"Me kuka Dafa ne Tsohuwa..? Cikin Haushi Hajiya Mama tace"Uwarka Safiya ce Tsohuwa don kaniyarka.."Baki ya Rike yana Fadin"Me yayi zafi Kika sako Sunan uwata Gatse haka..? Karkace kai Hajiya Mama Tayi Tana Fadin"Don ma Bance Aliyu Kai Tsaye ba..? Baki ya kama yana Mikewa Lokaci Daya yana Fadin"Kirashi mana ai ke kika Haifi Abunki ni miye nawa..? duk Tsiyarki dai baki haifeni balle kice zaki Dakeni Ni kinga ma Tafiyama basai kin ga mutum bama ballatana ki gayamai mgana.." Yafada yana Bayyana yadda yaji Haushin Kiran sunan Mamarsa Datayi,Alhaji Tsoho na Gefe yana Mirmishi Cikin Tura Haushi Hajiya mama Ta Rakashi Da Fadin"Kwarai na Haifeka kuwa..Tunda na Haifi Uban daya kawoka Duniya kaga kuwa bama Duka ba zanyi sakaka Cikin Daki nayi maka Dukan Tsiya sai na barka kwance.."Ko Tankata bai yi ba ya Fice yana Fadin"Sai kuma kiyi..Ji dai da wannan Rudadden Tsohon Mijin naki.." Da karfi Tace"Bana ga Rudadde ba..Rudadde ya wuce Ubannanka Bashir ko Aliyu.."Yana Jinta Daga Falo kai ya Girgiza yana Fadin"Gaskiya Tsohon chan ne Daya ce Rigimarki su Baban kaduna suka kwaso.."Abayyane yayi mganar Dakinsa ya Shiga Wanka yayi ya Sauya kaya kana ya Fito Kitchen ya Shiga wajen Tabawa suka gaisa Cikin Sanyin Murya Take Fadin'Ya zainullahi yake ne Hadiru..? Tura baki yayi yana Fadin"Kai Tabawa..Wai kema Hadirun nan Har dake.."Dariya Tayi Tana Fadin"Eh mana wannan Shine zamu kira namu na Mutan Da..Ko Bakin ku na yan zamani ne Hadiru..'Kai ya Rausayar yana Fadin"Ba wani kuna dai Batamin suna kuma ba kowa yaja ba sai Tsohin chan Da matarsa.."Tabawa Tayi Dariya kawai Haddir yace"Zain yana nan Lafiya..Bai dai jin Dadi ne yanzu ma Shi nazo samar ma wani Abu Allah yasa kinyi Tuwon nan naki mai Dadi Tabawa..'Cikin alhini tace"Allah Sarki..Allah bashi Lafiya Jarabawa ce Allah ya bashi ikon Cinyewa damu gabadaya..! Haddir ya amsa da Ameen Kafin Tabawa tace"Akwai Tuwon Shinkafa Miyar Danyan kubewa Wanda nayi ma Alhaji Tsoho ne.."Da sauri Haddir yace"Alhamdulillah..Saka mana Cikin Kula nayi gaba Dashi Daman na Dade banci Tuwon ki ba Tabawa.."Tana Dariya tace"Na Dumaman Alhaji Tsoho ne fa ko nayi muku wani ne..? Da Sauri Haddir yace"No..Samana wannan Tafiya zanyi na bar zain Shi kadai..Yaci yanzu banda Hadama yace harda wani Dumaman Safe..? In yayi mgana gayamasa Manyan Jikokinsa na Bukata kin basu.."Tabawa na Dariya tace"Shikenan kuwa..! Saka musu Tuwon Tayi Cikim kula Miyan ma Haka wacce Taji Kashin Rago da manshanu Dauka yayi ya Fice yana mata Godiya Ta Rakashi da Allah kiyaye Hanya da kuma sakon Gaisuwarsa ga Zain ko Dakin Alhaji Tsoho bai kara Lekawa ba Saboda yadda hajiya mama Ta gama bata mishi Rai abayan Motarsa ya Jera komai ka fin ya Shiga ya Tasheta ya Fice Daga Haraban Gidan Bayan Maigadi ya wangalemai get. Yana Bisa Hanya Dadyn Abuja ya Kirashi sukayi mgana ya kara gayamai Halin da ake Ciki Daddyn Abuja ya Sauke Numfashi yana Fadin"Yanzu muka gama mgana Dashi ya Usman Din..Dama na sako mai nganar Zain din kashe wayarsa yayi ya Riga yayi Fushi Dashi ne sosai na kuma Kira Ya Bashir namai mganar Shima ya nuna Ma Ya Usman din yayi Daidai ne bazai saka baki ba..! Haddir acikin Ransa yace"Daman ai wannan haka zai ce.."Haryanzu bai manta zafin marin Dayayi mai ba Cikin Damuwa yace"Daddy meye Abun yi Kenan..? U hv to do Something fa..'Daddyn Abuja yace"Karka Damu...Muna ta Shiryan Shiryan Dawowa nan Bauchi Dukkanmu gabadaya Har sai an gama Bikin Kanwarka Hamdiya kafin mu koma Insha Allahu i will Tary may Best naga komai ya Daidata kaji ko..? Ajiyar rai Haddir ya Sauke Kafin yace'"I Truth u Daddy...."Daddyn Abuja yace"Tanque Son..Ina zain din bani shi a waya nayi mgana Dashi..?Haddir yace"Yana Gidansa yanzu haka ina kan Hanyata ta zuwa ne naje na Karbomai Tuwo Gidan Alhaji Tsoho..'"Jinjina kai Daddyn Abuja yayi kafin yace"Alrigh in ka isa Call me Ina son nayi mgana Dashi.."Haddir yace"Ok Daddy..Ka gaida Mom..! Daga Haka suka yanke Kiran Shi kuma Haddir ya Cigaba da Driving Dinsa Bai jima ba ya isa Gidan yaji Dadin ganin Zain yaji Sauki Har ya sake yin wanka ya Fito Falo Har ya Shiga Kitchen ya Dafa Ruwan Coffea,Haddir ya Nuna Jin Dadinsa Sosai ganin Zain din ya Taahi da kafarsa ba kamar kwana Biyu nan Dayake Wuni Kwance ba Tare sukaci Tuwon Suna santi kafin Haddir ya maida Sauran ya saka Cikin Fridge,Shima irin na Alhaji Tsoho zai yi Dumame kenan Bayan ya wanko Hannu ne ya Dawo ya Kira Dadyn Abuja yabama Zain sukayi mgana Sun Dade yana ta Fada Cikin Hikima da Salama yana kuma Nuna mai Kuskusaransa kana ya bashi Tabbacin zai zo Bauchi bazai koma ba sai komai ya Daidaita Zain nata Godiya yana kuka kafin Wayar nasu ta kare sai alokacin ne Haddir ke Fadamai Sakon Alhaji Tsoho Duk da Zain yaso yaji me ya Faru Dayaje Tahowa da Firstlove..? Ammh sai yaki gayamai komai Illah cemai Da yayi Zareena da Nene na Gaisheshi Cikin mamaki yace"Ashe Har yanzu suna Sona..? Dariya Haddir yayi yana Fadin"Ai ba"a sauya ka ba..Kanan nan amatsayin Yaya Daktan ka.."Sai da Zain ya Murmusa da kalaman Haddir Cikin Sanyin murya yace"Ya jikin Abba..? Haddir yace"Yaji Sauki Shima.."Daga haka ya yanke mganar ya Dauko wayarsa ya Fara Latsawa Shi kuma Zain ya koma ya Jingina da Kujera ya Fada Zurfin Tunani yana so ya Tambayeshi Zaina kuma sai ya kasa Domin baya so yaji wani Labari mara Dadi akanta,Shiyasa yayi Shuru da bakinsa Ammh Abun nacin Ransa da Zuciyarsa.. ***** Washegari kuma Tun Wajen karfe 10am na Safe Zareena da Zainab da Little Umma da Jalal suka zo Gidan Zain sun iskeshi Shi kadai Haddir baya nan ya Fita Zuwa Cikin asibiti,Yaji Dadi da kuma mamakin ganinsu Domin bai taba tsammanin Wani Daga Ahalinsa zai zo Dubashi ba Karban Little Umma yayi yana Kallon Zareena yana Fadin"Ammh Abba bai san kun zo ba ko..? Kai ta gyada mai Tana Fadin"Bai sani ba..Gidan Alhaji Tsoho nace zani..Umma ma bata sani ba Nene ce kadai ta sani tace na Gaisheka kwarai ita tabamu ma wannan Ferfesun Kayan Cikin Tace mu kawo maka.."Idanuwansa suka Ciko da kwallah yabi kulan Dake Hannun zainab da kallo kafin yace"Allah Sarki Neneta..Na Saka Zuciyarta Ta Raunana saboda ni..Allah na Tuba Allah ka yafemin.."Suma cikin Tsausayawa sukace Ameen Jalal ne ya Hau gadon yana Fadin"Uncle baka da lafiya ne..? Kumatunsa ya Shafa yana Fadin'"Eh Sojan Jaawad...Ina Babanka.? Zareena ne tace"Yana katsina ya samu Hutu ne...Daman kuma akwai Bikin Diyar yayarsa Jibi ma zai zo yaDaukemu mu Tafi Chan Family House dinsu sai an gama Biki zamu dawo insha Allahu.."Yana Mika mata little Umma yana Fadin"Allah ya kaimu ya kuma kaiku lafiya.." Ta amsa da Ameen Shuru ya Biyo Baya Kafin ya Dago yana Fadin"Ya Firstlove take..? Tabar yin kukan...? Zareena tace"Tadai Sauki kam..Nadai jita dazu ita da Umma Tana ta yi mata Fada kamar zata Dageta kan Kukan Da takeyi..'Cikin karaya da wani Irin Soyayyarta Dake Cikin Zuciyarta yace"Bazan iya kwana ban je na ganta ba.."Da Sauri Zareena tace"Ya zakayi da Abba..? Umma ma bazata barka ka ganta ba Domin Jiya marin Aboki Haddir ne kadai batayi ba kan yace yazo Tafiya da ita.." Ido ya sakarmata yana Fadin"I know.."Yafada Cikin wata Murya Kamar yayi kuka kafin yace"Zan je koda zai Koreni ne..Zan je na Duka na Bashi Hakuri..Shi da Umma na kuma Dukama Firstlove na kuma Roketa Data Yafemim.."Zareena Tace"Shikenan ammh karka kaje kai Kadai..Ku Tafi Tare da Aboki Haddir.." Kai ya gyada mata yana Fadin"Eh Tare zamu..Yanzu ma Shi nake jira zamu je gidan Alhaji Tsoho yace yana son ganina Ko bama Haka ba ni da kaina Zani Shima na Rokeshi Gafaran Abunda na aikata da kuma Kuncin dana sakasu Shi da Hajiya Mama..'Cikin Sanyin Murya Zareena tace"Ya kamata..Allah daidaita komai.." Ya amsa da Ameen basu wani Dade ba suka wuce Zasu Biya School su kai Zainab Da Zareena Ta Fadamai haka ne ya Kalli Zainab yana Fadin"Zee Kun Fara Test ne...? Kai ta Girgiza mai kafin tace"Bamu Fara ba mu..Ammh wasu Duk sun Fara Yaya Dakta ina Jin ma Harda su Anty Zaina Domin na Hadu da kawarta Anty Laila take cemin yanzu zasu Shiga Test ne.." Cikin Karfin Gwiwa yace"Dole zan je na Roki Firstlove gafara..Na Dawo da ita Gida ta koma makaranta bazan yi Sanadiyar Ruguza Burinta nayin karatu mai Zurfi ba. ****** Su Zareena basu kai awa da Tafiya ba sai ga Haddir ya Dawo Daman Zain ya Riga ya Shirya Cikin Riga da wando na Wata Blue Din Shadda Fitowa kawai yayi suka Wuce,Suna Hanya ne Haddir ya juyo yana kallonsa yadda Duk yayi Zuru Zuru ga Kasumba Tayi mai yawa Cikin Damuwa yace"Ko zamu Biya Shagon aski ne ka Rage wannan Gashin..? Kai kawai Zain ya Girgiza kafin yace"Bashi ne agabana ba Haddir...Muje gidaanmu Dagachan sai mu wuce Gidan Alhaji Tsohon Da Sauri Haddir ya kalleshi kafin yace""A"a ba yanzu ba Zain..Abba nacikin Fushi bazai Saurareka ba.."Zain Cikin Takaichi yace"Banga Laifinsa ba..Ko Bazai Saurareni ba Zanje na Duka na nemi gafaransa Koda zai min Koran karene..' Haddir zai yi mgana Zain ya Dagamai Hannu yana Fadin"Komai ya Faru ninaja..Abaya Abba yamin haka..? Amsa ita ce A'a Saboda Naji na Dauka zan Tunkarin wannan Yakin Insha Allahu da Tsarkakken Zuciya Allah na Tuba ka yafemin.."Yafada yana Jin Taruwar kwallah acikin Idanuwansa Haddir bai kara mgana ba yayi Shuru yana Fatan in sun isa Allah ya Kwantar da Zuciyar Abba. Allah kam bai amshi Addu"an Haddir ba Domin Suna Shiga Falon suka ci karo da Umma da Nene,Dukkansu Mikewa sukayi suna Bin Zain da ya Shigo abayan Haddir da kallo Cikin wani yanayi Umma kallonsa Take Tundaga sama Har kasa ganin yadda ya Sauya Cikin kwana Uku kachal,Nene kuwa Har ta Fara Hawaye ganin yadda yayi wani Baki ya Rame kamar bashi ba Cikin Dimuwa da Tsausayi ta Nufeshi Tana Fadin"Zain...! Bata karisa Gareshi ba Shima ya Taho da Sauri Zuwa gareta Da Murnan ya samu kafadan da zai Kwanta yayi kuka Yaji Muryan Abba yana Fadin"Kul...Aisha karki Sake ki karisa kusa Dashi..Kinji ma nagaya miki..! Yafada Cikin Kakkausan Murya,Gabadayansu suka waiga suna kallonsa yana Tsaye Daga Gaban Korodon Dakinsa Cikin Bakar Jallabiya Shi kanshi ya Rame din ganinsa yasa Zain ya Zura mai ido yana Jin Tahowar kwallah Cikin idanuwansa cikin Takun Rauni ya Fara Taku Zuwa gareshi Sai dai mai Cikin Tsawa Abba yace"Kul..Karka kuskura ka kara somin nan...Bana son ganinka..! Yafada Cikin Tsawa da Fushi Wanda Harta Zaina Dake kwance Ta Fara Barci Ta jita Ta tsshi afirgice Tana Raba ido Shi kuwa Zain Cak ya Tsaya Idanuwansa Sun Fara Zubda da kwallah Cikin Raunin murya yace"A...Abb...! "karka ka kara Kirana da wannan Sunan Kirani kai Tsaye da Usman Dina zai fin Dadi da naji kana Kira da Sunan Ubanka Zainullahi."Ya fada bayan ya Tarema Zain din Numfashi,Yanayin yadda yake mgana zaka Fahimci Ransa kuna yake Domin Shi kanshi Idanuwansa sun kala sun yi Ja Cikin Sagewa Gwiwa Zain yaji Kafafunsa sun kaisa kasa ya Zube Bisa Gwiwoyinsa yana kuka kuka mai Cin ran Mai Sauraro Cikin Fada Abba ke Fadin"Wama ya baka izinin Shogomin Gida...?baka ji Sakona bane..? Na sallama maka na Nace ka Tafi Chan ka zauna da karuwarka Dadironka Domin Ita ce Rayuwarku ta Dace da Juna bamu ba..! Yafada Jijiyoyin kansa na Mikewa yana Numfarfashi Da Sauri Haddir yace"Abba kayi Shuru hakanan Saboda lafiyarka.."Abba ya juya kallonsa kan Haddir yana Fadin"Kai da ka damu da lafiyata..Toh in kana so nayi Shuru kace ya Tashi ya Fitarmin Daga Gidana Tunda bada Kwabonsa aciki na Siya Gidan ba.." Jin haka yasa Zain ya Fara Rawan baki yana Fadin"Zan...Zan Fita Abba ammh sai na Rokeka Gafara..Don Allah Abba Don Annabi ba Domin Halina da Tarin Laifuka na ba..Ka yafemin Wkh Abba na Tuba bazan kara ba Na Tuba nabi Allah Abba bazan kara ba..."yake fada yana wani kuka mai Cin rai Nene da Gudu ta karisa Kusa Dashi itama ta Zube Cikin kuka Take Fadin"Don Allah kayi Hakuri Alhaji ka yafemai..Shifa Bawa ne kuma Bawa zai iya aikata Kowani irin Laifi Alhaji Don Allah karka Koresa Daga Gidanka in ka koresa ina zashi..?... Itama Ta Fada Cikin kuka Ganin Haka yasa Haddir ma ya Isa Kusa da Zain Shima ya Duka yana Fadin"Don Allah Abba kayi Hakuri..ZAIN yayi Laifi kuma ya Gane Kuskuransa Don Allah Abba ka yafemai.."Umma Dake Tsaye Kai kawai ta Kauda Tana kuka Zaina kuma Dake Kofar Dakinsu k'asa Kasa Daukanta Tayi Sai da Ta Jingina da Bango tana wani kuka mai Cin rai Lokaci Daya Da Tushe Bakinta kada Kukanta Ya Fito. Abba kuwa kai ya kauda Cikin Tsawa yace"Ya tashi ya Fice Daga Gidana nace..? Zan kira mai Jami"an Tsaro Wlh in bai Fita ba."Ganin Zain Bashi da Niyyar Tashi ne yasa kawai ya Fara Laluban wayarsa Dake Aljihun Jallabiyansa Ya Zarota Ya Fara Kokarin Kiran waya Nene da Haddir sun ma kasa Mikewa Ballatana Zain da kansa ke Duke ya Hada Hannayensa alaman Roko Idanuwansa na Zubar da kwallah . Cikin Bazata Suka Ji Abba ya Daga waya yana Fadin"Dpo....!Bai Karisa ba,ZAINA ta bayyana Afalon Tana Dingishi Lokaci Daya Tana Dafa bango Tana Fadin"A'a ABBA...DON ALLAH KADA KA KIRAMA DA'N DA KA HAIFA DA CIKINKA YAN S A.N.D.A..'Tafada Cikin Rarrabe mganarta Saboda kuka Cak Abba ya Tsaya da mganar Da yake yi ganin Zaina wanda Ya kwana Biyu bai sakata a ido ba. Haka ma Zain Cak Kukansa ya Tsaya Nene da Haddir ma suka Dago suna kallonta Haka ma Umma Ganin Abba ya Tsaya ne yasa Zaina ta isa Gabansa ta Zube Tana kuka Tana Fadin"A"a Abba Hakan bai kamata ba...Duka Abun na Cikin Gida ne Don Allah kayi Hakuri kada ka Koreshi Daga Gidanka Da jikinka Gabadaya..! Tsura mata ido Abba yayi Cikin Tsausayamata yana Ganin itace ma Abun Tsausayi Wayarsa ya kashe ya maida aljihun gaban Jallabiyansa Ya Saka Duka Hannunsa ya Tallabo kafadunta Ya saka Kuma Hannunsa Duka Biyun ya Daukemata Duka Hawayenta Yana Fadin"Naji bazan kiramai Jami"an Tsaro ba..Ammh ya Tashi ya barnin gida..! Zatayi mgana ya Hanata Da Daga mata Hannu Lokaci Daya Ya Kai kallonsa ga Zain wanda ya Kura musu Ido Shi da Zaina wacce yake jin kamar yaje ya Rumgume Zaina ya Fashe mata da kuka Ta Fahimci Nadamarsa Da Yadda yayi kewarta. Cikin Kakkausan Murya Abba ya kalli Zain yana Fadin"Wlh Tallahi Ko Saboda Cutar da wannan Marainyar Allah da kayi Zainullahi Allah bazai barka ba..Kuma nima bazan Taba yafe MAKA BA...!!! Kowa Abba yabi da kallo Wanda ya Juya yana Tafiya Yana Fadin"Aisha Ki gayama Dan'ki ya Fita yabarmin gidana..In na kara Fitowa na ganta Abun bazai mana kyau ba.." Ya Fadin haka ya Shige Dakinsa ya Banko Kofarsa,Kawai sai Zaina Ta Sulale nan ta Fashe da kuka Zuciyarta na wani Rawa Saboda ita Abba bazai yafe ma Zain ba..? Ta Shiga uku Kar tayi Sanadiyar Raba D'a Da Mahaifinsa..? Ina zata saka kanta In haka ta Faru..? Zain Da ya Fara Rarrafe kamar karamin yaro yana kuka zuwa ga Zaina sai da Taji kawai Numfashin Mutum Gabda da Ita Tana Dago Fuskarta Datayi Jabe Jabe da Majina Da Hawaye suka Hada Ido Hudu, da Zain Kowa tsayawa yayi yana Kallon Kowa..Kuma kowa da Abunda Yake Sakawaa cikin Ransa,Yana kallonta yana Zubar kwallah itama Tana kallonsa Hawayenta na Bulbulowa kamar an Bude Famfo. *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             2️⃣4️⃣ "Ita Zaina Tana Kallonsa ne Da Dukkan Zuciyarta Mai cike da Soyayyarsa Kaunarsa da Kuma Tarin Tsausayinsa da kuma yardansa Idanuwanta na Fidda Hawayen karaya da Rauni Ganin yadda ya Rame ya Fita Hayyacinsa Cikin kwana Uku Kachal. Shi kuma ZAIN yana kallonta ne Cikin Raunin Zuciya,Karaya da Ban Hakuri da kuma Soyayyah da kaunarta Hade da Tarin Tsausayinta ganin yadda ta koma Kamar wacce bata da Ishashan Jini ajikinta,Gabadaya Jikinsa Rawa yake wajen Saka Hannunsa ya Riko Nata Hannu Cikin Rawan baki Dana Murya ya Furta.. "FI...rsT....LO..ve...'Ya fada Gabadaya Jikinsa na Daukan Rawa Dukkansu sai da Zukatansu suka amsa Cikin Fitan Hayyaci da wani irin Muradi mai Girma da kuma Nenan sauki da Waraka ga Halin Dayake Ciki Taji ya afka Jikinta kawai ya Rumgumeta da wani irin karfi Wanda ba Domin Ta saka Dayan Hannunta ta Tallafe kasan Cafet din ba babu Abunda zai Hanata batayi Bayaba ya Bita sun baje atsakar Falon ba Saboda Tsabar irin Karfin Rumguman Da yayi mata. Da karfi ya matseta Har sai Da Taji bata iya Fitar da Numfashi,Kansa yake Tusawa Saman Kirjinta Lokaci Daya yana sakar mata wani marayan kuka wanda Sai ya Tada Hankalin Mai Imani Nene da Haddir kuwa Wani irin Abu Suke ji akansa Ransu na Tsausayin Duka Zain din da Zaina,Ita kuma Umma Kuka take kawai Batare ma Da tasan kukan Me take yi ita ba,ta dai sani Zain ya kasanace mafi soyuwa acikin Ranta Tun yana karaminsa Bata iya Juran kukansa Sai dai ta Boye ko kuma ta kauda kai Saboda Nene. Jin yadda yake kukan ne yasa Raunin Zaina ya kara Bayyana Cikin Wani irin azama ta Dago Hannunta zata Rumgumeshi,Sai kuma ta Fasa Domin Alokacin Hotunan Zain da Dina ne Cikin yanayin Da ita kadai ta sanshi yake Gilma mata Gefe guda kuma Tana Tuno mganarsa na Yarda da cewa Cikin Jikin Dina nashi ne da Sauran mganganu,Gabadaya Jikinta ya Fara karkarwa Cikin Sarewa Da Duk wata yarda da Tsausayi kawai Ta Janye Hannunta Lokaci Daya ta Fara ja da baya Tana Kokarim kwace Jikinta,Ganin Tana Mutsu mutsun kwace kanta ne yasa ya Dago Da kansa Fuskarsa Duk Ta baci Da hawaye yana kallonta Itama Shi Take kallo Cikin mamaki yaga tana ja da baya Hannu ya mika zai Rikota da Sauri Ta kara matsawa Baki ya Bude yana Fadin"Firstlove...! Kai ta girgiza mai Tana Fitar da kwallah,Sai kuma ta Fashe da kuka kawai Tana Girgiza mai kai tama kasa Mgana Zain ya Duka Hannu Bibbiyu ya Riko Kafar zaina yana kuka yana Fadin"Firstlove...Matata Farincikina...Halimatu Abdullahi Gada..My Firstlove my World,Kece Rayuwata Zaina In baaki bazan iya Rayuwa ba..Naji na yarda naci amanar Soyayyarmu naci Amanar yardan Da kikamin ki Taimakeni ko ki kara bani Dama ta Karshe Don Allah..Ni zainullahi Abubakar Saulawa nayi Miki Alkawarin bazan kara Dabi"ata ta neman mata ba,ammh Plz Don"t Leave me i Can"t do Without u..! Ya karishe Fada yana Kife kansa Jikin Kafanta yana kuka,Itama kukan Take Lokacin Har Jikinta ya Fara wani irin Tsuma Umma ce Ta Lura da haka da Sauri Ta Share Hawayenta ta isa Garesu Cikin Fushi ta saka Hannu ta Fizgo Zaina ta Mikar da ita tsaye wanda yasa Zain ya Dago Idanuwansa Jajir yana Kallonta Cikin kaifin Idanuwan Uwa da Danta Take kallonsa Shima haka Cikin Karaya yace"Ummmaa..! Kai ta kauda Kafin Ta Kama Hannun Zaina kawai ta Nufi Hanyar dakinta da ita Cikin Murya wacce ba Sauti yace"Don Allah Umma ki yafemin...Ki yafemin ki bani Matata itace Rayuwata.."Cak Umma ta Tsaya sai kuma kawai ta Cigaba da Tafiya Har gadon Ta kai Zaina ta Zaunar da ita ganin Tana Neman Shidewa ne Saboda Kuka yasa Ta Zura mata ido Cikin Takaichinta Tana Fadin"Ko Na barki zaki Bishi ne..? Da Sauri Ta Girgiza kai Cikim Kuka kwafa Umma Tayi Tana Fadin"Toh ki kiyayeni Da min wannan kukan mara amfani..."Daga Haka kawai ta Fice Daga Dakin Harda Turo mata Kofa kan gado kawai Zaina ta Malale tana Sakin kukanta Zuciyarta ta Kasu kashi Biyu ne na Farko Kaunar Zain da Tsausayinsa na Biyu kuma Kishinsa da kuma Bakinciki Wanda yaki barinta Ta Kalleshi Lokacin Dayake kuka yana Rokonta Gafara. Umma kuwa Falon Ta koma ta Iske Nene Rumgume da Zain yana kuka Tana Lallashinsa Mirmishi Takaichi Tayi kafin tace"Nene ki gayama D'anki...Ba yata bace Rayuwarsa wannan Dadarion nasa Uwar Dansa ko yarsa itace Rayuwarsa Ita zai je ya Dauko tamai Duk Abunda Mata kema mijinta Dama ai sun saba.."Daga Haka kawai ta kada kai Zuwa Dakinta Zuciyarta kamar Tayi Bindiga in ta Tuna da Abun kunyar da zain ya Jawo musu. Zain ya gama Sarewa da almarin Umma cikin Karaya da Zubar kwallah ya Dago yana kallon Nene Lokaci Daya yana Fadin"Nene Umma ta Tsane ne kamar yadda Abba ya Tsaneni.."Kansa ta Shafa Tana Fadin"A"a kadaina Fadin Haka ka Tabajin Inda Uwa ta Tsani Abunda Ta Haifa da Cikinta?ko kuma Uban daya Tsani Dan sa wanda ya kasance mafi Soyuwa Garesa..? Da Sauri Zain yace"Nene yana Faruwa..Tun Ballatana Yaron in ya kasance yayi watsi da Tarbiyan da suka bashi da yardansu..."Yafada Yana Runtse Idanuwansa Cikin Kunar Zuciya Kansa Nene Ta Shafa Cikin Son Kwantar mai da Hankali tace"Ko Daya..Koda Ya kasance Haka yarona zasu mai afuwa Domin Shima Dan adam ne wanda Baya Wuce Kuskuransa..Basu Tsaneka ba Bacin Rai zai sakesu Lokaci Kadan Insha Allahu kaji ko..? Kura mata ido Cikin Samun Salama da kalamanta yace"Zasu yafemin Nene..? Kema zaki iya yafemin Abunda na aikata gareku naja muku Abun kunya Nene ni kaina ina Jin kunyar kaina da Abunda na aikata ."Yafada yana kokarin Durkusa mata da Sauri ta Dagoshi Tana Fadin"Basai ka Dukamin ba Ni Dama uwace mai afuwa gareka ammh kuma mai Kokarin Doraka hanyar gyara..?Meyasa ka zabi Yin Tarayyah da matar da ba taka ba yarona..? Wannan Dabi"ar Ba ita na Koya maka Tun kana karami na Karantar dakai Kallonka iya Halas Dinka ne ba Haram ba yarona.."Cikin Nadama ya Riko Duka Hannuwan Nene yana Fadin"Hakane Nene Wlh kina gayamin Ammh ban yi aiki Dashi ba..Da ace nabi mganarki da Abunda Addinina ya Hanene da Ba haka ba ammh sai na Bi Son Zuciyata Nene..Wlh Tallahi Neneta Daga baya nayi Nadama naso ya kiceta acikin Rayuwa sai Abun ya gagara na Rasa Dalilin wannan Bala"in.."Yafada yana Sakin Numfashin Nadama da Danasani.. Shuru Nene Tayi Tana kallonsa Tana wani Tunani aranta kafin  tace"Shikenan kadaina Kuka kuma ka Daina Damuwa kajiko..Ina Tare dakai Har Abada yarona kuma bazan Runtsa ba Sai naga komai ya Daidaita Karika Cin Abinci kaji..?kaci Ferfesun dana aika maka Dashi..!? Kai ya Girgizamata alaman A"a Cikin So da kauna ta Shafa Kumatunsa Tana Fadin"In ka koma Gida kaci kaji ko..? Ina wayarka..? Cikin Kasala yace"Tana gida Tun Ranar dana Kasheta ban kara kunnata ba.."Nene tace"Ka kunna wayarka Don in Rika Jin Lafiyarka kar ka kara Zuwa Tunda yace bayaso kaga bai da lafiya kada Hakan ya jawomai Wata matsala Zuwa gaba in komai ya Daidaita da kansa zai Kiraka kaji ko..? Cikin Kura mata ido yace"Nene Matata fa...? Umma ta Hanani ganin Matata..?cikin son kwantar mai da Hankali Nene tace"Itama din zata Dawo kaji ko..? Umma ta isa ta Rabaka da Halima ne..? Da sauri yace"Ko Mutuwa ce tazo Sai dai Ta Daukemu Tare In ba haka ko Ita bazan Taba bari Ta Daukemin Rayuwata ba Ta tafi ta barni ba.." Ya karishe Fada Cikin son Tabbatar da mganarsa ba Nene kadai ba Hatta Haddir Dake gefe sai da ya Dara Cikin Tsausayama Zain domin baya Tunanin Umma zata maida mai Halima sai dai indan Alhaji Tsoho ne ya tsawatar mata Abba ne kuma awannan karon bazai goyi bayan Dan nashi ba. Cikin Dariya Nene tace"Toh kagani..? Zata baka Matarka ko koma Gidanku kuci gaba da zaman Auranku.."Da sauri yace"Insha Allahu Neneta..Shiyasa nake matukar Kaunarki Uwata Kinfi kowa Fahimtata.."Yafada yana Kissing Din Hannunta kansa ta Shafa Tana Fadin"Allah yayi maka albarka...Ka rika addu"a kaji ko Domin Tsari Daga magautan Duniya kaji ko Yarona..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Insha Allahu Neneta..Ammh zan Dinga zuwa koda Abba zai koreni ne..'kai Nene ta gyada mai kafin tace"Ba yanzu ba...kabari zuwa Jibi Haka Lokacin yadan Sauko kagane..! Jinjina mata kai yayi kafin yace"Shikenan Neneta..Zamu Tafi Chan Gidan Alhaji Tsoho.." Cikin So da kauna Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"Muje na Rakaku Har waje...Hadiru muje.."Daga haka suka Rankaya Zuwa Haraban Gidan sai Lokacin Umma ta Juya zuwa Cikin Dakinta Daga Jikin Kofarta Inda Ta makale Tana Hangen Abunda ke wakana afalo Kwalla Take Sharewa Tana Sakin Mirmishi Cikin Takaichi tace"Maraba dake Salihar Uwa Nene...Nayi alkawarin Zan tsaya a Uwar Halima kadai Shiyasa bazan Taba bari wani ya Fahimci Raunina a kan Zainullahi ba..! Tafada Tana Ta Sharan kwallah Cikin Rauni da Sarewa Gefe Daya kuma Tana jin wani karfin Gwiwa kan Hukuncin Data yanke na Raba Auran Zain da Zaina wanda Har Cikin Zuciyarta Take jin Kunar Abun ammh bata da yarda Zatayi Ko don Zain yake Danta bai kamata ta bari Zaina ta kara Cutuwa ba Itama Ya' take gareta Shakikiya wacce ta sami asali Daga kaunar Datake ma Mahaifiyarta Maryama. Nene Bata Dawo cikin Gida ba Har Sai da Taga Tashin Motarsu Zain da Fitarsu Daga Gidan Tana Shiga Falon suka Ci karo da Umma Wacce ta Fito Daga Dakinta kallon Kallo sukama juna kafin Umma Takauda kai Ganin Nene ta kura mata Ido Dakin Zaina Ta Shige gabanta na Faduwa Kada Nenen ta Fahimci Tayi kuka Mirmishin Takaichi Nene ta saki kafin ta kada kai Zuwa Shashen Abba Domin Taga Halin Dayake Ciki. Su Haddir kuwa suna Zuwa Gidan Alhaji Tsoho suka Iskeshi yau a haraban Gidan bayan an sakamai katuwar Darduma ammh Shi yana saman Kujeransa ne saboda zaman kasan zai mai Wahala ne,Jalal ne agefesa yana ta mai Gwarancinsa Shi kuma Alhaji Tsoho Muwadda Malik ne ahannunsa yana Dubawa Tunda Motarsu Ta Shigo Haraban Gidan ya Dago Daga karatun Dayake yana Kallonsu Har suka Fito Daga Motan Shi da Haddir suka Jero Zuwa Garesa Bakinsa ya Fara Motsi wajen Neman musu Tsari Daga Mutum da aljan Domin har yau har Gobe Haddir da Zainullahi Sune Sanyin Idanuwansa Soyayyar Iyayansu Gabadaya Ta Koma kansu. Har suka kariso yana Kallonsu Cikin karantar yanayin kowanensu Ramar da Zain yayi tafi komai Dagamai Hankali Jalal ne ya watsar da Tab din Hannunsa ya isa garesu ya Rumgumesu yana musu oyoyo Zain ya Riko Hannunsa yana Shafa kansa hakama Haddir har Zuwa gaban Alhaji Tsoho Gabansa suka Gurfana kamar masu Neman Gafara Zain kuwa Rauninsa ya bayyana yana ji Haddir na gaida Alhaji Tsohon ya amsa Rabin Hankalinsa na Wajen Zain wanda yayi Shuru ya Dukar da kansa kasa Yana Jin Kunyar Alhaji Tsoho Shiyasa ya kasa Dagowa su Hada Ido.. Cikin Dattako Alhaji Tsoho yace"Zainulallahi...! Jin ya kira Sunansa ya sa ya Dago Kansa yana Kallonsa kwallah suka Tarumai Waje Daya Cikin Mamaki Alhaji Tsoho ke Fadin"Subnallah Ciwon Har yakai Haka ne..?kaga yadda ka Rame ka lalace Cikin kwana uku Kachal.."Jin haka yasa kawai ya Fara Rarrafawa Zuwa Kusa da Alhaji Tsoho ya Rike kafansa Cikin Rawan murya kamar zai Fashe da kuka yace"Ka...ya...fe...Min Alhaji Tsoho..Ina jin kunyar Hada ido Dakai.. ka Yafemin batamaka Sunan Zuru"a Danayi na Tuba nabi Allah kuma Nayi alkawarin Bazan kara Sha"awa ko Jin ina son aikata Zina ba Insha Allahu.."Yafada Lokaci Daya yana Fashewa da kuka Saman Cinyar Alhaji Tsoho ya yada Kansa yana Rera kukansa kamar Wani karamin yaro Cikin Kukan ne yake Fadin"Kowa ya Daina Sona saboda Zunubai na..Abba na Fushi Dani naje gidansa ya Koreni Umma ma Taki Saurarana,Ta kuma Hanani mgana da matata Nene ce kadai Mai Sona itace kadai ta iya min afuwa da Tarin Laifukana Don Allah Alhaji Tsoho kada kaima ka Juyama Rokona Baya in kaki yafemin bansan Kuma wa zan kama ba.." Yafada Cikin Karayan Murya Shuru Alhaji Tsoho yayi Zuciyarsa na Sauka a hankali Ahankali Littafin Hannunsa ya Mikama Haddir Shi kuma da Sauri ya saka Hannu Biyu ya karba,Kana Alhaji Tsoho ya mika Hannunsa saman kan Zain ya Dafa  Cikin Muryan Tsufa yace"Bar wannan kukan Zainullahi...Bar wannan kukan..Domin bai kamaci Namiji kamar ka dashi ba..Tashi bari kaji ko" Yafada Cikin Sanyin Murya Cikin Salama da Yayewar Kunci Zain ya Tashi Daga Kafan Alhaji Tsoho yana Fadin'Ka yafemin..? Alhaji Tsoho yace"Ni daman bani kayi ma Laifi ba Zainullahi Ubangijinka kayi ma Laifi kuma Tunda kace kayi Taubatun nasuha...Shikenan Allah ya yafemana Gabadaya Allah kuma ya Tsaremu Da Imaninmu ya Rabamu Tabewa duniya da Lahira.."Cikin Farimcikin Zain da Haddir suke amsawa da Ameen Karo na Farko da Zain yaji Wani Sauki acikin Zuciyarsa Tun Faruwar lamarin. Cikin Son Sauke wata Salaman Zain ya kalli Alhaji Tsoho yana Fadin"Ina ta Rokon Allah Gafara Kan Zunubai na baya..Shin Allah zai Gafartamin...? Alhaji Tsoho yace"Sosai ma ai Allah Gafurun Rahimun ne Zainullahi Komai Girman Laifinka awannan Duniyan Allah mai Rahma ne kuma mai Jinka Kaga dai Girman Laifin Shirka ko..? Toh Shima Allah na yafewa matukar mutum yayi Tuban Gaskiya kuma ya Roki Allah Gafara,zai gafarmaka Saboda Haka Ka Cigaba da Istigifari Allah mai yawan karban Tuba ne Allah ya yafe mana.." Haddir da Zain suka amsa da Ameen wanda ya Zarce da Fadin'Allah na Tuba...Na Tuba.Astagafurulah..Astagafurullah.."Yake ta Fada Alhaji Tsoho na kallonaa yana gyada kai kafin Ya cigaba da Fadin"Shiyasa ako da yaushe ina gaya muku kuma zab kara Gaya muku..Komai kuke Arayuwar wannan kada ku bar Tafarkin Allah Domin Wanda ya Bijerema Allah zai ga samakon Haka Tun a Duniya..Zina Babban Zunubi ne da Allah yace Kada mu kusanceta Domin Ita Zina abace mai kawa mai kuma Dadi,Kusanta ta na Rage kima,Da rage Daraja Rashin kwanciyar Hankali Tana saka Rashin kunya tana saka Tabarbarewan Rayuwa da arzikima Gabadaya Kaga kenan Bata da wani amfani Ga Rashin Kwanciyar Hankali kullum Shedan na kawata mana ita ammh mai Kusantar Zina Bashi da wani kwanciyar Hankali Gwara kada mu Kusanceta Ma"ana mu kauce ma zama Cikin Shedanun matan da zasu Ribacemu aikata ta Allah yama na Tsari.." Dukkansu Jikinsu yayi sanyi Barin ma Zain wanda yayi Kasake yana Sauraran Alhaji Taoho kafin ya amsa da Ameen Cikin Rauni yace"in kagaya maka wata gaskiyata Alhaji Tsoho Zaka yarda dani..? Cikin Dattako Alhaji Tsoho yace"Saboda me bazan yarda dakai ba Zainullahi Ai har yau har gobe akwai yarda tsakanina Dakai fadi mganarka karka Damu..' Da Sauri yace"Wlh ban Taba Jin Natsuwar Zuciyata wajen aikata wannan Zunubin ba Alhaji Tsoho..Tun bayan Barinmu London Nadai na Neman kowacce mace Alhaji Tsoho ina Son Zaina Har cikin Raina ba kuma na Jin Dadin cin Amanarta aboye..Sai dai Bayan Dawowarmu gida Naji Komai ya Fita akaina ammmh sai me Sai na rika jin In ban Kusanci mace ba kamar zan Mutu macen ma bakowa ba Sai Dina Ita kadai nake jin im ban je gareta ba Zan iya Mutuwa..ammh Wlh Tallahi Na Daina na Tuba har Cikin Zuciyata.." Kura masa Ido kawai Alhaji Tsoho yayi yana kallonsa acikin Ransa kuma yana Fadin Haba Biri yayi kama da Mutum Koda Hali yasa Jikansa ya gamu da Shedancin mace Cikin Muryan Tsufa yace"Na yarda Dakai...Hakan yana Faruwa ne in muka Manta da addinmu muka Shige Cikin wadanda ke da Bambamcin al"adu da addinmu da kuma Cakuduwa Cikin Mata Wanda sam bai dace ba Shiyasa wani Lokacin Tsantseni da kamun kai Ba iya ga Mace ba harga Namiji ma yana da amfani..! Zain yace"Hakane Tabbas Alhaji Tsoho..Nima Harda zama Cikinsu da kuma Biyema Abokan Karatuna wadanda ba addinmu Daya ba.."Kai kawai Alhaji Tsoho ya gyada yana Fadin"Allah ya tsare mu.."Suka amsa da Ameen kafin ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru ku samo Wani Likita wanda zai maye Gurbin ita Dinar.." Kai Haddir ya gyada kafin yace"Ok..Shikenan.."Da Sauri Zain yace"Don Allah ina neman Wata alfarma Alhaji Tsoho..? Yana Kallonsa yace "Ina Jinka."Kansa ya maida kasa kafin yace"Ina so Don Allah ka bada izinin azubar da Cikin nan.."Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A'"a badani za"ayi wannan Danyan aikin ba..Na Farko ance Cikin Kuskure ne Cikin ya Shiga shii kashe Rai fa..? Shi ai da gangan ne...Zata Dawo Gidanku ta Haifeshi Daganan Ta tsarkama sai a Daura muku Aure indai Ina da Rai ko bani Dashi zan bar ma Ubanninku Wasiyar haka.." Cikin Wani yanayi Zain yace"Toh Ta zauna Gidansu ta Haifa mana Alhaji Tsoho.."Dakuwa ya aika mai Dashi kafin yace"Gidan ku Zata Haifeshi Duk wa yajawo in ba kai ba..?kuma Gidan Usmana nace ba Gidanka ba.."Cikin kunyar kansa yace"Ni bana ko Son ganinta ne Alhaji Tsoho..". Cikin Tura Haushi yace mai"Allah yanzu kuma.? Dawa ya kai ka kake Jure kallonta Har aka kawo Yanzu..? Jin Alhaji Tsoho yace hakane yasa ya Runtse Ido yana Fadin"Kadda ra ce da Jarabawa..ammh Allah ne Shaidata Firstlove ce Kadai macen Da nake so kuma itace Rabin Rayuwata Gabadaya.."Hmm kawai Alhaji Tsoho yace Wanda Yasa Sai da Haddir ya Murmusa nan fa Alhaji Tsoho ya Cigaba da Musu Nasiha yana Nuna musu Illar kusantan Zina ba Zain kadai Da tayi ma Illah ma Hatta Haddir yaga illanta kuma ya Tsorata ma da kallon Abunda ba Halas Dinsa ba. Sun Dade nan wajensa kafin su Dunguma Zuwa Cikin Gida suka barsa Shi kadai ya Cigaba da karatunsa,Dama Jalal ne kuma Tun Dazu ya Ruga Cikin Gida,Acikin Gidan Itama Hajiya Mama zain ya Duka yana bata Hakuri ta Dagoshi ta Sharemai Hawaye tace bakomai Ya nemi Gafaran Allah,Sun dan Jima agidan ganin Zain din yadan saki Jikinsa,suna ta Hira da Zareena da Hajiya mama sai ga Tabawa Itama akayi da ita kafin suyi musu sallama suka Tafi Sun zo sun yi ma Alhaji Tsoho sallama ne ya Dago kai yana kallon Zain kafin yace"Gobe ka Shirya ka koma Bakin aikinka..Ka Cire damuwa Insha Allah bayan Bikin Hamdiya zan Daidaita komai.." Daga haka suka mai sallama suka Tafi Daganan Direct asibiti Zain yace su wuce kaawai Domin yana Jin yadan samu Salama kaso mafi Kadan,cikin Fargabansa ya Ragu acikin asibitin ma sai mamakin Ramar Zain ake nan dai yace bai da lafiya Daman Zain ya Shigar da Korafin Rashin Lafiyar Zain din Office din Haddir ya zauna bai iya Duba patient ko Daya ba sai Zuwa Gobe sai dai yana Zaune Haddir din na Duba maraasa Lafiyar sallah kadai ke Tadasu sai Xuwa yammah suka bar Cikin asibitin Zuwa Gidan Zain din Bayan sun Tsaya Bisa Hanya sunyi sallar mangariba. Ferfesun da Nene ta aiko da Zain Dashi Shi suka ci suka Koshi..Haddir yaja wayarsa yana Amfani da ita Shima Zain din Wayar nashi ya Dauko yayi ta ganin Sakonin mutane na Jinsa Shuru Sakon da yafi bata mai rai Shine sakon Dina Tana Ce mai wai Unborn yahanata Barci Saboda Bakinciki bai san sadda ya saki Katon Tsaki ba wanda sai da Haddir ya Dago yana kallonsa bai dai Tambayesa ba ganin ya Tashi yana Sakin Tsaki zuwa Cikin Bedroom dinsu ya Bishi da kallo kawai yana Fatan komai ya Daidaita kamar yadda Abun ya Fara Daga yau. ***** *Bayan Sati Daya* Bayan Sati da Daya da Faruwar Lamarin daya wargaza Farincikin Duka iyalan Dr.Saulawa Zuwa Lokacin Duk Wanda ya kamata yaji Abunda ya Faru ya Riga yaji. Bangaran Dina kuwa Tuni Umminta Maimuna ta iso Daga Sudan Wanda Kwamishina da kansa ya zaunar da ita ya gayamata Komai kuka ta saka Wiwi kuma ta bashi Duka Laifi Domin Lokacin sunyi Sunyi ya basu Rikon Dina yaki gashi ga Abunda ya Faru Abu Daya ya sanyayamata rai karban Cikin da Iyayen zain sukayi da kuma Komawarta gabansu ta Haihu ayi musu aure lalle ta Shaida Gidan Gidan Dattako ne da karaminci Ammh Tayi ma Dinar Zaga zaga kamaar ta Daketa Daga Karshenta ta kara Dorama Hajiya Batula laifin Rashin Rike amanar Dinar ita kuma tace Daga Mahaifinta ne ya Riga ya sakar mata komai Abunda Taga Dama Takeyi. Allah ya Taimaki Dinar Cikin nata bamai Laulayi ba ne Amai ba koda yaushe take yi ba sai dai yana Sakata Cin Abinci Sosai da Cin kwalama ta Kara zama wata Baturiya Fatar ta na Sheke Abunda ke Daurema Hajiya Barula Kai Ganin Ko Damuwa Dina Batayi ba na irin Mace Tayi Cikin Shege ta Damu a'a ita kam Ma wani Farinciki Take da Tattalin Cikin kamar na Sunna Ita kanta Ummi Maimun din Abunda na Dina Tsoro ya koma Bata Domin ko Fargaban nan Bata Dashi Harkan gabanta kadai Takeyi ko ajikinta. Kwamishina ya Roki Ummi Maimun kan karta koma ta bari Ta Raka Dina chan Bauchi Su Tafi Tare Da Hajiya Batula Jin haka yasa ta Dakata da Tafiya ammh Tayi Shuru Da bakinta bata Fadama Kowa Daga Chan Sudan Abunda ke Faruwa ba ko Bakomai Dina kamar yata gareta Tunda Sara kanwa take wajenta sai ta koma ta samu Mahaifiyarsu Sameena ta Fadamata Tunda bai kamata ita aboye mata ba,Hajiya Batula ita ta Taimaka mata suka Hadama Dina Duka kayanta Waje Daya Kan sun Tsaida Ranar Lahadi Ranar da zasu maida ita Dinar Bauchi Wajen Alhaji Tsoho kamar yadda aka Tsara komai. Bangaran Zakiya kuwa sun kara Dinkewa da Dr.Imran ta sakamar Jiki ganin Gayen yasan Hannunshi kuma yana sakarmata Kudi Shashancinta kadai Take acikin gari ba Ruwanta Suna waya da Dina Duk Abunda ake ciki tana sane,Dr.Imran yasio yaji wanda yayi ma Dina Ciki da kuma Abunda yakai mganar Gidansu Zain sai Zakiya tayi wasa da Hamkalinshi kan cewa a matsayin Alhaji Tsohi na ma mallakin asibitin yana da Hakki Ya bincikin Abunda ke Faruwa da Ma"akatansa da Haka Ta Rufe Bakinsa Domin Har Abada Tana Mutumta Sirrin Dina kamar yadda Itama Take Mutunta Nata,Zakiya ko Tana so Ta Tuban ma Allah sai taji ta Kasa ta saba da Harkan Bariki da Harka da maza da kuma kama Manya kudade Bata iya bari kuma dan albashinta Tana ganin bazai Isheta Ta Famtama ma Rayuwarta ba,infact ma Tana ganin Bata samu irin Namijin Daya Dace da Rayuwarta ba ammh Duk Ranar data samu zata bar Rayuwar Bariki Tayi Aure kodon Faratama Babanta rai wanda kullum Taje gida mganar kenan Zakiya kiyi aure kibar wannan Rayuwa bata dace Dake ba kuma bazata haifar miki da D'a mai ido.. Sai tace"Zan yi Baba...Ammh sai na gama Tsayuwa da kafafuna bana son naje na Dawomaka irin Auran su Sahura ne..! ****** Ta Bangaran Zain an samu Cigaba Domin ya koma Bakin aikinsa aikin ya Fara Daukemao Hankali Daga Damuwarsa ammh fa Duk ya Sauya ya Rame ya zama wani Silent kamar ba shi ba Dina kuma Tuni Wata Dr polina ta maye Gurbinta,An cigaba da bama asibitin Gudummuwa kamar yadda ya kamata Kuma Kowa ya Tambayi Dina sai asanar dashi Ta ijiye aiki ne Da Ra"ayin kanta. Bangaran Abba ma ta Sauya Tunda yaji sauki Shima ya koma aikinsa sai dai game da Tsakaninsa da zain Ta na nan Jiya iyau,In Zain yaje gidan sai dai in yana Office ne ranar kuwa Daya Dawo ya ganshi ba zaman Lafiya Nene ce kadai ke kulashi sai Zainab dasu Saudart Zareena Bata nan Mijinta yazo ya Dauketa sun Tafi Katsina Umma da Abba Ko ya gaishesu basu amsa mai Zaina kuwa Bayan Ranar Ya kara Cin sa"a Umma na Kitchen ya Fada Dakin Tunda indai yazo bata bari yaje inda Take ya sameta kan gado kwance ya Bita ya kwanta Kusa da ita ya Rumgumeta yana Ta bata Hakuri ammh Zaina taki mgana sai kuka Ganin Taki yin Shuru ne yassa Ya Hade bakinsu Waje Daya Duk Kokarinta na ya saketa yaki Saboda yayi mata Riko na Sosai Dole Jikinta ya saki ta koma ta kwanta Tana kallonsa yana yadda yake so da Bakinta. Umma ce Ta shigo ta gansu Cikin Wannan Hali Ranar yaga Tashin Hankali Da Fushin Umma wanda bai Taba gani ba Tsawa Ta Dakamai Abunda yasa ya Gano ta Shigo Dakin kenan kuka kawai ta Fashe Dashi ludayin Miyan Dake Hannunta ta kwalamai agadon Baya Dama Tana Miyane Zuciyarta Ta bata Wani Abu ganin ta Fito bata ganshi a Falo ba kamar yadda yake zama kamar wani maraya gabanta na Faduwa ta Nufi Dakin sai kuma ta ganshi ya kwakwume mata y"a Cikin Hargagi Ta Rakashi Falon da Ludayin Tana Bugamai Tana hadin"Kasheta zakayi..? Na samu Ta Daina kuka Tana samun Cin Abincin Shine zaka zo ka maidata Gidan Jiya ko..?ka Rumgumeta Ubanka zatamaka..?ina Dadironka ko nace karuwarka kaje wajenta mana Wlh kar na kara ganinka kusa da yata Domin ita mai Tsafta ce ba Kazama ba irinka.."Tana gama Fadin haka ta koma Cikin Dakin Fuu Zain ya Bita da kallo yana Sosa inda ta Dakeshi da Ludayi Cikin wani yanayi yace"Samun Kamar Uwata aduniyanan sai An Tona..Mai Maida ya"yan wasu nata..My Mommh is Differnt and Special..' Ficewa Yayi Daga Gidan Batare ma Da yayi ma Nene sallama ba Kada Abba yazo ya ganshi ya jawo wani Matsala Umma kuwa Daki ta koma Wajen zaina ta sameta ta Takure kan gado Tana kuka Lebenta na mata wani Zugin Tsotsan zain yayi musu Gefe Daya kuma Tsausayinsa da Sonsa ya mamayeta Domin ayanayin yadda ya kamkameta yana Tsotsan bakinta na Tsabar yayi kewarta ne,Tunda Tanaji Jikinsa na Bari nan da nan wata Zuciya tace"Ke zaina dawo Cikin Hayyacinki kin manta Har ciki yayi wata ma karewarta..! Kika sani ko Daga wajenta yake..!. Tuna haka ne yasa ta kara Sautin Kukanta Umma na Shigowa itama Batayi Wata wata ta maka mata Ludayin Miyan Abayanta Tana Fadin"Rufemin Baki sakarya kawai Shashasha...! Gum Zaina Tayi da bakinta Tana Sosa inda Umma ta Daketa Cikin Hararanta Tace ganin Tana Kallonta"bar kallo na da wadanan kwalalan Idanuwan naki kafin naci miki Mutumci anan wajen..Ke sakaryace ace bansani ba ina nan ina miki yaki ki samu yancinki ammh baki sani ba ko..? Kina manne mai ko..! Tafi Chan wawiya karya yake da yana sonki da ganin Darajanki bazai barki kina Matarsa yaje yayi ma Wata Yar iska Karuwa ciki ba Harda bayan ya maidake sauna Daga baya yazo yana kwakwumarki.." Cikin kuka Zaina tace"Allah Umma bani na Kirashi ba ina kwance na naga ya shigo.."Cikin Bacin rai Umma tace"Ja chan meyasa baki kurman mai ihu ki kirani nazo naci mai Mutumci ba.? Wato kinyi mukus da bakinki kema kina so badomin Allah ya kawoni ba Kin kwakumeshi Don Ubanki har kin manta da Bakincikin daya Kunsa miki ko..!? Ita Zaina bata kara mgana ba Har Umma Ta gama Fadanta ta Fice Ta Bita da kallo Bakincikinta Daya yadda Umma Taga Laifinta alhalin ita bata ma san dashi ba Ganinsa kawai Tayi ya hau gado Ya zatayi Dashi..?kwalla kawai take Sharewa Ranar wuni Umma Tayi Tana Jin Haushinta Tayi banza da ita Ko irin Lallabanta Datake taci abinci yau din ko kallo Ta dai kawo mata abinci ta Dunkure mata nan Da taga Tana kuka baki ta Rike Tana Fadin"Ikon Allah don na miki Fada yasa kike kuka..? Yi hakuri In yazo Gobe ki bisa ku tafi..Ni nawa ido ne.." Jin tace haka ne yasa ta Marairaice Tana Fadin"Kiyi hakuri Umma kina Fushi Dani.."Kallonta batayi ta Fice ammh Ta Dan saki Fuskarta Shi ya sa ma Zaina taci Abinci Sosai ammh ko Rabi bata ci ba sai amai haka take fama kuma taki yarda Aje asibiti ita Kuma Umma bata son bata mata Rai Shiyaasa ta kyaleta. ***** Washegari ta kama asabar ne Tun safe sai ga Laila kawar Zaina ta Dira gidan tace Tunda ta Koma Gida Tayi ta Kiran Layin Zaina Tana Ringing ba"a Dagawa Kwana Biyu Daga Biyu kuma sai takejin wayar tana Kashe Dama zata Fadamata ne sun Fara Test tun Ranar Monday,Ganin Shuru Shuru ne yasa Taje chan Gidan Zainar megadi ya Tabbatar mata da Bata nan wajen Sati Daya Shiyasa ta yanke Shawaran zuwa Nan Domin tasan bata wuce Wajem Umma... Bayanin Da Laila ta korama Umma kenan ita kuma Umma sai ta sanar da Laila cewa wayar Zainar tana Cikin Jakarta sakamakon bata Da lafiya Shiyasa ba wanda yabi ta kan wayar,Dakin zainar ta Nuna mata tace ta Shiga tana Ciki. Cikin alhini da Tsausayin Halin Da zaina ke Ciki ta taka Zuwa Cikin Dakin acikin Ranta Dama Tana Tunanin wannan Abunda ya Faru sai ya Taba Rayuwar Halima Fiye data kowa acikin lamarin. *Janafty..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*             2️⃣5️⃣ "Koda Laila ta shiga Dakin Bata iske Zaina a ciki ba Ammh Taji kamar Motsi Daga kofar Toilet sai Aranta Tayi Tunanin ta Shiga Tiolet ne. Gefen Gado ta samu Waje ta zauna Tana Bin Dakin da kallo bata jima ba sai ga Zaina ta Bude kofar Tiolet ta Fito Daure da Towel,Ido Hudu suka Hada da Laila Dake zaune Tana kallon Kofar Toilet Gaban Laila ne ya Fadi Ta zaro Ido Tana kallon Zaina ganin yadda tayi Uban Rama Idanu Duk sun Zurma sai karan Hanci gashi Tayi wani Fayau da ita kamar mara jini ajiki. Cikin Mamaki da Al"ajabi Tare da Tsausayi Laila Ta bude baki tace"Halima...!!! Ta karishe Fada Cikin Muryan Amoh da Sauti. Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Zaina ta saki kafin ta Fara Takowa Zuwa Cikin Dakin Wardrope ta Bude ta Dauko Wata Doguwar Riga Baka Cikin kayan Zainab ne Domin Kayanta Duk Suna Lowcost Umma tace zata aika Zainab ta kwaso mata kila Ta manta ne koda yake Zainab din bata zama Saboda makaranta. Juyowa Tayi Dauke da Rigan a Hannunta Ta kalli Laila Dake Binta Da kallo Ido Cikin Ido Tace"Na"am Laila...! Karo na Farko da Zaina Tayi mgana da wani ba Cikin kuka ba Tun bayan Faruwar al"amarin. Laila Tayi Tsuru kawai Tana kallonta Imani da Tsron Rayuwa ya kara kamata Har zaina ta koma Tiolet Ta Zura Doguwar Rigar Data Shiga Dashi ajikinta sai da ma ta Fito Laila Ta kara ganin Ramarta Zaina Tana Bula Bula Cikin Bakar Doguwar Riga Kirar Armani Sai da Taje gaban Madubi Ta Dauko Man Vaseline kana Ta zo Ta zauna Kusa da Laila Tana kallonta Lokaci Daya Tana Fadin"Yanzu kike Tafe Laila..? Laila Ta saki Gauron Numfashi kafin tace"Halima Ciwon da kikayi Mai Tsawo ne da kika koma Haka..? Kinga yadda kika Rame kika Lalace kamar ba ke ba..? Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Zaina Tayi kanta na kasa Tana Shafa ma kafafunta mai tace"Eh nayi Cuta mana Laila...Cutar Gubar Da Namiji ne ta maidani Haka wacce kikayi ta Nuna min Illar Shanta nakiji sai da nashata Tamin yawa Gashi yanzu Tana min Illah Laila..! Ta karishe Fada kwallah Suna Cika mata kwarmin Ido Har sun Fara Zuba Cikin sanyi Jiki Laila Ta Dafa Kafadarta Tana Fadin"Na sani Halima ammh ai hakuri ma Mgani ne..? Tunda Abun nan ya Riga ya Faru bai kamata ki zauna kina Kokarin kashe kanki ba Tun Ranar da na muka Rabu ban samu Natsuwa ba Halima Tsausayinki ya Cikamin Zuciyata Tuna irin Rauniki game da Mijinki Ina ta addu"a Afili a Boye Allah ya baki Hakuri Da Dangana kada wannan Lamarin ya Shafi Rayuwarka Nayi ta kiran Wayarki Baki Dagawa Daga Karshe kuma Tana kashe,Naso nazo Sai kuma nake jin nauyi kada ace Jin Kwakwaf ya kara kawoni Halima ammh kina Raina Gashi Mun Fara Test Tun Last week Dakyar na samu nayi Miki Guda 2 sauran kuma ban samu Dama ba Shine Daman nazo naji lafiya..?na kuma gaya miki ya kamata ki koma makaranta Kada ki Rasa Semester Halima.." Kafin Ta gama Gaban Rigar Zaina ya Jike da Ruwam Hawaye Cikin karaya Ta Dago Idanuwanta Cike Tab da kwallah Tace"Laila ki gayamin Inda ake saida mganin Hakuri zan siya nasha Domin Zuciyata ta Daina Zugi..! Taya kike tsamanin ki ganni..? Ina Farinciki ko walwala Da Har wata Waya zata zauna ahannuna Tun Ranar da kika barni ban kara bi ta wani kawan Duniya ba Laila ina nan Inda kika Tarar dani ina Fama da Kuncin Zuciya Wlh Laila ina Ji Dama na Mutu na Huta da wannan Bakinciki Dake Cushemin Zuciya.." Tafada Tana Fasheewa da kuka Cikin Sigan Lallashi Laila tace"Nasan Abun akwai ciwo  Ammh ki Daure ki kuma Cirema Ranki ki Dage da addu"a haka ba Karshen Rayuwarki bane Halima..'Cikin wani irin Yanayi Zaina tace"Karshen Rayuwata ce Tazo mana..Domin ni ba zan iya zama Gida da Matar da Firstlove yagama Bata Dukkan Rayuwarsa Harda Tsaraban Ciki ba Tun waje zuciyata zata iya Bugawa Laila ba Zan iya Jurewa ba.." Jawota kanta Laila Tayi kan Cinyarta Ta Dora Tana aikin Lallashinta da bata baki Har sai da Taga ta Tsagaita da kukan kana ta Dago Tana Fadin"Ki koma makaranta Don Allah Halima..Bana so ki Rasa wannan Damar.."Da Sauri Zaina tace"Kina Tunanin akwai Abunda zan iya ganewa yanzu..? A"a laila karatu na irin ku ne masu kwanciyar Hankali Wanda wani Tabo bai taba Gifta ma Rayuwarku ba,kila Haka Allah yaso ya ganni Shiyasa ya Jarrrabaceni da wannan Jarabawar mai Wuyar Sha"ani.."Da Sauri Laila tace"A"a fa Halima kema baki da wani Tabo ai bake kika aikata Laifin ba Mijin ki ne.." Zaina Tace"Ni kuwa keda Babban Tabo akwai Abunda Tabo yafi Mijinka wanda kafi yarda Dashi kake matukar Sonsa da kaunarsa Tun tasowarka ace yau Ya Fifita wata karuwa Daga waje akanki yana Raba muku Rayuwarsa Tare Daga karshe Harda Tsaraban Ciki kuma tazo ta Raineshi acikin Gidan ta Haihu kuma Daga karshe ta Aure miki Miji akwai Abunda yafi wannan Babbam Tabo.." Cikin Karaya Laaila Tace"Hakane ammh...! Mganarta Ta makale ne da Shigowar Umma Dakin Dauke da Breakfast din Zaina Tana ganin Tana kuka ta bata rai da Sauri Zainar ta Share Hawayenta Gudun kada Umma sai dai bata san ta Riga Ta gani ba Cikin Damuwa Ta kalli Laila wacce ke mata sannu da aiki Ta amsa Tana Fadin"Ya haka Laila..?ya naga Tana kuka kuma..? Laila Tace"Wlh Umma Takan na mata mganar komawa makaranta Shine tace bazata koma Ba take wanman kukan.."Karamin Tsaki Umma Taja kafin tace"Kyaleta Laila...Mganar bazata koma makaranta Bai taso ba..Zata koma Dolenta in ta kara Warwarewa Karki Damu kinji ko.."Cikim Wani ganin Girman Umma Laila tace"Shikenan Umma Allah ya Rufamana asiri.." Umma ta amsa da Ameen Tana Kallon Zaina wacce ta Dukar da kai Tana Sharan kwallah Tana Shirin Barin Dakin Tace" Ba za ki bar wannan koken banza ba ko..? Inaga kin ga ban taba Dukanki bane Shiyasa...Laila ga kayan karyawanan ku karya"Cikin Ladabi Laila tace"Toh Umma sannu da aiki Umma na Fita Zaina ta Fito da Kukanta Sarari Laila sai ta Bita da kallon Tsausayi dakyar ta matsa mata Suka karya Shima Din Tea kadai tasha ta koma ta zauna Tana maida Numfashi Laila Kafin ta Tafi sai da tayi ta kokarin ganin Zaina taCire dmuwa kuma tace zata koma makaranta ammh har ta bar Gidan Zaina bata kara mata wata mgana ta dai tafi ne da ganin Umma ta Tabbatar mata da zata koma Har takai gida Tana Cikin wannan alhinin Abunda ya Faru da Halima yasa ta karajin duk wani Namiji ya Fita kanta Domin Tunda Firstlove ya iya aikata ma Halima irin wannan Katon Cin Amana koma waye zai iya aikata Haka sai dai Tana Fatan kada saboda haka zaina ta kuntata Rayuwarta har wani abu mara Dadi ya sameta. Laila tazo da safe zuwa yammah kuma sai ga Zafeera kamar an Koreto ajaran majaran Domin Inna Rukayyah Ta gayamata komai Tun Sadda Ta koma Hakika Zafeera ta Shiga Tashin Hankali Nan da Takaichi da Tsanar yayanta ya kamata Gefe Daya ga Tsausayin Zafeera wacce suka taso kamar ta gwaye tafi kowa sanin wacece Zaina ta kuma sani Tana Rauni indai akan Ya Dakta ne,Labari yakai kunnun kowa Domin Har Faruq sai da ya kirata sukayi mgana yace yana ta Kiran Layin zaina Tana Shiga Ba"a Dagawa sun dai yi mgana da Umma sau Daya Shi kanshi ya Shiga Damuwa Sosai Shi ya ma Karfafa Zafeera Gwiwan Taje Taga Halin Data ke ciki Domin sunyi mgana da Ya Sadiq yace ko da ya koma Zaria ya barta Daga ita Har Ya Dakta sunam kwamce ba Lafiya ita bata Damu dashi ba Domin Shine Silam komai Tafi Damuwa da Ukti dinta Tun a satin taso Zuwa sai kuma suna Test Dalilin Haka ne yasa tace Bari ta bari zuwa Weekend Tazo Taga Halin da Ukti Take Ciki. Tana Zuwa Dama da karamar Jaka tazo Tunda Ga Falo ta watsar da ita Cikin Luhu Luhun Ido Ta kalli Umma Dake Falo Tana Fadin"Umma ina Ukti..? Umma batayi mgana ba illah Dakin Data nuna mata ai Zafeera bama Jira cewarta ba ta afka Dakin Tana Kiran"Ukti...! Zaune Kwance ta Tsira ma Ceeling Ido Kamar amafarki Taji Muryan Zafeera Tana Kiranta da Sauri Ta mike sai ko ga Zafeera ta Fado Dakin Ido Ta zaro kafin tace"Ukti..! Cikin Rauni Murya kamar wacce Taga Wata Uwa ko kuma wata Shakiyar yar"uwa haka ta Sauko Daga kan gado ta Zura da Gudu Zuwa ga Zafeeran itama da Gudun Ta Tarbeta suka Rumgume juna Kamkameta Zaina Tayi kawai ta sakar mata wani marayan kuka itama Zafeeran kukan take kamar Wasu yara tun sunayi Daga Tsaye har suka Sulale suka zauna Suka Dungule waje Daya Suna kuka im kaga yadda suke kukan sai sun baka wani Irin Tsausayi kuma Lokaci Daya zaka Fahimci akwai tsantaan kaunar Juna da Shakuwa Sosai a tsakaninsu kuka suke bilhaqqi da Gaskiya acikinsu bamai iya Lallashin Juna. Umma ce ta Shigo ta same su ahaka Baki ta Rike Tana kallonsu kafin Tace"Ko kuma Lafiyanku kuwa..,? Miye haka ..? Hala gidan mutuwa ne nan da kuka wani Hada kai kuna ta ma Mutane wani koken Banza.."Tafada Tana Hararansu Dukkansu Da Sauri Zafeera ta Dago Tana kallon Umma kafin Tace"Haba Umma ba Dole nayi kuka ba..Kalli yadda Ukti ta koma kamar wacce ta Shekara Tana Ciwo..Tsakani ga Allah Ya Dakta bai kyauta ma kansa ba kuma ya Cutar da Zuciyar Ukti yayi Sanadiyar saka mata wani katon Tabo acikin Rayuwarta Wanda bazata manta Dashi ba Umma Tun ina kano da Inna Rukayyah Tagayamin Abunda ya Faru Kukana ya kasa Tsayawa ba kukan Tsausayin Kowa bane sai na Ukti Umma nafi Kowa sanin Rauninta kan Abunda ya Shafi Ya Dakta..! Tafada Hawaye suna kara Bulbulowa Daga Idanuwanta Umma Ta Kada kai Tana Fadin"Ba Dole ta Rame ba Zafeera Ta saka Damuwa acikin Ranta bata cin Abinci bata barci Sai kuka..Kuka Dai Dole kiga Ta koma Haka Ni kaina nagaji da wannan Ramar nata tun ina Lallashinta na Fara Biyo mata ta Bayan Gida..Gwara da kika zo ke kya gayamata Taji Ki gayamata Abunda ya Dace da ita Gwara Tun Wuri ta kama Jikinta in ba Haka ba ta zauna Takaichin Namiji ya kasheta Namijin ma wanda ya nuna ma Duniya baki da wani amfani yana Chan yana Shashancinsa da wata wannan bai Ishesa bama Harda Tukwaicin Ciki..! Zaina dai na jin Umma tama kasa Dagowa Domin bata da ta cewa Taya zata ma Umma bayanin ba ita keda alhalin Daina wannan kukan ba Abun Fitowa yake Daga Karkashin Zuciyarta Zafeera ta Sharbe Majina Tana Fadin"Danaji wannan Labarin Umma Yaya Dakta ya gama Bani kunya naci Sauran Maza sun Fita Daga kaina...Wlh bai kyauta ma Ukti ba sam Dame ta Rageshi..? Tunda muka Taso Tare nice Shaida bata san Soyayyar kowa ba sai Tashi Shi ya kasa ya tsare ya nuna mata Shine garkuwanta awannan Duniyar ammh Daga karshe sakamakonsa kenan..? Naji Bana son ma na ganshi Umma.." Tafada Cikin Tabbatar da mganarta Da Sauri Zaina Ta Dago Tana kallonta Cikin mamakinta Ammh ita Zafeera ba ita Take Kallo ba Umma Take kallo wacce tace"Hmmm...Ni abu Daya yafi Bakantamin arai wannan Lamarin ya gama Jajibo Abun kunyarsa maimakon Abun Duk ya tsaya kansa A"a hardamu ya Shafa Abun Bakinciki wai Dadiron nashi nan Cikin Gidan Zata Renon Dan Shegen Ta Haifa mana Duk agabanmu Don Allah Miya fi wannan Bakinciki da Takaichi.." Da Sauri Zafeera Ta Dafe Kirji Lokaci Daya Tana Fadin"Mun Shiga uku Umma injiwa yace Haka..? Umma tace"Inji Alhaji Tsoho mana.."Lokaci Daya Tana Cigaba da gayamata komai Zafeera Ta mike Daga Durkusan Datayi Tana Fadin"Gaskiya wannan Rashin adalci ne...Taya Abba zai ji da wannan Bakinciki..?gaskiya da sake bamai Haifama Dan Shege ko Shegiya acikin Gida Umma ta Zauna Chan Gidan Ubanta Shima ta Haifamai itama ai yar Barikin ce,Domin Ba"a Shege sai an yi Shegiya Umma" Zaina Ta kura ma Zafeera ido Ganin Ta Dauki Zafi acikin Lamarin Bata dai yi mgana ba Umma Ta Jinjina kai Tana Fadin"Ahto Nima Abunda nagani kenan..Kinsan Alhaji Tsoho mgana Daya yake baya Sauyata...Ammh Duk da wannan Bakinciki Daya kunsa mata Kin ganta nan Har yanzu bata Daina Sonshi ba Tana kuka wai Tana Fadin Bata jin Dadin yadda Abba ke Cewa bazai yafe ma Zain ba,kuma ya Hanashi Shigowa Gidanan In dai kinga ya Shigo Toh sai dai in baya Gidane wai ahakan ma Tsausayinsa Take bansani ba ko Matakin Dana Daukan kan bazata koma Gidansa bane yasa ta kasa Daina kuka..." Zafeera Ta waigo Tana kallon Zaina Cikin Takaicinta Tana Fadin"Ita nan har yanzu Sonshi Take Umma Duk da wannan Katotin Cin Amanar Daya aikata mata..? Tabe baki Umma Tayi Tana Fadin"Kema kya gani..Tambayanta kila Ta gaya miki..Bari naje na Duba Girki na Dawo ."Cikin gyada kai Zafeera Tace"Tom Umma..! Umma na Fita Zafeera Ta kalli Zaina Tana Fadin"Don Allah wai ke nan yanzu kukan Son yaya Dakta kike ko kuwa kukan Cin Amanar da yayi miki .? Zaina ta Dago Fuskata ido Jajir Tana kallon Zafeera kafin Tace"Ba kukan Soyayyarsa nake ba Ukti..Ina Tsausayama kaina ina Tsausayama Firstlove..Saboda ni Abba ya kasa yafemai ya hanashi Shigowa gidanan Umma bata mai mgana ko Gaisheta yayi bata amsawa Duk Saboda ni Ukti yaya zan Ji da wannan Abun..?ta dalilina Uba zai yi Fushi da Dan"sa hakama Uwa zata Juyama Danta Baya Abun na Damuna na rasa yadda zanyi.." Ta karishe Fada Cikin Raunin Murya kafin Zafeera Ta saki Wani Dogon Tsaki Tana Fadin"Aikin Banza..Har shi wani Abun ki tsaya kina Tsausayi ne..? Hala Shi ya Tsausaya ma kansa ne ballatana ke..? Kuma Da kike mganar ta Dalilinki Abba na Fushi Dashi Haka baki bashi Hakkinsa na Aure ne Daya sa yaje yana Iskanci da karuwa...? Cikin Kuka Zaina Tace"A"a Wlh Ina bashi Dukka hakkinsa..Bana taba nuna mai gajiyata ban Taba Juyama Bukatarsa baya ba Ukti Koda Ina cikin Jinin Haila ne Ina Kokarin wajen Kwantar da Hankalinsa Ban sani ba..Ban san Ta ina na Rageshi ba Ukti.."Zafeera Tace"Toh kin gani..Kenan babu Ruwanki bakuma saka hannunki wajen Zuwa yayi Iskancinsa Har yayi mata Wata ciki..Banga laifin Abba da Umma ba Ko ni nan Dayake Dan'uwana na jini naji ya Fita kaina naji kuma Wlh Duk Labarin kukan da Kwanciya Rashin Lafiyar da akace yayi bai bani Tsausayi ba Kece ma kika Fi bani Takaichi..." Zaina Ta Rausayar dakai Tana Fadin"Inda alkawari Ruwa ba zai Dafa Kifi ba Zafeera..Na yarda Yaci amanata kuma bai min adalci ba ammh kuma Sai nayi Duba da wani Abu ni wacece da Haka bazai Faru dani ba..? Kinga yadda Firstlove ya koma Ukti ya rame ya lalace Wlh Tallahi Ina Matukar Tsausayinsa acikin Raina.." Baki Sake Zafeera Take kallon Zaina kafin ta Kada kai Tana Fadin"Alkawarin yaci Ubansa..Wlh in Kikaga Ruwan bai Dafa Kifin ba Don Ubansa sai dai in ba"a sakoshi Cikin Ruwa ba..Kuma Tunda kina so ki Koma Wajensa Koma Ukti Ammh ki sani Babu Ruwana In Kika Kirani Watarana Kina kukan Bakinciki zai kasheki Kina ji kina gani zai Auri Abokiyar watsewar tashi akoma ana Miki ganin Daya bayan Daya Gefe Daya kuma Dan gaba da fatihq na Gifta muku acikin Gida.." Runtse Ido Zaina Tayi Tana Fadin"Haba Ukti..Kidaina aibata shi Haka karki manta Dan"uwanki ne fa.."Saboda Haushi Ko mgana Zafeera Bata mata ba ta Fice Daga Dakin Ta bar Zaina na Kiran Sunanta Kitchen Taje wajen Umma Ta kama mata aikin Abinci Sunayi suna Hira kan al"amarin Dayake Umma,Bata da wasu abokam Shawara sai ya"yanta Musamman ma Zafeera Tunda ita macece mai manyance da kuma Dattako kamar wata Tsohuwa. Tare suka gama Girki kana Umma ta wuce Dakinta Domin Domin Tayi wanka Itama Zafeera sai ta koma Dakin Domin ta Dauro alwala Kai Hade da Gwiwa ta iske zaina kan Sallaya bayan Ta Idar da sallah kai kawai ta Jinjina Batayi matamgana ba ta Shige Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne Umma ta kawo musu Abinci ta kuma sanar da Zafeera cewa Abba ya Shigo Daman yaje gaida Alhaji Tsoho ne Tace bari Tagama taje ta Gaisheshi Ganin Daga Umman Har Zafeera sun yi baanza da ita yasa ta sauko Ta Fara Tura abincin ko Rabi bata Ci ba Tatashi Zuwa Tiolet sai amai sai ta gama ta Fito ta Fada kan Gado Tana maida Numfashi Suka Bita da kallo kafin Zafeera tace"Anya Umma Ukti ba Ciiki gareta ba..? Da Sauri Umma tace"Bar mata Fata Zafeera..Ni da nake so arabu Salin alim.."Kai Zafeera Ta gyada Tana Fadin"Kuma fa Hakane Umma...Zamansu ma ai ya Haramta Saboda zata cigaba da zarginsa Tana ganin sa da Abun gwara kowa ya nemi Daidai Dashi.."Umma tace"Shi nagani..."Zaina Tana Jinsu Lokacin da Zafeera tace ko Ciki gareta..? Sai da gabanta ya amsa ta Fara Tunanin wajen wata na Uku kenan bata ga Al"adanta ba Da kuma yanayin Data samu kanta akwanakin nan Zuciyarta ce takara Tsinkewa Domin bako Tamtama Mganar Zafeera zata iya Tabbata Kunshe Bakinta Tayi kada Umma Taji kukanta kuma Ta Tabbatar ma kanta Umma Taasan Da Cikin nan da gaske sai ta kaita an Zubar mata Dashi Ita kuma bazata bari ba Domin Tana Son Cikinta kuma Tana Son Uban Cikin Tafi kowa sanin babban Burin firstlove aduniya Shine Yaga ta Haihu Bazata bari wannan Burin nashu ya tafi abanza ba Wata Zuciyarta tace mata Kin makara Domin Wata ta Rigaki Daukan kwayan Hallitan Haihuwansa a mahaifanta Tuna Haka yasa Duk wani Farincikinta ya gushe Kishi ya Rufe mata Ido sai kuka ammh kukan Zucci Sanin Daga Umma Har Zafeera Suna Jami"iya Daya ne kamata Tana kuka Dukkansu bada Sauki zasu mata ba. Zafeera Taje ta gaida Abba ya Dinga Mata Fadan me ya Dawo Da ita suna Shirin Fara Jarabawa Tace gobe da safe zata koma kana ya kyaleta,Zain kuma Har kofar gidan yazo sai dai Megadi ya Tabbatar mai da Abba yana Gida Shi ya Hanashi Shiga ya Juya kan Motarsa Zuwa Gida wanda yayi mai Fadi babu Firstlove acikinsa Ba Laifi ya Rage damuwa saboda Asibiti Duba Marasa lafiya ma na Dauke mai Hankali ammh Tabbas ya gama Ramewa ya Fige da alamu dai yana Jin Ciwo ammh Bayaso ya kwanta ya Cigaba da Tsayuwa kan kafafunsa Domin in ya nuna Rauninsa Babu abunda zai Sauya. ****** Har suka kwana suka Tashi Daki Daya Zafeera bata sakar ma Zaina Fuska Duk da Tana Tsausayinta ammh kuma Ta bata Haushi yadda ta kasa mantawa da Ya Dakta da wani Abunda ya aikata gareta. Bayan sun karya Zafeera ta Fara Shirin Tafiya ganin hakane yasa Zaina ta Fara kuka wannan Dalilin yasa Zafeera ta watsar da komai ta isa gareta ta Rumgumeta Tana ta lallashinta Da bata baki kan ta Cire Damuwa aranta ganin Zafeeran ta Sauko ne yasa tayi mata alkawarin zatayi Hakan Insha Allahu Zafeera taji Dadi ta Dinga Share mata Hawaye Cikin Shakuwa. Abba kuma yana Gida bai Fita ba yau weekend Misalin 11am na Safe sai ga Kiran Alhaji Tsoho Bayan sun gaisa ne yake Shaidamai Tun safe sukayi waya da Kwamishina Baban Dina kan Yau Ita kanwar Mahaifiyar yarinyar Datazo Daga Sudan da mai Dakinsa zasu kawo ita Dinar kamar yadda ya Tsara saboda haka sun Taso Suna Hanya agayara mata masaukin da zata zauna Har Zuwa Lokacin da zata Haihu Adaura musu Aure tatare Gidan Mijinta Shikenan.. Abba yaji Kamar yayi kuka ammh kuma bai da yarda zai yi Tunda tun yana yaronsa baya Jayayyah da Alhaji Tsoho ballatana yanzu da Girma ya kamashi Waya ya Dauka ya Kira Nene da Umma Dukkansu yace su Zo Dakinsa su sameshi Kusan Tare suka Shigo kowacce Cikin mamakin wannan Kiran gaggawan sanin ma basu Dade da Fitowa Daga Dakin ba Umma kuma Dama nan ta kwana. Cikin Kallonsu Dukkansu ya Isar musu da Sakon Alhaji Tsoho Dukkansu sun Ji wani Irin Barin ma Umma Nene ce ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Umm..Sai dai Dakinsu da Halima ke Ciki yafi Girma,Dayan karami Kuma nan Zareena ke sauka In Tazo,Kaga kuma Sauran Dakunan na Sadiq ne da Faruq kaga ai bama Sauketa Dakunaansu ba Duk basa nan,Suna Zuwa mana Hutu kwatsam ne.." Cikin Nazarin Mganarta Abba ya Sauke Numfashi Takaichi kafin yace"Shikenan agyara Dakin su Sa"adiya sai ta sauka aciki.."Cikin mamaki Umma tace"Ita kuma yar tawa taje ina..? Karfa ku manta Dakinsu ne Tun suna yaransu har girmansu kawai rana tsaka sai asaka wata Najasa aciki kuma alhalin Zaina Tana zaune acikin Dakin..? Umma Ta Fada Cikin Takaichi Nene ta kada kai Tana Fadin'Haba Umma ya kamata ki Daima aibata Wannan al"amarin da wani muguwar kalma Ko muna so ko bama so Cikin Jikinta Jinimu ne Tunda Danmu ya Digashi Kinga kuwa ya Kamata mu Cire komai mu Rumgume wannan kaddaran Tamu Hannu Biyu ammh naga ke kina Fifita Abunda kika Haifa kan Abunda Bake kika Haifa ba Umma.! Ta fada Tana kallonta Cikin Hawaye Mirmishi Takaichi Umma Tayi Tana Fadin"Halima yata ce Halak Makak..Kamar uwa nake gareta ke nice ma Uwartata kuma Ubanta ban damu da me zaki ce ba ammh ina so Ki sani ni ba irin Matan da Domin Nasu yayi Laifi su kare su ki Nuna yayi Laifin Saboda Don yana nasu ako"ina ina Bayan gaskiya..Na Riga nagama mganata Anemar mata wajen zama ammh ba Dakin Ya"yana ba wlh..! Tana Gama Fadin Haka ta Fice su Abba suka Bita da Kallo,Kallonsa Nene Tayi zatayi mgana ya Rigata da Fadin"Har kin Manta Fatima..? ki naka kenan ka so na wani..Tayi gaakiya uwar Sa"adiya take gareta Har Abada..Bari na Kira Alhaji Tsoho na gayamai.."Nene na Tsaye ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai Abunda Umma tace Cikin Muryann Dattako yace"Me Halimar take Acikin Dakin Usmanu.. ? Kace ma Fatima nace Injini Ta maida Halima Dakin Miijinta ita kuma Yarinyar ku sauketa nan Usmanu hakkinka ne ka kula da ita kaida Matanka Laifin wani baya Shafar wani mene ne laifin Abunda ke Cikinta..?babu Laifinsa na Iyayensa saboda haka kada ya karbi Hukuncin da ba nashi ba..! Abba dai Toh kawai yace batare da ya kara yin wata mgana ba Nene  ma bai kara mata mgana Bayan Alhaji Yace In sun Kariso Hajiya mama zata kariso Dasu nan Gidan Damuwarsa yake so ya Boye Shiyasa ya Nufi Hanyar Tiolet yana Fadin"Kije ki saka ko Zainab ta gyara dakin nasu Sa"adiya Alhaji Tsoho ya bada Umarnin a sauketa anan.."Daga Haka ya Tura Kofar Tiolet din ya Shige ya maida Kofa ya Rufe. Nene Fita Tayi zuwa Falo Ta samu Umma zaune Tana kallon Sunna Tv Ana Wa"azi ammh a zahirin gaskiya ba wa"azin Take kallo ba Hankalinta da Tunaninta na kan yadda Zuciyarta zata Juru zama da Dina acikin Gidanan da Suna wacce ke Dauke da Cikin Dan'ta kuma ba na Sunna ba Bakincikinta zai karu Kila har itama asameta da Hawan jini Daga sama kawai Taji Nene na Fadamata Umarnin Alhaji Tsoho na asauke Dina Dakin Su Zaina Umma ta Dago Tana kallonta Kafin tace"Toh in ko Hakane sai dai Zaina ta Dawo Dakina..Ban yarda Ta Hada wajen zama da Wannan Yarinyar ba Bazata ma sabu ba.." Nene dai bata kara mgana ba ta Wuce zuwa Dakin nasu Zaina ta Iskesu Zainab da Zafeera ke Hiran karati zaina na Gefe Tana kallonsu bata dai mgana Ammh kuma Daga Dukkan alamu Hiran na Debe musu kewa Cikin Dakewa Nene ta Kalli Zainab Tana Fadin"Zainab ki gyara Dakin nan ki Share ko'ina ga Baki nam Daga kano..! Zafeera ce tace"Baki kuma..!? Ko Inna Rukkaya ce Nene..? Kafin Nene Tayi mgana Umma ta Fado Dakin Tana Fadin"Ba Rukayyah bace...Yarinyar da Alhaji Tsoho yace zata Dawo nan ne suke Tafe yau..Kuma nan Dakin yace asauketa.."Dam!gaban Zaina ya Buga Har sai da ta mike zaune Dakyau Cikin yamutsa Fuska Zafeera tace"Dakin mu kuma Umma..? Ukti kuma ta koma ina .? Umma tace"Tashi ki Hada mata kayanta dana amfaninta..Dakina zata koma Kema in kinzo Hutu chan zaki Dinga Sauka Daga yau.."Tafada Fuska ba walwala,Zafeera ta Sauke Numfashi Tana Fadin"To Umma.."Daga haka Umma Ta Juya ta Fice Nenema tabi Bayanta Suna Fita Zainab tace"Har ga Allah bana son Dawowar yarinyar nan Gidanan..." Zafeera Ta mike Tana kallon Zaina wacce ta kurama waje Daya Ido Zuciyarta na Suya Cikin Tsausayawa tace"Ukti Tashi mu koma Dakin Umma..Bari na Kwashe miki kayanki.." Cikin karfin Hali Zaina tace"Bani ma da wasu kaya Dogayan Riguna guda 3 ne Hijabi da yan kayan kwalliya suma na Zainab ne Umma ta bani Duka kayana suna Lowcost..'Zafeera ta gyada kai kawai Ta Bude Wardrope ta kwaso mata kayan kana ta Tattara kayan Shafan gaban madubi,Dama zainab Dakin da Zaferea ke sauka ne nata Bata kwanan nan Dakin Kowa ya sani Dakin Zafeera da Zaina ne Tun abaya... Hannunta Zafeera ta Riko Har Dakin Umma ta Saka mata kayan sawan Cikin Wardrope kayan Shafan kuma ta Saka mata Kan madubi,Ta koma ta zauna Gefen Zaina wacce Tayi Tagumi kawai Haka itama Zafeeran Tayi Tagumin ganin haka yasa Zaina ta kalleta Cikin Sanyin murya Tana Fadin"Ya naga kin zauna..? Kin fasa Tafiyar ne..? Zafeera ta Sauke Taguminta Tana Fadin"Ina zani na barki Cikin wannan Ukti..? Ni kaina da bani bace Mijina ya aikata wannan Lamarin ina jin Dacin Dawowar yarinyar nan Gidanan Baki ji Zuciyata ba.."Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Zaina ta saki Batayi mgana ba Daman ance Hawaye Samun waje sukayi In Bala"i yayi bala"i kukan ma nemansa kake ka Rasa. ***** Karfe 12pm da wani Abu na Rana Su Hajiya Maimuna da Hajiya Batula da Dina suna Zaune falon Gidan Alhaji Tsoho Tabawa ta Cika gabansu da kayan Ciye Ciye da Shaye Shaye,Hajiya mama na gefe zaune ta Fito suka gaisa da Hajiya Maimuna da Hajiya Batula ba Shakka kam Hajiya Maimuna ko Hausanta baya Fita Da ka ganta kasan Daga Chan ta Fito Dina kuwa Tana Gefe Ta lafe kan Kujera Tana latsa wayarta Taci Wata Doguwar Riga baka Wacce ta Dan kamata kadan sai Tayi Rolling din da bakin gyalen Abayar Ta kara Kiba Da Fari Daga gani Cikin ya karbeta Hajiya mama sai kallonta Take Tana mamaki Dakyar Ta iya Daga baki ta gaida Hajiya Mama Shima sai da Hajiya Maimu tayi mata mgana. Bayan sun Sha Ruwa ne Hajiya Mama Tayi musu Jagora Dakin Alhaji Tsoho suka shiga suka gaisa sai alokacin Hajiya Maimu Ta kara ganin Kimarsa Sosai Take kuka Tana ta Godiya,Alhaji Tsoho yace Karta damu bakomai Kallon Hajiya mama yayi yana Fadin"Aminatu Ki Rakasu chan Gidan Usmanan Suga inda zata zauna.." Kai Hajiya Mama ta gyada cikinn alamun gamsuwa. Kallonsa ya koma kan Dina wacce Take ta kare ma Dakin kallo Tana wani Tabe baki yace"Zaki zauna Gidan Iyayen Zainullahi kamar yadda na Fada Daga Farko..Ina so kin san wani Abu zaki zaman neman gafaran Allah ne da kuma Jiran Wa"adin Haihuwan Cikin ki in kika Haihu ni kuma a Tabbatar da Tsarkin ki zan Daura miki Aure da Zanullahi ammh kuma baya Nufin zaki kara Wata Hulda Makamciyar wacce kukayi da juna abaya matukar kuna so ku Hallasta Auran naku." Kai su Hajiya Batula ke gyadawa alamun gamsuwa Dina kuwa kai ta Sadda kasa Tana Fadin"insha Allahu Alhaji..Nagode.."Kai ya gyada kafin ya sallamesu Sukayi sallama kan cewa Dagachan zasu koma Domin ba kwana zasu yi ba. Da Farko Motar da suka zo da ita wata katuwar Jeep Hajiya mama Zata Shiga sai ga Haddir ya Dawo Daga asibiti Hajiya Mama na ganinshi tace su bari Shi zai kaita sai su bisu abaya Ko Gidan Bata bari ya Shiga ba Ta gayamai Abunda ke Faruwa Kallon Kallon sukayi tsakaninsa Da Dina kafin ya Dauke kansa Motar ya koma Hajiya mama ta Shiga yayi Riverse ya Fice Daga Gidan Suma suka Shiga Mota suka Rufa musu baya. Suna Zuwa Afalo suka iske Nene da Zainab,Umma kuma tana Dakinta ne Nene ce ta Mike tana musu Maraba Direbansu kuma yana ta Shigo da Uban akwatina kamar za"a Bude Shago kusan Rabin kayanta Dina ta kwaso,Mamaki ya kama Nene da Haddir Zainab kuwa Dinar take kare ma kallo ganin tana ta wani Bin Falon nasu da kallo Tana wani yamutsan Fuska acikin Zucityar zainab tace"Kan Uba wannann ai yar Bariki ce.." Saman kujerun Falon suka yada Zango suka Fara gaisawa da Nene Sai ta Umarci Zainab Data Kawo musu Ruwa da abinci Hajiya Batula tace Bazasu Sha ba sun Sha Daga Gidan Alhaji Tsoho. Hajiya Mama dai suna Zuwa Dakin Umma ta Shiga Tunda ta Tamnaya akace Tana Ciki Zuwa Tayi tace ta Fito ba yadda Umma ta iya Dole tabi Bayan Hajiya Mama hakama Zafeera sukabar Zaina ita kadai Cikin Tsinkewar Zuciya. Sun kawo Falon Daidai Lokacin da Hajiya Maimu ke fadin"Nice kanwar mahaifiyarta Daga Sudan Sunana Hajiya maimuna kece Mahaifiyarsa..? Nene na Shirin Tayi mgana Umma Tayi Saurin Fadin"Eh itace sannunku da zuwa.."Dagowa tayi Tana kallon Umma kana suka gaisa Nene kuwa bata samu ma bakin mgana ba Hajiya maimu Tace"Mahaifinsa baya nan ne..? Nene Tace"Eh yadan Fita ne.."Hajiya maimu tace"Allah sarki..Mun fa Gode Allah ya saka da alheri Sai Hakuru Duk da Abun ba Dadi ammh Tunda an samu Fahimtar juna Shikenan ga Dina nan mum kawo muku ku Dauketa Tamkar yarku Don Allah kada ku saka mata Ido Duk Abunda ya kamata Don Allah akwaba mata Da na kowa ne mugu ne sai Mai shi..'Tafada kamar Tayi kwallah Nene kadai ta amsa da insha Allahu Umma da Zafeera Dinar suke kare ma kallo ganin ko ajikinta Sai ma Latsan waya Data keyi. Hajiya Mama ce ta Kalli Nene Tana Fadin"Nene ku kaita masauki mana.."Mikewa Nene tayi Tana Fadin"Toh Hajiya mama..Na Dauka zasu ci abinci ne.."Hajiya mama tace"Akai musu cikin Dakin.."Da sauri Hajiya Batula tace"Mun gode Wlh..Muna kan Hanya ne yau zamu koma.." Hajiya Mama tace"Ayyah ba laifi.."Nene ce kan gaba Suka Bita abaya Bayan Hajiya Batula ta kalli Dinar tana Fadin"Taso mana Dina.."Mikewa tayi Tana gyara zaman karamar jakar Hannnunta kafin tace"Kayana fa nan zan barsu Uwata.." Yadda ta Fadi Uwata din gatsal ne ya bama su Umma mamaki Hajiya Batula tace"Za"a Shiga dasu mana.."Da Sauri Hajiya Mama tace"jeki za"a Shiga Dasu.."Bata da yarda zatayi haka tabi Bayansu Zuwa Cikin Dakin suna Shiga Hajiya Mama ta kalli Zainab Tana Fadin"Ke zainab dake da Zafeera kuja akwatimam nam kubisu dashi.." Dukkansu basu so ba suna Tura baki suna komai suka ja su suka Shigar mata dasu wajem akwatina Shida fa,Koda suka Shiga sun iske Suna ta mata Fada da Nasiha Nene daman Tuni ta Fice Dukkansu Falo Kowa ya Dawo ya zauna su Zafeera da zainab sun Buga Tagumi Umma Tayi Zugudi Nene ma Haka Haddir na Gefe zaune yana Latsa wayarsa Zain ya Tura ma sakon Zuwansu Dina sai shi kuma yamai sakon Abba na gida..? Yace mai A,'a cikin Sauri yace gashi nan zuwa. Hajiya mama ta kalli su Umma Tana Fadin"Ina Baban nasu yaje ne..? Nene tace"Bai fadamana ba..Yadai ce zai fita Direban ya Daukesa kila Office yaje ko akwai wani Abu ya taso.."Hajiya mama batace komai ba sanin Ta sani Kawai dai yana Gujema Haduwa dasu Hajiya batula ne yana Jin kunyar a nunashi matsayin Mahaifin Zain Ita kuwa Dina ko ajikinta yadda kasan Cikin dam Sunna ne bana Shege ba. Su Hajiya Batula ma basu Jima ba suka Fito zasu Tafi,Su Umma suka Mike suna musu sallama Ba wacce ta Rakasu waje sai Nene Hajiya maimun Tana ta Godiya da kuma Rokonsu alfaram suyi Hakuri Tanayi Tana Sharan kwallah Nene taji Tsausayinta Sosai Hajiya Batula kuwa Batace komai ba sanin dai Dina ba yar Goyo bace ako"ina sai Ta Nuna bata da Tarbiya. Motarsu na Barin Gidan na Abba na Shigowa kilama sun Hadu a Hanya Yana Shigowa Falon yagansu Tsaye Cirko Cirko Ganin Hajiya mama ya Tabbattar da koma Miye Cikin Ladabi ya gaisheta Ta amsa Tana Kallon su Umma Lokaci Daya Tana Fadin"Wai ina yarintar nan Halima ne..? Tunda muka Shigo ban ganta ba..! Umma tace"Tana Dakina..Chan nace ta koma Tunda Dakin nasu ya zama na zaman wata.." Hajiya mama tace"Hakane..Ammh itama Alhaji yace Ki maida ta Gidan Mijinta zai fi zamanta anan Fatima..Sai fa hakuri Abunda ya Faru ya Riga ya Faru in muka sa Hakuri komai zai wuce ne.." Da Sauri Umma Ta Mike Tana Fadin"A"a Hajiya Mama..Wannan karon ba Gaddama ko Jayayyah da Umarnin Alhaji Tsoho zanyi ba...Na Riga na yanke Shawaram Raba Auran ZAINULLAHI DA ZAINA..!! DAM!DAM...! gaban ZAINA dake make Daga Kofar Dakin Umma Tana Jin Abunda ke Faruwa afalon sannan kuma Haka Gaban Zaina yayi wannan Bugawar Lokacin da yake sawo kansa Falon Nene,Abba,Hajiya Mama,Haddir,Zainab sai da suka Gwalo ido suna kallon Umma Banda Zafeera wacce ta Kada ido alamun Daidai kenan. Kowa ya kasa mgana ba Illah Umma Data Cigaba da Fadin"Dama Lokaci kawai nake jira kuma yayi Lokacin..Saboda Haka ya kawomin Takardan Sakin Halimatu Bazan bari Ta kara zama dashi ba Ballatana Har Cin Amanarsa ya kasheta Lokacinta baiyi ba..! Tafada Tana kauda kai Daga kallon Da Abba da Hajiya mama ke mata Muryan Zain suka ji wanda ba wanda yaga Shigorwarsa Falon Cikin Rauni kamar Cikin Muryan kuka yace..' "UMMAAA....! *Shakira...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️   *BOOK 1*            2️⃣6️⃣ "Gabadayansu suka Juya inda sukaji Tashin Muryan Zain din Yanayin da suka ganshi Dukkansu sai da ya basu Tsausayi Hatta kuwa da Abba Dayake Fushi Dashi. Durkushe yake kan gwiyoyinsa Daga Kofar Falon Domin Tun Lokacin da Umma ta Furta Rabashi da Firstlove yaji kafafunsa sun Gaza Daukansa Gabadaya Nan ya zube Bisa Gwiwoyinsa Idanuwansa sun kala Sun Jajir Cikin Wata irin Murya mai Cike da Rauni yake Fadin"Ummaa..! Don Allah..! Don Darajan Ma"iki ki yanke min kowani Hukunci Ammh banda Wannan bazan iya ba...Wlh kikace na Rabu da Fisttlove na Tabbata Ranar da na Saketa Nima Ranar zaki Rasani na Har Abada..! Yafada yana Sakarmata Idanuwansa Cikin Tabbatar da mganarsa Cikin Wani Irin Rauni da Tsausayi uwa kan D'anta Umma Taji kuka ya kwace mata ammh sai ta kauda kai da Sauri Cikin Daga Murya tace"Karya kake...Karya Kake Zainullahi...Baka son Halima da kana Sonta da baka aikata Abunda ka aikata ba,kaji ma Rantsuwan Dan Musulmi Wlh Tallahi Sai ka saketa Domin Har Abada bazata Cigaba da zama Dakai ba.." Ba zain kadai ba Hatta Abba wannan karon sai da ya kara sakarma da Umma Ido Saboda Jin yadda ta karfafa Rantsuwarta Haddir ya Zaro Ido Cikin Tashin Hankali yana kallon Zain wanda yayi zaman yan Bori akasa Zaina kuwa Dake make kuka ya kwace mata In zata Fito ta Fadi gaskiya koda wannan Al"amarin ya Faru Kaunar Dake tsakaninta da Firstlove bata ma Girgiza ba Tana Jin in ta Rabu Dashi bazata iya kara son wani Da Namiji ba acikin Rayuwarta,Lokacin da Umma ke Fadin bazata koma Gidansa ba Ta Dauka Daga baya in Komai ya lafa zata ssuko ammh Yau kam ta kara Tabbatar ma da kanta Cewa da Gaske Umma take zata raba Auranta da Firstlove wanda Allah ne ya kulla wannan kaunar Junan Tun tana Cikin Uwa Gareta Maryama. Cikinta Ta saka Hannu Tana Shafawa Cikin kuka da Hawaye da kuma wani kaunar Abunda ke Cikinta Ta kara Tabbatar ma da kanta Tana Dauke da Cikin Firstlove acikin mahaifiyarta wani Soyayyah da Kaunar Cikin nata suna kara kamata Har yau har Gobe Tana Son Uban Cikinta Shima Cikin Tana Sonshi ammh Taya zata Bijera ma Umarnin Umma..?Matar data Sadaukar da Farincikin Abunda ta Haifa Saboda nata Farincikin..?.har Abada bata jin zata iya Bijirema mganarta Taji tagani Duk Abunda ta yanke akanta Daidai ne, Koda Hakan zai sama Sillar Rasa Numfashinta ne ammh Taya ya zata Dauki Batun Rabuwarta da Firstlove kila Rabuwar nasu Tayi sanadiyar kaita Lahira ba wannan al"amarin da Umma Take hangoshi a matsala ga Rayuwarta ba.." Kowa kallon Umma yake cike da mamakinta Barin ma Nene Data Bude baki kawai Tana kallon Umma Zafeera ce kadai bata wani Damu ba ammh ita kanta Rantsuwan Umma ya bata Tsoro Hajiya Mama ce tace"Haba Fatima wannan Uban Rantsuwan fa..? In rai ya baci Hankali ake sakawa ya Nemoshi ai...Dukkanmu nan Ahali Daya ne kuma Abunda ya Faru bamu isa mu Kauda Faruwarsa ba Haka Allah yake lamarinsa ya Fitar Da Rayyaye Cikin Mattace kuma ya Fitar da Mattace Cikin Rayayye Bai kamata ki Daga Hankalinki ba Tsakanin mata da Miji sai Allah ki maida Ta Dakin Mijinta sai kiga sun Daidaita koma yazo ya wuce Batare da an samu Wata Matsala ba.." Kowa kalaman Hajiya Mama yasa ya Kore Mganar Umma sai dai Umma kada kai Umma Tayi Tana Fadin"Hakane Hajiya mama ba naki jin mganarki bane..Na Riga na gama yanke wannan Hukuncin Tun Sadda abun ya Faru..Kawai kuce ya sakarmin yata yaje ya zauna da wacce ya zaba kawai.."Tafada Tana Dukar da kanta Daga kallon Da Hajiya Mama da Nene ke Binta. Cikin Mamakinta Hajiya Mama tace"Ikon Allah..Fatima an Taba irin wannan kuwa..? Ki Dage kice Zaki Raba auran da bake kika Hada ba Fatima anya..? Umma ta Kada kai Tana Fadin"Na Riga na Rantse Hajiya Mama Sai ya saketa.."Da sauri Hajiya Mama tace"Tabdijam kya kuwa yi kaffara Fatima.." Nene Tace"Tabbas kuwa..'Cikin Jin Haushin Umma Abba dai na Tsaye bai yi mgana yau kam Tsausayin Zain ya Shiga Ransa Shiyasa ma Tun dazu ya kasa Cewa komai ita Kuwa Dina Tana Cikin Dakin da aka Sauketa Ta gama Duba ko"ina Har Cikin Tiolet din sai da Ta leka taga Komai Tsab ita kanta tasan karyanta Ta Raina Gidan su Zain kan gadon Ta koma ta kwanta Tana Lunshe ido Lokaci Daya Tana Shafa Cikinta Cikin so da kauna Take fadin"Na fara kusanci da Babanka..Lokaci Kadan ya Rage na zama Rayuwarsa Gabadaya..' Take Fada Cikin Farinciki Domin Kaf Rayuwar Dina ya Tafi ne kan So da kaunar Zain mallakarsa kadai ne agabanta Wayarta Ta jawo ta Kira Zakiya suka Fara mgana Tana gayamata sun iso Tun dazu Har su Hajiya Batula sun kama suna Cikin mganar take ta Jin Tashin Hayaniya Daga Falon ta basar ganin Abun na kara yawa ne yasa Tace ma Zakiya zata Kirata Tatashi Ta Bude Kofar ta Fita Domin Taga kuma Hayaniyar me ake kuma..? Turus Tayi Daga Kofar Dakin ganin Zain Durkushe akasa ya Hada kai da gwiwa gasu Abba da Umma da su Nene tsatsaye,Kamar wani Abu na Faru mamaki ya kamata sai dai Zain kawai ta kurama Ido Cikin Tashin Hankalin ganin yadda ya koma Kamar ba Zain dinta ba Tuni Taji Hankalinta ya Tashi ta Fara Taku zuwa garesa Taji Muryan Nene Tana Fadin"Abban Saudart Don Allah ka Saka baki mana..' Abba yana kallon Zain yace"Me kikeso nace Nene..?Tamin daidai ai mganinsa kenan komai ya Faru Dashi ai shi yaja ma kansa Daya Tsaya inda Allah ya Ijiyesa da Duk haka bata Faru dashi ba Bani da ikon Cewa wani Abu kan Hukuncin Fatima ayanzu haka Nene.."Jikin Nene Yayi sanyi Kawai sai ta Juya wajen Umma Tana Fadin"Don Allah Umma Zareena ki janye wannan Hukuncin ko don Tsausayin Halin da yaron nan yake Ciki..' Umma ta kalli Nene Ido Cikin Ido kafin Tace"Yauwa Ki gayama Da"nki ko ki Tursasa ya sakarmin yata..In har ya bani Takardam sakinta ni kuma nayi mai alkawarin Ranar zan yafe mai..! Galala Nene tayi Tana kallonta Jin haka yasa Zain ya Dago kansa ya Fara jam kafa Zuwa Gaban Umma ya Rike kafafunta yana Fadin"A"a umma ba wannan Hukinci ba..Naji ki bani wani mai Wahala ammh wannan Fa Daidai yake da Barazan Rasa Numfashina.." Yafada yana sakarmata kuka Nene da Zainab masu Saurin kuka Suma kukan suka saki na Tsausayin Zain ayayinda Zaina Take Labe Tana nata,Dina ma Cak Take Tsaye Tana sauraran Kowa Dake Falon da kuma kallon Zain dake wannan kukan in Ta Fahimta Daidai kamar mganar saki take jin anayi..? To wazai saka yake fadin Kamar Barazan Rasa Numfashinsa ne..? Firstlove wata Zuciyar ta bata amsa sai gabanta ya Fadi ashe an kashe maciji ne ba"a Sare kansa ba Yanzu ita Firstlove yake fadin in ya Rabu da ita zai iya Mutuwa daman tasan Za"a Rina Raba wannan Soyayar Ba abu bane mai Sauki Gyara Tsayuwa Tayi Tana so Taga Karshem Episode din. Jaye kafarta Umma Tayi da Sauri Ta kauda kai bata son kallonsa kar ya karya mata Zuciya ganin haka yasa ya koma Gaban Abba ya kama kafarsa yana Fadin"Allah ne gatana Abba kai ne gatana..Don Allah ka tayani bama Umma Hakuri kada Ta Rabani da Firstlove.."Shuru Abba yayi yana kallonsa ganinsa yana kuka sai ya karyamai Zuciya Da Sauri kawai ya kwace kafarsa ya Juya Zuwa Shashensa yana Share kwallah Kowa ya Bishi da kallo Cikin alhini. Yana Tafiya Hajiya Mama ta Duka ta saka Duka Hannuwanta Ta Dago Zain tana Kallon Umma Lokaci Daya Tana Fadin"Meyasa kike da kafiya da Taurin Zuciya ne Fatima..? Kalli yadda yaron nan ya koma..? Baki da Tsausayi ne karfa ki Manta Ke kika Haifi Zain da Cikinki ammh baki Taba Dubansa da Kallo Uwa da D'anta ba ko Sau Daya ba..?haba don Allah koda Aisha ke miki kara ai batace karki So Abunda kika Haifa ba ko... ? Yakamata ki Sausauta ma Zuciyarki Don Allah.." Umma ta Dukar dakai Tana Fadin"Don yana D"ana saboda Farincikinsa sai na bari Rayuwar marainiyar Allah ta Gurbace..? Kun Taba Tunanin Wani Hali yarinyar nan take ciki game da Abunda ya aikata mata..? Kun taba auna ya Girman cin Amanar wanda kafi yarda dashi yake..? Tana matsayin matarsa fa wacce ta Dauki Dukkan wani Son Da kauna da yardanta ta bashi Rana tsaka ace yana Tarraya da wata Harda Ciki..? Taya a matsayinta na mace mai Rauni Zata Dauiki wannan..?yarinyar nan kwana take kuka bata Cin Abinci bata Barci Saboda shi..? Shikenan don yana Namu bazamu Nuna masa Kuskuransa ba..? Bazan janye maganata ba sai nabi mata Hakkinta ya Saketa Ta zama Bata da Nauyin Kowa akanta Shi kuma ku aura masa Dadironsa Tasa su Cigaba da zama da ita ya zaba.."Umma nagama Fadin haka Ta Raba ta Jikin Hajiya Zata wuce sai Suka Hada ido Da Dina Dake tsaye tana mata wani kallo Sai yanzu ta Fahimci komai kenan Nene ba Shakikiyar uwa take ga Zain ba Umma ce mahaifiyarsa kuma Uwar Rikon Halima Shine yasa zata Kirata yar zaman Dadiro Lalle nema Kallon kallo sukama Juna Kafin Umma ta kauda kai ta Wuce Dakinta Tana Jin wani irin Takaichi da bakinciki in Taga Dina agabanta. Kowa afalon sai Lokacin Yaga Dina Bayan kuma mganganun Umma sun kashe musu Jiki Zain ma ya ganta Kallon kallon sukayi ma Juna cikin wani yanayi itama mai kallo So da kauna da kuma Muradi mai Girma Shi kuma yana Binta da wani kallin Tsana wanda yake jin yana Fitowa Daga karkashin Ransa Da farko Baya Jin yana Tsanar Dina ammh Tabbas yasan ba sonta yake ba kuma Wata Cikakkiyar Sha"awa game da ita baya Jinta sai dai kawai wani Abu ne da zamu kirashi kaddara Daga baya ya Fara Sha"awarta Sosai wanda in bai je gareta ba yake jin kamar zai Mutu ammh Tunda lamarin nan ya Faru yaji komai ya Fara Fita kanshi,Baisani ba Tun mganar daya Fadama Alhaji Tsoho ya Fahimci Dina bata bar mai Jika Haka Kurum ba, ya Dage da addu"a kuma Shima ya gayamai ya Daina Sakaci da addu"a wannan Dalilin Shi ya Raunana Sihirin Jikin Zain wanda Alhaji Tsoho ya Lalatashi Domin Zain yazo Wajensa yana bashi Ruwan addu"a wanda akayi Acikin Ruwan zamzan yana Sha,ayanzu ma Haka maimakon yaji wani Abu Daga gareta sai kawai yaji wata sabuwar Tsanarta Tana Huda Birnin Zuciyarsa yana Tunanin komai ya Faru dashi ayau itace Silan komai. Kowa Bin Dina yake da kallo Haka kowa da nashi Tunanin akanta Itama Tsaye take tana kare musu kallo ko kunya bata Jiba,Haka ma Zaina Dake Labe Take kallon Dina Sai dai bayanta Take gani Tunda tabama Fuskarta gaba ne ba Baya ba Haka kurum Taji cewa itace Tunda ita kadai bakuwa awajen Ballatana yadda Taga kamar Zain na kallon Barayin Datake Duk da kallon na Tsana ne ammh hakan bai saka Zaina ta iya Fahimtar komai ba Tana kallonsu Hawaye na Bulbulowa Ta Cikin Idanuwanta bata da kwanan Amin sai dai kawai ji Tayi Umma ta sakar mata Rankwashi atsakar kanta kana ta Dago a Firgice Taga Umma gabanta Tana Auna mata da Wata Uwar Harara Kanta ta Dafe Tayi Kasa da kanta Tana Hadiye kukanta. Cikin Takaichinta Umma tace"Uban wa kike leke..? Kuma kukan mi kike..? Saboda nace ya sakeki kike labe kina kallonsa kina kuka...? Da Sauri Zaina Tace"Ah..Ah Allah ni bashi..Bashi nake kallo ba.."Cikin Bacin rai Umma tace"Uhm...Kin zata bansan Halin da kike ciki bane..? Ina Kokarin kwato miki yancinki kina Kokarin ni kuma ki bani kunya ko kuma nace ki Nuna min iyakata ko..? Zan cire Hannuna akan Lamarinki Sai ki je chan ki koma Mai ni kam ba Ruwana Tunda Har yau har Gobe bai bata miki ba ahaka kike kukan Sonsa da Tsausayinsa.."Umma Ta gama Fada Cikin Sababinta. Da Sauri Zaina Tace"Allah Umma ni ban ce zan baki kunya ba..Kuma zan karbi Duka Abunda kika Yanke da Hannuna Duka Biyu kece Uwata Harda Ubana Umma Taya zan Baki kunya..? Zaina Ta Fada Tana kuka Umma Taji Dadi ammh bata nuna mata sai kawai ta Shige Cikin Dakin Tana Fadin"Ki koma ki samu wuri ki zauna ki koma maida wannan Hawayen naki Don banga Dalilin Fitarsu ba..Yanzu zan kawo miki abinci kici ki kwanta Allah sa kuma ki Cigaba da kukan naki..." Sum sum Zaina ta wuce ta zauna kan Wata Kujera kwara Daya Dake dakin Umma ta maida kanta kasa Tana Hadiye kukanta Lokaci Daya da Share Hawayenta Kallonta Umma Tayi kafin ta Girgiza kai ta Bude Kofar Tiolet ta Shiga ta Rufo. Achan Falo kowa ba wanda yabi ta kan Dina sai Nene wacce ta kalleta Tana kakalo Mirmishi Take Fadin"Kina Bukatar wani Abu ne yata..? Cikin wani irin kallo Dina Ta Rausayar da kanta kafin tace"Nop..Sai dai ina Bukatar hollandian mai sanyi Domin bana iya cin Komai in ba ita ba..Komai naci bai zama acikina sai na amayar dashi.." Tafada Cikin wani Salo Lokaci Daya Tana Shafa Cikinta Tana kuma kallon Zain Lokaci Daya Tana wani kashe mai ido Daya Kowa kuma ya ganta Haddir Dake zaune bai ji wani mamaki illah wani sakaran kallo Daya Bita Dashi Zain kuwa Takura yayi ya mike kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa Kawai ya Juya da Sassarfa ya Fice Daga Gidan Haddir ya Tashi zai Bishi Hajiya Mama tace"Kai ina zaka tafi ka barni..? Dawo yanzu zamu tafi.." Bai yi mgana ba yace"Ki sameni a waje kawai.."Yafada Lokaci Daya yana wucewa da Sassafar Duk Saurinsa bai cimma ba Zain ba yana Fitowa Haraban Gidan Motarsa na Ficewa sai kawai ya koma Jikin Motarsa Yana Latsa wayarsa ammh Cikin Ransa Damkan da Damuwa da kuma Tunanin wani zama zai Gudana da Dina da su Umma acikin gidanan. Nene ce kadai tace"Allah Sarki..Bari a samo miki ai sai a hankali.."Tafada Lokaci Daya Tana kallon Zainab kafin tace"Zainab jeki ki Dubata Cikin Fridge din Kitchen Nasan baza a rasa ba.."Ba yadda Zainab ta iya Dole ta mike zuwa Kitchen kana Dina Ta Juya Tana Fadin"Ta kawo min ina ciki..Plz ta Hadomin da Cup..." Tafada Tana Juya mazaunanta Zuwa Cikin Dakin Har ta Shige suna Binta da kallo sai da ta Shige ne Hajiya mama tace"Tabdijam...Allah ya Shirya..! Nene tace Ameen Zafeera kuwa baki Ta Tabe Tana Fadin"Dama duk wanda ya sai Rariya Daman yasan zata Zubda Ruwa.."Daga haka ta mike Zuwa Dakin Umma ta samu zaina Inda Ta zauna Tundazu ammh Ta Daina kukan sai na Zucci Tana ganin Zafeera ta sakarmata yake Tana Fadin"Tafiyarki inaga sai gobe ko..? Zafeera tace"Eh mana...Kinga na manta Dazu ban dauko karamar Jakar da nazo da ita ba achan Dakin.."Zaina tace"Kije ki Dauko mana.."Zafeera Ta mike Tana Fadin"Yanzu kuwa ina Umma..? Zaina tace"Tana Kitchen inaga.."Daga Haka Zafeera ta Fice sai da ta Fara Lekawa Kitchen Taga Umma ne ke Zuzzuba abinci Cikin Kololi Zainab kuma na Gefenta Tana Taimakamata kenan har ta kaima Hakimar Sakon nata,Falon Ta kallah ba Kowa Hajiya mama na Shashen Abba Nene kuma Tana Dakinta Juyawa Tayi zuwa Dakin da sallama Ta Shiga lokaci Daya Tana Tura Kofar Zaune kan Gado Dirshan ta isketa tana waya Gefe Daya ga karamin Farantin da Zainab ta Doro mata Holladian din da Kuma Karamin Cup. Dagowa Tayi Tana kallon Zafeera da Manyan Idanuwanta Itama ta sakar mata nata Batare da Tayi mata mgana ba ta Nufi Wardrope ta Bude ta Dauki Karamar Jakarta Gabda Zafeera Zata Fice ne ta Saka baki Tana Fadin"Hy ji mana.." Da kamar bazata Waigo ba sai dai ta waigo Tana kallonta Cikin yanga Dina ta katse wayar datake da Hajiya Maimun ta Kirata Taji ko sun kai tace suna Hanya ammh sun kusa,Lokaci Daya Tana Fadin"Arm...Zaki Kwashemim kayana dake cikin Akwatunan ki jera mim Cikin wannan Wardrope din Cos bana juran Daukan kaya Cikin Akwati and,kuma akwai Jakunkunana da Shoes dina suma ki samar musu matsugunni da kuma Kayan Shafa ne suma ki Jera min su...".. Cike da Mamaki Zafeera ke kallon Dina kafin ta Nuna kanta Tana Fadin"Wai ni kike nufi..? Cikin Gadara Dina Tace"Yes..Ke mana..Ko agida bana aiki da kaina yan aiki kemin komai so nan Gidan naga kamar baku da Masu aiki ke sai kiyi min mana Kodin albarkacin Son or Dota Dinki Dake Cikina.."Tafada Tana Shafa Cikin,Zafeera Ta karkace kai Tana ganin Bariki kafin ta saki Mirmishi Tace"Lalle...Kin Fado..Allah rabani da zama Uwar Abunda ke Cikinki..Kuma wannan aikin Dakike mgana ki Daga waya ki kira wanda yayi Miki Cikin Shi sai yazo yayi miki Aiko Darajan Abunda ke Cikin naki...Idiot.."Daga haka kawai ta saki katon Tsaki ta Fita Daga Dakin Ta Bamgo kofa da Karfi Wata Dariyan Shakiyanci Dina ta saki Lokaci Daya Tana Fadin"Dole ko soshi..Tunda Jininku ya Digashi.." Da wannan Takaichim Zafeera Ta koma Dakin Umma Ranta bace,Ta iske Zainab ta Shigo Da Farantin Abinci nan suka Hadu suka ci Zafeera na gayama Zainab yadda suka Kwashe da Dina Zainab Tace"Lalle nema...Gaskiya yarinyar Shegiyar kanta ce.."Zafeera tace"Allah yayi miki Tsari da zama da Karuwai Zainab...Yarinyar ta sangarce gata kyakyawa ammh Kyanta bai amfaneta ba Allah ya kyauta Gobe goben nan zan koma kano.."Zaina na Jinsu bata ce komai ba Zuciyarta Tatafi da wani Tunani Taya ya zamanta zai kasance acikin Gidanan da wannan Mara Tarbiyan..?lalle akwai zama kuwa indai Hakane..! Hajiya Mama tajima kafin Tatafi sai da ta kara kwantar ma da Abba Hankali ta kuma Umarci Nene kan Karta damu da komai ta kula Da Dina,Nene ta amsa mata da Insha Allahu Umma tayi Tayi ta tsaya taci abinci ammah Taki Dole suka kyaleta Har Haraban Gidan suka Rakota kafin Haddir ya Dauketa Zuwa Gida Suna komawa ta Labartama Alhaji Tsoho Duk Abunda ya Faru ta kara da cewa"Ka kira Fatima ka Tsawatar mata gaskiya...Ka kuma gayamata ta bama Zainullahi matarsa kada Zaluncin yayi yawa..". Alhaji Tsoho ya Murmusa Kafin yace'"In kirata nace me..?bayan Ta Riga ta Rantse so kike na sakata Tayi kaffara Aminatu..? Hajiyaa Mama tace"Eh...Ai tayi gaggawa ne..Kuma gaggawa Dama ai yana Tare da Danasani.."Alhaji Tsoho yace"To bazan yi kuwa haka ba...Tana Ganin Girmana bazan bari ta Daina gani ba Duk da nasan in na Kirata da kaima zata janye mganarta bazan yi haka ba..Ki barta Komai tayi Daidai ne,ai Uwar Halima Take na kuma ji Dadi da Nuna ma Duniya ita Uwa ce mai Adalci da sanin ya kamata.." Cikim Mamaki Hajiya Mama tace"Au Kaima kana goyon bayan Ta Raba auran yaranan..? Alhaji Tsoho yace"Ni ban ce ba...Dama waya isa ya Rabasu..?babu sai Allahn daya Hada Abun..Ki kyaleta Ta sauko yanzu Tana Cikin Fushi ne da Takaichin Abun kiyi mata Uzuri Abun yayi mata yawa Uwar Halima ce kuma Uwar Zainullahi in Ta Dauki Bangaran Zainullahi za"a ce saboda D'anta ne yanzu kuma Data Dauki Bangaran Halima sai muga Laifinta..? A"a ku rabu da ita ta Huce zuwa bayan Bikin Hamdiya ni da kaina zan saka akiramin ita Daga ita Har Usmanun Na sakasu Daki na Jawo Hankulansu yadda zasu Fahimta." Hajiya Mama ta gyada kai alamun gamsuwa Tana Fadin"Kuma fa hakane..Allah ya kaimu ai bikin ma yazo Jiya da mukayi mgana da Hannatu tace nan da kwana Goma tana Tafe.."Alhaji Tsoho yace"Eh..dazu Aliyun ke Fadamin Sauran Sati Biyu munyi mganar kawo kayan Aure Da yace nan za"a kawo ma hanashi nace yabama yan"uwan ita Safiyan Dama suje chan Abuja su karba.."Hajiya Mama tace''Hakan yayi Allah sa alheri.."ya amsa mata da Ameen Ameen kafin su cigaba da Hira. Haddir kuwa bayan ya Ijiye Hajiya Mama Gidan Zain ya wuce yaje chan ya sameshi Cikin Damuwa shi ya Dinga bashi baki kan yayi Hakuri Umma bazata rabashi da matarsa ba Cikin Tsinkewar Zuciya Zain ya kalli Haddir yana Fadin"Umma fa Har Rantsewa Tayi kan sai na saki Firstlove Haddir.." Haddir yace"Kai kuma sai ka saketan..? Zain yace"Sai dai in tace Zata Tsinemin zan saketa ba Domin ina Tsoron Tsinuwan ta ba a"a sai Domin nasan bazan kara Wata Rayuwa mai tsawo ba Tunda ban Ji Dadin Duniyar ba gwara na Rabu da Iyayena lafiya In naje lahiran Allah ya bani Dacewa.."Haddir ya kallesa kawai batare daya Kara mgana Shi zai iya Dafa Qur"ani ya Rantse Zain yana yi ma Zaina wani So ne wanda bai san iyakarsa ba ya sanshi Farin sani kamar yadda yasan kansa Zain ba Bukatu da kuma muradin wanda yake Girmamwa Fiye da na Zaina wanda Abunda ya Faru zai Dorashi matsayin kaddara da Kuma Shiga abokai Barkatai. Zaina kuwa Dasu Zafeera na Dakin Umma basu kara Lekowa ba Umma kuma Tana Dakin Abba chan zata kwana Nene ce keta Dawaniya Da Dina Da Daddaren Tuwo Zainab da Zafera sukayi Miyar Kubewa Danya Saboda Abba naso,Dama Tun bayan Rasuwar Maryama Su Umma basu kara Daukan wata mai Taimakonsu ba suka Hada Hannu suna Girkinsu ita da Nene Tun kafin yaransu su kawo Jiki bayan Girman Zareena ne ta karbi iyayanta Har Zuwa auranta Gefe Daya su Zafeera suma suka Taso,ga kuma Zainab,Mazan kuma dama ba wani aiki suke ba kuma Dukkansu ba anan Garin sukayi karatunsa ba sai dai indan Sunzo Hutu,Bangaran Girki bama su Rabashi Kowacce Yi take,Shashen Abba ne kadai suka Raba Tunda wannan ya zama Dole in Umma Tayi kwana Biyu Nene Tayi Biyu Shiyasa Gidan Abba babu Babban Teburin Cin Abinci ma"ana Dinning Saboda Koda wani Lokaci ba"a haduwa gabadaya sanda zasu kamallah na Rana yara na makaranta na Dare ma suke Taruwa suci afalo wani Lokacin Daga baya ma sai dai kowa ya Debo nashi barin ma da Gidan ya watse su Zain suka Tafi London da sauransu gaba gaba kuma suma su Sadiq suka Watse gidan duk sai yayi Rakwa Rakwa Kuma ba Dole bane sanda wannan ke gida wannan na nan Shiyasa basu Damu da Hadakan cin Abinci ba gaskiya Duk wanda yaji Yunwa yaje kitchen akwai a kula Abba ne kadai ake Shigar ma da nashi Falonsa Ranar kuma Dayake jin Nishadi abaje mai Darduma yaci a Falo Cikin Matansa da Ya"yansa. Nene da kanta ta kaima Dina nata Farantin Dinner ammh Tana ganin Tuwo tace ita kam Batajin Tuwo sai Dai adafa mata Maroconi da Kifi Nene batayi kasa agwiwa ba ta saka Zainab na Tura baki Tana komai ta Dafa mata sai da aka gama tace Bata ma son kamshinsa Fura Take so Tashi Nene ta Fita ta bama Direban Abba sako Yaje ya amso mata kana ta Karba Tasha Umma bata man san Wainar da aka Toyaba sai da Safe Zainab ke basu Labarin Abunda ya Faru domin agabanta komai ya Faru mamaki ya kama Umma Tana Mamakin Nene wani Lokacin Datake Daukan irin wannan Iskancin. Tun Safe Zafeera tayi Shirin Komawa kano Motar haya zata Bi,Tagama sallama da Kowa Har Abba ma ya sallameta Direban Abba ya Dauketa Zuwa Tasha Bayan tace ma Zaina sai Bikin Hamdiya zata dawo Da zata Tafi suka sarke Hannun Juna Zaina Harda Hawaye. Ganin Abba ya Fito Cikin Shirin Office Zainab yake kwalama Kira Ta Fito su ijiyeta makaranta Tana da Test da Safanan,Sai ga Nene ta Fito Daga Dakinta Tayi Wankanta ta Shirya Cikin sakin Fuska Ta gaida Abba ya amsa yana kallonta,Daganan Dakin da aka Sauki Dina ta Shiga ta isketa Cikin Bargo Tana Sharan Barci Domin Ko sallar asuba ma batayi ba. Tashin Tayi Tatashi Tana wani Tura baki Cikin Lallabi Nana tace Tatashi ta sa sauya kaya tazo  Ta gaisa da Abba zai Fita Tunda Jiya basu Hadu ba kamar tace bazata jeba sai wata Zuciya  ta kwabeta da Cewa Mahaifin Zain fa wanda ya Haifan miki Abun Sonki kuma ko Banza Taga Nene na kula da ita ba kamar Umma da Sauran kannen zain din ba Tashi Tayi Cikim kasala ta Fata Tiolet tayi Brush ta Dauro alwala tazo tacr bari Tayi sallah Nene ta cika da mamakin karfe 8am na safe dan Musulmi ke sallah Lalle Duniya Sallar ma nata Yar faki ce Tayi kuma da Wani mayafi ta Nade jikinta kan Kayan Barcin Dake Jikinta Riga da Wando masu kauri,Nene taso ta sauya kaya ammh Dina taki Tama yi gaba ta bar Nene na Binta da kallon Mamaki. Abba na Shirin Barin Falon Zainab na Binshi abaya da Jakar Briecafe dinsa,Umma na Falon itama  Yaji Muryan Dina na gaisheshi Ya waigo yana kallonta Cikin mamakinta ganinta Tsaye sama da kasa ya kalleta kana ya iya ganeta Cikin Sauri ya amsa mata bai ma Tsaya Sauraran Nene dake mai wani Bayani ba yace sai ya Dawo Zainab ta Rufamai baya Umma kuma ta kada kai ta koma Dakinta Ta gani Zaina Ta Fito Daga Wanka Nene kuma Tayi Tsuru kawai Dina kuma Mika Ta saki kafin Ta Tabe baki ta koma Cikin Dakin Har Cikin Ranta Tana Jin Haushin Yadda Nene ta Takura mata ta katse mata Barcinta mai Dadi kan Gadon Ta koma bayan ta Cire Mayafin Data yane kanta Dashi Ta koma ta kara Lafewa bisa filon. *Ina godiya da Sharhinku Both Wsop da wattpad..Keep it Up* *Janafty..* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*                  2️⃣7️⃣ "Ranar dai Nene Tayi ta Wahala da Bukatun Dina wani Lokacin ma har da iskanci acikin Lamarinta ammh bata nunawa saboda Ita babba ce kuma Bazaka Biye ma Mara Tarbiya ba Ballatana sanin ya kamata ba. Sai wajen 10am tatashi tayi wanka Breakfast din da Nene ta kawo mata bata ci ba Doya da kwai ne sai Tea da Dankali Tace bataci wai amai yake sakata Don Tsirfa waina Fulawa tace zataci Haka Nan Nene ta Fita ta Soya mata ta kawo mata ko kunya kuma ta karba ta Tsakura kadan Tabar kwanukan nan ta Tsallake ta koma kan gado Ta Fara Dannan waya Kayanta kuwa nan Gegen gado Ta Zubesu Data Bude akwatin zata Dauki Kayan da zata saka Ta saba agida komai zulai ke mata Shiyasa ta Tsallake ta bar komai haka Kila Tana Jiran Nene ko Umma su gyara mata ne Tunda Zafeera dai ta kara gaba Zainab kuma ta Shiga makaranta. Zaina kuma Tana Dakin Umma ko Lekowa Falo batayi ba Umma ce kadai ke Zirga Zirga Tsakanin Falo da Kitchen,Misalin karfe 12pm na rana Umma Ta gama Miyar agushinta Sai Taji kanta na Sara mata sai ta bar ma Nene Tuka Tuwon Shinkafan Tace zata Daki tasha mgani ta kwanta,Nene ta mata Allah ya kara lafiya ta karbi aikin Tana Zuwa Daki ta iske zaina ta Tsiri aikin Saka mata goggun kayanta da Jiya mai wanki da guga ya kawo Cikin Wardrope taji Dadin Ganinta ta saki Jikinta Yau watarana zaina bata kuka Sannu da aiki zaina tayi ma Umma itama Tayi mata,Wayar Umma ce tayi kara Zaina na kusa da ita ta Miko mata Tana Fadin Zafeera ce. Bayan Umma ta Dauka sun gaisa tace mata ta isa Tun dazu..Yanzu ma tana Cikin makaranta Fatan Nasara Umma Tayi mata kana suka yanke Kiran Tiolet Umma Ta Shiga Tayi wanka kana ta aiki Zaina Zuwa Kitchen ta Dauko mata Ruwa Ta sha mgani Ta kwanta,Bayan Zaina ta gama Jera ma Umma kayanta Cikin Wardrope dinta sai ta Rage mata Karfin A.C ganin ta Fara barci ganin kar zamanta ya Dameta sai ta saka wani bakin Vail Samam bakar abayan Dake Jikinta,Jiki ba kwari ta Fita Zuwa Falo wanda Tun Zuwanta Gidan batace ga Ranar da Ta fita ta zauna afalo ba. Sai da ta Leka Bataji Motsin kowa ba Kana ta Fito Falo Tana kallon Kofar dakin da aka Sauki Dina Shuru kamar ba kowa agidan,Su saudart suna makaranta adofane ta zauna kan Daya Daga Cikin Kujerun falon Tana Raba ido Bata so Dina ta Fito Ta ganta ba saboda komai ba Sai Domin kauce ma Haduwarsu,domin Zuciyarta bazata iya Juran ganinta Dauke da Cikin Firstlove ba. Cikinta ta kura ma Ido Tana Jin wani Shaukin Sonsa na kara Shigarta Da Tsausayin kanta Dana Firstlove wanda Tana da Tabbacin in Umma ta san da wannan Cikin bazata barshi ba ita kuma mai yunkurin Rabata Dashi Sai inda karfinta ya kare.! Bata ji Shigowarsa ba ballatana Sallamansa ba Tadai ji kawai Kofofin Hancinta na Shako mata kamshin Turaransa wanda ko Mutuwa Tayi aka Dawo da ita zata iya Shaida mai irin wannan Kamshin Cikin Mamaki Ta Dago kanta Karaf kuwa Idanuwanta suka Sarke Cikin Nashi yana Tsaye agabanta Sanye da wasu Ubansu Ameriacan Suit Masu kalan Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Nektie,mai Ruwan Toka kafarsa Tana sanye da bakin Takalmi Booth Hannunsa kuma Sanye da agogon Fata na kamfanin Rado Akallo Farko in kayi zaka ji kana marmarin kara kallonsa Saboda yanayin kyawunsa da Haiba sai dai in ka kura mai ido zaka Fahimci Baya Cikin Cikakkiyar natsuwarsa,Ya Rame Wuyansa ya Fito Haka ma Fuskarsa sai idanuwana da karan Hanci Kasumba ta Cikamai Fuska wanda abaya Saje ne kawai Zagaye da karamin Bakinsa Sabanin yanzu da ba gyara sai duk ya zama wani iri gashi nan ne. Yau tun Safe ya samu Kiran Gaggawa Daga asibiti,Wata mata ce zata Haihu kuma Jini ya yanke mata ya isa ko Fara Duba patient din bai ba Allah yayi mata Rasuwa ita da Abunda ke Cikinta Domin ta Rasa Jini Sosai Abun ya Tabashi Sosai Haka ya koma Office dinsa ya zauna Sukuku Dama Jiya kwana yayi bai yi Barci ba,Sallah yayi bayan ya Idar ya koma Tuban ma Allah gefe Daya ga Zullimin nganar Umma da Abun ya kwana aranshi,Kawai yaji ba wacce yake son gani Sai Firstlove agogon Dake Hannunsa ya Duba ya Tabbatar da yanzu Abba ya Tsufa awajen aiki,Ya yanke Shawaran zuwa yau ko ta Halin kaka sai yaga Matarsa ko da Umma zata Dakeshi ne. Shine yana Shigowa Falon kamar almara yaci karo da Zaina Zaune afalo ta kurama Cikinta ido,Farinciki yaje ji ko me bai sani ba kawai Ido ya Zuba Mata yadda itana ta sakar mai nata Idanuwan Hannuwansa na Cikin aljihun wandon Dake Jikinsa,kallonta yake da wani Managadisu Tare da Sonta da kaunarta kallon Ban Hakuri karki barni kallon Sha"awa kewa da kuma Muradi ita kuma Idanuwanta ne suka Tara kwallah kallon meyasa ka Cutar damu..?kallon Tsausayinsa kallon Soyayyarsa da kaunarsa kallon Girma kima Tare da wani kewa wanda Bata Taba Tsammanin zai yi Faruwa da ita ba. Hannunta kawai Taji ya kama ya Mikar da ita tsaye Kur tamai da ido Tana kallonsa bai Tsaya Bata samu zarafin mgana ba Taga ya Fara janta suna Tafiya yana Rike da hannunta,Ganin sun Nufi Dakin Umma yasa ta Kwalalo ido Waje Cikin Tsoro da Rawan Jiki Tace"Umm..Umma...! "Shiiii..." Ya Fada ba tare da ya Waigo ba sai ya sauya akalarsa zuwa Dakin Nene kamar wata Rakuma da akala haka Take Binsa Nene Dake Kitchen Taji kamar Motsi ta Fito kenan Taga Zain Rike da Hannun Zaina sun Shige Dakinta baki ta Rike acikin Ranta kuma sai Taji Dadi Cikin Sanda ta leka Dakin Umma Ta ganta kwance Tana Barci da Sauri ta Fito Tana Fadin"Haba...Naji Dadi ya samu Lokaci da zai gana da Matarsa..Haba Duk kin wani Takura ma yaro kin Hanashi kwanciyar hankali.."Tafada Tana kyafci Lokaci Daya Da komawa Cikin Kitchen din Ta Cigaba da Abunda Take yi. Suna Shiga Dakin Nene Ya Saki Hannun Zaina ya Murza ma Kofar key Cikin Rashin Fahinta zaina ke kallonsa kafin ma ta samu Zarafin mgana Taji sa ya Fado Jikinta Cikin wani Irin Rumguma mai karfi ya Rumgumeta Saura kadan ta Fadi Dakyar ta iya Daidaita kanta Bayanta ta saka Hannu Ta Dafa Gefen gadon Nene... Irin yadda ya sakata acikin Kirjinsa ya bata Tsoro,Matseta yayi ya Kamkame kawai Taji yana Sakin Numfashi Sama sama Kamar wanda zai Shide,kansa yake Tusawa Cikin Wuyanta Yana kara kamkameta kamar zai maidata Cikin Jikinsa,Tana Jinsa Kuma ta Fahimci Komai ban Hakuri da yarensa Numfashinta Take son Fizga ganin ya matse mata Wuya Yasa ta Fara mutsun mutsun Kwace kanta ammh yaki Sakinta sai ma kara Riketa Da yayi kam kam kamar wani zai kwace masa ita.. Ganin Ta kasa kwace kanta ne yasa ta Rabu Dashi kawai ammh Zuwa Lokacin Itama Rauninta ya bayyana Hawayenta kadai ke Zuba daga kwaryan Idanuwanta,Sai da suka Shafe wajen Mintina Goma ahaka kana ya Saussauta Rikon Da yayi mata Kafin kuma ya saketa lokaci Daya yana kallonta yadda Hawayenta ke Zuba Shima kukan Zuccin yake Domin Idanuwansa sun kala Sun Jajir kamar gawarshin Wuta. Tattausan Tafin Hannunsa ya sanya ya Dauke mata Hawayen Cikin Wani Raunin murya yake Fadin"Haba Firstlove..? Me nayi miki da Zafi da yasa kika Tsane ni haka..? Kin manta Ni dake mun Fadama Juna kafin Dayanmu ma yayi Laifi mun Riga da mun yafe mai..? Amh Why ki ke azabar Dani alhalin kinsan duk Duniya ba wacce Nake so da kauna sama Dake..? Yafada yana Rike da Fuskarta da Hannuwansa Duka so Take ta Bude baki tace me"Ita wacce kayi ma cikin fa..? Ba sonta kake yi ba..? Sai dai kuma ta kasa bakinta yayi mata wani irin Nauyin Data Kasa Furta komai,Runtse ido Tayi Hawayenta na Zuba kawai Cikin Fitan Hayyaci ya Jijjigata yana Fadin"Ki Bude idanuwanki ki kalleni kiga yadda na koma saboda Rashinki..Duk na Rame na Lalace Wlh Firstlove in baki Dawo Gareni ba kina gabda Rasani kin ji ma na Rantse miki.." Da sauri ta Bude Idanuwanta Tana kallonsa Idanuwansu suka Narke cikin na juna cikin wani yanayi ya Cigaba  da Fadin"Nasan Zuciyarki na Cike da Tsanata kan Abunda na aikata ko..? Me zan ce miki Firstlove Wlh Tallahi Har ga Allah ke kadai ce macen Da nake so kuma ke kadai nayi Burib ki zama matata,Dina tana Cikin Kaddara tane ammh ita kanta ta sani ban Taba Sonta ba...Ke nake so ke na kallo amatsayin Mace ke kadai ke sakani kukam kukan jin Dadi Firstlove Wlh Bata Fiki komai ba...Kin Fita komai Bata kai ki ba...Don Allah Firstlove Kada ki Dubi Tarin Laifukana Ki yanke min Hukunci Don Allah kiyi Hakuri kada ki bari Ummanki ta Rabamu plz...! Yafada Kwarmin Idanuwansa na Cikowa da Hawaye,Tuni Zaina ta saki kukan Data ke Rikewa Tana neman Dukewa a kasa Saboda kuka ya saka  hannuwansa Duka Biyun ya Tareta Lokaci Daya ya sakata Cikin Jikinsa,ganin irin kukan Data keyi ya Rurumai wutar wani Abu acikin Ransa Kawai sai ji tayi Ya Tallabo kanta Idanuwanta ta kara Runtsewa saboda jin yadda ya saka Bakinsa yana lasan Hawayenta kafin ya Dire Bakinsa kan Lebenta yana Sucking Cikin kwarewa da kuma Rawan Jiki kamar yadda Itama Zaina Jikinta ya Fara wani irin Rawa Kana ganinsu kasan Gabadayansu Suna Cikin wani yanayi Batare data sani ba ta Bude baki ta yi Ihu kawai Taji ya Zura Harshensa Cikin Bakinta ya Fara mata wani irin Sumba Sumbar da bai Taba Mata ba yawo kawai yake da Harshensa,Lokaci Daya yana kara Riketa gam acikin Jikinsa ganin Tana nenan Faduwa Ammh Duk da Haka Jikinta ba Karfi sai ta kara yin wani luu ammh haka ya Bita suka Tafi suka Zauna saman Cafet din Dakin Nene yana kamkame da bakinta gam yana mata wani irun Sumba Yana kuma kallon Idanuwanta Cikin wani Shauki. Ya Damke Bakinta ganin bata iya kwace kanta yasa Kawai ta Sakarmai Ragaman komai,ganin ta Saki ne yasa ya Saka Hannu ya Janye mayafin Data yane kanta Dashi Kalaban Dake kanta Suka Zube Duk da Kitson ya Tsufa Domin tun kafin Faruwan hakan Tayi shi Ammh kuma Tana wankeshi Saboda yayi mata Nauyi har wani Tashin Tashin Warin Daula yake yi ammh Shi bai Damu ba sai ma Shinshina kanta Daya Farayi da Hancinsa ammh ya kasa sakin bakinta sai da yaga Dama kana ya Saki bakin nata Bayan yaja Leben nata kamar zai Tsinka matashi Kirjinsa kawai ta Fada tana maida Numfashi Shima Sai ya Rumgumeta yana maida Nunfashi Lokaci Daya yana Shafa Bayanta Zuwa Kugunta Kokarin Tashi Take daga Jikinsa yaki sakinta Sai kawai ta Shammaceshi ta Turashi baya yayi kamar zai Fadi ta Fizgi kanta ta Mike da Sauri Shima ya Mike ta Duka Zata Dauki mayafinta Taji Hannuwansa Dumu Dumi kan Boobs dinta ya Rike da karfi yana wani matsa matsawa Cikin kwarewa da kuma wani irin Muradi mai Girma... Mikewa Tayi tana kokarin kwace Kanta ammh sai ma ya samu Damar saka kansa Tsakanin Wuyanta Lokaci Daya yana Matsan Boobs Dinta Da karfi Karfi Kuka kawai ta Fashe mai Daahi Har Muryanta na Fita Ita Tsoronta Daya kada Umma Tazo ta gansu me zata ce mata..? Umma bazata Kara yarda da ita ba Ga kuma Abubuwan daya ke mata Suna Rikitata so yake ya saketa Ammh yaki Sakinta Har sai da ya kara kaita kasa bata Fargaba Taga yana Kokarin Zare mata Rigar Jikinta kana ta Daddage ta Gantsaramai Cizo a Kirjinsa wanda yasa ya saketa da Sauri Ganin ya saketa Ta Yunkura Tatashi da Uban Sauri ta Rarumi mayafinta ta koma Gefe Tana Kuka,wani kukan mai Tsuma Zukatan mai Sauraro. Inda ta Cizeshi ya Shafa yana mata Wani irin kallo kafin yace"Baki Taba min irin wannan Cizon ba Firstlove..zo ki yi Ta Cizona indai zaki Huce kuma ki biyoni mu koma Gidanmu.."Yafada yana Mikewa Kamar zai kamota Tayi Saurin Ja baya Tana wani irin kuka Kura mata ido Yayi kafin ya mika mata Hannu yana Fadin"Taho...Taho Firstlove don karki kiki Tahowa gareni..Taho mu koma Gidanmu..Na Yarda Muna Zuwa Gidanmu ki kulle ni acikin Dakina kiyi ta Dukana Har sai kin Huce indai zaki Barni kuma Ki zauna dani na yarda na amince.." Yake Fada kamar yayi mata kuka,Tana Kallonsa Tana ja da Baya Cikin Kuka Da Tsausayinsa Take Fadin"Aah....Bazan iya ba..ba zan iya ba.."Tafada Lokaci Daya tana Juyawa Ta Bude Kofar Tiolet ta Fada da Sauri ya Bita sai dai yayi Rashin Sa"a Ta Riga ta Saka Makulli Jikin Kofan ya tsaya yana ta kwalamai Kira tamai Banza ta Sulale nan Kasan Tiolet din Tana sakin kukanta Bazata iya Binsa ba Ba saboda Laifinsa ba sai domin Umma uwa wacce Tayi mata Dukkan Hallarcin Duniya bazata iya watsa mata kasa acikin Idanuwanta ba. Tana Jinsa ya gama Kiran Nata da Buga Kofar Ya Taka ya Fice Kuka ta kara sakawa Tana Jin kamar ta Bude Kofar ta Bishi sai ba Hali,Kukanta tayi ta Sha abunta Kuka ne na Soyayyah kauna da kuma yanke kaunar duk Lokaci Daya. Shi Kuma zain yana Fita Cikin Wani irin kasala ya Fara Taku zai bar Falon,Yaji Kiran Nene Daga Bayansa ya waigo Cikin Saurin Basar da yanayinsa Kura mai Ido Nene Taayi kafin Tace"Me ya sameka..? Yana Shafa kafansa yace"Bakomai Nene..na shigo kina Kitchen.."Nene ta kada kai Tana Fadin"Eh...Naga Zaka Fita baka Shiga ka Duba yarinyar nan ba.."Cikin yamutsa Fuska yace"Wata yarinya kenan Nene..? Cikin Takaichi Nene Ta mai Dakuwa Tana Fadin"Bansani ba...Toh wacce ka Kakabamana Dole mana Ai kana sane jiya iyayenta suka kawo ta.."Sosa keya yayi yana Fadin"Nene don Allah kyaleta..ina da aiki asibiti Na Tafi.."Baki sake take binsa da kallo Har ya Fice bata samu zarafin mgana ba sai da ya Fita kana Ta kada kai Tana Fadin"Uhmm..! Nene bata koma Dakinta ba sai da Ta gama Kulla Duka Tuwonta cikin leda ta saka Cikin Wata katuwar Kula,Jin ana ta Kira kiran sallah yasa ta koma Dakinta ta watsa Ruwa Tayi sallah sai taga Zaina na sallah sai Lokacin ma ta iya Tunawa da ita Kada kawai tayi ta Shiga Tiolet tayi wanka Koda ta Fito Zaina ta bar Dakin Nene ta Murmusa Tana Fadin"Ta gudu Dakin uwarta kenan.! Umma kuwa sai da Zaina ta koma Dakin kana ta Tashi kan ya Saukar mata Ta Shiga ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan Ta Idar ne ta Zura ma Zaina ido ganin Tana ta wani Dukar dakai kuma Fuskarta ta kumbura kamar tayi kuka Cikin Mamaki tace"Meke damunki..? Da Sauri  Zaina Tace"Ba...Bakomai Umma.."Kuri Umma Tayi mata da ido Tana Nazartanta kafin ta mike tana Fadin"Ke dai kika sani..In ma Kukan nace zan rabaku ne Wlh sai dai kiyi tayi har Hawayenki ya kare bazaki Koma gidansa ba.." Daga Haka Umma ta Sabule Hijabinta ta Fice ta bar Zaina na Kokarin maida Hawayenta acikin Ranta Tana Tunanin da Umma ta gansu yau ai da ta kade har ganyenta. ***** *Bayan Sati Daya..*! Haka abubuwan sukayi ta Faruwa,Acikin sati Dayan bangaran Dina kuwa iskancinta sai Karuwa yake yi kayanta Data Zube sai dai Nene ta saka Zainab ta gyara mata ta Shiryamata kowanne ta ijiye abangaransa,Banda Nene kuma bamai Biye mata ballatana ya san da zamanta Itama Dinar bata Fitowa kullum Tana Daki Taci mai kyau tasha mai kyau sai Abunda ta Zaba shi Take ci Nene ta Daure mata Gindi Bangaran Umma kuwa basu kara ma Haduwa ba kuma kafarta bai Taka Dakin ba ballatana Abba Da bama yasan ganinta Ballatana mganarta Ragamarta komai yana Hannun Nene ne Shi Kanshi Uban gayyah bai Tana Zuwa Inda Take ba,itama Dinar bata Damu ba Saboda Zakiya tace ta bashi Lokaci Zai Dawo gareta. Dina Tana waya da Daddyta da Kuma Hajiya Maimu wacce ta koma Sudan kuma Tayi ma mahaifiyarsu bayanin komai har mgana sunyi da Dinar ta waya ta kara yi mata Fada da Nasiha Wanda bai wai Domin Dina ta Jita bane Yadai Shiga kawai ya Fita,Hajiya Batula kuwa bata Taba Kiranta ba itana ba Damuwa Tayi da ita ba Wayarta Daga Daddy sai Hajiya Maimun sai Zakiya take Doguwar mgana Dasu bayan su Bata da wannan kwaramiyan sai dai Shiga Kafafen yada Labarai Tana Chart dinta Hankalinta kwance Babu Abunda ya Shalleta Nene Bata Taba ganin inda Dan Shege ke zama ado ba sai Wajen Dina Alfahari Take da wannan Cikin Jikin nata wanda Allah ya Taimaketa Bai sakata Laulayi Sosai yanzu Damuwar Dina Daya Rashin sanin makomar Auran Zaina da zain kuma gashi bata ma Jin Motsinta acikin Gidan Fargavanta Daya kada ace Ta koma Gidan Zain dinta wanda bata Fatan haka Zakiya ce ta Lallashe da cewa ta bi komai a Hankali kuskuran kadan Zatayi zata Lalata Duka plan dinsu ta bari zata samu Lokaci Tazo koma miye Sai ta ganoshi kafin Tatafi da wannan mganar ta Saurara da har taso Ta Tambayi Nene Kan Zaina sai kuma Ta Fasa Tunda Zakiya ta kwabeta. Bangaran Zain kuwa Yasha Zuwa gidan in ya Daidaici Abba ya Tafi office Umma kuma Tana Daki ko Tana Kitchen sai ya Rutsa Zaina yayi ta mata magiya yana kwakwumarta,Nene dai ta sani kuma batayi wani abu ba Dagani Tana so ayi ma Ummi Shigo Shigo ba Zurfi ne bata Sani ba Haka zai zo yagama Nacinsa in bai ci Sa"a ba Ranar zaina ko mgana Batamai sai dai ma Ta Hadashi da kokenta,Duk da Haka bai Hakura ba sai ya latsata Don ya nuna mata bazai yarda arabasu ba Wajen kwana Hudu yana yin haka Ranar na Biyar Dubunsa ya Cika Umma Na Kitchen zaina na Dakinta Ta Fito Zata koma Daki Suka ci karo ya Riko Hannun Zaina zai Kaita Dakin Nene Daman nan ne Deport dinsa Daya ga Umma sai ya Dake ammh Zaina kamar tayi Fitsari saboda Tsoro wani mugun kallo Take watsamai Kafin ta Saka Hannunta Ta Fizge Hannun Zaina Ta Bishi Da katon Dundu Sai da Nene Ta Shiga Tsakani Haka Umma ke Fada ta Inda Take Shiga bata nan take Fita ba aka bar Nene da ban Hakuri Zaina kuwa Hannunta ta Fincika Zuwa Daki Cikin Tuhuma Ta kalleta Tana Fadin"Tun yaushe ya Fara zuwa yana Janki aboye ban sani ba..? Cikin Inda inda da Tsoro Zaina Tace"Tun...Tun..Ranar ne Wlh Umma bana so.ya.."Bata gama Rufe baki Umma ta make bakin Tana Fadin"Rufemin baki in baki so zai miki Dole ne..? Daukan ki yayi..? Wato kema munafuka ce bansani ba ko..? In gaskiya ne meyasa baki Taba gayamin ba..? Zaina na Hawaye Ta Bude baki Zatayi mgana Umma ta Sakarmata Dundunaye har guda uku agadon Bayanta Tana Fadin"In kuna Takaman ku yaran Zanani ne nima Uwar zamani ce..Bazan barki ya kara Cutanki ba Tunda ke kam baki da wayau Shashasha mara Tunani kawai.."Daga haka ta Fice ta barta Tana kokenta. Umma Taki barin mgana Ranta ya Baci Har Abba sai da ta gayamawa Tace yajama D'ansa kunni ya daina zuwa ya Horema yarta kunne agabanta ya Daga waya ya kira zain wanda Tun bayan Faruwan lamarin Abba bai Taba Kiransa ba Jiki na rawa ya Dauka ko amsa gaisuwansa Abba bai yi ba ya Sauke mai nashi Jidalin da Fadan Yace ya Daina Zuwar mai Gida ashe bai ji ba..?hala da kudinsa ya Gida gidan..? Daga Karshe yajamai kunni kada ya kara Zuwa gidan Ballatana Har yazo kusa da Zaina Daya na sonta da bai aikata wannan Shanshancin ba ya Dai Jira in wannan Cutar da yayi ma Mutane ta Haihu aka musu Aure ya Dauketa zuwa Gidansa Su Huta.." Ranar Zain yaga Fada iri iri Umma Tayi nata Abba ma Haka Numfashi kawai yake ta Saukewa washegari daya bama Haddir Labari sai da ya kwanta Saboda Dariya Shi kuma bai ga Abun Dariya ba wannan Abun a Tsausayamai ne gashi Firsrlove ya kasa gane kanta ya bata Hakuri kamar ya kwanta mata ammh Daga Dukkan alamu Tana son Goyon Bayan mamarta ne Shi kuma bazai bari haka ta Faru ba,yaji Fadan Abba ya Dauke kafa na kwana Biyu. ******* Yau da Bikin Hamdiya ya Rage saura kwana Biyar Dukkan wasu Shirye Shirye sun kamkama,Tuni an kawo Lefe nan Abuja Dangin Mama Safiya suka je suka karba Achan,Sai Zuwa Gobe zasu iso Yan Chan Abujan Dukkansu Inna Hannatu dai ta iso Da nata gayyar Inna Rukayyah kuma sai Gobe Zafeera ma ta Dawo Duk Yau din Gidan Alhaji Tsoho Suka Tafi Harda Umma da su Saudart Zainab ma bata Shiga makaranta ba Tare suka Tafi. Nene ce kadai agidan sai Zaina wacce Take cikin Damuwa Dazu sunyi mgana Da goggo Halima ta wayar Umma tace tana ta Kiran wayarta bata samu Ta Kira Zain Shine yace Tana Gida Wajen Umma,Shine ta Kira Toh itama Umman ahaka ta bari a Zaina bata da Lafiya Domin bazata ce komai ba yanzu Ta Kira sun gaisa da Zaina kana suka Cigaba da mgana da Umma Har take gayamata Bikin Hamdiya Tace zata zo Insha Allahu Daganan ta Duba Halimar Shine zaina ta Damu bata so Umma Ta tari Goggonta da wannan mganar ko bakomai Ita Mai Rufama Firstlove Sirrinsa ne ba kuma Tasan ya Goggon zata Dauki Lamarin ba Gefe Daya ga Laila Data Dameta Da zuwa kan Ta koma makaranta Ta Fadamata Ta Hakura da Karatu har Abada Tundai Gashi zata Rasa Firstlove. Tana Cikin Dakin Umma Kishin Ruwa ya Fito Da ita Har ta Shiga Kitchen din ta Dauko Ta Fito Tayi Mugun gani Dina ce ta Fito Falo Ta Rako Zakiya zata Tafi Daman dazu Taji Nene na Fadin Wannan kawar Dinar tazo Wajenta,Dina sanye Take da Wando Plazo sai wata karamar Riga Kallo Daya Zaka mata ko ba"a Fada maka kasan tana da Ciki Saboda yadda ya Budeta ba kamar Zaina da Cikin Jikinta ya saka Rama ba sai Laulayi don ma yanzu Yayi sauki ko aman ba sosai take yinshi ba Bata kara yarda ta kwanta bata lahiya ba saboda Umma kada ta Mtsa sai sunje asibiti asirinta ya Tonu wanda kuma Bata Fatan hakan Ruwa Take Sha alokacin da suka Hadu Sai da ta Dawo da Ruwa ta kware ta Fara Tari Dina ta kalleta sama da kasa Hakama Zakiya kafin su saka Dariya su Tafa Cikin Shakiyanci Zakiya tace"Topha ita wannan Daman Ta na gida nan..?na Zata ganin Matar so ta bayyana Tuni An koma Kauyen Tsoho da Tsohuwa..? Tafada Cikin wani Wulakantattacen kallo Datake Bin Zaina Dashi Wacce Taji har ta Fara Hawaye ga kuma wani Mugun kallo da suka Jefanta Dashi cikin Kishi Dina tace"Kema kya Fada Ba Zuciya Namiji ya gama nuna maka baka da wani amfani awajensa ammh ka manne..! Duk kukan Banza ne bata iya Rabuwa Dashi Tunda gashi Ta kasa ta Dawo Gidansu Ta Tare kamar gidan Ubanta.." Zakiya tace"Ayya yi mata Uzuri Matar Zain..Kinsan ba"a saba zaman kauye ba..Kuma da kike Fadin Ta Rabu dashi Toh in ta barshi wa zata kama..? Daman ai Taimakonta yayi ya aureta ammh Ita kanta taasan Wutsiyar Rakumi Tayi nesa da kasa..Kuma mganar gida kamar Gidan Ubanta Haka take gani mana kin manta nan Tsohouwa Tayi aikatau Tsoho ma yayi gadi Kinsan Dattakon iyayanmu na Baya Rikon Dan wani ba wani Abu bane..Kema ki barta Ta Raba agidanku ko yayane ta Rika Cin Jan miyar kar Abun yayi mata yawa ga Rabuwa da Zankadaden Miji ga kuma Komawa Kauye zaman Zawarci." Cikin Shakiyanci Dina tace"Allah ko Tawan..? Zakiya tace"Keda kikasan komai kuma..adai Daga mata kafa.."Dariya suka Sheke Dashi Harda Tafawa Lokaci Daya Dina na Fadin"An barta Tawan.."Zaina Da gabadaya kalamansu Zakiya yasa ta Jike da Hawayen Bakinciki da Takaichi Mganganunsu sun sakata ta Tuna Abunda ta manta,Kuka take so ta Fashe dashi ammh sai ta Danne Bata kara kallonsu ba ta Juya zuwa Dakin Umma Ko gani batayi suka Bita Da Dariyan Shakiyanci. Ko gani Batayi ta karisa Dakin Bata ma kai ga Haawa gadon ba ta Sulale nan ta Saki wani marayan kuka ita kuwa Dina sun Dade da Xakiya nan Suna Ta Mganganunsu sai ga Nene ta Fito ganinta ne ma yasa Sukayi sallama da Juna zakiya ta Juya ta Fice tana ma Nene sallama Ita kuma Dina ta Koma Cikin Dakin Nene ta Bita da kallo acikin Ranta Tana Fadin"Allah ya Shirya.."! *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*                2️⃣8️⃣ "Kuka kawai Zaina Take kuka mai Cike da Bakinciki Da Takaichi Gefe Daya Mganganun su Dina na kara mata amsa kuwwa acikin kunnuwanta,Dafe kanta kawai Tayi Tana jin yana Sara mata kamar zai Tsage gida Biyu. Hawayenta kuma Suna ta Zuba Suna Diga saman Cinyarta. Hakikanin gaskiya Su Dina gaskiya suka Fada mata Ita wacece..? Ba kowan kowa bace Eh gaskiya suka Fada ita din Diyar maryama Wacce tayi aikatau ne anan gidan kuma Diyar Abdullahi wanda ya zauna matsayin Megadi Kuma Ita Jika ce ga Mallam Umar gada Wanda Shima Gadin ne Sana"arsa,Itama Kakar nata Atine itama kamar mahaifiyar nata aikatau tayi sai dai me..? Sun yi Dacen Iyayen Gida irin Iyalan Alhaji Tsoho Tunda Gashi Basu Hada komai da ita ba Suka Dauketa suka maida Tamkar yarsu suka Kula da Rayuwarta suka bata Ingantattacen Ilimin zamani Dana addini Daga Karshe suka aura mata D'ansu mafi Soyuwa garesu Ita kuwa me zata ce ga wadanan Bayin Allah..? Dame zata saka musu..? Wani kukan Ta kara sakawa Tana Tuna kalaman Dina akanta na Cewa bazata iya Rabuwa da Firstlove bane ammh yaci ace Bayan haka yasa Ta gane cewa ita din ba kowan kowa Bace Tabbas mganrta na kan Hanya Inda Baya sonta bazai Fara Mu"amala da ita ba Har yayi mata Ciki ba me hakan ke Nufi..? Tayi kuskuran Yarda da Duka kalaman Bakin Firstlove Domin Duka ba gaskiya bane,ammh ba Laifinta bane Laifin Zuciyarta ne Data ke matukar Kaunarsa kuma ta Soshi da Zuciya Daya Kodomin Mganar Dina bazata yarda ta watsa ma Umma kasa a ido ba zata Nuna mata ko Babu Shi zata iya Rayuwarta..! Wata Zuciyar ta Tambayeta Zaki iya Zaman jura wannan Zaina..? Koda Tana Tunanin bazata Jure ba ya zama mata Dole Ta Jura hakan kuma Lokaci yayi da Zata Sam me take ciki nan fa ba Gidansu ba Tasan ina ne Tushenta Gada Ammh kuma Taya Tun abaya bata koma Musu ba sai yanzu da komai ya kare zata koma musu Babu Auran Tare da ita kuma Harda Tsaraban Ciki Domin in Ta Jure Rabuwa da Firstlove bazata iya Juran Rabuwa da Abunda ke Cikinta ba. Ta Dade Tana kuka Tana kuma Saka da warwaran makomar Rayuwarta kafin ta tashi Ta Fada Tiolet Tayi wanka Ta Dauro alwala jin ana kiran sallar La"asar yasa Ta Tada Sallar Ta idar kenan Sai ga Nene ta Leko Cikin Shirin Fita Tana Fadin"Diyar Umma na Shirya Zan wuce gidan Alhaji Tsoho..ki Shiyar Ummanki ta barmin Sallahun na Taho Dake chan.." Cikin Sanyin Murya Zaina tace"Bazan samu zuwa ba Nene sai gobe kaina ke dan Damuna.." Cikin Tsausayawa Nene ke Fadin"Ayyah sannu kinsha mgani..?kai ta gyada mata alaman Eh Nene tace"Shikenan Allah kara sauki ni na wuce..Keda Dina ne agidan ki kula kinji ko..? In Abban ku ya Shigo Abincinsa na Kitchen ki mikamai.." Cikin Ladabi tace"To Nene adawo Lafiya.."Daga Haka ta Fice Kafin Nene ta wuce sai da Ta Shiga Dakin Dina ta Isketa kwance kamar kullun Tana cin popcorn Tana ganin Nene ta gyara Zama Tana kallonta kafin ma Tayi mgana Ta Riga ta da Fadin"Zan Fita....Bakowa agidan Sai Halima zani gidan Alhaji Tsoho Saboda Sha"anin nan Daya Karato.." Cikin Mamaki Dina Tace"Sha"ani..? Nene tace"Eh...Daya Daga cikin Jikokin Gidan ne zata yi aure kanwar Haddir ne yar wajen Daddynsu na Abuja Shine Zasu zo nan ayi Bikin Daganan za"a wuce da Amarya Gidanta Dake kaduna.."Kai kai kawai Dina Tayi Kafin Tace"wai ni Nene haka zan Ta zama ba Fita..! Ina som komawa wajen aikina fa.." Nene taJuya Tana Fadin"Ina zaki da wannan Abun kunyar kuma..?koda yake ke ado ma kike da Ita ai ko cewa akayi ki Fita zaki ce bazaki Fita ba saboda kaucema Idanuwan Mutane gashinan Cikin ki har ya Fara Bayyana ko bama Haka ba Duk wanda ya kalleki yaga mai Juna Biyu.."Baki Dina ta Tura kawai Kafin Tace"Ai Duka Da Haihuwa ce..Kuma Yana da Uwa Da Ubansa.." Nene na gyada kai tace"hakane ba Shakka..Kinga Tafiyata.."Daga Haka ta Fice Dina Ta rakata da Harara,Nene bata ma Jira Direba ba Tunda yana Office Tare da Abba Da kafarta Ta taka Zuwa Gidan Alhaji Koda Taje duk an Hadu Falon Hajiya Mama ana ta Kira Hira Itama ta Shige Cikinsu Ganinta ita kadai yasa Umma ta Tace ina zaina Nene tace Tana Gida tace bata jin Dadi Umma Tayi Shuru tana wani Tunani Har ma Inna Hannatu ta kada baki Tana Fadi su daina barinta Tana zama ita kadai Ta Riga zama cikim Mutane ko Abun zai saketa,Hajiya mama ta kada baki Tace Tunda Uwarta Ta na Kokarin Raba auranta ai Damuwa yanzu suka kulla Inna Hannatu na jin haka tace Wlh itama Tana Bayan Umma abar Zain din ya zauna da Dina Tunda ita ya zaba nan fa Nene ta saka baki Tana kare zain kan yayi Nadama don Allah su karbi Tubansa Inna Hannatu tace har ga Allah komai ya wuce ammh fa Tana Bayan Umma yarinya karama Bakincikin yayi mata yawa ko ita Babba wannan Abun ya Faru da ita ya zatayi ganin sun Dake ne yasa Nene ta sakarmusu ammh fa tace su bazasu saki ba Sai dai ayi wacce za"ayi. Umma dai Zainab ta Nema kan Ta koma Gida ta zauna da Zaina Tsoronta Kada wani mgana ya Shiga Tsakaninta da Dina kana kuma Bata son yaudaranta Da Zain yake yi yana Zuwa yana Hore mata kunni,Dole Zainab Ta Shirya ta koma Gida koda Taje ta Iske ma Har Abba ya Dawo Zaina ta kawo Abinci nan Falo Ya zaunar da ita yana kara bata Hakuri da kuma yi mata Nasiham Hakuri da Takwalli Dawowar zainab din yasa ya barta suka koma Daki Tare Dina kuma na cikin Dakinta ko Motsinta ba"a ji. Sai Umma sai Dare suka Dawo Umma dai Haddir ya Dawo da Ita da su Zareenaa dasu Saudarta Nene kuma Zain ya Daukota Tunda Bayan ya Tashi Daga asibitin chan ya wuce,Inna Hannatu ta Kebe dashi Ta karamai Fada sosai da Nasihan Gudun Duniya ya Tabbatar mata Daya Tuba kuma yayi Nadama,Ammh yana Rokonta Ta saka baki Umma ta maidamai da Matarsa yayi ma Alhaji Tsoho mgana Shi kuma yaki Cewa komai,Inna Hannatu tace Itama Tana Goyon Bayan Umma wannan Shi ya sagar mai da Gwiwa har suka Iso Nene baki Take bashi kan kar ya Damu Umma Fade kawai Take,Bai Shiga Gidan ba yana Sauketa ya juya zuwa Gida Tunda Abba na Gida,Haddir ne ya Shiga Har suna Hira da Zareena sai chan dare ya koma Gida. ***** Washegari Bakin Yan Abuja Suka iso Mama Safiya da Hamdiya da kawayen Hamdiya Guda Biyu sai wata yayar Mama safiyar Amina,Daman Mama Safiyar yar Kano ce,Sauran Dangin suna Tafe gobe,Chan kuma sai ga Inna Rukayyah da Zafeera da Maryam yar wajen Inna Hannatu Daman Taje kanon Hutu sai Shema"u sun Dira Su Asma"u sai zuwa Gobe Gidan Alhaji Tsoho ya Cika ba Matsaka Tsinke Chan zuwa yammah kuma sai ga Mom Iklima ita da Takwanran Hajiya Mama Wacce suke kira da Hajiya Harda Amin aka zo Duk da basu samu Hutun makaranta ba Baban kaduna yace azo Dasu Saboda Yan"uwa kowa zai Hadu su ga yan"uwa da abokan arziki Mazan dai basu Riga sun iso ba sai Ranar jumma"a Duka zasu Hallara Harda Tawagan Angwaye. Su Zafeera suna Zuwa Gida Suka Wuce ita da Shema Harda kayansu,Nene da Umma daman tun safe suka Tafi Harda Zareena Zainab ce agidan sai Zaina sai Kuma Dina Hakima Zaina Tayi Murna da ganin Zafeera suka Rumgume juna Daman Umma tace Zafeera Karta bar Zaina agida Ta matsa mata su Taho Tare Sai da sukayi sallar suka ci Abinci suka sake wanka kana sukayi Shirin komawa Gidan Alhaji Tsoho Zafeera kuma ta matsa ma Zaina ta Shirya su Tafi da ta Fara Nokewa kan bata da kayan sawa tafarayi Zafeera ta Bata nata tace sai ta saka Dole Kanwar naki ta Shirya Ta saka kayan Zafeera Doguwar Riga Duk da Daman Zafeera Tafita Jiki ammh abaya Kayanta na yi mata Saboda ita tayi Cikar aure ammh yanzu Rigan Tayi mata wani Burum sai Dan Wuya,Zafeera ta Daukota mata mayafin kayan ta Bata Da Farko tace bazata saka ba Zafeera Ta Rantse mata sai ta Saka Dole ta saka Sun Fito Falo zasu Tafi sai ga Shigowar zakiya Wacce Dina ta Kirata kan tazo Ta Tayata zama Duka gidan sun Tafi sun barta ita kadai kallon kallo Sukayi ma Juna Daman Daga Zafeera har Shema yan Bana bakwai ne suma awulakance suka kalleta suka Dauke kai zaina dai Tana Rike da hannun Zainab Jikinta na Rawa Ita kuwa Zakiya mamakin yaran Take Shema cikin Kallon Tara Saura kwata tace'Wannan itace uwar Shegen..? Wacce tazo Goyon Ciki Gidan iyayen abokin Farkan nata..? Da Sauri Zafeera Tace"A"a ba ita bace..Abokiyar Shanshancin nata ne.."Shema Tace"Ko Daga gani Daman ba kima.Mudai an Hadamu da Bakin Gaddara.."Zainab tace"Wlh kuwa.."Kafin Zafeera ta Ja Hannun Shema da Zaina Tana Fadin"Let go.."Suka wuce Zakiya Data kame Tana Binsu da kallon Mamaki har suka fice Daga Falon. Kada kai Zakiya Tayi ta karisa Dakin Dina ta sameta Ade ade kan gado Tana Dannan waya Cikin wani irin Isgilanci Zakiya tace"Wasu Kwalayen yan iska kuma kuka samu agidan..? Nagansu tare da Kodaddiyar Kishiyarki Wacce Duk ta Rame ta Kode kamar Kudin Guzuri...! Dina Tace"Hmm Waya sani..Kila yan Biki ne nidai ina ta jin Hayaniyarsu.."Zakiya na zama Gefen gadon Lokaci Daya Tana Fadin"Lalle..Kam...Naji sunata mganganu ni Dariya ma suka Bani Dukkansu kananan yan Iska ne basu san me ake Kira Bariki ba Ballatana Iskaci.."Dina Tace"Nidai bar wannan mgana Cikin nan ya Fara isata na kosa na Haifeshi yamin Katanga da Abun kaunata Tunda fa nazo Gidanan ko Inda nake Zain bai Taba kallah ba ballatana na saka Ran wani kyakyawan kallo Daga Barayinsa.." Zakiya Tace"Karki damu...Sauran wata Biyar ki Haife Abunda ke Cikin ki Daga Lokacin kuma ai bashi da yarda zai yi zai saba mganar kakansa ne bayan Tarin Laifukansa Kisha Kurumin ki kin Riga kin zama Matar zain Ta har Abada.." Dina Ta washe baki Tana Sakin Dariya,Zakiya kuma Tana mata Mirmishi Cikin Tsausayamata yadda Ta Kwallafara akan Zain Wanda ita bata Fatan hakan ya Faru da ita,tafi son Rayuwar yanci Da kuma Sakewa nan Ta gyara zama suna ta Hira da Dina Rabi Duk Labarin Shanshancisu ne Da kuma Mafarkin Dina na Auran Zain. **** Umma Taji Dadin ganin Zafeera Ta Taho da Zaina Kowa ya ganta sai ya koka Ramarta Inna Rukayyah da Mom Iklima sai da sukayi mganan kan Ramar Zaina suka kuma yi mata Fadan Ta Cire damuwa aranta Ta kuma Dinga cin Abinci Tace Toh,Sai Ranar Alhaji Tsoho Ya ga Zaina Tun bayan Faruwar Lamarin Alhaji Tsoho Shi kanshi Yaga Ramarta Sosai ammh sai bai yi mata mganar ba Ya dai mata wasan Dayake mata Tunda yaga bata wani maida kai ba yasan Har yanzu Abun bai saketa ba,Daganan sai yan matan suka kebe kansu Dakin Hajiya mama Harda Hamdiya da kawayenta,Duk da Sauran kawayen suna Tafe gobe,Duka suna Tare ana ta Hira Zaina na gefe sai dai in Su Zafeera Sun sakota ta Dan Murmusa nan suka kai Dare sai Wajen 9pm na Dare suka koma Gida Taga dai Haddir ammh Bata ga Zain ba,wanda kuma ya ZO gidan Bai Kawo Cewa Zaina Tazo ba kuma yayi Tunanin Binta Gida sai yaga pass 6 Abba ya koma Gida sai ya Fasa Bayason Ran Abba na Baci saboda shi! Sai washegari  alhamis ya ganta Dayake sunyi Sister Day nan Filin Gidan Alhaji Tsoho akayi komai bayan anyi Hayan Konofi da kujeru Baki na Nesa Dna kusa sun kariso Dangin Mama Safiya Mota Biyu suka yo Daga kano Banda na Sauran garuruwa,Wasu ma suna Hanya basu kariso ba manyan ya"yan Inna Hannatu dana Inna Rukayyah duk sun kariso Da nasu Tawagan,Daddyn Abuja ma ya Iso aranar Baban kaduna ne sai Zuwa Gobe Suma Daga Barayinsu sunyi gayyah Sosai,Domim Katin ma Guda100 Suka Bugo wanda Abba ya Daukin Nauyin buga katin Gayyata Daga Gidan Saulawa Harta da chan katsina yan"uwan da suka Rage duk Hajiya mama ta Kirasu awaya ta sanar dasu Ganin gidan ya Cika ne yasa Haddir ya Tattara Inashi Inashi zuwa Lowcost wajen Zain wanda yaji Dadin haka Sosai,Yan matan kuma Ranar ma Gidan Abba suka yada Zango chan ya Cika da Iyayensu. Kowa ya maida komai bakomai ba an manta da Abunda ya Faru..Zaina ce dai suke Tsausayamawa Kowa yana nan nan da ita Bangaran Dina ba wanda ya Damu da Tambayarta ma Domin kowa haushinta yake ji Gwara ma Inna Rukayyah Tayi mganarta Tace chan gida suke Barinta Don karta Fito Labari ya Yada gari,Nene tace Tana Gida Ko Su Shema da suke kwana agidan ba ganinta suke ba,Tana Dakinta Bata Fitowa komai sai dai ayi mata Tana Daga Cikin Daki Nene ce ke wannan Wahalar Suna Gidan suna Sha"aninsu basu ma Damu da ita ba Itama bata Damu dasu ba Sai dai in Zakiya Tatashi aiki Sai ta Kirata tazo Ta Tayata zama,Su Wuni suna Shakiyansu wani Lokacin sai su Umma sun Dawo Take Tafiya. Ranar Daya ganta ana Tsaka da Sister Day din ne Sun yi Shigar Jallabiya baka,Wanda Zaina bata ma san Umma ta Siya mata Har taso ta Zuke zuwan Taga Umma ta Dauko mata Dole ta saka Zafeera Tayi mata Rolling Da Vail Din Harda Shafa mata Hoda da Man baki sai gashi Ta Fito kamar ba ita ba sai dai Rigar Ta bayyana Ramarta Sosai ,Abunda yasa ya ganta Daddyn Abuja ne ya aike su Shida Haddir suka je gidan Buredi suka Siyo Buredi mai yawa Cikin Booth Daga asibiti suka Biya suka Siya sai Suka Wuto Dashi Gida suna zuwa suka Iske ana Taron,Ganin mata sun yawa bai ma Tsaya gane kowa ba sai Haddir ne ya Tabashi Yana nuna mai Zaina wacce ke zaune kusa da Zafeera Ido ya kura mata Yana kallonta Cikin wani yanayin Ganin yadda Rigar Tayi mata kyau ne Sosai Tabbas ya sani Firstlove ta Rame sosai ko kula da matan Dayake wajen bai bi yi ba ya isa inda Suke zaune Tun kafin ma yayi mgana Umma Tazo Taja Hannun Zaina ta maidata Kusa Da ita Tana Hararan Zain wanda yayi kasake kawai yana kallon Umma Inna Rukayyah ce matayi ma Umma mgana kan ta Sausasauta ammh Taki mgana sai ma Hade rai Datayi ita kuwa Zaina Tama ji Dadin haka Domin bata kaunar Kara Haduwa ko Kebencewa da Zain. Jiki ba kwari ya Juya ya Tafi Ko Cikin Gidan Bai Shiga ba Haddir ne ya Shiga Ciki Buredin kuma yara suka kwashe Zuwa Ciki,Har suka Tafi Umma na makale da Zaina Bata matsa ma,sai Gabda Mangariba aka gama Sister Day din Aka koma Cikin Gida Ba Wuta katon Genenrator Din Gidan Alhaji Tsoho aka kunna Haske ya Gauraye ko"ina Dama su Zafeera da Shema da Zaina da maryama Haraban Gidan suka Shimfida Darduma katuwa Tun bayan da aka kwashe Kujerun,nan sukayi Sallar Mgariban kana suka Nufi Cikin Gidan Inda Hamdiya Take da Bakin kawayenta Yan wajen aikinsu da abokan karatunta da suka Sauka Dazu Da Rana. Koda suka Shiga Falon sun Tarar da Duka iyayen nasu suna Falo Inna Rukayyah,Inna Hannatu,Mama Safiya da yan"uwanta Mom iklima Umma,Nene da Sauransu sai Hira ake ana Dariya sai gasu Zafeera sun Shigo sannu da gida suka yi musu kafin su Wuce Zuwa Dakin Hajiya Mama Mom Ikilima ce ta Kura ma Zaina ido kafin Ta Daga baki ta Kirata Ta Juyo tazo Tana zuwa ta kara kallonta kafin tace mata Ki dinga cin Abinci kinji ko Sa"adiya Da Toh ta amsa kafin Tace Tatashi Taje Tana Tashi Mom Iklima Ta kalli Umma Tana Fadin"hmm wai ke Hajiyar Allah da kike kokarin Raba wannan Auran ina zaki kai Cikin Jikin Sa"adiya..? Gabadaya Falon sai ya koma kan Mom Iklima Cikin mamaki Umma ke Fadin"Ciki kuma..?ke Uwar Amin wata Sa"adiyan ce ke da Ciki Zaina..? Mom iklima tayi Mirmishi Tana Fadin"Toh da wace Sadiya garemu..Ita fa Wlh Ciki gareta.."Ido Umma da Nene suka kwalalo Umma Cikin Wani yanayi tace"Wai wani irin Ciki..? Badai na Haihuwa kike Nufi ba..? Mom iklima Tace"Shima fa gareta..Kina ina baki gane ba..? Yayi Wata uku in ma bai fi ba Wlh.."Nene ta washe baki Tana Fadin"Alhamdulillah.." Umma kuwa Tagumi Tayi Tana Fadin"Wlh bansani ba...Ban taba lura ba..Mau ciki da Rama kalleta fa ki gani.."Mama Safiya Tace"Nima Wlh mgana ne kadai Banyi ba ammh Tun Lokacin da Naganta Sai dai naga alamun Ciki Tare da ita.." Mom iklima Tace"Ai Indai Kasan alamun Ciki kana ganin Sa"adiya kaga mai Shigar Dan Ciki ajikinta.."Umma Ta saki Numfashi Tana Fadin"Wlh ban taba Lura ba..Naga sai Uban Rama Take,ammh Nima alamomin cikin sai yanzu na Fahimta Domin Kwana Take kwanaki cikin zazzabi,Ga Amai komai taci sai ta dawo Dashi Ni ban kawo komai ba Tunanin kila Saboda Damuwa ne.." Mama Safiya Tace"ai mata kala kala ne...Wata Zaki ga Ciki ya Sakata kiba Tundaga Farkon Laulayi wata kuma Daga Farkon zata Rame sosai sai Cikin ya Girma sai ta Murmure.."Nene Ta Daga Hannu Sama Tana Fadin"Alhamdulillah..Sai aba ma yaro na Matarsa yanzu.." Umma Ta Sauke kai kawai Tana Fadin"Umh...kawai batare da ta kara mgana ba Su Mama safiya suka Cigaba da Tattauna mganar suna gayama Umma Tayi Hakuri kawai ta maida Zaina Dakinta Abunda ya Faru ya Riga ya Faru Mama Safiya tace"Nifa addu"ata Allah sa in Yarinyar chan tatashi Haihuwa Ma yaron ya mutu tun aciki kowa ya Huta.."Duka suka ce Ameen Wlh Umma dai na Jinsu bata kara mgana ba ta Shiga Kogin Tunani. Dakyar Zaina Ta iya karisawa Dakin Hajiya Mama saboda Fargaba da kuma Tsoro a kunnanta Taji mganar Mom iklima Da mganganun su Umma Labe ba Dabi"arta bane ammh Jin Abunda Mom iklima Tace ne yasa Gabanta ya yanke ya Fadi Shikenan Abunda Take Boyewa ya Bayyana Shikenan Umma zata Rabata da Firstlove Lokaci Daya Kuma Ta Rabata da Abunda ke Cikinta Wasu Hawaye suka Zubomata Lokaci Daya Tana Dafe Cikinta Saurin Goge Hawayenta Tayi Ganin Zafeera Ta Fito Tana nemanta Tayi kokarin Shiga Cikin su Ta nuna komai ba komai bane ammh Cikin Ranta cike da Fargaba da kuma Tunanin Taya ya zata Tseratar da Cikin Jikinta Domin Tana Sonshi Tana ma jin aduniyar nan Shine Kadai Wani makusacinta. Umma ma abangaranta Haka Abun yazo mata Shiyasa anayin isha"i Ta kira zaina tace su zo su Tafi Gida sai tace dasu Zafeera zata Dawo Umma Tace ta wuce su Tafi Tun a Mota Take Sharan Hawaye Domin tasan kwanan Zencen ai kuwa suna Zuwa Gida Umma ta Tusata Daki ta Tsareta da Tambayan da gaske ne Tana da Ciki..? Tsoro ya kamata Ta Fara kuka Taki mgana Umma Ta kalleta Tana Fadin"Kukan ki ya Tabbatar min kin san dashi ammh Baki sanar dani bako..? Dalili kenan kika Hana muje asibiti ko kada ace kina da ciki naji ko..? Da Sauri Zaina tace"Ban sani ba Umma..Ban sani ba.."Take Fada Tana kuka Umma Ta girgiza kai Tana Fadin"Miye na kuka kuma Halima..! Nifa yakin so kanki nake miki Wlh..? shi Zain din ya sanda kina da Ciki..? Saurin Girgiza kai Tayi alamun A"a Umma Ta kada kai Tana Fadin'"Karki sake ki sanar dashi..Domin wannan cikin bazai sakani na Fasa Abunda nayi Niyyah ba Dole ya Sakeki..Cikin ma Zubar dashi zanyi.." Umma Ta Fada Daga karshe Cikin Gatse ganin yadda Zaina ke kuka aikuwa kalmar Umma Ta karshe Ta saka Zuciyar Zaina Tayu wani Rugurugu,Da Sauri Ta Dago Tana kallon Umma Cikin Firgici da Tsoro Cikin Hararanta Umma tace"Eh haka nace..Ki bar kallona da wadanan Idanuwan naki kafin Ranki ya baci.."Dole Zaina ta maida kanta kasa Tana Danne kukanta Ranar kwana Tayi kuka Umma na jinta Tayi mata Banza Tana ganin ikon Allah Ya zama Dole ta Yi Kaffaran Rantsuwanta ta maida halima Gidanta kafin Watarana ta maida kanta Ji Daga mata gatsen Zubba da Ciki Ta kwana tana kuka,Su Zafeera basu dawo ba Chan suka kwana sai da Safe suka zo sukayi wanka,Umma Tun Safe suka koma Gidan Alhaji Tsoho,Zaina kuna sai da Zafeera ta matsa mata kana ta koma Ammh kowa ya ganta yaga Ta Rage Walwala kamar baya,Zafeera Tayi Tambayan Duniyanan Taki mata mgana Gabadaya Tagama Rudewa Tana Son Firstlove Tasana san Cikinta Bata za iya Juran Rasa Ko Daya ba Aranar har yanke Hukuncin Neman Zain Tayi ta gayamai komai ta Fito Haraban Gidan ko Zata ganshi bata Ganshi ba Ranar asibiti ma ya wuni bayan an tashi ya Tafi Gida ba Saboda baya son ganin Matarsa ba sai sanin Halin Umma Ga kuma Mutane sun Cika Gidan ammh ya Guduri Niyye Ranar Daurin Aure Sai ya saceta sun gudu wani waje sunyi sati basu nam kila Daganan Umma zata bashi Matarsa. Washegari Jumma"a Aka Tashi Da Shirin Walima Baki kuma Duk sun gama isowa Baban kaduna ma Tuni ya iso,Basu da mataalan Wajen kwana Boysquaters suka Tare Dayake Yana gyarashi Lokaci bayan Lokaci Suma Ango da Abokansa sun sauka ammh Otel suka kama su. Da yammah akayi Walima Wata malama aka kira anan Haraban Gidan tayi wa"azi kan Aure akaci aka Sha aka kuma yi Rabon Abubuwa Domin Zuwan Daddyn Abuja yasa mota Biyu tazo Ta Sauke Ruwan Gora da kuma Drinks kala kala Da komai na Bukata Bangaran Abinci Daman Oda akayi sai dai aka kawo shi adafe wannan aikin Abba ne shi ya Dauki Nauyin komai. An Tashi Walima Kenan Sai ga Goggo Halima Ta iso Da matar Danta Isuhu,Zuciyar Zaina Ta kara Raunana ganin Goggo Halima Haka ta Rungumeta ta Fashe mata da kuka Dagota Tana Fadin"Ke kuma haka ake murnan sai kuka..? Umma Dake gefe Sai Jikinta Yayi sanyi Hajiya mama ce Tace"Uwa mai Dadi tayi kewarki ne Hali Dubu.."Goggo Halima ta saka Dariya Tana Fadin"Haba dai Hajiya Mama mai uwa Irin Umman Zareena da Nene wani kewa zai yi kuma..? Ga salihin Miji Irin Zainullahi Wlh Sa"adiya bata da wata mtsala sai Godiyar Allah.." Su Mama Safiya Da yan"uwanta da su Mom iklima suka ce"Hakane kam...Shagwaba ce kawai. "goggo Halima ta Tureta Tana Fadin"Ja chan..Banason Sarkaci Tafi wajen uwar taki kiyi Tabaran ita data Daure miki Gindi.."Umma ta Jawo Zaina Jikinta Tana Fadin"Taho nan Diyata...Ga inda ya Dace kiyi Shagwabar ki nan Bar Goggo Halima taji da Tsufanta.."Gabadaya aka saka Dariya ammh banda Zaina wacce ke Tunanin Abunda zai Faru gaba. Nan Su Zafeera suka bar Duka iyayen yan matan kuma Harda Hamdiya da kawayenta wajen su Takwas suka Tafi Gidan Abba su kwana Sai gobe su dawo Tunda Gidan Alhaji Tsohon ya Cika da baki Goggo Halima chan suka barta Cikin su Umma sai kwamawa suke da Hajiya Mama daman abokiyar yinta ce. Da suka koma Gida ba wanda ya Damu da Dina sai Zainab Data Shiga Wajenta Tunda Nene ta Roketa Ta Shiga ta Dubata,Tana Shiga sai da ta saka Ta Dafa mata kwai wai shi zata ci Ta isketa Zaune kan gado Tana kallo Cikin System dinta Harda cewa su rage Hayaniya Saboda Bata son Damuwa Dayake su kadai ne agidan Abba ma yana Gidan Alhaji Tsoho wajen yan"uwansa Harda Alhaji Tsoho wanda Shima yayi kaura Daga Cikin Gidan Saboda mata Zuwa nan Boysquaters. Dakin Umma Su Zafeera suke Hamdiya kuma da gayyarta suna Dakin Nene Zaina sai da ta bari duk sun yi wanka sun yi Shirin kwanciya kana ta Zare Jiki ta Shiga Tiolet din,chan ta samu Damar yin kukanta ya Isheta da kuma Tunanin mafita Ta Dade kafin Ta yanke Shawara da kuma Hukunci Duk da Abun Da zata aikata bazai ma kowa Dadi ba ammh Shine mafitan Cikinta da kuma Auranta Uwa uba ta Gujema ganin Auran Firstlove dinta da Wata mace irin Dina...! *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *BOOK 1*                2️⃣9️⃣ Sai da Ta Tabbatar da kowa yayi Barci kana tayi wanka ta Dauro alwala Ta Fito Daga cikin Bayin Sadaf Sadaf ta iske su Zafeera sun kwanta Duk sunyi Barci Alamun gajiya nan Taga Hamdiya Amarya Itama Ta baro chan Dakin tazo ne ta kwanta Saman Cafet barci ya kwasheta Saboda Gajiya. A hankali Ta Dauki Hijabinta Ta Zura Bayan Tunda a Tiolet din Ta maido Doguwar Rigar Abayan Dake Jikinta,Ta shinfida Darduma Ta Tada sallah Bayan Ta Idar ta Dade Tana addu"a Lokaci Daya Taji Natsuwa ya sameta,na game da Abunda Take Shirin aikatawa,Batare da wani Dogon Tunani ba Ta Mike Tanayin komai ahankali Saboda Kar Zirga Zirganta ya Tada Wata Daga Cikinsu. Side Drower din Umma Ta Bude ta Dauko Littafi da Biron Umma wanda Take Rubuta wasu Abubuwa Gudun mantuwa Komawa Tayi saman kujeran Dake kallon Kofa ta zauna ta Yagi Takardan Ta Dora saman Littafin kana Ta aza Biron zata Fara Rubutu sai kuma Wani Sanyi Jiki da kasala da kuma Tunanin anya Abunda zata aikata Daidaine..? In tayi hakan Tayi ma Umma adalci.? Ko Tayi ma Iyalan Alhaji Tsoho Adalci Wadanda suka Fifitata Fiye da ya"yansu..? Toh ammh in fa Tana Son Cikin Jikinta da kuma Igiyar Auranta Dole sai Tayi haka Bata damu koma me zai Faru ba Ta Tabbata Watarana zai Wuce kamar bai Faru ba Hawaye Taji ya cika mata kwarmin Idanuwanta Har suna kwaranyowa da Sauri ta saka Hannu Ta Sharce Hawaye Cikin Juriya Ta Aza Hannunta Cikin kwarin Gwiwa ta Fara Rubutun. Takai wajen Tsawon Mintina Talatin Tana Rubutun Tanayi Tana kuka,tana kuma yi Tana Tsayawa Domin wata zuciyar na sanyayamata Gwiwa ga aikata Abunda Ranta ya Rayamata ammh sai Tayi amfani da Zuciyar Dake Karfafa mata Gwiwan aikata Abunda Tayi Niyyah din har sai Da Ta kamallah Rubutun nata kana ta Ninke Takardam Tatashi Ta kaita Cikin kayan Umma ta sakata acikin Wardrope inda ma Hankalin wani bazai kai ba Umma kuma ta maida mata Littafnta da Bironta Inda ta Dauka Kana ta koma kan kujeran Da tatashi ta kwanta Kawai ba Domin Tana jin barci ba sai Domin bata da wata mafita sai na kwanciya. Mganganun Dina da kawarta Zakiya nayi ta yi mata amsa kuwwa Gefe Daya ga Kudurin Umma,Abu Daya yafi Firgitata Rabata da Cikinta da Umma zatayi wanda Bata iya Jurewa ba Hannunta na Bisa Cikin Tana Hawaye Cikin Zuciyarta wani kunci ne,Domin Ta sani Dina Ta Rigata Daukan Kwan Haihuwan Firstlove acikin maranta kenan Gaskiya ne Ta Fita matsayi Tun Da gashi Komai ya Bayyana..? Kuka Take ahankali kada wani ya Jita takai wajen Misalin karfe 3pm na Dare bata iya Barci ba Tana Ta kuka Da kuma Tunanin Makomar Rayuwarta da Abunda ke Cikinta In har ta Yanke wannan Hukuncin Datake Shirin yankewa. Bata san sadda wani Barci mai Nauyi ya kwasheta ba Sai da Taji Zafeera na Tashinta kan cewa Tatashi har an gama sallah Ta mike akasalance Idanuwanta Duk sum Kumbura sai da ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala Ta Fito kana Zafeera Ta Luura Da Kumburin Idanuwan Zaina Cikin Mamakinta Take Fadin"Ukti meya Kumbura miki ido Haka..? Da Sauri Zaina Tace"Bakomai...Idona ne Jiya Da Daddare ya Dinga Ciwo shiyasa..'Cikin Tsausayawa Zafeera Tace"Ayyah..Sorry bari mu Tafi sai asiya mgani ki saka..wlh ya kumbura miki Fuska Sosai kamar wacce Tayi kuka.."Yake kawai Zaina Tayi ammh acikin Ranta Tana Fadin ai kukan ne ma. Bayan sun Idar da Sallah Zainab da Zafeera Suka Tafi Kitchen Neman Abun karyawa Dayake su Umma Duk chan suka kwana Harda Abba su kadai ne agidan Daman chan nan Zaasu zauna sai ana Gabda Daurin Aure zasu koma Chan Gidan Alhaji Tsohon Tunda ana Daura Auran zasu Tafi da Amarya kaduna. Bayan sun gama Hada Breakfast Din Zafeera ta Mika ma kawayen Hamdiya nasu ta kuma Dauki nasu zuwa Dakin Umma Zainab ce ta Dauki na Dina ta Shigar mata dashi Ko Da ta Shiga Tana Cikin Bargo Tana Barci Ijiye mata kawai Tayi ta Fice Dinar ma bata sani ba Ta koma Daki suka karya dasu Zafeera,Hamdiya kuma ta koma Wajen Kawayenta suka karya Tare kana Suka Fara wanka Suna Shiryawa. Basu yi anko ba Kowa kayansa zai saka Zafeera da Zaina da Zainab Umma Tayi musu Atamfa Da Leshi Tun Shekaranjiya aka anso Daga Wajen Dinki ko Zaina dake gidan bata san da Dinkunan da Umma Tayi musu sai da suka Gani Ko kafin zuwa 10am na Safe sun gama Shiryawa Kowa yaci kwalliyansa ya Cakare Hamdiya Daya Daga Cikin kawayenta Tayi mata kwalliya Har Tayi ma Sauran kawayen dasu Zafeera Dama kunshi Da gyaran kai Daga Abuja Tayo Abunta. Zafeera da Zainab anyi musu makeup dan daidai Ammh zaina Taki yarda ayi mata Dakyar ta tsaya aka Shafa mata Hodo akayi mata Dauri aka kuma saka mata man baki,Dukkansu ukun less Din suka saka mai Ruwan marun,Da Pick sunyi kyau sosai sai dai kayan yafi Cika Zainab da Zafeera Saboda ya kamasu ammh Zaina sai yayi mata Rakwa rakwa saboda Ta Rame kuma Inaga Measurement dinta na Baya Telan nasu yayi amfani Dashi. An kawo musu Abinci Daga Gidan Alhaji Tsoho Shinkafa Friderice da Alala daman Drinks basu da mtsalanshi akwai agidan,Dukkansu Falo suka Fito Kowacce ta Cakare abunta suna Hira suna Dariya wasu kuma na gefe suna Hotuna irun su Zafeera Duk Rashin Son Kada Zaina Tayi Hoto sai ta matsa mata Zainab Ta Daukesu acikin Ran zaina Tana Tunanin kila wannan Hoton Shine Abunda Ukti zata Dinga kallo Tana Tunawa da ita. Dina Bayan Tatashi Tayi wanka Ta Shirya Cikin Riga da wando na yan kanti Breakfast din Ta Tea kadai tasha Ta Tureshi Gefe Tashi Tayi ta Bude kofan Tana kallon Abunda ke Faruwa acikin Falon Daya Bayan Daya Take kare musu kallo su basu ma Lura da ita ba,Zaina Take kallo Zainab na Daukansu Hoto Ita Da Zafeera mamaki ya kamata na ganinta ko ajikinta Har da wani kashe Dauri kamar ta Fito Falon sai kuma Ta Fasa Ganin duka yara ne kuma Batason Hayaniya yasa ta Maida Kofarta Ta Rufe ta koma ta kwanta Domin Bata Gajiya Da Barci kamar Cikin Jikin nata Yana yawan sakata Kasala da Barci. **** Bangaran Zain kuwa ya kwana da Gudurun yau ko ana ha maza ha mata ne sai ya Dauki Firstlove sun yi Nisa da garin Bauchi Bazasu Dawo ba sai Umma ta Sauya Ra"ayinta Tun safe suka Shirya Shida Haddir Tunda Daurin Auran 11am ne saboda angwaye Zasu wuce Da Amarya kaduna. Dukkansu Shigar Farar Shadda sukayi Harda Babban Riga wanda Daddyn Abuja ne ya Dinga musu anko Dukkansu Harda Shi da Baban kaduna da Abba,Dukkansu kuma Harda Babban Riga sai suka saka Bakar Hula da Bakin Takalmi Booth,da agogon Fata baki na kamfanin Rado Dukkansu sunyi kyau Duk da Zain ya Rame ammh yayi kyau yayi Haske sai da Ramar Jikij kawai Kuma ita ta Shafi Zuciya ne. Koda 10 tayi na safe suna Gidan Alhaji Tsoho ana ta Shirye Shiryen Daurin Auran da zai Gudana nan da Lokaci kadan Zuwa goma Da Rabi komai ya kamallah Haraban Gidan Alhaji Tsoho an gama Tsara komai an Malale ko"ina da Manyan Cafet sun Kawata Haraban Gidan Dayake Gidan Babba ne ammh Duk da haka wasu Motocin awaje aka Fakasu Musamman ma na Abokan ango da Tawagan yan"uwansa da abokan aikinsa Sojoji,Suma Abba ga nasu gayyar na Mutanensu Hakama Daddyn Abuja da Dangin Mama Safiya Suwa Shima Baban kaduna Daga Barayinsa ko"ina ya Cika da Mutane gaisawa kawai akeyi ana Farinciki In kaga zain bakinsa kamar gonar auduga Saboda yau ya gaida Abba kuma ya amsamai Har sunyi musabaha da juna Zain ya ji Farinciki har sai da yayi kwallah Zuwa Lokacin Da Time din Daurin auran ya kusa sai Alhaji Tsoho Ya Fito ya zauna Bisa Kujeransa Daidai Lokacin kuma su Zaina Motocin da suke je Daukansu suka ijiyesu Daga Wajen Gidan,Kanwar Mama Safiya ita taje tazo da Amarya da kawayenta Haddir ta saka ya kaita Sauran kuma Motocin abokan ango ne. Da kafa suka Taka zuwa Cikin Gida zaina Kamar ta Harde haka Take ji Sun saka mayafansu pick Zafeera da Zainab sun saka jaka kowannensu ammh Zaina Mayafin akanta ta sakashi Ta Jashi Sama saboda kada aga Fuskarta Daga Kugunta kuma Takardan Data Rubutu ne matse awajen Lokaci Bayan Lokaci Tana kai Hannunta wajen kada Takardan Ta Fadi. Zain Dake Haraban Gidan yaga Zaina Domin koda Ga Tafiyanta ya ganeta,Sake baki yayi yana kallonta Domin Rabom da ya ganta Cikin kwalliya Tun suna gidansu baki da Hanci ya saki yana kallonta Ita kuwa bata ma gansa ba kanta na kasa Har suka Shige daman Amaryance agaba Anty Gaje rike da ita sai Kawayenta sai su Daga baya Shiyasa har suka Shige ma basu wani Daga gansu ba ganin maza sunyi yawa aharaban Gidan.. Dakin Hajiya Mama suka yada zango su kuma su Zafeera suka Fice gaida su Umma,Umma ta Dinga Kolasu Tana sun yi kyau Kowa yaji Dadin ganin Zaina ahaka Har Hajiya mama sai da tace ko kefa Hali Dubu Mirmishi kadai Tayi mata Diyar wajen Anty Zareena ta karba Tana Jijjigatamata Ganin Tana kuka ita kuma Tana Shiryawa ne,Kowa ya ganta sai yayi mgana Ita Goggo Halima bata Fahimci komai ba Tunda ba wanda ya gayamata ammh Dai ta Fahimci Halimar ta Rame sosai kamar wacce Tayi Cuta Ammh dai Ta bar ma Ranta da kila Cikin ne ya sakata Rama Domin Taga Shigar Ciki awajen Halimar Taso Ta Tambayeta Zain Sai kuma Tayi Tunanin kila zai shigo bayan Angama Daurin Aure. Karfe 11:10am aka Daura Auran Hamdiya Aliyu Abubakar Bashir Saulawa da Angonta Hafeez Muhammad Ikra,Daurin Auran da Shedu suka Tabbatar Dashi,Wan Baban Ango Shine Waliyin Hafeez Shi kuma Baban Kaduna ya zama Waliyin Amarya Masha Allahu su Alhaji Tsoho Suna Daga Cikin wadanda suka Shaida Daurin Auran ya samu Hallartan Manyan Mutane kama Daga Lauyoyi masu zaman kansu Abokan aikin Dadyn Abuja Da Tsoffofin abokan Alhaji Tsoho Da ya"yansu wasu Tsoffin Likitoci wasu kuma sun Taka wani mukami agwammati,Sai Abokan aikin Abba Dana Baban Kaduna Dangin Mama Safiya da wasu Daga katsina,Abokan Angon Shi kanshi Da kuma Tawagar Iyayensa da Yan"uwansa,Zuwa abokan aikin su Zain da kuma Makota Da abokan arzuka Hardasu Dr.Imran da kuma Dr.peter Sun Hallaci Daurin Auran Bayan an Gudanar da Daurin auran aka Fara Fito da abinci da Lemuka ana ta Rabawa kowa yana zaune kan Cafet yana cin Abinsa da Naman kaza ga Ruwansa agefe ana Korawa da Lemu Haraban Gidan Alhaji Tsoho kamar wani Restaurant Haka ya koma. Daga cikin Gida Kuma ana Ta Shiryen Shiryen Tafiya da Amarya Nasihu Dama Tuni iyayenta sun mata su Umma dai ke karawa Da Hajiya Mama Alhaji Tsoho Daman Tun Daran Da suka iso yayi Mata nata Sosai,Kuka kawai Hamdiya Take ganin Da gaske Tafiya da ita fa Za'ayi Adaidai Lokacin kuma Zaina ta mika ma Zareena Yarta Ta koma Dakin Hajiya Mama Jakar Zafeera na Hannunta Ta bata ajiya Suna Chan Dakin Alhaji Tsoho suna Hadama Hamdiya kayanta. Ba kowa adakin sanda ta Shigo Duk suna Falo ana Tsaye Masu Shirin Tafiya masu Rakiya ma na Tsaye Baban kaduna da Abba Sun Shigo Har gida suna Fadan su Shirya 12 suka ce zasu Mika Hajiya mama Ta Tsara masu Tafiya Kaduna Tace Umma zata Tafi da Mom lklima da Inna Hannatu da Inna Rukayyah sai Dangin Mama Safiya kanwarta Da Diyar wan babansu Sai Ya"yan yan"uwansu yan mata Daga Barayin nan kuma Hajiya Mama tace Zafeera da Zainab da Shema da maryama duk zasu Tafi Asma"u ma da Zareena suma Duk Dasu za"a je Hajiya mama tace Goggo Halima ma Da matar Danta zasu Tafi Da Farko tace bazata ba Hajiya mama tace sai Taje Umma na jin da ita za"a Tafi Ta kuduri Niyya da Zaina zata Tafi Sai ta Fara Nemanta ammh bata ganta ba Zafeera tace kila tana Dakin Hajiya Mama Umma Ta taka Kafa zata Bita Hajiya Mama ta kirata kan da ita da Mom Iklima da kanwar Mama Safiya zasu kai Hamdiya Tayi sallama da Alhaji Tsoho da kuma Iyayenta wannan Dalilin yasa Bata koma Dakin ba suka Dunguma zuwa Haraban Gidan Kaya kuma Tuni wasu an Fara sakawa cikin Mota kuma Daman an je Tuni anyi jere chan kaduna wannan aikin Mom iklima ce. Zaina sai da Ta Tabbatar duk sun Ragu afalon kana Ta Tashi Daga Kofar Dakin Hajiya Mama inda Ta Labe Jakar Zafeera ta Bude Ta Taga kudi 3k sai ta Dauki 2k ta bar mata Sauran Lokaci Daya kuma ta saka Takardan Data Makale a kugunta Cikin Jakar Ta ijiye mata nan Gefen gadon Ta warware Daurin kanta Ta Rike kallabin Ahannunta Ta saka mayafinta Ta Yane kanta Ta zazzagoshi yarda bamai ganeta kuka Take kuka mai Cinrai hawayenta na Zuba Tana Sharewa Sikat din yadan mata yawa sai Tajashi sama Sai da ta Leka Daga Falon Taga duk ba wanda ya santa yawancin Dangib Mama Safiya ce Sadaf Sadaf Ta Fito Tana waige zata Fice Daga Falon Taji Muryan Hajiya Mama Da ta Fito Daga Dakin Alhaji Tsoho Tana Fadin"Ke waye nan zai Fita..? Dam!gaban Zaina ya Fadi tayi Saurin Share hawayenta kana ta Juyo Tana Fadin"Nice Hajiya mama..Zani waje naga Tafiya Amarya ne muyi sallama.."Hajiya Mama Da taci wani Ubansu Leshi Ta kariso Tana Fadin"Au Halima ce..? Eh gwara haka Kinga ke bai kamata ki Tafi ba gwara ki zauna in Uwar taki sun kaita sun Dawo sai ansan yadda za"ayi ki koma Gidan Mijinki.." Cikin Sanyin Murya Zaina Tace"Toh Hajiya Ma..ma.."Ta Fada Muryanta na rawa ganin haka yasa ta Dafa kanta tana Fadin"Karki damu kinji ko..Ga Nene ai ba da ita za"a Tafi ba saboda kada abar gidan ba kowa ga Amanar yarinyar nan a Hannunsu Kiyi hakuri gobe zasu Dawo Dukkansu.."Tafada Cikin Sigar lallashi tana ganin kamar zaina ta Damu ne za"a Barta ita kadai Saurin kwakwalo Mirmishi Tayi kafin tace"Bari naje muyi sallama.."Hajiya Mama tace"Hanzarta.."Ko gama Rufe baki bata yi ba ta Fice har tana Tuntube sai da Hajiya Maman ta Bita da kallon mamakin ganin kamar tana Sauri kuma bata Cikin Natsuwarta. Girgiza kawai Tayi ta koma Ciki,Achan Haraban Gidan kuwa Zaina na Fita ta Tsaya Daga Gefe,Tana Hango Hamdiya Durkushe gaban Alhaji Tsoho Da Abba Da Babban kaduna da Daddyn Abuja su Umma na Tsaye Daga Chan gefe kuma Tuni wasu ma Daga Tawagan anko sun Fara mikawa su Zafeera kuwa suna jikin wata Jeep Daga gani ita zasu Shiga Daman sun Taho Da kayansu Tun Daga Gida wajen ya cika da jama"a Shiyasa wani ma bazai gane wani ba an cika maza da mata Kamar an ce Ta kara Daga kai ta Hango Firstlove yana ma Zafeera mgana Bata san me ta gayamai ba Taga ya Nufi Wajen su Umma Kara Lafewa Tayi jikin Fulawan Dake Haraban Gidan tana kara Rufe Fuskarta Tana gani ya Rankwafa yana gaida Goggo Halima ta amsa Tana Shafa kanshi bakinta har kunni Daga gani albaeka Take sakamai Zuwa chan kuma ya mike ya Nufi Hanyar Shiga Falon gidan Sai Zaina ta kara Boye kanta Tana Danne kukanta ganin Firstlove ya Tada mata Duka wani Mikin Dake Zuciyarta,Wani irin Sonsa da kuma Raunin Rasa sa ya Bayyana Gareta Tana kallonsa har ya Shige Cikin jikinta ta Dafa Lokaci Daya wasu hawaye na Zubomata afili ta Furta"Nasan zakaji Ba Dadi in kaji irin Hukuncin dana yanke..Kada kadamu nayi hakane saboda Tseratar da Cikin ka da kuma Aurena Dake hannunka..da kuma kauce ma ganin wata Ta haifa maka D'a ko ya' ba ni ba da kuma kaucema ganin Wata a matsayin matarka..Ammh zan Dawo In da Rabo kuma nayi maka alkaawarin Kula maka da kaina da Abunda ke Cikina Insha Allahu.". Kuka Ta fashe dashi kamar Wacce aka Duka Har sai da Ta Duke jin kamar Motsi ne Daga Bayanta yasa ta waiga Tana Toshe bakinta kada wani ya jiyota,Ido ta zaro Tana kallon Zain Daya Fito kamar yana neman wani abu Jikinta ya Fara Rawa Ta Tabbatar da ita yake nema ya kamata tayi ta Fice Daga Gidan nan kafin komai ya kwace mata,Tana ganin ya Nufi Wajen Zafeera Tayi Zuruf ta Fito Daga maboyarta Ta Bayan Mutane ta Dinga Bi Tana ta kare Jikinta kada Zainab ko Zafeera ko Umma wani gane kayan Jikinta ya Kirata,Allah ya Taimake ta har ta kusa barin Haraban Gidan bata Hadu da wani idon sani ba Tana Gabda Fita ne suka kusa cin karo da Haddir ya Shigo yana waya ganin Hankalinsa yayi gaba ne yasa sau Daya ta Waigo ganinsa yasa ta Juya da Sauri Ta na gyara Gyalanta Shi kuma sai da yace mata Tayi hakuri kana ya koma yana kallonta ganin yadda take wani Sauri kamar zata Tashi sama mamaki ya kamashi Ko dai Barauniya ce..? Ammh kuma kamar Dazu Da suka je gidan Abba yaga kamar wasu da kayan nan Dayake shi bamai wannan luran bane yasa kawai ya Cigaba da wayarsa ya Juya ya Nufi Haraban Gidan. Hankalin Zaina bai kwanta ba sai da Taga Ta Fita Daga Haraban Gidan Alhaji Tsoho kana ta Dago Ta kalli Gidan Ta kara kallo Hawaye na Zuba acikin Idanuwanta kafin Ta Furta"Umma ki yafemin..Abba ka yafemin...Goggo Halima kema ki yafemin...Firstlove da Ukti kuma ku yafemin.."Kafin ta Fashe da wani kuka mai cin rai adaidai kuma Lokacin ne Motar Zakiya Wacce Dina ke Ciki ta Faka nan kusa da Zainar bata ma Lura dasu ba Tana kallon Gidan Tana kuka sai Da Taji muryan Dina wanda ko Mafarki Tajita zata ganeta kana ta waigo Gabanta ya yanke ya Fadi Data gansu Saurin Juyawa Tayi Tana Rufe Fuskarta Lokaci Daya kuma Tana Tsallakawa Daga chan Dayan Hannu Da kallo suka Bita Dukkansu atamfa Riga da Sikat suka saka ammh fa kayan sun kamasu Zakiya ta Zubo attch din nan Dina dai bata saka ba ammh Itama gashinta waje ga wani mayafi kamar basu basu saka ba. Ta gefen ido Taga suna kallonta yasa ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri kamar wacce Zata Fadi Hannunta daya Damke da Sikat dinta da kudin Dake hannunta Ganin haka yasa Zakiya tace"Ita wannan fa..? Tana sauri kamar wata mara gaskiya..! Hankalin Dina naga Haraban Gidan Take Fadin"Miye naki..? Kila barayin nan ne da suke zuwa Sata wajen Biki..Tagama Diban Rabonta Zata kara gaba.." Ta Fada Tana kallon Bayan Zaina wacce ta Fara musu Nisa Cikin Wani yanayi kafin ta Kauda kai Zakiya ce Tace"Umh...Lalle ana Shagali kalli fa da Yadda Gidan ya cika da manyan Motoci kalli yadda Gidan ya cika fa Shine ke din acuceki sai ace ki zauna agida ke kadai.."Dina Ta saki Dariya Tana Fadin"Kyalesu...Ai na bar musu megadin gidansu yayi musu gadin gidansu..Nima sai nazo aci bikin dani nima ai na zama yar Dangi.." Zakiya Tace"Kwarai...Kuma ai mu ai abun kunya gaba muka bashi ba Baya ba..Kuma Tunda Dansu ya bari ya Shiga Tarkonmu sai Hakuri.."Dariya suka kara sakawa harda Tafawa Kafin Zakiya ta kashe Motarta su Fara Taku zuwa Cikin Haraban Gidan Daman Zakiya ce Tazo Gidan Taga Dina ita kadai duk sun watse sun barta Shine ta zugata kan ta Shirya Suma sai sunje Bikin Dama Dina nason Fita Ta gaji da zama waje Daya nan da nan ta Shirya suka bar Gidan,Megadi kadai suka bari agidan Hatta su Saudart Tun Jiya suna Gidan Alhaji Tsoho. Achan Haraban Gidan Alhaji Tsoho Kuwa Zain ne ke Ta neman Zaina bai ganta kuma Da Farko Zafeera ya Tambaya tace mai Tana Dakin Hajiya mama ya Shiga Ciki kuma Hajiya Mama tace yanzu ta Fita Tace zatayi sallama da Amarya Har wajen Yaje bai ganta ba Haddir ya gansa yana ta Neme neme yasa ya Tambayeshi wayake nema yace mai Firsrlove Haddir yace yaje wajen su Zafeera kila suna Tare. Wajen su Zafeera ya koma ya kara Tambayanta Tace mai Tana Ciki yace ya Shiga ciki ance ta Fito nan Haraban gidan Mamaki ya kama Zafeera Sai Ta Fara waigen Neman Zainar Tana Fadin"anya Hajiya mama Tana gani kuwa..? ukti bazata Fito Cikin wannan hayaniyar ba.." Zainab Tace'Eh mana mun ma ce..Ta Fito Taga Tafiyammu Tace Baxata Fito ba..Jakar ma Anty Zafeera yana Hannunta fa.."Zafeera Tayi Shuru kafin tace"Bari dai na kara Dubata Ciki.."Zain dai sai yaji gabansa na Faduwa Zafeera ta koma Ciki Har Dakin Hajiya Mama ba Zaina ba Dalilinta Ta Rude Lokacin bata ma Lura da Jakarta ba tazo Tana kara Tambayan Hajiya mama Zaina ita kuma ta Rantse mata Wlh Ta ganta Har sunyi mgana tace mata zata tayi sallama da Amarya. Sai kan Zafeera ya kara Daurewa ta Fito Haraban Gidan Tana kara Duba Zaina bata ganta ba sai ta Hango Zain din Tsaye Da Haddir Daga chan kuma su Zakiya na takowa garesu Zafeera ta Rike baki Cikinmamaki Take Fadin"Su kuma wadanan agayyar wa..? Kusan atare ita dasu suka iso ga su Zain,Haddir da zain baki kawai suka saki suna kallo su Dina Cikin wani Takaichi suma kallonsu suke cike da wani Mirmishi Zafeera Ta kallesu A wulakance kan ta saki Tsaki Tana Fadin"Ba kima.."Kafin Ta maida Hankalinta kan Zain tana Fadin'Wlh Ya Dakta bata aciki..Kuma Hajiya Mama ta Rantse min ita ta gani har sunyi mgana Tce xata je tayi sallama da Amarya..? Zain hankalinsa ya maida kan Zafeera ya ma manta dasu Dina yana Fadin"Bata chan wajenm..? Ko tana tare da Umma..? Yafada yana nuna inda Su Umma ke Tsaye suna Jiran Iyayen Hamdiya su sallameta,wasu Mutanen tuni sun Shigo Motoci Amarya kawai ake Jira ango ma Tuni Yayi gaba. Zafeera Tace"Anya.? Bata wajen Umma Ai kaya iri Daya kuma saka da tana Wajen dana hangota.."Haddir Da kansa ke gefe ya waigo Yana kallon Kayan Jikin Zafeera haka suma su Dina suna Tuna ai yanzu suka ga mai irin wannan kayan Haka Shima Haddir Cikin mamaki yace"Irin wannan kayan Dake jikin ki Zainar ta saka..?Da Sauri Zafeera Tace"Eh...Dani da Zainab da ita iri Daya muka saka kuma ga Zainab chan.."Tafada Tana nuna Jikin Motan da Zainab ke Tsaye Tana kallonsu ganin kamar hankalukansu ya koma kanta yasa ta Bar Jikin Motan ta Nufosu. Sai Lokacin su Dina suka Gane wa ake nema suka kalli Juna ita da Zakiya kafin suyi mgana Haddir yace"Indai kuwa wannan kayan ta saka Dazu Da zan Shigo naga wata mai irin kayan nan Tana ta Tafiya da Sauri Ban dai ga Fuskarta ba ammh har kusa Bangaxan juna mukayi Ta Rufe Fuskarta da gyalenta.." Gaban Zain da Zafeera Dana Zainab Data kariso Duka atare ya Fadi cikin firgici Zafeera Ta waro Ido Tana Fadin"Ka ganta kuma da irin wannan mayafin na Jikinmu..? Kallon gyalen yayi kafin ya gyada kai yana Fadin"Eh Tabbas Shine ajikinta.."Salati Zainab Ta saka Zain kuwa Hulan kansa ya Cire Cikin Tashin Hankali Da Sauri Zakiya tace"Indai kuwa Mai wannan kayan ne da wannan Mayafin muma muganta Tana ta Sauri sanda muka Tsaya da Motarmu." Da Sauri Zain yace"Tana ta Sauri Tabi ina kuma..! ? Zakiya tace"Bamu sani ba Tadai tsallaka Chan hannun daman Ta Fara Tafiya da Sauri Da Sauri.."Zafeera Taji wani Faduwar gaba kafin tace"Ina Ukti zata bata gayamana ba..? Ko gida ta koma tun Nan din Taga an cika Ga Hayaniya..? Da Sauri Zain yace"Muje Haddir mu gani..kila ma gida ta koma.." ya Fada yana yin gaba kamar zai Fadi Haddir ya Rufaamai Baya Suka Fada Mota suka bar Gidan,Su Zafeera kuwa ko Takansu Dina basu bi suka Fara Tambayan yan"uwa ko wata Taga Zaina matar Zain..? Kowa sai yace A"a Dina kuwa kallon Zakiya tayi yana Fadin"Allah yasa Ta bace kar aganta Har Abada..! Zakiya Tace"A"ah...Adai ganta Din bacewarta Gabadaya Tamkar Faruwar wani abu ne.."Da Sauri Dina Tace"Me kenan..!? Zakiya Tace"Kedai kada kiyi Fatan Ta bace har abada..Gwara dai ya saketa Tana Duniyarsa zai Fi.."Daga haka bata kara mgana ba suka nemi Waje suka Tsaya suna Bin Kowa da kallon Daya Bayan Daya Bangaran yan bikin kuwa babu wanda yama lura Dasu. Su Zain basu Dade ba sai gasu Sun Dawo Zafeera Ta Taresu Tana Fadin"Kun ganta Ya Dakta..? Bai iya mgana ba Saboda yadda yake jin wani Faduwar gaba Da wani irin yanayin da bai Taba ji ba,Haddir ne ya Girgixa kai yana Fadin"A"a babu kowa achan sai megadi.."Juyawa kawai Zafeera Tayi batare Da Tayi mgana ba Wajen ya Hautsine Lokacin Su Abba Sun gama Nasihansu sun Mika ma su Umma Hamdiya Zafeera Ta Kutsa Cikin matan Ta Riko Umma Tana Fadin"Umma Baki ga Ta Tafiya ba, Ba"a ga Zaina ba..! Umma Ta waigo Cikim mamaki kafin tace"Wani irin baki ganta ba..? Ba cikin gida muka barta ba Dakin Hajiyaa mama.."Da Sauri Zafeera Tace"mun Dubata Ko"ina bata Umma Ya Haddir yace yaganta Ta Fita Daga Gidanan..Kuma sunje chan Gida Bata Umma.." Umma Da Taji Gwiwanta Tayi sanyi Tace'"Bangane me kike nufi ba Zafeera ba..? Zafeera Tace,"Umma ba"ga Ukti ba..Bamu ga Zaina ba..Mun Dubata ko"ina bata ina Tsoron Faruwar wani abu.."Tafada Tana Fashewa da kuka Wanda yaja hankalin Jama"ar Dake wajen Mom iklima Tace"Subhanallah wani irin baku ganta ba..? Kun Duddubata ko"ina baku ganta bane..? Kuka yaci karfin Zafeera Ta kasa mgana karisowan Zainab ne yasa tace"Bata gidanan Domin an ganta ta Fita...Kuma an je gida bata nan gashi ita ba waya ba ballatana akirata.." Gabadaya wajen sai aka saka Salati,Umma ta Fara Sauke Numfashi kawai Nene ma Tana chan Tare dasu Zain suna gayamata itama sai Taji Tsoro ita Taje tagaya musu Abba suma suka Fara Tunanin toh ina zata ko Gidanta Takoma..? Da wannan Tunanin Haddir da zain suka je chan gidan nashi Chamma Shuru bata nan Koda suka Dawo da labarin bata nan sai Hankula suka Tashi Aka Dakata da Shiryen Shiryen kai Amarya Alhaji Tsoho yace Kowa ya Shiga Cikin Gida,Bayan sun bama masu Daukan amarya Hakuri, Shima Cikin Gidan Su Abba suka Taimakamai ya koma Ya zauna Bisa Kujeransa Cikin Alhini ya kalli Zain yana Fadin"kun Dudduba ko Bisa Hanya baku ganta ba..? Haddir yace"Bata Alhaji Tsoho.."Goggo Halima da mamaki ya Cikata Ta kada baki Tana Fadin"To wai ina ma zata..? Me akayi mata..? Ba wanda ya iya bata amsa,Duka an Hadu waje Daya ana Ta Jajanta Lamarin Harda su Dina na Wajen ba wanda ma ya lura Dasu Zain na zaune kawai ya Dafe kansa Alhaji Tsoho yace Abba ya Kira Chan gada yaji koTa kira wani Daga chan aka Kira sukace bata Kira Kowa ba. Toh Ina Zaina Zata tafi..? Da Sauri Zafeera Tace"ko aje gidan kawarta Laila agani.."Batama gama mgana ba Zain ya Mike ya Fice kamar zai Fadi Haddir da Zafeera suka mara mai Baya,Suna Zuwa Gidansu Laila Ta Tabbatar musu da Cewa Rabon Da Taga zaina Tun Ramar da tazo Gidan Umma Ta Tabbatar masu batazo ba Zuwa Lokacin Zain ya Fara wani Tunani na Dabam Gabadaya Zuciyarsa Bugawa kawai take yi. Suna zuwa da Labarin Bata je chan Umma ta saka kuka kawai,Zainab ce tace a kira wayar Zafeera jakarta na Hannun Zainar,Zareena ita Ta Kira Wayar Zafeeran sai dai ana ta Kira Tana Ringing ba"a Dagawa,Hankula suka kara Tashi Zain ya Sulale yayi zaman Dirshan yana Fadin"Shikenan...Shikenan...Firstlove.."Haka kawai yake Fada kamar wani mara Hankali. Zainab ce Taji Fitsari ta Shiga Dakin Hajiya Ta yi Cikin bayinta Ta Fito kenan Ta ji karan Wayar Zafeera wacce Dagachan Falo Zareena ke kira Cikin mamaki Tabi Karan sai gata Gaban jaka Cikin Fargaba ta saka Hannu Ta Dauko Jakar Ta Bude Ta Dauko wayar Kenan sai Taji kuma Ta Taba wata Farar Takarda Tana Daukota Bayan Ta karanta Sunan Dake Jiki Ta Waro Ido jikinta na Rawa ta Kwashi gudu zuwa Falon Tana Fadin.." "Ga Jakar na gani Dakin Hajiya mama Da wayar..Ammh ga wata Takardan Daga Jikinta an Rubuta UMMA,ABBA,ALHAJI TSOHO,FIRSTLOVE,GOGGO HALIMA.." Tafada Lokaci Daya Tana Daga Jakar da wayar da Takardan lokaci Daya Gabadaya Ba zain kadai Daya mike da Sauri ba Hatta da Umma dasu Abba da kowa da kowa haka aka Mike ana kallon Zainab baki Bude da Fargaban Abunda Tace Tagani Jikin Takardan. _Nasan da yawanku wasu wannan Page din bazai musu Dadi ba sai dai ina so ku sani Bawa bai isa ya kauce ma kaddaransa ba Bayyanar Dina ga ahalin Dr.Saulawa ya kawo Rudani wanda ya kasa Daidaita Toh kila Bacewar Zaina ma wani Mafita ce zai kawo ahakan Kada ku manta Labarin nan Shashi na Daya muke bamu kai ga Shiga Shashi na Biyu ba Sauran Labarin da abubuwan da suka Faru Har su Daidaita suna Tafe,Ku karanta Cikin natsuwa ku kuma gane Labarin Tun Farko ya Tsaru ne...Nagode kwarai da Sharhinku Yan Amana Da yan Wattpad dina Allah ya bar kauna Ameen.._ *Janafty...* *ZAINAZAIN..!* _(Is a love Story and Betrayal)_ *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janaftyshakira*❤️ *END OF BOOK 1*                 3️⃣0️⃣ "Zain ya Fara Takawa da Sauri Zuwa Wajen da Zainab Take tsaye sai dai kafin ya karisa yaji kansa ya sara,ya Saka hannu ya Dafe kansa ya Daga kafa zai Cigaba da Tafiya yaji kafafunsa na Rawa Jiri na Dibansa ammh ya kasa Hakura aikuwa Hajijiya Ta Debeshi zata Fadar dashi Allah yasa Baban Kaduna da Abba Dake kusa suka Tarbeshi Ganin yayi Gefe zai Fadi Cikin Damuwa da wani yanayi Abba yace"Subhanallah..Zainullahi..? Ya kira Sunansa Jin Ana Kiran Sunansa Daga sama yasa ya Bude ido ganin Abba Da Baban Kaduna yasa ya mike ga kafafunsa yana Dafe kansa Kokarin Cigaba da Tafiya Zain yake yi Baban Kaduna ya Rikesa Yana Fadin"Dakata..Ina zaka..!? Baka ganin Jiri kake gani kana neman Faduwa..? Cikin Raunin Murya yace"Baba zan karbo Takardan ne..Na Tabbata Firstlove ta Rubuta shi.."Baban Kaduna ya Jashi Ya zaunar Dashi Saman kujera yana Fadin"Zauna..kai Hadiru karbo Takardan chan muga kome ke Ciki.." Yafada yana kallon Haddir Ba yadda Zain ya iya Dole ya koma ya zauna yana Sharan Zufa Lokaci Daya Yana Sakin Numfashi Sama Sama Abba na kallonsa Cike da Tsausayawa Haddir ya Taka gaban Zainab ya karbo Takardan ya kawo gaban Baban Kaduna Cikin Umarni Alhaji Tsoho yace"Kai Hadiru Warwareta ka karanta Kowa yaji..Tashafi kowa Tunda ta Shafi Fatima da Usman dashi kanshi Zainullahin da kuma Goggonta Halima ka karanta Kowa yaji.." Cikin Bin Umarni Haddir ya warware Takardan sai ga Dogon Rubutun Zaina ya Bayyana Cikin Budewar murya yadda Kowa zai ji ya Fara karantawa Yayinda Falon ya Dau Shuru kowa na Sauraransa Hatta kuwa da Umma Dake kuka Amarya Hamdiya na Gefen Mom iklima Tuni Ta bar kuka Ta koma Jajanta wannan lamarin yayinda Dina da Zakiya suka saka kunni suna son suji wani sako wannan Takardan Take Dauke dashi _Assalama irin Ta Addinin Musulunci Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta"ala Wabarakatuhu,Nasan  zaku yi mamakin ganin wannan Sakon nawa ammh kuma ya zama Dole Kuma Ina da Tabbacin Lokacin da zaku ga Sakon nan na Riga nayi Nisa da Garin Bauchi,Shiyasa nace Sakon kai Tsaye ga Umma ne Da Abba sai kuma Firstlove,Alhaji Tsoho da Goggo Halima kafin nace komai zan Fara da Neman afuwanku Bisa wannan Hukuncin Dana yanke batare da nayi Shawara da kowa ba..Nasan Cewa Wannan Abunda na aikata bazai muku Dadi ba in kuka nemi kuka Raasa kuma kuka Fahimci Cewa na Bar ku ne,Da Farko zan Fara da Baki Hakuri Umma Don Allah ki yafemin Ba"a son Raina na Tafi na barki ba kuma ba Niyyata Na Bijerema Umarnin ki ba ko na saba miki ba..!ko na Watsa Miki kasa a ido ba..! Umma Tun ina Jaririyata na Rasa Duka iyayena kika Tallafeni kika zama Uwa gareni kika Fifitani sama da ya"yan da kika Haifa,Da ace mata da yawa zasu koyi da irin Halinki da sun Dace kin kasace Uwa Tagari mai maida D'an wani nata kin Soni Da Zuciya Daya kin Fifitani kan Abunda kika Haifa Saboda kina So ki inganta Rayuwata kin Kuntatama Abunda kika Haifa saboda ni Umma Sai dai ni na kasa Miki Hallaci bazan iya juran Rabani da Firstlove ba da zaki yi ba Umma Ina sonshi ina kaunarsa Shine Raunina Shi na sani Shine komai nawa Umma Shine Duniyata Zuciyata bazata iya Daukan abubuwa Biyu alokaci Daya ba..Umma ban yanke Shawaran yin nesa daku ba sai da naga kin Fahimci ina da Shigar Cikin Firstlove ajikina Wanda Duk da banje asibiti an Dubani ba ammh Duka alamomin masu Suna Bayyana ciki Gareni Nayi kokarin Na Sirrinta Abun kada ki sani sai dai hakan bai Faru ba, kin gano ina da ciki kuma Kin Fadamin zaki Zubar dashi Saboda Kina son Cigabana baza ki barni na Cigaba da Zama da Firsrlove ba Umma ina son Cikina naji ina kaunarsa Kuma nayi alkawarin zan kare lafiyarsa Muddin Raina Koda wajen Haihuwarsa zan Rasa Raina Na yarda na amince na Haifama Firstlove Wani Abu Daga Tsatsona Daga karshe Umma ina mai neman Gafaranki Don Allah ki yafemim kuma ina Rokon alfarman da ki yafema Firstlove koda wannan ne alfarma ta Karshe da zaki man Ummata..Sai Abba Kaima Zan Roke Gafara Domin kaima Uba ne gareni ka Rikeni Tsakani ga Allah ka Hadani da ya"yanka ka Inganta Rayuwata alhalin ni ba Kowan kowa bace Face Diyar Maryamai mai aiki da Abdullahi megadi ammh baku Duba wannan ba ka Rikeni kabani Dukkan gata Ina matukar Gode maka ka cika Uba nagari Abba ka yafemin Don Allah Kuma ka yafemin Firstlove Abun da ya faru Bawa baya wuce kaddaransa,Abba bazan cigaba da zama ina ganin kana Fushi da Firstlove ba Kana hanashi shiga gidanka ba Duk Saboda ni ba..Shiyasa naga Tafiya ta itace Mafita kaima Don Allah ka yafema Firstlove Na Tabbata Nadamarsa ta Gaskiya ce bazai kara aikata makamancin haka ba,Sai Kai Firstlove Mijina Abun alfaharina Bangona Majingina komai zaka min aduniyan nan na Riga nayafe maka Duniya da Lahira,Kayi Rayuwa cikin Jajayen Fata kaga mata kala kala Wadanda suka fini komai da komai ammh kace sai ni din nan Kamin komai aduniya ka nuna min kauna Ka soni Ka kaunace ni kuwa dame zam saka maka.? Zuciyata tayi Rauni Lokacin da Naga Wata amatsayin Wacce kake Rabamana na Rayuwa da ita naji Dama na iya Fincike sonka acikin Raina sai dai ina Bani ke Sarrfa Zuciyata ba naji na kasa sai ma karin kaunarka da Tsausayinka dakeCin Raina akullim ina kwana kuka ne ba Saboda komai ba sai saboda Tsausayina da Tsausayin kanka bazan Juri Raunin Rasa ka ba kuma bazan Juri Raunin wata ta sameka ba kuma Bazan juri Raunin Rasa Cikin Jikina ba Shiyasa na zabi na Tafi waje mai Nisa Zuwa Lokacin da komai zai Daidaita ka sani na yafe maka Nima ka yafemin Tare damin alfarman Barin Igiyar Auranka akaina Koda bazamu sake Haduwa ba...Nayi maka alkawarin kula da kaina da Abunda ke Cikina In har muna da Rabon Haduwa Shikenan in kuma ta yanke sai da nace Sai Wata rana..! Alhaji Tsoho Dattojon arziiki kuma Wanda ya Tara Zuru"a ta kwarai Babu Abunda zan ce maka kai da Zuru"anka sai Godiya Allah ya saka muku da alheri,Kamin Nasiha na ki Jin mganarka nasan zakaji zafin wannan Hukuncin Dana yanke ammh kuma Shine daidai awajena Katayani Bama goggo Halima Hakuri kuma Don Allah komai zataji kan Firstlove kada Tayi Tir Dashi Ta Dubi mganar da Fuskan Basira,dangina da yan"uwa na Gada da kuma Ukti,Faruq,Anty Zareena da kowa da kowa nasan bazaku ji Dadi Ba Dake zainab Ammh don Allah ku yafemin ku sani Duk inda zani zanyi matukar kewarku..Kada kusha Wahalan nema na nayi Nisa Na Tafi bansan Inda zani ba ammh kuma In da Rabo zan Dawo Insha Allahu Zuwa wani Lokaci in kuma ba Rabon ganawarmu sai nace Allah ya Hada Fuskokinmu a Darussalam..masallam_! Gabadaya Falon ya Dauki wani irin Shuru kafin kuma ya Kaure da Salallami da kuma Koke koke Umma kasa ta Durkushe Tana Fadin"Innalillahi...Wayyo Ni Fatima me na aikata..? Nayi sanadiyar Yata ta bar gida ina zata..! Wlh koda na Rantse zan Raba wannan auran Daga Baya nayi Nadama har cikin Raina kuma nayi Niyyar maida ta Gidan Mijinta na yarda zanyi kaffara Saboda haka,Kuma mgana Ciki Wlh harga Allah Shine Shaidata Ba Har raina na Fada ba gatse nayi mata ganin tana kuka ashe ashe ita Ta Dauka Da gaske ne.."Ta karishe Fada Cikin Kuka Hajiya mama na Sharan kwallah Tana Fadin"Kinga Abunda kika aikata Ko Fatima..? Dama na gaya miki Abunda Hakuri bai bamu ba Wlh a kasasin bazai bamu Ba gashi yarinyar Tabar gida yanzu wani Hali zata Fada bamu sani ba.." Abba kansa kawai ya Dafe Yana Salallami Baban kaduna ma Haka su Mama Safiya Kowa dai afalon Sai salati ke tashi Zafeera da Zainab kuwa sai kuka Suke Dina ce kadai Take Farinciki Sosai Zuciyarta Kamar farar Takarda,Alhaji Tsoho kai ya Sadda kasa yana Kiran Sunan Allah,Goggo Halima kuwa Da ta Shiga Rudi Da kuma Rashin Gane ina aka Dosa ta kalli Hajiya Mama Tana Fadin"Hajiya mama me ya Faru ne..? Halima Tayi gangancin me ya Faru da zafi da zata yanke irin wannan Hukuncin Tana yarinya karama ga Danyan Ciki Tare da ita kai Innalillahi.." Hajiya Mama Ta girgiza kai Cikin Sharan Hawaye Tana Fadin"Bari kawai Halima Mganar mai Tsayi ce sai mun zauna.."Hajiya Mama bata gama Rufe bakinta ba Zain ya Mike Tsaye da karfi sai Lokacin ya samu Damar mikewa,Tun Sadda Haddir yake karanta Takardan Gabadaya Muryan Zaina ke mai yawo a kunnuwansa gabbansa sun saki Kafafunsa sun gaza Daukansa bai Kara Shiga wani irin Rudewa ba sai da ya fahinci Zaina Ta tafi Ta barshi Sannan kuma Tana Dauke da Cikinsa ajikinta Tundaga Lokacin bai kara Fahimtar komai ba Domin Jinsa Da ganinsa ne ya Dauke alokacin sai yanzu yaji kamar ya Dawo Cikin Duniyar. Gabadaya aka Zubamai Ido ana kallonsa ganinsa yana Nuna Hannu yana so yayi mgana ya kasa Runtse ido yayi wasu Zafafan Hawaye suka zubomai Cikin Rawan murya kamar mai In ina yace"First...L..O..v..e...Ta..tafi...Ta..barni.Kuma..Ta...na...Da...Cikii...naaaa...!bai ida karisa mgarsa ba Kawai ya Sulale ya Fadi nan da Karfi sai kaji Tim nan da nan Idanuwansa suka kafe ba Numfashi Cikin Tashin Hankali su Abba dasu Daddyn da Baban Kaduna da Haddir suka Rufu kansa Cikin Rudewa da wani Tashin Hankali Haddir da Baban kaduna Suka Tallafeshi suna Kiran Sunansa ammh ko Motsi Abba Dake gefe ya Rikice Hakama Su Umma sai kuka ya kara Tashi Dina Dake gefe ganin Zain baya Motsi ya Tada hankalinta Ta nufi Wajenshi Tana Zuwa Ta ture Haddir Dake Rike da kansa Baki ya saki yana kallonta Cikin Tashin hankali ta Rike Hannunsa Tana Fadin"Na Shiga uku plz zain don"t do this to me..Kada ka Tafi ka barni da Cikinka.In ita bata Sonka ni ina Sonka Zan zauna dakai nayi maka Duk Abunda take maka Don Allah ka tashi.."Sai kuma ta saka kuka Galala kowa ke kallonta sai Lokacin ma Su Umma suka ganta Cike da mamaki Wadanda basu san Labarin Dina ba suka saki baki Cikin mamaki irin su Goggo Halima. Kowa ya kasa mata Mgana Sai Baban Kaduna ne ya Fizge Hannun Zain din yana Fadin"Ke miye haka..? Wannan wani  Rashin Hankali ne..? Baki ganin Halin Dayake ciki..? Ya Fada Cikin Takaichi kamar ya maketa Kuka ta kara sakamai Zatayi mgana Zakiya tazo Ta jata Tana Fadin"Kuyi Hakuri Don Allah..Ta saka Control din kanta ne Da Halin Dayake Ciki ne.."Inna Hannatu Dake Gefe ta Lailayo Ashar Tana Fadin"Kaza kazan Halin Data ke ciki.. Duk son data kemai Takai mahaifansa ne..? Nace baga uwarsa nan da Ubansa ba Me kika ga sunyi..? Sai ke karan kada Miya Matsa ki bamu Waje Maras kunya"Sumi Sumi Zakiya Taja Dina Dake kuka suka koma Gefe Zakiya Ta kalli Dina Cikin Takaichi Tana Fadin"Ki Natsu Dillah..Kina da mtsala wani Lokacin.."Dole Dina Ta natsu ammh hankalinta na wajen Zain wanda Daddyn Abuja yace aje asibiti Alhaji Tsoho ya Dakatar dasu yaje su kawo Ruwan zamzam Hajiya mama ta kawo yayi addu"a ciki ya bama Baban kaduna yace su Shafamai afuska Cikin Ikon Allah yana Shafamai sai gashi Ya sauke ajiyar Zuciya Kafin kuma ya Fara Bude Idanuwansa. Ganinsa Akan Cinyar Haddir gasu Baban kaduna sun zagayesa Gefe Daya gasu Umma komai ya Dawo mai Zumbur ya Mike su Abba na Rikoshi Yayi Saurin Cire Baban Rigan jikinsa yana Fadin"Ku sakeni naje na Nemota..Wlh bazan iya Rayuwa bata ba...Bazan iya ba"Yake Fada kamar wanda ya Zare Baban kaduna da Haddir ke Rikesa Abba kuwa Da Daddyn Abuja kwalla suke dama sune masu Raunin ganin yaki yarda ya zauna yasa Alhaji Tsoho ya Daga baki ya Kirashi Sunansa. "Zainullahi...kai Zainullah yaka nan."Jin Alhaji Tsoho na Kiransa yasa ya Dakata da Neman Fitan Dayake ya Zubamai Ido yana Hawaye Cikin kuka yake Fadin"Alhaji Tsoho kagani ko..? Zainata Tatafi ta barni sai da nace ku bani matata aka ki bani..Ku barni na Taje na Nemota.."Alhaji Tsoho ya kalli Haddir yana Fadin"Hadiru zaunar Dashi.."Haddir ya zaunar Dashi Kan Kujera Dakyar sai Sambatu yake,Kana Alhaji Tsoho ya kalli su Umma da Nene dasu Zafeera Dake kuka yace"Kuyi hakuri kubar kukanan..Aminatu Tafi Da Goggo Halima Dakinki ki gayamata komai Ya kamata tasani yanzu.."Ba musu goggo Halima Tabi bayan Hajiya Mama Daman Ta kosa Taji me ya Faru Ga kuma Tashin Hankalin Data ke ciki na Takardan Zaina,Suna Tafiya Alhaji Tsoho ya juya yana kallon su Mama safiya Lokaci Daya yana Fadin"Hannatu da Rukayyah da Wasu Cikin yan"uwanki su Dauki Hamdiya Zuwa Dakinta Saboda kunga suna Waje suna Jiranku ba Dadi..Ku Tafi ku kaita Dakinta Allah basu zaman Lafiya.." Suka amsa da Ameen Jiki a sanyaye kafin Alhaji Tsoho ya Juya Ya kalli Haddir yana Fadin"Kai kuma Hadiru ka kara Komawa ka Dudduba Hanya da kuma Tasha..In Allah yasa batayi Nisa ba Shikenan in kuma Tayi Allah ya Tsareta aduk Inda zata je...Kaddaran Data Fadamana kenan sai Hakuri.."Haddir ya gyada kai yana Fadin"To Alhaji Tsoho.."Ya mike kenen Zain Shima ya mike yana Fadin"mu tafi Tare Haddir..! Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a Koma ka zauna..Ina zaka Cikin wannan Halin..? Cikin Karaya da Muryan kuka Zain yace"Taya Zakacemin na zauna alhalin Matata Ta bace ba"a ganta ba..? Bazan zauna ba din sai naje Wlh.."Yafada Harda Rantsuwa Cikin Fada,Alhaji Tsoho ya kada kai yana Fadin"Kai Bashir kamasa ya zauna..Ba inda zaka nace Zainullahi.." Zain zai kara mgana Baban kaduna ya Hanashi Da Fadin"Kaga koma ka zauna Jiri fa kake gani koma ka zauna.."Zain ya koma ya zauna yana Fadin"Baba Firstlove ce Fa tace wai Tatafi..? Ina zata..? Kuma fa Tace Tana da Ciki Baba Bata da inda zata Baba kabarni naje na Nemota.."Abba ya kauda kai yana Sharan kwallah Daddyn Abuja ne ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Karka damu za"a ganta da ikon Allah.." Shuru kawai Zain yayi ya maida Fuskansa Kan Tafukan Hannuwansa yana Rera Siririn kuka,Haddir yamike zai Tafi Zafeera Ta Mike Tana Sharan kwallah Tace"Zan bisu Alhaji Tsoho.."Da Sauri Umma ta mike Tana Fadin"Nima zani.."Da Sauri Alhaji Tsoho yace"A"a ke Fatima ki zauna..Kai Hadiru ku Tafi da Zafeera.."Kuka Umma Ta saka Zareena ta Riketa Tana Lallashinta. Haddir da Zafeera suka Fice da Sauri Suna Fita Yan Kai Amarya suka Fara Fita Zuciyoyi ba Dadi ba wanda yabi Takan Dina Da Zakiya inna Rukayyah da Inna Hannatu sai Dangin Mama Safiya,da Mom iklima Suka Tafi da Hamdiya Kawayenta Tun dazu wasu abokan ango suka yi gaba Dasu Inna Halima kuma Tana Dakin Hajiya Mama tana ta Sharan kwallah Bayan Hajiya Mama ta gayamai komai Tana Fadin"Wauta ne ke Damun Halima in banda Sarkaci Data saka kafa Tatafi ina zata..?Tana da Inda yafi nan ne..? Allah Sarki Hajiya Fatima kin cika uwa Nagari.."Take Fada Tana kuka Hajiya Mama na bata baki Su Umma na Falo suma suna nasu Kukan Domin Zain banda kuka da sambatu ba abunda yake,Jin kiran salla yasa Alhaji Tsoho yace kowa yaje yayi sallah Su Umma suka koma Ciki su Abba suka Fita Zuwa sallah Harda Zain din wanda Baban kaduna yake Rike Dashi Gabadaya baya gani Sosai In ya sakesa zai iya Fadi Sambatun ambaton Firstlove kadai yake gwanin Tsausayi da kuka, Mama Safiya kuma Sauran yan"uwanta suka Fara Shirin Tafiya Alhaji Tsoho Dakinsa ya koma Cikin Damuwa Domin yayi sallah. Dakyar Umma Tayi sallah sai kuka Take Tana Rokon Goggo Halima Kan ta yafemata itace Sillan komai ita kuma Goggo Halima na basu hakuri Nene da zainab har sun Share Hawayensu Kowa kagani Cikin Damuwa Mama Safiya sai Fadi Take Allah ya bayyana wannan yarinyar,Dina kuwa da zakiya ba wanda yasan Fitansu Sai dai aka ga basu Ashe Zakiya ce Taja Dina suka bar Gidan ganin Tana kuka Tana neman kara ja musu Abun mgana Gidanta ta kaita Tana Mata Fadan meyasa Ta cika Mtaala ne..? Yadda yau gidan Ya Rikice Daman gashi ana Jin Haushinta sai ace itace ma Sanadiyar Tafiyar ma Halimar. Bangaran su Haddir kuwa haka suka Dawo ba wani Labari mai Dadi Wannan Labarin ya sa sai da Zain ya kara Suma Cikin Daukewar Numfashi Hankula suka kara Tashi an Daukesa Zuwa asibinsu Kenan Ita ma Umma ta Suma sai da aka sakamata Ruwa Gida ya Rikice ko abinci ba wanda yabi ta kai Dangin Mama Safiya ganin ba Lafiya suka yi sallama suka wuce bayan Sunyi Fatan Allah ya bayyana Halima. Zain ya Shiga Doguwar Suma ne Dakyar aka Daidaita Numfashinsa aka sakamai Oxygen su Dr.Imran ne sukayi Attending dinsa Domin Dr.Haddir ya kaasa Tabuka komai Saboda Tashin Hankali Daki na musamman aka kai Zain Su Abba Duk suna asibitin Tare da Zain harda Zafeera kowanne kagani Hankali atashe acikin Zukatansu kuma Rauni ne Da kuma Fatan Allah bayyana Halima Abba kuma Yaji Tsausayin Zain dayasani da Tuni ya yafemai inda yasan haka zai Faru Daya saka baki Umma ta bashi Matarsa da Duk haka bai Faru ba addu"a kawai yake Allah Tada kafada Baban Kaduna kuma wani Abokinsa ya Kira Dake aiki nan Gidan Tv na garin Bauchi Ya gayamai Bacewar Halima Bashi da Hotonra Haddir ya saka ya Turamai Hotonta da kayan Dake Jikinta da kuma Cikakken Sunanta,Shima bai da Hoton nata awayar Zain dake Hannunsa ya Cira ya Turamai da Cikakken Bayanin Zaina din ko Allah yasa za"a dace yadai ce yanzu zai saka Duka Cigiyan In da Rabo za"a dace ko kuma wani yazo yabada Bayanin ya ganta. **** Bangaran Zaina kuwa Tana Ta Tafiya sai da Taga tayi Nisa da GRA kana ta Tsaya Tana Haki Domin ta Dade batayi Tafiyar kasa haka ba,waige waige ta Farayi saI kuma Lokacin Tunanin ina ta Nufa yazo mata Tana Tunanin Bayan Gada da kano Bata Taba zuwa ko"ina ba sai ko Lagos kuma yanzu bai kamata Taje ko Daya Daga Ciki ba Tana wannan Tunanin ne Taji mai adaidaitan Daya Tsaya gabanta yana Fadin"Hajiya Tafiya ne..? Kallonsa Tayi Sai kuma ta Juya Bayanta Tana tsoron kada ayi Saurin ganin Takardan nan abiyo Sawunta Sai kawai Taji bakinta ya Furta"Tasha zaka kaini inda zan samu Motar barin garin nan.."Bai damu da yanayinta ba Yace ta Shigo ya kaita da Sauri ta Shiga yaja suka Tafi,Tun acikin adaidaitan TaFara Kuka Tanayi tana Sharan kwallah basu Dauki Lokaci ba sai gasu Cikin Tasha Suna Zuwa mai Adaidaitan yace"Gamu Tasha Hajiya ina zaki ne Hada..? Cikin Muryan data Shake da kuka Zaina tace"Ina zani kuma..? Nima bansani ba.."Da sauri mai adaidaitan ya waigo Yana kallonta kafin yace"Topha..Baki sani ba kuma..? Cikin Sharan kwallah Zaina Tace"Eh ammh nan Motocin ina ne..? Mai adaidaitan yace"Motocin Lodin Bauchi Zuwa Fambeguwa da garuruwan Dake wajen har Zaria sai kuma na Bauchi Zuwa Zaria da kuma ta Zuwa kano.." Cikin Wani Sanyi Zaina Tace"Zaria..? zaria ta kaduna State.."? Mai adaidaitan Cikin mamaki yace"Kwarai Hajiya.."Zaina na kara Kallon Kudin Hannunta Tace"Bari na Hau ta Zarian.."Da sauri mai adaidaitan ya Fito yana Fadin"To muje na sama miki Motar.."Jin haka yasa ta Fito Tana Bin Tashar da kallo Tunda Take bata Taba zuwa tasha ba yau ga Dalili ya kawota Dankwakinta Ta warware ta kara Nanndawa aka Ta Rufe Fuskarta Dakyau Tabi mai Adaidaitan zuwa wajen da Motocin ke fake suna zuwa wani Dan Union  mai adaidatan yayi mao mgana Shi kuma yace mai Motar zaria Ko me yaceme.?sai ya juyo ga Zaina yana Fadin"Kinji yace Ba Motar da Zata Zaria Direct sai dai ki Hau Ta kano in kinje chan zaki samu ta Zarian Direct.." Zaina Bata da Zabi Sai kawai Tace"Shikenan.."Mai adaidaitan Ta kallah Tana Tambayanshi Kudinsa yace"Dari uku ne.."Dubu Dayan ta Dauka Ta bashi ya Fasa ya bata Chanji yana mata Allah ya kiyaye Hanya tace Ameen ta Wuce Tabi Bayan Dan Union din yana Fadin ko Tana da kaya ne..? Tagirgiza kai kawai Har wajen Mota sukaje Kiran Sharron Ta kusa Cika Sauran Mutum Biyu Ta Cika akace ta Shiga ta zauna Ta Shiga Ta zauna Tana jin wani Hawaye na cika idanuwanta Tana Shiga sai ga Wani yazo Ya Shiga Ba Jimawa kawai suka Tashi Sun Fara Tafiya kenan kwandasta yace kowa ya Hado kudin Mota Cikin kasala lokaci Daya Tana kara Rufe fuskata tace"Nawa ne kudin Motan..? Cikin Sauri kwandastan yace"Dubu Biyu ne Hajiya  kudin Motanki zuwa Kano."Waro Ido Zaina Tayi Gabanta na Faduwa Lokaci Daya tana kara kallon Kudin Hannunta Dubu Daya da Dari bakwai,kallon Kwadastan tayi Shima yana kallonta yace"Yadai Hajiya..? Cikin In ina Zaina tace"Don...Allah...ka..min hakuri...Kudina bai kai ba Dubu Daya da Dari bakwai gareni na zata iyakarsa 1500 ne.."Cikin kallon Sannu ko Kwandastan ya Bita Dashi kafin yace"Lalle nema kaji wata yar rainin wayau oga..? Direban Dake gaba yana Driving ya waigo yana Fadin Lafiya nan kwadastan ya kwashe komai ya gayamai Direban daman Dan Shaye Shaye ne yace"Bari na Tsayamu Sauketa..Karya Take Yanzu haka irin yan iska nan ne Masu Zuwa bariki bada kafar Dama ba.."Kwasdastan yace.." Daga ganinta kuwa oga."Yafada yana kallon Zaina wacce ta Dukar dakai Tana Hawaye Gabadaya hankalin yan Motan ya koma kanta kowa sai Tofa albarkacin bakinsu suke Tun alokacin  Zaina Taji ta Fara Nadaman Wannan Fitowar Datayi ganin Direban na shirin Tsayawa ne yasa wani Dake zaune agaba Tun Dazu bai ce komai ba ya ciro 300 ya mika ma Kwadastan ta baya yana Fadin gashi nan ya cikamata Suje Allah ya kaisu lafiya Sai Lokacin Kwandastan da Direba suka yi Shuru ya karbi kudin yace Zaina ta kawo na Hannunta ta mikamai sai Hararanta yake maida kanta Tayi kasa kawai Tana Hawaye Lokaci Daya Tana Share Hawayenta da Gefen Damkwalinta. Cikin Ikon Allah Wajen 3:00pm na Rana suka isa kano Saboda Rashin Mutumcin Direban Nan ko Tasha bai kai Zaina ba ya Sauketa nan Bakin Hanya Da yan Motan suka mai mgana yace Shi haka kurum bai yarda da ita ba Tunda dai an zo kanon Shikenan Zaina Taji ta Muzanta Sosai ko Tsayaawa ma Batayi ba Ta Juya ta Fara Tafiya yan Motan suka Bita da kallo wasu na Fadin gaskiyan Diraben ne Suma basu yarda da Zaina ba kamar wata mara gaskiya nan dai suka wuce suka Barta Tana ta Tafiya akasan Abakin Titi Motoci nata wucewa da Adaidaita Tafe take kawai Tana kuka da Nadaman Fitowarta Tana Tunanin ko Ta koma gida ne..? Ammh ina Taga kudin Mota..? Ina zata..? Wa zata Nufa..? Inda ma take bata ma sani ba Kuka kawai take Tana Sharan kwallah kamar an ce ta Juya sai ga Wata golf da sauri ta saka hannu ta tsaidata ta Faka agabanta Sai taja ta Tsaya Direba ne amotan sai wani a agefensa sai Wata Mace abayan Motan ita kadai ta Hakimce,Dukowa Direban yayi yana Fadin"Hajiya ina Zuwa..? Da Kamar bazatayi mgana Ganin Abunda wanchan Direban yayi mata ammh sai tace"Za...Zaria zani.."Da Sauri yace"Ikon Allah muma ma chan muka Nufa..Hajiya Don Allah bari na kara Mutum Daya.."Daga Bayan tace"Bakomai.." Ya Bude Ma Zaina gaban Motan yana Fadin"Kai bawan Allah gyara mata..Ta zauna ke Shigo.."Zaina tayi kwalkwal kafin tace"Ammh sai dai ka Taimaka min bani da kudin Mota.."Wani sakaran kallo Shima ya Bita dashi kafin yace"Allah ko..? Daman har yanzu akwai masu wannan Taimakon..? Gaskiya kiyi Hakuri ni Sana"a na Fito ba Taimako..". Da Sauri Zaina Tace"Don Allah ka Taimakamin.."Ta Fada Tana Hawaye karamin Tsaki yaja kafin ya Taka Motarsa yana Fadin"Kiyi hakuri kila mai Taimakon yazo.."Yana Shirin Tafiya ne Matar Dake Baya wacce ke Kallon Abunda ya Faru Tace"Ka Dauketa..zan Biya.."Da Sauri ya juyo yana Fadin"Zaki Biya fa Hajiya..? Ta gyada kai Cikin Washe baki yace"Shikenan Hajiya..Ke Shigo ki godema Allah hajiya ta Biya miki.."Jin haka yasa Zaina ta Sauke ajiyan zuciya ta kama Murfin Motan ta Shiga Tana Sauke Numfashi Idanuwaanta duk sun kumbura saboda kuka Sai da Ta Daidaita zamanta Tana matsawa Domin Taga kafadanta na Gogan Namijin Dake kusa da ita sai da suka Fara Tafiya kana ta waiga Bayanta Tana Fadin"Nagode Haji...! Mganarta ta makale ne Ganin Wacce Direban ya ke kira da Hajiya Wata kyakyawan Farar mace ce mai kyau Gata Fara ga Dogon Hanci da Tsukikin baki,Tana Sanye cikin Shigar Doguwar Rigar material Buba wacce Taji Stone work Kayan Jikinta masu Tsada ne haka kunnuwanta da Hannayenta duka Sanye da Zinare,ta saka wani Jan Vail Ta yane kanta Dashi Kamar yadda Takalmin kafarta yake ja haka Jakarta ma Dake gefenta Ja ce mai Tsada Dogon Hancinta yana Sanye da Hudun Hanci,Kallo Farko in kayi mata zaka Fahinci Tana da Zubi Da Fulani,Sannan kuma karamar yarinya ce mai akallah Shekaru 25 aduniya Tana Zaune Cikin Mota ta Hakimce Kamar Wata Sarauniya. Kara Waro Idonta Tayi Tana kallon Zaina Bayan ta Kauda Idanuwanta Daga Taba wayarta Cikin Basarwa ta kalli Zaina wacce ta saki baki da Hanci Tana kallonta Haka kurum Taji Matar ta Burgeta Cikin Sanyin Murya Tace"Bakomai..karki damu..! Tafada Lokaci Daya Tana Cigaba da latsa wayarta Cikin Sanyin Jiki Zaina ta Daina kallonta ammh Lokaci Bayan Lokaci Tana kallonta Ta madubi kuma In Matar ta Dago suna Hada ido,Haka kurum taji Matar kawai ta Burgeta Ganin Farko Da Tayi mata Haka suke Tafiya Zaina na kallonta ta Madubi Itama in Ta Dago sai Su Hada ido Ganin haka yasa in sun Hada ido sai ta sakar mata Mirmishi Domin bata san Dalilin Yarinyar ba na yawan Nacin kallonta Shida Saura na yammah suka iso Zaria ta Sabon gari suka Shiga Wajen Bayan gidan iya ya Sauke wannan Namijin sai itama Ta Hajiyar tace ya Sauketa nan Fakawa yayi ta Bude Mota ta Fito Tana Bude Jakarta bandir din yan Dubu Dubu Ta Fito Dashi ta zari Guda 15 ta bama Direban ya karba yana Ta Godiya,Wucewa kawai Tayi Tana wani irin Taku Lokaci Daya Tana Tsaida mai Adaidaita Baki zaina ta saki tana kallon Mace iya mace wacce ta mallaki komai na ajikin Mata,Direban ne ya katseta da Fadin"Ke wai ina zaki Sauka ne..!? Da Sauri Zaina Tace"Nan zan sauka.."Kallon Mamaki yayi mata kafin yace"toh ki sauka mana ko kina Jiran sai nace ki Sauka.ne..?."Batama Tsaya Jinsa ba Ta Bude Murfin Mota Ta Fita Tana Kallon Kyakyawan matanan ta Tsaida Adaidaita ta Shiga Direban bai bi ta kanta ba ya Wuce yana Murnan ya samu kudi a asama. Tsaye Zaina Tayi Tana kallo Matarnan Adaidaitan Data Hau ya Fara Tafiya kamar Wacce ta santa sai Taji in ta Bari Tatafi Zata Rasa Madafa,Kuka ta Farayi Tana Bin kasuwar da kallo Kowa sai Harkan gabansa kawai yake ba Ruwan wani ma Da ita bata Taba Zuwa Zaria ba sai yau Tana Cikin wannan Halin Taji an Dafa kafadanta da Sauri Ta Waigo Sai kawai Taga Kyakyawan Hajiyanan Ganinta yasa ta Sauke Numfashi Ta saki Mirmishi. Cikim mamaki Tace"Lafiya..? Na shiga adaidaita mai Adaidaitan yace min ga wata chan tana kallonmu Tana kuka ko Tare muke..? Sai da nace ya Tsaya na Fito na ganki lafiya..? Ina ne Gidanku..? Wata anguwa zaki..? Duka Ta Jero mata Tambayoyin Cikim kulawa,Da Sauri Zaina Tace"Bansan ko"ina ba..Bansan ina zani ba.."Cikin mamakinta Tace"Topha..Wajen wa to kika zo..? Sai Zaina ta Fara Hawaye Tana Fadin"Bakowa.."Shuru Tayi Tana kallonta kafin Tace"Shikenan bar kukanan ki gayamin me sunanki kuma Daga Ina kike..? Zaina Tace"Sunana Halima..Daga Bauchi nake.."Haka kurum Taji bata son Ta gayamata karya Cikin Kallonta sama da kasa matar tace"Bazan matsa naji me ya Fito Dake Daga Gida ba...ina ganinki naji kin bani Tsausayi kuma zan iya Taimakonki ammh Zan Fada Miki gaskiya Domin Ita ke Rike Dani har yau har gobe..Ni sunana AISHA FARIDA mutane Suna kira da SHOLLY  ni ba yar garin Nan bace Yar Gombace ammh na Zama yar Zaria Domin nafi Shekara Hudu acikinta kuma ni ba Zaune nake gaban Iyayena ba Zaman kaina nake in kin amince zan Tafi Dake gidan Dana ke zaune Gidan Uwar Dakina ce Dake nan anguwan gwado Gidan UWAR MATA..! Zaina Taji gabanta ya Fadi ta kalli matar sai kuma Taji ta Natsu da ita Cikin Ranta Tana Tunanin ina ta Barta Tatafi ina Zata Cikin Sauri Tace"Shikenan zan Biki nagode Anty Farida.."Mirmishi Aisha Farida Tayi mata kafin tace"Ok...Shikenan muje gida Sa"adiya kiyi wanka kiyi sallah kici Abinci ki Huta ko Domin naga Duk kin gaji.." Murna Ta kama Zaina Ta fara Hawaye Tana Fadin"Nagode Sosai..Nagode.."Aisha Farida tace"Karki damu.."Daga haka Taja Hannunta Zuwa Cikin Napen Din Tana Fadin"Muje mallam...! *Tammat Bihamdulillah...* _Alhamdulillah nan na kawo karshen wannan Labarin ZAINAZAIN kashi na Daya kamar yadda na Fada muku Labarin yana da Shashe Biyu ne mun gama Shashe na Daya zamu shiga Shashi na Biyu,Tabbas Zainzain kashi Na Daya yazo akyauta ne kamar yadda kuka gani sai dai kuma ku sani Kashi na Biyu na wannan Labarin IS NOT FOR FREE..!,Na Tabbata indai Soyayyar da na gani ne Dalilin Rubuta wannan Labarin Ko nawa na saka kudin Labarin nan zaku Siyeshi har ku ninkasa ma Nasan da yawanku Masoyan Amana ne Kama Daga Wsop Zuwa Wattpad Na Tabbata Zaku yi TuruRuruwa wajen Siyan Kashi na Biyun wannan Labarin Kodomin ganin Yadda Zata kaya Ga Zaina ta bar Gida ta Fada Hannu Aisha Farida Sholly kuma Sholly Zaman kanta Take agidan Uwar Dakinta Uwar mata yaya Rayuwar Zaina Zata kasance atsakiyar karuwai..? Yaya Rayuwar Zain zata kasance ba Zaina..? Yaya Dina.? Shin Tana Haihuwa..? Xata samu Nasaram auran zain da samun Soyayyarsa..? Yaya Duka Ahalin Zain Zasu ji da wannan Salon al"amarin Daya Faru dasu..? Wacece Aisha Farida..? Yaya Rayuwar Zakiya da Dina Zata kasance Daga karshe..? Shin Zaina Zata Haifi Cikin Jikinta ko kuwa..? Zata koma Ma Firstlove ko Rabuwarsu kenan..? Duka wadanan amsoshin Suna Cikin ZAINAZAIN kashi na Biyu ne Wanda zaku sameshi Cikin Farashi mai Sauki da yardan Allah.._ *ZAINZAIN PART 2 KUDIN KARATUNSA ₦250 NE KACHAL GA MASU AMFANI DA BANKI ZAKU TURA SHEDAR BIYANKU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK SAI ATURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 09069067488,KAI TSAYE MUTUM ZAI TSINCI KANSA A PAID GROUP,MASU TURO KATIN WAYA KUMA ZASU BIYA ₦300 NE KACHAL INDA ZASU TURO HOTON KATINSU TA WANNAN LAMBAR 09069067488,KAI TSAYE ZASU TSINCI KANSU A PAID GROUP DIN DA ZAMU FARA POSTING DIN ZAINAZAINA KASHI NA BIYU MUTANENMU NA NIGER KUMA ZASU TUNTUBI WANNAN LAMBAR WAYAR +22794775574 SAI KUNZO ALLAH YA BAKU IKON SIYA AMEEN...* *01/07/2021* *Janafty....*