*B2ZZ...0️⃣1️⃣* *Bismillahir Rahmanir Rahim* *IS NOT FOR FREE...Via Card ₦300via Bank ₦250, 0552179550...Jamila Umar Gtb or 09069067488..* *ZARIA* _Area:Sabongari_ *Anguwan gwado* "Tunda suka Shigo anguwar Halima ke ta waige waige Tana kallon Wurare Abun ya bata mamaki ganin inda suka Shigo anguwa ce Gatanan dai Sai Cikowar Jama"a ko"ina da kuma Rashin Tsarin Gina ginan Gidaje ko"ina dai gashinan Rakwachan kawai Haka Take gani acikin Idanuwanta In sun Hada ido da Farida sai dai kawai ta sakar mata Mirmishi Itama ta maida mata Martanin Mirmishinta ammh Azahirin gaskiya Jikin Halima ya gama yin Sanyi Tana Tunanin Ta shigo wani Fannin Rayuwa kuma na Dabam. Hankalinta ya Tsaya ne Cak Dataji Farida na Fadin Mai Adaidaitan ya Dakata anan Da Sauri ta Dago kanta Tana Kare ma Inda suka Tsaya kallo,tunda Suna Cikin adaidaitan Ta Hangi Dandanzon Mutane maza da mata Suna ta Shige suna Fita,Tana chan Tana kalle kalle Taga Farida Ta Fita Daga Cikin adaidaitan Ta Bude jakarta Ta zaro Naira Dubu Ta mikamai ya karba yana Ta Godiya,Lokaci Daya Ta Juya Tana kallon Halima Data kasa Fitowa Daga adaidaitan Tana Fadin''Sa"adiya Fito mana mun iso.." Jin Haka yasa Halima ta Gyara zaman mayafin kanta kana ta Sako Kafarta ta Fito Tana kara Jan Sikat dinta Daya kaimata Har kasa yana neman kadata Lokaci Daya kuma tana kara Damke Dankwalin Dake Hannunta,Tunda mai adaidaitan ya Saukesu Ido ya Dawo kansu Kamar Dama su ake Jira Riko Hannunta Farida Tayi Ta nufi wani Mulmulallan Gidan Siminti Ginin zamani Wanda yake Shafe da wani Fenti mai kurzukurzu kalan Ruwan kuka Daga Kofar Gidan akwai manyan Dakali Dama da Hauni Daga Gefensa kuma akwai wani katon Smybol da akayi Rubutu da Manyan Baki *GIDAN ABINCI NA UWAR MATA* Taga an Rubuta kana ta kai Duba da wajen Data ga Zirga Zirgan mutane maza da mata yafi yawa sai taga Daga bakin Wajen Tana Hanga ciki Waje ne Falo Babba,Wanda aka kawatashi da Kujeru da Teburan cin Abinci Rukuni Rukuni,Mutane Dai dai ku suna kai suna cin abinci Duk da bata Shiga wajen ba ta Fahinci Irin Gidan Abinci ne namu na Gargajiya ammh an zamanantashi. Kofar Da zata sadashi su da Shiga Cikin Gidan Dake Hade da Gidan Abincin Farida Ta Nufa Tana Rike da Hannun Halima Namiji Daya ne ke zaune kan Dakalin Sai wasu mata Biyu sun sakashi a Tsakiya kowacce kanta ba Dankwali sai Uban gashin Doki kuma Dukkansu Suna Sanye da Shigace ta Banza Wanda ya bama Halima mamaki na yadda mace Zata iya Fita Har Waje ta zauna cikin wannan yanayin. Namijin ne ya mike da Sauri ya sha Gaban Farida Yana Washe mata baki Gefe Daya yana Kura ma Halima ido Wacce ta koma Bayan Farida Ta Rabe Tun bada ga Irin kallon Banzan da Matan Dake zaune suke Jifanta dashi ba Ga kuma wannan Bakin Namiji Wanda Shaye Shaye ya maida shi Wani kamar mahaukaci. Cikin Mamaki da Hade Fuska Farida tace"Kacharalle Lafiyanka kuwa..? Bani Hanya na wuce..? Tafada Cikin Hade Duka Fuskarta Cikin Washe mata Jajayen Manyan Hakoransa yace"Allah taimaki Sholly dinmu..Allah ya Taimaki manyan Mata naku ba irin namu bane.Allah ya Taimaki Shalelen Uwar mata..Allah Huci Zuciyar Hajiya Sholly Dama Sannu da zuwa zan yi miki kawai..'Yafada Lokaci Daya yana kara Kure Halima da wani kallo Har yana wani karkace kai Tabe baki kawai Tayi taZuge Jakarta Ta Zaro 1k ta mikamai Tana Fadin"'Karbi..aje asha Ayi Tatil..Dama Ita kazo nema ba Sannu da zuwa kazomin ba.." Tafada Tana kokarin Jam Hannun Halima ammh sai yaki bata Hanya Karban kudin yayi Yana wani Sosa gemunsa Dashi Ganin irin kallon Dayake ma Halima ne yasa Jikinta ya Fara Rawa ta kara Rabewa jikin Farida Idanuwanta sun Cika da kwallah Cikin Fusata Farida Tace'Bamu Hanya Kacha..." Dariya ya saki yana Fadin"Miye na Fusata..? Abun bana Fada bane daman wannan Haja nake Tambaya Sholly itama yar Eh ya nen ne..? Da sauri Tace"Kul...Karka kuskura Wannan ba irin wacce ka sani ba..Wutsiyar Rakumi Tayi nesa da kasa Kar in kara ganin kana kallonta.."Da Sauri ya Daga Hannu alaman Saranda yana Fadin"Na Tuba nabi Allah na Biki...Shalelen Uwar mata ai in nakara sai ki saka Ta Korani na Shiga Duniya na lalace ko ba Haka ba Suby..? Wacce aka Kira da Suby Tawani Juya ido Tana Fadin"Uhm...mutum dai yasan Uwar mata Ta hana kawo Wata bakuwa gidanan sai da izininta.."Tafada Tana Wani Taunan Cimgam Tana kuma kallon wani Barayin Farida Ta Ja Hannun Halima suka Shige Tana Fadin"Ki kirata ki Fadamata Ni Sholly na kawo Wata Bakuwa bada saninta ba Kinji Suby..? Karamar yar iska kawai."Daga haka suka Shige Suka bar Suby na tura baki Tana Kunkuni Kachallare ya Kwashe Da Dariya Shida Adamalli Wacce Ta kalli Suby Tana Fadin"Ashe dai kina Tsoron..? Suby Tace"Bana Tsoronta...Ita din Banza..Karuwanci Take shi nake yi bata isa naji Tsoronta ba.."Kachallare ya karkace kai yana Fadin"Yo daman Uban wayace ba karuwanci kike ba Suby..? Ammh kema kin sani Duk Lalacewar Daji bai kai in Giwa ta Mutu Kiyashi Yajata ba Kinsan kaf karuwan Gidanan ba wacce Ta kama kafar Sholly Daga Sabbin Har Tsoffin su ku Wlh Baku kama Kafarta ba Yarinya ga kyau da Dirin mata ga Farinjini Sholly Tana Iskanci ammh nata mai aji ne Suby kema kinsani Gata dai Cikin Batattu irinmu ammh Zuciyarta mai kyau ne Shiyasa ta zama ta gaban Goshin Uwar mata bata da kamarta ko ya kika ce Adamalli..? Hannu Ta bashi Suka Tafa Kafin Ta Saki Guda Tana Fadin"Wlh Kam Fadi ka kara Kacha..mai Hassada da Sholly sai da fa ya yagaji ya Bari..Ta samu Duniya Allah ya Daga Tauraruwarta Inda Taso Bazata zauna acikin Gidan ba Domin Tana da kudi Tana Harka da masu kudin Shiyasa komai tace Uwar mata bata Musu da ita saboda Tana Ijiye mata yan Bugun Abuja.."Kacharalle yace"Sosai..Zainabu abu zakice mai mganin Tsofaffin zamani.."Suby Data Cika da Batse ta mike Fuu Ta Shige Cikin Gidan su Adamalli suka Rakata da Dariya. Kimanin Dakunan Dake wannan Gidan goma sha Biyu ne12 kenan Shida ajere Shida ajere kuma kowanne da Room Lambarsa ajiki Tunda Ga Room1 har zuwa Room 12 gida ne dan madaidaici mai karamin Tsakar gida ammh yana Shafe da Siminti,Suna Shiga suka ga wasu mata Biyu Zaune Suna Buga Lido,kofar wani Daki Dake kulle da kwado Lokacin da Halima ke kare ma Sauran Dakunan kallo Babu wanda ke Bude sai Guda Daya Shima kamar an sakayoshi ne Suna Shigowa yan matan Dake Buga Lidon nan suka Juyo suna kallonsu Ba Farida suke kallo ba Sun fi kura ma Halima ido Suna kallonta Cike da mamaki Itama su Take kallo Cikin mamakin Shigar da yanayinsu Daya Tana sanye da Gajeren wando na maza da wata Half vest,Dayan kuma Daurin Kirji ne da karamin zani Duka Cinyoyinta Suna Waje kawunansu ba kallafi Kowace gashin doki ya Zubo mata. Cikin Mamaki Dukkansu suka Mike Farida kuwa Cikin Daka musu Tsawa Tace"Wani irin iskanci ne kuma wannan Zuly da Deeze..? Kofar Daki na ne ya zama Dandalin Buga Lidonku..? Ku ina naku kofar Haraban..? Cikin Sanyin Jiki Wacce aka Kira da Zuly Tace"Yi hakuri Sholly ba..."Ku kaucemin Daga gani Don Allah bana son wani Dogom Turanci kada wacce ta karamin wannan iskanci...Kowaccenku ta Tsaya Inda aka ijiyeta bana son Iskanci da Burauba Wlh.."Tafada Cikin Bacin rai Lokaci Daya Tana Hararansu ba Gaddama suka Duka suka kwashe komai nasu suka Wuce simi simi suka koma Kofar Room8 suka Kafa achan Farida Ta Rakasu da Tsaki Tana Fadin"Kananan kwari.." Daga haka ta karisa Jikin Kofar Ta Bude Jakarta ta Fiddo wani karamin key ta Zura ta Bude katon Kwadon Dake Jikin Kofan kafin ta waigo Tana Fadin"Bismillah Sa"adiya..Shigo ki yi wanka kici Abinci ki Huta ko..? Halima Tayi Mirmishin yake kafin tace"Nagode Anty Farida.."Lokaci Daya Tana kokarin Cire takalminta Farida ta Dakatar da ita da Fadin"A"a shigo Dashi Ciki." Cikin suka Shiga Tana Bin Bayan Farida suna Shiga Farida ta saki Labulan Dakin Loksci Daya da sakayo Kofar Zully ta kalli Deeze Kafin Cikin Rada Tace"Wai kinga me nake gani..? Kardai Bayan karuwanci Bin mata Sholly ta koma..? Deezee tace"Hm...Bansani ba..Nidai Zully kyaleni da wannan Gulmar Koma menene ta koma ina Ruwanki Bariki gidan fa kazo ne nazo ne..Ko Uwar mata da muke karkashinta Bata ce maa Dole ga Abunda zamu yi ba Kowa Abunda yaga Dama yake aikatawa ai Yancin kenan.."Zully Tace"Lalle fa..Ammh ai ta Karya Dokar Uwar Mata Tunda Tunda aka samu mtsala kan wannan Yarinyar da Samira ta kawo Uwar mata ta hana kawo wata Bakuwar Fuska batare da saninta ba.."Deezee na Sosa kanta Tana Fadin"Kowa ya iya allonsa ya wanke Zully..In kikace Gulmar Sholly zaki yi Tayi haka zaki kare...Sai ta Biya allonta Tawanke tazo ta Hada da naki  ta karanta kuma ta Biya ta wanke Bariki ai gidan kazo nazo ne...Ammh kisani itama Shigowarta Sa"a ce Wanda yayi Sa"a ya gama Dacewa kamar Sholly.."Jin Deezee bata bata Fuska bane yasa Ta bar mganar suka Cigaba da Buga Lido Dinsu. Halima mamaki ya Daskaran da Ita ganin irin kayan More Rayuwan Dake Dakin Farida Daki ne Babba mai Ciki Daya sai ta saka wasu Hadaddun Labulaiya Ta Raba Falo da Uwar Daka Daga yammah ga Kofar Tiolet afalon akwai kayan kallo Kujera guda Biyu Daga kasa kuma karamin Cafet da Center Table,Daga chan kuma Gefe wajen kofa kayan Girki ne kama Daga gas Tukunya Filets Da kofuna Da sauransu sai kwalayan su Indomie Macaroni Cuscus,Taliya Madara Da sauran kayan Tea,su Complex da kwai ne Tarkace dai gasunan su Kittle ne Kaya dai gasunan kamar irin Kitchen Tunda ga Duk alamu nan take Girki Halima bata kara Sakin baki ba sai Da Taga ta Dake Labulan Daya Raba Dakin Ta Hangi Wata Dundumemiyar katifa Kwance akasa Dataji Shimfidu alfarma,Sai Gefenta kuma wani katom Wardrope ne mai kofa Hudu samansa kuma Tarin akwatuna ne masu kyau da Tsari Daga gefe kuma ma"ajiyar Takalma ne da jakunkuna Dakin in ka kalleshi zaka Fahimci cewa Dakin ne yayi kankanta da anga kaya acikinsu Kodaga yanayin Faridan zaka Fahimci yar gayu ce ta Karshe kuma Ta Shigo Harkan bariki a sa"a ta Tara Dukiya Domin kayan Kudi ne Duka Suka cika Dakin kuma Duk Gidan Dakinta yafi ko"ina Girma kuma ita kadai keda Tiolet aciki ba saboda komai ba sai saboda ita yar gaban Goshin Uwar Mata ce Tana Matukar ji da ita. Gyalenta ta Cire da jakarta ta Wurgasu nan saman katifan kana ta Cire takalminta ta watsashi nan gefen mika Tayi alaman ta gaji Sosai barci ne ma a idanuwanta Domin Jiya Alhajinta bai barta ta Runtsa ba, Juyowa Tayi ganin Halima na kallonta yasa Tace"Sa"adiya Taho ki zauna mana kin Tsaya atsaye..' Halima Ta kasa gaba ta kasa Baya sai da Farida tazo Ta Riko Hannunta Zuwa Gefen Gado Ta zaunar da ita Tana Fadin"Kinga inda nake Rayuwa ko Sa"adiya.? Zaina ta kalleta Tana gyada mata kai bata Damu ba Ta Mike Tana Fadin"Kafin na ce miki komai dai bari na kunna Gas na Saka miki Ruwan Dimi ki Shiga ki Watsa kafin ki Fito na sama mana Abunda zamu ci ko..? Kai Zaina Ta Daga Tana Jin Taruwar Hawaye kafin tace"Toh.Anty Farida.."Farida ta Saki kayattacen Mirmishi Tana kallonta Kafin tace"Ban taba ganinki ba sai yau..Ammh naji Lokaci Daya Zuciyata ta yarda Dake..Kuma Ta bani Damar kar na bari ki Tafi Tunda na Fahimci Kina cikin wani Hali aklllah Farko Danayi miki sai najiki kamar wata kanwata ta Jini,Da kika kirani da Sunan Anty Farida Sai naji Tamkar kanwata Zahra ce ta Kirani..Wanda Rabon da naji an Kirani Farida Tun ina Aisha Faridata kafin na koma Sholly.." Tafada Cikin wani yanayi Lokaci Daya Kuma da Taruwar kwallah acikin idanuwanta Zaina Tana kallonta da mamakin kafin tayi mgana Tayi Saurin Juyawa ta Share kwallarta Ta Fara Kokarin kunna Gas nan take ta kunna ta Dora wata Karamar Tukunya ta Bude wani karamin Botikin Ruwa ta Diba ta Cika Tukunyar kana ta saka Murfi Ta Rufe ta koma Kusa da Zaina Dake Zaune Gefen gado Tana Binta da kallo Tace'Sa"adiya me zaki ci.? Zaina Ta Sunkunyar dakai kafin Ta Dago Tana Fadin"Bakomai Anty Farida..Bana jin Cin komai...Da Farko na Fara Nadaman wani abu ammh Haduwata Dake ya sakamin Natsuwata Nagode Anty Farida.."Tana Fada sai ga Hawaye Sharr Farida Tace"Ashh...Sa"adiya Bar kuka Taho..Ta jata Jikinta Ta Rumgume kawai Sai Zaina ta saka mata wani marayan kuka Tana Fadin"Anty Farida naji nayi Rauni gabadaya na rasa kwarin Gwiwata ban kyauta ma Umma ba ban kyauta ma Abba ban kuma kyauta ma Firstlove ba...Taya taya zan saka Rauni a Ahalin da suka maidani Mutum Anty Farida na zama Butulu Saboda Dalilin Tseratar da Aurena da Cikin Dake Jikina Na baro Mutanen da bani da kamarsu Duk Duniya na gwammace na Shiga Duniya Allah na Tubaa yanzu In da ban Hadu Dake ba wata Rayuwa zan Fada..? Take Fada tawani Kuka mai Raunana Zuciyar mai Sauraro Ita kanta Faridan Sai da Jikinta yayi sanyi ta Fara Lallashin Zaina kafin ta Dago Tana Share mata kwallah Tana Fadin"Tun kallo Farko Da nayi miki naga alaman Sabon Ciki Tare dake.." Ido Zaina ta zaro kafin Tace"Dama ana gane inada ciki Anty Farida..? Mirmishi Farida Tayi mata Har Hakoranta suka Bayyana Waje ta Mike Tana Fadin"Eh..Ga duk macen Datake iya gane alamun hakan ba...Aganin Farko Danayi miki da yanayin Tsarinki da Shigarki na Fahimci ke ba Mutuniyar banza bace..Na farko akwai yarinta Tare Dake barin ki Haka zai sa ki Fada Hannun Banza Shiyasa na zabi Tahowa Dake inda nazabi Rayuwata Duk da nasan zaki ta mamakin Me ya kawo ni nan ko..?kinga abubuwa wadanda baki gane ba ko..? Nan ba Gidan kowa ba ne Gidan KARUWAI ne wanda muke karkashin Uwargijiyanmu Wato Hajiya Hauwa Uwar mata.." Zaina ta kwalalo Ido kafin Ta Dafe Kirji Tana Fadin"Mun Shiga uku gidan karuwai Anty Farida..!? Tana Mirmishi Tace"Kwarai kuwa Sa"adiya...Nan din Gidan Karuwai ne Duk wacce kika gani agidanam Karuwa ce zaman kanta Take da Zaman yancin kanta.."Cikin Faduwar gaba Zaina Tace"Har...Harda ke Ma Anty Farida..Ke...Karu..." Ta kasa karisawa Saboda mganar Ta mata Nauyi kana kuma Wani Tsoro ya Shigeta Farida Ta saki Wani Mirmishin Dayafo kuka ciwo kafin Tace"Eh Sa"adiya...Ni nan da kika ganni Karuwa ce mai zaman kanta Da kudin Kariwanci nake komai nake kuma Rike kaina nasan zaki mamakin Meyasa banji kunya Fada miki Haka ba..? Domin wasu Karuwan in sukaje wani waje sai su rika Boye zahirinsu ko..?ni Aisha Farida bana karya bana kuma mu"amala da mai karya Duk inda na Taka ban zan ji kunyar Fadin Ni Karuwa bace Domin Tunda uwa da Uban da suka kawoni Duniya suka Kirani Karuwa Toh me ya Ragemin Sa"adiya..? Mijina wanda na bama Duka Soyayyata da kaunata Ya kirani Karuwa akwai Saura ne..? Ya'yana dana Haifa da Cikina Suma an gaya musu ni karuwa ne ina da Wani Sauran Boye Ko kuwa Wani Sauran Kima acikin Wannan Duniyan ne Sa"adiya..!Babu Wata Sauran Kima Shiyasa a ko"ina bana jin kunyar Fadin Ni KARUWA ce mai zaman kanta.." Ta Fada Lokaci Daya wasu Zafafan Hawaye masu zafi Suna Biyo Kuncinta Zaina ma kuka Take Cikin Tarin mamaki Take Fadin"Dama..Dama kina da Aure har da ya"yana Anty Farida..? Toh duk suna ina da Kuma iyayenku me kuma kika aikata suka kira karuwa har yasa Rayuwarki ta koma Haka..? Hakika zan so naji labarinki Anty Farida Ada ina kallon Nawa Labarin yafi na kowa sai kuma yanzu na Fara Tunanin naki Labarin ba komai bane akan Nawa.." Farida Bata Juyo ba Tana So Tayi Control dinta kanta karan Wayarta yasa tayi Saurin Share Hawayenta Ta juya ta Nufi Wayarta Tana ganin sunan Uwar mata na Kira Ta Tabbatar da an kai mata Rahoton Dawowarta Da Sa"adiya Bata Daga Kiran ba sai ta yanke ta saka Wayar Cikin Mode ta Tura ta kasan Filo Kafin ta Waigo Ga Zaina Tana Fadin"ki bari zan Fada Miki komai ammh ba yanzu ba..Yanzu Tashi zakiyi kiyi wanka Kiji Dadin jikinki.." Tana Gama Fadin Haka ta Juya Zuwa Cikin Tiolet din Ta Dauko Wani Botikin karfe tazo Ta Zuba maZaina Ruwa ta Surka mata Ta Dauka Ta kaimata Bayi Tace Taa Tashi Ta Shiga jikin zaina asanyaye Tatashi Ta Cire mayafin Kanta Farida ta miko mata Babban Towel tana sakarmata Labulan wajen Domin Ta bata Damar Cire kayanta ganin haka yasa Zaina ta Tube kayanta ta Daura Towel din Ta kuma Rufu da gyalenta kana Ta Fito Koda ta Fito ma Farida Bata Dakin ta Fita da Sauri Ta Bude Tiolet din Ta shiga sai Tashin kamshin Dettol yake Tiolet na Na kashin mai Floshing ne,Bayin Tsaf Dashi Komai na Bukata akwai acikin Cikin Natsuwa Zaina Tayi wanka Ta Dauro alwala Ta Fito Ganin Duhu ya Shiga Gashi Batayi Salollin Dake kanta ba. Tana Fitowa ta Iske Farida na Soya kwai Tana ganin ta Fito Ta ce ta Shiga Ciki ga kayan nan ta Dauko mata ta saka ga Darduma  nan ta Shimfida mata Tayi sallah da Toh ta amsa kafin ya Bude labulan Daya Raba Dakin Ta Shiga Ta iske ta Dauko mata Wata Hadaddiyar Doguwar Rigar yar Dubai Tana da Irinta Wanda Firstlove ya Siya mata Tuna Haka yasa sai da ta Share kwallah Zura Rigar Tayi Tana so Tace Hijabi Taga wani mai kyau kusa da kayanta Farida ta Ijiye mata Ta Dauka ta Zura Ta Tada Sallar Azahar,bayan ta idar tayi La"asar kafin ta zauna Tayi Zugum Tana Tunanin Wani Hali kuma Chan Bauchi yake..! Tasan Zuwa yanzu sun samu sakonta..! Shigowar Farida ya katse mata Tunani inda Tace bari ta Shiga wanka,Wani Babban Towel ta Dauko Ta wuce Bayi bayan ta Fito ne Itama Tayi Sallolinta Lokacin ana Kiran sallae mangariba suka Mike suka Gabatar suna Idarwa Farida Ta Ja Hannun Zaina suka koma Falom Suka zauna saman Cafet Ta jamata Farantin Data Hada komai Indomie ne ta Dafa sai kwai DataSoya sai kayan Tea Zaina Tea dim kadai Tasha kwan kuma ta Fara ci kenan Sai Tatashi Da Gudu Zuwa Bayi sai Amai Farida Ta Taimakamata ta Wanke Jikinta bayan ta gama Kana Tazo ta matsa mata ta kara Shan Tea din Tunda bata son kwan itama sama sama Taci Indomie tace ta Koshi Ta hada komai Ta kwalama Zully Kira wacce suke Tsakar Gidan suna ta Shewa sai gashi Tazo Daga Kofar Dakin taTsaya Farida ta Leka Ta mika mata Farantin Ta karba Tana ta Godiya mamaki ya kama Zaina Bata dai yi mgana ba. Komawa Zaina Tayi ta kwanta kawai Tana Jin gajiya na Tambayanta Sai Lokacin Farida ta Kunna wayarta Tana Jinta tana waya Dawani sai Shagwaba take mai kamar yana Tambayan Ya ta iso Gida ne,Ita dai Sama sama Daganan Taji Idanuwanta na Rufewa Bata kuma Farka ba sai Wajen 12 na Dare Ta ganta saman Gado Farida Ta maida ita kuma Tana kwance Gefenta Sanye da kayan Barci Tana Barci Tuna batayi Sallar Isha"i ba yasa ta Ta mike Sadaf Sadaf sai ji Tayi Farida Ta Bude Idanuwanta Tana Tambayanta ina zata Tace Bayi alwala zatayi Tayi sallah kana ta Gyada mata kai. Bayan Tayi sallar sai ta kasa komawa nan kan Darduman  ta zauna Tana ta Tsiyayan Hawaye acikin Ranta Tana jin wani iri na yau itace zata kwana agidan karuwai Farida ce Tatashi Tace Ta Koma saman katifa ta kwanta Tana da juna Biyu kuma ana so Ta Rika samun Barci Sosai Batayi musu ba ta Mike ta koma kan katifan ta Dunkule Farida Ta Rufamata Bargo Tunda akwai Wuta Fanka na Gudu Gudu da dan iska iska..! **** *Washegari* *Bauchi..* Su Abba dukkansu sun Dawo Gida Haddir ne yakwana asibiti Wajen Zain wanda Har yanzu bai Farfado ba,Dukkansu har su Umma nan gidan Alhaji tsoho Suka kwana Wanda kuma sai da Aka kira mata Likita ya Dubata ya Bata manganuna Harda na Barci aka samu tayi ta Barci sai koken koken ya Ragu,Da Safe kuma Wajen 11am na safe sai ga su Inna Hannatu sun Dawo Domin suma Chan tunda suka Tafi ba wani kwanciyar hankali sai Zullimi Tun suna chan suke ta Kiran su Abba kan Yaya ake Ciki Suna gaya musu ba wani Labari sai dai addu"a Abba yayi kuka kamar mene duka yana Dora laifin akansa. Umma kuma an samu sauki Tunda tayi Barci ammh Data Tashi Sai Hawaye dai ba mgana Goggo Halima kuwa sai kiran Chan Gada take ko da wani Labari Ammh Shuru sun ce Zaina bata je Chan ba,Shi Kanshi Alhaji Tsoho yana Cikin Damuwa sosai Hajiya mama Fadi Take gata yarinya ga juna Biyu Oh Allah ka Tsare wannan yarinyar Nene kuwa dasu Zareena da Zainab suna Tare da Umma ne Domin Tana Bukatar wani Kusa Daita Baban kaduna kuwa yana ta Kiran Abokinsa Dan Jaridanan yana gayamai Shima ba wani Labarin Abun dai sai addu"a. Sai Zuwa yammah Haddir ya Kira Waya yace Zain ya Farfado Suka Dumguma Dukkansu Harda Umma Zuwa asibitin in ka ganshi sai ka Fashemai da kuka Cikin Kwana Daya zain ya Fita Daga Hayyacinsa sai sambatu yake yana kiran sunan Zaina yana kuka yana Kokarin tashi kan sai yaje ya Nemota Sai da aka kara mai alluran Barci Su Nene da kuka suka bar asibitin Zuwa Gida Daga Umarnin Abba  Dukkansu suka Tafi Gida Umma da Nene sai Zareena da Zafeera da Zainab dasu Saudart su Inna Hannatu kuma dasu Mama Safiya suka koma Gidan Alhaji Tsoho su Abba suka bari a asibitin Wajen Zain bawan Allah. Koda su Umma suka Dawo Gida Dina bata Gidan ba kuma wanda yabi ta kanta Zafeera Da kuka ya Kodar da ita Ta Taimakama Umma Tayi wanka Tasha Tea ta bata mganugunanta tasha sai barci Ranar ko Salollinsu gamasu Sukayi Waje Daya abinci kuwa sai dai Ruwan Tea suka iya Sha Duk Dauriyan Nene haka ta Zauna afalo Tana kuka Labari kuma yakai Ko"ina Sadiq babba ya Kira Waya yace Shima Sadiq karami ya kirashi ya gayamai Shima kuma Faruq ne ya gayamai Cikin kuka Zareena Daya kira Take gayamai Abunda ya Faru Cikin Rudewa yace Gobe yana Tafe. Dukkansu suna Zaune afalo Bayan Umma Dake dakinta Tana Barci,Kowa kagani Fuska ta Kode,da kuka kaya kuma Duk ya yamutse Domin Tun kayan Bikin Jiya ne ajikim kowa bama Natsuwar wanka ballatana na Sauya kaya Sai ga Dina ta Shigo Daga Rakiyan Kawarta Zakiya Sun Shigo Falon gabadaya su Nene suka Dago suna kallonsu da mamaki Suma kallonsu suke kafin Dina ta Daga Jajayen Idanuwanta da suka sha kuka Ta kallo Zakiya itama ta kalleta kafin Ta maida kallonta kan su Nenee Wacce Ta Mike Cikin Fushi Lokaci Daya Tana Share kwallar Idanuwanta ta Nufi Su Dina. *Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Duk mace mai aji bata Jiran abun sata In Ta isa Takai Mace Mallakan Komai nata Take...* *Shakira...* 7/8/21, 11:30 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣2️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Cikin Fushi Nene ta isa gabansu Dina Tana Fadin"Daga ina kike..? Kafin nan ma Uban wa ya baki izinin saka kafa ki bar Gidan nan..? Tafada Cikin Fushi da wani bacin rai,Dina da Zakiya suka kalli Juna Dina ta kasa mgana Saboda bakinta ya fara Rawa ne Zakiya ce ta Bude baki zatayi mgana Nene Ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Karki Sake ki sakamin baki badake nayi mgana ba..! Yadda Nene ke mgana Cikin Fushi yasa su kansu Su Zareena suka Fahimci Tana Cikin Bacin Rai Wanda bako da yaushe ake ganin Fushin Nene ba ammh kuma Bayyanan Bacin Ranta wani Abu ne da kada Mutum yayi Fatan gani. Zakiya Dolenta Ta Hadiye mganar Bakinta ganin yadda Nene ke binsu da wani kallo kamar takai Musu Duka,Hannu Nene Ta Nuna ma Dina Cikin Wani Tsantsan Bacin rai Tace"Kin san meyasa nayi miki mgana..? Saboda kaddara Ta Hadamu Zama Dake ne kuma kafin Uwarki da Matar mahaifinki su bar nan sun Damkamana Amanarki kuma mun Karba bai Dace mu saka Miki Ido ba Da kuma Cikin Yarona Zaina Dake ajikinki Domin Duk Abunda ya Shafi Zain ba abun Wulakantawan mu bane Ba Domin haka ba ke Har Kin isa..? Kee din Banza Da Wofi Wlh ba Domin wannan Bakar Kaddaran ba, irin ku marasa Tarbiya basu Isa su Tunkari wannan Gidan da ahalinmu gabadaya ba,Tunda kika Shigo Rayuwarmu muke Cikin wani Hali Kin sakamu Cikin Wani Hali Yanzu kuma Gashi Halima ta bar Gida Umma Zareena na kwance Zain na asibiti yana Sambatu Mu kuma muna Cikin Tashin Hankali bamu da natsuwa ammh ke ko ajikin ki ko..? Wlh kada na kara ganin kin Saka Kafa kin bar Gidan nan Indai Batare da Izininmu ba Wuce kibama Mutane Waje mara Tunani kawai..' Tafada Cikin Sauke Hannuta Dina da Maganganun Nene suka Shigeta musamman ma Datace Zain na asibiti Cikin Wani Hali sai Ta kara Raunana Dama gidan Zakiya ta kwana Ta na Cikin Damuwa Tun ajiyan taso Ma ta Dawo ammh Ta Hanata ganin Tana Cikin Damuwa Ga Ciwon kai ga Zazzabi sai da Tasha mgani,Shine Da safe bayan Ta samu Sauki Dinar ta Damu sai sun Taho Taga Halin da Zain yake ciki Suna Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Da Hajiya Mama suka Fara Cin karo Bayan sun gaisa ita take gaya musu Zain yana asibiti chan ya kwana su Umma kuma suna Gida itama sai ahankali Shine suka Nufo Gidan Da gudu Dina Ta Shige Dakin da aka Sauketa,Zakiya Ta Daga kafa Zata Bita Nene ta Dakatar da Ita Tana Nuna mata Hanyar Barin Falon Lokaci Daya Tana Fadin"Juya ki koma Inda kika Fito..Ba sai kin Shiga ba..Kuma kada na kara ganin kafarki acikin Gidan nan Don Allah ki bari Ranar da Aka Daura auran Aka kai Dinar Chan Gidan Zain din sai ki Share Kafa ki Dinga Zuwa chan ammh nan ki barmu mu Huta hakanan Don Allah.."Ta karishe Fada Idanuwanta suna kara Kadawa Dole Zakiya Ta Juya ta koma Baya Jikinta Duk yayi Sanyi,Dama Abunda Take gudu kenan Shiyasa Take kwabar Dina awannan Gabar Suna ganin Itace Silan komai Shiyasa Ta gayamata kada Tayi murnan Bacewar Zaina Domin itama Hakan sai ya Ta bata ta Haka Ta Fice Daga Falon Nene ta Rakata da Tsaki kafin ta koma ta Zauna Kawai ta saka kuka,Zainab ma sai kuka Take Zafeera kuwa sai Sharan kwallah Zareena kuwa Tana bama mai Sunan Umma Nono Jalal Na Gefenta Shima ya Rakube haka su Saudart Dina kuma Tana Ciki Tana ta kuka,Hankalinta Duk ya Tashi Na Jin Zain dinta na cikin wani Hali acikin Ranta kuma Tana ta yi ma Zaina Allah ya isa bata Tafi ba sai da Tatafi da kurwan Zain dinta. Kiran Daddy yasa Dole ta Tsagaita Da kukan ta Dauka suka gaisa yana Tambayanta Abunda Take bukata tace bakomai yace zai zo Sati mai Zuwa kuma sun yi mgana da Hajiya Maimu tace yakamata Taga Likita,Ko Daga nan Gidan akwai Likitan Dake Dubata ne tace A'a Sai yace mata zai zo Sati mai Zuwa ya ganta,Tace Shikenan sai yazo Daga haka sukayi sallama Ta Zurfafa wani Tunani Tana Tunanin Cikinta ya Shiga Wata na Hudu har ma ya wuce Ta kosa Ta Haifeshi Auranta Da zain ya Tabbbata Shine kadai Burinta. Su Nene kuwa sallar mangariba ya Tadasu kowa yaje gabatar da Sallah Umma kuma Har Lokacin Tana Barci sai bayan sun idar da sallan ne Zainab Ta Shiga Kicthen Ta Dafa musu Taliya sai Bayan Isha"i Abba ya Shigo Gidan Shima in ka gansa kasan Yana Cikin wani Hali,Duk ya Kode Saboda Tashin Hankali Suna ganinsa suka mimmike suna mai Sannu da zuwa suna kuma Tambayansa Jikin Zain din yace ya barosa har yanzu bai Farka ba Haddir ke wajensa su Baban kaduna ma sun Dawo Suna Gidan Alhaji Tsoho. Sai da ya Duba Umma kana ya Shige Shashensa yayi wanka yayi Sallah koda Nene ta Gabatar da abinci kasa ci yayi Ruwan zafi kadai yasha Nene ta kalleshi Cikin wani yanayi Tana Fadin"Shuru ba wani labarin Sa"adiyan..? Abba ya Sauke Numfashi Yana Fadin"Babu Neene..Ba wani Labari..Wlh nayi Nadaman Fushi da na rika nunawa kan Zain Dana saka baki Fatima ta bashi matarsa da Duk Haka bata Faru ba gashi yanzu mun bata Goma ko Daya bata gyaru ba Ga Fatima kwance ga Zainullahi can Yana Sambatu kamar ya Zare ya zanyi Nene..? Wannan Shekaran sai Godiyar Allah kawai.! Ya Karishe Fada kamar yayi kuka Cikin Wani Tsausayawa Nene ta karisa kusa Dashi Ta Dafashi Tana Fadin"Kayi hakuri...Kaddara ce Bamu da yadda muka iya Allah ya bamu ikon Cinta Insha Allahu Zain zai samu lafiya UmmanZareena ma haka Halima kuma Insha Allahu Zata Fada Hannu nagari kuma Zata Dawo Cikin Koshin Lafiya da ita da Abunda ke Cikinta kawai mu cigaba da gayama Allah.."Cikin gamsuwa da mganarta yace"Ameen Ameen Allah yasa..! Daga Haka ya koma ya kwanta ita kuma ta Rufa mai Blanket kana ta Dauki Tiran Abincin Data kawo mai Ta Fita Dashi Gabadaya itama Tafe kawai take ammh Rauninta abayanna Ranar Ko ita Datake Bi takan Dina Wannan karon ta Fita Batunta Domin Ta Bala"in Bata mata Rai Abunda Tayi Gidan Alhaji Tsoho Ita Ta lura kowa na Gudun Abun kunya banda Dina Ita Sonshi Take yi ma Zata gane bata da wayau ne in Sakaryace ita. **** *Kaduna* Malali Gra..! Daga Bakin Symbol din Shagon Tundaga Bakin Titi Zaka ga An Rubuta HAJIYA HAUWA UWAR MATA BAGS AND SHOES..! Daga kallon Farko in kayi ma Shagon zaka Fahimci ma mallakiyar Wajen Ta Kashe Dukiya Domin Duka Wajen Gilas ne,Sai wanda ya gani Waje je mai ban Sha"awa da Tsari Wanda kuma zai Dauki Hankalin mai Wucewa yaji Ko baya Sha"awar Siyan komai sai ya Shiga yaga yanayin Tsaruwan wajen... Daga Cikin Shagon Kuwa Jakunkuna ne da Taklma Masu kyau da Tsada yan Waje Cikin Kowani Kwaba,Babban Shago ne,Domin yana Fadi kuma yana da Girma kuma Cike da Kaya akwai yaran Shago Guda Biyu Namiji Daya mace Daya masu Taya Uwar mata kula da Shagon Amintattunta Duk da Itama Duka Harkokinta suna Garin Kaduna ne Domin Wajen Shekaru Uku da suka wuce ta baro Zaria Gidanta na nan a Acikin Malali Gra din Sai dai Taje Zaria Ta Dawo Saboda Akwai Harkokinta achan kama Daga Gidan Abincinta Zuwa Matattaran Karuwan data Tara Tana basu matsuggguni Suna karuwanci Suna Bata kudi Duk da Itama Din Tsohuwar karuwa ce mai Zaman kanta sai dai yanzu ajinta ya Girmi haka Ta zama Uwar mata Sai dai Ta samu yarinya Danya Sharaf ta Ji da ita ta kashe mata Kudi yadda Itama Zata jawo mata kudi Ta baza Hajarta Data samu Shiga Shikenan kuma Uwar mata Likafanta ya Daga Da haka Tayi Gida Da Motar hawa ta kuma Mallakin wannan Shagon Gidanta Na Zaria kuma wannan Tsohon mganace Tun Tana gwalewa da kanta Ta mallakeshi ba yanzu Data ke ganin Ta Girma da hakan ba. Dagachan Karshen Shagon Uwar Mata ce Zaune kan Kujera kawarta Hajiya Zabba"u na Gefenta Tana kallon yadda ake ta Jera kaya Dayake jiya Da Daddare sabbin Oders suka Sauka,Shiyasa tazo Taga yanayin yadda Za"a Tsara kayan Ita kuma Uwar mata Hankalinta na Bisa Wayarta sai Sakin Tsaki Take kafin Ta Dago Tana Fadin"Zabba"u Kina ganin Wulakancin da Sholly keman ko..? Tun Shekaran jiya da Suby Ta Kirani Tagayamin gata Ta Dawo da wata Bakuwa nake kiranta taki Daga Kirana Saboda Iskanci..! Tafada Tana kallon Hajiya Zabba"u sai Lokacin na kare ma Uwar mata kallo Wata katuwar mata ce mai Kiba,Komai na Jikinta mai Kiba ne Fara ce irin Farin Alluran kanti Gajren Hanci Gareta da wani katon Baki Sai Fuskarta mai Fadi,Hancinta da Hujin Zinare,Haka ma bakinta ma Dauke da Hakoran makka Ja da Fari Hakama Wuyanta da Hannayenta Duka Zinare Tana sanye da Doguwar rigar Shadda gezner,Taji paint work,sai kyalli Take Hannayenta Duka Tayi karin kumba kuma ta Cikasu da kalan Pick har kafafuwanta Wadanda ke Cikin wani Takalmi mai Tsini akallan Farko in kayi ma Uwar mata sai ka Kara kallonta Gata Babbace Domin zata bama Shekara 55 baya ammu Bata yarda Takai wannan Shekarun ba. Ita kanta Hajja Zabba"u Haka Take Domin wata Narkekiyace anci Bilicin har an gaji cikin Kulawa Tace"Ai Hajja kefa Uwar matace kuma Uwar Sholly kike Kin Fi kowa sanin Halinta.."Uwar mata Tace"Umh...Nasani Zabba"u ammh akallah Ta Daga Kirana Taji kiran me nake mata ko..? Hajiya Zabba"u Tace"Bazata Daga ba..Kila tasan Dalilin Kiran naki ne.."Uwar Mata ta Bude baki zatayi mgana kenan Taji Wayarta Tayi kara Tana Dubawa Taga Sholly ce ta Tura mata Naira Dubu Dari da Hamsin Cikin Washe baki Tace"Yar Halas muna mganarta..Sai ga alert dinta Ta Turo min 150k yanzu nan.." Hajiya Zabba"u Tace"Kai Uwar Mata kin yi Sa"an Haduwa Da yarinyar nan Wajen Shekara Hudu kina ta cin Moriyanta..'Uwar mata na wani irin Mirmishi Take Fadin"Bari kawai Zabba"u naci albarkacin Jikin Sholly kuma Har yanzu ina kan ci Inaga Alhaji Badamasi ya Sauke mata Kudi ne kinsan Tafiyar Datayi Kano Ta Rakasa Kai Wannan Alhaji akwai kudi Hajiya Ita kanta Sholly bata sani ba Kowani Lokaci yana Turamin Kudade fa.."Hajiya Zabba"u Tace"Ta sani Uwar mata..Kawai Samun masu Zuciyar Farida Cikin karuwai sai an Tona ne yarinyar Tana Burgeni Iyayanta Sunyi Sa"an Haihuwa sun Haifa kuma sun Bar miki Uwar mata kina Ta Moran Abunki.."Dariya suka kwashe Dashi Suka Tafa kafin Uwar mata Tace"Bari kawai Shiyasa nakeDaga mata kafa...Sholly Bata karya komai Dacinta Sai ta gaya miki Gaskiya Bata kuma munafunci Da Tsegumi Ita fa Dabam Take Na Hadu da Farida Cikin Halin Bakinciki Abunda ya Faru da ita na Dauketa na Taimaketa na Inganta Rayuwarta Kinsam Allah Zabba"u Bani nayi ma Sholly Tayin wannan Harkan ba Ita da kanta Tacemin Tana son Ta zama karuwa mai zamanta kanta Lokacin Danaji Haka naji Dadi Domim komai zai zo Min Da Sauki Tunda na Fahimci Yarinyar ta Mori Abubuwan da Zata Samo mana Kudade,Lokacin Tana Cikin Raunin Abunda ya baro ta da Gida,Tunda Naga na Fara samun Abun Duniya Ta Dalilinta naji bana Sha"awar Watarana Sholly Ta Tuba tace Zata koma garinsu Shiyasa na kai Sunanta wajen Mallam Gobe da Nisa nace ya kara Nesanta ta da Garinsu yakuma kara Wutar Bacin Rai Da Rauni kan Abunda ya Faru da ita wanda zai sa Taji Gwara Tayi zamanta anan Tana Cigaba da zaman kanta ni kuma ina Morarta.."Baki Hajiya Zabba"u Ta saki kafin tace"Ke Uwar mata..Kinfini Bala"i..." Uwar Mata Tace"Ah ki zauna Zabba"u..Dole yau ma zaki Rakani Zaria zan je naji kan wani Dalili Ta kawo min Wata Bakuwa batare da sanina ba Ko Ta manta abun ya Faru dani ne Abaya..? Nan fa Samira ta kusa akai ni Gidan yari,Ashe Yarinyar Data Daukomana Yar Sandan Ciki ne tazo Leken asirina ne,Karshenta da aka kamani Nan fa kaduna aka kawo ni awulakance State Cid Kamar Wata mara Gata Lokacin ba Domim nasan wasu Yan Siyasa da Ita Sholly Tana Harkan Da masu Garin gabadaya ba ai da yanzu bani a nan Zaune kina Sane dai Yadda akayi Ta Fadi Tashi kafin Case din nan ya Mutu Shiyasa nake Kiyayewa Duk da yanzu nawuce Hakan Domin Dan Zaki ya Riga ya Girma ba kuma yarda Za"ayi Dashi.." Hajiya Zabba"u Tace"Kwarai kuwa..Ai kin koma Ciwon ido yanzu sai Hakuri.."Dariya suka Sheke Dashi Suka Tafa Lokaci Daya suka Cigaba da Hiransu basu bar Shagon ba sai da aka gama Jera kayan Da komai da komai Wajen Azahar Direban Uwar mata ya Daukesu Zuwa Zaria awata katuwar Bakar Jeep Dinta. ***** *Zaria..* Yau kimanin Kwananan Zaina Biyu Cikin Wata Rayuwa Wanda Ko amafarki Bata Taba Fatan Shigowarta ba,Akwana Biyun Datayi Wajen Farida Tayi Nadamar Fitowar Daga Gida yafi Sau Dari Domin Rayuwar Data Shigo ba Rayuwar Da ta saba gani bane Wata Rayuwa ce da kazo nazo,Inda Allah ya Taimaketa Haduwar Ta da Farida Hakika Farida Macece mai Kirki da karamcin Tunda Ta Daukota Bata barta Ta Shiga Wata Damuwa ba komai ita ke mata Wanka kadai Zaina keyi Sai dai taci ta kwanta kawai Farida Bata Barinta Fita Ko kofar Daki. Washegarin Ranar da Tazo Gidan Haka suka wayi Gari da Fada acikin Gidan Tsakanin Deezee Da Suby Fada mummuna Harda Wukake Duk Dukk su yanke Junansu kamar Wasu mahaukata kuma Abun mamaki Babu wanda ya Damu Dasu balle ya Rabasu,kowa Harkan Gabansa kawai yake Zaina Taji Tsoro Ta Rabe Jikin Bango Tana ta kuka Farida na Gefe Tana danna wayarta Bata ma Lura da ita ba sai da Ta gama ne Ta ganta Tana ta kuka Shine ta Fara Lallashinta Cikin kuka Tana Fadin"Anty Farida..Ina jin Tsoro...Tsoro nake ji..! Sholly Tace"Kima Daina Jin Tsoro..Domin indai Wannan Abun ne yanzu kika fara ji kuma kika Fara gani..Bariki ba kamar Rayuwar da kika sani bane Rayuwar kazo nazo ne Sa"adiya ki kwantar da Hankalinki Nayi miki alkawarin Ni Aisha Farida Zan zameki Garkuwa Babu Abunda zai sameki kuma ba Wanda ya isa ya Tabaki acikin Gidan nan Ko ina nan ko ba na nan.."Da wannan kalaman yasa Zaina Taji Tadan samu Natsuwa Ranar da yammah kuma gidan ya Cika da Maza da mata sai Shaye Shaye suke sun saka Waka atsakar Gidan suna ta Kida Har Zaina Tayi barci Basu Daina ba Abun yadaina bata mamaki ta Fara Yadda ma kanta Lalle Rayuwar data Tsinci kanta aciki ba Wacce Ta saba gani bane. Washegari kuma Tun Safe Kuma aka kawo ma Farida Sakon Mota Cike da Kayan kwalama da kayan sawa kayan kwalliya Shopping dai kamar Za"a Bude Shago Tana JintaTana Godiya awaya kamar Harda Kudi aka Turo mata Su kacharalle suka Shigo mata Da kayan Cikin Daki Ammh sai da Ta Tura Zaina Cikin Labulen Wajen Saboda bata son su kara ganinta akwai haka kacha ke ta Dage yana kalle kalle Cikin Bacin Rai Sholly tace"Lafiya kake min kalle kalle Cikin Daki ko Kabani ajiya ne..? Da Sauri yace"Inafa ajiya..Wannan Hajar da kikazo da ita ne bangani ba ko an har anci kasuwarta ne..? Dogon Tsaki Taja kafin Ta Hankadashi Waje Tana Fadin"Kacharalle ka Fita Daga idona...Iskancinka da kwartancinka ya Fita Daga kan Sa"adiya Domin ita din kanwata ce ba kuma irin Wacce kake Tunani bane.."Cikin Mamaki yace"Au daman sunanta Sa"adiya ah kice Sady Bby ce,wai kanwarki Dama ai Bariki Har Uwa da Uba zaka samu Sholly kebagashi kin samu Uwa ba Uwar mata kamar hakane ba Laifi in kema Ta zama kanwarki Ammh ya kamata ki Fito da Hajan nan kawai ki Tallata ta kowa ya Taya mai Rabo ka kwashe.."Banza Tayi Dashi bata kara mgana ba Ita kuwa Zaina Tana jinsa Jikinta sai Rawa yake Tana Danne kukanta acikin Ranta Tana Tuna tana da fa aure Yanzu in ta Fada wata Rayuwa awannan Gidan Menene makomarta..!? Ganinta Cikin Wannan Halin yasa Farida Ta zauna Tana ta lallashinta Tana Fadin"Karki Damu da mganarsa haka suke kamar karnuka..Bazan Taba bari Kiyi karuwanci ba Sa"adiya ni zan Dinga Miki komai na Rayuwa Bazan bari Rayuwarki Ta Lalace ba.."Fadawa Jikinta Zaina Tayi Tana kuka Tana Fadin"Anty Farida..Meyasa na baro Su Umma..? Saboda Cikina ne da kuma Tserata da aurena..? Ammh yanzu na Fara Nadaman Abunda na aikata Anty Farida.." Farida ta Dagota Tana Fadin"Sa"adiya me ya baroki Daga Gidan..? Ki gayamin gaskiya Domin Bana son karya kuma bana Shiri da mai yinta.."Zaina Ta Sunkuyar dakai Tana Digan Hawaye ta Fara Bama Farida Labarinta Tunda Farko Har karshe Har Zuwa Haduwarsu Koda Ta gama Sai ta kara Rushewa da kuka Tana Fadin"Anty Farida Wani Nauyi na Damuna acikin Zuciyata...Firstlove ya Sakamin wani irin Rauni acikin Zuciyata,Bazan iya Juran ganinsa ya auri Dina ba Zuciyata Ta Raunana bazan iya Juran ganinsa da ita ba.." Farida Sholly Ta Dagota Tana Share mata Hawaye Cikin Taruwan kwallah acikiin Idanuwanta Tace"Ki Daina kuka Sa"adiya Lalle kin Hadu Da Daya Daga Cikin Cin Amanar D'a Namiji..Kinga Tsantsan Cin Amana kam Ayarintarki naga ma Kokarinki da Dauriyanki akwai Ciwo wanda ka yarda Dashi yaci amanarka kuma akwai Ciwo wanda yafi kowa saninka aduniya yaki yarda Dakai Sa"adiya kin ganni nan Nawa Labarin ba irin naki bame ni Sharrin Kishiya ya kawo ni wannan Rayuwar Da kike ganina ammh har yau bana Dora Laifin a kanta nafi Dorashi kam Mami da Abba na da kuma Shi kanshi Ya Musbahun Dayafi Sanina Fiye da kowa ammh ya Rufe ido ya Kirani karuwa Gaban iyayena da ya"yana Sa"adiya Naso na kashe kaina Allah ne yayi kwanana na gaba Har kika Hadu dani.."Tafada Tana Fashewa da wani marayan kuka Wanda Tunda Zaina Ta hadu da ita Bata Taba ganin Tayi kuka ba Zaina na Kokarin mgana Farida Ta Mike Tana Fadin"A"a Sa"adiya karki bani Hakuri..Ki barni nayi wannan kukan Shine samun Saukina da Salamana Ina da Ciwon Zuciya da Hawan Jini in ba kukan nayi ba bazan samu salama ba..Kada ki Damu Watarana In na samu Natsuwa zan baki Labarina kuma nayi miki alkawarin kula Dake da Abunda ke Cikin ki bazan matsa miki ki koma Gida a yanzu ba Saboda Zuciyarki ta Raunana Zan bari sai Lokacin Da kika ga Zaki iya Rike komai kuma ki Daure zan maidake Bauchi Da Hannuna Insha Allahu.."Daga haka ta Tura Kofar Tiolet Ta Shiga Ta kara saka kuka Sai Duk Jikin Zaina yayi Sanyi Yanzu mai kananan Shekaru irin Anty Farida ce keda Hawan Jini da Ciwon Zuciya..? Ya illahi Allah Sarki Hartaji ta Tsausayamata ta kuma Fara Tunanin Zamowarta karuwa ba Burinta bane Dole ya zame mata Ko daga yadda Faridan ke Tafiyar da Rayuwarta Abunda Yafi bata mamaki Sallah bata Wuce ta karatun Qur"ani Kuwa Dataji Tana yi sai da mamakinta ya Bayyyana acikin Ranta Tana Tambayan kanta Dama karuwai na Karatun Qur"ani Ta manta Zamann bariki kazo nazo ne kuma Kowasu Mutane akwai nagari akwai na banza aciki wasu su Dama chan Watsatsu ne wasu kaddaran Rayuwa ke sa su Tsinci kansu Cikin Wani Hali. Zaina na nan Zaune Sai Taji Ihu Mai Karfi Da kuma karan ana Dukan Mutum,Tun Bata jin Ihun Sosai har ta Fara Ji Domin abun atsakar gidan yake Faruwa Jikin Zaina na Rawa Tatashi Tana gyara zaman Doguwaar Rigar Farida Dake Jikinta Dayake Faridan Bata da Jiki sai kayanta suke zama ajikin Zaina din duk da sun mata Yawa ammh Tana maneji hakan Tunda Faridan tace in Ta samu Lokaci zasu Fita ta Siya mata Wasu kayan Ta Jikin Window din Dakin Ta Daga Labule Tana leken meke Faruwa Zuly Ce Ta gani Kwance Daga ita sai Sikat karami ajikinta Ba Riga sai Bra gabadaya Jikinta Awaje yake Gashinta kanta mai kama da Hammatan Dan iska Duk ya Bazu,sai wani Katon Namiji bakikirin Dagashi sai gajeren Wando Yana Tsaye kanta da Katon Belt yana ta Tsula mata Shi Tana Ihu Tana bangarewa Tana Fadin"Wayyo Allah na Shiga Uku.Zai kasheni Don Allah..Shafson kamin rai na Tuba nabi Allah bazan kara maka Sata ba.! Take Fada Tana kuka Tana Sosa Inda yake Dukanta Abunda ya kara Bama zaina Tsoro gasu Deezee dasu Suby nan Tsaye suna kallo suna Dariya,Harda Wasu ma bakin Fuska da bata sani ba Domin Ta Lura ba Dukkansu ke kwanan Gidan ba Sai suyi Kwanaki basu Gida Wasu ma Haryanzu bata sansu ba Basu Gida Gabadaya duk sun Fito Suna Kofar Dakunansu suna kallo Suna Dariya Wata Ma Daga Cikisu Taba Take Sha Tana Fesar da Hayaki Lokaci Daya Tana Fadin"Shegiya Zuly....Bariki ba Riba Gobe ki kara Hannun Bera.." Ta Kwashe Da Dariya Tana Fesar da Hayaki Zaina Ta Fara kuka Da Tsausayin Zuly ganin yadda Yake Tafkanta kamar Allah ya aikosa Yana Dukanta Yana Fadin"Ni zaki ma Sata Don Ubanki..? Watsatsiyar karuwa kawai Yau sai naci Ubanki naga mai kwatanki Shegiya mayya kawai.."Haka yake Fada yana Dukanta sai ga Kacharalle ya Shigo Har Zaina najin Dadi zai Cece Zuly sai dai Ina Shima Suby ya kallah yana Fadin"Ina Ta gidan Abincin Uwar mata nake jin Ihu Kamar na Kuka ashe kuma su Zuly ne ake amsan na Safe..? Suby Tace"Eh kasanta Hannun Bera gareta Sata ta karamai itama kamar Jaka Bata iya Rabuwa Dashi,Kusan koda yaushe sai ya Daketa kamar Wata Jakata"Kacharalle yace"Allahu Akbar...Su Zuly dai ba'a Shigo Bariki a sa"a ba.."Yafada Lokaci Daya suna kwashewa da Dariya Harda Tafawa Zaina Taji Wani irin acikin Zuciyarta Ta manta da Gargadin Farida na karta Fita Bata san sadda Ta Fita da gudu ba Ta isa ga Gabansa ya Daga Belt zai Tafka ma Zuly Zaina ta saka Hannu Ta Rike Belt dib Cikin Dakewa Tana kallonsa. Ba Shafson ba hatta su Deezee da su kacharalle haka suka Saki baki Suna kallon Zaina Wacce ta Yarfe Belt din Tana Fadin"haba bawan Allah baka da Imani ne me tayi maka Zaka Dinga yi mata wannan Dukan..? Kome Tayi maka ya kamata ka Daki mace haka..?Kai baka Daraja mace ne ko kuwa Kai Mata abun Wulakantawa tawan kane.? Tafada Tana Sakarmasa manyan Idanuwanta,Gabadaya Cak ya Tsaya yana kallonta Da Jajayen Idanuwansa Yana kuma Kare mata kallo Lokaci Daya yana Wani Lasan baki Bata bi Ta kansa ba,ta Isa ga Zuly Dake kwance Tana Kuka Ta Rikota Tana Fadin"Sannu...Sannu Tashi Kinji.."Zuly Ta Dago Tana kallonta Hawaye suka Wanke mata Fuska bata da Zabi Ta Riko Hannun Zaina Data ke Mika mata Ta Tashi Tana Dingishi Jikinta Duk ya Kumbura Saboda Duka Kallonta Zaina Tayi Tana Fadin"Ina ne Dakin ki..? Zuly Na Kuka ta nuna mata Room4 alamun nan ne Dakinta,Zaina Ta Rikota Tana Fadin"Muje na Rakaki Sannu..."Take Fada Tana Riketa Suna Shirin Fara Tafiya yasha Gabansu Cikin Bacin rai Zaina Tace"Bamu hanya mallam..' cikin Bariki Da zallar Iskanci yake kallon Wuyan Zaina da Rigar Tayi mata Rakwa rakwa Kirjinta ya bayyana,Yake Fadin"Ya zan baku hanya bayan Kudina ta satamin Kuma ta kashesu..Bazan baku hanya ba sai dai in zaki Famsheta ki Biya mata sai na Kyaleku ku wuce..! Zaina Tace"Nawa ne kudinka..? Cikin Shafa Gemunsa yana mata Wani irin kallo yace"Kudi ne masu yawa Kuma basu Zaki biyani ba mai kyau yar Shila.."Yafada yana wani Dariya Su Deezee suka yi Tsuru suna Tunanin Ina Sholly ko Ta fita ne..? Basu gama Rufe baki ba Zaina tace"Dame za"a Biyaka..? Kai Tsaye yana kallonta ya Fara Matsowa kusa da ita Cikin Bariki yace"Da wannan Lafiyayyan Jikin naki Zaki Biyani.."Yafada Lokaci Daya yana Kokarin kai Hannu zai Taba Kirjin Zaina kawai yaji an Damke Hannunsa yana Juyowa Kafim ma yagama Gane Waye yaji an Tsinkesa da Wani Mahaukacin mari sai da Belt din Hannunsa ya Fadi Cikin Huci Da Bacin Rai ya Dago Yana so yaga Wata mara kunya ce ta mareshi sai yaci karo da Sholy Tsaye Idanuwanta sun yi Jajir tana Jifansa da wani kallo Zaina kuwa Jikinta ne ya kama Rawa bata san sadda Ta kankame Zuly ba Itama ta Riketa Tana kuka Gabansu Farida Ta Tare Tana Nuna Shafson da Yatsa Tana Fadin"Kul din ka..Karka kara Kuskuran cewa zaka kai Hanunka jikinta sai na Sare maka Yatsu Wannan ba irin su Zuly bane da kananun Yan iskan da ka saba harka dasu bane Wannan Tafi karfinka Kada na kara ganin ko Kallonta kayi in ba Haka ba sai na Nuna maka Wacece Sholly.." Tana Gama Fadin Haka ta Juyo Wajen Zaina Rai bace ta Finciki Hannunta Tana Fadin"Sakarta..Waya gayamiki kana mgana acikin Rayuwar da mutum ya zabar ma kansa..? Ki barta ya kashe ta mana itace karamar yar iska take Harka da kazamai irinsu Kada ki kara Fitowa koda Kisan kai za"ayi agidan nan Shiga Ciki.."Tafada Lokaci Daya Tana Tura Zaina Dakinta kafin ta Waigo Tana nuna su Suby Da yatsa Daya Bayan Dayan kafin Tace"kun gani ko..?Wlh Tallahi..Ko bayan Idona kuka bari wani Dan Iska yayi ma Sa"adiya Kallon banza ko kukayi mata sai nayi Muku Rashin Mutumci Daya bayan Daya Kun sani na sanku Bani da Wasa.." Daga Haka ta Juya Fuu Ta Shige Dakinta Ta bar su Suby Tsaye,Shafson kuma yayi suman Tsaye Zuly kuwa Gefe ta koma Tana Makarkyarta Kacharalle ne yace"Tabdijam...Wani kaya sai amale su Shafson sai amaida yawu wannan Hajar dai bata Lasuwa.." *Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Jiya Daga fara Buk har an Fita dashi Waje bazan ce komai ba ammh ku sani Rashin Daraja ne ki jira abun Sata in kin isa mai aji komai kina mallakansa ne ya zama naki..* *Shakira..* 7/9/21, 3:09 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣3️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* ""Shafson Haka ya Tsaya baki Sake Hannu saman Fuska yana wani Huci Mai Kacharalle zai yi Shida Suby in ba Dariya ba Harda Da Tafawa Adamalle Data Fito Daga Dakinta Da wani BoombShort kamar Tana Juyi Tayi Guda kafin ta Tsaya gaban Shafson Tana Fadin"In Takamarka Daman Iskanci Toh ka Hadu da wacce ta Fika...Sholly Ta isheka komai Kaima ka sani sai dai Hakuri.."Kalaman Adamalle sun kara Tunzurasa Cikin Fushi ya Dauki Belt Dinsa Ya Tunkari Zuly Tana Kokarin matsawa Baya ya saka kafa ya Taliyeta Ta Fadi Ya Fara Dukanta kamar Allah ya aikosa ihu Take da karfi ana jinta Daga Cikin Gidan Har waje Zaina Dake Cikin Dakin Farida sai kuka Take Cikin kukan Take Fadin"Kina fa ji Anty Farida Har yanzu Dukanta yake yi fa..? Dariyan Takaichi Sholly Tayi kafin Tace"Gidan Karuwan kenan Sa"adiya...Kyalesu kwartonta ne abokin Shanshancinta ya Rainata ne kullum sai ya Daketa kamar Jaka ammh Bata iya Rabuwa Dashi Koda yaushe suna Tare..Mtseww ni bana son Iskanci In mutim zai sha giya yasha Ta Dubu kawai Tunda dai Giya ai duk giya ce.."! Zaina Ta kalleta Tana Sharan kwallah Tace"Ammh Anty Farida kiji Tana ta Fa ihu.."Farida Tace"sai me..? Ki bar Kukan nan fa Domin yanzu kika Fara gani yayi ta Dukanta bamai Hanashi Sai ma Kara Zugashi da zasuyi Barikin kenan.."Bata ma gama Rufe baki Ba Taji Sowansu kacharalle da su Suby Ko ajikinsu Ita Abun ma mamaki yake bata Indai wannan ce ake Kira Bariki Abun kam ba Tsari kam Wato Gidan kazo nazo ne kuma Kowa Wayansa Shi zai Taimakesa Jeep din Uwar mata na Parking kofar Gidan Taji Ihu Da Hayaniya Daga Gidan Ta Dago Tana kallon Hajiya zabba"u Lokaci Daya Tana Fadin"Ihu fa kamar nake ji Daga Cikin Gidan nan..? Hajiya Zabba"u tace"Bama kamar ba..ihu ne Nima naji.."Da Sauri Uwar mata Ta Bude kofar Motar ta Fito Tana Bin Wajen da kallo Hajiya Zabba"u ma ta Sauko Suka Fara Tafiya,Yan barikin Dake kofar Gidan suka Fara ganinta Yadda suke Girmamata sai Abun ya baka mamaki,ma"aikatan Gidan Abincinta da sukaji labarin Zuwanta suka Fara Fitowa suna mata sannu da Zuwa Cikin Bacin rai Ta Daga musu Hannu Tana Fadin"ku koma Bakin aikin ku zan dawo gareku.." Daga Haka ta sakai Cikin Gidan da Sasssfar kamar zata Kifa Hajiya Zabba"u ta mara mata Baya Suna Shiga suka iske su Suby sunyi Dafifi suna Shewa Shafson na ta Dukan Zuly kamar Allah ya aikosa Ran Uwar Mata ya baci Ta kalli Hajiya Zabba"u itama Ta kalleta Batayi Wata Wata ba ta saka Kafa Tayi Fatali da Botokin karfen da Adamalle ta Fito Dashi Zata Debo Ruwa Tayi wanka ji kake kwaram kwaram Chamm! Saboda yadda Ta Dagi Bokotin sai da ya isa Wajen Shafson ya Dakesa a kafarsa Gabadayan Wajen yayi Tsit,Suka kuma waigo Lokaci Daya suna kallon Wanda yayi wannan aikin Gabadayansu Rusunawa sukayi Ganin Uwar mata da kanta Cikin Ladabi Suka Fara gaisheta Da yi mata sannu da Zuwa Cikin Fadanci da Kirari Kacharalle yace"Manyan Manya mganin kananan Mata kaga Uwar mata da kanta ba Sako ba Hajajju makatan Hajiyar makka da madina Gaki ga Kawarki kuma Sahibarki Hajiyan Allah itama Sannunku da Zuwa Allah yaja da zamanink..! Bai Karisa ba Uwar mata Ta Dagamai Hannu Tana kallon Shafson Lokaci Daya Tana Fadin"Wani irin maguzanci ne ko nace Tashanshi ne ku keman agida..? Zaman Bariki na yarje muku kuyi min acikin Gidan nan ban baku masauki domin kuzo kuna min Hayaniya ba so Kuke yan anguwa sumin Bore..!? Tafada Cikim Bacin Rai Cikin Sauri Suby Tace"Bafa wani Abu bane Uwar mata kema kin sani Zuly ce tayi Halin Shi kuma Shafson kinsan sa Dukan Zuly Kadai ke sakasa Kiba.."Tafada Tana wani karkada Jiki Da kallo Uwar mata Tabi Zuly Dake kwance Tana kuka ta Daku kafin Ta saki Tsaki Tana Fadin"Ke ba Iskanci kika Fito yi ba Na lura Sata kika Fito yi ko..? Baki da aiki sai sata Zan Koreki fa Domin naga baki da wani amfani.." Cikin Kuka Zuly Tace"Don Allah kimin rai uwar mata in kika Koreni ina Zani..? Uwar mata ta bankamata Harara Tana Fadin"Inda kika Fito mana..Gwara Uban kowa Dake..Domin banda Kwana da yin kashi baki da wani amfani.."Adamalle Ta Tabe baki Tana Fadin"Tama Ci da kanta Toh Uwar mata.."Itama din Hararan Uwar mata ta Sakar mata kafin tace"rufemin baki kema ai Duk kanwan jace..Duk cikin Gidanan Daga Sholly sai Rufy su kadai nake Moransu Sauran sai Dai su Cikamin Gida da Kwartanyensu kananan yan Iska Wadanda Ko Wando Uwayensu basu gama saka musu Toh Bata yuyuwa Duk zaku bar min Gidana nayi Sabbin Zubi Tunda Duk Naga baku da wani amfani.."Gum kowacce Tayi da bakinta ba mgana Uwar mata Shafson Ta Sakarma Ido wanda yake kallonta yana Tsiyayan Zufa Cikin Tsirtar da yawu Tace"Kai kuma Daga ina..? Na bani ni Hauwa na bi Duniya na lalace Yanzu ke banda Saunanci me zaki yi da wannan kazamin Zuly..? Tir Dake Wlh Shegiya mai Sufar yan Ruwa.." Tafada Lokaci Daya Tana Wani Yamutsa Fuska ganin haka yasa Shafson ya Fara Taku Zuwa Wajen Uwar mata yana Fadin da katuwar muryansa"Hajajju Sata f..."Kai kai Tsaya inda kake karma ka kariso.." Ta katseshi Tana Dole Hanci Hajiya Zabba"u ma Baya Taja Tana Fadin"Hajiya Hauwa haka Gidan naki ya koma..? A"a kiyi sallama Wasu kam sun Jahilci kalmar Bariki gaskiya.."Tafada Tana wani Matse baki kamar Wacce Taga kashi Uwar mata Tace"Umh...Bari kawai Zabba"u Duka Sakarkaru na Tara su bama su samo wani Abun Kirki Ballatana su sayi kayan gyaran nan su gyara kansu kullin suna nan kamar wasu Jakuna ko ni ai bana zauna haka ba Ballatana su da Kuruciyarsu ammh sun koma kamar wasu Tsoffi Daga Wacce Fuska ta Kone sai Wace Duwawu ya Shafe sai Wacce Nonuwa suka kwanta kamar Silafas.."Jin haka yasa Kacharalle ya kalli Nonuwan Suby da suka kwanta kamar Silafas din ya Sheke Da Dariya Yana Fadin"Kwarai Hajjaju makantu Tun ana Tusa su Cikin Rigan Mama ayi Barazana Har suka Daina zama.."Yafada yana wani Dukewa Hararansa Suby Tayi Cikin Takaichi. Uwar mata Da Takaichi ya Cikata Tacigaba da Fadin"ni kuma Wlh na gama kashe Sisi kan kowaccensu Domin abaya nayi Wahala Dasu yanzu da zasu Famshemin Wahalata ina sai Kayan Haushi kawai Mtaww..Kai Shamo kake kowa..! Zo kaficemin Daga Gida kudinka kuma da Ta sata ka Dawo Da Daddare ka Famshe a Jikin Shegiya Tunda ita Bata da wata Zuciyar Cigaba sai ta Sata.."Ba Musu ya Kada kai yana kallon Zuly Lokaci Daya yana Nuna mata Hannu kan sai sun Hadu kawai kana yaja Babbam Jikinsa ya Fice Uwar mata Ta Bisa da Harara da Zubar da Miyau,yana Fita Ta kalli su Suby Daya bayan Daya Kafin Tace "Ina Zeezee Da Jido Suke..? nassn dai Zee Ta tafi Lagos ta raka wannan Alhajin nata Ita kuma Jido ina Taje..? Cikin Tura ladabi Suby Tace"Bata gayama kowa ba Uwar mata..Ranar da Sholly Tayi Tafiya Ranar itama Ta bar Gidanan.."Kada kai kawai Uwar mata Tayi kafin Tace"Zan Kirata awaya..Nifa bana son Jaye Jayen Masifa Allah sa wani mai maikon ya Dauketa Hotel Service ko Ta samo mana wani Abu na Tsani harka da yan Tayi nan da kuke yi Suby.. Suby Zatayi mgana Uwar Mata Ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Kowacce Ta kama gabanta Baku da amfani..Ita wanchan Banda Shaye Shaye ba bu abunda Ta iya ko..? Da Sauri Kacharalle ya kalli Rufy Dake Busa Sigari Tana Layi kafin yace"Hm bari Hajajju ai Rufy Ta Fara Haukacewa Da wannan Shaye Shayen.." Cikin Muryan Maye Ta Mike Tana layi Take Fadin'Kacharaleee...Uwarka ce Ta Haukace ammh bani ba Don mai Cin Uwarka.."Ta antayamai Zagi Uwar mata Ta saki Baki Ita da Hajiya Zabba"u Kacharalle yace"Uwarki dai Data ce Jeki kya gani badai Tawa Uwar Da Har ta Mutu Tana sakamin albarka ba irinki Da Uwa da Uba suka Sallama ba suka ce Jeki kya gani ba.." Rufy Tataso mai Uwar mata Ta Daga Mata Hannu Tana Fadin"Dillah ku Saurara min..Kai Kacha kama gabanka Don Allah baka da aiki sai karewa Gindin mata ina aikin Gogen Gogen Da na baka agidan Abincina...?ka wuce ka Tafi Chan yanzu zan Shigo..!? Baki ya Washe yana Fadin"Angama Hajjaju...Toh in ban Rabi Mata Ba Maza kikeson na Raba..? Mata Sune Mu mune su Uwar mata.."Tana Hararansa Tace"Fita Waje ka Jirani Nace.."Da Sauri yace"Angama Uwar mata mganin kukana.."Da Sauri ya Fice yana waka yana Fadin"Mata akama Sa"ana Mata..Macen da bata Sana"a Sauna ce Lale Lale maraba Da Mowar mata..! Yana Fita Uwar mata Ta Daga Baki Tana Fadin"Sholly Fito..Nasan kina jina Hajiyar mata Fitowa ne bazaki yi ba..Maza ki Fito keda Bakuwar Da Kika Dauko batare da Sanina ba.."Tafada Cikin Kakkausan Murya Zaina Dake Tsuma Daman Tun Zuwan Uwar mata Tayi Saurin Mikewa,Tana Wani Kifkifata Ido Tana kallon Sholly Dake shan Complex abunta Hankalinta Kwance Cikin Rudewa Tace"Anty Farida...Wa...' "karki Damu saka Mayafinki muje....."Farida Ta katseta Tana Mikewa Lokaci Daya Kofin Hannunta Ta ijiye nan saman Center Table din,Bata Saka mayafi kan Kayan Jikinta ba Ta kallo Zaina Data yane kanta da Mayafinta Datazo Dashi Idanuwanta Duk sun kumbura Saboda Kuka,Farida ta kalleta tace"Karki Damu Sa"adiya..Uwar mata bata da tacewa akan zamanki awajena..Ki kwantar da Hankalinki.."Sai ga Hawaye Sharr sun Zubomata Tana Fadin"Ina Fargaba..In na var Wajen ki ina zani..? Farida Ta Riko Hannunta Tana Fadin"Bazama ki bari Ba..Muna Tare Har sai kin ga Yuyuwar Komawar Ki Gida na maidaki da Hannuna Insha Allahu..Taho muje.."Tafada Tana Janta suka Fito Daga Dakin Tun da suka Fito Uwar mata ke kallon Zaina Haka Hajja Zabba"u Su Suby ma Daga Dakunansu sai Leke suke suna son kara ganin Zaina Sholly Ta Tsaya gaban Uwar mata Tana Fadin"Dama ai nasan Sai Magulmata sun Kiraki sun gayamiki ina ganin Kiranki na kyaleki Saboda Ni bana son Harkan Munafukai in zanyi Abu Kai Tsaye nake bana Kumbiya kumbiya kema kin sani.." Uwar Mata Ta Murmusa Tana kallon Sholly Kafin Tace"Nasani Shiyasa ban yi Fushi Dake ba Shalelena...Abunda ma yasa nayi Mgana Saboda kinsan dai Abunda ya Faru na Hana karban baki Batare da izinina ba ko..? Wacece ita wannan Din Da kika kawo Duk da naganta Yar Shila ce Sosai in Ta Kide Zata Zama kamarki Watarana ko zabba"u..?.."Tafada cikin jin Dadi. Hajiya Zabba"u Tace"Sosai ma..Hajar zatayi Daraja Uwar mata akashe mata Dala zaki Fanshe.."Dariya Uwar mata Ta kwashe Dashi Har suna Tafawa Cikin Wani Sakaran kallo Farida ke kallonsu Kara kallon Zainar Uwar mata Take Daga sama Har kasa Tana Ayyana Abubuwa Dadama acikin Ranta,Taji Zaina tace"ina wuni.."Tafada Tana Boyewa bayan Farida kamar ace kyat ta Gudu,Uwar mata ta Washe baki Tana Fadin"Lafiya lau yanmata ya kk..? Da Sauri Sholly Tace"Uwar mata wannan fa ba irin Wacce kike Tunani bace..Sa"adiya Sunanta kuma kanwatace ba Haja bace.."Wani Sakaran kallo Uwar mata Ta Bita Dashi kafin tace"Kanwarki..? Sholly yaushe kika Fara karya..? Sholly Tace"Ban fara ba..Gaskiya na gaya miki Kanwata ce ba Haja bace..' Uwar mata Ta kallesu Dukkansu kafin Tatabe baki kawai Ta kada kai Ta Juya Tana Fadin"Wannan mganar Bata nan bane..Ki Sameni Gidan abincina Zabba"u muje Zaman gidanan ya Isheni Shegu kazamai na Tara Sun kazancemin Gida ko Shara basu yi.." Hajiya Zabba"u tabi bayanta Suka Fice Sholly Ta Rakasu da kallon Kafin Ta Juyo Wajen Zaina Wacce ta Bude baki Zatayi mgana Ta Dakatar da ita da Fadin"Karkice komai...Muje mu sameta Kada ki damu ina tare Dake.."Daga Haka Ta jata suka Fice Suna Fita suka Fada Gidan Abincin Uwar mata Wanda zaina Tana ta mamakin Girman wajen Da kuma Turuwan Maza awajen sai Taga mata masu Kula da Wajen suma Din Duk kama suke da karuwan Kowacce Shigarta ba kyan gani Sanye da karamin Mini Sakat baki da Jan riga kamar Shine Uniform dinsu Tunda suka Shiga Wajen Mazan wajen suka Yi musu caa da Ido Sholly na Rike da Hannun Zaina ta Hade rai Shiyasa ba"a samu Fuska ba Cikin Office dinta suka Sameta Zaune ita da Uwar mata an kawo musu lemu da Snacks. Suna Shiga Uwar mata Ta Kalli Sholly Cikin Kakkausan Murya Tana Fadin"Ki gayamin gaskiya ita din Wacece..? Me kuma manufar kawota Gidana..?,sholly Ta kauda kai Tana Fadin"Sunanta Halimatus Sa"adiya kamar yadda na Fada miki Yar garin Bauchi kuma kanwa take awajena.." Uwar Mata Tace"Karya kike Sholly wannan ba kanwarki Bace ke Bafullatan Gomben ce..Ita kuma yar Bauchi ne Ta ina kika Hada Dangi da ita..? Malama ki gayamin Zaman me Zatayi agidana matukar ba Haja bace..!? Tafada Tana kara kallon Zaina wacce kanta ke kasa Ammh in ka Lura Jikinta ne ke Rawa kamar Mazari Ganin Haka yasa Farida Ta kalleta Tana Fadin"Sa"adiya koma Daki Ki jirani kinji ko..? Kada ki Tsaya ko"ina..' Zaina Ta gyada kai kafin ta Fice Cikin Fargaban Makomarta In Uwar Mata Ta Koreta ina Zata..? Sai dai ta koma Gida Domin Bata Fatan Daganan Taci Gaba Domin Bata san kuma Wajen wa zata Fada ba tana Fita Farida Ta Waigo Tana kallon Uwar mata Tana Fadin"Na gaya miki Ba Haja bace..Zata zauna awajena nadan Lokaci in Lokacin Tafiyarta Yayi zan maida ita Gidan Iyayenta Da kaina.." Uwar mata Tace"Akarkashinki Zata zauna kenan..? Bazai sabu ba sai dai ki bani ita na Tafi da ita Kaduna Na Gyarata achan Donin Har na Hango yadda Zata koma da irin Riban da zan samu Yarinya Itama kamar ki Take gata yarinya Karama ga Dirin Mata sai dai Rama ce ammh Zatayi ta cin Abincin Gina Jiki Tana Cikowa.."Farida Ta saki Baki Tana kallon Uwar Mata kafin Tace'Wlh Bazan iya baki ita ba Uwar mata kiyi Hakuri kawai..' Uwar Mata Tace"Lalle Sholly ina mgana kina cewa A"a..? Farida Batayi mgana ba Ta kauda kanta kawai Hajiya Zabba"u ce tace"To Ai naga itama Sholly Karkarshin Ikon ki Take Balle Wata Da ta kawo..? Uwar Mata Tace"Shi nagani..bar ganin Ina Sangartaki kina Abunda kikaga Dama Wannan Dalilin bazai saka na Dauki Raini ba Zaki bani yarinyar nan Sholly nagama Mganata.."Sholly Tace"Uwar mata Kiyi Hakuri..Ban ta Miki gadda ma ba ammh wannan karon Zan yi miki bazan iya baki Sa"adiya ba Haba Don Allah me kike nema Wanda bana baki shi..? In kudi ne Damuwarki Zan Dinga Ninka Miki Abunda nake baki Harda na Sa"adiya ammh Ki cire Idanuwamki akanta Don Allah..' Tafada Tana Hade Hannayenta alaman Roko Uwar mata Ta kalli Hajja Zabba"u itama Ta kalleta sai ta gyada mata kai kana Ta maida Kallonta kan Sholly na dan Lokaci kafin Tace"Kin Tabbata zaki Dinga Biya mata Haraji..??mganar Daukan Dawainiyar kanta wannan ya Rage naki Tunda ke kika ji kuma kikagani kuma In Wata Matsala Tataso Allah ba Ruwana.."Sholly Tace"Na yarda..Matsala kuma da yardan Allah bazamu ganta ba.." Jinjina kai Uwar Mata Tayi kafin Tace"Shikenan kya iya Tafiya.."Farida Tace"Ba shikenan ba Ina so Ki Fadama Sauran Kananun yan iskan Dake Gidanki Koda bana Gidan nan Kada wata ko wani ya sake yayi ma Sa"adiya kallon Banza..Ki Gargadesu akanta In baHaka ba kuma Zanyi Rashin Mutumci Wlh.."Uwar Mata Tace"Jeki..Zan gaya musu Balle ma sun san Duk Abunda yake naki ne ba irin nasu bane.."Farida Bata kara mgana ba Ta Fice Tana gyara Daurin Dake kanta Bayan ta Fito Maza na Tayi mata mgana suna Kiranta Sholly ammh Tayi musu Burus Domin Farida bata Harkan kananan kwarin dasu Suby suke yi dasu Ita Harkanta da Manya Kuraye takeyi Tana Fita Waje Taga Zaina Kacharalle da Suby sun Tare ta suna Ta Zuba mata Zence har Suby na Dafa kafadarta Ranta ya Baci Tana Zuwa Ta Daka musu Tsawa Dole suka Dare Kacharalle zai yi mgana Farida Bata Bi Ta kansa ba ta Figi Hanun Zaina Tana Fadin"Me na gayamiki ne..?nace ki Jirani adaki ko..? Nan fa ba irin Rayuwar da kika sani ba ne Ina Kiyaye Rayuwarki ne ke baki sani ba ko..? Haka Take ta Fada Har suka Shiga Daki kana ta Saketa Zaina Kamar Tayi kuka Tana Fadin"Ya zanyi Anty Farida..! ? Na Fito zan Tafi suka Tare ne suna ta cemin wai kina so ki Cuceni ne na Hada kai dasu Wlh zan yi kudi sai na fiki kudi.."Farida Ta kwashe Da Dariya Tana Fadib"Bariki Kenan Gidan kazo nazo..kinga yadda sukamin kema Watarana Haka zasu Miki Ba Amana da Yardan a Wadanda Watsewa da Duniya ta Hadaku Sa"adiya ki Rike wannan Koda Watan Wata Rana.." Zaina Tace"Ai ban ma Nuna na Jisu ba ko mgana ban musu ba sai Gaki.."Farida Ta wuce Tiolet Tana Fadin"Bari nayi wanka Zamu Fita nayi Miki Shooping Muci Abinci Har asibiti ma nake so nakai ki aduba ki Cikin ki Har ya Fara Fitowa bana so a samu Matsala.."Cikin Mamaki Zaina na Kallon Cikinta sai Lokacinta Taga ya Turo kadan bada yawa ba Mirmishi Ta saki Tana Shafa Cikin Kafij Tace"Nagode ma Allah Daya Hadani dake Anty Farida..Zaki Tayani Cika alkwarin Da nayi ma Firstlove kan Kula mai da kaina da Abunda Ke Cikina.." Take Fada Tana Mirmishi kafin kuma ya Rikide ya koma kuka,ammh Sai Tayi Saurin Share Hawayenta Bayan Farida Ta Fito Itama ta Shiga Tayi wanka Ta bata Wata Doguwar Riga baka ta Saudiya ta saka da Gyalenta ita kuma Riga da Wando Ta saka sun kamata ta Saka Siririn mayafi Dakin Suka Kulle kana Suka Fita ba wanda yace musu komai Suna Fita Waje suka ga Uwar mata da kawarta Zasu koma kaduna Kebewa sukayi da Farida sukayi mgana kana suka Shiga Mota suka Tafi Su kuma suka Gangara Titi suka samu adaidaita suka Hau. Cikin Sabon Gari Farida ta kai Zaina Wani Shago Datake Siyan kaya Ta sata ta zabi Dogayen Riguna da irin Kayan pakistan Haka,sai Riga da Sikat,bra,sikat da kuma kayan kwalliya,Takalma da Sauransu,Sai da suka gama Siyan komai Farida ta Biya kudi Kana Suka Dauka Daman Drop din mai adaidata Farida Tayi Daganan Restaurant suka je Farida Tayi musu Oda suka ci Abinci Daganan Ta Dauketa suka je Apple White ta Siya ma Zaina Gashashen Kifi da Ice Cream Kuma ta Lura Tana so Sosai Take Shan Ice cream,Daganan Wani Private Hospital Takaita Almadina Dama Tasan Wani Likita Suna zuwa Ta Fadi Abunda ke Tafe dasu ba Dadewa aka Bude ma Zaina Fayel Likita ya Dubata yace komai Normal Zasu Dawo nan da 2 week ayi mata Scan agani Ya bata mgangunar karin Lafiya kuma yace ta samu Hutu sosai Daganan asibitin suka koma Gida Koda suka je Gidan ya Cika wai Adamalle na Birthday Karuwai maza da mata gasunan kawayensu Sun Cika Gidan anata Rawa da Kida Haka suka Raba suka Wuce Zaina mamaki kawai Take ganin Maza da mata sai Shaye Shaye suke wasu kuma suna Ta Rawa wwsu kuma na Gefe suna Shanshancinsu. ******* Achan Bauchi kuwa Abubuwa duk sun Taru sun Rikice Bangaran Zain dai ba wani Cigaba Domin indai yana Farke Bashi da wani aiki sai sambatu Yana kuka yana Kiran sunan Firstlove mganguna da alluran Barci ake mai suke Taimakamai yana Samun Barci. Daga Baban Kaduna har Daddy Abuja ba wanda ya koma Duka su da matayensu suna nan ba kwanciyar Hankali,Umma dai an samu Taji Sauki Ta Daina koken sai dai Damuwa Ta Daina yawan mgana Kullun sai Ta Tagumi Chan Gidan Alhaji Tsoho ma sai a Hankali Hajiya Mama da goggo Halima Sune ma masu karfin Halin Matar Isuhunta Tuni ta koma Goggon Haliman ne sai an kwana Biyu Zata koma. Bangaran Dina Kuwa Ta Kara Shiga Taitayinta ganin Nene ma Ta Daina Bi Ta kanta gashi Tanaso Tasan Halin da Zain yake Ciki ba Dama bamai Bata Fuska sai dai Tayi ta zaman Daki Tana kuka Dole ta kira Hajiya Maimuna Tana kuka Ta gayamata komai ita ta Kira Kwamishina Ta gayamai abunda ke Faruwa yace shi bai sani ba Da yaso nan Weekend yaje Bauchin ammh zai yi Kokari Yaje Zuwa Gobe yaga Abunda yake Faruwa. Haka kuwa akayi Washegari Shida Direbansa suka Tafi Bauchi Sai da Alhaji Tsoho Yaga Kwamishina kamar Daga sama Bayan gaishe gaishe da Jaje aka Fara maida Yadda akayi,kwamishina ya Janjanta Lamarin Sosai Tare da Alhaji Tsoho suka Tafi cikin asibitin Tunda Duk su Abba na chan sai dai suka gansu kawai Lokacin da Alhaji Tsoho Yaga yadda Zain ya koma sai da ya Share musa kwallah Duka ya"yansa Nashi Sun Rame Atsaye ga Haddir Dashi Duk ya Zabge Saboda Fargaba Suna Dakin Zain ya Farfado yana ganin Alhaji Tsoho ya Fara Fadin"Yauwa gwara da kazo..Ka saka baki Alhaji Tsoho Su Abba Su bar na tafi naje na nemi Matata..Tunda su sunki Nemo Min ita Taya zan kwanta anan Wajen Ina Barci Bansan Wani Hali Matata ke Ciki ba..?ciki fa gareta ko Kun manta ne..? Yake Fada yana Tsiyayan Hawaye Su Abba dukar Da kai kawai sukayi Cikin wani Hali Alhaji Tsoho ne ya Dinga Lallashinsa yana Fadamai Insha Allahu Halimar Zata Dawo Da yardan Allah kana ya daina Sambatun sai kuka sai ajiyar Zuciya,,Alluran Barcin bata Sakeshi ba sai ya koma Sai da suka bar Dakin kana Alhaji Tsoho yace Su Dawo da Zaunullahi Gida adaina dura mai Abunda zai sakashi Barci Hakanan kada kwalkwawarsa Ta samu matsala Adawo Dashi Gaban Iyayensa zai Dinga mai Rubutu yana Sha zai samu Natsuwa Da yardan Allah. Da Shawaran Alhaji Tsoho akayi amfani Cikin Lokaci kalilan suka Dauko Zain din Zuwa Gidan Abba sai dai su Abba suka gansu kwatsam Dashi,Alhaji Tsoho da kwamishina Suma Dasu akazo Dakin Sadiq Babba aka Saukeshi Umma da Nene dasu Zainab da Zafeera suna Ta kai da kawo Kuma Alhamdulillah Ganinsa agida yasa Sai ya samu Natsuwa Zain din ba Sambatu ammh yana ta Bin Kowa da ido kawai Barinsa sukayi a Dakin Shida Haddir Dukkansu suka Fito Falo sai Lokacin Alhaji Tsoho yace Nene Tayi ma Kwamishina Jagora Zuwa Dakin Dina ya ganta Haka kuwa akayi Tana kaishi Ta Fito Dina na ganinsa Ta Mike ta Rumgumeshi ta Fashe da kuka nan ya zauna yana aikin Lallashinta Shi ya gayamata an Dawo da Zain Gida anjuma Ta Shiga Ta Dubashi Sai Lokacin taji Hankalinta ya kwanta bai Jima wajenta ba suka Fito Tana Rike da Hannunshi Ganin Daddy yasa Ta Duka Ta gaida su Abba suka amsa ba Yabo ba Fallasa Fatan Allah kara Lafiya yayi musu da kuma Sallama Har Waje Alhaji Tsoho yace Su Abba su Taka mai ya kawo ma Dina Katan katan dib Hollandian Dama yasan Taso ne Megadi ya kwasa Zuwa Ciki Tana Dagamai Hannu Har Motarsa Tabar Haraban Gidan Kana ta Dawo Cikin Gidan ganin ba Fuska yasa Bata Tambayi ina aka kai Zain ba sai Ta koma Dakinta nan Taga Duka Abunda Daddy ya kawo mata an Shigo mata dashi Sai kuma Taji bata ji Dadi ba ko bakomai ai su suke ci da Ita bai kamata a kawo matasu Duka ba sai tace bari Ta bari in su Abba sun Fita Ta Fita Tayi ma Nene mgana. Sai Bayan Isha"i su Alhaji Tsoho suka bar Gidan Bayan Zain ya Farfado Har Nene ta bashi Tea yasha Ya Tafi kan gobe da Safe Haddir yazo ya karbi Ruwan Zamzan din da zaiyi addu"o'in aciki arika bama Zain din yana Sha,Sun Tafi Da Jin Dadi ganin Zain din ya Daina Sambatun Alhamdulillah anga Cigaba Ranar Dai Haddir ya kwana Wajen Zain din Saboda Baza"a barsa Shi kadai ba Washegari kuma Yaje ya karbo Ruwan addu"an ya kawo aka Fara Bama Zain,Ranar su Mama Safiya da Sauran yan"uwanta da basu Tafi ba su Mom Iklima ne su Goggo Halima ne Harda Hajiya Mama inna Rukayyah Inna Hannatu,,Su Waleeda da su Lauratu hajiya karama dasu Muhammed Amin duk nan Gidan Abba suka Wuni Hamdiya ma Amarya Daga kaduna sai Kira Take Tana Jin Ya ake ciki. Washegari kuma Kowa ya Dauki Iyalansa suka koma Baban Kaduna da Daddyn Abuja Yan"uwan Mama Safiya ma Tun Safe suka Tafi,Goggo Halima ce kadai Ta Rage sai Zareena itama Jawaad Yace Ta zama Cikin Shirin Sati mai Zuwa Visar su zata Fito zasu koma,Inna Hannatu kuma sai yammah Jirginta ya tashi Zuwa Lagos Inna Rukayyah kuma sai da ta kara kwana suka Wuce ita da Shema da Zafeera,Zafeeran ma Saboda makaranta da Bazata koma ba,Aka bar su Umma suna Kula da Zain Wanda Sauki ya Fara samuwa Dina Ta Shigo Ta gaisheshi Sau Daya ya kalleta bai kara kallonta ba, Ya kauda kai Sai dai Kaga yayi Shuru kawai kamar me Wani Zurfin Tunani Daga Umma Har Abba yanzu Tsauyama Zain suke Sun kuma furtamai sun yafemai Tuni Suna kuma addu"an duk inda Halima Take Allah ya Bayyanata Shi kanshi Haddir sai da Sadiq ya Dawo ne ya samu Sukuni har ya koma Asibiti Saboda bashi ba Zain abun yayi yawa Zuwan Sadiq ne yasa yake barinsa Wajen Zain din yana Tafiya asibiti sai ya Dawo da yammah yake zuwa ya kara Dubashi Ba laifi Tunda ya Daina Sambatu kuma yakan ci Abinci yana kuma Mgana Daya zuwa Biyu. *Ki biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki Saka kudi ki siya abu kuma ki Fitar dashi..Mace mai aji Bata kiran Abun sata komai nata mallaka take..* *Janafty...* 7/10/21, 8:40 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣4️⃣ *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *Bayan sati Daya* "Bayan Sati Daya Da Dawowar Zain Gidan Abba Abubuwa Duk sunyi Sauki Sosai yake samun Sauki anata kuma ganin Cigaba Tunda yanzu yana iya yin Wasu Abubuwa da kansa kamar Wanka cin Abinci Da Sauransu Sai dai ya koma wani so Silemt Shuru Shuru ba mgana ya Rame Kamar bashi ba Ya Daina Yawan Kukan da Kiran Sunan Firstlove sai dai kuma Zaka ganshi Cikin Tunani mai Zurfi Wanda ba Tunanin Kowa yake ba sai Tunanin Yanzu Dama Da Gaske Zainarsa Ta barsa..!? Wani Hali Take Ciki..? Ina Take a Halin yanzu..? Yaya Abunda ke Cikinta..? In ya Tuna Haka acikin Zuciyarsa Rauni yake Ji Sosai kamar ya Zauna yayi ta kuka Haka akeji. Damuwarsa Ta Ragu ne saboda Yadda Yan"uwa kowa Hankalinsa ya koma kansa Domin Yanzu Zain ya zama Abun Tsausayi kuma Kowa ya Shaida Abunda ya Faru Tsakaninsa Da Dina Wata kaddarace ba wai Domin baya son Zaina ba Kowa ya Shaida wannan Kaunar Dayake mata Gashi Dalilinta yana neman ya Zauce Umma Da Nene Kusan Dakin Sadiq suke Wuni suna Kula Dashi Motsi kadan sun kama Tambayansa Ko yana Son Wani Abu ne Umma Tayi kuka Tana Rokon Zain Daya yafe mata Itace Sanadiyar Tafiyar Halima Shima ya Rumgumeta yana Share mata kwallah,yau gashi Umma Ta Cire alkunyar Data kemai Tana Nuna mai Dukkan Kulawarta Ita da Nene sai ka Rasa waye yafi Wani Kula Dashi Haka Abba ma in ya Dawo Daga Office yana Tare da Zain din yana Ta Mai Nasihan Daukan Kaddra Kuma Alhamdulillah ana ganin Cigaba Sadiq ya koma makaranta Haddir ma Ya koma Gidan Alhaji Tsoho Tunda yaga Zain din ya Fara samuwa sai dai Yace bazai koma Chan Lowcoat ba Ba Firstlove Dole kayansa aka Debo masa ya Tare gaban Iyayan Nashi Suma Hakan ya yi Musu Dadi Domin yanzu Sun Fi Bukatarsa Kusa Dasu Fiye da Kowa. Goggo Halima Ta koma Gada Da Tarin Damuwa na Farko Batan Halima Na Biyu Halin da Zain yake Ciki Ranar da Zata Tafi Da Tazo Ta kara Dubashi Suyi Sallama kuka Reras Zain yayi ma Goggo Halima Itama kukan Take Tana Shafa kansa Tana kuma Gayamai ya kwantar da Hankalinsa da Izinin Lahi lafiya lau Halima Zata dawo Garesa Ita da Abunda ke Cikinta Abba ya bada Direbansa yakai ta Har Gida Da Sha Tara na arziki Koda Ta Koma gida ya Fara Cika da yan"uwa Domin Daman Hankulansa atashe yake da Batan Halima da kuma Labarin da Matar Isuhu Tazo Dashi Goggo Halima Tana kuka Tana basu Labarin Halin da Iyalan Alhaji Tsoho ke Ciki na Batan Halima sai ma suka ga ai kara zasuyi musu na Tayasu Add"an Allah ya kare Halima Duk inda Take Allah kuma ya Bayyanata Ita da Abunda ke Cikinta. Zareena ma Jawaad yazo ya Dauketa ana Gobe Zasu Tafi,Daman Zarena ta gayamai Abunda ya Faru Domin bai samu Zuwa Daurin Auran Hamdiya ba Shima yayi ma su Umma Jaje sosai kafin Zareena Tayi sallama da iyayanta Tana kuka Sosai Suka Tafi Bayan Sun Biya Tayi ma su Alhaji Tsoho Bankwana chan ma da kuka Suka Rabu Tana kuma Fatan Allah ya Bayyana Halima Ko domin Dan"uwamta Zain ya koma kamar yadda Ta sanshi,Bayan Tafiyan Zareena sai Gidan yayi Shuru Kowa kagani Ba wani Walwala Zainab Ta koma Zuwa makaranta Saboda sun Fara Jarabawa. Allah Sarki kawar Zaina Laila Tazo Gidam Umma Tana ta kukan Batan Halima Tace Rabon Data ganta Tun Zuwanta Gidanan na Karshe Ta Shiga Har Wajen sa suka gaisa yana Ce mata Taga Yanda ya koma ko..?Firstlove Ta tafi Ta barsa In Tasan Inda Take tayi ma Allah da Annabi Ta gayamai ko nawa ne zai iya bata indai Zata gayamai Inda Zainarsa take zai iya bata. "laila Tun Tana Daurewa Sai da Ta Fashe da kuka Tana mai Rantsuwa Wlh bata san Inda Halima Take ba Umma ce Tajata suka Fita Daga Dakin Haka ta bar Gidan Tana ta kuka kamar karamar yarinyar Makaranta ta Wuce har sun Fara Jarabawa,tayi kukan Rashin kawa kamar Halima Tana Tuna Rayuwarsu a makaranta da Son karatun Zaina ammh yau Wannan Burin nata ya Tashi a abanza Duk wani Motsi na Zuciyarta sai Tayi Addu"an Allah ya Kare Halima aduk inda Take karin Abunda ke sakata kuka Dataji Labarin Halima da Ciki Ta bar Gidan Sai Taji ta kara Raunana Tana Fatan Allah ya Tsareta aduk inda Take Allah yasa Ta Fada Hannu Nagari... Bangaran Dina Kuwa Jikinta Yayi Sanyi Ganin yadda Zain ya koma Allah ya gani Tana Son Zain Ko Zaman Datake agidansu Saboda Kaunar Data kemai ne,Tana Shiga ta Dubashi Safe da yammh Ammh In ta gaida Zain baya amsa mata kansa ma yake kaudawa Saboda bayason ganinta Tana Tasomishi da wani Miki kuma yana ganinta Akan Itace Faruwan komai,Sai da Nene tamai mgana kana yake amsa mata in ta Shigo Gaisheta Wani Abu Dake sukan Ransa ganin Cikin Jikin Dina Har ya Fito Nene tace Dinar Tana Daga Cikin Mata masu Girman Ciki Alhaji Tsoho yayi ma Haddir mgana kan zai Rika Duba Dinar agida Har Zuwa Ta Haihuwa Saboda kada asamu Wata Matsala. Yanzu Dina Ta Rage zaman Daki,Tana Fitowa Falo Ta zauna Tayi Shuru,In Taga Umma tana Gaisheta Sai dai Umman ne bata mata wani kyakyawan kallo hae Gwarama Nene,Harta dasu Saudart Dake yara Dina ta Fahimci Sun Tsaneta Shiyasa Take Allah Allah ta Haihu a Daura mata Aure da zain dinta su koma Gidansu bata Damu da Kowa ba ada Tana Jin Dadi Da Tafiyar Zaina sai Daga baya Da Komai ya Rikice ta Fahinci Mganar Zakiya Gaskiya ne Datace Tafiyarta ba Mafita bace Domin Zain Zai zama sai ahankali kuma ko Ta aureshi Baxata Ji Dadinsa ba aikuwa Tagani Gashi Ta kanta yana neman ya Fara Hauka,Wannan Dalilin yasa Tayi Laushi ammh acikin Ranta Tafi Kowa Murnan Hakan Kuma Tana Fatan Allah yasa kada Haliman ta Dawo Taje Chan Ita da Abunda ke Cikinta su mace ta zama ita kadai ce Tauraruwa awajen zain Kuma Uwar ya"yansa,Zakiya dai bata kara Zuwa ba sai dai suna Mgana ta waya Lokaci bayan Lokaci. Su Baban Kaduna da Daddyn Abuja kullum Cikin Kiran waya Suke Tambayan ya Jikin Zain..? Kuma ba wani Labari ne..! ? Haka su Inna Hannatu suma Hankula dai sun Fara Kwanciya ganin Zain din ya Fara Dawowa Hayyacinsa sai dai suna ta Addu"an Allah ya Dawo da Halima gida Cikin Koshin Lafiya ita da Abunda ke Cikinta Allah kuma yasa Ta Fada Hannu Nagari Haddir kam ya Cika Aminin kwarai Kullum in ya Dawo aiki yana Wajen Zain yana kara Bashi Baki Shi Zain zai tama mganganu yana Rokonsa ya Tashi ya rakasa Neman Firstlove shi kuma yana Nuna mai Kada ya Damu Zata Dawo Sunanan suna gayama Allah Shima ya Cigaba da gayama Allah aduk inda Take Allah ya Tsareta Ita da Abunda ke Cikinta. Allah Sarki Zafeera Tana chan kano Duk ta Rame Saboda Damuwa Jarabawan ma Tana dai yi ne kawai ammh Tafiyar Halima ya Tabata Sosai Hakama Faruq na chan Chicago Cikin Damuwa Hotunan da Zafeera Ta Turomai ne wanda suka Dauka Ranar Bikin Hamdiya ne yake kallah yayi ta Sharan kwallah haka in ya Kira su Umma yayi ta Fadin Umma yanzu Shikenan haka zamu zauna Ukti ta bar Gida..? Yanzu in na dawo Hutu bazan ganta ba..? Umma sai Ta Share kwallah tace"Sai Hakuri Faruq..Addu"a zamu Tayata Dashi Allah yasa Tana Hannu Nagari Allah kuma ya Tsareta Ita da Abunda ke Cikinta,Haka zasu gama Zuciyoyi ba Dadi Zafeera kam kullim Dare sai Tayi kuka In Tana kallon Hotunansu Da Zaina Tun suna Yanmata Da wanda suke da Faruq tun suna gida album guda Gareta Tayi Ta kallo Tana kuka Tana Fadin"Allah ya bayyana mana ke Ukti Aduk inda Kike Allah ya kareki Dake da Abunda ke Cikinki.."Tanayi Tana kuka Sai da Shema Taga Abun nata ya wuce na Lafiya Ta Sanar da Inna Rukayyah Kana Tazo Tana Ta lallashinta Da Nasiha Ta kuma karbi Duka Hotunan Datake kallo yana sakata kuka ammh Duk da hakan Damuwar Abun na Cikin Ranta Karatun ma Jarabawar Ma Tana dai yi ne kawai ba Domin Tana Fahimta ba Fatanta akoda Yaushe Allah ya Tssre Ukti..Allah ya Sa Tana hannun Wadanda zasu kula da ita Allah kuma ya kaddara suna da Rabon ganawa da juna Ameen. ****** *Zaria.* Zuwa yanzu da Zaina keda Wajen kwana Goma a zaria akuma Gidan Uwar mata Hannun Aisha Farida Sholly Zuwa yanzu Ta Fara Fahimta wani irin Gida Take Ciki Ta kuma Fara Fahintar me ake kira Bariki Ta kuma Fara Fahimtar Wadanda ke Gidan irinsu Zuly Suby,Da Deezee Da Su Rufy Ta Lura Sauran kamar basunan Domin wasu Dakunan bata Taba ganinsu an Bude su ba Ta Fahinci kacharalle irin kawali ne mai kai ma Maza Mata Suna Shashanci Dasu Domin Duk shi yake kawo ma su Suby Costumer,Ta kuma Lura agidan suna Bala"in Tsoron Farida Ko kusa da Dakinta basa Zuwa Batare da Izininta ba, kuma kamar Faridan Tafi Shiri da Zuly Domin Ko wani Abu ne Zata kyautar ita take bamawa Tunda Ita Zuly kamar itace karshe agidan Barikin bai karbeta ba Watarana ma Abunda Zataji Gagaranta yake,Sun Ji gargadin Sholly da Uwar mata bamai Shiga Sha"anin Farida da ita Tunda bama Fitowa Take ba sai dai in Dambe ya Tashi Ko wani Abu ta Tsaya Jikin Window Tana Kallo Tana Hawaye Domin Yanzu Ta Daina Tsausayin kanta Ta Fara Tsausayinsu Suby Tana Tunanin in BakaFito Duniya ba ina Zaka san ana irin Wannan Rayuwar...? Tunda Farida Ta kawota Gidan Bata Fita Taje wani Waje ta kwana ba ammh Takan Fita Taje Ta Dade kafin ta Dawo In ma Girki ne Zuly take sawa Tashigo Dakin Ta Girka mata ko Kuma Ta bama Kacharalle Kudi Tace ya kawo ma Sady baby kamar yadda yake Fada abinci Taci kafin ta Dawo kwarai Farida ta Cika alkawari Domin Banda wanka Babu Abunda Zaina keyi sai dai taci mai kyau tasha mai kyau ta koma ta kwanta Ga Kallo Farida Tna kunnata mata Saboda Debe kewa ammh bawai Domin Tana Fahimta ba cikin Lokaci Ta Fara maida Jikinta,ga mgangunar Da Likita ya bata suna sakata Kiba Laulayin nata ma ya Ragu yanzu kuma maida Jikinta Take yi Tayi wani Fresh kowa ya ganta yaga mai Cikin Datake samun Hutu Duk da Farida ta Zame ma Zaina garkuwa bata Sakankance ba Ta manta da Addu"a ba, Koda yaushe Rokon Allah take ya Tsareta ya kuma Tsare Abunda ke Cikinta Saboda cika alkawarin Datayi ma Firstlove. Babu Wanda yasan Tana da Ciki Sai Farida kuma Bata gayama Kowa ba ko Uwar mata bata gayamawa ba,Kuma dogayen Riguna Take sakawa Cikin Daya Fara Tasowa yake Boyeshi Ko kuma pakistan Riga da Wando Abunta kanta kuma Sau Daya Farida Ta kaita cikin Sabongari aka ggyara mata akayi mata Kitso,Ba wanda Farida Ta yarda Tayimgana Dashi Daga Kacharallle sai Zuly Suma ba wai Ta yarda dasu bane kawai Tafi yarda dasu akan kowa na Gidan ne Shiyasa in ta Fita ta kan Bar Zaina da Zuly Tare acikin Dakin Tun Zainar bata sakin jiki Har ta Fara saki da Zuly Wacce Tace mata ainihin sunanta Zulaiha ce kuma ita yar Kauyen Yashe ne Dake garin Katsina Daganan ne bata gayamata komai ba ammh Zaina Tayi alkawarin sai ta Tambayeta Watarana me ya kawota wannan Rayuwar..? Ammh sai ta yanke acikin Zuciyarta Anty Farida Zata Fara Tambaya Labarinta Domin itace Bata mata kama da Wacce Rayuwarta ta Dace da zama karuwa ba yadda Take da Zuciya mai kyau ammh Faridan Taki ce mata komai ko Tayi mata Mgana sai tace mata Zata gayamata Komai Watarana. ****** Yau ma kamar kullum Farida Tun Safe Tayi Wanka ta Chakare Kwalliya kamar zata gasan kyau,Tace ma Zaina kaduna Zata Je Direba ma yazo Daukanta a wata katuwar Mota Kafin Tatafi Ta Kira Zuly ta Roketa Ta Zauna da Zaina Ta Tambayeta Abunda Take so Taci Ta Dafa mata Ta saka mata Ruwan Wanka Tayi wanka ta kwanta Ta Huta sai Zuwa Dare Zata dawo. Da Gudu Kuwa Zuly Daman Tun Jiya Rabonta da Cin wani Abinci Daman Wajen Sholly Take samu Sai Wajen Sady kuma ita yau ba Gida Ta kwana ba Taje Hause Services,Har Farida Tatafi Zaina na kara wani Nazari akanta Tun da Tazo Gidan Bata Taba ganin Farida Wani Kato yazo Wajenta ba Sai dai Ta kanyi mgana awaya Ko kuma aturo mata Sako ko kuma azo da Mota adauketa Tun Safe sai yammah Zata Dawo da Shopping kalakala nata Dana Zaina Komai ta samu sai ta Siyo ma Zaina kayan kwalama irin na masu Ciki har Gajiya Zaina Take da Cinsu Duk Ta Tusa shi Cikin karamin Firizan Dake Dakin Kada ya Lalace Ita dai da Idanuwanta Bata Taba ganin Wani yazo wajenta ba,ammh Tasan Farida Tana Harka da manyan Mutane Domin in ba Haka ba su waye ke bata kudi..?badai irin Wadanda su Zuly ke harka dasu ba Ko Ita ta Raina su irinsu Shafsoon. Zaina na Saman Kujera,Zuly Ta Shigo Cikin Fara"a suka gaisa Kana Tace mata me zata karya Dashi..?Zaina tace Ta Bata Complex tasha kawai Cikinta ya Cika Tasha Icecream Jiya Da Daddare da nama,Cikin Sauri Zuly Ta kunna gas ta saka Ruwan Zafi ta Hadama Zaina Complex cikin wani karamin Kofi Ta mika mata ta Fara sha kenan Taga Zuly na kallonta sai Tace ta Hada itama Tasha Ta kuma Dafa wani Abu Taci Karta Damu. Kamar an saka Zuly agidan Aljannah haka Taji nan da nan ta Hada Complex Kofi Daya Ta Tadashi,Da Sauri Ta Dora Indome guda Uku Ta Dafa Ta Hada da kwai Biyu,Bayan Ta gama Ta Juye afilet ne Zata Fara ci sai Zaina Tace Ta Daga Labule Saboda ba wuta Zafi ya Fara Shigowa Taga Zuly sai Zufa Take Nan da nan kuwa Tatashi Ta Daga Labulen Fuskar Tsakar Gida na kallonsu. Tsausayin Zuly ya kama Zaina ganin yadda Take cin Abinci Hannu baka Hannu kwarya Allah Sarki Itama ba Domin Ta Hadu da Anty Farida ba Da Tana Cikin Wata Rayuwa Mikewa Tayi Tsam Ta Bude Fridge ta Dauki mata Roban Yourghot din da Farida Tazo Mata Dashi Jiya Bata sha ba da Maltina Guda Daya Ta Nufeta Dashi Tana Zuwa Ta mika mata Zuly Data Fara Dawowa Hayyacinta Ta Dago Tana kallon Zaina da Sigan Tambaya Cikin Tsausayinta Zaina Tace"Karbi Ki sha..! Mirmishi Zuly Tayi mata kafin Ta karba Tana Fadin"Nagode...Sadiya.."Tafada Tana bude Maltinan ta kwankwade Rabi kana ta Ijiye komawa Zaina Tayi Ta zauna Tana kallonta kawai Dukkansu sai sukaji Muryan Adamalle akansu ta saki Shewa da Guda Da Sauri Zuly Da Zaina suka Dago Suna kallonta Zuly tayi ma wani kallo Kafin Ta kura ma Zaina Ido Tana kallonta Ganin Ta Cikin pakistan Riga da Wando ammh Ta yane kanta da wani karamin Vail,Baki ta Rike kafin Ta kara Leko Da kanta Dakin Tana Fadin"Ba Shakka Hajiya Zuly..Daman ai ke haka zaki kare ba Zuciyan neman nakai sai dai Kwadayi..Karki manta dai Duk wanda yahau Motar kwadayi Karshensa Tashar Wulakanci muna nan Dai zamu gani.." Tafada Tana kara kallon Zaina ganinta Ta kara Girma da Fari Tayi kuma Kiba Tana mata wani kallo Zaina ta kauda kanta kawai gabanta na Faduwa,Zuly ce ta Dago Ta kalleta Tana Bude Yourghout din Gabanta Tace"Eh din naji ai ba Wajen wata naje yin kwadayin ba ko..? Mtsww Kema kiji Da kanki Don Allah kafin Kizo Kiji da wata Mun Riga mun san komai Shikanshi Farkan naki Bake ke ke Ci dashi ba..? Me yake baki banda Yazo yayi Shaye Shayensa ya Tila miki Amai ya barki da Kwashewa..?hmm munsan komai Fankan Fankan ne ai bata Bada Kilishi.." Tafada Lokaci Daya Tana Zabgama Adamalle Harara Turus Adamalle Tayi Jin yau Zuly Tayi mata Wankan Tsarki Dariya Taji Daga bayanta Tana Waigawa Taga Deezee ce Daure da Towel da Botiki Zata wanka Sai ta Saki Dariya kafin Tace"Bariki Ba riba..Komai kayi ba Sirri sai kajishi aduniya.."Ta kara Dariya kafin ta Wuce bakinciki ya kama Adamalle bata kara mgana ba ta Wuce tana wani Turo Kugu kamar Wata mai Kurga. Da kallo Zaina Ta Rakata acikin Ranta Kuma Tana Fadin Topha,Ita dai Tana ganin Rayuwa kala kala bata Dawo Hayyacinta ba sai da Taji Zuly Tayi wata katuwar gatsa Kana ta Kalleta Tana Fadin"Alhamdulillah ya kamata Kice Zuly..Irin wannan gyatsan Bata da kyau Annabi ya Hana..".. Zuly Ta kalli Zaina kafin Tace"Nagode Sa"adiya.."Kawai Ta iya Fadi kafin tace Alhamdulillah a Ahankali mikewa Tayi Tana Fadin Bari ta Juyema Zaina Ruwan wanka kai ta Girgizamata kafin tace"bar wankan nan ba yanzu ba...Zauna Don Allah dama ina so Nayi Miki wata Tambaya..? Komawa Zuly Tayi ta Zauna Bayan Ta kauda Filer din Datagama ci Daga gabanta Cikin Mamaki Tace"Allah yasa na Sani Sadiya.."Zaina ta gyara Zama tana kallon Zuly kafin tace"Meyasa Kuka zabi irin wannan Rayuwar ne Zuly naga ku kan ku baku jin Dadinta banda Wahala da Wuya Babu Abunda kuke ci Ina amfani Rayuwar da Abunda Zaka ci mana yana Gagaranka Ki koma Gaban Iyayenki mana Zuly kinemi gafaransu Ki Tuba ga Allah Wlh na Tabbata Rayuwarki Zatayi Daraja Fiye da yanzu da Babu Komai Cikinta sai Rashin Kima da Rashin Daraja Kullum fa sai da wannan Katon yazo yayi Ta Dukanki kamar jaka.." Zuly Ta Sunkuyar dakai Hawaye suka Zubo mata Cikin Share Kwallah Ta Dago Tana Fadin"Da gaske ke kanwar Sholly ce Ta Jini..? Zaina ta gyada mata kai Mirmishi Zuly Tayi kafin tace"Ko Baki Fadamin ba Nasan gaskiya baki Hada komai da ita ba..Zan gaya miki Wata gaskiya Kinyi Sa"a Samun Uwar daki Farida Bazata Taba Cutar Dake ba Macece mai Zuciyar Zinare Shiyasa ma Uwar mata Ta barki Kika Zauna awajenta Batare da wata Matsala ba,Saboda Sholly Tana Tara ma Uwar mata Jari Sosai Fiye da Zaton kowa Shiyasa Ta kaasance yar Gaban Goshinta.."Zaina ta gyada kai Tana Fadin"Na Fahimci hakan ammh ku meyasa bakwa Tara mata kudin Data ke so..? Zuly na Sharan kwallah Tace"Ni ahakan ne zan Tara wani Kudi Sady..? banda Shafson ba Namijin Dake kulani Shima na In samu Abun d zan ci da kaina ne,Kullum in yazo Wajena Bayan ya kwantani kafin ya bani Wani Abu sai ya Dakeni ya maidani kamar Wata Dabba Daya Turke in zai Bata abinci sai ya Daketa Sa,"adiya Kada Kiji Watarana zaki Sha"awar wannan Harkan Bariki batayi ba..Bariki ba Rayuwa bace sam ."Ta Fada Cikin kuka Zaina ta Rarrafo Gaban Zuly Tana Dafa kafadanta Lokaci Daya Tana Fadin"Nasani Zuly Tunda nazo Gidan kece wacce na Fara Tsausayamawa..Shin Meyasa bazaki bar Wannan Rayuwar ki koma Gaban iyayanki ba..? Zuly Tayi Mirmishi Tana Zubar Hawaye Tace"Ina ina ma..Ina ma ace Ina da Iyayen..Da ina da Uwa da Uba da kuma Tsayayyin Dangi Da baki ganni anan ba Sa"adiya..Ni Da kika ganni nan Marainiya ce Ta uwa ta Uba Tun ina da Shekara Goma aduniya Iyayena suka Rasu sakamakon Ginin Daki Daya Fado musu Su da karamin kanina Yusha"u Maraici da Rashin Gata ya Kawoni wannan Rayuwar.."Ta Karishe Fada Cikin Kuka Kamar Zata Shide.. Zaina Har Taji Taruwar kwallah Saboda Tsausayin Zuly Cikin Lallashi Tace"Allah sarki Kamar Ni kenan ni ma Tun Ina Da Shekara Daya da wani abu aduniya iyayena suka Rasu..Allah ya jikansa da Rahma.."Zuly Ta amsa da amin kafin tace"Kema Maraicin ne ya kawo ki nan Sa"adiya..? Zaina Ta Girgiza kai kafin tace"Ban Taba Kukan Maraici ba Zulaihat..ban Tashi na Sanshi ba Ko masu Iyaye basu kai ni samun gata ba..Abunda ya Baroni Da gida Dabam..Kedai nake so ki gayamin Labarinki.." Zuly Tace"Labarina ba wani mai yawa bane Sa"adiya ba kuma mai Dadin ji bane..Da Farko Dai ni sunana Zulaihat Shehu Yashe ni Haifaffiyar garin Yashe ne ta Jahar katsina Uwana da Uba Duka yan chan ne na taso Naganmu bamu da wani Cikakkun Dangi kuma Mu Takalawa ne masu Neman na kansu,Babana Manomi ne Mamata kuma Masurfiya ce Dashi na tashi Naga suna Rufama kansu asiri Ni da kanina Yusha"u kadai suka Haifa Shima kuma Tare suka bar Duniya,Alokacin Iyayena Nada Rai bana Tallah sun Ingantamin Rayuwa sosai ina Zuwa Makarantar da Allo Data Islamya Ammh Bayan Rasuwarsu sai komai ya Tsayamin Cak na Fahinci maraici da Rashin Gata Baffa Idi Shi ya Daukeni Wanda suke Uba Daya da Mahaifina Shima Dalili Saboda Dan Gidan Da iyayena suka Mutu Suka barmun ne Yasa Ya Daukeni Ya Damkani Hannun Matarsa Larai. *Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki Siya abu kuma ki Fitar dashi Waje..Mace mai aji bata Jiran Abun Sata komai nata mallaka take..* *Shakira...* 7/11/21, 4:56 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣5️⃣*    *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*                 "Larai irin Muguwayen Matan kauyan nan ne wadanda basu san komai ba sai kansu da ya"yansu Tunda na koma Gidan Baba Idi nake Cikin ukubar Rayuwa Duka ayyukan Gida ni nake yi ga Tallan Shinkafa Safe da Rana da Yammah kuma Tallah Duka ya"yanta Mata ne ammh bata Dora musu Tallah sai ni,Gashi Baba Idi Shima Dan Duniyan ne Son Abun Duniya kuma Larai Ta Riga Tagama Mallakesa Da Shawaranta yake amfani Gadona kuwa Tuni Ya Saida Gidan Da Shawaran Larai suka Cinye kudin da sunan Suna Taramin kayan Aure. Makaranta Daga Ta Islamiya Harta Boko Duka na Daina Zuwa Larai Ta hanani Tun ina Son karatun araina Har na Cire Raina ganin Burina bazai Taba Cika ba,ahaka na kwashe Shekaru hudu acikin wannan Rayuwat Duk na Jeme na Lalace Wahalan Rayuwa ta maidani Wata Tsohuwa Rana Tsaka Yakubu Gala ya Fito Neman Aurena. Yakubu gala Dan wani Babban Manomi ne agarinmu,kowa yasan Yakubu gala ba yaron Kirki bane Shi kadai iyayansa suka Haifa sai suka Sangartasa Tun yana Yaronsa Takadiri ne Dan Shaye shaye ne ba Kwayar Da baya Korawa,Da kuma ya kyalla Ido yaga yarinya In yace yana Sonta zai aureta Shikenan an gama mgana tun Da Dadewa Ake Zargin Yakubu Dala yana Neman Maza Har dai Abun ya Tabbata Saboda in ya auri mace Ta Bayanta yake Nemanta Sai ya gama Morarki ya Dankara Miki Saki ya Kada ki Gida kije Kiyi ta Jinya Daga Karshe kuma Cutar Tsitsontsin Daya Saka Miki a Cikin Ciki suyi Sanadiyar Mutuwarki. Lokacin Daya Fito Neman Aurena na Tsorata Sanin Halin yakubu Gala Ko shi Lokacin Baba Idi yaso yayi gaddama ammh Da larai ta saka baki Dole ya amince kuma Mahaifin yakubu Galan ya Sakar musu Kudi Alokacib Bani da wata Mafita,Tun alokacin naso na Gudu sai kuma nayi Tunanin Bani da Wajen da zani Ina ji ina gani aka Dauramin Aure da yakubu gala akai ni Gidan iyayansa Ba wani Abun arziki Daga Tabarma sai K'walla da Tukwanen Girki Ranar nayi kuka na kuma Shaida Rashin Gata da Maraici Illah ne. Adaran Ranar ban Tsira ba Yakubu Dala ya Turmusheni Ya Sadu Dani Ta Baya ina kuka ina Komai yace saboda haka ya Biya Sadakina ammh ai ni kaina na san Cewa bam kai matsayin da zai So ni ba,Nayi kwanan Bakinciki Washegari Tun Safe na Gudu Gida na samu Larai Ina gayamata ina kuka ammh Larai Ta karyatani Ta kuma ta sani Ta maida Ni Tana fada Da mganganu Tana Fadin In na Kashe Auren nan sai dai na Shiga Duniya badai Gidannsu ba. Wannan Furucin na Larai yasa Bani da wani Zabi sai na Zama da Yakubu Gala yana yadda yaga Dama Dani a kullum sai ya Sadu Dani Ta bayana,Kamar Wata Dabba Safe da Rana da yammah Tun ina kuka har na hakura na Daina Tun Bana Fahimtar yakubu namin Illah har na Fara Fahimta ya Rarakemin Duburata da Rami Sosai sai na Fara Tsorata in yazo sai nayi gaddama haka zai Min Duka kuma ya kwanta Dani yayi yarda yaga Dama,Ganin in na Zauna Ni zan Cuta Ranar yazo zai yi ni kuma naki na bari ya kwanta Dani Ta bayana Ya Fara Dukana Ni kuma sai na Rarumi karfen Da nake kare kofata dashi na Bugamai saman kai ya Fadi a sume jini na Zuba ganinsa ahaka yasa naji Tsoro na Gudu Gida ina Zuwa gida Nayi Ta kuka naki gayama Larai Abunda ya Faru sai Zuwa Dare sai ga Uwar Yakubu gala Tazo Tana Fadin In Danta ya Mutu Nima sai an kasheni nan take gayama Larai naso na kashe mata d'a yanzu haka yana kwance a asibiti baisan inda kansa yake ba. Da Larai Taji haka sai ta Tsoratar da Baba idi kan cewa In Ya barni nacigaba da zama agidansa Zan jazamai Bala"i Gwara ya Koreni na kara gaba Shi kuma ya yarda Dashi suka Taru sukamin Koran kare ina kuka ina Komai ina Rokonsu ammh basu Tsausayamin ba,Na bar garin Yashe nayi Ta garagaram na Hadu da Wani Dan Daudu shi ya Taimakeni ya kaini Tafa Chan na Hadu da Hajiya Zabba"u Kawar Uwar mata Ita ta kawo ni Zaria wajen Uwar mata Ta karbeni ganin Halin Danake Ciki yasa Ta kaini asibiti Akamin aiki kan Dubura na da yakubu ya Rarakemin Bayan naji Sauki Uwar mata Ta Saka Jarinta akaina Har nayi makari Ta Tallatani kuma aka Siya Da Farko kamar na Shigo Barikin a Sa"a ammh Daga karshe sai komai ya Tsaya na Farko ba kyan Fuska ba na Jiki Har Uwar mata tazo Tana ganin Laifin Hajja Zabba"u Data kawo mata Ni Ta kashe kudi akaina Bata samu Riba ba Daman Batayi Niyar karbana ba ita ta Matsa mata Da taso ma ta sallamani ba,sai Kuma ta Fasa Tunda ganin ina ta kuka bani da Wajen Zuwa Daman kuma Tun Farko Hajiya Zabba"u ta gayamata Labarina da nata bata. Tun ana Zuwa Daukana Ina House Service har kuma nazo Sai dai kallo Daga nesa,Tun ina sanun Nacin Abinci har yazo yana Gagarana naso Uwar mata Ta Daukeni aiki agidan Abincinta Taki tace bani da kyan Fuska ballatana na Jiki Zan Korar mata Costumer,Dole na Hakura Dama Suby ce kawata Tunda nazo Gidan Itama Bata da Mutumci sai Taga Dama Take samin wani Abu Kacharalle ne ke Taimakona Shima sai yayi kawali ya samu Wani Abu sai Sholly wacce duk Gidan ba kamarta Bata da yarda ammh kuma Abun hannunta bai Rufe mata ido ba Shafsson Da kike gani shi kadai ke Tare Dani Ni kaina Bani da yarda zan yi ne Ina samun na abinci in na Koresa zan Zauna da yunwa bame bani Shiyasa Nake Hakuri Domin Nasani Rashin Gata da Maraici ya kawoni wannan Rayuwar na Gwammace zamana anan sau Dubu kan na Koma Gaban Larai na Tabbata bazasu karbeni ba..! Zuly Ta karishe Labarinta Cikin Wani Irin kuka mai Dafa Zuciyar mai Sauraro,Zaina da Tun da Zuly Ta Fara bata Labarinta Take kuka Kashirban mai Neman kuka ne aka Jefeshu da kashin awaki,Zuly Ta Dago Tana kallon Zaina kafin tace"kinji Takaitattacen Labarina Sa"adiya..Da ace yau Uwa da Ubana suna Raye da ban Fado wannan Rayuwar da bata da kima ba.." Take Fada Tana wani Kuka Hawaye Zaina Ta Share kafin Ta Dafa Zuly Tana Fadin"Hakika Labarinki akwai Taba Zuciya..Larai da Baba Idi sun yi Zalunci kuma Allah bazai barsu ba Yansu ina Yakubu galan ya Rasu ko yana Raye..? Zuly Tace"Ban sani ba..Ban kara Komawa garin ba..Bani da Masaniyar yana Raye ko Baya Raye.."Zaina tace"Allah Sarki..Kiyi Hakuri ki Daina kuka Inshs Allahu Watarana zaki Bar Wannan Rayuwar kuma Zan yi ma Anty Farida mgana Zata Taimaka Miki.."Zuly Ta Share Hawayenta Tana Fadin"Nagode...Nagode Sa"adiya Tunda nazo Gidan nan ban Taba Haduwa da wanda ya tsaya ya Saurareni kuma ya Fahimceni kamar ke ba..Nan Gidan Kowa kansa ya sani kuma babu yarda Saboda Cin Amana Tayi yawa abariki.." Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Zaina Ta kada kai Tana Fadin"Lalle Rayuwa Darasi ne..In kaji Rayuwar wani sai kayi Tunanin kai kana aljannah ne Allah na Tuba ka yafemim.."Take Fada Tana Sharan kwallah,Zuly Ta kalleta kawai ta kauda kai Ruwan wanka ta Juye mata ta Surka ta kaimata Bayi kana ta Fice Tashi Zaina Tayi tayi wanka bayan ta Dauro alwala Tazo tayi sallah ta Sauya kaya tayi sallah kana takoma Ta Zauna Tana Tunanin Labarin da Zuly Ta bata Allah sarki Allah kadai yasan adadin Matan da suke Shiga Gararin Rayuwa Saboda Maraici Da Rashin gata. Wajen 2pm na Rana Zuly Ta Dawo Dakin Ta girka ma Zaina Taliya mai Kifi sukaci Tare suna Hira kamar sun Shekara Tare Hakama Da Daddare Zuly Ta Dafa Musu Cuscus suka ci Har Wajen 10pm Farida bata Dawo ba sai Zaina Hankalinta ya Fara Tashi Zuly ke kwantar mata da Hankali sai 11pm sai ga Farida Ta Dawo da Niki nikim kaya Da Ledoji Ta Shigo Sai da Zaina Taga Dawowarta kana ta Sauke Numfashi Zuly ke Fadamata Damuwar da Zaina ta Shiga Dariya kawai Tayi,Ganin Zuly Ta Kula da Zaina yasa ta Bata leda Daya Cikin Ledojin Data zo Dasu Ta karba Tana ta Godiya Ita kuma Zaina Ta bata Ledarta ta Kaza da kuma Ice.Cream mai Sanyi ita kuma ta tube ta Shiga Wanka Bayan Ta Fito ne Tazo ta Fara Rama Sallolinta Tundaga azahar har Isha'i Duk Zaina na kallonta Sai da ta idar kana Zaina Ta kalleta Tana Fadin"Anty Farida ina kika je ne Haka Da bama ki samu yin Salollinki kan Lokaci ba sai yanzu..? Farida Ta Mike Tana Yaye Hijabin Jikinta Wardrope dinta Ta Turasa Ciki Dama Zani ne ajikinta ta Cireshi Ta saka wata Doguwar Rigar barci mai Taushi Tana Fadin"Naje nema mana Abunda zan Rike ki kuma na Rike kaina Sa"adiya..Kuma Zama ai bai kamani ba Ciki gareki kuma nayi alkawarin Zama Garkuwa gareki Zan kula Dake kamar yayar da zata kula da kanwarta Saboda ki cika ma Firtslove Burinsa da alkawarinsa Ki koma mai Ke da Abunda zaki Haifa Cikin Koshin Lafiya.." Zaina Da Hawaye suka Cika Idanuwanta Ta dukar dakai kawai Tana kallon Cikinta Farida na kallonta Tana Daga Tsaye tace"Sati mai Zuwa zamu kuma Asibiti ayi miki Scan..Sa"adiya ina Farincikin Haduwa Dake ta sanadinki Zan kara Zama uwa akaro na Biyu aduniya.."Tafada Cikin Wani Rauni Cikin Muryanta Cikin Natsuwa Zaina Tace'Anty Farida a nan Gidan Zan Haihu..? Farida Ta gyada kanta Tana Fadin"Eh Sa"adiya bamu da wani Gidan Dayafi wannan..Duk da zan iya kaiki wani Waje..Ammh dai bari mu gani In Hakan bai Samu ba zan Daukeki mu koma Wani Waje Daga ke sai ni sai ki Haihu achan mu cigaba da kula da Bbynmu Har Zuwa Lokacin da zan maida ke gida.."Zaina Tace"Tare da Zuly zamu koma ko..? Farida Tace"Zuly kuma..? Saboda mene Sa"adiya nan zamu barta Saboda Daman nan muka ganta.."Zaina Tace"Don Allah in zamu Tafi mu Tafi da ita Anty Farida..Yau ta bani Duka Labarinta Akwai Ban Tsausayi Cikin Labarin Maraici Da Rashin Gata ya kawo ta wannan Rayuwar nayi Matukar Tsausayamata kuma na kara Jin Darajan Iyalan Alhaji Tsoho acikin Raina da Tun Da nake Dasu Basu Taba barina na Dandani Maraici Ko Rashin Gata ba.."Take Fada Tana Sharan Kwallah Mirmishi Farida Ta saki kafin tace"Yaro Yaro ne..Yaro man kaza...Ban ce kar kuyi Hira da Zuly ba Saboda na Fi yarda da ita kan kowa na Gidan nan ammh ko Ita ban ce ki Saki da ita ba ina Fata baki Fadamata kina da Ciki ba..? Da Sauri Zaina Tace"A"a Allah ban Fada mata ba."Farida Ta gyada kai Tana Fadin"Yauwa..Kinsan Bariki ba Amana duk yadda kika yarda da Mutum sai yaci Dunduniyarki..Karki Damu in Abun Taimako yazo zan Taimaka mata ammh Ban yarda Ki sakar mata ba,Basu da Amana Kin ji na gaya miki Ina Tsoron ahada baki da ita Watarana acutar Dake." Zaina Ta gyada kai Tana fadin"Shikenan Anty Farida..Ammh ke yau zaki bani naki Labarin..? Farida na Dannar Wayarta Tace"Ki bari Insha Allahu gobe zan Fada Miki Komai tunda ba inda Zani.."Kada kai Zaina Tayi Tana kallonta ta Dauko wani mgani Ta balla Tasha da Ruwa Sai bayan Ta sha ne ta koma kan Gado Ta kwanta Daman Tun Fitan Zuly Ta sakama Kofar sakata Cikin Lumshe ido Tana Dafe kanta tace"Ib kin gama Chan Ice.Cream din Kizo ki kwanta Sadiya na dawo da Ciwon kai.." Zaina Tace"Allah ya sauwake..Ammh ya kamata kije asibiti Anty Farida.."Tace"Zan je..Ammh nasha mganin Hawan Jini ina jin Bp ne ne ya Daga.."Cikin Wani Tsausayawa Zaina ke binta da kallo ashekarun Farida bai Dace ace Tana Da Hawan Jini da Ciwon Zuciya ba ammh Wahalan Rayuwa da kuma yanayi ya Jefata Cikin wani Hali. Zaina Ta Dade batayi barci ba Bayan Tagama Shan Ice Cream Dinta Daga kan Kujeran Datake Zaune Data Runtse ido sai Dai Taga Rayuwarta da Firstlove Tana Gilma mata Allah sarki Haka Take Fadi Tana Shafa Cikinta Hawayenta na Zuba Cikin Muryan kuka Take Fadin"Ka yafemin Firstlove..Nasan aduk Inda kake yanzu kana Cikin Damuwa da alhinin Barinka da nayi alhalin nayi maka alkawarin bazan Taba Barinka ba..ba saboda komai na barka ba sai saboda Kauce ma ganinka a matsayin Mijin Dina na Biyu kuma nayi Nesa Dakai ko Zuciyata Zata Farfado Daga Raunin Datayi na uku kuma na Kula da Abunda Ke Cikina Duk da Umma Soyayyah da kauna ta Nunamin Ina Sonka Firstlove ina so na Tsira da auranka akaina Koda Hakan bazai amfaneni ba."Take Fada Tana kuka Farida na kwance Tana Jinta sai Ji tayi Tace"Bazaki Taba barin ma Wata Mijinki ba Sa"adiya Tun da dai yana Sonki kuma bai Juya Miki baya ba..Yaci amanarki ammh kada ki girmama Cin Amanar nashi na Tabbata ya Hadu da Shedancin Mata Gobe da Safe acikin Labarina Zaki Fahimci Gwara Namiji yaci Amanarka ta Bangaran Rayuwa Da yaci Amanarka Ta bangaran yarda da Amanar da ka bashi Ammh Rana Tsska ya manta Dasu yayi Fatali Dakai ya kuma Kiraka da Munanan kalmomi Saboda Abunda yagani ba Zahiri ba.."Kawai sai Ta jita Tana Shawaran kwallah sai Zaina Taji ai ita kukan Dadi Take yi Da Sauri Ta Share Hawayenta Ta Mike Kazan Cikin ledan Ko Ta bata batayi ba ta Bude Fridge ta sakata Ta Zo Gefen Farida ta kwanta Tana Fadin"Kiyi Hakuri Anty Farida ki Daina kuka..Nima kamar yadda kikayi alkawarin kula dani Har ki maidani gida Nima zan Kula Dake kamar yadda kanwa Zata kula da yayarta Bayan kin maidani Gida bazan bari ki kara Dawo ma Wannan Rayuwar ba Kema zan Kokarta na Rakaki har Gaban Danginki.." Cikin Daga Murya Farida Tace"Bazan Taba Komawa ba..Koma zan koma garesu sai dai naje musu Ziyaran gani da Ido A matsayin Cikakkiyar KARUWA mai Lasisi,"Tafada Tana Jin wani Bakinciki acikin Ranta Tana ganin Ranar da Abba ya nunata da yatsa yace Karuwa bazata Zauna na mai agida ba Tunda ta kashe Auranta Shima ya sallamata Ta Tuna sanda Anty Take ta kuka Tana Rokon Abba ya Tsaya yayi Bincike yaki Sauraranta Ta Tuna Sanda Mami ta kalleta Tana Zubar da kwallah Tace Kin Cuceni Farida Ashe Dankon Karuwa nayi na Tsawon Wata Tara aciki kuma nayi Nagudarta..? Tir dake da Auranki kike Karuwanci..? Allah ya sakama Musbahu.." Tuna Haka Yasa Farida ta Saki Bakinta kawai ta Fashe da wani kuka mai Cinrai Zaina ta Tsorata Ta Mike Zaune ta Rikota Tana Fadin"Anty Farida Don Allah ki Daina kuka.."Jin Muryan Sa"adiya yasa kawai ta Fada Jikinta Ta Rumgumeta Tana Fadin"Nasani Rashin Gogggo Ce aduniya na Tsinci kaina awannan Rayuwa yau da ace Goggo Fatu nda Rai na Tabbata Da yanzu Rayuwata bata Koma haka ba..Allah ya jikanki da Rahma Goggota Allah yakai Haske kabarinki Da Kina Raye ke kadai ce Zaki Fito ki gayama su Abba Aisha Farida ta ba Karuwa bace Wannan Sharri ne kuma Kazafi ne."Tuni Zaina Ta Fara kuka Itama jin Abunda Farida ke Fadi Faridan ma kukanta Take kamarzata Shide Zaina Tana kuka Tana Fadin"Anty Farida kece fa ke Hanami kuka indan inayi kece mai Sharemin Hawayena..Don Allah nima Ki bani Dama na Hana Hawayenki Zuba.."Da Sauri Farida Ta Dago kanta Bayan Ta Mike Zaune kan Gadon Idanuwanta sun kala Sun Jajir Tana fadin"A"a Sa"adiya Kiyi hakuri ba zan iya Miki wannwn al'farman ba Ki barni nayi kuka in ina Cikin Wannan Halin wlh Kukan ne Kadai Jin Dadina Wayyo kaina..Wayyo Kirjina Wayyo Zuciyata Ina kewar ya"yana ina Kewar Hassana da Usainata Ina Kewar Al"ameen arif dina Ina Tunanin Wani Hali Suke Ciki..? Kila ma Zubaida ta Kasheminsu Tunda bata kaunata ta Tabbata Bazata kaunaci Abunda na Haifa ba.."Take Fada Tana Sulalewa kasa Ta wani Dunkule Tana kuka kawai Gefe Zaina Ta koma Itama Tana kuka wannam karon ba kukan Tsausayin kanta Take ba Kukan Tsausayin Uwa Wacce aka Rabata da Ya"yanta Allah Sarki Anty Farida Lalle Kinga Jarabawa. Ranar haka sukayi kwanan kuka ba mai iya Lallashin Wani Daga Baya Farida Tatashi Taje Tayi alwala Tazo Ta Fara sallah Tanayi tana kuka Bayan Ta Idar ta Daga Hannu sama Tana Fadin Allah na Tuba Allah ya femin Itama Zaina alwalar taje ta Dauro Itama tazo Tabi Faridan Sallah itama Tanayi tana kuka tana kuma kallon Farida Da Hannunta ke sama Tana Ta Fadin Allah ta Tuba,Tun Zaina na Zaune kan Sallayar tana kallonta Har Barci yaci Idanuwanta ta koma ta Kwanta nan kasa Sai da Farida ta gama Duka addu"anta kana ta Tada ita ta koma Bisa gado ta kwanta Ita kuma gefen Gadon Ta Jingina Tana ajiyar Zuciya Tana Tuna sanda Taje bayi Tayi Kakin jini kenan ciwon Zuciyanta yana neman Tashi kenan..? Ta samu wani Salama Saboda kukan da tayi. ****** Kamar yadda Zaina ta kwana tana Kuka haka Zain shima ya kwana yana kallon Duka Hotunan Zaina yana kuka kuka mai Cin rai da wani Muradi mai Girma,Wasikarta Tana Hannunsa awajen Haddir ya karba Da ita yake kwana da ita yake tashi ya gama Haddace Duka kalaman Zaina na Ciki In ya Tuna Zaina nada Ciki sai yaji Rauninsa ya kara Karuwa,Yana kuka kukan Tsausayin kansa da kuma Kukan Tsausayin Halin Da Zaina Take ciki Da kuma kukan Nadaman Abunda ya aikata ya Tabbata Da Bai Zama mai aikata Zina ba da Duk Haka bata faru ba Gashi yanzu Auransa da Dina Dole ana kuma Nufin da ita zai zauna..? Wlh Tun Da yake da Dina bai Taba Sonta ba Sai Sha"awarta To yanzu Faruwan haka ma yasa yaji kamar komai ya Fita kansa Baya son ganinta in ta Shigo gaishesa yaga wannan Cikin sai yaji kamar shima gobe a nemeshi arasa sai dai bazai yi Sanadiyar saka wani Raunin azuciyar iyayan nashi ba Ammh yayi alkawarin Da kafarsa da kudinsa Sai ya Nemo Firstlove Duk inda ya kamata acikin Duniyan nan sai ya Nemeta yaji ya Dauki Dukkan Kaddaransa Zai Tashi Tsaye Da kafarsa Ranar Monday zai Koma aiki Insha Allahu Tun Daga Ranar zai Fara yawon Neman Firstlove zai Fara da Cikin garin Bauchi Da kewayanta kafin ya Fita Zuwa garuruwan Dake Makota dasu Batare da kowa ya sani ba shi Zai je ya Dawo da Matarsa da Cikinsa Kodomin ya samu Natsuwa ammh ya Tabbata Matukar Firstlove bata Cikin Rayuwarsa kamar kawai gangar Jikinsa ne ammh Ruhinsa da komai suna Tare da ita ne. Shima Daga Karshe alwalan ya Dauro yazo yana ta Sallah yana Rokon Allah ya Bayyana mai Firstlove aduk inda Take Ya kuma kareta ya Tsareta Har Zuwa Lokacin da Zai sameta,Haka ya Dinga addu"a yana kuka yana gayama Allah Shima nan kan Sallayar Barci ya kwasheshi. **** Washegari da Safe Farida Tatashi kamar ba ita ba,Ammh Daga ganinta bata da Walwala Tea ta Hada musu suka Sha,Kana Zaina taci Sauran kazanta Ta Jiya Ta Dora da Maltina Tana ta Jin muryansu Suby a tsakar gidan ammh bata ji Motsin Zuly ba Ganin Tayi Zuru ne yasa Farida Tace Mata"Zuly bata kwana agida ba...Kacharalle yayi kawalinta karki Damu Zata samu Abunda Zataji achan kici ki Koshi Saboda bake kadai bace.."Jin haka yasa ZAINA taci Ta Koshi Ta Kora da Maltina. Dukkansu sai da sukayi wanka yau Shigar Atamfa Dukkansu sukayi Cikin kayan Farida ne Zaina ta saka Tunda bata Siyamata Atamfofi ba sai dai kayan Kanti,Farida ita ta Share Dakin Tas ta kai Bolar Waje Zaina na jinsu Adamalle na Mata Gudan Da Kirari Sholloy ke mai kyau ce komai kika saka sai ya karbeki So suke ta sakar musu sai dai kuma basu samu dama ba Ta koma Daki ta barsu nan suna Gulamta da kuma Gulman Zaina Suna mamakin yadda Farida ke Ji da Zaina Da taki barinta Har yanzu Kowa yana ganinta da kuma mamakin yadda Uwar mata ta kyaleta basu san Farida Ta koma ta Tura ma Uwar mata Kashi Biyu Cikin ukun Abunda Take samu Wajen Maza Saboda Idanuwan Uwar mata yafi ta kan Zaina ya kuma Fita Domin Tuni bakinta ya Mutu Daman Burinta kudi ne kuma Sholly Ta Gama da wannan Bangaran. Sai bayan Sun gama Komai kana Farida Ta ja zaina suka zauna kan gado Suka Tankwashe kafa wayarta ma kasheta Tayi Kana ta kalli Zaina Tana Fadin"Zan baki Labarina..Ammh keman alkawarin bazaki kuka Sosai ba..! Da sauri Zaina Tace"Nayi..I promise Anty Farida.."jinjina kai Anty Farida Tayi kafin Ta Lumshe ido Ta Bude Cikin Sanyin Murya Ta Fara Fadin... "Sunana Aisha Farida kamar yadda kika sani.... *Ki biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki saka kudi ki Siya Abu kuma ki Yadashi a waje..Mace mai aji komai nata mallaka ta ke bata Taba Jiran Abun Sata...!* *Janafty...* 7/12/21, 9:14 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣6️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*            "Kuma ni Haifaffiyar garin Jahar Gombe ce,Mahaifiyata Ummu Salma wacce muke Kira da Mami Yar Gombe Ta uwa ta Uba Mahaifina Alhaji Abubakar Shehu Dan asalin Jahar Jemeta ne Dake Yola,Kinga kenan Mahaifiyata Bafullatan Gombe ce Mahaifina kuma Bafullatanin Jemeta ne Ta Gaba da Baya ni din na gaji Fullanci Ta ko"ina. Mahaifina Alhaji Abubakar Shehu Wanda muke Kira Abba Su Biyar ne wajen Babansu,Mata Biyu Maza Uku,Baffa Haruna ne babba sai Abbanmu sai Baffa Umaru sai Goggo Fatu,sai Goggo Zaliha su Uku Dakinsu Daya Wato Goggo Zaliha da Baffa Haruna da Baffa Umaru Tsohuwa Gita ita ta Haifesu mu kuma Abbanmu da Goggo Fatu Tsohowa Kaltume itace Mahaifiyarsu. Tun kafin Rasuwar Mahaifinsu ya kafasu Tunda asalin Babban Gidansu Gidan yan Boko ne Ko alokacin Alhaji Shehun ya Rike mikamin Manaja a ma"ikatar Nepa Ta Jemeta Shiyasa su Abba suma suka Kasance masu Ilimi ammh su Goggo Fatu Suna Gama Sakandiri ake aurar dasu. Dukkansu suna Jemeta da Zama ne Illah kawu Umaru Dake Zaune da iyalansa a Yola yana aiki da gidan Ruwa na Jahar sai Abba Dake aiki a hukumar Inec ta Garin Gombe,kuma ma agarin Gomben yayi karatunsa anan ma ya Hadu da Mamin mu har suka Daidaita sukayi aure. Mun Taso mun ganmu muna Rayuwa acikin Katon Gidanmu na Zamani da Wadata Dake anguwan New gra Gombe,Dani Da kanwata Zahra mu kadai Iyayanmu suka Haifa kuma suka Dauki Dukkan Wani Soyayyah suka Dora mana Alokacin gaskiya matsaloli sun Taso kan Rashin Kara Haihuwar Mami har su Baffa Haruna suka matsa sai da Abbanmu ya kara Auran Anty Yahanatu muna Kiran ta Anty Toh itama Tazo ammh kuma Bata Taba Haihuwa ba sai Dangin Abbanmu suka Fahimci Abun badaga Maminmu bane Daga Abbanmu ne,sai sukayi Shuru da bakinsu shi kuma Abba ko ajikinsa Yana ganin Tunda Allah ya bashi mu ya gama mai Komai. Tsakanina da Zahra ba wani Tazaran Nisa sosai Domin Mami Sai da ta Shekara bakwai da Abba kana ta samu Cikina wanda Tun ina Ciki nake ganin gata iri iri Daga Bangarori Da Dama,Lokacin da nazo Duniya kowa ya Shaida da Kanwar Abba nake kama Wato Goggo Fatu Wacce ke aure nan cikin Garin Jemeta Mganar gaskiya Kamana da ita ya baci yadda kikasan itace ta Haifeni Hatta Tsawona Idanuwana irin Nata ne komai da komai wannan Dalilin yasa Allah ya Dasa ma Goggo Fatu kaunata Sosai acikin Zuciyarta Musamman Saboda ni Take Dauko Kafa Daga Jemeta Zuwa Yola saboda Ta ganni Saboda itama Allah bai bata Haihuwa da yawa ba Da"nta kwara Daya ne Dal aduniya Musbahu Har Mijinta ya koma ga Allah sai Mutane ke Tunanin ko sun yi Gado ne Wajen Tsohuwa kultum Tunda itama su Biyu kadai ta Haifa Har ta koma ga Allah. Ban kai Shekara Daya da Haihuwa ba mami ta samu Cikin Zahra,sai da suka je asibiti Likita yace bakomai acigaba da Shayar dani in nakai Shekara Daya da wata uku sai ta yayeni haka kuwa akayi Ban ma kai ga Cika Da wata ukun ba aka Cireni A Nono Ranar Goggo Fatu Tazo Ta ganni Ina ta kuka nakin Cin komai da aka Damamin sai Taji Tsausayi na tace In har Abba ya yarjemata Zata Tafi Chan Jemeta ta yayeni Abba kuwa da Mami suka Hado mata kaya suka Bata Tatafi Dani Jemeta Tafiyar da Ban Dawo ba kenar chan nayi Rayuwata Har na Girma a Hannun Goggo Fatu kuma Ita ta aurar dani Takaini Har Dakin Mijina Allah Sarki Allah ya Jikanki da Rahma Goggo Fatu..! Farida Ta Fada Tana Share wasu Siraran kwallah Dake Zubomata kafin ta Cigaba da Fadin "Na zauna agidan Goggo Fatu Cikin gata da jin Dadin Rayuwa Tun ina rigima har nazo na Saba da ita,Goggo Fatu taci kashina Taci Fitsari na Komai nawa itace Mami kawai Wahalan Cikina Tayi da Naguda na Dana cika Shekara Biyu sai Abba ya nemi da na Dawo Gida ammh sai Shakuwar da mukayi Da Goggo Fatu yasa Mami tace a kyaleni na Kara Girma lokacin ma har an Haifi Zahra wannan Dalilin ne yasa sai bayan na Fara Girma ne ma na Fahimci ba Goggo Fatu ta Haifeni ba. Na Taso Gidan Goggo Fatu Ni da Da"nta kwara Daya mai Suna Musbaha Lokacin Mijinta nada Rai Domin kamar ina primary 4 ne Allah mai yamai Rasuwa sakamakon Hadarin Mota Lokacin Ya Musbaha yana Bording School a yola yana kamar Shekarar Fita Daga Sakandiri School bayan Rasuwar ma Abba yaso na koma Gida Goggo Fatu ta Fara Kuka kan in ya Rabata dani Bazata ji Dadi ba Musbahu ne kuma yana makaranta Ni kadai ce nake zaune da ita Wannan kukan na Goggo Fatu yasa Abbana yace ya bar mata Ni Duniya da Lahira sai dai Mami Taji Labari Daga Baya kuma Bata Nuna komai Domin Tana da kawaici da kunyar Fulani. Haka Rayuwa Ta Cigaba da Tafiya Da Dadi ba Dadi,Duk da Mahaifin Ya Musbahu ya Rasu ya bar Tarin Dukiya su Abba basu bar Goggo Fatu haka ba Duk wata suna Cika mata Store da kayan Abinci Shi kuma Baffa Haruna ya Dauki Nauyin Cigaba da karatun ya Musbahu Bayan ya gama Secondary School Lokacin ni kuma na gama primary Section. Duk a lokacin Gida Daya muka yi Rayuwa bana wani Sakin Jiki da Ya Musbahu Tunda bai Cika zama agida ba sai dai in ya Dawo Hutu koda kuma ya Dawon Kullum yana Cikin Dakinsa yana karatu,ni kuma Allah bai yoni Rayuwa mai Kirniya ba Tun ina karamata Nake da Hankali Koda yaushe indai ina Gida ina Tare da Goggo Fatu a Kitchen ina Koyon wasu Abubuwa awajenta Tsakani Dashi Gaisuwa ne da Girman Tsakanin Yaya da kanwa. Lokacin Daya gama Sakandiri School dinsa sai yace shi baya son Zuwa kasar Waje kamar yadda Baba Haruna yaso ya Tafi ammh Yana Sha"awar karatu a BUK dake kano Wannan Dalilin yasa Zamansa agida bai Dade ba aka gama mai komai ya Tattara ya koma kano da Zama Gabadaya yana karantar Engnearing..! In kika ga naje Gombe nayi kwanaki Har Wajen sati Daya sai dai in Goggo Fatu ce ta matsamin Muka Tafi Tare sai Ta koma ta barni na kwana Biyu wajen Iyayena Tunda suna mata kawaicin ammh Suma suna son Zama Dani Musamman kanwata Zahra,Mukan je Jemeta Family House din su Abba Dani da Goggo Fatu Ko kuma in wani Sha"ani ya Tashi Mukan je kuma Gidan Baffa Haruna Duk da shi Daman Hatta su Goggo Zaliha basu Damu da Zuwa ba Saboda Matarsa mai Suna Salamatu Suna Kiranta Mommy. Matan Baffa Haruna Uku ne kuma Mommy ce ta Biyu ammh kamar ita ke Fada aji acikin Gidan Baffa Haruna yanada Kudi Tunda Dan kasuwa ne Dake Shigowa da kaya da kasashen Ketare,Duka ya"yan Baffa Haruna Maza ne macensa Daya ne Zubaida kuma itace ta Uku kuma Diyar Mommy ce ita kadai Gareta Zubaida ba Sa"ata bace Sa"ar Zahra ne ta Girmi Zahra dai da kadan sai dai Tana da Girman Jiki Shiyasa Har ta Kamoni a tsawo,itama Din Fara ce Doguwa mai kama da Mommy sak tunda itama Bafullatan Adamawa ce chan ya Aurota Cikin Fulanin Daji Shiyasa ake Zargin Baffa Haruna ma Ba Banza ta barshi ba Shiyasa baya ji baya gani sai Mommy da Zubaida Domin gatan Dayake yi mata Ko ya"yansa Maza bai nuna ma wannan Gatan Sauran Matansa Kuwa Hakuri kawai suke ammh kamar Hoto suke agidan Mommy ce Matar so kuma Matar Gida. Tun Tasowar Zubaida ta kwaso Duka Halin Mahaifiyarta Mommy ga rawan kai ga Fi"ili da kuma Isa da Takama Tun Tana karama Take ji da kanta da Nuna ita din Watace Babanta nada kudi kuma Tana makaranta mai Tsada Tana saka kaya mai Tsada Ko cikin Dangi Ta Shiga ta Rika ma Kowa kallon Kashi kashi kenan ko Su Goggo Zalihan Batabari ba Gata bata da kunya Ganin Yarinta Tare da ita Shiyasa ba wanda yabi Ta kanta Da kuma ganin yadda Baffa Harunan bayason Laifin Zubaida komai kankantarsa. Tun asali Daman Jinina Dana Zubaidaa bai Taba Haduwa ba Ta Tsaneni Nima na tsaneta Ko Haduwa mukayi Family House din su Abba a jemeta Tsakanina Da Ita kallon kallo ne Domin Tana Jin Haushi yadda Kowa ke yabona wajen Natsuwata da Hankali Da kuma Rashin kwaramiyaniya,In tazo Haka ya"yan yan"uwa suyi ta Shige mata ammh Ni kuwa kallo Bata Isheni ba Ina Tare da Goggo Fatu ko In su Mami sun zo Ina Tare da Zahra ko kuma Tare da Saratu Diyar Goggo Zaliha wacce Sa"atace. Ashe Abun na Matukar Bakantama Zabaida rai Ganin Ina nuna nafi karfin na Dinga mata mgana ni kuma ganin ita Din ba Sa"ata bace shiyasa bana Shiga Harkanta uwa uba kuma Rashin Kunyata ganin har ManyaBata bari ba Bazan Taba manta Dalilin Daya sa Goggo Fatu Har ta Koma ga Allah bata Kaunar Zubaida ba Shine akwai Wani Lokacin da Bikin Diyar goggo Zaliha ya Tashi Duka Dangi an Hadu agida ana ta Sha"ani Ni da Goggo Fatu mun zo ita ma Zubaida sun zo Ranar Bikin Fada ya Hada Zubaida da Zahra Har ita Zubaida ta Dibi kasa ta watsa ma zahra afuska Mu muna Cikin Gida Ni da Saratu Tunda Lokacin muna yara bamu Zama yanmata ba Tunda muna Jss1 ne alokacin. Ni da Saratu muka Fita mukaje muka Tarar da Zubaida da Zugan kawayenta sun Tarun ma Zahra sai na Shiga na Raba ina Tambayan Zubaidan me ya Hadasu Bude bakin yarinyar sai ta kalleni Tayi Tsaki Tana Fadin Ni kuma awa..? Wai ni a yayar Zahra..? Dama basu san komai bane Ance ba Goggo Fatu ta Haifeni ba ammh kuma da ita nake kama ba Mami ba,waya sani Ko Goggon Fatun ce Mamata ta Gaskiya alokacin Data Fadi mganar karaf akunnan Goggo Fatu Taga Fitarmu Tabi yi sawu,ShineTana Zuwa Taji Abunda Zubaida Take Fadi gabadayanmu kuma muka Zura ma Zubaida ido Cikin Mamakin kalaman Zubaida. Goggo Fatu da Ranta ya baci da kalaman Zubaida Tana Zuwa batayi wata wata ba ta Tsinka mata mari Ta Dungure mata kai Tana Fadin karta kara Jin wannan mganar abakinta in ba Haka ba sai tayi mata Dukan Tsiya,Yin haka keda wuya Zubaida ta Saka kuka Har Da Birgima Tana Kiran sunan Mommy nan da nan Jama"ar Cikin Gidan sai gasu a Haraban Gidan Goggo Zaliha Mommy na Zuwa Hankalinta Tashe Ta Kama Zubaida Ta Tada ita Tana Faman Tambayanta wa ya Daketa Bude bakin Zubaida sai ta Nuna Goggo Fatu Tana Fadin Ita ta Daketa bata mata komai ba Daga Suna Fada da Zahra sai gani nazo na Shigar mata ina ta Dukanta Shine goggo Fatu na Zuwa itama ta mareta. Goggo Fatu ta saka Salati Tana kallon karamar yarinya da makirci Jin Haka yasa Mommy ta Fara Bala"i har tana Zagin goggo Fatu wai kan wani Dalili Zata Dakar mata ya" ai ya bata fi ya,ba sai gayan mganganu Take har Matar Baffa Umaru da Anty Yaha suka Shigar ma Goggo Fatu Wacce ta Fara kuka da cin Mutumci da Mommy ke mata Fadan ya koma kanta Nima Jikin Goggo Fatu na Koma ina kuka ganin Tana kuka,Mami ita ta Kira su Abba awaya ta gaya musu Abunda ke Faruwa Shi kuma yagaya ma su Baffa Haruna nan da nan sai gasu Lokacin Har Goggo Zaliha Ta ce Mommy Ta Tarkata yarta su bar mata gida ba"a auri Wata macen Daga wata Zuru"a tazo Tace Zata Taba mata yar"uwa ba Bata isa ba. Kalaman Goggo Zaliha sukayi Zafi Mommy na gayan mganganu Ta zari mayafinta Rike da Hannun Zubaida Zasu Tafi sai gasu Abba nan fa aka Fara Maida Zencen Abun mamaki Mommy na ganin Baffa Haruna Ta fara kuka Zubaida nayi Hankalinsa ya tashi ya Nufeta yana Tambayan Ba"asi Goggo Zaliha namai mgana bai iya Saurareta ba Mommy yake Saurara Tana kuka Tana Fadin Goggo Fatu ce Ta Daki Zubaida bata Mata komai ba Saboda Ni,Shine Saboda Tazo Tayi mgana Cikin lumana Matar Baffa Umaru da Anty Yaha suna ta Zaginta Har goggo Zaliha Tana ce mata ta bar mata gidanta ita da yarta Tana Fada Tana kuka,Abun mamaki maimakon Baffa Haruna ya Tsaya yayi Bincike a"a sai kawai ya Fara Fada yana Zagin Goggo Fatu yana Ce mata Meyasa Zata Daki Zubaida a kaina..? Mganganu dai na Cin Fuska da Cin Zarafi kamar ba yar"uwansa ba ya tsaya ma ya Saurari su Goggo Zaliha yaki itama Daga baya Fata fata yayi mata ya kuma ce Duka iyalansa su Tattaro su Tafi Tunda Haka Goggo Zalihan ta Bukata nan fa Gidan Biki ya koma wani iri Baffa Haruna bai Saurari Kowa ba sai  Mommy ita kuma ta kulla Abunda zata kulla  ba wanda ya Hanashi Tafiya Suna Tafiya Goggo Fatu na kuka ta kwasheni muka TafiGida Duk da Rokon da su Abba sukayi ta mata ta Tsaya Bakincikin Abun yasa ta kasa Tsayawa Har muka koma Gida Tana Sharan Hawaye Tana Jinjina Abun Wai yau ace Dan"uwanta ne zai ci Zarafinta saboda Matarsa da yarsa Lalle Duniya ce Tundaga Lokacin Goggo Fatu ta Fita Sha"amin Gidan Baffa Haruna Shi kanshi sun Dade basa wani gaisuwan Zumunci sai Da su Abba suka Hadu suka Sulhuntansu Ammh Goggo Fatu Ta Rike Abun acikin Ranta ta kuma Daina Zuwa Gidan Baffa Haruna Ballatana wani Hulda ya Hadata da Mommy da yarta suma ba ZUWA suke ba sai Kowa ya Zauna a matsayinsa. Kwanshi Tashi ba Wuya awajen Allah Ina SS1 Ya Musbahu ya gama Digree dinsa ya Dawo Gida Daman In ya samu Hutu bai cika Zuwa ba kano yake Zamansa Tunda shi ba Mutum bane mai Hayaniya Lokacin Da aka Turashi Service dinsa jemeta aka Turasa A hukamar Lantarki ta Jahar Dalilin haka yasa Baffa Haruna yace ya Koma Gidansa ya zauna tunda  ma"aikatar Tana kusa da Gidan ne, hakanFiyemai ya kama Haya ba yadda zai yi Domin Shi Musbahu asalinsa Bamai son Hayaniya bane ko Gidan Goggo Fatu bai cika zama ba Ballatana wani Gida,Dalilin yana Jin kunyar Baffa Haruna yasa ya Koma Gidansa da Zama aka Ware mai Daki Guda Da ababen More Rayuwa. Tun Dawowar Ya Musbahu Gidansu Zubaida Shikenan Tunda ta kyalla Ido Ta ganshi ya Shiga Ranta Dama ganinta Dashi Bai wuce sau Daya ba Gaskiya Shima a Family House dinsu Abba Lokacin ma Tun kafin ya Tafi Kano ne kuma afizge ta gansa,ammh yanzu Data gansa taga ya kara Girma kyansa ya Fito Da Zatinsa da Haibansa Hade da Duka kwarjinsa,In ka gansa Alokacin sai ka kara Kallonsu Domin Duk inda ake Neman gaye mai kyau da Haiba aka samu Musbahu anzo karshe,Gashi Miskili mara son Hayaniya. Tun daga Lokacin sai Zubaida ta Fara Shigemai da sunan Zai Dinga koyamata karatu Mkaranta Tun yana Basar da ita har yazo yana Dan Kulata Darajan Baffa Haruna ammh Shi kanshi Bayason Tana yawan Shigemai,Mommy kuwa Tasan komai Tunda Zubaida bata aiwatar da komai sai da Izininta Sai wani Jin Dadi Take Domin Musbahu Namiji ne wanda Ko wace Uwa Zatayi Fatan ya zama Surukinta. Zubaida Tayi iya Bakin Kokarinta ganin Musbahu Ya Fara Shiga Tarkonta Kuma Tayi Nasara Domin ashekara Dayan Dayayi agidansu suka Shaku Har Musbahu zai zauna yana Hira Sosai da Zubaida suci Abinci Tare har fita suna yi Tare,Lokacin da ya gama Bautar Kasar nezai koma Gida Domin Cuku cukun Dora Masters dinsa wanda ya nuna ma Baffa Haruna Ba aiki yake so ba yanzu Karatunsa zai Dora Da zai koma Gida haka Zubaida ta Dinga kuka kada ya Tafi a kuma Lokacin ne ta Furtamai kalmar Tana Sonsa Duk da alokacin ba wani Sonta yake ba sosai ammh Yana Sonta kuma tana Burgeshi Sai ya karba mata Tayin Soyayyarsa ammh Da Sharadin bazasu bayyana ma Iyayansu ba sai da Ta gama Sakandiri School dinsa Shima Lokacin ya gama Masters dinsa. Da haka sukayi Shuru da bakinsa har Musabahu ya koma Gidan Goggo Fatu Suna Cigaba da Soyayyarsu Da Zubaida ta Waya Batare da Goggo Fatu ta sani ba,sai bayan ya Koma BUK kano ne Yin Masters dinsa Mganar ta Fita Kuma Mommy ce ta Fitar da ita Tana wani Fi"ili ga sauran Matan Baffa Haruna Tana fadin Zubaida Zata Auri Musabahu ai hakan ya kamata Tunda Ai shi Baffan Haruna shi yayi ta Wahala da Musbahu gwara Ya auri yarsa Ko ya Famshemai Wahalarsa Mgana Tai ta Zaga Dangi Har tazo Kunnuwan Goggo Fatu ta Bakin Goggo Zaliha wacce Tatako da kanta Tazo Ta Fada mata Abunda ke Faruwa tace Itama abakin Matar Baffa Umaru Taji itama tace wajen Matan Baffa Harunan taji Zencen suka ce Mommy ke Ta Fadin mganar. Goggo Fatu na Jin haka Ta Daka Tsalle Tace Musbahu bazai Taba Auran Zubaida ba Aisha Farida zai aura gatanan itace Matarsa Tuni na Hanata Kula kowa shi nake ma kamu ammh Ya auri Zubaida sai dai bayan Ranta Goggo Zaliha tace Tana Bayanta Ba Saboda kowa ba sai Saboda Mommy Matar bata da Hali mai kyau Batare da Goggo Fatu ta Jira Kowa ba Ta Kira Musbahu tace yazo Gida Tana nemansa Yana Zuwa ta Zaunar dashi Ta gayamai Wlh sai dai In bata da Rai Zai auro mata Zubaida Ammh ya sani Indai Tana Numfashi Aisha Farida ce Matarsa Baya iya ma Goggo Gaddama ammh yaso ya Nuna mata Zubaidan yake so ba Aisha Farida ba Goggo Fatu Bata Tsaya ma Sauraransa ba Tatashi Ta bashi Waje. Da Farko yaso ya Hakura ya bi Abunda Mahaifiyarsa ke so sai dai kuma Yana son Zubaida Aisha Farida kuma kanwa ya Dauketa kuma ba Wata Shakuwa atsakaninshi da Ita Damuwa tamai yawa ya kasa Boyema Zubaida ya gayamata Tun da Taji haka ta tashi Hankalinta Tana kuka Tana Komai Tana gayama Mommy Ita kuma Tace Abunda bata yuyuwa kenan ta samu Baffa Haruna Tana gayamai Cewa ga Sakayyar Da Goggo Fatu zata mai Bayan ya gama Gina mata Rayuwar Danta Shine zata ce Bazai Auri Zubaida ba Sai Aisha Farida shi bama san mganar ba sai Lokacin da Farko ya yarda da mganarta ammh da Suka Hadu da Baffa Umaru ya Nusar dashi ya Tuna da Zumunci dake Tsakaninsa da Goggo Fatu Tunda sunyi Jinkiri Basu Furta ma Har Goggon Fatu ta Rigasu Furtawa sai dai Yayi Hakuri Musabahu ya auri Aisha Farida Allah barshi Daga Bayan sai ya Auri Zubaida.. Mgana Tayi Tsamari Domin Zubaida Harda kwanciya asibiti Saboda Damuwa Ni sai alokacin ma naji Labarin Abunda ke Faruwa Nima bani da Tacewa Domin ban iya Tsallake mganar Goggo Fatu,Bayan an sallami Zubaida Family House din su Abba aka Hadu gabadaya Harda Ni da Musbabu da Zubaida Inda Baffa Ya Dinga neman alfarman Goggo Fatu ta yarda ayi auran Mu Dani da Zubaida rana Daya da Musbahu Ganin Halin da Zubaidan ke Ciki Goggo Fatu ta Mike gaban Kowa da kowa tace Wlh sai dai bayan Ranta ammh Da Ranta Musbabu Bai da Wata Mata Face Aisha Farida har yau har Gobe Tana kallon Hoton Abunda Zubaida da uwarta sukayi mata Shi kuma ya Goyi Bayansu Bazata iya Juran ganinta a amtsayin Surukanta ba Tana kuka ta Fice Daga Dakin Jikin Baffa Haruna sai yayi Sanyi Abba na gefe bai saka baki ba ganin Hardani aciki ake mgana Ya Musbahu sai ya Fara mamakin meya faru ne...? Goggo Zaliha ce Ta zaunar dashi Ta sanar dashi Komai Tundaga Lokacin Yaji Zubaida ta Fitarmai akai Yaji ya Tsaneta Tunda ta Saka Goggo Fatu kuka ya koma Gida ya Roki Goggo Fati gafara ya kuma ce zai aureni Insha Allahu Goggo Fati taji Dadi Tana ta sakamai albarka Musbahu bai yarda ya koma Kano ba sai da ya san yadda yayi Ya Tusamin Sonsa Daman chan yana Burgeni kawai Rashin Samun Fuska ne yanzu kuma da ya nuna ba wata sai Ni,nima sai na saki Jiki na Nuna mai Shi nake so. Koda ya koma kano Soyayyah Ruwa ruwa ta wayar Goggo Fatu muke waya Koda yaushe sai dai in Yana karatu,Ba"a Saka manq Rana ba Sai da ya Fara Defence dinsa kana aka Tsaida Lokacin Bikin mu in na gama Makaranta nan da Shekara Daya Lokacin ya Musbabu ya gama Karatunsa har ya samu aiki. Baffa Haruna Sai Lokacin ya Dinga Nadamar Abunda ya aikata su Goggo Zaliha da Baffa Umari suka Goyi Bayan Goggo Fatu Abba ne ma yaje har Gida ya Roki Goggo Fatu ta bari ya auremu Duka tace sai dai in bata Raye Dole ya bar mganar Mommy da Zubaida suna Ji suna gani aka sanya Lokacin Bikina da Musbahu basu da yarda zasu yi ammh Mommy tayi alkawarin ko Zatayi yawo Tsirara Sai Zubaida ta Auri Musbahu Ko da Goggo Fatun Zata Rasa Rayuwarta za"ayi Bayan Ranta kamar yadda tace din. *Ki biya ki karanta Cikin Salama Mace mai aji bata Jiran Abun Sata mallakan komai nata Take..Rashin Daraja ne ki Siya abu da kudinki ki mai Dashi kamar Gwanjo ko wani Haja Mara Daraja..* *Janafty....* 7/13/21, 4:34 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣7️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*                "Sai da Mommy ta Taso da mganar ai shi yayi ma Musbahun komai har ya kawo yanzu ya kamata shima ya rama mai Abunda yayi mai sai alokacin Baffa Haruna ke Fadama Duka Matansa harda Mommy din Cewa duk Abunda yayi ma Musbahu bada kudinsa bane akwai Dukiyan Musbahun Da Yagada Wajen Mahaifinsa Tunbayan Rasuwarsa Goggo Fatu Ta dankamai komai a Hannunsa Tace tana Bukatar ya cigaba Da Juya Dukiyar har Zuwa Lokacin da Musbahu Zai mallaki Hankalin kansa ya maida mai Dukiyarsa kuma ayanzu Haka cikin kashi Uku na Abunda ya mallaka Kashi Biyu Gadon Musbahu ne kuma Duka yan"uwansa Duk sun sani Tunda agaban Idonsu akayi Domin su Zama Shaida. Jin haka sai Jikin Mommy yayi sanyi bata kuma da tacewa ammh Hankalinta ya tashi Ganin Halin da Zubaida ke Ciki Ta Rame ta lalace Saboda Rashin Musbabu shiyasa tayi alkawarin ko Zatayi yawo Tsirara ne sai Musbahu ya auri Zubaida Domin ko Ita Bata Nemi Abu ta Rasa ba Haka Zalika ma yarta bazata Taba Neman Abu ta Rasa ba. Ni kuwa Soyayyah Tsakanina da Ya Musbabu sai wanda ya gani Sai na Fara Tunanin Daman chan muna son Junanmu,kawai Rashin Sakar ma Juna Jiki yasa muka kasa ganewa,Shima haka yace min Ya tabbata ni yake so ba Zubaida ba,Kafin Shekaran Daya da aka Dibamana na Auranmu wata Shakuwa da Soyayyah mai Tsanani ya Shiga Tsakanina Dashi Bana iya Boyemai komai shima haka Goggo Fatu kuwa tafi Kowa Farinciki ganin Mu Hada kanmu yanzu Baya wani Dadewa Karkari yayi sati Biyu a kano zai Dawo Gida Har Gombe Munje Tare Abba da Mami da Anty nata saka mana albarka. Ana Saura Wata Biyar Bikim mu Ya Musbahu ya kamallah Masters Dinsa ba bata Lokaci Kuma ya samu aiki inda yayi Bautar kasarsa wato Hukumar Wutar Lantarki na Garin Jemeta Dama Tuni suke so su rikesa sai yakizama akan cewa zai koma karo karatu yana gamawa kuma suka Daukesa kuma da Babban Ofishi da kuma albashi mai Tsoka,ganin Bikinmu na gabatowa yasa Goggo Fatu ta Tara Su Abba dasu Baba Umaru da Baffa Haruna tayi mgana kan Dukiyar Musbabu Tace Tunda Nauyi ya hau kansa yanzu Ya kamata Duka Dukiyarsa ta Dawo Hannunsa Ko ya samu yayi wasu Shirye Shirye Cikin Lokaci Baffa Haruna ya gabatar da kudaden da Riban sai Goggo Fatu tace Baffa Haruna ya Raba Riban kashi Uku ya Dauki kashi Daya Ladan Juya Dukiya haka kuwa akayi sauran aka Damkama Musbahu Duka Dukiyarsa Baffanin nashi Kuma suka Bashi Shawaran ya saka Kudin Cikin Banki kafin ya Fara Shawaran Business din da zai yi da Kudade. Da Kudin Goggo Fatu ta saka ya Musbahu ya gyara Filin Gaban Gidansu ya Fitar da Flat Domin tace nan Take so mu Zauna Kusa da ita ni da Ya Musbahu Nima Da naji haka naji Dadi Domin na saba da Goggo Fatu bana son wani Abu ya Rabamu Cikin Lokaci Flat din ya kamallah Tunda ga kudi 2bedroom ne,da Falo sai Kitchen sai Haraban faka Mota wacce Batafi Biyu ba bai da Girma Bangaran kayan Daki Kuwa Goggo Fatu ta Hana iyayena siyan ko Tsinke Duka Ya Musbahu ta saka ya Siyamin Komai Domin tace Itace Uwata Goggo Zaliha kuma uwar Ya Musbahu. Biki Yana ta karatowa Shirye Shirye na kara Kamkama Tun Biki na saura kwana uku baki suka Cika Gidan Goggo Fatu Domin Duka Taron nan Za"ayi shi Su Mami da Anty Tun saurab Sati suke Ni kuma ina Tare da Saratu goggo Zaliha da Zahra sune kawaye ne Tunda bani da wasu Tarkacen kawaye,Ya Musbahu kuma yayi gayyah Domin Daga abokan aikinsa har abokan karatunsa Duka Sun zo Tun ana Gobe Biki a Hotel Duka ya Saukesu. An Daura Min Aure da Ya Musbahu Ranar Wata Jumma"ace 12/05/2018,da Misalim karfe 11am na Safe Inda Baffa Haruna ya zama Waliyin ango Baffa Umaru ya zama Waliyina Muna Cikin Gida Domin Duka Dagamu har iyayanmu nan muka zauna sai ga Labari yazo wai Zubaida ta suma Tana asibiti Bayan Taji an Daura aurena Da Ya Musbahu Daman Mommy da Zubaida basu zo Gidan Bikin ba,kuma ba Wanda ya Damu sai dai Sauran Kishoyoyin Mommy din ne suka zo. Saratu ke gayamin yadda Zubaidan ta Rame ta lalace Saboda Rashin Auran ya Musbahu alokacin matuka ta bani Tsausayi Tunda Daman shi da Kanshi ya gayamin Tana Kiransa Da Lambobi Da Dama Baya Daukan wayanta Tunda ya gayamata Tayi Hakuri bazai iya auranta ba ni zai aura Nidai Allah ya kyauta kawai na iya Cewa Aranar Goggo Fatu da Hannunta takaini Har kan Gadon Aurena Ta Dafa kaina Tamin Nasiha ta sakamin albarka Ta kuma Hada Hannayena da Hannun ya Musbahu tace ko Bayan Ranta bata yarda mu Raba Hannayenmu ba Ranar nayi kuka Sosai Domin naji Daci da Ciwon Rabuwa da kwana da Goggo Fatu wacce nake gani Tankar Uwar da ta Haifeni Duka Iyayena sunmin Nasihan zaman Aure da kuma Hakuri Zuwa Washegari kuma Biki ya Tashi Kowa ya koma Gidansa aka barni Daga ni sai Goggo Fatu Dake Chan Barayinta Sai dai akwai Kofa ta Gidana Inda zai kaini Gidan Goggo Fatu ko Kyakyawan Ihu nayi Zata jini Shiyasa ma sai na kwantar da Hankalina. Bazan Taba mantawa ba Ranar Litini da Daddare Ya Musbahu ya karbi Budurcina Cikin Soyayyah da kaunar Juna Kuma ya Cigaba da kula dani har na Warke muka Cigaba da zamanmu Gwanin Ban Sha"awa in ya Fita aiki da safe ni kuma nagama Abunda zan yi Shashen Goggo Fatu nake zuwa Musha Hiranmu sai Rana Tayi kana Zata kadani naje na Daura Girki Zamanmu abun Sha"awane Domin na riga na gama yardan ma kaina Ya Musbahu Garkuwata ce kuma Bangona ne Domin Komai na jin Dadin Rayuwa yana Min shi Watan mu Biyu da aure muka je gombe muka kwanan musu Biyu Muka je Gidan Goggo Zaliha Har Gidan Baffa Haruna Munje nan ma akace Mommy bata nan ita Da Zubaida suna Adamawa Wajen Danginta,Ban wani Damu ba Tunda ni Daman ba wani Shiri muke da ita ba. Auran mu da wata Uku na samu Ciki Lokacin ma Ya Musbahu na Shirin maidani makaranta ne Samuwar Ciki ne mai Lailayi Wannan Dalilin yasa Goggo Fatu ta Hana na Shiga wata Makaranta Saboda cikin ya bani Wahala yana karami sai da na koma Wajen Goggo Fatu da kwana Tana kula dani Bayan Haka kuma Zahra sunyi candy Tazo Tana Taimakamin Dalilin Dayasa ma na koma Gidana kenan sai da cikina yakai Wata Hudu Cikin na Biyar kana na Fara Dawowa Daidai Alokacin Kowa ya ganni sai yayi Tunanin Cikina yakai Wata Takwas Mamaki Mutane suke in sukaji Labarin Cikina Iyakarsa Wata Hudu ne. Cikina nada Wata Shida Goggo Fatu ta kwanta Rashin Lafiya Daga Dare Zuwa safe tatashi Da Laluran sai dai a kwantar a Tayar Wannan Halin Data Shiga Ya Dagamana Hankali Ni da ya Musbabu Wajen Watan ta Biyu asibitin Jaha ammah ba wani Cigaba Mutane suka Dinga bada Shawaran Adawo da ita gida ayi na Hausa bayan an Dawo Gidan an Fara na Gargajiya Shima ba wani Cigaba Domin Goggo Fatu ta Daina mgana sai kawai tabi Mutum Ido Tana kwallah. Wata Mata aka Samo Ya Musbahu na Biyanta Duk Wata Tana kula da ita Tunda ni gani nayi Nauyi Cikina yayi Girma sosai Su Abba suma ba"a barsu abaya ba Duk inda sukaji wani Taimako Zasu nemo su kawo a Jaraba Babu Wanda bai zo Duba Goggo Fatu ba sai Mommy Da Zubaida wanda ni kaina Sai da nayi mamakinsu ganin Irin Halin Da Goggo Take ciki Ta Daina ma gane wanda ke kanta ammh Mommy Bata Leko ba Duk da ance Ita kadai Ta Dawo Ta bar Zubaida Chan Adamawa wai Saboda ta samu Kwanciyar Hankali na kwana Biyu Shi kuma Baffa Haruna Daman bai da Ta cewa. Watarana Ranar da bazan Taba Mantawa da ita ba Cikina ya Shiga Wata na Tara Har Lokacin Zahra na Tare dani Alokacin Goggo Fatu tana watanta na Hudu da Rashin Lafiya kenan Ranar wata Jumma"a da misalin 11am na safe na Baro Sasan Goggon kenan Nazo nayi wanka sai ga Zahra tazo da Gudu Tana kuka ta Kirani Cikin Rudewa Nabi Bayanta Ina Zuwa na Iske Matar Dake zama da goggo, Ta saka Hannu Ta Rufe mata ido Tana Jan Mayafi Tana Rufe mata Fuska dashi Ganin haka yasa na Fahimci Goggo Tatafi Sai naji na kasa Tsayuwa da kafafuna Bansan Wani Lokaci naji ni na Kai kasa ba Saboda Jin Marata ta Murda Ina kuka ina Salati Radadin Mutuwar Goggo Fatu yasa Naguda Tatashi Gadangadan Zahra ita ta Kira Ya Musbahu Dasu Abba ta gayamusu kafin kace kwabo Sai gashi Ganin Halin Dani ke Ciki yasa ya kwashemu Zuwa asibiti ga Mutuwar Goggo Fatu ga Halin da nake Ciki Muna asibitin ya Kira Baffa Haruna ya gaya musu Rasuwar goggo Fatu. Allah Sarki Rayuwa ban iya Haihuwa da kaina ba sai da akayi Min C.S aka ciro Min Ya"ya Guda Biyu Duka mata Ina Kwance gadon asibiti aka Sallaci Goggo Fatu aka kaita makwancinta,nayi kuka kamar Idanuwana zasu makance,nayi kukan Rashin uwa Domin na Tabbata da Tana Raye da yau ban Tsinci kaina Cikin Wannan Rayuwar ba Rasuwar Goggo Fatu ne yasa na Fahimci Itace Gata na kuma itace Garkuwa Gareni. Ba"a sallameni Daga asibiti ba sai Ranar addu"an bakwai naje na Iske gidan Cike da yan"uwa sai Kukan Mutuwa ta dawo Sabuwa,Dakin Goggo Fatu Anty Yaha ta wuce dani nayi ta kuka Ni da ya Musbahu Domin mun Tabbata Munyi Maraici,Saboda Rasuwar Goggo Fatu yasa Bamu yi wani Suna ba Ya Musbahu yayi ma yaran Huduba da Sunan goggo Fatu da kuma Goggo Zaliha ammh zamu rika Kiransu da Hassana da Usaina. Saboda Halin Damuwar da muke Ciki,Yasa Gidan basu Watse ba sai Da akayi sati Biyu kana su Mami suka koma Gida Abun mamaki Mommy Tazo Gaisuwa ammh Fuskarta ba alamamun Jimamin Mutuwar na Goggo Fatu sai ma wani Murna Datakeyi ba wanda dai yabi ta kanta,Anty yaha aka barmin Tana Kula dani Duk da Zahra na Tare dani. Bata Tafi ba sai da mukayi arba"in Ni da su Hassana muka Maida Jikinmu,kana Ta koma Gida,Ta barmu Muna Cigaba da kula da kanmu,Ni da ya Musbahu sai muka koma muka Rungume junanmu Tunda Mun Rasa Goggo Fatu Uwa garemu,Bayan Rasuwar Goggo Fatu ya Shawarci su Abba suka bashi Shawaran ya Fara Sana"ar Motoci Yana Shigowa dasu da wannan Shawaran yayi amfani Ya Fara Sana"ar Shigo da Motoci Daga kwatono yana kawosu nan  yana Saidawa Cikin Shekara Daya sai ga ya Musbahu yayi Fice Yayi kudi na Shahara har ya Bude kamfaninshi na Kanshi,Lokacin su Hassana sun Fara Tafiya Dagani har shi Mun Sauya Rayuwarmu ma ta Sauya Mun bar Gidan nan Ya Musbahu Yagina mana wani Katon Gida mun Koma nan kuma sai ya saka yan Haya Kada abar Gidan Ba kowa,Ya Musbahu ya bani wani Jin Dadin Rayuwa ya Siyamin Motoci ya Budemin Banki Duk wata yana sakamin Kudi Ya maidani yar gata Dani da Iyayena Zahra tana Wajena Ya Sakata Jami"a Ita kuma ya Siyamata Mota Cigaban Rayuwa dai alhamdulillah. Ana Cikin wannan Halin na Fara Laulayin Ciki kuma alokacin ne Ya Musbahu yazo Min da mganar zai kara aure kuma ba kowa zai aura ba sai Zubaida mganar ta Dakeni kuma naji Zuciyata ta Tsinke Zubaidan Da Nadade ban Ji Labarinta Itce ya Musbahu zai aura Da Farko nayi Boren Ban yarda ba ammh sai Ya Musbahu ya Nuna Ko na yarda ko kar na yarda Sai anyi Auran Abun ya bani Tsoro ganin Bayaji baya Gani Ya Siya Mata Mota ita da uwarta sai barin Kudi yake musu Farko da Goggo Zaliha taji tace bazai yuyu ba,Mgana nakai wa Kunnin Abba Shi kuma yace sai anyi Tunda ba Haramun bane,Shi kanshi Baffa Umaru bai so Abakin Saratu nake jin Cewa ba Banza suka bar Ya Musbahu ba yadda aka ciwo kan Baffa Haruna Shima haka aka Ciwo na Musbahu baya Ji baya gani Shine dai Sai ya Aureta. Na Shiga Tashin Hankali ga Ciki Har sai na kusa barinsa ammh sai Mami da Abba suka so suna Ta bani baki da Nasiha Har na Dangana na barma Allah komai ammh Kowa sai yace na Dage da addu"a,Tun Fara mganar Auran ya Musbahu ya Daina Kula dani Ballatana Wani Soyayyah Da Tattalin Juna sai ya maida gabadaya Hankalinsa kan Zubaida Tun kafin ta Shigo nake Fuskantan Canje Canje Daga Wajen Ya Musbahu Ammh Duk na Danne Tunda in namai mgana sai yace wai na sakama kaina Kishi ne kawai Shi bai Sauyamin ba,Dole na Koma Gefe na zama yar kallo Duka Duka Bikin Wata Biyar aka saka anyi Cikina nada Wata Takwas ya Riga ya Tsufa Sa"adiya bazan iya bakin Labarin Irin Yadda Rayuwa ta koma Dani Bayan Shigowar Zubaida Rayuwarmu ba. Tunda Ta auri Ya Musbahu Ta maidashi wani Rakumi da aqala Daman ba Falt din mu Daya da Ita ba Wlh Tallahi Dani da Ya"yana sai muyi Sati bamu sakashi a Ido ba da Farko Yakan Dan Shigo ya Dubamu Daga baya kuma ganinsa ya komai sai Dai In na Fito Haraban Gidan na Jirashi In Gimbiyar ta Rakosa Shima Ina mai mgana Sai ya bata rai yace sauri yake ya Shige Mota ya barni nan Taaye,Tun ina Hakuri ina Hadiyar Bakinciki har na Gaza Tun Ina Boyema Zahra Har ta Fahimta Domin Ya Musbahu sai abincinmu ya kare ba Komai a Store Ballatana Cikin Fridge sai mu kwana Bamu ci ba gasu Hassana sun Fara Tambayan Daddynsu sun Daina ganinsa Ban Tsorata da wannan al"amarin ba Sai da Na Taba Zuwa Shashen Zubaida Wajen Ya Musbahu ina gayamai Bamu da kayan Abinci Komai ya kare agaban Matarsa yayi Min kaca kaca yace Bazai Siya ba Tunda in ya Siya ina kwashewa ina Saidawa wannan Bakinciki yasa na Koma Barayina da kuka ganin Haka yasa Zahra ta Kira Goggo Zaliha Ta gayamata Washegari sai gata tazo Gidan Tayi ma Zubaida kaca kaca Har ta mareta Ta kuma ce In Ya Musbahu ya Dawo yazo Tana Nemansa Tafiyarsa ba Dadewa Zubaida Ta Kira Ya Musbahu Tana kuka ta gayamai karya da Gaskiya wai Cewa goggo Zaliha tazo Mun Taru mun mata Duka ita bazata iya ba ta Tafi Gidansu kafin ya Dawo Gidan Ta tafi Gidansu Koda Yaje chan Gidan nasu Mommy tace bazata Lamunci ana Dukan mata ya ba sai ya Dau mataki haka ya Dauki Zubaida suka zo Shashenmu Yayimin Cin Mutumci Har yana Zgin Iyayena Danayi mgana ya Daga Hannu ya mareni Har sau Biyu su Hassana na kuka suka Tafi Garesa ya Musu tsawa ya Saka Hannu ya Turesu Suka koma Jikin Zahra suka Lafe suna kuka,Aranar nayi Nagudan Cikin Al"ameen na Haifeshi Cikin Halin azaba da Radadi Ina Haihuwa Zahra Ta Daga waya ta Kira Mami ina kuka Ta Fada mata Komai ita kuma sai Ta Kira Goggo Zaliha Ta gayamata ita tazo Taga Halin Danake Ciki Tana kuka tana komai ta kwashemu Zuwa asibiti aka Dubami Dani Da abunda na Haifa Daganan kuma Kai Tsaye,gidanta Ta wuce Dani Tace sai ta Koyama ya Musbahu Hankali,Ita Ta Kirashi da kanta Ta gayamai na Haihu kuma Ina Gidanta ammh Wlh har kwana Biyu da Haihuwa bai Leko ba sai da Baffa Umaru ya Kirashi yamai Fada kana suka zo Tare da Zubaida a tsaye ya Dauki yaron yamai Huduba da al"ameen ya ijiyeshi Ko kyakyawan kallo Ban samu ba ya Wurgamin 100k ya fice Goggo Zaliha sai ta kasa mgana Saboda mamaki Da Tsausyina ko Ragon da aka yanka na Sunan Al"ameen Abbana ya Siya Bayan Yaji Komai ya Dinga Bani Hakuri Goggo Zaliha taso Ta Rikenu sai ya Musbahu yayi Hankali ammh Abba ya Hana Dole bayan nayi arba"in ta maidani Gidansa Bayan Baffa Umaru ya Kirasa ya karamai Nasiha sai ya nuna kamar yaji Shi kuwa Baffa Haruna bama a mganarsa Tunda Shima sai a Hankali. Dawowata Gidan Ya Musbahu sai da nayi Nadama Domin sai da na gwammace dama Raba auran akayi Zahra Daman bata Dawo ba Gidan Goggo Zaliha tace zata zauna Wata mai aiki Mami Ta samomin Take Taimakamin,in kinga Rayuwar da Nikeyi sai Kin Tsausayamin kamar Dukiyar Ya Musbahu Watarana da yunwa nake kwana Nida Ya"yana watarana kuma Gari muke sha sai nafi Wata Bangansa ba sai dai Tashin Motarsa Hakanan nake Zaune ina addu"a Da Bautan Aure da kuma zaman ya"yana Bana iya gaya ma kowa matsalata Tunda ko na gaya Bamai mganin Abun sai ma abun ya kara kwabewa. Addu"a Bata Faduwa kasa Banxa al"ameen nada Wata Tara Ya musbahu ya Fara Dawowa Hankalinsa Ranar daya Shigo Shashena kamar yayi kuka yadda yaga na koma Nida su Hussaina muna Shan garin Rogo yayi ta Kuka yana Fadin meyasa ban gayamai ba Ranar ya Cikamana Store da kayan abinci ya kuma Dauki su Hassana yakai su Shopping ya Siya musu Kayan sawa Kala da kalan da kayan Ciye Ciye al"amin kuwa Da muke Kira areef sai Ranar ya Taba Daukansa Tun Ranar da yayi mai Huduba ganin wannan Abun yasa Hankalin Zubaida ya Tashi Ta Kira Mommy Ta gayamata Komai suka sake sabin Shiri. Ganewa Danayi addu"ata Ce Allah ya karba sai na Dage bana Zama sadaka ne duka ina Kokarin yi Cikin Wata Daya na Fara Dawowa Daidai Rayuwarmu Ta Dawo Cikin Sukuni wata Uku muna Cikin Hadin Farinciki Duk da bawai Zubaidan Ta Kyalemu bane ganin Suna ta asirin Baya Tasiri Daya Kamashi Lokaci kadan zai Sakeshi sai suka sauya Taku suka Koma Makirci. Tuna ana Turama Ya Musbahu Hotona Dani da wani Gaye wanda ban ma Taba gani ba Cikin Mummunar kama baya Bi Takai Har yaso har Office dinsa ake kawomai Hotuna na Nida gayen a Hotel muna Sheke ayarmu Duk wannan Abun Bantaba sani ba nasha Dai ganin Ya Musbahu yazo yana Tambayana ina naje nace mai ba Inda naje,duk bansan Makircin da Zubaida ke kulla min ba sai da Watarana na Tashi Ban Lafiya Ya Musbahu ya kaini asibiti akace Ina da Ciki naga Kamar ya Shiga Rudu har yana Tambayana Daman Ya Kusance ne nan kusa Ni kuma na gayamai Rabona dashi Tun Wata Uku da suka wuce kila Lokacin ne Rabo ya Shiga ammh sai naga kamar bai yarda ba ganin bai min mgana ba sai ban kawo komai ba ban yaye areef ba Na bari sai ya Shekara da Wata Biyu Tukunnah. Rana Ta Biyu da bazan Taba mantawa da ita ba itace Wata Ranar Monday,Ni kadai ce a Ashashena su Hassana basu nan Suna Gida Wajen su Mami Zahra Da tazo Tatafi Dasu,Dagani sai areef kuma Ranar Dakina Ya Musbahu ya kwana Da Safe mun Rabu lafiya ya Tafi aiki Nayi wanka Na Fita Falo na Bude Fridge na Dauki Lemo nasha ashe bansani ba Zubaida ta sakamin mganin Barci Daganan ban san inda nake ba sai Chan Wajen Kimanin Awa Biyar na Fara Jin Duka Kota Ko"ina akaina aka kuka ana Dukana Kaina yamin Nauyi na Bude idona ina ganin Dishi Dishi Cikin Hakane Idona ya Washe Abunda nagani ne ya bani mamaki ina Cikin bedroom dina ne kuma akan Gadona,Gefena kuma Tsaye su Abba ne da Mami da Anty Yaha sai Baffa Haruna da Mommy da Sauran matansa sai Zubaida Saratu da Zahra sai su Hassana da Usaina Areef na Hannun Zahra sai kuka yake hakama Abba da Mami Ya Musbahu ma kukan yake yana Bina da wani Kallon Tsana Cikin mamaki nayi Yunkura na tashi sai na kasa jin kamar wani Hannu ya Rikeni ina Duba gefena naga wani Namiji Kwance Kusa dani Tsirara Haihuwar Uwarsa yana Barci na Firgice zan matsa baya sai Lokacin Nima na Fahimci Tsirara naake naja Bargon da naganshi ajikina ina Kwala kara Wanda yayi sanadiyar tashin Saurayin yana wani Kokarin kamoni ganin ina ta mtsawa ne ina kuka yasa ya Fara mgana yana Fadin Meyasa nake kuka Kullim fa daman yana Zuwa da Zarar Mijina ya Fita kuma ba Hotel din da bama Zuwa,Sharri Dai Kala kala Wanda Saboda mamaki sai da naji Kaina ya Buga,nadai ji wani Lokaci ban dawo Hayyacina ba naji Saukar Duka kota"ina Abba na ne yaRufeni da duka yana yi yana La"anta na Wannan kuma Dan Iskan har ya saka kayansa ya Fice ba wanda yamai mgana Mommy sai Tafa Hannuwa Take Goggo Zaliha da  Anty Yaha sai Kuka suke dasu Zahra Hassana da Usaina suna kuka ganin Abba naDukana sai da Baffa Haruna ya Rikesa ina kuka ina Kokarin mgana na kasa ammh ina Girgiza musu kai Ya Musbahu yaFita yana kuka sai gashi ya Dawo da Hotuna ya watsamin ajikina wadanda ganinsu yasa na kara Zama kamar Zuciyarta ta zama Dutse Domin Abun yawuce Tunanina,Agaban Idona Mami Ta kalleni tace na Cucesu Na kuma Ci Amanar haihuwata da sukayi Tunda ina zina da aurena Agaban Idona Abba ya La"ance ni kuma ya Kirani da karuwa kan laifin da ban aikata ba agaban Idona Ya Musbahu yakalleni yace bai zai iya zama da karuwa ba ya Sake ni saki Biyu ya kuma Janye su Usaina Dake Jikina suna kuka ya kallesu yace Ni ban Chanchanci Zama uwa garesu ba Ni karuwa ce Sa"adiya Mami ta Tace ni Karuwa ce ina karuwanci da Aurena Haka Abbana Basu yarda Dani ba basu Tuna su suka Haifeni ba Haka ya Musbahu Ya aibatani kuma a Gaban Kowa da kowa yace Cikin Jikina ba nashi bane yamin Allah ya isa ya Fice yana kuka tare dasu Usaina Dake kallonna Suna kuka suna Kiran Umma Haka ma Mami taFita Tana kuka Tana Fadin na Cucesu Abba na kuwa kallona yayi yace Tir Dake Aisha Farida Tir Dake Tunda Kika Zama karuwa Kina Karuwanci da auranki Goggo Zaliha ne kadai da Anty Haya suka Karyata wannan mganar da kanwata Zahra Daga Lokacin naji kukana ya kafe kawai sai dai na Zucci su suka Taimakamin na Saka kayana suka Dauke ne Goggo Zaliha Domin Abba yace Har Abada Bashi bani agidan Goggo Zaliha ma Bai barni ba Har Gidan yazo ya Koreni Dagani sai kayan Jikina Ko mayafi ban dashi Goggo Zaliha ita ta bani Dubi Biyar kan naje kaduna Gidan Wata kawarta kafin Komai ya lafa Alokacin Zuciyata Ta Dake naji ai bani da wani Sauran Kima da Daraja awannan Duniya Shiyasa na kama Hanyar na Bar garinmu Da Duka Ahalina na bar Y'ayana da kowa nawa Tunda na zama abun Tur awajensu Direban Daya Taimakamin ya kawoni Zaria a dubi Biyar koda na Sauka na Galabaita ga Ciki ga Tashin Hankali ga yunwa na kwana ina Garagaram ba atasha Kafin Gari ya waye na Jigata Ga Jiri ga Wani Tari Dake Damuna da nayi sai aman jini cikin Hakane na Tsinci kaina a sabon gari Cikin kuma Wannan Halin ne Uwar mata Ta Bugeni da Motarta Ita da kawarta Hajiya Zabba"u. *Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Mace mai aji bata jiran Abun Sata komai nata mallaka take,Rashin Daraja ne ka Siya abu kuma ka maidashi kamar Gwanjo ko wani Haja..* *Shakira....* 7/14/21, 6:29 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣8️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Uwar mata ita ta Daukeni Takai ni asibitin ABU Chika cikin wannan Halin Sakamakon Bakinciki Da Wahalar dana sha yasa Cikin Jikina ya Zube wanda Daman Ko bai Fita ba Ina da yakinin sai na Cireshi Saboda wanda ya Digashi ma ya Shegantashi yace bana shi bane Banga amfaninsa Ba,Shiyasa koda na Farfado na samu Labarin Fitarsa hakan yamin Dadi.. Alokacin ne aka Sanar dani Ina da Ciwon Zuciya da Hawan Jini Lokaci Daya,Sakamakon Bakinciki Da Damuwa da sukamin yawa sai da nayi Wajen Wata Daya asibiti Ina Jinyar Zuciyata Da katon Raunin Dake Cikinta Uwar mata Ita Tayi ta Dawaniya Dani Domin Ranar dana Dawo Hayyacina ina kuka bayan Likita Ya Nuna min Uwar mata da Hajiya Zabba"u mataayin Wadanda suka kawoni asibitin Na Rike Hannunta ina Rokonta Tamin Hanyar na zama karuwa mai Lasisi wacce zata bada Jikinta ga Maxa suyi yadda suka ga Dama da ita Jin wannan Burin nawa yasa Uwar mata Taji Dadi kwarai ta kuma saki Bakin aljihu Tayi Dukkan wani Dawainiyana Har na Warke aka sallameni Direct kuma nan Gidan Tazo dani acikin wannan Dakin Domin da Farko kafin Uwar mata Ta Koma kaduna wannan Dakin Shine mallakinta Abaya. Zaina Dake Matsanancin Kukan Tsausayin Labarin Aisha Farida ta Dago Da Jajayen Idanuwanta Tana Fadin"Nan kuma..? Daman ta zauna anan gidan ne..? Farida Ta Gyada kai Tana Kokarin Sharban Hawayen da suke kwaranyomata Ta Cigaba da Fadin "Asalin Sunan Uwar mata Hajiya Hauwa"u kuma asalinta Batakafiyace Daga Zango Kataf Dake kudancin kaduna Uwar mata Ta kasance Duka Dangin Mamarta Ba Musulmai bane Babanta ammh ya Musulunta Daga Baya Duk da wasu Danginsa basu Musulunta ba toh Tatashi Cikin Wata Rayuwa ne sai ahankali Barowarta da Gida Tun Tana da Kuruciyarta ne Lokacin da Fadan kabilanci ya Tashi a Zangon Kataf Ta rasa Duka iyayenta da yan"uwanta Dalilin Dayasa tazama yar Duniya kenan. Uwar mata Tayi Yawace yawace har a lagos ta zauna kafin ta Dawo Tafa Daga Tafa Ta dawo marabajan Jos,Tafi Shekara Talatin Tana Harkan Bariki..Bariki Ta santa itama kuma Ta san Harkan Bariki Sosai Hajiya Zabba"u kawarta ce A Tafa suka Hadu kuma Tare suka Dawo Maraban Jos sukayi Zaman Dadironsu kafin Uwar Mata Ta kafu Tayi Tunanin ya kamata ta Fara kafa kanta Ta Hanyar Zama magajiyar karuwai mai zaman kanta Tunda alokacin Tayi Harka da Yan Siyasa da kuma Masu Fada a gwannati Sosai. Farko Dawowarta Zaria Gidan Abincin Da kika gani ta Fara Budewa Saboda badda kama In ta Ce Zata Bude Gidan karuwai kai Tsaye Zata iya samun Barazana sai ta Fara da Gidan Abinci Inda Ta Zuba ma"ikata Mata Suma din Duka yan Harka ne,Da Farko yan Anguwar basu Fargaba ba sai Daga Baya suka Fahimci wannan Gidan Abincin kura ne kawai da Fatar akuya Sai suka Fara Boren Dattajian anguwan kan Uwar mata Zata bata musu anguwa Har suka Saka matasan anguwan suka Yi Barna agidan Abincin Uwar mata Wanda yasa Ranta ya baci Takai mganar sama Tunda Lokacin Tana tare da Chairman na Local Goverment alokacin Domin har mganar takai ma Hukuma sai dai kuma Cikin Kwana Biyu Hukuma ta bama Uwar mata Lasisin Zama a anguwan Gwado kuma ba wanda ya Isa ya Hanata Tunda Tana da yanci Ganin Ta samu Wannan Damar Ko Shekara Batayi ba Ta Siya Filin Dake kusa da Gidan Abincin nata ta Gina Gida mai Dakuna 12,kowani Daki Ciki Daya ne sai wannan Dakin akayi shi mai Girma Da kuma Tiolet aciki Saboda Zata zauna aciki na Wani Lokaci. Koda na Hadu da Uwar mata Tana da karuwan dake zama a karkashinta irin su Suby Da Deezee,Da Rufy da ZeeZee duk nan na samesu dasu Gazalatu da Sharifa,Gazalatu Ta Rasu kasheta akayi sai dai aka Tsinci gawarta ita kuma Sharifa Ciki Tayi Ta dawo Dashi Uwar mata ta Koreta Daga Gidanta Domin bata yadda da Daukan Ciki ba ta yadda dai ta Taimakeka ka Samu Kudi ammh duk wata akwai Harajin da zaka Cire mata Zata yi Kokarin Ta Hadaka da manya Mutane ammh Kowani Service kikayi da nata Rabon Aciki domin Haka Tsarinta yake Cikin Lokaci kuma Tayi Suna ta Tara Abun Duniya. Bayan Zuwa ne su Zuly suka zo da su Jido,Deeza da Sarah dasu Kacharalle wanda ya kasance Kwalin mata yake ma Alhazai da Maza wadanda suke Biyansa,Farkon Zuwana Sunyi matukar mamakin ganin Tashi Daya Uwar mata ta Saukeni a Dakinta basu Gama mamaki ba sai da suka ga Tayi Min Sha Tara na arsziki Uwar mata Ta kaini Shooping Ta Siyamin Duka kayan kawan Mata da Kayan Shafe Shafe kafin na Cike wata Daya na Kide kuma na gane Harkan Dama gashi ina da kyawuna na Fulani Cikin Lokaci kadan Uwar mata ta sakani a Hanya Tashin Farko da yan Siyasa ta Hadani Dasu na Dinga Kawo mata kudi Domin suna sakarmin Kudi alokacin bana ma Ta Kudi Zuciyata kawai Ta Kekashe ina Jin Sautin Sadda Abba ya Kirani da karuwa Shiyasa sai naji ai ba kuma wani Abunda ya Rage,wannan Facakan da nake da kudi kuma Uwar mata Duka nake juye mata kudin bana Rage ko Sisi sai ta bani Duka Amanarta Ta kuma Jani ajikinta na Koma yar Gatanta Har tana Kirana Shalelenta. Wannan Dalilin yasa sauran Yan Gidan suka Doramin karan Tsana Sai dai Ni bana Tankansu Harkan gabana kawai nake,Kuma suna Shakkanta Domin bana Daukan Raini Kuma bana neman wajensu kuma sunsan nafi su komai da suke Takama dashi, Sa"adiya nabi Maza ban san iyaka ba kuma Duk nake sona ake Kuma Duk Namijin da nayi Tarraya dashi baya iya Barina Na Tara ma Uwar mata Kudi kuma Nima na Tarama kaina Ina Cikin Shekaru na Biyar da barin Gida da kuma Shigowa wannan Rayuwar ina da Kudi ban sa iyakarsu ba acikin Bankina na wannan Harkan Sa"adiya akullin kwanan Duniya ina Nadaman Rayuwar dana saka kaina ammh da Na Tuna Abunda ya Faru dani sai naji Zuciyata ta kara Kekashewa. Ina Shekara Uku da Haduwa da Uwar mata Ta koma kaduna ta Zama ta bar wannan Dakin nake zaune ciki, bayan ta Kera gidanta achan Ta koma ita da kawarta Hajja Zabba'u wacce suka Tafi makka da Umaru Tare,Ta kuma Bude Shagon sai da kaya da Takalma ta kuma Sauya Motar Hawa,Dalilin Dayasa Uwar mata ta Hana karban Kowacce bakuwa batare da izininta ba saboda Samira mai Room8 ta taba saukar wata bakuwa batare da sanin Uwar mata ba ashe SS ce Bincike tazo yi akwai Case yakai Har kaduna State Cid akan Uwar mata na Safaran mata tana sakasu Karuwanci Hukuma ta kamata sai dani da Hajja Zabba"u mukayi ta Shige da Fice da kuma Sanayar wasu manyan kasa yasa a kashe mganar wannan Shine ma karin Dalilim Dayasa Uwar mata ta bar Garin Zaria sai dai tazo Lokaci Bayan Lokaci Ta kuma kafa Dokar kada Akarbi Wata bakuwa batare da izininta ba. Aranar da kika ganni naje Service ne ni da wani Alhaji Badamasi Dan Chaji a kano yake ammh Iyalansa na Abuja,Yana da Tarin Dukiya sosai kuma Shi so yake ya aureni yana so na bar wannan Harkan ya Aureni ni kuma naki yana kashemin kudi kuma yana Kashema Uwar mata Wacce har kamin kafa yayi wajenta Ya aureni Taki bashi Fuska saboda bata san nayi aure,Saboda Tana samun Dukiya Daga wajena Munje Na Rakashi wani Taro sai kuma aka kiraahi Wata Daga Cikin Iyalansa ba Lafiya Dole ya Wuce Abuja bayan ya Bani Kudade kan na koma Gida sai yazo Shine Dalilin Haduwarmu ammh ba Domin haka ba,ba zamu Taba Haduwa ba. Farida Ta karishe Fada Tana Runtse Idanuwanta Cikin kunnan Zuciya dana Ruhi,Zaina Dake kallonta Cikin Tsausayinta Ta Dago Habarta Lokaci Daya Tana Share Mata Hawaye,itama Farida Hannu ta saka Tana Share ma Zainar Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Ina alkwarin da kikamin na bazaki yi kuka ba..? Zaina Ta Ja Majina Tana Fadin"Ya zanyi Anty Farida..?hakika Labarinki ya Chanchanta ayi mai kuka sosai..Gaskiya Kin Hadu da mummunar kaddara da kuma Sharrin Kishiya,abunda ya bani mamaki Tayaya bayan Kinsha Lemo kika Tsinci kanki Cikin wannan Halin..? Kuma waya Kira su Abba dasu Baffa awaya ya gaya musu..? Farida Ta Sunkuyar dakai Tana Kokarin Danne Abunda ke Taso mata Daga kasan Zuciyarta,Ta Bude Dara Daran Idanuwanta ta Saukesu kan Zaina Tana Fadin"Tunda nasha Wannan Lemon da Zubaida ta sakamin mganin Barci ban kara sanin Inda kaina yake ba nadai san na Sulale nan saman Cafet din Dakina na kwanta Daganan Sai Zubaidan Ta Tattabarda nasha Lemon Daman Tana Labe ne sai Tazo Tajani Zuwa Cikin Bedroom din Tamin Tsirara Sai Ta Fita Bayan awa Biyu sai ta Kira Yaron da ta bama aikin Wanda ake Hada Hotunansa da nawa Ana Turama Ya Musbahu yana Zuwa tamai Jagora Har Shashina Ta kuma gayamai yadda komai zai kamkama Sai ta Dauki areef Dake Barci Ta tasheshi Ya Fara kuka sai ta kawoshi Falo ta ijiye,lokacin yar aikina Bata nan tatafi garinsu Sai ta koma Shashenta sai da ta bar mganin ya Kusa rage karfi ajikina kana ta Daga waya ta Kira Ya Musbahu Tace yazo Gida Shashena wani Abu na Faruwa Yana zuwa ta Fashemai da kuka Tana Fadin daman Ta Dade Tana so Ta gayamai kullum in ya Fita sai wani yazo Gidan ya Shiga Shashena ya Dade kana yake Fitowa yau ma yazo Tunda ya Shige bai Fito ba kuma Tun Dazu Take jin kukan Areef Fadin Haka yasa Ya Musbahu ya Shiga Shashena da Hanzarina yana zuwa ya ganni Tsirara shima Saurayin Tsirara yana kwance ya Rumgume ni kam kam alamar bayan mun gama Shashancin mune mukayi barci Ya Musbahu ya Rude sosai yayi kuka kamar me yaso ya Kiramin Hukuma ne sai Zubaida ta Hana Ta bashi Shawaran ya Kira Gidanmu ita kuma bari ta Kira Baffa Haruna Wannan Dalilin yasa Ya Musbahu ya Kira su Abba wanda daman suna Garin na Jemeta sunzo Family House din mu da Niyar Har nan zasu so su Dubani kuma su Dawo dasu Hassana Suna Gidan Goggo Zaliha suna Jin Kiran ya Musbahu suka Dungumo suna Zuwa sai gasu Baffa Haruna ba Bata Lokaci Ya Musbahu yayi musu Jagora Zuwa Shashena suka Iskeni Cikin wannan Halin Wanda Dalilin sa ne nake Cikin Wannan Rayuwar sa"adiya.." Ta Karishe Fada Cikin kuka Zaina Dake Sharan kwallah Tace"Zubaida da Mommy bazasu Taba gamawa da Duniya Lafiya ba Anty Farida sun Zalunceki Kuma suma sai Sunga Sakayyah,Toh kuma duk ya akayi kika san duk wannan Abubuwan..? Farida Tace"Zahra Take maida yadda Zubaida ta Dinga Fada Tana kuka ni kuma sai a Hashashena na Hasaso yadda Ta Tsara komai Tunda Dagani sai ita agidan.."Zaina Tace"Ba Shakka Hasashenki Daidai ne Anty Farida..ammh meyasa bazaki koma Gida ba..?kila Zuwa yanzu gaskiya Tayi Halinta...? Farida Ta Girgiza kai Tana Fadin"A"a Bazan koma Gida ba..Koda na koma sai dai naje na kara Tabbatar musu da bakinsu akaina na Zama karuwa..Sa"adiya har yau har Gobe ina Tuna kalaman Abba da Mami akaina Sunyi Tur dani sun Kirani karuwa gaban ya"yana da a Dangina Mijina yayimin Allah ya isa ya sakeni gaban Iyayena da ya"yana yana Kirana karuwa Ki gayamin Sa"adiya akwai wata Sauran Kima Data Rage min..?bata Babu sam Bani da wata Sauran Kima Sa"adiya Shiyasa gwara ki barni na karasa Rayuwata ahaka Duk da ina karban mgani ammh ina ji araina Kila wannan Ciwon Zuciyan Watarana Shine ajalina..Ammu kafin nan sai na Cika miki alkawarinki zan maida ke gidanku Bauchi da kaina na Damkaki Hannun marikanki Ni kuma na Dawo nan na Cigaba da Harkokina ammh Ki sani ba anan Gidan zaki Haihu ba saboda Bariki ba kamar kowani Gida bane ba wanda yasan da Labarin Cikin ki Saboda haka ki Boyesa kada ya bayyana a cutar Dake nasan In kowa ya gansa ya Fito Zan Fuskanci Barazana Har Daga wajen uwar mata Saboda haka na yanke Shawaran Siyan wani Gidan Dabam batare da sanin Kowa ba mu koma Chan Har ki Haihu Lafiya..." Zaina Ta gyada kai Tana Sharan kwallah Tace"Har Zuly kada na Bari ta sani.."Farida tace"Eh..Itama kada ki bata yarda..Domin a bariiki babu yarda Babu Amana Ko bata ci Amanarki ba Watarana Za"aiya amfani da ita acutar dake..Ki kula da wannan.."Zaina ta jinjina kai alaman Gamsuwa kafin Ta koma Tayi Tagumi Tana Fadin"Kema Zaki koma Gida Da uzinin Allah Anty Farida..Na kuma Tabbata duk inda su Abba suke so sun gane gaskiya...Ko domin komai ba Domin su Hassana Anty Farida da kuma karaminsu areef.." Farida Ta Sauko Daga kan Gadon Tana Fadin"Kina Tunanin Su Hassana suna mim kallo uwa mai nagarta..? A"a suma a amatsayin karuwa suke kallona Sa"adiya."Daga haka ta Tura Kofar Tiolet Tana Kokarin Danne Abunda ke taso mata Daga kasan Ranta da kallo Zaina ta Bita aranta kuma Tana ganin Zuciyar Farida ta Riga Ta Kekashe Da Abunda ya Faru da ita ammh Ta Tabbata a yanzu Tuni Allah ya Tona ma Zubaida asiri,Bazata bari Anty Farida ta Dawo ma wannan Rayuwar ba Zata yi iya bakin Kokarin Taga Itama ta saka mata da Abunda Itama Tayi mata. ****** *Monday..* Yau ta kama Monday ne Tushen aiki Kowani ma"aikaci yana Shirin Tafiya wajen aikinsa ne Kamar yadda Take wajen ZAIN domin ya Riga ya guduri Niyyar Bazai kara kwanciya ba ganin in ya cigaba da kwanciya Watakila Har Abada bazai kara ganin Firstlove da abunda ke Cikinta ba ya yanke Hukuncun Tashi Tsaye ya Nemi Zainarsa a ko"ina afalin Duniyar nan batare da ya nemi Taimakon Kowa ba. Tun Jiya Lahadi da Haddir yazo ya Rakashi suka Tafi Gidansu Sun samu Tanimu megadi Cikin Damuwa Domin Gidan ya zama wanu iri ba Gimbiyar Dacta ba Dactan kansa yana ganinsu sai yaji Dadi bayan ya gaishesu ne ya Kalli Zain ganin yayi wani iri Dashi kamar bashi ba yace"Dakta Lafiya kuwa..? Ka daina kwana agidanan nan Gimbiya kuma Tun watan Daya wuce Bata gidanan Dom Allah kada ka gayamin kun Rabu da Gumbiya Halima ne Ranka ya Dade..? Ya Fada kamar yayi kuka Zain Da Kansa ke gefe yana Sauraran Tanimu megadi Har Haddir zai mai mgana Zain yayi Saurin waigowa yana Fadin"A"a Tanimu har Abada babu saki Tsakanina da Zaina..Ni dai da wadanan Hannuwan nawa bazan iya sakinta ba...Tanimu ka Tayamu addu"a Firstlove ta bar Gida bamu san inda take ba.."Yafada yana kallon Tanimu Cikin wani yanayi,wanda sai da Haddir ya kara jin Tsausayin Zain din daya koma kamar bashi ba. Kasa Tanimu megadi yakai Hannunsa Daya Dafe da Kirji Daya kuma Bisa Cikin Zaro Ido yace"Mun Shiga uku Dacta badai Halimatus Sa"adiya ba..?haddir ya bashi amsa da ita fa Kawai sai Tanimu ya Fara matsan kwallah yana Fadin"Innalillahi wa"inna Illaihirra"jun Kai Duniya ina zaki Damu..? da izinin Lahi Ya Allah ya Allah Duk inda Gimbiyar Dacta Take tana Tare da Tsarewar Allah..Allah ya bayyanata Allah ya bayyanata Dakta bakai kadai kayi wannan Rashin ba Wlh muma munyi Allah ya bayyanata.."Yake Fada yana kuka Zain na kallon Tanimu Lokaci Daya yana Fadin"Insha Allahu..Ameen Ameen ya Allah..Nagode Tanimu.."Haka suka Shige Cikin Gidan suka bar Tanimu nata kuka yana addu"an Allah ya bayyana Zaina. Kayansa Duka Zain ya Hado da duka Abubuwan da zai Bukata Ya Dade Cikin Bedroom dinsu yana Hawaye ya Bude Bangaran kayan sawan zaina yaga komai yana Cikin Muhallinsa ne,in ya Waiga sai ya Dinga ganin kamar zai ganta Dakin da Gidan Gabadaya suna Dawowa mai da Wata Rayuwar da sukayi acikin Gidan Zain ya karajin Zama bai Gansa ba Dole zai Tashi ya Nemo Zainarsa Ko zai samu Sukuni,Haddir ya Tashi suka Fita da akwatunan daya saka kayansa kama Daga Kayan sawa Zuwa Takalma da abubuwan da zai Bukata Domin bazai iya zama agidan indai ba Firstlove ba kuma su Abba sun yarda ya dawo Gida ya zauna Zasu fi samun Kwanciyar Hankali. Tun karfe 7:30am ya Fito Daga Dakin Sadiq da ya ke zaune aciki Yanzu Cikin Shirin Fita Yana sanye Suit masu Ruwan Toka na kamfanin armani ya Tsuke Wuyansa da Nektie,Kafarsa Sanye Cikin Takalmi Rufaffe na Fatar Damisa,hannunsa Rike da makullin Motarsa Da wayarsa kana mai kallon Farko zaka Hangi Damuwa Firgici da kuma Rama a tare dashi ba,Gashi ya zama wani so Cool kamar ba Dr Zain ba. Yaso ya Tafi Tun Lokacin ammh Nene Ta hanashi Ta matsamai sai da ya karya ita ta Dinga Fifitamai Tea din har ya Wuce yasha sai ga Umma da Abba sun Fito sun ji Dadinsa ganninsa haka Zain ya Duka Ya gaida Abba da Umma Abba ya Dagosa yana kallon kwayan Idanuwansa Tuni wani Tsausayi da kuma Soyayyar Uba da Dansa kawai sai ya Rumgumeshi kamar yayi kuka yana Fadin"Allah yayi maka albarka..Allah ya kareka Allah kuma ya baka ikon Cin wannam Jarabtan Rayuwar da Allah ya Dora maka kana da kananan Shekarunka Allah ya baka karfin Gwiwa da kuma Jarumtar Daukan wannan al"amarin Zain.."Yake Fada Lokaci Daya yana Bubbuga bayansa Nene da Umma suka kalli juna kafin su Rike hannun Juna Suna Fadin Ameen Ameen da karfi Zain ma Dagowa yayi yana kallon Abba Lokaci Daya yana Fadin"Ameen Abba..Nagode kwarai...Nima ku yafemin Halin Damuwar da na sakaku..." Abba ya Girgiza mai kai yana Dafashi Lokaci Daya yana Fadin"Shiii..Karka damu..Mun yafe maka Duniya da lahira..Allah yayi maka albarka.."Su Umma suka kara amsawa da Ameen Sallama yayi musu ya Fice da cewa zai Fara Zuwa Gidan Alhaji Tsoho kafin ya wuce asibiti Suka Bishi da Allah ya Kiyaye Hanya da kuma Kallon Tsausayi har ya Fice Daman Motarsa tana Haraban Gidan Haddir ya kawo mai ya Bude ya Shiga Bayan ya zauna ya saka Set belt yayi addu"a Hawan abun Hawa Domin abaya baya yi Duk kuwa da Fadan Da Firstlove take mai ammh yau gashi bata,Tazo taga ya koma yadda Take so Tashin Motar yayi bayan yayi Hon megadi ya Budemai get ya Fice sai gidan Alhaji Tsoho. Koda yaje Haddir bai Riga ya Fita ba,Suna Dakin Hajiya mama suna karyawa,Suna ganinsa Dukkansu suka zubamai ido Cikin wani yanayi Takalman kafarsa ya Cire bayan Ya Shigo da sallama Gaban Alhaji Tsoho ya Duka yana Gaishesa ya amsa mai Cikin Farincikin ganinsa ahaka Zain ya Juya a sanyaye yana gaida Hajiya mama kawai sai ta tashi Ta isa garesa ta Rumgumeshi Tana Fadin"Allah ya kara maka Juriya Jikana...Allah ya bayyana halima Lafiya Allah ya Tsareta duk inda take.."Gabadayansu suka amsa da Ameen. Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fadin"Zainullahi har an Fito..? Kai ya gyadamai batare da yayi mgana ba Haddir ne dake Shan Tea yace"Ka karya..?Zain ya Dago yana kallonsa Cikin Sanyin Da ya koma yace"Eh...! Kawai ya iya Fadi ya maida kansa ya Sunkuyar Alhaji Tsoho yace"Masha Allah..Allah yayi albarka naji dadin ganinka ahaka Zainullahi..Abu na gaba shine ka ga dai duka abubuwan da suka Faru ko..? Akwai sakaci da addu"a sai ka Dage kaji ko..?mganar Halima kuma muyu ta Rokon Allah Insha Allah Allah zai bayyanata..Amina mikomin Ruwan zamzam din chan.."Ya fada yana kallonta Tashi Tayi ta Mikomai Ruwan Zamzam din Dake Cikin wani Dan Gora shi kuma ya karba ya mika ma Zain yana Fadin"Karbi kasha...Ku daina sakaci da addu"a da kuma azkar Domin neman Tsarin Kanku Daga Shedanun Mutane Dana al"janu Hadiru yafi ka Kokari kan wannan Fanni kaima sai ka Dage.."Zain ya Gyada kai bayan ya karbi Ruwan yana Fadin"Insha Allahu Alhaji Tsohio nagode Allah kara Nisan kwana.." Alhaji Tsoho ya amsa da Ameen yana Fadin"Ku tashi kuje..Allah ya bada Sa"a.."Zain ne ya Fara Mikewa Ya Fice Kana Haddir Kusan Tare suka Jera zuwa Haraban Gidan kana Kowa ya Shiga Motarsa suka Fice Zain ne ke gaba Haddir na Binshi abaya Har Zuwa Cikin Haraban asibitin.. Likotoci da Nurses din Dake asibitin sunyi Murna da ganin Zain ya Dawo bakin aikinsa Batan kuma Zaina ashe ya Zaga ko"ina sai Allah ya kyauta ake mai da addu'an Allah ya bayyanata Ya Shiga Office dinsa yaga Tarin Folder nan da nan ya Fara Duba maarasa Lafiya Cikin wani Kuzari yana Tunanin kafin nan da 1pm na Rana zai bar Cikin asibitin ya Fita Domin Fara Neman inda Zainarsa ta Shiga Daga garin Bauchi. *Ki Biya ki karanta Cikin Salama Hajiya* *Janafty..* 7/15/21, 11:41 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣9️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*    "Karfe 1:30pm ya Fito Daga Cikin office dinsa Zuwa Haraban asibitin Lokaci Daya yana Duba agogon Fatan Dake Hannunsa. Ba haka yaso ba yaso ne Tun 1pm ya baro asibitin ammh Patient sunyi yawa kuma ya Dade bai Shigo Cikin asibitin ba Shiyasa ya zauna Har sai da yagama Dubasu Kai Tsaye masallacin Dake Cikin asibitin ya Shiga ya Daura alwala ya Shiga Masallacin Bangaran Maza ya Tada sallah bayan ya idar ya Rusuna gaban Ubangiji sai da ya Fara da Rokon Gafaran Allah Bisa Zunuban Daya aikata Kana ya Gangara kan addu"a awannan Fita neman Firstlove da zai yi Allah ya bayyanata Allah yasa tana Cikin Koshin Lafiya da kwanciyar Hankali Allah ya bayyanamai ita ya Dade yana addu"o"insa Kafin ya Shafa Cikinsa najin yunwa ammh Yanayin Dayake ciki yasa bai Damu daya Nemi abinci ba yana Fitowa Daga masallacin ya Fada Motarsa ya Bata Wuta ya Fice Daga Cikin asibitin. Abun Tsausayi Abun kuka Zain Duk inda yaga wasu Gungun Mutanesuna zaune haka zai Faka Motarsa yaje wajensu bayan sun gaisa sai ya Fito da wayarsa Hoton Zaina ya Bayyana da kayan Data bar Gidan Domin Zafeera ya Kira ya Tambaya Ta Turamai,In ya nuna musu sai yayi musu bayanin Ta bar Gida Sati Uku Daya gabata sai su ce basu ganta ba wasu Har suna bashi Shawaran yakai Cigiya gidajen Radio yace an kai ammh Har yanzu Shuru Tun wasu suna ganin Shirme har suka zo Suna Tsausayama Zain din ganin yadda yake wahala Sallah kadai ke Tsayawa ya Tsaidashi Bisa Hanya Tun bayan Faruwar almarin Da Alhaji Tsoho ya ankarar dashi Sakaci da Ibada bai kara bari sallah ta Wucesa ba. Ranar sai Bayan Mangariba ya Koma Gida ya Zagaya anguwanni ba adadi yana Neman Zaina ammh ba Nasara bai Karaya ba washegarima Daidai wannan Lokacin ya kara Barin Cikin asibiti ya Fita Neman Zaina Ranar ma sai Dare ya Dawo ba Nasara Allah Sarki sai da Zain ya Jera sati yana Zagaya Tashshon Garin na Bauchi Ba Wanda yace mai yaga Ko mai kama da Zaina Ammh Duk da haka bai karaya ba Babu Inda bai je ba agarin Bauchi Ba Wani Labari sai ya Fara Tunanin Lokaci yayi da zai Fara Duba  Zaina a Makotan garin na Bauchi Tunda dai Bata Cikin garin na Bauchi. Ranar Daya Cika kwana Bakwai yana Fita Ranar Haddir yabi Bayansa Domin Tun kwana Uku Da Fara Fitan Zain ya ankare da Haka Tunda yana Zuwa Office dinsa sai ace ya Fita abun sai ya Fara bashi mamaki yana Zaton Gida yake zuwa,ashe ba nan yake zuwa ba Domin yaje gidan yagani,Sai Yagayama Alhaji Tsoho shi kuma yace ya sakama Zain din Ido ya gano ina yake Zuwa,Dalilin Haka ne yasa yau din yabi bayansa abun Tsausayi sai da Haddir yamai kuka Dandalin masu adaidaita yaje Daya bayan Dayan yake nuna musu Hoton Zaina Koda wanda ya Ganta ammh Ba"a dace ba Domin Anyi Rashin Sa"a Mai adaidaitan Daya Dauki Zaina Zuwa Tasha Dan kano ne aiki ne ya Shigo Dashi Bauchi kuma Tuni ya koma. Zain Jikin Motarsa kawai ya koma Ya Dafe kanshi Zuciyarsa na wani Irin Suya sai kawai yaji an Dafa bayansa yana waigawa yaga Haddir Tsaye yana kallonsa Cikin mamaki ya Kara Waigowa yana Fadim"Haddir..Kai ne anan..?me kazo yi..? Haddir yace"Kai na Biyo..! Zain yace"Ni kuma..? Haddir yace"Eh mana na lura Dakai Tunda ka koma aiki Kullum iwar wannan Lokacin kake Fita Sai Nagayama Alhaji Tsoho Shi kuma yace nabi bayanka naga Ina Kake zuwa."Zain yayi Shiru kawai yana kallon Haddir kafin yayi wani Mirmishin takaichi Yana Fadin"Uhm...Ina kuwa Zani Daya wuce Neman inda Matata Uwar ya"yana Ta Shiga..? Kuna Tunanin zan zauna ne kawai ina ji inagani Firstlove Ta bar Rayuwata Gabadaya..? Ko kuwa kuna Zargin Wajen wata Karuwar na koma ko..?uhm..Wlh nayi Tuban Gaskiya Yanzu awannan Halin Da nike Ciki Duka Sauran mata ma Maza nake kallonsu babu Abunda ke Burgeni Balle ya bani Sha"awa Wlh Haddir Zaina Itace Gishinkin Rayuwata Rasata Tamkar Rasa Duka Walwalatace.."Ya karishe Fada kamar zai saka kuka. Haddir ya kara Damke Kafadarsa yana Fadin"Am Sorry...Na sani ba kuma wai Muna Zarginka Da sake aikatawa Wani Laifin bane Kaga baka da lafiya bai kamata kana wannan yawon ba Kazo mu koma Gida Zaina kuma addu"a zamu Dake dayi mata Insha Allahu Tana Cikin Koshin Lafiya,kuma Allah zai Bayyanata.."Zain ya Ture Hannun Haddir yana Fadin"No...Ba zan iya komawa Gida na Zauna Bansan Inda Firstlove take ba..Ba zan iya ba Haddir Bana samun Wani Kwanciyar Hankali.." Haddir yace"Is ok...Zo mu koma Gida kayi wanka ka Huta..Sai muyi mganar yadda zamu bullo da wata Hanyar kaji.."Zain yayi Shuru bai yi mgana ba Haddir ya Kara Dukan Kafadansa yana Fadin"Be a man..Kaji ko shiga Mota muje Plz..."Jin haka yasa Zain ya Kada kai Ya Bude Motarsa ya Shiga Shima Haddir ya Shiga Shine agaba Zain na Binsa abaya Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Haddir yagayamai Komai Shi kanshi Alhaji Tsohon kallo ZAIN kawai yake Cikin Halin Tsausayamai Domin yasani Tabbas ya Fada Wata Jarabawa mai yunwar Dauka Da kuma Halin kakani kanin Rayuwa. Ita Kanta Hajiya Mama sai da Tayi ma Zain din kwallah Tana kallonshi Duk ya zama wani iri Ya koma wani Shuru shuru baya mgana yanzu ma da suke gaban Alhaji Tsoho Kansa na kasa Baya cewa komai Alhaji Tsoho sai Nasiha yake tamai Nasiha yana gayamai ya Dage da addu"a suma iyayansa zasu Tayashi Insha Allahu Halima Zata Dawo Gida Cikin Koshin Lafiya ita da Abun ke Cikinta da wannan Kalaman ya Saussauta zuciyar Zain Yaji Jikinsa ya karayin Sanyi sosai Bai Bar Gidan ba sai da Hajiya Mama ta matsamai yaci abinci Kana ya Tafi bai Isa Gida ba sai da yayi sallar La"asar a massallaci. Ranar Wuni yayi Cikin Daki Yana Kallon Hoton Zaina yana Kananun kuka,Rayuwa gabadaya ta juya mai baya Umma da Nene suka jisa shuru suka Shiga Dakin Suna ta Lallashinsa Hakama Abba Daya Dawo Domin yanzu Zain Shine Abun Tsausayi,Hatta dasu Baban kaduna dasu Daddyn Abuja Kullum Cikin Kiran waya suke Tambayan ya ake ciki,Hakama su Inna Hannatu Kowa yana ta addu"an Allah ya bayyana Halima Cikin Koshin Lafiya. Nasihun Iyayansa da kuma Damuwarsa akansa yasa ya saki,Domim ayanzu baya iya yi musu Gaddama yana ganin Bayansu bashi da Kowa,Abaya ya Saba musu ammh ayanzu Bazai iya yi musu gaddama ba Komai suka ce Toh kawai yake Cewa. Haka Rayuwa Ta Cigaba da Gudana Da Dadi ba dadi,Zain Tundaga Ranar bai kara Fita Neman Zaina ba ya koma yana Wuni Cikin asibiti sai Dare yake Dawowa Saboda zaman asibitin ya fiyemai kwanciyar Hankali akan yazo ya zauna agida sai Tunani kawai da zai Tayi ammh Aikin yana Debemai kewa,ammh kuma Duk da haka bai zauna haka ba yabi masallatai Na garin Bauchi Ya kai Kokensa kan atayashi Addu"a Allah ya bayyana Zaina kullum kuma bayan ya Tashi aiki sai ya Biya bakin kasuwa ko Tasha yayi ma masu Bara Sadaka,Yayi Tsawalli da wannan Sadakan Allah ya bayyana masa Halima yasa Tana Hannu nagari,Alokacin in kaga Zain ya koma wani Gayinan kamar bashi ba,Baya aski Duk yayi Gemu Buzu Buzu ba wani gyara kai sai dai kawai ya saka kaya Fita Zuwa asibiti Bangaran Dina Kuwa sai dai gani Daga nesa,Domin Aduniyanan Ba wacce ya Tsana irinta Ko kallon arziki bata samu Daga barayinsa in Yana kallonta da wannan Cikin ji yake ksmar ya shaketa ta Mutu,Ita kanta Dinar ta Fahimci Haka Tsskaninta Dashi Daga Nesa ne sai dai in zai Fita Ta Rika lekasa ta Kofa Tana Kukan Soyayyarsa Dake kasan Ranta Gashi Zakiya bata kara Zuwa ba Tun Koran da Nene tayi mata,Sai dai suyi mgana awaya kuma ko Ta gayamata Hakuri Take bata ita kuma ta gaji Gaskiya ta Kosa ta Haihu a Daura musu aure ta Huta,Gashi Cikinta yana Cikin Watansa na Biyar ne ya Girma gashi nan ya Bayyana yanzu Ta Rage iskancinta ganin Bame bin ta kanta Dole ta kama kanta,Nene ne ta Mata dan Abunda Ba"a rasa ba. Mganar awon Dina kuma Alhaji Tsoho yace Haddir zai Dinga Zuwa Gida yana Duba Lafiyarta Ita da Abunda ke Cikinta Tunda dai Fitar Kamar wani Tonon asiri ne Dina bata so ba Taso Zain za"ace ya Dinga Dubata Abunda bata sani ba Ahalin da Zain yake Ciki inda zaa"a bashi Wuka Da Dina zai Fara yankawa Saboda Tsabar Tsanar da yayi mata yana ganin Duk itace Silam Komai itace Silan da yau aka wayi gari Firstlove bata Tare dashi Shi kuwa har wani kyalli Dina zatayi a wajensa yayi alkawarin bazai karayima iyayansa Gaddama ba Ballatana Har ya saba musu ba,Zai aureta kamar yadda suka Tsara sai dai Dina  zata sani zata kuma gane cewa Fadin nan Dayake yi na Baya sonta bai Taba kaunarta ba ba karya bace..Tunda yake da ita bai Taba Sonta bai Taba kaunarta ba baitaba Sha"awar auran mace irin taba..Ammh Tunda Tayi Sanadiyar Lalacewar komai Gata gashi Yadda zai Rayuwa Cikin Bakinciki Da Maraicin Rashin Zaina Haka itama zata zauna Dashi Cikin wannan Bakinciki da Rashin Madafa sai ya Tabbatar da Dina sai Tayi Nadaman Abunda ta aikata. ****** *Bayan wata Biyu..* Bayan Wata Biyu da suka gabata abubuwan suna nan yadda suke Ta bangaran Zain dai ba wani ci gaba yana nan jiya yau sai ma wami kara Ramewa da yayi ya kara Lalace Duk yayi baki yayi Gemu da kasumba kamar ba Zain dan Gayu ba Baya Fara"a baya Dariya baya zaman Hira Baya wata Walwala Duk Wani Abu na Jin Dadi Zain ya Riga yayi sallama Dasu acikin Rayuwarsa. Har kuma i yanzu bai Daina Sadaka da Zuwa masallatai yana Bada kudin Sadaka Domin arokamai Allah ya bayyanamai Firstlove bashi kadai ba Duka iyayan nashi basu Zauna ba suma Suna Tsaye kan addu"a barin ma Alhaji Tsoho Tunda sun ga Tabbancin Abunda Zain yake Fada In babu Zaina acikin Rayuwarsa shi ba Cikakken Mutum bane,Gashi kuma yana Faruwa Saukinta ma aikinsa da kuma Haddir Daya kasance aboki na gari Su kadai ke Debema Zain kewa sai kuwa Hotunan Zaina Da Kullum Da Hoton Awayarsa yake iya Samun Barci Har kuma yanzu yana Gida Saboda yace bazai iya zama Gidan da Sukayi Rayuwa Da Firstlove ba kuma yau awayi gari bata Har Abada bazai iya zama ba Dole aka kyaleshi anan Gidan su kansu su Abba Sun Fi Jin Dadin ganinsa kusa dasu Hankalinsu yafi kwamciya. Zafeera kuwa Bayan sun gama Exms Tazo Gida Dakyar ta iya Sati Daya ta Koma Itama Duk Ta Rame saboda Da Damuwa a yanzu ba iya Tsausayin Zaina Take ji ba har da Tsausayin Halin da Yaya Dakta yake Ciki Lalle ta yarda ta kuma Shaida Soyayyar Dayake ma Ukti bata karya bace Bayyana Dina kuma Wata kaddaran Allah ne Tatafi da addu"an Allah ya bayyana Zaina aduk inda Take hakama Laila Koda yaushe Cikin Kiran Umma Take ko Zataji wani Labari Ammh sai Umma tace mata Zaina dai Shuru har an kwarari Wata Na Hudu da barinta Gida Laila Tayi kuka Ranar da suka gama Exam Ta Tuna yadda zaina ke son karatunta ammah yau wani Dalili yasa ta watsar da Duka Burinta Allah Sarki Ita kanta Duka kamsin Salatin ta addu'anta Daya ne Allah ya bayyana Halima Allah kuma ya Tssreta ya Kareta ita da Abunda ke Cikinta bama Laila kadai ba Kowa Dake ahalin Gidan Dr.Saulawa Yana saka Wannan addu"an Cikin Duka Sallanlolinsa,Haka Zareena itama Tana Chan U.s Koda yaushe sai ta Kira waya its da Jawaaad suna Tambayan ba"aji wani Labari game da Zaina ba..? Duka dai Tambayan Daya ne Hatta Faruq ma Dake Chicago in ya Kira waya haka yake Fadi Balle Hamdiya itama Takan Kira Taji ko ya ake Ciki,Sai dai Fatan Allah ya Takaita abun ammh Zuciyoyi sun Fara sarewa,Umma da Zain kam azumin Alhamis da Jumma"a Baya Wucesu suna Tawasalli da wannan azumin Allah ya kare Halima aduk inda take ya kuma Bayyanata Cikin Koshin Lafiya. Dina kuwa alokacin Cikinta yana Cikin Watansa na bakwai me yayi girma Sosai Dayake Tana da Girmam Jiki sai kuma Yabi Jikinta ta zama wata katuwa Ganin Cikinta ya Fara Girma ne yasa Nene ta Fara Kula da ita sosai Ganin Amanace Itama agaresu,Dina Gabadaya Tana Cikin Damuwa ganin Ko kallo Bata ishi Zain ba Har Abba da Umma yanzu Tana gaishesu suna amsa mata ammh Shi Ta Lura ko kaunar ganinta ma bayaso Tunda Tazo Gidan Wajen watanta Hudu bai Taba Tako kafarsa Dakin ba sai dai Su Hadu afálo in zai Fita Ta Fito Tana wani Tura Ciki Tana yamutsa Fuska ita adole sai ya kalleta ya kuma Tankata ammh Ko Kallo Bata Isheshi ba batama sani ba Inda zata Daina giftamai acikin Ido Daya Ji Dadi Domin ya Tsani ya ganta ita da Cikinta kuma da sunan Wai Zamansa Take kuma Abunda ke Cikin Nata Shine Ubansa ba Domin bayason ya kara batama iyayansa rai ba Da Wlh da Tuni Tun bayan Tafiyar Firstlove shima ya Bita ya Shiga Duniya Sai Dina Ta Nemi kuma wanda Zatayi ma Burauba ammh Taci Darajan Masu Daraja Shiyasa Bai Taba Bi ta kanta ba Tunaninsa da Burinsa na kan Zainarsa da kuma Abunda ke Cikinta kuma yana lissafe da Cikin Yana kuma Tunanin Itama Cikinta ya Shiga wata na bakwai kenan Yana Fatan Allah ya Bayyanamai matarsa ta Haihu agaban Idanuwansa Shine Fatansa da Burinsa. Bangaran Zakiya kuwa bata kara Zuwa gidan Abba Wajen Dina ba,Ba Domin taji Haushi ba sai Domin Ta Kiyaye wasu abubuwan bata so Plan dinsu ya Tashi a banza ammh Tana Kiran Dina awaya Tana kuma bata baki kan Cewar datake Ta gaji da Cikin Jikinta da kuma Rashin Ko in kulan da Zain Ke mata ita kuma Zakiya sai ta Tausheta da Fadin Karta Damu Sauran kadan ta zama mallakin Zain alokacin bai isa kuma ya iya Wulakanta taba Tunda ta zama Matarsa kuma uwar ya"yansa,Da iri irin kalaman ne Zakiya ke Tausan Dina Datake Kokarin Fadin Tagaji Tana Chan Tana Cigaba da Iskancinta Itace Tarayyah da wannan Bin Wannan Har kuma aranta Tana Tunanin Namijin daya ya Dace da ita Wato Namiiji kamili wanda Bai yi Rayuwar Bariki ba. Kwamishina ya sake Zuwa ya Duba Dina Har sau Biyu Hajiya Batula ma Tazo ita dasu Waleed suka Kwana Daya suka koma,game da Lafiyar Dina kuma Da Abunda ke Cikinta Haddir ke zuwa Duk wata yana Cheking dinta Shima Din har ya gama Dubata da yi mata wasu yan Tambayoyi baya sakar mata Fuska Daya gama Abunda ya kawosa zai kwashi kayan aikinsa ya Fice shima kamar ya Tsaneta ammh kuma ba Haka bane Haddir ko Cikin yan"uwansa mata bai da Sakewa mace Daya yakan sake da ita Zareena ce itama Domin Tare suka tashi ne shiyasa. Bayan Hajiya Batula ta koma Kano ne ta samu Kwamishina Ta bashi Shawaran bai kamata abar Dina ita kadai ba Duk da Su Nene na Kokari akanta kuma Mutanen arziki ne basu Rike komai acikin Ransu ba bai kamata haihuwar Fari ba abarta Ita kadai Ko yaya ne ya kamata akwai wani nata akusa da ita saboda Halin Rayuwa Wannan Mganar Ta Shigi Kwamishina kuma ya aunata yaga gaskiya ne sai ya Kira Hajiya Maimuna sudan ya Tuntubeta kan ko zata zo Ta zauna Wajen Dinar har ta Haihu tace Daman itama Dinar na Ranta Shikenan Zata Shirya Tafiyan Zuwa Watan Gobe suka Rabu kan zai Kira Alhaji Tsoho ya sanar dashi haka kuwa akayi Daya Kira Alhaji Tsoho yamai bayani yace gaskiya ne bakomai sai tazo Ai yanzu anzama Daya Kuma Alhaji Tsoho da kansa ya Kira Abba ya gayamai Hajiya Maimuna zata zo ta zauna da Dina Har Ta Haihu bai yi Gardama ba  Domin Shima bazai Taba iya ma Alhaji Tsoho gaddama ba Kowa yaji sai yace sunyi Tunanin Mai kyau Domin fa Mganar gaskiya Ranar naka fa sai Nakan nan. ******* *Zaria..* Rayuwar Zaina agidan Uwar mata Wata Rayuwa ce mai Cike da Darussan Rayuwa,Kuma Rayuwa ce Datake gudanarwa kamar Rayuwar yaya da kanwa Domin Babu Wani Bukatan Rayuwar da Farida Bata Dauke mata Shi ba Zaina Bata Da maraici Ko kuma Wani Wahalan Rayuwa Farida Zata Fita Ta bada Jikinta abata Kudi Tazo Tayi ma Zaina da Abunda ke Cikinta Hidima kuma aciki Har Tabama Uwar mata nata kason Dalilin Dayasa Ta kyaleta Ta Zauna wajen Faridan kenan. Bayan Zuwan Zaina Gidan Zuwanta Uku,ammh bata kara mganar Zaina ba,Tunda Farida Tana Toshe bakinta da kudi,Zaina bata Fita Ko"ina Daga Daki sai daki bata aikin Komai sai dai taci ta kwanta In Tagaji Tayi kallo Komai zai Faru Gidan Farida Ta hanata Fita Koda bata Gidan sai dai In Tana Bukatar gani Ta Leka ta Window Daga Zuwanta Gidan zuwa Lokacin Datake Watanta Hudu acikin Gidan Ta kara Gogewa Da Rayuwa sosai,Banda Zuly Da karacharrale bamai Shigowa Dakin Farida suma Din Ita Ta basu Dama Ammh bata basu yarda ba Tunda Har Tsawon Lokaci babu wanda yasan Zaina nada Cikin Wata bakwai ajikinta Kuma Farida nakaita awo Duk bayan Sati 6 a asibitin Almadina,Kuma Ba wanda yasan Duka Siyayyan kayan Haihuwa Farida Ta gamashi Komai da Za"a Bukata na kayan Jarirai kuma Biyu Duka Ta Siya Komai Tunda anyi mata Scanning Likitan yace yan Biyu ne acikin Zaina Daya mace Daya Namiji Shiyasa ta Tanadi Komai Ko gajiya batayi Zaina Sai dai kawai Watarana Tayi Ta kallonta Tana kuka acikin Ranta Ta kare Lafiyarta ta martaba Auranta da Abunda ke Cikinta Ta gwammace ita ta Rika Fita tana Raba ma Maza Jikinta suna Biyanta Saboda Ita,Tana ji acikin Zuciyarta Farida bata Dace da wannan Rayuwar ba sam Mace Ce saliha mai Nagarta Tana Tsausayama Musbahu Domin yayi Rashin Kamilar mata haka kuma Tana Tsausayama Abba da Mami Domin sunyi asaran Nagartattaciyar Y"a haka kuma Tana Tsausayama Hassana da Usaina da arif Domin sunyi Rashin Uwa Tagari Haka zata zauna Tayi kukan Tsausayin kanta Da Kuma Tsausayin Farida ammh ita bata Damuwa Ko ajikinta. Tum Zuwanta Gidan Farida Bata Taba kawo wani Kartonta acikin Gidan ba saboda ita,Daman kuma Ita sai dai Ta Bika Chan waje ku gama abunda zakuyi ka Biyata Ita Karuwancinta ba kamar nasu Sady bame da kullum Yan Shaye Shaye Farkan nasu Zuly kuma Har yau bata Rabu da Shafsoon ba Domin In Ta Rabu Dashi bata da Kowa Ba Domin ma Zaina na saka Farida na Taimaka mata ba da ba haka ba Zeezee da Jido Sun Dawo Ranar da suka Dawo Kuwa party akayi agidan kwana sukayi Kida da Rawa Inda Sabo ai Zaina Ta Riga ta saba. In Kwana ya kama Farida awaje zata Damka Amanar Zaina hannun Zuly Da kacharalle ta sani Ko Za"a Hada Baki da Zuly acutar da Zaina Ta Tabbatta kacharalle bazai bari ba Namiji ne ammh yana da Amana kuma Farida Ta yarda dashi Shima kuma Abunda yasa yake ganin Girmamta Abun Hannunta bai Rufe mata Ido ba, Ko nawa ya Tambayeta zata bashi Ko ma bai Tambayeta ba Tana Bashi,Duk da Tasan Ko Ta Fita ba Ruwan Wata da Zaina ammh Gwara ta saka akular mata da ita Hatta su Zeezee da suka Dawo sun Ji Labarin Zaman Zaina Wajen Sholly,Ranar Har dakin suka Shigo Suna kare mata kallo Sai da Kacharalle yazo yace su Fita ko kuma ya gayama Sholly in ta Dawo Shiyasa suka Fita ammh kuma Zeezee ta Lura da wani Abu Bata dai yi mgana Ba Shigansu Dakin Lokacin Zaina bata saka Hijabi ba,Tana Cikin Manyan Dogayen Rigunan da Farida ke Siyan mata Tana sakawa Saboda Boye Cikinta,Lokacin Datake Zaune Cikin ya Turo Kuma Zeezee Tagani ammh Zuly da Kacharalle babu Ruwansu basu Taba Lura ba kawai dai suna Tunanin Zaina Tana son kayan Labarabawa Domin Koda yaushe Cikin Manyan Riganunsu Take. Wataranar Asabar Tun Safe Farida ta Shirya tace ma zaina za"a zo adauketa Zata je Abuja sai Tayi kwana3 zata dawo zaina Ta Fara kwalkwal kamar Zatayi kuka Farida Ta lallasheta da Fadin kada ta damu ga Zuly nan zata Dinga Tayata kwana da Kula da ita,ga Kacharalle nan ma kada ta damu ita dai Batayi mgana ba ammh Yau Tafiyar Faridan sai Taji Bataji Dadi ba kamar wani Abu zai Faru ammh Tana Ji Tana gani Tatafi Bayan ta barma Zuly Kudi ko Zata Bukaci wani Abu. Kwana Daya Ta Tafiyar Farida Suby Taji Labarin abakin Zuly ganin Ta daina kwana adakin ta sai Dakin Sholly Ita kuma zuly da wauta sai tace kwana uku Sholly Zatayi kafin ta Dawo Suby najin Haka Batayi kasa agwiwa ba ta Kira Shafsoon ta Gayamai Ga wata Dama ta samu da zai Mori yarinyar nan da Sholly ta mareshi akanta Daman Tun Faruwar Abun yayi alkawarin sai ya Dau Fansa ta Hanyar Morewa da Zaina Tun Lokacin ya saka Suby aikin yace zai Biyata 50k in dai ta samamai Wata Dama Ta Dade Tana neman Damar bata samu ba Sanin Farida Ta tare ko"ina ga kuma Zuly da kacharalle ammh yau bata da wata Damuwa Kacharalle baya nan ya Tafi kaduna Uwar mata ta aiko adaukesa Zuly kuma Zata san yadda Zatayi da ita Shafsson najin Haka ya saki Ihun Jin Dadi Yace in Komai ya Tabbata zai Cikama Suby kudinta yanzu Rabi zai Bata tace ta yarda suka Rabu kan ta Turomai Acct lambata Ya Turamata kudin Itama Tace mai Xuwa anjuma Dayaji Kira kawai ya Taho Gidan Lokaci Yayi Da Zata so Taga Yaya Sholly zata yi In ta Dawo Daga Hajar Dake ta aikin Boye wani ya Riga ya Wanketa Zata so Taga yaya Sholly Zatayi kuma Daman ba Tun yau ba Ta Tsani Sholly Tana Bukatar ganinta Cikin Kunci Ta tsani Cigaban ta da kuma Finsu da Datayi da komai harda wajen Uwar mata. *Ki biya ki karanta Cikin Salama..Amanata A hannunku Take kuma Tana Hannun Allah ne..* *Janafty...* 7/16/21, 2:36 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣0️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*   "Daga Zuly har Zaina basu san Abunda Suby Take kullawa ba Da yammah Rufy ta gayyato kawayenta Suka zo Tsakar Gidan Suka saka Kida suna ta Shaye Shayensu,Da rawa Gidan Duk sai ya Rikice Shiyasa Zaina na Daki Ko Motsi batayi Saboda Gidan ya Cika maza da mata Gashi Farida bata nan Zuly ce kuma Itama Ta Fice ta barta Tun Tana Lekonsu Ta window har ta Gaji Ta Koma ta kwanta Bayan Tayi sallar mangariba Maltina Tasha kawai taji Cikinta ya Cika sai ta koma ta kwanta Saboda Bata son Hayaniya Toshe kunnuwanta da Filo tayi Saboda Kada Taji karan Kidan da agogo Tayi amfani Ta gane Lokacin Sallar Isha"i Daman dashi Take amfani Tunda bata Tunanin akwai masallaci nan kusa. Har Ta idar da Sallah Zuly bata Shigo ba Shiyasa Ta Shiga Tiolet Tayi wanka Tazo Ta Saka wata Doguwar Rigar Barci mai Igiya,Ta Dade Tsaye Tana kallon Cikinta Daya Girma Sosai ammh Yana Boyewa Cikin Burma Burman Dogayen Rigunan Data ke sakawa ammh ai Duk wanda ya kalletaa yasan ba ita kadai bane Ganin ta kumbura Ko"ina ta Cika Irin dai na masu Ciki Ita Har mamaki Take Zuly Ko Kacharalle basu Taba Fahimtar Tana da Ciki ba ko Kila sun Gane kawai kallonta Sukeyi. Karamin Hijabinta Datake kwana Dashi Ta saka ta koma ta Kwanta Tana Tunanin Bazata iya barci Yau agidan nan ba matukar akace da Kidan nan zasu kwana kuma in ba wani Ikon Allah ba Dashi Zasu kwana Ta Fara Gajiya sai Juye Juye kawai Take,Sai kuma Tunanin Gida ya Bullo mata Ta Fara Kewar Firstlove dasu Umma Hawaye ya Cika mata Ido Tana Dafe da Cikinta Take fadin"Kayi Hakuri..Insha Allahu zan Sadaka da Ko zan sadaku da mahaifinku Watarana..I so much Miss u Firstlove..."Take Fada Tana Share Hawayen da suka Zobomata Ta Koma ta Rumgume Filo kawai Ta Fashe da kuka Kukan kewa da Soyayyah mai Tsanani Kan Firstlove dasu Umma Tana Fatan Allah ya basu Juriya kan Abunda ta aikata Musu. Cikin Wannan Halin Barci ya Fara Fizganta ganin Shuru Shuru bata ga Shigowar Zuly ba,Barcin nata har ya Fara Nisa Domin alokacin goma na Dare ya Wuce,Suby Ta Daga Labulen Dakin Ta Leka Ganin Hankalin yan Gidan ya Dauke yasa ta Karisa Shiga Cikin Dakin Tana Kallon Zaina Data Dunkule Tana Barcinta Cikin Dariyan Nishadi Suby Tace"Dakyau...Komai zai Tafi Daidai..Nagama da Zuly Tunda na Bata Juice din dana gauraya da mganin Barci Tana chan ta Bingire Dakina Tana Barci Yanzu Lokacin Shafsoon ne bari na Kirashi So sorry Sholly..' Ta Fada tana kara Sakin Wata Dariya kafin Ta Fice tana Kokarin Fito da wayarta Cikin Breziyanta Sai da ta Fita Kofar Gidan Tunda hayaniyar kida bazai saka Shafsoon ya jita ba,Tana Kiransa ya Daga yana Dagawa tace mai yazo Komai ya Zama Daidai Shi kuma Cikin Dariyan Shakiyanci yace gashi nan Zuwa Daman yana kusa Ya gama Jika kansa da mgungunar maza so yake ya Dagargaza yarinyarnan,Ya huce Takaichi Da Zafin Marin da Sholly Tayi mai gaban Mutane. Hankalan su Rufy da kawayenta Duk yana Wajen Rawa Shafsoom ya Salalo ya Shigo yana Shigowa Suka ci karo da Suby Ta Dagamai Gira karaf a Kan Idon Deezee sai Abun ya bata mamaki Sai ta maida Hankalinta kan Shafsoon Taga Sadaf Sadaf ya Sulala ya Fada Dakin Sholly ya Kulle Kofa gaban Deeze ya Fadi Ta kalli Suby Wacce Take ta Dariyan Mugunta Ta Shiga Rawa Tanayi Tana Girgiza Hankalin Deezee sai ya Tashi Data Fahimci Abunda Suby ke Shirin aikatawa,Da Farko taso ta Share sai kuma ta kasa Domin har ga Allah bazata so Shafsoon yayi ma Zaina wani Abu ba Kamar fa amana take ga Farida Mikewa Tayi Zumbur Tana Neman Zuly Tunda Tasan Ita Farida ke bama Amanar Zaina sai dai Bata ganta ba Waje ta Fita Neman Kacharalle Har Gidan Abincin Uwar Mata Akace mata yana Kaduna Sai Hankalinta ya Tashi Ta Rasa yadda Zatayi sai ta Tuna Tana da lambar Sholly Da Sauri Ta Dauko wayarta Ta Lalubo lambar Sholly Ta Kirata Wajen Kira Biyar bata Daga ba Ganin ba Mafita sai Deezee Ta Tura mata sako kamar haka. *Sholly Kina ina ne..? Ko ina kike ki zo Gida yanzu Suby Ta ci Amanarki Tayi ma Shafsoon Kwangilan Yarinyar Dake wajenki Yanzu naga ya Shiga Dakinki ya Rufe....Deezee ce..!* Tana Tura mata Ta koma Cikin Gidan da Gudu Tana Raba Ido Hankalinta Gabadaya na Kan Kofar Dakin Sholly Gabadaya Bata da natsuwa Gefe Daya kuma Tana mamakin Ina Zuly Ta Shiga..?kodai da ita aka Hada baki Za"a ci Amanar Farida..?Bata samu Amsanta ba Shiyasa ta Fara Zagaye kamar mai Rawa Tana Kuma kasa kunni cikin Dakin Sholly din Abunda yasa Bazata shiga ba Saboda Shafsoon yafi karfinta Dama Kacharalle na nan ne tasan in ta gayamai Shi zai iya Shiga ammh Ita bazata iya da wannan Gabjejen katon ba. ***** Zaina Na Cikin Barci Taji kamar Tana Shakan wani Numfashi Mara Dadi Gefe Daya kuma Tana Jin kamar ana Tabata Ana Shafa wuyanta Zuwa saman kanta kuma ana Kokarin Cire mata Karamin Hijabin Dake Jikinta kamar amafarki Tayi Zumbur Ta Mike Tana Kokarin Tashi sai Taji wani Kakkauran Hannu yariketa yana neman Maida Ta kwance,Abunda ya bata mamaki,shine ganin Wutar Dakin Tana kashe ne alhalin kuma Ita Tasan bata kashe ba Bata ganin Komai sai Duhu ko Tafin Hannunta bata iya gani Ballatana Taga wanda ke kokarin Maidata kwance ya Danne ta. Hankalinta ya Tashi Cikin Tsoro Ta Fara ja da baya Cikin Duhun Taga Mutum na Biyota kafin tayi wani Yunkuri ya Riketa Ta Fara Mutsu Mutsu Tana Fadin"Waye..? Zuly ce..? Wayyo Allah na waye nace..? Take Fada Tana Kokarin kwatan kanta ammh Ina Shafsoon yayi mata Riko na Sosai Cikin Zafin Nama ya Kama Hannayenta ya Murde Duka Biyun Da Dayan Hannunsa Dayan kuma ya saka Hannu ya Tuge karamin Hijabin Jikinta Hade da Ribbon din Data Daure gashinta,sai gashin ya watse Saman Fuskarta,Zaina Taji Numfashinta na Kokarin Daukewa ganin yana Shinshinar Wuyanta Lokaci Daya yana Shafa Wuyanta Zuwa Kirjinta gashi ya Rike mata Hannuwa Numfashi ma Dakyar take yinshi Hankalinta ya kara Tashi Data Fahimci Manufarsa gashi Bata iya ganin ko waye yake neman keta mata Haddinta ba. Ihu Ta Kurma Lokaci Daya da kuka Tana Fadin"Na Shiga uku Don Allah waye..? Ko waye ya Taimaka Kada ya ketamin Haddi ni Matar aure ce Don Allah kada ka ketamin Mutumcina Don Allah.."Take Fada Tana kuka Tana Kokarin Kwatan kanta Shafsoon ya saki Wata Karuwar Dariya Yana Kallon Fuskar Zaina Ta Cikin Duhun Dakin Yana Fadin"Matar aure..? Matar aure agidan karuwai..? Kuma kike kwana adakin karuwa..? Rufemin baki yau Mai Ceton naki bata nan sai nayi yadda naga Dama ke.." Yake Fada yana Saka Harshensa yana Lasan Wuyanta Zaina Taji Muryan yayi mata kama da wanda ta sani ammh Ta rasa gane ko waye Ga Zuciyarta na Tashi Jin wani wari na Fita Daga Bakinsa da Jikinsa warin Wiwi da Sigari,Kuka kawai Zaina Takara sakawa Tana Ihu Shafsoon ya Shafo Kirjinta yana Fadin"Kiyi ihun ki yadda kike so..Na Tabbata yau bame Jinki Har sai nagama Abunda zan yi Dake.." Jin Haka yasa Zaina Ta Fara Kokarim kwatan kanta Suka Fara Kokowa Cikin Hakane yaji ya Tokare Cikin Zaina Wanda yasa Ta saki Ihu Tana Dafe Cikinta Abun sai ya bama Shafsoon mamaki da Sauri ya saka Hannu zai kara Rikota Tayi saurin Zillewa ta Dirka Daga kan Gadon da karfi Duk da yadda Ya"yan Cikinta ke Juyawa alamun an Tabasu,Duhu ne bata ganin Ko gabanta Ammh bata yanke kauna ba ta Fara Bin Dakin Tana Cimnkaro da abubuwa,Lokaci Dayakuma Tana Toshe bakinta kada yaji kukanta ya gane inda take,Tana Ta Lalube Taci karo da Bango Kanta ya Kume sai tayi kasa ta saki Ihu,Shafsoon na jin Ihunta ya Saka Hannu a Aljihun wandonsa ya Lalubo wayarsa ya kunna fitilan wayarsa ya Haske Fuskar Zaina Wacce ganin ya Haskata yasa ta Mike Zumbur Tana Rawan Jiki shi ya bama Cikinta Daman ya Bayyana Shafsoon Dake kallonta Daga sama Har kasa sai ya saki baki yana kallon Katon Cikon Dake Cikin Zaina Ido ya kwalalo waje Kafin ya saki Dariya yana Fadin"Au Daman Cikin Shege kikayi Shine kike wani Fadin ke matar aure ce..? Kice an Dade ana Morewa Nima Kuwa ya zama Dole na More zama kifi Dadi Tunda kina da Ciki ko..? Yafada yana Kallonta Zaina Ta Fara Ja da baya Tsoro ya Cika mata Zuciya gashi ko Tayi Ihu bamai Jinta Kida da Hayaniya ya Cika gidan,Ta Fara ja da baya Domin sai yanzu ta Fahimci wanene yake neman Keta mata Mutumcinta,Wato Shafsoon ne kwarton Zuly Zuciyarta ta Fara rawa Daman Zuly ba da Zuciya Daya ta Dauketa ba Daman gaskiya Anty Farida ne Datace Dan Bariki ba abun yarda bane shiyasa Kwata kwata bata ganta ba ashe tasan me ta Shirya Ganin yana Nufota yasa Ta Kai ga Bango Hannunta na kasa Tana Laluban Abun Duka Tunda ba maceto sai Allah Cikin Ikon Allah taci karo da Karamar Tukunya saman Gas Da Ruwa aciki Sai ta Tuna dazu Zuly ta saka Ruwan zafi ai bata Jira komai ba Ta Daga Tukunyan da Ruwanta da komai ta Wurgama Shafsoon sai Saman kansa ya Saki Ihu wayarsa ta Fadi gefe Shima ya Duka Dafe da kanshi Ganin Haka yasa Zaina ta Nufi Kofa da Dan Hasken fitilar Wayar Shafson Ta samu ta Bude Kofa Ta Fice da Gudu Tana kuka Tana Fadin"Don Allah ku Taimakamim zai Ketamin Haddina.." Take Fada Tana kuka Tana Fita suka ci karo da Deezee wacce Daman ke Zagaye kofar Dakin Ta kasa Natsuwa Ita ta Riko Zaina ganin kamar bata Cikin Natsuwarta Ihun da Zaina keyi yasa Hankalin su Rufy ya Dawo kansu sai aka kashe Kida Daman ga Tsakar gidan da Haske kwai ana ganin Kowa da kowa Tunda akwai Wuta Tuni Duka Hankula ya koma ga Zaina Wacce ke Tsaye Ga Katon Cikinta gaba Daga ita sai Rigar Barci kanta ba Dankwali Duk Tayi wani Buzu Buzu da ita Tasha Kuka Batama samu Zarafin mgana ba sai ga Shafsoon ya Fito Dafe da kansa Ruwa Duk ya Jikasa kansa har ya Kumbura Harda Jini Suby Dake gefe ta Zaro Ido Tana kallon Shafsoom Da Zaina wacce Cikin Jikinta yabama Kowa Mamaki Har da kuwa ita kanta Deezee din. Shafsoon Kuwa da Ransa ya gama baci ya Nufi Zaina yana Fadin"Wlh baki isa ba..Yau sai na More da Jikinki Kina wani Tsoro kina kyarma,Cikn Jikin ki a ruwa kika sha..? Ina ce wani ki bama Jikin naki yayi yadda yaga Dama Dake..? Toh Nima yau ko Kina so ko baki so sai na Dandanin Zumarki alkawari ne na Daukan ma kaina.." Yafada Cikin Tabbatar da Mganarsa Yana kuma Nufar Zaina wacce ta Fara ja da baya Tana kuka Suby Ta Ratso Tsakiyar Wajen Lokaci Daya ta Saki Shewa Tana Fadin"Ahayye..Daman Abunda ake ta Boyen kenan Cikin Shege..? Lalle Sholly Ta manta ne Uwar mata bata barin a haifa mata Shege Cikin Gidan Sai dai ta sanda Inda zata kaiki ammh badai nan Gidan ba.."Zaina na kuka Cikin Bacin Rai Tace"Kada ki kara Kiramin Da Cikina Shege..Cikina ba D'an Shege bane Dan Sunna ne Cikakke mai asali.."Tafada Tana Kallon Suby kai Tsaye Wacce ta Sake Baki Tana kallon Zaina Daga sama har kasa Kafin Ta kalli Shafson Tana Fadin"Au Allah..?to kai fa kaji ashe Daman Tana da baki kake Tsaye Jata Zuwa Daki ka aikata mata Da Hujja.." Ta Fada Cikin Son Zigasa Jin Haka yasa ya Nufi Zainar da karfinsa sai dai me Dezee Ta sha Gabansa Ta Tare Zaina Ta Dawo Bayanta Cikin Daure Fuska Tace"Kada Ka kariso Shamsu..Yarinyar nan Amanar Sholly ne Kema Suby In da adalci bai kamata ahada baki Dake wajen Cutar da wannan Yarinyar ba ke baki ma Tsausayin Halin Data ke Ciki..? Gaskiya ka wuce ka Fita Ko kuma na Kira Uwar mata yanzu na Fada mata..' Dagashi Har Suby Dariya suka saka Kafin Suby Ta kalli Deezee Daga sama Har kasa Tana Fadin"Topha..Ikon Allah yau kuma Deezee kema Kin zama yar Koran Sholly kenan yo Allah na Tuba Dakike Fadin Adalci anan Gidan Uban waye adali Kowa fa Dan Iskan kansa ne kuma Ita Data kawota Gidan Ai Matsayin Haja take Tunda dai Tsan nan Gidan Gidan Zaman karuwai ne ba Wajen zaman Mutanen Kirki ba saboda haka Ko Zaki Mutu yau sai Shamsu ya More Allah da na san Kema Kina Tare da Zuly Da Tare na sakaku Barci.." Wani Kallo Deezee ke bin Suby Dashi Kafin Tayi mgana Suby Ta saka Hannu Ta Tureta gefe sai da Ta Fadi Ta isa ga Zaina ta Riko Hannunta wacce ke Zillewa Tana kuka ta Nufi Shafsoon Da ita Tana Fadin"Gata Shiga da ita Ciki acikin Dakin nake so kayi mata Fata Fata In Sholly ta Dawo Ta saka a konani In ta isa.." Shafsoon yayi Mirmishi ya saka Hannu zai Rike Zaina yaji karaf an Rike Hannunsa Cikin mamaki ya Dakata Lokaci Daya Dashi da Suby suka kai Dubansu kan wanda ya Rike Hannunnashi sai da gabansu ya Fadi ganin Farida Fuskar nan Ba Fara"a Cikin Bacin rai da kuma Nadaman yarda da wasu Datayi acikin Gidan nan Ganin yadda Farida ke Binta da wani Matsiyancin kallo ne yasa Bata san sadda ta saki Hannun zaina ma ita kuma Daman Rauninta ya Bayyana ta isa ga Farida ta Fada Jikinta ta Fashe da kuka Farida ta Rumgumeta Tana Jifan Shafson da Suby da wani Matsiyacin kallo. Daman Tana Hanyar Dawowa Zaria Taga Sakon Deezee,kiran ma Ta gani kawai Bata Daga bane bakuwar lamba ne ganin Sakon ya Daga mata Hankali Daman kuma Alhaji Badamasi ta Raka Abuja,taro Kuma sai Basu kai yawan kwanakin ba Tafiya ta kamashi zuwa Lagos na Tsawon Sati Biyu Yace tazo tamai Rakiya saboda Zaina yasa ta ce bazata jeba Shi kuma ya kyaleta Shine ya Hadata da Direba ya maidota Zaria bayan sun kai sa ya Hau Jirgi Lokacin Dataga Sakon Hankalinta ya tashi Ta Kira Kacharalle yace mata yana kaduna wajen Uwar mata Bata da Lambar kowa sai ta Zuly kuma wayarta yana Kashe Ranta ya Baci Zuciyarta ta Fara zafi Tana Tafasa,Tashin Hankalinta kada wani Abu mara kyau ya Faru da Sa"adiya Ina Zata saka kanta,Ta Fara Nadaman barinta Hannun Zuly Domin Tana Tunanin da Hadin bakin Zuly komai ya Faru Daman Suna gabda shigowa Zaria ne nan tace ma Direban ya saki Motan ana Jiranta agida nan da nan kuwa ya saki Motar sai gasu sun iso Ta Shigo Gidan ma ba wanda ya sani Duk Tana Tsaye akayi Diraman Deezee da suby Batayi mamaki ba sanin Suby Daman bata kaunarta. Bata iya Cewa komai ba kawai kai ta Kada kai Bayan ta Dago Zaina Ta Share Mata Hawaye Tana Fadin"Ki daina kuka..Matukar Ina Raye Haka zan maidaki gaban Iyayenki ko kwarzane bai Sameki ba..!kai kuma Katon banza Sakarai Wlh sai na Kulleka sai ka gane da wa kake Zencen,ke kuma Karamar yar Iska ba zan ce Miki Komai Ki Saurari Mganar Uwar mata..Deezee nagode Sosai Sadiya Muje Ciki.." Ta Karishe Fada Tana kama Hannun Zaina Zuwa Dakin Har sun kai Kofar Dakin Daga Suby Har Shafsoon sun kasa mgana Saboda sanin Sholly zata aikata Suna Shiga Dakin Farida ta maida Kofa ta Rufe kaawai sai Wajen ya Dau Ihun Rufy da abokanta da su Abokan su Jido ran Shafson ya baci ganin Deezee ta kalleshi Ta saki Tsaki ta Wuce kawai sai ya Shake Suby Yana Fadin ta Biyashi Kudinsa ganin Zata mutu ne yasa Mazan Dake Gidan suka kwace ta ammh Fa Taci na Jaki Domin har Ta Taba 5k cikin kudin nan 15k kadai ya samu aciki Kuma ba wanda ya kwaceta Banda ma Dariya Da Busan Sigari Babu Abunda su Rufy keyi Duk Zaina da Farida na Daki suna Jinsu basu kara Fitowa ba. Koda suka Shiga Dakin Tambaya Daya Farida Tayi mata Taci Abinci tace mata eh..Sai tace ta koma ta kwanta Ita kuma Ta Fada Tiolet tayi wanka Tazo Tayi sallolin Dake kanta ta Sauya kayan Barci Ta kwanta Gefen Zaina Jin Motsinta Daman tasan Batayi Barci ba Tace"Kada Ki damu Cikin Satinan zamu bar Gidanan..Alhaji ya bani Kudi masu yawa Zuwa Gobe in kacharalle ya Dawo zai Samamin karamin gida na Siya mu koma Chan Hankalina zai Fi kwanciya Duk kuwa Daman da nasan Kafin Gobe Uwar mata baxata barki Ki Zauna mata agida ba.." Zaina Ta Juyo Tana Fadin"Saboda Mene..? Farida tace"Saboda Abunda muke Boyewa ya Bayyana..Ko nawa zan bama Uwar mata bazata Taba yarda ki Haihu manta agida ba..Ta Hana kuma Dokarta ce Duk wacce ta bari Tayi Ciki Zata Koreta saboda haka Ki Zama Cikin Shirin Na Riga na sani Tuni Uwar mata Ta samu Labarin Komai Daman ko Bata Kirani ba Ni zam Kirata na gayamata Tayi mganin Suby Shafsoon kuma Kilama Yan sanda sun kamashi Domin Tun Ina Mota nayi waya da Shugaban Headquater su na nan Sabon gari Zai gane Kuransa ne.." Zaina Tayi ajiyar Rai kafin tace"Allah ya kaimu..Ammh Tare da Zuly zamu Tafi ko..? Kai Tsaye Farida tace"A"a ke wannan Abun da ya faru bai baki Tsoro ba..!? Zaina Tace"Ba laifinta bane itama yaudaranta Tayi..Tace fa mganin Barci Ta bata fa Tayi ta Barci Tun dazu.."Farida tace"Uhmm..Ki kwanta sai da Safe."Daga haka ta Juya Baya Tana Jan Blanket Ganin kamar yarinta da kuma Girma Cikin Kudi suna Damun Rayuwar Zaina Har yanzu. ***** Washegari Tun Safe Sai ga Kiran Uwar mata Farida Bata Daga ba sai da ya katse ta Kirata da kanta bata ma bari Tayi mgana ba Ta Shiga Koramata Bayani kan Suby ta kuma ce ko Ta Kirata Tayi mata mgana Ko kuma Ta sakayata kamar yadda ta sakaya Shafsoon Tun Jiya jin Haka yasa Uwar mata tace Zata Kira Suby Taci Ubanta Tun kafin ma Uwar mata Tayi mganar Zaina Farida ta gayamata Zata Bar Gidanta Zata Siya wani Gida ta Koma Inda Sadiya Zata Haihu Cikin Salama. Uwar Mata Da Taji Haka Cikin Tashin Hankali tace"Harda ke kuma Sholly..? Ina zaki kuma Ai ita Ta Karyan Dokan ki barta Tatafi mana.."Farida tace"A"a Ba Laifi Tayi ba Nice mai laifin Domin Daman da Cikin na kawotq na kuma san da Dokar karki Damu Komawata bawai yana Nufin Rabuwarmu bane Ana Tare.."Uwar mata Tace"Ban yarda ba Sholly in kin Dage sai Kin Kula da wannan yarinyar naji ki Zauna nan da ita Har ta Haihun ina ce ba Shikenan ba..?tunda ke kika Zabar ma kanki Rumgumar Dan Gaba da Fatiha wanda ba"a san ma waye Ubansa ba.." Da Sauri Farida tace"Ba Dan Gaba da Fatiha bane Dan sunna ne Cikin Sadiya Kamar kowani D'a da iyayensa ke alfahari dasu mganar kumana zauna da ita anan ta Haihu bata Ayanzu ban yarda da kowa ba Bariki ce Gidan fa nazo kazo..Bazan iya zama ba Saboda Cikin Satinan Zamu sauya wajen zama Kada Ki damu zamu yi mgana ta waya. "Daga haka ta yanke Kiran Hankalin Uwar mata ya Tashi da mganar Farida tana ganin kamar in Tatafi ta Raasata kenan Hajiya Zabba"u ta gayama Komai ita kuma ta bata Shawaran Ta Kira Suby Taci Ubanta Tukunnah. Haka kuwa akayi Uwar mata ta Kira Suby Ta Zageta sosai ta kuma Gargadeta kan Sholly ta kuma ce Tayi Hankali ba Domin ita da yanzu Tana Sakaye kamar Shafson Hankalin Suby ya Tashi Jin Farida ta saka an kama Shafson sai ta Shiga Taitayinta Uwar mata kuma aranar da yamma Ta Shigo Zaria ita da Kacharalle Da Hajiya Zabba"u kan Farida kada ta koma wani Gidan da zama ammh suka gama mganarsu tace Tana kan Bakanta Uwar mata taji Tama Tsani Zaina Saboda tana ganin Zatayi sanadiyar Rabata da Sholly Saboda Haushi Ko Tsayawa Batayi ba ta bar Garin. Farida Ta gayama Kacharalle Tana son Gida shi kuma yace ta Bashi kwana 2 sai gashi kuwa an samu wani a gyallesu Tudun Wata Flat house mai 2bedroom da falo sai Kitchen da Tsakar Gidan da Farida akayi Ciniki da Dilallai Miliyan 4 ta Siya Cikin Lokacin Ta Biya kudin Gida aka bata Takardu suka zama nata Washegari kuma suka Tashi da kwasan kaya Mota Guda Farida ta saka Kacharalle ya samo ta kwashe Duka Kayan Dakin Harda kayan sawansu Da duka Abunda zasu Bukata Komai Farida Bata bari ba Zuly kuwa Daman Tun Washegarin Ranar da Abun ya Faru bayan ta Farka Daga Barcin Dolen da Suby ta sakata Deezee ta gayamata Abunda ya Faru Tana kuka Taje Dakin Farida Tana bata Hakuri Tana yi mata Rantsuwan Bata san Komai ba Farida dai bata wani yarda ba Zaina ce Uwar yarda da Tsausayi,Toh Bayan ma an kwashe kayan da yammah Farida ta saka Kacharalle ya samo Musu Golf da zasu Wuce acikinta Koda Zasu Tafi Babu wanda Farida Tayi ma sallama Kacharalle ne ya Daga Murya yace Shalele Hajiya Zatayi Hijira Ita Da Sady Shi ya Fito dasu Rufy Daman Adamalle bata nan Tabi wani Saurayin nata Hotel Service. Ganin Zasu Tafi ne yasa Zuly Ta Fara kuka Farida ta Tatafi da ita Har da Dukawa Tana Rokonta,Tana Fadin mata bata da kowa sai ita sai Allah Shafson ne Tunda aka sakosa ya haye Mota sai kudu Daman chan yake Zuwa Neman kudi Farida Bataso Tafiya da Zuly ba ammh Zaina ta Fara kukan Tsausayinta Tana Rokon Faridan su Tafi da ita Shiyasa tace ta Hado kayanta su Tafi Tare Zuly sai Murna kamar Zata Suma Irin su Deezee sun manta Murna Kuma suna Kewar Tafiyar Farida ammh banda irinsu Rufy da Suby Da kamar su Xuba Ruwa akasa su sha Har Kofar Gida suka Fito suna ganin Tafiyarsu Wasu na Jimami wasu na kuka sai da Farida Zata Shiga Mota ne ta Juya ta kallesu Ta Daga musu Hannu Tana Fadin Allah kaddara saduwa su Deezee ne da zeezee kadai suka amsa banda su Suby Ita kanta Zaina Tana ma Gidan kallo Karshe har kuma acikin Ranta Tana Fatan Daga Ita Har Farida sun bar kara Dawowa Rayuwar Gidan nan Harda ma Zulaihat din. Wasu na Daga musu hannu wasu ana agayas suka Wuce Kacharalle ne agaba Domin zai Rakasu Har gayallesu suna Zuwa Daman already Farida ta saka Kacharalle ya samo mata ma"aikata Maza sun Share Ko"ina sun koma Jera komai inda ya Dace sai Abunda ba"a Raasa ba,Kacharalle bai Dade ba ya Koma bayan Farida ta Cikashi da kudi da gargadin ko Uwar mata bata yarda yabama wannan adireshin sabon Gidanan ba yace Alqur"an ba wanda zai gayamawa kana ya tafi Bayan Tafiyar sa ne Zuly da Farida suka Zage suka kara gyara Wasu Abubuwan Dayan Bedroom din Daman Farida ta Siya wata katuwar Katifa 6by 7 tace nan Dakin Zuly Zata Rika kwana Dayan Bedroom din Data kwafa gadonta da wardrope da Sauran kayansu kuma tace ita da Zaina wacce ke zaune Tana Kallonsu Idanuwanta na Cike da kwallar Tsausayin kanta da Tsausayin Yan"uwanta Mata masu baro Gidajen iyayansu saboda wani kaddara. *Ki Biya ka karanta Cikin Salama...Amanata na baku..Kuma Amanata tana Wajen Allah..* *Janafty..* 7/17/21, 2:25 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣1️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Rayuwar Zaina a sabon Gidansu Dake gyallesu Rayuwa ce Datake kwatanta ta da Garinsu na Gada,Domin Rayuwa ce Cikin Sauki da Sakewa ba Fargaba babu wani Dar Dar babu Hayaniya Ballatana wani abun da zai Damesu Suna Rayuwarsu ne kai Tsaye kuma su kadai Kullum Gidan yana kulle ne ko Harka da Makota Farida bata yarda su yi shi ba. Uwar mata Taji labarin Tashin Farida ta Kirata awaya Tana nacin Jin ina ta koma Farida bata Boye mata ba ta gayamata Suna Tudun Wada gyallesu,Jin Dadi da kwanciyar Hankalin Uwar mata Shine da Ta Tabbatar da Farida Bata bar Harkan Bariki ba Domin bata kaunar Farida yau tace ta Tuba ta bar wannan Harkan Domin Babban asara ce agareta Gabadaya. Zaman Zuly agidan kamar wani Garkuwa ne ga Farida duk da Dai bata cika sakarma Zuly Fuska ba sai dai akwai Shakuwa da Fahintar juna tsakanin Zuly da Zaina,Yes kuma Faridan Tana Jin Dadin Hakan Tunda Tana Fita koda yaushe ta barsu su kadai agidan Tana Tunanin Inda ace ba Zuly batasan kuma wa zata Dauko Ta kular mata da Sa"adiya ba,Ammh Duk da haka Bata Saki Jiki da Zuly ba har yau Tana Tunanin wata Rana Zuly zata iya cin Amanarta Duk da Ta Rantse mata Bazata Taba Fadama kowa ba. Tun Dawowarsu Gidan yau da suke da Sati Daya da Dawowa Suna zaune afalo bayan sun gama karyawa da Safe Zaina na zaune kam Cafet sanye da Doguwar Rigar Cikinta agaba ta Mike kafa Zuly ta saka mata Filon Kujera Ta bayanta yadda zataji Dadin zama,Tunda kafafuwamta sun Kumbura Alamun Cikin ya Riga ya Tsufa. Farida na Cikin Bederoom Tana Shiryawa Zata Fita Kaduna zata je Alhaji Badamasi zai aiko da Direba ya Dauketa Tana ta Sauri Tana Daga Cikin Dakin Taji Zaina na Tambayan Zuly" Zulaihat yanzu Watarana zaki iya Komawa Gida..? Zuly Ta kalli Zaina Tana fadin"Me zai hana Sa"adiya..? Wlh zan koma sai dai Tunani ban san ina zan je ba Na Tabbata Inna Larai da Baffa bazasu karbeni ba,...."Zaina ta ggyara zama Tana Fadin"Me zai hana..? Zasu karbeki mana kuma ma ina kyautata Zaton Cewa zuwa yanzu sunyi Nadama kuma Allah ya nuna musu Kuskuransu na watsi da Rayuwar maraya ni yanzu Bukata gareki Ki Cire komai aranki Ki kuma yi Tuba ga Allah kan wannan Rayuwarki Kiyi istigifari ki kuma yi Niyyar Tsarkaka kanki Daga wannan Rayuwar kiyi Istibura"i Ki Tabbatar Tsarkin Na Dattin wannan Rayuwar da kikayi.." Zuly Ta Dukar Dakai Kafim ta Dago Idanuwanta sun cika da kwallah Tace"Nagode Sa"adiya..Daman ina ta Fargabane Shin In na Tuban ma Allah Zai karbi Tubana..? Zama na Dake yasa na karu da abubuwa Sosai,naji Dadi da kika gayamin Allah zai iya yafemin Duka laifukana,Daman Tun Tuni naji wannan Rayuwar Ta fita Raina sam Nayi Miki alkawarin na bar Rayuwar bariki har Abada.."Zaina ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Karki Damu Zulaihat Ina Tare dake..Duk Abunda kuma baki gane ba Ki Tambayeni zan Koya Miki..' Da sauri Zuly tace"Yauwa Ina son na Koya Hausa..Karatun Islamiya Harda Turanci ma Don Allah Sa"adiya zaki koyamin.."?Zaina Ta gyada kai Cikin Tsausayin Zuly Tana Fadin"karki Damu Zulaihat zan koya miki iya Abunda na iya Insha Allahu.."Zuly Taji Dadi Sosai Sai Murna take tana ma Zaina Godiya,Farida na Ciki Tana Jinsu Sai dai Ta Murmusa wata kwalla na Zubo mata Tayi Saurin Sharewa Ta Tuna mganar Zaina na Jiya da Daddare bayan ta Dawo Ta Cire kayan Jikinta Zata Shiga Tiolet tayi wanka Zaina ta kalleta Tace"Anty Farida meyassa bazaki bar wannan Rayuwar ba..? Sam bata dace dake ba..? Sai da ta kalleta Sosai kana ta kada kai Tana Fadin"In na Bar wannan Rayuwar wazai ci Damu..? Wazai kula Dake da Abunda ke Cikin ki..? Karki Damu dani Daman ni Tuni Wannan Rayuwar ta Dace dani Sa"adiya Kedai nayi ma alkawarin Zan kula dake da iya karfina Kuma alkawarin danayi Miki na maidaki gabansu Umma sai na Cikashi ammu barin wannan Rayuwar bata Taso ba Sa"adiya Ko saboda ke da Abunda zaki Haifa bazan zauna ba Dole zam Rika Fita ina Bada Jikina Domin samun Abunda zan Rike kaina dake da kuma Zuly Datake Karkashina.."Tana gama Fadamata Haka ta Shige Tiolet Tana Jin wani kuka yana Taso mata da Nauyin Kirji ba Domin Tana zuwa ganin Likita da yanzu Ciwon nan ya kwantar da ita ko ayanzu ba sai ahankali karfi hali kawai Take in Tana Tuna wani Abubuwan sai Taji bama Rayuwar data dace da ita sai Wannan Rayuwar Tunda Ta rasa Goggo Fatu Tayi Babban Rashi arayuwarta. Sai da Tagama Shiryawa Tsaf Ta Fito Dauke da karamar Jakarta da wayarta Tana Fitowa Falon ana Kiranta Ta Daga Tana mgana Zaina da Zuly suka Bita da kallo sai da ta gama wayar Zuly ta gaidata ta amsa Tana Fadin"Zulaihat ki kula da Gida da Sa"adiya ku dafa Abunda kuke so kuci Kafin na Dawo...na Tafi Kaduna sai anjima zan dawo.." Zuly Tace"Allah Dawo Dake lafiya..Ammh bazaki karya ba zaki Fita..? Farida ta yamutsa Fuska Tana Fadin"In naje chan zan karya..Sai na Dawo Sa"adiya.."Zaina ta Daga kai Tana kallonta Fuskarta ba Fara"a tace"Don Allah Anty Farida kada ki kwana achan ki Dawo da wuri.."Farida na Mirmishi sanin Fushin Zaina ta wuce Tana Fadin"Zan dawo...Ko saboda ke Sa"adiyata.."Ba Zaina kadai ba Hatta Zuly sai da ta Murmusa ta Fice Zuly ta Bita Ta Kulle gida Ta bar Zaina ta Lumshe ido Tana Tunanin Hanyar da zata bi Ta Raba Farida da wannan Rayuwar ammh bari ta Haihu Tayi ma kanta alkawarin yadda Farida Za zama garkuwanta itama sai Tayi Sanadiyar Rabata da wannan Rayuwar Data ke Ciki. ****** *Bauchi..* Zakiya ne Tana Tafe Bayan Tatashi Daga Office dinta Zataje Wajen Dina Domin Tun Jiya Da Daddare Ta Kirata Tana mata kukan ita tagaji da Cikin Jikinta kuma Tana Cikin Damuwar Saboda Kwatakwata Zain Bata gabansa Ko son ganinta baya son yi Tana Tunanin kada Wahalarsu Tatashi a Abanza Jin Irin mganganun Da Dina ke Fada ne yasa ta yanke Shawaran Zataje Ta kwantar mata da Hankali Duk da mutanen Gidan basu Bukatar Zuwanta Zataje ko saboda Dina. Sai da ta Biya gida Tayi wanka ta Sauya kayanta Kana ta nufi Gidan Abba Dake Gra Tana Cikin Tafiya Motarta Ta lalace,dole ta Daga waya ta Kira Garejin Datake kai gyara Direct da ogan Tayi mgana kan tana so a aiko mata da Yaro Nan Wajen Gra zai Duba mata Motarta nan take ogan yace yanzu zai Turo mata da wani yaro zai Duba mata Motarta ta Insha Allahu. Jin Haka yasa ta koma Jikin Motar Tajingina Tana Jiransa Tagama yanke Shawaran in yazo Zata barmai key Din Motar ne Ta hau Abun hawa ta wuce Tunda yammh Tayi Misalin 5:30pm na yammah ne alokacin,Tana ta Jiran wajen Shida Saura ta kara Kiran ogan yace Mata kada ta Damu yaron ya Taho yana Hanya Ranta bace ta kashe wayar ta Juya baya Tana Waige waigen ganin Ta Ina Wanda aka Turo zai Bullo. "Assalamu Alaikum Hajiya Barka da yammah.." Taji wata Sanyayyar Murya mai cike da Zaki da wani Gardi mai Harbawa da Shiga Zuciyar mai Sauraronta Cikin Sauri Zakiya ta waiwayo Tana kallon wanda yayi mata sallama ido Cikin Ido Suke kallon Juna Tuni Zakiya Taji gabadaya Jikinta yana saki kamar wacce Taga wani Abun mamaki Kallonsa Take Cikin Buguwar Zuciya Dana Gangar Jiki. Shi kuwa Kallonta yake yana Jifanta da irin Kallonsa da Kuma Mirmishin Dayasan yana Rudar da ya"yam mata komai ajin mace kuwa Ja"afar yasan Kallon da zai yi mata taji Abun yana Shiga Cikin Zuciyarta Har Tsakiyan kanta. Sanye yake da Riga da wando blue Na kayan Kanikanci Wadanda sukayi baki Duk bakin mai alamun kayan aiki ne Kafarsa Sanye da Takalmi Shaku Shaku Shima Duk yasha Baki da Wahalan aiki ammh Duk ba wannan ya Damu Zakiya ba Illah kyan yaron da kuma Tsabar Haiba da kuma Wani irin kwarjini Dayake  Dashi wanda yasa Ta kasa Dauke Idanuwanta akansa Bata san Dalilin Daya sa Zuciyarta Take Bugawa Tana Tsalle Waje Daya in Tana kallon kwanyan Idanuwansa ba. Farin Namiji ne Dogo gint Karkkarfa Mai Dauke da Dogon Karam Hanci mai Dauke da Sexy eyes,sai Bakinsa karami mai Dauke da Pick lips,Doguwar Fuskar garesa kana mai kallon Farko Zaka Fahimci Duk inda ya Fito ya Hada Iri da Fulanin asali Ko kuma Shi din Ruwa Biyu ne kyakyawa ne ajin Farko Ya Dace komai Daman an ce Mutum Tara yake bai Cika goma ba ammh acikin Zuciyar Zakiya Tana ayyana wannan Zankadeden Saurayin ya gama Samun Goman Cif Cif a bangaran kyau da Zati. Ta Shagala da kallonsa Yana ta mgana Bata Jisa ba sai da ya saka Hannu ya Kada mata a saman Fuskarta kana ta Dawo Cikin Hayyacinta Firgigit Tayi Tana kallonsa sai kuma taji kunya Tayi saurin kauda kai Mirmishi yayi kafin yace"Hajiya nine wanda oga Usman ya Turo..Ina ne mtsalan bari na Duba Miki.." Yafada Cikin Sanyayyar Murya Daburcewa Zakiya Tayi ammh Tunda tasan kan Duniya sai ta wani Rausayar dakai Tana Bashi Key din Motar Tana Fadin"I don"t know..Kawai Ina Cikin Tafiya sai ta tsaya kum nayi nayi tatashi Sai kuma Taki Tashi.."Tafada Tana kallonsa Shima kallonta yake kafin ya karbi Key din Yana Fadin"Ok...Bari naDuba.." Daga Haka ya Bude Murfin Motan yaShiga ya Tada ita yana Dubawa Zakiya na GefeDuk wani Motsinsa Tana gani Gabadaya jikinta ya saki Idanuwanta sun kasa Dauke Ido daga kan Wannan Saurayin wanda Ta Tabbata ta Girmeshi Domin in yayi Shekaru bai Wuce Shekarun Sahura Kanwarta. Daga Cikin Fiton ya motan Ya Daga gaban Motan yana gani Duka Tana Tsaye Tana kallonsa Kayan aikinsa ya Fito Dashi ya Fara gyara kenan ya gano Mtsalan Saboda Shagala da kallonsa sam Zakiya ta manta Shawaran na Tafiya tabar mai Motar Cikin 30min Sai gashi ya kamallah gyara ya Rufe mata gaban Motan ya Shiga Motan ya Tasheta sai gashi Tatashi Tana Tsaye Taga yayi gaba kadan kana ya Dawo Baya ya Kashe Motar ya Fito Zuwa gareta Key din ya Mikamata yana Fadin"Hajiya ga key...An gama gyaran da yardan Allah.." Zakiya Ta kalleshi kafin Ta saka Hannu Ta Karbi key din Tana Fadin"Yauwa Nagode..Nawa zan baka kudin gyaran naka..? Kai ya sunkuyar kafin yace"Ah Bakomai Hajiya wannan gyaran ai bamai yawa bane ki barshi kawai.."Galala Zakiya ke kallonsa kafin tace"Haba dai Taya zan saka aturo ka kuma sai kaki karban Kudinka.? Ai Hakkin kane ya kamata ka karba Don Allah.."Tafada Tana Zaro mai yan Dubu Dubu Guda Biyar Daga Cikin Jakarta Kin Karba yayi sai ta matsamai kana ya Karba yana ta mata Godiya yana Shirin Hawa Mashin Haya,Tace kada ya hau ya bari ta maidashi Garejin Ba yadda ya iya Haka taDaukeshi agaban Motarta Zuwa Chan Garejin nasu Bata Shiga ba Daga Bakin Garejin ta saukesa Bayan yayi mata Godiya zai sauka kenan ta kalleshi Wanda Daman Tunda ta Daukoshi Take kallonsa Shima Daya Lura da haka sai ya Dinga satan kallonta da wadandan Idanuwan nasa. "Me sunanka..?kai dan nan garin ne..?kai yagirgiza mata kafin yace"Sunana Ja"afar Ni Dan asalin Garin Yola ne.."Zakiya ta Jinjina kai kafin tace"Ja"afar Nice Name...Kana da waya ahannunka..?bai mata mgana ba ya saka Hannu a aljihun wandonsa yaFito da Wata karamar Nokia Duk taci Ubanta yana Fadin"Eh Ina da ita gata ma.."Zakiya Ta kalleshi Cikin Tsausayawa ganin ga Namiji Har Namiji ammah Babu abokam Rayuwa,Wayarta Ta Ciro Dake cikin Jakarta Ta mikamai Tana Fadin"Sakamin Lambarka.."Cikin Sanyinsa ya karbi Wayar ya saka mata Lambarsa Yana Mika mata wayar ta Karba Tayi Saving din Lambar ta Kirashi sai ga Kiran ya Shigo Sai ta katse ya kalleta yana Fadin"Wani suna zan saka Hajiya..? Zakiya na wani Mirmishi Tace"Zakiya zaka saka.."Cikin Sanyin Muryansa yace"A"a Hajiya Zakiya dai.."yafada yana wani karya wuya kai ta Girgizamai Tana Fadin"No..Zakiya dai zaka saka ni ba Hajiya bace..Ko Hajiya nake awajen Ja"afar ai ba Hajiya nake ba Zakiya ta nake ko..? Ta Fada Tana kashe mai Ido Daya sai ya wani Daburce kamar bai saba gani ba ya Bude Murfin Motan ya Fice yana Fadin"Nidai Hajiya Zakiya zan saka..Waye Ja"afar Dake bazaki zama Hajiyarsa ba..? Kai kawai Ta kada kafin tace"In na kiraka zaka Daga Kirana.? Kansa ya Leko Dashi Ta Glass din yana Fadin"Me zai Hana Hajiya..? A shirye nake dana amsa Dukkan Kiranki Insha Allahu.."Mirmishi Ta sakarmai Tanakallonsa kafin tace"Nagode.."Hannu ya Daga mata itama Tadagamai kafin Taja Motar ta Tayi Riverse ta koma Kan Hanyarta na Zuwa Wajen Dina Ja"afar Dake Tsaye ya Bita da kallo Lokaci Daya yana Shafa Siraran Gemun da suka Fito Allah kadai yasam Abunda yake sakawa acikin Ransa game da Zakiya. Zakiya Tana Shiga Falon su Umma ana Kiran Sallar mangariba Kusan tare suka Shiga da Zainab Cikin Sabuwar Motarta Itama 306 wacce Abba ya Siyamata ta Dawo Daga makaranta sai ta Biya Islamiyan su Sauda ta Daukosu Kallon Kallon sukayi ma Juna Tsakaninta da Zakiya ba wanda yayi ma wani mgana kuma kusan Atare suka Shiga Falon Gidan Nene ce kadai Zaune afalo Tana kallon Tashar africa Tv,Umma ta Shiga Dakimta Zatayi Sallah da Gudu su Saudart suka Nufe Nene Dake musu oyoyo,Zainab kuma ta Zauna Kusa da ita sai Lokacin Nene Taga Zakiya gaisheta Zakiyan Tayi ta amsa Fuska ba Fara"a Kafin Tayi Shuru Tana Tsaye ganin haka yasa Nenen Tace ta Shiga Ciki Dinar Tana Cikin Jin Haka sai ya bata kwarin Gwiwan Tashi Ta Nufi Dakin Dinar Nene da Zainab suka Bita da wani Sakaran kallo. Tana Shigewa Dakin Zainab TaRakata da Tsaki Tana Fadin"Wlh Nene na Tsani ganin Dinar nan agidan nan wai bazatayi ta Haihu bane ta kama gabanta ba Kowa ma ya Huta..? Nene tace"Ko ta Haihu ba gabanta Zata koma ba Gidan Yayanku zata koma Zainab..Ya muka iya Wannan Abubuwan da suka Faru sune kam namu kaddaran sai Fatan Allah ya Tsaremu kawai Allah kuma ya Sauketa Lafiya,sai a daura musu auran Tatare gidan yarona Ina ce ba komai ya kare ba..?Zainab Ta kada kai Tana Fadin"Umh...Yanzu Nene shikenan Har yau ba Labarin Anty Halima ko..?ko yau sai da mukayi mganar da kawarta Anty Laila bayan mun Hadu a masallacin Cikin makaranta baki gani ba Nene Wlh sai Sharan kwallah take muna mgana Yau.." Nene ta Sauke ajiyar Zuciya Tana Fadin"Uhm..bari kawai Zainab...Muna yau mukayi waya da Goggo Halima Daga Chan Gada suma sunaTsumayin jin wani Mgana Daga garemu muma Shuru ne Zainab Mukam bama Cikin kwanciyar Hankali Ballatana yarona da kullum yake karewa a tsaye kamar kudin Guzuri saboda Batan Halima,sai dai kamar yadda Alhaji Tsoho yace addu"a ne kadai mganin Komai Insha Allahu mu Cigaba da gayama Allah Halima zata Dawo Cikin Koshin Lafiya.." Zainab Tace"Allah yaso ya kuma yarda Nene..Zafeera ma yau munyi mgana Ita kanta ga karatu ga Damuwa Nene.."Nene tace"Ai ba ita kadai ba Duka Ahalin gidan ne Sai dai mu Tayata da addu"an Allah yasa ta Fada Hannu nagari yasa koma Tsakanimmu akwai Rabon ganawa.."Zainab ta amsa ta Ameen kafin ta tashi Ta Shiga Ciki su Saudart ma Nene ta kadasu Suje suyi sallah ita Tana Hutu Shiyasa kuma sun gama Girki Tun dazu ita da Umma. Zakiya kuwa na Shiga Dakin Dina Ta ganta zaune saman Cafet ta Mike kafafunta da suka kumbura ga Tulalen Cikinta wanda ya kumburata Ta zama wata iri da ita Fuskarta Tayi kwaba kwaba komai ya Bude na alamun Ciki fa ya Tsufa Zakiya sai Da Taji Tsausayin Dina kusa da ita ta zauna Tana Jera mata sannu Cikin Taruwan Hawaye Dina Tace"Zakiya anya Ban kai kaina Cikin Mutuwa ba kuwa..? Kalli yadda Cikin nan ya maidani fa.? Zain baya kallona Sai nayi Sati ban sakashi acikin Idona ba Wlh bai Taba tako kafarsa Dakin nan ba sai sau Daya Indai Ina son ganinsa sai na Daidaici Lokacin Fitarsa Da Safe na Leka na ganshi ammh bai Taba mim kallon arziki ba Ballatana ya Tuna da Abunda ke Cikina.Anya Zakiya Ina Tunanin Komai namu bazai lalace ba kuwa..? Ina aikin da Boka yace yayi mana banga alaman har yanzu zain yana Sha"awata ba koda zamu Tsarkake auranmu ai kulawa yabawa ko..? Zakiya Tagumi tayi Tana kallon Dina Domin sai alokacin Ta Fahimci Irin Zafin da Dina keji acikin Zuciyatta game da zain Domi itama yau kadai data Hadu da Ja"afar yagama Tafiya da Zuciyarta Ashe haka Dafin so yake ita ta Fada Tundaga ganin Farko ganin Kamar Zakiya bata Ma san me take Fadi bane yasa ta Zungureta Tana Fadin"Kina Jina kuwa..? Sai Lokacin Zakiya Hankalimta ya Dawo kan Dina ta kalleta Tana Fadin"Najiki Dina..Ina Auna Dacin Da kike ji acikin Ranki ne wanda yau kawai na Tsinci kaina aciki yaya Zan kare Watarana Kuma..?Dina Tayi mata kallon Mamaki kafin tace"Topha Bangane ba..? Zakiya Ta gyra Zama kafin tace"Kema kinsan Dole na samar dake komai..ammh kafin nan bari muFara da naki Mtsalan yanzu dai menene Damuwarki Dina..?Ga ki acikin Gidansu Zain fa Ga Cikinsa ajikinki kuma Insha Allahu nan da wata Biyu zaki Haihu a daura muku aure da Zain,me kuma kike nema ahalin yanzu..? Dina Ta batarai Tana Fadin"Zain nake so kuma nake Muradin mallaka Zakiya ai kema kin sani..? Zakiya tace"Mallaka ta nawa kuma..?banda wacce kika mallaka kuma zaki kara mallaka nan gaba kadan.."Dina Tace"Ba wannan ba..Ni ban mallaki Zain ba Zakiya kuma bana Hangi mallakansa nan kusa Baki ji me nake Fada Miki bane ya Tsaneni faKo kaunar ganina Bayayi haka ne mallaka Nifa burina na Samu Zain Daidai da yadda nake so ya Soni ya Kaunaci kwatankwancin Yadda nake sonsa koma yafi haka ya nuna yana Sha"awata da son kasancewa dani kamar Baya.."Zakiya tace"Tab..Kema kinsan ai haka bazai Faru ba Dina Ba Soyayyar Zain kike son mallaka Shi kikesn Mallaka kuma na Taimaka miki Komai ya kusa Zuwa Karshe..Ai Tun abaya nagaya Miki Zaim bazaki Taba Samun Soyayyarsa ba Mace Daya ya baiwa Kuma Halima ce.." Dina tace"To yau ina Haliman inace bata Shiga Duniya ba wama ya sani Ko batama da Rai.."Zakiya tace"Kada kiyi Fatan Halima ta mutu..Kiyi Fatan aganta ta kuma Dawo Gida In ba Haka ba Har Abada baxaki samu kyakyawan kallo Daga Zain ba Daga ke har Shegen Cikin ki kuwa.."Ran Dina ya baci ta kalli Zakiya Tana Fadin"Bangane ba..? Zakiya Tace"zaki gane ne nan gaba..Alokacin da Zain zai Dankara Miki saki bayan anyi auran Domin bazai kara yarda yayi ma iyayansa gaddama ba Ki sani Halima itace Rayuwar Zain da duka ahalinsa Rashinta Tamkar rasa wani Gibi ne kuma yanzu ke yake kallo asilan komai Saboda haka Fatan ta Mutu ma bai taso ba Wlh kanki kawai kike sokama Wuka kina Kirari.." Dina Tayi Shuru Tana wani Tunani kafin tace"Naji..Ammh Ina son ki komamin Wajen malamin nan."Zakiya tace"Shikenan Zanfara gayamai ta waya yadda mukayi zaki Jini...Allah ya saukeki Lafiya ya mganar da mukayi a waya Ummi Maimun din zata zo Har Ki Haihun ne..? Dina Tace"Eh..haka Dady ya gayamin kuma itama munyi mgama da ita tace Watan Gobe zata zo.."Zakiya tace"Naji Dadin haka..Domin ni ban yarda da Iyayen Zain ba kada su kashe Yaron Tun Ranar da yazo Duniya.."Dina tace"zasu aika Musamman ma Uwarsa da wannan Shegiyar kanwar nashi.."Zakiya tace"Bar yan kutumar Uba Ta Allah batasuba suna ji suna gani Zamu yi auranmu Wlh.." Dina Ta kalli Zakiya Tana Fadin"Zamu auranmu kuma..? Zakiya tace"Yes..Nima na samu MrRight dina Insha Allahu kinayi aure Nima zanyi.."Dina tawashe baki Ta bata Hannu suka Tafa Tana Fadin"Bani nasha Shegiya kice kin Fada.."Zakiya na Dariya nan da nam ta kwashe komai ta gayama Dina Ta karishe Da Fadin"Ban taba sanin Haka so yake ba sai yau Dina..Zuciyata na Bugawa Saboda Ja"afar kuma nayi Dace na samu Daidai da Ra"ayina bashi da Kudi ammh yana da kyau sosai kashe mai kudi In aureshi Yarone wanda bai san Komai ba ba gane komai zai yi ba.." Dina Ta kara bata Hannu suka tTafa Tana Fadin"Dakyau Tawan..Gaskiya Tsarinki yayi fa..Kinga Shikenan kin samu Dami akala kawai.."Zakiya tace"Kwarai makuwa.."Dariya suka saka ma juna kafin su Cigaba daTattauna Zakiya na gayama Dina Zata kaishi Har kano Wajen Baba in suka gama Daidaitawa Tunda ta Lura kamar yaron yana da Saukin kai kuma Zata bashi Kudi Kudi kuma Babu Abunda basa kawowa. Zakiya Batayi Shirin Tafiya ba sai Pass 9pm suna Hira ko Salla ba wacce Tayi Tunanin tashi Tayi Bayan tayi sallama da Dina taRakota Zuwa Falo Saboda Cikinta yayi nauyi Daman Haddir yace mata ta Dinga MotsawaTa Daina zaman waje Daya Ta Rakota Falo kenan ba Kowa Su Umma Kowacce Tana Dakinta Sai ga Zain ya Shigo ya Dawo Daga asibiti sanye Cikin Suit black and White,Coat dinsa da wayarsa Hade da key din Motarsa suna Hannunsa ya Shigo Falon sai suka ci karo Gabadayansu kallo Daya yayi musu bai kara ba Zakiya tana gaisheshi yayi kamar bai jita ba da Sarsasarfa ya Karisa Dakinsa ya Banko Koda Daga Dinar Har Zakiya da kallo suka Bisa kafin su koma su kalli Juna Zakiya ta Jinjina kai Tana Hango Tsana mai yawa Daga Idanuwan Zain akan Dina Bata Fatan Hakan ta Faru ammh Zata Kira Mallam Taji da Haka tayi ma Dina sallama ta Fice ta Shiga Motarta ta Bar Gidan Tana Tunanin Ja"afar Domin har ga Allah yanzu ba Tunanin mafitan Dina bame agabanta Tunanin yaya Makomar kanta take domin a Hakikanin gaskiya Ja"afar ya Tafi da Duka Imaninta. *Ki biya ki karanta Cikin Salama Hajiya...!* *Janafty...* 7/19/21, 2:11 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣2️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Ranar Zakiya Dakyar ta iya Yin Barci Saboda Tunanin Ja'afar Daran nan gabadaya Tayi shine Cikin Tunaninsa da kuma Son ganinsa,zakiya tun adaran Jiya Tagama yardan ma kanta ta Fada Tarkon son Ja"afar wanda kuma yayi mata Mugun kamu. Washegari Idanuwanta Luhu Luhu Ta je wajen aiki Saboda Rashin Barci,Office din ma Tadai Zauna ne kawai ba domin Tana Cikin Hayyacinta ba Wuni Tayi Tunanin Ja"afar Data Runtse Ido kallonsa Yake Dawowamata Cikin Xuciyarta yana Sarrafa gangan Jikinta kamar Tana gabansa. Ganin Bazata iya jurewa bane yasa karfe 2:30pm na Rana ta bar Ma"aikatan su Zuwa Garejin su Ja"afar saboda ta ganshi Tana Zuwa kuma sai taci Sa"a Shi Ta Fara gani yana gyaran Wata Mota Tana ganinsa Ta Shiga Washe mai baki,shima Sai ya sakarmata Mirmishi Wajen ogansu Ta Nufa suka gaisa saboda Taji Labari Daga bakinsa yasa ta Fara mai Godiya Tana yaba aikin Ja"afar din nan yake gayamata Yaron bashi da wata mtsala,Sabon Zuwa ne bai Dade yana aiki Tare dasu ba,Maraya ne bai da uwa bai da Uba Taji Abunda take son ji bata Dade ba Tatafi Batayi ma Ja"afar din mgana ba ammh Shi ya gaisheta Ta amsa Farinciki na Cika Ranta Ta ganshi sai taji ta samu Sauki Haka ta koma Gida tana sakawa Tana warwarewa Tana ganin Ta Samu wanda ya Dace da ita Zata Jarabashi Tagani Indai irin wanda Take Muradi nezata sakarmai kudi Ta kuma Bayyanamai Bukatarta Ta Tabbata bazai ki ba. Da wannan Shawaran Tayi amfani ta Fara Kiran Ja"afar ta wayarsa suna gaisawa shi kuma ya kwantar dakai yana Bata Girmanta,Yana Nuna mata Kamar wani Sakarai wanda bai san Duniya ba,Zakiya Bata iya kwana Bata saka Ja"afar acikin Idanuwanta ba Shiyasa bata iya kwana Bataje garejinsu ba Koda Daga Nesa ne zata Tsaya ta gansa Taji Dadi Duk Abunda take yi Ja"afar yana sane da ita Ya kyaleta ne Domin ya Riga yagama Dana mata Tarko kuma ta kama kaf Labarin Zakiya a tafin Hannunsa yake Daman kuma Yasan bazai Tamai wahalan Fadawa Tarkon Daya saba Danama yanmata ba Ashe Rabon samun wannan Hajiyar ne ya kawosa Bauchi Lalle kakarsa ta yanke Saka. Gabadaya Tunanin Zakiya da Duka Rayuwarta ta koma Wajen Ja"afar ne da yadda zata Tsara musu Rayuwa mai kyau tama manta da Mganarsu da Dina sai da Dinar Ta gaji Da Jiran Kiran Zakiyan ta Kirata Tana kara Tuna mata,Sai alokacin Zakiya ta Tuna Bayan sun gama wayar sai ta Kira wayar malamin Tamai mganar ta kuma Sanar dashi Halin Da ake Ciki yace ta bashi kwana Biyu zai Bincika yagani komai ake Ciki zai Kirata ya sanar da ita. Aikuwa Bayan kwana Biyu sai ga Kiran Malamin bayan sun gaisa ya koramata Bayanin Abun yagani ya sanar da ita Yanzu zain yafi karfinsu Domin Kakansa ya Tsaya akansa kuma Shi kanshi yanzu ba zaune yake ba ya Mike da addu"a Dare da Dara ga sadaka da kuma Saukan Karatun Dayake sakawa anamai Tuni Sihirin Jikinsa ya lalace kuma ya gayamata ko an sake mai wani da wahala ya kamashi Mganar auransu da Dina kuma Da gaske ne yaga auran sai dai acikin Auran yaga Duhu sosai,Kuma Daga baya sai yaga Haske Tare da Tauraransa na Farko wanda yazo ya Tunkude Tauraron Dina baida Masaniya kan Abunda zai Faru agaba Ya kuma gayama Zakiya Ayanzu Zain ba wacce ya Tsana sama da Dina Zuciyarsa Daman bai Taba sonta ba asiri ne ke Dawainiya dashi yanzu kuma ya Lalace Jin wannan Labarin ya sanyayama Zakiya jiki Bata iya gayama Dina Haka ba Saboda Bata so Ta tashi Hankalinta itama kuma Ta Tada mata da nata Hankalinta,Sai kawai tace mata yace da Zaran ta Haihu aka Dauran auran komai zai Dawo Daidai da wannan mganar Dina Taji Hankalinta ya kwanta Batare da tasan me Zakiyan ta Boye mata ba. Sati Biyu da Haduwan Zakiya da Ja"afar ta riga tagama Tsara Yadda Zata Jaraba Ja"afar tagani Tunda Zuwa Lokacin Tagama yarda ma kanta Ta Fada Kogin Sonsa mai Tsanani wanda bazata iya Rayuwa bashi ba. Weekend ne Ranar Lahadi bata je aiki ba Tun safe ta shiga kasuwa Tayi Cefene,Tazo Tayi Lafiyayyan Girki da Lemukan sha Ta tsala wanka Taci kwalliya Da Damammun kaya Wadanda suka Fitar mata da Suran Jiki tayi Barin Turare ajikinta,Bayan mangariba ta Kira Ja"afar tace Ko zai zo Gidanta akwai mganar Datake so su Tattauna Cikin Ladabinsa yace mata Zai zo in yagama gyaran Dayake a garaje yabiya inda yake kwana yayi wanka Ta Turomai Adireshin Gidan nata Cikin Rawan Jiki ta Turamai Shiko Lokacin yana Cikin garejin Daman nan suke da Daki suna kwana Shida sauran kananun Kanukawa da basu da Gidan Iyaye nan kusa. Wanka yayi ya sauya kaya Zuwa Riga da wando duk sun Muje Na gwanjo ammh kuma suna wamke Tas dasu Mashin ya hau Zuwa Gidan Zakiya yana Isowa ya sallami mai mashin din kana ya Kira Zakiya yace mata gashi ya iso tace Gatanan Zuwa ba Dadewa sai gashi ta Fito Tana wani Rangwada da Rangaji Kamar wata Tarwada,Tun Daga nesa yake kallonta Cikin Mayen Kallo da wani Sha"awa har yana Sude baki acikin Zuciyarsa kuma Allah ne kadai yasan Abunda yake kullawa Tana karisowa ya Sunkuyar dakai Yana gaisheta bata amsa ba ta riko Hannunsa Zuwa Ciki ya Shiga Binta kamar Rakumi da akala. Har Cikin Falonta Takaishi Bayan ta Rufe kofar Falon kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta zaunar dashi kana ta Koma Kitchen Tana ta Jera mai abincin Data Hadamai Bisa karamin Center Table din Dake gabansa Bayan Tagama tace mai Bismillah ya Fara Nokemata yana Jin kunya Zakiya ta Zauna gefensa Tarika Diba Tana bashi abaki Da Farko kin karba yayi sai da Zakiya ta bata rai kana ya Rika Bude baki Cikin Tsoro yana karba ya Takure Waje Daya kamar ace Kai ya Zura da gudu. Sai da Ta Tabbatar daya Koshi kana Tattara komai ta maida Kitchen Tana Dawowa Ta Haye kan Cinyarsa ta Fara Shafashi Kota Ko'ina Cikin kwarewa da Bariki Tuni Jikinsa ya Fara Bari yana Kokarin Kauce mata ta Riko Fuskarsa Cikin Tafukan Hannayenta Tana kallonsa kafin ta Sumbaceshi saman Lebensa Tana Kokarin Hada Bakinsa da nata ne ya Daddage ya Tureta Sai da ta Fadi Gefen Kujera ya mike da Sauri yana Goge Bakinsa Cikin Sanyin yace"A'uzubillahi Haba Hajiya Zakiya me kike yi ne haka..? Karki manta ni ba Muharran minki bane bai kamata ki kebance Dani har kina Tabani ba wannan Haramun ne.." Yafada yana wani kauda ido Cikin Jin Dadi Zakiya ta mike Tana kallonsa Tana Kokarin isa Gabansa ya Daga mata Hannu yana Fadin"A"a kada ma ki kariso kusa dani  ni bakowan kowa bane face Takala bakanike mai gyaran Injinan Motoci Ina Kebe kaina Da Haramun Tunda dai Abun ya koma Haka kada ki kara Gayyata ta Gidanki indai kinsan Ba abun alhrri ne acikin Zuciyarki ba.."Yana gama Fadar haka ya Bude Kofa ya Fice da Sauri Zakiya Tana Tsaye Tana Binsa da kallo Farinciki ya Cika Zuciyarta Yana Fita Ta Koma kan kujera Ta Fada Cikin Farinciki Tana Fadi a fili"Allah nagode maka na samu irin Mijin Da na Dade ina jira.." Bata Damu da Fushin sa ba ballatana Tafiyarsa ba Daman Abunda Take son gani kenan ta Tabbata da yaron dan Hannu ne bazai gujema Tayinta ba Sai gashi ya nuna mata shi na Allah ne Taji Dadin haka,Lalle Zakiya Kina Nufin zaki ma Allah wayau ne..? Uhmm Bata Nemeshi Washegari ba sai da yammah tayi ta Kiranshi awaya bai Daga ba sai da Tatashi aiki Ta Bishi Chan garejin ta sameshi,Tayi ta bashi Hakuri Tana gayamai ba Nufinta kenan ba kawai Ta Jarabashi ne,dakyar ya Hakura yaran garejin Harda ogan nasu Suna ta mamakin Shige da Ficen da Zakiya Take wajen Ja"afar sai dai sanin Ja"afar don akwai kyau da kuma Haiba Kodomin haka yana Jan hankalin yanmata Da kyansa Zuwa Garesa. Da Daddare ta kara Gayyatan Ja"afar Zuwa Gidanta sai dai wannan karon Harda babban mayafi ta sanya Ta Rufe Jikinta Bayan Ta gabatar da abinci yaci kadan sai ta Fara Tambayansa Tarihin Rayuwarsa Shi kuma ya gayamata Cewa Shi Maraya ne bashi da uwa bashi da Uba yataso hannun kakarsa Wacce Ta Rasu Shekaru Biyar da suka Gabata Shine Dalilin Rasuwarta ya Shiga gararin Rayuwa Har Lagos yaje yayi Bin Mota yayi Faskare da saida Icce ayadda yake gayamata Basu da wani Dangi Shiyasa Rayuwar Tataso sai ahankali Har Allah ya kawo shi Garin Bauchi ya Hadu da wani saurayi shi yayi mai Hanya Zuwa wajen ogansa mai Garejin gyaran Motoci Har ya Daukesa yana aiki Dashi Zakiya Ta Tambayeshi ko yayi karatu yace mata iyakarsa Secondary Taji Tsausayinsa Sosai Harda mai Hawaye Daga karshe tace kada ya Damu Insha Allahu Zata mai Komai yake so arayuwa,Jin haka yasa Ja'afar yasa ya Dinga ma Zakiya Godiya Kamar ya kwantamata Tace kada ya Damu ya Dade agidan suna Hira sai Wajen 10pm ya Tafi Washegari kuma ta kama Jumm"a ne bayan an sauko Daga Masallacin Jumma"a Zakiya Tabiya Gareji ta Dauki Ja"afar ta kaishi Babban Shago Ta Jidan mai kaya kama Daga na sawa Takalma Agogo Kananun kaya da manyan kaya wanda Basu Dawo ba sai da suka Biya aka aunasa Ta bada dinki Ta kuma kaishi Shagon Saida waya ta Siyamai Waya mai kyau da Tsada babu Abunda Zakiya Bata Siya ma Ja"afar na gayu ba Daga Ciki Har Waje so Take ta Fito Dashi Ta kuma Nuna ma Duniya Mijin da Zata aura Shima ya isa kuma yakai Bayan nan kuma Ta kama mai Hanyar wani Gida nan kusa da Anguwan Datake zaune Ta Cikamai da kayan alatun Rayuwa Tace ya Dawo nan da kwana mganar aikin kanikanci kuma Tace karya Kara Komawa Tana da kudin da Zata Rikesa ogansa kuma Daman ta Riga Ta gayamai auransa Zatayi Ja"afar din bata gayamawa ba ammh Har samarin da suke kanikancin Tare sun san da Labarin wasu da yawa suna Taya Ja"afar murnan ya Tsinci Dami a akala Duk da bai Dade da Zuwa garin ba. ******* Yau Abba bai Dawo Gida da Wuri ba ya biya ta gidan Alhaji Tsoho ya gaishesa Shida Hajiya Mama ya kwana Biyu bai lekasu ba chan yayi mangariba yayi Isha"i Sai ga Zain da Haddir sun Shigo suma bayan sun gaisa ne da Abba zai Wuce sai suka Fita Tare da Zain din Ko agidan Alhaji Tsoho mganar Dayane kan Zain ya Cire Damuwa Halima addu"arsa take Bukata Damuwa Tana Bayyana akan Fuskarsa Duk ya Rame ya lalace kamar bashi ba Inda Allah ma ya Taimakesa Zuwa asibiti da Duba marasa Lafiya na Debemai kewa ammh Kowa yaga Dr Zain yasan Yana Cikin Tashin Hankali da Rashin Natsuwa. Bayan sun Dawo sun Dade aharaban Gida suna mgana da Zain da Abba,Abba yana mai Nasiha da kuma Jan hankali kan ya yarda da kaddara Tunda Shi Musulmi ya kamata ya Zama Jarumi Akan wannan lamarin,Zain dai yana jin Abba ne kawai ammh Tayaya Firstlove tabar Gida Dauke da Cikinsa baisan wani hali Take Ciki ba kuma ace ya zauna Cikin kwanciyar Hankali wannan ai bata yuyuwa Dole ne ya mike Tsaye Kan Jiki kan karfi Ko Allah zai sa adace Shiyasa Duk masallatan Jumma"an Dake garin Bauchi ba inda bai kai Neman addu"a ga Halima ba Da Fatan Allah ya bayyanata. Atare Uba da Dan'sa suka Shigo Gidan Umma da Nene dake Falo suka Tarbesu,Zain ne ya dan Zauna afalon yana wasa Da Saudart da Junior Abba kuma Ciki ya Shiga Nene tabi Bayansa Zain kuma Bai Dade ba ya Tashi Zuwa Cikin Dakinsa Umma ta saka Zainab takai mai abinci ko Ijiye Farantin batayi ba yace ta maida Baya Bukatar cin wani Abu Tana Fita ba Dadewa sai ga Umma da Kanta Ta Dawo Dashi Ya shirin Shiga wanka ne Yaji Shigowar Umma ya Dago yana kallonta Dauke da Farantin Abinci bai samu Zarafin mgana ba ta Ijiye nan saman Cafet din Dake Dakin Tana Fadin"Zainullahi Yanzu ace Fisabillahi Haka zaka Dinga zama baka cin Abinci..? So kake wani Cutar ta kamaka ta kwantar dakai tayi maka illah..? Wa gari ya waya in aka wayi gari Haka ya Faru..? Zain Ya Sunkuyar dakai kafin yace"Ba haka bane Umma..Kawai Bana jin Cin komai ne Nasha Tea a office Dazu.."Umma tace"Tea ne kadai zai rike ka..? Ina fa Lura dakai baka son cin Abinci in banice ko Nene muka matsa maka bafa..Hakuri zakayi mu kam muna Cikin wannan Damuwar na Rashin Halima ammh ka sani addu"a itace mafita Tunda Damuwar bazai Dawo da ita ba Face Allahn da zamu kaima kukan mu Shi zai Bayyana mana ita Cikin Koshin Lafiya da yardan Allah.." Zain Dayaji kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun kala sunyi Jajir,jijiyoyin kansa sun Tashi Radau yana jin wani Suya acikin Kirjinsa ya kalli Umma araunane yana Fadin"Umma Ni Damuwata Ina Firstlove ta Shiga..? Rashin Sanin Wani Hali take Ciki yana sakani Shiga Damuwa Uwa uba kuma Umma Ciki gareta Cikin Fari Umma Zaina Duka Nawa take..? Zata iya kula da kanta da Abunda ke Cikinta..?umma bazata iya ba Na tabbata aduk inda Take Cikinta ya Tsufa ta kusa Haihuwanshi Umma a ina Zata Haihu..? Tana ina ahalin yanzu..? In ina Tuna haka Umma sai naji komai ya Fita kaina Taya zan zauna ina Farinciki Ina cin abinci ina Nuna muku komai ba komai ba alhalin Zuciyata ba Huta ba Natsuwa Bazan iya ba Umma Wlh Firstlove itace Raunani da Duka Zuciyata Rashinta gareni kamar Rasa wani Bangare ne najin Dadina.." Ya karishe yana Runtse Idanuwansa Cikin Halin kuna da Bakinciki in ya Tuna wani Abu Umma da Kalamansa suka Sakata Jin Taruwan Hawaye ta isa Garesa sai dai ji yayi ta Dafa kansa Tana Fadin"Nasani Dole zakayi wannan Tunanin muna Muna yin irinshi..Wlh kullum bana iya kwana na tashi ban yi ma Halima addu"an Allah ya Tsareta ba Duk sadda Tunanin haka ya Fado maka kayi Tawasalli da sunayen Allah ka saka acikin Ranka aduk inda Halima Take tana Cikin Koshin Lafiya kuma da yardan Allah zata dawo garemu Cikin Lokaci kalilan.."Zain Daya Bude jajayen Idanuwansa yana kallon Umma Sai ta gyada mai kai Tana Fadin"Kadaina Damuwa kaji ko..? Insha Allahu Halima Zata dawo Cikin kwanciyar Hankali ita da Abunda ke Cikinta.." Zain ya Bude baki yace"Zata dawo garemu Umma..? Umma Tace"Da yardan Allah...Domin Ubangiji baya barci kuma baya Gyangadi Yana Karban Duka addu"an Bayinsa Salihai.."Da wannan kalaman Zain yaji hankalinsa ya kwanta Umma bata barsa ya Shiga wanka ba sai da Tajashi Ta bashi Abinci abaki yaci ta bashi Ruwa yasha kana Ta barshi ya Shiga wanka ita kuma Ta tattara komai Zuwa Kitchen acikin Ranta Cike da Tsausayin Halin da Zain yake ciki Gefe Daya kuma Ta Fatan Allah yasa Halima Tana Cikij Koshin Lafiya Har ga Allah Itama tana wannan Zullumin kuma in lissafinta yazo Daidai kamar Cikin Dina itama Halima Tana Kusa Shiga wata Takwas kenan koda ba"a aunata ba alokacin Ta Tuna Mom ikilima Data Fara gane Halima nada Ciki tace yakai watansa na uku alokacin In Hasashenta yazo Daidai Tare Zasu Haihu da wannan Yarinyar da Zuwanta ya Zame musu bala"i koma miye zasu Cigaba da gayama Allah Da Izinin Lahi Halima Zata Dawo Gida Ita da Abunda ke Cikinta lafiya. Nene kuma Tana Dakin Abba sai da ta Taimakamai yayi wanka Ta gabatar mai da abinci Daman Ranar ita kedashi Sai da yagama cin Abinci ya wanke Hannu Nene ta Hada komai Zuwa Kitchen ta maida kana ta Dawo Ta iske Abba ya saka wani Farin Gilashin mai karamai karfib gani ya Bude System dinsa gefensa ta samu ta Zauna Batare datayi mgana ba Ganin Haka yasa Abba ya Dakata da Abunda yake Ya juya yana kallon Nene yadda ta kurama wani Waje ido gs duk alamu akwai Abunda ke Damunta da kuma Mgana abakinta. Gyara Zama yayi yana Fadin"Hajiya Nene lafiya..? Daga gani akwai mgana abakin ki..? Meya faru ne..? Nene ta Muskuta Tana Fadin"Mgana kam akwaita Abban Saudart..."Yana Danne Danne Bisa System din sa yake Fadin"Uhm ina Jinki.."Nene ta gyara Zama Tana Fadin"Daman nace bari zan maka mgana Tunda naga ko nayi ma Umman Zareena mgana ba Kulani Zatayi ba kan mganar wannan Yarinyar Dake wajenmu ne Abban Saudart.."Kansa na kasa yana Cigaba da Abunda yake yi yace"Wata yarinya kenam..? Kuma wata mgana ce Da Fatima bazata Saurareki ba.? Nene tace"Yarinyar nan Dina mana..Mganar Cikin Dan'mu Datake Dauke dashi ne Abban Saudart kaga Haddir fa yace Watan Gobe ne zata Haihu Bamu siya ko wando na yaro ba ama Ture uwar,ammh ai Abunda ke Cikinta Dolenmu ne Abban Saudart Tunda Bawa fa bai isa ya Ture ko ya kaucema Kaddaransa ba Abun nan bafa yau ya Faru ba,Ba kuma Jiya ya kamata mu daina kallonsa ta wanmi Fannin mu kallesa da Idanuwan Basira ko ina akaje dai aka Dawo Wannan Abunda Zata Haifa Wlh ya zama namu har Abada Shine naga bari kai nayi maka mgana Tunda gashi Zain bama zan mai mgana ba Shi kanshi bayama Cikin Natsuwarsa kan Batan Halima bana so kuma na kara sakamai wani Rauni acikin Zuciyarsa.." Har Nene ta gama Mganarta Abba na Jinta bai ce komai ba sai Da tagama Kana ya Sauke Nunfashi ya Dago yana kallonta kafin yace"Ikon Allah har Haihuwan ya kusa zuwa kenan..? Nene tace"Da yardan Allah ta kusa sai dai muyi Fatan Allah ya Raba Lafiya.."Abba ya gyada kai yana Fadin"Ameen...Yaushe ne akace Kanwar maman nata Zata zo Daga Sudan ta zauna da ita..? Nene tace"Bansan Rana ba ammh an ce Tana Tafe Insha Allahu..Shiyasa nake son kafin Tazo Ta iske an siya komai,Ko bakomai ai an zama Daya Tunda bayan Ta Haihu aure Za"a Daura musu su Tare agidansu Kaga kuwa An Riga an zama Daya.."Abba yace"Hakane..Kada ma ki ma Zain mgana ki kyaleshi Ni zan bada kudin da za"ayi siyayyah In Fatima ba zata je ba ko keda Zainab sai ku Shiga kasuwa ku siyo Abunda ya kamata ya zamu yi..? Haka Allah ya kaddara sai Hakuri ita kuma Halima Allah ya bayyanata Shi kuma Zain Allah ya yayemai wannan Damuwar ya bashi Ikon Cin wannan Jarabawan Rayuwar Data sameshi.." Cikin Tsausayama Abba dashi Kanshi Zain din Nene take ta amsawa da Ameen Haka dai suka Cigaba da Tattauna mganar Har suka kwanta Kowa da Abubda ke Damunsa acikin Ransa Nene taji Dadi Dataga Abba ya saki ba kamar baya Koda yake ta lura Tun bayan Tafiyar Halima Abba yayi sanyi ya koma kamar bashi ba. Abba ya Cika alkawari Washegari 100k ya bama Nene kafin ya Fita yace su Tafi kasuwa ita da Zainab su siyo komai,ya fita ya barsu zasu Shirya su tafi Nene ta gayama Zainab Amotarta zasu Tafi Zainab din bata so Zuwa ba Jin Mganar Daga Abba yasa Dole ta hakura da Shiga Cikin makaranta Zain baima san Abunda ke Faruwa ba Tun safe ya Fice Zuwa asibiti Umma kuma najinsu ammh Tak batacr ba karshenta ma Daki ta koma Tana kuka Tana Kukan Nadama da Danasanin Hukuncin Data Dauka a dace Tun Farko ta baiwa Zain matarsa da yau Zaina bata bar gida da Ta tabbata da ita za"a shiga kasuwa itama tayo ma yarta Duka Siyayyan kayan Haihuwa. Sai wajen 11am suka Fita Suka Shiga kasuwa sai wajen 2pm suka Dawo Inda Nene ta Siyo komai da komai na Bukatan Jariria mai Amfani da mace Da Namiji Tunda basu san me Zata Haifa ba Kaya fa kamar za"aBude Shago hadd dan gadon Daura Bby,Bayan sun Dawo sun Dawo Gidan Alhaji Tsoho suka wuce da kayan suka Nuna Mishi Shi da Hajiya Mama suna ta saka albarka Alhaji tsoho yaji Dadi har acikin Ransa ya kuma yabama Usman kan wannan Abun da yayi yaji kuma azuciyarsa sun Fara karban wannan kaddaran da Hannun Biyu. Daganan Gida suka Dawo da kayan nan Falo suka baje suna kara gani Umma kuwa Ko Fitowa batayi ba Daman Nene tasan bazata Fito ba Shiyasa bata Nemeta ba,Kayan Nene ta kwashe takai Dakinta da Abba ya Dawo ta kwasa takai mai Yace kada taDamu ta kai ma Dinan Dakinta ta adana Bata kaima Dina ba sai Washegari Lokacin Zain yana Shirin Fita yaga Nene na Jidan Ledoji Zuwa Dakin Da Dina ke Ciki Cikin mamaki ya kalleta bayan sun gaisa yace"Nene lafiya.? Wannan kayan fa..? Nene ta Dakata Tana kallonsa Dauke da Ledojin overroll Tana Fadin"Kayan Jariria ne Abbanka ya bada kudi aka Siya Saboda Dina lokacin Haihuwan nata ya matso.."Kuri kawai Zain yayi ma Nene Kafin taga ya Rabata kawai ya wuce ya Fita kanxil bai ce ta Bishi da kallon Tsausayi Shi kuwa har yakai Cikin asibitu ransa na kuna yanzu Dai Ta Tabbata Dina agidansu Zata Haifi Cikin Shegen nan..! Kai kaichonsa Daya Biyema Rudun Duniya dana Shedan da ace yaji Tsoron Allah sa da Duk Haka bai Faru ba Cikin kunci Ya Shiga Cikin Office dinsa yana jin wani Nauyi acikin Kirjinsa haka ya Fara Duba patient duk bashi da wani Natsuwa ballatana kwanciyar Hankali. Dina kuwa Tana Kwance Tashiga Shigowar Nene da kayan niki Niki Tana Daga kwancen Ta Tashi Dakyar Tana gaida Nene ta amsa Tana ce mata"Ka kaya nan ki adanasu..Kayan Baby ne.."Daga Haka ta Fice Batare data Jira Cewar Dina Ita kuwa Dina Tuni Zuciyarta ta kawo mata Zain ne ya Siya Lalle malam yayi aiki Sosai kan Zain daman Tana Tunanin in bai siya komai ba In Ummi Maimun tazo Sai Ta gayamata Bata da komai na Tarban Haihuwa,Duk da Tasan Daddy bazai bar Ummi maimun tazo Hakanan ba Komai Tana da yakinin zai yi mata ammh na Zain abu ne na musamman awajenta wayarta Ta jawo ta Kira Zakiya Ta gayamata sai dai kuma Zakiyan bata Daga Kiran ba bata rai Tayi tana wani Tunani yanzu kwata kwata Zakiya bata son Daga wayarta sai Taga Dama ta lura gabadaya Hankalin Zakiya ya koma ga wannan Yaron Data samu yanzu bata Cika bi ta kanta ba Tabe baki tayi ta maida wayar gefenta Kafin ta koma ahankali ta kwanta Tana yamutsa Fuska Jin Dan Cikinta na Motsi. *Kuyi hakuri da jina Shuru..Sai ku rikamin Uzuri ga sallah ka Bikin kanwata da Za"ayi mun Shiga Hidima Da zarar na samu Dama zaku dinja jina Nagode..* *Shakira...* 7/22/21, 2:44 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣3️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *Zaria* _gyallesu.._! ""Zuly da ta dawo Zulaihat yanzu Rayuwarta Ta inganta Tuni ta Fara tsarkake kanta Gefe Daya kuma Zaina na Kokari wajen koya mata yadda Zatayi addininta da kuma yadda Zata karanta Bakin Hausa yayinda ita Kuma Farida ta Dauki Nauyin Kula dasu Duka Biyun. Uwar mata Hankalinta bai kwanta ba Sai da tazo Taga Inda suka koma kana Taji sanyi Domin Abaya Tana ganin kamar Faridan Ta Subuce matane Tare tazo Ita da yar Rakiyarta wato Hajiya Zabba"u,Lokacin Datazo mamaki Take tana kara kallon Zaina Da Katon Cikinta,ammh Batayi mgana ba Tunda Farida Bata Bada Damar haka ba Lokacin Dataga Zulaihat agidan Bata Yi mgana ba Tadai ce Faridan Taji tagani sai tayi ta kaya Daman Zulaihat din ba wani Tara mata abun Arziki Tayi ba Saboda Haka koda Ta ganta ta Sauya bata wani Damu ba. Bangaran su Suby kuwa Sai da Uwar mata tayi mata Tijira kana Ta Shiga Taitayinta Bayan Tashin Farida sai Suby ta Kwashe kayanta ta koma Dakin da Uwar mata tazo Tagani Tayi ma Kaca kaca ta kuma sa aka Fitar da Duka kayan Suby ta sakama Dakin Kwado Tace Bayan Sholly ba wacce keda Lasisin zama acikin wannan Dakin Tunda bata Ciki sai dai ya Tabbata yana Kulee,Wannan Abun ya kara Bakantama Suby Rai sai da Tayi kwallah Tana Tunanin Ta kashe maciji ashe bata sare mai kai Tana Ganin Tunda Sholly tabar Gidan Darajanta zai Ragu kuma Uwar Mata zata koma Tana ganinsu da Kima sai dai Ba haka abun yake ba Ita Sholly Tun Farko mai Sa"a ce kuma karuwa ce mai aji da Lasisi Uwar mata ta sani In Tayi Rashinta Bazata Taba Maida kamarta ba Domin kaf karuwan Data daukesu babu Wacce Ta kama kafar Sholly. Su Adamalle da Deezee sai Dariya suke ma Suby Domin Ranar a waje uwar mata Tayi mata Tijara Daman shi Bariiki Ko Dan Bariki baya Jin kunya Ko kyashi yaci maka Zarafi gaban Mutane Suby sai kuka Ta Ruga Xuwa Cikin Gida da Borin Kunya Kacharalle ne kadai yasan Inda Farida ta koma Ammh ya kama bakinsa Duk wanda ya Tambayeshi cewa yake bai sani ba Ko bakomai akwai Amana Tsakaninsa da Sholly bazai yarda wannan Amanan Ta Zube ba Suby Har Kudi ta bashi ya Fadamata yaki ya maida mata da kudinta Tunda Farida na bashi Wanda ma yafi wanda ta bashi. Bayan Kacharalle babu Wanda Farida ke Bari yana Zuwa Inda suke To wama ya sani..?uwar mata ce kuma Tana kaduna Hankalinta ya kwanta ganin Farida bata bar Harkan karuwanci ba Tunda duk sati Tana ganin aleart dinta Shiyasa bata ma Damu Data koma Gidan Malaminta ganin Komai ya Tafi Daidai Abunda Uwar mata Bata sani ba Koda Farida batayi ma kanta addu"a Zaina tana yi mata Tana mata addu"an Allah ya Rabata da wannan Rayuwar ya maida Hankalinta Zuwa Gida ahankali ahankali Tasirin Sihirin yana sakin Jikin Farida Batare da Ita Uwar mata ta sani ba Tunda ayan kwanakin ma Kullum sai Tayi mafarkin Su Mama da su Hasaana da Usaina Tana ganinta Cikin mafarkinta Suna kukan kewanta kuma Tasha ganin Ya Musbahu Cikin mafarki yana kuka yana Rokonta ta Dawo Gareshi In ta Farka sai Tayi kuka ta wuni Cikin Damuwa watarana ma Haka take wuni bata Zuwa Ko"ina Da ka ganta Tana Cikin Damuwa Dalilin Dayasa Jininta ya hau kenan Ta Fara Faman da Ciwon kai da Jiri sai da sukaje asibiti aka Dubata aka bata mgaguna Ita kuma Zaina akayi mata awon Ciki anan asibitin almadina inda Cikinta yake Cikin Wata na bakwai bai karisa Wata na Takwas ba ammh yayiGirma sosai Duk ya Cika Zainan komai na Cikinta ya Kumbura ya kara Girma sai kace Wata Big Mama ita kanta In Ta kalli Kanta amadubu sai Taji Tsoro ganin yadda Tayi wani Muni ga Kuma Girman Data kara Domin Ta Ninka biyunta Lokacin Farkon zuwanta. Babu Abunda Zata ce ma Zulaihat da Anty Farida sai Godiya Domin suna Bata Dukkan Gudummuwarsu Anty Farida Da Lafiyarta Take bata Nata Gudummuwar yayinda Zulaihat Take bata da karfinta Daidai gwargwado suna Kula da ita Farida ta zama kamar Uwa gareta Yayinda Zulaihat Take kallinta kamar wata yayarta Basa bari tayi Ihim ma Saboda yadda Suke ji da ita Wanka kadai ne Zaina keyi wanda zatacr Tana wahala ban dashi Komai yi mata suke Tasha Ta zauna Tayi kuka Tana Tunanin da me zata saka musu Bayin Allah da suka Sadaukar da komai nasu saboda Inganta Nata Rayuwar Tayi alkawarin Da Ikon Allah sai ta Rabasu da wannan Rayuwar Ta Fara Nasara kan Zulaihat saura Anty Farida wanda Take da Burin Ta Rakata Har Gombe kamar yadda Zata Dauketa ta kaita Har Bauchi Zulaihat kuma Bauchi Zata Tafi da ita Ta Tabbata ahalin Alhaji Tsoho bazasu ki karbanta su inganta Rayuwarta ba Rayuwarsu suke Gudanarwa Cikin kwanciyar Hankali Basu da matsalan komai yanzu Daga Sholly Har Zulaihat suna Jiran Haihuwan Zaina ne Tuni Har Farida ta Siyama Zulaihat karamar waya ta bata ahannunta Saboda In wani abu ya Faru bata Gida ta Kirata ta gayamata Domin Tagama yarda da Zulaihat din har ta Fara sakin Jiki da ita Tafiya takan kama Farida na kwana ammh hamkalinta nakan Su Halima ta Dinga Kira kenan Tana Tambayansu Lafiya tana Fadin Ko an buga Gida kada su Bude Ko waye in ba Kacharalle bane Zulaihat tace toh..bama su Budewa Gidan akulle yake Wuni kuma akulle yake kwana Karatin dasuke da Zulaihat yana Rage ma Zaina kewa sai da Tana Tuna makomar nata karatunta Data Rasashi Har Abada In Lissafinta yatafi Daidai Su Laila suna Aji uku kenan Sun kusa Hada Digrre dinsu Ita kuwa Gatanan zaman Kila wakalan Rayuwa Waya sani ma Ko wajen Haihuwa Allah yayi mata Rasuwa,Insha Allahu kafin haka Zata Rubuta Takardan Ta bama Anty Farida kafin Ta Haihu In Ta haihu Lafiya Shikenan in kuma Karshen Wahalarta kenan Zata Roketa Ta kai Takardan Har Gidan Ta bama Firstlove Ya Cire Tsammanin Tana Raye. ****** *Bayan Sati Biyu..*! Alokacin Tuni Hajiya Maimun ta sauka a Nageria agidan kwamishina,Koda ta Sauka Tuni Daddy ya bama Hajiya Batula magudan kudade Taje tayi ma Dina Siyayyan kayan Haihuwa Komai da komai ita kanta Dinar Akwati guda Kwamishina yayi mata na kayan alfarma. Da Hajiya Maimuna Taga kayan Sai da ta Jinjina Son da kwamishina yake ma Dina Hatta da madaran Shan na yara Gasunan kala kala Tana kallon Kayan Tana Sharan Hawaye bawa bai isa ya kauce ma Kaddaransa ba yau da ace Dan Sunna ne Dina Zata Haifa ta Tabbata Duniya sai ta Sheda Dina yar kwamishina Ta samu karuwa Shi kuma ya samu Jika Ammh Dalilin Abubuwan da suka Faru yau Dinar ma Bata gabansa Tana wani Gidan Chan Dabam ba Domin komai ba sai Domin Rufin asirinsu Duka Godiyarta ga Allah Daya ne Tunda Iyayan yaron masu Mutumci nr Da Dattako Shiyasa har suka karbi Cikin su kuma Yadda Da Duka Wahalansa Har Zuwa yazo Duniya ga wani karin Abun Jin Dadi kuma auran da zai Tabbata Tsakanin zain da Dina Yaron su bazai Taso Cikin Wulakantattacen Rayuwa ba. Kwamishina ya Tsara Tafiyar Weekend ne Ranar Lahadi kenan Saboda yana so Yaje Yayi ma Alhaji Tsoho Jajen Abunda ya Faru na Batan Halima Dina Ta Kira Hajiya Batula Ta gayamata Ita kuma Take gayamai Duk da ya Kira Alhaji Tsohon tawaya yamai Allah kyauta ammh akwai Bukatar yaje yakara Jaddadamai Godiyarsa ana Gobe zasu Tafi Kwamishina ya Kira Alhaji Tsoho ya gaya musu suna Tafe da Hajiya Maimuna Alhaji Tsoho yaje sai sunzo Ranar da Daddare Abba yazo yake gayamai yace in ya koma Gida ya gayama Matansa Wacce Zata Zauna da Dina Har ta Haihu Suna Tafe gobe Abba yace Shikenan ba Damuwa Allah ya nuna musu. Washegari kuwa da Wuri su Kwamishina suka iso Duk da Tafiyar Mota ce Gidan Alhaji Tsoho suka Fara yada Zango Bayan an gaisa kuma Da Jajen Batan Zaina sai Godiya Da Fatan gamawa da Duniya Lafiya ya Biyo baya Kwamishina Kamar ya kwantama Alhaji Tsoho Saboda Godiya Shi kuma yace Bakomai Kada ya Damu an Zama Daya basu wani Dade ba Lemo suka sha sai Ruwa Hajiya Mama Tayi musu Rakiya Zuwa Chan Gidansu Abba. Koda sukaje Nene ta Shirya musu Abinci kala kala Daga Umarnin Abba Shima kansa yana Gida,Koda suka isa sun samu kyakyawan Tarba ba kamar na Baya ba,Umma ce kadai Bata tsaya ba suna gaisawa ta koma Daki yau din Abba ya Fito sun gaisa da Kwamishina da Hajiya Maimuna Da Hajiya Batula Tunda da ita akazo Harda Walid da Walida,Bayan gaisuwa da Kuma ganin Juna,da nuna kayan da suka zo Dashi,Nene da Abba da Hajiya Mama suna ta Saka albarka, Nene tayi musu Jagora Zuwa Cikin Dakin Dina Wacce Farinciki ya Cikata Tun Jiya da Daddy ya gayamata Zuwansu Har Zakiya ta Kira ta Shaidamawa Tadai ce mata Zata Shigo ammh Ba Lalle ba sanin Zakiya yanzu Hankalinta baya kan Dina yana kan Ja"afar ne Wanda ya zama Jini da Tsokarta Lokacin da sukayi ido Hudu da Dina sai da suka Tsauyamata ganin yadda ta koma kamar ba ita ba Hajiya Batula kuwa Tana kallonta aranta Tana Fadin Uhm yarinya waya gayamiki Barno gabas Take kin kusa Fara Jin maza Tana Jinta Tana ma Kwamishina Shagwaba wai Cikin ya Isheta Shi da Hajiya Maimuna suna Lallashinta ita dai Tana Gefe Tana kallon Ikon Allah Sun Shisshiga da kayan da suka zo mata dashi Shine ma ta Nuna musu wanda Nene ta kawo mata Hajiya Batula na Daga kayan Tana Yabama wannan ahalin Saboda duka kayan Expansive ne Bana Banza Shi kanshi Kwamishina yana Jinjina ma Ahalin Alhaji Tsoho Domin yasani Cikin Dubu wlh sai an Tona za"a samu kamarsu. Nene da Zainab suka yi ta Shigowa da abincin da suka Shirya musu Hajiya Maimuna nayi musu sannu da aiki nan suka ci suka Sha suna Ta Hira Dina Bakinta yaki Rufuwa Saboda Farinciki Nan sukayi Sallar Azahar da La"asar Hajiya Mama Tuni ta koma Gida Sai da sukayi Sallar La"asar sukayi Shirin Tafiya bayan kwamishina ya Dawo Daga Cikin gari Daman Tun bayan Sallar azahar ya Shiga Cikin gari ya dawo Shida Excort dinsa. Da Zasu Tafi Abba da Nene har Haraban Gidan suka Rakasu Dina ma da Hajiya Maimuna Sun Fito Dina Ciki yayi Nauyi sai Dingisawa Take tana wani Cije baki Dina Harda kuka ta Rumgume Kwamishina Tana kuka Shi kuma ya Biye mata yana Lallashinta Dakyar ta Sakeshi ya Shiga Mota Hajiya Batula Takaichi ya Cikata Gamsamemiya Dake ga Ciki ammh Kina Abunda Walida ma bazai yi ba ita Har yau har Gobe Bata ganin Laifin Kowa sai na Dina Ta Tattaba ba Shege sai Da akayi Shegiya. Bayan Tafiyarsu Kwamishina,Hajiya Maimuna Ta kama Dina suka Koma Ciki,Ta Fara gyaran kayan da suka zo dashi,Tana Ijiyesu Cikin muhallinsu,Sai Chan bayan Mangariba Nene ta Shigar musu Da Dinner Har ta Dan Tsaya suna Hira da Hajiya maimuna kafin Tayi musu sallama ta Fito Ta koma Dakinta Tayi wanka Umma dai na Ciki Bata ma Fito ba Ballatana aganta. Bayan Nene ta Fito wanka ta Shirya ne Ta kaima Abba Abincinsa Ta Fito kenan suka ci karo da Zain ya Dawo Daga Asibiti bayan sun gaisa Nene ta Kalleshi Tana Fadin"Yauwa Nace ba..' Ya waiwayo yana kallonta Nene ta Cigaba da Fadin"Kanwar Mahaifiyar Dina Tazo fa..Yau suka zo Tare da mahaifinta da Matar Babanta da kannenta ammh su sun koma ita dai Ta na nan sai Dinar ta Haihu zata koma.."Zain yayi wani Jagale yana kallon Nene kafin yace"Nan zata zauna kuma Nene..? Nene tace"Eh Zata zauna nace Maka har Allah ya sauki Dinar Lafiya.." Zain ya kada kai kawai yace"Allah ya kyauta To.."Yana Shirin Shiga Dakinsa Nene tace"In ka natsa ka Shiga ka gaisheta.."Da Sauri ya waigo Yana Fadin"A"a Nene ni ba inda Zan Shiga ina ma Ruwana dasu.."Nene tace"akwai Ruwanka mana..Kuma Umarnin Abbanka Yace na gayamaka ka Shiga ku gaisa.."Daga Haka ta Wuce ta barsa nan Ya Bita da kallon Takaichi Da Bakincikin Dake Cikin Ransa Karamin Tsaki ya Saki ya Tura Kofar Dakin ya Shiga. Sai Da yayi wanka ya Sauya kaya Zuwa Farar Jallabiya Zainab Ta Shigomai da abinci Da Hannu yabata Umarnin Ta koma Dashi kana yace mata Tea Zata Hadomai Iya Bonvita kawai banda Madara,Ta Fice Zuwa Kitchen ta Hadomai ta kawomai yana Zaune Gefen gado Yana Duba wayarsa Sanda Zata Mikamai Mug din ta Hangi Hoton Zaina Daya Cika Sreendin Wayar Shi Zain ya Kura ma Ido yana kallon Cikin wani kewa da Muradi mai Girma Har ta Fice Tana Jin Tsausayin Ya Dakta acikin Ranta Duk ya koma wani Iri Dashi Saboda Chanjin Rayuwar Daya samu Allah Sarki Halima Ki Dawo ko Saboda kada Watarana Mu Rasa ya Dakta Gabadaya. Tuna Nene tacemai Umarnin Abba ne yasa Bayan yagama Shan Tea din Ya ijiye wayarsa nan Gefem gadon ya Zura wani Takalmin Dake gefen gadon ya Fice Zuwa Dakin Da Dina ke Ciki ya Dade a Kofar Dakin yana Tufka yana warwara kafin yayi Knooking din Kofar Daga Ciki yaji ana Bashi Izinin Shigowa ahankali ya Tura Kofar ya Shiga Da Karamar Sallamarsa Yana Tuna Tun bayan Dawowar Dina Gidsnsu yau ne karo na Biyu Daya Taka Kafarsa Cikin Dakin. Koda ya Shiga ya samu Dina Zaune Rashe Rashe a kasa Ta Jingina Bayanta da Gado Hajiya maimu Ta saka mata Filo Daga Bayanta Saboda Taji Dadin Zama Gefe Daya kuma Tana Matsa mata kafafunta da suka Kumbura suna Hira sama sama Yana Shigowa Dukkansu suka Dago Suna kallonsa Dina Kuwa sai da ta waro Idanuwanta Tana so Ta Tabbatar Zain din ne ko Mafarki ne,Dadai Ta Tabbatar dashi ne sai wani sanyi ya Cika Zuciyarta Tuni Ta Rika Godema Zakiya acikin Ranta Tana Tunanin Duk Cikin aikin Mallam ne. Hajiya Maimuna kuwa Tana ganin Zain ko ba"a Gayamata ba Ta gane shine Uban Cikin Dina ammh Daga kallonsa Kamili ne ga Natsuwa Bazaka Taba Zatom zai iya aikata wani aikin Assha ba Sai dai Ita kaddara ba Ruwanta Daya Nagartan Mutum yake Fadamai kawai Zatayi. Dakatawa Tayi da Abunda Take Tana gyara zamanta Dina kuwa Ido ta Kafeshi Dashi kamar wata mayya Shi kuwa Tunda ya Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa Kamar bai ganta ba Daga Nesa ya Durkusa yana Gaida Hajiya Maimuna ta amsa Cikin Fara"anta Ta kasan Ido yake kallonta aransa yana Fadin Ashe ga Inda Dina ta Dauko Kyau nan Domin Duk da Hajiya Maimuna ta kwana Biyu a Duniya kyawunta na nan bai Dishashe ba. Cikin Sanyin Muryansa yace"An zo Lafiya..? Tace"Lafiya Alhamdulillah ya muka same ku..? kansa na kasa yace"Alhamdulillah.."Daganan kuma sai yayi Shuru Idanuwansa na kallon Cafet din Dakin Ita kuma Hajiya Maimuna Tana Nazartan yanayinsa yayinda Dina Take Ta kallonsa Ganin Duk ya Rame ya kara Fita Hayyacinsa Kishi ya Cika Ranta Tana Tunanin Saboda wannan Shegiyar Zainar ne ya koma Haka Har Abada bata Batan zaina ta Dawo Gida ko aganta. Yana Shirin Tashi Hajiya Maimu Tace"Ya mukaji da wannan Abun da yafaru..? Allah ya bayyanata Allah ya kyauta na gaba an ce itama Matar naka da Ciki ta bar Gida? Ya za"ayi sai Hakuri Allah ya bayyanata.."Zain Sai Lokacin ya Dago kansa Karaf kuwa suka Hada Ido da Dina wacce Take jin kamar Taje ta Rumgumosa Cikin Tattausan Murya yace"Ameen Ameen Nagode.."Sai Lokacin Dina Tataba Jin Zain yayi mgana mai Tsawo Tun bayan Barin Zaina Gida Tunda bama ganinsa Take ba Cikin Kallon Tsana da wani Bakinciki ganin Yadda Cikin Dina yayi Girma Cikin yake kallo kawai yana Hasasho ajikin Zaina wani Tiriri na Fita Daga Ransa Cikin Sauri ya Tashi kamar zai Fadi Jin yadda Zuciyarsa ta Fara Zafi yace ma Hajiya maimu sai da Safe ya Fice ta Bishi da kallon Tsausayi kana ta juyo Tana Cema Dina"Allah sarki yaro karami ya Hadu da Jarabawan Rayuwa..Na Lura Batan Matarsa Ta tabasa sosai.." Dina Ta Tura baki Tana Fadin"Insha Allahu Tatafi kenan Har Abada.."Gum Hajiya maimuna ta Make bakinta Tana Fadin"Kul..Wawiya kawai kina ma wannan Halin na Siradin Rayuwa har Wata zaki ma Fatan Tatafi har Abada..? Dina Ki Kya kanki Wlh kada na karajin wannan mganar Daga Bakin ki Kina Ji ko..? Cikin Bata Rai da Tura Baki Dina Tace"Naji.."Daga Haka ta Tsuke bakinta ammh Har Cikin Ranta Bata Fatan Zaina ta Dawo Rayuwar Zaina Tana addu"an Allah ya Dau ranta a inda Taje kada Tataba Dawowa Har Abada Tana Jin Hajiya maimuna Nata yabon Dangin su Zaina ammh kala batace mata Domin Ranta Duk abace yake Saboda Tunawa da Yadda Zaina Tatafi da Duka Ruhin Abun kaunarta Zain. Shikowa Zain Dakyar yakai kansa Daki Jiri na Dibansa ya hau gado ya kwanta yana Sauke Numfashi Dole gobe yaje yaga Likita Dagashi sai Haddir ne suka san ya samu Hawan Jini Bayan Tafiyar Zaina Shi ya Hana Haddir ya gama iyayansu Bayan Dr.Imran ya gaya musu Saboda baya so Hankalin su Abba ya tashi Da Taimakon mgungunan Hawan Jini yake Tsaye da kafarsa har yau ammh ya sani Watarana sai ya Gaza Tunda Baya Kiyaye Dokar Likitoci na Rage Shiga Damuwa da Tunani mai Tsawo Wanda shi kuma kullum Cikin yake kwana Cikin yake Wuni. Daran Ranar Dakyar ya iya yin Barci Ciwon kai mai Tsanani ya Rufeshi ammh haka ya Dage ya Shirya Tun Safe ya Shiga asibiti Office din Dr.Imran ya Fara Zuwa Shi ya Gwada B.p dinsa ya kuma gayamai Jininsa yayi Mugun Hawa sosai sai ya Rage Tunanin Ganin Halin Dayake Ciki ne yamai allura ya kwanta nan Patient bed na Cikin Office din ya samu Barci Shi da Dr.Imran din ya Kira Haddir ya gayamai Daman ya Shigo Cikin asibitin sai yazo ya Duba Zain din shi ya zauna Tare Dashi Har ya Farka ciwon kan ya Sauka Har yaji Dama Ba yadda Haddir bai yi Dashi yazo ya maidasa Gida ya kara Hutawa yaki yace yana komawa Umma da Nene zasu Zargi wani abu Shi kuma ahalin yanzu bayason Damuwarsu Dole ya kyaleshi ammh bai barsa ya Duba Kowa ba Yajasa Office dinsa yace ya kwanta ya Huta Shi kuma yana Gefe yana Attempting din Marasa Lafiya. Har suka Tashi aiki Haddir ya Rakoshi Gida,kowa Motarsa ya Shiga,Har Ciki ya Shiga nan Falo suka ga Hajiya maimuna ta Fito suna Hira da Nene Umma na Gefe bata saka musu baki sai dau Tayi Mirmishin yake,Dayake ita Wayayyiyace bata Zaman Daki Tare Haddir da Zain suka gaisheta ta amsa Tana Yi musu sannu da Zuwa Daganan suka Shige Ciki Damann Shi Haddir din yaji labarin Zuwansu Abakin Hajiya Mama Tun Jiya bayason yana Tadama Zain Hankali Shiyasa basa ma wannan mganar da juna. Sai da sukayi Dinner tare kana Haddir ya wuce Gidan Alhaji Tsoho,Washegari kuma Haddir Abuja ya Tafi sai yace Zain ya zauna agida ya Huta Toh kawai yace mai ammh yana Tafiya ko Abuja bai kai ba Ya Shirya ya Tafi asibiti saboda baya son Zaman Gidan Da azarar ya zauna Shi kadai sai Tunane Tunane suyi mai Cha Ammh in yana asibiti yana Duba Marasa Lafiya hakan na Debemai kewa. ******* Azuwa wannan Lokacin Tuni Zakiya Tagama Saki da yardan ma kanta ta samu Miji Daidai da Ra"ayinta wanda kuma take so,Ta Riga ta gama Shakuwa da Ja"afar ta sakarmai komai nata Sirrinta kuma kalilan ne bai sani ba sai dai bata yarda yasan ita yar Bariki bace tayi kokarin Duk ta yakice Abokan Shashancin nata Tunda Tana so Tayi aure. Hatta Motarta Tana wajen Ja"afar Shi yake kaita Wajen aiki kuma yazo ya Dauketa Ko"ina Zasu Tare suke Zuwa wadanda suka san Ja"afar abaya in suka gansa yanzu bazasu gane shi ba ya zama wani Gaye mai Tashe Tunda Zakiya ta sakarmai kudi yana Yadda yaga Dama Hatta Bankin kansa ta Bude ta sakamai kudi Saboda Laluransa da baisai yagayamata,Tana so ta Tsarkake kanta ne da auransu kuma Bataso Ja"afar din ya Fahinci wani abu Shiyasa Bata Taba Nunamai Tana Sha"awarasa ba ammh yadda Take Mutuwar Sonsa da kaunarsa kamar Tayi mai Fyade haka take ji. Bata Fito mai da Niyyarta na Son Auransa ba sai da Tagama maidashi Dan gata ta sakarmai komai ta Fiti mai da maitatarta na son auransa,Da Farko ya nuna mata Shi fa bai da komai Ai Tafi karfinsa ammh sai ta Nuna mai kada ya Damu Tana Sonshi ahaka sai yace mata Shi bai da kowa agarin Bauchi sai ogansa,tace karya Damu Zatayi mgana Dashi Ranar Dayace ya amince zasu aure Rumgumesa Zakiya Tayi Saboda Farinciki Washegaro kuma bayan Taje gareji wajen ogansa Tagayamai komai yace Shi baida matsala Tunda Ja"afar din ya yarda suka Rabu kan Zata kai shi kano Wajen Babanta in ta Dawo Zata zo Suyi mgana kan Kudin Sadaki da Sauran Shiryan Shiryan aure Tunda kamar Shi Zai zama Waliyin Ja"afar din. Ranar Saboda Farinciki Tana Dawowa aiki ta Dauki Ja"afar suka Tafi wajem saida Motoci Tace ya zabi Duk wanda yake so shine ya Zabi wata 4Matic Fara mai kyau Nan take Zakiya Tabi ya Kudin kawai Facaka take da kudu Batare data Damu ba. Basu Samu Tafiya kano ba sai Weekend Saboda aikinta Duk Iskancin Zakiya Tana Daraja aikinta Amotar Ja"afar din sukayi Tafiya suna Hanyar Zuwa kano ne Dina ta Kirata Tana mata korafin Ta Daina Nemanta yanzu Har Hajiya maimu Tayi sati agarin Bauchi batazo sun gaisa ba sai Take bata Hakuri Tana gayamata yadda komai ya Faru nan take sanar da ita gasu ahanya zasu kano Zata kaima Babanta Ja"afar amatsayin Mijin Da Zata aura Take gayama Dina Kilama ta Rigata aure ayadda zakiya ke mganar Tana Dariya kamar wacce akayi ma gafara Dina Jikinta yayi sanyi ta Fara Tunanin anya wannan Rayuwar da Zakiya ta Tsinci kanta mai Bullowa ne..? Haka kurum take jin kamar Tayi gaggawa sakarma Yaron komai Duk da Bata Taba ganinsa ba koma menene Tana yi mata Fatan Ta samu Dacewa kan Abunda take Buri da so. *Sai kun sake min Hakuri..muna da Hidima ne ammh Insha Allahu in na samu Lokaci zaku rika jina Nagode..* *Janafty...* 7/25/21, 9:05 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣4️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *Kano..* Tsuru kawai Mallam Nuhu mahaifin Zakiya yayi yana Bin Ja"afar da kallo Mamaki da al"ajabi sun Cikashi na ganinsa wai amatsayin Mijin da Zakiya Zata aura. Duk da bai san Shekarun yaron ba Ammh ido ba mudu ba yasan Kima ya Tabbata Zakiya bazata Girmemai ba,Kuma ayadda yake gani wannan yaron yayi ma Zakiya yaro a matsayin wanda Zata aura sai dai bashi da tacewa ganin Yana Fama Kan Zakiya Tayi aure sai yau Allah ya amsa mai wannan addu"an ta kawo mai Mijin da Zata aura. Daman Lokacin da suka Zo yana Tsakar Gida kan Tabarma ne yana Shan iska nan suka Yada Zango,Ya Dade yana Jan Jasbahabsa bayan yagama jin Zakiya Tagama Kore bayananta bai yi mgana ba kana ya jinjina kai kawai kafin ya kalli Zakiya yana Fadin"Naji Duka bayananki Zakiya..Tashi Ki Shiga Cikin Daki zan yi mgana Dashi.." Batayi Gaddama ba Ta Mike ta Shige Dakin Amaryan Mallam Nuhu Daman ita ta Tarbesu Da suka iso,Sai da ta Shige ne Kana Mallam Nuhu ya kalleshi Sosai yana kara Nazarinsa Dakyau haka kurun acikin Zuciyarsa Yake jin bai yarda da yaron ba. Gyara Zama yayi yana Fadin"Ja"afar ya sunan Mahaifinka achan Yola din..? Ja"afar kansa na kasa yace"Sunansa Mallam Isma"il baffijo..."Mallam Nuhu yace"Sunansa kenan..? Dashi yake amfani kenan..? Ja"afar ya gyada kansa alamun Eh Shuru Mallam Nuhu yayi yana kara Nazarinsa kafin yace"Achan Yola wata Anguwa kuke zaune..,? Ja"afar yace"Muna lowcost Lokacin Iyayena Nada rai Daga baya kuma Dana koma Hannun kakana mun bar nan da Zama.."mallam Nuhu yace"Itama Kakar Taka ta rasu kenan..? Ja"afar yace"Eh Allah yayi mata Rasuwa Shekaru Biyar da suka wuce..."Mallam Nuhu yace"Allah ya Jikanta da Rahma..'Ja"afar yace"Ameen Ameen ya Allah Mallam Nuhu ya kara gyara Zama yana Fadin"Sauran yan"uwanka fa ina Nufin Koda anje chan Bincikawa za"a iya samun wani..? Ja"afar yace"Gaskiya a"a saboda Dangin Mahaifiyata ba yan nan bane yar Gudun Hijirace Daga Niger Mahaifina ya aureta Duka ta rasa Danginta Mahaifi na ma bashi da wasu Dangi Tunda na taso Bayan Iyayena Kakata wacce ta Haifi Mahaifina kadai na sani..." Mallam Nuhu ya Dade yana kallonsa kafin ya kada kai yana Fadin"Bakomai zamu Bincika kasan shi aure sai da Bincike Ba"ayinshi kai Tsaye.."Ja"afar yace"Hakane.." Shuru yabiyo baya Shi Ja"afar yana Zaune Kansa na kasa Mallam Nuhu kuma nata Jan Casbahan sa yana kara Nazarin Yaron da Zakiya ta kawomai a matsayin wanda Zata aura,basu wani jima ba Sallar azahar kadai sukayi anan ko abinci ma basu ci ba Lemo kadai suka sha sukayi Haraman Tafiya Har Zakiya Tashiga Mota Mallam Nuhu ya aika aka Kiramai ita Bayan Tazo ta zauna gabansa ya kalleta yana Fadin"Anya Zakiya kina ganin auran wannan yaron Da zaki yi Daidai ne..? Zakiya ta Muskuta Tana Fadin"Eh Baba Ina Sonshi kuma Shima yana Sona.."Mallam Nuhu yace"duk ba wannan ba..Yadda kika gayamin fa yaron nan bai da wata Sana"a Dame zai Rike ki..! Kuma ni aganina ba yaro ya Dace Dake ba Zakiya ashekarunki gwara ki samu Mai Hankali Wanda Rayuwarku zai Daidaita.." Zakiya Tace"Baba yana da Sa"ana fa Bakanikr ne..Kuma ni ina aiki na Tabbata zan iya Rikemu...Auran nan fa kake so nayi Baba gashi kuma Zan yi Meye kuma abun Damuwa Baba..? Mallam Nuhu yace"Uhm..Shikenan Allah ya sa albarka..."Zakiya tace"Ko Kaifa Baba..Ameen Ya Allah Haka Daman nake so ka Fada kawai.."Mallam Nuhu yayi Shuru kawai ganin Idanuwan Zakiya ya Rufe Bataji bata gani. Tana Shirin Tashi Ya Dakatar da ita da Fadin"Kin san cewa aure bazai Hallasta ba sai kin Tsarkaka..? Yafada yana kallonta Cikin Sunkuyar Dakai Zakiya Tace"Na sani Baba..Ina Cikin Isbira"in din ne ma.."Mallam Nuhu ya Girgiza kai Cikin Takaichi Yana Fadin"Kin san ya zaki Tsarkaka kanki kuwa Zakiya..! Da son samu ne Da kin Dawo Kin samu Tsarki sai adaura muku auran kamar yadda kika Bukata.. Zakiya Tace"Na sani Baba Ba jini uku bane..? Ka tsarkake kanka ga Duk wani Datti ko..? Mganar kuma na dawo nan Baba aikina In na Dawo nan akwai Damuwa Gwara na zauna chan nayi maka alkwarin Nayi Niyyar aure zan Tsarkake kaina Insha Allahu.."Mallam Nuhu ya gyada kai yana Fadin"Shikenan Allah ya Rufamana asiri.." Sallama Tayi mai ya Bita da addu"a Tabashi kudi yaki karba sai da ta Rantsemai cewa Cikim kudin albashinta ne Kana ya karba ya Bita da addu"an Allah Shirya Tunda dai Shi baxai yi mata baki ba kada ta kara lalacewa yanzu ma ya Ta kaya..? Ammh mganar gaskiya wannan yaron bai kwantamai arai ba yana ganin Kamar Zakiya Zata Tafka wani Kuskure ne ammh zai ce bincika akwai Wani abokinsa achan Yola yaji Wani abu game da yaron. ****** *Zaria..* Zaina na Zaune akasan Cafet Din Dakin ta mike kafafunta da suka Kumbura Zulaihat na Gefenta Tana dan Mtsa mata Kafafun suna Hira sama sama Farida kuma yau tana Gida Bata Fita ba Tana kan kujera Tana Latsa wayarta Zaina Zata muskuta sai Taji bayanta ya kage ta Fara Cije baki Tana Fadin"Wash...!Da sauri Farida tayi wurgi da wayar Hannunta Ta kariso Gareta Hakama Zulaihat Duk ta Rude kusan tare suke Tambayanta Lafiya..? Wani abu ne ke Damunta..? Me take ji..?. Abun sai ya bama Zaina Dariya ma sai ta Dara Lokaci Daya idanuwanta sun Cika da kwallah tace Cikin wani abu Dake Fitowa Daga Kasan Ranta. "Allah Sarki Umma..Allah Sarki Firstlove..Goggo Halima da Sauran yan"uwana na Tabbata addu"arsu ce Ta Fado ni Dani Hannayen masu kula dani Da so na..Allah zan gode mawa kawai Domin Nayi Rashin Wasu ahalin yau gani Cikin wasu ahalin.."Tafada Tana Sharan Kwallah Daga Faridan Har Zulaihat din kusa da ita suka Zauna suka sata atsakiya kowacce Ta Dafa kafadarta Cikin Soyayyah da kauna da Muradi mai Girma. Farida ce ta Fara mgana Tana Fadin"Karki Damu Sa"adiya..Ina Kallon ki ne kamar kanwata Zahra..Ina Miki kallon kamar ke din Wata ahali nane Nayi alkawarin kula Dake da Abunda Ke Cikinki Zaki Haihu Lafiya da Izinin Lahi.."Tafada itama yanayinta ya sauya Zulaihat kuwa ce Tayi"Ni kuma Ina Jinki Tamkar Wata Haske gareni Wacce Ta Fitar dani Daga Duhu Zuwa Haske..Tabbas Haduwa Dake Wani Cigaba ne Sa"adiya Anty Farida kuma Bani da tacewa da ita sai dai ina mata addu"an Allah ya Biyata da al"jannah Firdausi..! Zaina Dake Sharan kwallah Tace"Nagode muku sosai...Allah ya saka muku da alheri ya gadda kuke Kula dani Allah ya Biya ku.."Suka amsa mata da Ameen suna Mata Mirmishi Farida Tashi Tayi ta Shige Cikin daki Tana Kokarin Boye Kukanta Wanda Tuni Zaina ta Riga Tagani Tana Fatan Allah yasa Tunanin Gida ya Dawo ma Farida Taji Tana son Komawa Gida Tabar wannan Rayuwar. Farida kuwa kuka Tayi Sosai kewar Ya"yanta ya Kamata Tana Kallon Hassana da Usaina acikin Idanuwanta Tana kuma Tuna Al"ameen arif Tana Tunanin yanzu wani Hali suke Ciki..? Bata sani ba Shekaru Biyar ba wasa ba Tasani sun kara Girma sai dai Tana Fatan Allah yasa Zubaida bata Azabar da ya'yanta ba,Allah ya bama Ya Musbahu sauke Nauyin Dake kansa na Kula da ya"yanta Ba kukan komai take ba sai kukan Kewan Uwa da Abunda ta Haifa wanda abaya baya taso mata sai yanzu Take jin wani iri kewa kamar Ta Rufe ido ta Bude ta ganta agabansu,Ta Rumgumesu ko Zataji Dadi Sai da taji Motsi kamar Za"a Shigo kana Tayi Saurin Share Hawayenta Zulaihat ne Tana Tambayanta me Zasu Dafa ne Tunda Lokacin Safiya ne Wajen 11:30am na Safe Cikin Shakewar Murya tace"Ki Dafa kuskus mai Kifi Naga Sa"adiya Tana so..! Zulaihat Tace"Sosai ma.." Daga Haka ta Fice tabar Farida na Cigaba da kokawa da Numfashinta Zulaihat bata Damu ba Domin indai Farida ne Lokaci bayan Lokaci Tana Shiga wannan Halin sai dai suna kyaleta Tayi Tunanin makomar Rayuwarta Da kanta Domin itama Tana Fatan Allah yasa Farida Ta daina wannan Rayuwar Bata Dace da ita ba sam. ******** *Bayan Wata Daya..* A zuwa Lokacin Tuni Cikin Jikin Dina ya Shiga watan Haihuwansa ita kawai ake Jira,Bangaran zaman Hajiya maimu agidan Abba zama take Cikin wayewa da kuma sanin Rayuwa Duk Rashin Son Mu"amala da ita da Umma keyi da ita ita bata damu Duk da ta Fahimci ga inda Umma ta karkata sai bata Biye mata ba ta Nuna ita Babbace mai ilimi da Hikima. Bata yadda Tayi zaman Daki Da tagama Taimakawa Dina Zata Fito Falo su Fara Hira da Nene,Umma kuwa Har Dakinta Take Bita su gaisa Ko Kitchen ne suna aiki Hajiya Maimuna bata zama Zata Shiga suyi tare Tun Nene na Hanata Har tagaji Ta bari Domim Hajiya maimu tace Bazata iya zama Haka tafi son ta Rika Motsa Jikinta Tun Umma na Basar da ita har tazo ta saki Tunda Tsakani ga Allah Hajiya maimuna bata da wata mtsala macece mai Kirki mai ibada da Dattako Harta da Abba ya Sheda haka wani Lokacin in ya Dawo Gida da wuri haka zasu zauna suyi ta Hira Tana Bashi wasu labaran dake Faruwa a Chan Sudan suna kuma Tattauna wasu lamuran Dake Faruwa anan Gida Nageria. Hatta da Zainab Ta saki itama Saboda Hajiya maimu ta iya zama da mutane Sosai ko Haddir da Zain sun Shaida wannan Duk kuma Rashin Sakin Fuskar Zain Baya iya ma Hajiya maimu Saboda ko bai nuna ya ganta ba ita bazata Damu Ba in ya Shigo Zata mai Sannu da Zuwa da kuma Tambayarsa ya aikinsa Gidan Alhaji Tsoho kuwa in su Nene zasu ba"a baribta abaya Tana Binsu suje su gaishesu su Hadu da Hajiya mama suyi ta Hira Kowa ya Shaida Lalacewar Dina Tasowarta Hannun kwamishina ne Ammh Sun Tabbatar da tana Hannun Hajiya Maimu da ba haka ba. Ita kanta Dinar Tayi tajin Haushi wai Hajiya maimu Tana wani Shige ma su Umma bata Damuwa da ita Domin ta sani yarinta ke Damun Dina Har yanzu bata san me Duniya take Ciki ba Shiyasa take kyaleta in tana wani mganar. Zakiya Tazo Sau Biyu Zuwanta na Farko Tazo gaida Hajiya maimuna ne domin Tunda tazo bata zo ta gaisheta ba,Daga wajen aiki ma Ta Shigo adaidaita tazo Motarta na wajen Ja"afar ya shiga Cikin gari da ita Shiyasa ta Shiga adaidaita azuwan ne ta gayamata Sun je kano ma sun Dawo Insha Allahu Zasu aure Soon Dina tayi mata Fatan Alheri suka Rabu akan cewa Zata kawo mata Ja"afar din su gaisa. Shine ta Cika alkawari Ranar Lahadi Ta kawo mata Ja"afar Bayan sun Je yawon Shakatawansu sun dawo wata irin Soyayya suke nuna juna kamar su Lashe juna ba ma kamar Zakiya Data ke jin kamar Tana Cikin wani sabuwar Duniya ne Saboda Farinciki bata Ji bata gani Komai nata Ja"afar ne harta yan wajen aikinta sun Sheda Ja"afar a mtsayin wanda Zata aura Sai Zundenta ake Ana Fadin Zata yi Kuskure domin wannan yaron ba Sa"an Auranta bane ammh ba wanda ya Tareta ganin Idanuwanta sun Rufe bata ji kuma Bata gani. Komai nata ta sakarmai Sirrinta kuma ba wanda bai sani ba,abu Dayane ta Boyemai Zamanta yar Bariki nuna mai take ita ta Allah ce Hatta da duka Atm dints suna Hannunsa Duka Dukiyar da Zakiya Tagama Wahalan Tarawa Zata karar dasu ga Ja"afar Ta maidashi wani Babban yaro kamar wani Hamshakin mai kudi Haka daman take so ya koma. Lokacin da Zakiya ta kawo Ja"afar wajen Dina aharaban Gidan ta barsa Cikin Mota Bayan ta Shiga gidan sun gaisa dasu Nene ta karisa Dakin Dina Hajiya maimu Afalo ta barta Tare dasu Nene,Dina Taga Fuskar Zakiya ba wani Annuri take Tambayanta meya faru Duk da itama Tana Fama da kanta nan Zakiya ta zauna Cikin Damuwa Tana gayama Dina Babanta Mallam Nuhu ya Kirata yace Ta hakura da auran Ja"afar makaryaci ne sunan daya Fada yasa an mai Bincike a anguwan daya ce sun Zauna an Tabbatar da mai da ba mai irin wannan sunan bama su sansa ba ya Sheda mata Yana Jiye mata Watarana Tayi kukan da idanuwanta Zakiya Tana gayama Dina Sharri kawai Mallam Nuhu yahada saboda kada ta auri Ja"afar ammh Ja"afar bashi da wata matsala kuma Bazata Rabu dashi ba In bazai daura musu aure ba zata samu mai Shige musu gaba suyu aure ammh Ita Bazata iya Rabuwa da Ja"afar ba. Ta Gayama Dina Zata Siya Musu Sabon Gida zasu je su gina sabon Rayuwarsu bayan aure Ko da Izinin Babanta ko Babu Taji Tagani ba wanda ya isa ya Hanata Insha Allahu nan da wata uku ta zama matar Ja"afar mamaki ya Cika Dina Tana ganin Tana Haukan son Zain Zakiya tana ganin Wautanta ashe ita in Tatashi nata sai ta Fita Domin bazata iya ja da Mahaifinta kan wani Namiji ba Dina Mamakin Zakiya ya Cika tana Tuna sanda Take Fadin Allah ya Rabata da Son Namijin kamar ya Kasheta ita kaxa ita kaza sai gashi kan Namijin Tana Neman Bijirema mganar Mahaifinta wanda Daman Tuni Ita ta zama salamammiya. Dina Dai Bata iya mgana ba aranta tace sai taga Ja"afar din nan da Zakiya ta Maidashi Rayuwarta Bata kara Jin Zakiya Tayi kuskure ba sai da take gayamata yadda ta mallakamai komai nata kuma Tana gayamata Ita Zata bashi Sadaki ya bada komai kayan aure ita zatayi ma kanta kamar dai itace Mijin,Dina dai mamaki ya kumeta Tama kasa mgana sai kallon Zakiya take tana Jinjina kai. Zakiya Ta Daddako Dina Kan Taje su gaisa da Ja"afar ta ganshi ba Domin ita kanta Dinar na Bukatar ganin Ja"afar din ba ahalin Data ke Ciki na nauyin Jiki Dana Ciki babu Abunda zai Sakata ta Fita ammh Tana son ganin wanda ya Rikatata Zakiya haka. Suna Fitowa Falo suka ci karo da Hajiya Maimuna da Nene wannan karon Harda Umma Dukkansu baki suka saki suna kallon Dina Dake wani Tafiya atale kamar yar kaciya da Uban Ciki agaba ita adole mai Tsohon Ciki abun sai da yabama Umma Dariya ta Murmusa acikin Ranta Tana Tunanin Dina Bata san me ake kira Haihuwa ba ammh Zata sani Kwananan Zata gane bata da wayau ne Ranar. Kafin Hajiya Maimun Tayi mgana Nene ta Rigata da Fadin"Ke kuma ina zaki da wannan Kayan Cikin agaba..!? Ko tsauyama kanki bakya yi..? Hajiya Maimuna Tace"Uhmm..Kema kya Fada dai sai ina Haka..? Dina tayi saurin Cewa"Zan raka Zakiya ne na kuma gaisa da Mijin da zata aura Tare suke.."Hajiya maimuna ta washe baki Tana Fadin"Au..To..To Masha Allah Aure Zakiya zatayi..? Allah ya sanya alheri ba Laifi kuje ku gaisa Motsa Jikin ma wani Abu ne da zai Taima ka miki.."Zakiya ta Sunkuyar dakai alamun taji kunya Nene da Umma suka Bita da wani kallo Tare da kallon Dina Wacce take taku Cikin Bakar Doguwar Rigar Dake Jikinta. Suna Fita Haraban Gidan Ja"afar na Cikin Mota sai da Zakiya tayi ma Glass din Knooking kana ya sauke glass din ta leka Tana mai mgana kana ya Bude Murfin Motan ya Fito Tundaga sama har kasa Dina ke karema Ja"afar kallo har ya kariso gabanta shi da Zakiya Tana masa kallon Kurillah Yana karisowa Gabanta sai ta basar Cikin Murna Zakiya kemai bayanin ga kawarta Dina Datake bashi Labari Abun ya bata mamaki Dataji Zakiya na Shararamai karyan Tayi aure ga Cikinta nan ma ta kusa Haihuwa Cikin Fara"a yake gaishe da Dina ta amsa Cikin Fara"a Tare kuma da yi musu Fatan alheri suna Tsaye aharaban Gidan sai ga Motar Zain ya Shigo Haraban Gidan Tundaga nesa ya gansu sai dai Ja"afar din bai gane ko waye ba suma ganinsa sai suka Sha Jinin Jikinsu Har yayi parking din Motarsa ya Dade kafin ya Bude Murfin Mota ya Fito yana Sabe da Coat din Suit din Dake Jikinsa Ta gabansu yabi ya wucesu kamar ma Allah baiyi Ruwansu a wajen ba Dukkansu Da kallo Suka Bisa Har ya Shige sai Dina da Zakiya suka kalli juna suka Basar kawai basu Dade ba sukayi ma Dina sallama suka Tafi ita kuma Tana Takun Daya Daya ta koma Cikin Gida Tana Tunanin ya zama Dole ta ankarar da Zakiya Kuskuran Datake Shirin aikatawa Taga yau Tana sauri ammh Zasu yi mgana ta waya. Haka kuwa akayi Washegari Dina Ta kira Zakiya awaya bayan sun gaisa take cemata"Any Zakiya wannan Auran da Zakiyi ba kuskure bane..? Zakiya Tace"Bangane kuskure ba..! Dina ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Nagani Gabadaya Hadin bai yi ba Wlh..Wannan yaron ba ajin auranki bane Zakiya Ko kyansa ne ya Rudeki..? Naga dai Cikin Abokan Shashancin Naki akwai masu kyau ba Laifi kuma Wadanda basai kin Wahala dasu ba Su Zasu Wahala dake Ko Dr.Imran kika Samu wlh sai yafi wannan Yaron da Zaki aura Kiyi mai Wahala Da Lafiyarki da Dukiyarki.."Tun kafin Dina Tagama mgana Ran Zakiya ya gama Baci Daman Tana Wajen aiki ne afusace Ta Daki Teburin Gabanta Ta Mike Tana Fadin"Bangane bai dace dani ba..? Wannan wata irin mganar Banza ce Dina..? Ban taba Zaton akwai Abunda zan nuna miki amtsayin abunda nake so ki kishi ba Dina Har kin manta yadda nayi Fadin Tashin Ganin Burinki ya Cika..? Har kin manta..? Wani Taimako na nema awajenki Da Zaki Fadamin mganar banza Da kike mganar su Dr.Imran din ai nasan dasu kuma abunda na Dade ina gayamiki Shi zan maimaita miki yau Bazan auri wanda mukayi Harkan Bariki ba Nagayamiki Salihi zan aura Wanda bai san komai ba kema kin san Kowani Wanzami baya son Jarfa kuma mganar zan Wahala Dashi ina Ruwanki Ni naji nakumaa gani ko Mahaifina Wlh bai isa ya hanani auran Ja"afar ba Ballatana ke Ba In zaki Fatan alheri kiyi in kuma bazaki yi ba ki Kama bakinki kawai malama.." Dina Da batayi wani mamakin Zakiya ba Ta Jinjina kai Tana Fadin"Allah ya bada sa"a ba Nufina kenan ba..? Yanzu yaushe ne auran..!? Cikin gatse Zakiya tace"Nan da wata uku lokacin nagama Tsarkake kaina Kinsan nagayamiki Sahihin aure zanyi kamar yadda Zakiyi nakki..Mun Riga mun gama mgana da ogansa na gareji zai nemi Rakiyan wasu abokansa Zuwa Wajen Baba sukaimai Sadaki Da kayan gaisuwan iyaye in ya karba Fine in bai karba su Dawo Dashi Gari da yawa na Tabbata bazamu Rasa masu Daura mana aure ba.." Dina ta Kara Jinjina kai kafin Tace"Zai ma yarda Insha Allahu.."sai Lokacin Zakiya ta Sauko Tace"Allah yasa kin san Baba da Fitina yagama Damun kansa da Zakiya kiyi aure..Yanzu na kawo mai Mijin yana Min Korafi.."Dina Dai batayi mgana ba Har Sukayi sallama da Zakiya Ta koma kuma Tana Tunanin Abubuwan da suka aikata Tunda ga Farko har karshe Cikin Jikinta Ta kalla wani Tunani ya Shiga ranta Dayasa Taji gabanta ya Fadi taji Tsoro ya Shiga ranta Sosai. *Ki biya ki karanta cikin Salama...* *Janafty...* 7/25/21, 9:05 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ..B21️⃣5️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Bayan sunyi Haka Da kwana Uku Da Dina Zakiya ta Shirya komai ogan Ja"afar mai suna Oga Usmanu Bakanike da wasu abokansa Guda Biyu Suka Tafi kano Dauke da Sadaki 100k sai gaisuwan iyaye 50k sai Kayan Saka Rana sai Dai Kawai mallam Nuhu ya gansu kwatsam Dayake Zakiyan ta basu Full Address. Lokacin da suka iso suka ce ga abunda ke Tafe dasu Bai yi mamaki ba Domin Zakiya daman ba Tun yau take Tsallake Umarninsa ba Bai yanke Hukunci ba sai da ya Kira Dangin Mahaifiyar Zakiya Dake Minjibir ya kora musu Duka Bayani sukuma sukace babu Ruwansu ya bata abunda take so Tunda Daman Shi kanshi Bata Darajashi ballatana su Matansa ma haka sukece gwara ya aura mata Shi Tunda ita Taji Tagani Koma miye ya Faru Daga baya sai dai akirashi Darasin Duniya. Da wannan Shawaran ya karbesu Hannu Bibbiyu ya kuma Saka musu Ranar aure Nan da wata uku Daman dsshi Wani abokinsa ne suka karbi Mganar su Oga Usman suna mamakin Yadda Auren yayi Nisa Haka ammh sai Mallam Nuhu yakauda Zargin Hakan aransu Da cewa Zakiya ta Bukaci Haka saboda akwai Shiryan shirya da zata karisa Da haka suka Rabu bayan anyi musu abinci sunci sun sha kana Suka Juya Cike da mamaki ganin Ilimi Tare da Dattakon Mallam Nuhu kuma amtsayin Mahaifin Zakiya sai dai Basu yi wani mamaki ba sanin Halin Rayuwar yau ka Haifi Mutum baka Haifi Halinsa ba. Tun Kafin su isa Bauchi Mallam Nuhu Da kansa ya Daga waya ya Kira Zakiya yace Mutanen DataTuromai ya karbesu kuma ya Sanya Ranar auranta nan da wata uku Lokacin Tagama Isbira"i Dinta Daga haka ya Datse Kiran Ranar sai da Zakiya Ta Hada musu kayattacen Party Ita Da Ja"afar na Happy Enggement,Farinciki kuwa kamar zai kasheta Taso Ta Kira Dina Ta gayamata Komai yayi daidai sai kuma Ta Tuna yadda suka Rabu Ranar Taji ranta ya Baci Domin ahalin Da Zakiya Take Ciki In har wani zai Nuna bayason Auranta da Ja"afar Sai Taji Ta Tsaneshi Hakan ce ta Faru Tsakaninta da Dina sannan kuma Tana ganin Dina Ta Mata Butulci bayan Tagama Wahalan ganin Ta samu wanda Take so ammh yau ita Dina na adawa da abunda take so da wannan Dalilin ta Tattara Dina ta Watsar Ta kama Harkokinta Tana Tunanin ko Zataji sai Bikin ya kusa Kilama Ta Rigata Shigewa Daga Cikin Domin ayanayin Zain Datake gani da Jin Labarinsa Bata da Tabbacin Burin Dina zai Cika aikuwa Zata so ganin Dina ta Dawo Tana Rokonta Mafita Wlh sai ta Wulakantata. ***** Washegarin Ranar da aka Sanya Ma Zakiya Rana Misalin karfe 3:00am,Na Dare Dina Tayi Fama da Juyin Ciki,Kamar Zata Haihu haka Ta Dinga Ihu Tana kukan Zata mutu Sai da Ta Da da Kowa na Gidan Banda Zain Wanda Tunda ya Fito yaji wai Dina ce ke kukan Zata mutu Tana Dafe baya Yayi Tsaki ya koma ya kulle kofarsa acikin Ransa yana Fadin Dama ta Mutu Uban kowa ya Huta bai Taba Tsanar wani abu yadda ya Tsani Dina ba. Hatta da Abba sai da ya Taso Umma ma Haka dasu Zainab,Nene ce da Umma suka Shiga Dakin suka Iske Hajiya maimuna na Rike da ita sai Kururuwa take Tana Dafe Ciki Da Baya Tana Fadin Zata mutu Hajiya maimu sai mata sannu Take Tana Fadin kiyi salati Dina bar wannan wayyo din nan Ammh ina ko Jinta ma Batayi Duk ta Fita kamaninta Nene sai sannu Take mata Umma kuwa kallo Daya Tayi mata ta gane ba Haihuwa bace in Haihuwa ne karyanta Wlh Abba ne ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai Shi kuma ya ce Hajiya Mama Ta taso Haddir Su Je su gani Ita Ta Bugamai Kofa ya Bude yana Barci Tace yazo su Tafi Gidan Abba an Kira Dina Zata Haihu Cikin Tura baki ya Sako Jallabiya ya Dau key din Mota suka Tafi suna Zuwa Tundaga Falon Gidan suke jin Nishin Dina da kukanta Abba da zainab da Umma suna Falo Zaune Sai ga su Hajiya mama Haddir suna gaisawa da Abba yace ya shiga ya gani Tare da Hajiya Mama suka Kutsa Dakin suka iske Dina Ta fita Daga kamaninta Ta Cire duka kayaanta Daga ita sai karamin Sikat duk ta Fixge kanta kamar Wacce ake yankawa Yana kallonta ya Fahinci Juyin Ciki ne ba Haihuwa bace Haka kuma yagama su Nene yace zai Tafi Cikin asibiti ya Dauko allura zai zo yayi mata Zata samu Sauki Daga Nene har Hajiya Maimuna sun Fara gajiya da Ihun Dina da kururuwa harda Hajiya maimuna Bayan Fitan Haddir ta Dauki Zanin Dina Tana Rufemata Fararan Cinyoyinta Dake Waje Tana Fadin"Don Allah dago kanki Dina..Dakike wannan Ihun banza naki bana Haihuwan bane Juyin Ciki ne Toh.." Duk da Dina na Jin azaba sai da Tadago Fuska Duk Majina da Hawaye Tana Fadin"Ummi Juyin Ciki..?kina Nufin wannan bama Nagudan bane..? Hajiya mama ta Murmusa Tana Kallon Dina Tace"Haihuwa..? Daman kuna Jinta ne kawai abaki baku santa ba ko nace kuna karban Haihuwan ne batare da kusan Wahalarta ba Naguda Dabam Take sai Kinzo yinta Zaki Tantance ya take ammh Wata mace Bata isa ta Fayyace miki ya Zafin Naguda yake ba Shiyasa Akace Mace mai Naguda kafarta Daya aduniya ne Daya Lahira in kuma Ta Rasu alokacin Haihuwa tayi Shahada Saboda Girma da kuma Wahalar Dake Cikin Ita kanta Nagudan da Haihuwan.." Dina Sai Taji kukanta ya kara Yawa,Tana Tunanin ahaka ma Ba Nagudan take yi ba kenan Innalillahi,Bata Taba Zaton Haka Zafin Masu Ciki yake ba Tasha karban Haihuwa Ta Dinga ma Mata Masifan sun damesu da kuka ashe ashe Haka suke ji sai ta kara Sakin kuka Tana jin Nadamar Biyema Shaearan zakiya yanzu duk wannan Wahalan Tanayinshi wajen Haihuwan Dan Shege ne kai Abun yazo mata Cikin wani yanayi ai sai ta koma Tana kukan Kasa kasa ba Dadewa Haddir yazo da Abun awom Naguda ya sake Dubata ya Tabbatar da ba ita bace ammh any Moment Tana iya Zuwa allurai yayi mata Harda na Barci nan kasa ta Bingire Tana Barci kamar wata mahaukaciya Hajiya maimuna da Nene suka Kamata suka maida saman Gado. Haddir shi ya Fita Falo yana ma Abba Bayanin ba Haihuwa bace Juyin Ciki ne,Umma na Gefe Sai da Ta Dara aranta tace Iskancin yarinyarnan dayawa yake Tunda tasan ta Gwale kafa Tabi Namiji ai sai ta Shiryama Haihuwa Sai alokacin Hankula suka kwanta Tunda ta samu Barci sai Gabda Asuba Haddir ya Dauki Hajiya mama suka Koma suka Iske Alhaji Tsoho ya kasa Komawa Barci Daman yace in Takai Safe bata Haihuwa Dole akaita wani asibitin Kudin ta Haihuwa achan kar abarta agida wani Abu ya Faru Sai yaji aiba Haihuwa bace Hajiya mama sai Fada take Tana Fadin sai Rakin Tsiya ammh da sai Iskanci Haddir na Jinta bai Tankata ba. Washegari da Safe yaje Office Din Zain bayan sun gaisa ya kallesa yana Fadin"Ya mai juyin Ciki. ? Hop bayan Tatashi ba Wata mtsala..? Zain na Cigaba da Duba Folder din Patient din dake gabansa yace"Wata mai Juyin Cikin kenan..? Haddir yace"Dina mana ko kana Nufin duk wannam Ihun Data Dinga yi baka Ji bane..? Karamin Tsaki Zain yaja kafin yace"Mtseww..Naji sai me..? Zan fito na Tayata ne ko kuwa.? Ai ita Ta Neman ma kanta Ta zata Haihuwan wasa ne..? Ai Mace Daya ce Zaka ga Tana Cikin Wannan Halin na Dimauce Firstlove dina itama Ina kyautata Zaton Duk inda Take ta Kusa Haihuwa kuma zanji ajikina Koda bama Tare ammh Wannan Tsinanniyar yarinya Dana Tsana wlh Ina addu"an Allah yasa ta Mutu Daga ita Har Abunda ke Cikinta.." Da Sauri Haddir yace"A'uzubillahi Haba Zain wannan kalmar bai Dace ba ko bakomai ai Cikin Jikinta nakane kuma babu kyau yima Bawa Fatan Mutuwa kaima ka sani.."Tsakin ya kara ja yana Fadin"Gwara ta mutu yanzu.ammh in ta Bari ta Rayuwa Ta kuma yarda Aka Dauramama aure Wlh sai na Kasheta da Bakincikina yadda Sanadinta na Rasa nawa Farincikina Nima sai Nayi sanadiyar Rasanata Farinciki.."Daga Haka kawai ya Mike yana gyaran Zaman Tektie din Wuyansa ya Bude Kofar Office din ya Fice ya bar Haddir baki Hamgame yana Binsa da kallo kai ya Girgiza yana Tunanin wani abu Tabbas yaga Tsanar Dina mai tsanani akwayan Idanun Zain Tabbas Zamansu bazai yi Dadi ba. Ranar Daya Dawo da yammah Nene ta matsamai sai ya Shiga ya Duba Dina Batare data Sani ba ya Gudu Gidan Alhaji Tsoho ko gidan ma bai kwana ba Washegari ma Haka Daga asibiti Chan ya wuce Daga Alhaji Tsoho har Hajiya mama ba wanda ya Tambayeshi Ba"asi Haddir ne ya san Abunda ya Faru Dayaje gidan Duba Dina Nene ke Fadamai har Abba na Fadan meyasa Take Takuramai ne ta Kyaleshi Tafasan Halin Dayake Ciki Dina kuwa Tagama Fita kamininta Tun kafin ma Ta Haifi Abunda ke Cikinta. ***** Kwana uku da Faruwar Haka Nagudar Gaske ta kama Dina Wannan karon da asuban Ranar Alhamis ne Tatashi da Abun Daga Shiga Tiolet Tayi Fitsari Sai bayanta ya Kage Daganan kuma sai Taji wani azaban Ciwo ya Biyo baya mai Wuyar Misali Ta Fara kuka Tana Kiran Sunan Hajiya maimu Wacce ke Tahiyan Karshe na Sallar asuba da Sauri Ta Sallame ta Runtuma cikin Bayin.. Halin Data samu Dina ya Tabbatar mata da Cewa Haihuwa ce Tazo mata Dakyar ta kamata suka Dawo Falo bayan Wayyo Allah da zan Mutu Ummi bayana Kafafuna kuguna Zan mutu Babu Abunda Dina Ke Fadi. Nan kan Cafet Ta kwantar da Dina Wacce ta Saki Jikinta Gabadaya Tana wani Mirginawa Cikin azaban Ciwo Bude Kofa Hajiya Maimun Tayi Ta Fita Zuwa Dakin Nene ta kwankwasa mata Daman itama Ta Idar da salla Lazimi Take Taji Buga Kofa arude Tatashi Ta Bude sai Taci karo da Hajiya maimuna Tun ma kafin tace wani Abu ta Fahimci yau Dina ana kan Gwiwa. Cikin Sauri Suka Nufi Dakin Umma Hayaniyarsu Nene ya Fito Da ita Daga Daki ita da Zainab Ganin Kofar Dakin Dinan abude yasa suka Fahinci komai Tare da Zainab suka Shiga Dakin sai dai Halin da Zainab Taga Dina yasa Dole ta Fice bata da komai ajikinta sai Wata karamar Rigar Barci Ko pant bata Dashi sai Faman Bude kafa Take Tana kiran Wayyo Allah Hajiya maimuna na Buge kafa Tana Fitowa suka ci karo da Abba ya dawo Masallaci Daman Zain bai kwama agidan ba Tun Ranar dayayi musu Yaji yana Gidan Alhaji Tsoho. Zainab Tagayama Abba Ga Halin da Dina ke Ciki,Ba bata Lokaci ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai shi kuma yayi mata addu"am sauka Lafiya Nan take ya Shaida ma Hajiya mama ya kuma Umarceta da Su Tafi ita da Haddir da Zain ammh Koda Suka Dawo masallaci Hajiya mama Ta taresu da Halin da ake Ciki Tsaki kawai Zain yayi ko mgana bai yi ba ya Shige Dakin Haddir ganin haka yasa Hajiya Mama tace Haddir din ya Taho suje ya Dubata bai yi gaddama ba ya Sauya kaya suka Tafi Gidan Abba. Koda sukaje Dina Ta Fara galabaita Da Fita Daga Cikin Hayyacinta Haddir yana ganinta yace Haihuwa ce,Shi kuma bai da wasu kayan aiki anan Sai dai atafi asibiti Hajiya mama Ta Kira Alhaji Tsoho ta gayamai yace Bayason mganar nan Ta Fasu a garin Bauchi ne Acigaba da mata addu"an Allah ya Sauketa Lafiya yanzu zai yi Mata addu"a aruwan Zamzam Zain zai zo Dashi yanzu..Da Mganar Alhaji Tsoho kowa yayi Cirko Cirko ana Jiran ikon Allah kawai ammh Duk mai Imani yaga Dina sai ya Tsausayamata Sosai Hatta ko da Umma yau da ita acikin Dakin tama manta Abunda Ke Cikin Dina Dan Shege ne. Misalin Karfe 7:30am na Safe Zain Da ko ajikinsa ya Shirya zai Tafi asibti Alhaji Tsoho ya Ritsashi ya kuma bashi Ruwan addu"a yace yakai Gida yanzu abama Dina tasha Ba yadda ya iya Haka ya karba ya Tafi yakai iyakarsa Falon Gidan inda Zainab da Haddir da Abba ke Zaune Abba kadai ya gaida ya Mikama Zainab Ruwan addu"an awani Jug ya Fice Daga Haddir har Abba kanzil ba wanda yace mai. Zainab Bata iya Shiga ba Umma ta kwalama Kira ta Leko Ta karba,Ta Shiga Dashi Nene da Hajiya Maimuna suka Tada Dina suka Bata Ruwan addu"a Kadan tasha ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi ai wasa Farin Girki sai Dina ta Rikice Naguda ta Dawo Sabuwa,Nene ta lekata Taga bama alamun kan yaro na Tahowa da alamun Dina Zatayi Tsawon Naguda kenan kuma mace mai Tsawon Naguda Wahala take Ci sosai. Tun abun ana Daukansa wasa Har yaWuce wasa Tunda Har Goma na Safe Dina na Fama bata Haihu ba,Daman tun Safen Hajiya Maimuna ta Kira Hajiya Batula tagayamata ta kuma ce ta gayama Kwamishina Cikin Dubara Allah yasa yana Gida yana jin Labarin Dina na Naguda Hankalinsa ya Tashi ya Hada musu Tafiya saboda Sauri ma Flight sukabi Zuwa Bauchi Saboda su isa kan Lokaci aikuwa Misalin 11am na safe sai gasu sun iso sai dai aka gansu kwatsam. Kwamishina Dai bai Shiga Dakin ba nan Falo ya Tsaya Wajensu Abba da Haddir wanda ke Shiga yana Dubata Lokaci Bayan Lokaci ammh Daganan suna iya jiyo muryan Dina Cikin Raini da galabaita Tana Kiran Zata Mutu Ko Hajiya Batula Data ga Halin da Dina ke Ciki sai da Taji Ta bata Tsausayi Tana Tunanin yau inda Dan Sunna ne ai baza"a ki kaita asibiti ba ammh Gudun Fasuwan mganar angwammace Tayi ta Shan wuya agida. Sun bata Ruwan addu"an Duka ta Shanye Haihuwa Shuru Alhaji Tsoho nata Kira Haddir na Gayamai bata Sauka ba yafara Tunanin akaita asibiti kada Yar Mutane ta Mutu Sai ya Kira Abba awaya yace mai Su Hajiya Mama su Dauki Daina Haddir ya kaisu wani asibitin Kudi Dake Cikin gari Ta Samu kulawa Achan kila ta sauka Lafiya Abba yake shaidama Haddir shi kuma Sai yace A"a Yace Abba ya Jirashi yana zuwa ya Fita da Sauri ya Shiga Mota sai Cikin asibiti Yana Zuwa kai Tsaye Office din Zain ya Nufa yana Shiga ya Iskesa yana Duba wata mara Lafiya yanayin yadda yaga Haddir din ya Shigo aransa yaji Dadi Domin ya zata Zai ce mai Dinar ta Mutu da ita da Abunda ke Cikinta ne sai kuma yaji sabanin Haka Haddir sai yayi ma karyan Cewa Alhaji Tsoho yace ya dauki kayan aiki Yaje gida ya Duba Dina Tunda Bangaransa ne kada Ta Mutu agida. Da Farko yaso yaki Zuwa ammh Jin Alhaji Tsoho ne ya Umarcesa sai yakasa yin gaddama hakanan ba Domin yaso ba ya Kwashi kayan aiki suka Tafi Kowanne ya Shiga Motarsa Koda suka je suka iske Abun mamaki Hatta su Abba suna Dakin,Suna Shiga suka iske Dina Rike da Hannun kwamishina Tana kuka Tana Cije baki Sai dai An Rufe mata Jiki da wani Zani Fadi take su kira mata Zain ta Nemi Yafiyarsa kafin ta Rasu sai gasu sun shigo.. Tana ganinsa Sai ta saki Hannun kwamishina Tana kallonsa Cikin Wani azaban Ciwon Da Dina Take Tunanin Bazata Rayu ba Burinta na auran zain bazai Cika ba Ta Kiran Sunansa"Zainnn..." Kallonta yayi Ido Cikin Ido ya Tsaya Cak da Karamin akwatin kayan aikin Dake Hannunsa Haddir ne ya Turasa yana Fadin"Kaje mana Zain.."Taku Zain ya Farayi Kowa na Binsa da kallo Har Zuwa gaban Dina Tun kafin ma ya Durkusa ta yafito Hannayensa Cikin Fitan Hayyaci Take Fadin"Ka yafemin Zain..Don Allah ka yafemin ko Zan mutu naje gaban Allah Cikin Salama Hakika na Cutar dakai Nice Silan komai nice Silan Barin Zaina Gida Nice Sillan Zubar da Kimarka Data iyayanka kuma Nice sillan Fushi da iyayenka keyi akanka Duka nice Sila ba Saboda komai ba sai saboda son da Nika maka da kuma Idona ya Rufe wajen Mallaka ka ammh Wlh ba Laifina bane Zakiya ce ta Dorani kan wannan Shawaran Don Allah ka yafemin.." Take Fada Tana kuka Ga Zafin Naguda Sai Umma sai suka zama wasu Shuru suna kallon Ikon Allah Kwamishina ya kalli Dina yana Fadin"Meya Faru Dota..?Dina na kuka tana Fadin"Kaima Daddy kamin afuwa nayi sanadiyar bata maka Suna...Domin neman wani Cikar Burina Ban Taba Duba Hakan dana aikata wani Illah ne gareka ba amtsayin ka na Mahifina Daya bani Kowani Jin Dadin Rayuwa.."Kanta ya Shafa Cikin Tsausayinta yana Fadin"Bakomai na yafe miki Duniya da Lahira Dina Allah ya saukeki Lafiya .! Zain kuwa Daya kusa yaji Wani irin Laifi Dina ke Rokonsa da ya yafemata Cikin Karfin Murya yace"Ina Jinki wani Laifi kikamin Da kike Rokona gafara..? Kuma ya akayi yau kika yarda duk kice sanadin komai.?."Dina Dataji wani azaban Ciwo ya Dawo mata ta Dafe bayanta Tana Fadin"Na Cutar dakai wajen Baka kaina kana Lalata dani Mganar gaskiya ni nakai kaina gareka bakai ka kawo kanka ba kuma na Zalunceka wajen kai sunanka Wajen Boka ya sakamaka Wata Muguwar Sha"awata wanda in baka Kusanceni bazaka iya Rayuwa ba.."Gabadaya Dakin sai aka Dauki Salati Hajiya Mama na Tafa Hannu Tana Fadin"Nifa Koda naji wannan Batu..". Ita kuwa Zainab Daman Tunda Dina Ta Fara mgana ta Kira Zafeera Bayan ta Dauka tace ta Saurari abunda ke Faruwa Umma kuwa acikin Ranta Sai Taji Wani iri ashe daman Zain ya Hadu da Shedaniyar Macece Dina kuwa Cikin azaban Ciwo ta Shiga Bada Labarin komai da yadda Zakiya Ta Hada Duka plan dinsu da komai da komai da hotunan Data Turama Zaina Har zuwa yau din nan sai da Ta Fadamusu ta karishe da kuka Tana Fadin"Don Allah Umma Nene Da Abba ku gafartamin Wlh ko hanyar Gidan Boka bansani ba Zakiya tajani takaini Ina Son Zain na Tsakani ga Allah banta Tunanin zan iya Cutar dashi ba..Gashi yau Ina Dauke da Cikinsa bata Hanyar aure ba,ina ji ajikina Mutuwa zan yi Me zan je na gayama Ubangijina kaichona Na Tabbata na zama asararriya na Taso Tun ina karama na Cikin Sakewa wanda Daddyna yabani Damar ganin Komai na Rayuwar nan zai iya Nema kuma in samu ashe ba haka bane Ina ji ajikina Zan Mutu..Mutuwa zan yi Don Allah Zain ka yafemin.." Zain da mamaki suka gaba Sandaranshi Dashi Idanuwansa sun kala sunyi Jajir yama kasa Wani Motsi Haddir kuwa daman aransa yasan za"a arina Zakiya tafi Dina zama Shedaniya Abba kuwa sai yaji wani Sanyi acikin Ransa Da Zain ba Cikin Hayyacinsa yake aikata Zina ba Hakama Umma da Nene Hajiya mama kuwa baki kawai ta Rike yayinda Hajiya Batula tace"Uhmm..Za"a rina Daman ammh ai Dukkanku Shedanu ne in ita Ta zama Wacce Shedan yama Fitsari akai kefa..? Hajiya Maimuna kuwa Ajiyar rai ta Sauke Tana Fadin"biri yayi kama da Mutum..Daman ni Tuni nasan wannan kawar Taki Dina ita ce ke Doraki kan wani Shedanci Tur Allah ya Wadaranku Wlh Daga ke har ita.."Daddy kuwa zaune kawai yake ya kasa mgana to yace me..? Shima yasan Shedaniya ce Sai ace kuma ka barsu tare da yarka..? Dole yaja Bakinsa yayi Shuru ransa na kuna wani Shashi na Zuciyarsa kuma yafi ganin Laifinsa akan kowa. Hajiya Maimuna Ta Kalleshi Cikin matse kwallah Tana Fadin"Duk Lalacewar Dina ba Laifin Kowa bane ssi naka Gaddafi..Da ace sanda Sarah ta Rasu ta kabamu Rikon Dina da Duk Haka bata Faru ba da kuma ace ka zauna ka kula da ita baka Sakrmata ba da Haka bata Faru ba Tun Sarah nada rai Siyasar ka kadai ka sakama gaba ba Ruwanka da Mtsalan iyalanka Koda ka auro Batula bata Saka kanta Wajen Bama Dina Tarbiya ba Tunda taga ga yadda ka Tsara Taka Rayuwr kai da yar Taka yau wa gari ya waya..?da kunyar Duniya Wlh gwara kunyar Lahira..! Kai ya Sunkuyar kawai bashi da tacewa Hajiya Mama ta gyada kai Tana Fadin"Duk da Haka Itama Batulan da nata Laifin ai Ko bakomai Dinar ya Take gareta Tunda Tana auran Ubanta Kuma ai Da na Kowa ne Mugu sai mai shi.."Su Umma suka ce Hakane Hajiya Batula bata ce komai Domin tasan gaskiya suka Fada Dina kuwa Mukurkusu kawai take Zain ya Dade yana kallonta kafin ya Murmusa Cikin Bakincikin ma sanin Dina yace"Ai shi Sharri dan aike ne..In da ka Turashi Zai je ammh kuma zai Dawo maka.." Yafada yana Tauna Lips dinsa na kasa Dina kuwa wani Zabura Tayi Tana Kiran Wayyo Allah Zata Mutu Mikewa Zain yayi yace Dukkansu suje waje banda Haddir zai Dubata Cike da al"ajabi suka Fice bama su kadai ba Hatta Zainab Da Shema da Inna Rukkaya da suka gama Sauraran Komai wannan al"ajabin ya Rufe musu. Suna Fita ya maida Kofar ya Kulle Yace Haddir ya Matso ya Taimakamai Dina nata Ihu ko Takanta Zain bai bi ya kware Zanin da aka Rufe Jikinta sai da Haddir ya kauda kai Shi kuwa aranshi yace ai babu wani Sauran Kima awajen Dina kuwa. Abun awon Naguda ya saka ya aunata sai yaga Haihuwan ta matso Kusa Tunda Yaron ya Fara Mutsu mutsun Fitowa Kanta ya Rike yana Fadin Tayi Nishi mai karfi Duk ta galabaita bata iyama Numfashi Sosai ammh Jin wani abu ya Tokare mata gaba yana Shirin yagata yasa ta kwamsama ihu mai karfi wamda yayi daidai da wani Kashi mai karfi yabiyo baya Cikin Ikon Allah kuma Tare da kan Bby,Haddir Da ya sanya Handglof ya Tari kan yaron Lokaci Daya ya Jawosa sai Dina ta Sauke wani Gwaran Numfashi ta koma ta Fadi Saman Cafet ta sauke Numfashi kamar wacce ta Mutu ta Dawo Tuni katon Jaririn da Haddir ya Daga kansa kasa Kafafunsa sama ya Daki Duwawunsa sai Kikaji ya Canyara kuka. "inya..Inya..!inya...inya....! *Ku Sake min min Uzuri don Allah...Yar"uwata ce Zatayi aure Wacce muka taso tare..Hidima da Surgullah sun min yawa ammh Zaku Dinga Jina Da Zarar na samu Lokaci..* *Janafty...* 7/29/21, 3:26 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣6️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Su Umma Dake Falo suka Hada Bakin Wajen Fadin Alhamdulillah Abba kuwa sai da sukayi Hannu da Kwamishina Suna ma Juna Barka Haka Hajiya maimuna da Hajiya Mama. Achan Dakin Kuwa Haddir bayan ya yanke ma yaron Cibi ya saka Zanin Dina Dake kan gado ya Nade Jaririn acikin Zani alokaci Daya yana kallon Jinjiri yana kara yima Allah Kirari Domin Gabadaya Yaron ba inda ya bar Zain Komai na yaron Kamar Shine yana karami Ko kadan Bai Dauko Dina ba yana Chan yana kallon Jaririn Har Uwa Ta Biyo Baya Dina na Kwance Tana maida Numfashi kasan Cafe din Duk ya baci da Jinin Haihuwa da kashin Dina,Zain Ya Dubata yaga bata Karu ba Ya Bude Dan akwatin Dayazo Dashi ya Dauko allura ya Fasa Wata karamar Kwalba ya Zuka yayi ma Dina a Hannu kafin Ya Zare safan Hannunsa Ko Takan Haddir Dake Nuna mai Jinjirin bai yi ba ya Dauki Karamin akwatinsa ya Bude Kofa ya Fita Su Hajiya Maimuna suka Taso mai Cikin wani yanayi yace su Shiga su gyara ta ita da Bby Hajiya Mama Fadi take badai Wata mtsala ko Zainullahi..? Zain Yana Bin Hanyar Dakinsa yace"Babu...Insha Allahu.."Daga Haka ya Shige dakinsa Ko su Abba Dake Falon bai bi Takai ba.ya Shige Dakinsa ya Bango Kofa kyankyamin kansa yake ji Tiolet kawai ya Shige wani abu na Shiga ransa yana Tunanin da ace Firstlove ce Da yanzu Da ita da Abunda ta Haifa da Jinin da komai zai Hada ya Rumgume ya kamkame ya nuna mata Tsatsan Godiyarsa Yana Chuda Jikinsa yana Jin Taruwan wasu Hawaye acikin kwarmin Idanuwansa. Umma da Hajiya Mama Dasu Nene da Hajiya Batula da Hajiya Maimun suka Yi Rige Rigen Shiga Dakin,Suna Shiga Haddir ya Mikama Hajiya Mama Jinjirin yana Fadin"Hajiya mama kalli kiga anya wannan Baby ba Photocopy Zain bane yana karami.." Da Sauri Hajiya mama ta karbeshi Tana kallonsa na wani Lokaci,Wasu Shekaru achan Baya suna Dawowa mata Ranar da Fatima da Aisha suka Haihu a asibitin Saulawa Wannan yaron Tamkar Zain ne Lokacin Dayazo Duniya Duk da yana Cikin Kazantan Haihuwa kamininsu bai bace ba. Tuni Hawaye sun Cika Idanuwan Hajiya mama Jikinta kuma ya karayin Sanyi Cikin Wani irin Tsausayama yaron da yazo Duniya yau tace"Allahu akbar..Allah kadirun Allahu akbar..Nene da Umma Zareena ku Taho kuga wani Ikon Allah.."Da Sauri suka Taho Wajenta Dama suna Wajen Su Hajiya Batula ne Inda Hajiya Maimu Ta kama Dina Zuwa Cikin Tiolet Don tayi mata wanka Hajiya Batula kuma Tana Kokarin Tsaftace Inda Kazanta Haihuwan ya bata sai Nene tace Cafet din Tsakar Wajen ya Tashi Aiki Ta Nananndeshi Afita Dashi kawai Sukaji Kiran Hajiya Mama. Su kansu Tsaye kawai suke sun kurama Sabon Haihuwan Ido Umma Taji Idanuwanta sun kawo Kwallah ba Domin Tasan komai da tace wannan Zainullahi ne yana karami Nene kuwa Sai da ta karbeshi Ta Rike a Hannunta Itama Jikinta yayi Sanyi Take Fadin"Allah Sarki..Tabbas wannan Jinin Zain ne..yadda kusan Zain Yana Jariri Ranar Daya Fito Duniya.Allah Sarki wannan yaron ga Shigo Duniya mai Cike da Rudani Iyayanka sun samar dakai bata Hanyar daya Dace ba Ina Rokon Allah ya Tsareka Daga aikata Zina Insha Allahu Bazaka Taso kaji wannan Bakin Fentin ba Tunda iyayanka Zasu zauna Waje Daya mu kuma Zamu Kokarin Boye Wannan Sirrin Kodomin ganin Cigabanka.."Take Fada Tana Sharan Kwallah haka ma su Umma Hajiya Mama na amsawa da Ameen. Nan da Nan Nene Ta taimakama Hajiya Batula suka yaye Cafet din suka Fita Dashi Haraban Gidan In mai Shara yazo zai Fitar Dashi Waje Haddir kuwa Dakin Zain ya Shiga Shima yayi wanka ya Iskesa har yafito yana Shiri zai Koma cikin asibiti Abba Shi ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Dina ta Sauka da Taimakon Zain da Haddir yayi Hamdalan da Fatan Allah ya Raya Daya Tambayi mai aka samu Abba yace Tukunah dai su Umma na Ciki sai sun Fito tukunnah. Yana Gama wayar sai ga Umma ta Fito ita ke gayamusu an samu Da Namiji Kwamishina sai da yayi kwallah acikin Ransa kuma yana Ta Neman ma yaron Tsari Daga aikata Abunda iyayansa suka aikata Suka Sameshi zainab Ta taimakama Umma suka Saka Ruwan Zafi Bayan ya Tafasa Hajiya Mama ta Diba Cikin Sabon Bahon wankan Bby Ta Faramai wanka Sauran kuma Umma Ta Diba abotiki Ta Mikama Hajiya Batula ta mikama Hajiya maimu Dake Tiolet Tanayima Dina Wanka. Dukkansu Suna Dakin Suna ganin Yadda Hajiya mama kema Jaririn wanka Cikin Lokaci ta Wankesa Tas Nene ta Miko Man Zaitun aka Shafemai Jiki Dashi Aka Sakamai kayan Sanyi masu Kyau Cikin wanda Nene ta Siyo ne,Sai Lokacin su Hajiya Maimuna suka Fito Daya Bayi Tagama Yima Dina wanka Duk tayi Laushi kamar ba ita ba Idanuwanta sai Lunshe wa suke Umma Ta kalli Hajiya Batula Dake gyaran Gadon Tana Fadin"da kin Fito mata da kayan da Zata saka Daga gani sun mata alluran Hutu.." Hajiya Mama Dake Kokarin Fita da Yaron Tace"Kada ku bari ta kwanta sai ta Cika Cikinta..Ke Nene Hado mata Shayi mai kauri kafin anjuma na koma Gida na Damo mata Kunun kanwanmu na Jegon mu na da.."Nene ta amsa da Toh kusan Tare suka Fita da Hajiya Mama da Nene Umma kuma Ta Tsaya Tana Taya Hajiya Batula gyaran Gadon Ganin su Dinan suna Tsaye ita kuma ta Dauko mata Kaya Hade da Pant da pad Ta Mikama Hajiya maimuna Tana Fadin"Kinga alamun akwai Ruwan Nono kuwa..? Hajiya Maimuna Tace"Eh Zai samu ko Zuwa gobe ne da yardan Allah.."Umma da Hajiya Batula suka ce Allah yasa Umma Fita Tayi Zuwa Falo Ita kuma Hajiya Maimuna ta Taimakama Dina ta saka Doguwar Hajiya batula ta Sakamata Pad dinta Cikin pant Ta bata ta saka kana suka Zaunar da ita Kokarin Kwanciya Take Hajiya maimuna Ta Riketa Tana Fadin"A"a kada ki kwanta sai kin sha Tea.." Cikin karaya da wani Sanyi Jiki da wani yanayin da Tunda Dina Take arayuwarta Bata Taba Tsintar kanta ba Tace"Zan kwanta ne Ummi..Ina jin wani iri.."Hajiya Batula tace"Ai wannan wani irin Dole ce haka kowacce mace Take ji in ta zama Uwa.."Jin haka yasa Dina Taji Toh in har hakane meyasa ta Zabi Ta Haihuwa bata Hanyar aure ba..?meyasa mataa Suke karuwanci su Haihu sukuma Yar da abunda suka Haifa Indai wannam Bakar azabar ake sha..? Lalle sun zama Jakuna Indai Kuwa suka Sha Wannan Wahalar suka kuma Banzatar da Abunda suka Haifa. Umma ce ta Shigo Dauke da Burner Ta saka Turaran Wuta Dakin ya Dauki Kamshi sai ga Nene da Wani katon Jug Dauke da Tea da Buradi awani Faranti Harda kwai ta bama Hajiya maimuna ita kuma ta mikama Dina ta karba Daman Cikinta ya Rarake Tana ji kamar Batataba Cin Abinci ba nan fa ta Fara Shan Tea din Tana Hadawa da kwai da Buredin kafin kace kwabo Ta gama dashi sai Zufa kawai yake Ketomata A Saman Goshinta Nene na kallonta tace"Masha Allah ta Fara samuwa.."Sukayi Mirmishi Dukkansu bayan Tagama tace Zata Sha Ruwa Umma ta Fita Taje Kitchen ta Dauko wani katon Fulas Cike da Ruwan zafi ta kawo shi aka Tsiyayamata da akabama Dina sai taki sha ta bata Rai Nene tace"karbi ki sha..Wacce Ta haihu bata Mu"amala da Ruwan sanyi Saboda Jego.."Dole Dina ta karba Tasha kana ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi Hajiya Batula tagyaramata kwanciya So take Ta Tambayesu Ina Jaririnta sai kuma Idanuwan Umma yasa Tayi Shuru da bakinta Umma da Nene suka Fita Zuwa Falo Inda Abba da kwamishina ke Zaune Yaron na Hannun Kwamishina ya kamkamesa Shi kuwa Abba yana Gefe yana waya da Baban kaduna yana gaya mishi Haihuwar Su Zain kuwa Tuni sun Fice Daga Gidan Asibiti Suka Koma Dukkansu Tunda sun bar Tarin patient achan. Bayan Komai ya kamallah Har Dina ta samu Barci Hajiya Mama ta koma Gida Taje ta Damo Kunun Da zai kawo Ruwan Nono,nan gidan Abba kuwa Zainab Ta Dafa kayattacen Abinci kowa yaci yasha Ruwa Natsuwa ta Dawo Jikinsa sai Lokacin Kwamishina yace Hajiya Batula ta Shirya su koma su Nene suka ce yammah Tayi yace kada su Damu Jirgi zasu bi Misalin Karfe 6:30pm na yammah Sai ga Haddir ya Shigo Bayansa Hajiya mama ne da Tabawa Dauke da katon Jug sai Kuma Alhaji Tsoho wanda ya Shigo yana Dafa sandansa nan fa su Umma baki yaki Rufuwa suna ta mai maraba da Zuwa Hakama Abba da kwamishina nan Falon ya Fara zama suka Gaisa Alhaji Tsoho yayi musu barka da arzkii Su Hajiya mama na Dakin da Dina take Lokacin Har Tatashi Tana Dauke da Jaririn Tana Kallonsa Wani Sonsa da kaunarsa na Ratsata Babban Abun Farincikinta yayi Kama da Zain ko ahaka ta samu ta Godema Allah gefe Daya kuma Tana Jin kunya Domin Kowa yanzu ya Fahimci Ita ce Shedaniyar ba Zain ba. Katon Jug aka cika mata da kunu aka mikamata kana Hajiya Mama ta karbi Jinjirin ta Fice Zuwa Falo ta Mikama Alhaji Tsoho ya karbeshi yana Hamdala Shima ya Dade yana kallon Sabon Haihuwar kafin yace"Masha Allahu...Abunda ya Hada Iyayenka Rabonka ne..Gashi yau kazo Duniya Allah ya Rayaka kan addinin Musulinci.."Gabadaya suka amsa da Ameen Dagasa yayi sama ya Fara mai Huduba acikin kunnuwansa Har ya gama kana yace Haddir ya bashi Dabinon Daya bashi yana Mikamai ya Karba ya saka abaki ya Tauna Kana ya sakama yaron abaki sai gashi ya Fara ma"mula Cikin Mirmishi Hajiya Mama tace"Allah ya Rayaka Bisa Sunna..Allah ya Tsare Farjinka Daga aikata Zina ALIYU ZAINULLAHI USMAN SAULAWA.." Gabadaya Kowa ya amsa da Ameen kenan Da Sunan Daddyn Abuja Alhaji Tsoho yayi mai Huduba bai wani Jima agidan ba Bayan Tafiyar Kwamishina da Hajiya Batula bayan Haddir ya Dawo Daga kaisu Filin Jirgi yazo ya maidasu Gida,aka bar su Umma da nene suna Taya Hajiya Maimun Hidima Zuwa Dare Tuni Haihuwan Dina ya Karade Duka Dangi Daddyn Abuja ya Kira yana yima Abba barka Tare da Jin Dadin Sunansa da Alhaji Tsoho ya saka Zafeera kuwa Dataji Labari Cewa Tayi an Cuci Daddyn Abuja da aka sakama Shege sunansa sai da Inna Rukayyah ta Tsawatarmata Zain kuwa ko kara ganinsa ma ba"ayiba Gidan Alhaji Tsoho ya kwana da Safe Umma ta Kira Hajiya Mama awaya Ta gayamata an samu Ruwan Nono har Dina ta Shayar da Aliyu wanda zasu Dinga Kira Daddy kowa yaron ya Shiga Ransa kuma yasa ya saki komai Hatta da Umma yanzu da ita ake komai Hakama Zainab Bata Taba Zaton Zata so yaron ba Haka tazo ta Daukeshi bayan Hajiya Mama tazo tamai wanka Ta Shigamai Hotuna Duk Ta Turama yan"uwa su Sadiq karami da Babba Faruq da Zareena da Zafeera wacce Data ga Hoton Sai da tace"Allah Sarki Fine Boy."ita kanta Taji Zuciyarta Tayi wani Rauni kadan. Kwana Hudu da Haihuwan Dina tana samun kulawa takowani Bangare Haihuwa ya Budeta takara zama wata katuwa sai dai Tayi baki Umma da Nene suna iya bakin Kokarinsu da Hajiya Mama Dake Jigila Kullum sai Tazo,Tuni Ruwan Nono ya samu Daddy sai sha Abunshi yake shima ya Fara zama Bulbul har kuma yau din Da ake kwana Hudu da Haihuwa Zain bai kara Takowa Gidan ba Har sai da Abba yayi mgana yace zai Kirashi awaya yamai Fada Dina Kuwa Bata Damu ba Domin Tagama yin Sanyi da Rayuwa Da Duniya kuma Har yau bata Kira Zakiya awaya ba yadda bata Nemeta ba itama Bata Nemeta ba Domin yanzu Gabadaya Taji Zakiya ta Fita acikin Ranta Tana da Tabbacin Ko yayane Zakiya ta bada Gudummuwa wajen Kara Lalacewar rayuwarta. Kowa ya Kira waya yayi Barka Hatta da Zareena dake U.S Ranar da Dina ta Cika kwana Biyar da Haihuwa sai ga Inna Hannatu ta iso da Kaya Niki Niki nan gidan Abba ta sauka Tunda sunyi mgana da Inna Rukayyah itama Tana Tafe Zaso su Suyi Taronsu isu isu Tundai Kaddaran Allah ya Riga ya Faru ba yadda bawa zai yi ita kanta Inna Hannatu Data Dauki yaron sai Taji ta saka ijiyesa Tana Kallonsa Tana Ayyyana Rabonsa ne Duk ya kawo Abunda ya Faru babu yadda Bawa ya iya. Aranar da Daddare Zain Yazo Gidan Domin Abba ya Kirashi yamai Fada Tare da Haddir suka zo Ya Shiga har Dakin Dakyar ya iyama Dina Sannu ta amsa Tana kallonsa kana Haddir ya Dauko Jinirin ya mikamai Ya karba da Farko ya kauda kai ne sai Daga baya ya Dawo da kallonsa kan yaron Sai da yaji gabansa ya Fadi Jikinsa yayi sanyi Kafafunwansa sunkasa Daukansa ya Dade yana kallon Yaron Shima yayi mai kur da ido yana Motsi da bakinsa da Hannunsa irin na Jarirai sai Zain yaji ya Fashe da kuka Wata Zuciya tace In ka Tsani Dina bai kamata ka Tsani Abunda ya Fito Daga Tsatson ka ba,kada ka manta babu Abunda wannan yaron yayi maka baisan komai ba Kai da Dina ne masu laifin bai kamata ka Dora ma yaron da yazo Duniya Jiya jiya ba karan Tsana.."Tunanin Dayake Tayi acikin Ransa kenan Baisan sadda yaji ya kamkame yaron ba yana Jin wani kaunarsa na Ratsata Daga Dina Har Haddir sai suka saki Baki suna kallonsa ya Dade Rumgume dashi kafin ya Saussautamai Rikon ya Dago Jajayen Idanuwan Dina yana kallonta kafin ya mikamata shi yana Fadin"Allah ya Rayashi..Allah ya saka ya Biyo Halin mai sunan ina Rokon mai Allah yamai Tsari da Daukan mugayen Hallayarki.."Yana gama Fadin haka ya sakarmata Shi ya juya yafice Haddir ya Kada kai ya mara mai baya Dina da Idanuwanta suka kawo Ruwa Tana kallon yaron tace"Ameen..Bana Fata Nima ya Biyoni..Ammh kuma ina Rokon Allah kada yasa yadda Nayi Rashin Uwa da kulawar Uba Wacce Tayi sanadin Zamowata haka kada Aliyu yayi Irinshi..Allah ya sa ka Tallfeshi Ka bashi Dukkan Tarbiyan Daya kamata.." Daga Gefenta Taji an ce Ameen Tana Juyawa Taga Hajiya Maimuna ne itama Cikin Sanyi da karaya yaron kawai Dina ta mikamata ta koma ta kwanta Tana Kokarin Hana kukanta Zuwa Ta Tuna wayar da sukayi da Daddynta kamar ma kuka yake yana Rokonta Gafara Domin yace shine Silan komai ita kuma tace Ta yafemai Domin bata ganin Laifinsa ya kasance Uba ne nagari mai Son abunda ya Haifa Kawai Gata da Rashin Kulawa ya sa ta Fada wata Rayuwa Dabam Wata Zuciyar tace"Dina Harda So..! ***** *Zaria..* Ranar da Dina ta Cika kwana Biyar da Haihuwa itama Zaina Tatashi Da Naguda Bata Cika EDD dinta da kwana Goma ba, Da Safe ne Nagudan ya Tashi Allah yasa Farida na Gida Hankali Tashe ta Fita Zuwa Bakin Titi ta samo Mota Koda ta Dawo ta Iske Duka kayan Haihuwan Zulaihat ta Hadasu Waje Daya ta kuma sanya Zaina Hijabi wacce ke Zaune Tana Cijewa sai dai su kansu sun jinjinamata kan wannan Dauriyan nata suka kamota Zuwa waje bayan sun sakata amota Zulaihat ta Koma ta Dauko akwatin da Key ta Kulle Gidan suka Shiga Mota sai asibitin. Asibitin Data ke awo suka ce Wato Almadina suna Zuwa aka karbeta sai Labour Room Suka kuma suka zauna zaman Jiran Tsammani Hankalinsu tashe Tun suna Jiran Labarin Haihuwa Zaina Shuru kawai kake ji Likiti yace su kara Jira Haihuwa bata kariso ba ammh Zaina na Ciki sai Shan bakar Wahala take ahaka fa har Dare ba wani Labari Nan asibitin suka Wuni ita da Zulaihat ko Ruwa basu iya kaiwa baki ba Sallah kadai ke Tadasu addu"a kawai suke Allah ya Sauki Sa"adiya Lafiya. Farida ta Fara Tsorata ne ganin Har gari ya waye Zaina bata Haihuwa da asuba sun shiga wajenta da kuka suka Fito sau Biyu ana sakamata Ruwan Naguda ammh Shuru ba Haihuwa Zaina Duk Dauriyan Ta Riga Tagama galabaita Tana kuka Tana Fadin Anty Farida ta yafemata In ta Mutu Taje Bauchi Gidan Dr.Abubakar Saulawa ta basu labarin Rasuwarta su Cire Tsammani irin mganganun Datayi ta gayamusu kenan suka Fito da Gudu suna kuka Zulaihat Da bata san Zafin Haihuwa ba Taji Tayi Tir da Rayuwar yan Barikin Da zasu yi Ciki a bariki kuma su Haihu Cikin wannan Bakar azaban Tun Likitoci na basu Hakuri Har Farida ta Sare ta Fara Bala"i Tana Fadin wani irin Haihuwa ce zasu bar yarinyar Karfinta ya kare sai Taso da Naguda suke suna bama Yarinya Wahala ammh suna Fadin su kara Hakuri Zata Haihu Ganin haka yasa Dr Dake On Duty yace sai dai ayi mata Operaton Farida tace Ta yarda gwara ayi mata acire Abunda ke Cikinta da wannan Bakar azabar Data ke sha. Nan da nan Farida Ta Biya Kudin aiki wajen 100+,Faridan Ita ta saka Hannu atakardan aiki aka Fara Shirin Shiga da Zaina Dakin Tiyata Lokacin da za"a Tafi da ita haka ta kamkame Hannayensu Farida tana kuka Tana Fadin su yafemata suma kukan suke suna Fadin Insha Allahu Za"ayi aiki Lafiya Suna Ji suna gani aka Shiga da Ita Dakin Tiyata Nan Farida ta bar Zulaihat Tatafi Masallacin Cikin asibitin Tana da addu'an Allah yasa ayi aikin nan Cikin Nasara In Sa"adiya Ta Rasu Bata da karfin Gwiwan Tunkaran Danginta da wannan labarin ba Uwa uba Firstlove mijinta Da duk inda Take ya Tabbata yana ji ajikinsa Sa"adiya Tana Raye. Tabbas Zain yaji ajikinsa Wani Abu na Faruwa yana asibiti acikin Office dinsa yana Duba Patient yaji gabansa ya Fadi Jikinsa yayi sanyi yaji wani Sanyi na Shiga Jikinsa Daman Tun bayan barin Zaina Gida yana Jin wannan yanayin Lokaci Bayan Lokaci Dayaji haka sai ya Danganta Haka Da Zainarsa ce koma Miye wani abu mara Dadi na Faruwa da ita. Kansa ya Dafe bayan ya sallami mara Lafiya Yana Jin Jikinsa kamar ba nashi ba afili ya Furta.."Kodai yau Firstlove zata Haihu ne..? Tuni yaji gabansa ya kara Fadi da Sauri ya Mike yana Jin Wani Zufa na Ketomai Ficewa Yayi Daga Office din Lokacin misalin 12pm na rana Masallacin asibitin ya Shiga bayan yayi alwala ya Dauki Qur"ani yana ta karantawa Domin yaji Faduwar gaban nashi yayi yawa ne bayan ya gama karatun ya Daga Hannu yana Addu"an Duk inda Firstlove Take Allah ya kareta Allah ya Sauketa Lafiya yana nan Cikin masallacin har aka Kira sallah bayan an Tada sallar an Idar ya karisa ga liman yace a sakashi a addu"a matarsa na kan Gwiwa nan da nan Liman ya sanar yana ta addu"a Jama"a na amsawa da Ameen Haddir na msallacin mamaki ya Cikashi bayan an gama Addu"o'in Jama"a sun watse Kana Haddir ya Karisa kusa da Zain yana kallonsa yace"Wata matar Taka ce Zata Haihu.? Bai Tankamai ba sai da suka Fito Daga Cikin Masallacin kana ya kalli Haddir yana Fadin"Wata mata gareni Bayan Firstlove?itace Zata Haihu yau naji ajikina.."Yana gama Fadamai haka ya wuce ya Nufi Cikin asibitin Haddir ya Bishi da kallon Tsausayi kawai kafin ya Kada kai yana Fadin"Toh..Allah ya Rabasu Lafiya.." Adaidai kuma Lokacin ne Daya Daga Cikin Nurse din da suka Shiga Tiyata da Zaina ta Fito Fuskarta Cikin Fara"a Zulaihat Dake kai da kawo a kofar Wajen Tataso Tana Fadin"likita yaya..? Ta Sauka..? Nurse din Tace"Alhamdulillah anyi aiki Cikin Nasara mun samu Nasara Ciro mata Ya"ya Biyu Duka mata.."Saboda Farinciki da Murna Jikinta Zulaihat ta Fada Tana Fadin"Alhamdulillah...Allah mun Gode maka ina ita Sa"adiyan Lafiya take ko.? Nurse din na Mirmishi Musulmace sun saba ganin haka Tace"Eh..Bata Farfado ba ammh Zuwa 4 zata Farfado yanzu za"a gyara su ita da Bbys din akawosu Dakin Hutu."Zulaihat Ta kara Daka Tsallake Tana Fadin"Kai Masha Allah..'Daganan kawai ta Kwashi Gudu Zuwa Haraban asibitin Msallacin ta Nufa Daman Faridan Tagayamata Tana Masallaci Tana Shiga ta Isketa Tana ta Jan carbi da Gudu Ta Fada Jikinta Tana Fadin"Albishirinki Anty Farida..? Farida ta Zabura Tana Fadin"Goro Fari kal Zulaihat..gayamin Sa"adiya ta Haihu ne..? Zulaihat tace"Ta haihu Yan Biyu Anty Farida duka Mata.."Ido Farida ta Zaro kafin ta Rumgume Zulaihat Tana Fadin"Alhamdulillah..Masha Allah Allah ne abun Godiya.."mutanen Cikin msallacin sai kallonsu suke Tashi Sukayi Bakinsu yaki Rufuwa Suka Nufi Cikin asibitinn... *Ku kara min Hakuri Don Allah..Banyi Editing ba* *Shakira...* 8/2/21, 2:37 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣7️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Da gudu Gudu Sauri Sauri suka karisa Cikin asibitin Suna Isowa Wasu Nurses guda Biyu suna Fitowa Da Jariran Guda Biyu Cikin kayan alfarma Daman Da zasu Shiga Tiyatan Sun karbi kayan Haihuwa. Hannu na rawa Jiki na Rawa Farida Da Zulaihat suka karbi yaran Suna kallonsu kwallar Farinciki ya Cika Musu Zuciya Duk da Farida Bata Taba ganin Firstlove ba ammh ta Tabbata Wadanan yaran Dashi Suke kama kuma Domin Doguwar Fuska Sa"adiya Kadai suka Dauko ammh Har Launin Fata na Ubansu ne,Farida Taji Saukan Hawaye Bisa Kuncinta Lokacin Data Haifi su Hassana yana Dawo mata kamar yau ne Zulaihat ne ta kariso kusa da Ita Tana Nuna mata na Hannunta Tana Fadin"Anty Farida kalli Basa kama da Sa"adiya..? Farida na Share Hawayenta Tace"Ammh suna kuma da Mahaifinsu ko Shakka bana yi.."Zulaihat Tace"Lalle kuwa In Hakane Mijin Sa"adiya Gangariya ne.."Mganarta Sai da ta saka Farida ta Murmusa suna nan Tsaye Likitan ya Fito Farida namai Godiya yace yanzu za"a Gunguro da Sa"adiya Za"a kaita Dakin Hutu Nan da anjuma Zata Farfado in sun shiga Dakin Kada Suyi Hayaniya suka ce Toh ko Minti Goma ba"ayi ba aka Gungurota Zuwa Daki na Musamman da Farida Tace a sskata suka Bi bayansu suna Shiga suka Tsaya kanta suna kallonta yadda Tayi wani iri Duk Wahalan Nagudan yagama Tafiya Da ita basu Dade aciki ba Nurse suka karbi yaran suka sakasu Cikin Dan gadonsu sukace suje waje su Jira Bayan Sun Fito ne Farida ta bama Zulaihat 1k tace ta koma Gida Tayi musu Abinci Ta kuma Hado ma Sa"adiya Zannuwa da Riga Tazo da kayan Tea da Fulas Din Ruwan Zafi da Zulaihat din ta Nemi su Tafi Tare sai tace baza"a bar Sa"adiya ba kowa ba Taje ta Dawo. Zulaihat na Tafiya Farida Ta Daga waya ta Kira Alhaji Badamasi Tagayamai Daman Shima yasan Labarin Zaina kanwar Farida ne ganinta ne kawai bai taba yi ba Yana Kashe ma Farida da kudi Sosai Tana gayamai Sa"adiya Ta Haihu nan take ya Turo mata 150k Farida Taji Dadi Duk da Tana da kudi a Hannunta ammh Tana Bukatar kudu sosai ga Hidiman asibiti Gana masu Jego da Babys. Bayan Shi sai ta Kira Uwar Mata Ta gayamata Uwar mata Dake Cikin Shagonta ita da Aminiyarta Hajiya Zabba"u Ta Tabe baki Tana Fadin"Wai Don Allah Farida waye Uban Cikin yarinyar nan..?gwara ki Maidamai kayansa ina Zaki iya Wahalan yara har Guda Biyu alokaci Daya..? Farida Tace"Suna da Uba kamar Kowani Yaron Sunna..Kada ki Damu Lokacin Kadan yaRage na Sada Sa"diya da Danginta ammh mganar ina Zan iya kula da yara Biyu alokaci Daya baki da Damuwar wannan Kafin Sa"adiya Ta Haihu yan Biyu ni nafara Haihuwansu kinga kuwa Duk wanda Zai baki labarin Yaya Haihuwansu da Renonsu Barin Nice.."Uwar Mata Tace"Uhm..Allah ya raya Zan Shigo Sati na sama Sai muzo Muyi Barka Domin kece gaskiya Sholly.."Farida bata ce komai ba ta Datse Kiran Tana Wani Tunani ita kadai. Har Zulaihat ta Dawo Sadiya bata Farka ba koda ta Dawo da kaya Niki Niki Ita da kacharalle suka Dawo Taje gida sai gashi yazo Shine take gayamai a asibiti suka kwana Jin Sadiya ta Haihu har yara Biyu Kacharalle nata Murna sun zo sun iske Farida na masallaci Sallar La"asar ta Shiga Dakin da Zaina Take ta Ijiye Fulas din Datazo Dashi da kayan Tea sai Basket din Data sako Abinci sai Ledan kayan Sadiya suka Fito nan suka ci karo da Farida Sun Tsaya suna gaisawa ne Likita ya Shiga Daki bai wani Jima ba ya Fito yana gaya musu Sadiya ta Farfado ya kuma ce kada su bata wani abu sai Zuwa Gobe da Safe Saboda aikin Jikinta suka ce nan suka Dumguma Cikin Dakin suka isketa Zaune an karamata Filo abaya Farida da Zulaihat Rumgumeta sukayi suna Murna itama Farinciki ya Cika Ranta Kacharalle na Gefe shima yana Dariya. Zulaihat da Farida suka Daukomata yaran acikin karamin Gadonsu suka Sauke mata kan Jikinta Ta kura musu Ido Tana kallonsu wani irin Abu na yawo acikin Ranta Kana ta Dago Tana kallon Farida Kafin Tace"Anty Farida..Gabadaya yaran nan basu Dauko ni ba Kinsan wa suka Dauko..? Da Zulaihat da Farida suka Hada Baki Wajen Fadin"Firstlove...! Mirmishi ta saki sai ga Hawaye bata Damu Data Share ba tace"Na Tuna Watarana Lokacin Tun Farkon auranmu ne muna Gaddama da Firstlove yana Fadin in na Haihu,Yaran Dashi zasu Dinga Kama Badani ba Ni kuma na Dinga Cewa Dani zasu Dinga kama muka kulla alkawarin indai na Haihu sukayi kama Dashi Yaci Gasan in kuma sukayi kama Dani ni naci gasan.."Tafada Tana Tuna Lokacin da Abun ya Faru. Farida Tace"Lalle...Aikuwa ya Cinye wannan gasan wannan karon.."Zaina Ta Share Hawayenta Batare da Tayi mgana ba addu"a take ma yaran acikin Ranta Bayan Tagama Ta Mikama su Farida su suka mikama Kacharalle ya gansu yayi Allah ya Raya. Nan asibitin yakai Dare kana ya Tafi daga Farida Har Zulaihat nan suka kwana Tare da Zaina Kowa baya son Tafiya,Washegari ma Jikin Sadiyar da sauki Tunda Har Farida Ta Taimakama sunje Bayi ta Dauraye mata Jiki kana Tasha Tea Likita yazo ya Dubata yaran kuma Tun Safe Nurse suka zo suka karbesu sukayi musu wanka. ******* *Bauchi..* Ayayinda Zaina Ta kwana Daya a asibiti da Haihuwa anan Bauchi Ranar alhamis ta Zagayo Gidan Abba na Cike da yan"uwana ana ta Hidiman Sunan Wanda Duka Hidiman Abba ne yayi Shi Tunda Uban gayyar ba wanda ya kara ganinsa Tun Ranar da Abba ya sashi Zuwan Dole. Inna Rukayyah ma ta iso Tun Jiya kuma Gidan Abban ta Sauka Da Farko Tace bazata zo ba Sai Da Inna Hannatu ta saka baki kana Daga Kaduna Kuwa Ba wanda yazo Daga Baban Kaduna Har Mom Iklima sai dai sun Kira waya sai Mama Safiya ce Tazo,Tunda anyi ma Mijinta Takwara Wanda Zainab tace Za"a Dinga kiran sa ARMAN. Bangaran Kwamishina kuwa Hajiya Batula Tazo Ita da Waleed da Walida Da kayan Barka Niki Niki na Bby dana Dina Wanda Kwamishina ya Siya mata sai kayan gara bangaran su Abinci Booth Guda Tazo Dashi Abba nata Fada ma,Hajiya maimuna kuwa ta Kira Chan Sudan ta sanar da Mahaifiyarsu Haihuwar Dina Tayi barka Har aka bama Dinan Tayi mata Barka da Fadan Yadda Zata kula da kanta Duk Da Kowa na iya bakin Kokarinsa Daman Da Hajiya maimuna Zata zo Tazo da kayan gyara da kayan kamshi irin nasu na Sudan yanzu sai ta Fito Dashi Tana yima Dina amfani Dashi. Abba Shi ya siya Raguna Guda Biyun da aka yankama Aliyu arman Shi kuma yayi Hidiman Abincin Da aka Girka da komai dai da komai Hatta da kayan Sawa ya Dinkama Dina Alhaji Tsoho Dayaji labari yana ta sakama Abba albarka Daddy Abuja ma ya aiko Mama Safiya da Sakon kayan Bby abama Takwaransa Kowa yayi bajinta kamar Ba wani Abu daya Faru Hatta Haddir sai da ya Siyaman Arman kaya masu kyau ko bakomai Jinin Zain ne Uban gayya ne kadai bai Damu ba Sai dai Kullin ina kallon Hoton Arman a wayarsa Wanda Haddir ya Daukesa ya Turomai Allah naji yana gani Allah ya Doramai son yaron ko bakomai Shi ya Digashi har yazo Duniya. Labarin Abunda Dina ta aikata ita da kawarta Zakiya yagama Zaga kannuwan Dangi kowa yaji sai yace Biri yayi kama da Mutum Daman Zakiya Daga ganinta Tafi Dina iya Shedanci Kana kuma Kowa Kwamishina yake Dorama alhakin Komai da Hajiya Batula wacce bata Dauki da A ya' ba koda ita bata Dauketa mataayin Uba ba ammh akallah ta Sauke Nauyin Dake kanta Allah bazai kamata Da Laifin yin Watsi da Rayuwar Dina ba. Alhaji Tsoho Da Hajiya Mama ke Koramai Abunda ya Faru Mirmishi kawai yayi yace mata"Na sani..Nasan Daman hakan zai ne ya Faru.." Cikin Mamaki Hajiya mama ke kallonsa kafin tace"Kasani fa kace..? Alhaji Tsoho yace"Eh..Tun bayan Faruwan lamari Zain yazo ya gayamin Wata mgana na Dora ayar Tambaya akansa na Fahimci ya Hadu da Shedaniyar mace tamai Sihiri Shi kuma yana Wasa da Addu"a Shiyasa Abun yayi Tasiri akansa Ammh Yanzu Insha Allahu ba ita ba Ko Wata ma Bazata iya Nasara akan Duka Jikokina ba.." Hajiya Mama ta Jinjina kai Kawai Tana Fadin"Allah ya Tsaremu Ai ko da Chan ma Hadiru yafi Shi Kokarin Azkar nake ganin.."Alhaji Tsoho yace"Ada kika sani ammh yanzu ya Dage...Mganar Hadiru kuma daman nagaji da ganinsa ahaka Bayan Yarinyar nan tayi Arba"in zan Daura musu aure da Zainullahi na Cika alkawarin Dana Dauka Zan Dawo kan Hadiru da yarinyar nan yar Wajen Usman itama.." Hajiya Mama tace"Wacce Zainab ko Zafeera..? Alhaji Tsoho yace"Zafeeran Dai Shedaniyar yarinya Ki Duba fa Taki yaron nan Ahmad kwanaki Aliyu ke gayamin yazo yana gayamai an sakamai Rana Aure.."Hajiya mama ta Waro Ido Tana Fadin"Kai don Allah...? Alhaji Tsoho yace"Ah..ya zauna yana Binta Tanamai Wulakanci ammh nayi Mata Takaicin Rasa Gwarzon Namiji irin yaron nan Ahmed.."Hajiya Mama tace"Uhm Sha"anin Zafeera sai ita Bakar Zuciya kamar Hannatu ce Uwarta Bashir Ubanta Yanzu hakama Hutu suke Inji Rukayyah ammh Datace ko Zata zo ne tace Allah ya Tsareta Zuwa Sunan Dan Shege.."Alhaji Tsoho yace"Asssha..Kalmar Tayi Muni Da yawa..Allah ya Shiryeta bari dai nagama da Zainullahi kansu zan Dawo ita da Hadiru Wlh sai nayi musu Tsiyata.."Hajiya Mama Tace"Wlh Daka kyautamin.." Da haka suka cigaba da Tattaunawa kan Batun ne acikin Ran Alhaji Tsoho kuwa Allah kadai yasan Abunda yake Tufka yana Warwara. **** Zakiya Bata san Dina ta Haihu ba Tunda bata Kirata ba itama Tuni ta Fita Batunta Tana ganin Dina Zata Juya mata baya ganin ta kusa samun Cikar Burinta Kawarta ce ta Kirata wacce suka bar Ajiyar Motar Dina agidanta akan Suzo su Dauka an mata Transfer din Wajen aiki Zata Bar Gidan Data kama Haya sai da ma Ta Kira Zakiya ta iya Tunawa Da wata Motar Dina Domin ta manta Shaf Tunda suka kaita ajiya da Farko Tayi Tunanin ta Kira Dinar ne ta gayamata ta kuma ce sai Taje ta Dauki Motarta sai kuma ta Sauya Shawara bayan Tatashi Daga wajen aiki Misalin 3pm na Rana Ta Kira Ja"afar awaya tace kada yazo Daukanta Zataje kaima Dina Motarta yace Shikenan in Taje ta Kirashi yazo Ya Dauketa tace Shikenan.. Daganan Ta samu abun Hawa Zuwa Gidan kawarta Bayan sun gaisa ne Ta bata Key din Motar Dama ita suka bama wa Koda Mtsalan Sauyawa Motar waje ya kama Tunda ba Gidanta bane irin Gidan Hayane mai Dauke da Flat Falt ba kamar ita da Ta Siyi nata Gidan ba ita kuma Dina Mahaifinta ya Siya mata,Bayan Ta karbi Key din Motar sukayi sallama Ta shiga Motar tana wani yamutsa Fuska ganin Motar Duk Tayi kura batama Zata motar Zata Tashi ba ganin an Dade ba"a aiki Da ita Daganan bata Zarce ko"ina ba sai Gidan Abba. Tana Zuwa Kofar Get din Tayi Hon Megadi ya Bude mata ta Sulala Ciki a  parking Space ta faka Motar kana ta Fito Tana gyara Zaman gyalen Dake Kafadanta Abunda ya bata mamaki ganin Waleed da Waleda a Haraban gidan suna wasa da Su Saudart Abun sai ya bata mamaki Cikin Haka ta Kwalama Waleed kira yana ganinta ya Taho yana gaisheta Cikin Harshen Turanci Kansa ta Dafa Tana Fadin"Waleed kai da wa kuka zo kuma..? Waleed yace"Mu da Mom muka Zo Anty Dina ce ta Haihu yau Suna Kema kin zo ne muje kiga Arman Anty Zakiya Bby mai kyau ne.."Mamaki da Al"ajabi ya Daskarar Da Zakiya Tun Lokacin da Waleed yace Dina ta Haihu Lalle Dina Wuyanta ya isa yanka yau itace Har Zata Haihu yau suna ammh Bata da Labari Lalle kuwa Bari ta Shiga Ta ga da wani Ido Dina Zata kalleta ai Ta Dauka ko bata Cikin Hayyacinta Zata Tuna da ita. Afusace ta Shiga Falon Gidan ko Sallama su Inna Rukayyah ne da su Umma ke Zazzaune afalon Zakiya Bata ji kunya ba Haka ta Wucesu Fuu Zuwa Dakin Dinar Data ga Kofar yau abude da Mutane aciki Su Umma suka Bita da Kallo Inna Hannatu tace"Wannan ba Shedaniyar kawar Dinan can bane..!? Umma tace"Itace..Mana..'Inna Hannatu tace"Kuma koke barinta Tana Shigowa gidanan.? Ai bai kamata kuna barinta Tana Shigowa ba,Ko itama Dinar Domin kaddara ta Hadamu ne da Tuni Ta bar Gidan nan itama matsiyaci.."Nene Tace"Ai tama kwana Biyu bata zo Gidan ba sai yau.."Inna Hannatu tace"Yadai kamata kam a tsawarta mata Irin su ai ba Mutanen Kirki bane barinsu suna Shigowa Gidan nan akwai Damuwa.." Zakiya kuwa Tana Shiga Dakin Ko Sallama batayi ba Hajiya Batula ne ke Ciki ita da Hajiya maimuna Wacce kema Arman wanka Dina na Zaune bakin gado Tana sanye cikin wani Leshi mai Tsada wanda Kwamishina yayi mata Fuskarta Duk Tayi Subu Subu Saboda Hajiya maimuna Bata mata Wasa Tanajin Ruwan zafi yadda ya kamata. Kan Dina na Sunkuya ne Tana ganin yadda Ruwan Nononta ke Zuba Taji Zakiya ta Kira Sunanta kai Tsaye da Sauri ta Dago Tana kallonta bama ita ba Hatta su Hajiya Batula sai da suka Dago Suna kallonta ba Wanda Ma ta Tsaya ta gaida  Cikinsu Hajiya Batula Dina kawai ta Tunkara Tana Jifanta da wani Kallo sai da Taje gabda da Ita kana Ta Tsaya Tana Fadin"Sannu Dina Gaddafi Sherrif mai Jego ko..? Tafada Lokaci Daya Tana mata wani kallo Mirmishi baki Dina Tayi mata kafin tace"Na"am Zakiya Nuhu Amaryar..Ko Amaryan Ja"afar Zence ko..? Zakiya da Kalaman Dina ya bata mamaki Cikin Gadara Tace"Eh Fadi ki kara Amaryan Ja"afar nake nan da dan Lokaci kadan ko baki so bane..? Dina Ta karkace kai Tana Fadin"Saboda akaina kike da Zan ji Haushi Domin zaki aure..? Ko Daya Wlh Murna ma Nake Miki Zaki yi aure ki bar Rayuwar Da kikeciki.."Zakiya Ta saki Kawai Tayi Tana kallon Dina Kafin tayi mgana Hajiya Batula Ta Rigata Da Fadin"Lafiyanku kuwa..? Zakiya uwar Yaro ki zauna mana..? Hannu Zakiya Ta Daga mata Tana Fadin"Ba zama ya kawoni ba..Nazo na kawo ma Dina Motarta ce sai kuma Naji Har ta Haihu yau suna ammh bani da Labari..? Hajiya Batula Tace"Ikon Allah Duk Amintan naku..? Toh ko Kun samu Mtsala ne..? Zakiya tace"Bansan mun Samu Wata Mtsala ba sai Dai kinsan Shi Dan Adam Daman Butulu ne.."Dina Ta kalli Zakiya Tana Fadin"Wani Bultulci Nayi Miki Zakiya.? Ni aganina Ban yi Miki Bultulci ba Tsakanina Dake Sai dai Ni nama ce Kekika Cutar Dani Kika Sakani na Fada Cikin Halaka Ga Zuwa Wajen Boka ga Zunuban Cikin da kikasa Dauka Har na Haifeshi batare da aure ba kin Taba Tunanin in na Mutu Wajen Haihuwa me zan ce ma Ubangijina..? Wlh Dina nayi Nadamar Duka Abubuwan dana Biye miki na aikata kuma na Fasa kwan na gayama kowa Zain bashi da laifi Nice keda alhalinki Duk Abunda ya Faru da Taimakonki Alokacin Ina Zargin Taimakona Kike ashe kina Neman kaini ga Halaka ne Bansani ba ai gashinan ke Zaki auran meyasa baki yi Cikin Shegen ba kafin kiyi Auran..? Sai ni kika Jefa Cikin Wannan Halin..? Wani Amsa Zan bama Allah in ya Tambayene meyasa na Haifi Arman Bata Hanyar Aure ba..?kin Cutar dani Zakiya kuma naji kin Fita Raina Nice ma Zan Miki Allah ya isa Wlh..Kuma Banga amfanin gaya Miki na Haihu ba Shiyasa ban gaya Miki ba Tunda ke ba Uwata bace.." Dina Ta karishe Fada tana Sharan kwallah Zakiya da Mamaki da al"ajabin Dina ya gama Kasheta Ta Saki Wata Banzan Dariya da Shewa kafin ta Daka Tsalle Tana Fadin"Hehee...Hehe..Yau Ranar Tsonon asirin Wata ne Wlh kowa Yazo yaji wani abu kunya Kowa yazo yaji..Wlh wanda yasha Tuwo Dani Miya yasha Don Ubansa.." Take Fada Tana Rike kugu Tana wani Girgiza Su Umma Dake Falo Cikin mamaki suka Rankaya Dakin da Dina Take suna kallon Ikon Allah,Zakiya Sai da Taga an Cika Daki Hatta Da Zainab Dake daki sai da ta Fito Jin Ihun Zakiya Hajiya maimuna Data gama yima wanka arman ta sakamai kaya Ta Rumgumeshi ajikinta Tana ganin Ikon Allah,Zakiya kuwa Sai da Ta Taka gaban Dina Tana wani Girgiza kafin tace"Ahayye...Naji Duk mganar Da kika Fada akaina Ta Ina Talle Zai ma Audi Gori..? Karuwanci Nake Shi kike yi Dina Ko ba haka ba..? Koda na ganki Daman chan kema Shedaniyar kanki ne sanda kika bama Zain kanki ina ina..?ni nasakaki Dole..? Kajimin yar Rainin Hankali mganar Zuwa Wajen Boka kuma ai ba Ni najaki ba da kafarki kika je kuma kika Saki kudi aka yi Mik aiki Lokacin Idanuwanki ya Rufe baki ji bakya gani saboda Zain Ni kawai nawa na Rakaki ne ammh Saboda Kin Raina ma kanki wayau kina Dora Zargin Lalacewar Rayuwarki akaina Kin Taba Zama Kiyi Tunanin ta Taya haka ya Faru..? Gwara ni Wlh Ko yau za"a Fada Albasa ce batayi Halin Ruwa ba ammh Kowa yasan Ubana Malami ne kuma Mutumin Kirki kuma Har Uwata Ta Rasu Tana da Shaida..?kefa..? Wlh ko Kaffara Ba Zan yi Ba Gado Kikayi Wajen Kwartoncin Ubanki..!! Ta Karishe Fada Cikin Kakkausan Murya Da Gadara Tana kallon Dinan Ido Cikin Ido Dina Dataji mganar Kamar Saukan aradu,Ta Mike da Sauri Tana Zare ido hakama Hajiya Batula dasu Umma Dina Cikin Karaya tace"Kwarton Ubana..! Zakiya Rashin Mutumcinki har yakai kan Mahaifina..? Zakiya Tace"Kwarai ke kika ja mganar Tayi Tsayi haka...Ko karya nayi Uban naki ba kwarto bane..? Wannan Taron Siyasan Dayake Zuwa Duk Cin mata yake Zuwa yi in ya karyata kirasa Ki Tambayeshi ya Taba Haduwa da Zakiya kawarki Wajen Kwartoncinsa,..? Zai Fada Miki Abokinsa ya Tabakai masa Ni a amtsayin Wacce Zai Raba Dare da ita Sai Kiji mai Zai ce Miki..? Zakiya Ta Fada Tana Wani Girgiza Jiki,Dina Ta Toshe kunni Cikin karaji Tace"Ya isa haka..Ya Isheki Zakiya.."Hajiya Batula kuwa Bata yi ji wani mamaki ba Domin Barewa batayi gudu Danta ya Rarrafa ba Ba Tun yau Tana Zargin Lalacewar Dina Ba Banza ba Hajiya maimuna Kuwa kai kawai ta Sunkuyar kunya Duk ya kamata su Umma sai Kallon kallon. Zakiya Ta Murmusa Tana Kallon Kowa Dai dai kafin tace"Nasan Zaki ji Durum Da jin wannan mganar ai na Dade ina Miki Shaguben haka baki gane ba Kuma Wlh ki Godema Allah ban manta da alherinki gareni ba Da yanzu Wani Labarin ake ba wannan ba Domin sai na Tabbatar da Uban naki ya Kusamin Ciki nima na Haife..Sai kash Ni bana wannan Cin Amanar kuma ina ganin Girman Tsohon Wasu Ko da ba Na Kirki bane.." Dina Ta Fashe da kuka Tanayi Harda Shessheka Zakiya Tayi Dariya Tana Fadin"Bama Kiyi Kuka ba Yanzu Zaki koka...Domin Na Tabbata Burinki bazai Taba Cika ba Kinga in hakan ta Faru sai ki gane ina da amfani.." Dina ta Dago Jajayen Idanuwanta Tana kallon zakiya kafin Ta Nuna mata Kofa Tana Fadin"Fice kibar nan Zakiya..Kije Duk Abunda kikayi zai koma kanki..Nidai nayi Nadama kuma Allah ya karbi Tubana Kije Allah zai min mganinki.."Zakiya tace'Umh daman ai ko baki ce ba Zan Fita Dina..Ga key din Motarki Kije Chan ki karata kada ki kara Nemana Nima haka bani bake Dina.."Tana gama Fadin haka ta Wurgamata Key din Motar ta Zo Zata Fita ta leka Arman dake hannun Hajiya maimuna ta saka Dariya Tana Fadin"Wlcom to d Word Dan Gaba da Fatiha.." Daga haka ta Fice tana wani Taku Tana Fita Dina ta Duke Tana kuka Su Umma kuwa Jiki sanyaye suka Koma Falo suna Jajanta Abun Daga Dinar har Hajiya Batula Ba wanda ya kara mgana Dina na kuka Hajiya Batula na Sauke ajiyan Zuciya. *Alhamdulillah Anyi Biki lafiya Lau an gama Lafiya Nagode Bisa Yadda kuka Karbi Uzurina Allah ya bar Zumunci Insha Allahu yanzu komai zai zama Daidai Da yardan Allah..* *Janafty..."* 8/3/21, 5:10 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣8️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Dina tayi kuka kamar Ranta Zai Fita ba wanda ya bata Hakuri ko yace karta yi kuka Daga Hajiya maimuna har ita Hajiya Batulan wacce itama Abun ya Daketa sosai Sai dai ajiyar Zuciya Bata bari tayi kuka ba ammh Tana kallon Dina Tana Tunanin Dole ta koka Domin Zakiya ba karamin cin Zarafinta Tayi ba. Achan Falo kuwa Su Umma sai Janjanta abun suke Daman masu aikin Naman hayansu akayi suka Gyara Naman suka Soya,Zakiya kuwa Tana Fita ko Ja"afar bata Kira ba Ta hau Abun Hawa ta koma Gida Ranta Fes Daman Ta Dade Tana so Ta Fayyacema Dina Komai bata samu Dama ba yau ta Cika mata Ciki Gwara Ta Fahimci Ita Iskancinta mai Lasisi ne gado Tayi. Yammah Nayi su Inna Rukayyah suka Tafi Gidan Alhaji Tsoho Chan sukeje suna Bama Hajiya Mama da Alhaji Tsoho Labarin Abunda ya Faru Hajiya Mama ta kama Salati Tana Salallami,Zain Lokacin ya Shigo Dakin Shida Haddir sun ji Komai Alhaji Tsoho bai yi mgana ba sai da Yaga Inna Hannatu Nata Zage Zage Tana Fadin kaddara ta sa Zasu Hada Zuru"a da bara Gurbi Lokacin ne ya Tsawarta mata Dole ta kama bakinta. Zain kuwa bai yi wani mamaki ba Sanin abaya yasha Zuwa Gidansu Dina yayi kwanaki Koda Kwamishina Bayanan ai Hajiya Batula na gidan ammh Bata Damu Data Bincika me suke aikatawa da sunan Abokin karatun Dina..? Ammh Ina sai dai kawai ta saka musu Ido Daman ai an ce Barewa bazata Taba Gudu Danta ya Rarrafa ba. Abunda yasa ma har ya tsaya yaji Mganar yana Cikin Farinciki Jiya yayi mafarkin Yaga Zain da yaro ahannunta Bayan ya Farka da Safe sai ya Danganta haka da Tabbas Firstlove ta Haife Abunda ke Cikinta Kenan Hashashensa ya Zama gaskiya Shiyasa ya Tashi Cikin Farinciki da Fara"a yaje asibiti ya Duba Maraasa Lafiya Daganan ya karisa masallacin Cikin asibiti ya bada Sadaka mai Yawa anan ne suka Hadu da Haddir Shine suka Nufi Gidan Alhaji Tsoho suka iske su Inna Rukayyah na maida Zencen Haddir kuwa aransa Allah ya kara yayi Daman ai Duk Taran da ba Alheri ake kullawa ba Allah sai ya Watse gayyar Gabadaya. Bangaran Dina kuwa kwana Tayi batayi Barci ba..Tana Tunanin ashe daman Duk Shaguben da Zakiya take kan yan Siyasa Da ita take..? Ammh Daddy bai kyauta ma kansa ba..? Wata Zuciyar ta Tambayeta da Cewa ke kin kyauta ma kanki ne..? Ai kema baki kyautama kanki da Rayuwarki ba Gabadaya Dina Tayi kuka Tana Tunanin Dole nema Rayuwarta Ta Lalace Tunda Daddy na Lalata ya"yan wasu Dole itama Wannan Munannan Tabon ya Faru da ita Abun Takaichi ma Gaban Mutane Zakiya ta Kira Daddy da kwarto..! Kalmar ne in Ta tuna Take mata Muni ko yayane Daddy Uba yake gareta wanda ya bada komai nashi Saboda Cigabanta Bazata so ko Taji Dadin wani na aibatashi ba. Hajiya maimuna ne Dataji kukan Arman yayi yawa Dina Taki Daukansa ta Bashi Nono Ta Tashi Tana mata mgana Cikin kuka Dina Tace"Ummi In na Tuna kalaman Zakiya sai naji kunyar kaina ya kamani..? Daddy fa Tace ma kwarto agaban kowa da kowa..? Hajiya maimuna Tayi Mirmishin Takaichi kafin tace"Daman ai irin wannan Ranar ne bawa baya so..Shiyasa gwara mu Shuka alheri kodomin Wata Rana Tunda Kowa ya sani Sheri Dan aikeni Inda ka aikashi nan zai Dawo..Ki Dauki Aliyu ki bashi Nono Ki kuma Daina wannan kukan Baki da yadda Zaki yi ki Kankare wannan kaddaran.."Da wadandan kalaman Dina ta Daina kuka ta Dauki Arman ta Rumgume wani Sonsa na kara Shigarta Tana ganin Shine nata aduka Duniyanan. Washegari Tun Safe Hajiya Batula Tayi Shirin Komawa Daman Direban Daya kawota yanan nan bai komai ba Su Umma suka Diban mata naman sunan da yawa da Farko ma Taki karba sai da Suka matsa mata Sama sama sukayi sallama da Dina Hajiya maimuna kuma Daman sai Dina Tayi arba"in an Daura auranta Da Zain ta Mikata Dakin Mijinta Zata Koma Sudan. Hajiya Batula Da su Waled da Wuri suka Dauki Hanyar kano ta Guduri niyyar in ta Koma sai ta gayama Kwamishina Komai ko zai Dawo Cikin Hayyacinsa koda ta Koma Baya nan yana Abuja Washegarin Ranar ya Dawo ta kuma Kwashe komai Ta gayamai Hajiya Batula na kuka Tana Fadin"Dame na Rageka..? Ban Rage ka da komai ba Sai dai ina so ka sani Wlh in Yayana yasan kana Neman mata bazai Baka Ni ba ammh nagodema Allah ko ahaka ka Tsaya kaga Karshenka Yarka Tayi Cikin Shege kuma Kawar yarka ta Tona maka asiri gaban Bainar,mutane Sirrikan Yarka me yafi wannan kunya..? In ma baka Daina ba ka Daina Tun kafin Itama Waleda wani ya Lalatata. " Kwamishina sai kuka yana ma Hajiya Batula rantsuwa Wlh ya Daina Tun Lokacin Da ya Fahinci Zakiya ce wacce abokinsa ya Hadasu tun alokacin ya Tuba ya Daina Neman mata Hajiya batula tana kuka ta barshi nan ta Shige Ciki kwamishina kwana yayi bai barci ba yana jin kunyar kansa Data su Umma da Labarin yaje Musu harda kunya ma Dina Data Kasance yarsa kaicho...Bariki Batayi ba Kuma bata da Riba Domin ita din Tana Rage ma Mutum Daraja Kimarsa awajen Mutane Yayi Nadama abaya ammh ayanzu ya kara Ninka Nadamarsa yana kuma Rokon Allah ya yafe masa Duka Laifinkunsa. ****** *Zaria..* Bayan Sati Daya..! Kwana Bakwai Zaina ta Shafe a asibiti Tana karban kulawan Likitoci Saboda C.S din da akayi mata Kafin Satinan Zulaihat da Farida ke ta Fadi akanta Bata ma da bakin Gode musu bayan Kacharalle sai Uwar mata ba wanda yasan Labarin Haihuwan Zaina Suby Tagaji da neman Diddiginsu ta Hakura uwa uba kuma Tana Tsoron Uwar Mata Da Kashedin Datayi mata Uwa uba kuma Harda ita da kanta Sholly din Shiyasa ko Bata ma Allah ta Daina Bin Diddingin Rayuwarsu. Uwar Mata tazo Ranar kwanan Zaina uku asibiti Tazo Ko Daukan yaran batayi ba Daga Cikin Dan gadonsu suka Lekasu Ita Da Hajiya Zabba"u suna wani Tabe baki,kamar sun ga Kashi Farida bata Damu ma Dasu ba sai kallon Zaina suke suna kare mata kallo Ita kuwa Uwar mata da Kawarta ma Wlh Tsoro suke bata bata iya Kallonsu Sun fi Kama da Tantirin karuwai sun Girma basu san sun Girma ba. Basu Dade ba suka Fita Bayan Farida Taje rakasu Uwar Mata Ta kalleta Tana Fadin"Kekam meke Damunki ne Sholly..? Yarinyar nan Zuly Uban me take yi zaune tana Miki..? Ita ba karuwa da ita zakiyi ba komai ba gwara ki Koreta takama gabanta kawai Tunda ita Karuwancin ma bai karbeta ba."Farida tace"Saboda me Zan Koreta..? sa"adiya na son Zama da ita kuma Nima Ina Jin Dadin Zama da ita bata da wata Mtsala ban ga aibunta Ba mganar karuwanci kuma Taga ba Riba ta bari Daman kuma ai bai Dace da ita ba..! Uwar Mata tace"Ah Lalle Dole ta bari Tunda Tana kwance kina Ci da ta.."Hajiya Zabba"u tace"Shiyasa Duk ta sauya ta kara Kiba ta Zama wata Mai kyau da ita.."Uwar Mata tace"Uhm ai ni Zuwan Wannan yarinyar ba alheri bane awajena Duk ta sauyaki Sholly Sai dai ina Fatan Tunda ta Haihu Zata koma Inda Ta Fito..! Farida Tayi Dariya kawai kafin Tace"Insha Allahu.."Uwar mata ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Yauwa Kokefa..Nifa Daman Fargabata Daya kada Watarana Kice Zaki bar wannan Sana"an da tayi Miki Riga Har da Wandon sakawa Sholly..? Farida tace'Wannan kada ya Dameki ai Ni na Zabi Karuwanci Dakaina ba Talla kikamin ba kin ga kuwa ai ina Jin Dadin Rayuwar nan yasa Kika ganni Cikinta Har yanzu.."Uwar mata Tana Dariya Tace"Hakane Shalelena..Nace ba Baida ke zaki biya Duka Bill din asibitun ba..? Farida Data gaji da Mgana da Uwar mata tace"Ni zan Biya wani abu ne..? Uwar mata ta ce'Bakomai Tana Kada kai Daganan Farida Tayi musu Sallama ta koma Ciki ta Iske Zaina Suna mganarsu da ZulaihatSuna ganinta sukayi Shuru basu Cigaba ba ita kuwa aranta Mirmishi Tayi Tana Tunanin waye zai gayanmata Uwar mata..?Tafi kowa sanin Wacece ita Tasan Sirrinka Da Duka Sharrinta. Ranar da suka kwana Bakwai aka basu sallama Tunda Zaina Taji Sauki,Har Tana Takawa da kanta Tayi ma kanta wanka ta Shirya, kuma Ruwan Nono ya samu yaran suma Sunyi Bul Bul Dasu,Dayake Zaina tana samun Cima mai kyau Ferfesun kayan Ciki da Nama take ci Tunda ta Haihuwa daTea mai kauri Cikin Lokaci Nonuwa suka Cika yaran suka Fara samu ammh da haka Likitan yace akwai Bukatan A kara da madara Zuwa gaba Saboda in sun kara wayau bazai Isheshi su sha su Koshi ba. Mota guda Farida ta sami suka kwashe kayansu Bayan Ta Biya Duka Bill din asibitin bata Damu da yawan kudin ba,An basu Sati Biyu su Dawo bayan an Rubuta ma Zaina wasu mgungunar karin Jinin Da yammah aka Sallamesu wajen 6:30pm suna Gida suna Komawa Zulaihat ta saka Ruwan Zafi Farida tayi ma Zaina wanka Sosai Tun a asibiti baaa saka Ruwan yayi Zafi Soaai bayan Tagama gasa mata Jiki Ta Koma ta wanke yaran Tas Zulaihat nata mamakin ganin Farida ta iya komai Da Daddaran ta Kira Kacharalle a waya ta Bashi Kudi tace ya Siyio mata Raguna Guda Biyu,Washegari kuwa sai gashi Dasu Shi ta saka ya kira mata Wani Mahauci ya yanka ya Gyara mata ita da Zulaihat suka Soya Zaina Ta rasa me me Zatace Da Daddare kuma sai ga Limamin masallacin Anguwan Daman Kacharalle tayi ma mgana wanda zai ma yaran Huduba yace karta Damu zai kawo mata sai ko gashi Sun zo Tare Bayan gaishe Gaishe Farida ta Dauki yaran takai mai ita da Zulaihat Daman sun gama mgana da SA"ADIYA kan sunan da yaran zasu ci. Tace Maryama da Fatima Domin Ta Tuna Firstlove ya gayamata in ya Haifi ya mace ta Farko Sunan Mahaifiyarta zai saka In ya kara samun wata kuma ZAI saka Sunan Nene Aisha sai dai ita tana son yima Umma Takwara Domin ance so So ne Umma uwace agareta Data gayama Farida taceTayi Daidai Ta gayama Limanin Sunayen ya Dagasu yayi musu Hudubu Bayan ya Tauna Dabino ya basu ya kuma Tofe da addu"an Neman Tsari da ZAI ,tafi Farida ta bashi 5k da Naman sunan yakai ma Iyalai yana ta Godiya bayan Tafiyarsa ne Farida da Zulaihat suka Zauna suna Zabo inkiyan sunayen da zasu Dinga kiran yatan dasu sai Zaba suke su Sauya Zaina na gefe Tana Musu Dariya. Dakyar suka Tsaida mga kan za"a Dinga Kiransu Maryama itace Babba ANAN ita kuma Fatima ANUN bayan sun gama suka waigo suna Tambayan Zaina Tana Dariya ta Daga Musu Yatsunta alamun Sunan yayi Zulaihat ta Daka Tsalle Daman ita ta samo sunan a wani Musliman Name wanda Kacharalle ne ya Bata Littafin.. Naman sunan su kuwa isu isu sukaci kayansu sai kuwa Kacharalle da Farida ta Dibanmawa Zaina kuwa da yawa Farida Ta Diban Mata tace taci ta More Abunta Ta Zubar da Jinin Haihuwa. Kwanci Tashi ba wuya awajen Allah Farida da Zulaihat suna Cigaba da kula da Zaina dasu Anan kafin Sati Biyun Da Zasu Koma asibiti Daga ita har yaran sun sauya sunyu Bulbul Dasu kida sukaje aka Duba wajen Dinkin akace ya Riga ya Hade Sai dai bata zata Dinga aiki mai Wahala ba yaran kuma sun ce Tana da Ruwan Nono kyau nan da wata Biyu Zuwa uku sun kara Wayau sai asiya madara adinga Basu Daganan suka Dawo Gida Suna Cigaba da kula da ita Su Anan kuwa Har gajiya suke da Goyo wajen Farida da Zulaihat Allah ya Dora musu kaunar yaran acikin Ransu Ita Zaina Tana Gefe ta zama yar kallo,Sai dai Farida na kula da Jegonta Sosai Tunda ita Ta Haihu Ta kuma san Komai bata ma Sa"adiyan Wasa. ******** *Bayan Kwana arba"in..* Yau Dina Take Cika kwana arba"in da Haihuwa Ita da Arman sun Chanza sun zama wasu Lukata ye dasu,saboda suna Samun kulawa Sosai Daga su Umma ga kuma Hajiya maimuna Data Dage wajen gyara Dinar Tunda aure Zatayi Bangaran Arman kuwa yaron ya Shiga ran Mutane Sosai Wuni yake hannun Zainab in Tana makaranta Hannun Nene ko Umma in Abba ya Dawo ma adauka kai mai Arman ya Fara wayau yayi Bulbul yana samun kulawa Nene Har Goyashi Tana yi in ya Fara Rigima Ranar Har Wajen Alhaji Tsoho Haddir da Zain suka kaimai ya kara ganinsa ya Sakamai albarka Domin Daga Zain har Haddir Arman ya Shiga ransuTunda kaf afamily din ba wani karamin yaro sai Shi Musamman in suka Dawo Daga wajen aiki suke yada Zango su Daukesa suyi ta mai wasa Zain kuwa yadda yaron ya Shiga Ransa har bama su Umma mamaki yake in ka ganshi Wajen Dina sai dai in Nono zai sha Dina Har acikin Ranta Tana Murna da Arman bazai Tashi Cikin wani maraici ba Tunda kowa ya maida komai ba komai ba. Ranar Datayi arba"in din Alhaji Tsoho ya Kira Abba sukayi mgana kan mganar Daura auran Zain da Dina,Sai yace a Tuntubu su Abban kaduna kana kuma akira shi Kwamishan aji nashi Tsarin kamar yadda suka Rabu Shi Abba Shi ya Kira Abban Kaduna da Daddy Abuja ya gayamsu Yadda Alhaji Tsoho yace yana so Ranar Jumma"a Daura auran Sai suka ce Akira Uban yarinya atambayeshi dashi Zain din mgana na Hannunsu haka kuwa akayi Shi Alhaji Tsohon shi ya Kira Kwamishina ya Tuntubeshi kan mganar Kwamishina Dayake jin kunyarsu su Alhaji Tsoho Tun Abunda ya Faru yace ai mgana na Hannunsu yadda ya yanke haka Za"ayi yace Shikenan In yayi mgana da Zain zai Kirashi ya gayamai Rana da komai da komai. Da Daddare bayan sun Dawo daga aiki Daman Tunda yayi Yaji bai koma Gidan Abba ba,Da Alhaji Tsoho yatuntubesa kan wannan mganar bai iya cewa komai ba yace yadda suka yanke nan take yace Jumma"a mai Zuwa sai Hajiya mama tace A Daga Zuwa na sama saboda ba"a sanar da ita Dinar ba Da wannan Shawaran ta Hajiya Mama aka Tsaida nan da kwana Goma sha Hudu Za"a Daura Auran Dina da Zain. Alhaji Tsoho Da kanshi ya Kira Kwamishina ya gayamai Shi kuma yace Allah ya Nuna mana,Da kansa ya gayama Hajiya Batula yace ta Kira Dinar Ta Tambayeta in da wani Abu Datake Bukata tace Shikenan Hajiya Maimuna kuwa Abba da kansa ya Sanar da ita tace bakomai Allah ya nuna mana Daman Tana son ta koma Suhaima ba Lafiya,Duk Abba ya Kira su Baban kaduna ya gayamasu su Inna Rukayyah kuma Hajiya Mama Harta Chan Gada Umma ta Kira Goggo Halima ta sanar da ita tace Zatayi Kokari tazo Taga Arman Daman Tun sanda akayi Haihuwan Umma ta Kirata ta gayamata suka Rabu Cikin kuka Bayan Goggo Halima tace"Umman Zareena har yanzu dai Ba Labarin Halima..?Umma Na Sharan kwallah Tace"Har yanzu Goggo Halima muna nan dai muna gayama Allah..! Goggo Haliman itama kwallar Take Tana Fadin"Allah ya Dawo da ita lafiya in tana Raye..In kuma karshen Saduwan kenan Allah ya Hada Fuskokinmu da alheri. "wannan kalaman shi ya saka Umma kuka da ita kanta Goggo Haliman Allah Sarki Rashin Zaina ba karamin Babban Gibi bane da Iyalan Saulawa in suka Tuna sai sun koka. Da Dina Taji Labari Bata iya Cewa komai ba Gashi Dai Burinta ne zai Cika ammh bata wani Farinciki ballatana Murna,Zuciyarta bata Farinciki da wannan auran Fargabanta Daya bata san wata Rayuwa Zata Gudanar ba In Gida ya Zama Na Daga ita sai Zain ba Bata dai nuna ma kowa ba ta bar Fargaban acikin Ranta Hajiya Batulane ta Kira Hajiya maimu sukayi mgana kan Abubuwan da za"a Bukata tace sai tayi ma su Nene mgana Data Tambayesu suka ce sai Abunda Alhaji Tsoho yace in Gidan Zain na Lowsot ne ba Mtsalan komai akwai komai na Rayuwa aciki in kuma wani ne basu sani ba Gaskiya Sai Abba ya Dawo sun Sanar mai. Da Abba ya Dawo Nene ta gayamai Shi kuma ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Abunda ke Faruwa sai yace A"a koda Halima bata nan bai kamata Dina ta Zauna agidan ta ba Domin Tun jiya sunyi mgana da Zain kuma yace bai yarda Dina Ta Zauna agidan ba Gida Gidan Zaina ne ba macen Data isa ta Shiga Abba ya Jinjina kai Shima yayi Tunanin haka Sai dai suka Rabu kan zai yi Tunanin a ina Za"a ijiye Dinar. Sai da sukayi waya da Baban kaduna Yana gayamai Abunda ke Faruwa shi ya kawo Shawaran agayaran Tsohon Flat din da Iyayan Zaina suka Zauna aciki Duk da ba abunda Falt din yayi Tunda ana KulaDaahi kuma baki na sauka aciki sai dai kayan Ciki ne kawai suka Tsufa sai an sauya Wannan Shawaran Tayi ma Kowa Barin ma zain Dayaji Gwara hakan ma Alhaji Tsoho yace komai yayi Dai Shi Abba ya saka aka afitar da Duka kayan Shashin agyara a Sake sabon Fenti ya kuma Sauya wasu kayan amfanin Gidan. Hajiya mama sai da Tayimgana kan me zai ce Abba ya Saka komai ga iyayan Dina Alhaji Tsoho yace Bakomai an Riga an Zama Daya Arman ya Hada su Har Abada ba yadda Abba zai iya Dole yabi Umarnin Alhaji Tsoho Bayan ya gaya ma su Nene suma basu da ta cewa aka Fitar da komai aka Fara gyara Cikin kwana Uku komai ya kamallah an saka Saitin kujeru Gadaje a guda Bedroom din da wasu kayan Kitchen din kana Su Umma sukayi Hajiya maimuma Jagora Taje ta gani ta Dudduba abunda babu sai saka albarka Take bayan sun Dawo ta Kira Hajiya Batula ta gayamata Komai Abba yayi komai Abunda babu kadan ne, ta gayamata ita kuma tace Zata Siya komai Tunda kwamishina ya bar kudi a Hannunta Zata Taho Ranar alhamis Tunda shi kwamishina sai Ranar jumma Zai Taho da Safe. Dina Duk Budirin da ake yi Bata Cewa komai Ballatana Uban gayyar Allah Sarki Laila kawar Zaina Tana kiran Umma Lokaci Bayan Lokaci Taji ko an samu Wani Labari Umma tace A"a Sai addu"a Taji labarin Haihuwan Dina abakin Zainab Tana Taya Zaina Kishi yasa bata Shigo Gidan ba Bikin ba wanda aka Gayyata Tunda daura aure ne kawai sai a Mika amarya Inna Hannatu tace Bazata samu Zuwa ba wannan karon sai Inna Rukayyah wanda Zata Taho Tare da Zafeera da Shema wannan karon dai ta Hakura Zata zo ganin Gida. Dina Kuwa Ba wanda Ta gayamawa Daman Zakiya ce konai nata kuma ga yadda suka Rabu Tama Goge lambarta basu kara Neman juna ba bata san Ina Isalinta ba Bata Labarin Halin Data Ke Ciki Ta kanta kawai take. Ranar Laraba Inna Rukayyah suka iso...da Safe da yammah sai ga Sadiq babba ya Sauka Ya gama Defence dinsa ya Dawo Gida Gabadaya Washegari da Safe sai ga Umar Faruq ya sauka Shima yazo Hutu gida ya kara Cika sosai da Farimciki wanda basu Taba yin irin shi ba Tun bayan Faruwan lamarim Kowa yazo Arman yake Fara Tambaya Domin Suna ganin Hotunan kyakyawan yaron Hatta Kuwa da Zafeera da Shema sai da suka Dauki Arman din yaron yana da Shiga rai sosai. Wajen La"asar sai ga jeep din kwamishina Dauke da Hajiya Batula Booth cike da kaya Bayan ita kuma bayanta Mota ne Cike da kaya ba ita kadai tazo ba ita da Kanwarta Mariya suka zo Kayan ma ba"a Shiga dasu Cikin Gidan Abba ba Shashen Da Dina Zata zauna aka Nuna musu suka sauke komai anan Hajiya maimuna tabisu Cham dasu Umma aka gaigaisa Bayan an kawo musu abinci da kayan Sha Daganan suka barsu suna kara gyara Dakunan sun saka Labulayan da kayan Kitchen din da babu sai zannuwan gado da abubuwam da ba"a rasa ba sai yaba Wajen suke Domin in ba an gayamaka ba sai kace Sabon Gini ne su Umma kuwa na Cikin Gida Cikin ya"yansu Dina na Daki ita Kadai kamar mayyah Arman na Tare dasu Faruq suna ta tuna Zaina suna kwallah da addu"an Allah ya bayyanata. *Janafty...* 8/3/21, 5:26 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣9️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Ranar da Daddare Nene ta samu Abba da mganar Kayan aure na akwati Zain bai ce komai ba Abba yace bari ya Kirashi bayan ya Daga waya ya Kirashi yace yazo Yana son ganinsa ba Jimawa sai gashi ya iso Abba ya sakashi adaki yamai Mganar Kayan Lefe Domin Nene tace bai kyautu Dina Taje gidansa ba kayan Da Zatayi Fitar Biki ba. Zain ya karkace Baki yace ma Abba Shi bashi da kudi a hannunsa Da Zai iya Yima Dina wani Hidima Da Abba ya Tambayeshi Ina yakai kudinsa sai yaki Fada yadai ce Yana wani Shirye Shirye ne zai yi wani Abu Dasu Daganan Abba bai matsa mai sai yaji komai ba ya Dai ce ko 50k ya Bama Nene asiya mata Ko kadan ne ya fi Babu ba yadda ya iya haka ya Cire ya bama Nene ita kuma ta Kira Telansu Daman bayan Dinki Har kaya yana Saidawa Dinkakku kawai Gayamai Tayi Tana Bukatar Shadda,Da Leshi da Material,Sai atamfa guda Daya Takalmi da jaka kuma da yammah ta Fita ta Siyi harda dan kunnaye Koda ta Dawo ya aiko da kayan ta Hada ta bama Hajiya maimuna Ta Raka da ban Hakuri Cewa bayan komai ya kamallah Zain din zai yi ma Dina Lefenta Nene harda Arman ta Siya ma Riga tace Shima yaci Biki dashi. Dina Data ga kayan Tasan Ba Zain bane ya siya koma Shine ba Domin Ransa na so ba Shiyasa bata Damu ba kamar ta sani Domin yayi alkawarin yadda Tayi Sanadiyar Farincikinsa Shima sai yayi Sanadiyar nata Bazai iya gaddama da iyayansa ba kuma ba zai iya Sakin Dina ba kamar Cin Fuska ne garesu ammh Yanan yana Wani Tsari Wlh sai Dina ta gwammace bata Aureshi ba. Washegari karfe 11am na Safe aka Daura auran Dina da Zain kan Sadaki Dubu100 wanda Baban Kaduna ya Biya,Kwamishina yayi ma Alhaji Tsoho kara yace yazama Waliyin Amarya Daurin aure bai yi wani Taro ba a haraban Gudan aka Daura auran Daga Zain sai Haddir sai Baban kaduna da Daddyn Abuja sai kwamishina da wani abokinsa sai Alhaji Tsoho sai Sadiq da Faruq su kadai suka Shaida wannan Daurin Auran. Tunda aka Daura Auran Zain ya Sukuyar dakai yana Jin wani Abu namai suya acikin Ransa Daman bai yi Niyyar Xuwa ba asibiti ya gudu Alhaji Tsoho ya saka Haddir yaje ya Taho Dashi Ji yayi kamar bai ma Firstlove adalci ba ace yau ta Dawo ta Iskeshi ya zama Mijin Dina Bakin Ciki haka yasa ya Tashi da Sauri Motarsa ya Fada yabar Haraban Gidan Cikin asibiti ya koma ya Shiga Office dinsa ya Zabga Tagumi yana ji kamar ya kurma Ihu Kewar Zaina da Komai nata ya Dawo mai Sabo ya Tabbatar ma kansa ya Zama Dole Dina ta Dandani Gudarta. Achan Gidan Abba kuwa Taron ba wani karKashi ballatana wani armashi Bangaran su Umma ne Zafeera da Shema Da Zainab ma sukayi wanka sukayi kwalliya Suna Hotuna su Faruq tunda suka Tafi Gidan Alhaji Tsoho basu dawo ba,Sai su Umma Abinci ma kadan suka Dafa bada yawa ba Tunda iyakarsu kenan Bangaran Amarya Dina kam ba"a mgana Domin Tun bayan da aka Daura auranta da Zain Ta rasa Duka Natsuwarta Daman Tun da Akayi ma Arman wanka yasha Nono yana Wajen Nene itama Tayi wanka ta Sanya wani Leshi Cikin wanda Hajiya Batula tazo mata dashi. Gashi dai yau Burinta ya Cika na mallakan Zain ammh meyasa bata Farinciki..?Meyasa Burinta ya cika acikin wannan yanayin..?Ta Tabbata Wani irin Zama ne zasu yi Tsakaninta da Zain wanda bazata Dora komai acikinsa ba har yau har Gobe Tana Son Zain kuma babu abunda ya Sauya acikin Zuciyarta In da zai karbi Tubanta da ban Hakuri da Zasu yi Zaman lafiya da kaunar juna Gefe Daya su na Renon Dansu Armaan sai dai ta san hakan bazai Taba Faruwa ba. Tana Zaune Hajiya Batula da kanwarta Mariya suna ta Hiransu su Waled daman In suka zo suna Tare dasu Saudart ne,Hajiya maimuna kuma Tana Falo Wajen su Umma Acikin mganarsu Take jin yau za"a kaita Gidanta kuma Gobe Tare da Hajiya maimuna Zasu wuce kano Tuni Dina Taji hankalinta ya Tashi kamar ta Fashe da kuka Sai ma tashi Datayi ta Bude Kofar Tailet ta Shiga Domin bata so Hajiya Batula ta Fahimci Tana kuka. Wajen uku saura na Rana sai ga su Faruq sun Dawo nan suka ci abinci suka zauna ana Hira Misalin 4:30pm bayan Sallar La"asar,Su Hajiya maimuna da Hajiya Batula su ka saka Dina ta sake wanka ta Shirya ta saka Mayafi ta yane kanta Inna Rukayyah ta musu Rakiya Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Dakin Hajiya mama aka Fara kaita bayan yan Nasihu Dai dai Sauransu aka kaita wajen Alhaji Tsoho dasu Abba Fatan alheri yayi musu da saka albarka. Sai aka bama Kwamishina Dama ya Kebe da yarsa bai ce mata komai ba illah Allah ya Zaunar da ita lafiya Daga karshe yace ta yafemai Dina ta Rumgume Kwamishina Tana kuka Shi kuma yana Lallashinta Sai gabda Mangariba suka baro Gidan Hajiya mama Tayi musu Rakiya da kara suka koma Gidan Abba wajen su Umma Hajiya maimuna ta Sake Damka Amanarta Wajen su Umma a karo na Biyu suka karba da Hannu Bibbiyu Tare da Fatan Allah ya basu ikon Rikewa. Daganan Harda su Umma aka Dunguma Zuwa Shashen Da Dina Zata zauna Banda Zafeera Datace bazata je ba Shema ce Taje Daman Tun Dazu Hajiya Batula Ta gama Tattara Duka kayan Dina Dana Arman dakomai nata Zuwa Shashen da Zata zauna Suka gyara mata komai,Saman makeken gadonta suka Sauketa suna Mata Fatan alheri Umma Dataji Hawaye ya Taho mata Tayi Saurin Sharewa Tana Tunanin Wannan Shi ake Kira Kaddara wanda ya bar Halima Daga Gida yau ga Dina Mtsayin Matar Zain ba wanda ya Isa yaja da Ikon Allah Basu Jima ba su Umma su kabar su Hajiya Batula nan suka koma Shashensu Nene ta Tafi da Arman Tace wajenta zai Kwana Su kuwa su Hajiya maimuna yan Nasihu ne da Shawarwari wanda Dina ta Tabbata ko Tayi amfani Dasu ba aiki zasu yi mata Tunda wanda Zatayi Domin sa yaTsaneta fiye da komai a Rayuwarsa. Bayan Dogon Nasihan sukayi mata Sallama suka Tafi suka barta Daga ita sai Halinta sai Lokacin Dina Taji kuka yazo mata ta kwanta kan gadon Tana kuka kamar ranta zai Fita sai kuma kewar Arman Dakyar Ta iya Tashi Ta Shiga Tiolet din Dake Bedroom din Taje ta Dauro alwala tazo tayi sallar mangriba Ta nan Zaune kan Darduma Tana Tunanin makomar Rayuwarta. A bangaran Ango Zain kuwa ba wanda ya kara ganinsa Kwamishina Gidan Alhaji Tsoho Xasu kwana sai Gobe zasu koma ,Haddir ne Daya Ga Dare yayi ya Nemi Zain din ya Lallabashi ya Rakashi Wajen Dina sai bai samu wayarsa ba Tana kashe Dole ya Hakura,Ammh Haddir bai ji Dadin hakan ba Tunda yayi ma Alhaji Tsoho alkawarin Zai kai Zain din harGida. Dina Kuwa Nan Tayi sallar Isha"i Ta koma Ta Zauna Tana Jiran Tsammani Tun Tana saka Ran ganin Zain har ta Fidda Rai da kayan jikinta ta kwanta Tana kuka,kukan da bamai lallashinta yau dai gata amatsayin Matar Zain ammh kuma ba amfani Ta Tabbata yanzu Zain yafi kowa Tsanarta kuma yana ganin Duk Abunda ya Faru itace sila Tana wannan kukan bata san sadda Barci ya kwasheta ba Batare data Leka ko"ina ba Ballata ta Rufe wani Kofa Tana Tunanin Duk Gida ne Babu Abunda zai Faru. Zain kuwa acikin Office dinsa yayi kwanciyarsa bayan ya kashe wayarsa Domin yasan Tabbas Kokowa bai Nemeshi ba Haddir sai ya Takuramai Shiyasa ya kashe wayarsa yayi kwanciyarsa Cikin Office dinsa yana Tunanin hakan ne kadai mafita koda garin Allah ya waye bai Damu ba Bayan ya Dawo masallacin Cikin asibiti ya Gyagice kawai ya Fara Duba Patient bai damu Daya koma Gida ba Ballatana yayi wanka yagama Tabbatar ma kansa Tunda Aka Daura mai aure da Dina Kila Sai ya kulla Zumunta da Kazanta Tunda office dinsa zai zama wajen kwanansa ne Tabbas. Haddir sai da ya Shigo Cikin asibiti yaga Motar Zain kana Tunanin yana asibiti ma ya kawomai Daganan Office dinsa yaje Direct ganinsa da kayan Jiya ya saka ne ya Tabbatar mai da Zarginsa ganin Zain din ya Hade rai ne yasa Haddir bai mai mgana illah Allah ya Shiryeka kawai Dayace ya Kada kai Zuwa Nashi Office din Zain yabi sa da Harara Ta Gefen ido Yana Tunanin Shirin Dayake in Haddir Yaji Daga baya bazai ji Dadi ba zai ce ba Shawarcesa ba. Chan agidan Abba kuwa Dina Datashi Da Safe ta Fahimci Zain bai Shigo Barayinta ba batayi wani mamaki ba Tatashi Bayan Tayi sallar asuba Tayi wanka Sai Lokacin Ta Zagaya Flat din yayi daidai na Misali ammh yadda ta Tsara rayuwarta Da Zain bata Tsammaci Zata kareta awannan karamin Shashen ba,sai dai bata da yadda Zatayi Tunda ita kam Cikar Burin nata ga yadda yazo mata bata iya Tsinana ma kanta komai ba,Damuwarta Arman Nononsa nata Zuba alamun yana Chan yana Rigima Duk ta damu Falo ta Fito Ta zauna Tana ji kamar ta Tafi Shashensu Umma sai ga Zafeera da Shema suna Dauke Da kayan Breakfast sai kuma Arman Dayake kuka. Tana ganinsu Dauke dashi Ta Mike Cikin Rawan Jiki ta karbeshi,Ta Rumgumeshi Tana Sauke Numfashi Shima yasan Dumin Jikin Mamarsa,Zafeera da Shema suka kalli Juna ganin Dina ta Zauna tana Fito da Nono Arman ya karba har yana Sauke ajuyar Zuciya sai kuma,ya basu Tsausayi Domin jiya Cikin Dare ya Tashi yana ta kuka Nene bata samu Barci ba Shine yanzu akace su kawosa. Sudan Zauna kadan Zafeera sai kallon Kofar Bedroom din Take wai Taji koda alamun mutun sai dai Daga Dukkan alamu ba kowa kana suka yi mata sallama suka Tafi Bayan Dina ta gama Bama Arman Nono sai yayi Barci taje ta kwantar Dashi Tazo ta karya Tea kadai tasha sai Kwai Dataci da Buredi,Daganan ta kwashe komai Zuwa saman Dining ta koma Ta Zauna Tana Cigaba da Saka da warwara Tana Tuna Irkn Amintar Dake Tsakaninta da Zakiya kamar ta Kirata sai wata Zuciyar ta Hanata Tuna irin Rashin Mutumcun da Zakiya ta aikata mata. Wajen karfe 10am na Safe sai gasu Hajiya Batula dukkansu Sunyi wankansu Dasu Waled sai Shirin Tafiya Hajiya maimuna na Shashen su Umma,jin yanzu Zasu Tafi ya saka Jikin Dina ya karayin Sanyi ta Dauko mayafinta Da Arman Zuwa Shaahensu Umma Domin suyi sallama Tunda Sai sun Biya Gidan Alhaji Tsoho Ta Chan zasu Wuce. Hajiya maimuna Saboda Sabon Zama dasu Umma Harda Hawayenta Su kansu su Umma sun ji Dabam Sun hadamata Turaman atamfa Abba ya bata kudi 5k da Farko taki karba sai da Su Umma suka matsa mata Anyi sallama Cikin Sabo da Mutumtawa Dina itama Tayi kukan Tafiyar Hajiya maimuna ammh Bata da yarda Zatayi Tana ji Tana gani Suka Shisshiga Mota suka Fita Daga Haraban Gidan Ita kanta Hajiya maimuna Tayi kuka ta Dauki Arman Tana ta sakamai albarka tace Zuwa Sati mai Zuwa Zata Tafi Sudan. Dina Shashenta ta koma Tana ta kuka Shi kanshi Arman kuka yake Dina Tana kukan wani abu Guda Daya na Rashin Sanin Tabbas kan wannan Rayuwar Data Sako kanta aciki Sai taji kamar Tabi Hajiya maimuna su koma Sudan Tare ammh Soyayyar Zain fa..? Taya zata iya Rayuwa batare dashi ba..? Ammh ai Shi bai Shirya Rayuwa da ita ba asali ms ya Tsaneta kuka kawai take bamai Lallashinta Daga Karshe ta Rumgume Arman Tana kuka Domin ahalin yanzu Shi kadai ne nata. Achan Gidan Alhaji Tsoho bayan Sallama da Fatan alheri Da Godiya daya Biyo baya Sai Alhaji Tsoho yace Baban Kaduna ya Kira Zain awaya yace yazo yayi sallama da Surukansa Daya Kirasa bai Daga ba sai ya Kira Haddir shima bai Dauka ba sai da ya kara Kira ya Daga ya gayamai Sakon Alhaji Tsoho koda Haddir yaje Office din Zain Ya gayamai Sakon Murje ido yayi yace ba inda Zashi yana kan aiki ne Haddir fa ya Fara Tsinkewa da Lamarin Zain Dole ya Kira Baban kaduna ya Zabga mai Karya Cewa Aiki yayi ma Zain din yawa ammh In yayi Sauki Zai zo. Da Alhaji Tsoho yaji haka bai Damu ba Kwamishina ma bai Damu ba yace bakomai,Hajiya maimuna ne taso Ta gansa Kafin Tatafi sai dai ta Fahimci baya son Haduwar Tasu Har Bakin Mota Hajiya Mama da Inna Rukayyah suka Rakasu dasu Abba bayan sunyi hannu da kwamishina yana yi musu Godiya Kamar ya kwanta musu Kafin ya Shiga Mota Jifa Jifan Guda 2 suka bar Haraban Gidan kana su Abba suka koma Cikin Gidan suna kara Tattaunawa Abubuwan da suka Faru Alhaji Tsoho na kara Nusar dasu yarda da Hakuri Komai sai ya Wuce batare da an sani ba. Alhaji Tsoho yayi amfani da wannan Damar yace Gobe kafin su koma bakin aikinsu yana son yayi Wata mgana dasu sukace Shikenan Allah yakai musu Rai. Kamar yadda ya Faru yau din ma Wasan buya akayi Tsakanin Zain da Haddir bai yadda sun kara Haduwa ba sai Washegari da Safe Dayazo Gidan Abba Shima yaje gaida su Umma ya bar su Abba agidan Alhaji Tsoho suna Kara sallama dasu Baban kaduna Hatta dasu Umma sun san Zain baya kwana agidan sai dai wannan karon basu da Hurumin cewa komai wanka yazo yayi ya Sauya kaya Da Suka Hadu da Haddir Fuska ya Hade bai ma bashi Damar wata mgana ba Sauri Sauri ya kara Ficewa Daga Gidam Ko Barayin Shashen Dina bai kallah ba Duk da yayi kewar Arman yaso ya aiki Zareena taje ta Daukomai sai yaga suna aikin Share Sharen Dakin da Dina Ta Zauna Shiyasa kawai ya Wuce abunsa. Aranar Inna Rukayyah Ta koma kano tabar Shema da Zafeera Zuwa Sati mai Zuwa Zasu Dawo Daddyn Abuja da Baban kaduna suma sun koma Cike da Farincikin Gudurun Alhaji Tsoho kan ya"yansu hakika yayi Tunani mai kyau kuma Dukkansu suna Maraba da Wannan Hadin Tunda sun Lura Duka ya"yan nasu so suke sai Sun Zama Tazurai ba aure Batare da sun gayama Kowa ba su kayi Shuru da bakinsu sai Lokaci yayi Ko Hajiya Mama Alhaji Tsoho bai sanar mawa ba Ya bari sai Lokaci yayi Tukunnah. Allah Sarki Rayuwa Dina Tana ganin Rayuwa Domin har yau Datake Sati Daya da Aure bata saka Zain acikin idanuwanta ba Tayi kuka har ta gaji,Tadai san Kwana Hudu da auransu Zainab Tazo ta Dauki Arman tace ya Dakta ya aikota Daganan Ranar kullum da Safe in yazo Gida yin wanka ya Sauya kaya kafin ya koma Cikin asibiti sai ya aika a Daukomai Arman ya gansa Hatta Abba ya Fahimci Zain baya kwana a Shashen Dina ammh bai mai mgana ba Yayi kamar bai gane ba. Yau da suka Cika Sati Daya da Aure Haddir ya Ritsashi Da Daddare acikin Office dinsa yace ko yana so ko bayaso sai Ya kaishi Gidansa yau ya gaji da yin wannan Wasan yar Boyen dayake yi ma Mutane Zain dai bai samu ta cewa komai ba yayi Kokarin yayi Zille ya Gudu Haddir ya Kasa ya Tsare suna Tashi Daga Cikin asibitin Gidan Alhaji Tsoho ya wuce dasu ya Sakashi Daki yayi wanka ya bashi Wata Farar shadda yace ya saka yace Wlh bazai saka ba Shi ba Farinciki yake ba Haka ya Lallabasa ya saka wata Shadda mai Ruwan kasa Daganan ya kaisa Wajen Alhaji ya Xayyanamai komai Alhaji Tsoho yaji Ransa ya baci ya Dinga yima Zain Fada da Nasiha wanda bawai bai ji bane yaji ammh Duka sun Shiga sun Fita ne yayi Riga yayi alkawarin yadda Dina Tayi sanadiyar Rasa Farincikinsa Wlh itama tabar samunsa har Abada. Sadda kai yayi ya nuna bakomai Hajiya Mama tayi mai Fada soaai ta kuma gayamai Hakkin Dina yanzu yana kansa ne,Sai ya Kitaye ya nuna musu yaji Fadansu har da yi musu Godiya nan kuwa bai Dauki Ko Daya ba Suka Fita Alhaji Tsoho da Hajiya mama suna saka musu albarka Da Haddir ya Daukesa bai Zame da shi ko"ina ba sai Tukubun Tsire shi ya Fita ya Siyo Tsire da Kaza da Lemukam Sanyi bayan ya Dawo ya bama Zain wai na Tarbam Amarya Zain ya Turbune Fuska yana ma Haddir wani kallo Kafin ya Kece da Dariya yana Fadin"Wacece Amarya din..! Dina..? Yafada yana Dariya Haddir ya ijiye ledan nan gaban Motan yana Fadin"Ohon maka Dan iska kawai koma Wacece ai kafimi saninta ni Daga Taimako kada Allah yasa ka kaimata din ." Ganin Haddir din yaji Haushi yasa ya Daki Kafadarsa yana Fadin"Sorry My Best Friend..!Haddir yayi banza Dashi kamar bai ji sa ba Ya Tada Motar suka bar wajen har suka kai Gidan Abba Ba wanda ya kara mgana. Haddir yana gama parking ya Kashe Motar ya Fito Dole zain ya Fito yana wani Bata rai Haddir ya kallesa yana Fadin"Ina Ledan kazan..? Zain yace"Baka Daukota ba Tana Cikin Mota.."Haddir yayi Tsaki yayi gaba yana Fadin"Au Daman ni kake jira na Dauko maka Kazan amarcin naka..? Lokacin da Zan rakaka Wajen Halima inace ba ledan na hannunka ba..? Zain yace"Ita kace.Ita din Annurin Zuciyata...Dina fa. ! Itace wacce na Tsana aduk Duniya.."Haddir yace"Kai dai ka sani..zaka Dauko ledan ne ko na kama gabana..?jin kalaman Zain yasa ya koma Motar ya Bude ya Dauko Ledan yana wani Tura baki Suka wuce Haddir na kallonsa ta Gefen ido Yana mamakinsa aransa yana Fadin Daga baya kenan. Kai Tsaye Shashen Da aka Saka Dina Suka Nufa Tunda Falon suke jin Kukan Arman Da Sauri Dukkansu suka karisa Falon Zain ya ijiye ledan na saman Center Table ya Shiga Cikin Bedroom din inda yake jin kukan Arman yana Shiga ya gansa akan gado yana kuka ya kusa ma Fadowa yayi saurin Daukanaa ya Rumgumesa yana Lalashi sai ga Dina ta Fito Daga Tiolet suka ci karo da Zain Dukkansu suka kalli juna Cikin wanu yanayi ita Dina na Faeincikin ganinsa ne shi kuma na Tsana ne Cikin Fada ya kalleta yana Fadin"Wani irin Iskanci ne Zaki bar yaro karami Shi kadai a kan gado yana neman Fadowa..? Cikin Sunkuyar dakai Dina tace"Kayi hakuri..Barci yayi na kwantar Dashi Na shiga na Yi alwala Shine ya tsshi ya Fara kuka.."Zain dai Dogon Tsaki yaja ya Fice Dauke da Arman yana Fadin"Ki Fito Falo ga Haddir yazo.." Da kallo Ta Bishi sai kuma ta saki Mirmishin Farinciki har Abada bazata Daina Son Zain ba Sallar ta Tada Sai da ta idar kana ta Fito Falo Cikin katon mayafinta su Dina an Zama musulmai,. Ta iske su Dauke da Arman Haddir yako lafe jikinsa yayi Shuru sai wasa irin ta jarirai yake yi Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ta zauna ta gaishe da Haddir ya amsa yana kallonta yana kuma Tambayanta Allah sa batayi Fushi ba..? Kanta na kasa Dina ta Girgiza kai Zain na kallon Gefe yana jin kamar ya Daki Haddie ganin ya Dake sai bata Hakuri yake na Rashin kawo ango kan Lokaci Daga Karshe yayi musu Nasiha Kafin ya Mike ya mikama Zain Arman Dina Tana ganin haka ta Mike Tana Fadin bari ta Kawo musu abinci,Bata fara Girki ba Sai gobe Daga Shashen su Umma aka aiko mata dashi. Haddir yace Alhamdulillah ya Gode Sallama yayi mata Ya Fice Zain yabi bayansa Dauke da Arman sun Dade suna mgana aharaban Gidan Haddir nata kara bama Zain baki kan yaji Tsoron Allah Zain kawai karkace kai kawai yayi yana Jinsa yana kuma kallonsa Adage ammh afili sai ya nuna ya Gode kuma zai Gyara,nan suka yi sallama Haddir ya Shiga Motarsa Domin Dare yayi wajen 9pm na Dare ko Shashin su Abba bai Shiga ba kuma sun ga Motar Abba alamun yana Gida Sai da Motar Haddir tabar Haraban Gidan kana ya koma Cikin Gidan ya Iske Dina na Tsaye afalon tana Jiransa Batare da yayi mata mgana ba ya Mika mata Arman ta saka Hannu ta karba Daidai Lokacin da Hannayensu suka Hadu da Sauri ya Jaye hannunsa yana Jifanta da wani kallo na Komai Mayanta sai kin barni. Ya juya yana Shirin Shiga Dayan Bedroom din yace"Ga Leda nan..Haddir ne ya mtsa sai an Siya.."Daganan yaja key din Motarsa ya Shige Dayan Bedroom din ya Banko kofa yana Tunanin Zai yi Lambo ne ya nuna komai Normal kafin Shirinsa ya kamallah bai da ko Jallabiya anan kuma Gashi Dare yayi Allah kaimu da Safe zai yi parking din kayansa Daga Shashen Abba ya kawo su nan zai Dinga zuwa yana kwana kada irin su Haddir su kara lura da bai kwanan Shashen ammh kuma Da kwanansa agidan da Rashinsa zai zama Duk Daya ne. *Shakira...* 8/4/21, 3:29 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣0️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Tunda ya Shige Dakin Dina bata kara jin Duriyar Zain ba Haka taja sanyin Jikinta ta Wuce Dakinta ta kwantar da Arman kana tazo Taja ledan Ta Bude taga abunda ke Ciki Bata da wani kwadayi abakinta sai ta Rufe komai ta saka Cikin Fridge din Dake Kitchen Wani yanayi na Shiga ranta Lalle Tsanar da Zain yayi mata ba kadan bane. Komawa Daki Tayi wanka tayi tazo Kusa da Arman bayan ta saka kayan Barci,Tunanin Duniya duk ya isheta Ammh ta wanni Fanmi sai taji Dadi ko banza Tana jin kamshin Zain din acikin Gidan yafi Abaya da Baya kwanan Gidan Ta Dade batayi barci Ba Tana Tunanin mganar Dataji Hajiya maimuna sunayi da Nene inda Ana gobe za"a Daura musu aure da Zain take gayamata Shashen Da take Zaune yau aciki Aciki Iyayan Zaina suka Zauna ta Tabbata da abaya ne ko sama da kasa zassu Hade bazata zauna ba sai dai ina ayanzu bata da wani Zabi ko ahaka aka Tsaya ta Tabbata Zaina Taci gari. Washegari kamar yadda ya Gudiri Niyya Tunda ya Fita Sallar asuba Tare da Abba da Sadiq da Faruq suka Dawo Abba nata sakamai albarka ko bai Fada ba yaji Dadin ganinsa Gidan kai Tsaye Cikin Gidan ya Shiga yabi Umma Da Nene Daki Dukkansu ya gaishesu Su Zafeera ne akitchen suna abun karyawa nan yake ji yau Zasu koma kano. Dakin Sadiq ya shiga ya Tattara Duka kayan sa Duka Dayake Dakin Dama basu dawani yawa wasu Suna gidan Alhaji Tsoho wasu ma kawai zai sake siya,Kayansa Dake lowsoct kuma bai ma bi ta kansu ba Rabonsa da Gidan har ya manta Ko albashin Tanimu megadi Haddir ke Zuwa yana Bashi Shi Tunda Firstlove ta bar Rayuwarsa ya ji gidan ya Fita Ransa... Kowa yaga Zain yayi parking din kayansa sai yaji Dadi ammh banda Zafeera da Zainab da suke Taya Zaina Kishi Nene kuwa Har waje ta rakashi Umma dai na Ciki ba fito ba Bayan sun Fito Haraban gidan ne yake Tambayanta waya kawo Motar Dina nan kuma Saboda yana ganinta ya gane Motar nan Nene ke gayamin Zakiya ta kawo mata Ranar da suka Rabu Baram baram kada kai kawai yayi Daganan Nene ta koma Shi kuma ya wuce Shashen Daya zama  Nashi yanzu. Koda ya shiga Dina Tana Kitchen Tana Dafa Ruwan Zafi Domin Tama rasa me zatayi Tunda bata iya komai ba Shi kanshi Ruwan zafin don yana Ruwa ne,Taji Shigowar Zain da Sauri ta Fito tana gaisheshi ko kallonta bai yi ba sai da yakai kayan Dakin ya Fito yana kallonta yana Fadin"Ina Arman..? Dina Tace Cikin Sanyin Murya"Yana Daki yana Barci..Ina kwana.."Zain bai amsa mata ya kada kai ya wuce Dakin Dina ta Bisa da Kallo wani Sanyi ya Shiga ranta na ganinsa da kayansa Ta Tabbata Kodai mgana mai Dadi bazai Shiga Tsakanibsu ba zai zauna agidan kuma zai kula da Dansa. Da Sauri ta koma Kitchen Tana Kokarin ta Soya kwai kada Zain ya Fita sai dai bataci Sa"a Ba Tana Kici kicin Soya kwan wanda sai da ta kira Hajiya batula ta gayamata yadda Zata Soya nan ne ma Take shaida mata Gobe Hajiya maimuna Zata koma Sudan bata Cikin Hayyacinta yasa kawai tace zata kirata Hajiya batula bata Ji wani mamakin kiran Dina na ya ake Soya kwai sanin Ko Dafa Ruwan Tea ma Dina bata iya ba Gata yayi mata yawa. Tana Kokarin Soya kwan Kawai Taji Fitarsa koda ta Fito ta leke ta window Ta Hango Fitar Motarsa daga gidan har yayi wanka ya Shiga kai kawai ta Kada wata Zuciya na Fadin Ki yi Komai saboda kanki kawai Dina Domin ko kanki Zaki Dafa awannan karon Zain bazai Dawo yana Miki kallon Mace ba. Dole ta koma Kitchen din ta Cigaba da Soya kwan Wanda duk ya Kone bata iya ba karshenta kasa Ciyuwa yayi mata Sai watsa mai Ruwa Tayi Lokacin Taji kukan Arman ta Ruga Zuwa daki Duk ta Fige ta Rame saboda ta Fara Wahala ga Arman ga kuma na Gida,wanka Tayi mai ta bashi Nono yasha yayi barci itama Taje tayi wanka Ta fita Falo Tasha Tea kadai Tazo ta Dauki Arman ta Saka mayafinta ta Nufi Shashensu Umma kamar yadda Hajiya maimuna tace kullum da safe ta Rika Shiga Tana gaishesu kuma taji Nasihan kullim Tana Shiga da Safe su gaisa ko bakomai hakan yana ma su Umma Dadi Tunda Dinar ta Darajasu. Lokacin Data Shiga ne ta iske su Zafeera na Shirin Tafiya Abba ya Fita Tun dazu nan falo ta zauna suka gaisa da Nene Umma Ma na wajen ita tama karbi Arman Dake ta Lumshe ido alamun barcin bai Ishesa ba,Yaron yayi Girma sai wayau yake abinsa Shema Ta karbesa Zainab Tana ta yi musu Hotuna Domin Arman yaro ne mai Shiga Rai Dina na Shashen Har su Zafeera suka Tafi Motar Haya suka Shiga Direba na Tare da Abba a office. Sai da suka Tafi Tana Shirin baro Shashen Tunda Arman yana Wajen Nene ta goyashi ya koma Barci Sai ga Goggo Halima ta iso Daga gada su Umma suna ta ina suka sakata,Kwallah ya Cika idanuwanta sanda Nene ta kwanto Arman ta mikamata Tana kallonsa Tana Kara Jinjina Gudurin Allah Tana kuma ma Halima Fatan Allah yasa itama ta Haife Cikin Jikinta Lafiya Goggo Halima Tayi tayi ma Arman addu"a da ita kanta Dinar Wacce taji duk kunya ya kamata Ta sani itace sanadin Tafiyar zaina ammh ko kadan Goggo Halima bata nuna mata ba, Ganin Arman din na hannunta yasa Tatashi Tatafi Shashenta Tana Tunanin me zataci yunwa take ji kamar Nene ta Shiga Ranta Ba Dadewa Zainab ta Biyota da abinci ta karba kamar an saka ta a aljannah Dama ta gaji ita ba iya Girkin nan tayi ba Batasan kuma Yaya Rayuwarta Zata kare ba Dambun Zogale mai Hanta Taci tasha Ruwa ta Hayr Bisa kujera ta kwanta Arman kuma na Chan Shashensu Umma nan barci ya kwasheta bata sani ba. Da yamma Daga asibiti Haddir da Zain Gidan Alhaji Tsoho suka je bayan ya gaishesu ya kwashi Wasu Daga Cikin kayanshi Zuwa Gida Har ya shiga ya Fito Dina Bata sani ba Tana  cikin Dakinta ta Shiga Tiolet tadai ji Motsi kuma Tasan shi ne Daganan Shashen Su Umma ya shiga sai yaga Goggo Halima murna ta kamashi itama haka ya zauna kusa da Goggo Halima yana kallonta kamar yayi kuka ganin ta Goya Arman Tsab Tun Safen nan yana nan Shashensu Umma Sai ya fara kuka akaisa yasha Nino. Zain najin Taruwar kwallah ya kalli Goggo Halima yana Fadin"Insha Allahu goggo sai kin goya ya'yan Firstlove da Wannan bayan naki insha Allah.."Goggo Halima na Sharan kwallah Tana Fadin"Allah ysa.Allah ya yarda Zainullahi Allah yasa zan ga wannan Ranar.." Ta Fada Tana Sharan kwallah ba Zain ba Hatta su Umma sai da Jikinsu yayi sanyi Zain ya Kada kai yana Fadin"Ina ji ajikina Firstlove Tana nan Lafiya ita da Abunda ta Haifa kuma Zata Dawo gareni da Zarar Lokaci yayi.."Dukkansu Suka Bishi da kallon Mamaki kafin Umma tace"Taya akayi ka sani...? Kansa na kasa yace"Ina yawan yin Mafarkinta kuma ayadda nake ganinta bata Cikin wani Wahalan Rayuwa kuma na ganta da yaro a hannunta acikin Barcina.."Ajiyar Zuciya suka Sauke Nene tace"Allah yasa haka.."Daganan suka Cigaba da Tattauna mganar Zaina har Abba ya Shigo Nan ya Tsaya suka gaisa da Zain da kuma Gogggo Halima ya Shiga Ciki Zain kuma Sai da ya Tsaya yaci Tuwon Shinkafa Miyar agushi da Nene tayi ya koshi Lokacin Arman yayi barci Goggo Halima Ta mikamai Arman din bayan yayi musu sallama ya Fice Zuwa Shashensu. Koda ya Shiga Dina bata Falo Sai ya wuce Bedroom dinta Direct ya isketa Zaune gefen Gadonta Tana waya yaji Tana Kiran Daddy shi yasa ya gane da Kwamishna take mgana bai Tsaya ma Jiranta ba ya kwantar da Arman nan kan gado ya Fice Dina Ta Bishi da wani Kallo Wanda ita kadai ta san Ma"anarsa. ***** *Zaria..* Bangaran Zaina kuwa itama Tuni Tayi arba"in Daga ita har su Anun sun sauya sunyi Kiba Jajir dasu Zaina Ruwan Zafi ya amsheta Haihuwa ya saka ta Kara Budewa ta zama Babba Daga Faridan Har Zulaihat din tafi su Girma su Anun kuwa basu da mtsalan komai Domin Iyaye uku Garesu in Farida bata nan suna Tare da Zulaihat in kuma Ta na nan suna Hannunsu Sun Fara wayansu na Jarirai Turbarkallah Masha Allah. Farida ce komai nasu bata kyashi Ta yarda ta Fita taje ta bada Jikinta abata kudi Saboda Hidimar Zaina da yaranta wadanda take gani kamar wasu alhalinta ga kuma Zulaihat da suka Riga suka zama yan'uwa Zaina akoda yaushe addu"anta Daya Allah ya karkata Hankalin Farida taji Tana Sha"awar komawa Gida Domin bata so Takoma Gida ta bar ta acikin Wannan Rayuwar ba Daga ita Har Zulaihat Tayi alkawarin yadda Suka Tsaya Domin Inganta Rayuwarta itama sai ta Tsaya tsayin Daka sai sun Samu Farinciki kamar yadda take samu Daga wajensu. Sun koma asibiti an Basu madaran da za"a Rika bama su Anun Farida ta siya aka Cigaba da basu ana Hada musu da Nono Cikin Ikon Allah Madaran ta Karbesu sunyi Kiba kamar ba su ba,Daman ko da suka Dawo an guwan basa harka da Kowa su kadai suke Rayuwarsu kuma banda Kacharalle da Uwar mata bamai Zuwa gidan Shiyasa ba wanda ya saka musu Ido Tunda ba"a ga wasu maza na kara kaina Acikin Gidan ba Farida bata kawo Maza ita haka Salomta yake sai dai ta Bika ka Biya Kudin aikinta kawai. Kuma Tunda suka Baro Gidan Uwar mata koda wasa Daga ita Har Zulaihat ba wacce ta kara Komawa sai dai In kacharalle yazo ya basu Labarin Abubuwan Dake Faruwa Shine ma ya gayamasu Fada ya kaure Tsakanin Suby da Rufy,Rufy ta Dauko Wuka ta yanki Hannun Suby Gida ya Rikice Suby Taje ta Dauko ma Rufy yan sanda Aka Tafi da ita da Uwar mata taji labari ta saka aka tafi Harda Suby din aka kulle bata zo garin ba sai da suka Ci Ubansu Bayan Tazo Tayi Belling dinsu tace su bar mata Gida sai da sukayi ta kuka suna bata hakuri kana ta Hakuri da alkawarin in suka kara Mata Dambe sai sun bar mata Gida. Daga Faridan Har Zulaihat Allah ya kyauta kadai suka ce Zaina kuwa abun ma mamaki yake bata kai Allah ya Rabamu da Mummunar kaddara ta gode ma Allah da suka bar Wanchan Rayuwar kuma Tana Fatan sunbarta Chan Har Abada kenan. ******* *Bayan wata uku..* Bayan Shafewar watanni uku Abubuwa Dadama sun Faru masu Dadi da akasasinsa Ta bangaran Dina dai ba masu Dadi bane Domin har yanzu da suke Cikin Wata uku da Aure da zain bazata Dora komai a zamansu ba Domin ba Zaman aure suke ba kowa yana Zaman kansa ne Bai Taba cin Abincinta bai taba kwana adakinta ba bai taba Cin Abincinta ba bai taba mata wani kyakyawan kallo da sunan Tana matsayin matarsa ba,Iyakarta Dashi ya Fita Tin Safe Zuwa asibiti Sai Dare yake Dawowa Tsakaninta Dashi gaisuwa Sai ko in ya Shigo Daukan Arman wanda yayi Wayau har ya Fara koyon Zama wani Lokacin ma Chan Shashensu Umma yake Tarar da Arman din. Wani Lokacin ma baya kwana agidan acikin asibiti yake kwana Saboda ko ya kwana ma agidan ba wani amfani Duk da Bata iya Girki ba Ammh Tana Kokarin ta jagwalgwala hakanan ammh Zain bai taba ma kallonta ba balle har ta saka Ran Watarana zai ci Ballatans Har ta burgeshi. Harkan Gabansa kawai yake yi bai Hanata walwala da Rayuwarta ba ammh ya kuntata mata Rayuwar nata gata dai Ta Cika Burinta na mallakan Zain sai dai bai mata wani amfani ba,Tun Dina na Hakuri har tazo ta Kasa Itama mace ce Tana Bukatar Namiji balle kuma Tana Ci ta Koshi koda yaushe in Ta ganshi Sha"awarsa kara kamata yake sai dai ta Shige Daki Tayi ta kuka kamar me bamai Lallashinta bata iya gayamawa kowa ba suna Waya da Hajiya maimuna Danginsu na Chan Sudan Sai dai tayi Shuru bata cewa komai,Haka ma ko sunyi mgana da Daddy ko Hajiya Batula sai dai tace komai Lafiya gashi duk ta Rame saboda Raino da kuma Tsotaon Arman inda ma Allah ya Taimaketa su Umma na Rage mata wasu Wahalwalun ai Data gane bata da wayau bata da wanda Zata gayama Damuwarta Zakiya ce kuma Bata ma san Isalin Zakiya ba Domin Ranar sunan Arman da suka yi Kacha kacha bata kara Nemanta ba itama bata Nemeta ba. Haddir taso tayi ma mgana da Farko sai kuma ta Fasa Tunda Shima ba ganinsa take sosai ba Sai Ko ta Shiga Wajensu Umma ko kuma Tabi Nene Ko Zainab Zuwa Gidan Alhaji Tsoho suke Haduwa Shima da sun gaisa Shikenan Ta rasa ya Zatayi da Rayuwarta Bangaransu Umma kuwa basu sanmeke Faruwa ba ganin Zain din ya kwantar da Hankalinsa yasa suka Fara Tunanin ya Fara Yadda da duka kaddaransa suna Tunanin kuma ya karbi Auran Dina Da Hannun Bibbiyu kamar yadda yake Nuna ma Mutane Faruq Tuni ya koma makaranta Sadiq ne kadai agida sai Zainab Zafeera ma tazo tayi sati Biyu ta koma Saboda makaranta Duka ahalin Basu manta ba Koda yaushe suna addu"an Allah ya bayyana Halima ya Dawo da ita Gida Lafiya kamar yadda ta Fita Zain kuwa kowa mamakin yadda ya koma yake yi ya Fara maida Jikinsa kuma baya nuna wata Damuwa ko kadan,Iyaye sun Fara Murna suna Tunanin Komai ya Daidaita batare da kowa ya sani ba ya Riga ya kamallah Duka Shirinsa jira kawai yake Lokaci yayi ya sanar kuma ya Tabbata azuwa Lokaci ba"a da yadda aka iya Dashi Tunda Bakin alkalami ya Riga da ya Bushe. Arman kuwa yana Kara wayau Kamaminsa da Zain yana kara Bayyana kuma yana kara Shiga ran Kowa acikin Gidan Hatta da Alhaji Tsoho da Hajiya Mama musamman ake kai musu shi ya wuni chan Tare da Zainab Tunda Ya riga ya saba da Dangi Baya Rigima sosai kuma ya Riga ya saba da kowa Shiyasa baya yawan Rigima ko bai ga Dina ba kuma suna Bashi Madaran yara in yayi kuka Shikenan sai Kaji Shuru. ***** Achan Zaria ma Tuni su Anun suma sun Fara Koyon iya Zama in ka gansu Turbakallah masha Allah,Yaran suna da ban Sha"awa Sosai in ka gansu Suma kamaminsu da Zain yana ta kara bayyana Kyansu na kara Fitowa. Kayan Wasa kuwa kusan Rabin Daki Farida ta cika dashi Tunda Anun da Anan din suna son Wasa sosai babu Abunda suka Nema suka Rasa Bangaran kayan saawa Madaransu da Ruwan Shansu Duka kafin Wata ya Kare Farida ta Tanadi komai ,Farida Zuciyar Zinare gareta Zaina Na jinjina ma Irin Zuciya ta Farida Domin Daya ce acikin Dubu. Da ita Zulaihat sune komai nasu Anun Sun Riga suma sun saba dasu in Farida bata nan data Shigo Zasu fara Zillo suna Rarrafawa Zuwa gareta in kuma Zata Fita sun kama kuka keman sai Zulaihat ta Daukesu Ta lallashe su suke yin Shuru Zaina Tayi ta mamakin Jarirai dasu ammh sai wayan Tsiya. Ganin Zaman Gidan babu Abunda suke yi yasa Zaina tayi ma Faridan mgana Zasu Shiga wata islamiyan Dake kusa dasu,Batayi gaddama ba ta basu kudu suka siya Form ita da Zulaihat Suka kuma Biya kudin Makaranta,Ammh tayi musu Fadan su kula da kansu bangaran matan aure suka Shiga 2pm zuwa 4pm na yammah In Zasu Tafi kulle gidan suke Zulaihat ta Goya Anun ita kuma Zaina ta goya Anan In Farida na Gida Bata Fita ba kuma sai su bar mata Tuni Su Zaina suka Zama yan makaranta Daman ita abubuwan da ake koya musu Bita ne Tunda duk ta iyasu Sai da Zulaihat wanda Zainar take kara Taimaka mata agida in da bata gane ba basu yarda sun yi kawance da kowa ba,sai dai gaisuwan Sama sama kuma amakaranta Kowa ya san Zaina Mamarsu Anun ce Zulaihat kuma kowa yana Tunanin kanwartace suma ahaka suka barsa basu yarda sun bama Kowa Fuskan da Zata Shiga Jikinsu ba saidai gaisuwan sama sama Tunda Farida ta gargadesu da su kula da kansu. ***** *Bauchi..* Yau ta kama Asabar din karshen Mako ne Yau gidan Alhaji Tsoho cike yake da duka ahalinsa Maza da mata Domin Tun Bayan Faruwar Abunda ya Faru na Zain da Dina sai yau kuma aka sake irin wannan Zaman Taron Wanda Alhaji Tsoho ya sake gamgamin Hadawa Saboda wani Kwakwaran Dalili nashi wanda suka Tsaidashi Shi da ya"yansa. Tun Jiya Bakin nesa suka yi ta isowa irinsu Baban kaduna da Daddyn Abuja da Inna Rukayyah Wacce tazo Tare da Shema da Zafeera Da Farko Zafeeera tace bazata je ba Ammah Alhaji Tsoho yace Inna Rukayyah Tazo da ita Inna Hannatu ma na wajen Kowa da kowa ya Hallara Zareena ce kadai bata awajen Harda Dina Ma Tazo Tana gefe Arman na Hannun Mama Safiya Haddir na Wajen Hakama Zain wanda Daman da Biyu yazo Kamar shi din ma yana Jiran wannan Ranar ne shima ya Fadi Abunda ke Ransa. Bayan Gaishe gaishe da kuma addu"an Bude Taro Da Sadiq babba yayi Alhaji Tsoho ya Fara Jawabinsa b kamar Kullum nasiha ne kan su hada kawunasu su zama Tsintsiya Daya madaurinta Daya kafin ya Gangaro kan Dalilin Zamansu da Abunda ya Tarasu. Sunan Haddir ya kira wanda sai da gaban Haddir ya Fadi ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho yana amsawa Kai Tsaye kuma ya juya alaqan Kiran nashi kan Zafeera itama sai taji Faduwar gaba Daman Tunda akace Alhaji Tsoho ya matsa azo da ita Ranta ba Dadi Tana ta Fama da Fargaba. Dukkansu suka amsa Jikinsu yayi sanyi Atare yace su taso su kariso Zuwa gabansa Kowanme Jikinsa bai basa ba suka mike suka isa gabansa suka Durkushe kuma Dukkansu ba wanda ya kalli Dan"uwansa. Sai da ya Dade yana Nazarinsu kafin yace"Hadiru da Zafeera ku Dago kanku ku kalleni..' Dukkansu Atare suka Dago Gabansu na Faduwa Alhaji Tsoho ya kallesu yana Fadin"Kusan Dalilin Taruwarmu anan wajen yau..? Suka Girgiza kai atare Alhaji Tsoho ya Kada kai kafin yaDago yana kallon Babam Kaduna Lokaci Daya yana Fadin"Bashir gaya musu Hukuncin da muka yanke akansu Tunda bazamu Zira musu ido suna Yadda suka ga Dama ba..! Baban Kaduna ya gyara Zama yana Fadin"Alhamdulillah..Daman ba wani Abu bane yasa muka Taru a nan wajen sai Domin mu Sanar da yaran nan abunda Babanmu ya yanke kuma ya nemi Shawaranmu mukuma muka ga Tabbas Mganarsa Tayi Daidai an hadu ne anan wajen Saboda Kowa yaji kuma yaShaida Mun yake Shawaran Hada Auran Haddir Da Zafeera Insha Allahu Auransu Zai Tabbata nan da Wattani Biyar Zuwa Shida Lokacin Ita Zafeeran Ta Shiga aji hudu amatakin karatunta Domin mun gaji da ganinsu suna Zaune babu Aure duk wanda akayima mgana sai ya Fara yimana yawo da Hankali ba.." Kowa afalon Baki ya Washe da jin wannan mganar banda Haddir da Zafeera wanda suka Dago suka kalli Juna Lokaci Daya kowa ya kauda kai Cikin Wani yanayi acikin Zuciyansu da basu Nuna ba Hajiya Mamace ta Saki Guda Tana Fadin"Alhamdulililah Alhaji ka Biyani..Lokaci yayi dasu Hadiru Za"a Daina zaman gauranci Ita kuma Wannan mara kunyar me Koran masu sonta Anyi mganinta abu yayi Dadi.."Dariya aka saka su Umma nata Masha Allah Zain dai na Gefe shima yana Dariyan Mugunta Dina kuwa Zaune kawai take tana Bin Kowa da kallo Tana so da za"a bata dama da Ta Fadi itama Damuwarta. Alhaji Tsoho ne ya kalli su Zafera Dake durkushe kowa yana Saka Abunda ke Ransa yace'Baku ce komai ba..? Atare suka Dago Bayan sun kalli Juna na wani Lokaci kana Kowa ya Kauda kansa Cikin Sanyin Murya Haddir yace"Bamu da ta cewa Alhaji Tsoho Abunda kuka yanke akanmu Shine Daidai .Allah ya sa alheri Zaku kullah..'Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Cikin Farinciki Zafeera kuma kanta na kasa tace"Banda ta cewa...Duk Abunda kuka yanke akaina Daidai ne sai dai Ina Rokon alfarman abari na gama karatuna sai ayi auran.." Alhaji Tsoho yace"Karki Damu..Ko Bayan auran Zaki ci gaba da karatunki da yardan Allah.."Ta kara Bude baki Zatayi mgana Alhaji Tsoho ya Dakatar da ita da Fadin"Bikin ku Zai Gudanan nan da wata Bakwai Insha Allahu.."Dole Taja bakinta tayi Shuru Falon kowa sai Fatan Alheri yake da Fatan Allah ya kaisu da rai da lafiya. Zain na Gefe ya Mike yana Fadin"Ina da mgana Alhaji Tsoho.."Kallo ya Dawo kansa Alhaji Tsoho yace"Muna Sauraranka Zainullahi..."Kansa na kasa yace"Kumin afuwa iyayena na yanke Shawara batare da saninku ba awattanin baya na Nemi wata mkaranta medicine School ne a India Mumbai medicine School inda naje nayi wannan karatun a baya, har na Samu ma kamallah Duka Cike Ciken da Zanyi nan da Kwana Goma Zan Tafi Chan zan je nayi wani Course na Wata Takwas Kan Harkan Fida da abunda ya Shafi Cututtukan mata.." Gabadaya Falon Kowa sai ya kallesa Dina kuwa Cikin mamaki da al"ajabi take kallon Zain Lokaci Daya taji wani Hawaye sun Cika mata ido. *Shakira...* 8/5/21, 4:10 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣1️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Gabadaya afalon ba wanda bai goyi bayan Zain ba su Baban kaduna sukace wannan Babban Cigabane gashi Zain din da kuma Cigaban Asibitin Saulawa. Matan kuwa suna Murna ganin Zainullahi ya fara manta Abubuwan da suka Faru tunda har zai koma karatu azuciyar iyayansa kuwa suna Fatan Allah yasa ba Saboda batan Halima bane zai yi Nisa Da Gida ba. Alhaji Tsoho ya Kada kai yana Fadin"Tunaninka Tunani ne mai kyau Zainullahi kuma naji Dadin haka..Sai dai Da ita iyalanka Zaka tafi ne..? Sai da Zain ya juya ya kalli Dina Wacce ke kallonsa Idanuwanta Cike da Hawaye da wani Raunin kar kamin haka kafin ya Dauke kansa Bayan ya Dallah mata Harara Cikin Sanyin murya yace ma Alhaji Tsoho"A"a Ba da ita zani ba Alhaji Tsoho karatu ne zan je nayi na wata Takwas kamar yadda naje nayi ashekarun baya Zuwa da Iyalina Zai iya Taba Abunda naje Dominsa,mun gama mgana da ita Zata zauna tare dasu Umma sai dai in na Samu Dama Kila nazo na ganku ko Sau Daya ne kafin na kamallH Insha Allahu.."Gabadaya kowa yayi Na"am da Tsarin Zain Dina kuwa kanta ta Dukar tana Sharan kwallah Cikin Zuciyarta tana kara Tabbatar ma kanta Zain ya Tsaneta Soaai Tunda har Zai iya Saka kafa ya tafi wata Uwa Duniya ya barta batare Daya Taba Dubanta a Matsayinta na Matarsa ba bai Taba Tunanin ita mace bane Tana da Rauni kuma ita ba Dutse bace Tana da Sha"awa Tare da ita Ta lura Yana Sha"awar yaga ya sakata Cikin Kuncin Zuciya kamar yadda yake Ciki. Kamar Ta mike ta karyatashi gaban kowa ta sanar Dasu ita bai Tsara haka da ita ba sai kuma Ta Fasa da Tunanin Kila har gwara Zamanta Tare dasu Umma ahakan ma ya ta kare,Balle ya Dauketa ya Tafi da ita Uwa Duniya Batasan kuma Wani hali Zata Shiga ba ta Tabbata Tsanar Datake gani a nan kadan ne da wanda zai nuna mata karshenta yadda ya Tsaneta ma ya barota Chan ya Dawo abunsa Tunda hakam ma bazai Damesa ba Illah ya gayama Iyayanta ta bace ne chan kuma kashashen Turawa Kila har ta gama gararanbanta ta Mutu bamai kara jin Labarinta da wannan Tunanin ta kama bakinta ammh Lokaci Bayan Lokaci Tana Sharan kwallah Zainab Dake gefenta na kallonta acikin Ranta kuma Tana Fadin Daman ya zama Dole ki koka Domin Wannan Ranar tana Zuwa Miki Daman.. Koda aka Tashi Taron Rayukan Kowa na Cikin Farinciki Banda Haddir da Zafeera da Dina Zafeera Dakin Hajiya Mama ta Shige Tana kuka ita an Cuceta arasa dawa za"a Hadata sai da Ya Haddir mai Shigen Girman kai Ko Dariya baya ma Mutane ita Jininsu sam bai Hadu ba Zainab da Shema nata bata baki Suna Nuna mata yanayinsa kenan Shi bamai Hayaniya bane ammh Taki yarda ita Damuwarta Daya makomar karatunta Tunda ta Tabbata Bayan Auran ba Binta Zai yi kanon Suje su zauna ba ammh kuma Bazata yi Shiru ba ana Gama Biki Zata koma kano Abunda Sai ya Nemi matar da Zai Zauna da ita su Umma na Falo bama su san Darun da Zafeera keyi ba su atunaninsu Tunda Suka Fadi wannan mganar Daga ita har Haddir basa Jinsu suna musu kallon Yara ne su masu Biyayya da Gudun Zuciyar iyayansu. Abangaran Haddir ma Hakan Ta kasance suna Hanya Zasu Tafi asibitin Zain ya Daukeshi a Motarsa Tashi ta Lalace Tana Gareji Gabadaya ya Zurfafa Tunani Bai Taba Zaton Iyayansu Zasu iyamai wannan Dukan Lokaci Daya bai Taba Shiryama kansa Aure nan da wata Takwas ba Yana Tsoron mata da Shedancinsu yana son Samun Mace Tagari wacce Zata soshi Tsakaninta ga Allah kuma ta Girmamashi da Duka ahalinsa bai Taba kin Zafeera ba sai dai Shima yana mata kallon Wata mace mai Girman kai mara Fara"a ga Tsiwa da Rashin Kunya sam Shi kanshi Jininsa da ita bai Hadu ba sai dai bazai Taba watsama Ahalin da suka maidashi Mutum kasa acikin Ido ba Ko bakomai Zafeera ya' take wajen Umma da Abba kuma Mutanen da suka Rikesa Tamkar Dansu komai na Rayuwa Abba yayi mai in ko yace bayason Zafeera bai kyauta uwa uba kuma yaga Duka iyayan nasu sun yi Na"am Da wannan Hadin Baya Fatan ya watsa musu kasa acikin Idanuwansu. Har suka iso Haraban asibitin bai sani ba sai da Zain ya Dafa Kafadarsa kana ya Dawo Cikin Hayyacinsa Cikin Sauke Rai ya kalli Zain yana Fadin"Yaushe muka iso..? Wlh ban sani ba..? Zain yana Kokarin Daukan Wayarsa yace"Ina fa Zaka sani kana Chan kana Tunanin Amaryanka Zafeera akun Umma.."Hararansa Haddir yayi Lokaci Daya yana Bude Murfin Mota ya Fito yana Fadin"Zaka sani ne Ina da Fada dakai wlh..Wai ka Shirya Zuwa karo Karatun wani Course ko ka sanar dani kaji ko Nima ina Ra"ayin Zuwa ko..? Zain Shima ya Fito Daga Motar bayan ya kulleta suka Jera Zuwa Cikin asibitin yana Fadin"Afuwan Abokina..Bana son Ka hanani ne wlh.."Hadddir yace"Ni na isa ne..! Ai bamai iya Hanaka Abunda kayi Niyyah Zain..Alrigh all d Best..Allah ya Bada Sa"a nima inaga Zan je ko Ameriaca ne nayi Kan Harkan Kwakwalwar kai Insha Allahu.."Zain na Dariya yace"Sai dai ka bari bayan Auranka ku Tafi da Zafeera Daganan kusha Honeymoon.."Duka Haddir ya Dagamai abaya yana Fadin"Uwar Honeeymoon ne ba Honeeymoon ba.."Zain sai Dariya yake shi kuma Haddir yasha Kunu Haka suka Karisa Cikin Asibitin kowa ya Wuce Office dinsa Ammh acikin ran Haddir farinciki ya kamashi ganin Zain yau yana Dariyan da tun Bayan Abunda ya Faru bai Taba ganinsa Cikin Farinciki irin na yau ba yana Fatan Allah ya Dauwamar da Farinciki a Rayuwarsa na har Abada. Washegari Zafeera ko Inna Rukayyah Bata bari sun Jira ba Suka Bi Motar haya Zuwa Kano Ita da Shema tayi ma Abba karyan Assigment gareta Zatayi Submutting aranar Dole aka barta Suka Tafi duk da Shema tasan karyace bata Fada ba,Dina kuwa Ranar kwana kuka Tayi da Neman ma kanta Mafita Zain bai ma san Tanayi ba yana Chan yana ta Shirin Tafiyarsa Ranar da yammah Inna Hannatu tabi Jirgi ta koma su Abba kuma sai da suka kara Kwana kana kowa ya Dauki Iyalansa Zuwa Gida. Zain nata Shiryan Shiryan Tafiyansa Yagama su Umma Zai Je har Gada yayi sallama da Goggo Halima ya Shirya Tafiyan ana Saura kwana Hudu ya Tafi sai kuma Arman ya Tashi da Zazzabin Da Amai Dole ranar ya Daga Tafiyan bai Tafi ba Asibiti suka Wuni da Arman din a Office din Din Haddir yana kula Dashi sai da aka sakamai Ruwa da allurai Tunda Zafin Zazzabin yasa har suma sai da Arman din yayi Hankalin Zain ya Tashi Sosai bai san yana son Arman ba sai Ranar Dina kuwa kuka Ta wuni yi hakama su Umma Kowa hankalinsa atashe acikin asibiti Kuwa kowa yaga Dina sai mamaki Daman ta na nan..?Abun mamaki gata kuma Dauke da yaro sai dai babu wanda yayi Tunanin yaron yana da wata alaqa da ita Dinar Tunda ma Daidaikun mutane ne suka gansu sanda suka Shigo asibitin Allah yasa Dr.Imram baya Cikin Asibitin da ko da Bala"i sai ya Gano Komai. Sai Dare suka koma Gida bayan Jikin Arman din yayi sauki har ya Farka Dina ta bashi Nono Shashen su Umma suka yada Zango saboda suma Tun Tafiyarsu suke kiran waya hankalu Tashe sai da suka ga Dawowarasu da kuma Arman Daya samu Sauki kana Hankula suka kwanta Nene ta karbeshi Taje tayi mai wanka da Ruwan zafi mai Zafi sai gashi ya samu Barci nan Suka barsa Wajen Nene suka Nufi Shashensu Har yanzu Dina bata Daina kukan ba Ran Zain ya baci ya waigo a Zafafe yana Fadin"Wai kukan me kike yi haka..?Dallah Kima mutane Shuru Tunda ba Mutuwa Arman din yayi ba.." Jin Haka yasa ta Damke Bakinta ta karisa Dakinta da Gudu Tana kuka ya Rakata da Tsaki Shima ya Taka Zuwa Dakin Dayake kwana ya tube kaya ya Shiga wanka bayan ya Fito ya Saka Jallabiya ya Shiga Kitchen ya Bude Frigde ya Dauko Ruwa yazo yasha sai ga Zainab da Kololin abinci Daman yunwa yake ji nan ya Zauna yaci ya Koshi ya tashi ya Shiga Ciki yayi alwala ya Rama Sallar mangariba da Isha"in data Subucemai ya koma ya kwanta Saboda gajiya Lokaci Daya barci ya kwasheshi. Dina Kuwa Dakyar tadaina kuka Taje tayi wanka itama Tazo Tayi sallah Ta koma ta kwanta Tana Kuka ita kadai tasan Halin Datake Ciki na Sha"awar kasancewa da Mijinta in taje ta Tareshi Wulakanci ne Zata gani ganin Idonta kuma in ta bari ya Tafi ya barta Kila Zata Fada wata Halakar a iya Hangenta ta kasa samun mafita,Shigowar Zainab ne ya katseta ta kawo Arman ya Tsshi yana kuka ta Fito Falo ta karbeshi sai Lokacin Taga Kololin abinci Ta kuma Fahimci Har Zain yaci Tunda ga Filet da Cokali nan Zama tayi ta bama Arman Nono Yasha ta Lallabashi yafara barci ta kai Shi Ciki ta kwantar kana ta Dawo ta Zuba abinci kadan ma ta iya ci ta Ture komai ko iya Dauke Kololin batayi ba ta Tashi ta Shige Ciki har ta kwanta Tana Tumanin Mafita har garin Allah waye bata samu Wata Mafita. Da Safen ma Tana gani Yazo ya Duba Arman ya bashi mgungunarsa Tana kwance kanta ke Ciwo ko ta kanta bai bi ya Dauki Arman suka Fice Shashensu Umma yakaishi Nene ta karbeshi yace ayi mai Wanka yaga Jikin nashi da Sauki Zai Tafi asibiti ya Fito kenan suka Hadu Da Haddir yazo Duba Arman suka koma Ciki ya karbesa ya Dubashi yace ba wani Mtsala basu Tsaya ba suka Tafi kowa ya Shiga Motarsa Zuwa asibiti. Zuwa yammah Arman ya Watsake yana ta Sha"aninsa,Dina kuma da Ciwom kai ta Wuni da kuma Tunanin Mafita,Washegari kuma Zain ya Tafi Gada Yaje yayi ma Goggo Halima Sallama Da Sha Tara na arziki da zai Tafi ita kuka Shi kuka yana Rokonta kada ta gaza wajen yin addu"an Allah ya bayyanamai Firstlove Shima Dagachan In Lokacin Zuwa saudiya yayi zai biya ya Tafi yaje gaban Ka"aba ya Roki Allah ya Bayyanamai Firstlove. Kwana Yayi a Dakin Goggo Halima suna Hira Sai da suka kusa Raba Dare daman kuma Tsakanin Goggo Halima da Zain sai Allah tana ta yimai Nasihan Hakuri da Rayuwa Dangin su Zaina kuwa sai zuwa gaidashi suke Tare kuma da Fatan Allah ya Bayyana Halima Koda ya Dawo garin bai Zauna ba Shirin Tafiya yake tayi Dina kuwa batama san Baya nan ba abakin Nene take jin Zain din yaje Gada Dangin Su Zaina sai taji ta kara Raina kanta Lalle ga Maganar Zakiya Datace kada Tayi murna don Zaina ta bace gwara aganta akan ace ba"a ganta ba Gashi kuma Tagani Tatafi da duka Rayuwar Zain Dana Ahalinsa. Zainab Ta Tambaya yaushe Zain zai tafi ita kuma ta gayamata Gobe Tashin Dare zai yi ammh ta Abuja Zai tashi so Gobe Haddir zai Rakasa Abujan yaga Tashinsu kana sai ya Dawo Tunda Taji haka sai hankalinta ya Kara Tashi ta koma Daki Tana wani Tunani Har ta dauko Waya Zata kira Zakiya wata Zuciyar Ta Hanata da Tunanin In ta Kirata Duk Wulakancin Dayayi mata ita ta Siya da kudinta Dole ta fasa sai Chan wani Tunani ya Fado mata taji ta yadda da Shawaran da Zuciyarta ta bata. Da Daddare ta Rubuta sako acikin Takarda ta aiki Direban Abba zuwa wani Babban Chemist ya Siyo mata Tana Kofar Shashensu kada ma ya Dawo Wani ya Tareshi ya karba mganin asirinta ya Tonu Duk da in ba Likita ba ba wanda zai san wani irin mgani ne Cikin lokaci sai gashi ya Dawo ta Karba da Sauri ta Shiga Ciki Daman arman na Wajen Zainab kai Tsaye Kitchen ta Shiga ta Samu Lemu Coke wanda Zain kesha Daman shi yake ijiyarsu Guda 3 ne ta kwashe Biyun Ta Dauki Dayan zuwa Cikin Bedroom dinta Ta Fasa kwalbar mganin ta Samu Sirijin Ta Zuka aciki Ta Tsira Cikin Lemon sai da yagama Shigewa tsab kana Ta saki Mirmishi Goge komai tayi ba wanda zai gane an saka wani abu ta maidashi Cikin fridge din Sauran 2 kuma ta Sakasu Karkashin Gadonta,Sirinjin kuma da kwalban mganin Ta Kullesu Cikin wata bakar Leda ta Tusa Cikin Wardrope dinta Yadda ba wanda zai gane akwai wani abu awajen. Da Sauri ta Shige Tiolet Tana wanka Zuciyarta Cike da Farinciki yau ko Zain naso ko Bayaso sai wani abu ya Shiga Tsakaninsu,Tana Cikin yin wanka Taji Shigowar Zain Shashen nasu daidai Lokacin ana Kiran Sallar Isha"i Tana Cikin Bayin Tayi Dariyan mugunta Koda ta Fito sai taji Motsin Fitarsa aranta ta saka Kila masallaci Zashi. Zain Daga masallaci Shashensu Umma ya Biya ya gaishesu Yaga Arman bayan Nene yana barci Abunsa Da ya nemi ya Tafi Dashi kamar Nene ta san wani abu Tace ya barshi Tunda yana Barci ne Haka yayi musu sallama ya Fice. Yana Shiga Direct Kitchen ya Shiga ya Bude Fridge abun ya bashi mamaki ganin Coke Dinsa ya Rage saura Daya Alhalin yasan Dina bata Sha bai Tsaya bama mamakinsa muhimmanci ba Ya Dauki Dayan Daya gani ya Hada da karamin Kofi Zuwa Falo kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Zauna ya Bude Lemon ya Tsiyaya ya kafa kai yasha Dina Dake leke ta Daka Tsalle alamun Murna Tarkonta ya kama kurciya. Cikin Bedroom dinta ta koma Tana Mirmishi Ta Fara Shiryawa Cikin Farinciki da Jinjina ma kanta yadda Lokaci Daya Tunaninta yayi aiki Sai da ta Gogama kowami Lungu na Jikinta Turaren kamshi Wanda Dan Sudane Hajiya maimuna Tazo mata dashi kana ta Dauki Wata arniyar Rigar Barci Sabuwa ce Cikin Wanda Tazo Dashi Tundaga Gida ne bata taba Sata ba Mai kalan ja mai Budadden gaba pant kadai ta saka bata Saka bra ba Nonuwanta da suka Cika da Ruwa sukayi wani Luhu Luhu suna wani kyalli Ta gyara gashinta Tayi mai parking mai kyau ta koma Gefen gado ta Zauna Tana auna Iya Lokacin da mganin Zai game Jikin Zain sai ta Fita Lokacin Tasan bashi da wata mafita. Munti Talatin Tayi tana Jiran kafin ta Fito Daga Cikin Bedroom dinta Tana wani Takun Isa Daga kofarDakinta ta Tsaya Tana kallon Zain Daya Durkushe Dafe da Cikinsa sai Hada Zufa yake Dariyan Farinciki ya kamata Ta Fara Taku Zuwa garesa Kamshinta na Tunkaransa Kamar almara haka Zain ya dago kansa yana Bin Dina da wani Kallo wanda ya kasa gane wani Hali yake Ciki..? Ya tabbata wannan yanayin Dayake ji ayanzu Rabonsa Dayajisa har ya manta Tun Bayan Tabarbarewan komai kuma ma bai Taba jin irin wannan yanayin ba yana ji in bai yi ba zai iya mutuwa. Shidai Dishi Dishi ma yake gani Yadai ga sanda Dina ta iso Gareshi Ta Tallafeshi Tana mgana bai ma Fahimtar me take Fada,Shi dai yaga Ta Tallefeshi Sun Shiga Bedroom dinsa Daganan bazai iya Dora komai ba Domin Komai Daya Faru ba Cikin Hayyacinsa bane Domin Gushewar Tunani ya kamashi Daya kasa Fassara abunda ya Faru. Shi dai ya Farka 6am na Safe ya gansa kwance kan gado Tare da Dina suna Barci sai Lokacin Komai ya Fara Dawomai Daki Daki bai Nemi amsan Kowa ba ganin Dina ba kaya Lullube Cikin Blanket da kuma yanayin Daya ga kansa da kuma abubuwan da suka Faru Jiya suka Fara Dawomai Ya gane Dina ce ta Sakashi Cikin Tarko Ko bai sani ba Shi Likita ne Tabbas kwaya ta sakamai a lemo yasha Domin Komai ya Faru Tsakaninsu Duk da yayi Bakinciki Kara Zama Daya da Dina ammh kuma bashi da ta Cewa Tunda shi Mijinta ne kuma Tana da Hakki akansa Gashi kuma yana Shirin Barim kasar kansa ya Dafe ya tashi ya Shiga Tiolet yayi wanka Tsarki Dana Sabulu yanayi yana Tunanin Zainarsa da kuma Irin yadda Dina ta iya Sakamai mganin Karfin Sha"awa Cikin Lemon shansa Lalle ashe bata Saduda ba Iskancinta na nan.. Ya Dade kafin ya Fito ya Fito Daure Towel ya ganta Ta tashi Zaune Tana kuka Ko kallonta bai yi ba ya Dauki kayansa ya Koma Cikin Tiolet din ya Zura ya zo ya saka Darduma yayi sallar asubar data Subucemai Ita kuwa Dina Tana kuka ne kukan Bakinciki gashi Dai Burinta ya Cika Komai ya Faru sai dai kuma Tsawon Daranan nan Zain Ambaton Firstlove yake kamar wanda ya Zauce Tayi bakinciki Sosai ta kuma Kara Tsausayama kanta ganin a Ke bancewa Tsakanin Mata da Miji ma Zaina Bata bar Ran Zain ba Lalle ta kara Tabbatar ma kanta wannan kaunar Daga Allah ce. Har ya idar da Salla bata bar kuka ba Ya Zo ya Fara hada kayansa Cikin karamin akwati Domin karfe 10am zasu bar Bauchi Shida Haddir Zuwa Abuja 7pm na Dare Jirginsa Zai Tashi Zuwa Delhi. Sai da yaga Abun nata na Iskanci ne kana ya Dago Rai bace bayan ya bar Abunda yake yake Fadin"kukan nan naki yana Cikamin kunni malama..? Yafada yana Kafeta da ido Sai Jikinta yayi sanyi ta kauda kai Cikin Sanyin murya tace"Kayi hakuri.."Karamin Dariya ta kama Zain sai da ya Dara kafin yace'Hakuri..? Sorry for u Self Malama Dina wannan kukan munafuncin naki ba inda Zai kaiki Kinsan dai Ni ina gabanki aharkam Likitancin nan ko..? Karya ne ki Min wayau Malama tashi ki Fitarmin adaki Tunda Abunda kike nema kin samu banga amfanin Zamanki ba..! Yafada yana Nuna mata Kofa Kunya Duniya ta kama Dina Taji ta Muzanta Cikin Sanyin Jiki ta Mike bayan ta Dunkule Cikin Bargon Jikinta Tunda bata da kaya Rigar barcinta bata ganta ba Ta gabansa ta Wuce tana wani Rangaji Da Tsaki ya Rakata Kawai har ta Fice ya Cigaba da Hada kayansa Cikin Kunar rai yana gamawa ya Fice Zuwa Shashensu Umma Chan ya karya ya iske har Nene tayi ma Arman wanka ta Shiryasa tana Fadin bai yi Rigima ba Sau daya ya Tashi Cikin Dare tana bashi Madara yasha ya koma Barci. Dina kuwa Tana wanka Tana kuka Tana Tunanin tayi aikin Burni Inji Tusa Ta gama Hada Duka plan dinta ya Fashe da ita Ina amfanin Abun kunya Mijinka ma sai ka Gusar mai da Hankali Zai kusance ka kuma Daga karshe ya gamo ka.? Bata Taba Zton Haka ake Jin kunya ba Daga Ranar da Zakiya ta Kira Daddy da kwarto sai yau Dakyar tayi Sallar Asuba Komai bata saka acikinta ba ta koma ta kwanta Tana kukan Wannan Abun Bakinciki. Tana Kwance sai ga Zainab Tazo Cikin Shirinta ma na Tafiya makaranta ne tace Ta fito bata san Yau Ya Dakta zai Tafi ba suna Haraban gida dasu Umma Dole ta Mike tana mamakin Tayi Nisan Tunanin Tunda bata ji Shigowar Zain ba Da Sauri Ta Zari mayafinta da Takalmi Tabi bayan Zainab Dukansu Gidan a Haraban Gidan ta gansu har da Abba Sadiq da Haddir ne Tsaye Wajen Motar Haddir din Akwatin Zain kuma Tuni aka saka Cikin Booth. Zain na Dauke da Arman suna kara sallama dasu Umma suna ta kwararamai addu"an Samun Abunda yaje nema Nene na Fadin ya Rike addu"a ya kuma kula da kansa Abba ma Haka Shidai sai Mirmishi kawai yake acikin Ransa yasan Fargaban da suke yi kada ya kara Komawa Ruwa Shi kuwa me ya aikeshi..? Ai Ruwan Daya Dake ka shine Ruwa. Dina na Gefe Tana kallonsu gabadaya ta kasa koda Motsi,Har sai da Zain din ya kariso gabanta ya Mikamata Arman ta saka Hannu ta karba Tana Kauda kanta Cikin Rada yace mata"Zan tafi ki kula da Arman..Sannan ba zan ce Miki ki kula da kanki ba ammh Ki sani Zunubi ne mai Girman yin Zina da Aure..Tunda kikayi iya Yimin Fyade na Tabbata bazaki Zauna haka ba sai dai Ina Gargadimki Da ki kiyaye.."Daga Haka ya Dago yana Mata Mirmishi kamar irin suna Sallaman Masoya Dina kuwa duk sai ta Raina kanta Idanuwanta suka Fara Tara kwallaj da Sauri ta Juya Dauke da Arman ta koma Cikin Gida su Umma suka bita da kallon Tsausayi suna Zaton kukan Tafiyan Zain ne hatta Arman Dake yaro yana waigen Babansa. Agabansu Umma Zain ya Shiga Mota Haddir ya Shiga suna Dagamai Hannu yana Daga musu suka bar Haraban Gidan Zain shi ya hana Sadiq Zuwa Tunda Haddir din sai gobe zai Dawo Abujan,Asibiti kuma wani Dr.Aliyu zai maye Gurbin Zain har Allah ya Dawo dashi lafiya. Sai da suka Biya ta Gidan Alhaji Tsoho Zain yayi mai sallama kana suka Dauki Hanya Wajen La"asar suna Abuja Sallah sukayi sukaci Abinci Lokacin Daddyn Abuja ya Dawo nan suka Zauna suna Hira har Sai 6:30pm sai da sukayi sallar mganariba kana Harda Mama Safiya da Hajiya karama suka Dumguma Raka Zain Zuwa Filin Jirgin Nmandi Azikiwe International Airport. Jiran kadan kawai sukayi aka Fara Kiran Jerin masu Tafiya Zain ne na 4 nan da nan sukayi sallama Bayan Rumgume juna da Haddir ya Dauki kayansa ya Wuce Layin Tantancewa wacce bata Dauki Lokaci ba 7pm da wasu Mintina Jirginsu Zain ya Lula Sararin Samaniya Sai da su Haddir suka ga Tashinsu kana suka Koma Gida Cike da kewa Musamman ma Haddir daya jisa Cikin wata irin kewa na Zain sai dai yana mai Fatan Allah yasa Abunda yaje nema ya Dauke mai Hankaki Daga Damuwa Da Tunane Tunane. Kwana Daya Shima yayi a Abuja Washegari ya koma Bauchi Cike da kewar Zain *Naga Sharhinku jiya Sosai kuma Naji Dadin haka..Sai dai Don Allah kada yau ayi kare jini Tsakanin Team Dina da Team Zaina...* *Shakira...* 8/6/21, 1:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣2️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Sai Washegari Zain ya Kira Waya ya sanar ya sauka Lafiya kuma gashi ma a Masaukinsa Daman Ta Internent yayi komai har Muhallin da Zai zauna har ya kamallah karatunsa kuma Dayake Wajen ba bakonsa bane sai komai ya zo mai da Sauki. Duka Kashe kashen da yayi na Kudi Da Guminsa yayi bai nemi Taimakon Kowa ba,Shiyasa Lokacin nan yaki yarda ya Siya Ma Dina Komai saboda bai yi Ra"ayin haka ba,sai da zai Tafi ne yaga in ya Tafi ya barta haka bai kamata ba ko Domon ita ba Domin Arman Shiyasa ya bar mata Daya Daga Cikin Atm dinsa anan Falo inda Zata gani,Duk da yasan Har yaje ya Dawo Zata Zauna karkarshin Kulawarsu Abba ne ammh a kallah ya Sauke wani Nauyi Dake kansa Tunda ya baro Nageria ya Tattara Dina da Duka Abunda ya Shafeta ya Watsashi Gefe Zaina ce kadai ya yarda Tunaninta yayi mai Kutse Cikin karatunsa. Dina kuwa Da Tun Tafiyar Zain ta kule kanta adaki Tana kuka yau ko Arman bata bi ta kansa ba Tun yana kuka har ya gaji ya Daina ya Bingire da Barci Gabadaya Sai yanzu take Nadamar Abunda ta aikata gashi Ta kare ba wani Riba sai kunya,Sai Zuwa yammah Ta iya Tashi tayi wanka tayi ma Arman ta Sabashi Zuwa Shashensu Umma Yunwa take ji kuma yanzu ko Ruwan Tea bata iya Dafawa da kanta. Taci Sa"a tana Shiga ta iske Zainab Ta Dawo makaranta Ta iske abinci ya kare sai ta Dafa Jallop Din Taliya da Kifi Nene tacr ta Zuboma Dina Din Daman Bata wuce Tayi,Arman kuma Umma ta Karbeshi ganin Daga ganinta yana ta Dariya nan Zainab ta Zuboma Dina abinci taci ta Koshi Sai Lokacin Hankalinta ya Dawo Jikinta Sosai,nan tayi Sallar mangariba da Isha"i Kana ta Koma Shashenta ita da Arman. Sai da ta koma ne ta Lura da Atm din Dake kan Center Table Din da wata karamar Takarda Sai da ta kai Arman Daki kana ta koma Falon ta Dauki Atm din Ta Duba Taga na Zain sai Lokacin ta Duba Takardan.."Ki yi amfani dashi.."Abunda Taga an Rubuta kenan ajiki Wani Mirmishin Takaichi ta saki Domin ita yanzu babu abunda Take Bukata sai Farinciki kuma Ta Rasaahi Ta riga ta sani sai dai bata da yadda Zatayi Ya zama Dole ta Zauna aduk yadda Rayuwa ta zo mata ahakan ma ta Gode ma Allah da iya Abunda ta Shuka take Girba. Jin Isar sa ma Sai da ta shiga Shashensu Umma Washegari taji Nene na Fadin ya Kirasu yace ya isa Yau da Safe,bata nuna bai yi mgana da ita ba Domin batama da Abun cewa sai dai ta Riga ta yanke ma kanta Hukunci bazata Zauna Bakinciki ya Kasheta Zata Rika Zama wajen su Umma ko bakomai Zata ci takoshi kuma Za"a kular mata da Arman kana Zata Rage zaman kadaici Da kewa Tunda yanzu Duka iyalan Na Saulawa Sun Daina Nuna mata wannan kyamar Ta Tun Farko Saboda Darajan Haihuwan Arman Da yaron ya Shiga Ran Kowa,Da kuma Duba da Kaddaran Samun Armam ne Duk ya kawo Abubuwan da sukayi ta Faruwa..Kuma Bawa bai isa ya Hana Kaddaran Allah ta Faru sai dai addu"a Tana iya Sauya kaddara. ****** *Ina Labarin Zakiya..?* Zakiya Tuni Ta Zama Amarya Tun bayan Wata ukun da Mallam Nuhu ya saka na Auranta da Ja"afar ya cika Bayan Ta Samu Tsarki Ma"ana jini uku agarin kano aka Daura auran Wanda Mallam Nuhu ya bama Ogan Ja"afar na Gareji Auran Zakiya Shi kuma ya karban ma Ja"afar kan sadaki Naira Dubu Dari... Zakiya itama Ana Gobe Daurin Auran ta Taho nan kano,Bayan Tagama Duka Shirinta ta Siyar da Gidanta ta Siya wani Babban Gidan Da Sauran kudaden Dake hannunta A anguwan baulu Area anan garin Bauchi Duka Shiryan Shiryan Bikin da Abubuwan da akayi duka na Auran Ko Biyar din Ja"afar bai yi Ciwon kai ba,Zakiya ce tayi komai ita tayi ma kanta Kayan Lefe na gani na Fada,Ita ta Siya ma Ja"afar kayan Fitan angonci da Duka Abun Bukata ita kanta Tasan Kudin Data Dade Tana Tarawa taci Ubansu sai dai bata damu bq Domin Daman Don Ta Mori Rayuwarta ne ta Tarasu yau kuma ga Ranarsu tazo. Hatta Duka Kayan More Rayuwar Dake gidan ita ta Siya komai saboda Tana so ta Fara Wata Sabuwar Rayuwa Shi kanshi Ja"afar din bayan ta sakarmai komai nata yasan Duka Sirrints,har Banki ta Bude tana Turamai kudi Domin nashi Hidiman ya zama kamar wani Bawanta ta maidashi wani Dan gata shi kuma sai Susuta yake da Salon Soyayyarsa tana kara jin Tagama yin Dace Duniya da Lahiya. Abunda ya Faru kuma Tsakaninta Dina kuma Sai da ta bama Ja"afar din Labari ammh bata gayamai gaskiya ba ta Dai Nuna mai Dina tayi mata Butulci Shi kuma ya bata Hakuri Tundaga Lokacin Zakiya taji Dina ta Fita Ranta tana ganin Ta samu Muradin Ranta bata Bukatar Kowa acikin Rayuwarta Shiyasa ta Watsar da ita ta Cigaba da Duka Shirinta. Dangin Mahaifiyarta Dake Minjibir sun zo Bikin Tunda Mallam Nuhu ya sanar musu Gida kuma Samira da Amarya Luba sunyi gayyah kuma Duka Kannen Zakiya sun zo Ana gobe Daurin Auran ta iso Amotar Haya Motarta ta Barta agida Tunda in za"a kaita Gobe Tashar Mota Zatayi yan"uwanta suje su kaita su Dawo kada ace aurants ya Fita Dabam tazo da Kudi na Hidiman Biki sai dai Mallam Nuhu bai karbi ko Biyar dinta ba Shi yayi Komai Yace Yarsa ce kuma Hakkinsa ne na ya aurar da ita. Taji Dadim haka Kanta ya kara Girma Kowa sai Tambayan Dina yake musamman kaninta da Suka sansu Tare da Dina sai tayi musu karyan bata kasar ne ita da Mijinta suka Dinga mamakin Daman Dina Tayi aure Zakiya tce musu eh Saboda bata son mganar Dinar sam,Ranar Daurin Aure kuwa Mota Hudu Daga Bauchi Ja"afar da abokansa da Waliyansa Shi dai a Motar da Zakiya data siyamai yazo Shi da wani abokinsa wanda suke aikin Gareji Tare kafin Allah ya Daga Darajansa. Karfe 11am na Safe aka Daura auran kuma Ba laifi yayi Jama"a Domin Mallam Nuhu ya Raba Goro ko Domin Mutane su daina mao kallon yaki Aurar da Zakiya ya barta Tana Lalacewa sai dai da yawan Mutane sun zo Ne Domin ganin ma idonsu,Kuma sun ga Mijin Zakiya aka koma ana Gulmar ai tama Girmeshi Kila Shima abokin Shashancin nata ne suka Daidaita komai dai menene Tadai yi auran kowa ya Huta.Wasu Daga Cikin Abokan aikinta sun mata kara sun je har kano Daurin Auranta Tawagar ango da Mutanensa aranar suka koma Bauchi ita kuma Zakiya Mallam Nuhu yace sai Washegari in da akayi Tashan Mota Biyu suka Tafi,Da dan kayan Dake Dake da Wasu abubuwan da ba"a rasa ba wanda Mallam Nuhu ya bada kudi aka yimata Duk da tace bata Bukatar komai,Duka kannenta sunje da Wasu Daga Cikin Dangin Mahaifiyarta sai Amarya Luba Samira Tana Gida bata je ba. Sunje sun ga Gidan Da Zakiya Zata zauna suka Dawo suna Labarin Cikin Daular da Zakiya Zata Zauna nan suka kwana sai Washegari ta saka aka maidasu bayan ta Cikasu da kudi sai mamaki suke Amarya ba Kawa kuma Komai ita take yi Shi Angon baya wani abu Wasu suna ganin Zakiya ta Tsinci Dami akala ne suna Ganin kyan Ja"afar ya Rudeta Wasu kuma Suna Tunanin Shi Ja'afar din yayi Sa"a wasu masu Dogon Tunanin suna ganin anya Zakiya bata yi kuskure ba kuwa..? Daran Ranar Ja"afar ya Kadaice Tare da Zakiya wanda da Farko kamar ita ta Sarrafashi sai da ga Karshen ya Nuna mata Shima ya Kware akan wannan harkan Daman Tayi banke banken mganin mata Harda Dinki Taje asibiti akayi mata Saboda Kada Ja"afar ya gane ita ba Budurwa ce,Sai dai abu Daya ya bata mamaki yadda Ja"afar ya Sarrafata ba Sarrafa ne na wanda bai san Hannunsa ba sai dai kuma Tayi la"akari da wannan Zamamin sai ta Daina wani mamaki,Da safe ya Dinga Lallabata Tana mai Shagwaba ita adole Ta kawo Budurcinta Wajen kwana Uku yayi yana Jinyarta Tana nuna mai taciCiwo shi kuma yana Biye mata kafin su koma suna ta Cin Amarcinsu Cikin Farinciki da kaunar juna Zakiya tana ganin ta gama yin Sa"a Duniya da lahira Data samu Ja"afar gashi yaro ga kyau ga iya Soyayyah. Sati Daya sukayi suna cin Amarci ta koma Office Daman Hutun Sati Daya suka Bata Kuma Tana Son aikinta Bata Hadashi da komai Dole ta Koma ammh Wuni suke suna waya da Ja"afar In Kuma tatashi aiki Shi yake Zuwa Daukanta Su Fita suje suci abinci sunyi yawo acikin Garinsu Ransu Fes Har Wasu Daga Cikin abokan aikinta Suna ganin Tayi Dabara Datayi auranta yafi wannan Gantalin Data Yi abaya. Auransu yasa Ja"afar ya kara Zama wani Jini da Hantan Zakiya ta Riga ta gama yarda Dashi ta sakarmai komai nata,Sirrinta da Duka Dukiyarta Babu Abunda bai sani ba sai Boyemai datayi Ita din Tayi Harkan Bariki kuma Tana Tunanin har Abada bzai Taba Fahimta ba Koda wani Zai gayamai Dina ce tasan komai kuma Basa Tare bata san Isalinta ba Tana ma Tunanin Kila Zain din ma yaki yarda ya aureta Tana Chan Gidan Kwarton Ubanta ita da Da"n Shege. Cikin Kwanciyar Hankali da Soyayya Da Muradi mai Girma Zakiya da Ja"afar suke Gudanar da Soyayyarsu Basu da Wata Mtsalan Komai na Rayuwa sai Zakiya Taga Dama take girki sai suyi sati suna Fita suna cin Abinci Basu damu ba Zakiya take Hidiman Tunda ta Hana Ja"afar aikin kanikancin Tace ba Girmanta bane Mijinta na Aikin Gyaran Mota Karatu zai Koma Zata nema mai Addmission anan ATBU bauchi ya Dora Karatunsa ya nuna mata bai san inda Takardan Sakandirinsa yake ba tace kada ya Damu Zata Siyamai Komai zai zama Daidai Shima zai yi karatu kamar Kowa Ja"afar yaji Farinciki ya Cikashi Sosai. ***** *Zaria...*! Achan Zaria kuwa abubuwa Duk sun Rikice Ga Farida Domin Bata da Natsuwa kwata kwata Saboda yawan Mafarkan Datake yi Tana ganin Goggo Fatu Da ya"yanta Cikin wani Hali Tun Abun baya Damunta har ya Fara Damunta yana Bayyana ajikinta. Ta Rame duk ta Lalace kamar ba ita ba gefe Daya kuma bata Samun Zama,Domin Uwar mata bata Kyaleta ba Koda yaushe Cikin kawo mata Sabbin Costumer take tana Zuwa House Service ko Hotel Service Kudi kam Kaca kaca haka take samu su kansu su Zaina sun Shaida hakan Domin Uban Siyayya Take Narko musu,Kayan abinci kuwa wasu basa karewa Wasu ke Tarar da wasu su Anun kuwa kaya ba adadi wasu basu Taba sakawa ba Tunda Suke Saboda kayan yayi musu yawa kayan wasa Kuwa sai Wanda ya gani Zaina Tana auna Ko Firstlove dayake Mahaifinsu sai haka A hidimar da Farida ke yi dasu Ita kanta da ita Zulaihat in ka gansu da Irin Rayuwarsu da kayan da suke sakawa ko Gidan Wani mai kudin albarka Tabbas Gasiiyan Uwar mata Tauraron Farida na Haskawa kuma Barikin ya karbeta Tun Farida na Boye Halin Datake Ciki har su Zaina suka Fahimta,Domin Ta Rame a tsaye sai Idanu da Dogon Wuya Duk Tayi wani iri in Tana Gida Sai ta Shige Ciki Ta zauna Tayi Shuru Cikin Tunanin zaina Data Fara Lura batayi mgana ba sai dai Tana Ma Farida addu"a a duka Sallolinta Allah ya maida Hankakinta Zuwa ga ya"yanta da Iyayenta Domin Kwata kwata Bata mata Sha"awar wannan Rayuwar. Yau ta kama Asabar Ne Jiya Farida ta Dawo Gidan Wajen kwananta Hudu Bata gida Tana Kaduna tace Tun kuma Jiyan Da Tadawo bata Fito Daga Cikin Bedroom ba Tana kwance Da Safe da Zaina ta Tambayeta sai tace mata batajin Dadi ne nan kuwa Tunanin mafarkin Jiya ne ya bata Tsoro Abbanta Tagani yana Kuka yana Kiran Sunanta Tana Kokarin Zuwa Garesa ne Wani Hayaki ya Tare Tsakaninsu anan ta Farka Tun Lokacin Bata Runtsa ba Mafarkin ya Tsaya mata acikin Ranta Ta kasa Sukuni gashi bata wani Jin Dadin Jikinta Ciwon kai da Jiri Ga shi bata da mgani ya kare kuma ta Dade bataje Taga Likita ba. Tana Jin Sallamar Zulaihat ta Runtse ido alaman Barci Take ganin Haka yasa Zulaihat ta Koma Falo Inda Zaina Take Zaune Tana karatun Littafin Ahalari Anun da Anan na Tsakar Falon suna Wasa da Kekensu Zulaihat tazo ta Zauna Kusa da Zaina Tana Fadin"Ni kuwa Sa'adiya bari nayi miki wata mgana..? Zaina ta Dakata da abunda take yi Ta Dago Tana kallon Zulaihat Lokaci Daya Tana Fadin"Ya akayi ne Ummu Anun ko Ummu Anan zan ce..? Zulaihat Tayi Dariya Jin sunan da Zaina take kiranta yanzu Tace"Duka Duk wanda kikace Daya ne...Ya"yana ne na Tabbata Ko Firstlove bazai Raba wannan kaunar ba (Dayake Zaina ta bama Zulaihat Duka Labarinta Ganin sun Riga sun zama Daya) Zaina Tayi Dariya Tana Fadin"Wane shi bai isa ba Zulaihat..ina Jinki Meya Faru ne..?zulaihat ta gyara Zama Tana Fadin"Game da Anty Farida ne ni kam baki Lura kwanakin nam duk ta Sauya ba bata san Zama damu koda tana Gida koda yaushe Tana Daki Kifa Duba Duk yadda take Kaunar su Anun yanzu bata Cika Daukansu ba.."Zaina ta Ijiye Littafin Dake hannunta Saman Kujera ta Muskuta Cikin Damuwa Tana Fadin"Uhm..Ashe kema kin lura..? Ai na Dade da Lura da yanayinta Zulaihat..Na lura bayan Damuwa ma Harda Rashin Lafiya na Damunta baki ga Duk ta Rame a Tsaye ba..? Ina Zargin Jininta ya hau kuma bataje asibiti ba.." Zulaihat ta sauke ajiyar Rai Tana Fadin"Nima Haka nake Tunani...Na shiga Damuwa ko Zamu sameta muje meke Damunta ne..? Zaina tace"A"a koda munje Bazata gayamana ba..Ammh Ki bari Zan Duba Lokacin Daya Dace zan mata mgana Allah yasa adace.."Cikin Sanyin Jiki Dana Zuciya suka Cigaba Da Tattaunawa mganar kafin su gangara kan Mganar makarantarsu. Zulaihat tatashi ta Shiga Kitchen Tayi musu abun kari suka zo suka karya kana Tayi ma su Anun wanka Zaina ta Shiryasu suka Hadasu da kayan Wasa bayan sunsha Nono Hade Da madaransu suka Kama wasansu har Lokacin Farida bata Fito ba Zaina da Zulaihat suka Zauna Zaina na kara ma Zulaihat Bitar karatun Qur"anin Inda Zasu Biya yau a makaranta. Sai Wajen gabda Azahar Farida ta Fito Duk ta wani Zama wata iri Wanka Tayi ta sha Tea,kadan ta koma Daki Daga Zaina har Zulaihat bayan gaisuwa basu ce mata komai ba sai Zaina ta Dafa Jallop din Shinkafa da Rana Kana ta Fito sukaci Tare har ta Saki ma Da Zasu tafi makaranta suka bar mata su Anun Allah ya Taimaka yaran suka Debemata kewa har suka Dawo Tana Walwalwarta Har Zuwa Dare. Bayan sun gama Hirarsu su Anun Tuni sunyi Barci Zulaihat ta Kwashesu Zuwa Dakinta Wani Lokacin Tare take kwana Dasu Farida Daman ta Dade da Shiga,Sai Zaina da Bayan sunyi Sallama da Zulahait Ta shiga Dakin Wanka Tayi saboda Taji Dadin Barci ta iske har Farida Tayi Barci Sai itama tabi gefenta ta kwanta bayan Tayi addu"An barci. Cikin Dare Zafi ya Tada Zaina an Dauke Wuta Tana Tashi Taga Farida Zaune kan gado Tayi Tagumi Batayi mamaki ba ta Mike Tana Tambayanta me ya Faru..? Kuma meke Damunta sai Farida ta kama kuka Dakyar ta iya Gayamata irim Mafarkan Datakeyi Tanayi tana kuka Zaina ta Rumgumeta Tana Lallashi kafin ta Dagota Tana Share mata Hawaye Tana Fadin"Anty Farida ki Tsaida Zuciyarki Waje Daya..ya"yanki da iyayanki da duka Danginki suna Bukatar ki ne,ina ji ajikina Ko wani Hali ake ciki Asirin Zubaida Ya Dade da Tonuwa..!" Farida Tayi Shuru Batace komai ba Zaina ta Dafa hannunta Tana Fadin"Kiyi Tunanin mganata..Ya kamata kiyi Tunanin komawa Gida kema ki bar wannan Rayuwar Don Allah.."Ta Dade Zaune batare da Tankama Zaina kafin ta Ture Hannunta Ta tashi Ta Shige Tiolet Zaina ta Bita da kallo aranta Tana addu"an Allah ya Sa Addu"antace ta karbu Domin ta fara Zargin Da hannun Uwar mata a Tsanar Komawar Gida da Farida ke yi. Tana Kwancen Taga Tazo ta saka Hijabi ta Tada Sallah Itama bata Koma ba ta mike taje ta Dauro alwalan Tazo ta Bita Sallar Bayan sun Idar kowa ya daga Hannu Sama yana Addu"a ita Farida Tana Rokon Natsuwa ne acikin Rayuwarta ita kuma Zaina Tana addu"an Allah ya karkatar da Hankalin Farida Zuwa Gida ya Rabata da Rayuwar Sabon Datakeyi. Kwana Biyu sai Faridan ta saki kamar ba ita har Tafiya ta kamata Abuja tatafi Bayan Tafiyanta da kwana Biyu Su Zaina suka Daina ganin Kiranta kamar ko yaushe Tunda in bata Gidan kullim sai ta Kirasu awaya sai gashi har aka kwana aka Wuni basu Jita ba,Sun kirata kuma wayar na kara ammh Bata Dagawa ba,hankalunsa gabadaya ya Tashi Barin ma Zaina da Duk ta Tsure ko abinci ta kasa ci Da Karachalle yazo yaji Labari Shima ya gwada kiranta bata Daga ba sai ya Kira Uwar mata ya gayamata itama sai nata Hankalinta ya tashi Ta kira Alhaji Badamasi Tunda Tana da Tabbacin Tare suka Tafi Abuja aikuwa ta sameshi shi yake gayamata Farida ba Lafiya kwanansu Daya da Zuwa Jiri ya Debeta ta Fadi suna wani asibitin kudi a Abuja Jininta ne ya hau kuma Gefen Zuciyarta ya Fara kumbura,Allah ma ya Taimaketa Bata kai kasa ba ya Tareta Data Fadi da ta samu Ciwon Barin Jiki tun jiya bata san Wanda ke kanta ba ammh Da Sauki yau ta Farfado sai dai sun mata alluran barci tana samun Hutu ne. Wannan Labarin da Karachalle yazo ma dasu Zaina dashi ya kara Tayar musu da Hankali Zaina kuka Zulaihat kuka su Anun ma suka kama Tuni Zaina tayi Damara tace sai taje Abuja Taga Halin da Farida ke Ciki Kilama Ta Mutu ne ba"a gayamata ba Lokacin da Karachalle ya kira Uwar mata yana gayamata Haka tana asibitin Tare da Farida da Alhaji Badamasin da Kawarta Hajiya Zabba"u. Jin Su zaina zasu Taho yasa Farida ta karbi wayar tayi musu mgana tace su kwantar da hankalinsu ta samu Sauki su Zauna agida Tana nan Dawowa Jin Muryanta yasa Hankalinsu ya kwamta har Zaina taci Abinci tabama su Anun Nono Jin Muryan Farida Domin da Farko Ta Fara kukan Maraici a karo na Biyu ammh Jin muryanta ya kwantar mata da Hankali. Farida kuwa achan asibiti Daga Uwar mata da Alhaji Badamasi suke akan ta bari ya Fita da ita kasar Waje ayi mata aikin Zuciya Ta samu Lafiya ammh Ta kafe taki yarda Saboda Tana Tunanin in Tatafi ina Su Zaina Zasu..? Wazai kula dasu..? Bazata iya Zuwa ko"ina ba sai ta Maida Zaina Bauchi kamar yadda Tayi alkawari Sunyi Sunyi ammh Taki yarda Uwar mata Haushi Duk ya Kamata tace in Domin Sa"adiya ne Tayi mata alkawarin Zata kula da su Har ta Dawo ammh Farida tace bata yarda ba Dole suka kyaleta Ranar Farida ta saka aka asallameta bayan Gargadin Likita na Rage Tunani da kuma kula da Shan mgani. Bata yarda Ta kara kwana ba Alhaji Badamasi ya Saka Direbansa Ya Dauko Farida Su kuma Uwar mata amotar ta taho Har Gyallesu Wajen 10pm Dare sai gasu da Zaina da Zulaihat Rumgume Farida sukayi suna kuka Da murnan ganinta itama sai ta Rumgumesu Tana Dariyan Farinciki Allah Sarki Tabbas su din Wasu ahali ne nata haka su Anun sukayi ta Mika mata Hannu suna Dariya ta Dauke su Tana Rumgumansu Cikin Farinciki. Uwar Mata suka kawota Har Gida ko Zama basu yi ba,Suka koma Zaina da Zulaihat suna Rige Rigen kula da Farida duk ta Rame kamar ba ita ba Zuwa kwana Biyu Farida na Gida su Zaina na kula da ita tana kuma Kiyaye Shan mgani sai ta Fara Jin Sauki Zuwa Sati Uku Farida ta Warke Garau Taji Sauki Sai kuma Ta Koma Bakin Sana"arta Duk da Zaina da Zulaihat din sunyi Sunyi Farida ta Zauna agida ammh Tace ba yanzu ba da Sauran Lokaci. *Adai yi Hakuri a Fahimci Juna Yan Gidan Zaina Da Dina..*🤣 *Janafty...* 8/6/21, 1:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣3️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *Bayan Wata Hudu..* "Bayan Wata Hudu da Tafiyar Zain Zuwa Lokacin Abubuwa sunyi Sauki ta Bangaran Rayuwa ga Iyalan Dr.Saulawa Sai dai ta bangaran Dina Akwai Bambamci Tana Zaune ne kawai ba Domin Tana jin Dadin haka ba Miji a kusa da ita bame gane Damuwa da Halin Datake Ciki Ba. Tun Tafiyar Zain bai Taba Kiranta awaya ba Sai dai sunyi mgana sau Biyu ta wayar Umma Shima ta shiga ne Taga suna Waya aka bata bayan gaisuwa Bai ce mata komai ba ya kashe Wayarsa Dina Tayi kuka Har Ta gaji da kukanta ta Hakura ganin bame Lallashinta gashi Dai ta Samu Cikar Burinta ammh kuma A banza Tunda bai da wani amfani agareta Kullum Daga Zaman Daki sai Zuwa Shashen su Nene ta Wuni achan Arman kuma yana Cikin Wata na Takwas ne yayi yawo har ya Fara Rarrafe yana Tsayuwa bai dai Fara Tafiya ba Gabadaya Rayuwarsa Tana Bangaransu Umma ne, Su ke kula dashi in ka ganshi Wajen Dina yaje shan Nono ne Zainab Ba inda bata Zuwa Dashi Ko Haddir Ranar Weekend zai zo ya Daukeshi ya kai shi Ya wuni Wajen Hajiya Mama da Alhaji Tsoho sai Dare yake Dawo dashi iya kulawa su Umma nayi mata Ammh ba nasu Take Bukata ba kulawan Zain take Bukata da Soyayyarsa sai Yayi mata Nisa kuma ta Tabbatar da mganarsa dayace Tunda ya Rasa Farincikin itama sai ta Rasa nata. Duk da tana samun Duka Jin Dadin Rayuwa Zuciyarta ba Farinciki Ta Zauna ta auna Tagani Cewa Barin Zaina Rayuwar Zaina bashi kadai yayi ma Illah ba Harda ita sai gashi Ta Koma Tana Rokon Allah ya bayyana Zaina ko Dalilin Dawowarta Zai sa Zain ya Dubeta amatsayin ta na matarsa Har Lambarsa ta Sata a wayar Nene Ta Rika Kiransa Tunda ya Dauka sau Daya yaji Muryanta Daga Ranar ko ta Kirashi baya Dagawa Dole ta Hakura Ta rasa wa zata Fadamawa Taji Dadi Dalilin Haka yasa Ta Tambayi su Umma Tana so taje kano Suka gayama Abba Shi kuma yace Taje Tunda Mijinta baya kusa. Zuwan Dina kano Tayi Sati Daya yasa Hankalinta ya Kwanta,Ta Samu Natsuwa Tunda Zasu Zauna Suyi Hira da Daddy da kannenta Da Take jawosu Jikinta yanzu,Domin Ta lura bata da kowa Bayan su,Hajiya Batula yanzu wani Girma Take bata Domin Duniya ta Fara Koya mata Hankali,Arman kamar kada ya Dawo Daddy da Hajiya Batula suna kaunarsa Balle su Waleed Har suna Cewa Anty Dina ta bar musu shi Dina na Dariya Domin Tasan ta koma ba Arman ta bani Wajen su Umma Haka Daddy ya Narka musu Uban Siyayyah ya bada Direba da Excort dinsa aka Maido ta Gida ita da Arman Ranar da suka Dawo kowa yayi kewar Arman wanda ya Fara Tata Hajiya maimuna Tana Sudan Dina na yawan aika mata Hotunan Arman Kuma tace mata Tana so Tazo Taga Dangin Mahaifiyarta ammh sai Zain ya Dawo kasar. Bayan Dawowar Dina Daga kano Ta Fara ganin Canji a atare da ita yawan cin Abinci Da kuma Kiba Datakeyi Wuyanta ya kusa Hadewa da Jikinta ga yawan Barci kamar kasa sai ta Fara Tunanin kila ta samu Chanji ne Dataje kano Kowa ya ganta sai yayi mganar Kibanta Ta kara kuma Fari da Cika Har Nene na Fadin Cikar Jego ne batayi ba sai yanzu Ashe ba haka bane Ciki ne Dina keda Shi ba"a sani ba Itama bata sani ba sai Da Watarana Ta Fadi Ta Fito Zata Shashensu Umma Ta Fadi Nan da nan aka Kira Haddir yazo ya Dubata yayi mata Wasu Tambayoyi Tun kafin ya Dibi Jininta Dina ta Fahimci komai Sai jikinta yayi sanyi Lalle Ta zama Wawiya Dabata gane Tana da Shigar Ciki ba kamar ba Likita ba sai dai Bata gane komai ba Saboda Tun, Haihuwan Arman bata kara yin Jini ba Shiyasa bata kawo komai ba alokacin ashe Abunda ya Faru Tsakaninta da zain Rabo ne yasa ta sakamai Mganin karfin Sha"awa har komai ya kamallah Domin Tana da Tabbacin Ranar ta samu wannan Cikin Tunda Tun bayan Auransu wannan ne Haduwarsu na Farko Kuma na karshe illah kuwa Domin da yammah da Haddir ya Dawo da Sakamakon Cikin Dina na Tsawon Wata uku ne da wasu kwanaki Dina na Jin haka Daman Tuni tayi Lissafi Domin In bazata manta ba Zain yana Da Wajen Wata Hudu da kwana Goma ne da Tafiya. Kowa yaji Labarin Dina Nada Ciki sai ya kara Sanyi Da lamarin Ubangiji ashe akwai Rabon Haihuwa a tsakaninsu Shiyasa komai ya Faru Kowa yayi Murna Wannan karon Fiye da Karon Farko Haddir da kanshi ya Kira Zain ya gayamai Lokacin Da yagamai ya kasa Tsayuwa sai da ya Zauna Da yayi lissafi shima sai ya Fahimci cewa Ranar da Komai ya Faru Tsakaninsu ne Dina ta samu Ciki Ranar Haka ya Wuni ba Walwala Jikinsa Duk yayi sanyi bai da ta cewa yanzu haka Firstlove Zata dawo Taga Dina ta Haifi Arman kuma Harda wani Ciki..? Da wani kallo Zatayi mai..? Bashi da yadda zai yi da Abunda Allah ya kaddara. Zafeera Dataji Labari a bakin Zainab baki ta Rike kawai Tana Jinjina Munafuncin Namiji Zareena kuwa Kiran Zain Tayi tana mai Tsiya Shidai ya kasa Mgana Ta kira Haddir Shima Tana mai Shakiyancin ango yasha kamshi Sai Lokacin ma mganar Bikin Ta taso mai Shidai Tunda akayi mganar bai kara Tada mganar ba kuma ba wanda ya kara mai magana abunda bai sani iyayansu suna nan suna ta Shirinsu batare da sun Saureresu ba Haka ma Zafeera itama bata damu kanta ba Sanin Datayi Auran nan Dole ne sai ta maida hankalinta kan Jarabawan da zasu yi na Shiga aji Hudu nan da wata Biyu da wani Abu,Tunda shi Uban gayyar bai Taba Nemanta ba itama Baya gabanta Daman ko Lambarsa bata dashi Sai dai in Ta Tuna yau gata Zatayi aure ba Ukti a kusa da ita sai Taji kwallah ya kamata Tana addu"an Allah ya bayyanata Suna mgana da Laila ta Chart kullum mgarta kenan An ji Labarin Zaina Tace mata Wlh Shuru ne haka zasu yi ta Tattaunawa Cikin Jimami Suna addu"an Allah ya bayyanata Lailan Ta gayamata an saka Ranar Auranta anan Bauchi In Lokaci yayi Zata zo har Gida ta kawo ma Umma kayan Biki Koda Zafeera Taji haka bata iya gayamata itama Zatayi aure ba Tunda Mijin ma bazata Dora komai akansa ba Shi yana mata kallon mai Girman kai itama tana mai kallon Haka sun Ki bama Junansu Dama ballatana Su Zauna su Fahimci juna. Samuwar Cikin Dina yasa Duka Su Umma suka koma suna Kula da ita Har wata yarinya mai aiki suka samar mata Domin ta Rika Taimakamata,Kwamishina da Hajiya Batula sun zo sun Duba Dina suka Koma Ganin Taji Sauki Sosai Cikin yayi mata kyau kamar na Arman,wanda akeTunanin nan da wata Biyu Dina Zata yayeshi Tunda yayi wayau Sosai Sai ya Wuni Shashensu Umma bai Damu da Nono ba Sai abubuwa sukayi ma Dina Sauki,Sai dai Tunanin Zain da kaunarsa suna nan acikin Ranta Zakiya kuwa bata san isalinta ba sai da taje kano Sun Shiga Shopprite ita da Hajiya Batula da su Waled Da Arman suka Hadu da wata Ashanty da sukayi karatun Prine Collage Tare Nan take ce mata bata ganta wajem Bikin Zakiya ba Dayake ita Ashanty taje suna Mgana da Zakiya ta waya Dina Taji mamaki ammh Sai ta Boye mamakinta kawai tace Lokacin bata nan ne Sai Ashanty tace haka Zakiyan ma tace nan take mata Tsegumin Zakiya tayi kuskuran auran wannan yaron ta sakar mai komai nata awannan zamanin ba"ayi ma Maza Haka Dina dai bata Tofa ba tace Allah ya kyauta Bayan Sun Dawo gida ne Hajiya batula ke Tambayanta Daman Zakiya tayi aure ne..? Dina tace bata sani ba Domin Rabonta da zakiya Tun Ranar sunan Arman Hajiya Batula tace yafi ne gwara Kowa ya kama kansa Tunda zaman ba Mutumci. Dina Tana ma Zakiya addu'an Allah yasa kada Ja"afar ya zama Jarbta Gareta kamar yadda Zain ya Zame mata Komai ya Faru Tsakaninsu bazata so wani Abu ya Faru da Zakiya ba ammh Tasan tama kanta karya Dole ne Daga ita har Zakiyan sai sun Girbi Abunda suka shuka sai dai Tana Fatan Koma menene Allah yasa ya Tsaya mata haka Tunda Ta Tuban ma Allah Ko Rashin Samun yadda take so ga Zain Allah ya barta Ta gane bata da wayau. ****** Achan Zaria kuwa Jikin Farida Gabadaya yaki Dadi Cikin Wata Hudun nan ta kwanta asibiti ba iyaka Ciwo Biyu ne ya Hade mata Lokaci Daya ga Hawan Jini ga Ciwon Zuciya. Gabadaya Ta Rame ta Fige kamar ba ita ba Tayi baki,In kaganta sai ka Tsausayamata Saboda yadda ta koma,Ga su Anun Sun yi wayau suma Sun Fara Tatata Zaina da Zulaihat su kansu basa Cikin kwanciyar hankali Domin Farida ce komai na su yau in Ta Fadi ta Mutu Sun Shiga uku sun gama Lalacewa. Yanzu Bata Cika Zuwa Ko"ina ba Saboda Jiki yaki Dadi kuma Taki Cire Damuwan Dake Damunta In Abun ya tashi Ta Dinga Aman Jini kenan Sai Lokacin Ciwon Farida Suka San Alhaji Badamasi da Idanuwansu sun kuma Shaida Bayan Abokin Shashanci Shi din mai Son Farida ne yayi Hidima da ita Suma kuma yayi dasu babu Abunda suka nema suka Rasa na Bangaran Rayuwa sai dai Zullumi na Zuciya da ganin Halin Da Farida ke Ciki. Ita Kanta Uwar mata bata da Natsuwa Domin Inta Ra sa Sholly Tayi Rashin Gibi Sosai acikin Harkallanta Dole ta Dage wajen Ganin Faridan Ta yarda Alhaji Badamasi ya Fita da ita Kasar Waje anyi mata aikin Zuciya sai dai Duk Hikimarta Farida taki yarda Ta gwammace Ta Zauna ahaka ammh Tace kafarta Bazai Taba Taka ko wata kasa ba Batare da Zaina ba dasu Anun ba Jin haka yasa Alhaji Badamasi yace sai yayi Visa har da Zaina sai su Tafi Dukkansu nan ma Tace A"a ita bata Bukatar ta Warke Tafi Bukatar Mutuwar ta Da komai ita da Rayuwarta Bata da wani Sauran amfani Ba Ahali ba ya"ya ba wani Jigo Daga Sa"adiya Da su Anun sai Zulaihat ne kadai Zasu kukan Rashinta da kewarta Sai dai Tana Fatan Kafin Karfinta ya kare Ciwon nan ya Zama ajalinta Zata Cikama Sa"adiya Alkawarinta na maidata Hannun Ahalinta kuma ayadda take jin kanta yanzu Lokaci ya kusa yi da Hakan Zai Faru. Uwar mata Ganin Farida ta Nuna Taurin kai sai ta Hadata da zaina Tace tayi ma Faridan mgana Ta bari afita da ita ayi mata aikin Zuciya ko ta samu Lafiya Tunda Saboda ita Farida tace ba inda Zataje Zaina Saboda Samun Lafiyar Farida yasa Ta amince Faridan Taje ko"ina Neman Lafiyanta kada ta Damu da ita ammh Fafur Farida taki yarda Dole Dukkansu suka Zura mata ido Allah yasa ma Tana Da mgunguna Tunda Tana Zuwa ganin Likita abun sai yake Zuwa da Sauki. Akwai Ranar da suka kwana Cikin Tashin Hankali Farida kwana Tayi Datayi kaki sai Amai Kamar bazata kwana da Rai ba da asuba Zulaihat ta kira Uwar mata Ta gayamata Hankali Tashe Ta Kira Alhaji Badamasi ta gayamai shi kuma yace Uwar mata Tayi Shatan Mota Suzo Abuja Uwar mata Karachalle ta Kira tace yaje ya Samo Mota yaje ya Dauko Farida ya kawota Kaduna jin haka yasa ba Bata Lokaci ya samu Shatar Mota yaje Gidansu Farida ya iske Zaina da Zulaihat nata kuka Yana gaya musu sakon Uwar mata Zaina tace Zata je Farida na Cikin Ciwo ta Hana tace su Zauna agida Insha Allahu Indai taji Sauki Zata Dawo Ta zama Cikin Shiri Zata maidata Gida Tana kuka suna kuka Aka Tafi da Farida Anun da Anan Harda Birgima Domin Sunan Anty Farida shine abu na Farko da bakinsu ya iya Fada Cikin Yaren su na yara suna ganin Mamarsu na kuka da Zulaihat farida kuma Za"a Tafi da ita suma suka Fara kuka Allah Sarki ko yaro yasan mai kyautatamai. Tunda aka Tafi da Farida su Zaina basu samu kwanciyar Hankali ba sai bayan kwana Biyu da Farida ta Kirasu ta gayamusu Gata acikin wani asibitin kudi dake Abuja an Dorata kan mgani Taji Sauki su kwantar da Hankalinta ta na nan Dawowa jin haka yasa sukaji Hankalinsu ya kwanta Har suka iya cin Abinci Ammh Fa Zukata sun Raunana. Dama Da karachalle ya kaita Kaduna Uwar mata da Hajiya Zabba"u suka Tafi da ita Abuja Koda sukaje Direct Wani Babban asibiti,suka Nufa da ita Inda Alhaji Badamasi ya basu address din Suna Zuwa aka karbeta Daman already yayi ma Wani Babban likita bayani wanda kuma karatunsa ya shafi masu mtsalan Zuciya shi yayi attempting dinta har ta Dawo Hayyacinta Uwar Mata da Hajiya Zabba"u suna Tare da ita Abuja Alhaji Badamasi kuma nata Wahala dasu. Chan Gidan Uwarmata kuwa Labarin Rashin Lafiyan Farida Tuni yakai musu Suby kamar ta Zuba ruwa akasa Tasha aranta kuma Tana addu'an Allah yasa Faridan ta Mutu taga karyan Tsiya su Deezee ne da Adamalli suka Tsauyamata Kalaman Suby kuma ba wanda yaji mamaki Sanin Daman Bata Taba kaunar Farida ba Kowa sai Tambayan Sa"adiya yake Domin Tunbarinsu gidan basu da labarinta yanzu hakan ma ba wani Labari akanta Tunda Farida Ta Toshe Duka Hanyar Samun Labarin Karachallre ne Daman ya Fada musu Farida ba Lafiya Tana Abuja Shima Domin yaga Ciwo ne bai Zata wasu Zasu ji Dadin haka ba Daganan ya kama bakinsa yayi shuri yana Tunanin Irinsu Suby ba imani acikin Zuciyarsu. ****** Bangaran Zakiya Amarya Kuwa Anga Ribar amarci da Aure Domin Tana Dauke da karamin Ciki Dan kimanin Wata Uku,Tuni Fi"ili da iyayi ya karu Wajen Zakiya sai dai kuma Cikin ya zo mata da Bala"in Laulayi da amai Har da kwanciya asibiti tayi,aka Kara mata Ruwa Ja"afar ke kula da ita Duk da Shima ya Fara karatunsa a ATBU Bauchi yana karantar Political Sciences,Zakiya tayi Shige da Fice ta sama mai Takardan Sakadiri Har ya samu Gurbin karatu a jami"ar kuma ita tayi Duka Kashe kashen da komai Domin Uban ya"yanta ya Samu Tsayuwa da Kafafunsa Watarana. Ganin Halin Data ke Ciki Komai sai dai ayi mata Wahalan Laulayi sai Wajen aikinta suka bata Hutu ta Dawo Gida da Safe kafin Ja"afar ya tafi makaranta shi zai Mata komai in ya Tafi kuma Wuni Zatayi kwance Tana Zubar da Miyau Sai dai in Taji Kishi ko tana Bukatar wani abu Tatashi taje ta Dauka Ja'afar Baya Dawowa sai Dare,Tun Abun baya bata mamaki har ya Fara Bata ba Ranar da Ja"far baya Cewa suna da karatu har Asabar da Lahadi sai yace mata suna da Assigment ko suna da Group Dicussiom Ga kuma yawan Cewa ance akawo kaza kudi ba Kanana ba Zakiya In Tana so Taji wani Shakku game da Ja"afar sai ya Shafe mata wannan Sakkun Abunda ya Fara bata mamaki Duk Wata Tana Raba albashinta Biyu ne Tana Turamai Rabi Sauran kuma Tayi hidimar kanta Data Gida Tunda ta Daukan ma kanta ammh Ko Rabin Wata baya kai masa sai yace sun kare ta karamai kudi karatu ya Cinye kudin da Mota,Tun bata Dora abun a Mizani har ta Fara Ga kaiwa Dare awaje sai ya Dawo yace yana Gareji yaje su gaisa da abokansa Haka zai barta ita kadai tayi ta Wahala Abunda ke kara sakawa tana kara yarda dashi Shine in ya Dawo haka Zai ta Wahala da ita yayi Girki ysyi mata wanka in Tayi amai ys Share Da wannan kyautatawar nashi Da Yadda yake Nuna mata Soyayya yasa Koma Wani abu ya Shiga Ranta Take Saurin Fiddashi. Taso ta koma Dataji Sauki Sai ya Nuna mata A"a ya kamata ta samu karin Hutu,Dole ta Biye mai Ta kara Sati Uku Cikin Hutun da suka bata kana ta Koma Bakin aikinta abokan aikinta sai Tayata Murna suke ita kuma Tana jin Dadi acikin Ranta Tana ta Tunanin Daman Haka Allah yake lamarinsa Tagama Cin Duniyarta da Tsinke Gashi yau tayi Auranta Da wanda take so kuma Take Muradi har da Rabon Ciki ita aganinta wata mai wayau ce da Dubara bata Taba Tunanin Talala Allah yayi mata ba. Labarin Samuwar Cikinta Har kano Mallam Nuhu Dayaji ya kirata awaya yayi mata Fatan Alheri Duk da yaji Hankalinsa ya kwanta ammh Haka kurum acikin Zuciyarsa yake jin bai yarda da Ja"afar ba Tunda Daga Binciken dayasa akayi masa in yayi mgana Lubabatu ta kwabeshi Da Fadin yayi Shiru kawai yayi mata Fatan Alheri Dole ya kama bakinsa yayi Shuru acikin Zuciyarsa kuma Yana Taya Zakiya addu"an Allah yasa Alheri ne da Sanadin Shiryuwanta yasa ya Kulla wannan Auran.. ****** Farida ta Dauki Tsawon Wata Daya agarin Abuja kafin Taji Sauki Kamar ba ita ba ta Fara maida Jikinta Uwar mata Sati Daya Tayi a Abuja ta Dawo a asibitin akwai Nos masu kula da Mara Lafiya Kudi Alhaji Badamasi ya saki suka Dinga kula da Farida har tasami Sauki an Dora ta again kan mgunguna ammh Likitan yaja mata kunni Zuciyarta Tana ta kumbura Kada ta kai karshen da sai an yi mata aiki Da kuma yawan Saka Damuwa Dake kawo mata Hawan Jininta Duk tace Zata Kiyaye kana da gargadin Cin Abinci mai Gina Jiki da samun Hutu Sosai. Alhaji Badamasi da kansa ya Dawo da ita kayan Dubiya irin na masu Ciwonta iri iri katan katan din Madara maltina da kayan karin Jini su Zaina sunyi murna su Anun da suka Fara dan Takawa sai Murna suke Anty Farida ta Dawo Bakin Zaina da Farida yaki Rufuwa ganin Farida Ta Dawo Cikin Koshin Lafiya Duk da ko da take chan suna mgana ta Waya Alhaji badamasi bai Dade ba ya Tafi Bayan yaJadda musu Farida ta Rika samun Barci da Hutu. Jin Haka yasa Bayan Tayi wanka Taci Abinci tasha magungunarta Su Zulaihat suka Janye su Anun ganin Zasu Dameta suka barta Tayi barci Sosai sai bayan Mangariba Tatashi Daman Tun bayan Rashin Lafiyan Farida suka Daina Zuwa makaranta suka koma sunayi agida. Zaina ce ke karama Zaina karatu Dukkansu suna Sanye da Hijabai ne bayan sun idar da Sallah,Su Anun kuma suna Gefe Anan Tana Hawa kan kekensu na Koyon Zama ne Anun kuma tana Wasa da Wani Abun wasa mai kara Zaina sai Dakamata tsawa take tana Kiran Anun ne Datadaina Kada abun ya Tashi Farida Daga Barci. Suna Cikin Hakane sai ga Faridan ta Fito Daga Bedroom din Tana Mirmishi tace"Barta ta Tasheni..Daman ya kamata na Tashi nayi sallah.."suna Jin Muryanta Daga Anun din har Anan dukkansu suka yarda Abun Wasansu suka Nufeta suka Rumgume ta kamasu Tana Dariya Dayake Tafiyarsu Ta Nuna Sosai Zulaihat ce ta Dago Tana Fadin"Anun Anam kada ku kada Anty baku ganin Bata da lafiya ne.." Farida Ta Daukesu Dukkansu Tunda Daya bazata yarda ta Dauki Daya ta barta ba,Dole ta Hada Ta Daukesu Tana Nishi ta is kan Kujera Ta zauna Zaina Tace"Allah ki daina Biye musu kina Daukansu Kada su kada ke Baki da lafiya.." Farida na Dariya Tace"Ku kyalesu mana Sa"adiya da Zulaihat zan saka kafar wando Daku kuna Takurama ya"yana nan da Wata Biyu fa ba ganina Zasu yi ba sai dai suga su Umma Dasu Nene.." Gabadaya Daga Zaina har Zulaihat ido suka sakamata Cikin Mamaki Zaina tace"Umma da Nene kuma..? Farida tace"kwarai kuwa..Domin Insha Allahu Zamu Fara Shirin Tafiya Bauchi nan da wata Biyu da yardan Allah Zan je na maidake ga Marikanki kamar yadda nayi Miki Alkawari Sa"adiya Tukafin Wannan Ciwon yayi ajalina in barki Cikin Rayuwar kila wakala.."Zaina kai ta Sunkuyar sai Hawaye Zulaihat ma Jikinta Duk sai yayi Sanyi ita kanta Farida Dauriya take Mirmishin karfin Hali Tayi Tana Fadin"Me ye kuma na kuka..? Keda Zaki Farinciki..Zaki koma ma Firstlove dasu Umma Da kyautarsu Anun..Kinga Zulaihat Daukan munsu na samu nayi Sallah.." Zulaihat ta Mike ta Daukesu ita kuma Farida ta Mike Zuwa Ciki Domin Tayi Sallah Tana Jin Gwara ta Sauke wannan Nauyin ta maida Sa"adiya Bauchi In ta Mutu bayan Haka bata bar Baya da Kura ba. Ita kuma Zaina kitchen ta Shige Tana kuka haka kurum Take jin Wani kewa da wani abu Data batasan Ko miyeshi ba na kewar Farida da Tunanin me Zataje Bauchi Da Tarar..? Firstlove ya auri Dina..? Ta Haihu..? Me ya Faru bayan Tatafi..? Duka wadanan Amasoshin Suna sakata Fargaba da Faduwar gaba. *Janafty...* 8/7/21, 10:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣5️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *BAUCHI..* "Achan Bauchi kuwa an Tashi Da Hatsaniyar Biki aranar Asabar din Duka Gidajen Biyu suna Cike da jama"a yan"uwa da abokan arzuka Gidan Abba nan Amarya da Tawagarta suke Taronsu a Shashen Dina su Umma kuma suna Shashensu suna nasu Taron tare dasu Mama Safiya da wasu Daga cikin Danginta da Su Mom Iklima. Su Inna Rukayyah kuwa da Inna Hannatu Harda Goggo Halima su manya ne Suna Gidan Alhaji Tsoho suna nasu Sha"anin Tare da yan katsina Sauran Danginsu Hajiya mama kowa ka gani Fuska Cike da Annuri da Farinciki wanda Rabonsu da irin Wannan Farinciki sun Ma Manta sai gsshi da suka Fauwala ma Allah komai suka Dauki Kaddaransu komai yazo ya wuce kamar bai Faru ba. Haddir Ango baya Tare da kowani Aboki sai Sadiq Babba Duk da yana kaninsa Shi ya Rufamai Baya a Hotel din da Sauran Abokan karatunsa suka kwana Shida Sadiq achan kuma sukayi wankansu suka Shirya kana Suka zo nan Gidan Alhaji Tsoho da Safe Suka bar Sauran abokan achan sai sun gama Shiryawa, Haddir ya Sanya Farar Shadda Dinkin Zamani Harda Babban Riga sai yayi amfani da Hular Dara baka da Bakin agogo da Takalmi Rufaffe baki Shima Sadiq sai yayi mai kara shima yayi irin Shigarsa yau ya Chanji Matsayin Zain wanda Da yana nan Tare zasu Zuba wannan Angon Suna Tafe suna kwalisa haka Su Hajiya Mama suka Dinga Fadi bayan su Haddir din sun Fito su Abba kuma Tun Safe suka Fita haraban Gidan ana gyara Inda Za"a Baza Dardumai Saboda Mutane masu Zuwa Daurin Aure Tunda bakin Nesa sun Taso. Bangaran Amarya Zafeera kuwa sai wanda ya gani anyi mata Dilkan Amare Tayi kyau kamar ba ita ba Tun Safe Tayi wanka Ta Sanya Wani Leshi Cikin na akwatinta ne Wanda Mama ta bata Shi Ita ko kayan ma bata gani ba Suna Gidan Alhaji Tsoho Daman bayan an gama Daura auran Bikin Zai koma Chan Tunda chan Zasu Tafi Duka Hardasu Umma Dagachan ne Za"a Dauketa Zuwa Gidan Auranta. Tun Safe Mai makeup din da Zainab ta Dauko Tazo ta Fara ma Amarya kwalliya su kadai ne ashashen na Dina ita ta Fita Shashensu Umma Arman Daman Wajen Nene ya kwana Zareena Tayi musu wanka Ta Shiryasu Sunci Fararan Shadda Suma Harda Arman wanda sadiq Babba ya Dinka musu in kaga Arman sai kaji kamar ka Saceshi ka Gudu Saboda kyansa Umma da Nene sukace Wlh kamar Zain yana karami ne Sadiq karami da Faruq suka Daukesu Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Wajen Daurin Aure Dashi Arman din da Junior sai Jalal din Abinci Daman Duka aikatau suka bada Tun Safe an kawo komai Cikin Manyan Kololi Drinks kuma Tun Shekaran Jiya aka Sauke Tare da Ruwan Gora. Lokacin da aka Gama ma Amarya Makeup sai waje ya Dau Sowa da ihun ganin yadda Tasha kyau sai kiga kaga Flash na Tashi Zafeera Duk Sonta Data Daure sai da Hawayenta Data ke Rikewa suka zobamata In Ta kalli Hagu da Damanta bata ga Ukti ba sai taji wani Rauni ya kamata Allah Sarki yau Ranace mai matukar Farinciki gareta Wanda Ta Tabbata da Ukti na nan Bata da Wata Damuwa sai gashi yau bata agefenta Fada su Shema suka Fara mata ganin Zata Bata Sauran kwalliyata Dole ta Tsaida kukanta Daganan su Shema suka Fara Wanka Da Shiryawa Tunda 2pm Mama Safiya Tace Zasu Tafi Chan Gidan Alhaji Tsoho Din. Dina na Shashensu Umma sai ga Hajiya Batula dasu Waleeda Farinciki ya Cikata tatashi ta Tarbota Tana Tambayan Daddy Hajiya Batula tace Sun Saukesa shi da Waleed Gidan Alhaji Tsoho Su Umma suka karbi Hajiya Batula Hannu Biyu Tunda yanzu an zama Daya Tuni aka Cika Gabanta da abinci da abubuwan sha sai Kallon Dina Take yadda ta saki jiki ana ta Hidima da ita Umma ta Kirata Nene ta Kirata abun sai yayi ma Hajiya Batula Dadi kamar tayi kwallah Tana kara Godiya ga Allah Daya Hadasu da mutanen kwarau irin Iyalan Dr.Saulawa da Wasu ahalin ne Tabbas Dina da yanzu Tana Cikin Wata Rayuwa ammh kalli yadda Tayi Kiba Harda Rabon wani Cikin Bayan Dina ta gama Jera ma Hajiya Batula abinci da kayan Ruwa ta koma ta Zauna suna kara gaisuwa Hajiya Batula Tana Tambayan Arman Dina tace Su Faruq sun Tafi Dashi Wajen Daurin Aure Hajiya Batula tace Zasu hadu da kwamishina achan Daman Koda yaushe Cikin Zencen Arman din yake Sun dan Taba Hira da Dina kan mganar chan Suda ne domin Hajiya Maimuna Ta Kirasu Ta gayamasu kakar Dina bata da lafiya Hajiya Samina Har an kwantar da ita asibiti Shine Hajiya Batulan ke gayamata Taji kwamishina na Zencen zasu je Dina ta marairace wai Zataje Hajiya Batula tace Mijinta Baya nan Ta Bari in ya Dawo ya barta sai Tatafi Dole Dina tayi Shuru Bata Jima ba Tace bari taje Tayi wanka ganin har su Umma sunyi wanka Sun Shirya. Tana Komawa Shashenta Taga Amarya da kawayenta sun Cakare basu yi anko ba aammh Kowacce ta saka kayan Nuna Sa"a Ana ta yi musu makeup Ganinta yasa Shema tace Matar ya Dakta kije kiyi wanka Kizo ayi miki kwalliya Dariya ta kwace mata Domin sunan Da Shema ta Kirata ya sanyayamata Zuciya sosai Ta kada kai tace bari taje ta Shirya Kada ta watsa mata a kasa a ido Ta Wuce Ciki Tana Koda kyan da Zafeera Tayi Duk Da taga Fuskarta ba Walwala. Wanka Tayi ta Shirya Cikin Wani Tsadadden Material Wanda yaji stone work anyi mata Dinki Buba Tayi kyau ta Gyara Gashinta ta Fito Falo ta Iske har Hamdiya Dake da Ciki Tayi kwalliya itama suka Tarota ta Zauna akayi Mata Duk da bamai yawa bane ammh Tayi kyau Saboda Daman ita mai kyau ne bayan anyi mata Dauri Ta koma Daki Tana kallon kanta a madubi ita kanta ta Shaida Tayi kyau Tun Bayan Samuwar Cikin Arman Bata kara Kwalliyan Datayi kyau kamar ta yau ba wani Dan kunne Zinarenta ta saka Hannu da Wuya Wanda Daddy ne ya Siyamatashi ta Dauko Sabon Mayafi da wani Takalminta mai Tudu Tana Fitowa su Zainab suka Sakamata Ihu suna Daukanta Hoto ga Dan Cikinta Daya Bayyana Shema na Fadin kyanshi Yaya Dakta yaga wannan wanka Ita dai sai Mirmishi Take acikin Ranta kuma Tasan ko yana garin bazai Damu ba da ita ba ballatana Har ya yaba mata Ko bakomai Taji Dadin Rayuwarta yanzu Tunda Ta samu kwanciyaar Hankali Zain kuwa Daman Ta Gama sanin ya Riga yayi mata Nisa Har Abada... Amarya Zafeera Dake gefe Ta cika Kamar Zata Fashe gabadaya Haushin yadda suka Rufu kan Dina suna Ta yabon kyanta ne ya kamata Tana Tunanin Wlh ko ba Ukti a wajen ne akallah a Nuna Kishinta karamin Tsaki Taja tatashi Fuu Ta Fice sai kowa ya Bita da kallo Dina kuwa ta san Dalilin haka suma su Shema sun Fahimta Basu ce komai ba itama Dinan Bata Nuna ma ta saki Mirmishin Dole tabi bayan Zafeera Zuwa Shashensu Umma. Tana Shiga ta iske Zafeera na Rumgume da Umma tana kuka Umman ma kukan Take Su Mama Safiya na basu baki Daga yanayin mganar ta Fahimci kan Zaina suke wannan kukan Sai Taji Jikinta ya karayin Sanyi kawai sai ta Juya ta Koma Mom iklima Ta ganta sanda ta Shigo kuma ta koma sai ita kanta Dinar Taji ta bata Tsausayi ba Laifinta bane haka Allah ya kaddara. Shashenta ta koma ta Shige Daki Itama Tana kukan makomar Rayuwarta Wlh yanzu addu"a take Allah ya bayyana Zaina Kila Ko Darajanta ta samu wani Kyakyawan kallo Daga zain Yanzu tafi Bukatar yaga Zainarsa Domin ta kara yarda da itace Rayuwarsa,Kukanta ya Tsaya ne da Zainab ta Shigo Tana RokontaTazo Ta Tayasu Bama kaawayensu abinci nan da nan ta saka Tissue ta Share Hawayenta ta Fito kamar ba ita ba ta iske Zareena tazo anyi mata kwalliya Tana ta Duba agogo wai an kusa Daura aure Jawad zai zo su Asma"u natayi mata Tsiya suna Dariya. Nan suka Hadu da Dina da Shema da Zainab sukayi ta Bana Mutane abinci har kowa ya samu kana suka zauna suma suka ci suna Cikin cin Abincin ne Faruq ya kira Wayar Zafeera Dake hannun Shema tana Dauka sukaji ana Daura auranta da Haddir Abba Shine Waliyin Ango Haddir sai Daddyn Abuja Yazama Uban Amarya suka Nema suku ma suka basu Nan da nan Shedu suka Shaida Daurin Auran Dr.Haddir Aliyu Abubakar Saulawa Tare da Amaryansa Zafeera Usman Abubakar Saulawa kan Sadaki Mafi Daraja 200k sai sukaji waje ya Dau Hayaniya da Hamdala suma Daganan sai suka Dauki Ihu Shema ta Mike tana ,Juyi Tana Guda ta kwasa Zuwa Shashensu Umma Zafeera na Dakin Umma tana Zuwa ta Fada Jikinta Ta Rumgumeta Tana Fadin"Finally Mrs Haddir Aliyu Abubakar Saulawa...Aure ya Dauru Allah ya baku Zaman Lafiya.." Kawai sai Zafeera ta saka kuka Su Mom Iklima me zasu yi in ba Dariya Ba Mama Safiya ne ke kare mata Tana Share mata Hawaye Tana Fadin Amarya bata kuka Ranar Bikinta. Achan Farfajiyan Gidan Alhaji Tsoho Kuwa ya Cika da baki na Nesa Dana kusa Hatta da Mijin Inna Hannatu da na Inna Rukayyah Duk sunzo Tare da manyan Ya'yanasu Abokam aikin Haddir ma su Dr.Imran Dr.Petter,Dr Aliyu da Sauransu Da Sauran Abokan karatunsa Suna ta bashi Hannu Tare da Tayashi Murna Bakinsa a Washe Bazaka Taba gane wani yanayi yake Ciki ba su Faruq ne suka Mike suka Fara Raban Abinci Zasu yi Repction Su Arman na kan Darduman da Alhaji Tsoho ke kai da ya"yansa Tare da irinsu kwamishina Haddir na Gaisawa da baki yaji karar wayarsa yana Dubawa yaga zain ne yaTuromai Sako da Sauri ya Duba sai yaga. *Alhamdulillah..Mrs Zafeera Usman Abubakar Saulawa..Ina nan ina Kintatan Lokaci by Now nasan ka tashi Daga gwauro..Allahu ya baku Zaman Lafiya ina gaida kowa da kowa ka Fada musu I Miss my Home.* Kayattacen Mirmishi Haddir ya saki kafin ya maida wayarsa aljihu Hakika yafi kowa kewar Zain musamman wannan Rana Da Ya kasance bashi a kusa Dashi,Ya cigaba da karban gaisuwan baki Cikin Fara"a wasu Tafiya sukayi basu Tsaya ba wasu kuma sun Tsaya har akayi Reception kana suka Watse Sannu Sannu baki suks Fara Tafiya Haraban Gidan ya Rage Mutane sai irin su Abba da su Kwamishina suna kan Katuwar Darduman da Alhaji Tsoho ke Zaune shi da ya"yansa da Jikokinsa da Tattaba kunnuwansa su Arman dasu Jalal. Chan Gidan Abba kuwa sai Shagali akeyi su Zainab suka kunna Mp a Shashen Dina suna ta Chasewa abunsu Ransu Fes,Zafeera kuwa na Shashensu Umma kwata kwata Ranta babu Dadi Ga Rashin zaina ga Damuwar an kakaba mata auran Wanda Bata so kuma babu Wani Jituwa Tsakaninsu. Anayin Sallar azahar Aka Fara Shirin Tafiya gidan Alhaji Tsoho,Mama Safiya ta Kira Haddir tace suna Bukatar Motoci Sai shi kuma yayi ma Sadiq mgana da Sauran abokansa Motarsa kuma Faruq ya bama key din Sadiq yana da Tashi Motar Abba ya Siyamai bayan Dawowarsa su suka je Gidan Abba kwaso amare dasu Umma sai da suka Jirasu suka Gama Hada kaya Tawagan Amarya Da Zafeera Na kawayenta Dasu Zainab suka Fara yin gaba sai da suka kaisu Kana suka Dawo suka kwashi su Umma da Amarya Gidan Babu Kowa Sai Megadi hatta da Dina Motar da Nene ke Ciki Ta Shiga Ita Da Hajiya Batula da Mom iklima,Sadiq babba ke Tukasu sai gidan Alhaji Tsoho Inda suka samu Tarban su Inna Rukayyah Tunda Abun Duka Gida ne Tuwona maina Sai Tarban Dangin Mama Safiya. Zafeera Dakin Hajiya Mama aka kaita,Ta Rumgumeta Tana mata Guda Alhaji Tsoho suna Haraban Gidan ammh yace zasu shigo Ciki Saboda yima Amarya Nasihu Tunda da Wuri yace za'a mikata Gidan Mijinta Haddir kuma ya Tafi Masaukin Bakin da Sauran abokan sa suka Sauka. **** Koda suka Shigo Garin Bauchi Anun da Anan sun Dade da yin Barci Don ma sun Tsaya Bisa Hanya sunyi Sallar azahar sukaci Abinci Saboda yaran kana Suka Dauki Hanya Tunda suka Shigo Cikin garin Bauchi Zaina Taji gabadaya Ta rasa natsuwarta Tana Tunanin kamar Jiya ne ta bar Gida gashi yau Zata koma me zatace ma su Umma..? Da wani ido Zata kalli Firstlove bayan ta bashi kunya..?Me zata Tarar...? Yaya Labarin Dina..? In ta tuna Hakan sai taji Bata da wani karfin Gwiwa ta Cikin nikabinta Take Share Hawaye Bataji Ba ashe Farida nata mgana sai da Zulaihat ta Tabata kana ta Waigo Tana kallonta. Farida Dake kujeran gaba tace"Gamu agarin Bauchi Sa"adiya Wata anguwa ne Gidan Abba yake.?."Cikin Sanyi Jiki Dana Zuciya tace"GRA..! Direba najin haka ya kada kai Daman Daga ganinsa ya saba Kila Shigowa garin Cikin Lokaci kadan sai gasu Cikin Gra Zaina sai Bin Ko"ina da kallo take lalle ko yau kabar waje gobe ka Dawo sai kaga ya Sauya maka Taga abubuwa sosai wadanda suka Chanzamata acikin Idanuwanta ji Tayi Direban na Fadin gasu Cikin GRA ina ne gidan..? Da kwatace da komai Sai gasu Kofar Tamgameman Get din gidan Datayi Rayuwa aciki Cikin Sanyin Murya Farida ta Kalleta Tana Fadin"Nan ne gidan Sa"adiya..? Zaina na kura ma Gidan Ido Tana Tuna wasu abubuwa ta gyada kai Tana Fadin"Eh nan ne Anty Farida.."Farida bata ce komai ba Sai da ta Bude Murfin Mota ta Fita kana ta leko Tana Fadin"Ku Zauna amota bari na yi mgana da Megadi..Mai mota don Allah bari nazo..'Da Sauri yace bakomai Zaina kuma kai ta kada Zulaihat kuma banda Kallon Gidan babu abubda take aranta Tana Tunanin Daman wannan Daulan Zaina ta baro ta Fada Wata Rayuwa..? Suna kallo Farida ta Buga Get din Audu megadi ya leko Zaina na kallonsa Shine dai Audi Megadi Cikin kallon Rashin Sani yake Bin Farida dashi sai ta gaisheshi ya amsa Yana kallon Motar dasu Zaina ke Cikin Cikin Alamun kamar bai yarda da ita ba yace"Baiwar Allah Lafiya..? Ko bikin gidan kika zo ne..? Cikin mamaki Farida tace"Lafiya lau Baba...Eh gida nan nazo Daman yau ana Biki ne..? Da Sauri yace"Eh Diyar Megidan ke Aure Zafeera basu ma Dade da Tafiya Chan Babban Gidan nasu ba Gidan Alhaji Tsoho ba Daga Chan za"a kai amarya Dayake Duk na Gida ta Aura Hadiru ne ta aura.."Farida ta Gyada kai Cikin mamaki kafin tace"Shikenan nagode..Bari mu karisa Chan gidan.."Da Sauri yace"Kinsan gidan ne..?.Farida tace"Eh Baba nagode.."Da haka ta Dawo ta Bude Mota ta Shiga Tana Fadin"Ba kowa agidan wai suna Gidan Alhaji Tsoho..". Zaina ta Zaro Ido Cikin Faduwar gaba Tana Fadin"Na Shiga uku ni halima meya Faru haka..? farida tace"yace Biki akeyi yau..Zafeera ce ke aure wai ko habiru take aure na Manta.."Wani irin Zabura Zaina Tayi Tana Fadin"Yau Ukti take aure..? Wa kikace Ta aura..? Cikin Mamaki Farida tace"Wani suna Ya Fada Habiru ko wa..? Na manta Wlh yace dai suna Chan Dukkansu mu karisa Chan Tunda kinsan Gidan.."Zaina da Bakinta yaki Rufuwa sai kuka Cikin kukan take Fadin"Allah na gode maka Da na Dawo akan gaba..Ukti yau tana aure...Kuma Tana auran ya Haddir ayau,lalle na Cika mai Sa"a Ko bakomai zan wanke Laifina na yau kadai Mu kasance Tare da Ukti.."Daga Farida Har Zulaihat ba wanda yayi mata mgana Farida tace Direba yaja su Tafi Zaina ta Dinga Nuna Hanya Tafiya kadan sai gasu abakin get din gidan Alhaji Tsoho koda yanayin Wajen zaka Fahimcia acikin Gidan ana wani Taro. Farida ta Waiga Tana kallon Zaina Tana Fadin"ki Zauna amota Zamu shiga Tare da Zulaihat da su Anun,In Lokacin Shigarki Tayi zan Kira wayarki..Direba ga kudin Motarka In Na kirata sai ka Sauke mana kayanmu.."Tafada tana Mikamai yan Dubu Dubu 20k ya karba yana ta Godiya da Toh Zaina ta ce Daman gabanta sai fadi yake Tana kallo zulaihat ta Dauki Anun ita kuma Farida ta Dauki Anan Duk da suna Barci ammh jin an Daukesu suka Farka suna kallon Sabon Waje Zaina na gani suka shiga Gidan Tunda yau get yana Bude ne saboda Sha"ani. Tun da suka Shiga gidan Zulaihat ta saki baki Tana kallon Tsaruwan Gidan ita kanta Faridan Sai da ta Jinjina Ganin basu gane Kofar da Sadasu da ainihin Babban Gidan bane yasa suka Tambayi su Jalal Dake Wasa aharaban Gidan Tunda Lokacin su Abba sun Shiga Ciki Saudart Dake da wayau ita ta Tsaya Ta kurama Anun Dake Hannun Zulaihat da kallo ganin Kamar Arman karami Su kansu sunga yanayin kallo sai dai Tun kafin suyi mgana sai ga Arman ya Rugo da gudu suna wasa da Waleed Daga Zulaihat har Farida baki suka saki suna kallon Arman suna kuma kara kallon su Anun Wlh in ba Domin yanzu suka Shigo garin ba sai suce su Anun yan Uku ne wani ne ya sace Arman. Boye mamakinsu sukayi da Saudart ta Nuna musu Kofar da Zata sadasu da Falon Hajiya Mama Farida da Zulaihat suka wuce suna waigan Arman suma ma Haka su Saudart ma Haka Balle su Anun din da sukayi wani iri suna Bin Kowa da kallo. Falon ya Cike da yan"uwa da abokan Arzuka Amarya Zafeera Tana Dakin Alhaji Tsoho dasu Abba sun Taru suna yi mata Nasiha su Umma ne ke Falo ana Hira Dina na gefe suna Hira sama sama da Hajiya Batula kwamishina bai Dade da Tafiya ba su Farida sukayi sallama acikin Falon Gabadaya su Umma suka waiga suna amsawa Farida ce kan gaba Zulaihat na bayanta. Umma,Da Nene da su Mama Safiya Hankalinsu ya koma kan su Farida Hajiya Mama Dake kokarin Fitowa Daga Dakin Alhaji Tsoho itama ta amsa Sallamar sai dai me tunda suka Shigo Kowa ke kallonsu da Tsabar mamaki da al"ajabi ba kuma komai yasa Kowa ya saki baki yana kallonsu Farida ba sai Anun da Anan Dake Hannunsu wadanda ganin Idanuwan Mutane duk suka Rikesu suna kauda kai. Kowa afalon yarasa bakin mgana sai mamaki da al"ajabi Umma ta Mike Tsaye tana kara Kurama Anun ido wacce Harta Bakinta irin na Zain ne hakama Nene ke kallomsu Hajiya Mama da Bata iya gani ta kyale ta Shiga Tafa Hannu Tana Fadin"Wa nake gani yaran suna kama dashi..? Ku Dubamin Jama'a yara kamar Yaron nan Arman Zainullahi Tsab Fuskarsu fa.."Kalaman Hajiya Mama ya Dawo da Duka Hankalin Mutane Falo harda kuwa Na Dina da Hajiya Batula suma sai suka Fara Ankarewa da Abunda ke Faruwa. Kowa ba bakin Mgana Mama Safiya ce ta isa kusa da Farida ta Na kara kallon Anan kafin ta kalli Farida Tana Fadin"Ikon Allah..Wlh Hajiya Mama yaranan Duk yadda akayi Jininmu ne bayin Allah Daga ina kuke dauke da yara masu kama da ahalin mu.."Zuwa Lokacin Har su Zainab Dake Dakin sun Fito Falo ganin Falon yayi Shuru anata mgana. Farida ta Murmusa Tana Fadin"Wacece Umma..!? Ina Nene..? Ina Goggo Halima..? Ina Alhaji Tsoho..? Ina Abba..? Ina Firstlove..? Duka Sunanayen Data Lissafo bai Razasu ba sai Sunan karshe Wato Firstlove gabadaya sai suka Zuba Mata ido kafin kace me an Zagaye su Farida Bakin Umma na Rawa ta Rike ma Farida Hannu Tana Fadin'"A..i..na kika san wannan sunan..? Ko kin Taba Haduwa da Halimana ne..? Tafada Hawaye na kawo mata sai Yanzu ta kara kallonsu Anun Taga Kamanin Halima Atare da yaran Farida tayi Mirmishi Tana kallon Umma kafin tace"Ko ban sani ba kece Umma ko..? Da Sauri Umma ta Daga mata kai Anan ta Mikamata Tana Fadin"Karbi Jikarki...Takwaranki ce sunanta Fatima Zainullahi Usman Saulawa muna Kiranta Anan..." Gabadaya sai Falon ya Dau Salati da Sallami ana maimaita sunan da Farida ta Kira jiki na Rawa Umma ta karbi Anan wacce ta Bare baki Zatayi kuka Farida ta kalleta Tana Fadin"Shii..Kada kiyi kuka...Nan gidanku ne Anan yan"uwan Ummanku ne.."Tafada Tana kara kallon Kowa Dake Falon Zuwa Lokacin har su Abba sun Bayyana Domin Hajiya Mama ta Ruga ta sanar dasu Abunda ke Faruwa Zafeera har tana Tuntube Dataji Labarin Wata Tazo da yara masu kama da Arman kamar kuma Tana san Wani abu game da Zaina,Goggo Halima ma Tuni ta Fito Tama kasa mgana sai kuka acikin Ranta kuma Tana Fatan Allah yasa Halima ta bayyana ko labarinta Kawai sai ganinta akayi gaban Farida Cikin Hawaye Zafeera ke Fadin"Ina Uktita..? Don Allah Tana ina..? Kada ki sanar dani Ukti ta bata Raye don Allah..? Zulaihat ce wannan karan ta Mikama Zafeera Anun Tana Fadin"Ga yar"uwar Haihuwar Anan..Sunanta Maryam muna Kiranta Anun.."Da wani Sauri Zafeera ta karbi Anun Tana kallinta Cikin kuka Take Fadin"Wlh wadanan ya"yan Ukti ne da Yaya Dakta ne..Ko Rantsuwa nayi ba zanyi kaffara ba Cikin Data Fita Dashi ne.."Take Fada Tana kuka Tana Rumgume Anun Zuwa Lokacin Umma ma Ta Fara kuka su Abba kuwa mamaki ya hanasu mgana Alhaji Tsoho na gefe yana Hamdala acikin Ransa Umma ta Durkusa agaban Farida Tana rike da Anan take Fadin"Don Allah bayin Allah kuyi gaggawan gayamana ina Halima take..? Kada kucemin ta Rasu wajen Haihuwan yaran nan Wlh Zukata Dadama zasu Raunana Ba kuma mu da karfin Gwiwan gayama Zain cewa Zainarsa Bata da Rai.." Take Fada Tana kuka kowa kuma sai Jikinsa yayi sanyi Dina Dake gefe sai Zufa take tana Zare ido Farida Batace komai ba illah Waya Data Daga ta kira Layin Zulaihat Dake hannun Zaina Cikin Rawan baki Zaina ta Daga wayar Farida tace"Ki shigo Ciki Sa"adiya.." Kowa sai ya koma kuma kallon Farida da kuma Jin sunan Data ambata,Sai kuka ya Tsaya Cak kowa ya Zubama Kofa Ido Cikin Fargaba da Damuwa Zulaihat kuwa Tana Gefe kawai tana Hawayen Taya Sa"adiya Murna ita yar gatace gaba da baya. Zaina Da Direba ya Sauke bayan ya Sauke Duka kayansu akwatinsu ne Daman ta Rika Jansu Tana Shiga dasu Haraban Gidan ganin bazata iya Dauka ba yasa ta barsu nan Cikin Faduwar gaba da wani Fargaba ta Nufi Falon Hajiya mama Lokaci Daya kuma Tana Tuna Ranar da Ta bar Gidan a irin wannan Lokacin Da Siririyar sallamarta ta Shigo Sanye da nikabinta Turus Tayi ganin yadda Falon ya Cika Abba Umma,Nene Alhaji Tsoho,Goggo Halima,Hajiya Mama,Mama Safiya,mom iklima,Baban kaduna,Dadyn Abuja zainab,Shema,Zafeera,Zareena Da kowa Dake Falon ya Sakarmata ido Sai taji kafafuwanta sun Fara rawa ta kasa ma Daga kwayar idanuwanta Saboda Rauni da wani kunyar da suka kamata. Umma Ta Mike Dauke da Anan bakinta na Rawa tace"Ina ji ajikina yata ce..Halima ce....Don Allah ki Bude Fuskarki Ko hankula Zasu kwanta.."Zaina da kuka yaci karfinta Kafafunta na rawa sai da ta Duke kana ta Saka Hannu ta Cire Nikabin Fuskarta ta Bayyana Gabadaya sai Falon ya Kaure da Kabbara. "Allahu Akbar..Itace Wlh..Zaina...Halima..Sa"adiyace.."Hayaniya ta Cika Falon Atare Umma,Nene,zainab da Zafeera da Zareena suka isa ga Zaina sai Tajii Duka sun Duka Sun Rumgumeta Cikin kuka Ita dasu Anun din gabadaya suna Fadin"Alhamdulillah..Allah ya karbi addu"an mu ya Dawo mana da Halima Lafiya.." Suke Fada suna kuka Suna Dariya Zaina ma kukan Take ta Rumgumesu Tana Fadin"Ku yafe..Min...Ku yafemin.."Kaawai take iya Fada tana wani kuka Dina Dake gefe ta Share kwallah Tana Hamdala Batayi Bakinciki da bayyanar Zaina ba Hakama Falon kowa ke Hamdala Goggo Halima da Hajiya mama sai da suka kai goshinsu kasa Saboda Godiya ga Allah Shema kuwa na Gefe Tuni har ta Kira Haddir awaya ta gayamai ai yadai jita ne bai yarda ba shima ya Kamo Hanya yana Fatan Allah yasa haka ne Tare yake dasu Sadiq dasu Faruq. Zulaihat da Farida ma an manta Dasu suna Gefe suna kara Jinjina ma Tsantsan kauna da kuma Soyayyar da wannan ahali kema Sa"adiya ya wuce yadda ta basu labari. *Ina Bukatar addu"anku kan Allah yayi min Zabin Alheri acikin Rayuwata In Abunda nake so acikin Zuciyata Alherina ne Allah ya Rikemin shi Ya Tabbatarmin da alheri ya Kauda Sharrin Dake ciki in kuma babu Alheri Allah ya Musanyamun da Abunda Zai zamemin alheri Duniya da Lahira Ameen Nagode..* *Janafty..* 8/8/21, 1:27 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣6️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Daga Umma Har Zafeera Haka suka Rirrike Zaina suka Taso da ita Zuwa Tsakiyar Falon kamar in suka Saketa Zata sake Guduwa ne Anun kuma da Anan Sun koma Hannun Nene da Zareeba sai kallon Kowa suke ganin sun zo Bakon wajen da kuma Mutanen da basu Taba sani ba. Gaban Hajiya Mama da Goggo Halima su Umma suka Dire Zaina kowanne Fuskarsa Tayi Jage Jage da kukan Farinciki mara Misaltuwa Zaina ta Dago Tana kallon su Goggo Halima Tana Zubar Hawaye ta Rike Hannayensu Duka atare ganin Suna kuka Tace Cikin Taushin Murya.."Zaku iya yafemin..? Me nayi kenan..? na saka ku kuka fa.? Take Fada Tana jin wani irin Tahowar kwallah da kuka alokaci daya atare suka Rumgumeta Cikin Kwallar Farinciki Hajiya Mama ke fadin"Baki mana Laifin Komai ba Halima wannan kukan da kika ga munayi na Farincikin ganinki ne kin Dawo Cikin Koshin Lafiya Tare da Rabon da kika Fita Dashi acikin ki kin Dawo mana Dasu Suna kallonmu muna kallonsu wannan kadai ya Ishemu kukan Farinciki Halima.." Zaina sai ta kara Volume din kukanta Goggo Halima ta Dago Tana Share mata Hawaye Tana Fadin"Bar kuka Halima..Allah ya Karbi addu"an mu..Allah mungode maka.."Take Fada Tana Share mata kwallah Zaina ta Kwantar da kanta kan Hannun Goggo Halima Tana Fadin"Goggo Ina su ya isuhu da Sauran Mutanan Gada..?!Nasan suma na sakasu kuka ko..? Goggo Halima tace"Kada ki Damu yanzu zaki wanke musu Zuciya da Farincikin ganinki kin Daawo Cikin Koshin Lafiya sai dai ina Miki Fatan Allah yasa Kada Hakkin wannan ahalin ya kamaki Halima Sun Shiga Tashin Hankali Saboda Rashinki Ni kaina Wlh Halima kara nake musu ammh Sun kai makura.."Take Fada Tana Sharan kwallah Zaina Taji Rauninta ya kara Bayyana ta Kara Fashewa da kuka Tana Fadin"Ku yafemin..Wlh Nima Tunda na Tafi nake Cikin kewarku...Nayi kuka Har bansan iyaka ba,ba Domin na Hadu da masu kaunata ba da yanzu ban Dawo agabanku Cikin wannan yanayin ba.." Abba ne ya karisa Gaban Zaina ya Dafa kanta yana Fadin"Ki daina kuka Sa"adiya mu babban Farincikin mu Daya kin Dawo Gida lafiya so sai mu gode ma Allah mu daina Tuna Baya.."Jin haka yasa Zaina ta gyada kai Tana Fadin"Abba ka yafemin..Nayi Butulci gareka...n.."Kai Abba ya girgizamata bayan ya Rufe mata baki ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Sa"adiya.."Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Haka Zaina ta Dinga su Baban kaduna tana Kuka Tana Fadin su yafemata Ana cikin Haka ne sai ga Haddir ya Shigo kamar an jehosa Sai da yaga zaina kana ya gasgata mganar Shema Alhamdulillah yake Ta Fada acikin Ransa Su Faruq kuma suna Shigowa sukaci karo da akwatin su Zaina su suka Daukosu suka Shigo Dasu Cikin Falo ba karamin mamaki da Murna sukayi ba da ganin Zaina ba Faruq ya kirata Cikin Zumudi"Ukti..' Ta Juyo Tana kallonsa ta Mike Tatafi gareshi Tana Fadin"Ahki.."Rumgume juna sukayi Cikin Farinciki Faruq ya Dagota Hawaye sun Cikamai ido Yana Fadin"Ina kika Tafi kika barmu muna ta kuka,Ina kika je kikabar Umma Cikin Damuwar Rashinki..? Ina kika Tafi kika bar Ya Dakta Cikin Halin Rayuwa mara Dadi Ukti..? Zaina Tana Hawayen Farinciki Take Fadin"Labari ne mai Tsawo Ahki..Ka yafemin kukan dana sakaka..Ya Sadiq sannunku Ya Haddir Ina murna fa.."Take Fada Tana kallonsu suna kallonta suke Cikin yanayin Farinciki Haddir kusa da ita ya karisa yana Fadin"Alhamdulillah..Allah na gode maka Daka Dawomin da Farincikin Aminina gida Lafiya Allah ne abun Godiya Allah ya sa karshen Wahalan kenan Zaina ta Zain.."Gabadaya Falon sai da kowa ya Murmusa Zaina ta Sunkuyar Dakai Tana son Tambayan Zain Domin bata ganshi ba Anun ta Fara kuka Tana Hannun Umma Hankalin sai ya koma kansu,Anun na Fara kuka Anan ta Fara ganin yar"uwata na kuka Farida Dake gefe ta kalli Zaina Tana Fadin"Daukesu ki shayar dasu Sa"adiya kinsan Rabonsu da Nono tun Safe fa..."Su Haddir ne wannan karon ke mamakin ganinsu Anun basu gama mamaki ba sai da su Umma suka kawo ma Zaina su ta Zauna ta Shige Cikin Hijabi ta Fara Shayar da Anun kana Sai da ta Koshi ta mikama Umma Ita Tana Fadin"Umma riketa Takwarki ce.."Umma da Farinciki yacika Ranta tace"Haka wacce kuka zo Tare tace..Nagode Diyata Allah yayi albarka.."aka amsa da Ameen kana Zafeera ta miko mata Anan Tana Dariya Hararanta Tayi tana yar Dariya Ta kara Shigewa Hijabi Tana bata Nono Gabadaya ita aka Sakarma Ido Haddir kuwa wani Farinciki ne ya kamashi yana Tunanin in Zain ya samu Labarin zaina ta Dawo har da Ya"ya Biyu Dayake Fadin yana Mafarkin Zainarsa ta Haifi Abunda ke Cikinta Tabbas So ba karya bane ya yarda ayau din nan. Bayan Tagama Bama Anan Nono Ta Mikama Zafeera Tana Fadin"Rike Diyarki...Anan Maminki ce Zafeera..'Anan tabi Zafeera da kallon Rashin Sanin Kowa sai kallon yaran yake da Sha"awa Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Bangane wannan wariyar ba Amaryata Halimatus Sa"adiya..?ni baki bani Ya"yana na Dauka ba..! Domin bana ce Tatattaba kunnina ba." Gabadaya Falon kowa yayi Dariya Zaina Kunyar Alhaji Tsoho Take ji ta mike Tana Raba ido Umma da Zafeera suka kai mai su Anun suka Doramai kan Jikinsa Zaina ma ta Matso kusa Dashi Ta Zauna Tana Sharan kwallah Alhaji Tsoho ya kurama su Anan ido kamar yadda suke kallonsa yana Mirmishi wani Sanyi na Ratsashi Cikin Farinciki yake Motsi da bakinshi kafin ya Dafa kawunsu Daya Bayan Daya yayi musu addu"a kafin yace"Allah yayi muku albarka..Allah ya raya fatima Ib kika gado mai sunanki Kin yi sa"a Domin Fatima gatachan ita ce marikiyar Mahaifiyarki Halima Ke kuma Maryama Ki gado Hakurin Maryama Kinci Sunan Maryama mahaifiyar Halima ce Allah ya Jikanta Allah yasa Hallayarta na gari ya Bita Ita da Abdullahi da Mallam Umar da Marigayiya Atine Allah ya Hadamu dasu acikin Aljannar Allah.."Yake Fada Cikin Wani yanayi gabadaya Falon sai da kowa ya Share kwallah barin ma Zaina Data Ke ta kuka su Abba nata amsawa da Ameen Alhaji Tsoho ya Kalleta yana Fadin"Bifa na bar auran nan Dake Halima..Na samu Sabbin Amare masu Jini ajika.."Dariya aka saka gabadaya suma kamar sun san Abunda yace sai suka Fara Dariya Farida da Zulaihat na Gefe Suna kallon Tsabar kauna da Soyayyar Tuni kewar Gida Dana ya"yanta ya Shige Farida Har tana Share kwallah Dina ma Tana gefe sai kuka Take Kuma ta rasa kukan Farinciiki take ko kuma kukan Dawowar Zaina sai dai Tana Murna ga ahalin nan da yau Allah ya Bayyana wacce Rashinta ke sakasu kuka Musamman Zain. Alhaji Tsoho ne ya Lura ZainaTaki barin kuka ya muskuta Yana kara Rike su Anun yana Fadin"Halima ki daina wannan kukan hakanan Don Allah..Dukkanmu nan mun Riga mun yarda da kaddara mun kuma bar komai a Hannunsa Shi muka Dinga Roko Har ya amsa mana ya Dawo mana Dake lafiya.."Zaina ta kara Saka kuka Tana Fadin"Ina jin kunyarka Alhaji Tsoho..Tunda kafin nazo Duniya ka zama mai Alheri ga Kakanina da iyayena Har nazo Duniya kuka Daukeni kai da Duka ahalinku Kuka maidani yar Gata Kuka Sharemin Hawaye baku Taba sakani kuka ba,baku barni nayi kukan Rashin Gata ba ammh yau gashi ni na sakaku fa..Abba ya Fifita ni qsn Duka ya'yansa ya ki Firstlove saboda ni Alhaji Tsoho Umma Taki Abunda ta Haifa acikinta Saboda Ni Alhaji Tsoho Daga karshe na Nuna Butulci gareku na Tafiya na barku Wlh ina Jin kunyarku Inaji kamar Duk Duniya Tana kallona a matsayin Bulutu wacce bata san karaminci ba.." Alhaji Tsoho ya girgiza yana Mirmishi yace"Ko Daya Halima..Tafiyarki wani Rubutattace ne Daga Allah..Allah ya Rubuta wadanan yaran ba anan garin Zaki Haifesu ba Cibiyarsu na garin Da kikaje kuma Kila Tafiyarki Allah yasan zai iya Warware wasu abubuwa Da Dama Duk da mun Shiga Damuwa Saboda rashin sanin Takamammen Ina zaki..? Wani Hali Kika Fada ammh ayau komai ya wuce Tunda gaki kin Dawo da kafarki kuma keda Abunda kika Haifa Cikin Koshin Lafiya Sai dai kawai muyi ma Allah Godiya.." Kowa sai gyada kai yake yi alamun gamsuwa da kalaman Alhaji Tsoho Baban Kaduna ne yace"Ki Daina kuka Hakanan Sa"adiya yau din Ranar Farinciki ne garemu..Suma Da kika ga suna kuka na Murnan ganinki ne ki Dakata kukanan hakan kafin suma yaran nan su kama Domin gasunan sunyi Shuru suna kallonki kina kuka.."Sai Lokacin aka Lura dasu Anun Dake ta kallon Zaina suna Bata rai alamun suma suna Gabda Fara kukan Kowa Sai Kallonsu yake da Sha"awa Zafeera ce ta Duka tana Share ma Zaina Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Ukti.Daina wannan kukan..Ki bari sai mun Shiga Ciki Sai na Dargagji Bakin ki Da kika sakani kuka.." Zaina na Dariya ta Tsunguleta Cikin Farinciki Tana Fadin"Mara kunyar Amarya.."Hararanta Zafeera Tayi Tana zama kusa da ita Tana Fadin"Su Amare manya.."Wani kallo Zaina Tayi mata irin zamu gamo Dinan Hajiya Mama ce tace"Ke Halima nifa na Kosa naji Da kika bar gida ina Kika Je..? Zaina Ta Dago Tana kallon Barayin da su Farida suke Tana Nemansu Sai ta gansu Chan Gefe da Hannu ta yafitosu suka Taso suka Taho Matsa musu Tayi saman Cafet din Tana Fadin"Ku zauna na Nuna ma Ahalina Wadanda suka Zama garkuwata su kuma bada Komai nasu saboda ni.."Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah Farida da Zulaihat suka samu nan kasa gefen Zaina suka Zauna sai kowa ya koma ya zauna irinsu Nene Dake Tsaye suna Kallon su Farida Tunkafin Zaina ta bada labarin har wasu sun Fara saka musu albarka acikin Ransu Zaina ce Ta muskuta Tana kara kallon Kowa Dake Falon har Idanuwanta suka Sauka kan Dina wacce ke gefen Hajiya Batula sun Dade suna kallon Juna Cikin Wani irin Fargaba Domin Zaina bata so Taji wani labari kan Dina Cikin Jikinta take kallo tana Wani Tunani Kardai ace Cikin Data bar Dina Dashi har yanzu bata Haihu ba..? Farida ce ta Katse mata Tunani Da Fadin"Wai Sa"adiya Ina Firstlove ne..?Kamar ban gansa acikin wannan Taron ba kuma banji Kin Tambayesa ba..? Zaina ta Dukar da kai Domin Tun Zuwanta Idanuwanta ke son ganin Firsrlove tana kewarsa Sosai Duk da Tana jin kunyarsa Alhaji Tsoho yayi gyaran Murya yana Fadin"Zainullahi Baya kasar nan Tun Wata bakwai da suka wuce ya Tafi india hallatar wani Course akan Harkan Fida,ammh Insha Allahu ya kusa kamallawa nan da wata Daya zai Dawo Da wannan nake Rokonmu Dukkanmu anan wajen munsan Halin da yaron nan ya Shiga Bayan Barin Halima Gida abubuwa sun Faru marasa Dadi ammh Alhamdulillah komai ya zama Daidai yanzu Kuma mun san Cewa Rashinta ne yasa yayi Nesa da Gida Toh In har ya samu Labarin Dawowarta na Tabbata kun Tabbata bazai bari ya Cimma abunda yakaisa ba zai Tattara ya Dawo kuma in hakan Ta Faru dukkamu bazamu ji Dadi ba da wannan nake Rokon kada wanda ya Fadamai Dawowar Halima mu jira Har yagama abunda yakaisa ya Dawo lafiya koma Menene sai yazo Daga baya.." Kowa afalon yayi Na"am da Mganar Alhaji Tsoho Harta kuwa da Haddir Daya Tabbatar ma kansa Zain bazai yarda ya kara kwana agarin Delhi ba yau zai Taso Zuwa Gida Baban Kaduna yace"Tabbas Mganar Alhaji Tsoho mganace mai kyau..Saboda haka kada wanda koda waasa ya sanar da Zain Labarin Dawowar Sa"adiya.."Kowa yace Insha Allahu Bazai Fada ba Zaina kanta na kasa Jikinta Duk yayi Sanyi Jin irin Halin da Firstlove ya Shiga saboda Rashinta ga kuma Dina Wanda Ita kanta Tafi Tsayama arai Shin wai anyi Auranta da Zain ne ko yaya ne..? Itafa ta kasa gane komai. Ganin Duk kowa ya Zuba mata ido ne ana Sauraranta yasa ta Fara Bada Labarin Ranar data bar Gidan Har Zuwa Haduwarta da Farida da duka Rayuwar Da Tayi agidan Uwar Mata Zuwa Tashinsu da komawarsu gyallesu da Haihuwanta Da Duka Rayiwar da tayi achan da Labarin Farida da Labarin Zulaihat Ta kareshe da Fadin"Anty Farida ta zama garkuwa gareni..Ta yarda ta Fita Ta bada Jikinta abiyata kudi Saboda Takula dani da Abunda ke Cikinta Tun su Anun na Ciki take wahala dasu har sukaxo Duniya Wlh Tallahi Ko da Da Rana Daya basu Taba wani maraici ba Komai na Rayuwarmu Ta kare mana shi..Tana da Ciwon Datake Bukatar Tsallaka wata kasa Domin nemab Lafiya ammh Saboda ni da Su Anun taki yarda taje Ko"ina Saboda ta Cika alkawarin Mikani ga Ahalina ga Zulaihat nan ita ta kasance wata Uwa ce ga su Anun Taci kashinsu da Fitsarinsu komai na Rayiwarsu ita take yi musu ni kawai sunan ni na Haifesu ne ammh Duka Wahalarsu Zulaihat ce da Anty Farida suka Dauki wannan Nauyin Tunda na Tafi basu Taba barina nayi kukan wani abu ba sai dai kukan Rashin ku da kewar Duka ahalina ammh ba kukan yau na Nemi wani abu na Rsaa ba ni kam dame zan saka musu..? Ku tayani nuna kauna da Godiya garesu don Allah.."Tafada Tana Hada Hannayenta Waje Daya kowa afalon kuka yake Zafeera kuka Share Share haka su Umma sun koka da Wannan irin Rayuwar da Zaina ta Fada ammh sun Godema Allah da Haduwarta da Farida Labarin Farida ya Tsuma Kowa Rashin gatan Zulaihat ya Taba Duka Zukatan su Umma Rauni Hardasu Abba. Ita kanta Farida kai ta Sunkuyar Tana kuka Hakama Zulaihat Dina kuma,Kukan Nadama kawai take Tana Tunanin su da suka Zabi Bariki da kansu ashe akwai wadanda Rayuwar Barikin ma Ba"a son Ransu suke yinta ba wani Sanadi ne ya kawosu Cikinsu kafin kace me kalmar Godiya yabo Tare da Jinjina da addu"o'i ne ke karade Falon ga Farida da Zulaihat Hajiya Mama ta Rike Hannuwan Farida Tana Fadin'"Wannan Rayuwar ba ita ta Dace kamilar nace irin ba..Wannan Rayuwar bata dace da kamilar Uwa irin ki ba...Tun kafin naji irin Taimakon da kikayi ma Jikata Halima naji Kin Shiga Raina kidaina kuka da yardan Allah zamu sadaki da duka ahalimki kuma Insha Allahi Zubaida da uwarta sai sunyi mutuwar Wulakanci.."Nene tayi Saurin Cewa"Fade ma Bata baki Hajiya Mama na Tabbata yanzu sun ga Sakayyah.." Hajiya Mama Ta kalli Zulaihat Tana Fadin"Ke kuma Kidaina kuka...Daga yau baki ba kukan Rashin Gata Daga yau kin Zama mai gata Kamar kowacce ya"Zaki koma ga Danginki Insha Allahu na Tabbata Larai Nemanki Ido Rufe take Domin Fadin Allah ne baka Taba Cin Hakkin Maraya ka zauna Lafiya..' Mama Safiya Tace"Ina..Ai Tuni Allah ya Dade da Nuna musu Kuskuransu ammh Dai Zumunci ya Lalace awannan Zamanin.."Kowa sai Tofa albarkacin Bakinsa yake Alhaji Tsoho yayi Shuru bai ce komai ba sai da Surutun yayi sauki kana ya Fara mgana"Hakika Allah ne abun godiya kuma Shine Sarkin Duniya..Daman Tafiya akace mabudim Ilimi Daman kuma Kaddaran Haduwa dasu ne ya Fitar Dake Daga gida yau Dalilin haka mun san Labarin Wasu Mutane guda Biyu wadanda Labaransu suka Bamu Tsausayi kuma muka Dauki Wasu Darussa babu abunda Zance Face Allah yayi Muku Sakayyah da Gidan Aljannah Firdausi ke Farida da Zulaihat Allah Ya Jikanku kamar yadda kuka ji kan Halima Allah ya Tallafa muku kamar yadda kuka Tallafa mata sannan Daga Karshe ke Farida Zamu maidaki Gidan Wajen Danginki Da kafata zani Domin na an karar dasu kuskuran da iyayanki sukayi wajen aibataki wanda Tabbas Shiyasa Kika Fada Harkan karuwanci Domin Kaifi ne da bakin iyaye wanda yafi ma Kaifin Takobi.."Su Abba sai gyada kai suke alamun gamsuwa Hajiya Mama tace"Tabbas furucin Iyayanta akanta Shi yake Binta har yanzu..Kuma Shi ne Dalilin Fadawarta wannan Harkan.."Farida Dake kuka Ta Mike kamar Wata mahaukaciya Tana Fadin"Kuyi hakuri..Ban kawo Sadiya gabanku da Rokon ku maida ni ga Dangina ba..Duk da ina Jin kewarsu araina ammh Bazan koma ba Koda zan komai sai dai naje na Nuna musu Shedar Karuwancin da suka Kiramin ba inda zan koma Zan koma Zaria na Cigaba da Abunda suka kirani Dashi Har Abada bana Fatan su ji Labarina.."Daga haka kawai ta Kwashi Gudu Zuwa Dakin Hajiya Mama Kowa ya Bita da kallo. Zaina da Zulaihat hankalinsu ya Tashi sun Tashi Zasu Bita Alhaji Tsoho ya Dakatarsu yana Fadin"Ku koma ku Zauna..Na Fahimci wani abu..Sihiri na Dawainiya da ita wanda ke kara mata Wutar abun aranta kuma yana Nesantata da Kusantan ahalinta koma yayane akwai wanda baya so ta bar wannan Harkan.."Salati su Hajiya Mama suka Dauka Zulaihat da Zaina suka kalli Juna suka Hada baki Wajen Fadin"Uwar Mata ce..! Alhaji Tsoho yayi Mirmishi kafin yace"Bazata so Ta bar wannan Harkan ba kamar yadda kuka bada Labari Tunda Tana samun Kudi ta Bangaranta kada ku damu Zata Dawo Daidai da kanta zata ce Zata koma ga ahalinta da ya"yanta Tunda kun Riga kunzo bazan Taba bari ta koma Chan ba Insha Allahu Zata koma Cikin ahalinta wanda duk inda suke sun Dade da yin Nadama yanke Hukunci Cikin Fushi da Rashin Bincike.."Kowa ya gyada alamun gamsuwa Kafin Alhaji Tsoho ya kalli Baban kaduna yana Fadin"An kira Sallar La"asar ko Bashir..? Baban Kaduna na Duba agogon Hannunsa yana Fadin"Yanzu dai za'a kira Alhaji Tsoho.."Gyada kai yayi yana Fadin"Sai mu tashi muyi sallah..Halima tafi da baki Dakin Hajiya Mama abasu abinci kuci kuyi wanka da Sallah ku huta ita Faridan ku kyaleta Tayi kukanta kada kuce mata komai..Hannatu da Rukayyah da Ke Umman Zareena ku Shirya ku mika Zafeeraa Dakinta Alhamdulillah yau Komai ya zama sai Godiya ga Allah kai Takwara na Babba Rufemana Taron da addu"a.." Sadiq babba Shi ya Rufe Taron da addu"a kafin Taron ya watse Zainab da Shema suka kama akwatunan Su Zaina zuwa Dakin Hajiya Mama Umma da Nene suka karbi su Anun su Inna Hannatu da Inna Rukayyah Dake zaune gefe duk al"ajabi ya kamasu suma suka mike Zaina da Zafeera suna Rike da Hannun Juna Ta Riko Hannun Zulaihat Suka Nufi Dakin Hajiya Mama Sauran kawayen Zafeera suna Wani Daki Ganin mganar ba nasu bsne basu Fito ba su Hamdiya suka Biyo Bayansu Harda Dina su Abba kuma dasu Haddir suka Fice da Alhaji Tsoho Domin su Daura alwala su Tada sallah Suna Shiga Dakin Hajiya Mama suka Iske har Farida ta Shiga Tiolet tayi alwala Sai Zainab ta bata Darduma da Wani Dogon hijabi Zaina na Rike daHannun Zafeera kamar wani Zai Rabasu Dina ta Shigo Dakin Kai tsaye wajen Zaina ta Nufa tana Zuwa sai ta Rumgumeta Gabadaya sai kowa ya saki baki ana kallon Ikon Allah kafin ta Dago Tana Mirmishi tace"Almdulillah..Ina Murna da Dawowarki Gida zaina." Cikin karaya da Hawaye acikin Idanuwanta zaina tayi yake Tana Fadin"Nagode Dina.."Kawai ta iya Fada kai Dina ta gyadaa mata kafin ta Kada kai Zata Fita sai ga Arman ya Shigo da dan Gudunsa na yara Jalal ya Biyosa yana Fadin yazo suyi alwala Ganin Dina yasa ya makaleta yana Fadin Momy Cikin mganarsu na yara ita kuma sai ta Rikeshi Tana Tambayan Jalal me yafaru nan yake Fadin Uncle Faruq ne yace suyi alwala suzo suyi sallah Shine ya gudo Cikin Gida. Dina Tayi Mirmishi Tana Fadin"Kai baka son Sallar ne..? Jalal kamasa kuje ka nuna mai yayi ko Arman din Nene da Umma.."Kai ya Dagamata yana Dariya kafin Jalal ya Rike hanmunsa suka Fita Dina bata waigo ba itama Tabi bayansu Zaina Data Daskare saboda mamakin ganin Arman ta Dago Tana kallon Zafeera kafin tayi mgana ta Rigata da Cewa"Aliyu zainullahi Usman Saulawa Arman keman Shine Cikin da kika Tafi kikar bar Dina Dashi.."Zaina tayi Jagale gabanta na Fadi tace"Toh...na..naga taana da wani Cikin kuma.? Zafeera ta Kauda kai Batayi mgana ba Hajiya mama da Goggo Halima Dake Kofar Dakin suka kariso Goggo Halima Tace"Wani Cikin ta samu..Bayan ta Haifi Arman tayi arba"in an Daura musu aure da zain.."Kowa sai ya kura ma Zaina ido Farida Dake sallah Bata idar ba ta sallame haka zulaihat suka Nuna mamakinsu. Cikin Lallami Hajiya Mama ta Dafa Kafadar Zaina ganin tayi ma Goggo Halim kuri da ido wani abu na sukan Ranta wanda bata iya gane komai ba tace"Kiyi Hakuri Zaina..Komai ya wuce an zama Daya kaddaran Zuwan Arman ne ya Haifar da komai kinji kada ki Damu kanki kowa ya Tabbata kina nan a Sanyin Idanuwan zainullahi.."kowa Abunda Zaina Tayi sai da ya basu mamaki Mirmishi ta saki kafin tace"Laa..Hajiya Mama bakomai Wlh..Hakan yayi daidai ma..Allah sarki Arman na Tabbata ba zai tashi Cikin Gori da maraicin wani bangare ba."Daga haka bata kara cewa komai ba ta Sabule Jikinta Ta Shige Tiolet ta barsu nan bata yarda Tayi kuka ba ko kadan Domin ai yanzu Ita ta Riga ta san Rayuwa ta kuma san Juriya ammh in tace bata jin Kishi Tayi karya sai dai kawai ta Shanye wajen nuna Gogewarta arayuwa yanzu. Wanka Tayi ta Dauro alwala ta Fito kamar ba ita ba kana tace ma Zulaihat ta Shiga ta Watsa ruwa Mikewa Tayi Tana Tambayansu Anun Hajiya Mama tace suna Chan Dakin tare dasu Umma Tanayi ma su Anun din wanka,Kowa sai mamakin Zaina yake yadda bata nuna komai ba da kuma mamakin ganin Takara Cika da Girma Har Farida sai da tayi wanka suka Sauya kaya suka zo sukaci Abinci suka Koshi Zafeera sai kallon Zaina take duk inda tabi Hardai Ta gaji da Daka mata Duka Tana Fadin"Wai wannan kallon fa..? Bafa ya Haddir bane Jira Lokaci kadan ne yanzu zaMu mika ki kije Chan kiyi ta kallonsa ki More.." Mikewa Zafeeran Tayi zata Rama Dukanta Zaina ta Boye Bayan Farida Tana Fadin"Anty Farida kin ga Ukti Ko..?dukana Zatayi Daga na gayamata gaskiya."Farida na Dariya tace"Yi hakuri Zafeera..Ko Mutuwa tana Jin kunyar Uwa da Anty saboda haka Raga mata..'Zafeera tace"Badai son kai ba Ko Anty Farida..? Farida tace'Wlh ba son kai..Waya isa ya Shiga Tsakanin ku..Jata ki Rama.."Zaina na Jin haka ta kwabe Fuska mai Su Zainab zasuyi in ba Dariya ba Zulaihat ma Dariyan Take Tana Fadin"Kullim kafin mu kwanta sai Sa"adiya Ta bani labarin Rayuwarta ita da Ukti Zafeera...Sai da na ganin ma Idona na Tabbatar da abun ya wuce yadda take fada..'Nan su Zainab suka zauna suna bama su Farida labarin Tashin su Zafeera su kuma Rigima Har Falo sai da Goggo Halima da Hajiya suka Raba Fadan Kowa kagani Fuska Cikin Farinciki Sai da suka Matsa gefe ne Zafeera ke Fadin Zaina ta Cika ta zama wata Big Mama ita kuma Tana Dariyan Farincikin yau gata Cikin Damginta tace mata Haihuwa ne ya Budani kema kwana nawa ne..? Yadda naga Idanuwan Ya Haddir bazai yi wasa ba.." Duka Zafeera ta kaimata Tana Hararanta kafin su koma Hiran Rayuwa nan take Fadamata Laila Tayi aure Zaina tace Dole taje gidan Laila Allah Sarki kawar Amana kana ta koma bata Labarin Abubuwan da suka Faru bayan Tafiyarta da Tashin Hankalin da suka Shiga da Ciwom zain da Barin gidansu da komai da auransu da Dina Zaina Sai hawaye suna ma Cikin mgana basu gama ba,Su Inna Rukayyah suka Tada Hiran suka Tafi da Zafeera suka Shiryata Koda 5pm Tayi an gama Shirya Amarya sai kuka Take Tana kuma makale da Zaina kamar wani zai kwace Mata ita su Anun kuma sun zama yan Gida Suna Kwakwame da kakaninsu Nene da Umma su Farida ma suna Cikin su Zareena ana ta Hira yadda kasan an Shekara Tare. Daddyn Abuja Shi ya Dauki Amarya amotarsa ita da Zaina da Goggo Halima sai yayar Mama Safiya sai Faruq Daya Shige Gidan gaba,su Farida Motar Sadiq babba suka Shiga,ita da Zulaihat da Zainab da Shema su Anun na Tare dasu Umma Direban Abba ya Daukesu Dina ma Motar Kwamishina suka Shiga Tunda Gobe zata koma,Hajiya Batula sai bata Wasu Shawarwari take kan kada Tace Zatayi Kishi Da Zaina aran Dina tace me zai kaita Ai Zaina tayi mata Nisa Sosai Arman kuma yana Tare da su Zareena da Jalal Motar Haddir suka Shiga wanda Sadiq karami ke janta Sauran kawayen Amarya kuwa Abokan Haddir suka Daukesu sai Gidan Zafeera. Har kan gadonta dayaji Shimfidun alfarma zaina takai Zafeera sauran kuma suna ta yawata Gidan suna ta Dubawa suna Santi Zaina dai na Tare da Zafeera Tana ta bata baki Ba"a Dade ba Bayan an gama gyare gyare Akace azo atafi Duka aka Tarkatasu Domin Umarnin Alhaji Tsoho ne ba wanda zai kwana Tunda kusa ne kuma an gama komai..!Zafeera taso ta Rike Zaina Tana kuka Umma ta Hana tace ta wuce su koma Gida Zafeera naji Tana gani Kowa ya Fice ya barta ita kadai Tana kuka Zaina na ta yi mata alamun Sorry din nan shi ke kara sakata kuka. *Janafty...* 8/9/21, 3:25 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B22️⃣7️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Gidan Alhaji Tsoho suka koma ana ta maida Zence Goggo Halima Tuni ta kira yan Chan Gada ta sanar dasu dawowar Zaina wasu basu yarda ba sai da ta Hadasu sukayi mgana da ita ta waya kana suka yarda nan da nan sukace gobe suna kan Hanya Dole ne suzo su Taya Iyalan Alhaji Tsoho Murnan Dawowar Halima. Su Anun kuwa sun zama yan gata Suna Wajen Abba ya Dauki jikokinsa yana jin wani Farinciki mara Misaltuwa Farida kuma Tana Tare da Zareena sai Hira suke kamar Sun Dade da Haduwa Zaina Taji Dadi ganin babu wanda ya nuna kyama ga Farida Zulaihat kuma duk suna Tare dasu Zainab. Dina ma duk suna nan Tare sai Dare Zaina taga Arman ta Daukeshi Tana kallonsa sai Tsausayinsa ya kamata ta Rumgumeshi Tana Fatan Allah ya Rayashi Kowa yaga Jarumtar Zaina Umma acikin Ranta tace Zainata ta karo Ilimin wani abu Boye da Damuwarta da kuma Rashin Nuna gazawa uwa uba kima Taga Juriya acikin Idanuwanta Lalle wata Tafiya Mabudin ilimi ne kamar yadda ta kasance Wajen zaina. Basu koma Gidan Abba ba sai Dare bayan sun ci Abinci nan Gidan Alhaji Tsoho Direban Abba da Sadiq ya kwashesu Zuwa Gida nan sukabar su Mama Safiya da Danginta Su Kuma suka Dawo Gida suna Dawowa Zareena Taja Farida Zuwa Dakinta Datake sauka su Kuma su Zaina suka yada zango Dakinsu na baya ita da Zulaihat sai Shema Data Biyosu ita kuma Zainab ta koma Dakinta Suna Gajiye ne kowacce sallah kawai sukayi suka kwanta su Anun kuma Suna Tare da Abba sai Wajen 10pm na Dare ya Dawo Tare dasu Anun dasu Faruq, Lokacin Tuni Zaina Tayi Barci Nene ta karbesu Tayi musu wanka Ta basu Tea suka sha sun Fara Rigima Daga Baya sukayi Shuru barci ya Daukesu Dina ma Tare suka Dawo Sai Su Umma sukace Tatafi Shashenta da Hajiya Batula dasu Waleed Taji Dadi kuwa ta kwashe Suka Tafi zam sufi samun kyakyawan Sakewa. Haddir Ango kuwa ba wanda ya Rakashi Zuwa Gidansa Shi kadai ya Tafi bayan ya Tsaya kan Hanya ya siya kazar amarci Da madaran Holladian ya Shiga Dashi Ciki Duk da ba auran Soyayyah sukayi ba,Ammh bai Taba Jin ya Tsani Zafeera ba Tunda dai Iyayansu sunga Dacewarsu Tare yakamata su zauna Suyi ma Juna adalci. Sai da ya Shiga Dayan Bedroom din da kayansa da yazo Dashi yayi wanka ya saka Jallabiya kana ya Shiga Bedroom din da Zafeera ke Ciki ya sameta Idanuwanta Biyu Tana ta kuka Zama yayi gefenta Har Tana Saurun Matsawa sai abun ya bashi Dariya Ledan Kazan ya ijiye mata kafin ya Fara mgana Cikin Sanyin murya Farawa yayi da Godiya ga Allah Sannan ya gangaro kan Hakkin iyayansu akansu Da kuma Muhummancn Biyayyaj garesu Daga karshe ya gayamata zasu yi Zama na Fahintar juna amatsayinsu na yan"uwa yayi alkawarin bazai Taba Takura mata,Itama ta saki Jikinta nan Gidan Mijinta ne in Tana Bukatar wani abu ta gayamai Shi zai iya Bakin Kokarinsa Wajen Sauke Nauyin Dake kansa Mganar makarantanta kuwa Hutunta na Karewa yayi mata alkawarin zai maidata kano da Hannunsa Shidai Fatansa ta saki Jikinta su Zauna Lafiya. Tunda ya Fara mgana Zafeera Taji Jikinta yayi Sanyi ashe ba ka yanke ba ba kyau yanke Mutum Hukumci baka Zauna dashi ba da Farko Kallon mai girman kai take ma Haddir ammh kalamansa yasa ta Fahimci yana da Hankali da Natsuwa sai ta samu kanta Dace mai Insha Allahu bai Takura mata ba yace Taji kazan ta kwanta Daganan yayi mata sai da Safe ya fita Tabishi da kallo Tana Sauke Numfashi Tana Jin yunwa Shiyasa Taji kazan Kadan Ta Kora da madaran ta kwanta Tashi Tayi ta Sauya kaya Zuwa na barci Daman bayan Fitansu Umma tayi wanka Tayi sallarta Fargaba yahanata sauya kayan Tana Tunanin wani abu zai Faru sai gashi ya bata mamaki Ko Hannunta bai Taba ba,addu"a barci Tayi ta koma ta kwanta sai kuma Taji kewar Shema ta Kamata Tare suke kwana sun Komawarta kano Gidan Inna Rukayyah sai ta koma Farincikin da suka Shiga Sakamakon Dawowar Zaina ayau Lalle Allah ne Abun Godiya Tana wadanan Tunane Tunanen bata san sadda Barci ya kwasheta ba sai da Taji Haddir na Tashinta Lokacin ma yayi Shiri Zai Fita masallaci sai Da ya Tabbatar tatashi kana ya Fice Zuwa masallaci. Bai Dawo Gidan ba sai 6am na Safe koda ya Dawo ta Koma Barci Shima Da Gajiya ajikinsa ya Koma Ciki ya kwanta Wajen Goma yaji Knooking ya Taso ya Bude sai ga Direban Abba da kayan Karyawansu ya karba yamai Godiya ya Tafi kan Dinning ya ijiye komai ya koma Ciki yayi Wanka ya Sauya kaya yana Fitiwa Falo suka Hadu da zafeera itama ta Fito Tayi wanka Gaisheshi Tayi ya amsa Cikinn Kulawa Yace mata suje su karya Tare suka zauna suka karya Duk da ba mgana suke ba ammh Kusancinsu ma wani abu. Bayan sun gama karyawan ne ya samu Kiran Mom Ilklima Kan kada ya Fito yau ya zauna agida ya kula da Amaryansa yana Dariyan jin kunya yace zai Fita yaje suyi sallama da abokansa Tace Shikenan bai tsaya ba ya gayama Zafeera zai Fita sai ta Fara nuna Zatayi kuka yace Yanzu zai Dawo. Saboda kada ya barta ita kadai Yana Zuwa sukayi sallama ya Dawo Gidan Zafeera tagama cika Ta Kira Umma Kan Zaina dasu Zainab suzo Umma tace ba wanda zai zo ta zauna agidanta Zaina kuma Tana barcin gajiya Kada ta Dameta Har sai da Tayi kwallah Har Shema ta Kira ammh Tace bazata zo ba sai Gobe in Zasu koma kano Zata zo Suyu sallama Dole Zafeera ta Hakura ganin Haddir din ya Dawo Gidan Tare suka wuni Duk da ba wani mgana ke Shiga Tsakaninsu ba Tabbas sun Debema Juna kewa Abincin Rana da Dinner Dare Duka Direban Abba ya kawo musu Basu da mtsalan komai Sallah kadai ke Tadasu kallo ma daya kunna Bai dameta ba Wayarta take ta latsawa. Washegari Tun Wajen 10am Sai ga su Inna Rukayyah da Su Inna Hannatu da Shema sun zo mata Sallama zasu Tafi Zafeera Taga ba Zaina Ta Tambayeta Shema tace Taso Zuwa kuma Sai ga yan Gada sunyo waya suna Hanya ammh Zata zo ko Zuwa gobe ne ita da Zainab basu wani Jima ba suka Tafi Haddir ya Dauki Inna Hannatu da iyalanta Zuwa Filin Jirgi suka Hau suka Tafi Inna Rukayyah kuma Direben Babansu Shema yazo ya Kwashesu Zuwa Kano cike da kewar Zafeera. Su Babban Kaduna da Daddyn Abuja Duk Ranar suka koma Saboda Aiki,Dangin Mama Safiya sai tun Safe suka kama Hanya,Mama Safiya kafin sun Wuce sun Biya sun kara yima Amarya da ango Nasiha,Hakama Daddyn Abuja Duk Sun Biya sun kara yi musu Fadan Nasiha da zama Lafiya kafin su wuce sai Zuwa Dare Umma Ta kirata Ta bata Zaina sukayi mgana kan Gobe Ta na nan Zuwa ita dasu Farida da Anty Zareena yau baki sukayi yan Gada suna na ma nan sai Gobe zasu koma Zafeera tace Tana Jiranta Domin akwai mgana. Dina kuwa baiwar Allah da ita ake ta Hidima Hajiya Batula kuma Tun Ranar Lahadi ta koma Kano bayan tayi ma su Umma Sallama Da yan Gada suka Shigo Har nan ta Shigo Suka gaisa kana ta Shiga wajensu Zaina suka gaisa Har taDauki su Anun Arman ma yana wajensu Zainab suna ta wasa da su Anun din Abun mamaki yara kamar sun san su Jini Daya ne sai suka saki Jiki Dashi Zaina bata nuna ma Dina komai ba ko afuskarta Ta nuna Dakewarta da Jajircewarta wanda Bata yarda ta nuna mata wani abu ba,alhalin Allah kadai yasan ya Take ji in Taga Dina kuma ta Tuna amtsayin Zaman wa take. Yan Gada sunyi murna Da Dawowar zaina aka nuna musu Farida Da Zulaihat amtsayin Wadanda suka Taimaka ma Zaina suna tayi musu Godiya Daganan Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Chan ma suka kwana sai da Safe da zasu Tafi Suka biyo sukayi ma su Umma Sallama Tare da goggo Halima suka wuce bayan su Umma sun Cikata da kayan arziki tatafi Tana Fadin sai taga Zaina agada ita dasu Farida,Zaina tace insha Allahu suna Tafe aran Farida kuwa itama Tana saka ran Tafiyarsu Gobe ko Jibi. Zaina basu samu Zuwa Gidan Zafeera ba sai a washegarin Ranar da yan Gada suka Tafi suka samu Zuwa Shima sai da Abba ya basu Izini Zainab ta Rakasu Chan suka wuni Har da su Anun Da Arman da Anty Zareena dasu Jalal da Saudart,Zafeera murna kamar zai kasheta Saboda ganin yan"uwanta Ranar ta Fara Girki Zainab da Zaina da Zulaihat suka Taimaka mata ta Dafa Jallop din Shinkafa aranar Daman Haddir ya Koma asibiti Duk kewa ya Damu zafeera ammh Zuwansu yasa Taji sanyi yana Office ya kirata yaji ya take Daman ya karbi Lambar wayarta Da gaske yake zai kula da Amanar da ya hau kansa kuma zai Sauke Nauyin Dake kansa ta Dauka bayan sun gaisa tace su Zaina sun zo ma sai yaji Dadi yace mata patient sunyi yawa kila sai Dare zai dawo Tacr ba Mtsala sai ya Dawo. Sai da suka gama cin Abinci kana Zafeera Taja zaina Zuwa Cikin Bedroom Dinta Harda turo Kofa Zareena tana Tsokanarsu da Gulmamu Farida na Fadin ta kyalesu Hira ce ta barke sosai a Tsakaninsu Zafeera na kara bata Labarin Abubuwan da suka Faru Zaina Tayi kukan Tsausayin Halin da Firtlove ya Shiga akanta ta kuma Gayama Zafeera Shi take son gani Zafeera tace kada ta damu Soon Zai Dawo sun karkato kan mganar Haddir sai ga Zafeera yau na yabonsa zaina ta Fara Dariyan Shakiyanci har Zafeera Taji Hauahi sai Daga baya Ta Saurereta har ta bata Shawaran ta saki Jikinta ta Rike Mijinta Domin Wlh Haddir samun kamarsa sai an Tona su zauna su Fahimci Juna sosai Zafeera ta yarda da Shawaranta Sosai kuma Tace zatayi aiki Dashi. Bayan La"asar suka Fara Shirin Tafiya Domin zasu Biya ta Gidan Alhaji Tsoho Tun Ranar Biki rabonsu dashi Zafeera tace basu isa su Tafi ba Ta Dauki waya ta Kira Haddir Tana mai Shagwaban gasunan zasu Tafi sai yace ta bama Zaina wayar ta karba ya Roketa su zauna gayinan zuwa in yazo sai su tafi kada su bar Zafeera ita kadai Zareena naji ta Faramai Tsiya yana Jinta ya Datse sai Wajen Biyar ya Dawo Zareena ta Tasashi da Tsiyarta Bai biyemata ya kyaleta Yaji Dadi Dayaga Zafeera Harda Girki Tayi yana ta ma Zaina Godiya yana Shaida mata Zain ya kusa Dawowa Domin jiya sun yi waya ya gayamai kadan ya Rage ya kamallah Cikin Karshen watan nan ko Sabuwar wata yana Tafe Zaina acikin Ranta Tana Fata Da kuma kaguwa tasaka Firstlove acikin Idanuwanta Ta Rokeshi Gafara ko Allah yasa zai yafeta sai da yaci abinci yayi wanka ya sauya kaya yazo ya Dauki su Anun yana Musu wssa har sun saba dashi. Sai Wajen 6pm na yammah suka bar Gidan Har wajen Mota Haddir da Zafeera suka Rakosu suna Daga Musu Farida Tana ganin Girman wannan Ahalin kowa nasu ne tunda suka zo ba wanda ya nuna musu wata kyama da sukaje gidan Alhaji Tsoho haka suka Dinga Hira da Hajiya Mama da Alhaji Tsoho kamar sun san juna afakaice kuma suna ta mata Nasiha sai bayan Isha"i suka Tafi bayan Alhaji Tsoho yabama Farida Jarka guda na Ruwan addu"a yace ta Dinga Sha tana Shafawa ajiki Ta karba Tana ta Godiya Koda suka koma Gida Umma nata Fadan sun kai Dare awaje ko Tsoron Su Anun su kamu da Mira basa yi Zainab nata Dariyan Umma ta jikokinta take ji. Farida Ta yi ma zaina mganar Tafiyarsu ita kuma tagayama su Umma Abba Dayaji da kansa ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Shi kuma yace Su bari sai Zainullhi ya Dawo bai sako mgabar komawar gida ba yace kafin nan Insha Allahu da kanta Zata nemi ta koma da yarda Allag Jin Abunda Alhaji Tsoho yace batayi gaddama ba Domin Tsohin yana da kima acikin Idanuwanta Bangaran Zulaihat kuwa ko ajikinta Domin Tabbas Nan ma Gida ne awajenta. Bangaran Uwar mata kuwa Tafiyar Farida tagama Daga mata Hankali Hatta da Alhaji Badamasu bai san Farida ta Tatafi Bauchi saiDa suka zo ta Fadamai ya Tada hankalinsa kan zai Biyota ta Dakatar dashi Shidai ya Fadamata yana Sonta in ta amince zai aureta ita kuma tace Bazata auresa ba su Cigaba da Harkan Bariki kawai Uwar Mata Hajja Zabba"u ta Kira ta gayamata Abunda ke Faruwa ita ta Zugata su koma Wajen malamin Da yayimata aiki kan Farida aikuwa suka koma ya yi Dube Dubensa cikin kasa yace Tabbas Zaina ba alheri bace Zata Hanata Dawowa kuma zata Rabata da Harkan Gabaki Daya Ammh kada ta Damu zai mata aiki Farida Zata Dawo da kafarta Cikin Farinciki suka Zube mai kudi suka Tafi ya kwashe kudinsa ya Soke yana Musu Dariyan wawaye Domin ba aikin da zai Dakatar da Farida komawa ga ahalinta Domin suma Chan basu zauna bA suna ta addu"an Allah ya bayyana Musu ita araye ko amace. Zaina sai da Tayi sati da Dawowa garin Bauchi Zainab Ta rakasu Gidan Laila,Ta wayarta Tayi musu kwatancen Gidan Zainab ta Kirata zata zo bata gayamata Zaina ta Dawo ba ashe ma itama Lowcost Take zaune Tare suka Tafi da Zulaihat dasu Anun Farida ce kadai Tana Gida Tare da Zareena da suka Zama kawaye Sosai. Karamin Falt ne gidan Laila Ita Tazo ta Bude musu karamin Get din gidan ba karamar Girgiza Tayi ba da ganin Zaina Kafin su Rumgume juna suna Murna sai kuma kuka Laila Tayi murna Tayi murna kanar mene ta Dauki su Anun ta Rumgume Cikin Farimciki Bayan sun shiga Cikin Gidan ne ta Daga waya ta Kira Mamanta ta gayamata ga Halima har ta bata sukayi mgana Tana yi mata barka da arziki Tace zata zo har Gidan bayan nan ta Kira mijinta ma"aikaci a Hukunar Ruwa nan da nan sai gashi Tace mai ga Halima nan ya zauna yana Ta murna yana gayama Zaina Tunda ya Hadu da Laila Damuwarta Dayace na Rashinta Shiyasa yaasan Labarinta Zaina Sai hawaye Domin Ta Tabbatar da laila mai kaunarta ne nan ya Dauki Su Anun yana yi musu Wasa nan Suka barsu suka Shige Ciki Zaina na bata Labarin Rayuawar Datayi bayan Barinta Gida Laila Tayi kuka kuma Ta jinjinama Farida ta kara Gayamana Zaina kada ta bari ta koma Zaria Daganan sai Gida Zaina tace Insha Allahu nan Laila ke bata labarin Haduwarta da Mijinta Ahmed bayan Barinta Gida,Da irin yadda ya nace sai da ayi Auran ammh ita duk ta gama Sakewa da Namiji Zaina tace Wlh ta Daina Daukan haka Kaddara ce abunda ya Faru da ita da kanta Take Fada Mata Zain ya auri Dina Har tana da wani Cikin Laila Tayi matukar mamakin ganin Zaina wannan karon ta iya Daukam komai da kanta Sabanin Baya Lalle Rayuwa kenan ko Zaina bata goge kan karatu ba ta goge kan Harkan Rayuwa. Zaina Tana ta Tambayan yan Course dinsu Laila na gayamata Zaina Taji Hawaye Lokaci da Laila tace zasu Shiga aji Hidu ne yanzu sauransu shekara Daya da wani abu su kamallah Zaina ta Murmusa tace bakomai indai da Rabon Karatu Zatayi Domin bata Cire rai ba nan suka Wuni sai gabda mangariba suka Tafi Bayan Laila ta cika su Anun da kayansu Choculate Daman aikin su kenan Shan Zaki Abba ya Siyo musu Faruq ya Siyo Musu zainab Tsaraban kenan bayan ta Dawo Daga makaranta. ****** Bayan Sati Biyu..! Bayan Sati da Biyu da Bayyanar ZAINA abubuwa sun Daidaita Farinciki ya wanzu a Duka ahalin Alhaji Tsoho Zafeera da Haddir kuma Satin suka Fara Cin Amarcinsu Domin Ta bada kai Bori ya hau Rayuwarsu suke gudanarwa Cikin Farinciki da kaunar Junan da basu san yauahe suka Fara ba. Zaina kuwa ta kwantar da Hankalinta kamar ba ita ba sai kara kiba take Farida kuma bata kara mganar komawa Zaria ba kuma tana amfani da mganin Alhaji Tsoho kuma Alhamdulillah da alamun Nasara,Su Anun an zama yan Bauchi sune Dakin Umma Dakin Nene Shashen Abba su Shiga nan su Fita su da Arman Har Shashen Dina suna zuwa watarana Har wanka take musu Tana so yaran Sosai haka kawai Allah ya Doramata Sonsu Zaina bata Taba Shiga Shashen ba Duk da nan ne Shashen da iyayanta suka Zauna ammh bata Taba Shiga ba sai in Dinar taShigo Gaida su Umma su Hadu su gaisa Abun na bata mamakin ganin Zaina Ta zama wata babar Mace ko mganarta ma ta Manya mata ta koma sai dai in Tayi Laakari da inda ta zauna da kuma Tunanin Ta Haihuwa Idanuwanta sun kara Budewa. Zulaihat kuwa bata da bakunta ba wanda bata saba dashi agidan ba Hatta Abba ma kuwa Haka zasu zauna dasu Faruq afalo suyi ta Hira suna Dariya Sadiq ne bai Cika Hayaniya ba ammh Shima yana Sakin Jiki Haka Ahalin suke basu nuna kyama ga wanda Yake Bako Duka Daya suke Daukan kowa. Zain kuwa yana waya dasu Umma ba kuma Wanda ya Taba gayamai Zaina ta Dawo,an barshi yarda Alhaji Tsohon yace sai dai kila yaji ajikinsa Domin ya gayama Umma Hankalinsa ya Dawo Gida baisan Dalili ba ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai ya kamallah Abunda yakaisa nan da Sati Biyu zai gama Komai yana Tafe Alhaji Tsoho najin haka ya kira Abba sukayi mgana yace Su Umma su je Chan gidan Zaina Su gyara a Share ko"ina Domin da Zain ya Dawo Aranar ya wuce da Matarsa da ya"yansa Gidansu yakwashe Tsawon Lokaci Cikin Wata kewa wanda zaina ce kadai Zata Gusar mai da wannan kewar Hajiya Mama tace Shawarace mai kyau. Abba na komawa Gida ya gayama su Umma sukace ai ba Damuwa Nene tace Zataji da gyaran Gidan Umma Taji da gyara yarta Umma tace Taji bakomai Tun adaran Abba ya Kira Zaina ya gayamata Halin da akeci na dawowar Zaina Cikin Sati Biyu Da kuma Shawaran Alhaji Tsoho Duk Dokinta sai Taji ya koma Ciki CikinLadabi ta amsa ma Abba Umma kuma su Zareena da Farida Taje ta Fadamawa sukace Hakan yayi wannan Tunani mai kyau ne. Washegari kuma Tun Safe Nene da Farida da Zulaihat da Zareena suka Tafi Gidan Zaina Suka Fara gyara sun iske Cikin kayan abinci akwai wadanda suka Lalace irinsu Dankalin Turawa,da Kwai da Sauran haka acikin Fridge kayan Miya Duk Sun Rube har sun Fa Wari suka kwashe komai suka Zubar suka wanke Wajen suka Fara gyaran Gidan Daya yi kura Domin an Dade ba"a Shigo ba Tanimu Megadi kuwa baki yaki Rufuwa Da Nene ta gayamai Gimbiyan Dakta Zata Dawo sai yammah suka koma Gida suka gayama Abba Abubuwan da za"a kara Tunda Daman yace su duba in akwai abubuwan da babu suyi mgana Kayan abinci wasu basu Lalace ba ammh Wasu kam sai Bola Abba yace Shikenan za"a Cika Store Din Insha Allahu. Umma kuwa Goggo Halima ta Kira ta Shaidamata Halin da ake Ciki Tace Shikenan zata aiko da Isuhunta da kayan gyaran da Zata Hadama Zaina din Umma Tayi ta Godiya kana suka yanke Kiran Umma dai Daga bangaranta Ta Fara sakata Tana Shiga Cikin Ruwan bagaruwa Data Dafa mata da Sakata Shan kayan Marmari da madara da Zuma,Zainar ta Fadamata Data Haihu Farida ta mata amfani da Ruwan bagaruwa Umma ta Jinjina ma Farida duk da Karancin Shekarunta Ta yi ma Zaina Jego mai kyau. Abba ya bada kudi an Cika ma su ZainaStore da kayan Abinci da komai na Bukata kuma an Sauya mata Sabbin Labulai da Zannuwan gado sai wasu kayan Kitchen kayan Daki ma Abba yaso ya Sauya kayan Gidan Gabadaya sai Umma tace Ya bari Zuwa gaba Tunda basu Lalace ba,kwana Biyu da mgana da Goggo Halima Isuhu yazo da Sako Dagachan bai kwana ba ya Juya leda Cike da Tsumin mata sai Turaran Jiki dana Daki,sai Gumbar nasha da Madara da kuma Hadin Zuma kaya dai da yawa,nan da nan Umma ta kimkima takai Dakinsu su Zaina tace nan da kwana Goma Zata Shanyesu Duka ita dai Zaina ba Mgana Domin Tagama Sarewa Da samun kamar Umma sai antona. Dina Duk bata san meke Faruwa ba Taga dai ana ta Shige da Fice sai da Ta Tambayi Zainab Ta gayamata Ranar tayi kuka kamar me ta kara Tabbatar ma kanta Zain bai Dauketa a mata ba Tana Dauke da Cikinsa ammh Ko Sau Daya bai Taba Damuwa da ita ba sai dai Bata Damu ba ta Riga ta sani Allah ne ya kamata Tunda wajen Cikar Burinta ta saba mai Shiyaasa ya barta da Daburanta Tana Tunanin gashi Zaina ta Dawo bata Bakinciki Sai ma Taya zain Murna Datake Tana Tunanin Kila in Zaina Ta kasance Tare Dashi Kila zai iya yimata wani kallo Na arziki ko ba na Soyayyah ba. Shiryan Shiryan Dawowar Zain kadai ake tayi Umma Har mai Dilka ta kira Tayi ma Zaina Domin tace kamar Amarya Haka take so amaida mata ita,Zaina ta Kara kyau Fatar ta da Murje Sai Sheke take Ita kanta Tana Jin Sauyin yanayi atare da ita saboda magungunar datake Sha Ba wanda take so da Muradin gani irin Firstlove Zafeeraa Tazo Gida Sau Daya Haddir ya kawota Taga Zaina ta koma Amarya ai sai ta karkace kai Tana Sakin Guda Zaina na Hararanta su Farida na Dariya Abba ya Dinkama Zaina sabbin Dinkuna Har da su Farida da Zulaihat su Anun kuwa Haddir yace shine Uba Shi yaje dasu Shida Zafeera sukayi musu Shoppig din kayan sawa dana ci Zafeera kuma taki Tafiya tace sai Zain ya Dawo Zasu koma Duk da Daman Sun samu Hutu ne. Har Satin Biyun Ta kare ammh Ba"aji Daga Zain ba sai ranar jumma"a Da Daddare Zain ya Kira Wayar Haddir yace Zai sauka Nageria gobe da Karfe 5pm na yammah zai Sauka Ta Lagos In ya sauka zai Hau Jirgi zuwa Abuja in ya sauka yazo ya Daukesa Jibi kenan Haddir yayi murna Sosai yayi mai Fatan Sauka Lafiya nan Zain din fadamai Abunda ma ya Tsaidashi Wata Takardan ya Tsaya karba ammh yanzu komai ya Zama Ready. Suna mgana ya gayama Zafeera ita kuma ta kira su Umma ta gaya musu Umma na jin haka ta Saka aka Kira mai Kunshi akayi ma Zaina Washegari kuma taje akayi mata gyaran kai Zaina ta Fito kamar Amarya su Umma basu Damu da sanar da Dina ba Tunda suna Tunanin suna mgana ta waya Sai da ta Shigo ne Taga Nene ta Soya Nama take cema ya Shirin Taran yaronta gobe,Sai Dina ta Fara kame kame ammh sai tayi Fuska kawai ta basar Nene ta Fahimci wani abu sai dai Bata Nuna mata ba Koda Dina ta koma Shashenta Tayi kuka Kafin ta Share Hawayenta Ta tashi ta Dan gyara Gidan ta Raasa wa zata Kira sai ta Kira Hajiya Batula ta gayamata ita kuma ta bata Shawara tayi Girki ta kuma ci gayun Taran Megidanta kada ta Damu da komai. Jin Haka yasa ta Fara Shiri Direba ta aika kasuwa yayi mata Siyayyah ta waya ta Duba Girkin Tayi Farar shinkafa da Miyar ganye mai nama sai Kunun Aya ta kuma soya kaza Tayi pepe,Kuma Alhamdulillah Tayi ba Laifi Kunun Ayan ne Zainab ta Taimakamata sukayi Tare,Bayan sun gama ta koma Tana gayanma su Umma Ba wanda bai ji yaji Tsausayin Dina ba Shiyasa da Umma ta kawo Shawaran ko su maida zaina Gidan Gobe da safe ne kawai in Zain din ya Diro ya sameta Chan da Abba yaji sai ya gayama Alhaji Tsoho Shi ya Hana yace su Duba fa su gani yana da wata Mata kuma in sukayi haka basu yi ma Dina adalci ba Domin in Zaina ya ga Halima ya Tabbata Dina Zata Dade bata ganshi ba Tunda Tana da Hakkin akansa abari Zuwa ya kwana Biyu sai su maida Zainar Dakinta Hakan Shine adalci Jin haka yasa kowa yayi Na"am da mganar ammh Banda Zafeera Datace ya kamata Abar Masoyan gaskiya su Sake bai kamata ayi musu haka ba. Koda Jirgin su Zain ya sauka afilin Jirgi na Nmadi Azikiwe International Airport,Abuja su Mama Safiya da Daddyn Abuja suna Zaman Jiransa zain yayi Kiba ya kara Fari Sai kuma kasumba Daya bari Yakara Girma alamun ya samu Hutu da jin Dadi,Dagashi sai jakar kayansa Sai kuma Wata jaka Da yayi ma Firstlove Tsaraba Sai su Umma dasu Abba sai Arman Da kuma Abunda Firstlove ta Haifa yana ji ajikinsa Firstlve ta kusa Bayyana Soon. Mama Safiya ta Rumgume Zain Hakama Daddyn Abuja Cikin Farinciki Ganinsa ya sauya kamar bashi ba,nan suka Dumguma Zuwa Gida Dakin Haddir Dake gidan ya Sauka su Lauratu nata Hidima Dashi sai da yayi wanka ya yi Sallolinsa yaci Abunci Suka zauna ana Hira Yabama Daddyn Abuja Labarin Chan,yana Sanar dashi yana so ya koma Yayi karatunsa na zama Consultant. Barinsa sukayi Yaje ya Huta Saboda Gajiyan Tafiya bayan Shigarsa ne Dadyn Abuja sukayi waya dasu Abba inda suka gayamai Zain ya sauka Lafiya sai Gobe zai kariso Haddir ma Zain din ya kirashi Ya gayamai Shiyasa Washegari Tun Safe Suka Dau Hanyar Abuja Shi da Zafeera data matsa sai taje 10am suna Abuja Zain mamakin ganin Haddir yayi kiba ga Zafeera agefe Abun sai ya bashi mamaki yace Lalle Hadiru an samu Wajen Hutawa. Basu Tsaya ba kamar Zain din yasan akwai abun mai mihummaci Dake jiransa suka Dauki Hanyar Abuja Suna Mota yana ji Zafeera na waya dasu Umma bai kawo komai ba Sai Wajen 3pm na Rana suka iso Bauchi Direct gidan Abba suka Wuce Suna yin Hon Gabadaya su Umma suka yo Haraban Gidan,Zaina Dake Dakin Umma anyi mata Makeup wacce Kawar Zainab tazo tayi mata,Tana sanye da Doguwar Shadda Gezner Taji Stone Work sosai Anyi mata Dauri ta Dauki Kyau Sosai kamar ba ita ba su Anun ma sunci gayunsu Abba ma yana gida bai je aiki ba Sadiq,Faruq,kowa dai yana Gida ita kanta Dinar ta Shirya Cikin Doguwar Rigar material Saboda Cikin Jikinta,Arman ma yaci gayunsa Tunda Da Safe kafin su Haddir su wuce Abuja sun Biyo Ta gidan shiyasa ta san an Tafi Daukosa. Tunda Zaina Taji Hon Taji ta Rasa Natsuwarta Sosai Jinin Jikinta sai ya Dauke na wani Lokaci kadan nan suka barta suka Fice Zuwa Haraban gidan su Saudart nata Ihun murnan ga Yaya Dakta. Tunda suka Shigo Haraban Gidan Zain ke Cikin Farinciki ganim Duka Kannensa da iyayansa suna Jiran Saukarsa Saboda su Tareshi,Nene da kanta ta Bude mai Mota Tana mai oyoyo Rumgumeta yayi yana Fadin Neneta,kafin ya isa ga Umma itama ya Rumgumeta Daya bayan Daya yabi ya Rumgumesu Abba ya Dafa kansa yana mai Addu"a su Jalal Duk sun Nanikemai ya Daga Arman sama yana mamakin Girmasa Dina na gefe tamai Sannu da zuwa ya amsa yana kallonta Daga sama Har kasa ya kauda kai Su Zulaihat da Farida na Baya rike da Anun da Anan sai Lokacin Zain ya kula dasu Da Farko mamakin Bakin Fuska Daya gani yafarayi sai dai kuma su Anun sun sa ya kasa mgana ya Daskare Tsaye Sanye da Riga da wando Blakt and White Sai Doguwar Bakar Rigar Data kaimai Gwiwa da kuma Hula Fecing Cap Dinsa Farida sai da Taga Zain ta Tabbatar da Su Anun shi suka Debo kyau na Dukan kyau kenan. Zain ya Daskere yana kallon su Anun kawai yama kasa mgana Kowa ya kalli Inda yake Kallo Nene Taje ta karbo su da kafarsu tace su Taka su Tafi Wajen zain suna zuwa gabansa yaji kafafunsa sunyi Rauni yaji ya Durkushe gabansu Yana Binsu da kallo Nene ta Kallesu su Anun Tana Fadin"Anun da Anan ku Je wajensa ABBANKU NE..! Mamaki ya kara kama Zain Dayaji kalaman Nene ya Dago Daga kallonsu Anun Cikin mamaki bai samu Zarafin mgana ba Umma tace"Dauke su mu Shiga Ciki Zainullahi zaka ga Komai da idanuwanka..." Jikinsa sai ya Fara rawa Sai da Nene ta Turamai su Anun yaji ya Rumgumesu Tuni yaji wani Natsuwa ya kamasshi Bai kawo cewa Ya"yan zaina bane ammh Yaji Soyayyarsu ya shiga ransa Sosai ya Rumgumesu ya Mike Tsaye Dauke dasu Abba yace su Shiga Cikin Gida sai komai ya Biyo Baya yana Dauke dasu Anun ya Riko Hannun Arman suka Nufi Cikin Gidan Dina Dataji Hawaye ya taho mata Tayi Saurin Sharewa Ta Bi bayansu Umma. *Janafty...* 8/10/21, 6:44 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣8️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Dukkansu suka Nufi Falon Abba,Kowa kaga Fuskarsa Cikin Farinciki da Annuri,Suna Shigowa Falon kamshi ya Daki Hancin Zain,Ga kamshin Girkin Ga na Turaran kamshin da suka Turara gidan domin abinci kala kala suka yi Saboda Dawowar Zain din. Kan Daya Daga Cikin kujerun Falo Zain ya yada Zango Dauke dasu Arman dasu Anun Gabadaya su Umma kuwa zagayesa sukayi Cike da Farinciki wanda ya kara bama Zain mamaki su Anun yake ta kallo suma suna makale Dashi Anan kuwa Lamgwabewa Tayi saman Kirjinsa Kamar tataba ganinsa kalmar da Nene ta Fada Shine Abunda yake mai yawo kuma uwa uba su Anun Daya kasa Dauke Idanuwansa Akansu yana ganin Tsabar kamarsu da Arman sannan kuma Suna mai kama da Firstlove Wanda Zuciyarsa ta Fara rawa nan take. Cikin Sanyin Jiki ya Dago yana Bin Kowa da kallo kafin ya Sauke kallonsa kan su Farida Cikin Alaman Tambaya da Rashib Sani yace"Umma Naga bakin Fuska baki Mukayi..? Kuma wadandan yaran fa Umma..? Naji Nene tace suje wajen Abbasu kuma ni dai nasan Zareena ba yan Biyu ta Haifa ba kuma Zafeera bata Haihu ba Ballatana nace ya"yanta ne.." Umma ta saki Mirmishi Farinciki Kafin ta karisa kusa dashi Ta Dafa kan Anun Tana Fadin"Ga Fatima Takwarata Anun kenan sai Maryama Anan Dukkansu ya"yanka ne Zainullahi.." Mamaki da wani irin Sakewar Zuciya ya samu Zain Cikin mamaki yake kara bin su Anun da kallo kafin ya Dawo da kallonsa kan Umma ya kuma Kara Bin Kowa da kallo ganin Fuskar kowa Cikin Farinciki yasa ya kalli Abba yana Fadin"Abba kaji me Umma tace..? Taya suka zama ya"yana..? Abba ya gyada kai yana Fadin"Da gaske take Zainullahi..Ya"yanka na wajen Halima ne.."Zain sai yaji kamar Kiftawan mgana Abba yace Halima Idanuwa ya Zaro yana Fadin"Halima...? Wata Haliman Abba...? Nene ta karbe da Fadin"Wata Halima muke da ita anan gidan kuma Yarona..? Halimar ka Firstlove kamar yadda kake Fadin Ya"yanta ne Daga Cikin Data bar gida dasu..Aisha Farida da Zulaihat suka Taho Dasu.."Ai Nene bata gama Nuna mai su Farida ba Zain ya Mike da Sauri Anun da Anan ya Sauke Arman kuwa sai da ya kusa Faduwa Zainab Tayi Saurin Tareshi kada ya Fadi agaban Farida Zain yaci Burki Kirjinsa na Dukawa kamar zai Faso Rigarsa ya Fito Saboda Fargaba da Rawan Zuciya gaban Farida ya Zube Cikin Rawan Murya Dana Zuciya yake Fadin"Don Allah..Baiwar Allah ki Taimakeni ki gayamin inda Firstlove take..Kada ki gayamin Wata mgana da Zata Nesantani da Firstlove ki gayamin ina kika ganta ina kika ga ya"yana..! ? Don Allah kada ki Fadamin mganar da Zatayi Sanadiyar Rasa Numfashina Gabadaya Domin Saura na ne agabanki Zaina itace Rayuwata itace komai nawa saboda ita Kalli yadda na Dawo Ki Taimakeni ki gayamin koda Labarinta ne ko Zanji Sanyi.."Yafada Idanuwansa na Cikowa da kwallar Fargaba kada ace mai Firstlove bata yau agidan Duniya.. Kowa afalon sai da yaji Tsausayin Zain Dina na gefe Tana Sharan kwallah Farida da Taji kamar tayi kwallah Ta saki Mirmishi kafin tace"insha Allahu Bazan taba gayamaka Abunda zai Saka Numfashinka ya Bar gangan Jikin ka ba..Ka Tashi Tsaye Ba zo garin nan ba sai Tare da Halimarka kuma ayanzu hakama Tana Cikin Gidanan.." Wani Sakin baki Zain yayi kamar Wawa kamar yana Koyon mgana yace"Tana cikin Gidan nan kuma..? Umma tace"Kwarai da gaske...Halima..Halima Fito Mana.."Tafada da Dan karfi Kowa sai ya Zubama Kofar Dakin Umma ido Harda shi Zain din da Sanyin Jiki yasaka kafafuwansa yin sanyi. Zaina Dake Kofar Dakin Umma Hawaye ya gama Bata mata Kwalliyarta Tana jin Duk Abubuwan Dake Faruwa a Falo Duk Zakuwarta na Haduwa da Abun Sonta yau taji ta kasa kunya Mai tsanani ya Rufeta da nadaman Tafiya ta barsa,Dakyar take Daga kafa Saboda kasala da Rashin kuzari Taja Kofar Umma ta Fito sai gata ta Bayyana Zain daya kafe wajen da ido kamar Zuciyarsa zata Fito Haka ta Harba Daya ga Zaina ta Fito Wani irin Jim yaji kamar zai Mutu saboda wani Abu Daya shiga Zuciyarsa na Murna da Farinciki. Kasa Dago kanta Zaina Tayi saboda Kukan Dayaci karfinta Nene ta kalli Zain Dayayi mutuwar Tsaye yana Bin Zaina da kallo Daga sama Har Kasa,Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"Yarona ga Halima...Kayi Hakuri ta Dawo Tun last Month..Alhaji Tsoho ya hana agayamaka saboda ka samu Damar karisa Abunda yakai ka..Anun da Anan sune Cikin Da ta bar Gida dashi Farida da Zulaihat suka Rakota Labari ne mai Tsawo sai ka natsa Zakaji Komai.."Shi dai yaji Nene na mgana ammh bazai ce ga Hakikanin me tace ba Shi dai kawai kamar Walkiya sai gashi agaban Zaina wanda bai san yaushe yazo gabanta ba Cikin kallon kamar in na Rufe ido zan Daina ganinki yake mata Ganin Taki kallonsa yasa ya Daga bakinsa yayi masa Nauyi yace "Firstlove....!. "Firstlove...! In har kece ki Dago Idanuwanki ki kalleni Dashi kadai zan gane ke nake gani ba Gizon da kika sabamin bane.." Zaina Dataji kafafuwanta sun Fara rawa Ta Dago Idanuwanta Cikin Zubar hawaye ta saukesu Cikin na Zain cikin wani irin Soyayyah Tsausayi kewa da kuma Muradi da kauna Hade da Zazzafar Kauna mai Zafi da Radadin kewa acikin Zuciya haka suke kallin Juna Zaina Data gama Raunana ta Lamgwabe kai Zain kuma Hannuwansa na rawa ta saka ya Riko Kafadunta yana Fadin"Firstlove Daman zan sake ganinki arayuwata..! Ina kika Tafi kikabar Mahadin Rayuwarki..? Wanda kika san cewa in baki bazan iya Rayuwa ba.."? Yafada Twagayen Hawayen Farinciki suka Zubomai Zaina Data gama jin kunya da kalaman Zain ta Bude baki Cikin Kuka tana Fadin"Ka...ya..fe...min First...Love...ka..!bata ida mgana ba Yayi jawota Jikinsa da karfi yayi mata wata Rumguma mai Zafi Kamar zai Tsaga Kirjinsa ya sakata itama sai ta ware Hannayenta ta Rumgumesa Ta Fashe da kukan Data ke rikewa Shekara Daya da wani Abu tama manta da Tarin iyayansu Dake wajen haka suka kamkame juna suna kukann Farinciki. Su Umma Kai kawai suka kauda suna Sharan Hawaye Zafeera kuma Tafi ta Farayi musu Cikin Taruwan Hawaye Tana Fadin"Finally...Yau dai Komai ya kare ga ya Dakta ga Ukti...Allah ya bar wannan kaunar har agidan Aljannah.."Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Farida ma Baya ta juya Tana Sharan Hawaye kewa da Son ganin ya"yanta da iyayanta na Damunta Hakana Zulaihat Itama Tana Hawaye Tana Dariyan Farimciki Dina kuwa kukan Tsausayin kanta Take ba wanda ya sani ta samu Ta Sulale Zuwa Shashenta. Anun da Anan da suka ga Zain da Zaina na kuka sai suka Nufesu sukaje suka Rungume kafafunsu ssuma suka saka kuka atare sai falon ya Dau Dariya Abba na Dariyan Farinciki yace"Sai ku hakura da kukan Tunda ga ya"yanku nan sun Fara suma.." Nene kuwa baki ta Rike Tana Fadin"oh yaran zamani da wayansu ake haihuwansu ji yara wai sun san iyayannsu na kuka.."Aka saka Dariya kowa kagani Cikin Farinciki atare Zaina da zain suka Duka yana Share mata Hawaye yana kallin yace"Nagode Firstlove...Kin Saka Sunayen da suka Zama Ra"ayina.."Mirmishi ta sakarmai Dukkansu suka Taru suka Rumgume yaran Cikin Tsananin Farinciki Zaina ne ta Hangi Arman na Tsaye yana Kallonsu Kamar zai yi kuka ta Dago kanta Tana Fadin'Taho mana Arman.". Sai da ta Fada kana kowa ya Lura dashi da gudu kuwa yaisa garesu Shima Zaina ta Hadashi Dashi suka Rumgume sai Zain yaji ya kasa mgana kamar ya Hadiye zaina dasu Anun haka yake ji sun Dade ahaka sai dai Nene tace ya isa haka ya tsshi yazo yaci Abinci Zainab da Zulaihat suka Shiga Kitchen suka Fara Jido Kololin abinci Zafeera kuma ta Shimfida katuwar darduman atsakar Falon Domin Kayattaciyar Walima suka Shirya saboda wannan Ranar. Zain yana Rike da Hannun Zaina kamar Wani zai kwaceta ko kuma zai waiga yaga bata gani yake kamar mafarki yake wanda baya Fatan ya Farka Daga wannan Mafarkin mai Dadi yana Rike da Anun da Anan kamar zai maidasu Ciki ganin haka yasa Zaina ta Dauki Arman saman Jikinta Duk kunyar su Umma yau nemansa Tayi ta rasa kugu da kugu suka zauna ita da Zain suna Jifan juna da wani kallo wanda su kadai suka bar ma kansu sani. Ko abincin ma Sama sama Zain yaci yana ta bama su Anun abaki Da Nene taga bayacin Abincin sai tace"Yarona kaci Abinci mana..Kyalesu Anun sun koshi fa.."Zain ya Tsaida kallonsa kan Zaina kafin ya Dawo da kallonsa kan Nene yana Fadin"Neneta don Allah ki gayamin gaskiya Shin da gaske ne gani ga Zainata ko kuwa Dai mafarki nake yi..? Gabadaya suka sakamai Dariya Harda Zaina Zareena Dake gefensa Ta tsunguleshi Acikinsa sai da yayi yar kara Domin yaji Zafi Cikin Dariya tace"Yanzu ka yarda ba mafarki bane ko Sai na kara maka da mari..? Hararanta yayi yana Fadin"Wazaki mara..?Lalle kuwa da kin gane baki da wayau kuwa gaban ya"yana ki mareni ko ban Rama ba Jalal Son zai Ramin ko yaron Uncle..? Jalal ya washe baki ya Daga kai Bai san me akace ba ya cika baki da Naman gabadaya aka kara saka Dariya Haddir yace"Ku kyaleshi mafarki ne.."Hararansa yayi yana Fadin"Kai nifa Haushinka nake ji ace Firstlove ta Dawo baka Kirani ka Fadamin ba..? Kafi kowa sanin yadda Na kusa raaa Raina Saboda Rashinta gaskiya baka kyautamin ba.."Umma tace"Umarnin Alhaji Tsoho ne..Baka gashi kaje ka Dawo ba kuma ka sameta ba ni banga Abun Damuwa ba.." Kallonsa ya maida kan ZAINA itama shi Take kallo Cikin wani irin yanayi ya kara matse Hannunta Har sai da ta motsa Cikin Sanyinsa Ya kai bakinsa kusa da kunnuwanta yana Fadin"Naji ajikina Daman duk inda kike kin kusa Bayyana gareni sai dai yaushe ne bansani ba..Ki yafemin Firstlove ki kuma yarda da so Dayane ke na baiwa shi.."Zain ta Kallesa ido Cikin ido kafin Ta saki Lallausan Mirmishi ita me zatace..? In tace Firstlove baya kaunarta bata mai adalci ba Duk iya Labarin Halin Daya shiga bayan barinta gida sannan Umma da kanta ta bata Labarin da Dina ta Fallasa na kai Zain gidan Boka,ko ba Domin haka ta Riga yanzu ta kara Gogewa daRayuwa ta kuma yardan ma kanta Mace sai da juriya. Mirmishin Data sakarmai ya kara Narkarmai da Zuciya ya Bude baki zai yi mgana ta Girgizamai kai Tana Fadin"Ba sai kace komai ba Firstlove...na yadda da Duka Abubuwan da suka Faru kaddaran Zuwan Arman Duniya ne ni kuma bazan Taba ja da ikon Allah ba.."Mamakinta ya kara kamashi ya saki baki yana kallonta Abun sai ya bata Dariya Tana Dagowa suka Hada ido da Umma sai Tayi Saurin kauda kai Zain ya Duke yana mata mgana ta Shareshi Sai Lokacin ya ankare dasu Abba ma Karamar Dariya yayi yana Fadin"Dole fa yau su Abba su Dagamin kafa..Shekara Daya Da wani abu cikin na Biyu ban sakaki a idona ba Tabdijam suma sun san akwai mgana..! Haka dai Taron cin Abincin ya Tashi Cikin Farinciki Zainab da Zulaihat suka kwashe komai suka maida Kitchen kana aka sake komawa saman kujerun Falon aka zauna Wasu kuma suna zaune akasa irinsu Faruq da Zainab da su Saudart Zain ya matsa sai Zaina ta bashi Labarin Inda taje bayan ta bar Gida Tayi tayi ya bari sai gobe yace bai yarda ba Tana kusa Dashi yana Rike da Hannayenta Su Anun na kan Jikinsa Itama Arman na kan Jikinta har yayi barci ba wanda bai ji Zaina Ta Burgeshi ba ganin yadda bata Bambamta Arman dasu Anun. Zaina ta Fara bama Zain Labarin Barinta gida Tundaga Fitarta Haduwa da Farida da duk Abubuwan da suka Faru Zulaihat kuma ta karesheu da bashi Labarin Shafsson da Suby Zain kafin ma su gama ya Fara Huci Cikin Zafin zuciya da Kishi yace"Allah ya soshi..Daya kuskura ya Tabamin Mata wlh da sai na saka duka an karar da Danginsu Wlh.."Kunya ya kama su Umma Haddir ne ya Dakeshi a Kafada yana Fadin"Ko kunyan su Abba babu..? Sai Lokacin ya Fara sosa kai yana Dariya su Anun ya Sauke ya mikama Umma Anan don Har ta Fara Barci ya nufi inda Farida ke Zaune ya zauna Kamar me Neman gafara yafara Fadin"Nagode sosai Antynmu..Allah ya saka Miki da alheri kin Daukin Nauyin da Nine ya kamata na Dauka yadda kika kularmin da Zainata da ya"yana Allah ya kula dake da Duka ahalinki Aranar Gobe kiyama Allah yayi Miki sakamako da Gidan Aljannah Bakina yayi kadan Wajen Gode miki Sai dai nayi Fatan ki gama da Duniya Lafiya.."Kowa ya rika amsawa da Ameen Idanuwan Farida suka kawo kwallah Cikin Mirmishinta kamar kullum Tace"Bakomai Wlh..Sa'adiya kamar kanwa take gareni kuma Sanadinta yau duka mun zama Daya.." Zain yace"Wlh Hakane..Ina Fatan nima Zan zama kaninki Ki zama Antyna bawai Firslove bace kawai zata rika kiranki da Anty Farida ba.."Yafada Cikin Zolaya Farida tace"A"a Anty Aisha Farida duka naku Duka Ban fa kada ku kwacema su Anun Antysu.."Gabadaya su Umma suka saka Dariya saboda yadda Ta Fadi mganar Shima Zain sai da ya Dara gaban Zulaihat ya koma ya zauna yana kallonta itama kuma sai Tayi Saurin sadda kai Cikin jin Nauyinsa Cikin Sanyin murya yace"Zaki min alfarman na zama yayanki ke kuma ki zama kanwata..? Falon sai ya Dau Shuru Zulaihat Ta Dago Cikin Taruwan kwallah tace"Me zai hana..? Ni da na rasa kowani gata ahakan ma ina Daukan kaina kamar mai Cikakkiyar yanci ne zama na acikin Dangin Sa"adiya.."Hawayenta suka Zubi Sharr Zain ya saka Hannuwansa ya Share mata yana Fadin"Kin Daina kukan Maraici da Rashin gata Daga yau..Ni zan zame miki yaya Umma ta zame miki uwa ita Da Nene Alhaji Tsoho da Hajiya Mama su zame miki kakani Abba kuma ya zame miki Uba su Faruq su zame miki yan"uwa da Yardan Allah.."Zulaihat da Farinciki ya saka ta saka Abba ya gyada kai yana Fadin"Da yardan Allah kuwa kidaina kuka..Zamu kai kije garinku Ko domin sanin kina Raye ammh Tun kafin Zain ya Furta munyi mgana zaki zauna Tare damu da Alhaji Tsoho.."Kowa yaji wannan Mgnar Musamman ma Zaina da Farida da suka Tashisuka Rumgumeta suma kamar su saka kukam Nene ce ta lura Tundazu ba Dina awajen yasa tace'Wai ni kam Jama"a ina Dina take...? Zainab tace"Ta koma Shashenta Tun Dazu.."Kowa sai yaji ba Dadi Abba ya kalli Zain yana Fadin"Ka tashi ka karisa Shashenka Zainullahi..Ko bakomai matarkace tana da Hakki akanka kuma ka barta Wata Takwas Tana zaman Jiranka Tashi Kaje.."Zain dayaji kalamam Abba kamar Darma ya samai Cikin Firgici yace"Abba tare da Zaina zamu tafi ammh ko..? Abba ya Girgiza kai yace"A"a kaje Wajen Matarka Daman ai iyayanka sunje chan gidan naku sun gyara komai Zuwa jibi Zasu rakata ita Sa"adiyan gidanta Kaga in mukayi haka Allah bazai kama mu da Rashin Adalci ba.." Nene tace"Tabbas..Kayi Hakuri yarona tashi kaje..Kada damu da Sa"adiya ita Ta fahimcemu.."Zain Dayaji kamar yayi kuka yama kasa mgana Abba ya mike ya wuce Shashensa Haddir kuwa Dariya ce ta kusa kamashi Shima ya mike yana Fadin Zafeera tazo su Tafi Mikewa tayi tana yi ma su Umma sallama Tana kallon Zaina Wacce ta marairaice Tana kallon Zain da Bacin rai suka bayyana saman Fuskarsa,Basu musu mgana ba suka wuce bayan sun yi ma su Farida sallama. Zulaihat da Zainab suka Dauki su Anun Nene ta Dauki Arman zuwa Dakinta Umma tabi bayan Abba Sadiq da Faruq kowanne ya mike suka Zuwa dakinsa Zareena ta Tashi ta Dauki Jalal da yafara barci su Saurdat kuma Nene ta tafi dasu Dakinta Lillte Umma na Hannun Farida ne Falon ya watse aka bar Zain da Zaina suna zaune suna kallon Juna. Ganin yadda Bacin ransa ya bayyana ne yasa ta Marairace Tana Fadin"Haba mana Firstlove kayi hakuri Ka tashi ka Tafi..Ban Dade da Dawowa ba tafini hakki akanka.."Zain Daya ji kamar zaina ta watsa mai Ruwan zafi ne ya Dago a Zafafe yana kallonta kafin yace"Is ook..Daman Dake aka Hada baki ko..? Ta ina tafiki Hakki akaina Shekara nawa Bamu ga juna ba yau din ma baza abarni naji Dumin ki Ba Zainata kin ga anyi min adalci kenan..? Yadda yake mganar ya kara Raunanata wani sonsa da kaunarsa yana Ratsata ita kanta karfin Hali take ammh Tana Bukatar Mijinta akusa da ita Cikin Tsausayinsa ta Dora kanta sanan Kafadarsa Tana Fadin"Am sorry...Kayi hakuri kaji Firstlove dina mukayi hakurin wadannan Wattanin ballatana Hakurin kwana Biyu..? Bai mata mgana ba illah Kanta Daya Daga ya Mike Daman kayansa Chan Shashen Dina Aka shiga dashi Tana ganin haka tasan Ransa ya baci Tana Mikewa Ta Rumgumesa kamkam ta baya atare suka Sauke Numfashi Sun fi Minti Biyar ahaka kafin ta sakeshi gabansa tazo tayi Dage ta sakarmai Sumba mai Tsawo kafin tace"Sai da safe Firstlve..Ka kularmin da kanka kaji ko..? Baisan Sadda ya Daga Mata kai Mirmishi ta sakarmai ta wuce Zuwa Dakinsu ya Bita da wani irin Kallo ta san yana kallonta Shiyasa take wani kara Juyamai har ta Shige yana kallonta Kamar wani gaula kafin ya girgiza kai ba Haka rai yaso ba ya Fita Zuwa Shashensu Abun mamaki yana Shiga yaga Dina zaune afalo ganinsa yasa Tayi mamaki Domin bata saka Ran ganinsa ba,Kallo Daya yayi mata ya Kauda kai ya kama Hanyar Dakinsa sai yaji muryanta Tana Fadin"Ina tayaka Murnan Dawowar Zaina. "Cak ya tsaya Lokaci Daya yana waigowa Cikin Mirmishin Da Tun da sukayi aure bai taba yi mata ba Taga yace mata,"Nagode..."Daga haka ya Tura Kofa ya Shiga Dakin ya kullo Tabishi da kallon so da kauna da kuma Tsausayin kanta Ksfin Ta Kada kai ta Shige Bedroom Dinta Tana Daure Abunda Taji acikin Ranta,Shi kuwa zain ranar bai iya barci ba kwana yayi yana Sallar Godiya ga Allah daya bayyana Masa Firstlove dinsa washegari kuwa Daga sallar asuba ya Nufo Shashensu Umma Har Dakin su Zaina ya iskesu ita da Zulaihat da Zainab Zaina tana barci su kuma suka Fice suka barsa Sai dai Tana Barci Tajita Cikin Jikin mutum Tana Farkawa ta ganshi bata isa ta hanashi Abunda Ranshi ya Rayamai ba Ta Biye Mishi suka Maimata Abunda suka Dade basu yi ba koda bai mata komai ba ammu ya yi Romamcing dinta Sosai Anan yayi Breakfast dinsa duk kuwa da Koran dasu Nene sukayi mai yaki Tafiya yana nakike da Zaina da su Anun sai Wajen goma ya tafi yayi wanka yazo yaje Zaina tazo ta rakashi Gidan Alhaji Tsoho Umma ta Hana Dole ya Tafi dasu Anun da Arman chan din ma Nasiha Sosai su kayi ma Wannan karon bakinsa har kunni Shi kan Duka Damuwarsa ta kare yana Gidan Haddir yazo suka Tafi Gidansa Dashi bai Dade ba ya Tafi bayan yayi ma Zafeeran Nasiha a matsayinshi na yayanta Sai yammah ya koma Gida yau din ma sai da Abba yayi da Gaske ya bar Shashensu Umma ya koma Shshensu yana Manne da zaina kamar wani xai kwaceta ita dasu Anun Dina kuwa sai dai Hakuri Domin ta zama yar kallo. Washegari kuwa Tun Safe Zain ya kwashi Zaina suka koma Gidansu yace basai an Rakata ba baya Bukata Umma taso ta hana Abba yace ya Dauketa suje ai matarsa ne Dina Kuwa tana Shashenta Tana kuka Kukan Nadama da Rabuwa da Masoyi Domin tasani ita da Zain sai kallo Daga nesa Ganin yadda yake wani Rawan kafa ne Nene ta karbi su Zaina tace gobe za"a kawosu. Fadin irin Soyayyah mai Hade da kaunar da Zaina da zain suka Nuna ma juna bata Baki ne kuma sai na Cika wannan littafin ban gamashi ba mai karatu kadai zai iya Hasashen Abun Tanimu megadi Daya ga Zaina Har sai da yayi kwallar Farinciki addu"a kuwa tashashi kamar ya goyata Ranar Akan gadon Auransu Da suka Dade basu Haushi ba sun Hau shi kuma Sun Raya sunnar Ma"aiki sosai Gyaran da akayi ma zaina sun kara Taimakawa wajen Fitar da Zain Daga Hayyacinsa ya Dinga Sambatu Da kukan Don Allah kada ta kara Barinsa Ssi da Tagaji ta Rufemai baki kana yayi Shuru. Sallah kadai ke Fitar da Zain Daga Gidan Tunda ya Dawo bai Taka yaje ko"ina ba basu kara Fita ba sai da sukayi Sati Daya Cur kana suka zo gidan Abba Shima Dalilin Rasuwar Kakar Dina achan Sudan Wanda kwamishina ya kira Zain ya Rokeshi ya bar Dina su Tafi saboda Taga Danginta na chan Shine Dalilin Zuwan nasu kowa ya gansu sai ya kara kallonsu Saboda kyan da sukayi Zain Tuni Zaina ta saka ya aske wannan gashin bakin da Sajen yayi kiba ya Fara maida Jikinsa Su Anun Kuwa Daman yaye su kawai Nene da Umma sukayi suka Hada da Arman ganin yaran basu da Rigima Iyayansu na chan na cin Amarci Koda Zain yazo ya gayama su Abba Rokon kwamishina Abba yace Shima ya kirashi ya gayamai Alhaji Tsoho ma yace Ya barta Tatafi Taga Danginta Zain bai Damu ba yace Allah ya kiyaye Hanya. Zaina Da kanta ta Shiga Har Shashen Dina suka gaisa Tayi mata gaisuwa ta amsa Tana Sharan kwallah ga Cikinta ya girma Domin ya Shiga watansa na Bakwai sai Ta bama Zaina Tsausayi Domin har Fada sukayi da Zain akanta Kan tamai mgana ku Dubata ya Rika Zuwa yanayi ammh yace Kada ta karamai mgana babu Ruwanta,Dole ta Kyaleshi tunda Haka ya zama Sai yau Zain ya Taba Yin mgana Datafi Daya da Dina Bayan yayi mata gaisuwa kuma yace ta Shirya Gobe Babanta zai aiko da Direba ya Dauketa ta Chan kano Zasu tashi Zuwa Chan Sudan din ya kuma bata kudi 100k yace ta Rike a Hannunta Dina taji mamaki Sosai sai ta Danganta hakan da Dawowar Zaina Bata san Cewa kawai yayi Ra"ayi bane ganin Zataje ganin Danginta ya kamata ya Fita Hakkinta. Washegari Kwamishina ya aiko da Direba aka Tafi da Dina bayan Tayi ma su Umma sallama Arman wajen Nene ta barsu suka Rabu kan in ta isa Zata kirasu ta Hadasu da Hajiya Maimuna suyi mata gaisuwa Har Motarsu Ta bar Haraban Gidan suna mata Fatan Allah ya kiyaye Hanya Ta Dauki kaya da dan yawa Tunda zata kwana Biyu achan Taga Dangi Domin ta Dade bata je ba,Koda Tatafi Zain bama zo ba sai da yammah Suka zo shi da Zaina Saboda Tafiyar Zareena Gobe da Zuwan Jawaad wanda nan zai kwana Gobe zasu hau Jirgi Zuwa Lagos ta chan zasi tashi Zafeera ma agoben Haddir zai maidata makaranta Shiyasa suka zo Gidan Abba sukayi sallama da Zarrena nan suka iske ma Zafeera Tazo sallama dasu Umma tare suka Fita Zuwa Gidan Alhaji Tsoho sai Dare kowanne ya Dauki Matarsa Zuwa Gida Su Anun dai suna Wajensu Umma Zain Dayaji An yayesu Sai da yayi Fada wai sun yi yara dayawa Umma tace Kaniyarsa ai da ya Dauki Matarsa bai Tuna da yaran ba sai Lokacin yaji kunya. Zareena sun Tafi hakama Zafeera Haddir ya maidata har kano Gidan Inna Rukayyah Sallaman kauna yasa nan ya kwana sai Washegari ya dawo Gidan Abba ya Rage Daga Zainab sai Zulaihat da Farida Duk kuma sai sukaji kewa Domin Sadiq ma ya samu aiki a kamfaninsu Abba Faruq kuma sati mai zuwa zasu koma makaranta Shida Sadiq karami,Zain kuma da Zaina suna Gidansu suna Cin Soyayyarsu sai da Zain yayi Da gaske ya koma Bakin aiki Kamar dai Baya kafin ya Duba Patient Goma sunyi mgana yafi sau Biya Suna Tambayan Lafiyan Juna Dina kuma Bayan sun isa sudan ta Kira Umma sun yi mgana da Hajiya maimuna sun mata gaisuwa har Abba ma ya gaisa dasu Ta kuma Kira Hajiya Mama ita da Alhaji Tsoho suksyi musu Ta"aziya. Shine zaina ta matsamai sai da ya Karbi Lambar Dina ya kira Yayi mata gaisuwa kuma Ya bama Zaina ita tayi mata Bayan sun yima Hajiya maimuna Tana Ta godiya da saka albarka Tana kuma yima Zain barka da arziki Da dawoewar Zaina ya amsa baki har Kunni Dina Ta Fara Tunanin Lalle Zaina itace komai na Zaim Tunda Dalilimta yau har yana Kira yayi mata gaisuwa Ita Da Hajiya Batula dasu Waleeda da Kwamishina suka Taho Sudan dim ammh Su zasu Dawo su barta sai Tayi wata Daya Dayake daman Duka Dangi An gaya musi Dina tayi aure har wasu na Fadan ba"a gaya musu ba banda Kakar Dinan Data rasu ba Wamda yasan Abunda ya Faru Shiyasa koda suka ganta da Ciki basu Damu ba. Bayan Sati Biyu da Tafiyar Dina Farida ta Fara Tunanin Gida da Cin Dacin Rayuwar Data gudanar Ta Farajin Zata iya komawa Gida Domin Taga ya"yanta da Iyayenta Alhaji Badamasi yanzu tama Daina Daga Kiransa Uwar Mata kuma bata kara nemanta ba Tana Jiran Ta Dawo da kanta kamar yarda Boka yayi mata karya Farida Sai ta Wuni kuka Cikin Damuwa duk su Umma Na lura da ita ana Jira ta Furta Damuwar da kanta sai gashi ta samu Umma tana kuka Tana gayamata Tana son ta koma Gida Cikin jin Dadi Umma tagayama Abba Shi kuma ya gayama Alhaji Tsoho wanda ya bada Umarnin ashirya Tafiya Gombe cikin Lokaci kuma Hardashi zai Tafi Duk da ya Dade bai yi Tafiyar Mota ba. Da zaina taji Labari tafi Kowa Murna Zain shi ya Tsara Tafiyan Ranar asabar Saboda aikinsu,Duka Gidan zasu Tafi Yara ne kadai za"a barsu wajen Hajiya Mama da Tabawa Ranar Jumma'a Su Faruq jirginsu ya Tsshi a Lagos Ranar asabar da Safe kuma Tun Misalin karfe 8:39am na safe suka Dauki Hanyar gombe,Motar Abba da Direban ke Tukasu Abba ne agaba sai Alhaji Tsoho saboda kafarsa kada ya matsu. Motar Zain kuma Zaina da Farida Da Zulaihat sai Nene da su Anun Da Arman Motar Haddir kuma Umma da Zainab da Sadiq sai Anan Dake barci ajikinta Suka Dauki Hanyar Gombe su Baban Kaduna duk sun san da Tafiyar sun bisu da Allah ya kiyye Hanya sun yi Gudu Bisa Hanya Wajen 12pm na Rana suka Shigo garin Gombe Lokacin Tuni Farida ta Fara kuka ganinta a garin Data Fidda rai da Dawowa garinn Lokaci Daya Abubuwa Dadama suna Dawomata kamar yanzu Abun ke Faruwa. *Kuyi hakuri Ban cika alkawari ba..Wlh Bamu da wuta bana da Chaji wannan Ma dana samu bashi da yawa ammh da Zarar na samu Chaji Zaku kara jina da yardan Allah..* *Shakira...* 8/12/21, 8:31 AM - Buhainat😝: *ZZ...B22️⃣9️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* "Farida ita ta Dinga yin kwantace har kofar gidansu wanda Motarsu ce agaba sai tasu Alhaji Tsoho na Biye dasu abaya. Farida Tayi matukar mamakin ganin yadda gidansu ya koma Duk da abaya tasan suna da Rufin asirin Allah ammh Yadda Gidan nasu ya koma ya bata mamaki an kara Fadadashi an karamai Girma an Sauya tsarin get din Gidan Daga karami Zuwa Babba Da farko ta Fara Tunanin,kilama ba gidan bane sai da ta kwankwansa get din Sabon megadin ya leko suka gaisa Data gansa sai Jikinta ya karayin Sanyin Tambayarsa Tayi Sunan Mahaifinta ko nan ne gidan yace mata Eh bai yi gaddaman bude mata get ba Ganin yadda take diban kama Sosai da Alhaji Duk da bai Taba ganinta ba ya Tabbata tana da alaqa da ahalin Gidan Get ya Bude musu suka Sulala Da Motocinsu Zuwa Haraban Gidan Farida bin Ko"ina na Gidan da Kallo Tana ganin yadda aka gyara komai na Gidan ba yadda Tatafi ta barsa ba,Firftowa sukayi Daga Mota Har da Alhaji Tsoho yana Dogara Sandar sa Farida na Tsaye ta kasa shiga Hawaye kawai take Sharewa Umma ce ke Lallashinta da bata kwarin Gwiwa Har ta samu Damar Fara Tafiya Tana tunkaran Kofar da Sadasu da Cikin Gidan Duk da itama an sauyata wannan Chanjin da Farida Ta gani haka kawai yake sata Faduwar gaba. Tura Kofar Falon Farida Tayi Bakinta Dauke da sallama Cikin Rawan Murya su Umma na Binta abaya su Mazan sun Tsaya Daga waje Tukunnah,Suna Shiga Babban Falon babu kowa Tsit kamar ba Motsin Mutane Sai dai Falon ya kawatu da Kayan More Rayuwa Farida sai Bin Ko"ina da kallo Take Tana jin kodai Tayi kuskure su Mami sun Tashi Daga wannan Gidan ne bata sani ba..? Bata samu amsarta ba Wata yarinya da bazata wuce Shekara Biyu da Rabi ba Ta Fito Daga wani Daki Dauke da Teddy a Hannunta Tundaga Nesa Farida ta sakarmata Ido Tana kallonta Cikin wani yanayi kamar yadda Itama yarinya ta Lura dasu ta tsaya Tana kallonsu Farida hawayenta sun kara gudana wanne dai ba Hassana bace kuma ba Usaina bace Domin yanzu sun fi haka girma To wacece..? Duk yadda akayi Ahalinsu ne domin Taga Tsananin kamarsu da Zahra sai dai Tafi Zahra Haske da Kuma Dogon Hanci. Yarinyar ganin Bakin Fuskokin da bata sani ba sannan kuma Taga Farida Wacce Maminta ke yawan nuna mata ita a Hoto Sai Taji Tsoro ta Ruga Zata koma Daki Tana Kiran Mama mama Anty..! Haka take Fadi karaf suka ci karo da Anty Yaha ta Fito Daga Dauke da Karamin Kofi a Hannunta Tana Fadin'"Aisha Farida taho ki karishe shan T..."mganarta ta makalene da karon da sukayi da yarinyar Har da ta kusa barar da Tea din Dake hannunta Cikin Fada tace"Kinga gani ko..? Kirika Tafiya ahankali mai Sunanki Tana da Natsuwa da Hankali" Tafada tana Dan Mirmishi bata ma Lura da su Umma Dake tsaye ba Farida kuwa Tana kallon Anty Yaha tana Jin wani kuka na Tsso mata sai ta saka Mayafinta Tana Toshe bakinta Yarinyar ta Dago Daga Jikin Anty Yaha Tana Nuna mata Farida Tana Fadin"Mama..Anty ce.."Tafada Tana nuna Mata saitin su Farida Anty yaha ta Dago da kanta karaf suka Hada Four Eyes da Farida ai sai ta zabura Taja baya Lokaci Daya Tana Sakin Kofin Dake hannunta Tea din ya Bare sai da Yarinyar ta Tsorata taja baya Cikin Tafiyar Mamaki da wani Rashin Kuzari Anty Yaha ke Tafiya Tana Nuna Hannunta kan Farida baki na rawa tana Fadin. "Ais...Aisha...Fa...Farida....! Take Fada da son Tabbatarwa Aisha Farida Da Kewar Gida da komai na Rayuwarta ya Dabaibaye Rayuwarta yasa bata san sadda ta kwashi Gudu ta Fada Jikin Anty Yaha Tana Fadin"Anty...Anty..Nice.."Take Fada Tana wani irin kuka da wani Wawan Rumguma Ta Rumgumeta Tana Fashewa da kuka Kamar Wasu kananan yara Anty Yaha Fadi take"Ina kika Shiga Farida..? Wata Duniya kika Shiga muna ta nemanki kika barmu Cikin kewa? Haka Take Fadi Tana wani irin kuka Itama Faridan kukan take Zaina Dake gefe sai Sharan kwallah take,Daga bayansu Suka ji ance Cikin wata irin Murya mai Cike da Rauni"Da gaske ne Aishata ce ta dawo Gida..? Kokuwa dai mafarkin dana Sabayi ne..? Ko a mafarki Farida Taji wannan muryan zata shaidata Muryan Mami ce Cikin Sagewar murya Ta Dago kanta sai Cikin na Mami Dake Tsaye Daga Kofar Daki Kallon Farko zakayi mata kasan cewa ta Rame ta lalace Tayi baki kamar ma bata da Lafiya Farida Taji gwiwanta ya Sage kamar An Jona mata wani Abu Kukanta yana kara karuwa Cikin wani Fitan Hayyaci ta Furta.."Mami na...! Kafin ta Zura da gudu Zuwa gareta ta Fada Jikinta Ta saki wani marayan kuka Mami ta Rike Farida Tana Sharan kwallah take Fadin"Ashe da Rabon zam sake ganinki na nemi gafaranki kafin Allah ya Dauki Raina.? Ki yafemin Farida a matsayina na uwa Ki yafemin Ban Dube ki nayi miki kallon yarinya mai natsuwa ba na jefeki da kalmar da bata dace dake ba da kalmar da wasu sukayi amfani wajen bata Miki suna Ki yafemin Farida wlh Tallahi Tunda kika bar Gidan nan banta Barci Cikin kwanciyr Hankali ba Aisha ki yafemin..' Mami Take Fada tana wani kuka Farida Ta kukan Mami ya Dauketa nata Ta Dago Tana Share ma Mami Hawayenta Tana Fadin"Mami ki daina kuka..Nice yakamata na Roki gafaranku baku ba.."Take Fada Tana kuka Anty yaha nata Sharan kwallah sai Lokacin Ta Lura da su Umma baki ta Rike Tana Fadin"Kai.Aisha Farida Tare kike da baki baki mgana ba..? Tafada Tana goge Hawayenta Sai Lokacin Farida Ta Tuna dasu Umma ta waigo Tana Fadin"Don Allah Umma kuyi hakuri ku kariso..Anty Harda Maza suna Waje Fa ina Abba yake..? Anty Yaha ta kalli Mami itama ta kalleta Sai Anty Yaha tayi Saurin Kauda Zencen da Fadin"Kuma kika barsu a waje..? Maza ki Shigo Dasu.."Tafada Tana Komawa Daki ta Dauko mayafi ta Dauki ma Mami ta kamata zuwa kan kujera su Umma ma duk sun zauna suka Fara gaisawa dasu Mami Sai ga Farida ta Shigo dasu Zain Alhaji ne Agaba Da dan Sandansa yana Dogarawa sai Abba da Haddir da Zain sai Sadiq Dake rike da Arman Zain kuma yana Dauke da Anan Haddir ya Dauki Anun. Alhaji Tsoho da Abba suka zauna kan kujera su Zain kuma suka samu kasa suka Zauna Aka Fara gaisuwa Anty yaha ta mike Zuwa Kitchen ta Dauko musu Lemo da Ruwa Kana ta koma Daki Ta daga waya ta Kira Goggo Zaliha ta gayamata Dawowar Farida Bayan ita Baffa Umaru ta kira ta gayamai Sai ta Kira Musbahu ta Fadamai ga Farida ta Dawo Gida da wasu Mutane yana jin Haka sai da yayi Sujidun Shkuran na Godiya ga Allah yace Jirgi zasu Taso Daga Abuja Zuwa Gombe da yardan Allah. Farida na Kusa da Mami sai kuka Take Yarinyar Dazu Dake Makale Gefe Farida ta kallah Tana Fadin"Mami wannan yarinyar fa..! Banga Abba ba ina Zahra kuma..? Anty Yaha Dake Fitowa Daga Daki Tace"Zahra Tayi aure a kano..Wannan Diyar ta ta Farko kenan Sunanki taci Aisha Farida sai kaninta Mai sunan Abbanku....'Farida taji hawaye ya Tarun mata haka suma su Mami ke ta Sharan Kwallah ta Kira Takwaranta tazo ta Rumgumeta Tana ta kuka Kamar ta santa ta ko Nane ajikinta Tana kallon Bakin Fuskoki. Girki AntyYaha tatafi Kitchen Ta Dora kafin isowar su Goggo Zaliha Zahra ta kirata bata sameta ba sai dai ta kira Mijinta ta Sanar dashi Komai Zahra Take ta bari tazo Gida Aisha Farida ta Dawo Taliya da Kifi Sharp Sharp Anty Yaha ta Dafa musu ta Zubo akololi tazo ta Kawo Ta ijiye su Umma nata mata Sannu Alhaji Tsoho ne ya gyara zama yana Fadin"Ina shi Mahaifin Faridan..? Ina son ganinsa kafin Duka bayanan su Biyo baya..' Mami Sunkuyar Dakai Tayi Tana Kuka,Sai Anty Yaha ce Dake Sharan kwallah da Haban gyalenta Tace"Allah yayi masa Rasuwa yau wata bakwai kenan.."Gabadaya aka saka Salati Farida kuwa mikewa Tayi Jiki na rawa Hannu Dafe Kirji Tana Fadin"Abba ya Rasu..? Na shiga uku ni Farida Abba ya Rasu yana Fushi dani bai yafemin ba..? Take Fada tana wani Gunjin kuka Mami ta kamata ta Rumgumeta suna Cigaba da kukan Tare Abba ya Girgiza kai yana Fadin"Allah ya Jikansa da Gafara.."Su Umma suka amsa da Ameen Alhaji Tsoho kuma Shuru yayi kafin yace"Allah ya jikansa Allah yamai Rahma.."Anty Yaha ta amsa da Ameen Ameen tana kuka ta Cigaba da Fadin"Ya rasu da sunan Ki Farida abakinsa..Ya Rasu yana ambaton ki yafemai yayi kuskuran yanke hukunci ba Bincike ya Rasu da kewarki da son ganinki.."Ba Farida kadai ba Hatta su Umma sai da sukaji Taruwar kwallah Tuni Mutuwat ta Dawo sabuwa su Mami sai Kuka suke Su Umma na basu Hakuri ammh kamar suna kara Zugasu ne sai da Alhaji Tsoho yayi ta musu Nasiha kana suka Tsaigata Cikin Muryan Data Dakushe Mami ta kalli Anty Yaha Tana Fadin"Kin kira Goggonsu Zaliha kuwa Antynsu..? Anty Yaha tace"Eh na kirata na kira Baffa Umaru ma na gayamai Ban samu Zahra ba ammh na kira Mijinta na gayamai nace Farida ta Dawo Gida.."Mami na Sharan kwallah tace"Musbahu fa..? Farida ta Dago Daga kukan Datake tana kallonsu Mami Anty Yaha tace"Shima na Kirasa yace yanzu Zasu biyo Jirgi Zuwa nan din.."Mami ta kada kai Tana Fadin"Allah ya kawo su Lafiya Don Allah ku dan jinkirta Iyayan nata su zo..Naga kamar Daga waje mai Nisa kuke..! Zain ne yace"Bakomai sai mu jira...Daga Bauchi muke..! Anty Yaha tace"Allah Sarki ashe duk tsawon wannan Lokacin kina Bauchi Aishafarida..? Farida na Kuka Tayi Mirmishi tace"Bana Bauchi Ina Zaria duk Tsawon wannan Shekarun..! Mami ta kalleta Cikin Raunin murya tace"Zaria kuma Farida..? Farida na wani irin kuka tace"Eh Mami Labari ne mai Tsawo sai mun zauna Zan gaya muku irin Rayuwar Dana Tsinci kaina Bayan barina Gida.."Kawai sai ta kara sakin kuka Zaina ma Sharan kwallah take Ita da zulaihat Zain ne ya Miko mata Anan Da tafara kuka Yace ta bata Nono sai ta Dauke ta Ta Dago Tana kallon Farida Tana Fadin"Anty Farida ina so nayi sallah.." Tafada Bata so ta ba Ma Anan Nono gabansu su Abba kunya Take ji Haddir ya Duba agogon Fatan Dake hannunsa yana Fadin"12:40pm kai Lokacin Sallah ai yayi muma ya kamata mu yita kan Lokaci.."Alhaji Tsoho yace"Tabbas hakane Zamu yi sallah.."Anty Yaha ta Mike Tana Fadin"Bari na Bude muku Shashin Baki sai kuje chan kuyi sallah kafin Lokacin nasan sun Kariso.."Abba yace"Ba laifi. Daki Taje ta Dauko key din Shashen Bakin ta Bude musu Alhaji Tsoho yace Jam"i zasu ja Bayan kowa yayi alwalansa Alhaji Tsoho Da bazai iya Tsayuwa ba saboda Kafa ya zauna Haddir yajasu sallar bayan sun idar Alhaji Tsoho ya Dinga Janyo ayoyo yana Fassarama Su Abba da Jikokinsa yana Nuna musu illah Yima yaro Baki wanda ke Binsa Duk inda yake wanda Kalaman da iyayan Farida suka Jefeta dashi Shi ya kaita ga Fadawa wannan Rayuwar. Anty Yaha da Farida nan suka kawo ma su Abbba abincinsu da Abun sha suka ci suka sha Su Umma kuma na cikin Gidan bayan sunyi sallah sun natsa suma aka gabatar musu da abinci suka Sha suna zaune afalon sai ga Goggo Zaliha ta Shigo Tana kuka Tana Fadin Ina Faridan take ne..? Farida na ganinta ta isa gareta ta Rumgumeta Tana ta kuka Basu gama Koken ba sai ga Baffa Haruna da Baffa Umaru sun iso suma ai sai Kukan Rasuwar Abba ya Dawo Sabuwa Baffa Haruna yana kuka yana cewa Farida ta yafemai Shine Silan komai Daman Tuni Anty haya ta kira su Abba tace su Iso Falon su Baffa sun iso agabansu komai yake Faruwa. Cikin Alamun Rashin Sanin Inda manganun Baffa Haruna ya Dosa,ganin haka yasa Anty Yaha ta kalleta Tana Fadin"Bayan Tafiyarki da Shekara Biyu Sirrin Boye ya Bayyana...Mummy ta Haukace sakamakon Fasa Tulin Duka Siirinta Dake Cikin Fulawowin gidan Baffa Haruna,Shikenan ta Haukace Ta rika Fadin Duka abunda ta aikata ita da yartaa Harda Asirin Datayi tayi Sanadiyar Rasuwar Goggo Fatu da kuma asirin da sukayi ma Musbahu ya auri Zubaida da wanda sukayi mai ya juyar da Hankalinsa zuwa kan ZUBAIDA..faruwar wannan Lamarin ya Tsorata mu sosai ganin Haka yasa Zubaida ta Tsorata Da bakinta ta Taramu ta Fadamana duk makircin da suka kullamiki wanda yayi sanadiyar Hawanjini ya kwantar da Abbanki yayi ta Jinya yana ganin Shine Silan Tafiyarki Tunda shi ya Koreki,Har Allah ya Dauki Ransa Mummy bayan An kaita gidan iyayenta Baffa Haruna ya saketa Achan ta Gudu Ta shiga Duniya ba"a ganta ba Zubaida kuma Musbahu ya saketa saki uku yanzu Haka tana Gida Tana Fama da Jinya na Ciwon Cancer Nono Har Guda Daya ya Rube an yanke yanzu Dayan ma ya Harbu..." Kowa Sharan kwallah yake afalon Farida na wani irin kuka Tace"Ina ya"yana..?Anty Yaha tace"Suna Wajen Musbahu Daman Tun bayan tafiyarki suna Wajensa yana kula Dasu bayyanar gaskiya yasa yayi kuka sosai kuma yazo ya Roki gafaranmu Shi yake Dauke da Duka Nauyinmu Bayan Rashin Lafiyar Mahaifinki Har Rasuwarsa wannan Gidan ma Da kika gani shi ya gyaramana shi ya bamu Dukkan wani ajin Dadin Rayuwa Zahra Tayi aure Shekara Daya da barinki Gida a kano Wlh Farida kullum addu"a muke Allah ya bayyanaki Dakyar su Baffa Haruna suka saka Musbahu ya kara aure Wata yar Nan Jemeta ya Aura mai Suna Bara"atu Wata Biyar kenan da auran suna Abuja inda Musbahun ya koma da aikinsa Yayi gida achan Duka dasu Hassana da Usaina suna Wajensa ya sakasu a makaranta Satin Daya wuce ma suna Gidanan nan sukayi mana Hutun karshen mako.." Farida kuka kawai Take Abubuwa Biyu sune ke kara sakata kuka na Farko Rasuwar Abba na Biyu kuma Da yau Taji Labarin Mummy ce Tayi sanadiyar Mutuwar Goggo Fatu sai taji ta kasa Daina kuka Nene da bata iya Shiru sai da Tayi mgana Tace"Sakamakon Daya kamata Dasu kenan..Duk wanda ya aikata Zalunci Tun aduniya zai ga karshensa.."Umma tace"Sosai ma Allah ka Rabamu da Zuciya mara kyau..."Gabadaya aka amsa da Ameen Ana Cikin Haka sai ga su Hassana da usaina Sun Fara Shigowa da gudu suna kiran Umma Domin tun achan Musbahu ya gaya musu Umma ce ta Dawo yaran basu manta da Uwarsu ba Farida na jin muryansu ta tashi ta isa garesu ta Hada ta Rumgume Tana kuka Tana Fadin ashe basu manta da ita ba Areef ne Bai ganeta ba sai ta Jawosa ta Rumgume tana Fadin Umma ce Al"ameen dina Duk da bai ganeta ba Dumin Jikin uwa na Dabam ne haka Farida ta kamkame ya"yanta Tana Dariya Tana kuka Lokaci Tana Dagowa taci Karo da Musbahu Da Matarsa Bara"atu Kallo Kallon sukayi ma Juna Wanda Tayi Saurin Dauke kanta Ta tashi Dauke da ya"yanta ta koma Gefen Goggo Zaliha ta Zauna Tana Sharan kwallah. Baffa Umaru ne yaga Musbahu ya Tsaya Shuru kamar bazai Shigo ba sai ya Daga baki ya Kirashi yace ya shigo sai ya Shigo ya zauna suka gaisa dasu Abba da Alhaji Tsoho ganinsu manyan Mutane Bara"atu ma Ta gaishesu ta samu gefe Ta zauna Tana Kallon Farida wacce Daman tasanta a Hoto a matsayin Mamarsu Hassana. Goggo Zaliha ce ta kalli Farida Tana Fadin"Aisha Farida kinji Abubuwan da suka Faru Bayan Tafiyarki..ina so ki gayamana ina kika ke Bayan barinki gida Meyasa baki Je kaduna Gidan kawata Kamar yadda nace ba..? Farida Ta sunkuyar dakai Tana Kuka ta Fara basu Duka Labarin Barinta Gida da Komai da komai da Rayuwar da Datayi a gidan Uwar mata,Da Haduwarta Da Zaina da Haihuwarsu da Maidata Bauchin Data yi har zuwa yau da Suka iso nan ta karishe Cikin kuka Tana Fadin"Na Yanke Shawaran Shga Duniya ne Tunda har iyayena suka Ambace ni da Karuwa Da Duka Ahalina sai naga bani da wani Sauran kima Da kaina Na nemi naZama Karuwa mai zaman kanta saboda Fushin Abubuwan da suka Faru dani.." Kowa sai kuka yake Goggo Zaliha na Girgiza kai Tana Fadin"Ba laifinki bane Farida..Makircin muguwar Kishiyace Tsakaninmu da Zubaida da uwarta Allah ya isa.."Alhaji Tsoho yayi gyaran Murya yana Fadin"Ai aduka Abubuwan da suka Faru akwai Sakaci da addu"a da kuma Baki da iyaye kiye ma ya"yansu batare da Sun tsaya sunyi Bincike ba..Na Farko dai Dukkanku kunyi Sakaci da addu"a har taci galaba akanku kaima Musbahu kayi sakaci Sosai...Sai kuma Bakin da iyayen Farida sukayi mata na Kiranta Karuwa batare da sun yi Bincike ba Duk ya Taimaka wajen Faruwar haka Shiyasa ana son komai yaro zai maka ka Daure ma Zuciyarka kada kayi mai Baki Domin zai Bisa.."Kowa sai gyada kai yake yana Yarda da mganar Alhaji Tsoho Baffa Haruna yace"Tabbas hakane...Mun yarda muyin Sakaci da addu"a abaya ayanzu kuma Insha Allahu mun gyara.." Kowa ya amsa da Allah yasa,nan aka Cigaba da Tattauna Agaban kowa da kowa Musbahu ya Duka ya bama Farida Hakuri tace ta yafe ya kuma ce yana so a amaida musu da Auransu da Farko taki yarda wai Ita fa karuwanci Tayi bata Dace da zama matar kwarai ba sai da Alhaji Tsoho ya kara yimata Nasiha kana ta yarda Bayan Godiya da Fatan alheri ga Su Alhaji Tsoho da kuma jin Dadin Karamcin da sukayi musu suka Dawo da Farida gida Ana kuka sai aka koma Dariya Lokacin ana Kiran Sallar La"asar suka Hadu Duka Mazan suka Hadu sukayi Jam"i matam kuma na Cikin Gidan sai Lokacin Zahra ta iso Bata Dade da Zuwa ba sai ga Saratu itama Tayi aure Harda yarta Daya Aseeya. Gida sai ya koma Kuka kuma Zahra da Farida suka Rumgume juna da Saratu suna kuka Sosai da sukayi suka gaji kana aka koma Tambayan Bayan Rabuwa sun gayamata Abunda,ya Faru bayan Batanan da duk Abunda ya Faru dasu Mummy itama ta gaya musu Irin Rayiwar da tayi Suka Hadu suna ta kuka da kuma Tuno Rasuwar Abba sai da sukayi suka gaji kana suka Hakura suka koma Hiran yaushr gamo. Su Abba dai Yammah Tayi kwana ya kamasu Dole suka Tsaya sai.zuwa Gobe, abincin Dare ma a Restaurant Musbahu yayi Oder akaci akasha Matan Acikin Gida suka kwana Mazan kuma Shashen Baki Da safe ma Oder Abun karyawa Musbahu yayi musu sukaci suka sha suka Fara Shirin Tafiya Karfe 10am na safe suka Rakosu Haraban Gidan Farida suka Rumgume dasu Zaina suna kuka Kamar kada su Rabu haka su Anun ma Suna ta kuka Sabo Sun Rabu kam zasu yi mgana ta waya Tunda Zaina Tayi sabuwar waya wacce Zain ya siyamata sun Rabu Cikin Dattako da Godiya su Abba na Godiya su Baffa Haruna na Godiya su Umma sukace sai Bikin Maida Auran Farida zasu dawo Mami Walwarta ya Dawo haka aka Rabu Cikin Mutumci Har suka Bar Haraban Gidan suna Daga musu Hannu da Fatan Allah ya Tsare su kuma suka koma Cikin gida suna kara maida Zencen dayi ma Allah Godiya Daya Dawo Da Farida gida Hatta da Bara"atu ta saki Jikinta Domin Daman Musbahu ya gayamata komai Duk Ranar da Farida ta Dawo Zasu maida auransu. Sai wajen yammah suka iso Bauchi Saboda basu yi gudu ba,Gida aka Fara kai Alhaji Tsoho Saboda ya Huta,Bayan sun sauke su Umma Zaina da zain suka Nufi Gidansu Domin warware gajiya nan dai suka bar ma su Umma ya"yansu suka Tafi gidansu Domin Basu gama amarcinsu ba. Sai Washegari suka samu waya da Farida suka gayamata sun iso Lafiya Daman tana da Lambarsu su Umma Duk ita ta kirasu ta yi musu bangajiya suka Rabu Cikin Jin Dadi,Ko bakomai Farida ta koma Cikin ahalinta Saura Zulaihat wanda Abba ya Tsara Tafiyan sati mai zuwa. Haka kuwa akayi sati na Zagayowa suka Tafi yashe Dangin Zulaihat,Sun Tarar da Baffa ya Rasu wasu Daga cikin ya"yan Larai duk sun Kara lalacewa Harda Barawo wanda Gwammati ta kama Larai kuma tana kwance tana Fama da Jinya Kafarta ta Rube Tun bayan Sanadin Saran Macijin shine Sila Bata da mai kula da ita Tana kwance adaki sai wanda yaga Allah yaga Annabi Gidan Gabadaya Warin Kafar Larai yake wanda yake Fitar da Ruwa Gwano Dataji Zulaihat ce da kanta Haka take kuka Tana Rokonta Gafara Zulaihat na kuka tace ta yafe mata yakubu gala najin Zuwan Zulaohat yazo yana Bata Hakuri Shima ya Shiryu Har yayi Aure ya Haihu koda Abba ya Nemi Zai Tafi da Zulaihat ta zauna Wajensa Maigari bai yi Gaddama ba Tunda kowa yasan Zaluncin Larai ga Zulaihat Haka kuwa akayi su Zain ko Tsausayin Larai basu ji ba Abba ne kadai ya Bada 50k ayi mata mgani Suka Tattara suka Dawo Bauchi Da Tunanin Tabbas Mutum yaji Tsoron Duniya Domin Bai sam wani Hali zai Kare ba. Bayan dawowarsu da kwana Biyu Zain yaje ya samu Alhaji Tsoho Da Tambayar ya makomar yankan da Farida Tayi ma su Anun..? Da kuma Rainon su da akayi da kudin Haramun..?Shin za"a kara Musu Sabon yanka ne ko kuwa dai Wannan din yayi bakomai..? Alhaji Tsoho yace kada ya Damu Yanka yayi Ai Abunda ya Faru Tskanin Farida ne da Ubangijinta Ita Zata Nemi Gafaran Allah mganar su Anun kuma yara ne kuma Tayi musu Komai da kyakyawan ZUCIYA saboda Haka babu bukatar kara Tabbatar da Sunansu Sai mganar Zaman dasu Zaina sukayi Wajenta Tana Ciyardasu da kudin Haramci Suma ba Hujja bane Tunda suna sane ba Cikin Rashin Sani bane sunyi Haramcin Sai dai Allah gafurun Rahimun ne su Rokeshi Gafara zai yafe musu ammh Ko gobe ba Hujja bane ka zauna ana ci Dakai da Haramun Da gangan. Da wannan Bayanan Zain yaji Hankalinsa ya kwanta ya Koma Gida yana Gayama Zaina Tayi ta kuka Tana Fadin Bata da mafita ne Zain ya Dinga Lallashinta Dakyar Tayi Shuru Tundaga Ranar suke neman gafaran Allah Ita da Zulaihat. ****** *Bayan wata Biyu..* Bayan Wata Biyu Abubuwa Dadama sun Daidaita Tuni Zulaihat ta zama yar gida Har Abba ya sama mata wata Private school da hanya dakomai aka sakata SS1 sai dai kuma Sadiq nayi mata Lesson In ya Dawo Gida da yammah Tunda Tasu Tazo Daya Farida kuma suma waya koda yaushe Bikinta da Musbahu nan da Kwana Arba"in kuma duk su Umma zasu je suka ce Zafeera Ta Dawo Hutu sau Daya Tayi Sati Uku ta koma ammh Shi Haddir din yana Zuwa in ya samu Lokaci Kamar Ranar weekend Tana chan Tayi Rashin Lafiya sai ga Labarin Cikin Wata Biyu da kwanaki ashe Lokaci Daya suka Dauka da Zaina ita ma ta Fara Laulayi ana Dubata itama Cikin Wata Biyu da kwanaki sai murna da Farimciki Wajen Duka Iyalan Alhaji Tsoho. Dina ta Dawo bayan ta Shafe wajen kwana50 asudan koda ta Dawo Cikinta ya Shiga watan Haihuwarsa Haihu ko yau ko Gobe Tun bayan Dawowarta Zaina ta matsa ma Zain Dole ya Raba musu kwanqa yau in ya kwana Wajentq Gobe wajen Dina zai kwana sai zaina ta saka aka Dawo mata dasu Anun Harda Arman yana wajenta bata Nuna Bambamci Dina kuwa ta Tabbatar da Darajan Zaina take ci da Har yanzu take samun kulawar Zain Duk da dai babu Abunda ya kara Shiga Tsakaninsu Sai dai ba laifi yanzu yana Kulata da Tambayar Lafiyarta Har ya bata kudi Masu yawa yace Zainab Ta rakata ta Siya kayan Haihuwa haka kuwa akayi Zainab da Zulaihat suka Rakata tayi Siyayyah kayan Haihuwa sai dai wannan karom Dina batayi Awon Ciki ba. ***** Yau a Wajenta Zain ya kwana ya kai Dare yana aiki Cikin Sytem dinsa bai yi Barci da wuri ba Duk da ba Daki Daya suke kwana ba tana jin Motsinsa Shiyasa yau bai tsshi da wuri ba kuma Ta kama Lahadi ne ba aiki. Fitowa tayi Daga Bedroom dinta Zuwa Kitchen da katon Cikinta Ruwa ta Dauko Ta Tsiyayo a kofi tazo Ta zauna afalo Tana Sha Kamar amafarki Taji ana Sallama Dago kanta da Zatayi taci karo da wata yar matashiya Mata Da katon Ciki Tana Sanye da Wata Riga baka da Hijabi Duk yaji Jiki Ta Rame ta lalace Tayi baki Fuskarta sai Kuraje Manya duk sun bata mata Fuska sai karamar Jakar matafiya Dake hannunta. Arazane Dina ta mike tana Watsar da kofin Dake hannunta Cikin Nuna ta da Hannu tace. "Zakiyyyyya!!!!..." *Kada ku saka Ran ganin wani Update din yau..Sai gobe da Safe In Allah ya yarda..* *Janafty...* 8/12/21, 11:32 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B23️⃣0️⃣* *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb* *END* _ALHAMDULILLAH_ "Zakiya Da take Tafiya Dakyar ta Fara takowa cikin Falon tana Sakin wani marayan Mirmishi Wanda kiris take jira ta Fashe da kuka ga Katon Cikinta Datake Faman Turoshi kamar ya Kifata. Dina Data Daskare a tsaye Tana kallon Zakiya Cikin mamaki da Al"ajabin ganin yadda Zakiya ta dawo,sai da Zakiya ta iso kusa da Dina kana ta Bude baki tace"Na"am Dina..! Kinga yadda Allah ya Maidani ko..? Dina Ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Zakiya me ya Faru Dake ne haka..? Zakiya bata samu Daman mgana ba ta zagaya ta Nemi Waje ta zauna Tana Sauke karamar Jakarta Lokaci Daya Tana Mike Kafarta Saboda Cikin  jikinta,Dina ta Zo gefenta ta zauna Tana kare mata kallo Cikin mamakin ganin Cikin Dan Wattanin da suka Dade basu hadu ba. Zakiya bata kara mgana ba sai da ta Dauki Ruwan Da Dina ta Dauko ta kafa a kai Bata Sauke ba sai da ta Shanye kana Ta sauke Gora Lokaci Daya da Numfashi,Dina Da mamakin ganin Zakiya yasa ta kasa mgana sai dai binta da kallo kawai sai da Zakiya Taji ta Natsu kana Ta Dago Tana kallon Dina Lokaci Daya Tana kare ma Falon Kallo Tana Fadin"Nazo ina Tambayan Megadi Ina kike Zaune sai ya sanar dani ai kina ma Wannan Shashen ne Dina..! Dina Data Zaku Taji me ya Faru da Zakiya Tace"Eh nan nake Zaune Zakiya..Meya Faru Dake ne..?Gabadaya kin Sauyamin..? Zakiya Ta Share Hawayen da suka kwaranyomata Tana Fadin"Allah Sarki Rayuwa Dina da alamu Kekam kinyi Nadaman Wasu Abubuwan da muka aikata Tun afari Tunda gaki Cikin Jin Dadi Har da wani Cikin..Ni kuma Dina na Fara Girban Abunda na Shuka Tun a Duniya..." Tafada Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka Dina sai Taji Gwiwanta yayi sanyi Cikin Alhini tace"Meya Faru Zakiya..?Ina Ja"afar din..? Wattanin Baya Da muka Hadu da Ashanty Take Fadamin Kinyi Aure A Bauchi..'Zakiya Tana Matsan kwallah Tana Fadin"Ashe Hashashen da kika gayamin gaskiya ne...?ashe Ja"afar ba Sona yake ba..? Ashe ba Mutumin Kirki bane..? Ashe Dan Damfara ne Ja"afar Bansani ba Wlh Dina ayanzu haka Ja"afar ya kwashemun komai nawa Daga karshe ya Hadani Da Abunda zai kasheni Har Abada.." Take Fada Cikin kuka Da Nadama mai Karfi Dina Ta Dafa Kafadarta Tana Fadin" innalillahi  Zakiya Don Allah ki Daina kuka ki gayamin Abunda ya Sameki Kika koma Haka..?garin ya Ja"afar ya Rabaki da komai naki..? Zakiya Ta Dago Tana Sharam kwallah Take Fadin"Tun Bayan Kafin Auranmu Dina na Riga na Sangarta Ja"afar komai ni nake mai Har komai na Auranmu ni nayi shi Bayan Aure ma bata Sauya Zani ba Nice Mijin Babu Abunda bana mai na Sakashi a Makaranta na Bude mai banki Ina Raba kudin albashina Kashi 2 ina Bashi Rabi ammh Kafin Sati sai yace ya kare Ban Fara Damuwa da Lamarin Ja"afar ba sai bayan Samuwar Cikin nan nawa Dina Ja"afar ya Sauyamin Gabadaya in ya Fita Gida sai Dare yake Dawowa wani Lokacin ma sai Tsakar Dare,Da nayi mgana sai yace Makaranta yake Wuni Danayi Bincike sai na gani sai yayi Sati ma bai Shiga makarantan ba Daya Lura na Fahimci komai sai ya Fara Sauyamin ya Daina Min Dariya ya Daina Kula dani kamar baya Ashe Duk yana Hadamin Tarko ne Dina Tabbas naga Mganar Baba Dayace Ja"afar makaryaci ne Address din Daya bada Na Karya ne Tabbas Hakane Ashe Ja"afar Dan Bariki neDina Kamar yadda nake yar Bariki Ashe Dan Damfara ne Haka yakee Dayaga Kana da kudi sai ya aureki Da Suffar Daya Aureni Daga Karshe ya Damfaresu kmar yadda ya Damfare ne Bayan Haka ba Haka kurum yake barin su ba sai ya Lura Miki Ciki Ya likamiki Cutar Dayake Dauke da ita Daga Karshe ya Kwashe komai naki ya Gudu ya barki.."Zakiya ta karishe Fada Tana Wani Gunjin kuka. Dina Ta Saki Salati Tana Fadin"Mun Shiga Uku Zakiya Wani irin cuta kuma..? Zakiya na kara Tsananta kukanta Tana Fadin"Cutar nan mai Karya Garkuwan Jiki Mana Dina.."Ido Dina Ta Zaro Tana Fadin"Kanjamau Fa kenan Zakiya..! ? Zakiya na Sharan Kwallah Tana Fadin"Eh Ita Dina..Ashe Ja"afar na Dauke da wannan Cutar mgani yake sha bata nuna ba Kuma Kinga Kenan Tabbas Ina Dashi Tunda munyi aure kuma Munyi Tarayyan Aure ba adadi.." Dina Ta Dora Hannu akai kawai Tana Salati Zakiya Tana Sharan Hawaye Tana Fadin"Kafin ya Tafi ya Rubutamin Takardan Sakina Har uku da wadanan Bayanan anan yake Fadamin In je a gwadani ya bani Tsaraba Da ya saba ba mata irina Wato kanjamau da kuma Ciki Dina Nayi kuka Kamar zan yi Hauka Ja"afar yagama Cutata ya kwashe Duka Atm dina ya Saida Gidan dana siya ya saida Motata ya Saida Motarsa Harta da kayan Cikin Gidan ya Saidamin su kayan sawa ne kuma Duk ya sace ya saida Dagani sai kayan Jikin sai wadanan kayan na Tsira Harta da Ogansa na Gareji yace sai Daga baya ya samu Labarin Ja"afar Dan Damfara ne Dina Bani da komai Tun Faruwar Abun nan na Rasa wa zan Dosa Sati Biyu Wadanda suka Siya Gidana sukabani yau kuma ta Cika Suna BuKatar Gidansu Hatta da wayata Ja"afar bai barmin ba Dina gwalagwalaina Duka ya sace ya Tafi Dasu Bani ko Kudin Motan da zan je kano sai kika Fadomin arai nace bari nazo nan naji nasan Insha Allahu Ba"a rasa wanda zai kaini Gidanki ba ashe kina ma nan.." Dina Dake kuka itama Ta Dago Fuska Shabe Shabe da Hawaye Tana Fadin"Aikin ki fa Zakiya..?zakiya na Kwallah Nadama da Bakinciki Tace"Tun Wata Biyu da suka wuce Ma"aikatanmu sukayi Sallaman Ma"aikata Hardani aciki Dina.."Gabadayansu kai suka Hada suna kuka Zakiya na Fadin"Tabbas Abunda na aikata ne nake Girbanshi Tun aduniya Dina...Gwara ke Kin yi Auranki Cikin Daraja Harda wani Rabon..Arman bazai Tashi Cikin Wata Rayuwa ba Dina Nifa Kalleni Cikin nan ko yazo Duniya ina zan ga Ubansa..? Wlh Dina Nayi Nadaman Zamowarta yar Bariki Domin Babu Riba acikin Wannan Rayuwar Sam sam.." Dina Na Sharan Majina Tana Fadin"Babu gwara Zakiya..ni kaina Abunda na Shuka nake Girba wannan Cikin da kika ganmi Dashi Rabon sa ne ya kawosa Tun bayan Auranmu Zain bai taba min Kallon Mace ce ba Tunaninsa da Zuciyarsa suna Wajen Zaina ce Ni na sakamai mganin Da komai ya kamkama Har na samu wannan Cikin Kingani ina zaman karban Duka Hukuncina ne Daga Allah na Ammh ni nasan Dawowar Zaina gareni Tamkar Haske ne.."Zakiya cikin kuka Tace"Zaina ta Dawo..? Dina ta Daga mata kai Kafin ta Fara bata Labarin Dawowar Zaina Ta karishe Da Fadin"ina jin Rayuwata kamar ba Rayuwata ba Zakiya ba. nayi Nadaman Abubuwan Dana aikata abaya da nasan Cikar Burina na auran Zain ba alheri bane Wlh Tallahi da ban yarda Mun Shiryawannan Plan din ba..Sai dai kash aikin gama ya Riga ya gama kuma Bamu isa mu Dawo Da Hannun agogo Baya ba.." Hada kai sukayi suna kuka sai da ya ishesu kana suka Tsagaita Zakiya Ta kalli Dina Tana Fadin"Dina nazo ne ki Taimakeni Ki bani Masauki na kwana Zuwa gobe da Safe ki Taimakamin da kudin Mota na Koma kano yanzu bani da inda yafi Chan aduniyan nan.." Dina Ta Bude Baki Zatayi Mgana Zain Dake Tsaye Kofar Bedroom dinsa Tun Dazu ya daga Murya yana Fadin"Bazaki Taba Samun Masauki anan Gidan ba Zakiya..Sai dai Zan iya baki Kudin Motan da Zaki kara Nisa da garin Bauchi na Har Abada.."Gabadayansu suka juyo Inda Sukaji Muryan Zain Cikin Wani irin yanayi ganin irin Banzan kallon Dayake Binsu Dashi Dukkansu alamun Dukka ya gama jin Mganar da sukayi da komai da komai sai Kunya da Nadama ya kamasu Dukkansu suka Saukar da kai kasa Cikin wani Alhini da Nadama mai Tsanani. Takowa ya Farayi zuwa  agabansu cikin Shigan Shadda Fara da alamu ya Shirya zai Fita ne,Sai da yazo gabdasu kana ya Dakata yana Binsu da wani kallon Kadan kuka gani Kafin ya kada kai ya Tura Hannu Cikin Aljihu ya Zaro Kudi da bai san ko nawa bane ya Zube kan Zakiya yana Fadin"ga kudin Mota nan ba Kano ba ko Lagos ne na Tabbata zasu isheki..Alhamdulillah da Abunda ya Faru dake ko bakomai Kinga kin Fara ganin Karshenki..Nakuma baki wannan kudin ne ba Domin na Tsausayamiki ba sai Domin ki Kara Nesa da garin Bauchi Domin Ina ganin kamar nayi wani Babban jihadi ne na rage Mugun Iri awannan garin..Aje chan Acigaba da Zaman karban Kaddara bama ga Cutar Daya saka Miki ba ko wannan Cikin Da Zaki Haifa baki san ina Zaki ga Ubansa ba Ya Isheki Takaichi Da Nadama.."Yana gama Fadin Haka Ya Nunata da yatsa yana Fadin",Minti Biyar na baki ki Fice mana Daga gida..In ba Haka ba Wlh Zan saka Arakaki har Tasha.."Yana gama Fadin Haka yayi tsaki ya Fice yana Hararan Dina Datake Tsiyayan Hawaye. Yana Fita Zakiya Ta kara saka kuka Tana Tattara Kudaden Daya Zube mata Tana Fadin"Bari na Tafi Dina kada na Jaxa Miki..Don Allah ki yafemin Abunda ya Faru abaya..Bansani ba Ko Karshen ganawarmu kenan.."Tafada Tana Mikewa Lokaci Daya Tana Daukan Jakarta Dina Dataji Ta kasa Daina kukanta Ta Mike ta Rumgume Zakiya Tana Fadin"Na yafemiki..Nima ki yafemin Zakiya..Ina ji ajikina Kina Kano Zaki ji Labarin Mutuwata..Ina ji kamar ganawar mu Ta karshe kenan.."Zakiya Tana Sharan kwallah Tana Fadin"Ki Daina Fadin haka Dina da Ikon Allah Zaki Haihu Lafiya.." Haka dai sukayi ta Kokensu har Haraban Gidan Dina Ta Rakota suka Rabu Tana kuka Itama Zakiyan Tana kuka kana ta Koma Cikin Gidan Ta wuce Bedroom dinta Ta Fada kan gado ta Fashe da kuka Haka Zakiya Har takai Tasha Tana kukan Nadama da yima Bauchi kallon Karshe,Ta samu Motar kano ta kusa Cika sai Kawai ta Hau ta kudendena kanta Cikin Hijabi Tana kuka Har Mota Tatashi Bata iya Dagowa ba Saboda Tana gani Kamar Mutane sun san Abunda ya Faru da ita. Zain kuwa Shi ya gayamasu Umma Daya shiga gaishesu suna ta alhini Nene tace Abunda Zakiya ta aikata ne take gani Tun aduniya ita kuwa Zaina da Zain ya gayamata sai ta Fara kukan Tsausayin Zakiya Zain sai ya saki baki yana kallonta Saboda yasan Halinta Haka take da Tsausayi abu kadan Cikin nan sai ya sakata Rigima da yawan koke koken Daya gane haka sai ya koma yana Lallashi Ranar gidanta ya kwana Cikin Farincikin Dadin da Zaina ta Juyar dashi yama manta da wata Dina wacce ta kwana kuka Da kuma Alhinin Abunda ya Faru da Zakiya Gabadaya sai taji kamar itama akwai Sauran sakamakon da Zata Girba Gabadaya Taji Duniyan ta Juya mata baya. Har washegari Tana cikin wannan Halin ko Shashensu Umma bata leka ba Tana so ta Kira Zakiya Taji ta isa Lafiya..?ammh bata san Hanyar da Zata sameta ba,Dole ta Hakura Kwana Biyun nan Haka tayishi Cikin Wani Hali Ga Zain bata kara ganinsa ba Tundaga Ranar Daman yana Gidan Zaina ne Arman kuma yana wajen su Umma shi dasu Anun Sunzama yan gatan su Umma da su Zainab Ballatana Zulaihat da indai Ta Dawo makaranta Tana Wahale dasu Ita Haka Allah yayi ta akwai son yara,kuma Yaran sun saba da ita har kuwa shi Arman din Daman yaron Inda ake Lallabasa Chan yake. Kwana Biyu da Faruwar Haka Dina ta Fito Daga Shashenta Zata Shashensu Umma Ta gaishesu Cikin Ikon Allah kamar an kwasheta an Kifar Akasa haka Ta Fadi kan Cikinta nan da nan Jini ya yanke mata Lokaci Daya ta saki wani karan azaba Wanda ya Tunkudo dasu Umma Daga Shashensu suka iske Dina kwance Cikin jini bata Numfashi Hankali Tashe suka Fasa Ihu Allah yasa Sadiq yana Gida bai je wajen aiki ba Bayajin Dadi Shi ya Daukesu Zuwa asibiti Bayan ya kama ma su Umma sun kamata sun sakata a Mota Zulaihat Bata Gida Tana makaranta Zainab ce kadai agida Ta tsaya wajensu Anun da suke ta kuka Ganin Halin Da Dina take ciki. Ba tare da Tunanin komai suka kawota asibitin Saulawa Kuma akaci sa"a Dr Imran ne ya karbesu yayi mamakin ganin Dina acikin Halin Mutuwa ko Rayuwa kuma bai yi mamaki ba Daman Dr.Aisha Tataba gayamai Dina Tayi aure ta auri Zain Abun ya bashi mamaki Taya YaDina da Zain zasu yi aure ba wani Labari Lokacin Suna Tare da Zakiya Ya Taba mata mganar Ta tabbatar mai da Tabbas hakane toh Lokacin da aka kawo Dinan ya kara Tabbatarwa ganin su Umma ne suka kawota. Halin Data ke ciki yasa ya Kira Dr Haddir ya sanar dashi Wanda Saboda Rudewa ma Su Umma sun manta da Haddir da Zain din anan asibitin suke aiki,sai da suka gansa kwatsam Kofar emergency Bai Tsaya yi musu mgana ba ya Shiga Dakin Halin Daya ga Dina ya Razana shi Jini Ya yanke mata sai Zuba yake Cikin Ikon Allah kuma Ta Farfado ammh sai Sambatu take Dr.Imran da Dr.Aisha suna ta Kokarin Tsaida Jinin Kallo Daya yayi mata yasan Cikin Jikinta ya samu mtsala ganin Ya Jirkice kuma Jini ya Yanke mata akwai yuyuwar ayi mata Tiyata Cikin lokaci kafin ayi Biyu Babu. Cikin Tashin Hankali ya Fito yana Tambayansu su Umma garin yaya haka ta Faru.?Nene ke gayamai Faduwa Tayi suma suna Daga Shashensu Sukaji Ihunta Koda sukaje sun isketa kwance Cikin Jini Bai tsaya Sauearansu ba ya Nufi Office din Zain Cikin Damuwa. Ya iskeshi yana Tsaka da Duba Patient Cikin Tashin Hankali yake gayamai Abunda ke Faruwa Tashin Hankali Sosai ya bayyana Cikin Idanuwansa ya Mike da Sauri  suka Fito Daga Office din Sa Haddir namai bayanin Abunda ya Fahimta game da Hadin da Dina ke Ciki Hankali Tashe yayi ma wata Nurse mgana kan ta kwashi Folder din Dake kan Tuber dinsa Takai ma Dr.Peter shi Zai Tafi Emegercy ne. Cikin Gaggawa suka karisa Kofar Emergency din inda su Umma Suke Tsaye Hankula tsshe bai ko Tsaya yi musu mgana ba ya Danna Cikin Dakin ya iske Dr.Aisha Da Dr.Imran nata Kokarin Tsaida Jinin Dake Zuba Daga Jikin Dina ammh Abun ya gagara Dr.Aisha na ganin Zain Ta Nufeshi Tana Fadin"Yauwa Dr.gwara Daka zo Matarka Ta Fadi ta Bugu Cikinta Jini ya yanke mata ina Tunanin Yaron Dake Cikinta Shima ya samu mtsala Me zai hana ayi mata Tiyata Domin Ceto ta ita da Abunda ke Cikinta.."Yana Jinta Tana mgana Kokarin Saka Handglop yake cikin Tashin Hankalin Ganin irin Halin Da Dina ke Ciki Zuwa yayi ya Fara Dubata yana gani Domin bai Zata ma Tana Numfashi ba ammh Yana Zuwa Kusa da ita Ta Bude ido Cikin Azaban Ciwo Hawaye na Zubo mata Tace"Zainn....! Kuri yayi mata da ido Yana kallonta Sai ya samu kansa da Riko Hannunta a karo na Farko Yana Fadin"Gani anan Dina..Kada ki Damu yanzu zan Miki Tiyata insha Allahu Komai zai zama Normal.."Wani Mirmishin Dayafi kuka ciwo Dina Ta saki Kafin Ta kara Damke Hannusa Tana Fadin"Ina Zaina Take..?cikin Mamaki Zain yace"Zaina Tana Gida Dina..Ki..""" "Don Allah ka Kiramin ita..Ina son mgana da ita ne.."Da Sauri Zain yace"A"a Tiyata zamu shiga Dake yanzu..Ki bari in Komai ya Daidaita zan Kirata Tazo Kuyi mgana.."Da Sauri Dina Tace"A"a Dom Allah Nidai kakiramin ita Ina son na ganta In har baka Kirata ba yanzu bazata zo ta sameni ba Lokacin Dakake mgana ba.."Ba Zain kadai yaji Mganar ta Dakesa ba Har Haddir da Dr.Imran da Dr.Aisha sai da sukaji wani iri Cikin Sauri Zain ya Kara Damke Hannun Dina Yana Fadin"Ki daina Fadin haka..Bazaki Mutu ba Insha Allahu zaki Tashi...Dr.Imran Ku shirya kai da Dr.Aisha zamu shiga Tiyata.."Yafada yana Kokarin Sakin Hannun Dinan Ta kara Damkewa Cikin Haawaye Hade da Mukurkusu Take Fadin"Don Allah ka Kiramin ita..Ka kuma Kira Daddyna ka Fadamai Yazo mu gana in muna da Rabon ganawa In kuma yazo ya iske gawata Don Allah ya yafemin Nima na yafemai Duniya da Lahira.." Sai ga Zain najin Gabadaya Kalaman Dina na Neman sakashi Kuka Haddir ma Dake gefe Ma sai da Zuciyarsa ta Tsinke Cikin Dauriya Ya kalli Zain yana Fadin"Plz ka kirasu..Komai zai iya Faruwa fa.."Yafada Cikin kauda kansa Daga kallon da Zain yake Binsa Dashi waigawa yayi yana kallon Dina wacce ta sakarmai Mirmishi Lokaci Daya Hawaye suna kwarara ta Gefen Idanuwanta Cikin Karaya da Sanyi Jiki Zain ya Fita Daga Dakin su Umma namai mgana Hannu kawai ya Daga musu gefe ya koma ya Kira Wayar Zaina Sai da ta kusa Katsewa ta Dauka Bacci ma take ya tasheta  Ta Fara mai Shagwaba sai Taji yanayin Muryansa ba Dadi kafin Ta Tambayesa yace Ta shirya Tazo asibiti yanzu ga Halin Da Dina ke ciki ai sai Zaina Ta Fara kuka nan da nan Tace gatanan Zuwa Daga ita sai ya Kira Kwamishina Abunda ke Faruwa Cikin Rudewa yace gasunan zuwa Hankali tashe yake Gayama Hajiya Batula ga Abunda ke Faruwa Daman yana Gida Ranar bai je ko"ina ba. Zaina Ko Kaya bata Sauya ba Rigar Barci ne Doguwa ajikinta Ta Zura Dogon Hijabinta Ta Fito Bata tsaya Hawa Motarta ba Ta Fito Ta Hau adaidaita Tanimu megadi nayi mata mgana Bata ma kulasa ba Hankalinta yayi gaba Koda ta isa Har an Shirya Dina Za"a Shiga Da ita Tiyata Allah ya Taimaka alokacin Jinin ya Tsaya Ta iske Dinan an Gungurota Sanye da kayan Tiyata Ta Rike Hannayen su Umma Tana ta kuka Tana Rokonsu Gafara Sai ga Zaina Tana ganinta Ta Dinga mikamata Hannu ta kama Da Sauri Tana Fadin"Gani nan Dina ..! Dina Na Jin kamar Ranta zai Fita ta Damke Hannun Zaina Tana Fadin"Naji Dadi Da kikazo Lokaci bai kure mana ba..Zaina Ki yafemin Abunda nayi Miki Domin inaji ajikina Raina ya kusa Barin gangar Jikina.."Zaina Data Fara kuka ta kamkame Hannun Dina Tana Fadin"Ni bakimin Komai ba Dina Wlh in ma kin min na yafe miki Duniya da Lahira..Kuma Ki daina Fadin Zaki Mutu Insha Allahu ba zaki Mutu ba.."Dina Ta Runtse ido Hawaye suka Kwaranyomata Tayi Mirmishi Cikin Karfin Ciwo Tace"ayyah..Lokaci ya Riga ya kure Zaina..kedai alfarma Daya nake Rokonki Dashi Shine ko Bayan Raina ki Zame ma Arman Uwa Zain ya Zame masa Uba Don Allah kada ki bari yasan Cewa Bake bace Mahaifiyarsa ba, ina Rokon ki ko Bayan ya Girma kada ki Fadamai Ni mahaifiyarsa ne saboda Bazan so yaji Labarina da Ta Hanyar dana Samesa ba Don Allah Zaina Ki Rike Arman Ki Hadasu dasu Anun kada ki Taba Rabasu ki Zamemai uwa ta gari wacce Zai yi alfahari da ita Har Karshen Rayuwarsa.."Ba Zaina ba Hatta su Umma sun Fara kuka Zaina kuwa sai ta Duke Tana kuka Tana Fadin"Ki Daina Fadin haka Dina..Bazaki Mutu ba Insha Allahu Tare zamu Reni Arman.."Dina Ta kara Rike Hannun Zaina Tana Fadin"Ki Min wannan alkawarin Zaina na gayamiki Lokaci ya kure.."Nan da nan Dina ta Fara Shakuwa sai kuma Jinin ya kara yankewa yana Zuba Da Sauri zain Ya isa Wajen yana Riko Hannun Zaina Zai Rabasu Dana Dina ammh suka ki Sakin Juna Dina Cikin Azaban Fitan rai Tace"Zaina kimin alkawari..Kimin Don."Bata karisa ba zaina tace"Nayi miki wannan alkawarin..Nayi alkawarin Zan kula da Arman kamar ni na Haifeshi kuma ba zan Taba bari ya gane niba Mahaifiyarsa bace.."Dina na jin Haka ta saki Mirmishi jin Dadi kafin tace'"Nagode Zaina.."Daga Haka Ta kauda kai Zain ya Rike zaina Dake wani kuka ya mika Hannunta ga Umma shi kuma yabi Bayan Nurses din da suka Tura Gadon Dina zuwa Dakin Tiyata Dr.Imran da Dr Aisha suma Cikin kayan Tiyata suka Rufa musu baya Hakama Zain Haddir ne kadai bai Shi ga ba ya Tsaya Daga waje suna Shiga suka Turo kofa. Ko Gama Shiga Dakin basu yi ba Dina Ta Fara wani kakari Dukkansu suka Dakata Cikin Tashin Hankali Zain ya Fara Fadan Su shiga da ita yaji Dr.Aisha na maimaita mata kalmar Shahada sai ya tsaya Cak Tunda yaji kalmar Dina Ta karshe Tana Fadin"La"ila ha"illahu..."Daganan bata karisa ba Ba mala"ikun Daukan Rai ya Zare mata rai sai idanuwanta suka Kafe ko"ina na Jikinta ya saki Dr.Aisha Ta saka Hannu ta Rufe mata ido Tana Hawaye tace"Allah ya Jikanki Dina...Allah ya karbi Shahadanki..Kin Rasu kina Dauke da Juna Biyu Allah yayi Miki Rahma.."Dr.Imran da Sauran Nurses da Jikinsu ya gama yin sanyi suka amsa da Ameen Domin duk sun san Dr.Dina Tayi aiki a asibitin Tare dasu barin ma Dr.Imran Dayaji Jikinsa yayi sanyi Sosai. Zain kuwa wani irin Dum yaji Daya Tabbatar da Dina Ta Rasu sai ya juya kawai ya Fice yana Zarw Safar Hannunsa Cikin wani yanayin Da shi kadai Zai iya Fassarashi ya Fito su Umma suka Taso suna Tambayanshi ya ake Ciki..? bai tsaya wani Tunani ba ya Bude baki yace"Sai Hakuri Umma..Allah yayi ma Dina Rasuwa.." Ai sai gabadaya suka Dauki Salati Haddir ya Dafe kai yana Salati Shi da Sadiq Umma da Nene sai kuka Zaina kuma Jikin Umma ta Zube Tana Sakin Kuka Da dukkan karfinta Zain Office dinsa ya wuce Ya Dauki wayarsa ya Kira Abba ya gayamai Abunda yake Faruwa Abba yaji Abun kamar Daga sama sai ya Fara Salati Zain da Kansa ya Kira Hajiya Mama ya gayamata itama Sai ta Fara kuka da Salati yace kada ta taho yanzu zasu Taho da gawan nan Gidan Alhaji Tsoho ayi mata Sallah Bayan Sun gama wayar take gayama Alhaji Tsoho Shima yaji mutuwar nan yace Allah ya Jikanta yana ta Jera mata Addu"o"in Dacewa. Kafin kace kwabo Rasuwar Dina yaje kunnan kowa,Baban Kaduna da Daddyn Abuja Haddir ya Kirasu ya gayamasu sukace dukkansu suna Tafe Insha Allahu,Zafeera Dake kano Taji Rasuwar nan tace Zata Biyo Inna Rukkayah su zo Tare,Inna Hannatu kuma tace sai gobe Goggo Halima kuma Zain ya Kirata ya gayamata Tace gobe Tana Tafe kowa sai Fatan Dacewa yake ma Dina. Cikin Lokaci kadan Aka saka gaawan Dina a Ambulance zuwa Gidan Alhaji Tsoho Sauran kuma suka Biyo bayansu a Motoci Suna zuwa Gidan kwamishina na isowa sai dai ya iske gawa Allah Sarki yayi Tawakkali addu"a kawai yayi mata su Hajiya Batula ne keta kuka,Kwamishina da kansa ya Kira Hajiya Maimuna Daga Sudan ya gayamata Rasuwar Dina Sai kuka Tana Tambayansa Bata da lafiya ne..? Yace Mata Ajali ne yayi kawai.sai Hakuri Chan Sudan Da Hajiya maimuna Ta sanar da Labarin Rasuwar Dina Hankula sai ya tashi masu kuka nayi masu Sharan Hawaye da Tagumi Duk sunayi nan da nan Hajiya Maimuna ta Fara Neman Visan Da zata Taho. Zain kuwa Ba wanda zai iya cewa ga yanayin Dayake ciki,Ammh Shi kadai yasan yadda Rasuwar Dina ya Dakeshi Zaina kuka Take har suka iso Gidan Alhaji Tsoho Zainab da Umma ta kira wayarta Ta Fada mata Itama sai kuka Zulaihat kuwa Sadiq Kadai ya Tuna da ita yaje ya Daukota Daga makaranta Daganan ne yake Fadamata Rasuwar Dina Itama sai Hawaye Shiyasa Gidan Alhaji Tsohon ya wuce da ita Zulaihat ita ta kira Farida Ta gayamata Rasuwar Dina Farida Taji Mutuwarta Sosai Ta kuma san Tabbas Zaina Zatayi kukan Rashin Dina. Ba"a Sallaci gawan Dina ba sai Da akayi idar da sallar Mangariba kana aka yimata Sallah Bayan su Babban Kaduna sun iso Goggo Halima da Hajiya Mama da Tabawa sukayi ma Dina wankan Gawa Allahu Akbar su Zaina suna ji suna gani aka Fita da gawan Dina Zuwa Haraban Gidan Alhaji Tsoho Allah sarki Rayuwa kenan Mutane Da Dama suka Sallaceta suka kuma Rakata Zuwa Gidanta na gaskiya. Daman Haka Rayuwa ta Gada Ka Shuka alheri Domin Watarana Za"ayi kamar baka ne,Bangaran su Anun Zainab Tazo dasu,Zaina Ta karbi Arman Ta Rumgumesa Tana Tuna Mganarta Da Dina na karshe Tayi alkwarin Zata rike Arman Kamar su Anun Baxata Taba Nuna mai Bambamci ba,Haka suka wuni karban gaisuwa su Abba Suna Haraban Gidan suna karban gaisuwa Tunda abokan Siyasan Kwamishina suna ta Zuwa Washegari Harda gwannan Jahar Bauchi yazo Ta"aziya,Aranar kuma Inna Hannatu tazo ita da Mijinta suka kwana Daya suka koma Bayan sun yi gaisuwa abun gwanin Ban Tsausayi Farida ta Kira Har Zain tayi mai gaisuwa,Harda su Anty Yaha da Mami sun gaisa Sun ma su Umma gaisuwan Rasuwar Dina Har da Zaina Ma sunyi mgana. Sai da akayi Sadakar bakwai Gida ya watse Baban Kaduna da Daddyn Abuja kowanne ya kwashi Iyalansa suka koma Hamdiya ma Tazo Daga kaduna Tayi gaisuwa ta koma Zafeeera bata bi Inna Rukayyah sun koma ba Saboda suna hutu Ga Ciki ya Fara Bayyana Sai Shagwaba iri iri,Shema dai ta koma itama an saka mata Rana Ranar bakwai su Umma suka koma Gidajensu a kuma Ranar ne kwamishina da iyalansa suka koma Kano Cike da alhinin Rashin Dina Shida Hajiya Maimuna wacce ta iso Ranar da akayi Hudu Ta kwana uku suka juya kano Ranar da Dina Tayi bakwai da Rasuwa sai dai Fatan Allah ya Jikanta da Rahma. Laila Ma tazo Gaisuwa Domin Zaina ta kirata ta Fada mata da Tazo ta ke cema Zaina ta kara Tsorata da lamarin Duniya yanzu,Ta kuma yardan ma kanta Dan"adam ba abakin komai yake ba wajen Ubangiji Ita kanta Zaina haka take Fadi Tana kuma godema Allah Tun Zamanta da Dina wani Sabani bai Taba Shiga tsakaninsu ba Koma ya Shiga kafin ta Rasu sun yafi Juna,Zaneera bata samu zuwa ba sai dai ta kira waya Tayi ma su Umma gaisuwa Domin kwamishina yayi musu kara yace su akayi ma Mutuwa shi kawai Uban Dina yake Abun gwanin ban Tsausayi. Zaina kuma Ta koma Gidanta Sai da Zain yayi da gaske Zaina tabar Arman wajensu Umma da tace sai Ta Taho dashi yace ta bari ta Haihu Mana Sai ta Faramai kuka Tana Fadin Zata Cika Wasiyan Dina ne ya Lallabata Da Za"a Daukomata shi Tare dasu Anun Daya kira Umma ya gayamata sai tace yazo ya Dauki Yaran ya kai mata Hakan zai Rage mata Radadi da kuma Zafin Mutuwar Dina Haka kuwa akayi Yaje ya Dauko mata su ya kawo mata sai aka samu Lafiya,Zain har mamakinta yake yarda Take kula da Yaran Musamman ma Arman kamar ta maidashi Ciki Wani Lokacin Haka Anun da Anan zasu yi ta Kuka taki Daukansu tana Chan wajen Rawan jikin Kula da Arman Zain sai dai ya Daukesu kawai ba Halin mgana saboda Sanin Halin Zaina na yanzu komai akayi kuka kamar wata karamar yarinya Shima Lallabata yake yi. Ganin Haka yasa Zain yasa Goggo Halima tayi mgana aka basu Diyar Isuhu Kaltume ya Daukota Saboda ta Taimaka ma Zaina ga ciki ga wahalan yara Tunda Ta matsa ma kanta Kaltume din Shekararta 15 Ta gama Jss Zata Fara SS sai kawai Zain ya Daukota yazo ya sanya Ta makaranta Tana Zaune Saboda Ragema zaina wasu ayyukan,Kuma ba Laifi Tana Kokari sosai kuma zainan Taji Dadi Tana Dauke mata wasu Hidomomin Koda Zain ya Dawo Daga asibiti Sai ta bar ma kaltume din yaran Taje ta kula Dashi. Bayan Wata Biyu da Rasuwar Dina Lokacin Cikin Zaina na wata na Shida ita da Zafeera suka Tafi Gombe Bikin Komen Auran Farida Da Musbahu Harta da Zaneera sai da ta zo Bikin Saboda Amintarsu da Farida Tayi Nisa Tun Ranar al"amis suka Tafi Da Zaina da Zafeera da Zainab da Zulaihat da Umma Nene sai Ranar Daurin Aure zata Biyo su Abba Zaina Tazo da Kaltume saboda su Anun Da Tazo dasu Farida Taji Dadi sosai na ganin karan da Iyalan Dr.Saulawa sukayi mata Goggo Halima Bata zo ammh ta aiko da sakon kayan gyaran Amarya Abba ma ya bada Gummuwa 100k,Mami da Anty Yaha suna ta Godiya dasu Goggo Zaliha. Tare dasu duk akayi Shagulgula Zahra ma ta iso Dasu Saratu sun Hade Cikin su Zaina ana ta Hira ana Dariya Alokacin ne Zain ke Tambayanta Ya labarin Uwar mata Farida tace bata dashi Domin ta Karya Layinta kuma Tun zamansu bayan sunan garinsu Gombe bata san wani abu akanta ba bata da Hanyar samunta Alhaji Badamasi ne kuma Shima ta yanke alaqa dashi Zaina tace gwara Hakan Domin Daman Burinta kenan Taga Farida ta koma Rayuwar Kamar kowacce mace mai yanci. Zubaida kuwa Allah yayi mata Rasuwa itama Lokacin Dataji Labarin Dawowar Farida ta Rikice Tana ta kuka Da Rokon Akaita Ta nemi gafaranta toh Farida Taje har Chan Family House din su Mommy Inda Zubaida ke jiyan Da Taga Halin Da Zubaida ke Ciki sai da Tayi mata kuka Taji To kuma me ya Rage mata..? Bata da wani Sauran amfani Tun aduniya Taga Karshenta Zubaida na kuka Tana Rokon Farida gafara tace ta yafe mata Data koma Gida Ta kira Ya Musbahu Tana Rokonsa Ya Taimaka Ya kai Zubaida asibiti Tana zaune agida ba wani kulawa yace Tsakaninsa da ita Har Abada Bazai Taba yafe ma wacce Tayi Sanadiyar Mutuwar Mahaifiyarsa ba jin Haka yasa Dole ta kyaleshi Tunda har Baffa Haruna ma yace shi da ita Har Abada ko Sati Biyu Farida Batayi da zuwa ba Allah yayi mata Rasuwa Farida ta kara Tsorata da Duniya ta kuma kara Jin Tsoron Allah ya kara kamata Allah ya tsaremu da aikata Aikin Danasani. Ranar asabar aka Maida Auran Farida da Musbahu Su Zain da Abba da Haddir da Sadiq duk sunzo Daurin Auran Tare suka zo da Nene Ana Daura auran suka Juya saboda Ranar Aka Tafi da Amarya Abuja su Zaina ne yan Rakiya chan suka kwana sai Washegari suka Dawo Bauchi da kayan Biki Niki Niki,Farida bakinta yaki Rufuwa da wannan karan Haka Zaina Burinta ya isa Yau Farida gata Cikin Tsabbataciyar Rayuwa Kamar yadda take Fata sai da tayi kwallar Farinciki Washegarin Ranar da suka Dawo Daga Abuja Zaneera ta wuce katsina Yayar Mijinta Allah yayi mata Rasuwa Dagachan kuma Bazata Dawo ba Zasu koma Ranar da akayi uku dai su umma sun je gaisuwa Chan katsinan basu kwana ba suka Dawo. ******* *BAYAN SHEKARU BIYAR..* Bayan Shekaru Biyar da suka Gabata abubuwa Da Dama sun Faru wasu na Farinciki wasu na aka sinsu Sai dai na Farincikin yafi yawa. Acikin Farinciki ne sune Harda kamallah karatun Sadiq karami da Faruq sun Dawo Gida Har sun Fara aiki Sadiq karami yayi Auransa da Matarsa Hafsah yar kanwar Mom Iklima ce ya aura Dake kaduna Baban Kaduna an samu Suruka. Sai kuma Auran Sadiq babba da Zulaihat wanda da kansu suka Hada kawunsu aka sha Biki Abun yayi ma kowa Dadi Sai da Ta kamallah Secondary School din kana akayi Auran yanzu har ya neman mata nan ATBU bauchi Ta Fara Rana Daya akayi Bikinsu da Zainab da Hajiya Mama karama A gidan Alhaji Tsoho,zainab a Lagos Tayi aure Yaron kanin Mijin Inna Hannatu Haka ma kannen Haddir Lauratu da Waleeda ma sun yi Auransu Shekaru Biyu Daya Gabata. Zainab Har ta Haihu Ta samu Mace Taci Sunan Zaina Sa"adiya Suna Kuma kiranta da Zaina ne,Zainab kuma Tana da Ciki Tayi Jinkiri wajen Samun Ciki ammh su Lauratu Duk sun yi Haihuwan Daya Dayansu Tunda Har Zainab din Ta Rigasu aure Zafeera da Zaina kusan Lokaci Daya suka Haihu Zafeera Ta Samu Namiji yaci sunan Zainullahi Sai Zaina da Yarinyar taci Sunan Aisha suna Kiranta da Aira,Zafeera Ta gama karatunta Har tayi Service sai da Haddir yace ba aiki Bayan Zain karami Ta kara Haihuwan mai Sunan Abba Wato Usman suna Kiransa Abba karami sai Zaina itama Data kara Samun Mace Taci Sunan Hajiya Mama Amina suna Kiranta da Hajiya karama. Bangaran Farida itama Ta Samu karuwan yan Biyu ma wannan karan Duka mata yara sukaci Sunan Zaina da na Zulaihat Domin bazata Taba mantawa dasu ba Har Abada Zumunci ya Dore an zama Daya Tazo Sunan Aira itama Zainan Taje Sunan Su zaina ita da Zulaihat Zumunci kuwa da Zareena sai Abunda yayi gaba Har U.s sai da Taje ita da ya"yanta da Mijinta Musbahu wanda arziiki yaci Uban na Da Yayi kudi Soaai na Ban mamaki Farida ta Sauya kuma suna Zaune Lafiya da abokiyar Zamanta. Lokacin da Suka zo Kaduna Bikin Hajiya mama karama Dayake a Kaduna akayi Bikin Zaina ta Hadu da Suby Tana bara abakin Randa Duk ta kode ta zama wata Tsohuwa karfi da yaji Shine Take kuka Tana gayamata Uwar mata Ta rasu yan Kidnapping Suka Harbeta a Hanyar kaduna Suka kuma Tafi da Hajiya Zabba"u Cikin Daji Har yau ba wanda yasan Labarinta,Daman Tun kafin Haka Jarabawowi keta sauka mata Shagonta ya kama da wuta Babu Abunda aka Fitar Gidanta kuma  Gwammati Ta Karbe tace Filin tane aka Saida mata Tayi Gini Bayan Faruwar Haka kuma Yan anguwa Suka yi Fata Fata Da gidan Abincinta da Gidan karuwan suka Fatattake su suka Kone wajen Ta gayama ta Deezee ta koma garinsu su Zeeze kuma bata san isalinsu ba Kacharalle kuma Yayansa yazo Ya Tafi Dashi Daman dan nan Kauri ne Dake kaduna Rashin Ji da Daudu yasa ya gudo Daga Gida Labarin Dai ba Dadin Ji Suby Tana kuka Tana Rokon Zaina Gafara Tana kuma Tambayan Ina Sholly Zaina ta Fito da waya Ta Nuna mata Sholly ita da su Hassana da Usaina da Arif da Musabahu da Yan Biyun data sake Haihuwa  da kuma Hoton Zulaihat da Sadiq da Yarinyarsu Suby sai kuka da Nadaman Rayuwa nan Zaina ta Zube mata kudi Ta shige Mota suka koma Gidan Baban Kaduna Dayake Zulaihat bata zo Bikin ba Saboda makaranta Yasa sai da a waya Zaina ta basu Labarin Abunda ya Faru Dukkansu sukace Daman Hakan ya Dace da Irinsu Uwar mata. Bangaran Kwamishina Mahaifin Dina Tuni an sauke shi Daga kwamishina Shekaru Uku da suka Gabata duk yayi Laushi ya koma Wani nagari Bayan Rasuwar Dina sanadin haka ya gina Makaranta sadakatul Jariya ga Dina Hajiya Maimuna ta koma Sudan Hajiya Batula ta kara Haihuwan Mace Alhaji Gaddafi ya maida mata Dina Saboda kaunar dayake ma Dina yanzu ya gyara Kasuwanci ya koma yi ya bar Siyasa yana kula da matarsa da yayansa Domin ya Fahimci Shine Babban kuskure a Rayuwar Dina,Zumunci kuwa sosai da sukeyi da su Abba Kwamishina yace ko Babu Arman iyalan Saulawa Sun Gama yimai komai arayuwa Ballatana ga Arman a Tsakani,In suka samu Hutu Zaina ta kan matsa ma Zain sai ya saka Direba yakai Arman kano yayi musu Hutu Tun Arman yana kin Zuwa Saboda ya saba dasu Anun Har ya Fara sakin Jiki sai dai Har yau har gobe ba wanda ya Taba gayamai ba Zaina bace Uwarsa kawai An nuna mai Kanon ma gidan yan"uwane. Bangaran Zakiya kuwa Ashe Koda ta koma Gida Mallam Nuhu bai karbeta ba sai Da ta gama Gayamai Abubuwan da suka Faru da ita yace Shine Daidai ya Koreta yace badai Gidansa ba Ta kara gaba Tana kuka Tana Komai ta Tafi Bata da wajen zuwa Dole Tatafi Minjibir Dangin Mahaifiyarta suma Duk wanda yaji Tana da kanjamau sai ya gujeta Dakyar wacce suke Uba Daya da mamarta Uwani Ta bata Faka ammh ita ke aikatau Tana ci da kanta Ta Haihu Y'a mace Yarinya ba inda ta bar Ubanta ko Ragon suna ba"a yankamata ba Taci Sunan Siyama Yarinyar Tun Haihuwarta Take Cikin Rayuwar Talauci da Wahala Zakiya Ta kara Lalacewa ta Jeme,Ciwo na neman ya kwantar da ita Dole ta Fara Zuwa Cikin Kano Tana karban mgani abangaran masu irin Cutarsu,Bata san Dina ta Rasu ba sai da akafi shekara Lokacin da Sahura Kanwarta Tazo garin Dayake yar Mijinta nan take aure Shine da Tazo suka Hadu Take gayamata Dina Ta Rasu samira Mahaifiyarsu Ta Hadu Da Hajiya Batula Take gayamata Ta Rasu bata ma Haifi Cikin jikinta ba Zakiya Taji wannan Mutuwar sai da ta kusa Tayi Hauka Tana Tuna Rabuwar da sukayi Da Dina Ashe da gaske ne Rabuwar Karshe sukayi Mutuwar Dina ta kara Saka Zakiya Ta kara Jin Nadama ta kara Shiganta Tayi kuka Har taba Uku Lada Tana Fatan Allah ya Jikan Dina ita gashinan Tana Girban nata sakamakon yau ita ke Rayuwa a kauye Cikin Kazantattaciyar Rayuwa da kuma Cutar Dake jikinta ga kuma Siyama wacce kullum Take Kallonta Tana kukan Bakincikin Damfaranta da Ja'afar yayi. Tuni Shashen da Dina ta zauna da Sadiq zai yi aure ya Saka aka Bugemai wajen aka karamai Fadi da kuma girma ya gyara Shashen Aka saka Zulaihat anan Su Umma da Nene kuwa Farinciki ya Dabaibayesu Kowani Buri nasu ya cika Jikoki sun Fara Dabai bayesu Hakama Tsoho mai Ran karfe Alhaji Tsoho Yana nan Da lafiyarsa sai dai Rashin Lafiyan kafarsa kawai Haka Hajiya Mama Burinsu ya gama Cika ya"yansu suna Da Hadin kai suma Jikokinsu da Tattaba kunnuwansu suna na alfahari dasu ta kowani Fanni Cigaban Rayuwa ya Dabaibaye wannan ahalin. ****** Zaina Ta koma makaranta Tayi Degree dinta sai dai Su Laila sun Tsere mata itama Har Masters Tayi ya"yanta Uku,gwanin Ban Sha"awa. Zaina Ta cika alkawarin Data Daukar ma Dina ta Rike Arman kamar Dan Data Haifa kuma ba wanda zai gansa yace ba ita Ta Haifesa ba zaina naji da Arman tana Sonsa Duk wanda ya Tabasa zai ga Bacin Ranta Harta dasu Anun kuwa Kowa jinjinama Zaina yake ganin yadda Tamaida Arman Dan gata Dan gaban goshi. An sakasu makaranta Shi da su Anun Kaltume na nan Tare Dasu Ta gama Secondary School Har ta Fara Fce,Batayi Aure ba Tana Tare da Zaina Tana Tayata Kula da yara ga Aira ga Hajiya karama Zain kuma Asibiti Saulawa yanzu ya Bunkasa ba kamar da ba yanzu a Nageria ana ji da asibitin Sosai Suna yawan Samun katin gayyata Daga Manyan asibitoci shi da Haddir Basu Zaune Waje Daya Sai suyi Sati Biyu basu Gida Suna Chan wajen Karban gayyata Domin kara ma Juna sani. A wannan Satin ma Zain wani asibiti ya karban ma gayyata Dake Ilorin Yaje yayi sati Daya ya Dawo a gajiye Tunda ya Dawo Yake barcin gajiya Dakyar ya Tashi ya iya Sallan Asuba ko Massalaci bai je ba agida yayita Ya koma ya kwanta Ya Kamkame Zaina ita kuma Bata jin Dadin Haka Domin yanzun Bata samun Lokacinsa Sosai Saboda Baya Zama. Karfe 7am na Safe Zaina Tatashi Kitchen ta shiga Domin Samar da Abun kari Asabar ba makaranta Boko sai da Hadda da Zasu Tafi Hajiya karama kuma Gidan Su Umma zata kaita yau Tana son samun Zama da Mijinta sosai ko Ta gayamai albishir Dake Cin Ranta Tun Satin Daya wuce. Dankali Ta soya musu da kwai Sai tace su sha Complex da Madara Dakin yaran Ta wuce Domin Taji Hayaniyarsu Kaltume nata Fama Dasu Tana shiga Aira ta Rugo da gudu Ta Rumgumeta Tana Fadin"Gud Mrning Mommy.."Dagata Zaina Tayi Tana Fadin"Mrning my Swt Dota Kin tashi Lafiya..? Tafada Tana Shafa kumatunta Aira Ta bangale Baki wacce ke Tsananin kama da Zafeera Tana Dariya Kaltume na Shirya Anan Tana Ta Tura baki Anun na gefe Tana Dariya Zaina ta karisa Shigowa Dakin Tana kallon Anan Data bata rai Cikin Mamaki Take Fadin"Ah kaltume me ya samu Anan din Daddy ne naga Tana bata rai..? Tafada Lokaci Daya Tana Sauke Aira Daga kan Jikinta Kafin Kaltume Tayi mgana Arman Dake gefe Sanye da kayan Hadda yace"Gud Mrning Mommah.."Zaina Ta Dago Tana kallonsa Hannuwanta ta Bude mai Ya Taho da Sauri ya Fada Ta Rumgumeshi Tana Fadin"Mrning My Swt son Ka tsshi lafiya..? Yana Mirmishi kamar Zain yace"Lafiya lau Mommah Ina Daddy..? Zaina Tace Tana Shafa kansa "Daddy Yana barci bai Tashi ba Son.."Kai ya gyada Mata yana kara kwanciya kan Jikinta sai Ta shafa kansa Tana Mirmishi Taji yace"I Love u Mommah.."Cikin Kaunarsa tace"Love u too Son..Allah yayi maka albarka.."ya amsa da Ameen Shida Kaltume Tana Dariya ganin Haka yasa Aira ma Ta Rumgume Zaina da Arman Tana Fadin"I Love u Mommah.."Sai Zaina Ta Fara Dariya Kaltume Ta Dago Tana Fadin"Mommy wai fa Saboda nace Anan ta Tsaya na Shiryata Shine take wannan bata ran Anun kuma na mata Dariya...' Zaina Tace"Kyaleta Ki Gyara Min Diyata Hajiya Yanzu In su Arman zasu Tafi Hadda Ki bisu ku sauka Gidan su Umma anjuma zamu shigo Nida Daddynsu.."Ta Fada Tana kallon Hajiya karama Dake ta Tsalle Tana wasa da kayan wasa akan gado ba ta wuce Shekara Daya da Rabi ba sai Lokacin da Ta lura da Zaina ai kuwa Ta Tako Zuwa Gareta Ta saki su Arman TaDauketa Tana Dagata sama Ita kuma Tana Dariya Sai Lokacin Anan ta saki ta gaishe da Zaina itama Anun ta gaisheta Ta amsa Tana Shafa kansu Tana sska musu albarka Tattarasu Tayi Suka Nufi Falo suka karya Ta bar Kaltume na Shirya Hajiya karama Daman Tayi mata wanka Suna Cikin karyawan sai gata ta Iso Ta gama Shiryawa ita da Hajiya Karama Zaina ta karbeta Ta Bata Nono Itama kuma kaltume ta Zauna tana karyawa Dankalin da kwan Zaina ta saka musu cikin Fulas,Saboda sai 6pm suke tashi Tana Hade da islamiya ne. Bayan sun gama kaltume Ta Fita da jakunkunansu Zuwa Mota Tunda Zain ya Daukan musu Direba Zai biya dasu Ta Gidan Haddir ya Dauki Zainullahi,Shima nan yake yi zuwa Sukuma yaran suka Shiga Cikin Bedroom dinsu suka Tada Zain wai zasu Mai sallama zaina na su bari su bari suka kiji sai dasuka Tadashi Dole ya mike yabi kowanne da Rumguma da peck kana suka yi musuBye bye suka Fice Hajiya karama kuma Zaina ta Fita Falo Ta mikama Kaltume ita da Jakar Madaranta da ruwanta Tace akai ma su Umma Da Nene Tunda su zama iyayan yara Yanzu Zulaihat takai nata chan Zafeera Takai nata itama Zaina Takai Gidan Abba yanzu ya koma Gidan yara. Sai da suka Tafi ta Dawo Cikin Bedroom din Ta iske Zain kwance Cikin bargo ammh ba barci yake ba ya Dai Lumshe ido Tana ganin haka Tayi Mirmishi Ta Lallaba zata Fada Tiolet Tayi wanka Taji mganarsa"Firstlove ina zaki Tafi kuma ki kara barina..? Yafada Lokaci Daya yana Riko Hannunta Daman Kofar Tiolet din na kusa da gadon ne,Waigowa Tayi Tana Mirmishi Shima sai ya Bude idanuwansa yana kallonta Cikin Shagwaba tace"Wanka zan yi fa."Tashi yayi zaune yana rike da Hannuwanta yana Fadin"Wanka me..? Zo kawai ahakan ki Firstlove.."Yafada yana Shafa Hannunta cikin Salo Lokaci Daya yana Jifanta da wani kallo Shagwaba ta Faramai Tana Bubbuga kafa Tace'Ahakan..? Na shiga kitchen ina Tsami fa.." Dariya ta kamashi sai ya Dara kana Ya Jawota Ta Fado Jikinsa Ya Kamkameta Yana Fadin"Eh naji..Yau tsamin Jikin Matata nake son na shaka.."Yana Fada yana Shinshina wuyanta Zaina Ta Fara Nokewa Tana son kwatan kanta Sai ya Fara yi mata Chakulkuli Sai ta Fashe da Dariya ta Wuntsila gefe Shima ya Bita ya Danneta yana Shinshinan wuyanta shi adole sai yaji tsamin Data keyi Dago kansa yayi yana bata rai yace"Ni fa ban ji tsamin ba Firstlove...! Hancinsa ta Lakuce Tana Fadin"sabon Unborn din ka ne ya Hana kaji Tsamin.."Tafada Lokaci Daya tana sakarmai wani kallo Dakatawa yayi da Shinshinanta yana kallontaCikin Dariya zaina ta Sagalo da Hannayenta ta wuyansa Tana Fadin"I Hv preganant Firstlove nan da Wata 6 zaka sake zama Daddy..'wani kallo ya sakar mata kafin yace"are u sure..? Sai da ta sakarmai Kiss a Kumatunsa kana Tace"Yes..VerySure Firstlove dina mai Gugan Dadi.."Tafada Tana Dariya Kamkameta Yayi Cikin wani Shauki Lokaci Daya Yana Sumbatar kowani gaba ta Jikinsa Tana Tayashi Sai da sukayi suka gaji kana ya Dago Fuskarta Yana kallonta Cikin kwayan Idanuwanta Yake Fadin"Tanque..Nagode Firstlove..Allah ya Biyaki da aljannah..Nagode Matata Mai Rijiyar Dadi.."Kunya ya kama Zaina Ta boye kanta akirjinsa Tana Dariya Tana Fadin"Nima nagode Zumata..Allah ya Biyaka da aljannah da yarda kake sona kake kula Dani ni da ya"yana.." Zain na chan wata Jahar Dakyar taji Sanda yace"anthing For u Ummu Arman.."Ta saki Mirmishi Tana Fadin"Nagode Abuu Aira.."Daganan bata kara jinsa ba ya kamkameta yana ta Kokarin kai kansa inda zai samu sauki Itama sai ta kamkamesa Domin Har ga Allah sunyi kewar juna wajen Sati Biyu basu hadu ba sai da Kawai Romancing saboda baya ssamun zama ammh yau kam Till Dowan ne duk sai an Rama bashin Baya. *Alhamdulillah...Tammat Bihamdullahi...* *Hakika Godiyata Ta Tabbata ga Allah Subuhanahu Wata"ala Daya nuna min yau na kamallah wannan Littafin Lafiya kamar yadda na Farashi Godiya ga Fiyayyan Halitta Annabi Muhammadu Salallahu Alaiwasallam Tare da iyalansa da Sahabbansa Gabadaya Ina Godiya ga Duka Tarin Masoyana Yan ZAINAZAIN PAID GROUP,nagode muku da Soyayyar da kuka nunamin Wajen Siyan wannan Littafin Allah ya saka da alheri Nagode kwarai Allah ya Jikan iyayanmu Allah ya bar zumunci Ameen* _ke kuma mai Hannun Bera Da kike Dauka kina yawo Dashi..Ki sani Nauyin Hakkin na dana wadanda suka saka kudinsu suka Siya suna wuyanka kuma Allah baya yafe Laifin Wani da wani.._ *Janafty* *Shakira..* *Intelligent writer"s* *ZAINZAIN PART2* *12/08/2021*