𝘓𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝘯𝘢 𝘬𝘶𝘥𝘪𝘯𝘦 𝘢𝘬𝘢𝘯 𝘧𝘢𝘳𝘢𝘴𝘩𝘪𝘯 𝘕600 𝘬𝘢𝘤𝘢𝘭 𝘷𝘪𝘢 𝘵𝘦𝘭𝘦𝘨𝘳𝘢𝘮. 08130229878 𝘈 𝘵𝘶𝘣𝘵𝘶𝘣𝘪 𝘸𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘓𝘢𝘺𝘪𝘯 𝘥𝘰𝘮𝘪𝘯 𝘒𝘢𝘳𝘪𝘯 𝘣𝘢𝘺𝘢𝘯𝘪. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) Sadaukarwa ga Marubuciya Azizat Hamza,Allah ya kula dake ya ƙara Miki ɗaukaka da nisan ƙwana mai amfani,Allah ya biya miki dukkan wasu buƙatunki na Alheri♥️ HALISH Sultan..a duk inda ki ke ina addu'ar Allah ya kula da ke. Saƙon gaisuwa ga dukkanin members ɗin Women of words writers association (wow). (COPYRIGHTS) All Rights are reserved. © Ma'ana babu wani sashe na littafin nan da na yarje a kwafa ko a sake masa samfari ta ko wacce irin siga. [DISCLAIMER ] Ƙirƙirarren labari ne,suna, guri , Character dukka fictional ne,idan yayi dai dai da rayuwar wani ko wata coincidence ne,it's fictional. [My Contacts info] WhatsApp:08130229878 Instagram:Chuchu_jay_ TikTok:chuchujay4 Wattpad/Arewapen:chuchujay Facebook:Ameenatuh Jameel. [WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION ]wow. Littafin Zunairah ya samun chanjin suna saboda suna yayi iri ɗaya dana wata marubuciya.ngd EPISODE 1:my life * 𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷 * بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ Tun kiran farko da Mama ta fara na ji ta amma nayi lamo a kan gado ina mai jin takaicin tashi ,duka duka ƙarfe shida fa na safe haka nan bana san tashin wurin nan, sai naje makaranta ya zamana ni ce ta farkon zuwa a ajin mu kamar wata mayya. "Zunairah na san kina jina Allah kada ki bari na ɗauko bulala because zan zane Miki jiki".jin Muryar Mama da kuma alamun tana takowa cikin ɗakin ya saka nayi Saurin tashi zaune wanda hakan ya yi dai dai da shigowarta,miƙa nayi ina mai saka murmushi a fuskata kafin na ce"NYene Mama"(ina kwana Mama). "Da ban kwana ba zaki ganni na tashi har na haɗa muku abin kari,Abeg my friend ki tashi ki shirya makaranta,kin san ba section ɗin ku ɗaya da Adavize ba amma ke da Ometere ku je chan ku ƙarata amma kada ku bari a daki mun Auta saboda Latti,maza ki tashi mu je mu haɗu mu ci"ta faɗa tana mai juyawa dan barin ɗakin. "Mama ni fa ba sunana Ometere ba,haka jiya na zo da abokaina ki ka kirani da Ometere suka ɗinga yi mun dariya ,I'm sure yanzu kowa a makaranta Ometere zai na kirana, Sunana Hauwa'u Please ko ki ce mun jiddoh,ita Aunty Zunairah da take san Ohunene ɗin ai baki faɗa mata sai dai Baba ya faɗa".ƙanwata Hauwa dake sanye da uniform bakin ƙofar ɗakin ta faɗa. Towel ɗina na jawo ina mai cewa"an dai ji haushi,yarinya duk inda mutum yake tushensa Yaren sa,ni kam ina alfahari da yarena,da za a daina kirana Zunairah ma ana ce mun Ohunene so nake amma either ways suna nan mai daɗi ne". "Aw wai dama Zunairah ba kiyi wanka ba?"Mama ta tambaya tana mai ignoring Hauwa'u . Kafin ta sake wani maganar na faɗa bathroom ina mai cewa"Mama wanka na da babu daɗewa". "To dai wallahi Veyanarisa ko mu cinye"(ki zo mu ci abinci).Hauwa'u ta faɗa . Ina jin fitarsu na fara wanka,kullum haka daily routine ɗin gidan mu yake da safe in dai maganar makaranta ce. Cikin kayan makarantana Green finafore da farin long sleeve,sai ƙaramun farin hijabina na shirya, Hauwa'u da Muhammad Adavize suna zaune suna jirana dan mu ci abinci,bakin nan na Hauwa'u ya yi tsini kamar zai taɓo sama saboda takaicin Mama ta hana su cin abinci kan sai na fito za mu haɗu mu ci ,haka gidan mu ya ke ,duk abu sai an jira kowa ake fara cin abinci,mu duka muke haɗuwa har Baba da Mama mu ci mun riga da mun saba dan idan ɗaya Baya nan sai muna ji babu daɗi. Zama nayi kan tambarman da suke ina mai taɓa Hauwa'u a cinya ina mai faɗin"Ometere ƙanwata ta kaina". Cikin jin haushi ta ce"Mama kina jinta ba,ki faɗa mata bana so". "To Inya dama kana ƙin identity ɗin ka".Baba dake fitowa daga cikin ɗakinsu ya faɗa yana mai zama gefen Mama. "Ni ban ce ba Baba ai babu wanda ya ji na ƙi Hauwa'u tunda babu yadda zanyi ga Hauwa'u ga Ometere ni kam na shiga uku ". Babu wanda ya sake kulata mu kayi Bismillah muka fara cin jallof ɗin taliyar Mama mai ɗan Banzan daɗi gefe guda kuma kowa da ruwan lipton ɗin sa da ya ji kayan ƙamshi. Bayan mun gama ne duka muka tashi domin tafiya makaranta gudun Lattin da Mama bata so,kallon Baba nayi :"wai Baba Har yanzu ba a gama gyara maka motar nan naka ba?Allah keke napep ba kowa ke shiga lungun makarantar mu ba". "Yace sai gobe Ohunene haka nan za ku yi ta haƙuri kafin na ƙarɓo ,nima dole sai a daidaita sahun nake bi ga tsada daga nan zuwa cikin gari ya isheni na sha mai ya yi min kwana biyu"ya faɗa yana mai saka hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya bamu,tun kafin mu fita na ɗauki nawa na bama Hauwa'u da Muhammad na su sanin halin Hauwa'u yanzu sai ta ce an bani abin da ya fi haka na boye dan rigima duk da a gabanta fa aka bada kuɗin. Sallama muka musu suna masu saka mana albarka kafin muka fita dan zuwa bright scholars School. Sunana Zunairah Buhari ,Asalin mu Yaren Ebira ne daga garin kogi karƙashin Ovehira amma mu mazauna Garin Kano ne cikin Unguwar Hotoro tsamiyar boka,sau tari idan na tambayi Baba mai ya kawo mu Kano daga kogi sai ya ce Karatu ya kawosa BUK da ya gama kuma sai ya samu aiki a gidan gwanmati,jin daɗin garin ya saka shi miƙe ƙafa ya zauna har ya Auro Mama Fatima wadda suke yan yare guda gari guda,mu ba masu kuɗi bane amma baza mu kira kan mu da talakawa ba tunda Álhamdulilah muna ci sau uku a rana ,Gidan Ebira shine mutanen layi ke kiran gidan mu . Duk yadda Baba zaiyyi ya yi ƙokari wajen ganin ya bamu ilimi mai kyau da kuma rayuwa mai kyau ,makaranta bai bari mun yi ta gwamnati ba,Duk yadda iyayen mu za suyi,sun yi ganin sun nuna mana yadda za mu so juna a tsakanin mu,Mu uku Allah ya basu amma Mama haihuwarta huɗu,ta haifi babban Yayanmu Abdullahi da mijinta na farko a kogi kafin ta Auri Baba,a yanzu yana zaune a okene da yan uwan mahaifinsa,bayan ta Auri Baba aka haifeni inda naci suna Zunairah,Baba ya ce mun ma'anar sa sunan wani Fure ne da ke gidan Aljanna,a sunan yare na ci Ohunene wanda ba sai an faɗa mun na dace da sunan ba saboda sanyina da haƙurina ya yi yawa da yake saka mutane ke tunanin bana da wayau ko za suci kashi a kaina ban tanka ba,abu guda da basu sani ba ,Ni haka Allah ya yi ne bana san damuwa. Hauwa mai shekaru sha biyar ita ke bina ,Ometere kenan rigimammiyar gidan mu,Tsakanina da ita shekaru Huɗu ne dan har Mama ta fara tunanin ba zata sake haihuwa ba sai ga cikin Ometere,bayan haihuwarta taci sunan Maman Baba Hauwa'u,dalilin da ya saka Baba ke kiranta da Inya kenan ma'ana Mamana. Mama ta bata sunan Yare Ometere ma'ana kyautar da aka daɗe ba'a samu ba,bayan shekaru Biyu kuma aka haifi Muhammad Adavize wanda ke da shekaru sha uku. Ni ina Ss3 inda a yanzu muke shirye shiryen rubuta WAEC Hauwa'u kuma yanzu ta shiga Ss1 Muhammad kuma zai shiga Js1,Bana da wani buri a rayuwa da ya wuce naga ina rubutun littafan Turanci duk da turancin ba yarena bane na farko,idan aka bamu Littafin makaranta na amfani ciki nake ɗaukar guda ɗaya nayi rubutu a ɓoye ba tare da kowa a gida ya sani ba,sai na aje Bayan Mutum ɗaya ta karanta,Aminiya ta kenan Anisah Ibrahim,tun muna primary school muke tare ,Ni da ita irin ƙawayen nan ne da ake kira inseparable idan ka ganni dole za ka ganta,ita ɗin Yaren Idoma ce na garin Benue ,Agatu local Government amma mazauna garin Kano ne kamar mu, Ni da ita secret keepers ɗin juna ne dan sau tari a makaranta har malamai kan tsokane mu da yan biyu. Abun da ya fara jana rubutu shine soyayya,ni ɗin mayyar soyayyace idan na faɗa ban iya ba,gani da shegen yarda kamar duk duniya Babu na banza,kana raɓata ka nuna mun soyayya shikenan kamar wawuya sai na baka dukkan yardata,Mama ta ce ba wawanci bane dabi'a ce,Ni tawa ɗabi'ar kenan ,idan na zaune da biro na bisa takarda wani irin shauƙi ke kamani ,ni kaɗai nayi ta murmushi ,kuma fa a hakan bana da wani saurayin da nake kulawa although akwai masu bina,tun wani saurayina ma'aruf da nayi ma san mutuwa ya gudu ya barni ban sake sakewa ba dan na sha wahala dalilin rashin sa,a matsayin amateur writer abin da na ƙware kenan ban sani ba gaba idan na san inda na dosa na fara Cautionary tales yanzu akan abun da zan nusar ba nace ba dan na ga mostly marubuta sukan nusar akan abubuwan da suka shafi Zaman Aure ,zamantakewa ta mutane ,abubuwan zahiri da sauran su amma nikam Zunairah na rubuta soyayya kawai mai ƙalubale karshe kuma ya zama happy ending .menene daɗin idan babu happy ending?I just hope Nima rayuwa ta yi mun happy ending yadda bana da aiki sai rubutun Happy ending wanda at the end of the day aminiyata kawai take karantawa ta yi appreciating ɗina ta ƙara mun ƙarfin gwiwa kan zan iya amma na bari sai mun gama secondary kafin na nuna ma duniya talent ɗina. Tunda na shiga cikin makaranta Anisa kawai nake nema,sakata cikin idanuna first thing a makaranta shi ɗaya yana faranta mun rai ,jin ihunta a bayana ba ƙaramun razanani ya yi ba,ɗane ni tayi ta baya tana dariya,nima dariyar na saka dan baza mu taɓa girma ba idan muna tare da juna,ganin Baba discipline master yana nufar mu da ƙatuwar bulalarsa ya saka muka ruga da gudu muna dariya,dukan sa Babu daɗi gashin mun tsaya a inda in har ya shigo ɗin sai ya zane mu. Bayan assembly dukkan ɗalibai suka wuce aji, Mathematics ne da mu first period,Ina mamakin masu cewa suna san Maths domin ni Zunairah a wannan bangaren kaina fanko ne ,a barni dai bangare Literature in English,duk ajin mu babu Guru a wannan fannin Kamar ni. Bayan mun gama classes ɗin kafin lokacin break aka fita break,ina ƙokarin tashi Anisa ta riƙe mun hannu, kallonta nayi kafin na ce"break time baby". "I've got something for you". Zama nayi ina mai facing ɗin ta jin abin da ta ce,hannu ta saka cikin jakarta ta ciro wani box da aka yi wrapping da ledan wrap mai kyalli, miƙa mun tayi tana murmushi,cikin rashin fahimta na karba ina juya box ɗin ina kallonta ina san sanin na mene ,dariya ta saka sosai kafin ta nuna ni tana mai faɗin"kada ki ce mun na last year za muyi,Zunairah wace irin mutum ce ke?for God sake today is your fucking birthday ". Hannu na saka bisa bakina dan wallahi da gaske na manta,bana da wannan tsari na birthday or something wanda dalilin hakan ya kan saka nama manta cewa wai ranar murnar Haihuwarta ta zagayo, rungumeta nayi ina mai jin hawaye na san zubo mun,haka nan last year ita ta tuna mun birthday na dan gida dama sun saba bani surprise bayan makaranta,amma bayin Allah nan suna da wani abu,suna fa sane amma a yadda na fito gida ma babu wanda ya ce mun koda Barka sai zane ni ma da Mama ke faɗin za tayi. "I love You best friend,thank you very much kina ɓata ni da yawa".Shafa bayana tayi a hankali kafin ta furta "happy fully nineteen bitch I love You ". Bana da wata ƙawa da ta wuce Anisa wallahi har cikin jinina nake jin ta,.Buɗe box ɗin na fara,wani mayen agogon Amiri designer na gani,da mamaki na kalleta na ce"babe Amiri?this is much". Ƴar dariya tayi kana ta ce "kin chanchanci fiye da haka gurina Zunairah so chill and Rock your Amiri and after school akwai more surprise,but I don't know yadda za muyi da Hauwa'u da Muhammad". Ɗan shiru nayi dan babu ma yadda za a yi Hauwa da Muhammad su tafi gida su kaɗai ni ina wani gurin daban,kama hannunta nayi "babe it's okay,wannan ma kaɗai ya isa cos men nawa ya yi worthing agogon nan ma kansa". "250 thausand"ta bani amsa,ban san lokacin da na aje mata kan cinyarta ba ina mai zaro ido. "Dubu ɗari biyu da hamsin fa Anisa ina ki ka samu kuɗi haka and ki ka yi wasting a kaina?bama zan iya kai agogon nan gida ba tambayar Mama da Baba kawai ya ishe Ni,what?250? No now". Dariyar da ta saka ta dakatar dani, kallonta kawai nake dan banga abin dariya ba,sai da tayi mai isarta kana ta ce"hala kin manta Babana ɗan Siyasane Mama head ɗin NGO,Yayana Halil Custom,ni kuma only female child ko?baby we are loaded so dan na cutting miki agogon dubu ɗari biyu da hamsin chicken change ne so dan haka i wont take baza ki bini ba after school driver na waje ya kaimu ni kuma har gida zan aje ki". Mantawa nake Anisa ɗiyar masu kuɗi ce ganin yadda ta sake sosai dani,duk wani fancy abu mai kyau itace,wani fancy sneakers, sandals,bags,hatta pen ɗin da take amfani da shi fancy ne,dukkan littanta kuwa tayi wrapping ɗin su da Wrapping set na Strawberry short cake nima har nawa sun samu wannan arziƙin although abun hannunta baki ɗaya bai dameni ba domin shi kuɗi yana cikin manyan abubuwa dake gurɓata Alaƙa. "Ina za muje to"na tambaye ta. "Idan na faɗa Miki ai ya tashi a surprise kuma "ta bani amsa tana dariya. Yanke shawarar driver ɗin nata ya aje su Hauwa'u gida nayi idan ya so mu sai mu hau adaidaita sahu.a Haka muka tsayar da maganar muna jiran lokacin tashi ya yi,haka kawai na ƙagu naga Wannan surprise na best friend ɗina kafin naje gida na tarar da na dangina na san suma sun shirya mun. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay EPISODE 2: unexpected sin *𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷* Tunda muka hau keke ni da Anisa tunanina yana gida duk da na cewa Hauwa'u ta faɗa ma Mama mun je duba wata ƴar ajin mu ne bata da lafiya,duk irin bin diddigi na Hauwa'u bata bi ba sai to da ta ce mun kasancewar ina tare da Anisa Sannan na san idan ta faɗama Mama haka zata amince tunda kowa ya sanni da Anisa,saboda yadda muke kowa a gidan mu santa yake har Baba. Kuntau muka nufa,dama ni bana da kuɗin motar zuwa kuntau ,kuɗin motana daga CBN Quarters ne inda makarantar mu take zuwa Tsamiyar boka Naira Ɗari ,sai wata ɗari da hamsin da nake da a jaka,haka nan ta bada 2000 mu biyu ko tayi bata yi ba. Koda muka isa Kuntau a ƙofar wani haɗaɗen gida Mai keken ya aje mu bisa jagorancin Anisa,kuɗinsa ta bashi ta kamo hannuna ganin yadda nake bin gidan da kallo,"gidan wane Wannan ɗin?"na tambaya ina bin ta. "Idan na faɗa Miki ai surprise ya tashi surprise kuma ,ke dai ki biyo ni,kin san ba zan kai ki inda za a siyar da ke ba ko?". Shiru nayi na bita,Knocking gate ɗin tayi,wani matashin Saurayi ne ya zo ya buɗe wanda kana kallansa ka san mai gadin gidan ne,gaishe mu ya yi nima na gaida shi amma Anisa kam gaba ta ci har a lokacin hannuna cikin nata,wayarta ta ciro daga side purse ɗinta ta kira ta ce "mun zo"kana ta kashe. Ni dai baki ɗaya na ƙosa naga Wannan surprise ɗin da za a yi mun ,Allah ya sani dan dai kawai Anisa ce ,ƙofar na buɗewa bata yi wata wata ba ta ja hannuna muka shiga ,Falo ne madaidaci mai kyau wanda ya tsaru da kayan ƙawa,"zauna ina zuwa".ta faɗa kafin ta Haura madaidaicin saman da a ƙalla zai ɗauki ɗakuna biyu,juye juye na fara ina san ganin wanda ya buɗe mana ƙofar, ƙarar waƙa mai sanyi da ya fara tashi ya saka na ƙurawa gurin da waƙar ke fitowa ido,cart ne ya fara fitowa ɗauke da wani ƙaton cake kafin mutumin da bana expecting ya bayyana yana mai murmushi ,tashi nayi tsaye cikin yanayi na kiɗima ,ƙarasowa ya yi inda nake yana mai murmushi bakin nan ɗauke da chewgum yana tauna kamar wata tsohuwar karuwa. Ƙokarin saita kaina nake gudun kada ya fuskanci halin da bayyanar sa ta jefani. "Yaya Adam"na ambaci sunansa,.ɗaga mun gira ya yi yana mai sakin cart ɗin mai ɗauke da cake ɗin da sunana ke rubuce gwanin sha'awa wanda da ace a gidan mu ne aka mun irin sa tsalle kawai zan fara ina murna saboda haɗuwa da ya yi,amma ina ta wani murna ina gaban ɗan iskan nan gashi Anisa ta wani haura ta barni,wallahi da na san shi zan tarar babu abin da zai saka na biyo ta. Yaya Adam cousin ɗin Anisa ne wanda ya daɗe yana nuna yana sona tun ina minor,akwai ranar da muka taɓa haɗuwa a gidansu Anisa har yake ce mun nazo mu je mu huta a hotel sai ya kai ni gida,tun daga ranar na tsorata dashi musamman da yake ta aikin bijiro da yana sona ita kuma Anisa baiwar Allah bata da masaniya sai tura mun shi take ,na tabbata da ta san ya taɓa mun zancen banza baza ta taɓa ƙokarin haɗani da shi ba,ni kuma gashi ina jin nauyin faɗa mata ɗan iska ne dan duk cikin cousins ɗinta Adam yana cikin waɗanda take shiri da su. Matsowa kusa dani ya yi ,kafin nayi aune ya rungumeni ƙam a jikinsa yana faɗin happy birthday love,ƙokarin ƙwacewa nake amma ya yi mun abin da ban taɓa tsammani ba,idanuna na zazzaro jin leɓensa bisa nawa yana ƙokarin sada bakinsa da nawa ,ban san lokacin da nayi masa wata irin mahaukaciyar hankaɗa ba,hannu na ɗaga na ɗaukesa da mari,take hawaye ya fara bi mun kunci ga wata karkarwa da ta kawo mun ziyara,hannu ya ɗora bisa kumatun yana mun wani irin ɗan iskan kallo yana lasar leɓensa kamar wani tsohon maye,ganin yana sake tunkaroni ya saka na wawuri ƙaramar wuƙar dake kan cart ɗin ina mai zazzaro idanuna ina nuna shi da ita. Bakina na karkarwa na ce"kana matsowa sai na Chaka maka wallahi".hannunsa ya ɗaga alamun surrender har a lokacin yana mun wannan ɗan iskan kallon da nake jin kamar nayi ta marinsa har sai wannan marin ya ɗauke wannan yanayin nishaɗin dake kan fuskarsa. "Zunairahhhhhh..."ya ja sunana cikin wata irin siga ta riƙaƙƙuna yan bariki. Cigaba nayi da nuna wuƙar jikina na karkarwa hankalina kuwa idan ya yi dubu ya tashi. Hanyar fita na nufa ,bai hanani ba bai kuma biyoni ba,burina kawai naga na fita a ɗakin dan bana tunanin Anisa ma,ina jin tana kiran sunana lokacin da na buɗe ƙofar na fita,biyoni tayi amma gudu kawai nake iya ƙarfina har na bar cikin gidan,Allah ya saka jakata na bayana ban sauke ba kuma ina da kuɗi a ciki duk da na san ba isa ta zai ba,hakanan na fara trekking ,sai da na rage tafiya sosai kafin na samu wani mai adaidaita sahu ya ɗaukeni akan Naira ɗari biyu da hamsin ya aje ni tsamiyar boka. Na jima a bakin layin mu ina saita kaina gudun kada kowa gidan mu ya fahimci halin da nake ciki sanin cewa a yanzu suna nan suna jirana. Da sallama bakina na shiga gida ,banga kowa tsakar gida ba kai tsaye na shiga Falo ina sake jaddada Sallamata,cracker ɗin da aka saki ya razanani kafin suka fara fitowa daga ɗaki da cake madaidaici hannun Baba suna masu mun waƙar happy birthday.take na fashe da kukan da nake jiran nayi,cikin tashin hankali Mama ta ƙaraso ta kamani jin yadda na fashe da kuka. "Seduwe suné? "(mai yasa ki ke kuka?)Mai ya faru?,mama ta tambaye ni cike da damuwa. "Ayamo hine"(ina farin cikine)Mama,na kasa riƙe kukana. Rungumeni mama tayi,tana mai kissing kaina kafin su Baba suka ƙaraso suka bani runguma baki ɗayansu,take naji dukkan wata damuwata ta yaye,haka nan na sake ina mai jin kamar babu abin da ya sameni. Mama ta bani ƙyautar wata azurfa da nake ta maitar ta bani amma tace Maman baba ta bata baza ta bani ba,Baba kuma ya bani set ɗin Eweh(beads)wanda aka kawo daga kogi ashe yana ta ajiyar su yana jiran birthday na yazo ya bani,sarka ne da ɗanƙunne da abun hannu masu kyau. Hauwa'u ta bani sabon journal mai pen a jiki wanda ta tara kuɗin break ɗinta ta siya mun . Muhammad kuma ya bani set na pens ɗin barbie doll masu kyau wanda Hauwa'u ta shiga sahad da kuɗinta da nasa suka siya mun. Al'adar gidan mu ce sharing gifts ranar birthday kowa yana san Faranta ma ɗan uwansa ,ba san kai ba yan gidan mu muna da san junan mu da tausayin juna. Haka ranar ta ƙare mun cikin farin ciki,duk yadda zan yi na yi ganin na manta da wani Adam da abin da ya yi mun,abu ɗaya na sani wanda shine ban yafe mishi ba ,Allah ya isa na,sa'arsa ɗaya ɗan uwan Anisa ne da saina mishi wulaƙancin da bai taɓa tunanin zan mishi ba,amma kash duk wani abu da ya danganta da Anisa mai daraja ne a gurina. Washegari muka yi shirin makaranta kamar kullum ,Muhammad muka fara ajewa kafin muka wuce namu gurin,na riga Anisa zuwa kasancewar babu assembly ranar ya saka direct aji na wuce ina mai jin kunyar haɗuwa da Anisa haka nan kawai dan Ban san mene zan faɗa mata ba. Latti tayi na zuwa dan lokacin da ta shigo har an fara first class,a chan sit ɗin baya ta zauna kasancewar namu an zauna ,naji daɗin hakan dan ko kallonta ban bari nayi ba.malamin na fita daga class ɗin Economics teacher na tsaye yana jiran sa ,ba ƙaramin daɗi naji ba duk da na san dole muyi magana amma atleast na samu break. Ille kuwa ana fita break ta dawo gurina ta zauna,ina ƙokarin tashi ta kamo hannuna ta ce "kamar muna da pending magana,mene ya saka ki ka gudu ina ta kiran ki baki ko juyi kin kalleni ba?,wani abu Yaya Adam ɗin ya yi Miki?". Ajiyar zuciya na sauke kafin na zauna ina mai kallanta"Ni nace miki ya yi mun wani abu?,kawai ina tsoran kada nayi dare ne". "Zunairah kenan,i thought na faɗa Miki har gida zan sauke ki and na yi imani da Allah idan Mama ta ji tare muka fita babu abin da zata ce,ban ji daɗi ba,he told me ai daga ya ya hugging ɗin ki ne,he was wrong for doing that duk da ba wani aibu bane shi yake gani a gurin sa amma ai da kin tsaya,har magana nayi mishi ya ce na baki haƙuri,ki yi haƙuri".ta faɗa tana mai bina da kallon da ta san bana iya ce mata a'a idan har ta marairace mun, although bai faɗa mata part ɗin kiss ɗin ba nima sai na zaɓi da na ɓoye mata. "Dan Allah kinji ki yi haƙuri ba zai ƙara ba na Miki alƙawari"ta sake faɗa tana mai marairacewa fiye da farko. "Naji na haƙura but gaskiya ba zan iya cigaba da kula Yaya Adam ba ,yanayin rayuwarsa da tawa ba iri ɗaya bace Anisa kema kin sani,da ace wani ne ma da wallahi sai na masa wulaƙanci but ɗan Uwanki ne ,ni kuma duk abu indai ya dangance ki ba zan iya mishi wulaƙanci ba". "Baki haƙura ba kawai zakice mun besty,nace Miki ya ce fa ki yi haƙuri ba zai sake ba, besides har kyautar da ya tanadar Miki ya bani na baki zai baki haƙuri da kan sa".hannu ta saka ta ciro ƙwalin waya na Tecno ƙirar pop 10. Dariya kawai nayi taƙaitacciya,yo ko giyar wake na sha ita kanta ta san ba zan taɓa karɓar wayar yaya Adam ba,koda kuwa ita ta bani ba shi ba zan ƙarɓa ba,sai nace da iyayena mene? "Bafa zan karɓi wayar nan ba Anisa ba da wasa nake ba,So ki ke na shiga uku hannun Baba da Mama su ce dan basu bani bane and Baba ya yi mun alƙawari ina gama secondary school zai bani waya so i want to give him that chance bana san sage masa gwiwa, understand me please". Mayar da wayar tayi haka without further nagging kafin ta ce"its okay,so Daddy ke tambayana wani course zanyi idan naje BUK,like duh I told this man fa Journalism muka zaɓa but this man is trying to push me to public relation ni ba zan iya ba muna tare a Buk,idan ban samu ba ko ke baki samu ba i will stick to wanda kika samu ke koda Kazaure ne,so suke su turani Canada ba zan iya ba" Ɗan shiru nayi ina nazarinta,ina mamakin Anisa ,wai ka samu damar tafiya Canada ka samu karatu mai inganci amma kace kai a'a ba za ka je ba, Journalism shine burina ,naji ance a bangarensu ana rubutu,burina naga ina rubuta Jarida na shirya dukkan wani content ɗinta abun haka kawai yana bani ƙawa,lokacin da zamu yi jamb Anisa bata cike ba sai da na cike kafin ta cike duk wani abu dana saka a nawa kama daga management school,second choice,Kazpoly ,da makarantun Fashion and design,ko da nayi mata Magana akan kada ta biyeni sai cewa tayi idan babu ni babu ita,abun yana burgeni sosai Wallahi amma bana san ace ta cutar da kanta dan kawai tana san alaƙarmu ta ɗaure,Bature yace out of sight is never out of mind,ni dai na san duk inda Anisa zata shiga a faɗin duniya ba zan taɓa cireta a Zuciyata ba haka nan ita. "Idan har yana san naje Canada ɗin ya biya mana tare". Murmushi nayi lokacin da maganarta ta jawo ni daga duniyar tunanin,Baba ne zai barni naje Canada da kuɗin wasu?tab har yanzu Anisa bata san su wane iyayena ba,bamu raina namu bamu hangen na wani. Tashi nayi na ɗauki jakata ina cewa"well Journalism is my purpose,I found my purpose a chan ban san mene ke ki ka samu a gurin ba,don't rush babes". "I found you"ta faɗa itama tana mai tashi,fara takawa nayi dan barin ajin tana gefena,dawowa tayi ta gabana tana takawa da baya tana cewa"idan ya zama na ɓata i want you to be there for me,na fi sabawa da ke ,Sabone da bana san wani daban ,i choose you babe,so your royal majesty Ohunene I want you to hold my hands and guide me in bayero University ". Ɗukawa tayi kamar yadda ake yi a gidan sarauta,ban san lokacin da na saka dariya ba sosai musamman da ta kusa kaiwa bakin kofa,kin faɗa mata nayi na cigaba da dariya sai ji tayi ta bige. Dafa gurin tayi tana faɗin"occh you're wicked wallah Zunairah ".muna dariya a tare muka fita domin zuwa yin break. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay EPISODE 3:viper in her bosom. *𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰* Tunda ta rabu da zunairah bayan tashi makaranta take jin ranta ya mata wani irin nauyi,babu abin da ke ɓata mata rai kamar yadda a kullum zunairah ke nuna ita mutuniyar kirkice,yana ci mata tuwo a ƙwarya musamman da ya zama babu yadda za tayi sai dai ta ɓoye muddin tana so ta cigaba da naɗewa a sheƙarta,bata da wani buri da ya wuce a rayuwa a ce yau ta wuce zunairah,ta san cewa rayuwa ba gasa bace amma a nata fagen ta shata layin tsere tsakaninsu,dole ne duk yadda za ayi at the end of the day ta cinye wannan tafiya ta tsakaninta da Zunairah. Idan za'ayi jarabawa hana kanta sakat take burinta guda ɗaya wanda bai wuce taga ta fi Zunairah cinyewa ba sanin idan ba haka ɗin ya kasance ba ta gamu da kumfar baki a gida dan basu da aiki sai faɗin ta kalli dai Zunairah,basu taɓa nuna mata nata ya yi sai dai a ce da Zunairah ce da ya fi haka,kada ma mahaifinta ya ji labari,he like comparing them wanda hakan yana mutuƙar ɓata mata rai. Exam na ƙarshe ta wuce Zunairah wanda ta saka hakan a ranta matsayin farin wasan dan baza ta ɗaga mata ƙafa ba idan sukaje jami'a,yana ɗaya daga cikin dalilin da ya saka ta nace sai course ɗaya za suyi amma bayan haka ko burgeta aikin jarida bayayi,this is a war that she must win,kamar yadda zunairah tace Journalism is her purpose,ta yarda ita ba nata bane dalilin hakan ya saka take ƙara ƙaimi wajen ganin ta daketa a nata so called purpose ɗin da ta ke ikirari.koda ƙasar da tafi kowacce ƙasa tsadar da jin daɗi za a kaita tayi karatu baza ta je ba,tana nan Buk da zunairah taga tsakaninsu wane zai winning. Ɗabiun Zunairah na munafurci suna ɗaya daga cikin abin da ke ɓata mata rai,dan a nata yardar duk wani sumi sumi da zunairah take yi munafurci ne,ta bata waya tana wani faɗin bata so bayan ta san ko babanta zai siya mata waya ba zai iya affording wadda Adam ya bata ba,tana jin haushin dabi'unta na nuna bata san abin duniya,ko kayi mata Abu ta mayar dashi wani babban abu kamar wadda ka bama duniya,that particular attitude yana kaita maƙurar da take ji kamar ta shaƙeta sau tari. Ƙawance su ya fara lafiya ƙalau kafin ta san kanta tayi wayau dan a gida ko chocolate aka bata da suna nursery sai an bata na Zunairah take tafiya,ba zata ce ga yadda aka yi ba amma makarantar bata dace da tsarin arziƙin mahaifin Zunairah ba but haka nan ya saka ta ,haɗuwarsu ya fara da gurin zama da aka haɗa musu kafin term ya ƙare sai shaƙuwa ta ƙullo tsakaninsu tun kafin su san ma menene shaƙuwar,haka nan Anisa bata da aiki sai maganar Zunairah Buhari wanda hakan ya saka iyayenta suka santa sai suka ƙaunaceta kamar yadda suka ga ɗiyarsu nayi. Duk da cewa zunairah ta fi Anisa ƙokari bata damu ba ,idan tazo gida tana cewa an koya musu kaza zunairah ta cinye sai babanta ya dinga mata mitan zunairah zai koma siya ma abun daɗi da teddies Banda ita,har ga Allah a lokacin ko a jikinta dan takan ɗauki nata na gida ma ta kaimata,hassadar bata fara ba sai da suka shiga primary 5,haka kawai sai tana jin bata so ta fita,da suka zana Junior WAEC lokaci guda Zunairah ta zaɓi Art. Anisa was not expecting that dan tunaninta ƙokarin zunairah science zata kaishi,burinta bai wuce ta zama Doctor ba domin a tunaninta itama Zunairah haka ne dan har ta fara tunanin yadda za su fafata a Wannan fagen amma wai aikin jarida,haka nan ba dan tana so ba itama ta zaɓi Art ,abun da ke ƙona mata rai shine idan Zunairah ta ce mata wai ba purpose ɗinta bane,yo ai ta daɗe da aje wani purpose da kowa ke tunanin, purpose guda ta riƙe wanda shine wuce Zunairah a rayuwa. A ƙofar gidan su Adam driver ɗinta ya faka ta fito,kai tsaye ta shiga tana mai share gateman ɗin dake gaida ta ,shi kuma kamar masifa Indai zai ganta sai ya gaisheta. Kai tsaye tana shiga ta murɗa handle ɗin kofar falon ta shiga tana ƙwala mishi kira,jin bai amsa ba kuma tana jin motsi a sama ya saka ta haura ,duk takunta nishin da take ji yana kusanto ta,daga ɗakin yaya Adam ne,kai tsaye ta isa ƙofar ta murɗa,ba tayi mamaki ba ganinsa tayi kan mace yana ta aiki ita kuma tana ta faman surutai,basu ma san ta buɗe ƙofa ba dan haka ta koma dan jiransa dan ta san last abun da za tayi shine katsesa,iyayen Yaya Adam sun tafi vacation dan haka gidan ya zamana a hannunsa shi kaɗai yake sheƙa ayarsa. Bayan wasu lokuta taji suna saukowa suna ƙananun dariya,macen ta fara ganinta ,cike da tsoro ta dafe ƙirjinta dan bata yi tunanin ganinta ba dalilin hakan ya saka ta tsorata. Tsaki Anisa tayi tana mai bin su da kallo,yaya Adam ne ya sauko yana faɗin"sis Ani yaushe ki ka zo,You should have call me". Wani kallon ta masa kafin ta saka hannu cikin jakarta ta ciro wayar ta miƙa mishi ta ce"Zunairah taƙi karɓan wayarka Sannan ta ce dan Allah ka rabu da ita and Nima da nazo gidan nan na goyi bayan ta domin da ace na san kana fucking Yaya Hibba ba zan bada gudunmawa ta ba". Da sauri Hibba ta matso inda take tana cewa"innallahi cousin sis ta yaya zan fucking Yaya Adam?he's my cousin for God sake,Allah ya kiyaye, besides ni ba mazinaciya bace kada ki sake dangantani da wannan harkar ". Dariya Anisa ta saka sosai kafin ta sake miƙa masa wayar da yaƙi karɓa yana kallon ta"yaya Adam ka karɓa na wuce dan Allah,dan naga alamun yarinya ake san mayar Dani,for your information Yaya Hibba kina wannan Surutan na shigo baku ma san na shigo ba and ni a samanki naga Yaya Adam and it doesn't seem like yana koya Miki assignment ne". Shiru duka suka yi ,ganin ya ƙi ƙaraɓar wayar ya saka ta aje mishi kan kujerar ta juya ta fita ,biyo bayanta Hibba tayi tana mata Magana amma tayi mata banza. Hibba yarinyar ƙanwar Mahaifiyar Adam ce,bangaren Anisa kuma yarinyar ƙanwar mahaifintan ce, tunda mamanta ta rasu ta baro Nassarawa ta dawo gidan su Anisa ,duk yadda mutanen ƙauyen Aila na ciki Benue suke mitar ta dawo ta zauna da yan uwan mahaifinta abun bai iyu ba dan a cewar Mahaifin Anisa Hibba baza ta iya zaman ƙyauye ba tunda ko iyayenta ɗin cikin Lafiya na Nassarawa suke da zama,tun lokacin ya dawo da ita gidansa. Anisa ta ji daɗin zuwanta dan dama bata da yar uwa Yaya Halil kuma ba mazauni bane ,idan ma ya zauna ba hirar da take sakewa ba suke, its always about school da abin da take so a siya mata ,babu zaman wannan gossip ɗin na mata,amma Hibba kuwa zasu zauna su ɗan tattauna abin su duk da cewa Hibba ɗin ta bawa Anisa kusa shekaru huɗu. Abin da ya ɓata mata rai da abin da ta Kama suna yi da Adam shine ɓata mata Rayuwa da yake,ta san Yaya Adam baya ji amma bata taɓa tunanin zai bi ta gida ba ,a hakan ko Zunairah a wannan gaɓar dai bata fatan mata ya lalata mata rayuwar,Hassadar da ke tsakaninsu bata tunanin a Zuciyarta ta kai wannan stage ɗin,wani lokacin idan tana irin wannan tunanin sai tama rasa ina ne ta dosa a tafiyar,shin har yanzu tana san Zunairah ɗinne kamar farko ko kuwa competition,idan competition ne mutane kan bin ko wane irin logic domin gannin sun cinye amma a Wannan gejin ta fi son Free and fair competition,bai kai deep ɗin da zata so Adam ya lalata ta ba dan haka dole Ya manta da Batun Zunairah. Tana shiga gida a falo ta tarar da mahaifiyarta tana kallo,abun da ta tsana ta tambayeta shine abin da ya fara fita bakinta bayan sun gaisa,wai ina Zunairah. "Tana lafiya"ta bata amsa a taƙaice kafin ta yi ƙokarin shiga ciki domin Cire kaya. "Ya kamata dai ta kawo mana ziyara ". Tana jin Muryar Enen na mata maganar tayi mata banza ta wuce ciki, enough Zunairah drama for the day,sai a jira na gobe (Enen da Idoma shine sunan da Anisa take kiran mamanta,ma'ana Mama). Bata jima da dawowa ba Hibba ma ta dawo a tsarge domin duk a tunaninta Anisa ta faɗa abin da ta kamata tana yi,idan kuwa ta tona mata Asiri ta shiga uku dan ta san ƙarshen zancen sai ta koma Benue ,ganin sun gaisa da Enen faran faran ya saka ta doshi ɗakin Anisa,kwance ta tarar da ita kan cikinta tana danna waya,zama tayi gefenta,ko kallonta Anisa ba tayi ba ta cigaba da taɓa wayar cike da tsoro ta fara magana . "Nisa I'm sorry Mana,it's not like Ina bin maza ne,Ni da Yaya Adam muna soyayya ne and bana tunanin big deal ne dan mun ƙarama soyayyarmu ɗanko ,i just want you to understand Aurena zai yi". Da Mamaki Anisa ke kallonta kafin ta ce"shi Yaya Adam ɗin ya ce zai Aureki?". "Eh". Wani dariya tayi ƙarama kafin ta tashi ta zauna ta kamo hannun Hibba."yaya Hibba you deserve better than Yaya Adam, he's a user and definitely yana using ɗinki ne kawai dan ya biya ma kan sa buƙata amma there is no way on earth da Yaya Adam zai yarda ya Aureki bayan kin bashi jikinki,wallahi ƙarya yake,I'm not judging you tunda abin da ya faru ya riga ya faru amma gaskiya ki fita harkarsa If not zaki barni da rashin zaɓi na faɗawa Enen". "Insha Allahu ba zai kai nan ba ma Neesa na rabu da shi I'm sorry".ta faɗa cikin zaƙuwa da san Anisa ta yarda da ita amma babu ma yadda zai iyu ace wai ta rabu da Adam zadai ta zama careful gaba kada a sake kama su." 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) EPISODE 4:when life gives you tangerine *𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷* Kamar da wasa muka fara zana jarabawa har ya kai da muna kan rubuta tourism paper ɗin ƙarshe,dukkan yan set ɗin mu kowa uniform ya sha guga ga graduation gown da muka sha Sky blue jira kawai muke mu gama muje mu haɗu da iyayenmu dan ko ni tare muka zo da Baba da Mama,dama su Hauwa'u an basu hutu, Theater Hall ya sha decoration inda nan aka aje iyayen Yara inda mu kuma muke jarabawar ƙarshen mu cikin Rehearse Hall,baki ɗaya papers ɗin a Theater Hall muka yi kasancewar ya fi girma da ya zamana kuma za'ayi amfani da shi sai aka gyara mana Rehearse dan mu yi a ciki. Zumuɗi kawai nake da murnar da ya saka ina gamawa ban tsaya wani Cross checking ba nayi submitting,dama Tourism ba wani wahala ne da shi ba,ina fita Anisa ma ta fito,cike da wani irin ihun murna muka rungume juna muna masu faɗin"we are graduates" Sir Umar Ali ne ya leƙo yana mai faɗin"Mss Buhari and Ms Ibrahim I'm sure kun san wasu basu gama exam ba,so I will appreciate it idan ku ka samu guri ku ka zauna har yan uwanku su fito ku yi making entrance cikin Theater Hall as real graduates". Ƴar dariya muka yi a tare kafin muka samu guri muka zauna hannunmu cikin na juna ,cike da zaƙuwa Anisa ta ce"best farin ciki nake wallahi na kasa yadda wai yau zamu bar bright scholars,and guess what yau har da Yaya Halil aka zo mun". Ganin yadda take ta giggling ya tabbatar mun tana cikin farin ciki ɗin har zuci musamman batun zuwan Yaya Halil, he's always absent duba da yanayin aikinsa gashi Anisa na masifar ƙaunarsa kamar ranta. "Gaskiya dai Yaya Halil ya kyauta da ya samu zuwa"na faɗa ina mai tayata murna.sake damƙe hannuna tayi tace"girl I'm beyond happy,ai ya sani na faɗa masa idan bai zo ba wallahi sai bikinsa zan tsiro zuwa ƙauye,matarsa kuma bani babu ita ta kuma haɗu da ƙanwar miji". A tare muka saka dariya ina cewa"wa ya ga Anisa ƙanwar miji da kanta". Muna nan zaune aka fara fitowa kowa da nashi salon nuna murnar,bayan duk mun gama fitowa Principal ɗin mu da taci gayu cikin kaya kalar graduation gown ɗin mu ta shigo tare da vice ɗinta da sauran malamai,cike da murna tayi addressing ɗin mu kafin muka haɗa layi guda,tana gaba crew na kiɗa na baya,a haka muka fita da parade har cikin Theater Hall,abun gwanin sha'awa haka appearance ɗin mu ya kasance ga iyayen mu,sai da muka shiga kafin kiɗan ya tsaya,tafi gurin ya ɗauka ganin yadda duka muka cire hulunan mu maka ɗora so a kafaɗa muna masu musu duƙan girmamawa da kai,kai kace a command muke,gurin muka samu muka zauna banda masu muƙami,dama Ni ba prefect bace,Anisa ce labor prefect ,layi sukayi su shida inda shadow prefect ma su shida,vice principal ne ya sanar da handing over da zasuyi na beret ɗin su,dama abun ka da aka daɗe ana practice kada aji kunya,band ne suka fara ƙida inda prefects ɗin suke parade a hankali suna masu bin ƙidan,umarni commander na parade ya basu da su cire hulunan su su ɗora bisa kafaɗa,suna cirewa suka taka da parade zuwa gaban shadows ɗinsu ko wacce ta ɗora beret bisa kan wadda zata maye gurbin ta,tafi gurin ya ɗauka inda iyaye da dama suka tashi suna ɗaukar hoto da bidiyo, bayan sun gama kowa ya koma ya samu guri ya zauna. Sosai principal ta tsara komai dan kuɗin da muka bayar ba da wasa ba,ya ci sunansa kuɗi,bayan gudanar da bikin raba kyautuka inda naci har guda biyu,punctuality da kuma zama ciki head na top 5 ɗin aji,Anisa kuwa guda uku ta samu,na aikin da ta gudanar da tana prefect da na zama ta biyu cikin top 5,da kuma na gayu,bata wasa ba da aje karin guga a kaya,iyaye suka fara fita kafin mu,muna fita na rungume Anisa ina tayata murnar kyautukanta,da murnar itama ta tayani har tana tsokanata tana cewa"na kwace mata head of top five but ta bar mun". A haka muka riske iyayenmu a wajen gurin,ban mamakin ganin su tare da yan gidan su Anisa ba,ina zuwa Hauwa'u ta ɗane ni tana faɗin"congratulations love,yayata ta zama graduate"kowa sai da abun ya bashi dariya wanda ya saka naji kunya musamman ganin Yaya Halil yana darawa sosai, "Sauka a jikina ni ji yadda ki ke kunyatani kamar wadda na gama University , secondary dai nagama"na faɗa ina mai ƙin sake haɗa ido da Yaya Halil wanda rabona da shi har na manta,zan iya cewa tun Muna primary,shekarun kam da yawa,ya sake kyau da Haiba abin sa kamar ba yayan Anisa ba dan ya fita kyau sosai. Gaishe da iyayen Anisa nayi inda ta gaida nawa wanda suka amsa mu cikin soyayya,Daddyn Anisa ne ya dafa mun kaina ya ce"my daughter head of best five cikin class of 25, you're blessed,Allah ya Miki albarka,naji daɗi sosai"godiya na mishi ina mai jin Yaya Halil na kirana da Brainy ,ƙanwata kuwa batayi ƙasa a gwiwa ba wajen cewa:"ai Guruwa ka ke ji Yaya Halil,tana bacci ma tana karatu".dariya mukayi. "Daddy atleast ka ce congratulations tunda ba na ashirin da biyar ɗin naci ba".Anisa dake gefen Yaya Hibba ta faɗa. ENEN ce ta yabeta ta hanyar cewa,"kin san muna alfahari dake ,shi yasa muna san kasancewar Zunairah a rayuwarki,Allah ya sake haɗa kan ku ya kawar da shaiɗan tsakanin ku". "Amin"muka amsa a tare ,bouquet ɗin Naira ɗari ɗari Hauwa'u ta bani tana mai cewa"gashi nan na 10k Ni da Muhammad,and I made it with love "ganin ina mata kallon ban yarda ba ya saka ta rumtse Idanunta ta ce"naji Baba ya cika mana amma ai zamu biya sa na faɗa mishi bashine so don't give me that look,". Dariya Anisa tayi wanda ya Saka Nima ɗin nayi kafin na ƙarɓa bouquet ɗin da chocolate a wani ƙaramin box, Hauwa'u kenan akwai sai ire iren waɗannan abubuwan, hotuna muka ɗan yi kafin muka yi haramar kama gaban mu,gayyatar mu taron walimar da za a yi ma Anisa iyayenta suka mana amma Baba ya basu haƙuri kan Nima walimar zasu haɗa mun,sun so a haɗa amma Baba ya ƙi,haka nan suka haƙura. Bayan kowa ya ɗauki hanyar motar su na koma Hall dan nayi matuwa,ina jin Anisa na faɗa mun ita kam ta tafi mu haɗu wajen school. Slum book ɗina na manta wanda dukkan wani detail na yan ajin mu yana ciki sun cike . "Hope ƙanwata ta ga abin da take nema". a tsorace na juyo dan ban yi tsammanin sa ba."Yaya Halil?"na faɗa cikin sigar tambaya,kan desk ɗaya ya zauna yana mai ɗaga mun gira ɗaya kana ya ce"hala ba kiyi maraba da ganina ba,dama na zo ne na tayaki neman abin da ki ke nema,Allah ya sa ban laifi ba". Murmushi nayi ina mai girgiza mai kai kafin na ɗaga slum book ɗin ina mai nuna mishi,karɓa ya yi,kamar ya buɗe sai kuma ya nuna yana murmushi ,hannu ya saka ya ciro bandir na kuɗi ya miƙa mun,kallon kuɗin nayi kafin na kalleshi,zuba mun ido ya yi Nima na zuba mishi,ki ƙarɓa tunda ban siya miki komai ba kuma kun ƙi yadda da zuwa gidan mu so wannan ne kyauta ta. Girgiza kai na fara ina faɗin"Nagode Yaya Halil amma ba zan karɓa ba Allah,dan Allah kada kace sai na karɓa"ganin da gaske nake duk na ruɗe ya saka ya mayar aljihunsa ya ce"na ji amma zan siyo Miki kyauta na kawo Miki har gida amma sai kin karɓa". Murmushi nayi ina mai yin ƙasa da kaina ban iya faɗin komai,wayarsa ya miƙa mun,kallon wayar nayi na kalleshi,."ki karɓa ki saka mun number ɗin ki,I'm very sure kin san ba zan gane gidan ku ba sai na kira ki". "Yaya Halil ai bana da waya"na faɗa mishi ina ɗan murmushi. Da mamakin faɗin bana da waya ɗin da nayi ya buɗe baki kafin ya ce"ki ce dai baza ki bani number ɗinki ba saboda kada yayanki yace yana sanki". Haka nan sai naji kunyar maganar sosai da ya saka na kasa haɗa ido dashi illa sake tabbatar mishi da nayi wallahi bani da waya,ya yi mamaki wanda ni ban ga abun mamaki ba ,haka nan muka jera a tare yana mai ce mun zai dai zo ko ya ya ne amma dole zai kawo min gift. "I'm sure yanzu ina komawa gida zan tarar da waya Baba ya siya dan dama ya ce ba zai siya mun waya ba sai na gama makaranta".na tsinci kaina da faɗa Mishi gudun kada ma ya siya mun waya dan na san kaɗan daga aikin sa kenan ni kuma Allah ya san ba zan taɓa karɓa ba. kawar da zancen ya yi ta hanyar nuna burgewar tsarin Baba,haka ya yi ta jana da wasa yana mai sake tabbatar mun ko da waya ko babu zai zo gida kuma muna da magana mai girma ,da haka muka yi sallama,already su Anisa sun wuce hakan ya saka ya wuce motarsa bayan ya sake sallama da su Mama. Da muka koma gida ƙaramar walima suka haɗa mun ,mama Ta yi mun abinci mai daɗi da kaza Baba kuma ya bani kyautar waya ƙirar Infinix smart 10, Murna kamar zan yi mene,addu'a na ɗinga bin Baba da shi dan sosai naji daɗi wanda bana iya misaltawa,murnar da Hauwa'u da Muhammad ke tayani sai ka rantse su aka siyawa wayan,ina kan wannan murnar ban fita daga ita ba Baba ya sake kasheni da wata,hannunsa da ke miƙa mun Laptop nake kallo,nuna laptop ɗin nayi kafin na nuna kaina ina mai kallan Baba ,ƴar dariya ya yi ya kaɗa mun kai kafin ya ce"ga system nan saboda makaranta da assignment da ɗan abun da baza a rasa ba".ban san lokacin da na rungumesa ba ina kuka. Haka ranar ta kasance mun ranar farin ciki da jaddada soyayyata da sake tabbatar da muddin na rasa dangina na shiga uku. ******************************************* *𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰* Tunda ta shiga Mota wani tuƙuƙi ya tare mata maƙoshi Idanunta da tunaninta sunƙi fita daga bouquet ɗin da Hauwa'u ta bama Zunairah,ta san ba ƙaramun party za'a haɗa mata ba a gida amma ta so itama yadda aka kawowa zunairah money bouquet a kawo mata wanda yafi nata ,ga babban abin da ya sake shaƙa mata shine ganin yadda Daddy ke aikin koɗata dan ta ci na ɗaya,that was supposed to be her place amma ta sace Mata,tunda suka shiga motar take expecting mitar Daddy,ta so ta hau motar yaya Halil amma ya ce shi ba gida Zaije straight ba,har ta cire ran ba zai maganar ba ta tsinci Muryarsa yana mai faɗin. "Yanzu Anisa baki ko da kunya ba,and baki jin cewa ya kamata ki Bama iyayenki masu sponsoring karatun ki haƙuri ba,i mean ina san sanin menene a upstairs ɗin Zunairah da ke naki upstairs ɗin babu". "Amma Daddy da 1 mark ne kawai ta wuceni fa,atleast ka ce mun sannu da ƙokari after all babu wanda ya wuce ni bayan ita ". Cike da spark ya Juyo yana mai cewa"shi 1 mark ɗin baza ki iya cinsa bane?". "Daddyn Anisa dan Allah ka kalli Titi kana tuƙine idan munje gida sai ayi maganar nan"Enen ta faɗa ganin ya mayar da hankalinsa kan Anisa ga kuma tuƙi yana yi . Zumɓura baki kawai Anisa tayi tana mai jin yadda yaya Hibba ke shafa mata hannu a hankali cikin siga ta lallashi. Koda suka isa gida bai ƙasa a gwiwa ba ya cigaba,ƙin tsayawa tayi a gurin ta wuce ɗakinta dan idan zata tsaya sauraron Daddy at the end of the day faɗa za suyi,ta yaya ma za a yi tabar Zunairah ta cigaba da winning akan ta idan sun je University?the more suna nuna mata Zunairah ta fita the more tana san ta ga ta buge ta a komai,ba dai winning suke so tayi ba,to yanzu suka fara . Shigowar Enen ya tsayar da ita daga wankan da ta yi niyyar shiga,wata gown ta kawo mata mai kyau,ajewa tayi kan gado kafin ta isa gareta,riƙe mata hannu tayi tana murmushi kafin ta ce"kinyi ƙokari yarinyana,cin na biyu ba abu bane mai sauƙi,". Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai rungume Enen kana ta ce"mene abin wahala idan daddy ya faɗa mun haka?Enen I'm trying ,Ina duk abin da zan yi ganin ban Bama Daddy kunya ba why this? kullum a rayuwarsa ban kai inda yake so ba,shin fault ɗina ne idan Zunairah ta ci Marks fiye dani?". Kaɗa mata kai Enen ta fara tana mai cewa"you're doing your best kuma kina yi yadda ya kamata kada ki biye ma Daddy and na san yanayi ne saboda ke, Sweetheart duk abin da ki ka ga iyaye sun yi a rayuwar ɗan su dan samun cigabansa ne because mu namu ya wuce,kada ki saka maganar Daddy a zuciya,and baki sani ba idan baki nan yana yabon ki". "To Enen ego ba zai barshi ya faɗa a gabana ba ko,I'm sick and tired ". Lallashinta Enen ta dinga yi har ta samo kanta amma deep down abin yana cikin Zuciyarta,babu ma yadda za a yi Zunairah ta cigaba da wuceta,idan tana da wani tunanin na Chanza makaranta a yanzu ta sake tabbatar da inda Zunairah ta je nanne itama zata je. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) EPISODE 5:unknown broken code. *𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷* Bayan ƙwana huɗu da gama makarantar mu,ina zaune ina gyarawa Mama egusi seed kafin ta dawo daga Barka da taje unguwa uku gidan wata ƙawarta,so nake nayi na gama na ɗora mata tuwan dan na rage mata aiki,na san halin Mama bata so a sa mata hannu a egusi ɗinta shi ya sa ban ma yi attempting ba Illa gyarawa da nake,ina san Miyan Egusi ɗin Mama daɗi kamar kada ka daina sha. Hauwa'u da Muhammad tare suka wuce islamiyya babu ɗan tayani hira sai sabuwar wayata da na ƙunna Haddar da zan bada ina ji lokaci guda kuma ina aiki,ƙofar aka ƙwanƙwasa kafin Kuma Muryar wani yaro ta bayyana inda yake cewa "wai ana sallama da Zunairah ". Wani irin faɗuwa gabana yayi dan sabon abu ne,Ni dai na san bani da wanda zai zo gurina dan ni ba saurayi gareni ba saurayi kuma shine kawai zai tsaya ƙofar gida yace ana sallama "Zunairah kuwa?"na tambaya jin yaron bai bar gurin ba. "Eh wai inji Halil"ya bani amsa yana mai barin gurin,da Mamaki nake sake maimaita sunan,wane kuma Halil?kamar ba zan fita ba sai kuma dai na aje tray ɗin na shiga ɗaki na ɗauko ƙaton hijab ɗina na fita,Turus nayi lokacin da idanuna suka sauka kan nasa,jingine ya yi jikin mota hannayensa naɗe bisa ƙirjinsa,baƙin yadin da ke jikinsa ya saka haskensa ya bayyana, Murmushi yake watso mun wanda yake bayyana haƙoransa,gira guda ɗaya ya ɗaga mun gannin na tsaya ni ban koma ba ni ban ƙarasa ba. "Ko ba a maraba dani na koma?" "A'a Yaya Halil ina dai mamaki ne yadda ka san gidan"takowa nayi ina mai bashi amsa har na isa inda yake ina mai yin ƙasa da kaina na gaishe da shi cike da girmamawa. "Lafiya lau yan mata sanin gida kuma ki daina mamaki ai mai san ɗaukar abu a guri baya bari ya yi ƙasa a gwiwa,well ranar graduation ɗin ku na bi ku a baya,I'm sorry idan nayi ba dai dai ba i just can't help it,like I promised na ce zan zo sai yau Allah ya bani iko".Buɗe gidan zaman baya ya yi ya ciro wata leda ya miƙa mun yana mai ƙarawa da cewa"ga kyautar ki,kamar yadda ki ka gargaɗeni a wayau ban sai waya ba,yanzu tunda ga waya a hannunki sai ki saka mun number ɗin ki". Kallan wayar dake hannuna nayi kafin na kalli leɗar,kamar ya san zan kawo uzurin da zan ƙi karɓa ne ya ce"bana san a mayar mun da kyauta, dan ke na siya kuma zaki karɓa idan ba so ki ke na je na faɗawa Mama ba,dama ina so na shiga mu gaisa". Hannu na saka na karɓa ina mishi godiya kafin na faɗa mishi Mama bata nan ni kaɗaice a gidan,ganin yadda nake ta jin kunya haka nan ya saka bai ja ni da surutu ba ya mun Sallama a kan za muyi waya,haka nan naji ni cikin wani irin nishaɗi da ni kaina ban san ya akayi na faɗa cikin ba,wani irin burgeni kawai na ji ya yi,idan za a tambayeni zaɓina dangane da namiji,zan iya cewa ina san mutum kamar Yaya Halil dan ya haɗu ta ko ina ,ɗan gayune sosai . Leɗar na buɗe dana shiga gida ,kayan ƙwalliya ne da Turaruka sai kayan cimma na ƙwaɗayi,wani ɗan box ne a wrapping wanda ke ɗauke da note ɗin da ya saka gabana Faɗuwa sosai,I LOVE YOU ZUNAIRAH,na karanta ya fi a irga ,buɗewa nayi ina mai zaƙuwa da san ganin menene a ciki,wani zobe ne wanda aka saka kalmar Z a cikin glass ɗin sa,ni dai ba sanin zobe mai tsada nayi ba amma daga gani mai tsada ne yadda yake ta ƙyalli abin sa,to na dai karɓi kaya ban san ta yadda zan faɗa ga yan gidan mu ba,zance na ɓoye ma bai taso ba Mama kawai zan fara faɗawa,da haka na yanke shawara da Zuciyata na kai kayan ɗaki na aje. Na gama ƙwashe tuwo na saka a leda kenan wayana ta hau ruri,number ce wadda truecaller ɗin ke Bayyana Halil Ibrahim, murmushi na tsinci kaina da yi kafin na ɗauki wayar bakina ɗauke da sallama,ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce"har na fara jin tsoron baza ki ɗauka ba". "Saboda mene ni kam zan ƙi ɗauka?na buɗe kaya nagode duk da sun yi yawa Yaya Halil". Ƙaramun murmushi yayi wanda ina jin sautinsa kafin yace"I guess kinga rubutun ciki mene amsa ta?". Wani irin kunya naji ina ji kamar wanda yake tambayata a gabana,tsintar kaina nayi da cewa "Allah ya sa ba tsaddaden zobe bane dan bana san in fita dashi a hannuna a sace ni". Cike da murna da san fahimta ta ya ce"kenan na samu ƙarɓuwa?, look Zunairah I've been having crush on you,tunda na ganki na farko naji kin burgeni,that's of course lokacin da ki ka fara girma,amma a ranar da na sake saka ki a ido a makarantarku,kin tafi da komai nawa da zan iya sauke wuyana ki hau,da gaske ina sanki Zunairah kuma Aurenki nake so nayi,amma ba zan miki dole ba idan ban Miki ba ki faɗa mun kin ji?".. Idan ance na kwatanta kaina a kan sikeli na ɗari a wannan lokacin ban ma san a nawa nake ba amma fa Yaya Halil ya ƙwamishi zuciyata duk da irin abun nan na mata zai hanani bada kaina da wuri dan haka na nemi da ya bari nayi tunani. Murmushin ya yi yana mai cewa "na samu karɓuwa kenan,ki ce na gyara zamana ,kin san idan mace tace za tayi tunani yana ɗaya daga cikin alamun nasara,yanzu dai ki ce naje na fara tara sadaki?". Kunya ta saka na kashe wayar ina mai jin Zuciyata na bugawa da sauri da sauri,na kasa yarda wai na samu soyayya a gurin da bana tsammani,wai ni da Yaya Halil?abun kamar almara,wayata na kunna na shiga last call ɗina da nayi da Anisa,na daɗe da number ɗinta a rubuce dan ta saka na mata alƙawarin ina samun waya number ɗinta zan fara kira,ana siya mun Sim kuwa ita ɗin na fara kira inda ta nuna mun murnarta kamar ma ta fini har tana faɗin itama ƙawarta ta fito fili,Sai da ta gama ringing ba a ɗauka ba,har wani tsuma nake burina na ji na fesa mata soyayyar da na samu daga yayanta,na san ba ƙaramun farin ciki za tayi ba ,ina ƙokarin sake kira kiranta na shigowa,cike da zaƙuwa ta ce"Besty guess what?Ina ta san kiranki ki ka kirani ya I've found love,baki ganshi ba ya haɗu iya haɗuwa,yaran ƙawar mummy ne Khalifa wannan immigration da na faɗa Miki ina having crush a kansa,kin gane sa?". Da murnar da na kasa ɓoyewa na kaɗa kai kafin na ce "Finally babe crush ɗin da ki ke bai tashi a banza ba,i can't believe this,tell me more". Cigaba tayi"ina faɗa Miki Walimar da Aka haɗa mun a gida suka zo to cut the story short bai tafi ba sai da ya faɗa mun yana sona and of course na amince,ki fara tanadar duk wani abu da ki ka san Aure ya ƙunsa,we have a wedding to plan". "To hajiyata ,yaushe aka fara soyayya da har kin fara maganar Aure?".. "Hmm Ohunene,you see that guy?he's mine and Idan ina kallansa ji nake kamar har mun yi Aure,muna nan da ke Aurena dana Yaya Halil za a haɗa dan daga samun budurwa jiya jiya har ya fara maganar Aure,ke ki ji zaƙewa da Daddy ya tambayesa sun daidaita wai sai cewa ya yi tukunna dai"dariya ta saka sosai a ƙarshen maganar ta kafin ta ƙara da cewa"Allah ya sa ba gaja bace ko wata ƴar talakawan yaje ya ƙwaso dan Wallahi idan bata mun ba ubanta zataci". Wani irin faɗuwar gaba naji ya sauka min, Chanza shawarar faɗa mata ɗin nayi na ja bakina nayi shiru har muka gama wayar duk da yadda zuciya ke ce mun na faɗa mata ɗan Wannan karan shine farko da na fara ɓoyewa Anisa abu,haka nan sai na tsinci kaina da tsoron faɗa mata nice duk da na san zata ji daɗi atleast ni ɗin aminiyarta ce dan haka na sake ɓalle maɓallin Zuciyata dan adana soyayyar Yaya Halil ta yi yaɗuwa,na san wannan karan ba zan samu karayar zuciya ba. Da mama ta dawo kamar munafuka haka na shiga ɗakinta,doguwar rigar da ta fita da ita take cirewa tana faɗin"bari na zo na ɗora miya Allah ya sa baki ɗora mun ba". "Ban ɗora ba amma Mama na kusa fara ɗorawa idan bana ɗorawa ɗin yaya zan iya?"na faɗa ina mai zama kan carpet da ledar a hannuna kamar wadda ta ƙwaso ganimar yaƙi. "Shi ya saka ai nake yi tare dake ,tunda komai tare muke yi,so ki ke ki lalatani idan kin fara makaranta ko kin yi Aure na shiga ta kaina,ki dai biyoni kitchen mu yi tare". Ƙarasa saka hannun rigar ta tayi kafin Idanunta suka sauka akan ledar da nake ta chikukuyewa baki. "shi wannan ɗin mene a ciki?" "Mama dan Allah kada ki yi mun faɗa ban roƙesa ba haka nan ya kawo mun and sai da na ce mishi ya yi yawa amma ya dage sai na karɓa wallahi ban roƙeshi ba". Hular dake hannunta ta saka ta ƙaraso inda nake ta zauna tana mai faɗin "taƙaita mun zance?wane shi wane ya baki let me understand "saurin tashi nayi ta kamo hannuna ta zaunar tana mai faɗin "Izewano?(Ina zaki?) Mene a cikin ledar wane kuma ya baki?". Na san tsakanina da Mama bamu ɓoye ɓoye,har soyayyata da nayi ta baya da Ma'aruf ta sani duk da ta kan kashede ni kan har a lokacin ban kai soyayya ba amma na kula,chance wanda zan experience menene ma soyayyar,da ya karya mun zuciya na faɗa mata ta sake jaddada mun dama irin wannan soyayyar ta gaji haka shima na saka shi cikin sanin wacece ni , menene zan ji idan soyayya ta bar ni Sannan ta yaya zan shawo kan matsalata,duk yana cikin karatun rayuwa,.a wannan bangaren na Yaya Halil sai na tsinci kaina da jin nauyi da kuma fargaba,ban sani ba ko dan ya ce Aurena zaiyyi?wanna idea ce da bata taɓa kawo mun cikin rai ba ban kuma taɓa tunanin samun soyayya ba ƙwana Kaɗan da gama secondary ɗina. Ledar Mama ta buɗe tana mai Ganin kayan ciki,sai da ta gama ta mayar kafin ta miƙo mun hannunta,kamawa nayi ina mai yin ƙasa da idona. "Kalleni nan"ta faɗa Idanunta cikin nawa,cike da nauyi na kalleta,tambayata ta farko itace"wane ya fara koya miki Sex education?". "Ke ce " "To ina so ki sani babu wani abu da zaki yi discussing da wani wanda ya shafi rayuwarki da ya wuce ni,ni Mahaifiyarki ce kuma abokiyar shawararki,mu kashe mu binne babu wanda ya ji which I'm very sure ba zan taɓa ɗora ki a kan hanyar da zaki cutu ba,haka nake da Mama na ina so kuma nima ace ina da wannan shaƙuwar da yarana,so now tell me kina san Halil ne?" Cike da nauyi na kaɗa mata kai inda ta umarci da na faɗa da bakina ba wai ɗaga kai ba dan tana so ta ji na ambata da bakina. "Ina san shi Mama"na bata amsa. Murmushi tayi kafin ta ce"that's very Good na san yaran kirki ne although ba wani sanin sa nayi sosai ba tunda ba zama nake da shi ba,but iyayensa mutanen ƙwarai ne wanda na tabbata ba daga gidan banza ya fito ba,bana da right na faɗa Miki wane zaki so da wane baza ki so ba,. "Kinga a time ɗin mu Mamana kance ba zan Auri bahaushe ba kada ma na fara kawo mata maganar bahaushe,to Nima lokacin bana ra'ayin su,amma yanzu kam rayuwa ta waye it doesn't matter yarene ko a'a Indai Musulmi ne kuma ɗan gidan tarbiyya babu amfanin banbance bambancen aƙida,it doesn't matter wai Halil yaron idomawa ne ,idan yana sanki yana girmamaki just go for it ki yi Addu'a muma muyi ta taya ku dashi,but one thing ki faɗa mishi babu unnecessary siyaya,i mean wannan kayan sun yi yawa,Allah ya yi muku Albarka ya rufa Asiri,but ki kula". Gaɗa kai nayi ina mai yin murmushi,har ta tashi ta nufi hanyar fita na tsinci kai da cewa"Mama zan iya saka zoben". Dariya tayi tana mai kallona kafin ta ce"ki Bama Hauwa'u ita zata saka ko ni ki bani sai mu yi ta yawo da symbol ɗin soyayyarki a hannu". Wata irin kunya naji ta kamani da ta saka na sunkuyar da kaina,.bata ɓoyewa Baba haka magana bata wuce kunnen ƙannena ba haka Hauwa'u ta yi ta rawar jiki wai sun yi siriki ɗan gayu. Kullum sai ya kirani duk da ban faɗa masa na amince ba sai da muka ɗauki sati guda a haka kafin na ɗauki hoton zoben dake hannuna na tura masa ta WhatsApp na aika mishi saƙon na amince,.Murna kamar zai maida ni ciki ta wayar , condition guda na bashi wanda shine siyayya mara amfani kamar yadda Mama ta Umarceni,ya amince amma ya ce ba haka ke nufin ba zai mun ƙyauta ba tunda ai ƙyauta na ƙara dangon ƙauna. Kafin na farga soyayya mai ƙarfi da Tsafta ta shiga tsakanina da Yaya Halil,har a wannan lokacin na Gagara faɗawa Anisa,haka zata Kirani ta bani labarin Khalifa idan ya zo gurinta da irin kyautukan da yake mata,neman lokaci nake da rana yadda zan sanar mata da soyayyar da nake da ɗan uwanta,dalilin hakan ya saka na hana ya faɗa a gida nice duk da ya so sanar dasu ɗin tunda a maganar da yake mun so yake ina shiga shekara ta biyu haka a jami'a ayi Auren mu dan na samu damar adjusting a makaranta tunda first year shine tushen gina karatunka. Shin yaya Anisa zata ɗauki soyayyar mu?tambayar da nakan yiwa kaina da yake sani fargaba,na san tana sona ba zata zamar min ƙanwar miji ba kamar yadda take faɗa,nasan alaƙar mu ƙarfi zata ƙara ,i can't wait naga irin farin cikin da zata nuna mun lokacin da ta ji nawa labarin farin cikin. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:6: curiosity *𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov Tunda na shirya zuwa duba Anisa nake jin gabana yana faɗuwa , tsoro nake ji kada wani daga cikin yan gidan su ya gano wani abu,ji nake kamar wadda nake wani abun mara kyau ko wata ɓarauniya da tayi sata take tsoron kada a kamata ,tace mun dai bata da lafiya,duk da ban san taƙamaimai abin da yake damunta ba amma yadda take son nazo na san bayan ciwan Labari zan sha ,duk da Mama bata san ina fita amma idan abu ya shafi Anisa bata saka Question mark saboda yadda da tayi da ita . Wayata ta hau ruri, ringtone ɗin da nasaka mishi na daban shi ya tabbatar mun da Wanda ke kira kafin idanunna suka sauka ƙan Sunan da nayi masa Saving da *Babyluv* wani irin faɗuwa naji gabana ya yi kafin na iya ɗauka bakina ɗauke da sallama ,ina jin sautin murmushin sa a lokacin da ya amsa ni ya ce"nayi ƙewar muryarki da fuskar ki Abar ƙauna". Daga tsayen da nake na zauna ina mai wasa da ƙafafuna ina murmushin ƙauna,ni kaina bana gane irin halin da soyayyarsa ke jefa ni,wallahi ina san Yaya Halil da yawa ."Nima nayi ƙewarka Babyluv,ba dai ka ƙi zuwa hutu ba kana can kana kallon yan matan Abuja,aikuwa video call ɗin ma na kusa daina ɗauka"na faɗa ina mai pouting baki kamar ina gabansa. Murmushi mai sauti ya yi kana ya ce"ki daina ɗaukar Video call ɗina fa ki ka ce,kina so ayi yaƙi a Kano,and yan matan Abuja babu wadda ke gabana ,besides da eyes mask ma nake yawo a bayan rigata kuma an saka Halil na Zunairah". Dariya na saka ,yaya Halil yana da barkwanci sosai,suna cikin ɗabiunsa dake burgeni,gashi baya da girman kai,ɗabiunsa na ƙwantar da kai ke sakani sake faɗawa soyayyarsa Koda na fito Mama da su Hauwa'u suna zaune suna kallon sharrin girkin Gabon,yau ranar hutun makaranta ne,kallona Hauwa'u tayi nima na kalleta nace"yanzu Hauwa'u bazaki rakani ba?". "Allah Antynmu ta kan mu baƙi zan yi ,ga Adavize ki ja ku tafi". Kafin na kira sunansa ma ya katseni ta hanyar faɗin"home work da rubutun hadda zan yi". Ganin yadda na ɓata rai ya saka mama yin dariya tana mai cewa"i thought baki so ana bin ki gidansu Anisa gashi nan yau kina so sun ƙi zuwa,sai ki yi tafiyanki su yau ne ranar su". "Ai wallahi babu wanda zan sake kai wa wani guri mama ki zama shaida"Sallama nayi mata na wuce inda take cewa na gaida Anisa da jikin na kuma gaida mata Enen ɗin ta sosai ,ban wani sha wahalar samun abin hawa ba kai tsaye ya saukeni unguwarsu Anisa ,na jima bakin ƙofar kafin na shiga dan ji nake ina shiga Anisa zata gane ina soyayya da Yaya Halil ,cire komai nayi a zuciyata lokacin da na gargaɗi kaina da "Zunairah ba sata ki ka yi ba ,Soyayyace babu kuma wanda zai ce Miki dan mene"a haka na shiga gidan bayan na gaida mai gadin gidansu. Babu kowa a falon nasu,sallama na fara ina hangen ta inda zan ga mutum,duk da na san hanyar ɗakin Anisa kuma Enen ta sha faɗa mun idan na zo ban ga kowa ba na nufi ɗakin ta,amma a yanayin tawa tarbiyyar baza ta barni na ƙutsa kaina kai tsaye ba kamar wadda ba Musulma ba,maimakon na zauna sai na fara kiran layinta ina kalle kalle. "Surprise!!!" Da sauri na juya jin muryarsa,Hannu na saka bisa bakina ina kallonsa da Mamaki dan ban taɓa kawo zan iske shi ba duba da mintuna mara sa yawa nayi waya da shi yana Abuja,takowa ya yi yana kallona yana murmushi kafin ya sake faɗin"I told you na aje Miki surprise amma kamar baki farin ciki da gani na". Kallonsa nake cikin ido ina mai jin shauƙi kafin na ce"amma mai ya sa kace mun kana Abuja?". "Well kamar yadda nace zan baki surprise gashi nan na baki,jiya da dare na dawo jin kin ce zaki zo duba Anisa ya saka na yi amfani da wannan damar ki zo na gabatar dake ga Enen taga wadda ke neman zautar mata da ɗa".ya ƙara maganar yana mai kashe mun ido. Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarceni,ƙasa nayi da murya ina mai kallonsa kafin na matso daf dashi idanuna cike da fargaba nace"babe ba munyi magana a kan haka ba fa, wallahi ban shirya ba". "Aikuwa ni na faɗa musu,abun da ba wani sharri muke aikatawa ba,Aure fa muke san mu yi ba wani abu ba mene ne ɓoyewa?". Jin amsar da ya bani da kuma yanayin da gaske yake maganar ya saka na juya ina mai cewa"idan na tafi sai ka faɗa ɗin amma kuma ba zan sake maka magana ba daga yau". Dariya ya saka sosai yana mai shan gabana yana faɗin"daga wasa,I'm just joking fa,idan ki ka daina mun magana sai nayi ya ya da rayuwata,ni wasa nake miki". "Wane irin wasa?". Muryar Anisa ta Iske mu,a tare muka juya wani irin fargaba na ji ina ji,ni kaina ban san mene yake damuna ba,ko mene abun ɓoyewa oho. "Wai yace baki nan ne har na juya zan wuce yake cewa wasa yake"na faɗa ina ƙarasawa gurinta,kallon yaya Halil take har na Kama hannunta inda shi kuma ya juya yana mai ɗauke idanunsa daga kanta ya yi bangaren da nake tunanin nasa ne. Sai a wannan karan ta kalleni kafin ta ce"idan ban sani ba sai nace Soyayya ku ke, dan yadda yaya yake kallanki wallahi sai wani ya rantse soyayya kuke ke da shi"dariya ta sake fashewa da shi tana mai faɗin baza ta iya misaltawa ba kafin ta ja hannuna muka shiga ciki bayan ta shaida mun Ene bata nan.Kallan ɗakin nata nayi ganin yadda aka canza komai,kamar ta fahimci kallon da nake ta zauna gefen gadonta tana mai cewa: "Kina kallon sabon design ɗin ɗakina hala?wallahi Yaya Halil ya canza mun komai,zo muje ki ga cikin wardrobe ɗin har da kaya". Fito da kayayyakin ta fara tana mai nuna mun,sunyi kyau sosai haka nan sai na jini cikin farin ciki kamar ni aka sauyawa kaya,ɗayan wardrobe ɗin ta buɗe tana mai cewa "ga nan waɗancan har da wanda sawa ɗaya nayi mishi,kin sanni bana da yawan maimaita kaya,har Enen ta ce za a fita dasu a kai gidan Marayu na ce ta aje Zunairah ta zo sai ta zaɓa". Wani irin zafi na ji a ƙirjina lokacin da ta faɗi maganar amma na danne ɓaccin raina na yi faɗa da shaiɗan ɗin da yake san hassalani na gwasile Alherinta,cikin mutunci na ce"aikuwa da kin bar Enen ta kai kayan nan gidan Marayu dan ba zan ɗiba ba , besides ai kin san cewa jikina da naki ba iri ɗaya bane". Kallo na tayi na daƙika kana ta ce"hope ba ɓata Miki rai nayi ba,I'm sorry ni wallahi ba da wani abu na ce ba,zo ki zaɓa cikin sabon ma dama inda da niyyar ɗiba miki wasu".ta ƙarasa zancen tana mai aje doguwar rigar da ta ɗauko tana buɗa mun ta nufi sashen sababbin,dariya reaction ɗinta ya bani, kafaɗarta na kama na juyo da ita ina mai faɗin"Ani I mean it ba zan karɓi kayan ki ba,and ba wai na ɗauki maganar da wani abu ba,kyauta ce fa ki ka mun ta hanyar san Faranta mun, it's just that kada ki manta kin fini jiki na fiki tsayi,Kinga kuwa kayan ki ba za su mun ba,yanzu bama wannan ba ya jikin ki mene yake damunki?kin san yadda ki ka tada mun hankali kuwa?mama na ta mun faɗa wai ban tsaya na ji mene yake damunki ba tun a waya". "Okay fine kin yi winning,jiki na da sauƙi,dama ƙoda ne ta sani gaba but I'm okay, although abun ba daɗi kwana biyu ɗin chan but yanzu ba Matsala,bari ki ga gifts ɗin da Khalifa ya kawo mun"ta ƙarasa maganar tana mai kwace hannunta daga nawa ta nufi ɗaya gefen wardrobe. Shan gabanta nayi cike da tashin hankali"ciwan ƙoda Anisa har ki kwanta asibiti amma ki kasa faɗa mun?rabu dani da wasu gifts abeg ya ki ke yanzu,ya jikin ?". "Stop being a drama Queen best friend,I'm okay and ni na hana Enen faɗa Muku,kin san na fi so a ganni a best halittana."kamo hannuna tayi wanda Idanunta suka sauka akai,cike da tsantsan Mamakin da bata yi yunƙuri wajen ɓoyewa ba ta ce"wane ya baki wannan zoben mai shegen tsada da aka yi engraving sunanki ciki piece of diamond?". "Diamond kuma?ba dai diamond ba".na faɗa ina mai mayar da hannun baya,kamo hannun tayi tana mai sake kalla lokaci guda kuma tana san cirewa daga hannuna wanda ban ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ban bari ta cire ba,amma fa jikina ya yi sanyi,wai diamond menene haɗin Zunairah da diamond?"" "Wallahi diamond Zunairah,zan kasa gane diamond ne ko zan Miki ƙarya?Wane ya baki?ina ki ka samu? Mu gani dan Allah". Gyaran murya nayi ƙarama kana na ce"zoben Alƙawari ne ,saurayina da nayi ya bani although da na san diamond ne ba zan karɓa ba"take ta rikice tana mai sake tambayata cikin ƙaguwa,wanene wannan guy ɗin?aikin mene yake,?,a ina ku ka haɗu da shi?,mene sunansa?,Dariya ta bani jin lokaci guda tana san sanin baki ɗaya Waɗannan informations ɗin a bakina,how wish zan iya faɗa mata,amma maganar zoben da ta tashi sai na ji ina san magana da shi kafin na sanar mata da yayanta ne dan haka na ce da ita zan sanar mata cikin ƙwanankin nan. Duk yadda ta yi nacin san sanin wanene ban iya faɗa mata ba ,a haka ta haƙura tayi respecting decision ɗina kan idan na shirya na faɗa mata wannan saurayi da nake ta ɓoyewa ,fatanta ɗaya Allah yasa ba ɗan yankan kai bane , murmushi kawai na ɗinga yi,har na hango fuskarta lokacin da ta san Gaskiyar,duk da rashin sanin wanene ɗin bata ɓoye irin farincin da take tayani ba har tana tsokanata na fito daga kogin san Ma'aruf zuwa ga mysterious guy,cikin hirar da muke ne na ce"yauwa Anisa,so nake na ƙarɓi Draft na littafaina especially Love Scenery ɗin nan". "Mene za ki yi da shi"ta tambaya tana mai nuna interest ɗin ta ,gyara zama nayi ina mai sake yashe baki "Kinga yanzu mun gama makaranta and ina da smartphone ina da laptop so nake na cigaba da rubutu a matsayin Career and Kinga Wannan Love Scenery ɗin?I was told zai karɓu sosai ". "Inji wane ya ce Miki hakan,i mean beside me wane ya san da shi?".ido ta zuba mun tana neman jin amsata wanda ban ƙasa a gwiwa ba na bata Amsa"wata marubuciya na haɗu da ita mai kirki,ina yawan karanta books ɗin ta kwana biyu da na yi waya so sai na tambayeta shawara because sananniyace and litattafan ta na fita sosai a Ebooks tana samun kuɗi,so na bata labarin idea ɗin da nake da shi especially na Love Scenery and she told me idan na sake shi duniya zata so shi,and she will be there to Guide me,ba ki ji yadda na ji daɗi ba, Although da farko i was beyond Nervous amma yanzu kam ji nake kamar ban taɓa shiryawa ma Rubutu ba yadda na shirya karɓarsa yanzun,i want the world to hear me shi ya sa na zaɓi harshen Turanci duk da zan rubuta Hausan idan tafiya ta yi tafiya but yadda Hausa na bai goge ba ina san na ƙara gogewa duk da masu jin Hausa kawai ne zasu karanta ,but it will worth it dan akwai issue da nake san addressing wanda society ɗin mu yanzu ke fama da shi a hannu ɗaya muma Kinga mun zama Hausawan tunda muna cikin su". "Kin zama dai amma ni Anisa har ƙwanan gobe Idoma na ke Ba abin da ya haɗani da Hausawa da issues ɗin su"ta yi saurin bani amsa. Dariya na saka dan amsar nata ya bani dariya,"idan banda abin ki Anisa ai Hausawa sun mana rana tunda muka zo garin su muka Zauna,ki cire cewa Khalifa Yaren Margi ne either ways dukka Muna da matsalolinmu, idan kuma ki ka zauna ki ka duba sai ki ga abun kusan iri ɗaya ne,duk yarukan da ke akwai idan mun yadda abu guda ne sai dai banbanci na Al'ada amma abubuwan da ke faruwa in circle guda ɗaya ne a matsayin mu na mutane". Taɓe baki tayi ta ce"ke dai ki ka jiyo,ni yanzu bama wannan ba drafts ɗin ki na littafi babu ko ɗaya da na san inda suke,but since kece ki ka rubuta I'm sure zaki sake har ma ki yi wanda ya fi wancan,i trust you,ko kuma ki sake labari because ba zan ɓoye Miki ba ba wani daɗi ya yi ba,don't take me wrong ita da tace ki rubutu ba karantawa ta yi ba,amma ni as a Bookworm na san irin littafan da ke ɗaukar hankalin masu karatu,Kinga Love Scenery ba zai taɓa ɗauka ba, besides yarinta ya yi yawa ciki which I can understand ya danganta da lokacin da ki ka rubuta shi," Shiru nayi ina nazarin maganarta,duk da ina san gamsuwa da batun nata amma sai na yanke shawara kawai zan rubuta shi ta wani salon na daban ba kamar new version ɗinsa tunda na riƙe labarin akai na,a haka ta bani ƙwarin gwiwa da tabbatar mun tana tare dani ɗari bisa ɗari. Har nayi Haramar wucewa Enen bata dawo ba,na so na sameta mu gaisa ,riƙe jakana Anisa tayi tana mai shagwaɓe mun fuska kan na ƙwana bata gaji da ganina ba, dariya nayi na miƙa hannuna ina mai cewa"bani jakata tukunna"maƙe kafaɗa tayi kamar wata yarinya wanda yin hakan ya saka na ƙara darawa ina mai jinjina ƙarfin halinta,horn ɗin da aka yi daga Chan ya saka a tare muka kalli gurin kafin ta ce"Kinga mu je ya Sauke ki,yadda yake ta haɗe ran nan ba san kai ki ɗin yake ba,na fi tunanin ƙwarjini ki ka mishi wallahi". Dariyata na ɓoye kafin muka taka ta rakani har bakin motar tana mai sake faɗin"yaya Halil kayi haƙuri dan Allah"ta bashi haƙurin nan ya fi irga, murmushi kawai nake ina mai hango abin da ni kaɗai nake gani a idanunsa. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da muka fita daga cikin gidan,dariya na saka wanda ya rasa abin da zai ce mun illa tayani da ya shiga yi mun dariya. "Wallahi za ka dace da actor irin wannan haɗe rai kamar mugembu ya ga Amitha,kai wai a dole an dameka kana hutawarka zaka ma ƙawar ƙanwa alfarma,okay oo in munje last bus stop sai ka aje ni kamar yadda ka ce da fari"na faɗa abin na sake bani Dariya. "Baby you caused all this,ni kuma bana so a ce na Miki abin da baki so,i will respect your decision,idan da ace zan bi abin da nake so,da zan nunawa kowa ke tawa ce ,idan na fara rawar kai kam,hmm sai kin ce mun ya isa haka,yanzu dai bari na fara kai ki shopping ina san na fake da hakan nayi ta ganin fuskar ki". Dubansa na yi kafin na ce "aikuwa baza ka kaini shopping ba plus dama ina san nayi da kai,mene ya saka ka siya mun expensive zobe, diamond for that matter?". Dariya ya sa wanda na kasa gane ta menene kafin ya ce"baby is just a piece of diamond,after all Bama pure bane duka,ki yi addu'a na yi kuɗi sosai zan siya Miki abin da ya fi na hannunki don kin yi Worthing more than duk wani abun da ki ke tunani,dan Allah ki daina magana idan na yi Miki kyauta sai ina ji kamar ban iya ba". "Aikuwa baka iya ba,dan baka iya siyan Abu kaɗan ba ko mai madaidaicin kuɗi,ba komai bane about spending unnecessary money,bance kada ka mun kyauta ba,ina dai so ka na kintatawa ka daina ɓarna da kuɗi,and ni ka sauke Ni gida Babu wani shopping da zanyi"na ƙara maganar ina mai ɗan haɗe rai. Ganin da gaske na haɗe rai ya saka ya samu gefe ya faka motar ya juyo yana kallona inda Ni kuma na sake haɗe rai na juyar da kaina ina mai kallon window,waƙar Auta waziri ya fara rera mun wanda yake faɗin sanki kamar ƙanƙara a ƙwalba,dariya sosai na saka ina mai toshe kunnuwana dan shi kan sa ba sai na faɗa masa ba, he's a terrible singer . "Thank God Kana da aiki baza ka fara tunanin ci da waƙa ba cos babu inda za ta je".jin abin da na faɗa ya tabbatar mishi da na haƙura dan haka ya cigaba da zolayana da waƙoƙin da na tsinci kaina a nishaɗi domin su ,baza ka ce mun da wani Age gap ba dan aƙalla zai bani shekaru goma sha amma yadda yake zama yaro gabana sai abin ya sakani cikin jin daɗin.i found duk abin da nake nema ga Yaya Halil,ƙwanciyar hankali, soyayya,Farin ciki,shaƙuwa,babu abin da ya barni ina lalube domin samu,bai bar wata kafa ba ,dalilin haka ya saka bana jin akwai wani ɗa namiji da zai kawo mun tangarɗa dan kuwa soyayyar Yaya Halil ta shiga ko ina na jikina,kamar dai yadda dabi'ata take haka nan na zura dukkan jikina sanin babu wani matsala da zata ɓullo mana da yardar Allah. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchu jay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:7: Love ,treat,threats. *𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov Cikin Aminci rayuwarmu ta cigaba da tafiya inda komai yake tafiya mun dai dai Álhamdulilah,kamar yadda na ayyana a raina zan fara rubutun Love Scenery littafina da draft ɗin sa ya ɓata haka ya kasance,komai na cikin littafin a yadda na rubuta shi a baya sai na gyara shi na sake tsarinsa ta wata fuska daban amma dai Story line ɗin da Characters ɗina duk sune,sai da na kamalla rubuta shi kafin na fara saukesa a kan manhajar Wattpad da inkit da Dreame amma abun mamaki yadda nake expecting ƙarɓuwarsa ba haka abun yake ba,domin da nayi ƙoƙari shiga paid program ɗin su lokaci guda aka yi rejecting ɗina bayan sun gama reviewing littafin,da nake faɗawa Adda Ramlat marubuciyar da ta ɗora ni a kan hanya sai take ce mun kada na sare ,ba lokaci guda nasara ke zuwa ba sai anyi faɗi tashi tukunna ,a hankali lokacin da baka tsammani sai kaga abun ya zo maka kamar saukar ruwa ,da ƙwarin gwiwar da ta bani na cigaba da updating a wattpad ina mai sakawa a raina yanzu tafiyar ta fara sa'ar kuwa bata ga mutum Ubangiji ke badawa. Ina ƙwance ɗakinmu ina typing a system ɗina Hauwa'u ta shigo da gudunta hannunta riƙe da wayana da na bata tana game,tashi nayi daga ƙwancen da nake ina mai matsawa da sauri kada ta takani kafin na ce mata "Ometere Are You okay? Mene hakan?". Zama tayi tana mai nuna mun wayar dake hannunta"Auntyna Kalli ki gani comments ɗin dake cikin littafinki na Wattpad yana cewa wai kin saci littafin wata writer ,kalli nan handle ɗinta midnight Authoress".tashi nayi ina mai karɓar wayar ba tare da na damu da Hauwa'u ta kunna mun data ba ta shiga mun wattpad much more har ta san ina rubutu,abin da ban taɓa tunanin wani a gidan mu ya sani ba,shiga handle ɗin dake ɗauke da sunan midnight Authoress ɗin nayi, idanuna kan Followers ɗinta guda miliyan biyar suka sauka,kafin Wannan verifying button ɗin wanda ke nuna Wattpad ma sun san da ita,a hankali na yi scrolling zuwa ga littafanta wanda sunan da yan comment ke ta ambata na littafin nata na fara nema "BLUE",kafin na fara ganin wajen Guda shida baya,Bio ɗinta na duba,mutuniyar Najeriya ce yar garin Abuja baya ga wannan bata da wani information nata da ta ɗora , wannan littafi Mai suna BLUE har watty program ya shiga ,gashi nan ɗauke da tambarin wattpad,fita na yi da zumar zan duba daga baya inda na cigaba da karanta hate comment ɗin da na samu ƙarƙashin Littafin,harda masu ce mun daga fara Career ta ta rubutu na ɓata ta hanyar satar rubutun wasu,na rasa kuma na wa zan sata sai popular writer kamar midnight Authoress. Ganin Hauwa'u nata zura kai ya saka na kashe wayar ina mai kallon ta kafin na ce "wane yace ki shigar mun wattpad?". "I'm sorry Aunty Zunairah ban tambayeki ba,amma bana tunanin abun ƙi ne dan an san a gida kina rubutu,kyauta ne Allah ya baki why hide it?kin fi kowa sanin Mama da Baba baza su taɓa ƙin baki goyan baya ba, you're not doing anything Bad,kin san dalilin da Baba ya siya mika laptop kenan,ya sani tun baya ,har Mama duk mun sani mun bi ki ne a yadda ki ke so". Shiru nayi ina mai kallon ta kafin na rumtse Idanuna na ce "yanzu it's all over ,babu wani amfani because na haƙura,I mean just look inda abun ya kaini ,i cant even face people tun kafin aje wani gurin,". Kafin na sake magana muka tsinkayi Muryar Mama tana mai cewa"yarinyana We fall ,we raise and we move on,babu wani Nasara da zaki gani a rayuwa wadda bata zo da faɗuwa ba,mu Danginki ne,duk abin da zai faru dake mune dai zaki juyo garemu ki bamu damuwarki mu nemi Solution,rubutu is not a bad thing na kasa fahimtar dalilin da ya saka ki ke ɓoye mana,but Either ways we respect and do as you wish,but Kinga Wannan ƙaramun tangarɗa da ki ka samu,kada ta dameki kada Kuma ki bari ta zama sanadin barin abin da ki ke so,we are here for you as a family and we will support you". I was emotional,ban san lokacin da na fashe da kuka ba na rungume Mama wadda ta fara lallashina tana mai shafa mun kai tana mai sake tabbatar mun komai zai zamar mun dai dai,one thing I love about my parent is that,a kullum suna koya mun how to Win ba wai na zauna na miƙe ƙafafuna ba and I love that,wannan lallashin shine ya ƙara mun ƙarfin gwiwa da ya saka na ƙi cire pages ɗin dana ɗora illa ma sai na saka ma raina ba zan daina rubuta Love Scenery ba ,sai dai at the end of the day zan Bama makaranta abun da Babu a BLUE dan haka na yunƙura domin karanta Abin da Wannan littafi ya ƙunsa,na sha Mamaki lokacin da na gama karatunsa dan Wallahi da ace zan ma marubuciyar nan rashin adalci zance littafina ne kawai ta sace,Amma tayaya ina Kano tana Abuja,na tabbata kawai saɓani ne. Idea daban na sake na cigaba da rubutu na ina mai ignoring comments ɗin jama'a,I'm sure I will be there ,koda Adda Ramlat ta kirani a waya itama ƙarfin gwiwar ta bani,ba zan manta da Alherinta ba. Admission ɗin mu ya fita cikin Aminci,inda ya zamana mun gama komai lecture kawai ya rage za mu fara attending,koda Monday ta zagayo idan ka kalleni za kasan ina cikin nishaɗi,Hijaban da Baba ya ɗinka min guda Shida na ciro ina tunanin wanne ma zan saka,haka na gama ruwan idona daga ƙarshe na ɗauƙi Farin ciki na saka,ina san Abu fari,yau da yake ranar Farko na ina san na zama mai Sa'a dan haka na zaɓi farin,na riga na chamfa Farin abu Sa'a ne a gurina,bayan mun gama Kari Baba ya fita da su Hauwa'u, kasancewar ba hanyar mu ɗaya ba ƙwataƙwata ya saka na ce mishi suje kawai Ni zan hau daidaita sahu,kuɗi Baba ya bani ya mun addu'a ya min Nasiha,daga bisani Mama ma ta sake jaddada nata a kan na kiyaye domin jami'a ba kamar Secondary bace,gurine da zan haɗu da mutane iri iri,da masu tarbiyya da akasinta,wasu idan suka ganka a suturce burinsu su girmamaka su tayaka riƙe mutuncinka,yayin da wasu burinsu Su bankaɗa kan su lalata maka tarbiyyar da kazo da ita. Har Mama ta rakoni ƙofar gida sake faɗi take"Ohunene ki kiyaye babu ruwanki da Malaman jami'a,wasu su basu da amana dan Allah". "Mama insha Allahu zan kiyaye"na bata amsa kafin nayi addu'ar fita daga gida na fita,a hankali nake tafiya domin fita titi duba da yanzu abin hawa yana ƙaranci cikin layin mu dole sai ka fita wajen titin,motar da ke biye a bayana na kaucewa jin motsin ta na koma gefe,horn aka fara mun ,kamar ba zan juya ba amma jin dani ake ya saka na juya ,Motar Habibi ce gabana murmushi nayi ina mai tsayawa ina kallon ƙofar da zai bayyana,fitowa ya yi yana ƙada key ɗin hannunsa,jakar da ke rataye a kafaɗata na sake riƙewa ina mai sake faɗaɗa murmushina, takowa ya yi ya ce"Babyn Habibi ,first day a university I hope baki tunanin zan barki ki tafi ke ɗaya?". "Wait kana nufin ka ce mun ka zo ne kawai dan ka yi dropping ɗina school?ba zan tambaya yadda ka sani ba Since Anisa ma yau zata fara shiga ,but ya ka san yanzu zan fito a makaranta,7:15 am "na faɗa ina bin sa da ido. Jakar hannuna ya mun alama da na bashi kafin ya buɗe mun mota yana mai mun alamun na shiga ,ba musu na tako na shiga, kafin ya rufe ya duƙo yana kallona kafin ya ce"kada ki manta i was once a JJC,Nima na je makaranta 7:00 farkon zuwa na". Hannu na saka na rufe ido ina dariya inda shima ya sa dariya kafin ya zaga ya shiga motar,haka ya dinga tsokanata ina biye sa ,koda muka isa makaranta na so ya ajeni bakin Gate gudun haɗuwa da Anisa amma ya ƙi,haka nan ƙirjina na dukan huɗu huɗu ya shiga da ni,sai da ya je bakin department ɗin mu kafin ya yi parking, kallona ya yi ganin yadda nayi tsuru tsuru yar dariya ya yi kafin ya ce"why are you behaving kamar ni da ke muna aikata abu mara kyau?na kasa yarda kina wannan abun ne saboda Anisa,for God sake ƙanwata ce bata da hurumin zaɓar wadda zanyi soyayya da ,ina sanki babu abin da Anisa ta isa ta yi dangane da hakan,besides za taji daɗine ace yau matar da ƴaƴanta zai Aura ƙawartace sun saba ba sai sun fara sabon shaƙuwa ba, at this point na fara tunanin ba Anisa ki ke ɓoyewa ba,maybe baki san na ɗauki step forward saboda kina tare da wani". Saurin juyowa nayi ina kallonsa dan ban taɓa tunanin zai zargi ina tare da wani ba bayan shi,"so all this while zargin da ka ke mun kenan?". "No Baby ba haka bane kawai na fara feeling insecure ne"hannu na ɗaga mishi kafin na ce"yaisa Nagode "buɗe motar nayi na fita ,yana ƙokarin buɗewa ya fito domin biyoni Anisa ta bayyana a gurin,ganina ya saka da Mamaki ta sake kallon motar,kafin ta ce wani abu ya yi ma motar key ya bar gurin,bin motar tayi da ido kafin ta dawo da kallonta gareni ta ce"wannan ba motar Yaya Halil bane?naga kuma kin fito a ciki yana ganina kuma ya juya kamar bai sanni ba ya wuce". "Mun haɗu a hanya ne ina tahowa shine ya rage mun hanya,amma tafiya da ya yi kam kilan bai kula da ke ba"na bata amsa ina mai kamo hannunta da zummar mu tafi,ƙwacewa ta yi ta ce"he saw me now,sai da na roƙeshi akan ya kawoni makaranta yau driver na baya nan ni kuma bana da license tukunna ya ƙi,yanzu kuma sai na ganku tare?". Ganin irin kallon da take munne ya saka nayi dariya ina mai gudun kada ta gano ni kafin na ce "babe calm down yanzu taho dani da ya yi ma ai kamar ya yi miki alfarma ne ,na ce miki a hanya na ganshi ya rage mun hanya". "Wacce hanyar,tunda dai na san daga gida abun hawa zaki hau ta ya akayi ya ganki a hanya ya ɗauko ki bayan ba guri ɗaya muke ba, ku haɗu a hanya kuma abu guda ne,either kin san zai zo ko kuma kun yi communicating"ta sake firing tana zuba mun ido. Kafin ma bata Amsa mutumin da na tsana fiye da kowa a dangin Anisa ya cece ni,kiran sunanta yake amma yana gani na ya washe baki yana dawowa inda nake yana na faɗin"baby!!". Yaƙe nayi ina mai cewa"ina kwana ya Adam "kafin na matsar da jikina daga inda yake .lasar leɓe yake yana kallona yana faɗin "Masha Allah, watanni kawai kin sake kyau Zunairah ,nayi missing abubuwa da dama gaskiya ". Sosai Anisa ta haɗe rai ta kamo hannuna tana mai cewa "bana so Ya Adam mun yi maganar nan da kai ba sau ɗaya ba, ba biyu"da haka ta ja hannuna muka nufa inda na fi tunanin nan ne class ɗin mu,ban mamakin yadda ta samu seat ɗin gaba ba,Anisa ake faɗa muku,a lokacin da nayi tunanin ta bar maganar Yaya Halil a gibar ta kamo maganar munje Sallah inda take cewa "Zunairah kina san Yaya Halil?". Sarƙewa nayi da yawon bakina dan ban taɓa tunanin zata mun wannan tambayar ba,tambayar ta nayi da wane irin tambayane wannan?. Ƴar dariya ta saka tana mai san kawar da tambayar kafin ta ce"I'm sorry abun da na san zai wahala ya faru after all na san cewa Yaya Halil ba irin mazan da ki ke so bane ,how dumb of me". Nima dariyar nayi yadda tayi amma deep down fargaba ta ziyarceni,cikin rashin Sanin nauyin furucina na ce"idan nace ina san shi fa?". Kamar an ɗauke mata wuta haka komai nata ya tsaya inda na kasa karantar yanayin da furucin nawa ya jefa ta ,dariya na saka kamar wata taɓaɓɓiya ina mai mata dukan wasa ina cewa "babe im kidding ji yadda ki ka saka serious face,kin manta ina da boyfriend"ƙarasa maganar nayi ina mai nuna mata zoben dake hannuna,sai a Wannan lokacinne ta saki jikinta ta ce"well har na so na manta hakan,but mind you duk lokacin da ki ka fara san Yaya Halil ki ka ji kina san dumping waccan boyayyen gayen akan sa,na zama ta farko da zan sani domin nice kaɗai zan iya baki taimakon da ki ke buƙata,dan nafi kowa sanin wanene yaya Halil,duk da macen da yake so baki cikin tsarinta amma zan ƙoƙari nayi 1 or 2 a san ya za a yi". Sosai maganar ta yi mun nauyi a ƙirji,sai naji raina ya ɓacci da Yaya Halil, maganar na fara haɗawa guri ɗaya da wadda ya yi mun,ko so yake ya rabu dani dan ya gano ban kai yadda yake so mace ta kai ba?to mene ma yake so ɗin?ban sani ba wadda zan tambaya kuma a yanzu dai a moment ɗin da muke ciki last wadda zan tambaya ita ce. Kada kuga laifina ina so idan ina soyayya ko ina na cike gurbi gurin wanda nake so,yaya Halil yana nuna mun soyayya sosai,amma fitar maganar nan bakin Anisa sai sheɗan yake ƙara zugani kan maganar da ya faɗa mun ɗazu na kai karshen batun a kan yana san rabuwa dani ne dan ya samu wadda ta fini,baki ɗaya na kasa yarda maganar san kowa ya san muna tare ta kawo faɗan,ya san bana so a sani shine yake amfani da hakan dan nayi fushi nace a rabu. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchu jay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:8.:first fight *𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov. Baki ɗaya na kasa cire Maganar Anisa a raina,har na koma gida abun na damuna musamman da ya ƙi kirana,na duba wayata ya fi sau adadi ko zai kira ni,lokacin da Baba ya kira na haɗa shi da Mama baya samun wayarta jikina na ɓari na ɗauki wayar tunanina shine, atleast ina san na saurari haƙurin da zai bani dangane da ƙazafin da ya yi mun na ina tare da wani daga nan sai na kawo wancan maganar,amma har magrib bai kirani ba,haka na cire rai ina mai jin Zuciyata na mun wani irin zafi,na tambayi kaina ya fi a irga mene yake damuna ?. Bayan sallar magrib ina yi ma Adavize tilawar hadda wani yaro ya shigo wai ana sallama da ni,wata irin faɗuwar gaba naji ta ziyarceni,cigaba nayi ban tsaya ba inda Mama ta ce yaje yace ina zuwa,har yaron ya fita ban dakata ba,ganin haka ya sa mama ta ce"Hafiza sai ki sauke karatun nan haka Ometere ta cigaba mishi,kinji ai ana Sallama da ke a waje na san kuma kina san zuwa ɗin". kunya ce ta kamani sosai, tashi nayi na shiga ɗaki,ina jin Hauwa'u ta karɓi karatun sai dai tun kafin aje ko ina sun fara faɗa. Sallama nayi ma Mama kan zan fita tace na kula,na san fitar nan ko mu shirya ko mu sake wani faɗan,abun mamaki wannan shine faɗan mu na farko tunda muka fara soyayya. Yana cikin mota bai fito ba ga motar duk tint Sannan ban san shi da ita ba,chogewa nayi na tsaya,horn ya yi amma na yi mishi banza,ai ya san bana zance a mota ba kuma zan fara a motar da take duk duhu ba gefe da gefe ,gaba da baya ganin bana da alamun takawa ya saka shi buɗe motar zai fito,ganin hakan ya saka na haɗe rai sosai ina mai kashe inda zai fito da ido. Saurin ja da baya nayi ganin wanda ya fito daga motar yana kaɗa key ɗin sa ,idona na sauka cikin nasa ya kashe mun ido guda ɗaya,ya akayi wannan ɗan iska ya san gidan mu?. tambayar na mayar masa zuwa fili "Ya Adam mene kake a ƙofar gidan mu?" Yar dariya ya yi yana mai takowa yana cewa"mai san tsuntsu ai shi yake bin sa ya jifeshi". "Kada ka sake kirana tsuntsu"na faɗa cikin rashin zato da tsammani,dariya ya saka sosai jin abun da nace kafin ya ce "kin yadda ina sanki kenan tunda har kin amince ke tsuntsu ce,to forget about that,rashin iya Hausanki bai dameni ba,a haka nake san ki nake san kasancewa da ke matsayin matata,akan abin da ya faru tsakanin mu yanzu nake san gyarawa,dan Allah Zunairah ki kalleni ki manta da wani Halil bai dace dake ba". Wani irin faɗuwa gaba ce ta kawo mun ziyara,ganin reaction ɗin da nayi da ido ya saka shi kecewa da wata shaƙiyyiyar dariya yana mai ɗaga mun gira ya ce"You heard me,kina tunanin ban san kina Soyayya da Halil ba?I'm not his little Naive sister Anisa ,Adam nake duk yadda ki ke tunani kuma na wuce Nan,ina da kaifin basira,a kallo ɗaya ba sai an faɗa mun soyayya ku ke ba ,ballanta kuma na ji daga bakin da soyayya ake yi da shi',Halil ya faɗa mun so which koda bai faɗa mun ba na san ke dashi kuna soyayya'". Wani irin duka ƙirjina yake ,haɗe rai nayi sosai kafin na ce"to sai mene idan ka san muna soyayya ni da shi?,after all soyayya kace Muna yi ba iskanci ba,and Ina so ka sani ta ko ina ya fika tunda shi ɗin ba ɗan iska bane kamar ka mai neman duk hanyar da zai bi ganin ya keta haddin mace,kaga information ɗin nan da kake da shi idan kaga dama ka kaishi duk inda ya yi maka bai dameni ba, abu guda ɗaya nake san ka sani,kada ka kuskura ko da wasa ka sake taƙo ƙafar ka ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina,ina roƙonka kafin na sigar da police report kan harassment ". Na juya zan shiga gida ya danƙo hannuna ,yin hakan da ya yi yazo mun a bazata,kalle kalle na fara gudun kada wani ya ganni hannu guda kuma ina kiciniyar hannun da ya damƙe da ƙarfi ya ƙi saki,kamar haɗin baki sai ga dannowar Motar Halil,sake kallon hannuna cikin na Adam nayi kafin na mayar da hankalina kan motarsa ina faɗin"ka sake ni dan girman Allah".maimakon ya sakeni ɗin sai ya mayar da dubansa direction ɗin da nake kallo,wata irin dariya ya saka yana cewa "ki ce Romeo ne ya zo well Kinga ya tarar da majnun ya riga da zuwa". Riƙon da ya mun akwai azaba amma azabar bata dameni ba ,damuwata guda ɗaya kada Yaya Halil ya tadda mu cikin wannan situation ɗin dan ko da wasa ban taɓa faɗa mishi na san Adam ba,duk roƙon da nake ma mitsiyacin nan bai sake ni ba har sai da abin da nake gudu ya faru,tsaye yaya Halil ya yi a kan mu yana kallon ikon Allah yana mai faɗin"mene yake faruwa anan?kai Adam mene hakan ka riƙe mata hannu besides me ka ke yi a nan?"yana maganar ya saka hannunsa ya fincike riƙon da Ya Adam ya yi mun. Dariya ya Adam ya yi irin mai shaƙar da wanda ake yi wa ya ce"kaji mun wata tambaya da Halil,i mean ka kalli Wannan yarinyar da kyau,ka kalli haɗuwarta fa,Nima ka dubani,ka ganni bakin gidansu ,sai ka tambayeni me nake yi?ni Adamu?,well it's understandable tunda kana tunanin kai kaɗai ake bawa ka ci,to Nima ina ƙwasar abin da ka ke samu ne". "Innallahi waina illahir rajiun Ya Adam ka ji tsoron Allah "na furta hawaye na bi mun kunci kamar suna jira musamman ganin Ya Halil ya zuba mun ido,dariyar da Adam yake ce ke shigar mun ƙwaƙwalwa kamar zata Haukatani ga kallon da nake ƙarba daga gurin wanda nake so fiye da komai domin da ace kallo na kisa da tuni a wannan gurin na mutu,hannu na ɗaga na zabge algungumin da mari kafin na ce"duk Ku bar ƙofar gidan nan idan babu wanda yake da gadonsa".ina kai karshen maganata na juya na koma gida har ina haɗa hanya,ina jin Ya Adam yana dariya sosai ya wuce motarsa ya bar Yaya Halil A gurin wanda Allah kaɗai ya san abin da ke cikin zuciyarsa domin ni banace ba musamman da irin kallon da yake bani wanda na kasa fassara abin da yake nufi. Da na shiga gida Mama bata nan su Hauwa'u ne inda na barsu,ina ji tana tambayata abin da ke faruwa nake kuka, banza na mata na shiga cikin ɗakin mu ina bakin ƙoƙarina wajen ganin na shanye kukan amma ina shiga ya ƙwace mun,mene na yiwa Adam a duk faɗin duniyar nan da ya nemi ya ɓata mun Alaƙata da Ya Halil a Wannan gejin da muke kan saɓani?.Tambayar da nake ta yiwa kaina kenan ,I'm sure akwai mata da yawa da zasu bashi kan su waje ba sai ya sha wannan wahalar ba ,mene ya saka ya zaɓi da ya ɓata tawa rayuwar bayan ya san ba zai taɓa samun abin da yake so daga gareni ba,1 minute ya ce yana sona,1 minute ya nemi ya maidani mutuniyar banza gurin mutumin da ke ganin kimata da mutunci na,tunanin hakan kawai ya saka kuka na ya kasa tsayawa baki ɗaya. Ina jin motsin Mama nayi saurin goge hawayena,tambayata ta fara lafiya? Hauwa'u na bayanta wanda ita taje ta kira Mama ta ce mata wai ina ɗaki ina kuka dana shigo daga waje,kasa magana nayi sai kukan da nake ta yi wanda duk yadda na so na riƙe na kasa,Mama na ƙokarin zama kusa dani Muhammad Ya shigo da gudu ɗakin yana cewa "Mama Brother ɗin nan dake zuwa Gurin Aunty Zunairah ya shigo wai yana san ganin ki". Kallona Mama tayi nima ita ɗin nake kallo,"me kuma zan mishi?"na faɗa ina ƙokarin tashi ina ƙarawa da "Mama bari naje na sallameshi".mayar dani tayi ta zaunar ta ce"Ni yake san gani ba ke ba,idan kuma gaskiyane baki dashi to wannan is another story,if not ki zauna a nan naje na ganshi, Hauwa'u je shiga dashi falo ina zuwa" . Kuka na sake fashewa dashi musamman da ban san abin da zai faɗawa Mama ba,bata bi ta kaina ba ta fita a ɗakin tana mai sake jaddada mun kada na kuskura na fito a ɗakin nan idan ba so nake raina ya ɓaci ba. ******************************************* *𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓* Tunda ya shawo ƙwana ya ga Zunairah da Adam hankalinsa ya yi mugun tashi Musamman ganin hannunsa riƙe da nata,tambayar da yake ma kansa abin da Adam yake a gidan su Zunairah,dama sun san Juna?sanin sai ya fita zai samu amsa ya saka ya buɗe Motarsa ya fita amma ga mamakinsa sai yaga riƙon da ya yi mata da bawai riƙone da ta yi na'am da shi ba,bai wani tunanin ba ya ƙarasa ya kwace hannunta yana mai tambayar dalilin da ya saka ya riƙe mata hannu da kuma abin da yake a ƙofar gidansu,Amsar da ya bashi ba ƙaramun kaɗa mishi hanji ya yi ba duk da ya yarda da Zunairah ɗari bisa ɗari sannan ya san ƙaryar Adam fiye da tunaninsa dan zai iya cewa babu maƙaryacin da yafi Adam a danginsu,idan ya zula maka ƙarya sai ka fara tunanin baya da ƙwakwalwa ko yana fama da larurar Hauka dan kai mai ji kana sauraro ka san ƙarya yake amma haka zai dage ya yi ta Zillo ta. Kallon Zunairah yake Bama ya sauraron abin da Adam ke faɗa burinsa guda ya gama ya tafi ya gana da ita dan tun maganar da ya faɗa mata ya kasa nutsuwa dalilin da ya saka ya biyo baya kenan . Jin tace su bar ƙofar gidan ta juya da gudu ya saka yaji wani irin nauyi,yana jin dariyar Adam har ya bar ƙofar gidan ,kamar ya tafi amma sai yaji ƙafafunsa sun ƙin amince mai da yin hakan ,baki ɗaya tunaninsa abin da yake bashi ya bita ciki,tsintar kansa ya yi da bin umarnin Ƙafafunsa wajen bin Zunairah cikin gidan,sai da ya shiga tukunna ya farga,Muhammad ne kawai a tsakar gidan wanda yana jin shigowar mutum ya ɗago ya zuba Mishi ido. Ganin hakan ya saka yace ya yi mashi magana da Mama Wanda shi kansa bai san abin da zai ce mata ba,sai a Wannan lokacin Muhammad Ya gaishe dashi kafin ya tashi ya shiga dan kira mishi Mama Tunda Hauwa'u ta shiga dashi Falo yake neman abin da zai faɗawa Maman,zuciyarsa ta riga ta faɗa mishi idan har bai shigo ɗin ba Zunairah ta ƙwace mishi har Abada inda shi kuma bai shirya hakan ba,Mama na Sallama ya sauko daga kujerar da yake ya zauna ƙasa,da fara'arta ta shigo ciki tana cewa"Malam Halil ka zauna mana ka sakko ƙasa". "A'a Mama nan ɗin ma ya yi,ina wuni Mama?". "Lafiya lau Álhamdulilah, ya mutanen gidan?"ta amsa tana mai zama kujerar dake kallonsa . "Álhamdulilah Mama,dama nace bari na shigo mu gaisa idan da hali kuma na ga Zunairah yadda ta shigo ɗinne na kasa jurewa nace bari na shigo mu yi magana". Cikin san sanin Abin da Yake faruwa Mama ta ce"fatan dai lafiya?don har yanzu kuka take bana tunanin kuma Good time ne da zaka ganta da kun daidaita ɗin,ku ɗinga haƙuri da juna ita alaƙa irin wannan idan Ubangiji ya haɗa dole ne mu koyi haƙuri,ba zan nace sai naji abin da ke tsakanin ku ba ,amma ku ɗinga haƙuri dan Allah". Kamar jira yake ya fara Rero mata abin da ke faruwa inda ya sake jaddada mata ko a yanzu ba shine ya ɓatawa Zunairah rai ba dan uwansa ne Adam ,musabbabi ma bai san mene ya haɗasu ba,ƙarawa ya yi da cewa"Mama wallahi ina san Zunairah sosai dan Allah ki bata haƙuri ta saurareni ,kuma ina so iyaye su san da hakan, insecurities ɗin da take dashi a kaina insha Allahu zan ƙoƙari wajen bata tsaro idan shine ya saka bata san yan gidan mu su san muna Soyayya,maybe tana tsoron banbancin Yaren mu,ita Ebira ni Idoma,Mama mazan Yaren mu Muna riƙe mata sannan gidan mu babu ƙabilanci,insha Allahu ba za ku yi kuka dani ba ,itama kuma ba zata yi dana sanin Aurena ba". Kunyar maganar nasa Mama ke ji sosai duk da ta gamsu da yana san Zunairah tunda har zai cire kunya ya zo gabanta ya furta mata wai yana san Zunairah,bayan ya gama ya tashi ya masu Sallama ya wuce gida zuciyarsa kamar an cire masa wata damuwa duk da bai samu ya ga Zunairah ba. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:9:Cat out of Bag *𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov. Ina jin Mama na mishi Sallama tana mai sake jaddada mishi kada ya manta ya sanar da Enen tana gaisheta sosai,yana tafiya ta shigo ɗakina,ina ƙoƙarin tashi ta ce mun "yáàtùû(zauna)ina zaki je?we need to talk. Zama nayi kamar munafuka ina aikin sinnar da kai,itama kusa dani ta dawo ta zauna tana Nazarina kafin ta ce"Zunairah kina san Halil kuwa?i mean idan ba san shi ki ke ba ya kamata ace kin faɗa mishi sai ya daina wahalar da kan sa ya samu mafita,saboda wannan yaron na gani a idanunsa yana san ki ,na kasa gane wane dalili ne zai saka ki ce wai baki so kowa ya sani a gidan su,shin wasa ya zo ku yi ?I'm very sure ba Ten ten ya yazo yace yana so ku yi ba ke dashi ,banga dalilin da zai saka ki ce wai baki so kowa ya san cewa kuna soyayya' ba,dan haka yanzu ina so ki faɗa mun menene a zuciyarki dangane da shi,idan baki san shi ne tell me,sai mu san ya ya zamuyi". Shiru nayi ina mai jin wani irin Nauyi,sai da ta sake maimaita mun tambayar kafin na iya cewa"Mama ina san shi "ina ƙokari wajen sake ƙasa da kaina dan bana so mu haɗa ido,hankali ta mayar kaina sosai kafin ta ce",to let me understand boye boyen na menene?". "Mama kawai ina tunanin Yadda Anisa zata ɗauki abunne ,Kinga ni da ita tare muka tashi ,mu aminai ne,rana ɗaya Mama sai taji ina soyayya mata da Yaya?"amsar da na bawa Mama dariya ta sakata,sai da tayi yar daƙiƙiya kafin ta ce"ban san wane musuluncin ne ya baku wannan ruwayar ba na cewa idan kina ƙwance da ƙawarki kada ki yi soyayya da yayanta,look here my darling,kina wasa da damar ki,akwai damar da idan ta wuce ba ta dawo maka,i trust this guy sannan na san yana sanki ,kada ki bari wani nonsense belief naku ya rinjayi farin cikin ki,I'm sure ita kanta Anisa yadda take ƙaunarki farin ciki za tayi ba wai ta miki baƙin ciki ba,ki yi tunani mai zurfi ki zama mace ki riƙe abin da ki ke dashi a gabanki". Shawarwarin da Mama ta bani sun ratsani sosai,sai a wannan lokacin nake ganin wautata na ɓoyewa Anisa , Message ɗin ya Adam ne ya katse ni daga dialing number ɗin da nake niyar yi na Anisa."Babe I will let the cat out of the bag,xx Adam ". Tsaki nayi ina ignoring ɗin shi da inda ya samu number ɗina,blocking ɗinshi nayi baki ɗaya kafin na kira Anisa ,ina mata kira ɗaya ta ɗauka na sanar mata idan mun haɗu a school gobe akwai labari,zan faɗa mata wanda nake dating,duk yadda ta ƙagu akan na faɗa mata a lokacin ƙi nayi dan maganar ba ta waya bace,magana ce da ya kamata ace gani gata muna kallon juna sai a yi ta ,haka nan nayi ta duba wayata ko Yaya Halil zai kirani amma bai kira ba,tun ina saka rai har na cire,mayar da hankalina nayi wajen fuskantar Anisa a makaranta,na aminta da zan freeing kaina daga ƙejin da na yiwa soyayyata babu gaira babu dalili. Washe gari na riga kowa tashi na fara kamawa Mama aiki,sai da na gama komai kana na shiga wanka sanin Lecture ɗin ƙarfe tara ne dani,baki ɗaya sukuku nake jina ,na saba Ya Halil zai kirani first thing in the morning ya san yadda na tashi ,sai nake jina kamar wadda bana da lafiya,sallama na yima Mama,har na kai bakin ƙofa ta kirani,kallona tayi kana ta ce"Zunairah ba dole sai Halil ya nemekine zaki nemesa ba,girman kai ba naki bane,kun samu misunderstanding sai a san yadda za a yi a gyara ba wai kice sai shine zai nemeki ba domin a yadda nake gani nutsuwarki bata nan".Kunya ta kamani sosai na kasa cewa komai,ganin nayi shiru kuma ni ban iya tashi ba ya saka ta cewa"kije makaranta kada kiyi latti,Allah ya yi maki albarka ya bada karatu mai amfani ". Haka na wuce ina ta tunanin maganar da Mama ta faɗa,idan na kira ni ban san mene zance mishi ba,ina tafiya ina nazari naji horn ɗin mota a bayana,saurin matsawa nayi ba tare da na juya ba amma na tabbatar da na matsa a kan hanya,jin motar bata sauri ne ya saka na juya raina a ɓace musamman da na fahimci bina ake,wani faɗuwa gabana ya yi ganin motar sa,so nake na juya amma ƙafafuna sun ƙi barina nayi hakan , tsaye nayi ina kallonsa inda shi ma yake cikin motar yake kallona,shi bai fito ba bai kashe motar ba shi kuma bai tafi ba,wayata da ta ɗauki ruri a jakana ya sakani dawowa duniyar kallonsa dana tafi,juyawa nayi da sauri kafin na saka hannu cikin jakar na ɗauko wayar ina tafiya cikin hanzari,faɗuwa tayi yadda na cirota a ruɗe,hawayen babu gaira babu dalili naji suna bin kuncina na rasa na mene,faɗuwar wayarce ko mene ba nace ba,ni dai kawai naji hawaye na sauka,duƙawa nayi hannuna na karkarwa zan ɗauka amma kafin na ɗauka ya rigani,ɗauka ya yi yace mun"ina zaki je ki ke gudu kamar kin ga dodo". Kasa kallon idanunsa nayi,ganin yadda muke a tsugunne tare ya saka nayi saurin tashi na juya mishi baya ina raba idanu ina mai yin wasa da hannuna,Zuciyata kuwa wani bugu take mun kamar nayi ma sarki ƙarya,dawowa inda nake ya yi ya miƙo mun wayar kafin ya ce"we need to talk babe ,ki zo muje na aje ki makaranta sai muyi magana a hanya dan Allah ". "Ni zanyi latti sauri nake "na faɗa ina mai gudun haɗa ido da shi,murmushinsa mai burgeni ya yi kafin ya mayar da wayar aljihunsa ya juya ya nufi motarsa,bana da zaɓin da ya wuce na bisa ,kafin na ƙarasa ya buɗe mun ƙofa,bance komai ba na shiga ya rufe ya zaga ya mata key,tunda muka fara tafiya babu wanda ya ce komai ,ganin baya da niyar magana ya saka nima nayi mishi shiru ai shi ya kamata ya fara magana ba ni ba,Har muka kai makaranta bai ce mun komai ba sai da muka shiga harabar makaranta ya faka motan dai dai inda ya saba ,ganin baya da niyar magana ya saka na fara kokarin buɗewa zan fita amma sai naji ya yi locking door ɗin,kallona na mayar gareshi . "Ka buɗe mun na fita". Marairaicewa ya yi da ido kafin ya furta abin da ban tsammanin shine zai fara fitowa a bakinsa ba "ina sanki ZUNAIRAH,wallahi sosai da sosai,kinji".Kallon cikin idanunsa nayi na rasa abin da zance,hawaye suka tarar mun kafin na farga sun fara zuba,"ka buɗe mun na fita kada nayi late muna da lecture". "Na sani amma dan Allah kada ki bari wani abu ya samu soyayyarmu,i understand idan kince kada mu faɗawa kowa amma zamu dawwama cikin ɓuyane,Mama sun san dani amma Enen bata san dake ba and ina so na nunawa duniya baki ɗaya ina sanki ina san na Aureki,dan Allah ki bani chance na tabbatar Miki da hakan". Ganin yadda ya marairaice ya saka ni cewa "Ya Halil babu abin da ke tsakanina da Adam". Ɗan murmushi ya yi ya ce"na sani ,Adam!! Is a bad story but ganinsa tare da ke bai saka naji wani abu ba dan na yadda babu abin da zai haɗa ki da mutum kamar Adam....". Katse shi nayi."Cewa ya yi yana sona amma ban amince mishi ba ,shine ranar ya zo,har ya ce mun wai ka faɗa mishi muna tare abun da ya faɗa maka kuma wallahi ƙarya ne". "Forget about kowa da duk abin da ya faru,I'm sorry abun da na faɗa Miki wai ko kina tare da wani ne i just said it,saboda I was frustrated and.... " "Ya wuce Habibi mu kalli abun da yake gaba mu daina kallan baya and insha Allahu steps ɗin da na ɗauka da farko zan gyara ,You can tell Enen about us ni kuma zan faɗawa Anisa ". Ɗan dariya ya yi yace"ke da Anisa dai Sai Allah,kada ki damu Anisa zata sake sanki fiye da baya ,kije kada na saka ki yi latti zan zo anjima". Buɗe mun ya yi kafin na buɗe ya dakatar dani,fita ya yi ya buɗe mun ƙofar ya duƙa kafin ya ce"i love you".sunkuyar da kaina nayi ina murmushi kafin na ce"i love you ".matsawa ya yi na fito ,yana ƙokarin taka mun na dakatar dashi nace ya tafi kada ya damu,kafin ya bani Amsa Aminiyata ta bayyana ,da mamaki take bin mun da kallo Nima ita ɗin nake kallo musamman jin ta ambaci sunana. "Amma wannan ba wani coincidence bane ,care to explain?".. "Anisa !!"na kira sunanta ina mai jin wani Nervousness. "Wane zai Miki explanation ina wasa dake ko?"ya Halil ya faɗa yana mai tsareta da ido,ganin zai ɓata mun abin da na shirya ya saka nayi saurin matsawa gareta na Kama hannunta ina cewa "muje zan Miki explanation ɗin ni da kaina"muna barin gurin da yake ta ƙwace hannunta tana mai cewa "Zunairah ina ji,mene yake haɗaki da ya Halil wanda ba ki faɗa mun ba,na tabbata yau ba a hanya ku ka haɗu ba,abin da nake gani tsakanin ku kuma kaina ya kasa fassara menene care to explain?". "Anisa calm down zan faɗa miki".wayarta da ta fara ƙara ne ta katseni,ɗauka tayi tana mai cewa"wai ya Adam mene kake ta damuna dan Allah zan kiraka ina abu mai amfani"kashewa tayi tana kallona ta ce"Uhum ina ji". "Ashe dai ke ce". Tare muka kalleshi jin muryarsa ,cikin ƙaguwa Anisa ta ce"wai dama ya Adam bina ka ke,mene ka ke san faɗa mun wanda sai ka yi ta damuna,I'm in the middle of something ni yanzun". Kafin ya yi magana na yi hanzari wajen cewa"ina dating YAYA HALIL Anisa "a wani irin 360 ta juyo tana kallona ta ce "pardon?"rumtse Idanuna nayi na sake maimaita mata,dariya ɗan iskan nan ya kwashe dashi ya na mai cewa"damn it da kin bari na yi wannan Alfarman na faɗa mata mai ya sa za ki mun haka". "So kaima ka sani?"ta mayar da tambayarta da kallonta gareshi,ɗaga gira guda ya yi ya ce"Uhum ina ta binki na fesa miki best breakfast kina mun ihu so that's it,your brother and best friend are having illicit affair". Kalmar illicit ɗin da ya faɗa ta mun zafi amma ba ta ita nake ba ina san karantar yanayin da na jefa Anisa,murmushi tayi tana mai gyara zaman jakarta kafin ta ce "first period Computer application ne kizo mu tafi kada ta shiga ta hana mu,Ya Adam thank you zaka iya wucewa".gaba tayi ina mai bin ta a baya ,atleast koda bata yi magana ba ni dai na sauke nauyin dake kafaɗata ,guri ɗaya muka zauna a class Mrs Jenna na mana dictation ma a cikin nawa take kwafa,idan bata gane mene na rubuta ba zata ce mene Wannan,ni dai baki ɗaya a tsarge nake har aka gama lecture ɗin nan,tana fita Communication in English ya shigo muka ɗora,har lokacin ban fahimci ina ta dosa ba dan ko a ido bata nuna mun wani abu ba,bayan mun fita har abinci mukaje ci tare ,ɗanwake muka siya kamar yadda muka saba ita ta ɗauke kwanon tana faɗin ladana ya ƙare,kullum haka muke Indai muka siya ɗanwake ita ke ɗauke ƙwanan ta lashe mai da yajin wai ya fi daɗi,duk yadda naso kawo maganar Yaya Halil sai ta kauce ta kawo wani zancen ,ganin yadda ta saki jiki ya saka na saki nawa ina tunanin na karɓu,sai naji banji daɗi da na ɓoye mata ba ,mai ma nake tunani da ɗin. Bayan mun gama dukkan wani activities na school muka fita don tafiya gida,muna tsaye muna jiran keke ta ce mun"Daddy zai siya mun mota Kinga mun huta na aje ki gida nima na wuce,bana san driver yana kawoni makaranta ,I need my space ". Murmushi nayi nace"Allah ya tabbatar da Alheri"wayarta ta ciro ta fara nuna mun hotunan motoci,wata Prado mai kyau ta nuna mun ta ce irinta take so a siya mata,sai na tsinci kaina cikin mutuƙar farin ciki har inda tsokanarta wa ya ganta gaban mota. Haka muka sha hirar mu ,ni aka fara saukewa ina ƙokarin bashi kuɗi ta hanani ta hanyar cewa "ki bari zan bashi"cike da naci nace gaskiya ta bari na biya amma ta ƙiya har mai adaidaita sahun ya kunna ta leƙo da kanta tana kallona kafin tace "Besty i will appreciate it idan ki ka kawo ƙarshen Puppy love ɗin dake tsakaninki da Yaya Halil dan bana goyan baya bazan bada goyan baya ba kuma,sai dai idan zaki zaɓi soyayya sama da ƙawance da muka daɗe muna ginawa ni dake,Code ɗin basa da yawa,Don't date my brother and don't date my ex ". Kafin na fita daga sukar da maganarta ta yi mun ta umarci mai Adaidaita sahun da ya ja su wuce,kamar wata bebin roba haka na tsaya ina bin hanyar da kallo har suka ɓacewa ganina,ban taɓa tunanin wai Anisa zata ce na zaɓi ita ko Halil ba, shin mene ma ya haɗa ƙawance da kuma abin da nake dashi tare da Ya Halil?shi kuma wannan sababbin abin da ba zai saɓu ba da take kira code daga ina aka samo su?. "Aikuwa Wallahi Aunty bata isa ba, wai ki zaɓa ko ita ko Yaya Halil, wannan ɗin wane irin banzan Code ne?" Juyawa nayi jin Muryar Hauwa'u,cikin ɓacin rai nace"laɓe ki ke mun ko?". Ɗaga hannunta tayi sama ta ce"wallahi A'a Auntymu Fitowa kawai nayi fa zani shagon dan Fulani na siyo siga na tsinkayi maganar ta ki yi haƙuri". Raɓawa nayi ta gefenta ina cewa "saura ki faɗawa Mama dan Allah zaki ga ya zamu ƙare ni dake "da haka na shiga ciki ita kuma ta fita,Mama na tarar tana hira da Aunty Muna wata yar Yaren mu da suka tare bayan layinmu,tunda taji ana kiran mu gidan Ebira ta shiga jikinmu ,take kuma sai ta samu shiga ,abunka da anga yan yare guda sai ya zama kamar yar uwarmu,dan wasu ma cewa suke muna da alaƙa dama,gaishe su nayi Mama ta mun sannu da zuwa inda take cewa akwai Kunun gyaɗa a kitchen naje na ɗauka na sha ta saka mun siga tuntuni ta aje mun,su kuma su Hauwa'u ta basu suje su siyo. Tasan wani lokacin ina shigowa gida ina kukan yunwa shi yasa takan fara aje mun Abu mai ruwa ruwa,kunun na ɗauko na shiga ɗaki ,duk yadda nake san kunun gyaɗa sai naji na kasa sha,Anisa ta Shammaceni,ashe duk share zancen da take tana jirane mu zo rabuwa kenan ta faɗa mun bata yadda ba,to amma dole sai ta yarda zan soyayya i Zunairah?bansan yaushe wannan dokar ta shiga tsakaninmu ba,gaskiya zan amince da komai banda barazana da abin da na gama sawa rai,bana wasa da soyayya musamman a yanzu da na samu wanda nake so yake sona,dole ne idan Anisa na sona da gaske kamar yadda ta faɗa tayi Farin ciki da farin cikina,ban taɓa kin abu idan tace ba sanin ba zata cutar dani ba,amma a wannan karan kuwa dole ne Anisa tayi haƙuri ta Barni da abin da nake so dan bana tunanin zan iya ɗaukar wani heartbreak ɗin a karo na biyu,nayi nisan da idan aka mun haka zan samu matsala ainun. Sakin jikina nayi na cigaba da hidimomina inda har kirana Yaya Halil ya yi ya shaida mun zai zo,ban saka komai a raina ba ban kuma faɗa mishi ya muka yi da Anisa ba muka sha soyayyar mu ya tafi,kamar ba muyi faɗa ba sai komai ya dawo kamar ranar da muka fara musayar kalmar soyayya,har na ƙwanta ina sake tabbatarwa da kaina ba zan bari wannan damar ta ƙwace mun ba musamman yadda na ga murnar da yake jin nace ya sanar da su Enen abin dake tsakanina dashi,har yana tsokanata da kawai gobe zasu zo. introduction. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 08130229878 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟10.Love or Friendship *𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈* Tana jin tashin hankali tana shiga tashin hankali amma wanda take ciki a yau ba ƙarami bane,jin kalmar Yaya Halil na soyayya da Zunairah kawai sai da ya so ya tsayar mata da dukkan wani tunani da take dashi,ina ma hakan zai iyu?ai wallahi ko ana muzuru ana shawo babu uban da ya isa ya haɗa wannan alaƙa ta zuba mishi ido,Yayanta fa wanda take ƙauna,taya za ace ta zuba ido tana kallo Zunairah ta ƙwace mata kashin soyayyarta,ba zai iyu ba ba zai faru ba. Haka wunin ranar ta yi tana ƙunci duk da ta rasa ta inda zata fara ta kuma rasa wanda zata tunkara da maganar,tana zaune falo tana tunani Muryar Mahaifiyarta ta datseta inda take cewa"Aikuwa Halil kayi kyan kai da ya zamana Zunairah itace wadda ka ke so ,Anisa kinji wani labari mai daɗi kuwa,ko da yake ai wannan labari ma ke ya kamata ki bani karin haske". Turo baki tayi gaba ta tashi tana mai cewa "aikuwa "cikin ɗaki tayi zuciyarta na mata ɗaci musamman da ta lura da yadda Yaya Halil ke washe baki,aikam zai yi ya gama dan wallahi dole ne a watse,daga ɗaki tana jin yadda Enen ke murna kamar wadda aka bawa duniya ,tayi tsaki yafi a irga ,kwanciya tayi tana ta juye juye kan gado ,ji take ƙirjinta na mata wani irin zafi kamar zuciyarta zata fasa mata ƙirjinta. Haka ta wuni ranar kafin ta samu kwarin gwiwa da dare wuraren tara ta nufi ɗakin Halil,tsaye tayi tana tunanin ta inda zata fara,kafin ta ƙwanƙwasa ya fito,kallonsa tayi cike da fargaba ta ce"fita za kayi yaya Halil?". Kallon kansa ya yi kafin ya kalleta ya ce"da daren nan ni kam Nisa ina zanje , besides singlet fa ki ka gani jikina". Turo baki tayi ta ce"na sani ko gurin Zunairah zaka and ai ba zan mamaki ba idan kaje da singlet ɗin maybe ta koya maka abin da bai kamata ba".hannu ya saka ya yi folding yana mai kallonta kafin ya ce"mene maganarki ke nufi Anisa?". Juyawa tayi tana cewa"shikenan ai yanzu ina magana sai a fassarani,amma ni ka sani brother babu wanda ya damu da damuwarka sama dani". Cikin rashin sanin inda ta dosa ya kamota ta kwalar rigarta,sai da ta dawo tana kallosa kafin ya ce"me ki ke nufi?wani abu ki ke ɓoye mun?". Dan kalle kalle ta fara kafin ta rage murya kamar tana tsoran kada wani ya jita kafin ta ce"muyi magana a ciki yaya bana san wani ya ji".bai mata musu ba ya juya ya koma ciki ta bi shi,zama tayi bakin gadonsa kafin ta tattara dukkan kwarin gwaiwarta ta ce"Yaya Zunairah aminiyatace ,babu wanda ya santa fiye dani,and na yi imani da Allah ba matar da zaka Aura kayi alfahari da ita bane,na san abin zai baka mamaki kace daga bakina wannan maganar ke fita,amma ina so ka sani wallahi ba sharri nake mata ba,and ba wai ina cewa bata da hali mai kyau bane,dan har gobe bana da ƙawar da ta wuce ita amma dai Maganar Aure gaskiya bana goyan baya". Daga zaune kan mudibin da yake ya kura mata ido bai ce komai ba,ganin yana mata irin wannan kallon ya saka tace"yaya baka ce komai ba". "Uhum ina sauraranki dan baki faɗi maganar da ya kamata nace komai ba har yanzun,ita Zunairah ɗin mene tayi ,tana da mugun hali amma ki ke tare da ita,ina ƙoƙarin na saka maganarki kan sikeli ne na Auna dan ban san taƙamaimai ina ki ka dosa ba". Ɗan cije leɓenta tayi ta ciro wayarta tana mai cewa"zan nuna maka wani abu amma dan Allah yaya ka rufe mata sirrinta bana san kowa ya sani,and ka san mene yafi damuna,da ace zata canza da tuni ta canza amma bata da tunani na sake ɗabiun banzanta". "For God sake Anisa idan zaki nuna mun ki nuna min,idan ba haka ba ki bari nayi relationship ɗina in peace"ya faɗa cike da ƙosawa. Bata tsaya further ɓata lokaci ba ta kunna masa abin da take kira well kept evidence. *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏 𝘗𝘖𝘝* Introduction to mass communication shine first period ɗin da muke dashi,yau ko da na shiga makaranta na ɗanyi latti amma sanin malamin baya da matsala sai abun bai dameni ba,ban mamaki ba ganin Anisa bata jire mun guri ba sannan bata kirani ba,idan ta rigani shiga aji takan kirani tace mun an shiga,zaune take tare da wata course mate ɗin mu da suka fara shiri kwana biyu Safina Bala,sai wani Saurayi da ban wayi sunansa ba danni bana da wannan shige shigen. Class rep ɗin mu Imran ne ya mun guri na zauna har yana tsokanata yau akwai Quiz yana tare dani ya san zamu buge kowa,haka aka yi Quiz ɗin roll ɗin mu muka ci na farko,Use of English ne second period mai ɗaukar mu ya sanar da class rep ba zai samu damar zuwa ba dan haka sai ya zamana 10 mun zama free ,ina haɗa kayana dan tafiya gida Anisa tazo tana mai cewa"ƙawata yau mene ya saka ki latti?". Dan murmushi nayi ina mai kallanta na amsa mata "ban samu abun hawa bane da wuri wallahi shi yasa nayi latti,and kin san Malam A Bello baya da matsala shi yasa ban damu ba ,da dai A A Garba ne na san Dama ba zan samu aji ba". Jakata da nake ƙoƙarin ratayawa gefen Kafaɗata ta karɓa ta rataya ,kallonta nayi ,gira ɗaya ta ɗaga mun tana mai cewa"zaki iya amfani dani matsayin mai riƙe Miki jaka indai zaki rakani". "Ina ɗin zan raka ki?". "Kin san dai ai ba zan cutar dake ba,kizo muje dan Allah"ta faɗa tana mai kamo hannuna ,haka nan na bita ina tunanin yadda zata ɗauki hukuncin da na yanke ,sai da na bari mun fita daga class nace ",Besty baki tambayeni decision ɗin dana yanke kan yaya Halil ba". Juyawa tayi tana kallona tayi murmushi kafin ta ce"well I'm all ears ,mene decision ɗinki?". Ɗan shiru nayi kamar ba zan magana ba,zura mun ido tayi,cikin dan dakewa nace"Anisa look here babu inda addini ya haramta alaƙata da Yaya Halil,ni dake kamar yan uwa ne,kada ki bari wani code na Bature ya yi mun katangar ƙarfe da farin cikina,Wallahi a tare da Yaya Halil nake ganin Rayuwata nan gaba ,ina san sa ina san kasancewa dashi,bayan relationship ɗina na baya da Ma'aruf ke shaida ce yadda nayi ta fama,idan na rabu da Yaya Halil zan faɗa cikin hali mafi munin na baya ,ba zan zaɓa tsakanin Ƙawance ko Soyayyata ba,duka nake so koda za'a Kirani mai san zuciya,ki yi haƙuri". Wani irin kallo take bina dashi ranta a mutuƙar ɓace,cikin yanayi na ɓacin rai tace"haka ki ka zaɓa Zunairah?". "Im sorry"shine Abin da na furta ina mai jin babu yadda za'ayi ta sake mun tunanina ,zan iya bar mata komai nawa amma ba zan bari na cutar da kaina ta yadda zan illata kaina da kaina ba,bayan na gama sakankancewa da tayi fushi ta kwashe da wata irin dariya,sosai take dariyar kamar wadda ta zare inda ni kuma nake kallonta fuskata babu yabo babu fallasa,matsowa tayi kusa dani ta dafa kafaɗata kafin tace"saki ranki mana mene hakan?God Kinga yadda ki ka zama serious kamar wadda tayi wani babban laifi?well kin cinye jarabawar da nake san miki dama ina son gwadawa ne naga kin chanchan,Yayana,and kamar yadda nake expecting kin cinye, welcome to the house,ki saurareni da kyau,ni da ki ka gani well wisher ɗinki ce ,duk abin da ki ke so idan ban nema Miki ba ba zan ƙwace Miki ba, ballantana ma sai inda karfina ya ƙare wajen nema Miki farin ciki,ke nifa ko Khalifa ki ka ce kina so ni mai bar mikice". Dariya na saka jin wai zata bar mun Khalifa ,as if"kece zaki bar mun Khalifa,da anyi ruwa da ƙanƙara,balle ma ba zan taɓa having interest kan Khalifa ba,shi naki ne nima kuma ina da mai bani Zazu". "Sai dai abin da ya fi Zazu,ni dai ga yayana na baki amana kada ki ci amanarsa domin duk abin da Yaya Halil ke so nima ina so ina kuma taimaka mishi wajen ganin nima na so wannan abin fiye da tunanin mai tunani,yanzu dai muje kada mu makara". Tsaye nayi bakin wata dallekiyar Mercedes ina mai jin Zuciyata bata bani goyan baya ba da na shiga ba,buɗe murfin baya Anisa tayi ta tura nii tana mai cewa ,nace miki za muyi latti,Khalifa dake zaune kujerar mai tuƙine ya mun murmushi yana mai cewa"Barka ƙawarmu,ina wuni?". "Ina wuni ya gida,ya Aiki?" "Álhamdulilah mun gode Allah". Da wata irin siga ta shagwaɓa Anisa ta ɗora kanta bisa kafaɗarsa tana mai kamo hannunsa kana ta ce"i miss you Chocolate ",wani irin kunya abun ya bani musamman ganin yadda Khalifa ke ƙoƙarin ɗagata daga jikinsa idanunsa kuma na gareni ta mirror,saurin ɗauke ido nayi ina kallon gefe lokacin da idanunmu ya sarƙe a na juna,ji nake kamar na buɗe na fita dan ban san wane iskanci ke damun Anisa ba kuma. Juyowa tayi ta kalleni tana mai yin murmushi kafin ta ce"da ace baki dating da na shaƙa miki,sai Allah ya saka kin fita sahun yan nema, Chocolaty ka san Zunairah da Yaya Halil soyayya suke,kasan har tazo gidanmu ya mayar da ita gida bata faɗa mun ba ashe ni suka maida bi ta chan suna pretending,Besty kin iya munafurci, tsakaniki da Allah lokacin baku tare?kada ki ji kunyar Baby".. Yaƙe kawai nake na kasa cewa komai,kana kallo ka san a takure nake musamman jin maganar da ta ɗakko gaban Khalifa,shine ya katse ta hanyar cewa"Ayya Allah ya sanya Alheri,ki ce muna da biki nan kusa".ƙwace hannunsa ya yi da ya kai ƙarshen maganar cikin sigar dabara amma da yake ƙawata ta iya zubar da mu ta sake kamowa tana cewa"Who knows a fara yin namu,cos nan da wasu watanni ina jiyo ƙamshin Aure". "Allah ya amsa Mana ,bari muje kada mu tsayar da Zunairah ko?"ya faɗa yana mai yi ma motar key,ni dai da ban san ina zamuje ba nawa ido,a Zuciyata kuwa ina ta saƙa da warwara,dan dole na yima Anisa maganar yadda take ta taɓa Khalifa wanda ba sai ya faɗa maka baya na'am da hakan ba , gidan babbar yayarsa muka je ,shima nan Anisa tayi ta zaƙewa,ban sani ba ko abin da take ne zai saka su san ta waye ko mene oho,amma nifa a nawa belief ɗin ba dai dai bane, zaƙewa ba shine zai saka a san kai ɗin a waye ka ke ba. Koda muka tashi tafiya leda biyu ta mana tana ta mana godiya,har Kofar gida suka kaini,ina ƙoƙarin shiga gida ta fito da ledar hannunta tana cewa"wannan ɗin wa ki ka barwa?" "Anisa mai yasa baki faɗa mun inda zamuje ba,ina kuma da magana dake". Jiki na rawa ta saka mun ledar a hannuna tana cewa"naji muyi magana gobe ,kiyi haƙuri,yanzu Khalifa na jira ki gaida mun da su Mama ". Bata jira abin da zan sake faɗa ba ta koma motar tana mai ɗaga mun hannu,haka nayi tsaye har suka wuce kafin na shiga gida,ban tarar da kowa ba sanin Mama na islamiyyar da har yanzu aka ƙi gamawa,sau tari nakan tambayeta yaushe zata yi sauka sai dai ta ce mun mene amfaninta ,kullum yi ake,karatun matan Aure kenan haka mukan tsokaneta,ledar na buɗe naga doguwar riga mai kamfala da gyale a ciki,ajewa nayi ina mai niyar bawa Hauwa'u ba dan Alheri bane dama ni ba zan karɓa ba. Sallar Azabar da aka fara kira nayi kafin na dumduma Egusi dake fridge na dauko Saƙwara dan ban yadda na ci abinci gidan Auntyn Khalifa ba duk yadda tayi ta nacin mu ci ɗin,sai da na samu natsuwa na koma na ƙwanta sai kuma damuwar ƙin naimana da baiyyi ba ,na saba kullum shine ke fara kirana a waya,yau da bai Kirani ba sai na ɗauki hakan da ƙilan yana wani abune sai kuma ga Anisa ta ɗauke mun dukkan lokacina. Kiran wayarsa nayi a karo na uku bai ɗauka ba, tunanin baya yanayi na ɗaukar wayar ya saka na tura masa saƙon idan ya gama ya ya Kirani ina kewar jin muryarsa,bai mayar mun da saƙon ba kamar yadda nayi tsammanin zai maido, idan har nayi masa dropping message baya ɗaukar lokaci zai dawo mun dashi ya faɗa mun ko yana aiki ko yana wani abun amma zai kirani,haka dai ban ɗauki abin wani abu ba na ƙwanta ko zan ɗan samu bacci bashin na asuba da ban yi ba. Wajen yamma Mama ta dawo take faɗa mun ta tsaya meeting ne nasu na yan ajinsu tunda dama duk inda ƙarfe biyu yake ta dawo gida, kaya da Auntyn Khalifa ta bamu na nuna mata nake shaida mata munje tayi haƙuri ban faɗa mata ba,ko da nace Hauwa'u ta ɗauka mama tace ba zai iyu ba ai babu daɗi a maka ƙyauta ka ƙi sakawa,koda ita bata gani ba ai ita Anisa zata gani taji daɗi. Naso na dai Bawa Hauwa'u na san kuma zata ji daɗi amma abin da Mama tace shima gaskiya ne,na mata ko sawa biyu ne na Bawa Hauwa'un. Har daren ranar Yaya Halil bai nemini ba,abun da ya bani mamaki shine da na hau WhatsApp na ganshi online, message nayi mashi bai reply ba ,sai abin ya fara damuna a wannan stage ɗin na san dole akwai wani abun,to amma menene shi? 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟11.Fire breakout *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* Tunani yana neman ya saka na zauce ,yau Friday ranar da nasan dama dole zai zo gurina da dare,duk da haka da wuri na shirya dan zuwa makaranta duk da period ɗaya garemu Report writing,ko abincin kirki ban ci ba,burina na samu Anisa na tambayata lafiyarsa,Sai da nayi awa ɗaya a makaranta kafin ta zo, straight gurina ta nufa ta zauna duba da class ɗin sai Sha biyu muke dashi ya saka da yawan ɗalibai da dama basu kai ga ƙarasowa ba. Cikin damuwa na ce"Anisa Yaya Halil fa lafiya ƙalau yake?". Cire jakarta tayi daga kafaɗarta tana mai ɗan zaro idon alamun tambaya tana cewa"Well last dana tuna ƙalau yake dan shine ya ajeni makaranta yanzu ya wuce and ai kya bari mu fara gaisawa atleast sai ki tambaya ,Anisa ya darenki ?ya ki ka kwana ya kuka rabu da masoyinki?but its okay yanzu bari na fara kiran Yaya Halil". Kamar Nace kada ta kira amma sai na rabu da ita ɗin dan ƙasan Zuciyata ina san naji mene ne faruwa,muryarsa da nake kewace ta shiga cikin kunnuwana. "Yayana kana ina ne?". "Kamar ya ina ina?ke dai ba na aje ki makaranta ba,gida nake san na koma nayi bacci tunda kin katse mun". ya faɗa daga ɗayan bangaren da Alama yana tuƙine. Matso da wayar tayi kusa dani ta sake cewa"well hala baka Kira Zunairah ba". "WHO IS SHE? wacece wata Zunairah,dan Allah kada ki dameni kafin ki ɓata mun rai na ɓata miki"yana faɗin hakan ya kashe wayarsa,i was shocked,hawaye naji suna neman cika mun ido,saurin gogewa nayi ganin yadda Anisa ta zuba mun ido,ɗan murmushi nayi nace "well lets talk about you". Cike da kula ta ce"mene ya faru tsakanin ku?wani abu ki ka mishi?no nama tabbata babu abin da zaki mishi wulaƙancine kawai irin na ɗa namiji,Allah bari naje gida na sameshi,lokacin da yake zuwa yana kalamiyeki da zancen ƙauna ai bai tambayi wace ke ba,lokacin kuma da zai je ya siya miki Zobe mai tsada duk bai san da wannan wacece ɗin ba,zan koma wallahi dole ya jini ko na jisa,wane irin abu ne wannan". Murmushin yaƙe nayi ina ƙokarin danne abin da ya taso mun a ƙirji kafin na sake salon maganar "manta da wannan maganar yanzu dai dama ina san miki magana kan jiya,ba wai dan kiji haushi ba amma Anisa yadda ki ke taɓa Khalipha bai kamata ba,i mean he's not your Muharram ,Muna fakewa da soyayya muna kama hannun juna wallahi babu kyau, sannan ni gani nake ba sai kin zama loud bane zasu gane kin waye ba,ba wai kuma dan na ɓata Miki nake faɗa ba,kinsani ba zanga abin da zai cutar dake nayi shiru ba ". Maganar ta ɓata mata rai dan ya nuna a fuskarta amma sai cewa tayi"naji nagode ,Allah ya saka da Alheri zan gyara".daga haka bata sake cewa komai ba dangane da abin da na faɗa ɗin,da muna tashi makaranta ganin yadda taƙi walwala yasa na ce mata "Ani I'm sorry akan abin da na faɗa Miki I mean no harm ,idan na ɓata Miki rai kiyi haƙuri dan Allah ,ko'ina ina so a ga mutuncinki fiye da kowa su kuma maza abu kaɗan kakeyi sai mutuncinka bar idanunsu". Murmushi tayi "Zunairah wallahi ba haushi naji ba ,kawai naji kunya ne da kika faɗa sai kuma yanzu abin yake dawo mun amma insha Allahu zan kiyaye,Allah ya shirya tsakaninki da yaya Halil". Bance komai ba ,ban san mene zance ɗinba dan haɗuwarmu dashi baza tayi kyauba,muddin kuma bai nemeni ba bazan sake nemansa ba duk da nasan zan sha wahala domin nayi sabo dashi ta yadda tunanin rabuwa dashi kawai yana sakani shiga mutuƙar tashin hankali, addu'ata Allah ya kawo mun duk wani abu da zai tunkaroni da sauƙi. Duk haka na wuni bana da walwala a gida,da Mama ta tambayeni mene ke damuna ce mata nayi kawai kaina ke ciwo na gaji,na iddar da sallar isha'i aka aiko wai ana kirana inji Halil,sai da na gama adduo'ina kafin na tashi na fita ina mai sake danne ɓaccin raina,tsaye yake jikin motarsa yana danna waya ,sallama na mishi inda ya ɗago da idanunsa yana kallona kana yace"yan mata". Kamar ya sake tunzurani,wai yan mata,cikin ɗacin rai nace "sannu ,ka aika a kirani Allah yasa lafiya".Bai amsani ba illa kallona da ya tsaya yanayi kamar wanda ya ga wani abu a jikina ko fuskata wanda bai taɓa gani ba. "Kin Kirani ɗazu Allah yasa lafiya shi yasa nazo naji"ya faɗa yana mai mayar da hankalinsa kan wayarsa,tunda shekarar ta shiga ba'a taɓa raina mun hankali kamar yadda Yaya Halil ya raina mun ba yau,cikin tawa sigar ta rainin wayau ɗin nace"aikuwa ban san na kiraka ba ,kilan na kwanta bisa wayarne ta shiga contact ɗin tayi dialing,kasan waya na haka amma ni kam ban kira ka ba"misafar Who is she ɗin da nake san mishi ma sai na kasa illa tambayarsa da nayi idan da wani abu idan babu kuma zan koma gida ,abun mamaki sai cewa yayi babu zan iya wucewa,kafin ma na wuce ɗin ya rigani shiga motarsa ya mata key ya bar gurin bai sake ko kallona ba hawaye kawai naji suna zubar mun a kunci da haka na juya nima na shiga gida Amma fa abin duniya ya mutuƙar damuna. Koda Mama ta tambayeni har ya wuce ɓoye mata nayi nace yazo ne dama kawai mu gaisa,har na shiga ɗaki ina jin tana yabansa. A haka muka ɗauke watanni uku da Yaya Halil yana nuna mun halin ko in kula,zai kira sau ɗaya yace wai ya kira yace mun sannu, gidanmu kuwa ya daina zuwa,wata kalmar soyayya kam nama manta yaushe rabon da ya furta mun ,da ace zan iya da tuni na daina ɗaukar wayarsa,amma Zuciyata ta gaza yin mubaya'a dani atleast yana tare dani yana kirana a kullum koda sannu yace mun sai na ɗan samu peace of mind,koda mama ta tambayeni yanzu baya zuwa sai ce mata nayi an mishi transfer zuwa Lagos ne shiyasa,ban bari tayi zargin wani abuba na cigaba da dakon soyayya da ban san ina muka tsaya ba dan ina saman tekune bisa gadar sarƙa,a haka har muka zana jarabawa duk da banyi wasa ba ban bari abin da ke gabana ya hanani nuna ƙwazona ba,na dage nayi karatu na rubuta,ranar da muka gama jarabawar washegari ranar juma'a wadda zan iya kira da bakar rana gareni ,ina zaune ina yima Hauwa'u kitso Enen da Aunty Hibba suka yi sallama,rabon Enen da gidanmu har na manta,zuwanta yanzu kuwa na tabbata abu mai muhimmanci ya kawota,har nagama sawa a rai magana tace da Yaya Halil, farin cikin ganinsu naji sosai,cike da kunya na gaishesu ta amsa mini tana kirana yarinyarta tana mai saka mun albarka,tare suka shiga falon Mama tana mai musu maraba kafin ta kira Adavize ya ƙarbo musu minerals gidan Maman Baba maƙotanmu,hanawa Enen tayi ta ce ruwa ma ya isa a hanya suke ,sweet ta miƙawa Mama da invitation card tana mai cewa "sweet ne da invitation card ɗin bikin Halil juma'a mai zuwa ,dalilin zuwa da kaina kuwa ɗaya ne ba biyu ba,dan Allah Maman Zunairah kuyi haƙuri an rasa mai zuwa ya faɗa muku,ita Anisa wai kunya take ji can na barta gida tana kuka bakiji ba wallahi har zazzaɓi tace mun ya kamata ,ɗaki na barta kwance,ta saka abunne a ranta". Murmushi irin na dattaku Mama tayi kana tace "to Enennisa (maman Anisa )ni na kasa fahimtar inda tashin hankalin yake, Aurena fa za'ayi ba mutuwa akayi ba,shi kansa haƙurin na gaza gane ta inda muka cancanta,ai abun mu haɗune mu nuna farin cikinmu ga shi Halil mu yi mashi addu'a Allah yasa abokiyar Alherinsace" .. Maganar mama ta mutuƙar bama Enen kunya,daurewa kawai tayi ganin tazo ɗin ya saka tace"Mama Zunairah,shi Halil ya yi leading Zunairah har ta ɗauka suna soyayya ne ,nima kuma da ya fara faɗa mun wallahi na yarda dan ce mun ya yi ita yake so,to da ya kawo maganar wannan Auren ne na damu nake tambayarsa Zunairah fa,sai yake faɗa mun ƙawance ke tsakaninsu dama, although da sun fara da soyayya abun kuma bai working out ba, still dai naji ya kamata nazo na baku haƙuri,Abu ne Allah bai ba". Ko Mama bata faɗa ba ranta ya ɓacci tunda ai baki da baki Yaya Halil ya shigo har gidan nan har falonta ya kalli tsabar idanunta yace yana san Zunairah yanzu kuma sai yace wai abokantaka ce? "Bakomai Enennisa ai ba laifinsa bane ,laifin ita Zunairah da ta bari har abokantaka ya shiga tsakaninsu duk da ta san babu abota tsakanin mace da namiji,muna dai Amfani ne da zamani amma babu komai ai Ubangiji ne baiyyi ba".ƙwala mun kira tayi, hannuna yana riƙe da gashin Hauwa'u dana kama ina kitsawa,ni ban kitsa ba ni ban saki ba,ba niyata na ji abin da suke faɗi ba dan bama kusa da gurin ma Amma maganar da suke ba wai ƙusƙus bace,itama Hauwa'u batace na saki ba duk yadda na damƙe mata gashi ,jin Mama ta kira sunana ya saka na saki gashin wanda ya saka Hauwa'u yin yar ƙara,sai a lokacin na kula i was hurting her ita kuma ba zata iya katseni ba sanin halin da na faɗa. Riƙeni tayi ta ce"Auntyna kada kije bari na shiga"murmushin ƙarfin Hali nayi nace ta barshi zan shiga ai ni aka kira,daga kujerar da Mama take naje na zauna ina mai san sakin fuskata kamar babu abin da ke damuna,Mamace ta ce"so Ohunene ga nan invitation card ɗin Halil da sweet ɗin Aurensa I thought na faɗa Miki babu abota tsakanin mace da ɗa namiji?mene ya haɗaki dashi?". Danne kukan dake san ƙwace mun nayi na bata amsar da na sani ita take san ji a bakina"Mama ai ba abota muke ba,kamar yadda Anisa ta ɗaukesa Yaya nima haka na ɗaukesa,babu komai tsakanina dashi". "Masha Allah,to ki kalla IV ɗin nan nasa sunan matar da zai Aura Zainab dan haka Wannan zoben da ya baki na ajiya ki cire mishi ki Basu sai a wuce mishi dashi". Tashi nayi na shiga ɗaki na ɗauko ƙaramin akwatin zoben da ya bani na cire daga hannuna ina mai jin zafin ƙirji kafin na rufe na koma falon na miƙawa Enen,ƙarba tayi ta buɗe kafin ta kalleni,nayi murmushi nace "ajiya ne dama ya bani". Miƙama yaya Hibba tayi wadda ta saka cikin jaka ,ban tashi ba Mama ma batace na tashi ba tace "insha Allahu zamu shigo baki ɗayan mu tun safe,Allah ya sanya Alheri ya rufa asiri". Sallama suka mana suka wuce Mama ta rakasu har Kofar gida ,suna fita na saka hannuna na riƙe ƙirjina dan ji nake kamar zai faɗi ,Mama na shigowa na miƙa mata hannuna ina kiran sunanta da kyar ,da gudu ta ƙaraso ta riƙe hannuna,wani irin kuka na fashe dashi ina faɗin"Innallahi waina illahir rajiun Mama ƙirjina,Zuciyata zata fashe Mama na shiga uku". Shigowa Hauwa'u da Adavize sukayi suna masu tayani kuka ganin yadda baki ɗaya na rikice ina mai dafe da ƙirjina ina faɗin zan mutu,ba zan iya fassalta irin ciwan danake ji ba ji nake kamar an zuba mun wuta cikin ƙirjina,rungumeni Mama tayi tana faɗin Allah ya bani haƙuri,ji nake kamar tana ta wanka mun mari,ta ina zan fara haƙuri?ta ina zan fara?ta ina?wane irin cin mutuncine da wulaƙancine wannan,mene nayi mishi da zai mun haka?". Ranar ji nake kamar alƙiyamata kawai ta tsaya ,koda Baba ya dawo shima haka ya yi ta aikin lallashi ,ransa sosai ya ɓaci amma sanin nuna fushin a fili baya da amfani ya saka ya ce nayi ta addu'a Allah ya bani wanda ya fishi,da zazzaɓi na ƙwana na tashi,ban taɓa tunanin a rayuwata zan iya cigaba da rayuwa bayan cin amanar da yaya Halil yayi mun ba,ta mun suka lokacin guda,baban ɓakin cikin guda wanda shine ban san abin da nayi mishi ba. Haka nayi satin nan har ya zagayo bana da walwala sai dai na samu kulawa sosai gurin iyayena wanda dalilin hakan ya saka na fara sakewa duk da na san har abada wannan tabon ba zai taɓa barin Zuciyata ba,yana cikin Labarina. Ranar da bakin yazo haka Mama ta shirya wurin sha biyu zata, Hauwa'u ce ta shirya rai a ɓace dan bata da niyyar zuwa mama ta saka sai ta bita,Ni kuwa dama duk wanda yace naje sai naji dalilin da ya saka yace naje,ƙarshe ma ina jin sai na yi gagarumar gaba da mutum dan maƙiyina ne kawai zai ce naje bikin Yaya Halil,abun da yake ɗaure mun kai shine yadda ya samu mata cikin wata uku,sai na barshi kan dama tun muna tare yana neman ta,idan har ni na cucesa ai Ubangiji yana ji kuma yana gani zai saka mishi,idan kuma shine ya mun haka da gangan yaje zai gani. Suna fita na koma na kwanta ,ni kaɗaice a gidan Muhammad Adavize ya wuce hadda,bacci shine kawai abin da yake cire mun tunani a yanzu. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 12.Babysitting *𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈* Ta rasa ina zata tsoma ranta saboda irin farin cikin da take ciki,zata iya cewa rabon da ta jita cikin farin ciki irin Wannan har ta manta,tana jin Enen na bawa Yaya Halil labarin abin da ya faru da sukaje gidansu Zunairah Sannan da zoben da ya bata wai na ajiya,a yadda Enen ta ce wai sun ɗauki abun da sauƙi ta san ƙarya suke ita ai ta san komai ta tabbata Zunairah na chan cikin halin tashin hankali,shine abin da take nema,idan tana tunanin zata mata soyayya da Yaya har a kai ga Aure to tayi ƙarya,sai dai idan har bata raye ne za ayi wannan ta'asar. Cikin faɗa Enen ke cewa"nan haka kazo ina zaman zamana kace mun soyayya ku ke kai da ita ashe tsiyar da kake shiryawa kenan,wallahi naji kunya,dan kawai ka san ba zan maka dole bane shi yasa kayi mun haka" "Yanzu dai ai ya wuce Enen tunda mu dasu muna kan yarjejeniya ɗaya,i told you kuma ina kan matsayata ni da Zunairah abota muke". Ganin yadda ya ƙarbi zoben cikin karamar zuciya ya saka yana tashi ta bi bayansa ,yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tayi Saurin kiran sunansa,juyowa yayi ya kalleta ,idan bata yi ƙarya ba wallahi hawaye ta gani a fuskarsa,da Mamaki ta ce"Yaya Kuka kuma?Yaya Zunairah fa bata cancanci hawayenka ba,duk Halin da take ciki yanzu gwara ta shiga data jefaka a halin da gaba zaka zo kana danasani mara amfani,ga Aunty Zainab yarinya yar gidan mutunci beside babanta malami ne I'm sure ka samu matar da duk inda akaje aka dawo yaranka za suyi alfahari da kai ka sama musu uwa ta gari,Annabi ma yace....." "Kin gama?"ya katse ta ,da ƙwalaƙwalan Idanunta ta ke binsa tana mai zazzaresu ganin ya zuba mata nashi,"idan kin gama ki wuce ki bani guri kada ki sake zuwa gurin nan ki ce zaki mun wani wa'azi bana san iskancin banza da munafurci".shiga ɗakin ya yi ya banko mata ƙofa,taɓe baki tayi ta bar gurin,ya yi ya gama ta san ƙarshe abun zai zama labarin tunda gashi nan ai babu wanda ya sama masa Zainab,shi da kansa ya nemota,duk yadda taƙi jinin haɗa Aure da Hausawa gwara su sau dubu da situation ɗin da yake nema jefata na Zunairah. Kafin kace mene ta fara nuna damuwarta ainun dan kuka sosai ta zauna tana Yima Enen lokacin da taji an fara maganar Auren Halil,dama shi da Zainab sun taɓa soyayya shi yasa da ya koma bai wani sha wahala ba aka daidaita,cikin wata guda aka gama komai aka saka Auren,koda Enen ta tambayeta tsakanin Halil da zunairah ita da kanta ta faɗa mata soyayya suke wanda hakan ya saka Enen shiga damuwa amma da ta sake tambayarsa sai ce mata yayi shi abota suke ita ta ɗauka da wani abun,sarai Anisa ta san halinsa idan ya kafe a abu guda ɗaya musamman idan yaji kamar an yaudaresa baya juyawa yana da taurin kai ta wannan fannin ,ta san a yanzu ma kan batun Zunairah yadda ta bashi babban Blow babu yadda za'ayi ya Aureta ya sake yarda da ita ,makamin da tayi amfani dashi da shine zata cigaba da cin yaƙinta muddin ba na ƙasa da su sosai Zunairah ta kawo matsayin miji ba. Lokacin da Khalipha yazo da biyu ta dinga manne mishi dan tana so Zunairah ta ji kwaɗayin soyayyar da ke neman ƙwace mata kafin ta ƙwace mata , Sannan wai dan raini ita take ma nasiha kan tana mannewa Khalipha, ta riƙe kanta ne bata kifa mata mari ba amma aje zuwa ,sai tayi mata raunin da bata taba tunanin zata mata ba,sai ta fita ta ko'ina a nan ne zata fito fili ta faɗa mata itama zata iya abun da yafi wanda ta iya. Anisa ce har da zazzaɓi idan ta shiga ɗaki zata lafe tayi ta kuka Hibba kuma zata ruɗe ta kira Enen su zauna suna ta bata haƙuri a haka har ta kwana biyu kafin ta saki jiki. Ranar da ta zagayo bikin Yaya Halil maimakon ta zauna a gida ayi da ita sai take jin babban bikinta yana gidansu Zunairah a matsayinta na Aminiyarta yaci ace ƙwana tayi gurinta tana dannar mata ƙirji,amma kuma idan taje ta ƙwana ya zama bata ji kunyar yaudarar da yayanta ya yi mata ba,ya kamata ace a zahiri taji kunya sai wasan ya tafi dai dai. Koda ta faɗama Enen zataje ta dawo bata damu da sanin inda zataje ba musamman yadda gidan ya cika da yan uwansu da suka zo daga Benue chan ƙauye ,kai tsaye gidansu Zunairah ta nufa,koda taje su mama na ƙoƙarin fitowa tayi tsammanin ba zata samesu ba,da fari raɓeraɓe ta fara amma ganin yadda mama ta tarbeta sai abun ya bata Mamaki,ta fahimci inda zunairah ta tsotsi munafurci, Hauwa'u ce kawai bata sake mata fuska ba dan da tayi mata magana ciki ciki ta amsa mata ,dama tana cike a ita da ta tsinkayi tana faɗawa Zunairah ta rabu mata da Yaya,itafa dama tuntuni ba wani mugun san Anisa take yi ba Saboda Auntynta ya saka take dannewa amma ai ba sai anfaɗa mata Anisa nada zubin munafukai ba ko ƙwalaƙwalan Idanunta zasu faɗa maka ,tayi ta wani zuba su tana kallon mutane. "Anisa dama baki damu kan ki ba kinyi zamanki gida biki fa ku ke yi, Zunairah kuma ƙalau take tana ɗan fama da ciwan kaine ƙwana biyu shi yasa ma baza ta je bikin ba"Mama ta faɗa lokacin da Anisa tace wai ta zo ta zauna da Zunairah. Cike da makirci ta ce"Mama na san abin da Yaya Halil ya yi ba kyauta ba amma dan Allah mama kada laifinsa ya shafeni,ba zan iya cigaba da mu'amala mai kyau ba idan har ku ka nisantani da Zunairah,zafinta nawane ,daɗinta nawane,na san komai Mama koda su Enen basu sani ba,babu abin da muke ɓoyema juna ni da zunairah tabbas soyayya mai ƙarfi suke da Yaya ban san mene ya saka ya yi mata wannan yaudarar ba,shi yasa ba zan iya zama bikinsa ba sanin Zunairah ta fi buƙatata a yau fiye da kowace rana"ta ƙare zance tana mai sharce ƴar ƙaramar ƙwala wadda ta kashe jikin Mama,bata iya hanata ba tace mata ta shiga ɗaki ta sameta su zasu wuce. Ita ta kulle ƙofar gidan kafin ta nufa ɗakinsu Zunairah ,ƙwance ta tarar da ita tana bacci,bata tasheta ba ta zuba mata ido tana kallon yadda ta rame,cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta ji karayar zuciya tana mai jin dama bata san Zunairah ba a rayuwarta da bata mata abin da tayi mata ba,lokaci guda kuma wani bangare na Zuciyata ya sake tunatar da ita,tunda ta santa babu damar chanza baya ko yin nadama. *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏 𝘗𝘖𝘝* Cikin bacci naji kamar ana kallona,buɗe ido nayi na sauke kan Anisa,komai sai ya dawo mun sabo dan gani nayi kamar shine a gabana,zuba mata ido nayi sai kace wadda nake neman amsar wani abu a fuskarta,itama ɗin kallona take batace komai ba na ɗan wani lokaci Idanunta sun fara kawo ruwa,saurin kawar da kai nayi gefe ina mai rumtse Idanuna da hawaye suka gangaro daga cikinsu suka sauka bisa ƙuncina,daga ƙwancen da nake ta ƙwanta kan cikina ta rungumeni tana mai fashewa da kuka ,bana da zaɓin da ya wuce na tayata domin cikin satin da ya gabata bana da aikin da ya wuce kuka ,cikin kukan take faɗin"mene zan Miki na cire ciwon da yaya Halil ya ji miki a zuciya?". Ban iya cewa komai ba sai kuka da nake tayi kamar raina zai fita,sai da nayi iya gajiyata kafin na iya yin shiru ,shima dan ana gajiyane amma fa ba zan gaji dana Zuciya ba,ruwa dana nema ya sa ta tashi taje ta ɗauko min sachet water ,koda ta dawo na tashi daga ƙwancen danake na zauna na jingina bayana da pillow,wani irin ciwo kaina yake yi, paracetamol da ta gani kan bedside ɗin mu ta ɗauko ta ɓalla mun tana mai cewa"na san kan ki yana Miki ciwo,amma tukuna kin ci abinci?". "Bana jin yunwa" Zama ta gyara tana mai aje ruwan kafun ta ce"Zunairah kan namiji ki ke san ki kashe kanki ko kuwa menene?ya nuna baya sanki bai damu dake ba ,ya ci amanarki ya yaudareki akan mene zaki zauna ke ki illata kanki?koda kin mutu fa ina so ki sani kece ki ka mutu shi tarewa zai da matarsa babu abin da ya damesa,dan Allah kada ki jama kan ki ciwan da Namiji bai cancanta ba". "Yanzu shikenan Anisa sai kawai na rabu da yaya Halil?kin san yadda nake ɗaukan soyayya na ɗauki Yaya Halil da girma na bashi dukkan yardata,na bashi dukkan zuciya mene nayi mishi mai muni da zai saka mun da haka?wallahi babu abin da na yi mishi na yi tunani na duba ban gani ba"na ƙarasa ina mai jan majina ina share hawayena. "Namiji kenan Besty sai ki bashi duniya idan ya tashi ya zuba Miki wuta ki ƙone ki mutu,idan baki damƙi kanki ba Mission ɗin Yaya Halil kenan ,ni dai fatana ɗaya Zunairah Allah yasa baki bashi jikinki ba". A yadda na zabura ko ban bata amsa ba ta san maganar ta dakeni,wani irin kuka na sake fashewa dashi ina cewa"shikenan abin da wasu zasuna faɗa kenan,amma Anisa ke kin fi kowa sanin halina,duk zafin soyayyar da nake ma namiji ba zan taɓa iya bashi jikina ba mene ya saka wannan zai ɗarsu a zuciyarki?haka ake faɗa a gidanku ko? wallahi babu abin da muka taɓayi ko taɓa hannuna ban taɓa bari ya yi ba ki tambayesa Indai akwai saura imani a zuciyarsa ba zai mun sharri ba". Ganin yadda na ruɗe lokaci guda ya saka ta rungumeni tana kuka tana bani haƙuri tana cewa ta yarda dani ta tambayane kawai saboda tsoron abin da zai je ya dawo. Cornflakes ta ɗauko a kitchen ta haɗa mun , kaɗan nasha,shima sai da tayi ta mun magiya sannan,maganin da ta ɓalla mun nasha,tanata lallashina kamar karamar yarinya,Anisa na sona,Nima ina santa bazan bari abin da Yaya Halil ya yi mun ya ɓata tsakanina da ita ba,na saka hakan a raina,ga wani irin girmanta dana ƙara gani,ban tsammanin zata iya barin bikin yayanta tazo kula dani ba har ta goya mun baya. "Mene ki ke ta kallona?I hope ba tunanin Yaya kike ba?"ta tambaya tana mai nufar mudubinmu ta ɗauko kibiya da mataji a gurin da muke ajewa. "Kawai ina jin daɗi da Allah ya bani ke matsayin ƙawa,ina jin daɗin yadda ki ke nuna damuwarki kaina, Nagode Allah ya bar mu tare ya tsarkake alaƙarmu"na faɗa ina murmushi,tunda aka fara abun nan sai zuwanta na samu nutsuwar dana samu na amayar da abin da yake raina. Murmishi tayi ta fara mun tsifa tana cewa "kada ki manta kafin Yaya Halil ya zama ɗan uwana Namiji aka fara haifarsa,dan haka zan zaɓeki a kowanne irin situation domin kafin na zama ƴar uwarsa mace aka fara haihuwata,Kinga kuwa babu yadda za'ayi kina mace ina mace na zaɓi ɗan uwana Namiji daya cutar dake dan kawai yana ɗan uwana,ba'ayin rayuwa a haka ko nace bana rayuwata haka because akwai masu zaɓan ɗan uwansu,amma ni i choose you,so chill kiyi kukanki yadda ki ke so kina da kafaɗar ɗora kai,I'm sorry lokacin Ma'aruf we were just minors ban iya baki kulawar da ya kamata ace na baki ba,but in tambayeki mana,da Yaya Halil da Ma'aruf wane yafi baki one blow seven die?". Dariya na saka wadda na ɗauka ba zan ƙara ba,Anisa kenan a duk halin da ake sai ta samo abin da zatayi da zai sakani dariya. Ban bata amsa ba itama ta tayani dariyar tana dawo da lokacin da nayi ta kuka Ma'aruf ɗin da zan Aura ya yaudareni,har cewa mukayi lokacin zamuje gidansu dan hauka,Anisa kuma na faɗin sai ta saka yan zaman banza sun karya mata shi ta basu kuɗi ,a wannan zagayen koda zuwan da tayi ta zauna da ni kawai ta barni dashi na gode mata it means alot to me . Tana ƙarasa tsefe mun kitson karshen cikin huɗun dake kaina wayarta ya hau ruri,tana ɗagawa Muryar Yaya Hibba ya bayyana tana cewa"Anisa an ɗaura Auren gashi tun ɗazu Yaya Halil na nemanki ". "Nayi Mishi mene?kice nace Allah ya sanya Alheri ni nayi nisa"amsar da ta basu kenan ta kashe wayar tana mai cigaba da mitar da ban taya ba,shiru kawai nayi amma a Zuciyata tunanine kala kala,na kasa yarda wai Yaya Halil ya yi Aure da wata ba dani ba,Yaya Halil dai danake kira ,Baby Habibi,Ina san Sanin mene nayi mishi ya yi mun wannan ɗanyan hukuncin mai firgici,sanin koda na tambayi Anisa ba sani tayi ba ya saka ban tada zancen ba nayi shiru ina auna yadda zanyi dakon wannan cin amanar da ya ziyarceni. Haka muka wuni tare ba ita ta tafi ba sai da Mama suka dawo da Magrib,shima sai da Mama tayi da gaske dan a cewar ta kwana za tayi dani,da ace zata kwana ɗin dana so duk da nasan buƙatata zatayi yawa,bai kamata na kasance mai san kaina ba,tun fari ma bai kamata ace tazo ta bar bikin gidansu ba tunda dai kafin na zama ƙawarta Yaya Halil ne ya fara zama ɗanuwanta dole kuma ya zamo gaba dani. Da dare kowa ya zauna cin abinci nima na fito daga ɗaki,babu wanda ya yi mun wata tambaya ,zama nayi gefen Hauwa'u dake aiki washe baki,Shinkafe ce da miyar Alayyahu Mama tayi mana,tare dukka muka haɗu a babban tray ɗin da muka saba cin abinci,Mama na saka Mana Nama Hauwa'u tayi saurin ɗaukar nata ta ƙara a nawa Muhammad ma ganin abin da tayi ya saka shima ya ɗora nasa a kan nawa,murmishi nayi nace"to idan na cinye namanku sai kuci mene ?". "Dukkan satin da ya wuce mu muke cinye naki ,yau ki ci namu"Adavize ya faɗa,kafin na sake magana Baba da Mama sun basu nasu ,murmishi nayi ina mai danne hawayen dake san ƙwace mun kafin na ɗauki naman na ci,kafun na ƙwanta Anisa ta kirani tana mai sake tambayata anya ba sai tazo ba domin ta kasa cire tunanina da halin da nake ciki. Dariya kawai nayi ina mai cewa"I'm not suicidal Besty,ba zan kashe kaina ba ,na yarda da ƙaddarar da ke tare dani a yanzu ". hira ta ɗanyi mun wadda ta sakani nishaɗi dan labaran da ta bani sun sani dariya,yan gidanmu ma sun shaida dan saida Mama ta shigo taga da ita nake waya,ikon Allah kenan Yayan ya dasan ciwo ƙanwar ta zamar mun Magani 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 13: newlyweds *𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓* Shi ɗaya zaune ya nutsu yana kallon zoben Zunairah kamar yana karatun wani abu a jiki, jin an fizge ya saka shi ɗagowa yana kallon wadda ta raina shi cikin gidan da ita kaɗai zata iya fizge wannan zoben. Washe baki tayi ganin Z a cikin zoben ,cike da zumuɗi ta zura a hannunta tana ma cewa"Tuntuni Halil ka bani zoben na mene ka ke jira?". Daga zaunen da yake ya taso ya kama hannunta da ƙarfin tsiya ya cire yace"ai kinfi kowa sanin ba naki bane,bana san irin abin da ki ke mun Zainab". "Aw ashe baza ka cire wannan shegiyar yarinyar a zuciyarka ba ko Halil?,to wallahi ko ni ko kai a gidan nan,dan Ubanka idan kana ganin za kayi Auren Zaɓi biyu dani kayi tunanin zaka ƙuntata mun bayan nan wallahi sai dai mu ƙuntatawa juna" Juyowa ya yi ya daskare a gurin yana kallonta"dan Ubana?"ya maimaita cike da mamaki,juyawa tayi ta bar gurin tana gunguni,saboda tsabagen Mamakin da ta shayar dashi bai iya yin komai ba illa bin ta da ya yi da ido har ta shige ɗaki,wai dan Ubansa,kalmar nan ta samu gurin ta toƙare mishi wuya,shin mene ya jefa kan sa shi kam? Tunda yau Auri Zainab yau sati biyu kenan ya kasa gane gabanta balle bayanta,zai iya cewa sun yi zaman ƙwana goma lafiya although suma ƙwanakin tana ta aikin yaɓa masa magana dan kawai lokacin da suke tarawa ta Auratayya a daren farko su ya kirata da Zunairah,babu irin lallashin da bai mata ba sanin shine baya da gaskiya kuma ya ɗauka amma ta ɗauki abin ta riƙe a zuciya take ta tafka rashin mutuncinta yadda take so,koda yan uwansa na ƙyauye suka zo halin ko in kula tayi dasu amma basu ɗauki abin komai ba a cewarsu baƙunta ne amma shikam sarai ya san iskanci ne. Yayi soyayya da Zainab sosai kuma ya sota abin da ya raba su shine kule kulen samari da kuma rashin iya magana,da fari ya zata zata bari amma ganin abun gaba gaba yake ya saka suka samu nesantuwa da juna,ranar da ya rabu da ita baki ɗaya shine ranar da yaje zance gurinta wani Alhaji yazo tace dashi wai ya jirata,kamar a mafarki ta nufa gurin Alhajin ta shiga motarsa yana tsaye yana mamaki. Cikin son ya ga ƙarshen ƙarya ya jirata,sai da tayi wajen awa guda yana wajen yana jira kafin Alhajin ya tafi Sannan ta dawo gurinsa ,"kayi haƙuri kawuna ne"shine abun da kawai ta ce mishi ta cigaba da juya rafa na kuɗi daya bata, "To"yace mata ya shiga motarsa ya tafi bai kuma waiwayenta ba itama kuma bata damu ba sanin soyayyar ta da Halil kamar Tururuwa da gida ne duk inda taje zata dawo ta shiga ta ƙwana,ta sani zai dawo dan dama haka faɗansu yake ,zai daɗe kamar ba zai dawo ba daga bisani kuma sai ya dawo ɗin. A wannan zagayen ganin ya daɗe bai dawo ba ya saka ta fara bibiyarsa ,nan take tsintar soayyarsa da Zunairah,ta damu dan har ta fara yanke tsammani,kwatsam sai ga kiransa wai zai zo gidan su,bata wani ja mishi Aji ba musamman a lokacin da take neman miji gashi kowa da take kulawa babu na Aure babu ma wanda zata kira tace ya zo su yi Aure ya amince,Zainab yarinya ce da ake kira da Yar malam taƙi halin Malam,Ƙaddarar za suyi Aure ya haɗasu a wurin dinner na abokinsa. Bai wani ja mata rai ba ya kawo maganar Aure inda babu ɓata lokaci tayi na'am da hakan,basu wani yi bincike mai kyau ba,binciken da sukayi ɗaya ya nuna musu Babanta Malamine ,kuma Malami a irin Matsayinsu dan shine babban Malamin Sanata Hadi madugu,babban Sanata a wannan yankin,sannan yana harka da manya yan siyasa,baya da wani abu da zai ɓatashi,hasalima yana cikin mutane mafi kima a unguwar ,a nasu tunanin indai ƴa tashice ai kamar an tsinci dami a akala ne. Duk da shi ya kawo maganar Zainab amma dai Daddy ya fishi zumuɗi Ganin haka ya saka ya basu wuƙa da nama,Yana san Zunairah ba zai ƙaryata ba,yana mutuƙar santa fiye da yadda bai taɓa tunanin yana yi ba amma abin da Anisa ta nuna mishi ya danne dukkan wannan son ya rufe mishi idanu,babban abin da ya fi komai ɓata mishi rai shine yadda take kallonsa take mishi karyar ita ta Allah ce,ya riga ya saka ma ranshi ta yaudaresa tayi mishi ƙarya dalilin da ya saka ya yanke hukuncin da a yanzu yake ganin bai bi a hankali ba,ace Amaryar sati biyu har ta fara kallon Ango ta zagi ubansa? Yanayin duk yadda ya kamata ganin ya cire Zunairah a zuciyarsa duk da ta kama kamar danƙo amma a koda yaushe tunaninta shine ke hana mishi sukuni,yana san ya yi rayuwa da Zainab ya bata dukkan kulawarsa ko hakan zai rage mishi wani abun amma ya kula ga dukkan alamu bata san su zauna lafiya. Juyawa ya yi ya fita a gidan,bai ankara ba sai tsintar kansa ya yi a bakin layinsu Zunairah,daga Chan ya faka motarsa yana mai tuhumar kansa kan mene yazo yi nan ɗin?.Yana ƙokarin yiwa motarsa key yaga ta fito daga gida da wata mata,duk da daga nesa kaɗan yake hakan bai hanasa ganin yadda ta faɗa ba,murmishi take tayi matar nayi mata magana ,saurin ƙasa ya yi da kansa ganin sun nufo gurin da yake inda take kallon cikin motar,yama manta Tint ne glasses ɗinsa,duƙawa tayi bakin mirror ɗin motar tana mai gyara fuskarta Inda take faɗin"Aunty Muna ko ƙwalli ban saka Bafa kalli idona kamar Nama". Kamo hannunta Aunty Muna tayi tana mai cewa"muje haka dai yau ai sai kin rakani bikin nan,kin zauna a gida kamar wadda ke takaba,ai kuwa yau sai na karya Wannan sirri sai munje, kizo mu wuce kafin mai motar ya fito daga inda ya shiga yaciki tarar kallan masa mudubi bada izininsa ba" Dariya tayi ta ɗaga tana mai cewa"aikuwa duk wanda zai aje motarsa a nan gurin nisa yayi"da haka bai sake jin abin da suke faɗa ba Aunty Muna ta ja hannunta suka wuce,juyawa yayi yana kallonsu har suka sha ƙwana,rumtse idanunsa ya yi yana mai jin ƙwalla na fito masa,da ƙar ya iya kama kansa bai fito ba,dan ji yake kamar ya fito ya ɗauketa su bar nahiyar baki ɗaya su manta da wani abu ya faru tsakaninsu,su manta da komai sai soyayyarsu ita kaɗai ta zama abun da suka sani. Bai san ya yi ƙewarta ba sai da ya sake ganinta,Anya abin da ya yi mata ya kyauta?ya kamata ace ya tunkareta ,amma a yanzu ya sani hakan baya da amfani,ya san da ace ta san shine cikin motar ba zata taɓa koda bin inda yake ba, babban dalilin da ya saka ya sake mota kenan dan ya sani a yanzu shine zai zama number 1 stalker ɗinta . A haka ya tsaya yana tunanin da baya da amfani kafin daga bisani ya tashi motarsa ya nufi gida,gashi dai ya ɗauki hutun wata amma hutun baya da amfani kamar yadda ya zata zai mishi.A falo ya tarar da Enen da Hibba suna kallon TV show,Sallama ya yi musu kafin ya shiga ya zauna ya gaida Enen,da mamaki ta ce"Halil lafiya dai ka fito gida da wuri haka?". "Mu da muketa saurin mu iskeka gida ni da Anisa"Hibba ta ƙara tana mai kallonsa. "Well yanzu ma ai sai na aje ku,dama na fito ne na gaishe da su Enen,Daddy fa?". "Daddy kam ai ka san ba zaka sameshi gida a wannan lokacin ba ya fita, fatan Zainab ɗin tana lafiya".cewar Enen. ", Álhamdulilah tana gaisheku kafin na kawota". "Yayi bari su gama ɗin sai ka aje su". Tashi Hibba tayi tana faɗin zata je ta kira Anisa itama ta ɗauko jaka da Mayafi,kallonsa kawai Enen take ,ta sani akwai wani abu dake damunsa duk da bai faɗa ba ,duk da bata tunanin matsalar ta gidansa ce tunda dai ai baza ka haɗa Angon sati biyu da matsala ba. Sallama ya yi mata suka wuce ,tun a mota yake san magana da Anisa ,sai da suka isa Hibba ta fita, Anisa na ƙokarin fita ya ce"Anisa kin haɗu da Zunairah kuwa?". Juyowa tayi tana kallonsa"Yaya ba dai tunanin Zunairah ka ke ba?Yaya zunairah ba sanka take ba, hasalima cewa Mamanta tayi kamar yadda na ɗaukeka Yaya haka ta ɗaukeka kuma wallahi na yarda da abin da tace ɗin yaudara kawai take maka,ka Auri Aunty Zainab and na tabbata kayi dacen macen da zata goge maka duk wani tabo da Zunairah ta ji maka,Forget about her and move on"tana Kai ƙarshen maganarta ta buɗe motar ta fita tana Allah Allah kada ya sake biyota ya dameta da maganar wata Zunairah. Koda suka shiga a falo ta tarar da Hibba zaune ,da Sallama Anisa ta shiga ,ganin Hibba ya saka tace "Yaya Hibba ina Auntyn namu?". "To nima dai nayi Sallama amma bata amsa min ba shine na zauna na jira Yaya Halil ya shigo sai ya shiga ya yi mata magana". Baice musu komai ba ya nufin ɗakinta,ƙwance ya tarar da itana danna waya tana dariya,da mamaki yace"wai zainab bakiji ana sallama a Falo ba?". Bata kallesa ba ta ce"naji so kake duk wanda yake sallama na tashi da gudu ina rawa ina guɗa na ɗauka na goya?kaga nifa Halil duk wannan abin da kake ban bika da gudu ina ihu ina cewa ka Aureni ba fa,kada ka tada mun hankali,ai wallahi ka taro Bala'i tunda ka kira sunan karuwa kana kaina,a danginku ka ware mun Wanda ba algungumi ba". Wani irin abu ya ji ya zo ya tukare mishi wuya,wai shi Halil Zainab ke ciwa mutunci haka,tabbas idan ya biyewa zuciya sai ya mata shegen duka wanda abu ne da baya fata. Gyara tsayuwarsa ya yi yana mai kallonta kana ya ce "kinji na rantse idan baki tashi kin je falon nan kin tarbi baƙi ba zan Miki shegen duka,wallahi sai dai a yar da abin kunya,zan Miki matsiyacin duka wanda baki tunani,dama ai ina ciki dake na zagina da ki ka yi,yanzu ba sai anjima ba ki tashi ki fita ko kisha Mamaki". Sheƙeƙe ta kallesa kafin ta tashi tana mai gatsine baki,"dama ai ance mun mazan Edoma na dukan mata kamar jakai,to wallahi baza ka fara a kaina ba,kwalelen kare da roman Jaka". Fita tayi tana wani kaɗa masa jiki,ya rasa mene yake damun Zainab,idan da za'a tambayesa mene hakan wallahi bai san mene zaice ba,yarinya sai rashin kunya kamar yar ƙwaya. Bin bayanta ya yi,tana isa falon ta ruga da gudu gurin da Hibba ke zaune dan har sai da ta tsorata Hibba,hannu ta saka ta janye ta da ƙarfi ta ɗauki throw pillow ɗin da Hibba ta jingina dashi tana karkaɗewa kamar kashi ya taɓa "what sort of madness is this,baku san idan kunzo gidan mutum ba ku nemi izinin kafin ku fara taɓa masa abu,and who even asked you guys ku zauna mun bisa kujeru?" Sheƙeƙe suka yi duka suna kallonta domin ba haka suka yi tsammani ba,Anisa ce ta waske tace"ina Kwana Aunty". "Da ban kwana ba zaki ganni?bana san munafurci irin na dangin miji fa,mene? meye ya faru?,idan abinci ne ku ka zo ci yana kitchen kuje ku dafa kada yarinyar da tayi tunanin zata zo nan baligun da ita nayi mata girki ". Duk yadda ya so ya ɗauka ,duk yadda ya so ya cije sai da ya tsinci hannunsa bisa fuskarta, wani irin zazzafan Mari ya zuba mata mai ratsa ƙwaƙwalwa,lokaci guda dukkan gurin ya ɗauke wuta,bai iya cewa komai ba haka su Anisa duk sun mutu a zaune,dafe gurin tayi sai da Marin ya kai mata iya kaiwa kafin ta fasa wani uban ihu mai ratsa kai kafin ta zube a gurin ta fara buge buge,kafin suce kwabo ta banƙare kamar yadda halittar kwaɗo yake da yadda yake jan ciki ,a tare suka haɗe guri guda cike da Mamaki,jan ciki ta fara ta nufosu tana wani irin kururuwa tana cewa "kun taɓa mana goɗiya,yau kowa sai ya mutu,yau za ayi gawa Uku, wayyo Bala'i ". Ganin da gaske gurinsu take zuwa ya saka suka ɗiba a wani na kare baki ɗayansu suna masu gogar juna suka fita a falon, window ɗin motarsa Anisa ta fara ɗaga ƙafa kamar zata haura tana faɗin lailahaillahanta subhanaka inni kuntu minnazzalumin. Ganin ta gigice da yawa ga Zainab har tazo bakin kofar Falo ya saka Halil fincikota kamar baby ya mara bayan Hibba wadda har ta kai bakin gate. Datso kofar ya yi,Allah ya saka a Aljihu ya saka mukullensa,key yama gidan ya duƙa yana ajiyar zuciya. Dan suna da yadda da abubuwa da yawa ,irin su Ojuju,spirits duk da ba garinsu suka tashi ba amma labari yana tsoratasu dasu dan kawunsu har yanzu yana ƙauye yana fama da sharrin evil spirits, although sun san Aljanu da zasu gani jikin mutum da sauƙi amma basu taɓa ganin wani ya yi gabansu ba sai Zainab. "Yaya ƙwado fa ta zama"Hibba ta faɗa da mamaki har a lokacin tana haki. Anisa kuwa ba baki burinta guda ɗaya ta ganta gida amma gashi ta manta Jakarta da takalminta, wayarta kuma na ciki da babu abin da zai hanata tafiya,ita da gidan Yaya Halil kuwa sai ta Allah amma ba da ita ba dan har Zuciyarta ba wasu Aljanu suka faɗo mata ba ,kawai Matar yaya Halil tana cult ne,idan ba haka ba ta ina mutum zai iya banƙarewa ya koma kamar ƙwado?ajiyar Zuciyar da ta sauke ya saka suka kalleta a tare kafin suka ƙwashe da dariya. Cike da rashin fahimtar inda dariyar tasu ta dosa ta ce"mene kuma abin dariya?". "Kece mana Anisa ,da ki ke bin window ina zaki shiga?"Hibba ta faɗa tana sake ƙwashewa da dariya. "Yaya Hibba bafa abin dariya bane wannan,matar nan is possessed,kina ji tana zata kashe mutum amma ki ke dariya?ko nace ku ke dariya?thank God ba gidan zan ƙwana ba Yaya Halil ka cigaba da biyeta kai zaka ƙwana ciki". Dariyar suka cigaba dayi wadda ke mutuƙar bawa Anisa Mamaki,kamar yadda ta faɗa ita fa bata ga abin dariya ba. Mintuna mara sa yawa sai ga Yayar Zainab da Babban yayanta da ya kira sun zo,Halil ya fara ganinsu,Nadiya Yayar Zainab ta fara kula da ƙafar Halil babu takalmi,kafin kace mene ta kece da dariya,yayan da ya fito ne yaga ta sheƙa dariya. "Ke lafiya ki ke dariya?". Nuna ƙafar Halil tayi ta ƙara fasa dariya da ta kula Hibba ce kawai mai Takalmi,abin mamaki shima yayan goɗaigoɗai dashi wai sai ya fasa dariya har da riƙe ciki,sai su abin ya daina basu dariya kar ma ace Halil da yake wa Yaya Yunusa kallan mutumin kirki. Ita kuwa Anisa ai burinta bai wuce ta bar gurinba dan ta fahimci gidan mahaukata Yaya Halil yaje ya samo mata,atleast if not Zunairah ya samu wadda ta fita Mana. Basu iya gaishesu ba Yaya Yunusa yace ya buɗe gidan,buɗe musu ya yi suna shiga ,yana ƙokarin bin su Anisa ta ce"Yaya ka miƙo mun kayana ni gida zani". "Ni zan aje ku,if not ki shigo ki ɗauka da kan ki"da haka ya shiga gidan Hibba na binsa a baya ,ita kuwa Anisa guri ta samu ta tsaya tana jiran su fito dan baza ta shiga ba,da suka shiga zaune suka tarar da ita bisa kujera tana danna waya,Yaya Nadiya na ganinta ta ƙwashe da dariya, ɗagowa Zainab tayi tana kallonta kafin da murna ta tashi ta rungumeta ta ce"Aunty Nadiya Oyoyo,Yaya harda kai? Har na fara tunanin fushi daku wallahi". Abun sai ya zama kamar a Film,one minute tana nan tana musu ƙwaɗo tana faɗin zasu mutu,one minute yan uwanta sun zo ta tashi kamar ba ita ba, bai kuma cewa wani abu ba ya ɗauko tarkacen Anisa ya kama hannun hibba da ta ɗauki jakarta itama suka fita,yana jin Nadiya na mishi magana ya musu banza ya fita yana jin ɓacin rai. 𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️ 08130229878. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 14:Moving on *𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓* Bai tashi motar ba baice komai ba,zaman shiru suka yi na wani lokaci cikin motar kafin Anisa katse shirun"wai Yaya baza mu wuce ba?". Juyowa ya yi ya kalleta ita dake baya ya ce"Anisa bana san Enen taji maganar nan,magana ta tsaya tsakaninmu". "Kai Yaya,duk Abinda matar nan tayi amma kace kada mu faɗawa Enen? someone need to step in o dan waɗannan da ka kira ba mutanen kirki bane banga alamaba baki ɗayansu yan iskane". Sauke ajiyar zuciya ya yi ya rumtse idanunsa yana san ya yi reasoning da ita kafin ya ce"Hibba ki mata magana, wannan maganar bai kamata ace Enen taji ba saboda girman Allah fa,Satina biyu da Zainab da Aure sai kawai ace mata wai Mun fara samun matsala?come on". Hibba ta saka baki har Anisa ta amince bazata faɗa ba duk da abun bai wani kwanta mata ba,idan ba Hauka ba bayan ta gama musu wannan iskancin yan uwanta kuma su zo su yi musu dariya?.haka tayi ta jaljala abun a ranta har ya kaisu gida ya aje,bai shiga ba ya juya,koda ya koma gidan abin haushin da ya tarar ya fi wanda ya bari ,Yaya Yunusa ya wani baraje mishi a falo sai kai lomar abinci yake gefe ya yi kaca kaca da ladar fast-food wanda ga dukkan alamu ya ci ne kafin a gama Taliyar da ko a ido bata burgesa ba. "Har ka dawo kenan"Nadiya ta faɗa tana mai fitowa daga kitchen ita kuma hannunta ɗauke da plate ɗin shinkafa bayanta Zainab tana yin waƙa itama hannunta da plate ɗin indomie. "Kan ubancan,wato abinci daban daban suka dafa dan tsabar rainin wayau ,dama ace gararsuce sai yace tasu ce amma good stuffs ne wanda ya siya da kuɗinsa tsabar isknci,ya yarda da Anisa ta ce dangin mahaukata ne su,amma dole a nemo mai hankali fa"guri ya samu ya zauna yana mai sake jin takaicin Yaya Yunusa wanda tunda ya yi sallama ya amsa bai kuma ce mishi wani abu ba,cike da baƙin ciki yace"ko dai sai na kira Malam ne,naga kamar maganar sai hannunsa". "Malam kuma Halilu,mene ya kawo maganar Malam?". "To fisabillilahi Yaya Nadiya na kiraku kan maganar da na san kune za ku faɗa mata taji amma sai naga kamar ma goyan bayanta kuke, Wannan yarinyar bata da kirki fa,ga wulaƙanci gaskiya bazan iya ba,idan baza kuyi mata magana ba zan kira shi Malam,nasan shi dattijo ne zai tsawatar". Kamar haɗin baki sauka fashe da dariya dukansu wanda yin hakan ba ƙaramun saka harzuƙa Halil ya yi ba,saƙeƙe ya saki baki yana kallon ikon Allah,jikinsa ya fara kallo kafin ya mayar da kallonsa garesu ya ce"akwai kashi a jikina ko kuwa maganar da nayi ce tayi kama da kashi ya gitta?wane irin abu ne wannan,wai har da kai yaya Yunusa,to gaskiya A'a ku tashi ku tafi,dama ai nayi tunanin manyan arziƙine amma tunda abin har da rashin mutunci kawai ku zo ku wuce idan ma da abincin ne zaku tafi da ku ka dafa kashi kashi ta baku kula,amma gaskiya kuzo ku wuce kafin na harzuƙa ace nayi ma dangin matata wulaƙanci ". Da zafi Zainab ta taso."Ni zaka cima mutunci gaban yan uwana?" "Kina zuwan nan wallahi sai na burma Miki hannu a baki wallahi,sai na fasa Miki baki ya yi jini kin rasa Waɗannan ƙazaman haƙoran naki da sukayi wutsiyar kare,Ni zaki cewa ina ma yan uwanki wulaƙanci,wanda suke min fa? "Ganin ya dunƙule hannu ya saka Yaya Yunusa ya jawota baya yana faɗin"Calm down Halil ba wai wulaƙanci bane kayi haƙuri iskokan Zainab ne sun iya iskanci shi yasa kaga munyi dariya mun saba da halinsu na banza". A wannan moment ɗin ji yake kamar yayi mishi mugun duka,"wato iskanta sun iya iskanci to ai nima Yaya Yunusa wallahi na iya,kada ku damu zan yiwa tufkar hanci kuje kawai Nagode ba damuwa ai iskanci ne yazo gidan ɗan iska ku gaida gida,zan maganin abun "bai bi ta kan Nadiya dake kiran sunansa ba ya wuce ya shiga ciki,yadda ya buga ƙofar kamar zai ɓalla ya saka Zainab ɗan firgita. "Wow this is amazing Zainab shi mijinki bai san wasa bane?"Nadiya ta faɗa inda Yaya Yunusa ya aje spoon ɗin da yake cikin abincin ya ce"Dallah Nadiya zo mu bar mishi gidansa ,mene a ciki idan ba tsiya abincin kuma ɗan ubansa sai mun tafi dashi,ke zuba mana a kula ai ya san ba tsiyarsa muke ba". "Bari kaga na zuba da kaina ubanwa muke tsoro,na fahimci idan muka biyema yaron nan ƙarshe iyaka zai mana da gidan yar uwarmu"cewar Nadiya wadda ta nufi kitchen dan juyin sauran abincin da suka dafa, Food pack Zainab ta ɗauko musu aka jera komai kafin suka kama gabansu,Nadiya na faɗa mata duk wanda bai raga mata ba kar ta raga mishi. "Wallahi kada ki ɗagama kowane shege ƙafa dan na kula mijin nan naki dan iskane"Yaya Yunusa ya faɗa cikin siga ta gaɓunta,haka suka gama suka wuce kafin ta koma cikin gidan tana mai juya huɗubar yan uwanta,wanda bai raga mata ba bazata taɓa raga mishi ba daga Halil har danginsa. ******************************************* *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* Kula da nayi rayuwa baza ta tsaya ba domin wani abu guda ɗaya na rashin jin daɗi ya saka na tattara dukkan lamurana na miƙawa Allah kamar yadda iyayena kan bani shawara,Mama zata ce mun"Ohunene duk abin da ki ka ga ya faru da bawa to tabbas baya da hanyar guje masa dole kuma sai ya faru Indai yana cikin zane na ƙaddarasa,dole ki yi haƙuri da Halil,duk wani abu da ya faru Alherina,yana nuna Miki tsakaninki dashi babu Alheri,idan kuwa da Alherin sai kiga daga baya kamar ba'a samu ɓacin rai ba". Kalmar watarana mu na sake komawa da Yaya Halil kawai da Mama ta faɗa sai da naji wani ɗacin a bakina,tunda na duƙufa da roƙon Allah kuwa sai nake jin koda yanzu aka bani dama na Aure shi ba zan amince ba, mutumin da ya yi mun haka kafin Aure ina ga idan ya Aureni ɗin?.Yaya Halil ba mutumin da ya dace nayi sha'awa bane matsayin wanda zanyi rayuwa dashi, forever is too long to joke with,bana ganin Forever ɗina dashi. A hankali sai nake jina sakayau kamar wadda aka saukewa nauyi,cikin yan satikan na fara jin sauƙi duk da nasan ba zan warke ba,amma mene sai na nemi abin da zai ɗebe mun ƙewar komai na ƙunci,duƙufa nayi wajen cigaba da rubutuna na littafin Love Scenery wanda Álhamdulilah sai nake ganin nasara tattare da hakan musamman a Arewapen da aka mun recommending ,a matsayina na Yar Arewa sai abin ya sake burgeni musamman ganin yadda aka karɓeni a manhajar duk da a sabuwa nake,sai nake jin tuntuni ina na tafi nake kokawar samun guri a inda wata ta bigeni har ake tunanin na sace mata fasaha,amma fa ban bar sauran Apps ɗin ba wanda suma a hankali aka fara karɓata musamman da suka kula Labarina ya sha banban da na 𝘔𝘪𝘥𝘯𝘪𝘨𝘩𝘵 𝘈𝘶𝘵𝘩𝘰𝘳𝘦𝘴𝘴 ga waɗanda suka bani dama kenan fa. Na gama sakankancewa akan baƙin ciki da fargaba zai barni sai kwatsam wata ranar Lahadi Muna zaune a tsakar gida,ni ina assignment ɗin makaranta da zamu koma Hauwa'u ma nayi na makaranta Mama kuma na ragewa Adavize gashi da clipper ɗinsa ,Sallama Aunty Muna tayi da sassarfa tana kuka tana mai ambatar "Mama Zunairah akwai tashin hankali" Sakin kan Adavize Mama tayi ta je gurin Aunty Muna tana tambayarta "Lafiya?.Uncle Abdulbaƙi ne ya shigo yana kiran sunanta yana cewa"wai kam Muna ba nace Miki kada ki zo ki tada musu hankali ba?"aikuwa take tashin hankali ya ƙwanƙwasa mana ƙofa dukkanmu lokacin da ya ce wai Baba yana state CID a kan case ɗin Satar Waya. Ruɗewa sosai Mama tayi ta fashe da kuka ta doshi ƙofar gida wai zata gurin Baba,Uncle Abdulbaƙi ne ya dawo da ita yana bata haƙuri yana cewa"Maman Zunairah abin zamu bi a hankali yanzu chan zamuje ni da maƙocin ku Malam Bello,dan Allah kiyi haƙuri ba wai ance ya yi sata bane". Ɗaga hannu Mama tayi sama tana kiran Allah tana mai gyara Zaninta ta ce"Abdulbaƙi Allah da nake bautawa ya fi Allahn wanda mugaye ke bautawa,Baban Zunairah ba ɓarawo bane ba kuma zai fara sata a yanzu ba da girmansa da yayansa da mutuncinsa,ka barni naje na samu yan sandan sai na faɗa musu hakan su ma". Mu kuka Mama kuka babu wanda zai ce da wani ya yi shiru ,gidanmu sai ya zama kamar gidan yaran da akewa allurar rigakafi,da ƙyar suka lallashi Mama shima sai da Malam Bello ya tabbatar mata zasu dawo da Baba cikin aminci,idan sunje basu dawo ba da shi ɗin ba sai a koma da ita gobe. Ai tana jin wannan Magana ta sake rushewa da kuka tana maimaita"aw yanzu sai ya ƙwana?"jin haka ya saka muma yaransa muka cigaba da rusa namu. Munsha kuka iya kuka,daga bisani Mama tace ai wannan kuka ba zai mana ba kowa yaje ya yi alwala ya yi Sallan Nafila ya faɗawa Ubangiji Mai kowa mai komai halin da muka faɗa duk da yana kallo kuma yanaji. Da su Uncle Abdulbaƙi suka je duk yadda suka so basu dawo da Baba ba saboda yadda case ɗin ya yi girma dan ko ganinshi ba'a bari sunyi ba amma an faɗa musu abin da ya faru,lokacin da suka kama Baba sai ya bada number ɗin maƙocinsa Malam Bello wanda shi ya sanar da Uncle Abdulbaƙi abin da ke faruwa. Dayake ƙwana biyu baya fita da mota ta samu Matsala sai yake hawa motar haya,to yana dawowa ranar sai ya ke dan rage ta daga gidan Gwamna duba da kuɗin dake jikinsa basu da yawa kafin ya hau abin hawa,kwasam sai yaga motar yan sanda har guda biyu sun kamo wasu a ciki suna bin wani dake ta tirƙar gudu kamar dai ƙwace musu ya yi,yana zuwa daidai saitin Baba suka cimmasa,Baba ya gama ruɗewa sai ya kasa gudu ya tsaya,ganin hakan ya saka wannan yaro da suke bi ya riƙe Baba Tsam yana faɗin "Oga ba haka muka yi da kai ba,kace duk rintsi baza ka bari a kamamu ba". Still Baba ya yi a gurun yana kallon yaran da ke kallansa cikin ido yana faɗa mishi maganar da bai ma san ina ta dosa ba,kafin Baba ya farga sai gani ya yi shima an daɓa mishi anƙwa tare da wannan yaro,.wai sai da suka je CID yake jin wai barayin wayane da suka damu yankin Tarauni aka kama sannan a cewar barayin Babane shugaban su,idan sun saci wayar shi suke kaiwa ,shine yake saka su yana biyansu wani abun,kuma wai Baba ke basu Layar ɓata. Abin Mamakin shine yadda duka yaran shida suka amsa sharrin na farkon akan abinda ya faɗa gaskiyane Baba ne ogansu,duka suka bada shaida guda ɗaya,ba a fara tuhumar Baba da ya mutu a zaune sai da aka ciro abubuwan dake jikinsu na tsubu,wai sai cewa sukayi Baba duk ya basu. Ɗaukar Baba akayi aka kai ɗakin DPO wanda yake san magana dashi ta san fahimta,suna so kada ya basu wahala suma kada su basu wahala a kaisu kuto a yanke musu hukunci,cike da rashin jin daɗin al'amarin DPO ɗin ya kalli Baba ya ce"Malam Buhari Muhammad daga kallonka dai kayi zubin mutane masu kamala na yi mamaki da ka saka kanka cikin irin wannan ƙazamar harkar,gaka dai aikin gwamnati ka ke yi gidan Gwamna ma amma kuma kana bada gudunmawa wajen ɓata mana tarbiyyan yara,saboda Allah yaran nan duk zaka haifesu amma ace kai kake goya musu baya wajen ganin ɓarna ta yaɗu?ka san yaran nan har kisa sunayi?ko da yake ai ba sai na tambayeka ba tunda kaine Uban gidansu,yanzu dai Bama wannan ba ka faɗa mun dalilin da ya saka kake goya musu baya ka ke saka su, bana san ta kaimu da sai an taɓa maka lafiya". Kuka kawai Baba ya fashe dashi Yana sake jaddada musu Wallahi ƙarya suke mishi hasalima shi bai san waɗannan yaran ba". Duk yadda suka bi da Baba maganarsa guda ɗaya ce,hakan ya saka DPO sawa a ɗauke Baba aje a bashi kashin tsiya,Allah sarki Babana,duk wannan Azabar bata saka ya amsa laifin da bashine ya yi ba,bayan sun masa matsiyacin duka har da karaya aka watsosa ɗakin da aka kulle yaran cikin Azaba,yanaji ɗaya daga cikinsu na cewa"Amma kamalu baka kyautawa tsohon nan ba,kalli yadda kwalawan nan suka mishi ragaraga fa". "To Habu dan Allah idan kwalawan sun shigo kace sharri nayi mishi kagani,ka dai san Oga bamaiyi zai kuɓutar damu ko? to idan muka ambaci sunansa aka zo aka kamashi mu wanene zai cecemu?shi wannan tsoho Eh mai sunan Daraja Allah yayi zai ɓara gyaɗar da bai soya ba ya kuma fige kazar wahala,kaddarasa,idan za ka ja eh banƙareren bakinka ka ja ka yi shiru". "Sai da kai mataimakin Oga,wanda ya bi wani bayanka Uwassa,Hubule na Atikar farm Centre mai shikafa da waken yan gata Allah wallahi "ɗaya daga cikin yaran ya faɗa. Ɗan sanda guda ɗayane ya leƙo ya ce"baza kuyi mana shiru ba ko ai mun saka ku?". "Sai Oga,ka huce haka nan"cewar Habu,Baba yana jin su bai ma iya faɗin komai Azabar dake ratsa tsohon jikinsa kawai ta ishe sa. Da safe Labari ke iske mu inda Malam Bello yace Mama tazo suje,suna maganar ne naji yana cewa Uncle Abdulbaƙi da ace wani babban zai shiga da abun yazo da sauƙi,da Mama suka wuce duk da Muna cikin tashin hankali haka nayi ta lallaɓa Su Hauwa'u suka wuce islamiyya duk yadda Hauwa'u ke nacin dan Allah kada na musu dole amma ganin rashin amfanin zaman da zamuyi mu haɗa kai muyi ta kuka gwara suje ɗin. Bayan wucewarsu abin duniya ya isheni,wane muka sani mai kuɗi mukam?duk inda tunanina ya kai na rasa wane zan kamo,ina wannan tunanin Anisa ta faɗon mun,ko wanka banyi ba na doshi gidansu na san idan naje daddynta zai taimakawa Baba. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 15: *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* Ganin nake kamar mai adaidaita sahun da na hau baya sauri,tsaki nayi har yafi a irga,tun yana tambayata lafiya ina ce mishi ƙalau har ya mun banza shima,daga gani na kaishi maƙura tsakin da nake ta bugawa,ban ji baƙin ciki ba sai da na sauka wai babu chanji. Da mugun takaici nace "amma mai keke sai da na faɗa maka ɗari biyar ce a hannuna kafin na hau ko?". "To Hajiya ki yi haƙuri a samu mana haba dan Allah,mutum ya yi ta tsaki kamar bashi da lafiya,Allah ya sa ba dani ki ke ba,yauwa abokina ɗan raba mun mana"ya maida zancensa kan ɗan uwansa mai adaidaita sahu,ni dai bance Mishi komai ba dan idan na biyesa ba ƙaramun faɗa za muyi ba a yanayin yadda nake jina,miƙomun chanji na ya yi yana mai cewa"Ƴar wahala". Na gefen dana sauka ne ya ce "dan Allah bawan Allah mu wuce ke kuma kiyi haƙuri kada ki biyesa". "Zaka samu daidai kai ne a gaba, wallahi"daga haka ban sake cewa wani abu ba na shiga layin su Anisa ,ni nake tafiya amma ji nake kamar ƙafafuna basu sauri duk irin saurin danake,sai da naje bakin gate ɗin gidansu sai ƙafafuna suka tsaya ,idan na shiga mene zan ce musu?after abin da Yaya Halil ya yi mun ya kamata ace nazo neman taimako su?take naji wasu hawaye sun fara zubar mun a kunci lokaci guda kuma maganar da mai Napep ɗin ya faɗa mun na ƴar wahala ya fara dawo mun,sai kawai naji maganar tayi mun wani ciwo da ta bada gudunmawa wajen sake fashewa da kuka na mara sauti,Aikuwa Ƴar wahalar ce ba komai ba,idan ba haka mene zai kawoni ƙofar gidansu Anisa neman taimako,ina self respect ɗin? "Mene ake da self respect bayan wanda yake riƙe mun respect ɗin danake taƙama dashi yana chan a kulle akan tuhuma mafi muni da ƙasƙanci"ina tsayen nan ina so na ƙwanƙwasa aka buɗe,Yaya Halil ne ya fito bayansa biye da Wata mata da ba sai an faɗa mun matarsa bace, Saurin matsawa nayi a kiɗime na ɗauke kaina ina jiran su wuce,tsaye yayi yana kallona,ganin yaƙi fita ya saka ta fito tana cewa"kaga malaika ne da ka Maƙale a gurin nan ko.."ɗaukewa maganar da take niyar yi tayi tana mai kallona kafin ta kallesa ganin ya yi mun ƙuri ya saka ta gano wacece ni,cike da sigar tambaya ta ce"Zunairah??"kallonta nayi a karo na farko ban dai amsa mata ba,Kama hannunta ya yi kamar wadda za tayi mun wani abu yana mai cewa"No Zainab bana san fitina". "Aw fitina Halil?fitina?da wannan yarinyar ka ke cin amanata ko ?shegiya ki ke yawo da wani tsayi kamar daren mutuwa,to wallahi karya ki ke,yanzu ubanki ki ka zo yi gidan nan dan Uwar babanki,Shegu matsiyata masu bin maza har gidan iyayensu" Rasa abin yi ya saka na fashe da kuka,na juya zan bar gurin ya rugo ya riƙe hannuna yana mai faɗin"mene yake damunki Zunairah?i can see it a idanunki wani abu na faruwa,menene ya faru? ". Ƙokarin ƙwacewa nake ganin Zainab na faman huci,cikin rasa wani abu da Zanyi nace Mishi gurin Daddy nazo ni ba gurin ka nazo ba". "Ka barni ni sai na tambayeta matsiyaciya yar iska". Ganin ta sake tunkaroni ya saka ya mayar dani bayansa ,ban ƙokarin Matsawa ba kula da nayi kamar bata da hankali,hannuna ya kama yayi gidan dani yana mai ƙokarin tare Zainab daga tunkarata,gyalen jikinta ta cire ta ɗaura a ƙugu ,tana mai yin wani shewa,ganin haka ya saka muna zuwa ƙofar na shiga da gudu inda tayi wani kukan kura ta yo ƙofar gidan itama amma sai ya tareta cikin zafin Nama,da gudu na shiga gidan ko sallama banyi musu ba na banka cikin falon ina zazzare ido". A tare suka taso suna tambayar Lafiya?,kuka kawai na fashe dashi,Anisa ta taso tazo inda nake ta rungumeni tana tambayar menene cike da damuwa,kafin na bada Amsa Yaya Halil ya shigo yana tare Zainab da ke rugowa da gudu tana faɗin wai sai ta kasheni. Enen ce ta tareta"menene hakan Zainab?". "Enen ki barni nayi maganin damuwata,wai yarinyar nan ashe har yanzu cin amanata suke da Halil,Kinga yadda suke magana da ido tsabar shaiɗanci?". Cike da jin haushinta Yaya Hibba ta ce"Wai ke kam mene damuwarki Aunty Zainab? Shi ya faɗa Miki wani abu ke tsakanin su". "Kada ki raina mun hankali Hibba,wa zaku mayar ɗan iska?ku dai da ku ke danne abin da yake zahiri saboda munafurci ku cigaba da yaudarar kan ku amma ni babu wanda zai Hainceni na yafe".ta faɗa cike da masifa tana mai tunkarar Zunairah da ke gefen Anisa tana ta kuka,ita ba wannan ma yake damunta ba,damuwar dake Zuciyarta tafi wannan haukan da Zainab ke gwadawa. Daddy da ya ji hayaniyarsu ya fito dan dama gama sallama da su Zainab kenan ya koma ciki kasancewar weekend,cike da mamakin faɗan da ake ya ce"mene ke faruwa ne ?". "Daddy Zina Halil yake ".Zainab ta tarwatsawa kowa kunne. A tare suka maimaita kalmar ZINA,? "mene ku ke maimaitawa kamar anyi mishi ƙarya,idan ba haka mene tsakaninsu shi da Zunairah,Daddy sigina suke ga juna ". "Kin wuce mu tafi wallahi kafin na saɓa miki"Yaya Halil ya faɗa ganin zata masa haukan da ta saba gaban iyayensa,a wannan point ɗin ya yarda idan aka kai Zainab asibitin mahaukata babu ɓata lokaci zasu bata gado. "Ja matarka Halil ku wuce gida "Enen ta faɗa tana mai mamakin ɗabi'ar Zainab,babu musu ya fincikota suka fita tana ta ihu tana zage zage har suka bar cikin falon baki ɗaya. "What madness "Daddy ya faɗa,yana ƙoƙarin juyawa Zunairah ta ce "Daddy gurinka nazo". Juyowa ya yi "Ni?" "Eh Daddy taimako Nazo kayi min dan Allah ,idan kayi min ba zan taɓa mantawa ba,and wannan abin da Matar Yaya Halil ke faɗa babu gaskiya ciki,babu abin da ya haɗani da Yaya Halil bayan mutunci ". "Kada ki damu da wancan abin tukunna dai taimakon menene ki ke so,wani ne baya da lafiya ko mene?". "Daddy Baba ne,yana state CID sun kullesa akan case ɗin satar waya tun jiya sunƙi bari kowa ya gansa?". Zama daddy ya dawo ya yi yana mai cewa"to mene ya faru garin yaya?".Labarin abin da ya faru na bashi cike da mamaki yake mayar da abin,kowa a falon na bashi tausayi daga kallonsu, tausayin nake so na basu a taimakawa Babana,dan naji ance idan aka kaika bompai sai Allah zaka dawo daga nan idan ba kayi wasa ba Abuja za a wuce da kai,idan kuwa aka kai Baba Abuja mun shiga uku mun lalace. "To su haka kawai sai su ambaci sunansa babu wani ƙamshin gaskiya kuma?" "Daddy!!!! Please kafi kowa sanin Baban Zunairah mutumin kirki ne just help him na san zaka iya daddy"Anisa ta faɗa tana mai zuwa inda yake jin abin da yace,duk da naji Haushi sai na danne tunda naima nake . "Wallahi Baba baya sata Daddy ,abu na karshe da Baba zaiyyi shine sata kawai dai tsautsayine da ƙaddarar da bawa baya iya tsallake mata". Shiru Daddy ya yi kamar yana nazari kafin daga bisani yace"ki je gidan zanje chan ɗin,zan kira commissioner of police".ban masa musu ba na tashi na tafi gida,lallashina Enen ta ringa yi har ta haɗa ni da driver muka wuce tare a Anisa wadda Idanunta ya kaɗa saboda Kuka da ta sha. Da mukaje gida a ƙofar gida muka tarar da Yaya Halil,ji nake kamar na mishi shegen duka ko uban me yazo ya yi mun oho,ina fitowa kai tsaye na shiga gida Anisa ta tsaya dashi inda take faɗa mishi abin da ya faru,wucewa ya yi shima station ɗin cike da damuwa mutuƙa,da ta shigo take faɗa mun yaje station ɗin. Mun gama saka rai haka Mama ta dawo wai har yanzu ba'a sake su ba,kana kallonta ba sai an faɗa maka gwiwowinta sun sage ba,cike da sarewa take faɗa mana wai kuto za a tura su washegari,Anisa ta fara kiran Daddy wanda ya shaida mata kada ta damu case ɗin ba zai kai har aje kotu ba,mu dai shiru kawai mukayi dan a wannan gejin kukan ma yaƙi zuwa.ɗaki Mama ta shiga ba dai tace komai ba. Da kulawa Anisa ke faɗa mun"Zunairah komai zai zama dai dai babu abin da zai faru da Baba". "Allah ya sa domin idan wani abu ya faru da Baba ina mai tabbatar Miki Anisa Mama zata samu damuwa idan Mama ta faɗa wani hali kuwa Kinga Asirin mu ya gama tonuwa". "Insha Allahu babu abin da zai faru,baki yarda da Daddy bane?komai idan aka haɗa da siyasa za'a dace,Daddy fa influenced ɗan siyasa ne kada ma ki yi tantama akan abin da zai iya" "To Allah ya zaɓa abin da ya fi zama Alheri "na faɗa ina mai tausayawa rayuwarmu tun kafin ta zama abin tausayi domin da Akwai tausayi Ita ta dafa mana shinkafa tunda dama gidanmu ba'a rasa miya,Aunty Muna kuma ta kawo tuwo,Anisa ce kawai ta iya ci sai Adavize da Hauwa'u dana titsiye su ci shikafan ko kaɗanne.Tuwon na kai ma Mama duk da na sani zai wahala ta iya cin abinci ni kaina ba dan Anisa ta saka mana tare tana mitar muci ba da babu abin da zan iya ci,. Tunani zata wuce ganin har munyi sallar isha'i ya tabbatar mun kwana ne za tayi,ban dai tambaya ba amma tunanin zata ƙwana ɗin kawai ya saka naji wani irin farin ciki,ina jin daɗi dana Samu ƙyautar Anisa,ita ɗin ƙwace da kowa zai so ya yi Alfahari da ita. Wuraren ƙarfe sha biyu na dare bacci har ya ɗauke mu naji Knocking kamar a mafarki,ni kaɗai na iya farkawa Anisa kam bacci take sosai ba damar na tasheta,dama su Hauwa'u ɗakin Mama suka ƙwana,wayata ce ta hau ruri,layin Yaya Halil da na mayar da Sunansa zuwa LESSON LEARNED ne ya Kirani,kamar bazan ɗauka ba dan sai da ta katse ya sake kira kafin na ɗauka. "Muna kofar gida da Baba ki zo ki buɗe". Wuntsilowa nayi daga kan gado,banyi tunanin ko saceni zai yi ba ko ya yi mun wani mugun abin,Babban abu mai muhimmanci shine Babana da ya ambata. A tsakar gida naga Mama da ƙatuwar fitilar ta tana tambayar wanene,kafin a amsa mata nace Mata "Baba ne ". Rige Rige mukayi wajen buɗewa,there Comes Baba an Mishi tara tara an kamo shi kamar kayan wanki,ban san ya akayi na fáshe da wani irin Kuka ba. "Ya mutu ko Halil?"Mama ta tambaya cikin wani irin yanayi da baza ka iya fassara abin da ya ƙunsa ba. "a'a Mama ya samu karaya ne a ƙafarsa guda ɗaya da hannunsa"ya faɗa yana mai kamo Baba abokin tafiyar nasa yana bin bayansa,sai a lokacin baki ɗayan mu muka kula da ɗaurin da ya sha,ɗaki aka shiga dashi,gado aka ajesa kafin Mama ta Mishi shinfiɗa Sanin jinyar karaya kan gado ba zai iyuba,wani bulo dake kitchen ɗin mu aka ɗauko dan ɗora masa ƙafa,abin haushi duk abin nan da ake Hauwa'u baccinta take shaƙa har gwanda adavize ace yarone. Godiya Mama ta yi ta musu,ni dai ban iya cewa komai duk da naji daɗin abin da suka mun har cikin Zuciyata. Itafa ƙasar nan tamu ta gado sai Kana da wanda ka sani,bafa wai baza a iya bane lalacine kawai irin namu,yaran da suka wa Baba Sharri babu wanda ya tuhumesu ko ya yi tunanin karya suke,an magana sunce ai rai shida baza suyima mutum guda ƙarya ba,amma menene hikimar bincike?.Baba fa duk Wannan baƙar Azabar bai amsa laifinsa ba amma har ake ƙokarin tura su kuto,mu dai ba bincike aka zo akayi gidanmu ba amma sai cewa sukayi an tara hujjojin da zasu kai su Baba kotu,da Daddy ya shiga a wunin Ranar aka fito da Ogansu Bamaiyyi inda suka ƙaryata kansu suka tabbatar da sharri sukayi wa Baba, bincikene wanda da ace anyi tun farko da ba'a taɓa wanda baiji bai gani ba,sai gashi da sanannen ya shiga anyi abin daya kamata ace anyi,wata shari'ar sai a lahira domin duk inda Baba ya juya ya ji azaba sai ya tsinewa masu hannu da tsaki da suka jefa shi cikin jidali. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 16:call it a day Jinya Baba ya fara cikin samun kulawa daga iyalansa, Álhamdulilah ana samun sauƙi dan bakinsa da ya kumbura ya sauka,muna dai shan yan dubiya,kama daga gurin Aikinsu har zuwa maƙota, ranar gidan su Anisa baki ɗaya suka zo sake duba shi,a nan ne Mama ta samu tayi musu isasshiyar godiya , kayan marmari da abubuwan taɓawa suka kawo mishi,fruits kam baya yankewa dan ko bamu siya ba Anisa zata zo takanas tace Daddy da Enen sun aikota ta kawo,sun bamu kulawa yadda ya kamata domin a wannan stage ɗin kallon yan uwa na fara musu ba iyayen ƙawa ba. Yaya Halil ya kan Kirani mu gaisa Sama sama ,na kasa samun ƙarfun gwiwar ƙin ɗauka mishi Wayarsa sai nake jin wannan Alheri da ya mun ya sanyaya mun Zuciya duk da ban manta yaudarar da ya mun ba,amma kamar yadda ya faɗa sai na ɗauki matsayin Yaya na bashi,akwai ranar da ina tare da Anisa ya Kirani kamar ba zan ɗauka ba amma sai na ɗauka,jin na ambaci Sunansa ya saka ta juyo a ɗari tana kallona. "Yaya Halil kuma?" Ban kulata ba sai da muka gama kafin ta sake dawowa kusa dani tana mai faɗin"kada ki ce mun ruwa ki ka koma". "Ruwa kuma?". "Eh mana,kada ki ce mun Yaya Halil ya samu nasara wajen yaudararki da daɗin baki ku dawo Soyayya da shi after duk abin da ya yi miki". Dariya nayi ganin yadda ta zazzare ido tana san jin amsata,"calm down babe babu abin da ke tsakanina da Yaya Halil bayan mutunci,after duk abin da ya yi mun kina tunanin shawara ce mai kyau na ƙi gaisawa dashi?Anisa wani lokacin ya kamata muna kallon Alheri kafin mu duba sharri,Yaya Halil bai Aureni ba haka Allah ya ƙaddara,duk abin da Ubangiji ya yi shine dai dai, Kingani komai ya zauna a gurinsa mai zai hana a cigaba da rayuwa kamar ba'ayi ba a manta abin da Ubangiji bai nufa ba?". "Amma Zunairah wannan abin fa akwai haɗari,da kike faɗin ya taimakeki ince Daddy ne kan gaba,mene ya yi Bayan zuwa ya tsaya har abin ya ƙare sai Umarni da Daddy ya bashi ya kawo Baba gida,kada ki bari ki koma baya kan namijin da bai cancanta ba, wallahi idan ki ka ce zaki Auri Yaya Halil Babu abin da zai hana matarsa banka miki wuta ki mutu dan bata da hankali". Ganin yadda tayi maganar da gasken gasken ya saka nima na saka tawa gasken waje bata tabbaci,"Anisa ba zan auri Yaya Halil ba koda zai rabu da matarsa ,na san you're looking out for me amma ki ƙwantar da hankalinki,irin wannan alaƙar ta yanke tsakanina a Yaya Halil ". "Da gaske?". "Insha Allah,yanzu dai ki cigaba da duba mun Draft ɗin page ɗin nan da zan ɗora anjima kada ki damu idan aka fara bani contract a Dreame zaki dara ". A haka muka shashantar da maganar Yaya dan dama babu amfanin tada ta.washgari Monday muka yi resuming makaranta abin da nayi missing shine baccin safe,first week of resumption muka koma ni da Anisa, idan kaga dama kira mu Mayun boko,maitar ta saka mu zuwa idan ance yau za a koma ai akwai dalilin komawar koda kuwa revision ne an ɗan tada mana ƙwaƙwalwa ,bayan gama Lecture Anisa ta kira Khalipha ya zo ya ɗauketa,jin hakan ya saka na ce"guess ba tare za mu wuce ba". "Aikuwa baki isa ba,tare zamu wuce zai fara dropping ɗinki gida in yaso mu sai mu wuce" Sanin koda nayi mata musu ba yarda za tayi ba ya saka nace to kawai,bayan wani lokaci ya kirata akan yazo ,dama muna bakin department ɗin Computer science nan muka gama cin Awara,powder ta ɗauko a jakarta ta ɗan shafa bisa fuska kafin ta shafa lip balm ,ni dai kallonta kawai nake,Anisa na san Khalipha da yawa ina mai mata fatan Ubangiji ya saka su ɗin Alherin juna ne dan da ace Khalipha zai ma Anisa abin da Yaya Halil ya yi mun ina ji ita sai mutuwa,.Tunanin hakan kawai da nayi sai da na nemi tsari da shaiɗan dake nema ya ɗarsa mun haddasa a zuciyata . "Ya ki ka ga fuskata? All set ko?". "Kin haɗu kilan idan Khalipha ya ganki yau straight waliyansa zai kira yace a ɗaura kawai daga nan sai gidansa". Dariya ta saka sosai tana mai tashi kana ta ce"ana zuwa wannan gurin,soon zamu zo nan i can't wait to have you as my chief bride maid ke nifa kafin na gama Buk nake san kama Khalifa a hannu dan ba zan bari a ƙwace mun shi ba,so nake na samu lokaci na mishi maganar Aure idan zai turo kawai ya turo". Ni dai murmushi kawai nake ina tsoron bada amsar da zata fito kamar ina baƙin ciki a haka har muka isa inda motar Khalifa take ,yana ganin mu ya fito yana murmishi,cike da shagwaɓa ta ce"Babyna Allah yasa baka jira da yawa ba". "Ban jira ba idan ma na jira ai gimbiyata abin a jirata ne,ƙawarmu ina wuni"ya mayar da idanunsa kaina. Kafin na kai ga amsa mishi Anisa ta karɓa"nifa bana gane ƙawarmu ɗin nan da kake yi fa,Zunairah ƙawatace ni kaɗai bana so wannan ai salon ƙwace ne". "Naji Allah ya baki haƙuri,babu wanda zai ƙwacewa Anisa Zunairah,ƙawar Baby ina wuni". Nima ina wuni ɗin nace Mishi,hannu Anisa ta saka dan buɗe gidan gaba ,Khalifa ne ya katse ta,"babe Farouk yana gaba ne tare muke". "And so,sai ya fito ya dawo baya kasan gaban mota nawa ne". Buɗe motar wanda aka kira da Farouk ya yi ya ce"ran ki shi daɗe yau sai dai a koma baya ,ai muna zaman lafiya ki ka taso mu dole yau ki zauna a baya". Haɗe rai tayi sosai tana mai cewa"to Allah yau sai na nuna maka motar Saurayina ce ba taka ba". A yadda suke yi Khalifa na musu dariya na fahimci Farouk da Anisa basa shiri,kowa na ganin Hanjin juna,ni dai gefe na koma na tsaya Khalifa na musu dariya,ni kaina ba so nake Farouk ɗin ya shiga bayan ba,idan ma ba iskanci irin na Anisa ba mene laifi idan ta shiga bayan mun zauna tare?. Juyawa tayi akan tafiya za tayi idan har Farouk bai bar mata gaba ba, Khalifa ya ci mata yana bata haƙuri inda Farouk ya fito gidan gaban yana mai cewa"ai sai ki zo ki zauna ɗin mara zuciya". Yana ƙokarin buɗe bayan ya kula dani dan ina jin sai a lokacin ya san tare muke,murmishi ya faɗaɗa da ya dora idanunsa a kaina,ganin ya zuba mun ido yasa nima na zuba mishi,buɗe mun ƙofar ya yi ya ce"Bismillah mai kyau da ace na san da ke waccan ɗara wada ɗin take ai bazan tsaya biyeta ta ba,cikin bugun zuciya guda zan dawo baya na zauna kusa da macen da tunda garin Allah ya waye banga mai kyawunta ba,infact na daɗe banga mai kyawunta ba". Wani dogon tsaki Anisa ta ja tana mai kiransa da Fuck boy kafin ta buɗe gaban motar ta shiga ,nima shiga nayi bangaren da Farouk ya buɗe mun kafin ya zaga shima ya shiga,Khalifa ne ya ce"ran gimbiya ya huce"kafin ya tada motar ni dai baki ɗaya na kasa samun nutsuwa musamman ganin yadda Farouk ya zuba mun ido, "Dan Allah ki faɗawa bawan Allah nam sunanki ko zan ƙara a cikin Zuciyata na ƙara kaimun bege ki,kinga idan na haɗa da sunanki mai kyau mai daɗi sai abin ya fi armashi". "Ummm kaji mayaudari,idan ka tashi sai ka faɗa mata yan mata nawa ka yaudara" "Khalifa hold your babe oo,ita ta samu gurin fakewa ni shine zata bata mun rawata da tsalle,kalli nan ƙawarta ki manta da wannan dan kawai naƙi santa kafin ta koma ga abokina shine take baƙin ciki". Ai kamar jira take ta juyo ta fara masifa tana faɗin"wallahi tallahi kai ka san nafi ƙarfinka,sannan baby ya fika ta ko wace irin siga,i will never choose you over him".hannu ta saka tana mai ɗorawa bisa gemun Khalifa wanda murmishi kawai yake yana tuƙi ,ni dai Allah Allah nake a saukeni na Kama gabana ba wannan nazo yi ba,koda ace Farouk da gaske yake dangane dani sai dai ya yi haƙuri na rufe babin saurayi,ko zanyi ba yanzu ba ,a yanzu karatuna shine Soyayyata dan na kula soyayya bata karɓeni ba. A haka Farouk da Anisa sukayi ta musayar zance har aka kaini ƙofar gidan mu,ina ƙokarin fitane Anisa ta dakatar dani ta hanyar faɗin"yauwa baby baka yi wa Besty jaje ba,Babane wallahi aka kulle a station akan case ɗin satar waya wai yaran sunce shine Ogansu ,kasan yanzu kuma al'amarin basu tsaya wani bincike ba suka karkarya Baba,har za aje kotu ma Daddy ya yi stepping in abun babu daɗi yanzu haka Baba jinya yake ,Allah ya sa ba akai ga kuto ba da yanzu yana gidan maza babu hakkinsa". Wani abune yazo ya tokare yawon da nake niyar haɗiya,kallona Khalifa ya yi cike da tausayin halin da ta zayyana masa da Baba ya faɗa yace"Ya Salam,Allah ya sake kiyaye gaba,Allah ya bashi lafiya ai ban sani ba da nazo na dubashi,kuma laifinkine Anisa da baki faɗa mun ba". "Yanzu ma ai bai ɓacci ba zaka iya zuwa ka duba sa"ta faɗa. Murmushin yaƙe kawai nake da ya buƙaci shiga duba Baba,fita nayi da zummar zan sanar da Mama kafin su shiga ɗin,kamar wadda laka ta karyewa a ciki haka na shiga gidanmu,ina mayar da Kofar na jingina da gate ɗin ,rumtse Idanuna nayi sai jin hawaye nayi,shin mene ya ɓata mun rai?. Mutunci Anisa tayi mun saurayinta yayiwa Babana jaje ya duba lafiyarsa Amma dole sai ta zayyana dukkan abin da ya faru da Baba,ba domin Anisa bace sai nace da biyu tayi min,na kasa haɗa abun ,sai nake jin zafin da ya kasance gaban abokin Khalifa ne,idan wani ya fahimta wani ba zai fahimta ba,cewa za ayi kilan ma dan Daddy dinta ya shiga ne aka yi siyasa aka fitar da Baba amma da saka hannunsa. "Auntynmu lafiya?". Buɗe idona nayi na saka su cikin na Hauwa'u dake sanye cikin uniform ɗin islamiyya,saurin goge hawayen da ya zuba kan kumatuna nayi ina cewa"lafiya mana,baku wuce ba uku saura ina Muhammad ɗin,Mama fa". Wucewa nayi ina kiran sunan Mama gudun kada Hauwa'u ta gane kuka nake,bina tayi da kallo har na shiga falo ,Mama ke Niyar fita tana kiran Hauwa'u. Kaina na saka nace"inya ki zo mana kina ji ana kiranki" takowa tayi daga inda na barta a tsaye ta shigo falon,Naira ɗari biyu Mama ta bata:"dan Allah Inya ki bawa Adavize kuɗinsa ya siya abin da yake so bani da chanji shi ya saka na haɗa muku".. "Cewa yake bana bashi kenan,ni Mama ba sai kin faɗa mun Inya ba muna fita zan tsaya shagon Baban chakwai na bashi kuɗinsa". "Naji dai Allah ya yi muku albarka ya bada ilimi mai amfani". Kallonsu nake ina mai ayyana abubuwa da dama da yaso ya mantar dani abin da ya shigo dani gida sai ga Muryar Anisa tana Sallama. "Wa nake ji kamar Anisa"Mama ta faɗa tana buɗe labule,shigowa Anisa tayi bayanta Khalifa da Farouk waɗanda suka tsaya nan ita kuma ta nufo falo tana cewa "wallahi Mama ina nan ina jiran Zunairah,wai Khalifa ne yazo duba Baba shine nace su shigo jinta shiru ". "Allah sarki ina nan ina sallamar su Inya ne,maraba shigo dasu mana Bismillah malam Khalifa maraba". Bance dai komai ba har ta kai mun dukan wasa a kafaɗa,daka bakin ƙofa suka duƙa suka gaida Baba wanda ya amsa musu duk da bai san su wane ba,Kuɗi Khalifa ya ciro a aljihunsa ya aje ma Baba,Mama ta ɗauka ta maida mishi,inda Baba ke cewa ai iya dubasa ma da sukayi ya isa ba sai sun bashi kudin ba,duk yadda ya yi Baba ƙin karɓa ya yi,gidan mu Muna da wadatar zuciya,idan har da kuɗi zaka siyemu zaka daɗe baka samu kasuwa ba. Ban rakasu ba Mamace dai ta taka musu tana mai sake musu godiya,kafin ta dawo ta mun maganar su na shiga ɗaki,tunda nake wannan ne karo na farko da naji zafin Anisa fiye da tunanina. Duk yadda na guji maganar sai da Mama ta tada mun tana mai faɗin wai suna da kirki na sake musu godiya,to kawai nace na cigaba da duba handout ɗina ,ganin kamar bana san maganar ya saka Mama rabuwa dani ta koma gurin Baba,da dare Anisa ta kirani, ina ganin kiran nata amma na kasa ɗagawa dan nayi fushi da gaske da ita. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟17: Negative Scene *𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈* Tunda Farouk ya fara maganar Zunairah taji baki ɗaya bata da nutsuwa,Farouk yana samu dan har ya fi Khalifa samu yana cikin babban dalilin da baza ta iya barin wata alaƙa ta ƙullu tsakaninsu ba,duk da cewa abin da ya faru da Baban Zunairah sharri aka yi mishi amma sai ta tsinci nishaɗi cikin hakan,atleast sun fahimci su ɗin kaskantune da family ɗinta zasu iya yi mata alfarma. Da biyu ta kawo maganar Baba ga Khalifa ganin Farouk yana neman tsaƙalewa iyakarsa shi ya saka ta saki bomb,tana kallon fuskar Zunairah ta san bata ji daɗiba amma daɗinne bata so ta ji dama,shi ya saka tayi suggesting su shiga gidan, although basa da kazanta,kullum gidansu tsaf yake amma tana so Farouk yaga cewa ita ɗin ba sa'arsa bace ba tsararsa bace ,sosai ta samu satisfaction lokacin da ta kalli idanun Zunairah,jin shiru bata fito ba ya saka ta ɗauki wayarta kamar tana magana da Zunairah sai cewa tayi gamu nan,babu musu suka bita cikin gidan kai tsaye tunanin an musu isone. Ganin Khalifa ya ciro kuɗi abun sai ya ƙara mata armashi amma wai sai suka ce baza su karɓa,"shegu munafukai" ta ayyana a ranta,da suka fito suna Mota Farouk ya ce"mutumina family ɗin Zunairah sun burgeni,and ke kuma da kika hanani sunanta ai gashi nan naji a ƙyauta,yar baƙin cikina kawai,abeg see how humble they are". Juyawa tayi tace mishi"na faɗa maka dai ka fita hanyarta,nayi maka baƙin cikin wallahi jelar raƙumi tayi nesa a ƙasa, Zunairah ta fi ƙarfinka sau babu adadi,ka saka kawai a ranka ƙwalelenka". "Ashe?to dan Allah Anisa idan har na nemi soyayyarta ta bani ki kasheni saboda baƙin ciki yarinya sai kace na kashe mata wani,senior ma hold your babe o". Ganin da gaske abun na san zaman musu faɗa ya saka Khalifa saka baki"ku yi haƙuri idan ba za kuyi ba nikam zan fita a motar nan ku yi dambe". Kallon Khalifa tayi ranta na sake ɓacci tace"babe nayi dambe da Farouk fa kace?ni? ,tsaya kawai na fita ".ganin yadda ta ɓata rai sosai yasa Khalifa ya fahimci da gaske take,magana yayi ma Farouk akan ya bari,badan yaso ba ya yi shirun amma har ransa a kan zunairah ya fara jin haushin Anisa. Bata bi ta kansu ba da suka isa gida suka aje ta,kai tsaye ta wuce gida,fitowa Farouk ya yi ya dawo gaba yana cewa "Man da gaske fa nake ina san Zunairah,i just see my future with her,but na kula babe ɗinka zata zamar mun matsala ". Key ya yi ma motar ya yi reverse kafin ya ce"well bani da wani abu da zan iya faɗa maka bayan yi maka fatan nasara,amma bana jin Anisa zata zama matsala a Soyayyarka,i mean mene zai dameta ". "Exactly abin da nake san sani,ban san mene zai dameta ba,idan babu ta bani space mana,she's getting on my nerves,amma kaga wannan Babe ɗin Zunairah na samu destination kawai". "Amma ita Fatima sai kayi yaya da ita?".ya tambaya hankalinsa na kan tuƙin da yake. Gyara zamansa ya yi yana mai rumtse ido "Khalifa ka san Fatima ba zaɓina bace ba kuma ba zan Aureta ba,Umma ce kawai ke kiɗanta take rawar ta ,ai na faɗa mata sannan tayi mun alƙawari duk lokacin da na kawo mata matar da nake so za'abar maganar Fatima,ni dai yanzu na kamu,ni bance Anisa ta bani number ɗintà ba da kaina zan nemawa kaina after all na san gidansu". "Babu abin da zance maka sai fatan Nasara cos Zunairah ta fita daga heartbreak wanda nake tunani ya yi affecting ɗinta sosai and yadda na tsinta gun babe this is not the first time". Juyowa yayi yana kallon Khalifa "shi kuwa wane mai asarar ne ya yi missing out wannan babe ɗin mai tsada". Ƴar dariya Khalifa yayi yana mai cewa "kada ka kuma kiran brother in-law ɗina asararre ka godewa Allah gimbiyar arewa bata jika ba". "Kana so kace mun Halil ya yaudareta,well asararsace ba nawa ba and kai ka sani duk wani heartbreak da take fama dashi i can mend it indai ta bani chance,kada ka manta Farouk fa ake Magana kai dai ka zuba ido kayi kallo". "To ai shikenan mutumina all the best Allah ya sa ka dace "cewar Khalifa da yake jin har ransa yana fatan Farouk ya samu Zunairah. Tunda Anisa ta shiga ɗakinta take safa da Marwa tana saƙa da warwara,ta rasa mene Matsalar Zunairah ,daga ta bata wannan ciwan kan sai ta nemi ta bata wani babu gaira babu dalili,bata gama ji da yaya Halil da ya dawo bibiyarta ba yanzu ga Farouk,big catch kamar Farouk wanda da ace babu Khalifa ita mai iya soyayya dashi ce dan ya haɗu aikuwa ko ana muzuru ana shawo babu yadda za ayi wannan alaƙar ta haɗu, wayarta ta ciro ta shiga number ɗin Zainab da ta samu wayar Enen,tunanin mene za tayi da zai Haukatata ta wulaƙanta Anisa cikin makaranta take. Sim card ɗin da take Data dashi ta tura mata saƙo"𝘩𝘢𝘳 𝘺𝘢𝘯𝘻𝘶 𝘮𝘪𝘫𝘪𝘯𝘬𝘪 𝘺𝘢𝘯𝘢 𝘣𝘪𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩 𝘥𝘢𝘻𝘶 𝘮𝘢 𝘢 𝘏𝘪𝘭𝘵𝘰𝘯 𝘩𝘰𝘵𝘦𝘭 𝘯𝘢 𝘨𝘢𝘯𝘴𝘶,𝘨𝘢𝘯𝘴𝘶,𝘈𝘶𝘳𝘦𝘯𝘬𝘪 𝘯𝘢 𝘤𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘩𝘢𝘥𝘢𝘳𝘪 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘣𝘢𝘬𝘪 𝘧𝘢𝘳𝘬𝘢 b𝘢,𝘻𝘢𝘬𝘪 𝘪𝘺𝘢 𝘮𝘢𝘨𝘢𝘯𝘪𝘯 𝘢𝘣𝘶 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘬𝘪𝘬𝘢 𝘻𝘰 𝘉𝘜𝘒 𝘮𝘢𝘴𝘴 𝘤𝘰𝘮𝘮𝘶𝘯𝘪𝘤𝘢𝘵𝘪𝘰𝘯 𝘥𝘦𝘱𝘵 𝘥𝘢 𝘴𝘢𝘧𝘦". Sakon yana nuna mata yaje ta cire layin ta karya tana addu'ar Allah ya saka gobe zainab tayi mata tijarar da tunda take babu wanda ya taɓa mata irinta,Farouk kuwa ta san tana da wani babban gurbi a zuciyar Zunairah da zata saka mata dafinsa a Zuciyarta. Tana zaune yaya Hibba ta shigo da sassarfa tana neman dan kunnen Anisa irin nata,tashi tayi ta ɗauko mata tana mai cewa"na san ya Adam za ki bi ku fita ,ki dai bi a hankali ". Dafa mata kafaɗa tayi,"sis ki ƙwantar da hankalinki next 2 months za ayi mana introduction nan zaki gane duk abin da nake faɗa Miki babu ƙarya a ciki". "Um"kawai Anisa ta faɗa ta bata ɗan kunnen ,duk wanda ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka,lokacin da zai mata ciki ya yi denying ɗinta a nan ne zata zo ta ciki musu gidan da tashin hankali. Da safe babu wanda ya tasheta dan zuwa makaranta dan yau farar Safiya take a gurinta,Driver dake ajeta shi kansa ya yi mamaki sanin wacece Anisa Indai wurin nawa ne,yau ita ta jira Zunairah a makaranta,da fara'a ta tareta amma ga mamakinta sai taga ta zauna bata ce mata komai ba ta fara fito da litattafai,sai abun ya zo mata a wani iri domin tunda take da Zunairah bata taɓa mata irin haka ba ko da wasa. Matsowa kusa da ita tayi sosai ta ce"Besty wane yau ya ɓato Miki rai?". Rumtse ido tayi ta juyo tana kallonta kafin ta ce"abin da ya faru jiya Anisa it shouldn't repeat it self,banji daɗi ba yadda ki ka kawo maganar Baba,bai kamata ba,kin san cewa magana ake ta Babana mene ya saka zaki faɗa ma Khalifa,har da baƙon fuska a gurin,idan wani ya fahimta kina tunanin kowane zai fahimta,wani ma cewa zaiyyi dan Daddy ya shiga aka saki Baba Amma da saka hannunsa,gaskiya banji daɗi ba". Sakin baki Anisa tayi "aw yanzu Zunairah dan na faɗawa Khalifa abin da ya sameki mara daɗi ya yi Miki jaje ya zama matsala?". "Ni ban ce Miki ya zama matsala ba,amma yadda ki ka faɗa mishi bai kamata ba ba dole sai kin faɗa Mishi duk abu da ya faru ba idan dole sai ya sani,a barshi ma Khalifa ne kaɗai,mene ya saka za kiyi magana irin wannan gaban Farouk wanda ban sani ba". "Ko kice wanda ke ƙokarin toasting ɗinki ba, kina tunanin ni kuma na faɗi hakan dan ya janye,in one word Zunairah kawai ki ce na Miki baƙin ciki". Kallonta Zunairah tayi na daƙikai tana mamakin abin da tace,daina kallonta tayi ta ce"duk abin a kika ɗauka haka ne,amma ni na faɗa Miki kada ki sake mun irin haka".cigaba tayi da ƙarasa assignment ɗinta wanda bata iya ƙarasawa ba jiya dare saboda baƙin cikin. Kallonta kawai Anisa take tana sake sake a ranta,a hankali ajin nasu ya fara cika,class rep ne ya shigo inda yake shaida musu yau Lecturer ya ce ba zai samu zuwa ba,kafin kace mene aji ya ɗauki ihu inda wasu suka fara ɗaukar jakarsu dan tafiya, Zunairah ma assignment ɗin ta mayar jaka dan dama na malamin ne,kamar ance Anisa ta ɗaga ido ta hango Zainab bakin hall ɗin nasu tana kalle kalle,itama Zainab ɗin sai Idanunta ya sauka a direction ɗin su,ai a zabure ta ƙaraso ciki har tana haɗe kafa,ita kuwa Zunairah baki ɗaya bata ma kula da ita ba,kafin ta ankara sai taji saukar bulala a jikinta ta ko ina,a ruɗe ta tashi sai a lokacin ta kula da mai dukan nata,bata tsaya mamaki ba ta fara neman hanyar gudawa,kamota Zainab tayi ta cigaba da tsula mata bulala tana faɗin"mijina baza ki daina binsa kuna iskanci ba ko?,uban mene ya kai ku hotel ke dashi jiya". Tasowa Anisa tayi tana kiran sunan Zainab kan ta bari amma bata karasa ba dan hanata sai hargagi dai take,yan ajin da suka rage ne suka riƙe Zainab dake aikin ɗura ashar akan Itafa sai ta kashe Zunairah,babban baƙin cikin Zunairah kuwa ba dukan bane ɓata mata suna da take a cikin aji,tashi tayi da gudu ta fita a ajin tana jin dama duniyarta ta tsaya a wannan lokacin. Biyota Anisa tayi a baya da jakarta ta kamo hannunta wai su gudu,baƙin ciki takaici ya saka ta fizge jakarta tana mai cewa"ke sai ki yi ta gudun mana, kada ki biyoni"da haka ta bar gurin inda Anisa ta fashe da dariya ganin ta sha ƙwana,fitowa Zainab tayi,ganin Anisa ya saka ta ce"ina shegiyar tayi,ko da yake ai kema munafukace ba faɗa za kiyi ba". "Ina cewa hanya guda ɗayace ta fita daga Nan,ta inda ki ka biyo nan ne hanyar komawarki itama nan ne zata bi amma duk abin da ya sameki ke ki ka jawa kan ki". Tsaki Zainab tayi ta bi hanyar da Zunairah ta biyo,wayarta ta ciro ta kira yaya Halil ta ce masa ai ga nan Zainab ta zo Makaranta tana zane Zunairah,bin bayansu tayi bayan ta gama tada mishi hankali,so take tayi nawa da abin yadda har Yaya Halil zai zo dan ya ce mata yana kusa da makarantar nasu. Zainab na barin gurin Allah ya ɗora Idanunta kan Zunairah dake jiran keke,kamota tayi ta baya kamar kayan wanki kafin ta ɗauketa da mari ta cigaba da zaginta tana faɗa maganganun ɓatanci a kanta,zafin hakan ya saka Zunairah ta biyeta ,kafin kace mene dambe ya kaure tsakaninsu,ƙoƙarin raba su ake dan masu daidaita sahun nan duka suka yo kan su,kafin securities dake bakin ƙofa,kafin Zunairah ta kula Zainab ta kamo mata hijabinta wanda ta sauke mata shi har ƙasa,tana aiming rigarta wani ɗan takifen dan Napep ya ɗauke ta da mari yana faɗin"dan uwarki tsirara zaki yi mata, shegiya mahaukaciya". Wani irin ihu ta fasa tayi tsalle ta dira ta zube a ƙasa,ganin haka kowa ya dare a gurin,har da Zunairah,me Napep ɗin da ya mareta ne ya cire belt ɗin jikinsa yana cewa"ai mu abin nema ya samu Aljanu ?wallahi kin zo gun masu maganinsu". Kafin ya kai ga dukanta ɗaya daga cikin security ɗin da yazo ya hanasa,ihu kawai take a ƙasa tana ta mirgine mirgine ,duk waɗanda tazo inda suke sai kaga sun dare,Anisa kuwa tana chan gefe tana video duk wani abu da ya faru,mai dan sahun nan ne ya bi bayan zunairah da yaga ta juya dan barin gurin tana mai riƙe gaban hijab ɗinta,"Hajiya ina zaki na aje ki". "Tsamiyar boka"ta bashi amsa idanun nan sun kaɗa sunyi ja saboda kuka,tana kokarin shiga keken nashi sai ga Yaya Halil domin yana zuwa Anisa ta nuno mishi ita ,bai bi ta kan Zainab ba ya nufeta,riƙe keken dake niyar tashi ya yi ya ce"Zunairah ki tsaya muyi magana ". Kallonsa tayi amma ta gaza faɗin komai illa ɗauke ido da tayi daga kan sa,ganin haka mai sahun ya ce"Malam ka sakar mun Keke ko na fizgeka Wallahi ". Ganin zai fizge shi din ya saka ya saki suka bar gurin ,komawa yayi kan Zainab da ke ta hauka,sun daɗe a gurin ana abu ɗaya kafin iskanci da take ya lafa,da kanta ta tashi ta shiga motar Halil dan dama bada mota tazo ba,jikin nan nata biɗubiɗu,Anisa ma su tabi tana mai jin itafa an biyata,gida ya Kaita ƙin fita tayi sai da ya fita ya jawota waje ya yasar nan compound kafin ya koma motar ya fita a gidan Anisa na gefensa,sai da suka bar gidan ya faka motar ya kalli Anisa ya ce mene ya faru? Matsar ƙwalla tayi ta ce"Yaya wallahi yau Aunty Zainab kam ta ɓatawa Zunairah suna a makaranta,wai ance an ganku tare a hotel jiya". "Ita wane ya ce mata hakan?"ya tambaya ransa babu daɗi. "Oho,nima Yaya wallahi ban sani ba,bari kagani har recording nayi maka sanin ba zan iya dakatar da ita ba amma ai ina da hujja akanta".Yana gama kalla ya tashi motar yana tunanin menene ma zaiyyi zuciyarsa tayi masa sanyi dangane da abin da Zainab ta aikata. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟18:Behind all odds *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* Kuka kawai nake a cikin Napep ɗin da na hau,duk da babu sauti amma hawaye fa ɗaya bisa ɗaya,bini bini mai keken nan yana juyowa yace mun nayi haƙuri,da muka shigo tsamiyar boka ne na nuna mishi layinmu dake jikin masu wankin Hula,da yake gidanmu ba can ciki yake ba a layin muna shiga na nuna mishi gidanmu,daidai ƙofar ya tsaya kuɗinsa na fara lalube zan bashi ya katseni ta hanya faɗin "Ita rayuwa dole bawa ya haɗu da jarabawa,idan mutum kuwa ya san kamala ba sai an nuna mishi mutum mai kamala ba,daga ganinki na san ke mai mutunci ce kuma duk abin da wancan mahaukacinyar ta faɗa a kanki na san karya take,kuma muna nan zata haɗu da daidai itane a gaba,kalle itane ke da asara musamman yadda ta wulaƙanta kanta waje wulaƙantaki,da zafi ki yi haƙuri". Kuka ne mai ƙara yake san fito mun amma na danne sai hawaye,ɗauke idona nayi daga kallonsa na ce"nawa ne kuɗinka?". "Ki ɗauka akan yau driver ɗinki ya ɗaukoki,idan mun haɗu gaba sai ki bani,ki saving sunana a ranki da Khubaybu mai keke "da haka ya ja adaidaita sahunsa ya yi gaba tsintar kaina nayi da yin murmushi ban bari yadda yake magana ba ya wuceni wajen gane mutumin Kaduna ne (itane,wancan kalle,),ban taɓa tunanin zan samu dan adaidaita sahu mai mutunci ba,tun haɗuwata da wanda ya kaini gidan su Anisa da damarmakinsu sai nake ganin kamar duk basu da kirki. Gida na shiga ina mai sake riƙe hijabina,ina shiga gida ɗaki nayi niyar guduwa amma mama ta ganni,cike da tashin hankali da Mamaki ta ce"ke lafiyarki ki ka shigo kamar wadda tayi kokawa?". Ɗauke kai nayi na ce"lafiya ƙalau Mama,"hannu ta saka ta jawo hijab ɗin da nake riƙewa ta ce"ba dai Lafiya ba Ohunene wane ya yaga miki hijabi?,faɗa ki ka yi a makaranta?,eh ye ye muga fuskanki wane ya yaƙusheki?" At that point bana da halin ɓoye mata kawai sai na fashe da kuka ina ma faɗawa jikinta,bata hanani ba illa ma sake rungumeni da tayi tana mai ɗan buga mun bayana ,sai da nayi wanka naci abinci kafin Mama ta sake tambayata abin da ya faru,ban cire mata komai ba na faɗa mata,ita kanta abin ya yi mata ciwo dan haka nan tayi ta yagar faɗa Baba yana ɗaki sai dai kaji ya ce"Áhé(ayi haƙuri)"kamar ƙara tunzirata yake haka ta cigaba da faɗan,Mama bata iya fushi ba,gata da nacin faɗa da su Hauwa'u suka dawo ni ina ɗaki ma naji tana bawa Hauwa'u labarin abin da ya faru,ko kayan makaranta basu cire ba suka haɗu sunata ƙwashewa Zainab albarka ni dai ina jin su bance komai ba na koma na rufe ido na. Wuraren la'asar muka ji Sallama a bakin gida,Mama ce ta leƙa,ina ji tana maraba Muryar Anisa dana tsinkaya ya sa na fahimci zuga aka mana,ƙaramin tsaki nayi na cigaba da danna wayata, can baya sun shiga ɗaki Sai ga Mama wai nazo munyi baƙi,cikin fuskar damuwa nace "Mama su waye,kice musu bacci nake yi ". "Aikuwa ba za a yi haka ba,mutanen da ke gabana ba za iya musu ƙarya ba Zunairah ki tashi muje ki sako hijabi".haka nan ba dan ina so ba na tashi ɗin naje,ganinsu duka sai da gabana ya faɗi,ɗan falon namu da kyar ya iya ɗaukarsu,daga Chan bakin ɗakin Mama na zauna ina mai gaishe dasu,idanuna na sauka kan na Zainab naji wani sabon baƙin ciki ya taso mun,sai abin da tayi mun ya dawo mun kamar sabo, fuskokin sun mun yawa amma na fahimci da Daddy,da Yaya Halil,Zainab,Anisa sai wasu fuskokin da ban gane ba. "Malama Zunairah ko?" Kallon wanda ya yi maganar nayi,mutum ne dattijo wanda yake sanye cikin shiga ta mutunci ,"Nice"na bashi amsa. "Yauwa ni sunana Malam isa Umar mahaifin Zainab,naji abin da ya faru tsakaninku,ko kusa ko alama banji daɗi ba nasan abin da ya faru ya faru amma ina so ki yi haƙuri ki duba wannan majalisi da muka tara domin ke ki yafe mata ita Zainab ɗin,shi Ubangiji yana san mai hakuri da yafiya,wala ala abun ya miki mutukar zafi duk da dole ke ya yi miki,ga nan ita jairar ban bari ta rintsa ba lokacin da shi mijinta ya kaimun ƙararta ,nazo har gidanta na tasata gaba mukaje gidan su iyayen mijin nata na ɗaukosu kana muka zo nan, wannan abu bai daɗi ba bama fatan kuma ya sake maimaita kansa,Ah ina ita Zainab?". "Gani"ta faɗa tana mai cin magani. "Maza ki bata haƙuri har sai tayi na'am an samu mubaya'a ta haƙura". "Yi haƙuri"ta faɗa ciki ciki.Ganin yadda take aikin haɗe rai kamar wadda ka saka cin tuwo ba miya ya saka nace "banji ba,ki buɗe baki da kyau,ai lokacin da ki ke dukana a makaranta baki rage volume ba kuma da kina ɓata mun suna bakinki kamar zai taɓo ceiling Energy ɗin zaki saka waje bani haƙuri tunda ai kin san yadda ki ka ɓata mun suna a makaranta baza ki iya gyarawa ba,sai dai in idan ban sani ba zaki yi using same approach". "Ohunene !!"Baba ya kira sunana daga cikin ɗaki,Mama ce ta ce"Baban Zunairah ka tashi kenan". "Eh buɗe mun labule ina kallon Zunairah da idona,gaban mutane masu girma ki ke faɗan magana haka,idan baki ji kunyar kowa ba ai zaki ji na manya da suka zo har gida suka nemi alfarmarki". Gaishe da Baba Sukayi inda ya amsa musu yana sake basu haƙuri,ji nake kamar na jawo baba daga ɗakin na fama ciwan dake ƙafarsa da kullum bamu iya bacci idan ya taso masa . "a'a Malam Buhari ka rabu da ita ai hakkin tane ,an ma yarinyar nan ba dai dai ba a rabu da ita"Daddy ya faɗa yana mai bawa Zainab mugun kallo,sake bani haƙuri tayi da ɗaga murya,naso nace ya yi ƙara da yawa zata fasa mun kunne amma kunyar mutanen da ke gabana ya saka nayi shiru. Babanta ne ya tambayeni na yafe nace "eh na yafe malam amma gani gata ga Yaya Halil gaku ayi mun iyaka da ita ,babu abin da yake tsakanina da Yaya Halil,ni soyayya ma bamu taɓa yi ba ai ya faɗa ,koda munyi soyayya ai tayi winning tunda ta Auresa,ni ta rabu dani ta daina harassing ɗina,babu komai tsakanina da mijinta babu kuma abin da zai shiga tsakanina da mijinta nan gaba".. "To ke kin jita mutuniyar banza wallahi idan wani abu ya sake haɗata dake ni dakene,kuma ai shi Halil mijin mace huɗune laifine idan ya nemi mace ya Aura?"cewar mahaifinta. "Ba laifi bane Baba amma laifine idan alaƙar ta wuce ta neman Aure ". Jin abin da tace ya saka Yaya Halil cewa ,baza ki daina dangantani da ɗabiar banza ba ko Zainab?. Murguɗa baki tayi ,haka Babanta ya yi ta mata faɗa inda ni kuma akata bani haƙuri,ko haka Allah ya bar Yaya Halil bisa yaudarar da yayi mun ai ya isa haka,shiyása aka ce ka kyautata alaƙarka,da ace ya san ba zai Aureni ba bai kamata ace ya nuna mun soyayya ba har ta kai ga ya mun yaudarar da ban taɓa tunanin a duniya zai mun irinta ba,sai nake jin a zuciyata na yafe mishi ko zai samu sassaucin abin da yake ji tattare da iyalinsa . Bayan sun wuce ne Mama kecewa "ai kin mun dai dai da kika nuna masu ke jininace,yar banzar yarinya mai kama da Mayu". "Maman Inya ki daina biyewa ana haka dake oo"Baba ya faɗa. "Abeg Baban Zunairah ka barni na faɗi abin da ke cikina tunda ai ba a gabansu na faɗa ba,ba ayi mun dai dai ba nikam,kaga yadda yarinyar nan ta yagar mun fuskar yarinya ne?wallahi taci darajar masu daraja da ni da kaina zan mata wulaƙanci". Ni dai bance komai ba amma tunanin yana kan Yaya Halil,ina jin tausayinsa har rai na,na san mutane da yawa idan suka ji Labarina zasuji haushin tausayin da nake mishi amma i can't Help it mutum ne da muka yi soyayya dashi dole ne sauran tausayinsa ya tsaya mun a ƙirji domin duk wanda aka haɗa Aure da mutum kamar Zainab a yadda na fahimceta sai ta saka mishi ciwan zuciya. Da bayan sallar isha'i ina zaune ina fama da kaina wai aka buga ƙofa ana Sallama da Zunairah,abun ya bama kowa mamaki , Mamace tace ma wanda ya shigo ɗin yaje yace nayi bacci,naji daɗin hakan duk da ban san wane ba,ina jin Mama nata faɗa akan anzo ban gama fama da abin dake damuna ba za ana mata passing na neman yarinyar kamar tace nema mata saurayi take,Mama kenan idan ta rikice baka gane mata ko kaɗan,Ni dai ina ji ban ce komai ba ina dai mamakin wanda yazo nemana ne. ***************************************** Duk yadda na kawo zanji kunyar zuwa makaranta wayewar garin ranar sai naji ba haka bane musamman da Mama ke nuna mun kada na bari wani abu ya kaini ƙasa ko menene shi,idan nace zanji kunyar kallon mutane bisa abun da ya faru to tabbas mutane sune zasu na bani ra'ayoyin da zan rayu da su dan haka na shirya tsaf cikin shirina na makaranta,da fari ina tunanin na saka niƙab saboda ciwan dake fuskata amma sai rashin amfanin yin hakan ya fi amfaninsa yawa. A inda muka saba zama ni da Anisa muka zauna,kallona take yi tunani ko bazan mata sallama ba ,ban iya gaba ba bazan fara da Anisa ba,ina dai cikin ɓacin rai kuma na faɗa mata cikina,duk kus kus ɗin da ake a aji ina ji na zaɓi dana share ,Sallama nayi mata kana nace"ya kuka je gida jiya?". Kamar dama jira take na kawo wani abun da zai haɗamu magana ta washe haƙora "lafiya lau wallahi ke Kinga yadda Malam ya ci mutuncin Zainab,wallahi duk zatona babu mutumin kirki gidansu ganin yadda yayanta Yunusa ya ɗinga ma Yaya dariya ranar da tayi mana Aljanu,wannan da ke tare da Baban nata ai shine yunusan". "Allah sarki Allah ya shiryesu"na faɗa ina mai taƙaita maganar gudun kada ta shiga inda ban Kaita ba duk dan mu shirya,.Wani course mate ɗinmu ne da ya fi kowa zarra yazo har inda nake,kan desk ɗin mu ya hau yana mai cewa"Zunairah baby ,kin san fa na dade ina sanki but idan za muyi soyayya touchy touchy love za muyi". Dariya abokansa suka saka daga baya suna masu faɗin" Enoch & Zunairah,hope dai baza ta baka ciki ba first encounter dan ga dukkan alamu itace zata ma namiji ciki maimakon ya yi mata". Marin da Anisa ta ɗaukesa dashi ya saka na ɗago kai,ya shigesa sosai babu ƙarya dan yadda ya tashi kamar zai shige jikinta abin ya bani tsoro,hannu ta saka ta turasa baya inda yake cewa"i will join you "yana mai dukan kirji itama tana mayar masa tana cewa idan ya fasa. Ganin abin zai zama faɗa ya saka class rep ɗin mu ya shiga yace zaije ya kira securities idan baza su bari ba,nuna Anisa yake da yatsa yana cewa"RUN if you see me outside just run". "Abeg Enoch if you don't kill me outside no be your mama and papa blood you be". Kamo hannunta nayi na zaunar ina mai cewa"ya isa haka Anisa bai Worthing kulashi ba". "Ki bari na nuna mishi shi ƙaramin shege ne,yan iska da jira suke wani abu ya sameka su mayar dashi abin wasa ,ya yi messing da wrong person dan Wallahi akan ki zan faɗa da kowa,we might have our differences amma its me and you against the world,I'm sorry akan abin da nayi Miki earlier ki yafe mun banyi dan na ɓata Miki ba kinji?".. Hmmm Zunairah wawuya a alaƙa tuni na narke a zuciyata naji babu kamar Anisa,harshe da haƙori ma sukan saɓa dan mene ni da Anisa baza mu saɓa ba kuma mu dawo mu shirya? Murmishi nayi nace "na yafe Miki ya wuce and Nima ki yi haƙuri a kan yadda nayi reacting ban kyauta ba ban ji daɗi bane kawai ". A haka muka shirya kamar ba abin da ya shiga tsakaninmu ,da muka je siyan gurasa ne take ce mun"Kinga Farouk ɗin nan abokin Khalifa mutumin banza ne,and naga taketakensa kamar so yake ya shiga rayuwarki,kin san Allah ba mutumin kirki bane kada ki fara bashi fuska". "Aikuwa duk abin da ya ƙwaso ya zo gurin da bai kamata yazo ba,ki ƙwantar da hankalinki,ni ai na daɗe da rufe babin soyayya kuma sai dai ƙilan nan gaba,amma ni kam yanzu na bawa namiji lokacin da zai ɓata mun aikuwa sai dai idan ba niba". Ni baki ɗaya ma Farouk baya cikin irin zaɓina,bai ma kwanta mun a zuciya ba balle mu fara maganar soyayya,haka tayi ta nuna mun illolin Farouk wanda suka ƙara taoratani dashi, babban abin mamakin shine yadda Khalifa ke tare dashi tunda dai tace budurwa da yake tare da ita har ciki ta zubar ,"Allah ya shirya mana mazan Nan kawai amma basa da kama "na faɗa wanda hakan ya kawo karshen maganar Farouk a ranar. Driver yazo ɗaukarta nace ba zan bi su ba dan haka itama tace baza ta shigaba muje mu hau ɗan sahu,a bakin inda suke tsayawa muka tsaya muna neman na hanyar mun. "Malama Zunairah tafiya ne? ". A tare muka juya muka kalli mai maganar ni da Anisa da mamakin jin yadda aka kira sunana randomly. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟19:Karma comes *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* "Khubaybu ɗan Adaidaita?"na faɗa ina san gasgata shi ɗinne dan encounter ɗin mu zan iya cewa ban masa kallan ƙurilla ba amma a ƙwana ɗaya ba zan mantashi ba. Dariya Anisa ta saka jin sunan da na kira kafin tace"ke kuma ina ki ka san wannan? ". Ban bata amsa ba na fuskance sa ina mai saka hannuna a Jaka nace"yi haƙuri ashe fa kana bina kuɗi,baka ma faɗa mun nawa bane,kaga har gida ka kaini kuma ni kaɗai". Murmishi yayi yace"muje yau sai na aje ku in yaso sai muyi lissafi ". Hannun Anisa da tambaya ya cika mata kai na ja ina ma cewa"to,Besty mu je".bina tayi amma na san tana san jin ƙarin bayani,bai wani ja mu da hira mai tsayi ba wanda hakan ya burgeni,bana san Mutum mai shegen surutu,da muka kusa shiga unguwarmu ne yake tambaya itama Anisa nan take? "Ka sauke mu duka gidan su Zunairah "ta bashi amsa kafin na bashi tana mai yin murmushi tana kallansa,wanda ko ba'a faɗa mun ba na san dariyar raini take mishi,na san halin ƙawata sarai ta wannan fannin,sai da ya kaimu ƙofar gidanmu muka sauka,sai a yau na mishi kallon tsanake ta yadda duk ina na ganshi zan gane sa,"mungode mai Napep yanzu duka nawane kuɗinka?". Murmishi yayi ya saka hannunsa cikin gashin dake kansa wanda aka yiwa dada yace"ni dai Aunty Zunairah ki bar kuɗin nan na ranar na yafe amma na yau ku bada ɗari biyu ke ɗari ita ɗari Allah ya saka musu albarka". Wata irin dariya Anisa ta saka tana mai sake maimaita kalmar Aunty Zunairah kana ta ƙara da faɗin"kai yanzu goɗai goɗai da kai kake kiranta Aunty?and wa zaka kalla anan kace mana daga Buk zuwa hotoro Naira ɗari?da janin wa za kayi kuɗi da shi,abeggi brother shaggi karɓi kuɗinka"dubu ɗaya ta ciro a jaka ta miƙa mishi,bai karɓa ba ya zuba mata ido,sai naji babu daɗin abin da tayi mishi ɗin,kuɗin na karɓa na turata nace "shiga gida dan Allah". "Gwara na shiga dan ina dariyar nan raina ɓaci yake".shiga gidan tayi tanata mita. Dawowa nayi na tsaya nace"dan Allah Khubayb kayi haƙuri ba ɗabiarta bace ban san mene yake damunta ba,kayi haƙuri". Maimakon ya yi addressing abin da nake faɗa sai cewa ya yi"sunana a bakin ki daɗin faɗa,Khubayb,last da naji wanda ya Kirani da sunan dai dai har na manta ". "Well idan zan tuna kaima da bakinka da ka tashi faɗan sunanka ce mun kayi Khubaybu dan adaidaita ".Dariya nayi kaɗan wanda shima ita ɗin ya yi yana mai kallona ,kuɗin da Anisa ta ɗauko na miƙa mishi da nayi realizing hira nake da ɗan adaidaita sahu kamar wata sakara,mutum da ba saninsa nayi ba,idan ma kidnapper ne ko serial killer Allah kaɗai ya sani. Kamar ya san mene a zuciyata na tsinkayi muryarsa yana cewa"ni ba serial killer bane ko wani mugu,ni ɗan garin Kaduna ne cirani ya kawoni Kano a bakin Buk kuma sai naga abin da ya tuna mun da yan biyu ta,i was like idan abun nan da Kowaisah yake faruwa fa?da bazan tsaya ba sai inda karfina ya ƙare shi yasa na bada same Energy". "I was like?"na faɗa da mamakin jin turanci a bakinsa. "Hajaju Turanci Yarene kawai kowa zai iya ,mun ɗan tsinta but yadda ki ke curious labarin sai mun sake haɗuwa,zan anfani da wannan mu sake haɗuwa sai na cigaba da baki labari kada na baki tsoro da surutu, although Nima yau na fara gaban Aunty Zunairah ". Naira ɗarin da ya ce zai ɗauka ya ɗauka ita ɗari ni ɗari ya bani chanji kafin ya ce mun sai gobe,yaja ɗan sahunsa. Tsaye kawai nayi ina bin adaidaitan da kallo har ya bar layin ,bai bari na sake bashi haƙuri kan Anisa ba,i can't believe wai ni Zunairah ce yau na tsaya hira da ɗan Adaidaita sahu,abun da ban taɓa ba,na san da Mama zata fito ta ganni da sai tace mun babu kamun kai Indai Mamace. "Idan kin gama sakin baki kamar wata doluwa kina kallon ɗan iskan mai keken da ya mirza kansa da Sosan katifa sai ki shigo gidan Mama na biɗarki". "Kece doluwa kin ji haushi da yin laɓe"na faɗa ina mai bin bayanta,ashe bata shige ba laɓewa tayi. "Ki dai cigaba da bawa strangers dama,wama ya sani ko ɗan dumbule ne yadda ki ke fama da sirantar nan da kayan Nono ba wuya zai dumbular Miki ɗaya ya sace". "Ah Anisaaaa!!". "Aw baki yadda yanzu ana satar Nono a jikin mutum ba ko? shikenan ki cigaba da bawa Kowa fuska future Mama one breast". "Allah ya shiryeku,wato har da masu satar Nono yanzu duniya,kai ni ƴasu"Mama ta faɗa tana zaune kan doguwar kujera. "Wallahi Mama yanzu akwai su,wai idan suka saka maka hannu guda a ƙirjinka shikenan sai wani bayanin ake shi yasa idan kaga baƙon fuska ka fara Cross da hannunka kana ɓoyewa".Ta faɗa tana zama tana mai karawa da gaishe da Mama tana mai tambayar jikin Baba "To Allah ya shiryesu,lafiya lau,sannunku da dawowa Sai a nemi abinci kuma,Babanku kuma yana bacci jiki da sauƙi tunda har an ware ɗaurin sai abin da baza a rasa ba ". "Ina wuni Aunty Anisa?Mana mun wuce"Hauwa'u ta gaishe da Anisa a daƙille ta wuce ranta a ɓace,bin Hauwa'u tayi da kallo kafin ta juyo ta kalleni tana mai ɗaga mun gira guda ɗaya"besty nayi ma Hauwa'u wani abu da ban sani ba?". "Ke Hauwa'u zo nan "Mama ta ƙwala mata kira amma ta riga ta fita a gidan,ni na san tun abin yaya Halil ne da ta tsinkayi Anisa na faɗa mun na rabu dashi,shikenan Hauwa'u ta saka ta a rai,ko maganarta ake bata saka baki amma a baya har ƙebewa suke suna hira,amma a zahiri sai cewa Anisa nayi"kin san halin Hauwa'u ta iyu islamiyya ne bata san Zuwa". "Aikam dai Hauwa'u ai bana jin idan tayi sauka zata yadda ta koma hadda, Zunairah ga chan dambu a kitchen ki zuba muku yau ni da Muna muka yi". "Mama damun shinkafa?"Anisa ta tambaya?. "Eh na shinkafa yaji zogale kam na san za kuji daɗinsa ". Ina tashi itama ta bini kitchen,mai isar mu na saka mana kafin muka wuce ɗakin mu,muna cin abincin ne ta ce"amma wai na tambayeki ina ki ka samu wancan guy ɗin,ƙazamin mai Adaidaita sahu ɗin chan ". "Anisa stop being mean Ina ki ka ga ƙazanta a jikinsa,kina da wulaƙanci abin da ki ka mishi kuma bai kamataba,ranar da matar Yayanki ta zo Makaranta ai shi ya kawoni gida". Tsayawa tayi daga cin abincin da take"aw Allah wato yayane ke ba yayanki bane kenan". "Kema ai kin san ba abin da nake nufi ba kenan kada ki yi mun wata fassara". "Yayi amma wannan gayen mai Adaidaita ɗinnan rashin kunya fa sai ta saka yace yana sanki,kin san su maza akwai kai kansu inda Ubangiji bai kaisu ba,yadda yake Miki wannan sumi sumi ɗin at the end of the day sai ya fito ya ce yana sanki,har na hango reaction ɗinki,wayaga kin Aure mai Napep". Ganin irin dariya da take ya sakani janye plate ɗin ina cewa"dan Allah kada ki saka mana yawu a abinci menene kuma aibu idan na Auri mai Napep,baki san sun iya kula da gidan su ba,look ni fa ba ina neman miji mai kuɗi bane ina neman mijin da zai soni ya mutuntani ya mutunta dangina,idan babu wannan duk wani kyalli kyalli shirmene". Jan plate ɗin tayi"naji matar Khubaybu mai Adaidaita, naga alamun kin kamu Kinga idan zaki fita sai yana saki a baya". banza nayi mata na cigaba da cin abincina,dan bata amsa ma bata da amfani Indai Anisa ce a har muka gama,wata Hirar muka ɗauko aka aje ta Khubaybu duk yadda take san ayi dan naga alama bazata daina zaginsa tana kushe masa sana'a ba. Sai da muka yi bacci muka tashi kafin bayan munyi Sallah ta wuce,da Hauwa'u ta dawo mun kwanta nace mata "Hauwa'u mene ya saka ki ke ma Anisa irin abin a ki ke mata?". "Auntyna nifa tun abin da ta faɗa Miki kan Yaya Halil sai nake jin haushinta,har yanzu kuma sai nake jin kamar ita tayi silar rabuwar ku,nifa Aunty tsakani da Allah ba zan iya ƙawancen da kuke ke da Aunty Anisa ba,kin bata yadda da yawa,baki tunanin komai idan zakiyi mata wani abun,kullum kina nuna mata kina yinta,I'm just scared ita ɗin red flag ce because friendship ɗinku kamar ke kaɗai ki ke yi Allah yasa nan gaba kada ta yaudareki". "Da zata yaudareni Hauwa'u da tuni tayi,kada ki manta mun daɗe tare,maganar Yaya Halil kuma ina so ki cire wannan a zuciyarki,dama ni dashi ba rabon juna bane, tsakanina da Anisa kuma insha Allahu sai Alheri,i might be overbearing amma ai ba wai bana da wayau bane,muna faɗa mu shirya wanda haka alaƙar gaskiya ta gada a ɓata a shirya". Jin amsata tayi kafin tace"Allah ya saka to hasashe kawai nake yi,dama ina ta san faɗa Miki,kin san yanzu Midnight Authoress ashe tana da hardcopy na littattafanta?ɗazu mun shiga wani bookshop ni da ƙwayena naga littafan ta". Wani abu naji a ƙirjina wanda ya yi mun kama da hassada,ɗan adam kam baya rabo da ita once in a while sai dai ya fi karfinta,saurin kawar da jin dama nice nayi kafin nace"Allah ya ƙara mata ɗaukaka muma Muna fatan Allah ya kaimu inda suke ". "Amin Auntyna ai ke kam sai kin fita ma insha Allahu,rubutu ma wallahi kin fita iyawa kawai dai ta fiki Fans ne da daɗewa tana rubutu amma kema kina hanya insha Allahu". Naji daɗin addu'anta cike da farin ciki na amsa da Allah yasa,ita ta rigani yin Bacci ni sai da na tsaya nayi ɗan rubutun da ba zan rasa ba. ******************************************* *𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓* Baki ɗaya tunda al'amari Zainab da Zunairah ya faru sai yake jin baki ɗaya baya da nutsuwa,ya rasa mene yake damun zainab,watarana tayi ƙalau watarana kuma ta fi tsohon Babur fitina,a wannan gejin ya yarda da cewa Auren garaje ba shine ba,Anisa ta nuna mishi video ɗin Zunairah da Adam suna kiss ranar da ya haɗa mata birthday,ya kasa yadda wai duk wannan lokacin Zunairah fuska biyu take nuna mishi,abu ɗaya ya yi la'akari dashi wanda shine taje gidansa wani abu yana faruwa tsakanin su,a lokacin ya ɗau zafin da bai auna komai ba sai kawai tunanin ganin Adam da yayi a gidansu da kuma yadda ta ruɗe da hannunta dake cikin nashi. Mene ya saka waɗannan abubuwan kawai ya duba?, baiyyi tunanin maybe one-time mistake ne da bai kamata ace ya yanke mata hukunci ya rabu da ita ba sai a yanzu da yake ganin abune na yafewa tunda ba turmi da taɓarya ya gansu ba,but still kiss fa abin ya kasa bari masa ido da zuciya da tunani,Zunairah ɗinsa da yake so kamar rai da ɗan uwansa Adam,duk da ba wani shiri suke ba amma ai ɗan uwansa ne. Abu na kamata da yake ganin dama shi ya yi shine fuskantarta ,kamata ya yi ya mata magana amma ya gaza ya yanke hukunci ya Auri Zainab da a yanzu yake dana sani. Bayan gajiya daga gurin aiki da yayi ya kamata ace an tarbesa tun a falo amma abin baƙin cikin sai ganin falon ya yi kamar anyi sukuwa, tsaki ya yi ya shiga cikin ɗaki bai damu da nemanta ba,kwance ya tarar da ita kan gado tayi baje baje a sigar kwanciyar rubda ciki tana ta jan minshari,tun safe da ya fita ya barta haka nan take ko wanka batayi ba indai ba wai tayi ta mayar da kayan baccin da ta cire jiya ba,tsaki ya yi ya shiga bayi,yana shiga ya dawo a sittin sakamakon bayan gidanta da ya gani cikin seater batayi flushing ba,haba ya ji wari amma duk tunaninsa warin bayin da bata san wankewa ne,duk masifar da zaiyyi ta ƙi aminta da zaman ɗakinta sai nashi,a cewar ta idan ya keɓe karuwai yake kira. Hannu ya ɗaga ya samu mazaunen da ta ɗaga sama ya ɗaɗa mata duka da ƙarfinsa,a zabure ta tashi tana ƙokarin haye fuskar gado tana faɗin"wane ?su wane?". "Shine your eyes sai kiga wane ƙazama kawai,ki tashi kije ko kora kashin chan da ki ka yi wallahi ko na Miki rashin mutunci,idan ba ma ɗabi'ar mahaukata ba ina ka taɓa barin kashi a masai har ka zauna a ɗakin ka iya bacci?". Tsaki tayi tace"dama shine ya saka ka tasheni daga bacci?kada ka sake kirana ƙazama ai na aje ne idan na tashi na kora bacci ne yaci ƙarfina,kai ka rantse da Allah baka taɓa ajiyar kashi ba?". Wani maƙoƙon bakin ciki ya tokare mishi zuciya, tunanin wane irin hauka zai mata ya fara,belt ɗinsa dake gefen gado ya nufa ya naɗeta bisa hannu ya ce"dan Allah Zainab kada ki tashi ki kora ƙazantar chan". Tashi tayi tana ɗaga mishi hannu tana cewa"wallahi kada ka fara,naji zan kora shima dan kawai ni nayi,amma wallahi idan ka bari wannan abar ta taɓani zamu samu gagarumar matsala da kai". Banɗakin ta shiga ta danna abun flushing ɗin tana mai doɗe hanci da baki kamar wani ya yi mata,fita tayi a ɗakin tana sosa kai tana cewa"ba dan halinka ba wallahi". Scanning dakin yayi da ido,babu abin da yake face wari ga ko ina kacakaca. "Ni kam na shiga uku,mata ga iskanci ga rashin tarbiyya ga ƙazanta da wanne zanji ni Halilu?". Ƙofar ya nufa ya kulle kafin ya rage kayan jikinsa ya fara gyara ɗakin,zanin gadon ya fara cirewa kafin ya sake wani ya gyara ɗakin ,bayan ya gama ya shiga bathroom,wankewa yayi kamar baya san jikinsa yana lissafa ta gama shiga mishi daki taje chan nata tayi duk wata ƙazanta da za tayi amma banda ɗakinsa,buƙata wannan ba dan ta zamar mishi dole ba babu abin da zai saka ya kusanci Zainab,ya yi ta tsaki kenan idan ya gama ita kuwa ko a jikinta,gashi wani lokacin sai ya biyata kudi . Shin a duniya ma kam ina zai fara kai ƙarar Zainab,ta zamar mishi fitinar da bai san ta inda zai shawo kanta ba. Bayan ya gama dakin ya ɗauki sassanyan ƙamshin room freshener ,cikinsa da ya fara kukan yunwa ya sashi ya fita domin newa kansa abinci, sai da ya tabbata ya saka key dan yanzu ɗakinsa a nan ne kawai zai samu ƙamshin Rahma. Baje ya tarar da ita a falo tana cin gugguru tana kallo,riƙe ƙugunsa ya yi ya ce"wai ni kam Zainab mene hakan?ki kalli fa falon nan dan Allah.". "Aw aw kana so kace mun kawai aiki nazo yi sai na fahimta ,to wallahi bari kaji ni ba boyi boyi bace ba zan Shara ba idan ban niyya ba,duk lokacin da naji ina san yi babu mai jina amma yau kuwa ƙazanta day ce shi yasa ko wanka banyi ba,kasa da hastag ƙazanta day,ka Barni na sarara idan na isheka da wari ka rufe hancinka ni da wanka sai dare " "Aw ashe ma za kiyi ai ni duk tunanina baki ɗaya baza kiyi ba,to ina san ki sani ɗaki mun raba ki koma naki ba zai iyu ki mayar mun ɗaki kamar na yan iska ba,Kinga falon nan haka wallahi ko shi ba zan ɗauka ba ki san yadda za kiyi na dai faɗa Miki". Kitchen ya nufa yana ji tana cewa wallahi bai isa ba,shi dai bai kula ta ba ya shiga kai tsaye,window ɗin kitchen ɗin ya gani a buɗe kudaje nata waƙe bisa ƙwanikan da tayi amfani dashi,daga gani ta shiga tsaminsu ya isheta ta buɗe window ɗin,kai wannan mata akwai annakiyar ƙazama. Fita yayi ya tarar da ita tana tsince falon, tsaki yayi yace idan kin gama Wallahi ki gyara kitchen ɗin chan aikin banza kawai,ta saka karfi da yaji ya koyi tsaki kamar wani tsaka,kullum wannan matar tashi da sabon salon dabi'u take,kamar wasa ta fara ƙazanta gashi yanzu tana san zama mata dabi'a ko ma yace ta zama. Car key ya ɗauko,ya juya baya ta biyosa kamar zata dakesa,yana juyowa tayi saurin duƙawa kamar zata ɗauki abu,kaɗa kai yayi yace "Allah ya mun tsari da shaiɗancinki Zainab"da haka ya fita yana jin tana ta dariya kamar ta zare,at this point ya fara tunanin ta zare ɗin ba kaɗan ba shine shima take san ya haukace bayan Allah ya fita. 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎 Na 𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay) E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟20: *𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏* Tafiya nake kamar wadda laka ta fashewa a ciki,yau da kasala na tashi , na san idan na zauna a gidan babu abin da zanyi,ina ƙoƙarin tsallaka titin Adaidaita sahu ya tsaya,daɗi kasheni ,da saurina na ƙarasa nace"BUK". Ganin Adaidaita sahun Khubayb ce sai nayi mamaki, Khubayb?na faɗa da mamaki dan ban taɓa tunanin nan ɗin hanyarsa bace. "Barka da safiya Hajiya Zunairah muje ko?". "Idan har ba za ka ɗauka passenger ba zan hau ba". Dariya yayi wadda ta bayyana haƙoran da ban ƙasa a gwiwa ba wajen hango teeth gap ɗinsa "kada ki damu ai aiki na fito Allah zan ɗauki passenger ".Murmishi nayi kafin na hau Adaidaita ina mai fadi mishi ina kwana. "Kin tashi lafiya ya kwanan Mutanen gidan?". "Álhamdulilah ". "Masha Allah"da haka ya tashi Adaidaita sahun muka ɗauki hanya,muna tafiyane yake ce mun ,"mai zai hana ki bani number ɗinki idan nazo unguwarku da safe sai na ɗaukeki mu wuce makarantar,Kinga kin huta kuma nima gashi daga nan nake lodin passangers,in case kinyi Mamaki kince wannan mene ya zai na kawo shi nan da safe ko kuma ki yi gudun zan latti sha kuruminki a nan tsamiyar boka na samu gurin zama kwanan nan". Ban ce komai ba illa murmishi da nayi na ƙarbi wayarsa na rubuta mishi numberta,godiya ya yi mun ya kira layina number ɗinsa ta shigo nayi saving da Khubayb. Bai sake mun wata dogowar hirar ba har muka cika Adaidaita sahun da yan makarantarmu ,da na haɗu da Anisa haka nan na ganta kamar wata mara lafiya baki ɗaya tayi pale da ita kamar wadda bata da jini,cike da damuwa nace da ita"Anisa baki da lafiya ne?". Cikinta da ta riƙe take nuna mun tana cije baki wanda ba sai an faɗa maka tana cikin ciwo ba,bata da lafiya idan ba abun Anisa ba mene ya kawo ta makaranta? Kama mata kafaɗa nayi ina mata sannu duk da ban san takamaimai mene ba amma ganin cikin da take nunawa ya saka na barshi a kan cikinta ke ciwo,duk yadda ta so mu gama lecture abin sai ya ci tura,excuse muka ɗauka muka bar hall ɗin ,rasa abin yi nayi musamman ganin ta rike gefen cikinta ta kasa cigaba da tafiya tana kuka,Nima kukan nake dan kaina ya kulle na rasa tunanin mene zanyi, Khubayb ne ya faɗo mun,babu ɓata lokaci na kirasa ,lokaci mara yawa ya ɗaukesa ya zo,tare muka taimaka aka sakata cikin Napep ɗin a wannan point ɗin she's unconscious,pass ya basu a bakin gate kafin muka ɗauki hanya,kuka kawai nake ina kiran sunanta akai akai cike da tsantsan tashin hankali,tunda nake da ita ban taɓa ganinta cikin yanayi irin wannan ba,Yaya Halil na kira na sanar mishi,nan ne yake cewa mu wuce da ita asibitin da suke zuwa na Garkuwa zasu same mu chan,a haka muka ɗauki hanya dan zuwa Asibitin Garkuwa,ban mamakin ganin Yaya Halil a chan ba,kai tsaye aka shiga da ita emergency domin bata taimakon gaggawa. "Mene ya faru?".yaya Halil ya tambayeni. "Dama na shigo makaranta naganta wani iri na tambayeta shine take ce mun cikinta,to muna Lectures abun sai yaci tura muka ɗauki excuse to muna fitowa kuma shine sai hakan". Baice komai ba amma damuwace fal ransa,zuwan Enen ce take faɗin "Halil kidney ɗin ne ko?". "Wallahi Enen ina gudun abin da muke tsoro shine zai faru,shi yasa nace ayi aikin nan tuntuni ta tsaya gardama ke da Daddy ku ka biyeta". Ni dai da ba fahimtar inda zancen nasu ya dosa ba addu'ata guda ɗayace Allah ya bata lafiya ya kawo mata wannan al'amarin da sauƙi,bayan wasu lokuta likita ya fito yake mai shaida musu sun samo kanta amma tana bacci,neman yaya Halil ya yi da yana san magana dashi,jin hakan ya saka Enen shiga ɗakin. Bayan wasu lokuta ni duk lokacin ina waje gudun kada na shiga tunda babu wanda ya mun tayi,Yaya Halil ne ya dosuni,da damuwa na tashi daga zaunen da nake ,da ya ƙaraso gurina ne nake tambayarsa jikin nata shine yake faɗa mun"kidney failure ne,tana fama da ESKD,end stage kidney disease dalilin kidney cancer wanda dole sai an mata transplant,last time na faɗa musu doctors ɗin sunce tana buƙatar wani amma yarinyar nan ta kafe kan a ɗorata a kan maganai". Rasa abin faɗa nayi sai hawaye dake bin kuncina ɗaya Bayan ɗaya, bakina na karkarwa nace"amma Yaya Halil will she survive it?". "Abun da muke fata kenan,insha Allahu she will survive it,cikin ni Ko daddy ko Enen I'm sure duk wanda tissue ɗinsu ya zama compatible zamu bata, she's going to be okay"ya bani amsa kamar bai yadda da kansa ba. "Zamu iya shiga ciki"ya sake faɗa. "Taje ina munafukan Allah?" Muryar Zainab Pagal ta Mana sallama, sunan da Hauwa'u ke kiranta dashi kenan,da zafinta ta ƙaraso tana mai cewa"Hala tayi ciki kun zo ku zubar?". "Ya subhanallah Menene hakan wai Zainab mene yake damunki da a rayuwa baki da aiki sai jawa mutane Bala'i? tukunna ma da kika fito wa ki ka tambaya?". "Aw sai na tambaya?kai ka ɗako daɗironka kuka zo nan ka tambayeni?'A'a dan haka ka rufe mun baki ba wannan nake san ji ba,uban mene ya kawoku asibiti tare?ai tunda ka taho nake binka a baya ina mamakin abin da kazo yi ashe ga amsata". Wani irin kaɗa jiki take,ni dai babu abin da nake sai kallon ikon Allah,ace mace kamar yar daba,bata da aiki sai faɗa, Wannan idan aka ce maka tayi shure shure na masifa cikin mamanta ba zaka Musa ba,juyawa nayi na shiga ɗakin da aka mayar da Anisa na barsu su ƙare lafiya,ina ji tana ihun na dawo ko na kasa gane kaina,ban kula ta ba sanin babu amfani biye wadda bata tsoran iyayenta ko kaɗan,da ace tana tsoronsu babu abin da zai saka ta sake kulani,ina ƙoƙarin shiga ɗakin naji an turani cike da faɗa yaya Halil ya ce"wai mane haka Zainab baki ji ko?da ciwon Anisa za muji ko da tijararki?". Sai a wannan lokacin ta kula da Anisa dake kwance baki ɗaya ta sauya kama lokaci guda,mayar da kallonta tayi kan Enen wadda babu abin da take sai aikin hararar Zainab,cike da borin kunya tace"Enen ashe Anisa ce rai hannun Allah ai ban sani ba,ya jikin nata,na zata wallahi Halil tare yake da yar iskar nan duk da bana lamuncin hirar da na tarar sunayi". "Álhamdulilah Zainab da ki ka san Anisa ranta a hannun Allah yake ba a naki ba,nayi imani da Allah da ace ranta a hannunki yake da tuni kuma wannan haukan ki ciresa,ace ke a rayuwa baki da aiki sai bala'i,kada fa ki saka kiyi abin da zai dameki dan Allah na gaji da Lamuni". Haɗe rai tayi wanda ya nuna Maganar Enen tayi mata Zafi sai wani cije baki take, kai wannan da ace namiji ce ba ƙaramun shiryayye za ayi ba,wallahi duk tunanina ba zata kuma cewa wani abu ba ganin Enen ta mata kashedi,wai sai cewa tayi "mumze a huce amma gaskiya ni bana san kina mun magana a haka,babu wanda na taɓa idan nayi faɗa akan abuna a ɗaga mun ƙafa kada a danne mun hakkina". "Aw Halil ɗinne abun ki?"Enen ta tambayeta baki buɗe,sake tsuke baki Zainab tayi kamar ka saka almakashi ka datse ɗan banza. "To Enen mene ki ke so na faɗa". Jin furucin da tayi ya saka Yaya Halil da Yake binta da kallon Mamakin kama hannunta ,sai da yaje bakin ƙofar ya ɗaɗa mata duka a baya kafin ya watsata waje ya saka key,duka ƙofar ta fara tana yan ihunta kafin lokaci ɗaya kuma muka ji shiru. Tsaki ya yi ya ce"masu tsaron asibitin sunyi gaba da ita, wallahi Zainab sai da haka,idan tana wani abun kamar bata da hankali". "Anya Halil yarinyar nan bata ƙwaya kuwa?"Enen ta faɗa cike da alhini. "Babu wata ƙwaya baya ga iskanci wallahi,kamar a kanta aka saukar da dukkan wani iskancin duniya kullum kuma abun nata sake gaba yake". "A dai bincika dan wannan yarinyar ban yarda babu sharrin ƙwaya ba, kana kallon cikin Idanunta kamar an tsaga rashin kunya?gaskiya da sakel ace duk duniya Zainab tayi maka matsayin mata?". Ganin za su wuce suyi maganar da bai dace gabana ba ya saka na sauya zacen nace"yanzu Enen yaushe suka ce zata farfaɗo". "Ƴata yi haƙuri ina nan ina mita ga Anisa da likita yace kada a cika ta da hayaniya, ya dai ce zata farfaɗo bai faɗi lokaci ba,Nagode sosai da ki kayi saurin kawota asibiti Allah ya yi Miki albarka ". "Amin Enen ai yima kaine,bari dai na wuce in yaso ko da su Mama sai mu dawo tunda ban faɗa musu ina nan ba ". "Ai kada ki damu,ki huta idan ta tashi na faɗa mata kin wuce amma kada kice zaki damu kanki wai ki dawo anjima,ai nayi admitting ɗin mu har ayi mata aiki idan yaso gobe idan da hali sai ku zo ɗin ,suma ai ba a tasosu ba zato ba". Ba dan na so ba dai na ɗauki maganar Enen,Yaya Halil ya yi tayin kaini gida,ban ƙasa a gwiwa ba na ƙiya sanin mene sakamakon binsa a motarsa,ƙila dai ƙarshe so yake matarsa ta ƙoneni kowa ya huta,duk yadda naso aka kada ya mayar dani gida haka Enen ta saka baki dole muka jero a tare muka fito. "Baki da wata tambaya da za kiyi mun?"muryarsa ta katsen saƙesaƙe zuci. "Yaya Halil ya kamata nayi maka wata tambayar ne ban sani ba?I mean mene ya kamata na sani?". Ɗan sosa kansa ya yi da yatsa ɗaya kafin yace"akan Zainab mana,baza ki tambayeni komai ba?". "Yaya Halil mene ya saka zan tambayeka abin da ya shafi gidanka?ko wane gida da nasu kai shine na gidan ka ina maka fatan Allah ya sassaita maka,matarka ce kana santa tana sanka atleast zaka iya nuna mata daidai,ni Alfarmar Abu ɗayane dama shine ka faɗa mata babu abin da ya taɓa shiga tsakanina da kai dan Allah ta daina kawo mun hari". Gani nayi ya tsaya daga tafiyar da yake,juyawa nayi na kallesa,ganin kamar maganar ta masa ciwo a yanayin fuskantarsa ya saka na cigaba da tafiyata,ganin da gaske bana da lokacinsa ya sa ya tako sai da yazo inda nake yace"mai yasa ki ke san denying abun da muke dashi a baya?". "Bakaji kace a baya ba,kai kana ma ɗaukarsa baya amma ni kam Yaya Halil na binne wannan,zaifi idan kaima ka binne tunda dama ai abu ne da ka ƙi.". Kafin ya yi wata maganar na hangi Khubayb,wallahi baki ɗaya na manta tare muke dashi,yana tsaye jikin ɗan sahunsa yana kaɗa mukulli,kallon direction ɗin da nake kalla yayi kafin yace "wane wancan ɗin?". "Wanda ya kawo mu Asibitin all thanks to him ƙilan da Bamu san mene zai faru ba". Takawa nayi yana biye dani,sosai naji daɗin ganin Khubayb atleast ya sakar mun mara nayi fitsari,da muka isa gun Khubayb da damuwa yake tambaye lafiyar Anisa amma wai abin haushi Yaya Halil sai cewa yayi "maigida nawane kuɗinka?". Kamar nayi ta kifa mishi mari haka baki,wai maigida nawa ne kuɗinka,murmishin yaƙe nayi nace mishi"Yaya Halil ɗan uwan mu ne banyi zaton yana jirana". "Aw Sannu"shine Abin a ya iya faɗa,yan kallo muka bar gurin,muna fita cikin asibitin na sauke ajiyar zuciya,a nan ne nake faɗawa Khubayb jikin Anisa ,yaji tausayinta sosai inda yake mata addu'ar samun sassauci. Da naje gida nake faɗawa Mama ,ta shiga damuwa sosai inda take cewa goben insha Allahu za suje,da tunanin Anisa na ƙwana baki ɗaya na rasa mene yake mun daɗi,ban taɓa tunani Anisa bata da lafiya har haka ba,sai nake jin kamar ban zamar mata ƙawa ta kirki ba tunda har ban iya gane bata da lafiya har haka ba. ********** Da safe banje makaranta ba muka wuce tare da Mama,abinci mai kyau Mama ta mata muka wuce, har Daddy muka tarar a asibitin,sunji daɗin zuwan mu ,ina zuwa na rungume Anisa wadda tana ganina ta fashe da kuka tana faɗin"Kinga halin da na shiga ba". "Sai ki faɗa mata rigimar da ki ka tada mana "cewar Daddy. Kallona take cikin ido hawaye cike a Idanunta,hannuna da ta riƙe take rubbing a hankali Idanunta a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalleni. Sai na fara tsoron abin da zanji daga bakin nata,ɗagowa nayi na kalli su Enen wanda suma sun kasa haɗa ido dani,a tsorace nake tambayar su mene ya faru ina kuka,Mama ma tayani tambaya tayi ganin baki ɗaya kamar mun zama surukai dasu. "Anisa idan har kin ɗaukeni ƴar uwa wadda take ɗaukar damuwarka tata kiyi mun magana dan Allah , Wallahi gabana faɗuwa yake sosai tsoro nake ji".na faɗa ina sake riƙe hannunta. "Zaki iya bani abu idan na tambayeki?"ya tambaya a yanzu tana kallon cikin idona. Da sauri na kaɗa kaina ina mai cewa"indai bai saɓawa Shari'a ba bai kuma fi ƙarfina ba Anisa zan baki,abu koda shine ƙarshe a hannuna zan baki ni na haƙura,zan baki ko mene shi". "ZUNAIRAH INA SO BANI ƘODARKI ƊAYA". Hmmm to fa kunji dai abin da Anisa ta bukata daga Zunairah. Shin zata iya yiwa Anisa wannan sadaukarwar ko kuwa zata gagara? Ƙoda fa Hmm Nima dai ban san mene zai ce ba. Domin san cigaba da bin littafin Cin dunduniya kuyi maza kuyi payment ɗinku akan Naira 600 kacal domin cigaba da samunsa a telegram ko ku bibiyesa a Arewapen kan handle ɗina mai Suna Chuchujay. 8130229878 Opay Amina Jamil Adam