MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI) ƊANƊANO! ƊANƊANO!! ƊANƊANO!!! 1 DAMATURU Hadarine gagarumin gaske a garin namu na Damaturu, misalin ƙarfe huɗun yamma ne, amman yanayin duhun garin in ka kalla, zakayi tunanin asubane, ga wata sassanyar iska dake busawa tare da ƙananun yayyafin afumangai da aka soma yanzu. Jama'a sai gudu suke yi, yayin da da dama suka ƙara sauri. YAHANASU: Sauri_sauri gudu_gudu nake tafiya, bana fatan shan dukan ruwa. Hijabin dake jikina harya soma jiƙewa, dan yayyafin ya ƙaru sosai. Da sauri nasha kwanar lungun bayan layinmu, wanda inna ɓulla zai kaini, kusa da gida. A cikin lungun akwai wani tsohon kango, wanda ya kasance matattarar ƴan shaye_shaye. Zaman su a anguwar yana cima mazauna wannan anguwa tuwo a ƙwarya. Gashi matasan daga can wata anguwa suke zuwa. A guje nazo zan wuce wannan kangon. Banyi aune ba naji an fisgoni da matsiyacin ƙarfi. Ihun tsoro nayi, amman kafin in gama wangale bakina, naji an cusamun tsumma a bakin nawa. Jikina sai rawa yake yi kawai, ga kangon akwai duhu bana ganin mutanen dake ciki sosai. Ga wani irin mugun warin sigari dake tashi a wajan. Ban gama tantance fari da baƙiba, naji hannun wani matashi a jikina ya fisge hijabin dake jikina. Tare da daƙumo mun ƙirjina. Fitsarine ya soma zubowa a ƙasana, hawaye ya gama wanke mun fuskata. Kokawar ceton kaina na soma yi da wannan matashi, nice naushi, da yakushi, abun takaicin bakina a toshe yake. Ina cikin wannan dambarwa, naji an daddanne mun hannayena, cike da rashin imani wannan matashin yai mun mummunan fyaɗe. Zafin yagani da yayi ne, yasa na fisge hannayena a hannun matasan da suka daddanneni. Dutsen dake kusa da kaina na ɗauka da zafin nama, na rotsama wannan matashin a kai. Take kanshi ya fashe, jini ya wanke mun fuskata. "Ta kashe Tijjani, kai mu ware tun kafin asirinmu ya tonu" Cewar matasan samarin. A guje suka fice a cikin kangon. Ruwa ake zubawa kamar da bakin ƙwarya. Jikina sai kakkarwa yake yi, da ƙyar nasa hannu biyu na ture wannan tsinannen matashin wanda tunda na buga mishi dutse bai motsa ba,. Da sauri na rarumi Hijabina na mayar jikina, da ƙyar na miƙe tsaye, raɗaɗi da yaji_yaji nake ji a ƙasana, zuchiyata kuwa dan tsoro kamar zata faso ƙirjina ta fito. Cikin jan ƙafa na fice a kangon. Bana ko ganin hanya sosai, sabida ɗimuwa, ga ruwa da akeyi, harda ƙanƙara, sai dukana ruwannan yake yi. Amman bana jin dukan ruwan sam, damuwata shine, darajata da wani tsinanne ya keta mun, shikenan nasan na shiga ƙuncin rayuwa da tasku kenan. Da ƙyar nasa hannu na tura get ɗin gidanmu na shiga. Babban gidane mai cike da jama'a sosai. Sai jan ƙafata nake yi kawai, da ƙyar na iso ƙofar ɗakinmu. Suna zaune suna kallo na faɗo ɗakin a jiƙe sharab, jikina sai ɓari yakeyi, idanuwana kuwa kamar garwashin wuta. "Yahanasu lafiya kike kuwa da zaki tawo a cikin irin wannan ruwan mai ƙarfi?" Mahaifiyata ce ke magana, amman in buɗe baki nayi magana na kasa. Hannu na saka a ka, na shiga runtuma kuka mai tsuma zuchiya. Gabaki ɗaya na tashi hankalin ƴan uwana, duk sun miƙe tsaye suna kallona. " Ya Innana jini a ƙafar Yahanasu" Cewar Fanda. Wakil Yayana ya dubeni yace. "Yahanasu kiyi magana dan Allah kin tayar mana da hankali, meke faruwa, meya sameki?" Ya Innana mahaifiyarmu ta iso kusa dani, bata ce komai ba, taja hannuna zuwa uwar ɗakinta. Akan gadonta ta zaunar dani." "Yahanasu ki cire kayan jikinki tukunna, koma menene ya sameki ki kasance mai juriya mana, kin ɗaga mana hankali ainun" Tausayina dana mahaifiyata yaimun dirar mikiya a zuchiyata, jikina ya tsananta rawa ainun, idanuna suka shiga kakkafewa. A gaggauce Ya Innana ta zare mun hijabina, ganin rigata a kekkece da tayi , ya tashi hankalinta sosai. Da sauri hannu na rawa ta ɗaga mun zanina. Matsawa baya tayi da sauri hannunta dafe a ƙirjinta, tana zubar hawaye. Jikinta ya mace mus tama rasa me zata yi mun dan ta bani kulawa. Duk girmana sai Innana ta dena ganinshi. Tana hawaye ta cire mun kayan jikina tas, bargo ta yafa mun. Sai naga ta rungumeni tana kuka mai fitar da wani irin sauti, mai tada hankali. " Ya Innana, ku buɗe ƙofar dan Allah" Wakil ne yake magana. Maganar Wakil ita tasa Innana dakatawa da kukanta. Ban ɗakin ɗakinta ta shiga, bata jima ba ta fito, hannuna ta kama ta ɗagani tsaye. Rungumeta nayi ina kuka. Ni kaɗai da ire_iren waɗanda suka shiga ƙangin fyaɗene zasu gane irin raɗaɗi da azabar da nake ji." Mun kasa magana daga ni har Ya Innana, an rasa wanda zaice da wani kar yayi kuka. Har cikin bayan gidanta ta kaini, ta tara mun ruwa a bokiti, wanda take ta sawa a kittle. "Ki gargasa jikinki, saimu tafi asibiti. Amman garin yaya hakan ta faru dake?" Firgicewa taga nayi, har ina zabura. Ba shiri tace. "Shikenan ya'isa. Koma waye yai miki wannan aikin, wallahi kotu ita zata shiga tsakaninmu, wallahilƙudrat da zan ganshi saina kasheshi, sai dai aimun duk abinda za'ayi mun." Fita tayi fuu, ni kuwa sam na kasa yin wankan, asalima wani irin zazzaɓine yake shirin halakani Ya In na na" Na ambaci sunanta a wawware. Ba shiri ta dawo har tana tuntuɓe" Mutuwa zanyi Innana, zafi zai kasheni" Hannuna yana cikin nata, tana ɗigar hawaye tace. "Bazaki mutu ba." Wanka ta soma yi muni, tana daddannamun jikina da tawul, saida tazo yimun tsarkine, hankalinta ya kuma tashi. Gashi jikina ya saki kamar zan sume mata. Da ƙyar muka fito a bayan gidan, doguwar rigarta ta buɗe durowa ta zura mun. Ta samun suwaita da hular sanyi, fita tayi da sauri. Innana: Tana fitowa yaranta suka baibayeta da tambayoyi. "Wakil kayi maza kaje ka sanarma Ba Bakuri, za'a kaimu asibiti tunda Babanku baya gida, ko Bulama ƙarami sai ya kaimu" Kafin yace wani abu sai suka jiyo sallamar mahaifinsu Ba Modu a ƙofar ɗakin. Fanda ce ta amsa mishi a raunace. Shigowa yayi da fara'a kamar yadda yake a kullum, dan Ba Modu ma'abocin far'a ne sosai. Ganin iyalenshi a wani irin hali da rabon da ya gansu a halin, tun rasuwar Mahaifiyarsu Hajja Yahanasu wacce ta kasance kaka ga yaran gidan. Innana ya kalla hawayenta bai tsaya ba, daga kallonta kasan cewar tayi kuka ta ƙoshi, ga tashin hankali sosai a fuskata. "Innana Lafiya kuwa ki ke zubar da hawayenki a gaban yara, meke faruwa?" Cikin muryar kuka tace. "Ba Modu Yahanasu ce wani azzalumin yai mata fyaɗe, tana ɗakina a cikin mawuyacin hali, har firgita take yi" Tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka mai zafi" Tashin hankalin da iyalan ɗakinnan suka shiga ba'a magana. A tare suka shiga ɗakin dan ganin Yahanasu." Yahanasu: Ihu na ƙwalla mai ƙarfin gaske, ina yunƙurin tashi, dan ba ƙaramin firgitani shigowarsu tayi ba. Muna haɗa idanu da Wakil na sanƙare a wajen, numfashina ya ɗauke" Innana: "Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun. Allah ka tsinema wanda yaci mutuncin yarinyarnan ya keta mata haddinta. Ya Allah ita kuma ka rufa mata asirinta ka bata miji na gari" Kuka take yi mai zafi. Da sauri Ba Modu ya isa kan Yahanasu, shima hawayen yake fitarwa, taɓata yayi, tabbas babu sauran rai a jikinta. Da sauri ya fice a ɗakin ya nufi shashen babban wansu Bakura a firgice. Sallama ya shiga yi, da kiɗimammiyar murya, hawaye bai dena gudana a idanunshi ba har sanda matar wanshi Hajja Gana ta fito. Ganinshi a wannan mawuyacin yanayinne yasa ta koma da sauri ta kirawo wan nashi. A hanzarce ya fito, tabarau ɗinshi a hannu, ganin ɗan uwan nashi na kuka ya gigita mishi duniya ainun. "Modu menene ya saka zubar hawaye duk jarumtarka?" "BaKura, Yahanasu akaima mugun aika_aika fyaɗe akai mata. Tana ɗakin Uwarta a sume" Sun kiɗima sun razana ainun, Hajja Gana kuwa, fashewa tayi da kuka, abunka da mace, kuma uwa. A gaggauce suka nufi ɗakin Innana dukkansu. "Wakil maza ka samu Bulama a kawo mota ƙofar ɗakinnan, a ɗauki Yahanasu" Baice komai ba ya fita. Cikin ƙanƙanin lokaci gafatanin ƴan gidan suka san halin da ake ciki. Cirko cirko suka yi a tsakar gidan ko wacce fuskarta cike da alhini. Bulama da Wakil ne suka saka Yahanasu a mota, a gidan baya suka shinfiɗeta. Baguji kishiyar Innana ta shiga gidan bayan tana kuka, taima Yahanasu matashin kai da cinyarta. Bakura ya shiga gaban mota, shi da Bulama ƙarami. Da sauri motar ta fice. Modu ya dubi mata da yaran gidan yace. "Kuyi haƙuri, kuma ku sata a adda'a kawai. Innana ki shige muje Wakil ya kaimu asibitin. Fanda ke kuma ki shiga cikin gida. Jiki a mace suka wuce garejin mota. A bakin titi suka hango dandazon jama'a yara dama manya. Har babu hanyar wucewa a ƙafa ma, balle kuma ababen hawa. Bakura ne ya sauke glass ɗin motar ya yafito wani matashi da hannu, matashin ya iso wajan. "Lafiya meke faruwa ne haka" "Wallahi Baba wani ɗan shaye_shaye ne, aka ciro gawarshi a cikin kangon lungun gidan lado, shine jama'a suka taru" Jinjina kai Bakura yayi yace. "Allah ya kyauta. Taimaka yaro ka buɗa mana hanya, mara lafiya ne damu" Da sauri matashinnan ya kutsa kai cikin dandazon mutanennan yasa aka bubbuɗa musu, suka wuce. Specialist (General Hospital damaturu suka shiga da sauri, dan anan suke ganin likita. Cikin gaggawa, ma'aikatan kiwon lafiya suka fito da gadon tura marasa lafiya, aka ɗaura Yahanasu akai. Dai_dai shigowar motar su Wakil. Gudu_gudu Nurses suka shige da Yahanasu ɗakin jinya na mata, Dr Zangina yana biye dasu a baya. Baka jin maganar kowa a wajan, sai amon kukan Baguji da Hajja Gana, Innana kuwa, bata da kuzarin yin kuka mai sauti, hawayene kawai ke gudana a kumatunta. Wakil yana gefe yayi jigum, Bakura da Ba Modu kuwa, sai ajjiyar zuchiya kawai suke ta yawaita saukewa, iya tashin hankali suna cikinshi sosai. "Wai a cikin ruwan da akeyi ɗazu ta shigo gidanne, a ina abun ya sameta, kuma tasan su waye, a cikinku Modu wa yarinyarnan taima wani bayani ?" Bakura ne yake musu wannan tambayoyin a jere. Ba Modu yace. "Bakura ni kaina banda masaniya akan komai gaskiya,shigata gidan na tarar dasu a falo cikin damuwa. Innana ta faɗa miki wani abune?" Ajjiyar zuchiya Innana ta sauke sannan tace. "Nayi yinƙurin tambayarta, amman a ɗimauce take ainun bata iya bani amsar komai ba, sai firgitata dana kuma yi" Bakura yace. "Bulama Ƙarami a nemi ofishin ƴan sanda mafi kusa ayi report maza. Shi Wakil ya tsaya ko za'a buƙaci wani abun. "To Ba BaKura" Sa kai yayi, ya fice da hanzari. Yana fita sai ga wata tawagar. Bagulaji da Ahmada wan Yahanasu, da Dala tafe suma a kiɗime, nan duk aka haɗu akai tsattsaye ana jiran fitowar likita. Matan suka rufu akan Innana wacce take ta faman hawaye, sai rarrashinta suke yi. Bakura yace. "Za'ayi duk wani bincike daya kamata ayi. Wannan abun baza mu barshi ba, duk wanda aka kama da yin wannan aika_aikar wallahi bazan raga mishi ba. Maman nawa za'aima wannan cin zarafin?" Yana cikin sababin Dr Zangina ya fito. "Amm mutum ɗaya zata iya shiga ta zauna da'ita. Anyi mata allurar bacci mai ƙarfi, sai gobe da rana zata farfaɗo. Sannan dan Allah a kiyaye yin motsi da wani abu mai ƙara, dan gudun firgitata. Bakura ku same ni a office da Modu" Bakura ya dubi Innana yace. "Innana ke da su Baguji duk kubi Dala ya mayar daku gida. Hajja Gana ke ki shiga ki zauna da Yahanasun, in yaso saiki kwana da'ita. Mu kuma zamu je a soma bincike." Harga Allah Innana ranta baiso hukuncin Bakura ba sam. Gani take yi a irin wannan lokacin bai kamata ace za'ayi mata wata kara ba. Ya kamata a barta kusa da ɗiyarta, wala Allah ta samu sassaucin zugin zuchiya. Ko da ta koma gidanma, me zata yi acan? Ita dai ba bacci zata yi ba, ba iya cin abinci zata yi ba. Amman tasan Bakura shine uba, Babban wa dake zartar da ko wanne irin hukunci akan kowa, kuma dole kabi ko baiyi maka ba. Duk da dai ya kasance adali mai ƙaunar ganin farin cikin kowa. Da jan ƙafa tabi ayarin su Baguji suka tafi. Hajja Gana kuma ta shiga ɗakin majinyatan jikinta a mace. "A gaskiya wanda yai ma yarinyarnan fyaɗen azzalumine sosai, dan yayi mata muguwar illa. Sai da nayi mata ɗinki uku, ga raunuka wanda suke buƙatar kulawa, shi yasa take cikin firgici. Bacci take amman tana firgita, duk ƙarfin allurar da akayi mata. Fatanmu shine inta farfaɗo ta dawo dai_dai. Dan akwai yiwuwar ƙwaƙwalwarta ta taɓu. Amma zuwa gobe likitan kwakwalwa in yazo, za'a kaita gwajin ƙwaƙwalwa. Allah ya bada haƙuri. A wannan karon sai da Bakura ya zubar da hawayenshi sosai. Ba Modu kuwa sai cizan leɓe kawai yake yi, zuchiyarshi na tafarfasa. Babu wanda yace da kowa komai, Bakura na gaba. Ba modu na bayanshi, duk sun goya hannayensu a baya. Suna fitowa farfajiyar babban asibitin, motar ƴan sanda ta shigo, motar Bulama na gaba. Bakura yaja tunga ya tsaya, jirine ke shirin jefar dashi, da sauri Ba modu ya riƙeshi. "Bakura kayi a hankali, kayi haƙuri ƙaddara ta riga fata, adda'ar samun lafiya zamu yi mata. Shi kuma Naseer ba lallai bane ya aureta, dan wannan lamarin babbane, ni tunda abun ya faru nake hasaso fuskar iyayen yaronnan." Bakura bai iya tankawa ba, har ƴan sandannan suka iso garesu. "Ba Bakura ga ƴan sandan sun iso, suna buƙatar ganin Yahanasun, kuma suna son ganin likitan daya dubata. Kuma zasu gudanar da bincike, da zaran Yahanasu ta samu damar yin magana. A wannan karon Ba modu har yafi Bakura dauriya. Wucewa suka yi ciki, su kuma su Bakura suna tsaye a wajan, har suka fito, Bulama ya mayar dasu gida. Gidan a hargitse yake sosai, duk wanda ka gani a cikin damuwa da taraddin halin da Yahanasu take ciki yake. Bakura ya wuce ɓarayinshi, Ba modu kuma ya shiga ɗakin Ya Innana. A falo ya tarad da Fanda, da Fanna data tawo gada gidan mijinta a kiɗime, sakamakon kiranta da Bulama ƙarami yayi, ya sanar da'ita halin da ake ciki. "Fanna kece a tafe, sai kika ji abunda ya faru da ƴar uwar taki ko?" Fanna tace. "Bawa (Baba) Naji amman a wanne halin take ne?" Zama yayi ya dubesu yace. "Adda'arku take buƙata kawai, zata samu lafiya da izinin Allah. Sannan ƴan sanda zasu yi duk binciken daya dace, dan zaƙulo duk masu ruwa da tsaki a cikin wannan mummumunar aika_aikar. Ki daure ki koma ɗakinki, gobe saiki wuce asibitin daga can gidan naki. Gobe ƴan gidannan ma zasu je. Ina Innana?" Fanda tace. "Tunda ta shigo ta shige ciki, ta kulle ƙofar, munyi bugun duniya taƙi ko da kulamu ne, Yaya Ahmada ma ya shigo ya ganta, amman bata bashi dama ba" "Kuyi mata uziri kunsan a kiɗime take, dole a bita da laluma, bari in sameta." Wucewa yayi ya barsu a falon. Kwankwasa ƙofa yayi tare da kiran sunanta. Jin muryarshi yasa ta taso da wuri ta buɗe. Hijabine a jikinta, idar da sallahnta kenan. Hannunta ya riƙe suka koma ciki, a bakin gado yai mata masauki, ya zauna dab da'ita, hannunshi a cikin nata. "Innana nasan kwatanta tashin hankali da damuwar da kike ciki ɓata lokacine. Amman muyi haƙuri dukkanmu mu tungumi ƙaddarar data faɗa kan Yahanasu. Muyi mata adda'ar samun lafiya, da rayuwa mai ɗaurewa a gaba, kuma duk abinda ya kama na bincike, zamu gudanar dashi da izinin Allah" Cikin rauni tace. "Yara suka ce, anga jakar Yahanasu a cikin kangon gidan Lado. Harda ƙyallen atampar dake jikinta. Dala yace kar a taɓa har sai hukuma tazo" Gabanshi ya faɗi da ƙarfi, hawayen dake shirin zubo mishi ne, ya haɗiye, yace. "A kangon lungun gidan Lado? Kaddai wannan yaron da aka tsinci gawarshi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka keta ma Yahanasuna haddi? Ina zuwa bari in samu Bakura, muje mu samu Dala a wajan, kafin ƴan sandan su zo" Da sauri ya fita a shashen, harda gudu_gudu yake haɗawa. Da Ba Bakura da Baana ƙaninsu, sai Ahmada, da Ba'a kaka, sai Bulama Fari. Ko wanne ɗaki suna da Bulama, ko wanne Bulama da inkiyarshi. Tare duk suka ɗunguma zuwa kangon lungun gidan na Lado. A wajan suka samu Dala, da Abokinshi Mustapha suna tsaye. Shiga cikin kangon suka yi. Ga jakarta a yashe a ƙasa, ga kyallen rigarta yagagge a ƙasa, ga tsumman da aka rufe bakinta dashi, sai jini malala a ƙasa. Suna cikin kangon, sai ga ƴan sanda da Bulama Ƙarami sun shigo. Motar ƴan sandance, ta jawo hankalin mutanen anguwa, har suka soma fitowa, sabida a tunaninsu wannan matashin daya mutu a kangonne ƴan sanda suka zo dan ganin kangon. Malam Mato ne ya shigo cikin kangon, ya dubi Ba Bakura yace. "Alh Bakura, ashe kaima kaji abinda ya faru a wannan anguwa? Yanzu haka gawar tana gidana, yara sunje kiran ƴan sanda, ina cikin gida, Mata suka ce sunji motar hukuma ta shigo" Ɗan sanda da jin haka yace. "Alh muna son a nuna mana gawarnan, dan akwai binciken da zamu gudanar akan gawar. Kai kuma Ayuba, a ɗauki jaka da ƙyallen kayan asa a mota." Umarnin mai gidanshi Ayuba yabi. Daga kangon kuma, suka rankaya gidan Alh Mato dan ganin wannan gawar. Yarone saurayi santalele a kwance, kanshi a tsage, har zuwa lokacin jini na ɗan zuba, kanshi wani irin askine mara daraja, ga zip ɗin wandonshi a zuge. Wannan Kofur ya zuba ma gawarnan idanu ƙur, sannan yace. "Alh Zamu tafi da gawarnan asibiti, in an samu iyayenshi, sai ai musu kwatance ofishinmu akwai binciken da za'a gudanar mai zafi akanshi. Ayuba a ɗauki gawarnan asa a mota." Gawar aka ɗauka zuwa cikin mota, al'umma sun haɗu a layin anyi cirko _cirko. Suna fitowa motar ƴan sandan da Alh Mato yasa a kira suka iso suma. Kofur Madaki yai magana dasu, suka juya. Kallon su Ba Bakura yayi yace. "Alh a lokacin da abun ya faru, Yahanasun waya soma ganinta?" Ba Modu yace. "Mahaifiyarta ce ta ganta" "Good, ina buƙatar ganin mahaifiyar tata, ku kuma Ayuba ku jirani a wajan motarnan. Kai Kofur madaki wajan Innana akayi, yai mata tambaoyi da dama, daga ƙarshe ya karɓi riga da hijabin jikin Yahanasu, yai musu sallama ya tafi. Ko da dare yayi, gari yayi tsit, idanuwa da dama bacci sam ya gagari idanuwansu. Ba Bakura, Innana, Ba Modu, kusan akan sallaya suka raba darensu, suna roƙon Allah kan Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a cikin wannan lamarin. Innana a kan sallaya ta kwana, kuka kuwa tayi shi, har fuskata ta kumbura tayi suntum da'ita gwanin tausayi." Tun sassafe, gidan ya tashi da kaya_kaya kamar yadda ake tashi a kullum. Mata da yaran gidan, sai zuwa ɗakinsu Yahanasu suke, suna sake jajantama Innana halin da Yahanasu take ciki. Da misalin goman safe sai ga Mama Gana ita da ɗanta Ya Ari, sun iso daga Yobe. Ƙanwace ga Ba Bakura, Ya ga Ba Modu, ita ta cika nono ya karɓa. A ɓanrayin Ba Bakura ta sauka. A falonshi ta yada zango sai sharar hawaye take ta faman yi. "Yanzu Ba Bakura ashe abunda ya faru kenan? Oh na tausayama wannan yarinya." Ba Bakura yace. "Waya faɗa miki Mama Gana?" Cikin kuka tace. "Bulama Fari ne ya faɗamun a waya, shine fa nace bari in tawo, ayi komai dani zaifi. Ina shi Modu ɗin?" "Modu yana cikin gida, gara da kika zo ma. Dan inason in Yahanasu Allah ya bata lafiya akwai taron da nake son haɗawa a gidannan, akan ita Yahanasunne kuma, kinga gara da kika tawo" Tana share Hawaye tace. "Ina Hajja Gana banji ɗuriyarta ba. Kafin ya bata amsa, matan ƙannen nata suka shigo da sallama dan su kwashi gaisuwa. Mama Gana macece mai zafi da saurin fishi, gata da hargowa, haƙuri kowa yake yi da'ita. Dan inta zo daga Yobe saita gundiri kowa a gidan da jarabarta. Sai dai tana da kirki, gata da son sada zumunci. Shi yasa ko aure ne ya taso a gidan, ita ke shigema matan ƙannen nata gaba. Gaggaisawa akayi, aka shiga jajantawa juna. "Ohh Innana dare ɗaya harkin faɗa wallahi. Ki dinga sassauta ma kanki, adda'a zamu bita dashi, Allah ya toni asirin duk wanda ke da sa hannu a wannan lamari. Ƙannen nata ne suka yo sallama suka shigo. Da yara mazan gidan. Duk ɗaya bayan ɗaya tai ta tambayar yaran iyalansu. Daga baya matan ƴaƴan nata suka shigo su uku suka gaisheta. Su Dala basu yi aure ba tukunna. Amman an tsaida lokacin dama harda su Fanda, da Yahanasu a cikin waɗanda za aima auren, yara kusan goma za'a aurar. Ba Bakura yace. "Modu ai saimu hanzarta muje asibitin sha ɗayan rana tayi. Wakil yana can ya kai musu abinci." Shisshiryawa suka yi, mota uku suka nufi asibitin. A hakanma, sai da aka ba ƴan matan gidan Haƙuri kan cewa inta dawo gida sa ganta." ZURIYAR GIDAN BULAMA BUKAR BULAMA.......✍🏻 Sai mun haɗu zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu cikin rayayyu. Ya kuka ji salon? Labarine mai ɗauke da ɗumbun darasin rayuwa. Ku kasance dani on 20 July in sha Allah. Zaku iya biyan kuɗin karatu tun yanzu masoyanmu. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._ _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 07068606171 Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number. 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B) 2 Wannan labarin ya faru a gaske. Babu wani abu dana ƙara, saima waɗanda na ɗan sakayesu, dan gudun ɗaga ma masoyana hankali. Sadaukarwa garuku iyaye mata. Duk wata uwa ta duniya wannan littafin sadaukarwa ne a gareta. Gargaɗi. Ban yarda a sarrafamun littafina ta ko wacce siga ba. Yin hakan take dokace, a kiyaye. Nasiha. ( Mu guji ta'amali da miyakun ƙwayoyi domun kare lafiyarmu. Wannan saƙone daga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi) Saƙon gaisuwata Zuwa gareku Maman Khairat Ummu Nabeela Maman Yasser Maman inteesar Jinjinar ban girma a gareki.(Ambassador)Rashida Adamu Abdullahi mai sa'a, kuma women lida ta ƙungiyar 13_13, bugu da ƙari ƴar gwagwarmayar ƙwato hakkin mata, ƴar siyasa, kuma ƴar kasuwa. Shugabar ƙungiyar Mata Jarumai Association of kannywood atis ZURIYYAR GIDAN MARIGAYI BULAMA BUKAR BULAMA. Shine mahaifinsu Ba Bakura. Shi cikakken Babarbarene ( Kanuri) Gaba da bayanshi, mazauna Damaturu. Auren zumunci suka yi shi da Matarshi mai suna Yahanasu. Kasancewar Baburawa akwaisu da ƙabilanci, aurensu kuma da tsauri, hakan yasa wasu yaruka basu fiye aurensu ba,.Su da Shuwa arab, banbancin al'adunsu kaɗanne, sunyi matuƙar kama a al'adance sosai.Bulama ɗan boko ne sosai, manajer ne a bankin first bank dake garin DamaturuYaranshi Biyar huɗu maza sai ɗaya mace. Bakura shine babban ɗan Bulama, wanda ake kira da Ba Bakura, Ba ko Bawa yana nufin ( Baba a yaren Kanuri. Matarshi ɗaya itace Hajja Gana. Mata mai sauƙin kai da son mutane. Itace suruka ta farko a cikin gidan Marigayi Bulama. Yaran Ba Bakura biyar. Bulama Babba shine ɗanshi na farko, Ma'aikacin banki ne shima, ya gado takwaran nashi. Yana zaune a garin Kaduna da matarshi mai suna kofur Zubaina, sai yaranshi biyu mace da namiji. Macen sunanta Maryam taci sunan mahaifiyar matarshi Zubaina. Namijin kuma sunanshi Bakura suna kiranshi da Bawa. Bulama Babba shine kaɗai yake auren bahaushiya, kuma shine kaɗai yabar garin Damaturu da zama, sai dai ya shigo ziyara. Daga baya ma ziyarar ta gagara, ko waya saiya shafe fin wata biyu bai ɗaga waya ya kira iyayenshi ba. Aike kuwa da duk wata sai yayo aiken kuɗi masu tsoka, duk iyayenshi sai an bibbisu da kuɗinnan, ba dan basu dashi ba, sai dan biɗar albarkar iyaye, kuma shike riƙe da gidan ada, kasancewarshi babban ɗa a gidan. Ya taso cike da soyayyar ƴan uwanshi sosai. Amman matarshi ta shiga ta fita ta raba shi da kab ƴan uwanshi, babu mai zuwa gidanshi, tunda baya neman mutane, kuma ko an kirashi sai yayi ra'ayi yake ɗauka. Ko da yaushe Hajja Gana a cikin damuwa da ƙunar zuchiya take, bata jin daɗi sam yanda mace ta rabata da ɗanta data reni cikinshi harna tsawon wata goma sha biyu, yaron da sai tiyata akayi mata aka cireshi a jikinta, ta kuma sha baƙar azabar jinya. Ko da yaushe a cikin hawaye take. Ba Bakura shi kuma ko da yaushe a cikin bata haƙuri da tausarta yake. Wannan kenan. Sai mai bi ma Bulama Gunsum, matarshi ɗaya mai suna Yalewa, sai ɗiyarsu ɗaya mai sunan mahaifiyarsu, suna kiranta da Ba gana. Lauyan gwamnati ne shi. Sai mai bin Gunsum. Bukar, Shi bashi da aure, yanzu ne dai ake shirin yin gagarumin bikinsu, shi ɗan kasuwane babba a babbar kasuwa, yana da shagunan suturu, yana da shagon kayan ƙwaliya da shafe shafe na mata, kasancewar fannin kasuwanci ya karanta. Sai bai binshi itace Fandau Babba, tana gidan mijinta tana aure a Yobe, ita kuma malamar makarantar sakandare ce. Sai ƴar Auta Aisa ita kuma a wani kamfani take aiki, itama kasuwancin ta karanta, tana aure a Damaturu, soja ne mijinta, suna zaune a barrak. Sai mai bin Ba Bakura itace Mama Gana. Tana aure a Yobe itama, yaranta Huɗu dukka maza. Yurom ne babba, sai Ya Ari, sai Mainam, sai Bulamanta. Principal ce a Babbar makarantar mata dake Yobe. Masifaffiyace ta bugawa a Jarida ( maman Yaseer kanta ta sara mata) Sai dai tana da kirki da son ƴan uwa sosai, kuma kasancewarta ita kaɗaice mace a cikin ƴan uwanta, sai suka ɗaurata take jan ragamar auren yaran gidan, itace haɗa akwatuna, itace gyaran Amare, da siyan kayan ɗakin amaren. Maza kuma ita ke haɗama matansu akwati, sannan da ita ake komai dai. Sai mai bi mata Ba Modu. Yaranshi Takwas, matanshi biyu Innana itace uwar gida. Yaranta biyar. Bulama Baƙi shine Babba a ɗakinta. Likitan ƙashine a wani asibiti mai zaman kanshi, sai Wakil, shi kuma nurse ne a wani asibitin shima mai zaman kanshi sai Yahanasu, ita kuma ƴar jarida ce, tana aiki a gidan talabijin dake kan tauraruwar ɗan adam, lamta ta ɗari da tamanin da biyu. Fandau ƙarama, malamar makaranta ce itama, tana da aure. Sai Fanna Wacce bata soma aikin ba tukunna, kammala karatun nata kenan. Wakil da Yahanasu, da Fanna ne basui aure ba a ɗakin. Kuma suna daga cikin waɗanda za'a haɗa a aurar dasu. Surukan gidan duk suna cikin gidan, gidane mai bala'in girma wannan kenan. Sai kishiyar Innana mai suna Bugulaji, ita yaranda uku maza mace ɗaya. Ahmada shine babba, shike taimakon mahaifinsu da kula da gidan gonarshi, yana riƙe da ɓangaren masu gasa kifi su jera a kwali, shike kula da kifayen da ake kiwatawa, shi ya zaɓi taimakon mahaifinsu, amman yana da kwalin digri ɗinshi a fannin kanikanci, yana ɗaukar albashi mai tsokar gaske daga wajan mahaifin nashi, kasancewar kamfanin bushasshen kifin Ba Modu babba ne sosai. Ya na da mata da yaro ɗaya. sai mai bi mishi Dala, shi kuma likitan idanune, baida aure, suna daga cikin waɗanda za'a aurar, shi da Autarsu. sai autarsu Yabulu, ita kuma yanzu take kan haɗe digri ɗinta a fannin Jarida. Sai mai bin Ba Modu, Baana, matanshi biyu, Baguji, da Yana. Yaransu bawai. Mata huɗu maza uku. Ya Sufaim itace babba, sai mai bi mata, Aisa, Bulama ƙarami, Ba'a Kaka, Ya gana, ya gaji. Dukkansu suma ma'aikatan gwamnati ne. Tsabar son bokon wannan familyn ba'a aurar da yarinya har sai ta kammala digrinta na farko, ta soma aiki sannan sai tayi aure. Kuma basa bada auren ƴaƴansu mata a waje, mazan ma a cikin family suke zaɓa. Family ne mai kyau, da daɗi, ko wanne a waye yake. Basu da tarin dukiya mai yawa, amman suna da rufin asiri sosai. Kab matan yaran gidan suna cikin gidan tare da yaransu suma, waɗanda za'a kuma aurowar ma anan gidan zata zauna. Suna da tarbiya sosai yaran gidan, cikinsu ba wanda baiyi saukar Qur'ani ba, gasu da girmama juna sosai, ko wanne ɗaki akwai Bulama, kuma ko wanne Bulama yana da inkiya. Ba Bakura shine jagora kuma jaraba, shike riƙe da ikon gidan, sai umarnin da ya bayar ake zartarwa. Wannan kenan" Dawowa labari: Yahanasu. Da kuka na farka da safennan, banda firgita da iface ifacen dana dinga yi cikin dare. Da dama jama'ar dake ɗakin suna jinyar marasa lafiya, gani suke kamar makarai ke damuna. Tsabar ɗimuwace, da raɗaɗi, ko ina ciwo yake yi mini. Hajja Gana tayi kuka harta gaji, ko rintsawa ban barta tayi ba. "Yahanasu wannan kukan ya'isa haka zaki iya jama kanki wani ciwon kuma a ɓata goma ɗaya bata gyaru ba. Ga Ya Hajja Gana kin hanata cin abinci, kema babu abunda kika saka a bakinki." Wakil ne yake mun Magana cikin sigar rarrashi da kwantar da kai. Hajja Gana tace. "A'a Wakil batta ta koka, ni kaina kwana nayi ina faman kukan tausayin Yahanasu. In sha Allah za'a gano wanda yai mata wannan aika_aikar. Ƴan sandan kace suna hanyar zuwa ko?" Ta tambayeshi cikin sigar taushi. Kai ya ɗaga mata halamar "E" Ni dai sai faman kuka nake yi kamar wata ƙaramar yarinya" Hango su Mama Gana nayi, da su Ba Bakura, da sauran ƴan gidanmu. Wani irin yam_yam nake ji a jikina, takurewa nayi waje guda, na harhaɗe ƙafafuna. Ji nayi na muzanta, ina jin kamar tsirara kowa ke kallona, ina ganin kamar suna ganin mikin dake ƙasanane. Su kansu ganin yanayin kunya da tsarguwar da nayi, ya kaɗasu, sai sharar hawaye matan suke yi. Ba Bakura sai ajjiyar zuchiya kawai yake faman yi, idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya Innana ta matso kusa dani tana rarrashina da muryarta wacce take ƙarfafani. Take wani dangana da tawakkili ya saukarmun, hawayena na dinga ƙoƙarin sharewa, amman sai sabunta kansu suke yi. "Hajja Gana kunci abinci kuwa?" Ba Bakura ke tambayarta. "Babu wanda yaci abinci, ko runtsawa banyi ba. Yahanasu firgita tai ta yi da daddare, har daddanneta ma'aikatan jinyar suka yi, da ƙyar ta dawo nutsuwarta da naita tofeta da adda'a." Mama Gana ce ta matso gadon da nake kwance ina sauke ajjiyar zuchiya, na kasa ɗagowa in kalli kowa dan wata kunyace take kamani. "Taimaka mun Innana ki ɗagata ta jingina, tasha tea. Sai a nemo ruwan zafi ta gaggasa jikin nata" Ya Innana ta zaunar dani, ta jingina matashi a bayana. Mama Gana da kanta ta bani tea nasha, badan inason in sha ba, sai dan ganin na rage ma iyayena damuwar da suke ciki a kaina. Ƙwaƙwalwata ce, ta haskomon sanda wanna matashin ya keta rigata, yake shan ƙirjina. Ahhhhhh" Na saka ƙara mai doɗe dodon kunnuwa, ƙoƙarin durowa na ya soma yi. Su Bulama baƙi ne suka daddanneni, inata fisge fisge. Ma'aikatan kiwon lafiyane suka rufu a kaina. Allurar bacci suka zurkuɗa mun, luu naji bacci na ɗibana, dishi dishi nake ganin dangina." Ba Bukura: "Modu muje gida dukka maza mazan mu sauke ma Yahanasu Qur'ani mai girma, muyi addu'o'i ayi sadaka, mu yi tawassali da wannan aiyukan Allah ya dawo mata da nutsuwarta. Wakil kai kuma na wakiltaka kaji da ɓangaren ƴan sanda. Hajja Gana da Innana ku ku zauna da'ita. Bugulaji ku kuma a koma gida aita taya Yahanasu da Adda'a. Zanga likita kafin mu tafi" Yana gama magana yayi gaba, Ƙannenshi suka bi bayanshi, saida suka bar ɗakin matan suka fita su kuma. "Dr yaya halin da yarinyarnan take cikine? Hankula duk sun tashi" Dr ya dubi Ba Bakura yace. "A taya ta da adda'a. Ƙwaƙwalwarta babu wata matsala. Dan jiya dole likitan ƙwaƙwalwa saida yazo ya dubata. Ɗimaucewa tayi, wani sa'in yana iya fin hauka ma, sannan a tsorace take, tsoronne ya sanyata cikin ɗimuwa, a sakamakon abunda ya faru da'ita. Sabida ƙwaƙwalwar tata, tana hasko mata abunda ya faru da'ita, shi yake haddasa mata wannan firgita da ihun. Sannan daɗin daɗawa tana cikin zafin ciwo sosai, dan taji raunuka manya. Sai dai muna iyakar ƙoƙarinmu wajan bata kulawa." Jikinsu a mace mus suka bar asibitin. Gabaki ɗaya manya da yara, maza da mata, Ba Bakura yace su je falonsu ayi saukar tare. Kasancewar suna da yawa, yasa nan da nan suka sauke Qur'ani mai girma. Sukaita ma Yahanasu adda'a. Ba Bakura yayi tofi a ruwa a kofi, ya zuba a cikin gora, yace akai Asibiti, in Yahanasu ta farka a bata ta sha, a shafe mata jikinta da ruwan tofin. Sannan ya wakilta Bulama ƙarami a yanka rago, ayi sadaka, sannan a nemi miskinai a basu sadakar kuɗi. Duk yasa aka harhaɗa kuɗaɗen sadakar. Zukatan ƴan gidan duk a jagule. A cikin wannan yanayin na damuwa, gidansu Nasiru mai shirin auren Yahanasu suka ji abunda ya faru da Yahanasu. Ba shiri mahaifin Nasiru ya wakilta mahaifiyar Nasirun akan taje gidan taji me ake ciki. A kunyace Bagulaji tayi ma mahaifiyar Nasiru bayanin halin da Yahanasu take ciki. Kuma tace zasu je asibitin zuwa dare su dubo Yahanasun. Lokaci ɗaya zancen Anyi ma Yahanasu fyaɗe ya bazu a anguwa, labari har ma'aikatar su Yahanasu sunji labari. Zuga guda suka je dubiya asibiti. Amman sun tarar da su Hajja Gana a waje, a zazzaune, dan ba lokacin dubiya bane lokacin, jajanta musu sukayi, suka ajjiye ledar lemo da ayabar da suka harhaɗa kuɗi suka sai mata. Ofishin ƴan doka: Wasu Tsofaffi mata da miji na gani zaune a ofishin D p o matar sai matsar hawaye take yi. Shi kuma namijin sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. "Kuka ba naki bane, yin wannan kukan yana nuni da cewar kina bin bayan mummunan aikin da ɗanki ya aikata ko? Fyaɗe yayi mata fa, ita kuma zafin keta mata haddi da yayi yasa ta kwaɗa mishi dutse ya mutu. Ai yafi mishi sauƙi daya mutu, dan da iyayen yarinyar daya ma ɗanyan aikinnan sun kama shi da rai, da ɗanye zasu cinyeshi." Mahaifin matashin da yayi ma Yahanasu fyaɗe yace. "Ranka shi daɗe, maganar gawar yaron, a taimaka mana muje asibiti mu ɗauka, ayima yaronnan sutura. Ko a yanzu yaga aya, tunda da yanzu yana cikin makwancinshi, mutuwar wulaƙqnci da ƙasƙancin da yayi ma ya'isa, mu kammu dama ya riga ya zame mana ƙarfen ƙafane, ni bana jin takaicin mutuwarshi sam, na dai fi son ayi mana alfarma a bamu gawar mu binneta, abunda ya shuka shi zai girba ba, kuma duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." D P O yace. "Zaku iya ɗaukar gawar ɗanku, tunda likitoci sun gama bincike, maniyyin da aka samu a jikin yaron, maniyyin ita yarinyar da yaima fyaɗene, ƙwararru sun auna. Da ƙyar aka samu yarinyar ta tabbatar ma mai jinyarta, cewar ita ta kashe yaron. Babu wata doka da zata yi aiki akai, sabida a cikin ɗimuwa da fitar hayyaci take, babu wata doka da zata hau kanta, domun a hanyar ceton nata ran ne ta kashe taƙadarin ɗanku dake neman tata rayuwar, kuma duk mutumin da yayi kisa domun kuɓutar da kanshi daga kisa, bashi da laifi, kamar yadda ba'a shari'a da mahaukaci, haka ba'a zartar da hukunci akan ire_iren su Yahanasu. In kuma kuna ganin a turaku kotu to" Cikin sauri iyayen wannan mamaci suka ce, babu wani kotu da zasu je, su sun yafe, kuma a ta ya su roƙon gafarar iyayen Yahanasu. Haka suka fita harda godiya a hakanma.Da haka wannan zancan ya mutu mus, ba'a ƙara tado dashi ba. Lokaci yaita tafiya cikin damuwa da zulumi. Babu laifi Yahanasu tana samun sauƙi, kuma ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai ta zama shiru_shiru bata son magana sam. Ranar da iyayen Nasiru suka zo dubata, kasa magana tayi dasu sai hawaye, Nasiru ya tausaya mata ganin yanda tai wata iriyar muguwar rama, kamar ba Yahanasu ba. Kwananta goma a asibiti aka sallameta, suka dawo gida, da jikin nata ya ɗan yi ƙwaɓi sai ta soma yin azumin daya wajabta a kanta na kisan kai da tayi. Wannan kenan. YAHANASU: Ina kwance akan gadon Ya Innana ina karanta littafin addu'o'i, Ya Innana ta shigo da sallama, ita da Fanna. Waje ta samu ta zauna a kan gadon, Fanna kuma ta zauna a kujerar dake cikin uwar ɗakin. "Yahanasu, abunda zan sake somawa dashi shine. Haƙuri da yarda da ƙaddara. Bana jin daɗin ganinki a cikin wannan yanayin. Sai ciwon damuwa ya kamaki ai. Jiya Yaguji har ɗakinnan ta shigo ta sameki, amman kinƙi ce mata komai. Kiyi haƙuri abunda zai faru ya riga ya faru, saimu rungumi ƙaddara baki ɗayanmu, ni na fiki jin zafin yadda rayuwa tayi dake, amman ki sani hakan ba wai yana nufin ƙarshen rayuwarki ba ne. Jibi akwai taro da Ba Bakura ya tara, duk ƴan uwa za'a taru. Abunda ya tsayar da Mama Gana kenan bata koma ba. Maganar janye aure da iyayen Nasiru suka yi, suka ce a dakace su kuma. Karya baki tsoro, rayuwarnan cike take tab da ƙalubale, kiyi haƙuri, hakan karya dame ki, in ma rasa Nasirun ki ka yi, Allah zai ɓullo miki da mafiyinshi, kuma in dai har ya gujeki, ki sani dama ba masoyinki bane, sai ki gode ma Allah da ya sa akai walƙiya." Murmusawa nayi na dubi Ya Innana. Ni dama aure da sha'anin maza duk ya fice mun a raina. Inason ni kaina a bani lokaci in samu cikakkiyar nutsuwa tukunna. Mikin dake zuchiyata dai har abada bazai gogu ba nasan wannan. Ya Innana, na karɓi dukkan ƙaddarar da rayuwa zata zo mun dashi a gaba ma. Allah shike tsara mana rayuwa ba mu ba. Duk yanda kuke so haka zanyi. Maganar dakatar da maganar biki da iyayen Nasiru suka yo aike kuma. Ya Innana, ni a tawa fahimtar iyayen Nasiru basa son ya Aureni ne, shima kanshi ya dena sona, ƙila dama ba son gaskiya yake yi mun ba, gangar jikina kawai yake so. Sun mance cewar babu wani bawa dazai iya tsallake wani abun da kanshi, face wanda ubangiji buwayi gagara misali ya tsallakar dashi ba. Ni a sanar da iyayen Nasiru cewar na haƙura na janye gabaki ɗaya. Tun kafin su su ce muku hakan, dan nasan zaku ji ciwo gaya. Ku taya ni da adda'a Ya Innana, ina cikin damuwa mai yawan gaske, zuchiyata zafi take yi mun" Ya Innana ta dubeni da kyau tace "Naji daɗi da kika fahimci inda surukanki suka dosa, janyewarki, da danganarki ta matuƙar faranta mun. Kuma nasan lallai turbar haƙuri da juriyar dana ɗauraku akai, lallai kun hau. Na sani na baku tartibiyar tarbiyya da akeson ko wacce uwa ta baiwa ƴaƴanta. Mun baku ilimin Arabi da Boko. Yahanasu ni kaina zanfi son ki manta da Nasiru ki shiga sabuwar rayuwa. Allah yayi muku albarka duka" Da Ameen" muka amsa ni da Fanna. Haka dai lamurana suka ci gaba da tafiya. Duk wani jin daɗi da ake ganin jin daɗine, ni bana sonshi, bana kallonshi ma a matsayin jin daɗi. Bana son hayaniyar kowa, kuma ban cika son fitowa in haɗu da jama'a ba, tsoron kowa nake ji, gabana faɗuwa yake yi, ko da ƙaramin ƙara naji a gefena, ko wata sowa. Wayata ma kashewa nayi, na tura a jakata. Yau gidan namu an tashi da shirin gudanar da taron da Ba Bakura ya haɗa. Har munyi wanka, mun karya Ba Modu kawai muke jira." Ba Bakura: Waya ce a hannunshi, yana ta faman kiran wayar Bulama Babba. Amman tana ringin ba'a ɗagawa. Sunturi ya shiga yi a babban falon nashi. Idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya rasa meya canja mai tunanin ɗanshi, da har ya gujesu haka. Aita kiran wayarshi bazai ɗaga ba, kuma shi bazai kira ba. Zuwa duba iyaye da dangima sai ya bushi iska yake yi. Zama yayi akan kujera, yana kallon lokacin da Bulama Babba yake rarrafenshi a falon. Da kuma lokacin da yake raba dare yana aiki a falon. Yarone mai ƙulafacin iyaye da ƴan uwa sosai. Ko lokacin da ya tafi Kaduna karatu, ba'ayi tunanin zai iyaba ma. Amman a haka ya daure, sai dai fa kullum sai yayi kiran waya. Lokacin da ya soma ɗaukar albashi kuwa, ƙannenshi mata sunji daɗi sosai, mutum ne wanda abun hannunshi sam basu dameshi ba. Wani irin jiri Ba Bakura yake ji daga zaune, sanadiyyar damuwar juya musu baya da Bulama Babba yayi hawan jini ya dokeshi, ko da yaushe a cikin shan magani yake. Sabida shaƙuwarshi da Bulama Babba ta dabance, dan aboki ya ɗaukeshi ba ɗa ba. Hajja Gana ce ta shigo cike da sallama, tana sanye da lafaya mai kalar baƙi da fari, tasha ƙunshi baƙi, ga ƙamshi na tashi ta ko ta ko ina a jikinta. ( Kunsan kanuri ma ba baya ba wajan ƙamshi da ƙunshi) Kallon me gidan nata tayi, kallon shari'a, kawar da damuwarta tayi ta nemi waje ta zauna, sannan tace. "Bulama ya ɗauki wayarka kuwa, ko har yanzu matarshi bata bashi izinin ɗaukar wayarmu bane?" A raunace take maganar muryarta tana rawa tamkar mazari. Kallonta Ba Bakura yayi, yace. "Tun jiya nake faman kiran wayarshi, har yau bai ɗaga ba, yanzu na gama kiranshi amma ina. Bana neman dukiya a wajan Bulama Babba dan da dukiyata yaci yasha, yai karatu, har ya zama mutum, yayi aure. Tunda matarshi da yaranshi yana ganin sun isheshi rayuwa, ai shikenan. Bazan sake ɗaga waya in kira Bulama ba, ko zuwa yayi karki sake ki kawoshi gareni, in kuwa ki ka yi Hajja Gana zaki ga fishin Bakura. Duniya ce ai mai ido a tsakar ka, akwai ranar da zai gane babu abunda yakai Ahali daɗi." Tari ne yaci ƙarfinshi. Hajja Gana kuwa, sai haɗiɗiyar zuchiya kawai take yi, ta rasa me zata ce. Iya damuwa da tunani, harma da kukan babu wanda bata gaji dayi ba. Tana ji tana gani, ɗanta data ɗauki ragamar kula da rayuwarta, yau an wayi gari ya fifita wata mace sama da'ita mahaifiyarshi. Sallamar Ba Modu da iyalanshi ne ya katse musu damuwar da suke ciki. Sun zauna ba'a jima ba, Mama Gana ta shigo. Ba Baana da nashi iyalan suma sun shigo. Falo ya cika dam da iyaye da yara. Kowa ya saurara yana jiran Ba Bakura. Ba Bakura: "Modu ka buɗe mana wannan taron da adda'a domun kawar da shaiɗan, da naiman albarka." Ba Modu ya tashi tsaye ya gabatar da adda'a mai tsayin gaske, aka shafa ya zauna. Falon ya sake ɗaukar shiru na wasu daɗiɗu kowa da tunanin dake cikin zuchiyarshi. Ba Bakura kawai ake saurare ya soma magana......✍🏻 Mrs Bukhari ce GIDAN ƘAMSHI. Hajiya in kina neman turaren wuta, turaren kaya, turaren tsugunno, turaren wadrope, turaren mopping, turaren labule, humrori nau'i daban daban, KULACCHAM masu ɗan karen daɗi dan gyaran fatarki, Room freshner masu ƙamshin daɗi. To ki nemi Mrs Bukhari in dai harkar ƙamshine kin samu. Turarena na manyan mata ne, ba daku ake yi ba kucakai. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal. Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 3 Ina miƙa saƙon godiya a gareku masoyana na haƙiƙa, naji daɗi sosai da yanda kuka so littafin mai ido a tsakar ka duniya. Ina alfahari da masoyana na faɗin duniya. Masoyana na niger ban barku a baya ma, ni da ku son so fisabilillah. Saƙon gaisuwata a gareki. Fatima Sulaiman, nagode da soyayya. _*YADDA ZAKI BURGE MIJINKI*_ _1⃣-Garin Nahal_ babban cokali 2. _2⃣-Garin yayan bagaruwa Qaramin cokali 2._ _3⃣-Garin kanimfari cokali 1._ _4⃣-Garin almiski ko ruwan almiski._ _Zaki kwabasu gaba daya, yayin da zakije gun mai gidanki sai kiyi turarensu ki tsuguna ya shiga gabanki, Insha Allah maganar birgewa gun mai gida kin gama dashi ko harararki ake daga sanan an daina......_ BA BAKURA: "Da farko inaso in soma da ku mazan gidan. Masu iyali da waɗanda suke shirin ɗauko iyalin. Yarane ku masu ilimi, kuma masu taimakon iyaye da ƴan uwa. Duk kun haɗe kawunanku, ku ke ciyar da gidan, mu ƴan kuɗaɗenmu in mun samu sai dai muyi ma kanmu hidimar da muke so, da matanmu, da taimakon masu buƙata. Kune kula daci da shanmu, kune kula da abun hawanmu, sutura, kula da ƙannenku, kula da iyayenku matan duka. Alhamdulillah ko a yanzu na faɗi na mutu, na cika wasiccin da iyayenmu suka bar mun, cewar in kula da ƙannena. Na kula dasu, na kula da matansu, na kula da yaranmu duka. Gashi kuna kulawa damu a Yanzu, dama duk ɗan daya samu tarbiyya daga wajan iyayenshi, da izinin Allah, Allah zai dafa ma iyayen ta hanyar shiryar musu da wannan yaron, domun ya kula da tsufansu, mu kam Alhamdulillah shine abunda zance. Abinda zanja kunnenku akai shine, kar kuyi sake da adda'a kamar yadda ɗan uwanku Bulama Babba yayi sake da yin adda'a, har Matarshi taci nasarar rabamu dashi. Yau shekara biyu bansa Bulama Babba a idanuna ba, a wannan shekarun baifi sau huɗu mukai waya ba, shima wayar da muka yin, ni na ke soma kira, sannan saiya kirani. Babu ciwon da yafi wannan, ka haifama duniya ɗa, ya tare a jikin matarshi da danginta, yasa ƙafa yayi fatali damu. Mahaifiyarshi, kusan kullum saita zubda hawayen damuwar rashin ɗanta. Ta ɗauka ban sani bane, ina sane, kuma ina gani. Kuyi ƙoƙari karku yi sake a raba mu daku. Ku kuma matan, da masu auren da waɗanda suka ɗaura ɗambar shiga gidan aure. Kuji tsoron Allah ku mutumta mazajenku ku mutumta iyayen mazajenku, ku mutunta dangin miji, kar ku bari muyi kuka daku. Duk da nasan kab ɗinku babu wanda yake auren bare, acikin ku masu auren. Marasa aurenma babu wanda ya zaɓi bare, duk ƴan uwan junane, aurene na zumunci wanda aka haɗa da kyakykyawar niyya, dan ganin mun haɓaka zuri'a da kuma haɓaka zumunci. Wanda a wannan lokacin zumunci yayi ƙaranci, badan komai ba, sai dan dena auren zumunci da akayi. Yara kansu ya waye, sunfi ƙarfin ace musu suyi, suyin. Zamani yazo da sauye sauye, waɗannan dalilan su suka rushe mana zumunci, mu kuma in Allah mun ɗaura ɗambar haɓaka zumuntarmu. Yahanasu itama tabi sawon Bulama Babba, Nasiru dai Kanuri ne, amman ba danginmu bane. Duk da dai auren ma reto yake yi, dan gane da abunda ya faru, gani nake yi kora da hali iyayen yaronnan suke son suyi mana. Ni kuma na yanke hukuncin cewar mun haƙura, zamu mayar musu da kuɗin gaisuwar da suka kawo. Sannan babban maƙasudin wannan zaman dana tara yau, sabida Yahanasu ne, da kuma tunatar daku girman zumunci, da girman kula da iyaye da ƴan uwa. Allah ya isa akan duk wanda yayi yunƙurin rushe mana farin cikin gidannan. A matsayina na uba a gidannan, ba a wajan Yahanasu ba harma a wajan Innana da Modu. Zan ɗaura auren Bulama Babba da Yahanasu, za'ayi biki irin wanda ake yima duk wata ƴar gata. Amman bana fatan wani daga cikinku ya sanar da Bulama Babba wannan lamarin. Mama Gana, kece zaki kai Yahanasu Kaduna ɗakin mijinta. Ki faɗa mishi ban yafe mishi ba, in yabar ɗiyata ta zubar da hawaye, ban yafe mishi ba in ya bari sanadin aurenshi da Yahanasu ya kawo rabuwar kan zuriyar Bulama Bukar. Me magana yayi, dan ina ganin dukkan abunda zan faɗa, ya ƙare kuma, ina mai ba Yahanasu da Innana haƙuri a bisa wannan hukunci dana zartar, amman wannan aure babu makawa." Yahanasu: Gabana sai dukan uku_uku yake yi. Tunda Ba Bakura ya furta zai haɗani Aure da Bulama Babba. Hantar cikina ce ta soma disko, wani irin jiwa na ɗibana daga zaune. Ta ina zan soma da namijin da matarshi ta rabashi da mahaifanshi, ni wanne irin zama zanyi dashi kenan? Innalillahi wa'innailaihil rajiun, rana zafi ina ƙuna, ni Yahanasu da wanne zanji? Haƙiƙa Ba Bakura ubane, kuma ba'a taɓa ƙetare umarninshi ba, tunda ya haɗa aurennan nasan kamar anyi an gama ne. Amman nasan rayuwata zata dawo abun tausayi da kwatance ne. Sai dai Ya Innana ta horar damu, juriya da haƙuri, da ɗaukar dukkan wani abun da zai samemu na tashin hankali, ya zama ba komai ba. Lokaci ɗaya, manyan al'amura suka sameni masu girman gaske. Na rasa darajata, gashi za'a aurad dani ga mijin tace. Hawaye tuni ya gama wanke mun fuskata. Satar kallon Ya Innana nayi. Itama hawayene ke fita da ga idanunta, tana yi tana sharewa da hannun lafayarta daga ganin fuskarta bata so wannan haɗin ba. Dan tasan cutuwa zanyi sosai. Ba Baana ne yayi gyaran murya yace. "Ni abunda nake gani shine, ko za'a tambayi Bulama Babba tukunna aji ra'ayinshi dangane da hakan? Sabida gudun kwaɓewar zumuncin. Kunga dai yaronnan fa sai abinda matarshi hamshaƙiya tace, kar mu zo ayi abunda daga baya za azo ana cizon yatsa. Bakura kayi haƙuri bawai ban girmama umarninka bane, face gudun abunda ka je ka zo" Yana cikin jawabi Mama Gana tace. "Zancan ɓur kenan inji tusa. Baana baka gane inda aka dosa ba ga dukkan halama. Ni abunda na fahimta shine. Zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne . Zamu haɗa auren Bulama Babba da Yahanasu sabida zumunci, sannan shi ɗan uwanta ne zai fi bare riƙe ta da daraja, duba da asarar budurcinta da ta yi. Zamu haɗa auren Yahanasu da Bulama Babba sabida ta shiga rayuwarshi wala Allah ta sanadiyyarta shima ya samu rangwame, Allah ya kuɓuto dashi daga hannun azzalumar matar da yake aure, sannan zai kare mutuncinta a matsayinta na wacce ta rasa darajarta ta ɗiya mace, sai yafi kowa sanin kimarta, tare da taya ta jin ciwon abunda ya farun da'ita. Kuma shine kaɗai yake da nisa, kuma shi kaɗai yake auren bare, wannan aure da Bulama Babba yake yi da kofur Zubaina, kowa yasan tun fil azal babu wanda yaso haɗin, kanuri sai kanuri." Ba Modu yace. "Koma dai sabida menene. Ba Bakura shike da iko akan kaina, dama iyalan nawa. Ni bani da ja akan duk abinda zaka zartar. Kaine da wuƙa da naman, Yahanasu taka ce Bulama Babba naka ne, tuwo na mai na. Fatanmu shine Allah yasa ayi damu. Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki ɗaya." Ba Bakura, ya fashe da kuka shi da Hajja Gana. Haƙiƙa kukansu ya bayyanar da zafin da zukatansu suke yi akan ɗansu ƙarara. Take a wajan naji cewar zanyi biyayya irin biyayyar da iyayenmu sai sunyi alfahari dani. Da yardar Allah zan share ma Ba Bakura hawayenshi, in sashi farin ciki da walwala." Alkhairi akaita sanyawa haɗina da Bulama Babba. Daga bisani Mama Gana ta rufe taron da adda'a. Mu yara da iyayenmu mata, duk muka fito. Su kuma su Ba Modu suna wajan ɗan uwan nasu, suna ƙoƙarin kwantar mishi da hankalinshi. Jikina a saɓule na zauna a kujera. Ya Innana ta zauna a kujerar dake fuskantata. Bulama ƙarami yana zaune a kujerar da nake, Wakil yana jogane a hannun kujerar da muke. Fanna, da Fanda suna ƙasa. Kowa jikinshi a mace, duk wanda na kalla, sai in ganshi cikin damuwa. Ya Innana uwa ta gari wacce bata nuna sarewarta tace "Ina horanki da yima iyayenki biyayya. In har kina son rayuwarki tayi albarka, to kibi iyayenki. Ki riƙe adda'a da tsaiwar dare,ki lizimci karanta Qur'ani mai girma ba dai mutum ba sai dai Allah, ki dinga haɗe saukar Qur'ani duk sati, kinga dai yadda nake yi ai. Karki bari sanadinki a ɓata wannan zumuncin. Kome zai faru dake ki jure, kar ki tunkari kowa da ƙorafi, Bulama Babba ɗan uwanki ne, duk abinda ya miki mara daɗi ki shanye. Ki nutsu ki riƙe gidanki da mijinki. Ga Fanda, duk abinda ya shige miki duhu ki sanar da'ita. Ke kuma Fanda kiji tsoron Allah ki ba ƴar uwarki nagartacciyar shawara. Yahanasu ki nutsu ki zama mai girman daraja a idanun mijinki. Karki gaza wajan yi mishi hidima. Aljanna kika je nemowa, duk wuya ki ɗau jumurin shanyeshi. Ki samama Ba Bakura da Hajja Gana farin ciki. Ki shirya Wakil ya kaiki gidan Yanunu ƙanwata, tai miki gyara, sabida kina buƙatar gyara na musamman. Zata baki wasu surrukan da dabarun zama da miji, da abokiyar zama." Gabaki ɗaya nasihar Ya Innana ta ɗaure ƙashi da jijiyoyin jikina. Dajin muryarta kinsan tana cikin tsananin tashin hankali da damuwa. Ya Innana, na rungumi zaɓi iyayena, ina fatan ya zame mana alkhairi baki ɗaya. Ƴan uwana gudunmawar da zaku bani shine adda'a, ku yawaita mun sadaka da nufin Allah ya kareni da dukkan wani sharri." Kuka na rushe dashi mai ciwo. Dan har wani ɗaukewa numfashina yake yi. Sai yamma Wakil ya fitar mun da akwatina, ni kuma na shiga cikin gida yima matan gidan sallama, sannan na fito muka tafi Ya Innana: Wayarta taja bayan fitar su Yahanasu ta doka kiran ƴar uwarta. Ƙara ɗaya_biyu aka ɗauka. "Assalamu alaikum Yaya, an wuni lafiya, ya Ƙarfin jikin Yahanasu?" Ajjiyar zuchiya Innana tayi tace. "Jiki da sauƙi, sai rashin sakewa, da rashin son magana yanzu da take fama dashi. Ga wani babban al'amari daya ɓullo cikin rayuwarta. Bansan ta inda Yahanasu zata iya wannan rayuwar ba. Ba Bakura ne ya haɗata da Bulama na wajanshi, zai musu aure. Shi kanshi Bulaman sai yanda matarshi tace mai fa yake yi, shine za'a aura mishi mace,macen ma Yahanasu, ina cikin damuwa Yanunu, yanzu haka ma Wakil zai kawo miki Yahanasun, suna hanya, amman zasu biya su sauke ƴar uwar tasu a gidanta. Ta zauna a wajanki. In bikin ya gabato, ta dawo cikin gidan, ki yi mata dukkan gyaran da zai farfaɗo mata da darajar gabanta." Yanunu tace. "Kuma Yaya haka kina ji kina gani za'a bama yaronnan Auren Yahanasu, bakwa tunanin makomar rayuwarta ne, koko me? A cikin zafi da raɗaɗin fyaɗe take fa, yarinyar da take cikin tsananin damuwa shine za'ayi mata auren dole, a wannan halin da take? Yaya asiri fa gaskiya ne, tunda yaci ma'aikin Allah." "Yanunu nasan asiri gaskiya ne, tunda yaci ma'aiki Arrasul ( S A W) amman bani da ikon yin jayayya da umarnin da Ba Bakura ya yanke. Ko Modu bashi da wannan ikon balle ni. Wallahi ni kaɗai nasan a irin tashin hankalin da nake ciki, dukan yayi mana yawa, shi yasa ma na turo miki ita, in ina ganinta tausayinta zai iya ingizani in bijirema Modu." Sun jima suna tattaunawa, amman mafita dai basu da ita, sun shige damuwa ainun" Yahanasu. Tunda muka fito, zazzaɓi ya rufeni mai zafi, zuchiyata sai naji kawai tana raya mun, in kashe kaina kawai in huta. Wata zuchiyar tace, gara in gudu. Wata tace mun in buɗe murfin motar da nake ciki in faɗo ƙasa. Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun itace kalmar da naita jaddadawa a hankali, ina dafe da ƙirjina. Ahankali nake jin ina dawowa dai'dai. Amman har muka iso gidan Yanunu ban dawo haiyacina ba. Muna shiga na zarce ɗakinta, bance dasu komai ba. Su kansu basa son cewa dani komai. Zama nayi a bakin gado, ina tunano fuskar Bulama Babba, da matarshi Kofur Zubaina. o ikon Allah, a ƙirji da cinyar Bulama Babba na gama wasannina, domun ya kasance mai son yara. Daga mazan har matan, babu wanda bai goya ba. Ni kuwa, ina tuno lokacin da ake goya ma Bulama Babba ni, muje kai niƙa. Hawayena na share . Na rasa darajata, farin ciki ma gashi ina dab da rasashi, wato haka rayuwa take faruwa, dole mutum mai rai, wata rana ya faɗa cikin jarabawar rayuwa, duniya juyi juyi kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi, duniya zancen banza, duk wanda ya bari duniya ta ruɗeshi yayi wawa, duniya mai idanu a tsakar ka. Yanunu ce ta shigo hannunta riƙe da plate cike da wani irin farfesun nama. "Cinye wannan cicciɓin Yahanasu. Ki share hawayenki, da kaina zanje in samu Ba Bakura ɗin, muyi magana, aurennan bazai yiwu ba, ai wanna ma zalunci ne, kuma mahaifinki ya zura idanu ya kasa cewa komai." Dubanta nayi nace. Dan Allah Yanunu karki je, zan aureshi, nima na amince, babu bawan daya isa ya zaɓarma kanshi rayuwar da yake so, kuma ace ya samu hanyar ba gargada. Ƙila aurena da Bulama Babba shine abunda yake rubuce a allon ƙaddarata. Na rasa ma darajata, na fauwalama Allah komai. Babu wani zafi da raɗaɗin da zanji wanda ya wuce zafin fyaɗen da akayi mun." Ina kaiwa nan sai kuka. Na tashi hankalina sosai. Ni kenan a cikin kuka, da kulle kaina a ɗaki. Yanunu ta rasa yanda zata sani. Ni kaina fatan mutuwa nake yima kaina sosai. A hakan take ta gyarani da magunguna, wasu naci, wasu nasha, wasu kuma na wanka. Ga kullekham ta matan aure, da shu'umar humra da nake shafawa, sabulun wankana ma, ƙamshinshi bana wasa bane. Ni ɗince dai bana cikin hayyacina. Kullum a cikin kai kukana ga Allah nake. Ƴan gidanmu duk wanda ya kawo mun ziyara da kuka yake tafiya. Hakan da na gani ne yasa na daddage na aro nutsuwa na ɗamfara ma kaina, shine na soma ganuwa. Nasiru kuwa bai ƙara ganina ba, bai kuma jin muryata ba,ni banma san yanda aka ƙare da zancenshi ba. Wata ranar juma'a ina zaune a uwar ɗakin Yanunu, na jiyo muryar Hajja Fati ƙawata, suna gaisawa da Yanunu kamar a mafarki. "Ki shiga tana ciki, sai kika ji abunda ya faru da'ita ko?" Hajja Fati tace. "Wallahi jiya na shigo gari, ummanmu take labarta mun abunda ya faru, Allah ya kiyaye gaba." "Uhmm Ameen, ki shiga tana cikin wancan ɗakin" Ni dai ina jiyosu, saiga Hajja Fati ta shigo da gandamemen ciki a jikinta. Ganin cikin ya sani jin sanyi da farin ciki a raina. Dan Shekara biyar da auren Hajja Fati, amman ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Magunguna babu irin wanda bata sha ba na samun ciki, daga na Gargajiyar, harna asibitin. Har aure mijinta ya sake sabida rashin haihuwar nata. Hajja Fati ƙawata ce ta ƙut da ƙut, maƙotanmu ne, kuma tare mukai karatu, tun daga primary har sakandare, Ba Bakura ne ya biya mata kuɗin karatu, kasancewar mahaifinta ya jima da rasuwa. Hajja Fati kece da safennan haka, sai kace wacce tayi mafarkina? Sai naga abun arziki ashe an samu, shine ko a waya baki bani labari ba" Jikinta a mace ta zauna. "Yahanasu kece kika rame kikayi duhu haka, kin ganki kuwa yanda kika zama? Ki ɗauki dangana mana Yahanasu, ki yi fatali da abunda ya faru dake, ko dan kwanciyar hankalin Ya Innana. Naga ita kanta tayi rama sosai sai wuya" murmushi nayi mata kawai, sannan nace. Na riga na dangana, dan da'ace ban dangana ba. Da yanzu na biye ma sharrin zuchiya na halaka kaina. Hajja Fati wannan ramar tana da nasaba da rayuwar dake tunkaroni a gaba, abunda ya faru a baya ya shige ai, mikin dai yana cikin zuchiyata abadan. Ta yaya zan soma rayuwa da Bulama Babba, alhalin sai abinda matarshi tace mishi. Duk da kullum a cikin adda'ar neman dacewa nake, amman kuma zuchiyata a cikin zulumi, da taraddadi take a ko da yaushe Hajja Fati" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Zahiri maganarki abin a duba ne Yahanasu. Auren soyayyarma yaya yake cikawa balle auren dole? Ni kaina abubbuwan da nake fuskatanta a wajan Ahmad ai abun bana wasa bane. Yahanasu tunda Ahmad yayi aure, na zama banza, sharar gidana ta fini daraja a idanunshi. Allah ya dubeni ya soma bani ciki kafin amaryar. Nayi tunanin hakan zai sa Ahmad a farin ciki. Amman wallahi ta cikin amaryarshi yake yi. Kwanakin baya na dawo gida ai nayo yaji. A ranar Umma ta mayar dani. Yahanasu Umma taƙi ta saurareni in faɗa mata halinda nake ciki ma. Sai cewa take yi in riƙe maraicina in dubeta. Ke ga ciki, ga damuwa, hawan jini ya rufar mun, da naga zan mutu ba shiri na soma shan kayan maye. Su kaɗai nake sha in samu nutsuwa a zuchiyata Yahanasu, to in ban sha ba, mutuwa zanyi, takaicin ɗa namiji dubi yanda ya zubar mun da ajina, duk gaye na. Amman yanzu dubeni fa" Da kallon mamaki na bita. Da ace a bakin wani naji labarinnan bazan taɓa gasgatawa ba. Hajja Fati da Ahmad wata soyayya suka gudanar mai ban sha'awa kafin aure. Duk wanda yasan Ahmad, to dole yasan Hajja Fati. Haka itama duk wanda ya santa, ya san Ahmad. Amman yau shine ya juya mata baya, har take shirin halaka kanta sabida shi? Haba Hajja Fati, me ya kaiki shan kayan maye, adda'a ya dace ki kama, amman ba ki kama abunda zai iya taɓa duniyarki ba. Ya kike ganin randa Umma zata san halin da kike ciki zata ji? Karki bari ki halaka kanki a kan namiji" Dariya tayi mun. "Bafa zaki gane bane Yahanasu. Sai lokacin da tsananin damuwa ya kamani ne, nake shan abun maye, da zaran nayi bacci na farka, sai kiji zuchiyata sawai da'ita, shi kanshi kaina sai yayi fayau. Kuma raba dare nake yi, ina adda'ar Allah ya bani mafita Yahanasu. Takaicin ɗa namiji, da kishiya yafa wuce tunaninki. Balle ke mai mugun sa abu a ranki, maganar da ba wata magana ba ma, saita hanaki bacci. Harfa Deepretion ne ya kamani lokacin cikina yana wata na huɗu." Dubanta na kuma yi cikin sarewa nace da'ita. Ki dai kiyaye, kuma ni ina ganin ki koma makaranta ki haɗa digiri ɗinki, ki ɗan samu aiki. Rashin lokaci zai iya rage miki matsala. Amman sai anyi biki zaki koma dai ko?" Dariya tayi. "Har Kaduna saina kaiki ai Yahanasu." Ganin Hajja Fati yasa na ɗan saki jiki na, sai hira muke yi na yaushe gamo. A wajena ta kwana, sai washe gari Sannan ta koma gida. Innana: A ɗakin Bagulaji matan gidan duk suka taru, harda Innana, Mama Gana tana ta tsara yanda al'amarin bikin ƴan matan zai kasance. "Ni ina ganin ayi jeren yarannan da wuri sabida a huta. Maganar kayan katako kuma, zuwa gobe Ni da Bagulaji zamu je Kasuwa, sai mu zaɓa musu abunda ya dace. Ke kuma Yaguji, ke da Ya kura. Sai ku duba mana kayan kitchen. Ɓangaren Labulaye da su kafet kuma, sai Innana ta ɗauka, tunda ta iya zaɓe, mu samu mu gama komai cikin tsanake, Ba Bakura ya tura mun kuɗin duk abunda za'a buƙata. Cewar Mama Gana kenan. Innana tace. "Maganar cincin, da su nakiya kuma, nayi ma Umman Hajja Fati magana, tunda dama ita ke yi sana'arta ce. To na faɗa mata gobe Wakil da Bulama ƙarami zasu kawo mata buhun fulawa bakwai, na cincin, da dublan, buhu ɗaya na alkama domun yin alkaki, sai buhun sikari. Sai buhun shinkafar tuwo,da rabin buhun suga, da kayan ƙamshi. na siya an kai gidan Baba Gwamma, maganar nakiya da zata yi. Sabida a samu a kammala komai, kafin gidan ya cika da Baƙi. Abincin biki kuma Hajja gana tace. Tayi ma wata mata, mai yin sana'ar abincin biki. Zata yo abinci kala uku ranar ɗaurin auren, sabida baƙi. Bagulaji tace. "E nima tayi mun magana, sabida ta bani wasu atampopi da lace tace in ba telana ya ɗinka ma Yahanasu su. Shine da nake karɓan kuɗin dinkin take sanar dani maganar abincin ƴan ɗaurin auren. Allah yasa ayi damu wannan bikin. Ba Bakura yana kashe ma wannan biki kuɗi sosai gaskiya. Kamar ba'a taɓa yin biki ba a gidan haka yake ji. Dariya suka yi dukkansu. Shirye_shirye sosai suke yi, abun babu kama hannun yaro. Ana biki saura sati guda, gabaki ɗaya an gama komai, amaren anje anyi musu jeransu. Mazan kuma, ko wanne ya gyara inda zai ajiye matarshi. Gida ya soma cika da baƙi, ƴan Pataskum ne, ƴan maiduguri ne, ƴan yobe ne, jama'ar Yola ne. Duk kowa ya tawo,duk inda ka gilma yaren kanuri da kamshin humra ke tashi, duk matar da ka gani, zaka ganta saye cikin lafaya, hannu da ƙafarta kuwa yasha ƙunshi baƙi. gidan kuwa yasha fenti sabo. Iyayen amare, da angwayen kuwa ko wacce ɗanta ya gyare mata ɗakinta, anyi musu fenti. Atampa super sukaima iyayen nasu Anko, na ranar ɗaurin auren kenan. Dan akwai walima da zasu gudanar a cikin gidan ranar ɗaurin auren kamar yanda dama suke yi, duk aure. Ga tarin al'adun auren Kanuri da ake gudanarwa, babu ko guda ɗaya da ake bari, sabida al'adune masu dogon tarihi, a cikin yaren Kanuri. Yahanasu: Tun biki saura sati guda, Yanunu ta dawo dani gida. Can ɓangaren Ya Bagulaji kishiyar Ya Innana ta kaini, sabida kara. Ƙawayena duk muna can, Yaguji ƙanwata ɗiyar Ya Bagulaji ita kuma ta koma ɗakinmu ita da nata tawagar. Ni dai na dawo kalar tausayi, babu wuya sai kuka, gabaki ɗaya na sare. Ga gidan ya cika dam babu masaka tsinke, duk inda ka ratsa yare ke tashi. Hajja Fati tana tare dani, da ƴan tsirarin ƙawayenmu data gayyata. Haka aka shiga gudanar da al'adun biki iri daban daban....✍🏻 Mrs Bukhari ce. Ya kuka ji labarin? Yawan comments zai iya sawa zuwa yamma ku sake jina da sabon feji, dan kuji yadda wannan biki zai kaya... Ina da humrori da turarukan wuta irin da kanuri da sudanawa, siyan na gari mai da kuɗi gida, kayana ingantattune sai kin gwada zaki tabbatar. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal. Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 4 *BABBAN ALBISHIR GAREKU MASOYA LITTATTAFAN GAWURTATTU UKU. AKWAI KYAUTA TA MUSAMMAN DA MUKA SAKA DOMUN KU MASOYANMU. WAƊANDA SUKA JAJIRCE WAJAN TAYA MU SHARE ƊIN LITATTAFAN MU DOMUN SOYAYYA. AKWAI KYAUTAR BAN GIRMA DA MUTUM UKU DAGA CIKI ZASU SAMU. BUGU DA ƘARI ZASU SAMU DAMAR KARANTA LITTATAFAN GAWURTATTU UKU NA WANNAN ZANGON KYAUTA. BUGU DA ƘARI MUTANE BIYAR DA SUKA BIYA KUƊIN BOOKS ƊINSU DA ZARAN MUN GAMA FREE PAGE, SUMA SUNA DA KYAUTAR BAN GIRMA DA GAWURTATTU UKU ZASU BASU. AMMAN BIYAR ƊIN FARKO BA. AN RIGA AN DAƊE DA SOMA BIYAN LITTAFIN GAWURTATTU UKU, TUN KAFIN MU SOMA POSTING. WANNAN MUNA MAGANA NE DA WAƊANDA ZASU BIYA BAYAN MUN KAMMALA FREE PAGE ƊINMU. ( FATIMA SULAIMAN ITACE TA FARKO DATA SAI LITTAFAN GAWURTATTU UKU TUN KAFIN MU SOMA. TATA KYAUTAR TA MUSAMMAN CE) DOMUN ƘARIN BAYANI SAI KU TUNTUƁEMU A NUMBOBIN WAYAYOYINMU. MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU ✍🏻* Yahanasu: Haƙiƙa Kanuri suna ɗaya daga cikin ƙabilun da suka fi ko wacce ƙabila iya riƙon aure, dama gudanar da Al'adu a yayin Aure. Al'adun nasu sun haɗa da. *BAWARAM* Kalmar Bawaram tana nufin Iyaye maza. Idan kuma a aure ne aka ce Bawaram tana nufin kayayyakin da ango yake yi wa dangin Amarya, waɗanda suka haɗa da kayan. Uwa, matar uba, da ma ƙannen uba, da yayyensu, babbar yar Amarya, kakannin, mai kitson Amarya, da uwar ɗakinta in tana dasu, duk sai ango yayi musu kaya. *FAFURAI* Fafurai kuma, wani akwati ne da gidan Amarya suke yiwa Ango, abunda ake sawa a cikin akwatin sun haɗa da, shaddaji, da yaduna, huluna, da, takalma, agogo, turare, sallalaya, Qur'ani da sauransu. Kuɗi ake kashewa bana wasa ba, sabida dangin amarya suna son yiwa ango bajinta. *WUSHE_WUSHE* kuma bikine da ake gudanarwa tsakanin ɓangaren amarya da ɓangaren ango, ana gobe ɗaurin aure. Ɓangarorin biyu sukanyi shigar al'ada irin ta Kanuri su haɗu a wani farfajiya, ko, waje mai fili dan gudanar da wannan bikin Al'ada. Mu a gidanmu muke gudanar da wannan biki, kasancewar gidan da girma. A wajan bikin ana keɓe Amarya da ango, a wani ƙayataccen gado, sa'ilin da makaɗan gargajiya ke kiɗa. Ƴan mata da abokan ango kuma, zasuita rausayawa a gaban ango da Amarya, irin rawar al'ada. Daga nan kuma sai liƙin kuɗi tare da yin hotuna kuma. Wushe_wushe na ɗaya daga cikin bikin auren Kanuri da yaruka da dama suka ara suka yafa a Najeria. *QLATUL* Yana nufin wanke kai, mata kaɗai ake yima. Ana gudanar da wannan bikine, idan aure ya rage saura kwana uku. Yadda ake yinshi shine, Iyayen Amarya ke wanke mata kai da karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kiɗan ƙwarya, wanda tsofaffin mata ke waƙa cikin harshen Kanuri. Shi wannan kiɗan ƙwaryar, irin na al'adar ƙabilar hausawane sak. *KALAWA* Tamkar shaɗi yake, sai dai shi ba'a duka. Yanda ake yinshi, akushi ake tanada, da bushasshen karkashi, da ɗanyar shinkafa. Sai a ɗaura ango da Amarya akai su zauna. Dama an riga an ɗaura tuwon buski a wuta, ana saukewa da zafinshi za'a ɗebo, a zuba a tafukan Amarya da ango. Amarya da ango, sai su juye wannan buskin na hannunsu a cikin akushi. Ana yin haka har sau uku, sai a goge musu hannayensu, a shafe musu da bushashahen karkashi. Daga nan sai ƴan uwa da abokan arziki, su zo suyi musu kyaututtukan arziki, wasu har gida da mota ake basu, ga masu bada kuɗi, ko sarƙar gwal, ko kuma jari. Ma'anar bikinnan shine, kamar yadda suka jure zafin abincin da aka zuba musu a hannu, Allah yasa su jure zaman Aurensu fiye da hakan. *KA'AJI* Ka'aji yana nufin turaren wuta, ango shi yake yi ma amarya. *HUMRAM* Turarene na ruwa wanda ake shafawa a jiki, mai ɗauke da surruka masu dama. (Mai bukata tayi mun magana ina siyarwa) shima ango ke yinshi, ko ya bayar da kuɗi ayi ma amarya. *KULECHAM* Mai ne mai ƙamshi, tare da ɗumbun sirrikan itatuwan gyaran fata, da laushin fata. ( Me so tayi mun magana ina saidawa)Shima ango ke bada kuɗin siyanshi. *KALAM WURI* Wani abune ƙarami kamar kabbasa, wanda ake manne shi da kuɗi gaba ɗayanshi a bawa Amarya ta tafi dashi ɗakinta, a matsayin kyauta. Duk lokacin da buƙatar kuɗi ta taso mata, kuma babu kuɗi a hannunta, saita zari kuɗi daga cikin wannan kuɗaɗe ta kashe wutar gabanta. Ita wannan al'adar takwarar Amarya ce take yi, idan bata nan ta mutu, sai ƴaƴanta su wakilceta. *KNDAI* kalmar kndal yaren kanuri ne. Kndal wani ɗan kwanone mai kama da akushi, wanda ake saƙashi da kaba ( ADUDU SUNANSHI DA HAUSA) Ana yi mishi ado da fure, sai a zuba goro, dabino, Shi wannan amarya ake ba ta tafi ɗakinta dashi. Idan mijin mai cin goro ne, sai ya dinga cin goro a ciki, in mai cin dabinone, sai yaci a ciki. *KUSUSURAM* A binda ake nufi da wannan kalmar ana nufin kai kayan lefe. Yadda ake kai lefe a al'adar Kanuri. Idan aka tashi kai lefe gidan iyayen Amarya. A al'adar Kanuri ana haɗawa da tinkiya, masu ƙaramin ƙarfi kenan, masu dashi kuma bijimin sa suke haɗawa dashi. Za'a ɗaura atampa a wuyan dabbar a yayin da za'a kai kayan lefen. Wannan atampa da aka ɗaura a wuyan dabbar idan anje gidan iyayen Amarya suna ba da ita kyauta ga wanda ko waɗanda suka riƙo dabbar, aka tawo da lefen. *WUSHE WUSHE YAA'YE* Shi kuma ana yinshi ne a ranar Alhamis Yadda akeyi shine. Dangin Amarya zasu haɗu su yi nakiya, a yayin da ɓarayin ango kuma zasu kawo musu goro tare da yi musu sannu da aiki, sai ɓarayin Amarya su ba su wannan nakiyar. *NALLE* Sa lalle kenan yake nufi, ranar talata akeyinshi. Ɓangaren ango zasu kai buhun lalle, da katon_katon na minti, da huhun goro, da tarkace dai iri iri. *TULUR* Tulur a Kanuri yana nufin bakwai. Shi tulur a auren Kanuri kuma yana nufin zaman bakwai da mace ɗaya ko biyu suke yi a gidan amarya na tsawon kwanaki bakwai. A wannan zaman waɗannan mata zasu dinga ma Amarya share_share girki, wanke_wanke da dai sauransu, ita kuma zata samu damar kula da mijinta. Bayan kwanakin sun cika ango yana yiwa waɗannan matan kyautar Atampa da sabulai da turare, wani ma harda ƴan kuɗaɗe. *KSAI LEWA* Gaisuwar iyaye. Ana yinsa ne a washegarin ɗaurin aure, inda ango da abokanshi zasu kai ziyarar gaisuwa zuwa gidan iyayen Amarya, tare da godiyar bashi ɗiya da'akayi. *KAULU* Wannan al'adar angwaye kaɗai ta shafa, washe garin ɗaurin auren shima akeyi. Karkashi ake damawa da ruwa, sai mahaifin Ango ko ƙanin mahaifinshi, wani lokacin ko mai gidanshi na wajan aiki. Sai a shafe hannayenshii da wannan ruwan damammen karkashin. ( Wannan fata ne, na duk abinda zai samu ya yauƙaƙa, ma'ana yayi albarka) *GANGA KURA* Shi kiɗan gargajiya ne, wanda dangin ango da dangin amarya, ke haɗuwa a waje guda, su rausaya a tsakani, tare da yima juna liƙi. Waɗannan al'adun suna daga cikin jigon da ya sa Kanuri suka fi ƙabilu da dama juriya wajan riƙon aure. Sabida kuɗaɗe masu tsokar gaske ake kashewa wajan hidimar biki, hakan yana daga cikin dalilin da yasa sauran ƙabilu suke tsoron auren matan Kanuri, sabida tsadarsu. Kuma hakan yasa matan kanurai sai sun gansame suke aure. Domun samarin ba ƙaramin tanadi suke shafe shekaru suna yi ba kafin akai ga yin aure. Wannan yasa ba'a saki a cikin ƙabilar Kanuri sabida tsadar da aure yake dashi. Namiji na tunanin in ya saki matarshi, sai ya kuma kashe miliyoyi kafin ya samu nasarar mallakar wata macen. Dukkannin wannan al'adun sai da aka gudanar dasu, waɗanda ake gudanarwa a tsakanin ango da amarya ne kaɗai, ban samu halarta ba, kasancewar nawa gogan yayi mun nisa. Amman Ba Bakura yayi rawar gani, dukkannin wani abu da ango ke yi, saida yasa akayi mun. Hajja Gana, itama tayi ƙoƙari sosai a nata ɓangaren. Ba Modu shima ya kashe kuɗi sosai a cikin akwatin Ango, kasancewar su Ba Bakura sunyi ƙoƙari sosai a kaina, shima saiya zage, ya zuba tsadaddun kaya na alfarma. Ya danƙa akwatin a hannun Mama Gana. Bayan an kai ko wacce Amarya gidanta. Munsha kukan rabuwa da juna sosai, amaren su Bulama ƙarami suma duk an kakkawosu. ni kuma washe gari ake shirin kaini nawa gidan, jina nake yi wani sukuku, a daren ranar da ake gobe zamu tafi, Ya Innana ta mun nasiha, tare da ɗorani akan wani karatu, na iya jawo hankalin miji zuwa gareka, ta bani wasu turaruka haɗi na musamman, tace in adanasu, da sun ƙare inyi kiran waya na sanar da'ita, za'a turamun da wasu, ranar kusan raba dare nayi ina kuka. Motoci uku Ba Bakura ya tada na ƴan rakiyana, motar kaya tuni tayi gaba. Ina gurfane a gaban Ba Bakura, sanye nake cikin lafaya ja jawur, mai adon Golding, wuyana da kunnena maƙale da ƙaramar sarƙar gold wacce aka saka mun a cikin kayan lefe. Ƴar duma duma ce ni sosai, dan nafi kowa ƙiba a gidan. Gajerace ni, kuma baƙa wulik, dan abune mai matuƙar wuya ka ga farin kanuri. Hancina gajerene, kuma mai ɗan faɗi, fashin goshi ne, tunda daga goshina har ƙarshen hancina, da wasu zane bibbiyu masu faɗi a gefen fuskata, haka yake a zane a fuskar ko wanne ɗa a cikin gidan. Su Ba Bakura ko fuskarsu babu masaka tsinke da zane, nasu irin na asalin kanurai mazauna tsakiyar ƙauyene. Ina da gashi mai laushi, da ɗan tsayi dai_dai misafi na zahiri, dan jelar kitsona bata wuce tsayin wuyana ba. Idanuna manya ne, bakina kuma ɗan madaidaicine, mai kaurin labɓa leɓennan baƙiƙƙirin dashi, ina da wushirya a tsakiyar haƙorana da suka kasance mai ruwan madara. Kirjina cike yake da mama, amma bani da tudun madaunai, bani da shape asalima nafi girma ta sama ba ta ƙasa ba, saɓanin mata masu diri da suka fi faɗi ta ƙasa. A taƙaice bana cikin sahun kyawawan mata sam na kaina na sani. Kuma nasan ni mummunace sai dai Alhamdulillah na samu ilimin addini mai zurfi. Ba Bakura "Mama Gana, ga Yahanasu na danƙata a hannunki, ki danƙata a hannun Bulama Babba. Ki sanar mishi inya wulaƙanta Yahanasu, tamkar mu iyayenshi ya wulaƙanta, kuma bazan yafe mishi ba. Ki zauna da'ita ke da Yanunu kuyi mata Tulur ɗinta, ( zaman bakwai) Bana son a tauyeta. Sannan ki kaita gidan Abokina Alh Munka'ilu, zan baki number wayarshi, zai samo mata aiki, gidanshi yana nan ta wajan SULTAN BELLO Babban masallacin juma'a na Kaduna. Yahanasu Allah ya zaunar dake lafiya a gidan aurenki, Allah ya miki albarka bisa umarninmu da kika bi, nima zanzo da kaina inga ɗakin ki in sha Allah. Motar da zaki shiga a kaiki a ciki, na mallaka miki ita, ki dinga zuwa wajan aiki da'ita. Kuje Mama Gana" Fitowa akayi dani, sai zagaye akeyi dani wajan iyayena maza, kowannne cikinsu kalmar haƙuri da juriya dai suke ta faman nanata mun. Daga bisani muka shiga mota, mu ka ɗau hanyar Kaduna. Tafiya ce wacce bazan taɓa mancewa a cikin tarihin rayuwata ba, kamar yadda yau ta kasance ranar da babu wani abun da zai zo ya gogemun ita a zuchiyata. Damuwar da nake ciki, ya wuci gaban gwatance ko misalin da mai karatu zai fahimta. Idanuna a buɗe suke, ina kallon jejunan da muke wucewa da gudu, a zahiri inka kalleni abunda zaka yi tunani kenan, amman a baɗini kuma, tunanin rayuwar da zan tsinci kaina a ciki nake yi. Yanzu har aka gama shagalin bikinnan Babu Bulama Babba, babu labarin ya bugo waya, kuma yasan da zaman bikin yaran gidan, dan bikine da aka tsaida lokaci shekara guda daya wuce. Kuma tun daga lokacin da aka sa bikin, aka sanar mishi. Ajjiyar zuchiya na sauke, na dawo da dubana cikin motar, Hajja Fati ce a gefena da jaririyarta a hannu tana bata nono, sai Mama Gana a kusa da'ita. A gaban motar kuma, Bulama ƙarami ne yake janmu, suna zaune shi da Yanunu, sabida tsabar soyayyar ƴan uwantaka ne yasa ya baro filleliyar amaryarshi, yake son rako ƙanwarshi. Hawayene ya gangaro a kumatuna. Allah sarki gidanmu me daɗi, wani sa'in haka zamu haɗu a babban falon Ba Bakura mazanmu da matanmu, mu zuba biski miyar kuka a babban farantin silver maita ci, ana barkwanci, maƙaryata irinsu Bulama ɓaki suita bamu labaran ƙarya, ana dariya. Surutattun ciki kuwa dama ni da Yaguji ne, baki kamar na cakwaikwaiwa, haka za muita faman zuba. Murmushi ne ya suɓuce mun a lokaci ɗaya. Haka mukaita shatata gudu kamar me. Bamu muka tsaya ba sai a wata tasha a Bauchi. A tashar muka fito akayi Sallah, Wakil ya sai mana balango da gurasa, da abun sha. Muka kuma ɗaukar hanyar Kaduna, Ta Bauchi muka ratse muka bi, sabida hanyace samɓal mai kyau, hanyar samunaka a dagargaje take, duk da munyi zagaye, amman tafiyar tayi sauri, misalin ƙarfe biyar ɗin yamma sai gamu a Kaduna. Bulama ɓaki ya juyo yace. "Mama Gana, nifa na mance layin gidan Bulama Babba fa, sau ɗaya na taɓa zuwa. Mama Gana tace. "Hmmm ai dole kowa ma ya mance, ni kaina bansan layinba. Ka kira Wakil a waya, su shige gaba mubi bayansu, in ya san gidan. Suna cikin Magana sai Mama Gana tace. "Shikenan ma, kaga ga motar kayan Yahanasun ma a gabanmu, su Bagulaji ne a ciki, bisu ita ai duka haihuwar matar Bulama Babban tazo." Gabana ya tsananta faɗuwa, muna tafe tiryan_tiryan har muka shiga Kakuri maƙera, kwanar layin BABBAN DODO muka shiga, layin masallacin idi. Anguwace wacce ta tara ƙabilu iri daban daban, ta kuma tara masu kuɗi da talakawa a waje guda. A bakin wani ɗan madaidaicin gidan ƙasa muka tsaya, masu motar kaya sai faman hon suke. Mama Gana ta fita a cikin motar, ni dai da idanu na bita. "Me gadi ya kanaji ana hon, amman kaƙi ka buɗe mana get" Cewar Mama Gana kenan, dan ta'isa wajan ta samu mai gadin na tambayarsu daga ina" "Hajiya kiyi haƙuri dan Allah, da gani nasan ku ƴan uwan oga ne, amman uwar gida tace mun duk wanda yazo a irin ranakun asabar da lahadi, kar in barshi ya shigar mata gida, sabida ranar hutunsune" Cikin Faɗa Mama Gana tace. "Dalla rufa ma mutane baki, dokar banza, muna iyayen nashi? Wakil ku bani waya in kira shi Bulaman" Wakil yace. "Mama da shi mai gadin ya kira a wayarshi, in yaso ya baki, ko yaga number na ba ɗagawa zaiyi ba" Ai nan ta soma ruwan jarabar, ita mai gadi kawai ya buɗe mata get mu shiga. Ni kuwa ina daga cikin mota sai hawaye. Da ƙyar Ya Bagulaji ta shawo kan Mama Gana ta yarda aka kira Bulama Babba a wayar mai gadi. Wayarshi ya ɗaga ya kira Bulama Babba, ringin biyu abun mamaki ya ɗaga. "Mai gida, kana da baƙi a bakin get, ƴan uwanka ne, duk zanen fuskokinsu irin naka ne, ga kamanni." Bamu ji mai Bulama Babba yace ba, mai gadin yace ma su Mama Gana" "Yace yana zuwa" Jigum_jigum duk suka yi a wajan. Bulama Babba: Da mamaki na miƙe tsaye, na ajjiye Maryam da take hannuna akan doguwar kujera. Zubaina ta kalleni tace. "Kuma Abban Maryam kana ganin ba gidan da suke nema bane suka rasa ba? Ko kana tunanin danginka zasu shawo tafiya tun daga Damaturu ba tare da sunyi kiran waya ba?" Kai na girgiza mata nace. Bana tunanin sune, duk da yace akwai kama, kuma suma duk suna da zane a fuskokinsu, bari dai inje in duba" Ina kaiwa nan, na nufi ƙofar fita, a Guje Bawa Ba Bakura Ƙarami ya biyoni. "Abba zan bika" Kallon yaron nayi, ina jinjina irin tsananin kamanninshi da Ba Bakura takawaranshi. Bance mai komai ba, muka nufi get, ina fitowa nayi arba da ƴan uwana gudan jinina, da iyayena. Farin cikin daya ziyarci zuchiyata ya wuce gaban a musalta, sai washe musu baki kawai nake yi, in kalli wannan in kalli wancan." "Kaga kasa me gadi ya buɗe mana get mu shiga daga ciki ko, amman in fa matar taka zata baka damar yin hakan" Maganar mama Gana ta dira a zuchiyata, naji zafi ainun. Ni banga laifin Zubaina ba, banga dalilin da yasa ƴan uwana ke ganin laifinta ba. Motocin da naga ni a ƙofar gidan, abun ya matuƙar ɗaure mun kai ainun. Umarni naba mai gadi ya buɗe musu get, duk motocin suka shiga ciki, ina jaye da Ba Bakura Ƙarami, dubana yayi yace. "Abba waɗannan su suwaye?" Ni kaina naji kunya da wannan tambayar da Ba Bakura ƙarami yaimun, kafin in bashi amsa, Mama Gana tace. "Allah wadaran naka ya lalace, yaronka ɗan shekara takwas, bai san ɗanginka ba, to yaushe ka kaisu suka shiga dangi balle su saba damu. Albasa dai batai halin ruwa ba. Dalla shige gaba ka nuna mana hanyar shiga cikin gidan, tun kafin ranka ya ɓaci" Da sauri nayi gaba, suka bi bayana. Duk da jarabar da Mama Gana take yi, bai hanani jin daɗi da sanyin ganin ƴan uwana, sunyi gayyar kawo mun ziyara ba. Amman dai naji kunya, dan ƙannena sun kikkira wayata har sun gaji sun watsar dani, sabida bana ɗagawa. Da sallama na shiga falon. "Mama Gana Ya Bagulaji bismilla ku shigo, ah Yahanasu ƴar lukuta, dama har dake?" Na tambaya cikin farin ciki. Cikin zumuɗi na soma kiran Zubaina, sabida mun shigo bata falon. Maryam zo ga Babanninki" A guje Maryam tazo, amman Wakil yayi yayi da'ita taje taƙi. "Ku shiga ga waje ku zazzauna. Bari in kira Zubaina" Zama suka yi, sai ƙarema falon kallo suke yi, tsugunnawa nayi cikin fara'a na soma gaishesu ɗaya bayan ɗaya. Su kuma yara_yaran suka gaisheni. Mama Gana ya su Ba Bakura, da Hajja, da su Ba Modu?" A fusace tace. "In kana son kanka da arziki karka kuma tambayata kowa, ba abunda muka zo yi ba kenan. Mandiyar bata jimu bane, data kasa zuwa ta gaishe da iyayen mijinta? Ko da yake ina muka samu darajar hakan a wajanka, balle ita." Murmushi nayi na miƙe, na nufi ciki. A kitchen na samu Zubaina a tsaye ita da ƙannenta mata biyu, da muke riƙonsu. Asiya, da Nafisa. Zubaina ta dubeni tace. "Wai shin suwaye haka na gansu bataliya guda, tun daga tsakar gida nake ta faman jin yare? Kuma dana leƙa sai naga motoci, harda motar kayan ɗaki? Da fara'a a yalwace a fuskata nace Ke dai bari kawai Zubaina. Asiya ku kaima Baƙi ruwa da jus maza. Ku ɗauki ruwa catoon biyu, lemo ma haka. Dawo da dubana nayi kan Zubaina nace. Zuba musu dambun kajinnan in kai musu" "Amman tambayarka nake yi su waye ko?" Iyayenane da ƙannena suka zo ganinmu, ina tunanin ko dan sun jini shirune, basu san aiki bane yai mun yawa ba. Nafi shekara biyu ban leƙa Damaturu ba. Ki yi maza kizo ku gaisa, bari in kai musu dambun." Kular da aka zuba dambun kajin na sura dukanta, na kwashi kwanuka na fita na bar Zubaina da sakakken baki." Zubaina: Kusun uwa ni za'a kawo ma iskanci ni da gidana? Yanzu meye abunyi, yaya zanyi da baƙinnan, Allah yasa ba zuwa suka yi dan su tuni asirina ba. Hmm amman bari in kira Mabaruka" Zufar data tsattsafomun na sharce, cikina tun shigowar wannan baƙin ya juya, tsabaragen tashin hankali. Ɗakina na wuce da sauri, na zari waya na kira Mabaruka. "Kofur Zubaina ya gidan, yau kece akan layi ran Sunday, ko dai oga baya gidane. Cikin ƙasa ƙasa da murya nace. Mabaruka ina cikin matsala babba, dangin Bulama ne suka zo daga Damaturu har mota uku, mazan su da matansu. Ni bansan ma ta yanda zan iya tunkararsu ba, kinsan fa sun tsaneni, sun riga sun gane ni na raba Bulama dasu. In ban rabashi da wannan bataliyar ɗangin nashi ba, yaya zanyi ma. Duk fa albashin daya samu a kansu yake ƙarewa, bini bini kuma gyaji yace zashi Damaturu, almurar uwarshi kuwa, ko da yaushe a cikin kiranshi take, in ma bata kira ba, shi zai kira. Amman tunda naiwa tubkar hanci wallahi ƙawata ko Damaturu na ambata, sai kiga yanayinshi ya canja. Muna fa zaman zamanmu suka tawo bataliya guda" Mabaruka tace. "Ciɓiri nannagi ƙawata, ai kuwa mai ƙwatarki a hannun waɗannan kanuran sai Allah. Shawara, ki sauke kanki kiyi musu tarbar mutunci, danki shafe zarginki da suke yi a zuchiyarsu, shima ko ba komai zaki ƙara daraja a idanunshi, ƙawata ke fa kika koya mun kissa, ni wajan malamai nafi ganewa, amman ai kissa na wajanki" Dariya nayi, na share zufar data ɓata mun fuska, nace. Ai ƙawata, wallahi ganin yawansu ne ya firgitani, amman kin ɗaurani a layi, sai munyi waya, gashi can sai faman kwaɗamun kira yake yi, kinsan baya ƙaunar in matsa a kusa dashi" Sallama nayi da Mabaruka, tare da sauke ajjiyar zuchiya. Da sauri na amsa kiran Bulama, nayi falo da sauri ina ƙaƙaro murmushin da kallo ɗaya za'ai mun a gane na bogi ne. Zuchiyata har wani tafarfasa take yi. A gefen Bulama na rusina, kamar yadda na ganshi a rusine. Cike da fara'a na soma gaishesu muryata na rawa. Amman ɗaiɗaiku daga cikinsu ne ma suka amsa mun, ƙannenshi kuwa, ban kalli kowa ba, jira nake su gaisheni, amman naji shiru. Kin sansu ai duka na sani, Hajja Fati da Yanunu ne kawai baki sani ba. Yanunu ƙanwar mahaifiyar su Yahanasu ne, Hajja Fati kuma ƙawar Ita Yahanasunce." Dariyar yaƙe nayi nace. Ayya sannunku da zuwa, gaskiya kun shawo hanya, bari in shiga kitchen su Asiya su kama mun muyi abinci, in yaso Nafisa saita gyara musu BQ." Da sauri na fita a falon har ina tuntuɓe, tsabaragen ruɗewa, babu komai a idanun dangin Bulama sai tsagwaron tsanata. Wallahi nima na tsanesu sosai, kuma in dai ina numfashi Bulama ya rabu dasu kenan, dan bazai ƙare a kansu su kaɗai ba. Su Asiya na tarar a kitchen suna surutai. "Cab Anty wannan baƙi haka cikin gida, sai kace wasu marasa hankali" Cewar Asiya kenan. Baki na taɓe nace Kinsan ƴan ƙauye akwai rashin kan gado. Yanzu dai ku ɗaura farar taliya, ku zuba ma mayunwata a kula, ku fito da miyar kajinnan a firgi, ku tsuga ruwa dan tayi auki, da kun gama sai in kai musu." Bulama: "Waini Bulama Babba naga wasu mata masu ƙirar samudawa a gidan naka, harma sunfi hamshaƙiyar matar taka girma, su kuma daga ina? Da fara'a nace. "Ya Bagulaji ƙannen Zubaina ne fa, ni nake riƙesu suna karatune, sabida ɗawaikiya tayi ma mahaifiyarsu yawa, Babansu shekara guda kenan da rasuwarshi, shine nace su matan bari in riƙe su, in basu ilimi, in sun samu mazajen aure sai in aurar dasu, su kuma mazan suna can gidansu Zubainar." Mama Gana tace. "Ba shakka fa, wayyo shugaban ƴan jin ƙai na ƙasa da ƙasa sannu. Lallai Bulama Babba matarka kwai makira, ta rabaka da iyayenka da danginta. Amman ta saki jiki sai hidima kake da danginta ko? Sau nawa Ba Bakura yayi kiran wayarka baka ɗagawa, uwarka harta haƙura ta dena kiranka. Babu ruwanka da ƙannenka, Babaninka ma haka. Bikin ƙannenka da akayi, haka akaita sa idanu, amman Bulama Babba daga kai har matarka babu ku, babu wasiƙa, sabida iskanci da wulakanci. Kamar mu iyayenka, shine wai take cewa a share mana BQ sabida ƙasƙanci, duk faɗin falonnan baku da ɗakin saukar baƙi kenan?" A ɗarare nace Mama Gana sabida tana tunanin zaku fi sakewa acanne sabida ku surukanta ne, shi yasa. Kuma anan ɗin babu ɗakin baƙi, ɗakuna ukune a falon. Nawa, saina ƙannenta, da nata shikenan" "Uhm ba shakka. Ai tunda kai kana da naka, suma tsintattun magen suna da nasu, ta kwana gidan sauƙi." MRS BUKHARI CE *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 5 SANARWA SANARWA SANARWA. ZAKU UMMU MAHEER MISS GREEN SHIRU BATA POSTING ƊIN LITTAFINNAN NATA MAI SUNA ZULFA, WANDA YAKE ƊAYA DAGA CIKIN TAWAGAR GAWURTATTU UKU. AYI MATA AFUWA, WAYARTA CE TA SAMU ƊAN MATSALA, DA ZARAN TA GYARA ZAKU JITA. MUN GODE DA ZAƁAR GAWURTATTU UKU. BULAMA BABBA Yahanasu, da Fanda, da Hajja Fati. Sai ka nuna musu ɗakin naka su kwana a ciki. Mu kuma iyaye, sai a kaimu ɗakin tsintattun mage mu kwana acan. Su Bulama ƙarami sai ka kaisu BQ ɗin su kwana acan. Tunda kai baka lissafi darajarmu ma baka sani ba." Jikina a mace yake da maganganun Mama Gana, nasan dole ta kasance cikin fishi, kuma dama itan mai zafi ce. Iso nayi ma Su Mama Gana ɗakin su Asiya. Su kuma su Yahanasu na kaisu ɗakina, na fito naja su Wakil zuwa BQ. Wai wannan kayan da na gani a mota fa Bulama ƙarami na wanene, daga ma ina kuke naga kamar biki zaku je ko?" Bulama ƙarami nake tambaya. Yace dani. " Ba biki zamu je ba, daga Damaturu kai tsaye nan muka tawo, mu kam gobe da asussuba zamu koma, Mama Gana da Yanunu kaɗai zamu bari anan. Su Baguji sunce a gaisheka. In an kira wayarka Bulama Babba baka ɗagawa sam, haka watan can daya wuce Ba Bakura yaita kiranka baka ɗaga ba, baka kirashi ba kuma. Wai akwai wani laifin da mu kayi maka ne daya sa ka guje mu? Bamu saba da kai a haka ba, tun muna yara kake kula damu, kai ke nan kullum a cikin goyanmu" Hawayene ya gangaro a kumatun Bulama ƙarami, Wakil kuwa idanunshi sun kaɗa sun zama jawur dasu, kamar zasu zubo da ruwa. Kasancewarshi mai taurin zuchiyane yasa kukan bai zubo mishi ba. Jikina yayi sanyi sosai, bani da amsar tambayar ƴan uwana, kuma wallahi ina tunowa dasu duk kwanan duniya, aikine da hidimar Zubaina da ƙannenta yake sha mun kaina. Kuyi haƙuri dan Allah Bulama ƙarami, da wakil, in sha Allah zan dinga kiranku, kuma ku ba su Ba Bakura haƙuri, suci gaba da yi mun adda'a. Dana samu hutu zan zo in sha Allah. Ya su Ba Modu, da Ba Baana, ina Ya Hajja Gana, yaya su yagaji suke, su Fanna? Haka naita jero tambayar ƴan uwana ina tuno da fuskokinsu. Hawaye ya cika idanuna tab. Wakil bari in barku kuyi wanka, sai muje masallaci, magriba ta kawo kai, kafinnan an gama abinci." Da murna na baro ɓangaren saukar baƙi zuwa cikin gidan. Asiya na tarar a falon tana kunna turaren tsinke, Zubaina kuma, fitowarta daga kitchen kenan hannunta ɗauke da ƙaton farantin silver cike da kayan abinci. Da sauri na ƙarɓeta na ajjiye farantin silvern a ƙasan kafet. "Am Dan Allah Bulama taya ni kawo musu ruwa, so nake gudu_gudu inje in yo wanka, in anyi sallah sai in kirasu suci abincin. Suna BQ ɗin dukkansu ko? Asiya ta share duka ɗakuna biyun dake ciki." Murmushi nayi mata. Sannu da aiki Maman Maryam, Allah ya baki lada, kin shiga aikin baƙi ba shiri." Dariya kawai tayi mun, amman da dukkan alamu akwai wani abun da akayi mata wanda ya ɓata mata rai. Ban dai ce komai ba akan wannan. Ai Mama Gana taƙi fur su je BQ, Su Wakil ne kawai suke BQ. Mama Gana suna ɗakin su Asiya. Su kuma yaran matan suna ɗakina. Kiyi haƙuri da sha'anin ƴan uwana, fitina garesu, musamman Mama Gana fitinanniyace ta gaske." Wucewa nayi ɗakinta dan gabatar da alwala, naji ana kiraye kirayen sallar Magriba, a tsaye na bar Zubaina bakinta a wangale." Zubaina: Kusun uwa, kai ya sa ƙannen miji akan gadon mijina, kuma dan kuturun wulaƙanci shi hakan bai dameshi ba? Tabb lallai Bulama yana wasa da ni wallahilƙudrat ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, nasan da wanne kalar ƙulunboton suka zo mun ma Ga uban kaya da suka shigo dashi cikin mota, kona uban meye oho, fuuuu na bi bayan Bulama." Yahanasu: Jikina a mace murus yake, tsoro da fargabar da nake ciki a bayyane yake. Ɗakin Bulama Babba na bi da kallo, lallai wato Bulama Babba haka ya yi kuɗi mu bamu da masaniyar hakan. Tabbb abun mamaki baya ƙarewa a duniya, a rayuwa da mun ɗauka Bulama Babba shi zai maye gurbin iyayen mu bayan ƙasa ta rufe idanuwansu. Sai gashi tun ƙasar bata rufe idanun nasu ba, yasa ƙafa yayi fatali da ƴan uwanshi. Ga matarshi da gani yana tsantsar sonta, dan sai haba_ haba yake yi da'ita. Zubaina kyakykyawar macece, mai duri sosai, farace fes wanke hannu ka taɓa, gata da hanci, gata da idanu masu kyau, ta kere mun gudu sosai ta ko wanne fanni babu wani abu dazan nuna mata, gata da kyan jiki, ba kya ce ita ta haifi yaranta ba. Hmmm na sauke ajjiyar zuchiya, tare da kallon ƙofar ban ɗakin da Hajja Fati ta fito, alwala ta ɗauro. "Yahanasu wai har yanzu uban tunanin kike yi ne? Karfa kije ki jefa rayuwarki a matsala. Haba Fanda ya kamata ki dinga bata baki ai ko?" Fanda ta dubi Hajja Fati tace "Kinsan Allah jikina yafi na Yahanasu macewa, dauriya kawai nake yi. Ke da ganin Bulama Babba da matarshi, kinsan da wuya matarshi ta bari ayi zaman lafiya. Ke kinga yanda zuwanmu ya ruɗa ta kuwa, jikinta da muryarta fa har rawa yake yi, sanda take gaisawa dasu Ya Bagulaji. Kina ganin data miƙe bin bayanta yayi da kallo bai dawo da hankakinshi kanmu ba har sai da ta ƙule. Yahanasu ni abunda zan faɗa miki shine ki yi haƙuri ki karɓi zaren ƙaddara ki saƙa a duk yanda kalar zaren yazo miki, me haƙuri shi ke dafa dutse har yasha romonshi. Ki riƙe adda'a, ki kuma riƙe azumin monday da alhamis kamar yadda kika taso kika samu Ya Innana tana yi. Sauran shawarwarin zamu baki, ki bari muci abinci, muyi wanka yau zamu raba dare ni da Hajja Fati muna miki darasi akan aure, dan kisan asalin girman zamantakewar aure, labari kawai kikeji, ƴan mata basa fahimta, da dama hangen dala ƴan mata suke ma rayuwar aure, musamman ma waɗanda suka auri masu mata, ki tashi kiyo alwala " Miƙewa nayi, bance komai ba, na shiga bayan gidan na ɗauro alwala na fito, Fanda ta shiga. Hajja Fati tana zaune a ƙasan kafet tana waya, da dukkan halamu da mijinta take waya. Tsuru nayi mata da idanu, ina kallon yanda take sharar ƙwalla. "Shikenan Baban Nasiba, tunda dai haka kace, kuma baka son in fadi gaskiya shikenan. Ni bani da kuɗin motar dawowane, shi yasa ma kaga ban dawo ba. Kuma nayi maka magana kace, in iyayena sun gaji da zamana su biya mun in koma ɗakina. Kasan Mama fama suke suma da kansu, nera biyar bana magani. Amman inna koma Damaturun zan nemi kuɗin mota in dawo" Galala ta sauke wayar a kunnenta. Kuka mai sauti ta fashe dashi. Cike da tausayinta nace Kiyi haƙuri Hajja Fati, ai da kin faɗa mun baki da kuɗin mota, dana baki, bai kamata ki dinga sa damuwa a ranki ba haka" "Hmm Yahanasu bazaki gane bane, kar Allah yasa rayuwarki ta ɗanɗani azabar ɗa namiji, ke maza da yawansu ko azzalumai ne. Mugun miji Allah ya haɗa ni dashi, mara tausayi, da tunani. Amman ba komai, bazan bari ciwon zuchiya, da hawan jini su kasheni a banza ba." Tana kaiwa nan, sai naga ta miƙe da sauri ta ɗauki jakar hannunta, ta ɗebo wasu magunguna, fin guda goma ta zuba a bakinta, tabi da ruwa. Tambayarta nake shirin yi, sai Fanda ta fito daga banɗaki. "Kukan wa nake ji ina bayan gida?" Ta tambayemu tana tsatsaremu da idanu. Kukan Hajja Fati ne, ita da Baban Nasiba ne fa" Kai ta kaɗa tace. "Allah ya kyauta, maza duk yanda ka kai da kyautata musu, sai sun gano inda ka gaza, Allah dai ya bama mata haƙuri da juriyar shanye ƙunci da hawan jinin namiji. Mu yi Sallah muje mu samu su Mama Gana, ni yunwa ma duk ta bi ta isheni." Hijabai ko waccenmu ta zura, muka soma sauke farali. Kofur Zubaina: Cikin ɓacin rai da huci na sameshi a cikin ɗaki, fitowarshi daga bayan gida kenan. "Wai Abban Maryam da gaske kake yi, ƙannenka sabida raini a ɗakinka zasu kwana? Bari kaji wallahi baza su kwana a ɗakinka ba, bazai ma yiwu bane. In ba dai da wata manufar suka zo ba, me yasa zasu kwanta a ɗakinka. Kenan ni bani da wani mutunci da ƙima a idanka ma kenan ko, to su Asiya ina zasu kwanta su?" Kukan munafurci na fashe dashi, duk da inajin mugun ɗaci a zuchiyata. Naso danne baƙin cikina na ganin danginshi, amman sai da suka turani har zuwa bango hankalinsu ya kwanta. Tsattsareni da idanu Bulama yayi, yana nazartata. Cikin kissa na isa gareshi na faɗa ƙirjinshi, ina shessheƙa. Sabida Allah fa Bulama, ina laifi dan sun sauka a masaukin baƙi su ƴan matan, ɗaki biyu ne da falo fa acan. Ai bai kyautu ace a ɗakinka zasu kwanta ba. A gadon fa muke kwanciyar aure, kuma kawai sai ƙannenka su kwana a kan gadon? Haba Bulama na. Sannan ni abinda ban gane ba, na gansu da sababbin kayan ɗaki cikin mota, wai daga ina suke, kayan kuma na waye?" Duk wannan maganar da nake yi, cikin karya harshe nake yinta, ko da asiri sai an haɗa da kissa, duk da ina da tabbacin Bulama bazai taɓa ganin aibuna ba, domun a hannu yake ram, bashi da tsumi bashi da dabara sai abunda nace mishi shi yake aikatawa. Hannuna kuwa yaja zuwa bakin gadonmu. A cinyarshi yaimun masauki. Dubana yayi da kyau, harda murmusawa yace. "Iya rigima, yanzu akan wannan matsalar shine harda kuka? To a mayar da wuƙar, ni kaina sanda Mama Gana tace wai su Yahanasu su kwanta ɗakina, naji irin abun bai dace ba. Amman dai na barsu sun shigane a lokacin sabida in kauce faɗan Mama Gana, wallahi duk ta bi ta fitineni. Zasu koma BQ su ɗin, amman Mama Gana in ba so kike ta tara mana jama'a ba, a barsu a ɗakin su Asiyan shikenan kukan ya ƙare? Su Asiya sai su kwanta a nan ɗakin, ke kuma sai ki kwanta a ɗakina" Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, nayi Murmushi mai cike da kissa tare da shafo gemunshi nace. Shikenan kuwa, ai kasan ina kishin shimfiɗar mijinane, sirrinmu ne fa, ko kusa bai dace ƙannenka su hau kan gadonmu na sunna ba. Sai maganar kayan da suka tawo dashi a mota fa?" Na ƙagauta inji na meye kayan. Su kam bansan na meye ba gaskiya, dana tambaya ma sai Mama Gana tace wai sai da safe naji. Uhm bari muje masallaci da su Bulama ƙarami saina dawo" Miƙewa yayi ya fice. Ƙugu na riƙe tare da bin bayanshi da uban harara. Hmmmmm Bulama kenan. Karen haukane ya cije ni da zan bar ƙannenka su kwana a cikin ɗakinka? Kalan suje su yi mun birne _birne, ko su tono mun nawa binne_binnen da nayi. Tabb lallai ma waɗannan to wai me suke nufi da nine wai?" Tsaki naja mai ƙarfi, na shige bayi, wanka nayo tare da ɗauro alwala na fito. Asiya da Nafisa ne suka shigo rai a dagule. Da kallo nake binsu, ina son jin meke faruwa. "Wallahi Anty kiyi ma dangin mijinki magana fa, ni wallahi zan ci uwar tsohowane babu abunda ya dame ni. Dan na fita zafin kai fa. Sun zo sun cika ma mutane gida da ƙauyanci, sai yare suke ta mana munafukai" da sauri nace. Wai meya haɗaku da su ne Asiya?" "Daga shiga ɗakinmu fa. Muka same su sai faman zaginki suke yi. Shine fa wata shegiyar tsohuwa mai bakin aku ta daka mana tsawa, wai mu fita mu basu waje, an turomu jin gulma. Ke ki ji fa, naji tana cewa wai Abban Maryam ɗin zai shigo ya sameta ne" Kai kawai na shiga jijjigawa, ina ta'ajibi. Baƙin ciki tare da neman tudun dafawane ya hanani magana sam. Zama nayi a bakin gado hannuna riƙe da haɓata. Wato ma zagina da suke yi a Damaturu bai ishesu ba, har sai sun zo gidana sun zageni, sun hanani rawar gaban hantsi ko? Da kyau, zanyi maganinsune ki barni dasu kawai dani suke zancan. Ku zauna bari in yi Sallah. Maganganu cunkushe a zuchiyata nayi Sallah, na sake kayan jikina daga atampa, zuwa doguwar rigar lace, hoda fara kawai na murza a fuskata. Ina zaune a gaban mirror Bulama Babba ya shigo "Kune anan Asiya, yau su Maryam sunyi muku tawaye ko, sun shiga dangi? Dubanshi nake yi, ina karantar yanayinshi, sai wani murna yake yi da ganin ƴan ƙauyen danginshi, cike da kissa nace. Dan Allah ka ɗan shiga ɗakin su Asiya, ka fito musu da akwatinsu zasu je gida?" Da sauri yace. "Sabida me zasu je gida, ba nace su su kwanta anan ba?" E kace. To kayansu suka je ɗauka a ɗakinsu. Shine su Mama Gana sukaita zaginsu, wai ka tara karuwai a gidanka, sun rasa gane wacece ma mai gidan a ciki. Babban abinda banji daɗinshi ba ma shine, Baba da sukaita ƙundumama ashar yana kabarinshi." Na ƙarashe maganar ina hawayen kissa. Shi kuwa take yanayinshi ya sauya, daga farin ciki izuwa baƙin ciki. Idanunshi suka kuma yin ja, dama jajayene idanun nashi. " Kuyi haƙuri, zanyi musu magana. Babu inda zasu je, ina zuwa" Fuu ya fice. Na yi Murmushi kawai na share hawayena, na fita falon nima, dan in kalli bidiri" Bulama Babba: Cikin zafin rai na fita falo. Wakil da Bulama ƙarami na gani a zaune suna kiciniyar buɗe gidauniyar abincin da aka dire musu. Ƙofar ɗakin su Asiya ce tayi ƙara. Su Mama Gana ne suka fito, jin ƙaran ƙofar yasa su Fanda suma suka fito, duk suka shigo falon. Zubaina ma fitowarta kenan. Jikina sai naji yayi mugun sanyi, na zuba ma ƴan uwana abun ƙaunata idanu ina murmushin da bansan sanda ya subce mun ba. "Bulama sa ƴar dokar matarka ta kawo mana babban faranti, yau abincin tare zamu ci, a falonnan. Allah sarki Bakura yana shiga farin ciki, in yaga wani shashi daga cikin iyalanshi sun haɗe waje guda suna cin abinci a akushi guda. Dariyar farin ciki nayi, ko babu komai na shiga farin ciki jin furucin Mama Gana. Zubaina ɗakko mana faranti maza" Zama nayi a kusa da Wakil, ina zama Maryam ta dawo cinyata ta zauna. Zubaina ta kawo farantin Fanda kuma ta juye taliyar a faranti, ta kwarara miyar akai. Gabaki ɗaya muka matso tare da yin bismilla dan soma cin abinci. Salab naji abincin a bakina, abunda ban saba ji game da girkin Zubaina ba kenan, gashi miyar tayi ruwa, bata ko kama taliyar ma. Dubanta nayi, tana zaune ta jawo laptop ɗinta tana aikinta. "Wannan wanne irin girkine haka kamar an wanke kan mahaukaciya, haka kake gasuwa da irin wannan girkin? To ina ma zata iya girki tana aikin police, aikin da a tarbiyya na maza ne aikin, ina matar aure ina kama ɓarawo ko ɗan ta'adda." Da sauri na tari Mama Gana da cewa Kiyi haƙuri Mama Gana kefa uwace, karki zubar da kimarki a gaban yarinyar nan." "Dalla rufa mun baki shanyayyen kawai, wa yake neman daraja a wajan marar daraja irin azzalumar matarka? Ahir ɗinku damu wallahi Bulama. Kuma wallahilƙudrat in baka ce baƙar almurar matarka ta fice mun daga nan ba, saina ci ubanka Bakura" Da sauri na juya, muka haɗa idanu da Zubaina wacce fuskarta ta jiƙe sharab da ruwan hawaye. Laptop ɗinta ta ɗauka tare da wucewa kamar kububuwa. "Haba Mama Gana in hankali ya gushe hankali ake turowa ya nemo shi. Kai kuma Bulama ƙarami kuje ku siyo mana abinda zamu ci yinwa muke ji. Allah ya bamu lafiya, ni dai Bulama bazan sake tako ƙafata da sunan zuwa gidanka ba, ko mai zai faru da kai. Ka zauna da matarka kaita ma danginta hidima." Cewar ya Bagulaji kenan, Yanunu tace. "A haɗu ayi haƙuri dai, mu iyayene, mu kai zuchiyarmu nesa dan Allah, ke Gana kiyi ma Allah ki dena magana. Sannan shi Bulama Babban yaje ya nemo mana abincin da zamu ci, a bar mata abincinta." "Ai wallahi har in bar gidannan bazan sake cin abincin matarshi ba, ya san yanda zai yi damu, shashsha wanda baison mutunci ba. Albasa dai batai halin ruwa ba" Fuu Mama Gana ta shige ɗaki tana gama magana. Su Ya Bagulaji suka mara mata bayanta. Kaina ya ɗauki caji sosai, na dubi ƙannena duk ransu a jagule, Fanda da Yahanasu har hawaye suke zubarwa. Inason ƴan uwana bana son ganinsu a wannan halin. Dan Allah kuyi haƙuri ƙannena, ku dena kuka Zubaina bata kyauta ba, kuma zan yima tubkar hanci. Wakil ku zo muje mu kawo musu abinci, kar yinwa tai musu lahani. Tare muka fita, bamu daɗe ba muka shigo, Kaji gasassu da masa na siyo musu hilimi guda. Muka shigar musu da abun sha. Ni kuma muka wuce masallaci dan gabatar da sallar isha. Yahanasu: Bayan fitarsu Bulama Babba da kyar na dena kuka, sai da su Mama Gana sukaita lallashina. Ni tsorona Allah, tsorona su barni a wannan gidan, tare da makirar matar Bulama Babba. Mama Gana tace. "Dalla ki share hawayennan, tun yanzu so kike su gano logonki, wallahi in kika bari matarshi ta takura miki ke kika so Yahanasu. Kema fa mata ce, kuma bugu da ƙari ƴar uwarshi, kima saki jikinki, kafin in tafi saina tabbatar tsintattun magenan sun bar gidan, dan zasu iya haddasa muku fitina a zamanku." Nan sukai ta bani baki, ana haka su Wakil suka kawo mana abinci. Sai da mu ka yi sallah sannan Hajja Fati ta je kitchen ta ɗakko mana faranti muka baje kaji, da masarnan. Bamu ci ba har sai da su Wakil suka dawo sallah. A ɗaki muka ci, a faranti ɗaya, Bulama Babba sai Murmushi yake yi. Mama Gana wannan zaman saiya tuna mun da gida, lokacin ina ɗan sakandare, mama Gana kin tuno? Ni sai ince sai da su Wakil zanci abinci. Lokacin suna yara dan in ban mance ba, Su Wakil da Bulama ƙarami da Bulama Fari, da su Ahmada, da Dala duk dai yara yaran maza suna firamare, hanci duk majina. A lokacin su Yahanasu, su Fandau suna yara ƙanana, Fanna da Yabulu, da Ba'a kaka duk goyonsu ake yi su kuma a lokacin. Haka za'a zuba mana Buski da miyar kuka, muita ci. In an aikeni kai niƙa sai na goya Fanna ko Yabulu nake zuwa. Kafin a haifesu kuma su Yahanasu nake goyawa. Akwai wata rana da kare ya biyoni ina da goyon Yahanasu a bayana. Naje ɓarjin Masarar buski. Na ɓarar da masarar naita gudu, Yaha na bayana sai kuka take yi. Muka faɗa kwata, har kanta ya fashe, sai da akai mata ɗinki, bazan mance da wannan lokacin ba" Dariya muka saka dukanmu, Wakil yace. "Ni ina tuno lokacin da muke tsaiwa a bakin get muna jiran dawowarka, ka bamu biskit ko abincinka daka rage. Ahmada gashi da shegen kwaɗayi. Kai kuma kana zuwa sai ka tsugunna a gabanmu ka rarraba mana biskit guda guda" Bulama Babba yace. Lokacin sabida ku saida na dena kashe ko sisi a makaranta, biskit ɗin ku nake siya ma. Abincina kuma, rabi nake ci in kawo muku rabin. Abokina Jabir Dauda da mun sha kwanar layinmu, zai ce Bulama Bakura ga mayun ƙannenka can masu nacin tsiya suna jiranka" Dariya dukka aka kuma sakawa. Mama Gana tace. "Ai kaso ƙannenka sosai, mu a lokacin har mamaki kake bamu. A kwai lokacin da aka haifi Yahanasu, to tunda aka haifeta sai aka haifeta da shawara, ko idanu bata iya buɗewa. Ganin hakan sai aka riƙeta a asibitin. A lokacin kana wajena ni kuma nazo Damaturu sabida haihuwar Innana ɗin. Muna shiga da kaga Yaha da ƙarin ruwa a hannunta, sai ka fashe da kuka ka ƙanƙame Modu kana cewa. Ba Modu a cire mata tana jin zafi. A lokacin munyi mamaki sosai bana wasa ba, yanda ka tausaya matan shi ya bamu manaki" Ya Bagulaji tace. "Ai Baluma yayi abubbuwa sosai, tun yana yaro ƙannenshi suke jin maganarshi. Sabida duk abunda aka bashi su yake rabewa shi ya haƙura baki ɗaya ma. Ko wanne yaro ɗan gatan Bulama ne. Kullum a cikin saima su Dala tamaule yake. Kullum kuma in aka fita sai an ɓatar, amman bai taɓa gajiyawa ba" Munyi hira sosai, irin hirar da aka jima ba'ayi irinta ba. Sai kallon Bulama Babba nake yi. Sai nihaɗi da jin daɗi yake yi, tausayinshi ya kamani ainun. Gashi yanzu ya ware kanshi da danginshi, ko kira iyayenshi basa cin albarkacin haihuwa ya kira su, in ma suka kira, sai yayi ra'ayi zai ɗaga. Na ci alwashin da ƙarfin adda'a in Allah ya amince zai dawo da Bulama Babba ainihin Bulaman da kowa ya sani. Iyayenshi sai sun yi alfahari da wannan haɗin da suka yi. Ko banci ribar komai ba a zamana da Bulama. Inason inci ribar dawo da tunaninshi cikin iyaye da dangi, nayi wannan alwashin, ko da hakan zai zame mun ƙarshen numfashina. Zan sa Hajja gana farin ciki, da Ba Bakura. Domin su ɗin mutanene na gidi, kuma su suka tsaya ma rayuwarmu har muka kai matakin da muke kai. Ba Modu ya bamu labarin irin faɗi tashin da Ba Bakura yayi dan ganin ya tallafi rayuwarsu, ya ɗaurata akan turba ta gari. Alhamdulillah ya ɗaurasu bisa tartibiyar tarbiyya, ya basu ilimi, ya aurar dasu, ya basu wajan zama, ya ba ƴaƴansu ilimi. Madallah da babban wa irin Ba Bakura. Sai wajajen ƙarfe sha ɗayan dare Bulama yace zai je ya kwanta, gobe monday yana da zuwa aiki. Tare muka fito harda su Wakil. Muna shiga ɗakin Bulama Babba mu ka ga Zubaina a zaune akan wani teburi tana danna laptop. "Kun gama hirar ne? Cike da fara'a tayi maganar kamar ba ita bace ɗazu ta shige cikin gida fuu da hawaye a fuskarta ba. "Bulama bai faɗa muku zaku kwanta a BQ ba ne? Ai an riga an gyara muku ɗayan ɗakin" Fanda ta riƙo hannuna muka fita. A falon muka tarad da su Wakil, a tsayenma hira suke yi. "Lafiya kuma kuka fito Fanda?" Wakil ke tambayarmu. "Zamu je BQ ne ɗayan ɗakin mu kwanta acan kawai, mu jenku ko?" Fanda ta bashi amsa. Bulama Babba baice komai ba, mu kai mishi sallama a wajan mu dai muka barshi, yana bin bayanmu da kallo" Bulama Babba: Ajjiyar zuchiya na sauke, ban gushe ba har sai da suka fice a falon. Na rufe ƙofar falon, tare da kakkashe wutacen gidan. Ɗakina na nufa kai tsaye. Tana kan table ɗin da nake aiki, itama aikin take yi. Jin shigowata ne, yasa ta ɗago ta zuba mun idanu, tana mun kallon sai yanzu ka tuno dani. Sai tausayinta ya kamani, ta bar falo ɗazu tana kuka, Mama Gana taci mata fuska, amman ban sake waiwayarta ba. Ashe kina ciki, su Nafisa sun kwanta a ɗakinki, da su Maryam ko?" A ido a ido nake kallonta, tare da karantar yanayinta, Murmusawa tayi kawai, bata ce komai ba." Mrs Bukhari gidan ƙamshi ce. *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 6 takowa tayi har inda nake ina kwaɓe rigata, ta kama rigar ta taimaka mun na cire, kamar yadda ta saba yi mun a ko da yaushe. Ina samun kulawa fiye da tunani, Zubaina bata rageni tako ina ba. Zamanmu mai daɗine, kuma abun koyi, amman muna samun saɓani kamar yadda rayuwa take tafiya, kuma tana da yawan fishi sosai, da zaran wani abu ya haɗamu mara daɗi, take ƙaurace mun akan shinfiɗa, sannan duk tarairayar da nake samu a wajanta, ajjiyewa take yi a gefe, hakan ba ƙaramin galabaitamu yake yi ba dukkanmu, dan a ranar da muka shirya komawa muke yi tamkar mayu a shinfiɗa. Tunanina ta katse mun da cewa. "Ka shiga ka samu kayi wanka, na haɗa ma ruwan wanka, in ka fito ina da magana da kai." To Zubaina ta na gode, ina kuma ƙara gode miki" Ban ɗakin na shiga nayi wanka, tare da yin brosh, na ɗauro alwala. A zaune na fito na same ta, agogo na kalla, sha biyu saura kwata na dare. Wai kaddai wannan case ɗin ɗan luwaɗinnan kiketa faman yi har yanzu?" Kallona tayi taja dogon tsaki. "Kai dai ka bari, har yanzu bamu gama tattara bayanan daya dace mu tattara a kan mutumin ba, gashi A S P ya bamu lokaci, D P O ɗinmu gani yake kamar bama ƙoƙari akan case ɗin. Amman gobe zani kaciya ni da yara, zamu ziyarci gidan wasu yara biyu da shi mutumin yai musu fyaɗe, suna ƙarƙashin kulawar asibiti, sai ɗayan yaron dake anguwan dosa, sauran yaran sun mutu, amman mun tattauna da iyayensu. Ni bama wannan ya ɗaga mun hankali ba. Wallahi damuwata shine wannan kayan dake cikin mota, wanda ƴan uwanka suka zo dashi, amman Bulama ziyara kawai suka kawo mana kuwa, ni naga sunyi yawa ne ace ziyarace wannan kawai fa, sannan ga kaya cikin mota, duk da naga ba'a taɓa kayan ba, amman duk da haka na kasa samun nutsuwa" Zama nayi a kusa da'ita, na jawo hannunta ta dawo kusa dani. Ziyarace kawai, a gidanmu haka muke yi, in dai gidan ɗaya daga cikin dangi zamu je. Maganar kaya da kike yi, ni kaina bansan kayan meye ba maganar gaskiya, amman bai kamata kayan su ɗaga miki hankali ba ai, koma na meye, ko na waye dole zasu faɗa mun, zaki ji. Sai dai banji daɗin abinda ya faru ɗazu a falo ba. Kiyi haƙuri da dukkan maganganun Mama Gana, kuma kiyi taka tsantsan da ɓacin ranta, naso in taso in rarrasheki gudun fitinane yasa na zauna, amman zuchiyata tana tare dake. Amman Zubaina garin Yaya abincinki ya zama haka?" "Ni kaina ban sani ba, su Asiya na bari akan miyar, sabida an kirani daga wajan aiki kan maganar case ɗin ɗan luwaɗinnan, to kafin in fito sun gama miyar, kayi haƙuri bansan haka suka yi ba. Sannan ka bata haƙuri su ci abincina hakan ba zata sake faruwa ba" Murmushi nayi. Baki san Mama Gana ba ne. Ai bata haƙuri da zanyi shi zai sa ta zazzage kwandon faɗa, kuma tunda tayi rantsuwa ko kin dafa abincin bazata bari kowa yaci ba. Karki damu zan dinga siya musu har zuwa lokacin da zasu tafi. Su Wakil ma da asuba zasu juya kamar yadda suka ce mun. Gobe ƙarfe nawa zaki fita office?" Kuka ta fashe mun dashi. "Bansan me nayi ma ƴan uwanka suka tsaneni ba Abban Maryam, wallahi ni kuma ina ƙaunarsu sosai, dan Allah in akwai wani halina da ƴan uwanka basa so ka sanar dani in gyara" Rarrashinta na shiga yi, ina jin zafin kukan da Zubaina take yi. Aikin faranta mata rai na shiga, dan nasan shine kaɗai zai kwantar mata da hankalinta. Yahanasu: Ɗakin baƙi muka shiga kai tsaye. Katifa ce babba a yashe a ƙasa, sai ban ɗaki, shikenan abunda ke cikin ɗakin. A bakin katifar na zauna, Fanda ta zauna kusa dani, Hajja Fati ta zauna a ƙasa tana ba ɗiyarta nono. "Yahanasu zaman aure fa haƙuri da juriya shike rayar dashi. Da wasa kar ki sake ki zama mai raki da ƙorafi, sannan ki koyi tursasa zuchiyarki wajan ɓoye sirrin gidan aurenki. Fitar da laifin Bulama Babba ko laifin matarshi, ka iya jawo targaɗe ko karayar aurenku. Mu dukka dangin junane, abinda ya yi ki, shi ya yi Bulama Babba. Ba Bakura tamkar mahaifi yake ga su Ba Modu. Kiyi ƙoƙarin ganin kin sa Ba Modu a cikin farin ciki, ta hanyar tattala musu zumuncinsu. Da zaran kin fitar da magana, a kwana a tashi, za'a iya samun rashin daidaito, ko kuma gagarumin RIKICIN CIKIN GIDA. Bulama Babba bazai cutar dake ba, a hannunshi duk muka girma, tun bai mallaki hankalinshi ba, yake yi mana hidima, ni tausayinshi ma nake ji wallahi. Sabida da kin ganshi, kinga wanda baya cikin hayyacinshi, matarshi ƴar duniya ce, ko a fuska duniyancinta ya fito, ki bi su a hankali, ki kwantar da kai kiyi tsantsar biyayya ga mijinki, ɗan uwanki, dan Allah ki rufa mana asiri. Ki duba sabida halin dattaku irinna Ba Bakura,ya haɗa aurenki da Bulama Babba ne sabida ya sama miki sauƙin rayuwa a cikin ƙunci, duba da iftila'in da ya yi kotse a cikin rayuwarki, muma ya taɓa zuchiyoyinmu, ki dinga tunawa da wannan." Jikina sai naji ya sake macewa mus, har nake jin ko da yankar naman jikina Bulama Babba yake yi, shi da matarshi, zan bishi zan zauna dashi, ko dan in faranta ran mahaifana, kuma in kare dagulewar zumuncinsu mai kyau ta dalilina. Hawayene yashiga zarya a kumatuna, Hajja Fati tace dani. "Kuka ba naki bane, bai kuma kamace ki ba. Yahanasu ki dage akan adda'ar Allah ya baki yaddar mijinki, ya kare ki daga sharrin dukkannin wasu masharranta. Ki yi haquri, muma da mu kai auren soyayya kina ganin yanda muke fama, ni kaina gudun kar in tsunduma Mama a halin damuwa ne yasa nake zaune da Baban Nasiba. Amman wallahi zaman cutuwa nake yi. To Mama tana da ciwon Suger, ga hawan jini, kullum nasiharta dani shine, in zauna inyi haƙuri a gidan mijina. Shawararki dai kawai zan ɗauka, na komawa makaranta, zan nemi ƴar sana'a in kama dan in samu in dinga biyan kuɗin makarantar. Mata da kike ganinsu a taron gidan biki ko suna, ko makaranta, ko ma'aikatu. Damuwowinsu na gidan aure wata da zata huda miki cikinta, kiji halin da take ciki tsakaninta da mai gidanta. wallahi sai kin ɗauka ba'a duniya kike ba, tsabar firgici. Maƙwociyarmu Maman Binta, bari kiji abunda ya faru da ita. Bazawarace Allah yayi ma mai gidanta na fari rasuwa. Suna zaune a wani ƙauye a nan Yola. Bayan rasuwar mijinta, ta shiga takaba, tana da yara uku da shi, biyu maza Babbar itace Binta mai shekara goma sha biyu. Data gama takaba, sai dangin mijinta mai rasuwa, su ka sa akai rabon gadon ƴar gonarshi da ya bari. Aka raba aka faɗi na kowa, harda nata tumunin takaba. Sisi basu ɗauka sun bata ba, sai suka ce da dukiyar, da yaran nasu ne, zasu haɗa su riƙe. Suka bata tuminin takabarta, ta kama hanya ta dawo Yola. Bata jima ba ta yi aure, aka kawota nan kusa da gidana, ana zumunci da'ita. Mijin data aure mai ƙaramin ƙarfine, kuma bama ita kaɗai bace matar tashi, mai gadine a wani asibiti, ganin haka sai maman Binta ta nemi aikin shara da wankin ban ɗaki a asibitin da mijinta ke aiki, cikin yardar Allah ta dace. Tare suke zuwa su dawo tare, a haka ta haifi yara biyu. Data je ƙauye ganin su Binta, sai ta nemi tawowa da Binta, dan ta ɗan sata a makaranta, ta kuma dinga kama mata aikin gida. Ta tawo da Binta, ana nan ana nan sai Binta ta shiga ciwo, tana ɗaukar Binta ta kaita asibiti, gwajin farko akace ciki take ɗauke dashi. Maman Binta ta shiga tashin hankali tare da tuhumar Binta wanda yai mata cikin. Hmm abun mamaki mijin Maman Binta ne ashe yake lalata da Binta, sau uku yanai mata ciki, suna zubarwa, a na huɗunne Allah ya tuni asirinsu duka, tunda ba tursasama Binta yayi ba, da son ranta komai ya dinga gudana. Kunji fa ƙarshen duniya, da ire_iren halin da wasu matan suke ciki a gidajen aurensu, wannan ba komai bane wallahilƙudrat akan halin da wasu ke ciki. A razane na dubi Hajja Fati nace. Kuma ya makomar aurensu ta kasance Hajja Fati?" Murmushin takaici tayi mun tace. "Kema kinsan makomar rabuwace kawai ai, amman ya cutar da'ita. Haka suka tattara suka koma gidan iyayenta. Yarinyar harta haihu ma, gashi maman itama tana da yara biyu dashi, amman dasu ta tafi, dan har kotu suka shiga. Hmmm Yahanasu nifa kaina a cikin matsaloli masu tarin yawa nake, daga wannan ya lafa sai wannan ya ɓullo, wallahi har ya zame mun jiki." A wannan daren kamar yadda suka ce, zamu raba dare suna bani magana. Hakan kuwa akayi, kuma na ƙaru gaya. Amman ni har su kai bacci idanuna biyu. Alwala na ɗauro na shinfiɗa ɗankwalina, na soma kai roƙona ga mahaliccina, buwayi gagara misali. Na yi sallah har ƙafafuna sai da suka kumbure. Kuka nayi shi a gaban mahaliccina, tare da roƙonshi ya bani juriya, da ƙarfin zuchiyar ɗaukar duk abinda zai tunkaroni a zaman aurena. Ya bani hanyar ɓullewa ba tare da naje gaban waninshi na durƙusa dan neman tallafi ba. Ya bani juriyar kawaici, da yakana kamar Ya Innana. Daga ƙarshe na tashi, na sha ruwa dan ɗaukar azumin nafila. Saini na tashi su Fanda dan su yi sallar asuba, idanuna sun kumbura da ganina, kasan nayi kuka har hawayena sun ƙafe. Ina jiyo muryar Bulama Babba yana magana da su Wakil. Sallar Asuba muka gabatar dukkanmu, ina zaune ina azkhar, na jiyo dawowar su Wakil. "Fandau ku yi maza, asubar fari muka so tafiya. Amman Ba Bakura yace muje gidan Amininshi Alh Munka'ilu tare dukka." Bulama ƙarami ke magana da Fandau, fita tayi taje ta same shi. Yarinyar Hajja Fati sai canyara kuka take yi, Hajja Fati ta shiga aikin jijjigata, da ƙyar ta koma bacci. Wai ni Hajja Fati wannan maganin da naga kin sha jiya, na menene wai?" Dariya tayi mun. "Maganin cire damuwa, da sanya nutsuwane, da in na sha, sai in kwan in wuni ina cikin bacci, amman yanzu ya riga ya bi jikina, in ba haɗe haɗe nayi masu yawa ba, baya sani bacci. Sai dai in na kwanta bacci ina samun yin lafiyayyen bacci, hakan yana taimakamun wajan sauke mun hawan jinina, kinsan masu hawan jini anason su dinga samun bacci lafiyayye, musamman na dare." Idanu na zare nace Ke nan kwayar da masu shaye_shaye suke sha ne, kema kike sha Hajja Fati, har matsalar da kike ciki takai wannan ne?" "Tafi yanda kike tunani, kina cikin halin rashin samun bacci mai kyau kema, tun sanda akai miki fyaɗe, zaki fahimci ciwon rashin bacci shi kaɗai masifa ce. Ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji. Da zaki sha guda ɗaya bacci zaki yi mai kyau, a ƙalla zaki rage wani zugi daga cikin zuchiyarki, kuma kanki zai rage nauyi, zan baki ki ajjiye ƙila yai miki amfani" Murmushi nayi. Haba dai Hajja Fati, babu amfanin da zai yi mun. Duk da nasan rashin bacci, ciwone babba, ni bama shi kaɗai ke damuna ba, harda rashin son ganin kowa a kusa dani wallahi, yanzu haka jina nake yi kamar in kurma ihu fa. Sasaucin da nake samu shine karatun Qur'ani da nake yi, a duk sanda naji zuchiyata ta raya mun cewar, in kashe kaina zan huta. Amm...... Kukane yaci ƙarfina sosai, ga kaina kullum a cikin ciwo yake a ko da yaushe, sakamakon rashin samun lafiyayyen bacci. Rabon da inyi bacci mai tsayi, tun kafin wannan ƙaddarar ta dirarmun, tunda wannan abun ya faru dani, zuchiyata bata sake samun nutsuwa ba." Rarrashina Hajja Fati ta shiga yi, tana bani baki. Hawayena na share, muka fito falo. A nan muka samu su Wakil da Fandau suna tattaunawa. Duk idanu suka ƙura mun. "Lafiya idanunki da fuskarki suka kumbura haka Yaha? Nifa ina tsoron damuwar da zaki shiga bayan tafiyarmu, ga rashin son shiga mutane da kike yi, in muka tafi kar ki je ki kashe kanki da tunani" Wakil ne yake yi mun Magana cikin nuna kulawa." A'a bazan kashe raina da tunani ba. In kunji kabarin mutuwa ta, to daga rabbissamawati ne, kar ku damu ƴan uwana, na gode da kulawarku, zan iya kulawa da kaina ni fa ba yarinya bace" Bulama ƙarami yace. "Kajita fa Wakil, wai ita ba yarinya bace, yaushe yaushe yarinyarnan, ita da su Ba'a Kaka muke zuwa ɗaukosu a makarantar firamare?" Wannan maganar da ya faɗa ita tasa duk muka kwashe da dariya, nan sukaita ɗan jana da raha, har sai da na saki jiki dan kaina. Ƙarfe shidda muka shiga ɓangaren su Bulama Babba. Mama Gana da Yanunu, da Bagulaji muka samu a falon, suna saman kujera Bulama Babba yana gurfane a gabansu kamar mai ɗaukar gafara, faɗa mama Gana take yi sosai, Bagulaji da Yanunu sai bata haƙuri su ke yi. Dubanmu tayi tace. "Ku shigo ku zauna. Kai kuma ka biyo mu ɗaki dan akwai muhimmiyar magana da zamu tattauna da kai. Tunda dukkan ku fita aiki zaku yi ku barmu jiran gidan, tunda baka san mutunci ba, wallahi ka bini a hankali daga kai har matarka da ƙannenta na faɗa maka kenan. In banda iskanci har mu kake faɗama akwai muhimmin aikin da zata je ta gabatar, da uwarta ce tazo gidan ai bazata hofantar da'ita haka ba. Kuma wa zai bamu abincin da zamu karya kumallo dashi tukunna?" Ya Bagulaji tace. "Mama Gana ki bar yaronnan ya huta haka na roƙe ki, sannan ke kika ce bazaki kuma cin abincin matarshi ba, muma wallahi bama so akai kasuwa. Kai kuma Bulama kaci gaba da bin maras kunyar matarka Allah ya bamu lafiya. Kuma tunda baka ƙaunar zaman mu, zamu tattara mu bar maka gidanka yau ba sai gobe ba, ni dai bazan sake tako ƙafata in zo ai mun rashin daraja ba. Mama Gana mu shiga daga ciki mu sanar mishi abinda ya kawo mu, dan karma yayi tunanin dan kuɗin daya tara muka zo mishi gida" Da kuka ta ƙarashe maganarta, tare da shigewa ciki, suma baya suka mara mata. Shi kuwa Bulama Babba ba guiwa haka ya bi bayansu, idanunshi sun kuma rinewa, hawaye tab gurbin idanuwanshi. Ni kuwa tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, da sauri na fice a falon, na koma B Q ina kukan fitar hayyaci" Bulama: Gabaki ɗaya zuwan su Mama Gana ya zame mun matsala, tun sassafe an tusani gaba da tijara, sai kace wani ƙaramin yaro, ko iyayena naga ai sun shafa mun lafiya. Ɗan guntun tsaki naja a fili, bayansu nabi zuwa ciki. Sharar ƙwallar dana shigo na tadda suna yi, sai ya karya mun guiwa. Gurfana nayi a gabansu, ni dai bance komai ba, akwati na gani sabo fil a gabansu, a buɗe akwatin yake kayan maza na hango a cikin akwatin, harda su huluna zanna. Ya Bagulaji tace. "Wannan zuwan da kaga munyi, umarnine daga wajan Bakura, da Hajja Gana ba wai yin kanmu bane, kai baka bimu ba amatsayinmu na iyayenka, ai kuwa baka isa mu mu biyoka ba,. Wannan akwatin daga gani a gabanka, kayane wanda al'adar Kanuri ta tanadarwa ango, wanda yake fitowa daga dangin Amarya . A cikin akwatin akwai shaddajo, akwai yadika, wasu kayanma anyi musu ɗinki irin na sarakai, akwai takalma, turare, agogo, huluna, sallaya da Qur'ani. Dukka naka ne Bulama Babba. Ga Yahanasu nan Ba Bakura ya aura maka ita, ma'ana matarka ce ita a halin yanzu. Yayi hakanne dan sanin cewar ya isa da kai, kuma shi ya haifeka, ya ɗau jirimin tarbiyantar dakai, da baka ilimi. An haɗa aurenne a sakamakon ƙaddarar data gibta cikin rayuwar Yahanasu, aka samu wani azzalumi ya keta mata haddinta, yai mata fyaɗe. Anyi taro sosai kafin a haɗa aurenka da'ita. Kai dai jininta ne, muna da tabbacin in dai kana cikin hayyaci, da nutsuwa, baza ka bari wani ma ya cutar da Yahanasu ba, ballentana kai a kan kin kan ka ace ka cutar da'ita. Ya rage naka in ka hofantar da ƴar uwarka ka rungumi bare. A wajanka ne kaɗai zata samu nutsuwa, ba tare da ta fuskanci ƙalubale dangane da ƙaddarar data faɗo mata ba" Tunda ta soma magana jikina da hantata suke rawa, kalmar Aure data faɗa ya firgita tsigar jikina, ya jijjiga duk wata tsokar dake jikina. Maganar fyaɗe yasa na ɗimauta, harma na rasa wanne tunani zanyi, damuwata shine taya zan tunkari Zubaina da wannan zancan, sannan a matsayina na wan Yahanasu ya zamu yi mu gudanar da rayuwar aure, a rasa da wanda za'a haɗata saini, saida akai mata fyaɗe bata da wata daraja sannan za'a liƙa mun ita, mummuna da'ita ƴar lukuta wannan ai abun kunya ne ma a gareni ace Yahanasu ƴar lukuta matata ce, anya kuwa Ba Bakura suna ƙaunata kuwa? Ciwon kan da nake fama dashine ya kuma tsananta, sai tsalle zuchiyata take ta faman yi, in haɗiye yawu ma in samu salama abu ya gagara, sai dambe nake da yawun bakina. Ina cikin wannan saƙe saƙen na kuma jiyo muryar Mama Gana tana cewa. "Sannan Bakura yace mu sanar maka, in har ka kasa riƙe Yahanasu tsakani da Allah, to bazai yafe maka ba, ya kuma da cewa in kayi sanadiyyar wargajewar zumuncinmu, bazai yafe maka kan wannan ba. Da munso mu ni da Yanunu muyi ma Yahanasu zaman bakwai. Amman a halin yanzu mun canja ra'ayi, tafiyar da su Wakil zasu yi yau, na dakatar da'ita. Su bari zuwa gobe in muka gama yi ma yarinya jere, sai mu ɗunguma mu tafi baki ɗaya, sannan inaso ƙannen baƙar tijararriyar matarka su bar gidannan kafin mu tafi, domun hakan zaifi muku alkhairi baki ɗayanku. Ni dai na kasa cewa komai, sai ta'ajibi nake yi a zuchiyata, da ƙyar na ka da baki nace. Amman to a ina zata zauna ita Yahanasun, gidana na zaman mutum ɗaya ne, sai masaukin baƙi da nake dashi, kuma ƙannen Zubaina suna zuwa suyi mana hutun makaranta, acan suke sauka. Sannan Mama Gana kiyi haƙuri kar kice na yi miki rashin kunya. Amman su Asiya anan zasu ci gaba da zama tare damu, domun ni nake kula da su, kuma nauyin karatunsu akaina ya rataya" "Rufe ma mutane baki gafara, rashin kunya kuma na nawa, ai baka cika ɗan iska ba tunda baka haɗesu ka auresu dukka ba ƙarshen zama kenan. ƙannen Zubainar banza da wofi. A can BQ ɗin zamu jera kayan ita Yahanasun, sai ta zauna a can, ita kuma mai sarautar birnin zuchiyarka saita ci gaba da zama a nan, tunda dama nata ne, kar a takura mata, su sakata su wala da ƙannenta. In ƙannen nata maza sun zo hutun sai ka basu naka ɗakin su kwana, akwai wani gyara ko fenti da BQ ɗin yake buƙata ne?" A'a baya buƙatar gyaran komai, baifi wata ɗaya ba dana sabunta fenti, sai dai babu kitchen a ciki, bansan yaya zata yi ba" Ya Bagulaji tace. "Zamu ga dabarar da zamu yi mata dangane da wannan, maganar abincin kari fa Yaya zaka yi damu?" Me gadi zai kawo muku waina, tun ɗazu ya tafi siyowa, ni zan tafi office sai na dawo" Ficewa nayi a ɗakin, ina jin kaina kamar zai buga, ji nake yi kamar a mafarki, wai ni aka aurama Yarinyar da akaima fyaɗe, hmmm gaskiya iyayena ba ƙaunata suke yi ba. Ba wanda na kalla a falon, ɗakina na wuce kai tsaye, dan shirin fita office. Zubaina na samu a ɗakin tanai ma Maryam wanka, Bawa kuwa har ma ya sa kayan makaranta. Kallon Zubaina nayi, idanuwana sai wani zugi suke yi mun. "Meke faruwa Bulama, naga fuskarka ta sauya, duk da dai ina jiyo yanda ƴan uwanka suka dura a kan ka. Ka yi haƙuri kasan fa sai haƙuri da ƴan uwa, amman bana jin daɗin yanda suka tsangwameka, kuma duk dan sabida nine" No ba sabida ke bane Zubaina, ba sona suke yi ba. Tunda suka zo basu barmu mun huta ba. Ni wallahi bana farin ciki da zuwan nasu, shi yasa ma bana son zuwa inda suke. Mtwss. Naja dogon tsaki mai sauti. Kaya na sake, ko karyawa bana ƙaunar yi, Zubaina tayi tayi dani in karya, amman naƙi, jikina wani irin ɓari yake yi. Tsoron Zubaina na barazanar kekketa mun zuchiyata. "Maganar kayan da suka zo dasu cikin mota fa sun sanar da kai na menene, tunda sunce sai da safe? Ni har mafarkin kayan sai da nayi" Gabana ya yanke ya faɗi, amman bana iya ɓoyema Zubaina komai, kuma ko na ɓoye zata sani dan bama abun ɓoyewa bane. Bawa kuje ku samu su Asiya a ɗakin Momy ko maza yanzu zan zo sai mu tafi" Zubaina tace da Bawa. "Kace su baku tea ku sha, maza kuje" Nutsuwarta ta dawo dashi gareni tace. "Ina sauraranka, baka da lokaci, dan ka kusan yin latti" Jim nayi, bansan ta inda zan soma ba. Ba Bakura ne ya ɗaura mun aure wai da Yahanasu, shine suka kawota, kayanta ne a motar" Ajjiyar zuchiya na sauke, na dafe kaina tare da runtse idanuna, ina jin wani ciwo a zuchiyata, tare da jiran abunda Zubaina zata ce." Murmusawa naji Zubaina tayi, abun mamaki, dan ba abunda na zata daga gareta ba kenan, wallahi na ɗauka ƙaramar hauka zata yi mun. Hannuna ta zame mun zuwa ƙasa, tana hawaye, ga murmushi a fuskarta. Gabaki ɗaya ta rikirkitani. Ki dena asarar hawayenki, babu wata mace da zata samu irin kwatan so da kulawar da nake baki, Bulama naki ne Zubaina. Akan waccan kucakar yarinyar kike kuka, ta isa ta haɗa kanta da ke ne?" Murmushi tayi, ta sa hannu ta share hawayenta tace. Bulama wannan hawayen daka ga ina zubarwa bana komai bane, face tausayinka. Yau na kuma tabbatarwa lallai iyayenka da ƴan uwanka ba sonka suke yi ba, kuma suna adawa da aurenmu ne sabida ni ba Kanuri bace. Amman kayi haƙuri ka rungumi ƙaddarar data tunkaroka. Ta ɓangarena baka da wata matsala, Allah ya bamu zaman lafiya, kuma kar wannan yasa ka damu kan ka ma sam. Damuwar shine, a ina to zata zauna tunda dai ni na cinye nan?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan dama babban damuwata shine, bansan da wacce siga Zubaina zata fassara lamarin ba. Amman naga bata ɗauka da zafi ba. Lallai Zubaina ta cika matar rufin asiri, mace ta gari, mai son farin cikin mijinta da ƴaƴanta. A BQ Mama Gana tace zasu yi mata jeren. Zubaina me kike so inyi miki dan in faranta miki rai a matsayin dannar ƙirji? Ki sanar dani duk abinda kike so, ni kuma zan mallaka miki" Dariya tayi tace. "Wannan ka bari sai ka dawo sai mu tattauna. Ka ɗauki yarannan ku tafi, ni kuma zanje ƙauye bincike dangane da case ɗinnan, bansan ƙarfe nawa zan dawo ba, gashi inason zuwa in ga Mama." Key ɗin babbar motata na miƙa mata, ta harareni cikin soyayya tace "Wannan na meye to kake bani?" Rungumeta nayi tsam a jikina ina sauke ajjiyar zuchiya. Cikin raɗa nace mata. Na baki motar kyauta, ni zan riƙe taki. Zubaina duk abunda na mallaka naki ne, ke da su Mama, abinda kike son ayi a gidannan shi za'ayi Zubaina. ki ɗebi kayan abinci a store ki tafinma da su Mama dashi" Sakinta nayi, na ajjiye mata key ɗin motata na ɗauki tata, na fice a ɗakin, ina share zubar data tsattsafomun. A dai dai wannan lokacin da za'a auna ni, haƙiƙa jinina ya hau, tsabaragen rudanin da nake ciki" *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. MRS BUKHARI CE [26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B) 7 SAKON GODIYA. SAKON GODIYA TA A GAREKU MEMBERS NA CIKIN ( MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA PAID GROUP) KUN BIYA KUƊINKU, KUMA KUNA GWANGWAJENI DA COMMENTS INA GODIYA, NACE KU HUTA DA WANNAN PAGE ƊIN, NA SADAUKAR A GAREKU KUYI YADDA KUKE SO DASHI. GAWURTATTU UKU FANS GROUP KUMA INA MIƘA SAƘON GAISUWATA A GAREKU. BAN FA MANCE DA HAUSA NOVEL WWW. BATI. COM GROUP BA. IN DAI SHARHI NE KUN IYA. YA KAMATA MARUBUTA SU SAN DA ZAMAN WANNAN GIDA NAKU MAI ALBARKA. ZUBAINA: Yana fita na sulale a ƙasa, zaman ƴan bori nayi ji kake tim, na ɗaura hannuna aka na zunduma wani irin ihu. hawaye ya gama wanke fuskata, zuchiyata sai tsalle take yi mun. Ba ƙaramin dagewa nayi, na daure zuchiyata, ban rufe Bulama da duka ba tsabar ruɗani. Na danne ne dan gudun abunda kaje kazo, duk a cikin kissa da kisisina ne namu na mata. Duk da nasan Bulama a mallake yake, amman ance in kana da kyau ka ƙara da wanka. Yanzu duk irin shige da ficen da nayi dan in raba Bulama da iyayenshi, da danginshi, amman sai da iyayen Bulama su kai mun kishiya? Sabida neman mallaka babu irin surƙuƙun da ban shiga ba babu inda kafata bata taka ba, mune har shagamu, dukiya kuwa na narkar da ita sosai, ina kan narkarwa ma, sabida Bulama mutum ne shi mai yawan ibada, baya wasa da sallah. Asirin baya wani dogon zango a jikinshi, shi yasa akai akai nake gurfana a gaban malamai daban daban dan a sabunta mun asirin. Amman gashi daga ƙarshe mun zama mu biyu a wajan Bulama. Wallahi idan tsirara zanyi yawo sai nayi, amman wannan yarinyar sai dai ta zame mun ƴar aiki, ƴar reno da jiran gida, amman bata isa taji dai_ dai da ɗumin Bulama ba, da hakan ta faru gara Bulaman ya bar duniyar" Dariya nasa, ga kuka sharɓe sharɓe a idanuna na zama tamkar mahaukaciya, iyayen Bulama sun mugun sammaceni, amman zasu sha mamaki suma." Miƙewa nayi na faɗa ban ɗaki da hanzari a gaggauce na yi wanka na shirya tsab cikin riga da zani na Atampar koddibuwa, jakata na zara na fice a ɗakin Bulama, uniform ya kamata ace nasa domun zuwa office, dan akwai fitar da zamu yi zuwa kaciya bincike akan case ɗin dake gabanmu, amman sawun giwa ya take na raƙumi. Key nasa na kulle ɗakin Bulama da nawa ɗakin na fice. A tsakar gida na tadda gayyar tsiyar, zasu shiga mota, da halama wani wajen zasu, idanu na zuba ma Yahanasu, mummuna da'ita wai da ita aka haɗa ni kishi, iyayen Bulama sunyi kuskuren da zasu jima suna nadamar hakan a fili, nafita takota ina, ni banga da abinda zata ja hankalin ɗa namiji ba ma. Kafin in ƙarasa garesu, suka ja motarsu fuu, me gadi ya wangale musu get, Mama Gana ta leƙo ta tsittar mun da miyau har suka fice ina tsaye a wajan, nannauyar ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga mota nima na fice. Kai tsaye gida na wuce, dan in sanar da mahaifiyata halin da ake ciki. Anguwar Dankwata: Dankwata, anguwar shege da shegiya, in kaga ɗan halak baƙone. Wannan shine kirarin wannan anguwa, wacce ta cika ta batse da ƴaƴan talakawa marasa ɗa'a da kunya, unguwar da tayi ƙaurin sune a garin kaduna kenan, duk da akwai jerin sunayen unguwannin da sunansu yai shura wajan lalacewar tarbiyya, irin su Layin dutse, kabalan doki, kabala costine, da unguwar sarki, da sauransu dai, Dankwata itama tana ɗaya daga cikin irin wadannan unguwannin, amman hakan baya nufin babu masu tarbiyya irinta islama fa, a kwaisu sosai, sai dai ɓatattun su suka rinjayi kintsattsun anguwar, dalilin da yasa akaima jama'ar anguwar kuɗin goro kenan. Hancin motarta ta kutso dashi cikin anguwar, matan aure da zawarawan unguwa sai kallon Zubaina akeyi, ana zunɗenta, ba wanda take kallo, dan bata cikin nutsuwarta. A ƙofar wani gidan talakawa ta tsaya, mai ƴar ƙaramar ƙofar shiga, da kuma kofar shago irinna cikin anguwarnan, ƙofar gidan akwai dakali wanda yaji sumunti sumul sumul. Zubaina: Da hanzari na fito a cikin motar, na faɗa cikin gida. Ko bi takan munafukan matan layin banbi ba, nayi shigewata cikin gida. Mama tana zaune a gaban wanke_wanke tana yi, ga ƙosai da kununta akan tabirmar dake shinfiɗe a kusa da ƙofar shiga ɗakin nata. Sagir kuma ƙanina, yana zaune a turmi yana karyawa. Mama ta ɗago ta kalleni, kuka nake yi sosai, dan hankalina a mugun tashe yake matuƙa. Da sauri Mama ta miƙe har tana yarda kwanon da take wankewa. "Yau me zan gani ni Jummai ɗuwawu ya mutu ya bar zani Zubaina kece da kuka, ince dai ba asirin bane ya karye ya sako ki ba ko?" Gabaki ɗaya Mama ta ruɗe, dan Bulama shine, cinsu, shansu, sututarsu. Hatta gidan da suke ciki shi ya siya musu, a gidan haya mahaifinmu ya rasu ya barmu, bai bar mana gadon komai ba, sai gadon talauci. "Kiyi magana mana kin kaɗamun hanjin cikina, Sagir kana ganin ƴar uwarka a cikin damuwa amman kaƙi kazo kaji me ke damunta" Sagir yace. "Inji meke damunta in mata maganin me? Matar data ɗauka rayuwar ɗa namiji tamkar a hannunta take. Kowa ya ɗebo da zafi bakinshi, Mama ku dena sani a cikin irin wannan sabgar taku, ta ƙin Allah, duk iskancina tsoro kuke bani, dan muma ƴaƴanki Mama ba ƙyalemu kika yi ba, kullum cikin bamu rubutu kike mtwsss" Yana gama rashin kunyarshi ya fice yana fito. Ni bambi ta kanshi ba, Mama ce ta shiga ƙunduma mishi manyan zagi, tana kwashema rayuwarshi albarka. "Ki jini da yaro fa, da haka yake so, ai sai ya dena cin komai na cikin gidan tunda mijinki ne yake kawowa, wa ya siya mana gidan? gidan haya ubanku ya mutu ya barmu a wulaƙance a ɗaki ɗaya, ɗakin da in damina ta sauka, bamu da banbanci da na titi, dan duk ruwan daminannan a kanmu yake ƙarewa. Da ba dan ƴan uwana sun tsaya mana ba, karatun zamanin ma wa zai samu. Zauna ki faɗamun damuwarki, ni kuma in share miki hawayenki" Sulalewa nayi na zauna a kan taburma, itama zaman tayi a gefe na. "Menene yake faruwa Zubaina kike kuka, ince dai munafukan anguwa basu ganki kina hawaye ba ko? Dan yanzu sai kiji sunanki a majalisar matan aure da zawarawa" Hmmm Mama iyayen Bulama ne suka taɓoni, kinsan munafukan tsofaffinnan aure suka yi mishi da ƙanwarshi da suka taso gida ɗaya, sai ga baƙi jiya har mota uku sun kawo wata mummunar baƙar yarinya da sunan Amaryar Bulama, duk rabashi da danginshi da nayi, sai da suka ci galabar cusgunamun" Sallallami Mama ta soma yi tana tafa hannayenta tana faɗin. "Ni jummai naga ta kaina kishiya tara rana ɗaya, ta goma na ƙofar gida. Aure fa kikace Zubaina. Lallai da badan mun tashi tsaye da bin malamai akan Bulama ma da yanzu iyayenshi sun sa ya sakoki, sun toni asirinmu a unguwa. Ke Kanuri fa basu da mutunci, kuma da yawansu mayu ne, gasu da ƙabilanci, basason nasu ya fita ya auro bare. Muna zaman mu lafiya suna shirin tagayyaramu. Amman ke wanne hulunci kika ɗauka dan nasanki da zafin kishi, duk cikin yaranma ke kika biyoni. Nifa ranar da Babanku yace yana neman aure, a gadon asibiti na kwana. Gari na wayewa kuwa na shiga bin ƙauyuka ina yima bokaye da ƴan tsubbu biyayya, har sai da naji zancan auren ya watse sannan na soma iya bacci." "Mama ni da kwantar da kaina naso inyi in ɓullowa abun ta bayan gida. Dan yanzu haka Bulaman ya kuma gigicewa a kaina, baya son yaga kukana. Motarshi fa da safennan ya bar mun, yace ma in ɗebo muku kayan abinci a store. Amman ban ɗiboba sabida ƴan uwanshi kar su gani. Gashi yace in faɗi duk abinda nake so zai yi mun. Amman mama ni ƙona gidan zanyi cikin dare duk mu zama ganda" Mama ta buge mun baki tace. "Baki da hankali ne, kin ɗauko hanya me kyau kina son ɓata rawarki da tsalle. Ai yanda kika kwantar da kanki shine dai_dai, yaƙi ɗan zamba ne Zubaina. Zanje wajan boka duk yanda muka yi ni da kaina zan zo in kawo miki magunguna, kinsan dai aikinshi ba wasa, tunda shi ya juyar miki da hankalin Bulama. Ke dai zube kuɗi kawai, ki tashi karma kiji komai da ƙafafuwanta zata bar gidan, shima kuma bazai taɓa iya zama da'ita ba. Ke sai dai bayan raina ne zaku yi kuka Amman ba yanzu da rayuwata ba. Ke dai kafin ya sallameta ki samu ki kabci rabo mai mugun tsoka ki samu ki ƙarashe gininki, a zuba miki haya." Kuɗi masu kauri na ajjiyema Mama. Gasu Mama in basu isaba kice ya bamu maganin za'a kawo mishi ciko tunda an saba. Ni zan tafi" Baki Mama ta washe bayan ta dafi kuɗin tace. "Muje in ga motar mana." Tare muka fita da Mama. Matan unguwarmu muka gani, sun haɗa gungu guda na gulma, dama kullum a cikinta suke. Suna ganinmu suka soma dariya. "Ahh Maman Kofur Zubaina, Zubaina Amaryar mota ta samu ne? Kai Masha Allah." "Eh Jamila kinga, da safennan mijinta ya bar mata ita kyauta, albarkar aure" Da biyu Mama ta faɗama Jamila hakan, dan ita taƙi zaman aure fur, da an kaita data fito. Tsaki nayi na shige motata, mama na ɗaga mun hannu na wuce. Ban zame ko ina ba sai gidan ƙawata Mabaruka. Da sallama na shiga cikin gidan. Kishiyarta na tsakar gida, ta haɗe kan yaran gidan tanai musu wanka, ga tulin wanke_wanke a gefe, ga kayan wankin yaran duk a gefe guda. Da fara'a ta gaisheni cike da girmamawa, a yatsine na amsa mata nayi shigewata ɗakin Mabaruka. Tana zaune a ƙasan ledar ɗakinta tana kallon tashar Arewa 24 Tana ganina tayi dariya. "Sabon kabari mai sa a tuna Allah, makara motar ƙarshe , tsatsa mai kashe ƙarfe, shegiyar gyaɗa da ƴaƴan kanya, shegiyar uwa sai bukka, ke ce da safiya haka kofur Zubaina? Yau aikin ya garara Bulama ya taro match kenan, ina kika baro dangin mijin naki?" Ke baki san a cikin damuwa nake ba ko? Kefa na faɗama a waya cewar Iyayen Bulama sun mishi aure, danginshi matar suka zo kawowa ma dan rashin kunya" Ƙirji ta dafe tace. "Nifa nayi tunanin wasane Zubaina, yanzu ina kika baro kishiyar kika tawo nan, bakya gudun su miki wani binne binnen su sabautaki?" Basa gidan sun fita, duk da bansan inda suka je ba, amman basu isa su samu makarin asirina ba, nasha gabansu. Mabaruka wanne boka kika sani shege wanda baya tsoron komai? Ki haɗani dashi" Ajjiyar zuchiya tayi tace. "Hmmm ni ko nake da arne na kan dutse ma, dan bama musulmi bane. Shi yaimun aiki akan waccan shegiyar yarinyar, ke baki ganta na sakar mata aiyukan gidan ita ke komai ba? Shekara huɗu kenan ina juya kowa a cikin gidan, har uwar mijin ni juyawa nake yi. Amman ko hantararta bana yi, dan har kwancen kaya bata nake yi, in ba ƴan uwanta ma, Yayarta da suke ciki ɗaya, in tazo gidannan a nan inda kike zaune take zamanta, yaƙi ɗan zambane Zubaina, in kika ce ihu da hargagi zaki yi, fallasa kanki zaki yi, aje aita miki baki. Kwanciyar mage nayi musu, amman a baɗini suna shan gashi. Ina zaune a nan da kika zo kika same ni, zan jiyo ihunta yana jibgarta, ni nake zuwa ƙwatanta a hannunshi, har in dafa mata ruwan ɗumi na gashi." Sallamar kishiyar Mabaruka ne ya katseta. Shigowa tayi da kofin tea da plate a rufe ta ajjiye a gabana. "Ina wuni mu sake gaisawa, mun gaisa ɗazu a gurguje" Da Lafiya" Na amsa mata, sai fara'a take faman zabgawa, Kallon Mabaruka tayi tace. "Yaya me za'a dafa ne da rana, inason dana kammala aikin inje inyo mana cefanenne?" "Uhm Sagira ki dafa mana faten doya da wake, sai kisa bushasshen kifin da Adam ya kawo jiya yana nan a kitchen, da daddare kuma tuwon shinkafa miyar kuɓewa ɗanya, amman a siyo ɗanyen kifi Adam yafi so" Da "To Yaya" ta amsa ta miƙe ta fice. Bakina a buɗe na dubi Mabaruka nayi dariya, dan har naji ɗan dama dama a zuchiyata, kuma inajin nima hanyar da Mabaruka tabi ita zanbi, ko dan in yaudari dangin Bulama, dashi kanshi Bulaman, duk macen da bata iya kissa ba ansha da'ita. "Ƙawata ya kika ga aikin na kan dutse? Ai shiyasa kika ganni hankalina akwance, rabon kwana yake yi mana, amman wallahi har makara nake yi salla tsabar kwanciyar hankali. Ai namiji, da kishiya basu isa sun ɗagamun hankaliba, in ke baki yi musu hakan ba, kece zaki kwashi takaici da ciwon zuchiya a hannunki, daga ƙarshe in baki yi wasa ba ki jiki a kabari. Ai na taimaketa ma tunda na barta take zaman auren, bansa yayi waje da'ita ba. Gashi dama ba gata bane dasu, basu da wanda ya tsaya musu a family, dangin Baban nasu suna ƙauye, dangin mahaifiyarsu kuma, suma takansu suke yi" Mabaruka tashi muje ki kaini gun wannan boka nima yai mun irin wannan aikin da yayi miki, ko zanji salama. Da dana shigo cikin gidannan zuchiyata baƙa, amman yanzu zuchiyata kamar auduga dan haske." Dafani tayi tace. "Zan kai ki ƙawata, amman sai fa kin shirya dan aikinshi akwai mugun tsada, ya iya aiki amman fa saiya mugun talautaki, dan manyan kuɗi yake karɓa. Ki duba ɗakina sai da fa na siyar da komai nawa, ke hatta zanen ɗaurawa a shekaru biyu baya neman gagarata yayi. Gashi kina gani har yanzu ɗakina bai dawo kamar da ba. Akazo kuma cinikin su Adam yaja baya. Kinsan sana'ar saida motoci haka take, zuwa take yi. Yanzu abun yaja baya sosai, ni kuma aikina na asibiti ba wani aiki bane, ga ƙannena da mahaifana da nake kulawa dasu. Amman dai ina ganin biyan buƙata. Ke lokacin da aka kawota fa, bacci wannan bana iyayi, daga baya ma cikin dare sai inji kamar ana kiran sunana, so tayi ta fitar dani a gidan a haukace. Alhalin dani aka tara arzikin Adam, ni nasha wahalarshi lokacin da yake matsayin malamin makaranta mai ɗaukar nera dubu takwas a wata a matsayin albashi. Hannu ta bani muka tafa, nace mata. Kuɗi ba zasu zama matsala ba Mabaruka, yanzu haka sai da na ba Mama wasu kuɗaɗen, zata je mun wajan bokanta, shima yankan wuƙane. Babu kuɗi masu yawa a hannuna, amman dai ina da kadarori na zinarai a gida, sai in kaɗar dasu, ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba ai ƙawata, a wanne anguwar yake ne?" Dariya tayi mun, ta buɗe plate ɗin da Sagira ta ajjiye a gabana, wainar ƙwai da biredi mai yanka yanka ne a ciki, ta dubeni tace. "Ba lallai in kin karya ba, maza ki karya sai muje, amman fa a garin Jos bokan yake, kin taki sa'a ma da safe kika zo, zamu iya zuwa a yau harma mu juyo, sai dai zamu yi dare, ni dama night nake dashi a asibiti, ba dai wata matsala dai ko?" Koma akwai babu Mabaruka, ni kam banga ta cin abinci ba, taso kawai mu kama hanya, sai naje gida na ɗakko zinaran nawa, sai mu je senteral in siyar dasu a layin ƴan gwal." Cikin ƙanƙanin lokaci Mabaruka ta shirya cikin leshi na goduwar riga, fuskarnan tata taci bilicin tayi ɗoɗar, hannunta kuwa duk dabbara dabbara kamar an babbaka Adaga ( plantain). A wajan kishiyarta ta bar yaran nata, muka wuce gida na kwashe setin gwal ɗina wanda Bulama ya sai mun, da ɗan kunne da sarƙan da na saima kaina, ƙarƙaf nayi, muka je kasuwa na kaɗar, muka nufi hanyar Jos. Wayata ce ta shiga ruri Bulama ke kirana, gefe guda na samu na kashe motar, sannan na ɗauki wayar. Ango mijin Amarya ranka shi daɗe ango da girman kujerarka" Dogon tsaki ya ja, yace. "Bakya ji Zubaina, ai bani da wata amarya face ke, mai zanyi da wannan mummunar yarinyar. Bama wannan ba, kin ganni a shagon siyar da atampopi na mudassar and broda shine nace bari in kiraki, atampar wanne kamfani kike so? Far nayi da idanuna kamar yana ganina kana nace. Da yake duk atampopin da nake saye a hannun Hajiya Zulai nake siyansu, kuma nafi yarda da kayayyakinta, me zai hana ka bari in ka dawo ba sai mu je gida mu sameta ba?" Murmushi yayi mun yace. "To shikenan bari in sai takalma da mayafai da jakunkuna tunda dai na shigo shagon, da girmana goɗai goɗai ai bana shiga in fito ban sai komai ba, sai munyi waya, kuma ina ƙara baki haƙuri a bisa ɗanyan hukuncin da su Ba Bakura suka yanke mana, kuma ina kan tunanin yanda zan ɓulloma da lamarin, Ahmad ma yana office ɗina yana jirana, ashe ya shigo gari bai ko kirani ba. Sallama mu kayi da juna, wayar nabi da harara, Mabaruka sai dariyar ƙeta take yi mun. "Kai ƙawata a cikin wayar ma ba'a barshi ba harda uwar harara kuma? Ki dena ba kanki haushi, baki da wata matsala, wallahi in cewa zaki yi Bulama karya je aiki, zama zaiyi ya tusaki a gaba kuita soyayyarku. Ke dai ki daure zuchiyarki karki sake ki nuna mishi kishinki, itama haka kar ki bari tasan kina kishinta. In ma ya shiga wajan nata, bacci kawai zaita shantaka bashi da sauran kuzari, ballantana har yayi miki halin nasu na maza, dan ƙaramin aikin namijine yayi ruf da ciki akan yarinyar washe gari ki ganta da ciki. Kinga saiki tashi a tutar babu, kin aureshi tun bashi da wani abun hannu, kuna tare aka tara komai. Daga ƙarshe kina gani za'a raba gado ƙila ma kasonta yafi kasonki yawa, musamman in maza take haihuwa, tuminin takaba kuwa daidai za'a baku, kinga kuwa ai kwaɓarki tayi ruwa, shi asiri gaskiya ne, amman kissa da kisisina wani sa'in tafi asirin saurin aiki, duk macen da tayi watsi da kissa ai ta makaro wallahi" Wani ƙududun ƙwallon kishi na haɗiye, ya tafi tuƙuƙuƙuƙu har ya faɗa cikina. Ki dena wannan lissafin, ai nice mace kaɗai da zan gaje dukiyar Bulama ko ƴan uwanshi sai dai suyi hange Mabaruka. Babu macen da Bulama har ya isa ya kwarara mata maniyyinshi a mararta ta samu cikin da zata samar mishi da ɗa. Wallahi babu ita, nifa gani nake yi gangancine wannan rabon kwanan, duk ranar da asiri ya karye, zasu sadu da juna fa kenan? In kuwa haka ta faru ina kike tunanin zan iya saka kaina Mabaruka, anya ba kuskure bane sallama miji ga kishiya dan gadarar an zargeshi da surkulle?" "Babu ganganci a ciki. Ni dai shekara huɗu ina kan wannan tsarin kuma babu, saɓanin lamba da na taɓa cin karo dashi, ke nafa yadda da bokannan yana da muggan rauhanai baƙaƙe da yake aiki dasu, wallahi ko kashe yarinyar kikace yayi, ko shurawa bazata yi ba, sai dai mu koma gida mu samu gawarta anai mata wanka, ke munci dubu sai ceto fa. Ajjiyar zuchiya na sauke, har muka isa garin Jos Mabaruka tana bani labaran irin gumun da tayi a gidanta, ta kwaci ƴancin kanta. Munsha wuyar hanyar saminaka sosai, sabida har gobe hanyar a ratattake take sosai. Amman ko da muka shiga jos kafin mu isa Ƙauyan maza munyi tafiyar fin awa uku. Ƙauye Maza wani ƙauyene daga cikin ƙauyukan jos, yawancin mazauna ƙauyen Maza ba musulmai bane, musulman ƙalilanne. Ada duk musulman ƙauyan sun watse, sakamakon yaƙin ƙabilanci da aka lashe shekaru masu dama ana zabgawa, amman yanzu birnin na Jos Alhamdulillah kowa na zaune lafiya babu taraddadi. A bakin wani shirgegen tsutse mai abun tsoro muka tsaya, jikin dutsen ciyayine sosai, harda manyan bishiyoyi, duk da bana gani sosai, sakamakon hazon daya rufe gari, ga kuma hadari yayi baƙi sosai. Kallon Mabaruka nayi nace. Munzo inda bokan yake kenan ko?" Dariya tayi tace. "Za dai muzo, kinga wannan dutsen sai mun haureshi mun gangareshi, sannan zamu yanki hanyar gidan bokan, an faɗa miki abun na wasane wai? Zagewa zaki yi dan sai mun yi tafiyar data share awa biyu gaba jeji baya jeji." Naji tsoron dutsen sosai, dan dutsene gari guda, amman haka muka soma hawa dutsennan, muna hawa gansa kuka na zamar damu, ni dai jikina in banda rawa babu abunda yake yi. Ita kanta Mabarukan jikin nata rawa yake yi ita ma kenan da ta saba kawo ziyara, sai Allah kawai nake ambata, amman zuchiyata tayi taurin da babu abunda zai sata laushi, face inga na raba Bulama da dukkan masu raɓarshi, ita kuwa Amaryarshi kashinta ya riga ya gama bushewa, dan har hasaso irin azabtar da'ita da zan yi, dan wallahi Mabaruka bata komai, dan ni ba sauƙi a cikin lamarina. Da ƙyar muka gama hayewa tsaunin nan, dan dutsen yafi kama da tsauni, bayana na dafe. Wash Allah Mabaruka wallahi na gaji, bayana kamar zai rabe gida biyu, wai Allah, yanzu ya zamu yi mu gangare dutsennan? "Ki zauna ta zaune miki, garin kallon ruwa kwaɗo yai miki ƙafa, ke duk macen da kika ga ta kafa kanta a gidan mijinta, to sai fa data dage, kuma ko da Asiri sai an haɗa da kissa irin tamu na mata, farkon zuwana wajannan, wallahi dana koma gida saida Adam ya gargasamun jikina, ke dai daure mu gangara cikin likkafa, tafiyace miƙaƙƙiya a gabanmu." Haka mukaita faman gangarawa, tun ina salati a zuchi, har na soma yi da mugun ƙarfi, ban ankaraba, naji tuntuɓe da wani ƙaramin dutse, ai kuwa na gungura. Wayyyyo Allah na mutu na lalace, Mabaruka zan mutu" Cikin ihu gami da kururuwa nake magana, sai wata ƙatuwar bishiyace taimun burki na saki wawuyar tusa ji kuke buuuut, guiwata da hannayena duk sun kukkuje. Mabaruka sai ƙarfafani take yi, a taƙaice mun sha ɗan banzan wahala kafin mu gangare wannan dutsen. Muka yanki jeji, shima yi muke, yi muke kamar ma bama yi, duk tsoro ya gama kamani, sai karo muke da wasu irin tiƙa_tiƙam tuɓaɓɓun arna marasa riga, masu jan idanu, sai ƙanƙame Mabaruka nake yi, su kuma sai sannu suke yi mana da gurɓatacciyar hausarsu, a haka muka iso wata bukka, inda muka tarar da mata su biyar a kan layi, sai wasu manyan maza su uku, da ganinsu masu muƙamine sosai, dan suturarsu da yanayin murjewar fatarsu ta nuna hakan. Matan kuma guda biyun hajiyoyine da ganin yanda suke, sai kuma su biyun irinmu ne, masu fafutukar neman na rufin asiri. "Sannunku bayin Allah, waye ƙarshe dan Allah?" Cewar Mabaruka, dan ni tuni na samu gefe na zauna ina faman haki, wata mata tace. "Nice ƙarshe kinga yanzu na iso, tsoron da nake ji ma, kamar kwana zai iya kamani a cikin jejinnan, to ko yanzu ma ƙarfe biyar na yamma har tayi, yaushe ka gama har ka tafi, duk da daga nan Bauchi nake bani da nisa" Ɗayar hajiyan tace "Aini ban taɓa zuwa nan na tafi a ranar ba ni nafison kwanan ma, sabida amun aiki da kyau ba cikin sauri ba, daga Abuja nake zuwa. Yana da ɗakunan da yasa aka gyara na sauƙar bakin kwana." Ni dai ina zaune sai ajjiyar zuchiya kawai nake, faman saukewa. Mabaruka ta dube ni tace. "Ki kwantar da hankalinki a gindin magalin duk matsalolinki kike, ai ada ba juya Bulama kike yi ba, lallaɓashi kike yi, shi yasa ƴan uwanshi suka yi azarɓaɓin cusa masa ƴar uwarshi. Note ( Mata muji tsoron Allah. Ki sani bin bokaye halakace, bin bokaye babu abinda zai haifar miki face dana sani wanda hausawa suka kirayeta da keya ce. Akwai mallakar ta fisabilillah da mace zata yi ma mijinta, ta hanyar yi mishi biyayya, jawo ƴan uwanshi a jika, yima iyayenshi biyayya da hidima, girmama kanki. Da abubbuwa ire irensu masu yawa, wannan itace mallakar dana sani ta tsakani da Allah. Ki sani bin bokaye shirka. Kuma ki sani in kika mutu kina shirka, a wutar jahannama zaki dauwama ba faɗata bace. Ya ke ƴar uwata an faɗa miki wutar ubangiji wasa ne, ko kuma meye ya shiga kanki da har kika mance da mutuwa, kwanciyar kabari, hisabi? Wallahi wallahi in baki tuba kin dena bin bokaye ba kina ruwa, kuma kin shiga uku, ƙarshenki tun a duniya ba mai kyau bane. Ina kira ga duk macen data ci karo da wannan littafin tayi ƙoƙarin siyen nata kafin in kammala free page dan jin yanda ƙarshen wannan labarin zai kasance, na tabbatar zaki ilimantu, zaki kuma wa'azantu. Ki neme ni ta pc kawai mu sasanta, koma nawa ne da ke. Sannan karfa ku mance labarinnan ya faru a gaske ba ƙirƙirarshi nayi ba.....) MRS BUKHARI CE [26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) GAWURTATTU UKU 8 YAHANASU: Mun samu kyakkyawan tarba sosai a gidan Aminin Ba Bakura Alhaji Munka'ilu, tare da matarshi Hajiya Ramlatu. "Allah sarki Mama Gana naji daɗin wannan ziyarar taku sosai, jiya ya kirani muka yi magana shi Bakura ɗin, yake sanar dani abun arzikin da aka haɗa, mun jima ba muyi wayar ba ma. Bulama Babba kuwa, wallahi bai zuwa, na tura yara gidan ma, amman dai basu samu tarba mai kyau ba a hannun ita matar tashi, ita kanta iyalina Hajiya Ramlatu tana dai zuwa amman bata samun sakin fuska. Duk yaran Bulama Babban da'ita akayi sunansu duka. Ni kaina ina zuwa wajan Bulama Babba a Bankinsu ina kai mishi ziyara, Allah ya sanya alkairi, Allah yasa hukuncin da aka yanke ya zama shine mafi alkhairi" Cewar Alhaji Munka'ilu kenan, Mama Gana tace. "Ai wallahi Yaya Munka'ilu in dai Bulama Babba ne bazai zo ba. Yaje gida ma can Damaturu, wallahi matarshi ta shiga ta fita ta hana, sabida Bulama ba haka yake ba, yarone mai ƙawazucin iyaye da ƴan uwanshi, muna fatan wannan haɗin da akayi ya zama shine silar dawo da hankalin shi ga iyayenshi da ƴan uwanshi" Hajiya Ramlatu tace. "Adda'ar daya dace ayi kenan. Ita kuma yarinya ta kula da ibadarta, kar tayi sanya da kai kukanta ga Allah. In sha Allah zamu dinga zuwa dubata, akwai Zainab Auta zan haɗata da'ita zasu yi sa'a da juna. Sannan Alhaji Bakura ya faɗa mana a sama miki aiki, kuma fannin jarida kika karanta. Ta kwana miki gidan sauƙi, dan ina ɗaya daga cikin shuwagabannin gidan talabijin dake kan faifayin tauraron ɗan Adam, ki ba da takaddunki, in sha Allah kin samu aiki, nan da sati biyu in kin gama amarcinki sai ki kirani a waya, saiki soma zuwa aiki in sha Allah " Godiya muka shiga yi sosai da sosai, dama tafi da gidanka mu kayi, takaddun nawa Mama Gana ta ɗebosu dama, karɓa Hajiya Ramlatu tayi, Alh munka'ilu ya dudduba takaddun ya mayar mun da abuna. Sunyi ciye ciye sosai a gidannan, ni dai ina azumi nera dubu goma Alhaji Munka'ilu ya bani, ya ba su Mama Gana dubu sha biyar, Hajiya Ramlatu kuma ta basu dubu biyar, nima ta bani dubu biyar, sannan ta bani lalle na gargajiya, da baƙin salateb me yawan gaske. Sai da muka sallaci Azahar muka yi musu sallama, muka doshi gida. Nan kuma suka shiga gyare gyaren BQ, jere har da su Wakil, sun dage sai kafa gado suke yi. Ni dai ina zaune a falo nayi jigum, ni zazzaɓi ne mai ƙarfi ma a jikin nawa, ga zuchiyar ba daɗi sam. Tunda wannan ƙaddarar ta riskeni, na tsinci kaina a cikin wannan sabon yanayin, wanda bashi da daɗi sam, haka kurum sai inji zuchiyata tana rayamin in raunata kaina, ko in hallaka kaina ma baki ɗaya, gabana yaita dokawa kuma, bana samun nutsuwa har sai nayi karatun Qur'ani, ko kuma in kunna a wayata in saurara, bacci wannan bana samun yi, abubbuwa a lokaci guda duk suka kwaɓemun. Muna zaune da Hajja Fati muna tattaunawa, su Wakil suka fito daga uwar ɗakin da suka kafa mun gado, suka fice a gidan baki ɗaya. Mai gadi ne yayo sallama bakin ƙofa, Hajja Fati tace. "Kamar sallama nake jiyowa, bari in duba" Tashi tayi ta fita, ta bar mun ɗiyarta, a wajena bata jima da fita ba, sai gata da manyan ledoji cike da take away da lemukan sha. Fanda ta shiga ta miƙama, ta barni a zaune ni kaɗai, ina wajan su Wakil suka shigo kici kici da kitchen kabinet wanda ake ajjiyewa a ƙasa kawai, doguwa sosai. Cike da mamaki nake ta kallonsu, mai aikin fanfo dama tun kafin su fita yake ta aikinshi ta bayan windon wajan daining ɗin a wajan daining suka fitarmun da Kitchen mai kyau, an saka mun abun wanke_wanke a wajan an jawo ruwa ta wajan. suka yi jeren kayan kitchen, wajan ya bada tsari mai kyau, aka saka labule mai raga raga wanda bai tare komai ba, an dai sa shine dan ado. Falonma aka gyareshi tsab, sai ƙamshin turaren wuta ɗan asali yake fitarwa. sai magriba suka gama komai, duk muka yi wanka, mu kai Sallah sannan mu ka ci abinci,na kai azumina lafiya. Bamu jira komai ba, muka shige ɗakina, Su Wakil suka shige ɗakin da muka kwana jiya. Ni dai ina kwance hawaye na suntiri a gefen kumatuna, damuwoyin da suka aureni a darennan da yawa suke, yanzu inaji ina gani gobe duk Kowa zai watse ya barni, ni da ko bacci bana iyayi, ya rayuwata zata kasance shine ni kaina ban sani ba, gashi ina gudun yin abunda zai ɓata zumuncin iyayenmu, da kashe kaina zanyi, koma in gudu a nemeni a rasa. Amman in sha Allah duk rintsi duk wuya zan juri zama da Bulama Babba da matarshi, kuma zanyi musu biyayyar da suke nema daga gareni, fatana shine Allah ya dafamun. Bacci daya gagareni saina tashi na ɗauro alwala. Bulama Babba: Bayan gama wayata da Zubaina a cikin kantin sai da sutura na mudassar. Ina sayen takalma da jakunna, sai nayi maza na koma office, dan ma'aikacin banki bashi da lokacin ɓatawa, a ofishina na taradda Ahmad a zaune yayi jigum. Ahmad wannan jigum jigum ɗin da kayi na menene wai? Gashi ni kaina a cikin tsananin damuwa nake, Allah Allah nake yi in zo in same ka dan kaji halin da su Ba Bakura suka jefa ni a ciki. Ni na rasa wanne irin tsana sukaima Zubaina, ni kuma banga abunda Zubaina ta taɓa yi musu ba. Amman wallahi ko Damaturu na kaita, babu mai sake mata fuska, a takure muke cinye hutunmu mu dawo gida. Ajjiyar zuchiya Ahmad ya sauke ya dubeni yace. "Tun dana taso daga Lagos nake cikin tunani da ɗimuwa, Bulama mata masifane, kuma lallai zasu iya saka a cikin ukun da baka isa ka fitar da kan ka ba. In kaga rikicin da mu kai ni da Hajara za kai mamaki, Hajara sabida na bata damar kasuwanci shine take ganin a yanzu data kama ƙasa tafi ƙarfina, dan kawai Allah ya jarabceni da rashin aiki. Kuma fa kar ka mance duk a sanadiyyarta da iyayenta na faɗa cikin bala'in da Allah yasa ka fiddani da ƙyar, wai yau ni Hajara take ɗagama murya." Duban Ahmad nayi, ina jinjina abunda Hajara tayi mishi, mata kenan, yarinyar daya tsinceta a titi da farantin tallan mangoro har itace tayi kilin haka take gasa wanda yai mata komai a rayuwa? Take naji jikina ya mutu mus, dan ni kaina ina cikin kwatankwacin halin da Ahmad ya tsinci kanshi, naci bashin banki nera million biyar ba tare da saninsu ba, gashi har yau ko ragewa ban soma yi ba, ga bashin million biyu ma na kuma karɓa a yau ɗinnan, inason inyi ma Zubaina hidima dashi, dan ta samu raugwamen raɗaɗin da na yi imani da Allah zai dameta. Dukkan wata wahalata akan Zubaina da danginta nake yi, dan iyayena da ƴan uwana basu mori komai daga dukiyata ba,iska na fesar a bakina. Ahmad kayi haƙuri a bisa abunda Hajara tayi maka. Da ba dan kaine ka sanar dani da bakinka canjawar da Hajaran tayi ba, da wallahi bazan yarda ba. Wato sabida taga a yanzu ta fika arziki shine wulaƙanci zai biyo baya, waye ya ɗaurata akan tsanin har ta samu arzikin ba kai ba? Ta bani mamaki amman ka daɗa haƙuri ka kuma bata lokaci, zan kirata in sha Allah, ina to ka baro yaran? "Suna gida yaran tare da ƙanwata, na ɗauki Zulaihat na tafi da'ita Lagos ai tana karatu a hannuna, kusan ita ke kula da yaran ma, Hajara kasuwanci tasa a gaba, da nayi magana sai tace ai ita ke ciyar da gidan, kuma kuɗin makarantar Yara ita ke biyan rabi in biya rabi, wallahi ni gabaki ɗaya auren Hajara ya gama fice mun a raina" Da sauri na tare shi nace" Kai haba ka dena cewa haka Ahmad, ko babu komai Hajara tana taimakonka, tunda ta ɗauke ɗawainiyoyinka da yawa, sannan ko babu komai su Aneesa suna tsakaninku, ka daɗa haƙuri kasan mata hukunane su sai da lallashi. Ni fa aure su Ba Bakura su kai mun, ba da sanina ba sabida tsabar mulkin mallaka. Kuma kasan su rasa wacce zasu aura mun sai Yahanasu ƴar lukuta wannan mummunar yarinyar ƙanwar su Dala fa, ai ka ganeta ko wannan mai ƙibar? Ita fa aka aura mun, babba dani Ahmad, dan ma sauƙin dana samu Zubaina ba tai mun rikici ba, tayi ba zata sosai Gaskiya " Tsuru Ahmad yayi yana kallona, sannan yace. "Bulama bari in faɗa maka wannan gaskiyar dai wacce baka so, wacce take sawa mu rabu tsiya tsiya. Iyaye sun wuci gaban wasa fa, ya kamata ka dawo hayyacinka ka sani matarka bata isa ta kama ƙafar ƴan uwanka ba ma, balle iyayenka. Sannan ka sani suna da damar da zasu aura maka mata uku ba tare da saninka ba. Sabida sanda suka haifeka ai ba sanar da kai su kai ba. Ni a gaskiya lamarin yanda kayi watsi da dangi da iyaye abun ya ɗaure mun kai, domun ban sanka da hakan ba sam, nasan kai mai bala'in son danginka ne. Yarinyar da suka aura maka ƙanwarka ce, gashi ta zama matarka ni dai ina roƙonka ka riƙeta da amana, kar ka ruguza muku zumuncinku mai daɗi da ban sha'awa, ka riƙe ƴar mutane da gaskiya, kaine dai shugaba, ni wallahi sai in ga kamar tsoron Kofur Zubaina kake yi mijin police ko dai kashi take baka ne a ɗaki?" Ya ƙarashe zancen nashi da barƙwanci, Ahmad Abokinane tare muka taso mu kai wasan ƙasa dashi, a bayan layinmu a Damaturu yake, ada shima yana aikine a kamfanin rodi dake garin Kaduna, daga baya kuma sai ya bar wajan, ya koma Lagos da zama, a ƙarƙashin kamfanin shinkafa, daga baya kuma aka kamashi da yi ma kammani ɓarnar dukiya, Kamfani tace bazata yarda ba, shine har firzin. Da taimakon Allah dai na shiga na fita, aka siyar da motarshi da gidanshi na nan Kaduna, aka biya kamfani kuɗinta, shine har ya samu ya fito,amman aiki yaƙi samuwa, sai ƴar buga buga da yake yi a can Lagos ɗin. Matarshi Hajara kuma itama ƴar Damaturunce. Munyi aure da Zubaina da shekara biyu ya Auri Hajara, soyayyar da su kayi bata wuce ta wata shida ba, Ahmad ya aureta, ya kawota garin Kaduna suna zaune a hayin malam Bello, wajan makarantar silver bright. Yaransu Uku Biyu mata, sai Namiji da take goyonshi a yanzu. Harara na zabga mishi nace dashi. Ahmad kenan, ni sai in dinga tantama anya kuwa ka damu da farin cikin rayuwata kuwa? Allah shi ya halicceni ya kuma halicci so, wallahi so ɗaya ne tak kuma Zubaina nake yi ma shi, bazan iya kasa shi kashi biyu ba. Amman bazan iya cutar da Yahanasu ba kaima ka sani, sai dai fa ni bazan iya zaman aure da'ita ba." Nan mu kaita muhawara a tsakanina da Ahmad ko wannne cikinmu ranshi ya ɓaci, yana nuna mun hanya, amman ƙaunar Zubaina da son danginta ya makantar da rayuwata, irin makantar da bana iya tantance fari balle baƙi. A zuchiye Ahmad ya fita ya barni, hankalina sai ya tashi kuma, dan Ahmad masoyine kuma Amini ɗan ƙwarai, na dinga kiran wayarshi ban samu ba sam, Zubaina ma na yi yunƙurin in kirata amman wayarta ban samu ba. Jinjina nayi a jikin kujera ina tuno rayuwar da nayi da iyayena, da ƙannena masu ƙaunata, sai inji babu daɗi inna tuno da cewar na kan share tsawon watanni ba tare da na kira wayarsu na ji lafiyarsu ba. Kuɗina bazan iya tuna yaushe rabon da ya shiga hannunsu ba, in je in gansu abun ya zamemun nauyi. Wunin yau ban yi aikin kirki ba, lokacin tashi nayi na fice a office ɗin na nufi gida, kai tsaye na shige ɗakina, sabida tsabaragen damuwar data fitineni, ko masallaci na kasa zuwa a ɗaki nayi magriba nayi isha, bana fatan abunda zai sa in haɗu da ƴan uwan nawa ma, dan haushin kowa nake ji, kuma gobe ma da sassafe zan bar gidan, sai dai in ba Zubaina saƙo ta basu. Asiya da Nafisa ne suka bani abinci, na karɓi Bakura da Maryam a hannunsu na shinfiɗesu a gadona, nasan tunda naga Zubaina ta kai yanzu bata shigoba, tana da aikin dare kenan, dan case ɗin ɗan luwaɗinnan ya tsaya mata a wuya ainun, shi yasa ma ban kirawo wayarta ba, dan kar in dameta tana bakin aikinta, kuma dama haka muka saba gudanar da rayuwarmu." Zubaina: Har wajajen Magriba ma bamu samu ganin boka ba, ga mata biyu a gabanmu, mazan kuma duk bokan ya gansu tun ɗazu harma sun tafi. Wani saurayine ya fito, yake mana bayani da gurɓatacciyar hausarshi "Baba yace ya tashi aiki. Ku shigo muje in Kai ku wajan Ungo, ta baku masauki zuwa gobe sai ya soma duba ku" Ni dai wallahi duk na gama sarewa, ga tsoron wajan daya cika mun rai na, ko sallar azahar gashi bamu yi ba, ga magriba tayi. Mabaruka tana riƙe dani muka shiga cikin gidan bokan. Gidane ƙaton gaske, anyi ma gidan ginin dutse, suna kiwon aladu, da karnuka da akuyoyi a gidan, ga mata da yara masu yawa a gidan. Saurayinnan ya kaimu wajan Ungo uwar gidan boka. "Ungo baƙin Baba ne na kwana, a basu masauki." Matar Bokannan ta dube mu tace. "Ku biyoni muje" Muna biye da'ita ina ƙara ƙarema gidan kallo, mutanen cikin gidan ma ganinsu nake yi kamar ba mutane ba. Matan da suke gabanmu kuwa naga su babu fargaba sam a tare dasu. Mabaruka kuwa ita kanta tsurewa tayi. Cikin wani ɗaki ta shiga damu, ɗakine mai ɗauke da gadon ƴan boarding mai hawa hawa, guda biyu, ga kafet shinfiɗe malala a ƙasan ɗakin. Matar bokan tana fita na cabki hannun Mabaruka. Mabaruka ni wallahi tsoro nake ji, yanzu kina nufin a gidan bokannan zamu kwana?" Mabaruka tace. "Haba Zubaina to yaya zamu yi? Kinsan dai ba zamu iya shiga cikin surƙuƙin jejinnan ace zamu tafi ba ko? Kiyi haƙuri in dai da matsala kika zo, matsalarki ta kau." Ɗaya daga cikin matan da muka shigo tare tace. "Baiwar Allah banso na shiga cikin maganarku ba. Amman kin ganni nan,. Sau uku ina kwana a ɗakinnan da mata ƴan uwana musulmai, harma da arnan, babu abunda zai faru dake, da dukkan halamu ke sabon shigan zuwa wajan bokace, ashe sai kin yi fitsari zuwa gobe in kika shiga cikin inda bokan yake. Amman dai in duniya kike nema, ki kwanta kiyi barcinki da munshari dan kin sameta a tafin hannunki. Sai dai fa wannan boka aikinshi akwai tsada, yanzu_yanzu sai ya talautaki, amman ni tsabar iya aikinshi ne ma yasa nake zuwa wajanshi. Dan ban taɓa faɗa mai matsala bai magance mun ba" Ajjiyar zuchiya na sauke, na dubi wannan mata nace. To ya kuke yi ku yi sallah a gidan waɗanda ba musulmai ba kuma? Kinga ko azahar ba mui ba" Dariya ta saka mun tace. "Ki nemi waje ki zauna kinji Zubaina. Allah dai ya yafe, gobe in kika koma kya rama sallar a nitse, dan a cikin gidannan baki ba sallah" Rashin sallar ya jijjigani sosai. Amman haka matannan da Mabaruka su ka haɗu su kai ta fahimtar dani, ala tilas nayi haƙuri. A daren ranar nasha labarai daga bakunan matannan, da irin muguntocin da suke ta aikatawa, da kuma nasarorin da suka samu a rayuwa, da burukansu duk da suka cinma. Wannan hira tasu ta ƙaramin kaifin ilmi, dan na koyi darrussa masu tarin yawa a ciki, haka bacci yai awon gaba dani cike da zabarin son ganin gobe. Bulama kuma text nayi mishi cewar aikine ya riƙeni a office, acan zan kwana, amman gobe da safe zan dawo gidan, ya ba su Mama Gana da Amarya haƙuri" WASHE GARI: Tun asubar fari uwar gidan boka ta shigo tace. "Me gida yace wacce zata soma shiga ta je, ku kuma sauran ku koma kan layi" Da sauri nace. Inason zan zagaya makewayi in kama ruwa" Dan da fitsari tab marata na kwana, amman tsoro da muggan mafarkai sun hanani ko da motsawane" Bayan matar boka nabi, tai mun nuni da ɗan wani lungu. A ƙyamace na shiga nayi fitsarin, gashi ba ruwa, ni tsoron tambayar ruwan nayi tun farko. Ɗan kwalin kayana na cire, shi nasa na goge gabana na miƙe da sauri, dan sai naji kamar ana tawowa. A waje na samu Mabaruka, da Kattume a zaune a layi, Mansa itace ta shiga wajan boka. Tafi awa guda kafin ta fito, Kattume ta shiga. "Mansa ki tsaya mana sai mu rage miki hanya, ba kince a Ƙauyan Kamuru kike ba? Ai muma kadunan muka nufa" Cewar Mabaruka. Mansa ta yashe bakinta tace. "Ai kuwa na gode sosai, kunga ma shiga ku ga inda nake zaune ma, mayi zumunci duk da dai na girme muku nesa ba kusa ba. Amman ko babu komai ma dinga bama juna shawarwari. Zama tayi a gefe na, ni dai na ƙosa mu shiga wajan wannan boka. Kattume da yake tace magani da godiya tazo ta yima Boka bata wuce mintuna talatin ba ta fito, Mabaruka tayi mun jagora zuwa cikin bukkar tashi. Muna haɗa idanu cikina ya kaɗa, jikina ya shiga rawa, bokan na ganshi tiƙeƙen gaske sosai, ga idanunshi yayi biyar ɗin na Bulama a ja. Gashi na ganshi ba riga sai zani daya ɗaura, shima zanin iya guiwa, wani irin mugun wari ɗakin yake yi. Ga wasu gumakai masu abun tsoro takota ina a ɗakin ni dai jikina sai rawa yake yi. Uwar gidan boka tace. "Ku samu waje ku zauna, sai kuyi mun bayanin abunda yake tafe daku, in sanar mishi. Take bakina ya shiga kakkarwa, na kasa furta komai. Bokanne naji yayi ma uwar gidanshi yare, yana yi yana zare idanu, ai cikina sai ya ƙara ɗurar ruwa kamar fitsari zai zubo mun. Uwar gidan boka tace. "Yara Boka yace ku nutsu, ki faɗi damuwarki, in kuma kina jin tsoro ku fice ku bashi waje. Mabaruka tayi carab tace. "A'a Ungo wannan dai ƙawata ce, tana zaune da mijinta lafiya iyayenshi suka aura mishi ƙanwarshi, sabida basa son ƙawar tawa. Shine muka zo munason a mallaka mana mijin a hannu, sai yanda ƙawata ta juya shi, daga shi har danginshi, kuma a mantar dashi ƴan uwanshi. Ko iyayenshi ne suka faɗa bama so yayi, sai abunda matarshi tace mishi, duk da cewar daman kusan a hakan yake. Gaula dolo muke so a mayar dashi. Itama Amaryar ta zama sai abunda Zubaina tace mata, ta zame mata kamar baiwa, kuma a rufe mata bakinta karta kuskura ta kai ƙarar Zubaina, a sa mata kwarjininta, da tsoronta a zuchiyarta. Sannan muna son a lalata mishi gabanshi, ta yanda in ya je kwanciyar Aure da Amaryar zai koma kamar lagwani, in ya xo kwanciyar Aure da Zubaina sai ya zama namiji. A taimaka mana." Matar Boka data gama ji, sai ta zayyane ma boka dukkannin abunda yake tafe damu. Yayi magana amman ba mai yawa ba, cikin yarenshi na Tubi. Uwar gidan boka ta dube mu tace. "Yace duk abinda kike buƙata zaki samu, amman da sharaɗin duk abinda zai biyo baya kar ki zargi kowa. In dai mallakar miji da kishiyane kin samu, kuma har ki mutu kece sarauniya a gidanki" Da sauri nace. Na yarda da duk abinda zai biyo baya in dai ba mutuwa ko hauka, ko rasa Bulama bane, ni kuma a shirye nake ko nawa ne in kashe, ko da zan tafi tsirarane" Uwar gidan boka ta isar da saƙona ga boka. Dariya yayi, ya ɗaga hannayenshi dukka biyu sama, ya dinga wasu surkullen maganganu da ƙarfin tsiya. Sai ga wata ƙwarya ƙarama da wani tsumma ƙulle a hannunshi. Ƙwaryar ya sauke, ya miƙo ma Uwar gidanshi, tasa hannu ta amsa ta miƙo mun. Da sauri nasa hannu na karɓa. Wani irin maganine mai mugun warin tsiya, ga wani irin hunhuna da tsutsa a saman kwaryar. Amman haka uwar gidan boka tace in shanye maganin tas. Dana kafa kaina, na runtse idanuna ban ɗago ba, har sai da na shanye. Ƙwaryar na ajjiye ina ɗaga kaina sama dan wani irin amai ne naji yana taso mun. Wani ƙullukan magani ta karɓo a hannun boka ta ajjiye a cikin tsumma a gabana. "Wannan wanka zaki yi dashi da kin je gidanki. Wannan kuma kwalline wanda aka haɗa da kitsen maciji, da kitsen biri, shi kuma a ko da yaushe idanunki ya zama yana saye da kwallinnan, sharaɗin shine daya ƙare zaki dawo a baki wani. Wannan kuma hayaƙin gidanki zaki yi dashi, ki tabbatar mijin naki, da ita amaryar sun shaƙi hayaƙin a dai dai sanda yake tashi. In zaki zuba hayaƙin a wuta, ki ambaci sunan mijinki sau uku, kishiyarki sau uku, sai ki zuba hayaƙin. Wannan kuma a abinci zaki zuba musu, an gama in dai sun ci. Shi kuma wannan layar, a bayan ɗakin baccin mai gidan naki zaki tona rami ki birne kuma tsirara zaki yi sanda zaki birne layar, kar ki kuskure, sannan kar ki bari kowa ya ganki. Kuɗinki million ɗaya. In zaki dawo karɓar kwalli da wasu hayaƙin kuma dubu ɗari biyu zaki riƙo duk zuwa." Cike da murna na zuge jakata nayi ƙarkaf, Allah ya soni ma kuɗin sun kai, har da ɗoriyar dubu goma sha ɗaya, duk na tarkata na ajjiye musu. Muka fito da baya, kamar yadda aka umarce mu. Mansa na ganinmu ta miƙe tana yashe baki. "Har kun fito, sai mu je ko?" Jerawa mu ka yi, muna tafe Mabaruka na yi mun Dariya. Mansa tace. "Ai daga yanzu kin dena bin ƙananun bokaye, shifa akwai biyan buƙata, sai dai ƴan siyasa da masu sarauta sun ɓata shi da tsadar tsiya, ni yanzu dubu ɗari biyu ya chajeni na magani kawai, banda sauran ƙananun abubbuwa. Sai dai fa zuwa wajanshi na sa talauci. Dan wallahi da mijinmu mai arzikin gaske ne, amman a halin yanzu komai nashi ya ja baya, kuma ya tabtabkar asarori masu tarin yawa manya_manya. Amman wallahi ko nawa ya samu a gabana yake zube mun su, ni ke siya ma kishiyoyina hatsin da zasu ci, in fa naga dama kenan. In kuwa banso ba, sai dai ko wacce ta yi surfau ko wankau ta ciyar da kanta da yaranta." Mabaruka tace. "Ni kaina sanadin zuwana nan, na rasa abubbuwa da yawa, hatta Adamu sai da samun kuɗinshi ya ragu. Amman babban farin ciki shine ka mulki miji, ka juya kishiya yadda ranka ya so, kuma sai yanda ka tsarama mijinka sannan zai bi" Ni dai bana ma jin me suke cewa sosai, hankalina yana gida, burina in isa gida, ko dan in soma zartar da aikin da boka ya bani" MRS BUKHARI CE. Ina siyar da turaren wuta da humra, da KULACCHAM, ƙamshi nauyi da ban daban. Akwai shu'umar humra ma, ga turarukan tsugunno, ga turaren turara jiki, dana turara kaya, mopping musk, Arebian Roomfresher, turaren kafet da dai sauransu Mrs Bukhari ta tanadar muku domun samun nutsuwarku. Mai buƙata ya tuntuɓeni (08179523215) ina maraba da masu sayen ɗaya ko sari. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._ _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal. Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. [26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) GAWURTATTU UKU 9 Yahanasu: Tun asuba su Yanunu suka kammala shirin tafiyarsu tsab, harma su Bulama ƙarami ya saka musu jakunkunansu a mota. Ni kuwa ina kwance ina hawaye, ga wani irin mayen zazzaɓi wanda dashi nake tashi a bacci. Wakil ne ya leƙo ɗakin da muke yace. "Yahanasu mu kam sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, sai kun zo ganin gida, aita haƙuri. Ba Bagulaji Bulama Babba ya ba mai gadi dubu hamsin wai a baku, shi ya tafi wajan aiki. Matar gidan ma a wajan aiki ta kwana, ƙannenta da yaranta ne a cikin gidan. Mama Gana wacce ke tsaye tana gyara tsaiwar lafayarta tace. "Kamar yadda ya bar ma mai gadi sallahu, nima ga sallahu ka bayar a ajjiye mishi. Dan ubanshi tun kafin yazo duniya muke ta'amali da kuɗi, da wannan kuɗaɗe aka gina mishi rayuwarshi ta fannin ilimin addini dana zamani, dan haka ba kuɗi bane ya kawo mu, a bar mishi kuɗinshi. Yanunu, Bagulaji ku tawo mu tafi." Fita su ka yi duk rayukansu a jagule ba daɗi, Fanda ta dafani taji jikina kau. "Subuhanallahi Yahanasu naji jikin naki da zafi sosai ai" Ina sharar hawayen da ya zame mun jiki nace. Babu damuwa zan lallaɓa in sha magani, in naji jikin babu daɗi zan yi ma Bulama Babba magana ya kaini asibiti." Allah ya ƙara sauƙi tayi mini ta fita, Kuɗi na ciro nera dubu goman da Alhaji Munka'ilu ya bani, na danƙama Hajja Fati. Gashi nan ki kama sana'a kuma da zaran sana'arki ta kafu, sai ki yi ƙoƙarin komawa makaranta ki kammala karatunki, da zaran kin soma aiki, wasu matsalolin sai su kau" Karɓan kuɗin tayi tana godiya. Takaddar magani fara ta miƙomun cike da magunguna, nasa hannu na karɓa. "Yahanasu, karki bari kaɗaici da tunani, da takaici ya haifar miki da ciwon hawan jini, ko ciwon zuchiya, ki kashe rayuwarki a banza da wofi. Ciwon rashin bacci shi kanshi yana iya haukata mutum, wannan maganin baccine, da zaran kin kasa bacci ki sha guda biyu kawai, dan ki samar ma kanki da ƙwaƙwalwarki hutu da sauƙi. Bazai gusar miki da hakali ba sam, zaki yi normal bacci daga dare izuwa safiya, kuma duk cunkushewar da zuchiyarki tayi, zakiji nauyin yayi ƙasa wanda in a sikeli za'a ɗaura a auna bai wuce nauyin kwalin omo ba" Hannu nasa na karɓi maganin na ja durowar gefen gado na jefa. Tare da Hajja Fati muka fita, nayi sallama dasu, Ba Bagulaji sai hawaye take yi, ina tsaye a wajan har suka fice mai gadi ya rufe get ɗin gidan. In ɗaga ƙafa in koma ɓarayina abun yaci tura, kuka kawai nake yi, ina tuno mahaifana da dangina. Ƙannen Zubaina ne suka zo suka wuce ni, hannunsu jaye da yaran. Sai habaice_ habaice suke yi, suna zage _zage. Juyawata nayi na koma ɓarayina, a kujerar falo na kwanta, nan jikina ya shiga rawa, gashi bani da mataimakin da zai taimakeni. Kofur Zubaina: A ɗakin Mansa mu ka rama sallolin da ake binmu, dan ni dai kam sun riƙe mun wuya sosai. Anan muka ga irin mulkar abokan zama da Mansa take yi, dakama kowa tsawa take yi harda mai gidan, hakan ya ƙara mun ƙaimi sosai. Anan mu kai musayar number waya, muka kama hanyar Kaduna. Muna shiga Kaduna wayata ta soma ring, Bulama ke kirana. Allah ya taimaki mai taimakona, barka da safiya ango mijin amarya. Wato ko ɗan kiran da ka saba mun in zanyi aikin night jiya ba kai mun ba ko, harma na soma fuskantar canji kenan Bulama, duk ƙoƙarin danne kishina da nayi dan samun nutsuwarka? Ina kaiwa ƙarshe na fashe da kukan makirci har ina wani jan majina. Gabaki ɗaya na gama rikita kan Bulama, dama abu kaɗan ke ruɗashi, bashi da jumurin shanye abu, murya a raunace kamar mai shirin yi mun kuka yace. "Haba rayuwata, uwar ƴaƴana kiyi haƙuri ki share hawayenki, ni wannan yarinyar bata sani a idanunta ba wallahi, dan ko su Mama Gana ban bari mun haɗu ba." Jin ya furta haka sai nayi cak da kukan da nake yi mara hawaye, na karya murya nace. Nayi haƙuri uban ƴaƴana kishine ya motsa mun raina, kai kasan ina sonka, kuma kaine gatana, gatan dangina ma." "Nasani Zubaina ta, ina sonki, babu wani abu da zai iya taɓa sonki a zuchiyata, ni kin ganni a office ma. Dan da asuba na fice a gidan, yau zasu tafi, na dai ba da saƙon dubu hamsin ma mai gadi, nace in sun fito zasu tafi ya basu" Wani tuƙuƙin baƙin cikine ya turniƙe ni. Amman sai na shiga jero mishi adda'ar buɗi a bisa ƙoƙarin da yake dashi. "Babu komai matata, da daddare sai mu je mu dobo atampopin in mun dawo aiki ko? Sannan zan turo miki dubu ɗari ki riƙe a hannunki kya biya kuɗin ɗinki dasu. Far nayi da idanu nace. Godiya nake yallaɓai Allah ya ja kwana. Cikin taushin murya yace. "Ameen matata, bari inyi aikina, dan inna biye miki ke da zaƙin muryarnan taki, sai jikina duk ya mace" Dariyar da nasan in nayi ina motso mishi da duk wata sha'awar kasancewa tare dani nayi, kana nace. Ka shirya, domun yau zan kai ka ɗakin amarya ni da kaina, dan har kazar Amare ni da kuɗina zan siya ma, kai dai ka sha kuruminka. Ƙit ya datse wayarshi. Dariya muka saka ni da Mabaruka harda tafawa, tace. "Ƙawata bakya wasa da maza, ƙawata yanzu fa da ba dan kin cabki Bulama ba ko? Hmm yau da zai yi kwanan ɗakin Amarya wallahi da kinga kumumelesi. Ke ni fa ranar da Adam ya kwana a ɗakin Sagira kin san dan munafurci na maza har wani ihu ya saki, mutumin da ko nishi bayayi sai gashi ya ɓige da ihu. Jin wannan ɗan ƙara da Adam ya saki sai naji zuchiyata kamar zata tarwatse, banyi ƙasa a guiwa ba na fito saɗab saɗab na laɓe a tagar uwar ɗakinsu. Hmm takaici wallahi Zubaina ashe sambatu Adam ya shiga yi ma Sagira har yana ce mata yanzu yasan yayi aure, ashe mata suna suka tara. Ke haukatani fa Adam yayi, kiga yanda na fige na rame ni da gidana fa a lokacin" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Amman lallai maza basu da mutunci akan son ransu, yanzu yana nufin kenan Sagira ta fiki komai kenan a wajanshi,mu da muke aika kuɗin magungunan mata har togo. Hmm ai ni bazan lamunci ganin takaici ba, yanzun ma ji nake kamar bazan iya barin Bulama ya dinga yi mana wani rabon kwana ba" "Ƙawata wai ashe har yanzu tantama kike yi a aikin bokannan, duk abinda kika gani a gidana, da wanda kika gani a gidan Mansa, dana bakunan mutanen da muka haɗu duk baki gamsu ba wai? Hmmm ranar da nayi duk abubbuwan da bokannan ya sani, daga ranar har rana mai kamar ta yau Adam bai sake kusantar Sagira ba. Ɗan data haifa ma Allah ya ƙaddara zai zo duniya ne, tun a ciki nake aika mishi da boma bomai, shi yasa kika ga yazo ba lafiya, aikinane fa" Baki na washe ina dariya nace. Gaskiya ƙawata baki da dama, kinci dubu sai ceto." Ƙaran kiran wayata ne ya katse mana hirarmu A S P ke kirana, nasan akan case ɗin ɗan luwaɗinnan ne yasa ya kirani, ni nama sha'afa. A ƙofar gidan Mabaruka na tsaya, sannan na ɗaga wayar. Adam ne ya zo ya buɗe ma Mabaruka ƙofar mota ta fita, ya amshi jakarta suka wuce, suka barni da sakakken baki. Daga nan aiki kuma na shiga, naje na gabatar da duk binciken daya dace, a hanyar zuwa office na tsaya na sai waina da miya, lokacin har azahar tayi, ni nama mance ko karyawa bamu yi ba, in banda shayi da mu ka sha a gidan Mansa. Daga nan na wuce office na soma gudanar da aiyukana. Da yamma na fito na tafi gida. Duk a gajiye nake tulus sosai. Harara na doka ma BQ ina jin wani tururin kishi na rufe ni. A guje Maryam da Bawa suka tare ni, sunata murnar ganina. Kawunansu na shafa, ina jin farin ciki sosai. Babu abunda yake burgeni sama da kasancewa a cikin iyalaina. Asiya ta amshi jakata, Nafisa tace. "Anty tun ɗazu fa Mama take zaune tana jiranki." Ah da gaske Nafisa?" Nafisa tace. "Ai ta jima sosai a ciki" Da sauri na shiga cikin falon. Na tarar da Mama tayi baje baje a ƙasa tana cin shinkafa da miyar kaza, ga lemon kwalba da ruwan faro a gabanta. Wani daɗi naji sosai. A ko da yaushe in Mama tazo gidana tana santin irin daɗin da Bulama yake bamu, sai inji na tausaya mata, a lokaci guda kuma sai inji daɗi dana samu damar mallakar Bulama, dan ya tsamoni daga cikin ƙangin talauci, dama dai dani kab ƴan gidanmu suka dogara, ni kaɗaice nake aiki, su ko karatun kirki basui ba, in banda yanzu da Bulama ya ɗauki nauyin karatun nasu har zuwa jami'a. "Zubaina kin dawo? Ke zauna inna gama fasa ƙashinnan mayi maganar" Dariya na saka mata nace. Mama amman muje can ɗakina, dan Bulama ya kusan shigowa, kinga biyar ta gota, duk yanda akayi go slow ya samu a hanya ma." Abincin na ɗaukar mata muka shige ɗakina tare da banko ƙofar. Anan na labartama Mama duk halin da ake ciki, da magungunan da aka bani. "Da kyau ƴarnan ai ba'a bori da sanyi jiki. Jiya banyi baccin kirki ba, sai mafarkai nake yi, wai Bulama ya sakeki yayi miki korar kare yayi miki kafirin duka." Bakinta na toshe. Haba Mama wannan mafarki yayi tsauri da yawa. Aini da Bulama tamkar takone da ƙafa, mutuwa kaɗai ke iya rabasu." Magunguna ta sunto a bakin zaninta tace. "Kinga wannan, a cikin abun sha zaki zuba mishi, yai ta sha. Wannan kuma da jinin al'ada ake haɗawa a kwaɓa, na ranar farko, sai ki gasa naman saniya dashi ki bashi yaci. Shikenan fa ƙurunƙus" Godiya na shiga yima Mama. Haka na shiga store na haɗo musu kayan abinci rigijib, na je na sauketa a gida, a gurguje na dawo. Nako ci sa'a Bulaman bai dawo ba. Wanka na faɗa nayo da wannan garin maganin. Na tsara kwalliya na fito fes dani a cikin goduwar rigar kanti baƙa, na rambaɗa kwallin wajan boka, na fito shar. Daddumar cin abincinmu na nufa na buɗe kular miya na barbaɗa garin magani, miyar kajine zuƙu zuƙu. Ina miƙewa Bulama ya shigo kici_kici da manyan ledojin shagonshi dake kan titin isa kaita, shagon saida dogayen riguna na mata da maza irinna ijib. A guje Bakura da Maryam suka fito daga ɗakin su Asiya, sun riga sun haddace dirin motarshi. Sakin ledojin yayi a ƙasa, ya ɗaga Maryam sama yana ta juyi da'ita suna dariya. Bawa kuma ya kama mishi ƙafafunshi sai tsalle yake yi. Daya sauke Maryam sai ya ɗaukeshi shima. Sannu da dawowa Yallaɓai, yau me ya tare ka ka makara?" Ɗagowa yayi ya dubi tsakiyar idanuna: BULAMA: Kallon Zubaina nayi cike da so da kulawa, gabana ya bada wani bugu mai ƙarfi, take kaina ya sara mun, har sai da na ɗan kanne idona na gefen hagu. Sannan na sauke ajjiyar zuchiya, na kuma dubanta, sai Murmushi take zabgawa tayi kyau sosai, sai ƙamshin turaren Dubai gold take yi. Ke dai bari, kece kika sani makara, dan naje shagone na ɗebo miki wasu dogayen riguna da aka kawo su yau, wannan ledar kuma ki miƙa ma su Asiya suma ƴan mata su saka. Wow kinyi kyau fa gimbiyata" Dariya mu ka yi duka. Ɗakina na nufa, ita kuma na barota a tsaye tana kiran Asiya. Wanka nayi da ruwa mai zafi, kaina naji yana ta tsananta ciwo sosai, ga zazzaɓi da ke shirin kamani. A daddafe na ɗauro alwala na fito. Baƙar jallabiya na zura, ina kan fesa turarena mai suna one million sai ga Zubaina ta shigo. Gabana tazo ta tsaya, ta ƙura mini idanu, yau idanun nata sai naji kaifinsu tamkar yana kekketamun jikinane. Yallaɓai mun fa gode sosai da irin wannan ɗawainiya da kake yi, ubangiji Allah kar ya gajiyar dakai wajan kula damu." Hannu nasa a ƙugunta na hankaɗota jikina ta kuwa rumgumeni. Kaina wani irin saramun yake yi sosai, ba shiri na sake ta, na zauna a bakin gado dafe da kaina wanda nake jin kamar zai tarwatse. "Lafiya kuwa Abban Maryam naga ka dafe kan ka?" A hankali nace mata. Kai nane yake wani irin ciwo, sai sara mun yake yi. Kwakwalwar tawa kamar zata huje haka nake ji" Take Zubaina ta ruɗe ta shiga yi mun aikin sannu, gashi sai kiraye_kirayen sallah ake yi. Amman bana jin zan iya zuwa masallaci. Magani ta ɓallo ta bani da ruwa. "Gashi kasha, sai ka ɗan kwanta, inya lafa maka sai kayi sallar." Baki na buɗe ta zuba mun ƙwayayon maganin guda biyu, ta bani ruwa na kora. Sai taga na miƙe kuma. Da zafin nama ta zaunar dani. "Ina kuma zaka a cikin wannan halin?" Sallah kina ji har an shiga Masallaci, kinsan ita Magriba lokacinta ƙanƙanine" Kai ta girgiza mun tace. "Ina sai dai kuwa kayi sallarka a gida, komai sai da lafiya ake yi ai." Dadduma ta shinfiɗa mun, sai da na tada sallah sannan ta fita. Raka'ar ƙarshe sai a zaune na kawota, dan ciwon kan sai tsananta yake yi. Ina idarwa na kwanta a kan sallayar. Da sallama Zubaina ta shigo, hannunta ɗauke da babban farantin silba, da kuloli biyu a kai, da sauran tarkace. "Sannu ya kan?" To gashi nan dai. Zazzaɓi ma nake ji dai" Jikina ta taɓa, ai kuwa ta same shi kau. "Subuhanallahi ko asibiti zaka taso in kai ka ne, jikin naji da zafi kau? Janyota nayi jikina, na ƙanƙameta tsam sam bana fatan abunda zai sa ta motsa, ɗan dama dama na soma ji. Da ƙyar dar na daure naci abinci, dan kar in ɗaga mata hankali sosai. "To abu na farko da za'ayi shine, ya kamata kaje kaga halin da Yahanasu take ciki ko? Sannan sai ku tawo nan taci abincinta. Daga nan kuma ni da kai sai muje mu siyo kazar sayen baki, in kai ka ɗakin Amaryarka." Ƙur nayi mata da idanu cikin ɓacin rai sosai, dan banji daɗin yanda ta dangantani da Yahanasu ba sam. In hakan kike so ai shikenan, kin nuna mun baki damu dani ba, kuma bankai ki kiyi kishi akaina ba....." Shishsh ta ɗaura yatsanta akan laɓɓana, dole na dakatar da magana. "Bana son musu, kai dai je ka kirawota ku dawo tare. Wannan yarinyar bazan so ka shiga hakkinta ba. Su Ba Bakura ne fa suka aura maka ita. Ya zamemun dole in tayaka kai musu biyayya, wala Allah sa dena ganin baƙina. Kai dai kayi abunda nace kawai." Allah yayi miki albarka ƴar aljanna" Miƙewa nayi na fice a ɗakin, na nufi BQ ba don son raina ba, sai don in faranta ran Zubaina. A takure a kan gado na samu Yahanasu sai rawar ɗari take yi. Kaina na kawar nace mata. Ki taso muje kici abinci" Ban jira me zata ce ba na dawo falo, sai kallon tsarin falon nake yi. Idona ya kai wajan daining da aka mayar mata kitchen yayi kyau sosai. Sanye cikin farin hijabi har ƙasa ta fito. Sai ƙamshin humra take yi. Ina gaba tana biye dani har zuwa falon Zubaina. Yahanasu: Ba dan inaso ba na biyo Bulama Babba. Na biyo shine dan bana son yin musu dashi. Da siririyar sallama na shiga falon, Bulama na gabana. Wani hayaƙi na shaƙa mai ɗan karen yaji, take naji na sheƙeshi ya shigemun kwakwalwata, hancina duk ya buɗe. Sai naji kamar kaina na juyawa. Ahankali na soma karanto addu'o'in tsari da kariya. Waje na samu sai da nayi bismillah na zauna. Ina wuni Anty?" Nace da Kofur Zubaina da take tambayar Bulama Babba ya kan nashi. Cikin fara'a ta amsa mun gaisuwata. Bulama Babba yace. "Inaga gajiyar aikine, amman sai nake jin sauyi sosai a jikina. Amman ciwon kan da sauƙi, ina yarannanne?" Zama yayi a doguwar kujera, Kofur Zubaina ta zauna a gefenshi tace. "Asiya tana tsakar gida tana zance, Alhaji ne yazo wajanta. Nafisa kuma tana ciki tana chatting kasan ƴan mata da shegen son chart" Kai kawai ya girgiza ba tare da yace komai ba. Kofur Zubaina ta dubeni tace. "Bari a kawo miki abinci ko Yahanasu? Kiyi haƙuri bamu daɗe da shigowa gidan ba. Zan kawo miki angonki har ɗaki zuwa anjima" Ni dai kaina na sunkuye bance mata ci kanki ba, sai adda'a nake jerowa dan kaina ji nake kamar zai buɗe. Abinci ta kawo mun a plate da ruwan gora. Ni da nake fama da zazzaɓi bakin nawa babu daɗi sam. Amman gudun kar rashin cin nawa ya jawo wata matsala, sai nayi bismillah na soma ci. Noma baifi biyar nayi ba, na ajjiye abincin nasha ruwa. A hankali nace. Nagode Anty, ni zan tafi sai da safe" Wani murmushi tayi mai ma'anoni da dama tace. "To shikenan Yaha, sai na kawo miki angonki. Murmushi kawai nayi na fice abuna, bakina ɗauke da adda'a dan ji nake tsigogin jikina sai miƙewa suke yi. A hankali nake tafiya har na isa ɗakina, ban zauna a falo ba, ciki na kutsa kaina na shiga. Sallar isha na gabatar, sannan nayi azkhar ɗina. Ban gushe ba na jawo Qur'ani na soma katanta baƙara. Ina cikin karatunne wayata ta soma ringing. Hannu nasa na jawo wayar. Dala ne yake kirana, cikin zumuɗi na ɗaga wayar tare da karawa a kunnuwana. Amon sautin tane ya cika mun kunnuwana. "Yahanasu ina fatan dai kina lafiya kuma babu wata matsala ko? Dan Yanunu ta sanar dani irin tarbar da kuka samu a wajan Bulama Babba da matarshi. Ran Babanku Ba Bakura ya ɓaci sosai, dan bai daɗe da yin shiru ba, yau yayi faɗa sosai. Hajja gana tayi kuka kamar me" idanuna na lumshe, tausayin kaina da tausayin su Ba Bakura da su Ya Innana ya kama ni. Allah sarki uwa mai daɗi, jin muryarta ya sanyaya zuchiyata sosai, sai naji kewarta ta sake ɗaureni, cike da son kwantar musu da hankali nace mata. "Ya Innana wallahi babu komai, ɗazu ma Bulama Babba yazo ɗakina ya kirani, muka je babban falon gidan mu ka ci abincin dare, dan bai jima da dawowa daga aiki ba." Murmushin jin daɗi tayi tace. "Yanzu yana ina shi Bulaman?" Da sauri nace mata. Ya ɗan fita ne, amman ba jimawa zaiyi ba." Sai na kawar da zancan da tambayar yadda su Yanunu suka isa gida. "Lafiya lau, Yanunu gata nan tana baccin gajiya, Fanda kuma tana ɗakin Mamanku Bagulaji duk sai gobe zasu koma gidajensu." Ɗan murmusawa nayi nace. Ya sababbin Amaren gidanmu? Sai ranar da Bulama Babba ya kawo ni zan gansu, amman zan kira su Amada gobe sai duk su bani mu gaggaisa" "Hakan yayi kyau, kuma suma zasu ji daɗi. Da ko ɗazu sun kakkawo mana amaren har ɗaki anga juna. Ke dai abinda nake so dake shine, ki yi haquri da dukkan abunda zaki gani, ki kuma runtse idanunki, da kunnuwanki. In Bulama na ɗakinki miji in baya ɗakinki Yaya. Sannan ki dinga ziyartar gidan Babanku Alhaji Munka'ilu, ɗazu ma Ba Modu ya kirawo mun Hajiya Ramlatun nayi mata godiya a bisa aiki data sama miki. Kai mutanen suna da karamci, Alhaji Munka'ilu mutum ne guda da ɓari gaskiya" Mun jima muna taɓa hira, daga baya ta miƙa ma Dala wayar, muka ɓige da hirarmu ta zumunci, sannan mu kai sallama. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da yin Murmushi. Jin muryar Ya Innana da Dala ya matuƙar faranta raina. Sallama nake ta faman jiyowa a cikin falo. Da sauri na zari hijabina na fita falon. Zubaina na gani a tsaye sai kalle kalle take yi tana jijjiga kanta. Bulama Babba kuma yana daga bayanta, kamar wani yaronta. "Shige ciki ka zauna yallaɓai." Wuceta yayi, yaima kanshi masauki a 1 sitter. Zubaina ta dubeni tana sakarmun murmushi tace. "Amarsu ga ango na kawo miki fa. Kiyi haƙuri abokanshi duk na wajan aikine, Ahmad kuma baya kusa balle ya rakoshi. Ki zauna mana" Zama nayi a kujera mafi kusa dashi. "Masha Allah waje yayi kyau, cancaɗi. Yaha ga Bulama na kawo miki, zaiyi kwana bakwai a wajanki kamar yadda shari'a ta tanadar da hakan. Daga baya sai a soma rabon kwana kuma. Amman kiyi haƙuri ke zaki dinga yi muku girki. Kinga ni ma'aikaciyace bana zama sam. Kece a gidan ko da yaushe. Ango ni kam sai da safenku, ga kazarku nan" Ledar dake hannunta ta ajjiye a gefen ƙafarshi ta fice. Binta yayi a baya. Ajjiyar zuchiya na sauke kawai. Wai yau Bulama Babba aka rako ɗakina, da sunan mijina Allah me iko. Na tuno lokacin da nake zuwa ɗakinshi da kuka, a duk ranar da nayi ɓarna Ya Innana ta dake ni. Ranshi ba ƙaramin ɓaci yake yi da Ya Innana ba. Ita kuma tai ta mana dariya. Ina cikin tunaninnan naji shigowarshi, ba ko sallama. "Ki ɗauki kazar ki je kici, in kuma kin ƙoshi sai ki adana, kije kiyi kwanciyarki." Jikina a mace na ɗauki kazar naje na adanata a kitchen, na koma ɗakina. Ƙarfe sha biyu, ƙarfe ɗaya, ƙarfe biyu. Bacci ya gagari idanuna, sai tunanin duniya dake shirin tarwatsa mun rayuwata. Lokaci guda, komai na rayuwata ya jagule, ada ina rayuwa cikin walwala da farin ciki. Amman lokaci guda ɓakin ciki da damuwa suka maye gurbin walwala da farin cikina. Zubda hawaye ya zama aikina, bani da aikin daya wuce tunanin halaka kaina. Tashi nayi na soma abinda zai fishsheni duniya da lahira. Wajajen ƙarfe biyu da arba'in na soma jin motsin kamar ana haƙar wani abu a tsakar gida. Tsoro ya kamani sosai, da sauri na haye gado na duƙunƙuna a cikin bargo. Adda'a kuwa bata subce a bakina ba. Duk tashin hankali baya hanani karanto adda'a, sabida da irin wannan ginin Ya Innana ta gina ruhinmu. Macece ita mai sani, tana da ilmi a ɓangaren addini, dan ko digri ɗinta a fannin addini tayi shi, a jami'atul madina. Sannan bata gushe ba sai da tayi mastas ɗinta duk a ɓangaren abinda ya shafi addini a misra. Kanuri mutanene masu son addini, da karatun Qur'ani. Suna bama karatun addini mahimmanci fiye dana bokon. Da haka wajajen uku da rabi na dare bacci ya ɗebeni. Mugayen mafarkai ne suka farkar dani, wajan huɗu da rabi na asuba. Mrs Bukhari ce *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._ _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal. Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) GAWURTATTU UKU LAST FREE PAGE 10 Baccin da nake samu, baya wuce na awa biyu, wata ran na awa ɗaya ma nake samu, shi yasa kullum kaina a cikin ciwo yake. Adda'a na yi akan Allah yai mun tsari da abunda na gani a cikin mafarkina. Gabaki ɗaya jikina sai naji yana mun wani iri. Ba shiri na ɗauro alwala na soma karatun Qur'ani ba ƙaƙƙautawa, shi kaɗai ke iya sani samun nitsuwa, inna jini a makamancin irin wannan yanayin, duk da yau yanayin ya banbanta da irin yanayin da na saba shiga a baya. Ina zaune akan sallaya har akayi kiran sallah. Tashi nayi na gabatar da raka'atanil fajir, sannan nayi sallar asuba. Zama na gyara na dinga ragargazo mana adda'a ni da Bulama, tare da roƙon Allah ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna, ya bani juriya da jumurin shanye duk abinda zai faru. Sai ƙarfe bakwai na tashi akan sallayarnan, bayan na yi azkhar. Kaina kamar zai tarwatse na fito falon. Ba kowa, nayi tunanin yana ciki ma, ashe baya nan. Kitchen na nufa, nayi jim na rasa me zanyi da safennan ni ba kayan miya ba. Gas na kunna na ɗaura ruwan tea, nasa kayan ƙamshi niƙakke wanda aka yishi musamman na tea ne wato tea spices. Daya tafasa na tace, na zuba madara. Na buɗe fantekar alkaki da nakiya na shaƙe plate dashi, na ɗaura komai a tire. Fitowata daga Kitchen yayi dai dai da shigowar Bulama Babba. Cikin shirin zuwa office sai ƙamshin yake yi. A hankali na isa inda yake, bayan na ajjiye tiren akan teburin dake tsakiyar ɗakin. Ina kwana Bulama Babba?" Sai da ya zauna, ya amsa babu yabo, babu fallasa. Sannan yace. "Inason zan kafa miki wasu sharaɗi, daga yau kece zaki dinga komai na aikin gidannan. Tun daga kan girki, kawo wankin yara, da wankin motata da motar Zubaina. Ke kuma bazaki tuƙa mota ba, dan haka ki ɗakko mun key ɗin motar, zan yi kyauta da'ita. Zan baki kuɗin cefane ki je kasuwa ki siyo kayan miya, da duk abunda baki dashi na girki. Sannan ki sani bama cin yaji, sannan kar kiyi burabusko dan Yara basaso" Tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Jikina a mace na miƙe na shiga ɗaki dan ɗakko mishi key ɗin motata. Shi kuma ya gyara zama tare da jawo teburin da abincinshi yake kai zuwa gabanshi. Ina shiga ɗaki na ɗakko key ɗin motar na fito. A gabanshi na durƙusa na ajjiye mishi keyn a gaban tiren abincin nashi. Harna juya, ya kira sunana cikin sanyin murya. Da sauri na juyo. Idanunshi ya zuba mun, ni kuma na sauke nawa idon ƙasa, hawaye kawai nake zubarwa. Takowa yayi har inda nake, ya miƙo mun kuɗi, hannu nasa na amshi kuɗin. "Kuɗin cefanan kenan, ki nemi kasuwa mafi kusa kiyi siyayyar, ki dafa tuwon shinkafa, miyar egusi. Ki zuba ma Zubaina da ƙannenta ishasshe. Da safe kuma ni bakwai da rabi nake fita office, ga su Bawa suma bakwai da rabi suke fita Zubaina ita fitarta takwas ne, wani sa'in kuma biyar na yamma take fita. Sai kisan lokacin da zaki dinga tashi. Saina dawo kinji ko? Akwai kazarki ta Amarci karki mance da'ita ta lalace" Bakina na rawa, zuchiyata sai tsalle take yi nace. Ubangiji Allah ya dawo da kai lafiya, ya tsare gabanka da bayanka, adawo lafiya, kar ka mance da adda'ar fita a gida" Ina dasa aya na shige ɗakina, tare da faɗawa gado na saki wani marayan kuka. Bulama Babba: Kukan Yahanasu ba ƙaramin gasa mun zuchiya yayi ba. Amman na kasa rarrashinta ko jin tausayin halin data shiga. Asalima gani nake hukuncin da Zubaina ta yanke akan Yahanasun dai_dai ne. Tunda ko babu aure a tsakani, ni wanta ne, dan ta hidimtawa matata da ƴaƴana da suka kasance ƙannenta ai ba wani abu bane. Amman naso Zubaina ta bar mata motarta a hannunta, sai dai tayi fur fur fur, tace sai na karɓo key ɗin motar. Jin Zubaina nake yi a safiyar yau, ta mamaye ko ina na zuchiyata, bana ji, bana ganin kowa. Kuma inaji a shirye nake tsab in mata dukkan abinda zai faranta mata ranta. Numfashi na ja, na fice a ɗakin bana ko waige. A bakin mota na samu Zubaina. Key ɗin motar na damƙa mata, murmushi tayi nima na mayar mata. Ga keyn nan, sannan na isar da saƙonki, harma na bata kuɗin cefane kamar yadda kika ce. So daga yau zata soma aikinta." Dariya tayi tace. "Nima na samu in huta da maganar girki. Tunda mu ba zama muke yi ba, Asiya kuma itace dama mai girkin. Ita kuma aure zata yi nan kusa, Nafisa kuma uwar chart bata iya komai ba. Amman Bulama kayi ƙoƙarin siyo gado yau, sabida a kafa a ɗayan ɗakin, bai dace kaci gaba da kwana a katifa ba." Agogon hannunta ta duba, tace. "Ya kamata ka tafi kar kayi latti ko?" Murmushi nayi, ji nake dan so kamar in cinye Zubaina, nace da'ita. Sai abunda kika ce ai gimbiya" Far ta mun da idanuwa tace. "To nace ka shiga motarka ka tafi. Ina jiran fitowar su Asiya ne, zan sauke su a makaranta." Sallama nayi mata na shiga motata na fice a gidan. Idanu na lumshe, kaina sai aiki yake yi tamkar agogo tsabar chazuwa, sai tunanin abubbuwa barkatai nake yi, a haka har na isa office. Kofur Zubaina: Ihu nayi bayan fitar motar Bulama, lallai wannan boka bala'ine. Ji yanda Bulama ya dawo yaro a gabana, duk abinda nace mishi sai kawai yayi, ba tambayar dalili balle gardama. Hmmm yanzune uwar Bulama zata ɗanɗani baƙin ciki, da yanzu ne wannan mayyar Mama Ganar tazo, wallahi da korar kare zan sa Ɗan nasu yayi musu. Yaha kuwa kashinta ya bushe a gidannan. Ina cikin wannan hali na farin ciki Asiya ta iso ita da yaran. "Asiya maza ki shiga ɗakinku ki kwaso kayan wankin su Maryam dana ƙulle za'a kai wanki, dana Babansu duk ki kwasa ki kaima amarya, zata soma aikin Aljanna" Dani da Asiyan duk muka saka dariyar ƙeta. Maryam da Bawa kuma suka shige mota, sai surutu suke mun. Asiya da Nafisa na hango kici_kici da kayan wanki sun nufi BQ. Basu jima ba suka fito muka wuce. "Anty kinga idanunta kuwa, sun kumbura da dukkan halamu kwana tayi tana shirgar kuka" Murmushi nayi nace. Hmmm ba da ban na tashi tsaye ba, da nice zan kwana ina kukan. Yaushe zan iya. Ba dai burinsu su rabani da Bulama ba, shine yasa suka aura mishi ƙanwarshi ko? To ni na rabashi dasu, ɗan sauran umarninsu da yake bi, yanzu kam babu shi babu su, sai dai su suzo in da yake." Sai hirarmu muke mai daɗi da ƙannena, a makarantarsu na soma saukesu, sannan na sauke su Maryam, ni kuma na wuce office, dan yau operation zamu fita can kabala costine. Wasu ƴan daba ne, suka tada tarzoma jiya da daddare, kuma an shaida mana, yau zasu koma layin, banda kashe matasa uku da su ka yi, a cewarsu fansa ce suka ɗauka. Yau duk wanda ya ganni yasan ina cikin farin ciki, dan ko baki na kasa rufewa. Mama ce ta kirawo wayata. "Zubaina ni na jiki shiru ba wani motsine wai? Nifa ko bacci wallahi ban samu mai kyau ba, tunda kika faɗa mun wannan lamarin." Dariya nayi na girgiza kai, lallai mama tana ji damu sosai, burinta ta gammu cikin farin ciki da walwala. Mama ai aiki ya faɗa, banma yi amfani da maganin wajanki ba, na wannan tubin nayi amfani dashi. Amman Mama a cikin safiyar yau, naga abubbuwa kala kala, duk abinda nace ma Bulama cikin sauri yake yi mun. Hatta motar ita yarinyar da aka aura mishi, nasa ya karɓo motar, bazai yiwu ina hawa mota, itama tana hawa ba. Kuma daga yau, aikin girki, da wankin yara, harma da wankin motocinmu ya dawo kanta. Kuma ita kanta an rufe mata baki, babu wanda zata iya labartama halin da take ciki. Iyayen Bulama kuwa, zan iya sawa yayi musu korar kare in suka zo mun gida. Mama ni wannan bokan ma kaɗai ya isheni, babu buƙatar sai nayi amfani da maganin wajenki" Guɗa Mama ta shiga rangaɗawa, cike da jin daɗi. Na ɗaura da ce mata. Dubu ɗari uku ya bani yace in sai kayan dannar ƙirji, ga dubu ɗari na ɗinki, gashi jiya da daddare mun fita ya jido mun uban atampopi da leshika a gidan Hajiya. Ni yanzu ma in ya dawo inason ya sake mun kayan ɗakina, ayi mun fenti. Dan yarinyar da aka aura mishi ita, an narka mata kuɗi a ɗakinta, kinsan suna da yawa, ga zuchiyar yi" "Kai abu yayi kyau, kice harka ta buɗe sabuwa. Abun alfahari, gashi yau Alhaji Jabeer zai turo magabatanshi gidan Babanku Tanko, zasu ba da sadaki a tsaida rana. Bai daɗe da fita ba shi Alhaji Jabeer ɗin, yazo yana roƙonane akan yana son asa bikin karya wuce sati uku, zuwa wata guda. To shine na fayyace mishi cewar, mu dai ba masu hali bane, yarannan marayune wanda dangin ubansu suka watsar. Ke na farfaɗa mishi gaskiya da ƙarya. Mun kuwa yi nasara, dan yace hatta abincin da za'aci na biki zai kawo, shi dai Asiyar kawai yake buƙatar a wanke a kai mishi. Ai an gama aiki a kanshi, shi kam za'a yagi arziki sosai a hannunshi, gashi ba uwa ba uba, ballantana su zame mana ƙadangaren bakin tulu." Dariyar farin ciki nayi nace. Kai abun yayi kyau, Alhaji Jabeer ai mai kuɗine ɗan kasuwane sosai, zata huta sosai in ta aureshi, kakarku ta yanke saƙa. Zan biyo gidan inna baro wajan aiki, sabida asan me za'a dafa ma baƙin a kai gidan Baba Tankon, in ba haka ba sai su iya kunyata mutane. Kinga da saurayin Nafisa ya shirya ba sai a ganganɗa a ɗauresu tare ba?" Mama tayi maza tace. "Haba wannan yaron ai Nafisa tafi ƙarfinshi, karanbanine kawai irinna yaranmu mu yaku bayi. Ke dai sai kin zo" Da dariya na bi Mama mu kai sallama, ina jin farin cikin ƙanwata zata kasance ɗaya daga cikin matar manya, dan Alhaji Jabeer sanannene sosai, babban shagon sai da kayan dawakai yake dashi a Kasuwar Kurmi dake jihar Kano. A Kanon yake zaune da danginshi da iyalinshi, sanadine yai sanadin haɗuwarshi da Asiya, yabi wanka irinna matan Kaduna, da buɗewar idanu ya ruɗu, bai san kwata ya shiga ba" Yahanasu: Wankin da ƙannen Zubaina suka dure mun a gaba, na tusa a gaba, nayi shiru ina nazari. Wayata ce tayi ƙara, ina jawowa sai naga Ba Bakura ne yake kira na. A hanzarce na ɗaga cike da zabarin son inji muryarshi. Ba Bakura barka da safiya, ina kwana?" Murmushinshi da muka sanshi dashi yayi mun yace. "Yaha ya baƙunta, ina dai fatan ba wani matsala da kika gani ko? In kuma akwai ki sanar tun wuri aiwa tubkar hanci, ni ba surukinki bane, ni ubanki ne, ki saki jikinki" Dauriya na aro na yafa, a ƙoƙarina na son ganin na rungumi ƙaddarorin rayuwata, na sani duk abinda ya faru da bawa rubutaccen al'amarine, kuma ko ba komai Bulama Babba gudan jininane, nasan sharrin matarshi ne kawai wannan, amman na hango tausayina ɓaro ɓaro a idanu da muryar shi. Sannan fatana shine in daidaita BULAMA BABBA da mahaifanshi, ba in ƙara nisantashi dasu ba, nasan suna buƙatar ɗansu, kuma suna kewarshi. Muryar Hajja Gana na ce ta katseni. "Yahanasu kin tashi lafiya, ya tunani an dena dai ko? Murmushi nayi mata, na gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cikin fara'a. "Ina shi Bulama Babban ba dai fita yayi ya barki ba ko?" Ya fita, amman yace bazai daɗe ba. Kinsan aikin banki basa ɗaga ma mutum ƙafa ne shi yasa" Gabana sai faɗuwa yake yi, a karon farko dana yi ƙarya da girmana kenan. Allah yana gani inason in kare BULAMA BABBA daga fishin iyayenshi ne. Kuma hakan dana faɗa ya matuƙar faranta musu rai, dan ina jiyo Ba Bakura yana faɗin. "Masha Allah" Da haka su kai mun sallama. Hijabi na zura, na kulle ɗakina na nufi bakin get, na tarar da mai gadi a zaune a farar kujerar roba, yana jin rediyo. "Hajiya zaki fita ne?" Ya tambayeni yana yunƙurin buɗe mun get. E fita zanyi, inason zuwa kasuwar kayan abinci, ko kasan wata mafi kusa?" "E akwai kasuwar dogo, kasuwace ta kayan masarufi, kuma kayansu ba laifi akwai dama" Godiya nayi mishi na fita. A takaice na fi awa uku a kasuwa ina siyayya, duk na gama jigata, gashi ba ishasshiyar lafiya gareni ba sam. Ina dawowa nayi sallah, bayan mai gadi ya taimaka ya shigar mun da kayan ciki. Sai na fito da wanki shima na shiga yinsu, sauƙin dana samu kayan babu datti, wasu ma kamar ba'a saka ba. Sai da nayi sallar la'asar sannan na ɗaura girkin dare, tuwo da miyar duka na ɗaura lokaci guda. Jikina ko ina ciwo yake yi mini, amman inata sauri in samu in kammala girkin tun kamun Masu gidan su dawo. KOFUR ZUBAINA: Misalin ƙarfe huɗun yamma na tashi a aiki. Kai tsaye gidan Mabaruka na wuce. A tsakar gida na same su dukka da yaran da Sagira, wacce take ta uban wanke wanke. Mabaruka kuwa tana zaune a tabarma, taci kwalliya kamar zata gasar zaɓin sarauniyar kyau. Tana ganina ta shiga washe baki. " Ƴar sanda abokiyar kowa, ƙawata kece tafe da maraice haka?" Zama nayi a gefenta, muka gaisa da Sagira, idanu muka haɗe ni da Mabaruka ta kashe mun idanu, nima na kashe mata nawa. Ƙawata farin ciki ne yasa na kasa haƙurin mu game maganar a waya, nace ya kamata in yo tattaki inzo godiya ƙawata, kwalliya ta biya kuɗin sabulu dai. Na sakata na wala, kar kiso ki shiga zuchiyata kiga ƙyallin da take yi, Hmmm nifa sai yanzune na samu abunda nake so" Shewa Mabaruka tayi tace. "Muje ciki, in ɗauraki akan wasu surrukan ƙawata." Tafawa mu kayi, naja hannunta zuwa cikin ɗakinta, da yasha gyara sai ƙamahin turaren wutan gab gab yake yi. Zama muka yi tace. " Tunda kinsan Bulama na hannunki, fishi ko nuna kishi, ko tsangwamar kishiya ba naki bane. Ki kasance mai yawan fara'a sosai in kika ganta, musamman a gabanshi. Amman kiyi mata kisan mummuƙe, wannan nasan kin ƙware sosai a kai, nasan ba zaki bani kunya ba. In baki dage ba, itace zata dage a kanki. Kinga Adam yau zai dawo daga tafiya, na gama shan magunguna, na matsi duk na matsa, yau gidan zamu tayar ƙawata " Dariya nayi nace. Ai ƙawata jiya duk da dai naji zafin rashin Bulama a gefe na, hakan bai hanani bacci ba, kuma cikin kwanciyar hankali na gudanar da burne layar da boka ya bani. Ai ni na daɗe banga aiki yanka wuƙa irin wannan ba. Ƙawata nagode, bani account number ki in tura miki dubu ashirin kya siya ma yara wani abun." Da murna Mabaruka ta bani account numbern ta, a take na tura mata kuɗin, mu kai sallama na fito. Sagira sai faman cin uban aiki take yi, tamkar baiwa. Kai tsaye gida na wuce. A zaure naci karo da Sagir zai fita. Yana ganina yaja dogon tsaki yace. "Marasa tsoron Allah, da sannu zaku ga ƙarshenku yanda zai kasance" Da sauri nasha gabanshi, ina muzurai duk da ya kereni tsayi sosai. Na buɗe baki cikin faɗa da ɗaga murya nace. Wai kai dan ubanka ina wasa da kai ne, harda mama kake zagin cewar bata tsoron Allah? To ubanka muke tsoro kenan ko" "Ke wallahi in baki iya bakin ki ba, zan gwabgwabjeki ne wallahi, ba ƴar sanda ba, ko soja ce ke sai in tattakaki anan" Yana faɗan haka kafin ma ya rufe baki, na wanke shi da mari, ai kuwa kafin in sauke hannu ya rama. Nan kokawa ta kaure a tsakanina da Sagir mune har wajen layi, na ruƙunƙuneshi, sai dukan ƙafafunshi nake yi, shi kuma sai dundu yake faman zuba mun. Da ƙyar Mama tasa hannu ta janyomu cikin zaure, dan har magulmatan matan layinmu masu zaman gulma da tsugudidi sun soma taruwa.' "Sagir ka kasheni ka huta nace shege matsiyaci. Yarinya itace cinmu itace shanmu, hatta kuɗin makaranta wake biya muku in ba itaba, amman ka rasa da wacce zaka yi rashin darajarka sai yarka, me yasa baka da tarbiyya ne, tunda ka fara shaye shaye kake neman fin ƙarfina, hawan jini kake son ɗaura mun ko? Shikenan. Cikin hargowa da ɗaɗɗaga hannaye yace. "Ni gaskiya mama adena mun kutsu cikin rayuwata. Ba gara ɗan shaye shaye sau dubun dubata ba, da masu bin bokaye da ƴan tsubbu ba? Kija mata kunne wallahi ta kuma shiga harkata sai na sa huƙa na soki cikinta hangin cikinta sun futo, ƴal bura uba kai, batun makaranta da mijinta yake biya ya ma dena biya bama zuwa daga ni har musan yaudarace kawai" Yana gama rashin mutuncinshi ya bangaje Mama ya wuce." Mama duk kece ai kika sangarta wannan yaron yanzu jibi abinda ya zama, kina ganinshi kinsan a bige yake. Ɗan iska sisina ya dena gani wallahi, su kuma munafukancan har sun soma taruwa suna kallo, alhalin ko wanne gida da abun kunyarsu, mu da sauƙi ɗan daba muke dashi ai, babu wacce ta taɓa zubar da cikin shege." Hannuna Mama taja zuwa cikin gidan, a tsakar gida muka zauna Asiya sai aikin suyar kaji take yi. Ga moltina katon guda, da ruwan swan katon guda a gefe. Mama cikin damuwa tace. "Zubaina al'amarin Sagiru fa ya wuce intaha. Baya kwana yanzu a gidan sam, ga ɗiban albarka kashi kashi, yanzu ya gama boll da butocin gidan kin gansu can wasu har sun fashe. Kwararo kwararo suke shiga yawon shaye shayensu. Babban damuwata ma tafi yawa akan, Ƙaninku Musa. Jiya da asuba da mace naci karo a cikin ban ɗaki ta fito daga wankan salla fa. A cikin gidan ta kwana. Rashin mutumcin Musa har ya kai ya kwana da karuwa a gidan mahaifiyarshi? Hannu duk yanda akayi dangin mahaifinku suka sa musu, anga sune yarana maza, shine aka lalata musu rayuwa. Nama malam koke akansu, ya bani magani, yau zan soma zuba musu a abinci suci. Ko Allah zai nitsa mun su, su dawo cikin hankalinsu." Dubanta nayi, naga duk tabi ta damu nace. Mama ki dena tada hankalinki a kansu, kina damu, kuma ki dena tsine musu, ƙila ma bakinki ne ya bisu duk suka lalace ɗin. Amman guda nawa Musa yake da har yake bin mata Mama? Kinga ba cikakkiyar lafiya bace dake, ki kwantar da hankalinki dan Allah. Mama mu bar wannan zancan. Bulama ma fa ya shiga tarko wallahi, yanzu kam komai ya kammala, sai yanda naso za'ayi. Murna ce ta kama Mama kamar ba ita bace take cikin damuwa yanzu, yanzu ba. Wayar Asiya ce ta soma kuka, a guje Mama ta kai mata wayar. "Maza ɗaga ƙila baƙinne suka iso." Karɓar wayar Asiya tayi tace. "Alhaji ne ke kira Mama, bari in ɗaga inji." Ɗagawa tayi ta kara akunnenta. "Hello Alhajina, barka da hanya, kaddai har kun iso? Ɗan jim tayi halamar sauraronshi, kana tace. "To barkanku da shigowa garin gwamna, da fatan zaka gane kwatancen gidan Kawu Tanko da nayi ma ko?" Sai tayi dariya tace dashi. "To shikenan" Dubanta nake yi nace. Yaya ake ciki sun iso ne?" "E Anty suna kan gadar marabar jos. Bari inyi sauri nayo wanka, Mama ɗan ƙarashe mun aikin dan Allah" A guje Asiya ta shige banɗaki. Mama kuma ta shiga zuba pepper kickhen a cikin kula. Musa ne ya shigo da sallama. Yana ganina ya shiga dariya. "Anty Zubaina kece da yamma haka a cikin gidan?" Nice Musa ya karatun ana dai yi ko?" Dariya yayi yana sosa kai yace. "Anayi dukkanmu har Sagiru duk muna zuwa, yanzu haka ma jarabawa muke yi, ta zangon ƙarshe, zamu shiga level 2. Washe baki nayi cikin yaudara irin ta polisawa ban nuna mishi Sagiru ya sakar musu ɓera a yayi ba. To Allah yayi talmako" Mama ta daka mishi tsawa. "Dalla zo ka kwashi kayannan ka shigar mata mota, ka karata can gidan Babanku Tanko, tunda Allah yasa ka dawo daga yawon barbaɗar taka. Ba dai karuwanci ka zaɓa ba Musa, gaka ga bariki ai, batun makaranta da kake zancan jarabawa, Sagiru ya fallashi asirinku bakwa karatun. Kan ku ku kaima ai maza ne ku, kuyi abinda kuke ganin ya fiye muku" Yana kunƙunni yaje ya amshi kular hannun Mama ya fice, yana zagin Sagiru. Ɗaya bayan ɗaya ya zuba duk kayan a mota. To Mama bari muje, koma dai me ake ciki, zamu yi waya. Nasan ma Kawu Tankon zai kwaso dattin talaucinshi yazo yai miki bayanin komai ma" Dariya muka yi dukanmu muka fice a gidan. Kai tsaye zuwa anguwar dosa gidan Kawu Tanko. A ƙofar gida muka same shi, da almajirai manya yana biya musu karatu. Sana'arshi kenan tunda muka taso. Tsangayace dashi, wacce yake koyama yara karatun allo, kuma yakan tura ƙauye ƙauye a kawo mishi almajirai, har kangararru ana kawo mishi, kuma yana ladabtar dasu, ta hanyar duka, horo mai tsanani, da shan rubutu a ko wacce safiya, sannan suma suna yin karatu sosai, sai dai su basa bara, a ko da yaushe a cikin mari suke, iyayensu ke biyan kuɗin kulawa dasu. Da wannan sana'ar yake ciyar da matanshi biyu, da yaranshi fin goma sha. Duk da a halin yanzu duk ya aurar da yaranshi, maza da matan, jikokine cike da gidan dai. "Zubaina yau kuma kune a tafe a gidan namu, harda kai Musa idanunka kenan, ina sauran ƴan uwan naku? Sagiru ya fita, Asiya tana gidan Mama, Nafisa kuma tana gidana. Kawu mun same ku lafiya? Da fara'a yace. "Lafiya lau Zubaina, ya mai gidan naki da yaran naki fa?" Duk suna lafiya Kawu" To to madallah. Isiya ma yana hanya, nayi kiranshi tun jiya nake shaida mishi batun masu kawo sadakin Asiya. Yau yace zai tawo, duk inda yake yanzu ƙila ya kusa isowa ma. Tunda mu biyu muka rage muku, dole duk wani abun in ya taso mune dai ko da bama so zamu shige muku gaba, sabida martabarku ma." Ana cikin haka sai ga Kawu Isiya ya iso, da wata shadda jemammiya a jikinshi ɗinkin malum malum. Sai uban sauri yake zabgowa, malum malum ɗinnan na cika da iska. Yana isowa ya cika wajan tab da warin hammata" MRS BUKHARI ANAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGE, KU BIYONI DAN ƊAUKAR DARASIN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI. LABARIN YANZU ZA'A TSUNDUMA CIKINSHI GADAN_GADAN. KO YAYA WANNAN ZAMAN ZAI KAYA KUWA? KAR KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE, NERA ƊARI HUƊU NE, IN MA KUƊINKI BAI KAI BA KI NEMI ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBINMU ZAKI SAMU RAGI IN SHA ALLAH. *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. _GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._ _1-NIHLATUL-KHAIR_ 👇🏽 *(Ummu Affan)* _2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_ 👇🏽 *Badi'at Mrs bukhari* _ZULFA_ 👇🏽 *Ummu maher(miss green)* _Littafi ɗaya;400_ _Littafi biyu;800_ _Littafi uku;1000_ Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa 10K ne kacal. Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽 2K sati biyu 3k idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama 10k kacal. Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼 [26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 11 *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. Kawu Isyaka ƙani yake ga mahaifinmu malam Rabo. Yana zaune a ƙauyen Rano dake jihar Kano. Asalin mahaifar mahaifinmu kenan, cirani ne ya fito dashi garin Kaduna, har Allah ya haɗashi da mahaifiyarmu Maryam, wacce ake kira da Jummai. Dangin mahaifinshi, da dangin mahaifiyarshi dukka suna garin Rano, Kawu isyaka acan yake da zama tare da iyalanshi. Mukan je Rano in anyi rasuwa, amman ko sha'anin biki Mama bata zuwa balle kuma sha'anin suna, kasancewar dangin mahaifinmu ba ƙaunarta suke yi ba sam. Suma kuma sukan kawo mana ziyara jefi_ jefi. Amman dai a gidan Kawu Tanko suke sauka. Zama Kawu isiya yayi yace. "Wa nake gani kamar ƴar doka yarinya Zubaina ta wajan Jummai ko Tanko?" Kawu Tanko yace. "Itace , tare da ƙaninta Baffa Musa gasu." Gaggaisawa aka shiga yi, tare da tambayar mutanen ƙauye. Kawu dama mun tawo da abincin da za'a tarbi baƙinne dasu, bari mu shiga daga ciki." Dubana yayi yace. "Sabida kun raina mun arziki har kuke ganin bazan iya ciyar da baƙin da abinci mai kyau ba ko? Babu laifi Zubaina ku shiga da abincin, sai a basu nakun da kuka kawo, wanda nasa su Safiya suka dafa maci ni da almajirai na tunda damu ya dace da ba'a san asalin angulu ba sai a ɗauka daga misra take." Na buɗe baki zanyi magana, Kawu Tanko ya ɗaga mun hannu, rannan murtuk. Dole na miƙe na shiga cikin gidan. Musa na biye dani da kayan abinci. Muna shiga ana kiran sallar magriba. Wayata ce ta shiga kuka, Bulama ke kirana. Allah ya taimaki mai taimakona, barka da dare" Cikin kakkaurar muryarshi, mai kauri, da zurfi irinta mazan gaske yace. "Gimbiya ina kika shiga, yanzu na shigo gidan na tarar bakya gidan, sai Nafisa da yaran, kuma nasan ba aikin dare zaki yi ba. E ina gidan Kawu Tanko, masu kawo sadakin Asiya ne zasu zo daga Kano, shine Mama tace muje ni da Musa. Zuwa bayan isha zan dawo." Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Gidanne naji ba daɗi da bakya cikinshi, har wani duhu_duhu nake gani. Bari inzo in same ki a can gidan Kawu Tankon, ma dawo tare." Dariyar farin ciki nayi, lallai Bulama ya kamu sosai. A'a kayi haƙuri nima da zaran baƙin sun tafi zan tawo. Ka siyo gadon kuwa da nace ka siyo?" Ɗan tsaki yayi yace. "Nasiyo yana can ɓarayin nata, inna huta zanje in kafa" Kai da kanka, me yasa ba zaka ce ita ta kafa maka gadon ba? Ai ba aikinka bane. Ka tura Nafisa ta sanar da'ita ta gyara ɗakin. Kaci abincin?" To shikenan an gama, yanzu zan turata. Abinci kuma banci ba, yanzu ta kawo abincin ma. Wanka zanyi, inna dawo daga masallaci zanci, amman saifa kin dawo" Nan mu kai sallama na ajjiye wayata. Gaggaisawa mu kayi da Goggo Safiya, da Goggo Nafisa. Goggo Safiya tace. "Ya Jummai tana lafiya da sauran yaran dai ko?" Nace. Lafiya lau suke. Bari inyi sallah kafin baƙin su iso" Alwala na ɗauro nazo na gabatar da salla. Ina idarwa su Goggo Rakiya, da Mama Zakiya suka shigo cikin ɗakin Goggo Safiya. Ƙannen Mama ne su ɗin. Ashe wai Alhaji Jabeer tare da mata suke, masu kawo akwatin gaisuwa. Ana kan gaishe_ gaishen yaushe gamo, sai ga baƙi mata Musa ya rako su huɗu. Kai da gani kaga hajiyoyin Kano, kuma kana kallonsu kaga masu hannu da shuni, dan manyan atampopine a jikinsu, harda gwal. Tarbar arziki da karamci sosai suka samu a wajan su Goggo Safiya. Akwatinsu na gaisuwa guda uku, shaƙe da manyan atampopi da shaddajo, da mayukan shafawa, da sabulan ruwa, banda katan katan na lemo, da biskit Kaya dai sai son barka. Sunci kaji sun kora da ruwan gora. Bayan sallar isha kuma suka tafi, zasu je su kwana a gidan wata ƴar uwarsu a cikin gari, tukuicin nera dubu hamsin na basu, domun hausawa na cewa tuwon girma miyarshi nama. Bayan tafiyarsu ne, Kawu Tanko da kawu isiya suka shigo. "To Safiya, Nafisa, Zakiya, Rakiya, Zubaina, da kai Musa ga sadakin Asiya na karɓa. Sunce kuma shi Alhajin sun gama magana da Jummai akan sati uku za'a saka. To mun tsayar a hakan, ranar juma'a za'a ɗaura auren a ƙofar gidannan. Amman wa aka wakilta dan binciken halayya, da nasabar shi wanda Asiyan zata aura? Duba da yanda sharia ta ba da damar ayi bincike in za'ayi aure sabida gudun matsala" Goggo Rakiya tace "Duk wani bincike sai da babban wanmu Ɗan juma ya gudanar, tun kafin azo wannan fagen ai Tanko" Kawu Isiya yace. "To ai shikenan tunda kunyi bincike. Ga sadakinnan nera dubu ɗari biyu. Ni naso a rage yawan kuɗin ko dan neman albarkar auren, to amman su suka ƙi, dan sunso su bada abinda yafi hakan ma, mune muka ƙiya, tunda ba siyar da ɗiyar tamu zamu yi ba. Allah ya sa ayi damu. Gobe zan koma muma zamu gudanar da shirye_shiryenmu daga ƙauye in Allah yaso." Kuɗin sadakin suka miƙawa Goggo Rakiya. Daga nan muka ɗebi kayan gaisuwar muka tafi. Bani na shigo gidan ba, sai goman dare, dan sai da na koma gidan Mama, mu ka kai akwatunan, sannan na kai su Goggo gida." A falo na samu Bulama yana zaune yana kallo a NBC 2 Maryam na jikinshi tayi bacci. Murmushinshi ya sakarmun, wanda yake faranta mun rai a ko wanne hali na tsinci kaina. Maryam na zare daga jikinshi, na miƙa ma Asiya wacce muka dawo tare ita. Sannan na fuskanci Bulama. Kana zaune har goma baka je ka kwanta ba Bulama, kana da aiki fa gobe" jajayen idanunnan nashi ya zuba mun, yana wani ƙanƙantar dasu, na riga da nasan me hakan ke nufi. Dan irin wannan kallon mayatar daya saba yi mun kenan a duk lokacin da yake buƙatar shaƙar ɗumina. A daddafe muka ci abinci, kai tsaye muka wuce ɗakinshi, yai mun rumfa. Ni kuma na saki jikina, na kula dashi sosai, kamar yadda na saba, shi kuma ya zame mun tamkar mafaraucin zaki. Goma da rabi na rakashi har ɗakin Yahanasu. Tana zaune a falo ƙwalam, ta jiyo sallamarmu. Da idanu ta bimu, ciki ciki ta amsa sallamar. Ni kuwa sai baki nake washewa. Amarya sannu da aiki fa, mun haɗaki da aiki. Ga angonki na kawo miki." To kawai tace dani. Bulama muje inga fasalin ɗakin naka ko? A wajan muka barta da sakakken baki, hawaye tab gurbin idanunta. Ɗakin yayi kyau, har sababbin labulaye da santa kafet ta saka, sai ƙamshin turaren wuta ɗakin yake yi. Ni dai inata dariyar da na tabbatar haushi nake kuma cusa mata. A haka nayi musu sallama na fice. Hmmm dani kuke zancan, wallahi in dai ina numfashi haka zaki ci gaba da zama a cikin gidannan tamkar poster, ko status shashasha." Yahanasu: Wani irin suya ƙirjina yake yi mun. Tunani da damuwa sun damu rayuwata, na rabu da iyayena da ƴan uwana, an kawo ni nan dan inyi zaman aure, amman da dukkan halamu sai dai in zama ƴar aikin gidan kawai. Bana son in yi ƙorafi tun yanzu, idanu nake son in zuba in gani, Baluma Babba dashi za'a haɗa kai a cutar dani da gaske, kokuwa dai mafarki nake yi?" Hawayene suka sakko a kumatuna jikina a mace mus na shige ɗakina. Jakata na jawo na ciro maganin da Hajja Fati ta bani, guda biyu na watsa a bakina nabi da ruwa. Ina kwance ina karatun Alqur'ani, ina hawaye, nadamar shan maganin maye take ya shige ni, kuka na shiga rerawa mai ban tausayi. Bansan ma sanda wani irin nannauyan baccin da bansan anayin irinshi ba ya ɗebeni. Har wani tashi naji inayi sama, ina daga kwancen tsabar nauyin baccine ko meye oho. Bani na farka ba, sai biyar ɗin asuba, shima bawai dan baccin ya isheni bane, a daddafe da bango na shiga toilet, saida nayi wanka sannan naji ƙarfin jikina, kaina kuwa tamkar an sauke mun wani ginginemen dutse mai ɗan karen nauyi, nauyin dake danne da ƙirjina kusan rabi ya washe, sai na ke jin kaso ɗari cikin damowoyin da suka hanani sukuni, kaso talatin da ɗoriya sun kau. Ina idar da salla na yi kitchen da sauri. Doya da miyar ƙyai nayi musu na kumallo, sai tea mai haɗin kayan ƙamshi. Shida da rabi nayi sallama a babban falonsu, ƙanwar Zubaina ce ta leƙo, na bata kayan abincin, har zata koma nace mata. Dan Allah bari in ɗakko miki kayan wankinsu, ki adana musu" Ban jira ta amsa ba, na juya na ɗakko mata kayan wankin ƙunshi biyu. Sannan na shiga aikin wankin mota, ban dai iyaba amman haka na dinga dirjewa ina watsa ruwa, dana gama wanke na Kofur Zubaina, saina wanke ta Bulama Babba. Duk jikina yayi laushi, a jiƙe sharab na koma ɗaki na saki wani irin kuka mai gunji. A wajan ya fito ya sameni ina rawar sanyi, ina kukan fitar hayyaci. Cak ya tsaya a kaina, bai tambayeni meke damuna ba, baice inyi shiru ba, baice komai ba. Idanunshi sun kuma kaɗawa sunyi jawur, ni banbi ta kanshi ba, kukana naci gaba dayi. Bai bar kaina ba, har saida yaga bakwai da rabi na shirin gotawa, sannan yace mun. "Zan fita Yahanasu, akwai abunda kike buƙatane?" Kai na girgiza mishi. Babu, Allah ya tsare gabanka da bayanka, ya kareka daga sharrin masu sharri, adawo lafiya karka manta da addu'ar fita daga gida" "To Yahanasu nagode, ki share hawayenki ki dena kukannan." Yana gama faɗin haka ya fice a ɓangaren nawa. Haka rayuwar gidan taita tafiya cikin ƙunci da matsi. A haka Bulama Babba ya gama kwanakinshi bakwai a ɗakina. Kullum inayin waya da ƴan gidanmu, ko basu kirani ba ni zan kirasu a gaggaisa, ana washe gari zan soma zuwa aiki Ba Bakura ya kirani, yake cewa dani in shirya da wuri ƙarfe bakwai za'a zo a ɗaukeni. Naji daɗi sosai ko babu komai na rage raɗaɗin zaman gidan, dan ma ina afa magungunan da Hajja Fati ta bani, kuma inajin daɗin baccin sosai, tun ina tunanin sha, har na dena, domun zuchiyata sai sake ingizani take yi, shaiɗan kuma yana ƙara ƙawata mun maganin. Ibada kuwa, na ƙara ƙanƙameta gam, da naji sauyi a jikina, zan ɗauro alwala in shiga salla, ko da yaushe ina kai kukana ga mahaliccina. Iyayena kullum a cikin rufesu nake, da sunan lafiya lau nake zaune tare da Bulama Babba. Washe gari, ranar ya kasance a ɗakina Bulama Babba yake, bayan na gama duk ayyukan da nasan nike yinsu, yau tun bakwai na sallami kowa, cikin shiri na fito tsab, a kan kujera na samu Bulama Babba yana ɗaure igiyar takalminshi. A gabanshi na durƙusa nace. Bulama Babba" Ɗagowa yayi ya zuba mun jajayen idanunshi, nayi sauri na sauke kaina. "Lafiya Yahanasu menene?" Dama yau zan soma zuwa aikine, shine nace bari in faɗa maka. Hajiya zata zo ta ɗauke ni mu tafi" jim yayi, kana yace. "Wacece kuma Hajiya?" Nace. Matar Alhaji Munka'ilu aminin Ba Bakura" "Oh su suke aurenki kenan ko?" Nace. A'a kayi haƙuri" "Dalla rufa mun baki, to da izinin wa zaki soma zuwa aiki?" Kai tsaye nace. Da izinin Ba Bakura zan soma zuwa aikin, tunda shi ya ajjiyeni, kuma dokar gidanmu itace duk wanda zai auri matan gidanmu, akwai sharaɗin zasu ci gaba da aiki, kuma kasani." Iyakar abunda na faɗa kenan. Bulama Babba ya dinga zazzaga mun ruwan jaraba, yana caccakama iyayena maganganu kaifafa, akan basu bani tarbiyya ba ashe. Kuka kawai na saki, ni bansan dame akeso inji ba, da damuwar da take damuna, ko da masifar da Bulama Babba ya tsiro da'ita kwana biyunnan. "Babu inda zaki je, inga ubanda zai tilastamun akan saina barki kinyi aiki. Inace a garin zuwa aikinne kike zuwa yawon iskancinki, har kikai ma iyayenmu ƙaryar an miki fyaɗe ko? Sabida kin saba da bin maza shine kike son ki koma ruwa ko? To babu wannan ƙofar a gidannan. Tunda har suka bani ke bana so, bazaki taɓa jin daɗina ba, na faɗa miki." A wajen ya barni a durƙushe ina kuka kamar zan haɗiye zuchiyata. Ina jiyo muryar Zubaina tana tambayarshi ba'asi. Fyaɗen da akaimun ya dawo ɗanye a zuchiyata, dama mikin kullum a cikin nuƙurƙusata yake. Duk irin tarbiyyar da iyayenmu suka tsaya akanmu suka bamu. Yau ni Bulama Babba yake kira da ƴar iska, mara tarbiyya kuma, har Bulama Babba zai iya buɗe baki ya aibanta Ba Modu a gabana? Ai halin shi ya kula dashi ya bashi tarbiyya. Sallamar Hajiya Ramlatu ne ya katsemun kukan da nake, amman na kasa shanye yanayin da nake ciki, dole ta kutso kanta ta sameni a zube a ƙasa fuskata sharkab da hawaye duk ta kumbura. "Yahanasu lafiya kike rusa irin wannan kukan? Na haɗu da bulama shima na ganshi a cikin fishi sosai, ba dai har kun soma samun saɓani ba, daga auren naku ba?" Hawayena na shasshare nayi ƙasa da kai nace. Sannu da zuwa Hajiya, ina kwana?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Lafiya lau Yahanasu, ki taso dai yanzu mu kama hanya, tunda naga a shirye kike tsab" Kiyi haƙuri Hajiya, na gode da ƙoƙarinki a gareni. Amman Bulama Babba yace bazanyi aiki ba, abunda ya ɓata mishi rai kenan" Dubana tayi cike da maɗaukakin mamaki tace. "Ya baza kiyi aiki yake ba? Naga yanzu ya fice wajan aiki, matarshi na mara mishi baya da kayanta na ƴan doka zasu tafi aiki, kuma tunda nasan mahaifiyarshi ma'aikaciya ce, har sai da tayi ritaya sannan ta zauna a gida. Akanme zaice ke bazakiyi aiki ba, alhalin yasan ku ƴan boko ne, kuma kab ƴan gidanku babu mai zaman kawai. Ai wannan in dai Bulama Babba yayi haka baiso zaman lafiyar iyayenshi ba, kuma bai ɗakko hanyar haɗin kan gidan nashi ba ma. Ai wannan zalunci ne Babba, ina zuwa." Fita tayi, ta ɗanyi waya na mintoci, sai gata ta dawo ciki. "Zan tafi Yahanasu, zuwa gobe komai zai daidaita zanzo in ɗaukeki mu tafi aikin, ki dena kukan ya'isa haka" Har bakin motar ta na rakata ta ja ta tafi. Ni kuma na shiga aikace_aikacen cikin gida kamar yadda na saba. Wankin da nayi yau bana wasa bane, nasha wahala sosai. Na rame matuƙa, hakan yasa na ɗan washe kaɗan, ni kaɗai nasan irin zafi da raɗaɗin dake gasa ruhina. Misalin ƙarfe biyun rana na shiga kasuwa nayo cefane na, nazo na ɗaura miyar dare. Na fita tsakar gida zan kwaso shanya, dan garin hadarine sosai ya sauko, ruwa ne ma ke shirin kecewa. Mota na gani ta kaya, cike da sababbin kayan ɗaki, suna saukewa ƙasa, wasu na fito da tsofaffin na ciki, wanda suma sababbinne dan babu abunda ya same su. Sai lokacin na lura an sake ma ma ɓarayin sabon fenti mai kashe idanu dan ƙyalli. Kaina na girgiza na kwashe kayan na tafi ɗaki da abuna. Sai wajajen biyar na yamma na gama girkin dare. Tuwon alkama miyar ganye nayi da kayan ciki da stock fish. Ruwane ya ɓalle kamar da bakin ƙwarya. Akaita tabka ruwannan, ina zaune ina ribatar lokutana da tulawar Qur'ani mai girma. Har magriba ruwannan bai tsaya ba, amman ya ɗan dakata kaɗan. Ba Bakura: Tun ƙarfe huɗun yamma suke tsaye a bakin get ɗin gidan Bulama Babba, amman mai gadi ya hanasu shiga, duk da bayanin da Dala yayi mishi na cewar, mahaifan mai gidanne a cikin motar. Haƙuri ya basu kan cewar su kira mai gidan a waya in ya bada damar su shiga, sai ya buɗe musu. In bai ba da damar shigan ba sai suyi haƙuri. Ba Bakura ya kira kiran duniya Bulama Babba bai ɗauka ba. Ba Modu ma ya kikkira bai ɗaga ba. Hajja gana itama ta kira shiru. Gabaƙi ɗaya ran kowa ya dagule da irin halayyar ko in kula da Bulama Babba yake yi musu. Dab magriba Bulama Babba ya dawo wajan aiki yaga motar Ba Bakura a ƙofar gidan. Ji yayi da yasan zai dawo ya samu motar a wajan dama bai dawo yau ba baki ɗaya. Da gudu mai gadi ya buɗe mishi get ya shige. Mai gadi yabi bayanshi a cikin lema da sauri. Bulama Babba: Jim nayi a cikin motar, na kasa motsowa sam, dan nasan ba lafiya bane ya kawo su gidan ba, kuma nasan zuwan nasu ba ɗa mai ido zai haifar ba. Ni kuma duk abinda zai ɓata ran Zubaina bana fatan ya raɓeni. Amman a wannan karon zan ja musu layi akan irin wannan zuwan na bagtatan da suke yi mun, suyi zamansu a inda Allah ya ajjiyesu kawai. Buɗe murfin motar nayi, mai gadi ya ƙaraso. "Mai gida, waɗancan bayin Allahn sun jima sosai a tsaye a ƙofar gida, tun la'asar suke jiranka kuma sunce daga can Damaturu suke. Ɗan tsaki naja a hankali nace. Kace su shigo kaji" Da sauri ya koma Motar Zubaina ce ta shigo gidan a guje, sannan motar su Ba Bakura ta shigo itama. A hankali na buɗe lema na fito ina tsaye a kusa da motata, Zubaina tayi wuf ta fito. Sannan su Ba Bakura suka fito a cikin Motar. Kallonsu na shiga yi, inajin wani abu na motsa mun zuchiyata, Ni kaina bansan menene wannan abun ba, amman har ƙasan zuchiyata naji daɗin ganinsu, idanuwa da zuchiya suna kewarsu sosai. Sai dai kallo ɗaya zaka yi musu kasan a cikin ɓacin rai sosai suke. Sannunku da zuwa, kune a tafe haka? Irin wannan ai saiku sanar kafin kuzo, in kuka zo bananan kuma fa?" A ɗan daƙile na furta kalmar. Ba Bakura ya ƙura mun jajayen idanunshi, wanda suka kere nawa runewa, fuskarnan tashi murtuk yace. "Kayi haƙuri da zuwan bazata da mu kayi maka, na mance bamu da wannan ikon ko? Hakan ba za ta sake faruwa ba" Baki na buɗe zanyi magana amman Ba Modu yayi saurin ɗaga mun hannayenshi, ɗan harararshi nayi ƙasa ƙasa, dan mugun haushinshi nake ji shi fiye da kowa. Hajja gana hawaye naga tana sharewa ko na miye oho. Baki na taɓe dan nasan daman zuwansu ba alkhairi bane sam. "Nuna mana ɗakin Yahanasu, in da hali a raka mu. Mahaifinka baya son sanyi, ruwa na dukanshi" Cewar Hajja gana kenan. Juyawa nayi, suka bi bayana, ruwa sai dukansu yake yi, ni kuma ina cikin laima ina tafe kamar agwagwa tsabar taƙama. A bakin ƙofar ɗakin na tsaya nace Ga ɗakinnan" Ina faɗa nayi wucewata na barsu a tsaye a wajan suna doka sallama. A tsaye a tsakar gida inda na bar Zubaina nan na sameta, tana ganina ta saki ajjiyar zuchiya mai ƙarfi. Wucewa muka yi. Daga ni har ita a falo muka zube. "Bulama amman ya kamata ka sanar da su Ba Bakura su dena irin wannan tafiya ba sanarwa. Su yi kiran waya mana kafin su zo, gudun kar su zo bama nan." Tagumi tayi tana sharar hawayen da yasa duk na rikirkice da ganinsu. Nan na shiga tambayarta ba'asin zubar hawayenta. "Abban Maryam na rasa abunda nayi ma iyayenka da suka ƙi jinina. Ka duba fa, ko sannu da zuwan da nayi musu basu amsa ba. Cikin su babu wanda ya kalleni, nasan sai sun gama ci mun mutunci ma kafin su tafi" Kuka ta kuma raushewa dashi. Tsam na matseta a ƙirjina na shiga aikin lallashinta, santa da ƙaunarta na huɗa tsokokin jikina." Babu mai wulaƙanta mun mata in barshi. Ki dena kuka bazan bari sam su faɗi mummuna a kanki ba. Kuma zan faɗa musu kar su sake zuwa har sai sun kirani na ɗaga tukunna. Ai naga kiran nasu ban ɗaga bane kawai. Ashe a lokacin suna ƙofar gidan, dan mai gadi yace tun la'asar suke waje. Hawayenta na shiga share mata ,a hankali tace dani. "Ka samu kayi wanka ka sake kayanka, lokacin sallah yayi. Ni kuma bari in je mu gaisa" Sake ni tayi, ta shiga kiciniyar sake kaya. Ni kuma na wuce toilet raina duk ya dagule ainun. Yahanasu: Ina zaune ina kallon tashar Sunna TV naji kamar ana sallama a ƙofar ɗakina. Da sauri na isa bakin kofar na buɗe. Su Ba Bakura na gani a tsaye, jikinsu a jiƙe sharab har ɗiga suke yi. Hajja gana kuma sai sharar ruwan hawaye take yi. Da sauri na rungumi Hajja Gana nima na saki kukan. Riƙeni gam tayi a jikinta sai ajjiyar zuchiya kawai take sukewa. Hannunta naja inai musu sannu da zuwa. Biyoni suka yi ciki jiki a mace. Ni kuwa da hanzari na shiga cikin ɗakin Bulama Babba na ɗebo kayanshi kabtan guda uku, na miƙa ma Dala. Dala ku shiga ɗakin Bulama Babba ku sake kayan jikinku sanyi, gashi Ba Bakura baya son sanyi. Hajja mu shiga ki sake kaya. Ba wanda yace mun komai, a baya ta biyoni har cikin ɗakina. Doguwar riga ƴar itofiya na bata ja ta sake. "Yahanasu rashin lafiya kike fama dashine ko me? Naga kinyi wata iriyar muguwar rama mai tsoratarwa." Murmushin ƙarfin hali da ƙarfafa ma kaina guiwa nayi nace. Ciwo nayi Hajja, yaune ma naji dama_dama" kallona tayi da kyau taga yanda idanuna suka zurma, wuyana ya cika da ƙashi. Ni da nake da ƙiba Amman tashi guda na zube, duk da nayi rama tun a gida, lokacin da wannan abun ya faru dani. Amman sati biyu da suka wuce nayi biyun haka kumari. "Ƙarya kike yi ƴannan kice dai bakya jin daɗin zaman aure kawai, dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi ko Hajiya Ramlatu ta tabbatarmun da walakin goro a miya tsakaninki da Bulama Babba" Shiru kawai nayi mata, dan kuka ke shirin fallasa asirin da nake ɓoyewa. Da ƙyar nace mata. Babu komai Allah Hajja. Kawai dai kewar gida da abinda ya faru dani suke damuna." Murmushinsu na manya tayi kawai tasa kai ta fice, mara mata baya nima nayi. A falo muka tadda su Dala suna tsaye. Muna fitowa Ba Modu yace. "Bari mu fita mu nemi masallaci muyi Sallah ko?" A dawo lafiya Ba Modu" Kallona yayi idanunshi cike da rauni, kai kawai ya gyaɗa mun. Bayan sun dawo masallaci na gabatar musu da abinci. Amman sam sun kasa cin ko loma. Ana cikin haka Bulama Babba ya shigo da sallama shi da Zubaina. A yayyatsine Zubaina ta gaishesu irin gaisuwar reni da wulaƙanci. Hajja gana ce kaɗai ta kada baki ta amsa Bulama Babba ya gaishesu ɗaya bayan ɗaya, fuskarnan tashi babu annuri sam. "Ki tashi kije, inason zanyi magana da ɗana" Ba Bakura ya dubi Zubaina ya faɗa mata haka. Harta yunƙura zata tashi, Bulama Babba yace. "Zauna Zubaina" Zama ta gyara tana ɗan murmushin mugunta. "Ba Bakura ni ina ganin duk abinda zaka faɗa mun zaka iya faɗa mun ba sai Zubaina ta tafi ba. Tunda naga ga Yahanasu a wajan, dukkansu iyalainane, Zubaina itace uwar ƴaƴana, yin hakan dai dai yake da cin fuska ko san kai" mamaki sai da ya kama kowa a falon, hatta ita kanta Zubainar sai da ta kalli Bulama Babba da mamaki. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE Muje zuwa [26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 12 *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. Yahanasu: "Baka da hankali Bulama har lalacewar tamu ta kai kayi mana rashin kunya gaba da gaba, akan wannan matar taka marar ɗa'a da ladabi? Lallai kayi nisa baka jin kira" Da yare Ba Modu yayi ma Bulama Babba magana a zafafe, har yana kumfar baki, ni dai sai hawaye kawai nake ɗigarwa. Ba Bakura ya zuba mun idanu yana kallona cike da tausayina. Bulama Babba yace. "Gaskiya ai na faɗa Ba Modu a duba wannan lamarin dai, Zubaina fa banga abunda tayi muku kuka tsaneta ba." Zubaina cikin kisisina ta miƙe tsaye tana murmushi tace. "Duka kuyi haƙuri dan Allah, bari in baku waje dama gaisuwa nazo yi" Tana kaiwa nan ta fice abunta. Ba Bakura ya dubi Bulama Babba yace. "Sanar damu dalilin da yasa ka hana Yahanasu fita aiki alhalin kasan yin aiki yana cikin tsarin gidanku, uwarka gata bata daɗe da yin ritaya ba, da aikinta kayi wayo ka ganta, kuma da kuɗin albashinta wanne irin hidimace bata yi maka ba, Akan me zaka tauyema ita Yahanasu ƴancinta, alhalin ga matarka ita tana zuwa aikin, aikin ma na cuɗanya da maza, da ɓarayi, da ƴan iska iri_iri, aikin da har tone ɗin night ake yi. Bulama Babba yace. "Sabida ban yarda ita tayi aikin ba, in dai har ni nake amsa sunan mijinta. Sannan Ba Bakura ina neman alfarmarku dan Allah ku dena zuwan mana haka bagatatan ba tare da kun sanar ba. Ni ina roƙonku ku dena zuwa ni zan dinga zuwa duk shekara" Kuka na fashe dashi mai ƙarfin sauti ina ambaton. Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun A fili har sau uku. Ba Bakura kuwa tari ya soma yi, yana dafe ƙirjinshi dan ya shiga ruɗu ainun, yawun bakinshi ne ya ƙwarar dashi. Hajja kuwa hawaye kawai take ta zubarwa tun sanda Bulama ya soma magana. Dala yayi maza ya sauke kanshi ƙasa, Ba Modu sai ajjiyar zuchiya kawai yake saukewa yana ambaton. "Lahaula wala ƙuuwati illabillah, ya Allah" shine kalmar dake fita a bakin Ba Modu. "Bulama ni kake ma iyaka da gidanka da iyalinka, ka mance nine mahaifinka ni nan na ɗauki nauyin ci, sha, suturarka, maganinka, kuɗin makarantar ka, dama tarbiyyarka? Wannan mahaifiyarka ce fa wacce ta ɗanɗani zafi da azabar naƙudarka, ta raineka, kashi, fitsarinka duk ta cinye, In baka da lafiya aikinta shine kuka da tagumi, amman itace yau kake saka mata wata doka taka? Wannan fa Modu ne, wanda ya ɗauke dukkan ɗawainiyar karatunka da kula da tarbiyyarka, ya fifita sonka sama da yaran daya haifa. Lallai Bulama ashe abun naka yayi nisa sosai, kayi sake da adda'a wannan ba yinka bane tarkon shaiɗaniyar mace ka faɗa, amman. Amman ka sani kuma ka rubuta ka ajiye ni Bakura babu ni babu kai, babu zuriyarka baki ɗaya, wallahilƙudrat inka tako ƙafarka ka zo inda nake bazan taɓa yafe maka ba. Dala ka shaidama ƴan uwanka maza da mata, duk wanda ya sake tako ƙafarshi yazo gidannan ban yafe mishi ba, kai ko kiran wayar Bulama kuka yi, Allah ya'isa tsakanina daku. Ka sakarmun ƴa mu wuce kaje ka rayu da matarka, iyayenta su zamema uwa da uba, dama dangi. Ba da dukiya kake taƙama ba? Gaka nan ga dukiyar Bulama nace gaka ga dukiyar ga macen kuma, ga ka ga MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA, wacce tafi bagaruwa jima Ni bazanyi maka baki ba, amman babu ni babu kai." Hawaye ya soma fitarwa yana tari kamar zai mutu. Ba Modu yace. "Bakura kayi haƙuri, in hankali ya gushe hankali ake aikawa ya nemo shi. Kar akan sharrin mace kaima ɗanka baki ya ɓalɓance. Maganar ya saki Yahanasu bata tasoba, na riga dana bashi Yahanasu duniya da lahira, kuma in batai mishi biyayya ba bazan iya yafe mata ba, ko gutsurarta zasu dinga yi ƙarshe azaba, ta ci gaba da zama a ɗakinta. Bulama bai isa ya ɓata mana zumunci da dangantaka ba. Duniya ce mai ido a tsakar ka, kayi a hankali. Da mace da dukiya haɗarine dasu. Sannan ka sasssauta maganarka kan cewar baka yafe ma duk wanda ya kawo ma su Bulama ziyara ba. Karka zama silar kawo rushewar zumunci a tsakanin wannan ahali, idan basu zo gidannan dan Bulama da Zubaina ba, ƴar ka Yahanasu da take cikin gidan fa. Ku taso mu tafi kawai. Allah yayi muku albarka duka." Duka wannan maganar da Ba Modu yayi, yayine a cikin raunin zuchiya da sanyin jiki. Haƙiƙa ni kaina na tsorata da kalmomin Ba Bakura akan Bulama Babba, sai dai abunda suka kasa ganewa shine, ƙarfin sihiri ke aiki a jikin Bulama Babba ba haka aka barshi ba. Inda a hayyacinshi yake ko ni bazai iya yima wulaƙanci ba balle su Ba Bakura. Kukane ya kece mun jin kalmar in banma Bulama Babba biyayya ba ba'a yafe mun ba. Na rasa gane shin iyayena ƙyamata suke yi dan ƙaddarar data same ni, ko kuwa ƙaunata suka dena yi? Sallallamin da Hajja Gana take yi shi ya dawo dani hayyacina. "Nace ki taso mu tafi ko Hajja Gana. Ki share hawayenki ki dena kuka akan yaron da baison darajar hawayenki ba, ki fito mu tafi"Fita suka yi a cikin ɗakin, Ba Modu yana riƙe da Ba Bakura gam, Dala na biye dasu a baya. Ni kuma sai hawaye nake zubarwa. Kallona Ba Bakura yayi bayan ya zauna a mota idanunshi jawur, cike tab da ruwan hawaye yace. "Allah ya sanya ma rayuwarki albarka da abinda zaki haifa. Yahanasu Allah yana gani ban haɗaki da Bulama dan mu cutar da rayuwarki ko mu hofantar dake ba. Munyi ne dan ƙarfafa zumunta, da rufin asirinki dana ɗan uwana rabin jikina. Kiyi haƙuri da duk abinda zaiyi miki tsanani. Albarkar iyaye tana biye dake a duk inda kike, Allah yayi miki albarka, Dala ja mota mu kama hanyar Damaturu a yanzu" a tsaye a wajan suka barni ina tsiyayar da ruwan hawaye, na jima a wajan sosai kafin na koma ɗakina. A takure waje guda na samu Bulama Babba yana zubar da hawaye, a karon farko dana soma ganin hawayenshi kenan, idanunshi sunyi jawur abun tsoro, duk wata jijiya dake goshinshi tayi raɗa_raɗa. Wuceshi nayi na ƙule ɗakina, duk da na tausaya mishi sosai akan irin fishin da mahaifanshi suka tafi suna yi akanshi. Yau na kuma gasgata Asiri Zubaina tayi ma Bulama Babba ba haka ta barshi ba. Tsari na nema a wajan Allah. Akan Allah yayi gaggawar ɗaukar raina a ranar da zuchiyata kawai zata aiyana mun inje wajan boka zai biya mun buƙatuna. Sallar Isha na tayar dan tun ɗazu aketa kiraye_kirayen Sallah. Bayan na idar na ɗaga hannuna ina kuka a gaban mai duka akan Allah ya huci zuchiyar su Ba Bakura akan zafin da suka ɗauka akan Bulama Babba, Allah kuma ya kuɓuto dashi daga mugun asirin da Zubaina ta dabaibayeshi dashi. Sannan na nemi tsari da sharrinta, na sake roƙon juriya da jumurin shanye duk abinda zai tunkaroni." Bulama Babba: Ji nayi kaina yayi wani irin gingiringin, kamar zan tashi sama, tsabaragen firgita da ɗimuwar dana shiga. Haƙiƙa nasan iyayena sun ɗau fishi dani sosai. Banyi tunanin furucinsu a gareni zai girgizani ba. Jikina a mace na bar ɗakin yahanasu na nufi masallaci. Ban fito a masallacinnan ba sai wajan goman dare, ina zaune shiru kaina ya kaure da tunani. Zazzaɓi mai zafin gaske ya ɗumama jikina, da ƙyar naja ƙafa na koma cikin gida. Amman bayan kwana biyu na mance da babin su Ba Bakura, naci gaba da gudanar da harkokina. Ahmad ma ya kirani yana mun faɗa, tsaki kawai naja na datse wayata. Haka lamura suka ci gaba da tafiya lami lafiya. Bikin Asiya ya matso sosai harma Zubaina ta tattare kayanta ta koma gidansu, bayan na cika mata zabirarta da kuɗi masu kauri, itama Mama na bata kuɗaɗe masu kaurin gaske. Banda fenti da naima gidan ciki da waje. Kayan ɗakin dana sake ma Zubaina, saita kwaso nata na da ta jere a ɗakin Mama gidan ya fito shar. Dani akaita kai kawon bikin Asiya, tare dani aka ɗaura Auren a cikin maza a waje. Ina daga cikin mutanen da suka shiga jerin gwanon ƴan kai Amare Kano. Lallai Asiya ta auri hamshaƙin tajiri sosai, dan gidanta ya kai a kalla a kuma. Washe gari da safe muka dawo, sai lokacin na samu nutsuwa, na koma bakin aikina. Yahanasu: Haka rayuwa taita garawa dani, cikin ƙunci da damuwa. Ƙwayoyin maye kuwa sun zame mun tamkar ruwan sha, dan babu ranar da bana sha. Jiya jiya ya ƙare, sai maganin tari na siyo na kwankwaɗi rabi, rabin kuma ina jiran wani daren in sha. Ta ɓangaren su Ba Bakura kuwa. Bayan fitarsu daga gidan Bulama Babba masallaci suka nema su kayi sallah, sannan suka ɗauki hanyar Damaturu, dan Ba Bakura yayi rantsuwar bazai kwana a garin Kaduna ba. Basu suka isa Damaturu ba, sai da Asuba. Jama'ar gida sunyi matuƙar mamakin wannan dawowa ta su Ba Bakura. Ga jikinshi ya rincaɓe da ciwo, babu shiri aka wuce dashi asibiti dan jikin yayi tsanani. Bayan abubbuwa sun ɗan lafa ne Ba Modu yaja Innana gefe guda suka soma tattaunawa , nan ya sanar da'ita abinda ya faru wanda shine sanadiyyar tayar ma Ba Bakura hawan jininshi, har takai baya gani sosai. Ta shiga damuwa sosai, duk da dama tunda Yahanasu ta tafi, take cikin damuwa. Sai dai kullum a cikin yi mata adda'a take. Yakanarta da biyayyarta yasa ta kasa furta abinda ke zuchiyarta, illa iyaka tace. "Allah ya bata ikon yi mana biyayya, ya albarkaci rayuwarsu baki ɗaya. Shi kuma Bulama yayi kuskure mai girma. Kaje ka kula da ɗan uwanka, yana buƙatar kulawarku" kwanan Ba Bakura goma a asibiti yana jinya, kab ƴaƴan gidan maza da mata da surukan gidan, sun sha sunturi. Bayan an sallami Ba Bakura daga asibiti ne, ya haɗa taron yaranshi maza da mata. Ya kafa musu umarnin da su ka ji yai musu mugun tsauri sosai. Sai dai basu da ikon cewa komai, kuma sunji zafin abinda Bulama Babba ya aikata musu sosai, harda masu hawaye. "Daga yau na yanke dukkan halaƙarku da Bulama Babba. Ban yarda ku ɗaga waya ku jirashi ba, ko kuma shi ya ɗaga ya kiraku. Haka kuma ban yarda ku taka ƙafafunku kuje inda yake ba. Alfarmar da zanyi guda ɗaya ne shima sabida Yahanasu ne. Na yarjema matan in dai Yahanasu ta haihu suje ayi suna dasu, Baya ga hakan ban yarda aje inda Bulama yake ba, duk wanda ya take umarninnan ban yafe mishi ba" Rarrashinshi sukaita faman yi, ba rarrashin yayi haƙuri ya janye furucinshi ba sam. Haƙurin irin rashin ɗa'ar da Bulama Babba yayi musu suke bashi. Haka suka watse jikunansu a mace mus, Bulama dai ɗan uwansu ne, kuma akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninshi da kab yaran gidan. Yahanasu kuwa, kullum sai ta kira taji yaya jikin Ba Bakura. Iyalan cikin gidannan sun shiga damuwa, musamman ƴan ɗakin su Yahanasu da ƴan ɗakin su Bulama. Mahaifiyar Bulama kuwa tun da wannan lamarin ya faru bata sake samun lafiyar jikinta ba. Duk sanda ta samu damar keɓewa saita zubar da hawaye, dan tana matuƙar kewar ɗanta, kuma tana buƙatarshi a tare da'ita. Sai dai takan shanye damuwarta in tana wajan mai gidanta dan gudun yin abinda zai ƙona mishi zuchiya. Haka al'amura suka shuɗe tsawon wata biyu. Zubaina: Ina zaune a falo ina kallon TV. Naci kwalliya da kaya masu tsadar gaske. Bulama yayo sallama ya shigo. Da murna naje na taryoshi. Sai na lura yana cikin damuwa sosai, idanunshi sun kuma runewa. "Lafiya Abban Maryam meke faruwa? Ni da nake cike da albishir mai daɗi kuma. Sai gashi kashigo cikin damuwa." Baice dani komai ba. Hannuna yaja zuwa ciki a ƙasan kafet ya zauna ya tusani a gaba. Kai mun magana dan Allah meke faruwa, mutuwa akayi ko me?" "Babu wanda ya mutu. An sallameni a aiki ne Zubaina. Har sun bani takaddar sallama." Da sauri na miƙe tsaye inajin ruwan zufa na tsatstsafomun. Hankalina ya tashi fiye da yanda hankalin Bulama ya tashi, ban sani ba ko dan shi namijine shi yasa ya fini dauriya oho. An sallameka fa kace, akan me, me kuma kayi haka?" Bashin banki dana ci ba tare da bin ƙa'idar cin bashin ba, kuma kuɗaɗene da suka kai million goma, da million bakwai ne, to sabida hidimar bikin asiya sai na sake karɓar million uku. Sun bani wa'adin sati biyu in biya su kuɗaɗensu, ko kuma suyi gwanjon dukkan kadarorina su fidda kuɗaɗensu. A hakan ma sun raga mun ne, da sai sun miƙani firzin ma, amman duba da irin daɗewar da nayi ina aiki dasu, da irin jajircewata ne yasa su ka barni salin alin" Million goma fa kace? Na shiga ukuna ni Zubaina, Bulama an aura maka mace mai farar ƙafa daga shigowarta cikin rayuwarmu, harta salwantar mana da dukiyarmu da aikin naka ma. Yanzu me muke dashi da zamu biya wannan uban kuɗaɗen? Gashi shagon abayoyin naka, wannan karon ba'a zuba komai a ciki ba. Sai ƴan tsirarun kayan da baza su wuce million ɗaya da wani abun ba" Ina kaiwa ƙarshen maganar na fashe da wani irin kukan baƙin ciki da takaici. Hankalina ya tashi iyakar tashi. Bulama ya kasa rarrashina, dan shi zazzaɓine ma ya rufe shi. A daddafe mu kai sallah, abinci a wannan daren ya gagari bakunan mu. Anayin sallar isha. Bulama yai mun sallama zai je ya kwanta, dan a ɗakin Yahanasu yake yau. "Zanje in kwanta, zazzaɓi ke damuna sosai, bakina ɗaci yake yi sosai kuma" A ranar nayi_nayi da Bulama yaci abinci yaƙi. Haka ya fice yana tangaɗi. Yana fita Mama ta kira ni a waya. "Hello Zubaina Sagiru ne ba lafiya muna babban asibiti an bamu gado" Cikin damuwa nace. Meke damunshi kuma? Mama tace. "Faɗa su kayi, suka sossoki junansu, yanzu haka shi Sagirun cikinshi a farke yake. Tiyata ma za'a shigar dashi yanzu, muna cikin tashin hankali. Sai da muka ɗauko ƴan sanda sannan aka karɓeshi ma. A lokacin nayi ta kiran wayarki bata shiga." Jikina ya sake mutuwa murus a sanyaye nace. Bari in taso Nafisa mu tawo, yanzu ke da waye a asibitin?. Tace. "Ni da Rakiya ne, itama yanzu take son ta tafi, tara ta wuce" To Mama gamu nan, ni kaina a cikin wani irin tashin hankali muke yau a gidan, wani babban al'amarine ya faru" Taso in sanar da'ita a waya amma ina abun yafi ƙarfin waya. Nan da nan na fito daga ɗaki na nufi ɗakin Nafisa. Chartting ɗinta na jaraba take yi. Yara kuma duk sunyi bacci. Nafisa ki taso mu tafi asibiti. Sagiru ba lafiya, yaje ya jawo mana magana. Ki ɗauko Maryam, ni bari in ɗauki Bawa mu kaisu ɗakin waccan abar." Da sauri ta shirya muka fice. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Yahanasu nayi. Itace tazo ta buɗe mun ƙofar da halama daga bacci ta tashi. Tana buɗewa ta ganmu a tsaye. Ki shiga ki kirawo mun Bulama inason in bashi yara ni zan fita" Juyawa kawai tayi. Yahanasu: Da sallama a bakina na tura ƙofar ɗakin Bulama Babba. Kakarin amanshi na dinga jiyowa daga cikin ban ɗakinshi. Tsaiwa nayi cak a bakin ƙofar ina jiran fitowarshi. A mugun galabaice ya fito da bi bango, a bakin gadonshi ya zauna. Ya kalleni da jajayen idanuwanshi yace. "Yahanasu lafiya, akwai abunda kike buƙata ne?" Dama Anty ce tace inyi kiranka, wai zata fita ne" Maimaitawa yayi. "Zata fita kuma?" Ya girgiza kanshi, a hankali ya miƙe ya fita, na mara mishi baya. Ina fitowa na koma ɗakina, dan har bibbiyu nake gani, ga jiri da yake ɗibana, ko maganar da nayi da dabara nayi ta, dan harshena yayi mugun nauyi ainun, nasha maganin tari rabin kwalba. Ina faɗawa akan gado na sake lulawa duniyar bacci. Bulama: Ina buɗe ƙofa naci karo da Zubaina rungume da Bawa a hannunta. Na dubeta a tsanake nace. Lafiya kuwa Zubaina na ganki da yara da daddarennan?" A sanyaye tace "Zanje asibiti ne, Sagiru ba lafiya an basu gado, tiyata ma za'ayi mishi shine nake son zanje Mama ita kaɗaice a can ɗin. Ga yaran su zauna a wajanka ko?" Dubanta nayi jikina a mace, ina ganin kamar nafi Sagiru buƙatar kulawar Zubaina a cikin irin wannan yanayin da nake ciki, amman saita ɓige da haɗani da raino. Hannu nasa na ƙarbi Bawa a hannunta naje ɗaki na shinfiɗeshi, na dawo na karɓi Maryam itama. Sai kun dawo, ku gaishe da mai jikin" Wucewa su kayi, suka barni ni kaɗai a tsaye a bakin ƙofar. Ɗaki na nufa a hankali na zauna tare da tusa yarana a gaba ina kallonsu cike da tausayin yaya makomar rayuwarsu zata kasance? Gashi duk abinda na tara banyi tunanin in zasu iya biya mun wannan kuɗin da ake bina ba. Wayata na zaro na soma kiran layin Ahmad, duk da nasan ranshi a ɓace yake dani, amman bai fiye fishi mai tsayi dani ba. "Bulama kaine a cikin darennan kake kirana, inji dai lafiya ko?" Kai na girgiza nace. Kaiya Ahmad lafiyarnan babu ita a gaskiya, dan yanzu haka maganar nan da nake yi maka zazzaɓine kau a jikina. Ahmad na rasa aikina a gaɓar da nafi buƙatar aikin, a gaɓar da iyalina suke buƙatar kulawata. Ba rashin aikin bane yafi girgizani ba, face bashin banki da naci ba tare da bin ƙa'idojin daya dace ba. Kai ka riga da kasan komai Ahmad. Million goma suke bina. Sati biyu kacal suka yanke mun, ko in biya ko su yi gwanjon dukkan kadarorina su haɗa kuɗaɗensu. Ahmad ina cikin tashin hankali, ina cikin tsaka mai wuya" Salati Ahmad ya saka cikin muryar damuwa yace. "Million goma sha fa kace Bulama? Million goma kuɗaɗene masu yawan gaske, nasan kuma gidanka bazai wuce million huɗu ba tunda kayi mai gyare gyare, motarka data Zubaina duk ba zasu haure million biyar ba, tunda sun ɗan jima tashin hankali kenan wanda ba'a sa mishi rana. Yanzu kai wanne hukuncin ka yanke Bulama, ka sanar da su Ba Bakura halin da ake ciki?" Ban sanar ma kowa ba, bana son kowa yasan halin da ake ciki. Amman kai kam ina buƙatarka a tare dani Ahmad" "To Bulama matsalar itace kuɗin motar da zan zo wallahi bani dashi. Yanzu haka abunda za'aci a gidana da safe wallahi Bulama babu. A taƙaice Shayi da Buredi muka ci muka kwanta da daddarennan ma. Ni rayuwar Lagos ɗin ta isheni ta fice mun a kai, babu komai sai wahala kawai." Da mamaki nace. Ina kasuwancin da Hajara take yi kuma, da zaku zauna da yunwa cikin taraddadin me gobe zata haifar?" Ɗan murmushin takaici yayi yace. "Kuɗi sun rushe banda tarin tulin bashin data barni da biya, wasu ma sai yafewa su kayi. Wata matace ta haɗe kuɗaɗen nasu ta damfaresu, irin masu ƙaryar odar ɗinnan. Amman hukuma sunci nasarar cabketa, sai dai kuɗi kam babu, kotu ma aka turasu suke ta faman sunturi. Ni kam inaga tattarowa zanyi mu dawo Arewa kawai. Ko Kano sai in faɗa inci gaba da buga bugata kawai." Ajjiyar zuchiya na sauke. Na lula duniyar tunani. Duk arziki da muƙaman da Ahmad ya riƙe, yanzu duk sun zama tarihi. Ahmad ne yau bashi da abunda zaici da iyalanshi ma. Allah abun tsoro, duniya kuma zancen banza. Babu komai Ahmad yanzu yaushe kake son ka tattaro ka dawo Arewan?" Yace. "Kuɗin motar da zamu tawo kawai nake ta ƙwadagon haɗawa, kasan mu uku ne. Kuɗin motar mutum ɗaya ma, dubu goma ce a macapolo. Kaga dubu talatin ai ba nan kusa take ba." Haba Ahmad yanzu kana cikin irin halinnan shine ba zaka mun magana ba?" "Haba Bulama nauyin ai sai yayi ma yawa. Duka albashin naka nawa yake, ga iyalai? Ai babu komai wallahi" Ajjiyar zuchiya na sake saukewa nace. Zan tura maka nera dubu hamsin, sai ku shirya tafiyar taku, tsakanin gobe zuwa jibi, duk sanda kuka tsayar shikenan. In yaso sai ku sauka anan gidana, mu tattauna yanda al'amura zasu kaya" Nan mukai ta tattaunawa, muna jajantama juna. Falo na dawo na zauna. Sai tunane tunane barkatai da sukaita zuwan mun kaina. Daga ƙarshe nayi alwala nayi sallah, tare da roƙon Allah akan Allah yasa hakan shine mafi alkairi a garemu. Tun daga wannan lokacin na dangana, wata nutsuwa, da dawowa cikin hayyacina ya sameni. Ɗaki na koma na yi kwanciyata" Zubaina: Da isarmu muka tarar Sagiru an shiga dashi ɗakin tiyata, jini malala a ɗakin da aka fita dashi. Mama sai hawaye take yi. Mama ki dena yin kuka. Ai shi ya jama kanshi, kuma shine zai wahala. Irinsu ke tada rikici a cikin al'umma, wallahi ba da ban ke ba, babu abunda zai kawo ni asibitin, ɗan iskan banza da wofi, ɗan shaye_ shayen banza" Zage _zage na dinga yi ko zan ɗan samu sassauci a zuchiyata, dan gabaki ɗaya a cikin tashin hankali nake, ga ƙaramin ciki a jikina, wanda naita ɗokin dawowar Bulama domin in sanar dashi, dan na sanshi da son yara, Allah Allah nake yi gari ya waye in je wajan Mabaruka. A daren akaima Sagiru ɗinki, aka fito dashi ɗakin jinya. Kowa yayi shiru da abinda yake saƙawa, Goggo Rakiya ma ta kasa tafiya, haka muka kwana a zaune a kan tabarma, tare da masu jinyar ƴan uwansu. Ni damuwata ɗaya shine, a halin yanzu bani da komai ƴan gwala gwalan da nake dasu, su na haɗa na ƙunduma na kai kuɗin wajan boka. Sai ɗan fili guda ɗaya da nake dashi ina kan gini, yanzu shikenan abunda zan tsira dashi daga dukiyar Bulama? Kai ina ai sai ƙawayena suimun dariya, da gwalo duk ranar da suka ci karo dani ina daɓawa a ƙasa, zaman garinnan gagarata wallahi zaiyi. A cikin wannan tunane tunanen na kwana a zaune, banko iya runtsawa ba, ashe yin bacci ma samun wajene ke sa ayishi, ni inyi mana a daren yau, daren da yafi ko wanne dare muni da tsayi a wajena" LAGOS: Obhalande Tunda Ahmad ya kashe wayarshi bayan sun kammala magana da Bulama. Sai ya miƙe zumbul ya goya hannayenshi biyu a baya, ya shiga aikin kai kawo a falonshi, yana jinjina lamarin ubangiji, haƙiƙa sunga ishara, kuma sun ɗauki darasin da nan gaba in sun samu aiki, zasu tsaya tsaiwar daka dan ganin sun riƙe wannan aikin da kyau sosai. Hajara ce ta farka, tayi juyi a katifarsu taji Ahmad baya kai. Tana buɗe idanu ta ganshi a tsaye yana ta faman sunturi" "Abban Anisa lafiya da wannan tsohon daren amman kake tsaye?" Dubanta yayi tare da cewa. "Ki shirya ke da Zulai gobe zamu bar garin Lagos in sha Allah. Zamu bi motar yamma" Da hanzari ta miƙe tace. "Zamu koma Damaturu kenan kake nufi Ahmad, sai da komai namu ya galgance sannan zamu kwashi jiki mu koma ƙauye dan wulaƙanci?" MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE AKWAI FA TURARUKAN WUTA IRI IRI, DA HUMRORI MASU SIRRI SOSAI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN TURARA KAYA, TURAREN GASHI, TURAREN MOPPING, TURAREN TURARA JIKI DOMUN SAMUN DAUWAMAMMEN ƘAMSHI, ROOMFREESHNER. DUK WANI KAYAN ƘAMSHI MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TA TANA DAR MUKU, KU TUNTUƁENI 08179523215 NAGODE DA KASANCEWA TARE DANI. MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 13 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* Tsab Ahmad ya ƙarema Hajara kallo da kyau. Ya tuno a lungun daya haɗu da'ita tana tallen mangwaro, ya wanketa ya aureta, gidansu gidan talakawa futuk ko karatun boko ba'ayi, amman yau shi take faɗama wai Damaturu ƙauye ne." "Ji Hajara yana da kyau ki iya bakinki, kinganni nan? Wallahi bazan taɓa zuba miki idanu kici gaba da rainani a cikin gidannan ba. Ohh sabida yanzu bani dashi ko, ashe ladabi da sinsin ɗin da kike mun da kai, duk ba dan Allah bane? Ni da ya dace ace a yanzu ne zan samu cikakkiyar kulawarki a gareni, amman a yanzune kike ɓullo mun da salo_ salon wulaƙanci, dama ance mata haka suke da yawansu, ku ci ku goge baki. Duk da akwai matan arziki marasa manta halacci. Nine shugaba a gidannan, umarni nake baki ku tattare duk abinda zaku tattare zamu tafi gobe" jikinta ya ɗanyi sanyi amman ba wani sosai ba, tace. "Maganar zuwa kotu da muke yi akan ƴar damfarannan kuma fa yaya kake son nayi kuɗaɗena fa da yawa?" Harara ya zabga mata yace. "Ke in ma zaki cire ranki akan yiwuwar fitowar kuɗaɗenku gara ki cire rai, kibi abinda nace miki kaina ciwo yake yi mun. Tsaki taja dogo ta koma kan yagalgalalliyar katifarta ta kwanta, sai mis_ mis take da baki irinna mata marasa kunya. Washe gari kuwa tun safe Hajara ta soma fito da kayayyakin ɗakinta zuwa cikin tsakar gidansu. Gidane mai cike da ɗakuna falle falle ɗakuna sunfi ashirin. Da matan aure da zawarawa da karuwai, maza da mata, ƙabilu iri_ iri babu wanda gidan bai tara ba. Rayuwar kudu in ba ƙwaƙƙwaran sana'a gareka ba, ko wani muƙamin gwamnati, ko aikin kamfani ba. Ai wahalace kawai mai mugun girman gaske, ga tsadar rayuwa, uwa uba tsadar kuɗin haya. Duk kwaraɓewar gidan da su Hajara suke ciki nera dubu biyu da hamsin suke biya a duk shekara, ɗakine ƙarami ba babba ba, bayan gida a tsakar gida yake, girki kuwa sai dai ko wacce tayi a bakin ƙofarta. Zulai a ɗakin Maman Isa take kwana, kasancewar maman Isan bata da miji zaman kanta take yi. Amman sana'arta take yi, bama yarinya babbar macece. Hatsi tsada, kayan miya tsada, rayuwar kudu akwai tsanani sosai. Matan dake zaune a gidan duk suna sana'ar sai da abinci, kasancewar Obhalande anguwace data tara ƴan cirani na jihohin arewa da dama, anguwace da marasa ƙarfi su suka fi yawa, duk da masu kuɗin ma akwaisu, unguwar tana kallon barikin sojoji. hakan yasa sana'ar abinci take garawa. Hajara ma tana sai da kunun zaƙi ƙaramar gora nera ɗari, kuma ba ƙaramin ciniki take zubawa ba. Firjin nata sacewa akayi, shi yasa ma ta dena, wannan kenan " Matan gidan ko wacce tana tsakar gida, masu kayan sana'a na safe suna ta ragargaza ciniki. Masu masa, da ƙosai, da kulele ( Alala) da kunu sai faman ciniki suke yi. Masu abincin rana kuma sunata haramar soma gyare gyaren kayan miyansu, yayin da wasu ke iza wuta. Haliman Lokoja ta tashi tsaye ƙugunta a riƙe a hannayenta tace. "Me zan gani, yaji ko mutuwar aure Hajara da kike fito da kaya. In yaji ne sai ince miki kin gane hanya, in sakine ince miki zoki ɗau jar fulawa" Duk wannan maganar Haliman Lokoja tana yi tana yamutse mummunar fuskarta, wacce tasha kwalliya ta fito ɗoɗar take yi. Cikakkiyar karuwace mazauniya Lagos wacce ta fito yawon bariki, ta ƙare a karuwanci na ƙazanta, dan duk karuwan cikin Obhalande karuwaine, wanda mafiya akasarinsu ƴan cirani Arewa ke hutawa dasu da daddare, su ɗan basu wasu kuɗaɗen da basu taka kara sun karya ba. Hajara tace. "Allah ya tsari gatarina da saran shuka, bana ga saki ba. Dan duk lalacewar masa tafi ƙarfin kashin shanu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta. Matan gida, ina mai shaida muku yau zamu bar garin Lagos da zama, zamu koma Arewa a yafemu." Daga nan bata sake cewa komai ba. Gidan ya kaure da hargowa, kowa na faɗar albarkacin bakinshi, da masu cewa karsu koma, gwamma suyi zamansu su kama sana'a sai masu cewa gara su koma Arewar ya fiye musu. Hajara dai bata da wani zaɓi face bin Ahmad a yanda yake so. Ala dole sukaima kowa sallama, suka nufi tasha da tilin tarin ƴan komatsansu, na amfanin yau da kullum. Misalin ƙarfe takwas motarsu ta ɗauki titi sai arewa. Da motar dare yaso su hau, amman da yaje siyan tikiti anan ya sake ra'ayi" Kaduna: Bulama: Yau na wayi gari a cikin godiyar Allah, da dangana wanda hakan har yaso bani mamaki ainun. Ina dawowa daga sallar Asuba, nayi wanka na shirya tsab. Su Maryam kuwa sai sharara baccinsu suke yi, kasancewar yau asabar ne babu makaranta. Ɗakin Yahanasu na leƙa, bata ciki, sai da na fito tsakar gidan na ganta a gaban motata tana ta faman durzarta. Shiru nayi ina kallonta ina jin raina yana tafasa dana ganta. Ganinta ma bana ƙaunar yi. Ina cikin zaman zamana cikin farin ciki, iyayena da basa son ganin farin cikina sun auro mun mai farar ƙafa, daga zuwanta ta ruguza mun rayuwata. Da hanzari na isa wajan motar. Tana ganina ta soma kiciniyar gaisheni. Ni kuwa kallo wannan bata isheni ba, motata na shige naja na barta da moɗar ruwan da take kwarama motar. Ban zame ko inaba sai asibiti wajan su Zubaina. Da sallama na shiga ward ɗin da aka kwantar da Sagirun, bayan na kira wayar Zubaina tayi mun kwatance. Mama na ganina ta shiga washe baki tana mun gaisuwar ban girma. Hakan yana faranta raina ainun. Yanda Mama ta ɗaukeni tamkar ɗan cikinta, kuma take bani kulawa ta musamman. Zubaina kuma tana gefe ta zabga uban tagumi. Mama ya mai jikin dai?" Mama tace. "Toh gashi nan dai. Har yanzu bai farfaɗoba tukunna dai, amman muna sa rai zuwa anjima zai farka." To Allah ya ƙara bashi lafiya, Zubaina a rakani ofishin likita, inji daga bakinshi, ko akwai wani abun da ake buƙata. Ina Nafisa fa?" Goggo Rakiya tace. "Tatafi gida dafo abinci, bata jima da fita ba." Zubaina ta miƙe tana gaba ina bin bayanta muka fita. Yau baki da aiki ne Zubaina? Kinsan bazaki yi wasa da aikinki ba, dan shi zai ɗan taimaka mana kafin in samu wani aikin." "Inada night ne, sai da yamma zan tafi, ya kwanan damuwa? Jiya ko runtsawa banyi ba Bulama cikin tunani da taraddadi na kwana" Ɗan dariya nayi mata nace. Ni kuwa nayi bacci, na miƙa lamarin ga Allah. Sai dai yanzu dana fito tsakar gida, na haɗu da waccen baƙa mummunar yarinyar, wallahi sai mikin ya zame mun sabo. Ina zaman zamana an auro mun mai farar ƙafa, daga zuwanta komai nawa ya rushe lokaci guda. Ita kanta zata ɗanɗana kuɗarta, in dan kuɗi ta amince aka aura mata ni, to tafaru ta ƙare, sai in gani ai tare duk za'a sha wuyar ai ko?" Murmushi Zubaina tayi sannan tace. "Ai masu farar ƙafa babu irin masifar da basa haddasawa. Akwai wani maƙocinmu, attajirin gaske ne, irin masu kuɗinnan na da ne. Ɗan kasuwana, ya mallaki tireloli da dama. Yana zaman zamanshi yayo sabon aure. A takaice, duk kadararshi sai da ta narke. Tirelolinshi sukaita haɗari ana rasa rayuwa, da gidan da suke kawai ya tsira. Shima cikin dare kawai gobara ta kama gidan, babu abinda wutarnan bata lashe ba. Dole suka dawo anguwarmu da haya, hawayi yake siyarwa yanzu haka fa, kai bakace ya taɓa yin kuɗi ba ma. Jinjina kaina na dinga yi har muka shiga ofishin likita, muka fito ina cike da mamaki. Wayata ce ta shiga kuka, ina zarowa naga number Ahmad. Ahmad ba dai har kun iso ba ko?" Daga cikin wayar Ahmad yace. "A'a muna dai hanya yanzu muka shigo wani ƙauye, an tsaya cin abincine, shine nace bari in kiraka" Ai gara kuwa daka kira, dan insa ai muku girki, ka ganni a asibiti ƙanin Zubaina ne bai da lafiya. Amman yanzu zan koma gidan, zan sa a gyara muku waje, ai muku girki. Ahmad yace. "To shikenan sai mun iso, ka isar mun da saƙon gaisuwata wajan Madam, kuma inai mata ya mai jiki" Yana kaiwa nan ya datse wayarshi. "Ahmad ɗin garin zai shigo ne?" Nan na labarta mata dukkannin halin da Ahmad yake ciki, maimakon inji tayi magana, ko ta tausaya sai kawai ta taɓe bakinta. Ko da muka koma ɗakin da Sagiru yake a kwance, ya farka, sai surutai marasa kan gado yake yi, yana zage_ zagen shi bazai yarda ba, sai sun ɗauki fansa ko mutuwa zaiyi. Mama kuwa tayi shiru tana kallonshi, daka kalli fuskarta zaka ga cike take da damuwa a matsayinta na uwa. Goggo Rakiya ce ta balbaleshi da faɗa. "Haba Sagiru ka shiga taitayinka mana, kuma ku tausayama mahaifiyarku, tun jiya muke nan babu wanda yai baccin arziki, amman yanzu da farkawarka ka ishi mutane da zancan ɗaukar fansa_ ɗaukar fansa, abunda ya faru dakai bai zamema ishara ba ashe? Da yanzu kana lahira naga yanda za'ayi ka ɗauki fansar. Yara basu san komai ba sai tada ma iyayensu hankali wannan wanne irin zamanine haka?" Ni dai ina gefe ina kallonsu kawai, kuɗi na ciro a aljihu wanda bansan adadinshi ba na miƙa ma Mama, sannan nayi musu sallama na fito Zubaina na biye dani a baya. "Abban Maryam in an gama abincin sai ka dawo ka kawo mana namu ko? Ni na ɗauka zaka sa tayo abincin safe ka tawo mana dashi ai" kaina na dafe nace. Kinsan da yake hankalina ba a jikina yake ba, na sha'afa shaf. Amman zansa tayo abincin, zuwa rana zan kawo muku" Murmushi tayi tace. "Tayi kamar na mutane goma haka, dan nasan zuwa anjima asibitin zai cika da mutane, kuma inason ka bani kuɗi zan siyo kayan tea in ajjiye, kuma ba kuɗi ishasshe a hannuna" Nayi mamakin da Zubaina ta tambayeni wasu kuɗaɗe a cikin wannan halin da nake, duk da kuɗin dana dunƙula na ba Mama. Amman kasancewar bana ganin wallen dukkan abunda Zubaina ta aikata, a idanuna gani nake duk abinda tace ayi shine abunda ya dace. Kuɗaɗen jikina duka na bata, mu kai sallama na fice daga asibitin zuwa gida" Zubaina: Bulama na fita na shige motata, a guje na fice a asibitin. Kai tsaye gidan Mabaruka na nufa, da sallama na shiga ɗakin ba tare da na jira anyi mun izini ba. Adam yana rungume da Mabaruka ita kuma sai zabga shagwaɓa take yi. Suna ganina yai maza ya saketa, yana sosa kanshi. Kaina a ƙasa muka gaisa ya fita, Mabaruka ta mara mishi baya tare da ce mun. "Ƙawata bari in rakashi zaure in dawo" Jigum na zauna a kan kujera, sai wasiƙar jaki nake karantawa, gabaki ɗaya hankalina baya jikina sam. Sallama naji anyi, tare da shigowar kai tsaye kamar dai yadda nima nayi. Hadiza ce ta shigo ɗakin da ganinta kasan a ruɗe take, waje ta samu ta zauna. Hadiza kece a gari da safiyarnan haka? " Kallona tayi kamar tana tunani, daga bisani tace. "Hmmmm Zubaina ke dai ki bari. Aurenane ya mutu, shine kika ganni a firgice haka, kishiya ta hanani saƙat ni da yaran duka, ke ya kika ga yanda na lalace?" Dubanta nayi da kyau, tabbas Hadiza ta lalace sosai, tayi duhu kuma. Hadiza ƙawarmu ce tun ta ƙuruciya, tare mu kai karatun islamiyya da'ita. Tana Aure a Zaria. Ta auri mijinta tun yana talaka, daga bisani Allah yai mishi arziki, arzikinshi ke da wuya yayo sabon aure. A lokacin mun ba Hadiza shawarar ta tashi tsaye danta ƙwaci ƴancinta a gidan mijinta. Amman sai ta nuna mana ita bata akan irin layinmu,harma tana binmu da nasihar muma da muke bin malamai mu Daina, wannan kenan. Baki na taɓe nace. Gaskiya kin lalace sosai. To amman ke kika so ganin kanki a haka, dubeni da kyau ki gani, ga Mabaruka itama ai kina gani, Safara'u ita kuma tana can Abuja. A cikin ƙawayenmu kece kaɗai koma baya. Hadiza wa ya faɗa miki borno gabas take. Kowa fa da kika ganshi ba'a zaune yake ba. Zaka ɗan dinga neman taimako ko babu komai. Amman ko da muka baki shawara ai wa'azi ma kika jefemu dashi. Ai namiji da kike gani bashi da wani burin daya wuce, ya samu dama yai arziki ya ƙaro Aure. ke kuma da kika sha wahalarshi ya saki a kwandon shara ke da bola babu maraba. Duk da tashi tsayen da nayi akan Bulama, sai da munafukan iyayenshi su kai mai Aure, yanzu haka akwai kishiya a gidana Hadiza" Kai na girgiza ina mai cike da takaicin wai ni Zubaina ina da kishiyar da ake mana rabon kwanaki da'ita. Duk da ma ba kwanciyar aure akeyi da'ita ba. Amman zuchiyata a cikin zafi da raɗaɗin ganinta ta ke a ko da yaushe. Mabaruka ce tayo sallama ta shigo "Me zan gani Hadiza kece a gidan Ƴan bin bokaye yau kuma?" Hannu Hadiza ta kamo ma Mabaruka, bata ce komai ba, sai ta saki wani irin kuka mai tsuma zuchiya. Shiru mu kayi dukkanmu muna kallon ikon Allah, daga baya Mabaruka tace. "Kece ai da abin haushi Hadiza, yanzu me kike buƙata? Ki share hawayenki ki mun bayani dan Allah" Hadiza nan ta buɗe baki tana labarta mana irin ƙunci da takaicin ɗa namiji da tai ta ƙunsa, da takaicin kishiya iri iri, ga sakamakon haƙurin da ta dinga yi nan Muktar ya ƙare yai mata saki biyu tare da yi mata korar kare." "Danƙari sunan kare a lahira. Lallai Hadiza kinga duniya, duniya ta ganki. Amman in kina da kuɗi wallahi kafin ki kammala iddarki Muktar zai zo bikonki, kuma daga shi har kishiyar taki sai kin jasu a ƙasa, kin riƙo kuɗi ko?" Da sauri Hadiza ta ce ma Mabaruka. "Na riƙo kuɗi Mabaruka Gonata na siyar na riƙo kuɗin, bani da wani buri daya wuce in koma gidana, badan komai ba, sai dan sabida yarana. Wallahi baku ganni ba, a cikin ƙannena mata nake kwana, banda ikon ince su yi mun wani abun, sai sui mun rashin kunya. Mama ko gaisuwata bata amsawa, duk aikin gidanmu ni ke yinshi, sati na ɗaya a gidan, inna jima ya zaman zai kaya kenan?" Mabaruka ta saka dariya tace. "Uhm ki kwantar da hankalinki, ƙila gobennan kiga Muktar yazo har ƙofar gidanku zai tafi dake. Ƙawata Ƴar sanda ya labari ne. Ni na ganki wani kwasha_ kwasha ne?" Hmmm Mabaruka ba doke ki ganni a haka ba. Ai a cikin garari nake, Bulama ya rasa aikinshi, ga bashin million goma da banki ke binshi. Sati biyu kacal suka bashi ko ya dawo musu da ƙuɗaɗe su, ko su zo suima kadarorinshi gwanjo su cire kuɗaɗensu. Wallahi jiya ban rintsa ba, ina zan shiga a garinnan, ina zan saka kaina? Gashi zinaran dana mallaka duk na kaɗar dasu a neman biyan buƙata. Danma dai buƙatar ta biya shine. Nace Mabaruka ko wannan halin da muka shiga shine abunda boka yake nufin zai biyo baya ne?" MABARUKA ta shiga salati tana tattafa hannayenta tace. "Kinsan ni kaina irin hakan sai da ta faru dani. Amman gashi yanzu komai yana warwarewa, dan yanzu haka Adam abubbuwa sun warware mishi, sabon gida ma zamu koma sati mai zuwa. Amman bayan naje wajan boka da wata guda, duk wani tattalin arzikinmu sai da ya rushe, har sai da ta kai, nike ciyar da Adam. Na sayar da ƴar motar tawa, kayan ɗakina kansu sai da na siyar, hatta zanen ɗaurawa sai da yaso gagarata fa. Rufin asirin da muka samu, shine gidanmu da muke ciki. Zubaina haka aikin bokannan yake, amman komai zai dawo daidai" Kaina na kama wanda yake yi mun ciwo kamar zai tarwatse nace. Taya zan soma rayuwa a gidan haya a garinnan namu Mabaruka? Mutane da dama idanu suka baza suna jiran faɗuwarka, nifa wallahi a cikin ɗimuwa nake, gaskiya talauci fa masifa ne" "Zubaina ashe baki shirya neman duniya ba? Ke meye naki dan Bulama ya rasa aikinshi, ke da kike jan albashi sama da dubu ɗari, duk abinda kikeson yi, ko son ci ai zaki ci ma ranki. Shine a wahale shi da waccen jakar da masu dattin baki suka aura mishi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace mata. Kuma hakane Mabaruka, ni da in zauna takaicin ɗa namiji da kishiya ya haifarmun da hawan jini da hau, gara Bulama ya mutu ma baki ɗaya Wallahi. Kinga yanzu ne zanyi mulkina ma sosai. Ni damuwata bakin mutanene dama." Mabaruka tai ta ƙarfafani, har sai da ta samamun nutsuwa. Tare muka fito dasu, a tashar kawo na sauke su, zata raka Hadiza Jos wajan boka. Tuƙi nake yi, amman sai tunani nake ta fama dashi, zuchiyata sai aukin saƙe saƙe take yi mun iri daban daban, duk da na kasa samun matsayar tunanina, abu ɗaya na sani shine, ina yima BULAMA so mara musaltuwa, Amman zan iya bin ko wacce hanya ce dan ganin ni kaɗai na mallakeshi. Kayi haƙuri Bulama, sonka da ƙaunarka ne ya ja mun tsananin kishinka. Da in rayu da takaicin kishiya da iyayen miji na gwammaci ka mutu kowa ya rasa. Note: mata muji tsoron Allah akan kishin da zai rabamu da Ubangijinmu, kishin da zai kaimu ga halaka. Wannan rayuwa da mai tayi kama. Wai mai muka ɗauki kalmar kishi, da kishiya ne? Muji tsorom Allah mu dinga tunawa za'a mutu kuma akwai hisabi a tsakankanin junanmu" Yahanasu: Wayata na jawo na kira Hajja Fati, bayan mun gama gaggaisawa nace. Hajja Fati a ina zan samu wannan maganin da kika bani ne? Ya ƙare har na siyo maganin tari na yara, amman banji daɗinshi kamar yadda naji daɗin naki ƙwayoyinba. Su kaɗai nake sha in samu lafiyayyen bacci, ni gani nake yi ko a haka aka auna jikina ya haura sosai, Hajja Fati ina cikin wata iriyar rayuwa mai wuyar fassarawa gaskiya." "Haba Yahanasu kar kiyi sake ciwo ya kamaki a banza da wofi. Maganin dana baki yana da wuyar samu zancan gaskiya kenan, dan ba'a samunshi a kemis, nima wani yaron unguwarmu ne yake siyomun ya kawo mun a ɓoye. Da zaki fita haka kiga wani ɗan shaye shaye sai ki tareshi ki faɗa mishi sunan maganin, sai ya faɗa miki inda ake siyarwa. Wai babu wani abu daya shiga tsakaninku ne da Bulama, kamar hoto haka yake kallonki?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Kallo ma ai ban isheshi ba. Ga fishin da su Ba Bakura suke yi dashi, abun ni duk yabi ya dameni Hajja Fati. Amman zaman gidannan ya isheni, wallahi da badan furucin da Ba Modu yayi akaina ba, da sun wayi gari sun nemeni sun rasa na shiga duniya. Jina nake yi kamar a cikin kurkuku nake wallahi Hajja Fati, kullum zuchiyata a cikin damuwa take." Hajja Fati tace. "Zancan ki shiga duniya ma bai taso ba Yahanasu, nasara tana cikin biyayyar iyaye, kiyi haƙuri wata rana kece da riba babba. Ni dai shawarata shine ki dinga shan magungunanki, kina ɗebema kanki kewa, kar ki sake damuwa ta haifar miki da matsala. Ki nemama kanki mafita, karki bari iyayenki suga gazawarki" Jikina a saɓule mu kai sallama da Hajja Fati bayan ta faɗamun sunayen kayayyakin maye kala kusan uku, da kuma yadda zanyi amfani dasu. A zahirin gaskiya banso na jefa kaina a wannan rayuwar ta shaye _shaye ba, amman wani gefen na zuchiyata yana kuma ingizani kan cewar in sha kawai, in samu sassauci. Daga lokacin da na soma ta'amali da magungunan maye, daga lokacin na samu nutsuwar zuchiya, kuma a lokacin zuchiyata ta dena raya mun in kashe kaina, wannan firgicin da takurewa waje ɗaya ne ban dena ba , tun daga sanda wannan al'amari ya faru dani kawo iyanzu. Ga wahalhalu da wulaƙanci da nake fuskanta a wajan Bulama da matarshi. Hijabina na zara na fice a gidan, dan burina shine in samo wannan ƙwayoyin in haɗiya ko zan ji sanyi, jikina har wani rawa_rawa yake yi, yayinda zuchiyata take sake ingizani. Sai gani ina neman lunguna, domun nasan sune matattarar ɓata gari. Cikin sa'a na ɓulla wani lungu, duk da zuchiyata sai da ta tsinke, abunda ya faru dani ya shiga dawo mun, amman ganin wata mace mai hijabi harda niƙab a cikin kangon, hakan sai ya ƙarfafa mun guiwata, a can gefe na tsaya, wani ɗan matashi da bai wuce shekara sha takwas ba ya leƙo yace. "Yane Hajiya dame _dame za'a haɗo miki, akwai turaren wuta, akwai maggi, muna da macline, sannan kuma muna da fanta, akwai laka." Nan ya dinga jero mun kayayyakin maye, da irin adon maganar da bazan iya fassarawa ba, kasancewata ba Bahaushiya ba. A ɗarare na jero mishi wanda Hajja Fati ta faɗa mun sunayensu. Ni dai ina daga gefe ya koma kangonnan, wannan matar mai niƙab kuma sai ƙirga mata wasu magungunan kwalba akeyi a cikin wata ƙatuwar kula, da wasu magunguna a cikin takaddu, da gani dila ce ita kam. Wannan saurayinne ya dawo ya miƙo mun kayana a leda yace "Nera dubu uku kuɗinki Hajiya. Mu na nan, nan itace majalisarmu, duk sanda kike buƙatar ƙiri kawai ki antayo zaki taddamu CE masarautarmu cau cau Hajiya, a lafiya dai mata yanzu fa kuna wuta wallahi. Ni dai da sauri na karɓi ledar na cunkusa a cikin jakata, na bashi kuɗinshi, na fice da sauri a lungun ina waige. Zuchiyata sai harbawa take yi, inajin babu daɗi a jikina, nasan ba irin tarbiyyar da iyayenmu suka ɗauramu akai ba kenan. Nayi imani da Ba Modu zai san halin da nake ciki, babu abunda zai hana shi ya tsine mun albarka. Haka Ya Innana nasan saɓule hannayenta zata yi a kaina, ta sallamama duniya ni. Da wannan tunanin na koma gida, jigum nayi akan kujera ina tunanin, anya wannan hanyar zata ɓulle dani kuwa? Yayin da sheɗan shi kuma ya dinga buga mun ganga. Magungunan na harhaɗa na watsa a bakina na bisu da ruwa, hawayen daya zubo a kumatuna na share, ina cike da ɗunbun nadamar abunda na aikata." MRS BUKHARI CE MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B) 14 *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. Wayata ce ta soma kururuwa, ina dubawa naga Ba Modu ke kirana, gabana ya takarkare ya faɗi, ji nake tamkar ya kiranine dan ya tsine mun akan rayuwar dana jefa kaina, da in ina na soma gaisheshi, bayan na ɗauki wayar na kara a kunnena. "Uwata kina lafiya, yaya mai gidan naki?" Muryata na rawa nace dashi. Lafiya ƙalau Ba Modu, ya su Ya Innana da su Wakil?" Murmushinshi na dattawa yayi, kana yace. "Gashi nan a kusa dani, zamu je asibiti Baana ba lafiya jikin nashi yayi tsanani sosai, sai ki kirasu iyayen naki mata ki ji jikin nashi. Kuna zaune lafiya da Bulama ko, kuma ina fatan kina bin umarninshi akan dukkan abinda ya umarceki dashi, in dai ba saɓon Allah bane?" Hawayen da nake kireƙewa ne suka zubo. E Ba Modu" Abunda na iya furtawa kenan. Ya ɗaura da cewa. "Allah yayi miki albarka, kiyi haƙuri da dukkan abunda zaki fuskanta, rayuwa a cike take tab da ƙalubale iri daban daban, musamman a gidajen aure. Biyayya da haƙuri shine babban jari, da makamin da ko wacce mace ya dace ta riƙa. Ki sani babu abunda yake dauwamamme face ƙudura da mulkin ubangiji Allah. Yahanasu na horeki da yima Bulama biyayya irin biyayyar da bazai taɓa mancewa da alkhairinki ba, ko da a bayan ranki ne. Hakan shine kaɗai zai sani farin ciki, dukkan wani abu da zaki buƙata na kuɗi ki tambayeni zanyi miki Yahanasu. Dake da Bulama baku da banbanci, nafi son Bulama fiye daku, kamar yadda nafi son Bakura fiye da kaina. Kuma yanda nake ji akan Bakura da iyalanshi, hakan yake ji akan nawa iyalan, kinga kuwa ya zame miki dole kiyi ma mijinki biyayya" Jikina ya mace mus, sai da ya ɗaureni da duk jijiyoyin jikina Sannan yai mun sallama. Kiran gidan nayi, duk matan gidan iyayenmu, sai da na kira kowa na yi mishi ya jikin Ba Baana, shine kaɗai ban samu damar yin magana dashi ba. Ya Innana itama nasiha tai ta ragargazomun, tare da lallamina, Allah sarki uwa, burinta ta faranta ran iyalanta kowa yaji daɗinta, har ya shiga inuwarta ya fake" A hanzarce Bulama Babba ya shigo ɗakin. "Yahanasu, ki tashi kiyi girkin da za'a kai asibiti, ƙanin Zubaina bai da lafiya. Sannan Ahmad yana hanya da iyalanshi, suma ayi musu girki, sannan ki gyara musu ɗakina, anan zai sauka da iyalinshi." To Bulama Babba, akwai abunda kake son a girka ne, ko kuma in girka ko meye?" Zama yayi a kujera tare da dafe kanshi yace. "Ki dafa koma meye kawai" Nan da nan na shiga aikin girki, Awa sama da huɗu, nayi ina abu ɗaya. Tuwon shinkafa da miyar taushe nayi, naman rago nayi amfani dashi, kafin in yi girkin ma sai da na shiga kasuwa nayo cefanen miya dan ba komai muke dashi a firji ba, dana dawo ne na shiga aikin, ni ce har bayan isha ina abu ɗaya, sabida babu kuzari a jikina sam, nasha magunguna sun kashe mun jikina sossai. a gaggauce Na jera kulolin abincin baƙi a falo, wanda za'a kai asibiti kuma na fita dashi, mai gadi yasa a bayan mota. Bulama Babba yana zaune shiru, yayi wani irin mugun zurfi a cikin tunani, sai numfashi yake saukarwa. Abubbuwan dana ɓata na wanke, na kunna turaren wuta, sannan na dawo wajan Bulama Babba nace. Na gama komai, wanda za'a kai asibitin yana mota" Kai kawai ya gyaɗa mun, sannan yace. "Na saki girki wuni guda ki kai kina abu guda tun rana har bayan isha, ƴan Lagos har sun shigo Kano. Amman lafiyarki ƙalau kuwa, ko kuwa raini ne da iskanci yasa ki kai haka, ko kuma ƴan uwan Zubaina ne bakya so su ci abincin?" Kaina na ƙasa bance mishi komai ba, har sai da ya gama na bashi haƙuri. Miƙewa nayi na wuce ɗakina, ina jiyoshi yana waya. Ina zama a bakin gado na jiyo sallamar Ahmad da iyalanshi. Dole na saka hijabi na fito falon. "Malama Yahanasu Amaryarmu, kai masha Allah naji daɗin wannan al'amari sosai" Kaina na sinne na zauna aka shiga gaggaisawa. Hajara tace. "Yahanasu ya Fandau yaranta nawa yanzu kuwa? Rabona da'ita tun tana goyon wata baƙar ƴarta" Dariya nayi nace. Yaranta uku yanzu, ya hanya?" "Hanya an shata, wani irin wawan dereba mu ka samu mai mugun gudu ya dinga wasa da rayuwarmu a titi, ai da sai irin 12 na dare ko 1 ya kamata ace mun shigo Kano." Dariya tayi tana kallon Bulama Babba ta sake cewa. " " Masha Allah, Bulama lallai anyi gyara, gida ya fito yayi fes." Dariya yayi mata yace. "Hajara mutanen Ikko an dawo arewa, an baro cikin yarbawa masu kolokolo" Dariya suka yi shi da Ahmad, Ahmad yace. "Kai dai bari, Ikko ko wahala Bulama? Ai wallahi ina mamakin yaranmu matasa da suke zuwa Ikko ƙwadago, duk arzikin dake Arewa, har sai sunje Lagos zasu nemi kuɗi. Ka gansu a wulaƙance, basu da wajan kwana, ita kanta sana'ar basu da guda ɗaya, duk abinda aka samu yi akeyi kawai. Wasu sun zama ƴan ɓata gari, wasu basu da aiki sai shaye_ shayen muyagun ƙwayoyin da zasu kassara musu tunaninsu" Kaina na sinne ƙasa, nace da Hajara. Mu shiga daga ciki ku samu ku watsa ruwa, kuci abinci, ku huta" Jakunkunan kayansu mu ka shigar ciki, na ja yaran muka shige ciki. Duk su kai wanka, sannan su ka ci abinci. Hajara macece mai hira da son jin ƙwaƙwab, a fahimtata irin matannanne masu dukan cikin mutum dan suji abinda suke so. Bata san ko a gida, ƴan uwana suna saramun wajan zurfin ciki ba. Har Dala yakan kirani da munafuka in yaso jin gulma ni kuma na ƙi bashi haɗin kai. Allah sarki Dala nayi kewarsu sosai" Bulama Babba: Bayan Ahmad yayi wanka yaci abinci, sai muka fita dan kaima su Zubaina abinci. Kai meye shawararka Ahmad, wallahi ina cikin damuwa sosai, a hakanma daurewa nake yi Ahmad. "Ni shawarata anan shine. A gaskiya kar ka jira banki suzo su yi gwanjon kayanka, hakan tonon sililine. Ni a shawarce ka siyar da gidanka da duk abinda ke cikin gidan, da kayan shagonka dai dukka, a haɗa musu kuɗinsu akai musu, yafi rufin asiri, fiye da ace banki sunyi gwanjon gidanka. In wani abu ya saura, sai ka ɗan siya ma su Zubaina ɗan kayan ɗaki, ka kama haya kuma, sai kuma mu haɗu mu shiga neman sana'a" Gaskiya ne maganarka Ahmad, zamu tattauna hakan da Zubaina yanzu in muka je asibitin. Amman wallahi bansan ta inda zan soma neman aiki ba ma" Ahmad yace. "Ni kam daga Kaduna Kano na nufa acan zanje in ya da zango, zan nemi aiki inna samu to, in ban samu ba, sai in shiga aikin ƙarfi duk wanda na samu sai inyi, kuma kanon tafi kaduna sauƙin rayuwa. Na kira Safiyanu a waya yana kan duba mun waje, ranta mun kuɗinma zaiyi. Cewa fa yayi ana samun gida sukutum na dubu hamsin, ɗaki biyu da bayan gida da kitchen, da ɗan tsakar gida. Ai ya ishi talaka rayuwa muita adda'a Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar, nasan halin da kake ciki kafin ka ɗanɗana nina soma ɗanɗana, a cikin shi ma nake ni." Shiru nayi ina wani nazari a zuchiyata, a haka har muka iso asibitin. A wajan parking ɗin motoci muka haɗu da Zubaina da Asiya Amarya. Tayi ƙyau ta zama jawur, tana ganina ta soma washe baki. Asiya Amarya kece a gari? A lalle maraba da zuwa" Cikin wasa da dariya muka gaisa. Zubaina suka gaisa da Ahmad, Asiya sai ta ɗan ja gefe tana jiran Zubaina. Madam ina zaki je haka a cikin darennan?" "Ai da abinci zanje mu siyo, nace kar aikin yai ma Yahanasu yawa, ga hidimar su Ahmad, kuma mu na da baƙi a ciki sai tea muka wuni sha, ni aikin ma ban samu zuwa ba." Daɗi naji sosai a raina da Zubaina bata ji zafin Yahanasu ba, lallai ta cika mai sauƙin hali. A'a ai ta jima da gamawa, kin ganshi shi ya tsayar dani" Na nuna Ahmad. "Zubaina yaya mu ka ji da haƙurin abunda ya faru, ya mai jikin kuma?" Wani ɗan murmushin damuwa da tashin hankali tayi, dan har faɗawa Zunaina tayi, tace. "Kai dai bari Ahmad, tunda wanna labarin ya riskeni gabaki ɗaya babu abunda yake yi mun daɗi, ni Kadunan ta fice a kaina, wallahi da da hali garin zan bari, dan kaucema masu son ganin faɗuwarka suyi dariya" Carab na tari hanzarinta da cewa. Ni kaina garin nake son bari. To Ahmad yai mun magana Kano zai koma da zama, in kina ganin babu wata matsala, kuma zaki samu transpa a wajan aikinki ai sai mu kutsa Kanon ko, kinga gaki ga ƴar uwarki Asiya ma ko ya kika ce?" Ajjiyar zuchiya ta sauke ta lumshe idanunta, nima idanun nawa na lumshe ina jin sonta na nunkuwa a zuchiyata, ga tausayinta da nake ji. "Abban Maryam wallahi mu je, ni ko yanzu kace mu tafi ai da gudu zan bika, ai duk inda kake anan nake. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Sagiru yaron da suka je suka haɗu su kai faɗa, iyayen ɗaya daga cikin yaran sun zo har asibiti sun samemu. A gaskiya sunyi ma mahaifin yaron ɓarna sosai. A shagon mahaifinshi suka same shi, suka ɓarnatar da dukiyar shagon. So suke a biya su, kuma kuɗine kusan million uku. Kasancewata ta ƴar sanda ne yasa iyayen yaron su kai haƙuri basu shigar da ƙara ba, da kotu za'a shiga. Amman na basu haƙuri nace gobe zan kawo musu million ɗaya da rabi tunda su biyu ne su kai ɓarnar. Nasan baka da kuɗi kai kan ka taimako kake nema. Shine nace ko zaka amince in siyar da motata in biya kuɗin?" Ahmad yace. "To Zubaina Bulama dai yana buƙatar taimako bafa lallai bane in an siyar da dukkan kadarorinshi su biya mishi bashin da ake binshi ba. Ni ina ganin maganar siyar da motarki ki biya kuɗin da Sagiru suka je su kai ɓarna, baima taso ba. Sannan ai da kin bari an hukuntasu, in yaso ƴan uwa su haɗu a gagganɗa a biya waɗannan kuɗaɗen sabida shi kanshi Bulama yana buƙatar kuɗin motar ki a halin yanzu, tunda dole ku siyar da komai naku ku biya banki kuɗaɗensu." "Ahmad nima hakan naso. Amman mama ta ɗaga hankalinta har hawan jininta ya tashi, dole yasa nima nayi maganar motar. Amman tunda hakane abar zancan motar, ita Mama zan bata haƙuri, Sagiru kuma in danƙashi da kaina, ƙila a shiga kotu, kaga in bamu samu wannan kuɗin ba, sai a rufeshi a gidan yari har zuwa sanda zamu biya wannan kuɗaɗen." Kai na girgiza nace. A'a Zubaina mota taki ce halak malak, ni na sai miki. Ki siyar, a rufa wannan asirin, muma in sha Allah zamu tsallake. Sannan akwai shawara da Ahmad ya bamu. Nan na zayyane mata shawarar da Ahmad ya kawo, game da maganar siyar da kadarori in biya banki kuɗinsu, ba sai sun yi mun terereba. Tayi na'am da zancan har da ƙarawa da godiya ga Ahmad. Tare muka shiga ciki dukka da kulolin abincin, a cike ɗakin yake da jama'a. A tsaitsaye aka gaggaisa, mu kai musu sallama muka fita. Bamu zarce ko'ina ba sai inda mu ka san zamu samu dillalai masu siyan gida, da masu siyan tsofaffin kaya. Dillalan dai take suka biyo mu suka zo aka zagaya dasu ko'ina suka gani, dan ance da zafi_zafi ake dukan ƙarfe. Million shidda su kaima gidan kuɗi, ya ƙara daraja har da million guda. Bani da zaɓi take na sallamar. Nan muka ɗunguma wajan mai anguwa dan shaidar, wanda zai sai gidan kuma yazo da lauyanshi. Nan akaita cike ciken takaddu. Ana gamawa suka bani kuɗina a Ghana most go, nan na fitar da dillalai, mai anguwa ma na bashi wani abun. Sannan muka wuce zuwa shagona, dan dillalan sunce suna da masu siye. Kayan dake shagon dai na million biyu ne, amman da ƙyar suka saye million ɗaya kuɗi ya zama million bakwai da ɗauriya. Haka mukaita jigila bamu muka samu kan mu ba, sai sha biyun dare., washe gari masu ganin motoci suka zo su ka ga motata data Yahanasu. Nera million huɗu suka siya, kuɗi ya tashi million goma da ɗauriya. A cikin kwana uku dai muka kammala komai, an siyar da komai na gidan iyakar suturune,da abinci kaɗai suka tsira, sai ƴan tarkacen kayan kitchen, su ma an siyar da wasu manyan, irin su gas kuka, firji, da su oven, rice kuka da dange_dangensu. Amman alhamdulillah kuɗin sun cika harda ɗoriyar dan harda su laptop ɗina guda biyu duk na ɗunguma na siyar. A cikin kwana na huɗu muka mayar ma da banki kuɗinsu, muka shiga shirye _shiryen tafiya Kuma. Zubaina cikin ƙanƙanin lokaci ta zuge ta fita hayyacinta, kuka kuwa tayi shi ba iyaka, ana gobe zamu tafi taje gida tanason kwana a gida dan tayi ban kwana da su mama" Yahanasu: Tun sanda na fahimci abunda ke faruwa hankali yayi matuƙar tashi. Hajara ce ta ƙara fashe mun baƙin abinda ke faruwa. Nayi kuka sosai, har zazzaɓi saida nayi na kwana biyu. Na sanar ma Ba Modu halin da ake ciki. Hankalinshi ya tashi ainun. Washe gari Ba Bakura ya kirani, yai ta mun nasiha akan sabuwar rayuwar da zamu tsinci kanmu. Na dinga roƙonshi ya taimaka ma Bulama Babba ko da da hanyar da zai samu aikine, amman sai ya ce mun. "Yahanasu ko da zaku rasa abinda zaku ci, bazan iya taimakama Bulama da gumina ba. Muddin in yana amsa sunan mijin Zubaina. Kuma wallahi babu wanda zai taimaka mishi, na kuma jama kowa kunne. In kun nutsa ki roƙeshi ki zo ki duba Baana jikin nashi yana ta tsananta, ko magana bayayi" A daren nayi shaye _shayen da ban taɓa yinshi ba. Dan ni kaɗai nake jin inata surutan dana kasa tantance, shin mafarki nake yi ne ko ido biyu. Rufin asirina ɗaya ranar Hajara basu kwana a gidan ba, a gidan ƙawarta ta kwana. Tausayin Bulama Babba nake ji sosai. Cikin ɗan lokaci ƙanƙani ya fice a hayyacinshi. Asibiti ma Ahmad ya kaishi ya ga likita, sabida baida lafiya, damuwa da zafin karayar arziki sun haɗu sun zame mai ciwo sosai." Zubaina: Abubbuwa duk sun kacame mun, tun daga ranar da Bulama ya rasa aikinshi kawo yanzu. Gashi da Mabaruka ta raka Hadiza wajan boka, ya shaida mata yana nemana. Dalilin da yasa naima Bulama dabara a kan mota kenan, duk abinda na faɗa mishi ƙarya ce zallanta. Ko da mu ka je wajan boka, ya shaida mun, duk aikin da nayi a tsohon gidanmu, sai an sake yin sabo, tunda mun siyar da gidan. Haka na narka mishi uban kuɗi ya haɗamun komai sabo, harda wasu muggan asiran, muka kamo hanya muka dawo. Hadiza kuwa a washe garin ranar da suka je wajan boka, mijinta ya kamo hanya yazo bikonta, bata kuma sati ba, ta tattara ta koma gidanta. Lallai na yarda da aikin wannan boka, dan yafi ƙarfin a kirashi da yankan wuƙa. Mama kuwa da taji labarin rasa aiki da Bulama yayi, da barin garin da zamu yi, hankalinta duk ya tashi, dan Bulama shine gatanmu, sauƙinta ma Asiya mijinta shima yana hidima dasu Mama yanzu, fiye da Bulama kasancewar shi hamshaƙin ɗan kasuwane. Yau a gida zan kwana, washe gari zamu wuce Kano, tare da rakiyar Goggo Rakiya. "Oh ni Jummai yanzu gobe uwar haka kuna baƙon waje, yanzu sai kunje zaku tsinci kayan ɗaki irin su gado katifa ko?" Kai na gyaɗa nace Sai munje tukunna zamu siya, ni ina da kuɗaɗena a ƙulle a marata. Ƙoƙarin da zanyi shine, duk wata zan dinga turo kuɗi ana mun gini kawai, da zaran an gama sai in zuba haya, ina karɓar kuɗaɗena ga wannan dubu ɗari biyun Mama a ƙara a gini, ko ya kika gani Mama shawarata ai tayi ko?" Hannu Mama tasa ta karɓi kuɗaɗen da na miƙa mata, sannan tace. "Ƙwarai da aniya kin koyi farar dabara, karki sake hidimar gidan ta dawo wuyanki, ita kanta baƙar kadarar ki barta taje tayi aikinta ni ina ganin zaifi. Kinsan dai bazata kaiki yawan albashi ba, sai ku dinga amfana da nata kuɗin, kafin shi Bulaman ya samu aiki, ai yasan manyan mutane komai na ƙasarnan hanya ne, aikin bazai zame mishi matsala ba. Amman naji muku zafi. Ita kuma waccan baƙar kadarar ki sake saka mata karen tsana, ki bata wahala ainun da ƙafafunta zata bar miki gidanki ku zauna daga ke sai ƴaƴanki." Mun jima munata saƙawa da warwarewa, daga bisani bacci ya ɗebeni. Da sassafe sai ga Goggo Rakiya ta iso da shirinta tsab na tafiya. Bamu wani ɓata lokacin ba, mu kai ma Mama da su Nafisa sallama, muka koma can gidan. Ƴan bargunan da muke kwana akwai, da labulaye da suka rage duk su Bulama sun zuzzuba a cikin buhu. Da ƴan kayayyakin kitchen irinsu tukunya, plate da dai sauransu duk an kintsa kayan waje guda. Ƙaramar mota muka ɗauka sharon har ƙofar gida ta kwashe mana kayanmu, mai gadi Bulama ya miƙama keyn gidan muka fice a gidan. Kuka na saka mai tsuma zuchiyar mai sauraro. Bulama kuwa kanshi na sama, ashe shima hawayen yake zubarwa. Yahanasu kuwa dama tunda muka shigo gidan take hawaye. Goggo Rakiya da Hajara ne su kaita rarrashina, Ahmad shi kuma ya riƙe hannayen Bulama yana mishi magana. Murmushi kawai yayi, tare da maido hankalinshi gareni, yaita rarrashina. Ba ƙaramin daɗi naji ba da naga ko kallon inda Yahanasu take baiyi ba, balle ya rarrasheta akan kukan da take faman yi. Yahanasu: Tun mankas ɗin dana yi jiya da daddare har yanzu bai sake ni ba, da ƙyar nake iya riƙe kaina. Naji tausayin kaina sosai, yanda naga Ahmad ne kawai ya damu da kukan da nake yi, amman wanda nake zamanshi, kuma ɗan uwana ko kallon inda nake baiyiba, ta matarshi kawai yake yi, da yaranshi. Allah sarki ni, ban taɓa tsanmanin rayuwa zata iya juya mun baya haka ba, banyi tunanin Bulama zai iya watsi dani haka ba. Inna tuno da nasihar Ba Modu da Ya Innana sai inji jikina ya kuma mutuwa. Kukana na tsagaitar na dinga ragargazo adda'a tunda muna hanyar tafiya ne. Zuchiyata tayi zurfi wajan roƙon Allah yai mun mafita. Awa huɗu mu kayi a hanya kafin muka isa Kano. Ahmad yace "Bari in kira Musa agent inji me sunan anguwar, direba ka tsaya tukunna." Direba ya nemi waje ya tsaya. Ahmad ya kara wayarshi a kunnenshi, jim kaɗan ya soma waya. "Gamu mun shigo Kano musa ageint inane unguwar take?" Dake a hands free ya saka wayar muna jiyo abinda Musa Ageint yace. "Ƴan lemo zaku zo, bayan layin mai kalwa primary school, sai mu haɗu a dai dai mai kalwa, ni kuma sai inyi muku jagora zuwa gidan. Ahmad yace. "To shikenan ba matsala" Mai mota ya koma kan titi, sai gamu a ƴan lemo, ta cikin kasuwar ƴan lemo muka shiga. Anata sauke lemo da mangoro a tirela, ga lemo nan buhu_buhu a jibge, ga masu kashin, lemo, gwanda, abarba, a ƙasa sunata cinikayya tsakaninsu da jama'a. Ni dai sai baza idanu nake yi. Wayata ce ta shiga kuka, ina dubawa naga Ba Bakura ke kirana, da sauri na ɗaga. Ba Bakura ina wuni?" Da sauri Bulama Babba ya dubeni muka haɗa idanu, idanun nashi kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewar bai da lafiya. Ba Bakura yace. "Uwata ya hanya, kun isa kanon ne?" E yanzu muka iso, ko gida bamu shiga ba ma, ya jikin Ba Baana?" "Alhamdulillah sai yanzu hankalina ya kwanta, dan inata kiran wayarki bata shiga. Mamanku Hajja Gana ma ta kiraki bata samu layin naki ba. Amman zan sanar mata kun isa lafiya. Jikin Baana sai godiya, India ma su Bulama ƙarami zasu fita dashi domun a dubashi da kyau. In kun isa gida Maman naku zata kira." Hawaye na share, mu kai sallama da Ba Bakura dai dai isowarmu mai kalwa primary school. Wani mutum ne a mashin yai mana jarora yana gaba, motarmu na biye dashi har muka tsaya a bakin wani madaidaicin gida marar fenti. Yawancin gidajen anguwar ma babu fenti. Anguwace mai cike da yamutsi da hargowa, anguwace mai cike da tulin yara, kasancewar anguwace ta masu ƙaramin ƙarfi. Firfitowa mu kayi, Wannan bawan Allah shi ya buɗe mana gidan muka shiga. Ɗakuna huɗu ne a cikin gidan falle falle, sai ban ɗaki da kitchen, da ƴar rijiya a gefe, sai famfo da akayi a wani ɗan waje kamar wajan wanke_wanke. Gidan yasha tails tun daga ƙasa har rabin bango, fari sol, ba ƙaramin haska gidan yayi ba, tsakar gidan bata da wani girma. "To kunga gidan, sai dai ku kama dukka fa, ku raba biyu biyu tunda ku biyu ne, ga yara maza da mata. Bulama Babba yace. "Ai babu damuwa Musa dama mu biyun zamu kama. Zubaina ku shiga daga ciki, ko wacce ta zaɓi nata ɗakin. Mu kuma bari muje mu zo. Fita su kayi dukkansu. Zubaina ta lalleƙa ɗakunan ta zaɓi ɗaya. Hajara ma ta ɗauƙi ɗaya, ni kuma na faɗa na kusa da Hajara, dama a tsaye nake a wajan. Gudan daya rage su zulai ne da yara suka shiga. Kayayyakinmu suka jibge mana a tsakar gida, suka fice. Hijabina na rataye a igiya na shiga aiki, kowacce ta ɗauki tulin buhun kayanta ta shigar ɗakinta, ina jiyo ihun kofur Zubaina, ƙanwarta Asiya ce ta shigo da abinci da drinks niƙi_niƙi. Labulaye na kafa, bayan na goge ƙasan tails ɗin ɗakin da tsumma da ruwa. Sai na shinfiɗa babban bargon da nake kwanciya a kai, na shinfiɗa dadduma wacce taci rabin ɗakin. Akwatunana na jera a gefe, kayan kitchen kuma na fita dasu, na jibge a kitchen Alwala na ɗaura tukunna, nayi salla, sannan muka gyara kitchen ni da Hajara, Zulai kuma ta wanke tsakar gidan tas. Zubaina suna ɗaki da jama'arta suna gyarawa, yara sai tsalle tsallensu suke yi a tsakar gidan, abunka da yaro ba hankali. Sai yamma lis na samu kaina, har zuwa lokacin su Bulama basu dawo ba, har yaran Hajara sun soma kukan yunwa, dan ina gani Zubaina ta kira yaranta cikin ɗaki, yaran Hajara da suka shiga ta korosu. Dab Magriba sai gasu sun shigo kici kici da katifu. Bulama: Ina shigowa da Yahanasu na soma haɗa idanu. Tausayina fal gurbin idanuwanta, jikina sai yayi sanyi, a hankali nace. "Yahanasu zo ga katifarki ki kai ɗaki" A sanyaye ta karɓi katifar ta shigar ɗakinta. Na miƙa mata take away ɗaya da ruwan gora. Na shiga da ɗayar katifar ɗakin dana ga Zubaina a tsaye a bakin ƙofar ta ƙume kamar zata dakeni, sai jijjiga jikinta take yi. Ahmad kuma ya shigar da katifar hannunshi ɗakin Hajara, tasu da suka tawo da'ita aka saka a ɗakin yara." Umman Maryam ya dai naga ranki a jagulene?" Cikin ɗan ɗaga murya tace. "Ba dole kaga raina a jagule ba. Naga sai wani kallon waccan yarinyar kake yi, ka duba sai da fa ka sallameta sannan ka shigo wajena fa. Wato kafi damuwa da'ita kenan fiye dani da ƴan yaranka da tun tuni suke damuna da tambayarka" Murmushi nayi tare da girgiza kai. Haba uwargida sarautar mata, waya isa yaja dake a birnin zuchiyata? Ai babu. Kawai dai dan naganta a tsakar gidanne, amman me zan kalla a jikin Yahanasu, yarinyar da a bayana nake goyata, har wanta na goya. Ayi haƙuri a sakko. Yaran fa?" "Suna ɗakin ƙarshe, sai kuka Maryam take yi mun, sai da na aika Zulai ta siyo musu chixi shine tayi shiru, Mama Rakiya kuma ƙamshi Asiya sun tafi gidanta." Ledar dana shigo dashi na buɗe, na ware abincin yaran dukka da ruwa nace. Gashi to a basu nasu suci ko?" Yamutse fuska tayi. "Ba daɗi nake ji ba, ɗan miƙa musu mana Abban Maryam, su Maryam a ƙoshe suke, sai dai su Anisa da Zulai" Ledar na ɗauka na fice. Yaran na ganina suka shiga tsalle. Maryam na ɗauka nace. Yaya? Zulai ga abincinkun kuci maza." Na miƙa mata ledar, na ɗan zauna inata sauraren shirmen yaran. Daga bisani na fito. Ahmad da Hajara na samu a zaune a tsakar gida sun shinfiɗa taburma, sai fifita suke yi. Sabida akwai zafi sosai. Mrs Bukhari ce gidan ƙamshi [28/07, 12:57 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 15 Zafine ya fito daku ko Ahmad? Yanzu na fito daga ɗakin yaran, akwai zafi gaskiya a Kano, Kaduna tafi daɗi. Kafin in rufe baki sai ga wutar nepa ta haske tsakar gidan tanwar, sai dai kash bamu da fanka." "Kai dai bari kawai, amman Lagos tafi Kano zafi ai. Munyi sabo da zaman tsakar gidanne dai." Miƙewa yayi, dan har an soma kiraye kirayen sallar Isha. Leƙawa nayi ɗakin Zubaina. Shinfiɗa take a katifa. Zamu je masallaci, sai mun dawo ko?" "To sai kun dawo." Tana faɗar hakan taci gaba da aikinta. Zunaina: Ina jin fitarsu, na saɓi hijabi har ƙasa na saka, tik nake daga ta ciki babu ko kanfai a jikina, na fito wuf, shigar Hajara ɗaki kenan. Kitchen na shiga na ɗauki wuƙa na fice da sauri. Sai karo nake ci da maza masu zuwa masallaci. Bayan windon ɗakin Yahanasu na tsaya, na shiga waige waige, ƙafa dai bata ɗauke ba, amman babu mutane ta wajan, kasancewar babu kofofin gidaje ta wajan, banga mutum ko ɗaya ya gibta ba. Tono na soma yi da sauri, gabana na faɗuwa, sai da na gama tono tsab na sa hannu na cire hijabina, ba kunya ba tsoron Allah, sai dai cike zuchiyata take da taraddadi layar da boka ya bani na tura a ciki, na miƙe tsaye da sauri na mayar da hijabina. Da ƙafa na tsure ƙasar wajan nasa ƙafa na dandaɓe wajan. Da sauri na zagayo na shiga cikin gida. Hajara na tarar a tsakar gida tana sallah, sai da nayi ras, dan banso kowa ya ganni ba. Wuceta nayi na shige ɗaki, na kunna gawayin kanti, na banka hayaƙin magani, ina jiyo Hajara na tari, na tabbatar Yahanasu itama ta shaƙa, dan sai da na saurara na jiyo tarinta. Sai nabi hayaƙin da turaren wuta, na feffesa turare. Na saka kwalli, na cusa wanda boka ya bani a gabana. Sannan na zuba na abinci. Saina fito da ƙatuwar daddumata tsakar gidan. "Yanzu nake shirin leƙawa ɗakinki ni naga hayaƙi sai fitowa yake yi. Sai tari muke yi, hayaƙin meye?" A zuchiyata nace. Kajimun mata da shegen tambayoyin tsiya. A fili kuma nace mata. Hayaƙin maganin saurone, ɗan kaɗanne ya saura shine na bunka, kafin mu tashi yin bacci sun mutu" Shinfiɗa daddumar nayi a gefen ɗakina na zauna. Hajara ta muskuto tace. "Wai ni Zubaina wannan Amaryar taki bata son jama'ane? Ni naga ta ƙunshe kanta a ɗaki duk wannan zafin. Kamar tana da wuyar sha'ani ko?" Baki na taɓe na dubi Hajara da take jiran me zance. Ƙila Bulama ne ya ɓata mata rai. Ai tunda karayar arzikinnan ya sameshi take fishi da kowa. Yanda kika san dan kuɗinshi aka aura mata shi. Amman da lafiya lau muke zaune, yanzu zamannan da kika ga nayi, kiranta zanyi muci abinci ma." Zama Hajara ta kuma gyarawa gulma na cin takashinta, tace. "Uhmmm ai da yake duk matan gidan nasu masu arziki, da rufin asiri suke aure. Ai yarta ƙawatace Fanda. Nifa nuna mun tayi bata san ma da zancan rashin aikin ba, balle wani karayar arziki. Makira sai ni nayi mata bayani. Nan ta dinga runtuma kuka. Dariyar mugunta na kwashe dashi, harda shewa nace. Hajara baki da dama. Kema kinsan yana aurenta, gata ƴar uwarshi, saita iya rigani sani ma, kindai san halin mazan. Bakii ji ɗazu tana waya da Baban Bulaman ba muna mota? Duk abinda ke faruwa a gidan ita ke kai musu gulma" Miƙewa nayi naje ƙofar ɗakin Yahanasu nayi sallama. Sai naji tana kusurkusur kamar mara gaskiya, labulen na bangaɗa. Muka haɗa idanu tana tattare wani abu da sauri a baƙar leda. Ƙur na zuba mata idanu, kai da gani kasan bata da gaskiya. Basarwa nayi nace. Ki fito da abincin naki waaje kici, kema kya sha iska, ga zafi ma a ɗakin. A daburce ta amsa mun da '"To" Na saki labulen na dawo na zauna shiru ina nazarin. To me yarinyarnan take yi haka? Da dukkan alamu wani asirin take ƙunshewa, daman nasan ba banza aka aura mata Bulama ba. Amman sun makara, dan na rigata tashi a bacci, da ita da Bulama duk a ƙarƙashin ikona suke. Fitowa tayi da ƴar daddumarta itama ta shinfiɗa a ƙofar ɗakinta ta zauna, sai janta da hira Hajara take yi, suna cin abinci har su Bulama suma suka shigo. Nan hira ta ɓalle a tsakaninmu, Yahanasu tana gefe tsulum da'ita, ta kasa sakewa, sai Ahmed ke ɗan janta da taɗi jifa jifa, sai dai tayi Murmushi kawai, ni kuma fsrfesun kazar dana baɗe da garin magani na miƙa mata. Hannu biyu tasa ta amshi kwanon. "Babu dai yawa, abun ɗaukani. Hajara ga naku ke da yara. Asiya ce ta kawo mun." Hajara tace. "Muna godiya, bari mu dangwali arziki muma." Yahanasu dai murmushi kawai tayi. Ta ci kazar ta sha romon, ta na dai gefe a takure. Daga baya ma tayi mana sallama ta shige ɗakinta. Muma kowa ya watse. Bayan Bulama ya fito daga wanka ne, muka lula duniyar ma'aurata,a ɗakin Yahanasu ya kamata ya kwana, amman sabida maganin da boka ya bani inyi amfani dashine, yasa na riƙeshi a wajena. Muka wayi gari a cikin wannan gida. Gabaki ɗaya daren jiya bacci ya ƙaurace mana sabida jarabar zafi ga sauro. Bayan sun dawo sallah Bulama ya dawo ya kwanta yana ta rawar ɗari, kafin kace mai, sai amai sai suma. Cikin kururuwa na fita tsakar gida ina faɗin A taimakamun Bulama ya mutu ya barni da marayu, na shiga uku na lalace" Gabaki ɗaya kowa ya fito. Bamu tsaya wata wata ba, Ahmad ya nemo mai ɗan sahu, ni dashi muka wuce asibitin Murtala, shine mafi kusa damu. Cikin gaggawa da taimakon ma'aikatan kiwon lafiya aka shiga dashi ɗakin jinya na maza. "Zubaina ki samu waje ki zauna. Bari in tsaya a kanshi, kiyi haƙuri" Ahmad ya shiga cikin ɗakin da aka shiga da Bulama. Ni kuma nai masauki a kujeraun dake ajjiye a dogon falon dake kallon ɗakin jinyar maza, ga jama'a nan tsiraru a zazzaune. Kaina na dafe, ni wannan bala'e _bala'en wallahi sun isheni. Dame mutum zaiji da talauci ko da abubbuwan da suke ta faruwa?" Yahanasu: Cirko_ cirko aka barmu a tsaye a ƙofar gida. Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, yanda naga an fitar da Bulama Babba ranga_ranga. Sai Hajara ce ta riƙo hannayena ta shigar dani cikin gida. "To amman ko babu komai ya kamata ace an tafi dake, tunda ba Zubaina bace kaɗai matarshi ba. Ke bafa a raga ma kishiya ko a ɗaga mata ƙafa. Sai kin tashi tsaye zaki ƙwato ƴancinki bawai ki zauna kishiya na juyaki ba, Zubaina ba daɗi bane da'ita mara mutunci ce wallahi. Bari kiga in kira Abban Anisa inji wanne asibitin suke, in yaso sai ki tafi musu da abun kari in an gama. Kema kya ganshi ki samu nutsuwa, ke inma gado aka bashi, kamata yayi in yau wannan ta kwana gobe wannan ta kwana." Ni dai sai kallon Hajara kawai nake yi yanda take tsara magana. Ita ta kammala kayan karyawa, tea da biredi da wainar ƙwai. Ta zuzzuba komai ta haɗa a basket, sannan ta kira Ahmad ya tabbatar mata suna asibitin Murtala. Ta sanar dashi gani nan zuwa, hankalina ya kasa kwanciya. Ina dai jinsu yanata mata kwatancen ɗakin, daga bisani su kai sallama. "Yahanasu kije ai kinji duk kwatancen da yayi, in kin kasa ganewa sai ki yi tambaya. Ga lambar Abban Anisa ki kwafe in kin kasa gane ɗakin sai ki kirashi. Ki kintsa maza. Tsintar kaina nayi da bin umarnin Hajara, duk da ni kaina a kan kin kaina inason ganin halin da Bulama Babba yake ciki. Ruwa naja a rijiya na shiga na watsa. Sabuwar shadda ta ɗinkin doguwar riga na saka, na ɗauko sabon mayafi da sabon takalmi na saka, banyi kwalliyar komai ba sai kwalli dana zizara a baƙin idona, dan hankalina sam baya ma tare dani. Ina fitowa Hajara ta shiga kambabani tanai mun kirakin Amare. Murmushin takaici nayi mata kawai, dan nasan babu wani abun a kalla a yaba a tattare dani, sai dai ince Alhamdulillah na gode Allah da ya bani rai da lafiya kuma ya yi ni musulma, mahaddaciyar littafi mai tsarki. Ta bani basket ɗin abincin, sallama nai musu na fice. Da tambaya na hau ɗan sahun da zai sadani da asibitin Murtala, bamu da wani nisa ma. Bansha wuya ba wajan gane ɗakin da Bulama yake kwance. Da siririyar sallama na shiga ɗakin jinyar. A hankali na soma gaishe da marasa lafiya, har izuwa gadon da Bulama Babba yake kwance, idanuwanshi suna kallona. Wata uwar harara Zubaina ta sakarmun tare da jan dogon tsaki, ta kawar da kanta gefe can. Leɓe na cije dan naji zafin tsakin da tayi mun, na tsani tsaki sosai. Nan da nan Bulama Babba ya kawar da kallonshi a kaina. Ahmad ya karɓi basket ɗin hannuna, tare da miƙewa a kujerar da yake, ya nuna mun da hannu. "Zo zauna nan Yahanasu ashe zaki gane ɗakin?" Kai na ɗaga mishi halamar E, bayan na zauna nace. Bulama Babba ya jikin naka?" Can ƙasan maƙoshi ya amsa mun da cewa. "Da sauƙi, ai da baki zo ba, dan bana buƙatarki, wa kika barma yaran kuma da kika kwaso jiki kika zo?" Hawaye cike da gurbin idanuna na miƙe tsaye. Kayi haƙuri Bulama Babba, dama abincine na kawo muku gashinan, Allah Ubangiji ya baka lafiya yasa kaffarane?" Da sauri na fice bana ko iya ganin gabana. Har na kusa da get na jiyo muryar Ahmad yana kirana, ban juyaba naja tunga na tsaya. Gabana ya iso ya ƙuramun idanu. "Yahanasu na fahimci babu zaman jituwa a tsakaninki da Bulama,da ita kanta Zubaina, duk da nasan dama Zubaina ba lalle bane ta bada haɗin kai a zauna lafiya ba. Bama ita kaɗaiba, mata bakwa son kishiya sam.Ɗan murmushi yayi dan ya ƙarfafani, kafin ya ɗaura da cewar. "Na lura da hakan Tun ranar da nazo gidanku. Amman ni da shi ba mu zauna mun tattauna akan hakan ba, duba da irin jarabawar data afka muku. Amman ina mai baki haƙuri a matsayina na wanki, da kici gaba da adda'ar Allah ya karkato hankalin mijinki kema izuwa gareki. Akwai wasu addu'o'i da zan baki,muddin kika lizimci yinsu da ikon Allah zaki zama mai soyuwa a zuchiyar mijinki, duk da na san ke ɗin malama ce, ta yiwu kinsan addu'o'i n a kansu kike, ta yiwu baki sani ba. Ni tun lokacin da Bulama ya Auri Zubaina abokarmu ta samu tangarɗa, kullum a cikin raba hali muke. Shaƙuwa ce ke zaune damu kawai, amman da tuni na yar da Bulama, tunda duk abinda zan bashi na shawara, baya ɗauka, sai shawarar da Zubaina ta bashi. Ko da wannan abun ya faru sai da na tambayeshi ya sanar da su Ba Bakura halin da ake ciki. Cemun yayi baya so kowa ya sani, shi a wautarshi fishi yake dasu bisa ƙin iyalinshi da suke yi, da kuma aura miki shi da akayi. Inna samu nutsuwa zanje har Damaturun wajan Ba Bakura in bashi haƙuri. Amman zan tambayeki dan Allah kar kiji kunya da nauyin bani amsa kinji ko?" Kai na kyaɗa mishi, dan in nace zan buɗe baki nayi magana kuka ne zai ci ƙarfina. "Mu'amalar aure ta taɓa shiga tsakaninku, tunda aka kawoki?" Naji ya jeho mun wannan tambayar ta dira a zuchiyata tayi daram. Kaina ya shiga jujjuya tambayar, tare da juya maganganun Ba Modu da Ya Innana. Hawaye masu ɗumi suka gangaro mun, a cikin muryar kuka nace dashi. Wannan yana ɗaya daga cikin sirrin da labule da ƙyaure suka rufeshi, babu mahalukin da zai iya sani in yaye wannan labulen, nagode da kulawarka gareni. Bulama Babba ɗan uwanane, ko babu aure shi mai juya akalar rayuwata ne yadda yaso, hadda iyayenmu sai dai su kallemu da idanu kawai. Juyawa nayi na barshi a wajan, wannan rayuwar Allah ne kaɗai zai iya fiddani ba dai mutum ba, duk halin da na tsinci kaina yanzu, ko a gaba, muƙaddarine daga Allah, zan nuna ma iyayena na haifu, kuma ni mai biyayya ce, burina faranta ransu, ko da ni zan faɗa ƙunci. Adaidaita sahu na tare na koma gida, da ƙyar nake tafiya, ciwon kai da wani zazzaɓi_zazzaɓi nake ji. Assalamu alaikum mutan gidannan. Cikin dauriya nayi maganar tare da aro Murmushi na yafa a fuskata. Hajara tana tsakar gida tanai ma yara wanka, Zulai kuma tana shafa musu mai, tare da sama musu kaya. Da sauri Hajara ta yar da soson dake hannunta ta nufo ni. "Me zan gani ɗuwawu ya mutu ya bar zani, wai har kin dawo, to akan me, ya zaki bar kishiya da jinyar miji? Salesalin Bulama ya ga kamar ita kaɗai ta damu dashi." Zulai na kalla, da yara da suka zuba mana idanu, sai na yi ɗan tsaki nace. Bulama Babba ɗan uwanane Hajara, babu wacce zata fini sonshi, asalima a cinyarshi da bayanshi nayi yarintata ki san wannan. Dan Allah ki dena mun shishshigi a cikin lamurana. A zafafe na idasa maganata dan na lura ƙungurmar munafuka ce. Ɗakina na buɗe na shiga, na bar Hajara sororo da sakakken baki a wajan. Zama nayi a bakin katifata, tunani ya aureni, ɓacin rai ya ziyarceni. Tunowa nayi da baya, a lokacin ina ƴar gaban goshin Bulama Babba wata ranar Litilin da yamma lis, a lokacin ina haɗa digree na. Ina shigowa cikin gidanmu, naci karo da Fanna a ƙofar ɗakinmu tana gwada wani tsararren farin takalmi, Ya Innana tana zaune akan kujera tana ta yabawa. Ga su Ya Bagulaji a zazzaune. Sannunku da gida Ya Bagulaji" Na faɗa ina dafa Fanna kamar jira take tace mun. "Bulama Babba ya dawo ɗazu, shine ma ya kawo mun wannan takalmin tsaraba, ya kawo ma su Yabulu Jakunkuna. Ban jira ta gama faɗar abinda take faɗa ba, na zari ƙafafuwana da mugun sauri nayi ɓangaren su Ba Bakura. Ina jiyo Ya Innana na ƙirana banko bi ta kanta ba. Ba Bakura na samu a zaune yana karatun littafin hadisi a babban falo, yana ganina yayi murmushin manya yace. "Uwata an biyo Bulama Babba karɓar tsarabar ko? Ki shiga ciki, yanzu su Wakil ma suka fice" Kaina na sunne na wuce ɗakin Bulama Babba da sallamata a bakina. Yana kwance a kan katifarshi yana waya hankali a kwance. Sanye yake da baƙar jallabiya mai tsantsi. Ina mamakin yanda Bulama Babba yake son baƙaƙen kaya, irin asalin baƙaƙen kanuri ne shi, mai jajayen idanuwa, da baƙin baki, haƙoranshi ne kawai farare tar sai kuma ya ɗauko baƙaƙen kaya ya ƙara. Kallona yayi, yai mun Murmushi tare da yi mun nuni da in zauna a ƙasa da hannunshi. Da dukkan halama da matarshi yake waya, dan sai wani rage ƙatuwar muryarshi yake yi. Ina zaune duk na ƙosa ya gama wayar tashi, ai kuwa ya jima suna wayarsu kafin suyi sallama. "Yahanasun Bulama Babba mummunar gidanmu ƴar lukuta kece kika sake zama ɓakutu haka, kinga yanda kika yi ƙiba kuwa? Tashi tsaye in ganki mummunar gidanmu" Dariya muka yi duka, in da sabo na saba da wannan sunan, ada sanda nake ƙarama da zaran ya kirani da wannan sunan sai kuka, sai burgima. Amman dana girma kuma daya kira sunan sai ya bani dariya. Tashi tsaye nayi bisa umarninshi nace dashi. Ai na fika kyau duk munin nawa, kuma mace a ganta a cike ai shine dai _dai" Hararata yayi yace. "Ah ba wani dai _dai, da kinyi aure zaki tsofe da wuri. Maganar kin fini kyau kuma, dama ni bansa a ka ba, ina ruwan namiji da kyau? Kyau ai na mata ne Kiga fa matata wanke hannu ka taɓa gata kamar tsada" Dariya na kwashe dashi, shima dariyar yake yi. Ai ni naga ƙoƙarinta data amince harta aurenka fara sol da'ita kai kuma baƙi" "Oh kenan in ke nace inaso ashe ma baza ki aure ni ba ko? Ai gwanda da kika faɗamun" Sai ya haɗe ranshi tamau kamar ba Bulaman dana sani ba, mai raha da barkwanci ba. Wata ƙaramar jaka ya miƙomin. "Ga tsarabarki, tashi ki fice mun da gani, mummuna mai ƙaton hanci kawai" Haƙuri naso bashi amman yaƙi fur. Sai naji duk nabi na damu da ɗaure fuskar da yayi, na kuma ji kunyar abinda na faɗa mishi. A sanyaye na miƙe har na kai bakin ƙofa ya kira sunana" "Mummunar gidanmu" Da sauri na juyo sai naga yana mun dariya. Ashe zaulayata yake yi. Nima sai nayi dariya nasa kai na fita, wannan Kenan" Ƙaran da wayata take yi ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana shiga. Ba Modu ke kiran wayata, gabana ya tsinke ya faɗi, a ɗarare na ɗaga. Jin muryarshi wani iri yasa jikina ya shiga rawa. "Yahanasu ki nemi izinin mijinki ki tawo Damaturu Allah yayi ma Babanku Baana rasuwa. Za'ayi jana'izarsa ƙarfe biyun rana, sai ki sanar ma Bulaman" Kuka na fashe dashi, tare da salati, wayarce ta sulale a hannuna ta faɗi ƙasa, kai na haɗa da guiwa naita kuka. Hajara a guje ta shigo ɗakina, tambayar duniya babu wacce ba tai mun ba, amman na kasa magana ma, gabaki ɗaya na fita hayyacina. A wannan halin da nake muka jiyo sallamar su Bulama Babba. Wayata kuwa ƴan uwane suke ta kirani, na kasa ɗagawa, dan hankalinane zai kuma tashi. Ji nake kamar in rufe idanu in buɗe in ganni a Damaturu. "Hajara kukan wa nake ji a ɗakin kamar na Yahanasu?" Ahmad ne yayi magana a tsakar gida. Hajara tayi wuf ta fita tsakar gidan. "Yauwa Abban Anisa, wallahi yahanasu ce take ta faman kuka, na tambayeta taƙi yin magana ma, gashi naga sai kiran wayarta akeyi." Ahmad da kanshi yayo tattaki har ƙofar ɗakina daga wajan yace. "Yahanasu lafiya, wani abunne ya faru, ko kuwa akwai abinda kike so ne?" Daurewa nayi nace. "Allah yayi ma Ba Baana rasuwa, yanzu Ba Modu ya kirani. Gida nake son naje dan girman Allah" Salati shima ya shiga yi, tare da yima Allah kirari. "Allah ya jiƙan Ba Baana. Ki shirya kayanki tsab, bari inyi magana da Bulaman tunda naga jikin nashi da dama, sai mu ɗunguma mu tafi" Bulama: Ina shigowa gidan sautin kukan Yahanasu ya kaɗama kunnuwana ƙararrawa, banbi ko ta shirginta ba, balle inji me ye musabbanin kukan. Ɗaki na shiga, Zubaina na biye dani a baya, a bakin katifa na zauna, jikina ba ƙarfi ga damuwowi da suka haɗu suka damu zuchiyata, babu cikakkiyar nutsuwa da hankali atare dani, tunanin kanshi wani irin barkate nake yi. Babban abinda yafi ɗagamun hankalina shine, ta ina zan soma neman aiki ma? Yanda ƙasarnan tamu ta zama sai adda'a. Aiki sai ka siya, in kuwa baka da kuɗi sai dai ka zuba ido kawai. Ga karatun yara, ga kuɗin haya, ga abincin da zamu ci. Damma sauƙinta muna da dukkan kayan abinci wadatacce wanda a ƙalla zai iya kaiwa wata huɗu bai ƙare ba. Ina cikin wannan halin Zubaina tace. "Ina da babban albishir da nake son sanar maka, amman sai fa ka bani goron albishir tukunna." Murmushi nayi mata. Me kike so in baki a matsayin goron albishir to?" Matsowa dab dani tayi tace "So nake ayi gagarumin bikin suna in na haihu, shine goron albishir ɗin nawa, ciki ne dani" riƙe mata hannu nayi gam na ɗan matsa. Naji daɗin labarin sosai, dan ina da son yara, amman kuma bani da nutsuwar wani murna ko dariya" Allah ya raya mana cikin, ya kuma sauke ki lafiya, naji daɗi sosai. Bikin suna kuma za'ayi yadda kike buƙata in sha Allah, cikin wata nawa ne? Gashi yazo a watan rashin aiki." Dariya tayi tace. Kar ma ka damu aiki ai zaka samu ne, kuma nima gobe ko jibi zan koma aiki inda akai mun transpa." Muna cikin haka muka jiyo sallamar Ahmad, a gajiye na amsa mishi, na miƙe da ƙyar. Ina riƙe da labule nace. Ya akayi Ahmad? Kallona yayi da kyau yace. "Baka jiyo kukan Yahanasu ne Bulama?" Ina ji, to dame zanji Ahmad ka dubi halin da nake ciki, in ba'a rarrasheni ba, ai ba za'a sani rarrashi ba. Ai ko bana auren Yahanasu ƙanwata ce kuma zan iya bata umarnin abinda nake so, ko da kuwa a ƙarƙashin inuwar auren wani namijin take ba ni ba" Kafaɗata ya dafa, ya sassauta muryarshi raɗa_raɗa. "Haba Bulama mai da wuƙar, bai dace ka dinga kwaye ƴar uwarka a gaban kishiyarta ba. Kukanta mai daliline, daga gida aka kirata anyi rasuwa" Dim naji gabana ya harba. Kalmar innalillahiwainnailaihilrajiun na shiga nanatawa. Zubaina ta fito fut da taji ina ambaton Allah. "Ahmad lafiya wani abunne ya samu Yahanasun?" "A'a rasuwa akayi acan family House Ba Baana Allah yayi mishi cikawa, sai ku shirya mu kama hanya. In yaso Hajara da Zulai sai su kula da gidan" Carab Zubaina tace. "A'a inaga ku ɗin ku soma gaba, kafin sadakar bakwai zan zo, yin tafiyarnan zai iya bani gagarumar matsala a office, dan yau ya kamata inje aiki, sai muka wayi gari da wannan ciwo na Bulama, Allah ya jiƙan musulmi" Da sauri nace. Bari in haɗo kayana mu tafi Ahmad. Zubaina ki zauna ki kula da aikin ki tunda a halin yanzu aikin ki shi kaɗai muke dashi. Ahmad ya wuce ɗakinshi, nima na koma ɗaki na haɗa kaya kala huɗu a jaka, duk da bana jin son zuwa gidan ma, su Ba Bakura ne bana son mu haɗu, sabida nasan ba zamu kwashe da daɗi ba, bansan ma ko zasu marabci zuwan nawa ba ma. Doguwar riga kabtan na saka na shadda shole, brown na saka hulata zanna wacce tayi dai dai da kayana, haka takalmina. Humrar kaya na bi kayana dashi, banda ta jiki dana shafe jikina duka dashi. Dubu ashirin na zaro na miƙa ma Zubaina da take tsaye, na shafi cikinta. Ki kula mun da Baby na, ki dinga cin abinci. Dana dawo zamu duba makarantar data dace mu saka yaran, sai kuma mu shiga neman aikin yi" Sallama mu ka yi, na fito tsakar gidan. Yahanasu tana sanye da kaya da shiga irinta al'adarmu, tasha naɗin baƙar lifaya, ga ɗan akwatinta a hannunta. Sai yau na lura da wata muguwar rama da Yahanasu tayi. Duk wannan ƙibar tata ta zabge, sai ɗan haske kaɗan data ƙara. Gaba muka wuce ta bi bayanmu. Muna fita muka nufi tashar anguwa uku, anan muka samu motar Yobe muka shiga, munfi awa uku a tasha, amman har zuwa lokacin da sauran mutane biyu motar bata cika ba. Har muka yi sallar azahar, masa da balangu na siyo mana. Ta wundo na leƙo zan miƙa ma Yahanasu, sai naga ta zuba magani a bakinta ta kora da ruwa. Muna haɗa idanu nayi sauri na kawar da dubana a kanta, dan in muka haɗa idanu sai inji tamkar zan kurma ihu. Ledar naman da yogurt na ajjiye mata a kan cinyarta, mu kuma muka samu banci muka zauna ni da Ahmad. Ƙarfe biyu motar mu ta ɗauki hanyar Yobe. Tafiya yankin azaba, zamu isa, ba zamu isa ba haka mu kaita kwasar hanya, ni dai nayi shiru, kaina na jingine a jikin kujera na lumshe idanuna. Abubbuwa da yawan gaske ne su kai ta faɗomun a raina, tunane tunane kala kala. Bamu muka isa Damaturu ba, sai wajajen ƙarfe takwas na dare, motarmu ta samu matsala a hanya, munfi awa guda a yashe a gefen titi ana gyaran matar. Matan gidan suna ganinmu suka shiga murnar ga Yahanasu ga Yahanasu, duk da mutuwa a kayi a gidan, amman sun nuna jin daɗin su da ganin nata. Amman abun mamaki ba wanda yabi ta kaina. Mrs Bukhari ce *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. [28/07, 12:57 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 16 *MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!* Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online Gakayanmu kamarhaka Tafi budurwa duniyane Tsumin lahaula Gombar bujenki jagab Shu Umar zumarmu Mumuna da,aeki Makalemata Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara Dahuwar kaza cicibin kala kala Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari. Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma AMARYA MAI JEGO WACCE ZATAYI KOME Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji. Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure. Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo. YAHANASU: Da Ya Innana mu ka haɗa idanu, sai naga tayi turus tana kallona kawai. Na taka ƙafata kenan zan iso inda take, muka jiyo muryar Ba Bakura yana faɗin. "Wa nake gani a cikin gidannan kamar Bulama? Lallai wuyanka ya isa yanka, tun wuri kuma tun kana iya shaida kowa, ƙafarka a likkafa ka fice mana a gida, tunda ba da kuɗinka aka haɗa aka gina gidan ba. Wallahi ka fita ko in sa yara su fitarmun da kai a wuya. Ahmad ka jashi ku fice mun da gani, ke Yahanasu shiga ɗakin gyatumarki." Ƙafafuna in banda rawa babu abinda suke yi. Hajja gana wacce ta fito tana zubar da ruwan hawaye tace. "Amman daka bari ya shiga ciki yayi musu ta'aziyya tukunna kafin ya fice. In ya fice ma ina kake son yaje a darennan? Dan Allah ina nema mishi afuwa, ayi haƙuri kuma naji kace ita Yahanasu ta shiga ɗakin mahaifiyarta" A zafafe Ba Bakura ya dubeta. "Ina matuƙar ganin girmanki Hajja Gana amman wallahi da sai kinyi nadamar nema mishi wannan afuwar da kika yi. In har kinga na yafe ma Bulama to wallahi sai ya rabu da shaiɗaniyar matarshi tukunna, muddin suna tare babu ni babu shi" Mama Gana tace. "Ka yi dai dai Bakura. Ai kaga ita ishasshiyar ba tai gigin zuwa ba, ai kuwa data kuskure tazo da nayi rawar ƴan bori da'ita. Ahmad ka ja abokin ka ku fice, nan gidan mu ne muna da damar mu kori duk wanda mu ke so. Ke ko Hajja Gana baki ma kyauta ba. Ai kaza tana take ɗanta ne ba dan ƙi ba" Bulama Babba yayi sororo a tsaye yana bin kowa da kallo, an rasa wanda zai ba Ba Bakura haƙuri. Hajja gana kuwa sai sharar hawaye take yi. Ba Modu yace. "Ahmad ku fice umarni ake baku fa. Ita kanta Yahanasun ta fice tabi mijinta su koma. Ta'aziyya ku ka zo mana mun gode, kun san bama yin ma zaman makoki a gidannan" Mama Gana tayi maza ta kama hannuna ta shigar dani ɗakinmu, tana hararar Ba Modu. "Zauna anan, babu inda zaki daga zuwanki har sai anyi bakwai. Wannan irin muguwar rama kamar wacce ta haɗiyi allura fa?" Hawaye na shiga shatatarwa, ita kanta Mama Gana hawayen take fitarwa na tausayina. Haka Ahmad yaja hannun Bulama Babba suka fita jiki ba laka, kowa ya watse a tsakar gidan. Duk yanda Ya Innana ta kai da kawaici sai data tambayeni meke damuna, bayan na dawo daga cikin gidan, na bi kowa nayi mishi ta'aziyya. Ba komai, na dai ɗan yi ciwo ne kwanaki" "Hmmm Yahanasu baza dai ki faɗa ba. Kinga yanda kika zuge kuwa, Fanda fa ta fiki kumari sosai yanzu. Ki sanar dani matsalarki, ko dai ciki ne da ke?" Murmushi nayi, ga hawaye na zubowa a idanuna. Nace. Rashin kwanciyar hankali ne kawai, bani da ko da matsayin ƴar uwa a idanun Bulama Babba. Ni na ɗauka ko da aure nayi a wani gidan, na shiga damuwa, Bulama Babba me iya tsaya munne ba sai kun shiga ba. Amman kash sai gashi shine ya sani a garari" kukane ya ci ƙarfina, sai rairawa nake yi. Ya Innana kuma ta tusani a gaba sai Ajjiyar zuchiya take saukewa, da dukkan halamu yanayin da nake ciki yana gasa ranta. "Tun farko kuskurene yasa aka haɗa wannan auren. Gashi zumuncin da ba'aso ya taɓun ya taɓu, tunda dole Hajja Gana ranta ya sosu dake, sabida duk sanadin aurenki ne wannan abun suka faru har BaKura yace bashi ba Bulama Babba, Ita uwace, ko da ta ɓoye haushinki a zuchiyarta bazai taɓa goguwa ba. Tana ji tana gani an korar mata yaro. Kuma sabida shi duk tabi ta rame, kullum a cikin tunaninshi take. Ni dai abinda zance dake shine ki dage da adda'a baccin dare ba naki bane. In kika riƙe Allah da karatun Alqur'ani mai girma, da izinin Allah matsalar gidanki sannu a hankali zata kau. Muna cikin tattaunawa Ba Modu ya shigo ya zauna a bakin kujera. Ƙur ya zuba mun idanunshi. "Uwata kiyi haƙuri da ƙaddara, kiyi biyayya, zaki samu riba. Abinda nake so dake shine, ki shirya ki bi mijinki, nasan bazai wuce gidansu Ahmad ba. Wakil yana jiranki a waje." Da sauri na ɗago kaina na dubi Ya Innana, halamar ina neman agajinta a taimaka a barni in samu salama, carab kuwa tace "Amman Modu ba zaka bar yarinyar nan mu kwana ba, in yaso gobe a kaita can gidan su kama hanya su koma ba?" Murmushi yayi. "Ai tunda har Bulama bashi da waje a gidannan to ya zame mata dole itama ta bi mijinta, hakan shine kara. Innana kiyi haƙuri, itama uwata tayi haƙuri, irin haƙurin da Hajja gana tayi. Ku baku ji furucinta ba? Nifa duk abunda zai kawo kwaɓewar zumunci ba sonshi nake yi ba." Ina kuka na miƙe tare da zaran akwatina. Hannu yasa a aljihu ya ciro kuɗi ya damƙa mun ba tare daya ƙirga ba. Ya Innana tace. "Ina zuwa ki jirani kaɗan" fita tayi a ɗakin harta dawo ina share hawayena, ga wata iriyar yunwa dake sakutar cikina. Wata leda ta miƙa mun, na karɓa. Har bakin mota Ba Modu ya rakani, sai da ya ga tashin motarmu sannan ya koma. "Yahanasu kinga abunda aurenku ya ja a family ko? Yayyun Hajja Gana sai surutai suke yi, akan wai bai dace ba abinda akaima Bulama Babba ba. Naga yayyenta maza ma sun fita, kamar Bulama Babban suka bi. Zumunci na shirin samun tangarɗa, ni dama baku zo ba. Danna tabbatar wannan ramar taki sai ta kwantar da Ya Innana jinya. Kullum a cikin maganarki take." Cewar Wakil Ai Wakil nayi ɗan daka ce ban zo ba. Ka duba a barni in keɓe da mahaifiyata da ƴan uwana in ɗan ji sanyi amman abu yaci tura. Naso har gidan su Yabulu da Fanna duk in leƙa in gano" "Ai Fanna tana nan a cikin gidan, hankalinki ba'a kwance yake ba shi yasa baki ganta ba, tana bayanki. Tazo gidan ai tun sanda jikin Ba Baana yayi tsamari, dama tana fama da laulayi, uwar mijinta ce ma ta kawota, satin ta biyu." Murmushin farin ciki nayi, tare da sake jin tausayin kaina. Gidansu Ahmad bayan layinmu ne, muna shan kwanar layin, muka hango Ba Bature wan Hajja Gana tsaye a ƙofar gidansu Ahmad suna tattaunawa da Bulama. "Fita kije Yahanasu ni bazan ƙarasaba naga sun ɗauki abun da zafi. Ni wallahi Bulama Babba tausayi yake bani, ko sunanshi Ba Bakura ya kafa dokar kar ya kuskura yaji an ambata. Ni dai jikina yayi murus, kafin in fito sai ga Hajja gana ta wuce ita da ƙanwarta Hewa. A sanyaye na bi bayansu, Wakil kuma yana cikin mota bai tafi ba. A sanyaye na isa wajan, ina gaishesu. Hajja gana ce kaɗai ta amsa mun gaisuwata, tare da riƙemun hannuna. "Me kuma kika zo kiyi anan? Nan ɗinma kin biyoni ne dan ki sake rabani dasu? Gidan da nayi rayuwa a ciki, nayi guje gujena tun kafin a haifi kowa, yau shine akaimun korar kare, duk akanki kuma. "Kai ɗannan kar ka ɗaurama ƴata laifi, wanne irin cin kashi da cin mutuncine mu baka yi mana ba. Duk wannan jarabawar data sameka ai bazai wuce akan fishin da mahaifinka yake yi a kan ka bane. In banda uwa bata iya haifar yaro ta tsame hannunta a kanshi, wallahi da ko kallonka ba zan kuma yi ba. Mara mutumci wanda baisan ciwon kanshi ba. Ba Bature yace. "Ya isa Hajja Gana duk tashin tashina bai taso ba. Ni dai zan haɗashi da Alhaji sambo, ma'aikacin gidan yarin dake Kano. Ya nema mishi aikin gandiroba in bai raina ba, ya samu ya riƙe iyalinshi, kafin Allah ya ɓullo mishi da wani aikin, aikin ne a ƙasarnan yayi wuya. Tunda Alh Sambo ne, babu wani atisaye da zaka yi, ɗaukar ka kawai zaiyi, shima Ahmad ɗin in yana so ku je ku yi tare. Ni iyakar taimakona kenan, mahaifinka kuma kayi ƙoƙari ya yafe maka, in dai kana son rayuwarka tayi albarka. Mahaifiyarka ko itama ta huta, kai baka ga yanda ta rame ba? Ke kuma Yahanasu kiyi haƙuri Bulama wanki ne, kici gaba da yi mishi biyayya. Modu ne ya koroki ko?" Kai na gyaɗa mishi. "Na san Modu da kara da kawaici daga shi har Innana. Ahmad in zai je wajan Alh Sambon, sai ku tafi tare kaima ka kai mishi takaddun naka. Gobe ku kama hanya kawai ku koma, amman ku dinga ƙoƙarin kiran gida da dangi" Nan sukai ta mana nasiha, daga ƙarshe mu kai sallama muka shiga cikin gidan su Ahmad. Ranar daga ni har Bulama Babba babu wanda yayi cikakken bacci, sallah ya dinga yi, yana rera karatun Qur'ani. Nima alwala na ɗauro bayan na yi gamje gamjen magunguna. Washe gari haka dole muka sake nuƙo hanya. Bayan mun koma da sati guda Ahmad da Bulama suka soma zuwa aiki a babban gidan yarin kurmawa dake bayan gidan sarki, a matsayin ƙananun ma'aikata masu matsayin ( correctional assistant CA 1 na Ahmad kenan) na Bulama Babba kuma ( Correctional assistant CA2) Kofur itama ta kama aiki ka'in da na'in. Ni ma nan na bazama neman aiki, cikin yardar Ubangiji na samu, a gidan talabijin na tauraron ɗan Adam, akan lamba ta 127 gidan Tv mai suna Nagarta. Inda na riƙe ɓangaren mu tattauna, shirin dake zaƙulo matan dake cikin gida, dan jin tarihin rayuwarsu da irin gwagwarmayar su. Tuƙuru na mai da hankali akan aikina. Aikin gida kuwa babu wanda aka ɗauke mun, nike yin komai na gidan, hatta shirya su Maryam su tafi makaranta ni ke yi, sabida Zubaina tana fama da lalurar ciki. Hajara ma ta samu aikin shara a cikin makarantar su Maryam (AL FURƘAN) dake saman ƴan lemo, ita ke tafiya da yaran, tare suke dawowa kuma. Matsalolin gidan Bulama Babba babu sauƙi sai ƙaruwa, sabida ita kanta Zubaina a halin yanzu kullum a cikin rashin jituwa da Bulama Babba take. Sabida yanda rayuwa ta juya mishi, albashin nashi ba wani yawa, ita kuma bata taimakawa da komai a cikin gidan, da an taɓata tace gini take yi. Ni kuma albashina kusan duka a hidimar gidan data yara yake ƙarewa. Shaye _shayen muyagun ƙwayoyi kuwa, sun zamemun tamkar sallah biyar a rayuwa, dan bana ɗaga ƙafa ko sau ɗaya. A halin yanzu sai na yi haɗe haɗe sosai kaina ke iya ɗaukar caji, amman bana wasa da ibada, ban gajiya wajan kai kukana ga Ubangiji ba. Wata ranar alhamis da misalin ƙarfe huɗu. Ina zaune a dokin ƙofata ina yanka alayyawo. Muna ɗan taɓa hirarmu da Hajara, wacce take tsintar shinkafa. Itama girkin take yi, a gawayi yanzu muke girki, shima duk wata ni ke siya, na ɗauke ma Bulama Babba wannan nauyin. Banda kifi da nama da nake siya in saka a miya. A hakan na sai ma kaina gado, da wadrope. Duk da wannan siyan kaya da nayi ya haddasa gagarumin tashin hankali a tsakanin Bulama Babba da Zubaina. Dan a gaba ta tusashi kamar ɗanta ta dinga zazzaga mishi kwandon jaraba. Shi kuma sai faman rantse rantse yake yi mata kan shi ba shi ya siya mun ba. Bata barshi ba, har sai da yace mata kafin ta haihu zai siya mata sannan ta barshi ya sha ruwa. Bulama dai ya rage hantarata, tunda mu kan ɗan taɓa hira, misali ya tambayeni, Zubaina ta dawo, ko kuma ya tambayeni ya yaran? Shikenan abunda ke shiga tsakanina dashi, mu'amular aure kuwa, sai dai in jiyo yana yi da Zubaina, ni na zama fanko. Babu abunda ya kai haka ciwo, waɗanda suka ɗan ɗana irin wannan yanayin ne ka ɗai zasu fahimci halin da nake ciki, kullum ɗaukar kaina nake tamkar ba mace ba, tamkar mai wata nakasa a jiki. Har nakan tambayi kaina, ko dai haka mumana suke gudanar da rayuwarsu a gidan mijine? Ni dai nasan ba mai kyau bace, kuma bana kai kaina inda Allah bai kaini ba. Bulama Babba ne ya shigo da kayanshi na gandiroba, hannunshi biyu kici kici da cefane, anyi musu biya kenan, dan sanda zai fita nera ɗari uku ya bayar kuɗin abincin safe. Nan Zubaina yana fita ta aiki Zulai ta siyo musu kayan tea, da Indommie da ƙwai ta dafa, suka ci da yaranta. Da naje wajan aiki shine na ari dubu ɗaya a wajan abokiyar zamana a wajan aiki, shine nayo cefanen miyar kabewa, zan dafa buski. Da sauri na miƙe na karɓeshi, ina mishi sannu da zuwa. Abun mamakin shine yanda naga yana ta Murmushi, har yana tambayata ya gida ya aiki. A sanyaye nace. Lafiya lau, bari in kai maka ruwan wanka" Ina adana kayan a kitchen na zari bokiti na cika dam da ruwa, na miƙa mishi ban ɗaki, na dawo naci gaba da aikina, shi kuma yana tsaye yana gaisawa da Hajara. Misalin ƙarfe shida da kusan rabi na kammala komai, na share tsakar gidannan na wanke shi tas, sai na shiga bayan gida na watsa ruwa, ina zaune a kujerar tsugunno ina alwala, Bulama Babba ya fito da shirinshi na zuwa masallaci. Adawo lafiya" Nace mishi, da fara'a ya amsa mun da. "Allah yasa" Yana fita Zubaina ta shigo tana faman tura ciki gaba. Harara ta zabga mun, da ƙyar na cije ban rama ba, Amman turar da take yi mun ta kusan kaini bango. Jira kawai nake yi ta haihu, a soma rabon girki, dan yadda take jin zaman aure take yi, nima zaman auren nake yi. Yanda take jin aiki take yi nima aikin nake yi, haƙurina ya kai iyaka" Haka al'amura su ka ci gaba da shurawa, Bulama Babba dai ana samun canji, dam jiya abun mamaki ya kira number Ba Bakura bai ɗaga ba, ya kira ta Ba Modu shima bai ɗaga ba. Sai naga duk ya damu, harma yana tambayata yaushe rabon da inyi waya dasu? Sai nake sanar mishi, kullum sai munyi waya, in basu kira ba ni zan kira. A kwana a tashi harna shekara guda a gidan Bulama Babba, na dawo siririya sosai, sabida damuwa, da rashin samun nutsuwar aure. Ga sha'awar son kasancewa da mijina daya soma addabata, ga yawan shan kayan maye daya ƙaru mun, in ban sha ba, har ji nake kamar haukacewa zanyi. Wata ranar lahadi da daddare Zubaina ta suntulo ɗanta namiji mai kama da ubanshi. Murna a wajan Bulama Babba ba'a cewa komai. Da murna yazo ya same ni yake ce mun, in kira su Ba Modu in sanar mishi anyi haihuwa. Bayan kwana biyu da haihuwar Zubaina aiki ya kuma kacamemun, dan ma Hajara ta ɗauke mun hura wutar jego na asuba, ita ke hurawa, ni kuma in hura na yamma, ga aiki, ga hidimar yara. Ranar data ƙwan uku da haihuwa Bulama Babba ya shigo da wata atampa a leda chiganvi ya miƙo mun tare da nera dubu biyar. "Ki yi haquri kayan fitar sunane, da kuɗin ɗinki, sai ki yi maleji" Albarka na saka musu. Washe gari na ɗauki atampar, da lace ɗina na cikin kayan akwati na kai ɗinki, nice harda siyan ɗan kunne da sarƙa ɓarawon zinare da ake yayi. Ana gobe suna da yamma sai ga Bulama Babba da Ahmad da kayan gado da wadrope, harda dressing mirror masu tsada. Su da kansu suka jera komai. Inata jiran Kuɗin abincin suna, amman ko da Bulama Babba ya shigo na tambayeshi sai yake ce mun. Ai ƴan uwanta yanzu suka iso, ya ba ƙanwar mamanta kuɗin cefanen sunce zasu yi komai, Asiya kuma ta ɗauki nauyin drinks. Murmushi kawai nayi, bance komai ba, naci gaba da harkokina. Washe gari yaro yaci suna Yusuf. Bayan na gama share gidan na wanke tsab, sai na fita kasuwar ƴan lemo nayo cefanen jallof da kosulo. A gidan Maman Adam na shiga, muna hira na gama girkina tsab, itama ta tayani, sabida na ɗan gayyaci abokan aikina, kuma nasan tunda suka ce zasu yi girkinsu, ko ɗanɗane ba zasu bani ba. Dan tunda suka shigo gidan da daddren suka soma zubar da habaici. Hajara uwar gulma cikinsu ta ƙule sai shewa take yi. Ina shigowa naci karo da me jego da ƙawayenta, suna ta hotuna a waya, tayi kyau, sun fito shar dasu. Nima wanka na shiga, na saka atampar da Bulama Babba yai mana. Na sakko da akwati na ciro atamfa, na haɗa da rigar yaro dana siyo dubu tara, nayi sallama na miƙa musu. Sai wani kallon banza suke yi mun. Ni kuwa yi nayi kamar bansan me suke yi ba. Da yamma ƙawayena suka iso, da ƴan maƙota haka da ake gaggaisawa, na sake shiga na saka leshi na . Nan mu kai ta hirarmu, nima naji sanyi a zuchiyata. Da yamma lis suka soma watsewa, duk wanda zai wuce sai ya ɗan dungule hannunshi ya miƙo mun kuɗi. Ni kuwa inata amsa. Ai kuwa na samu kuɗi sosai, harda su omo da sabulai. Da yake nima mai ƙoƙarin bayarwace in naje suna ko biki. Na adana kuɗaɗena, suma omon na adana abuna, dan ba bata zanyi ba. Jira nake baƙi su watse inyi fito na fito daga ita har Bulaman dama duk wanda zai goyi bayansu. Na gaji ni ba jaka bace, naga halama saina tashi tsaye zan kwaci ƴancin kaina. In ba haka ba, a tsaye zuchiyata zata buga ta fashe. Zubaina: Tunda su Bulama suka dawo daga gida,muka shiga tababa, sabida ya riga ya saba ciyar dani abinci mai kyau, amman yanzu mune shinkafa da mai da yaji, mune tuwo, mune ɗan wake, mun saje mun zama kanawan sak, in ina son abinci mai daɗi sai dai in ratsa gidan Asiya in ciyo. Ko in zata zo gidana ta tawo mun da kayayyakin daɗi. Ni kuma bazan iya saka ƙwandalata a hidimar gidan Bulama ba. Kaina nake ginawa, dan harna kusan kashe ginina tuni, da ragowar kuɗin mota naci ginin, duk wata kuma albashina nake turama Mama duka, rabi su samun a gini, rabi ta riƙe a hannunta. Duk da nasan mijin Asiya bai ragesu da komai ba, amman nima ina neman albarka. Kullum saina kira Mama mun shafe mintuna muna tattauna matsalolin su Sagiru da Musa, a kullum abun nasu sake ta'azzara yake kuma yi, kullum a cikin jaye_jayen magana suke. Mama kuma ta fito tai ta faɗa da jama'a, dama haka Mama take, a kullum ita dai nata ne mai gaskiya. . Asiya kuwa da yake mijinta ya tsaya mata, a cikin wata shida ta gama gininta, harta zuba ƴan haya. Nafisa kuwa, tayi watsi da karatu, ta biye ma ƙawaye sun shiga gari neman dukiya, Mama kuma ta goya mata baya ɗari bisa ɗari. Ko da su Asiya suka zo suna, da zungureren cikinta, a hakan tayo tuƙi tazo. Dan bata fiye zuwa ba, sai dai ni daga wajan aiki in wuce can gidanta, in huce takaici abuna. Mabaruka da Hadiza, da Zainab ƙawayena sunyi mun kara. Naji kunya ainun da suka ganni a cikin wannan yanayin. Duk da Bulama ya gwangwajeni da kayan katako, amman zuchiyata ba tai fari ba sam amman da yake duk abokan cin mushe ne ban ji na damu sosai ba. A haka akai suna, washe gari kowa ya watse ya koma, bayan sun soye mun ragon suna. A ɗaki na ƙunshe abuna, Hajara kawai na ƙunsama. Amman waccan yarinyar ban ko bi ta kanta ba. Bayan sati biyu da haihuwata ranar da zan koma bakin aikina kenan sakamakon wani aiki na gaggawa da ake son a ɗauramu a kai, ina tsaye a ƙofar ɗakina ina kullewa, Yusuf yana goye a bayan yarinyar dana ɗakkota zata dunga kula mun dashi a office, ina biyanta duk wata. Murhun da Yahanasu take girki na duba, naga tukunyar ruwan wanka ne kawai a kai, da mamaki nace da Hajara dake zaune tana fifita wuta. Hajara, yau waccan yarinyar bata yi abun kari bane?" Dariya Hajara tayi harda girgiza kanta tace. "Ai kuwa tayi, yanzu ta tafi wajan aiki a gurguje fa" Kusun uwa ta fita fa kika ce, tana nufin ni da yarana ba wanda zaici abinci kenan ko me take nufi" Hannaye Hajara ta haɗa ɗaya ya daki ɗaya tace. "Wannan tambayar taki ai bani da amsarta. Amman dai ta fita wajan aiki. Yanzu naso in leƙo inyi miki magana, kar yara su sani latti naga har bakwai saura basu karya ba" A fusace na shiga ɗakin Yahanasun cike da ruwan bala'i da masifa na durarma Bulama. Yana zaune yana cin wani ƙazamin ɗumamen tuwo da ruwan bunu. Meye haka Bulama, wanne irin bura ubancine yasa ka bar matarka ta tafi wajan aiki ba tare da ta yi ma yara girki ba? Wannan ai wulaƙanci ne, kuma kana ganinta. Yanzu yaya kake son nayi? Operation ne dani a sabon gari da safennen, ya kake son nayi da yaran, ga Yusuf kwana yayi yana kuka." Miƙewa yayi tsaye ya fuskanceni yace. "Ai ina ganin taci ai mata uziri tunda ta kwashe tsawon shekera guda ita ke yin komai a gidan, kama daga girki, shara, wankan yara, wankinsu, da nawa da naki, gyaran ɗakinsu. Dan yau ɗaya data fita bata yi ba, ai kema sai ki kama. Ni nafa gaji da wannan fitinar taki, ya kamata ki san ni ba yaronki bane, balle kiyi ta takani. Sabida yanzu bani dashi shine kika kasa yin haƙuri dani. Dai dai da nera biyar ɗinki bana ci a gidannan. Matsa mun ni" Yasa hannu ya tureni gefe, ya fito. Ni mamaki ma yasa na kasa motsi gani nake yi, kamar mafarki nake yi ba gaskiya bane. Asirin ya karye kenan ko me, dan kwalli na ya ƙare, jiya nake magana da Mama akan ta aro mun ko da dubu ɗari biyar ne, inason in je wajan boka. yarinyarnan wato zuwa tayi aka karya mata asirin da na kashe uban kuɗi wajan yinshi?" A haukace na fito. Cukume Bulama nayi, ina ihu ina jijjiga kamar ƴar tasha, ina faɗin. In ka cika cikin uwarka baƙarnan da ubanka ka sakeni, ni dai kai ɗan halak ne, ba zina akayi aka haifeka ba. Bazan zauna da kai ba. So kake yi talauci ya kasheni kome. Bulama sake ni, nace ka sake ni ko." Ahmad ne ya fito da sauri ya iso wajan. "Baki da hankaline Zubaina kanki ɗaya kuwa, Bulaman kika cukume kina mishi irin wannan ihun kamar a gidan magajiyar karuwai? Ai kaga illar auren ƴar bariki wacce ta saba cin kwalar maza kenan" Cikin rufewar idanu, da zafin kishi nace. Ai nafi magajiya ma ni. Ya sake ni, in yana son kanshi da arziki, kar ka kuma sa mun baki a magana kuma tsohon munafuki" "Ki sake ni ko in daka ki a tsakar gidannan jahilar banza wacce bata san darajar aure ba, maras tarbiyya. Ko da yake a ina za'a koya miki tarbiyyar ma" Dariya na saka kamar mahaukaciya nace. Ni zaka daka? Ai sai dai mu daki juna ba dai ka dake ni ba wallahi, shege ɗan iska." Kafun in rufe baki Bulama ya yanka mun mari mai zafi. Banyi wata wata ba, na dunƙule hannayena na luma mishi a ciki, irin naushin da muke ma ɓarayi a cikin sell cikinsu ya ƙulle. Nan kokawa ta ɓalle a tsakaninmu, sai zibgata yake yi. Ni kuma sai cunkusama iyayenshi ashar nake yi, bakina duk jini, shi kuwa dukana yake yi kamar Allah ne ya aiko shi. Maƙota suka taru a cikin gidan. Maza su ka lallaɓa Bulama ya rabu dani, jikinshi har rawa yake yi, idanunshi ɗaya na fitar da hawaye. Ahmad ya ja hannunshi suka fice. A guje na shiga ɗakina, na tattaro kayana da kayan Yusuf na fito, bakina da hancina duk a dauje suna tsiyayar jini, gaskiya na daku irin dukan da babu mahalukin daya taɓa mun irinshi. Kunce goyon Yusuf nayi a bayan Zuwaira mai kula mun dashi, na mayar dashi bayana. Na kulle ɗakina na ɗauki jakata. "Zubaina in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Kar ki tafi gida Zubaina. Maganar gaskiya kece da laifi, irin zagin iyayenshi da kika dinga yi, ba dan yana da tunani ba, ai da tuni ya sauwake miki. Ni in banda a Lagos ban taɓa ganin irin wannan tsiya da wasali ƙasan ba. Mata ki haukace mana a gida sai kace a agege ko a ƙarƙashin gadar C M S" MRS BUKHARI CE wasa farin girki. Yanzu ne zamu shiga asalin labarin gadan_gadan. Ina masoyan Yahanasu ku fito ku taka rawa. Yau Kofur ta daku." [30/07, 7:32 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 17 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* Rufa mun baki munafukar Allah ta'ala, masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki. Ke da munafikin mijinki. Sai ku hanani tafiya ai, shegiya sai shegen tsigudidi" Ina faɗar haka Hajara ta tashi, ta soma jijjiga tana zage_ zage. Ni da ita sai da muka ci uwar sabada sannan na saka kaina, daman a kusa nake, na kuwa zage na kirɓeta sosa.i Kai tsaye tasha na zarce. Cikin awa ɗaya motarmu ta cika mu ka nufi kaduna. Sai huci kawai nake yi. Gashi bani da isassun kuɗin da har zanje wajan boka yaimun wani sammun, sai dai nayi dabarar ɗebo manyan zannuwan dana samu a sunan Yusuf. Ina zaune ina tunane_ tunane, sai ga kiran Mabaruka. A hanzarce na ɗaga nace. Dama ko baki kira ba, zan kira ki, so nayi sai na sauka a mota tukunna. Gani a hanyar zuwa Kaduna, waccan matsiyaciyar ta ruguzamun shirina, yau dambe mu ka yi da Bulama, ya dake ni na dake shi, baki ga yadda ya farfasamun fuska ba." Wani namiji ne a kusa dani ya wani juyo da sauri ya kalleni. Harara na galla mishi, ba shiri ya kawar da kanshi. Mabaruka tace. "Hmmm Zubaina ni kaina a cikin matsala nake mai girma, kin ganni a gida yau kwana uku kenan. Adam ne ya turo mun da takaddar saki a waya. Gashi nera biyar bana magani balle in je wajan boka, kayan ɗakina nayi tunanin ko in siyar, sai in je dama, sai kuma na tuno dake, kinji dalilin kiranki da nayi. Ashe kema asirin ya lalace?" Ƙwafa nayi nace. Ki rabu dasu, daga Adam ɗin har Bulama sai sun yaba ma aya zaƙinta, ƴan aiki sai sun fisu daraja, bari dai in shigo kadunan" Sallama mu ka yi, na sauke wayata. Awa huɗu ya shigar damu kaduna garin gwamna. Mama na zaune jigum na shigo gidan da kuka wiwi. Da sauri ta miƙe. "Me zan gani Zubaina? Asirina ya tonu meya same ki a baki da hanci haɗarin mota ki ka yi ko me?" Hmmm Mama Bulama ne ya dakeni. Tsinanniyar yarinyar nan sai da tayi kwanta_kwanta ta karya duk wani sihirin da ke jikin Bulama. Yau ba dan maƙota ba Bulama da kasheni zaiyi. Mama ta shiga salati tana tafa hannayenta. "Oh ni Jummai, to wai mema ya haɗaku har ta kai da duka, kaji mun matsiyaci sakin ki to yayi?" Ina fa bai sake ni ba, barin mishi gidanshi nayi. Sai na mugun gasashi kafin ya koma, sai yayi ta zubda hawaye, yana saka guiwarshi a ƙasa kafin na yadda in koma. Zama nayi na kunto yaron bayana, mama ta karɓeshi. "Kafin ki tawo kin sanar ma da ƴar uwarki kuwa, kar taje gidan bakya nan Bulama ya dakata itama. Kafin in bata amsa, muka jiyo sallamar wasu mata su biyu. A tare suka shigo, da gani uwa da ƴa ne. "Nanne gidan su Musa ko, kece mahaifiyarshi? Mama tace. "Nice baiwar Allah lafiya kuwa" "Sakina nemi waje ki zauna, yaro yazo gidan ubanshi. Kin ganta nan, ɗanki Musa ne yai mata fyaɗe, ta hanyar yaudararta da sunan zai kawo ta gaisuwar surukai yasa mata maganin bacci a lemo, naso in shigar da ƙara tun lokacin da abun ya faru, amman mahaifinta ya dinga lallaɓani dan gudun zubewar mutuncinshi a idanun duniya, bai duba hakkin yarinya ba. Tun daga ranar da Musa ya biya buƙatar shi da Sakina ya dena Zuwa zance wajanta. Kwatsam sai ga ciki ya ɓullo a jikinta har na tsawon wata uku. Shine na kawota ta haife yaron a gabanku, domun ku ke da alhakin ciyar da ita da abunda yake cikinta." Mama bata gama jin zancen ba ta miƙe nan suka soma buyagi da wannan baiwar Allah, itama naga halama da shirinta ta zo. Mama wannan hayaniyar duk ba ita bace mafita. Halin Musa babu wanda bai sani ba a unguwarnan. Ciki dai nashi ne, amman baiwar Allah ki tafi da Sakina, zamu ɗauki alhakin ciyar da'ita har zuwa ta yaye abunda ta haifa, sai mu karɓi abunmu. Mama ta dura tace "Akan me zaki ce musu haka Zubaina lafiyarki kuwa?" Mama case ɗin fyaɗe case ne babba wanda in ya je gaban ƴan sanda kai tsaye kotu ne, daga nan sai gidan yari. Mu lallaɓa a samu a rabu lafiya, ɗan kuka mai jama uwarshi jifa" Da ƙyar wannan baiwar Allah suka koma tare da bamu kwatancen gidan da suke. Mama ta fashe da kuka tana. "Ni na shiga ukuna wannan yara so suke su kasheni su huta kawai, kullum hawan jinina baya sauka sai kuma hawa, ni inaga gidan zan bari." Sagiru ne ya shigo da fito, sai wani cije baki yake yi kamar shugaban ƴan tauri, butoci da bokatan ƙarfen gidan ya soma yin boll dasu. Mama ta ƙura mishi idanu yana ta buyaginshi, kallona yayi. "Ke kuma yaushe a garin ne?" Banza nayi dashi, nan ya gama zage zagenshi ya wuce mu. "Kin ganshi nan, ƙwaƙwalwarshi ta gama lalacewa ya haukace, wataran haka zaki ji yana danna ihu a tsakar gida haka sittan. Shi kuwa Musa ko Ayu dole ya sara mishi, ɗakinshi baya shiguwa kullum da mace, kinga gashi ya bankama wata ciki, shikenan muma mun samu ɗan dakan kuka a gida." Ni gabaƙi ɗaya ma sai naji zazzaɓi na shirin kwantar dani. Mabaruka ce tayo sallama ta shigo. "Lallai Mabaruka yau kece a gidan namu, idanki kenan? Dariya Mabaruka tayi tace. "Mama ayi haƙuri damu, yanayin aikin asibiti ne sai a hankali, babu lokaci. Ina wuni Mama" Da fara'a Mama tace. "Lafiya lau, ya gyatumarki, da mai gidan naki?" "Duk suna lafiya Mama " Mama tace. "To madallah Allah yayi albarka" Hannun mabaruka na kama muka shiga ciki. Nan muka shiga tattaunawa, mun tsayar da matsayar gobe zamu shiga Jos, ni zan siyar da atampopina Mama zata ranto mun wasu kuɗaɗe in haɗa, mabaruka kuma zata siyar da Kayan ɗakinta tas mu rankaya mu je wajan boka, faɗa da cikawa. Bulama Babba: Jikina yana rawa muka fita daga cikin gidannan, mata sunyi cirko_citko a ƙofar gidan, haka muka rakuɓe gefe muka wuce, sai ambaton Allah nake yi, jikina na ɗaukar wani irin zafi irin na mashasshara mai ƙarfi. A dai dai ta sahu Ahmad ya tare muka faɗa. Jingina nayi a jikin kujerar a daidaita sahun, na lumshe idanuwana a hankali ina jin wani sanyi na huda dukkannin wata mafaka ta gashin jikina. Ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun irin wahalhalun da Zubaina ta dinga sani inayi mata, da irin wulaƙanta mahaifana, da ƙanwata Yahanasu da nayi, da irin ɓarin dukiya da naita ma makirar uwarta, da marasa kunyar ƙannenta. Dukkannin wannan al'amura dawomun suke yi kamar yanda ake tariyo faifayin filet sidi. Na tuno lokacin da na bijiro da zancan auren zubaina kalmar da Ba Bakura ya faɗa mun. "Bulama ni dai yarinyar nan ko da naga hotonta hankalina bai kwanta da'ita ba. Idanuwanta sun buɗe da yawa. Tunda mahaifiyarka ta ga hoton yarinyar, ta shiga tunani mai zurfi. Jiya ƙarfe biyun dare ta tasheni a bacci sabida zancan. A zahiri daga ni har ita hankalin mu bai kwanta da yarinyar ba, taya ma da hankalinka da tunaninka zaka auri ƴar doka?. Bance maka aikin doka ga mata haramun bane, ko ɗaya. Amman a zahirin gaskiya aikin yafi dacewa da maza, duk wani aikin kaki yafi dacewa da maza, duk da matan suma akwai muhimmiyar rawar da suke takawa. Domun dasu ake shigowa gidajen mata, su riƙe hannayen mata su tafi dasu. Buɗewar idanunta da gogewarta shi yafi ɗaga mana hankali. Mace mai wayewa da buɗewar idanu da yawa, tana da wuyar sha'ani, da wuyar sarrafawa. Amman bance ka auri ƴar ƙauye ba, dan gidanku duk ƴan boko ne, amman wanda suka ƙoshi da karatun addini, tunda a tsarina duk sai da kuka sauke Qur'ani mai girma, kafin kuka soma jami'a. Ina jiye maka me ka je ka zo, kuma kaine ka fita zakka a dangi. Dan babu wanda ya taɓa auro mana bare" "Kai Bulama ina tunaninka ya tafi ne, sai kiranka nake yi baka ko ji? Da sauri na kalli Ahmad harya fita daga cikin ɗan sahun yana tsaye. Jiki a saɓule na fito nima, muka sake hawa wani abun hawan. Da ni dashi babu mai cewa da wani kanzil, kowa da abinda yake tunani, a haka har muka iso wajan aiki. Kowa ya nufi block ɗin da yake kulawa dasu, dan soma gudanar da aikinshi, bayan mun cika takaddar shaidar zuwanmu, da lokacin da muka iso aiki. Zirga_ zirga nake ta faman yin ina duba mazauna cikin gidan yarin a hankali, amman babu nutsuwa da kuzari a jikina ko kaɗan. A hankali na zaro wayata tare da lalubar number Ba Bakura, cikin faɗuwar gaba da taraddadin me ka je kazo na kara a kunnena. Amman harta ƙaraci kuka ba'a ɗaga ba. Na kira sama da so bakwai, daga ƙarshe naji wayar a kashe. Da ƙyar na mayar da hankali na bakin aikina, na tabbatar da maganar bada abincin karin kumallon block ɗin dake ƙarƙashina, sai da na tabbatar kowa ya samu, sannan na koma gefe na kira layin Ba Modu shima ya ƙaraci kuka ba'a ɗaga ba. Idanu na lumshe ina jiyo wani ɗaci yana ratso huhuna har izuwa kan harshena, da ƙyar na fisgo numfashina daga huhuna zuwa ƙofofin shan iska na. Hajja Gana na kira, ban sameta ba, na kira Dala bai ɗauka ba. Ya Allah ka kawo mun agaji, nasan na cancanci ko wanne irin hukunci daga magabata na, ya Allah ka bani juriyar rashin iyayena har su sake yarda dani a karo na biyu, in sake zama ɗansu. Allah kana ganin komai, dukkan abinda ya faru bansan musabbabin faruwarsu ba, sharrin shaiɗaniyar mace ne yai tasiri a kaina. Zunaina kin cutar da rayuwata, Allah ka saka mun." Sauke kaina nayi wanda yake yi mun wani irin mugun ciwo, dole in ɗauki hutun aiki, in tafi Damaturu domun roƙon gafarar iyayena ko zanga dai_dai. Wasu hawayene suka gangaromun a kumatuna masu mugun ɗumi. Dana tuno da hawayen da mahaifiyata ta dinga zubarwa, a ranar da nayi musu iyaka da zuwa gidana, da irin tashin hankalin da na gani a fuskar Ba Bakura. Zubaina koma meye tamun ta rabani da farin cikina ta cuceni, wallahi Allah bazai barta ba. Ina komawa gida zan sallameta ta tafi gidansu, zama da'ita ya ƙare, dan rabuwata da'ita shine farin cikin iyayena da dangina baki ɗaya. Kaicona dana shigo mana da bara gurbi cikin zuriyarmu, kaicona da na zamto silar ɓacin ran iyayena da dangina. Abubbuwa sukaita dawomun kaina, inajin tamkar zan zare ne. Ƙarfe goma aka kaɗa ƙararrawar fito da fursinoni cikin yadi, sannan a lokacin wasu suna da ajujuwan ɗaukar darasi, akwai kuma ɓangarorin koyar da sana'o'in hannu iri daban_ daban. Juyawa nayi dan zuwa ɗakin hutawa, zazzaɓi ne mai zafin gaske a Jikina. Ina cikin wannan halin Ahmad ya shigo shima dan ya huta. Ahmad kana ganin Ba Bakura zasu yafe mun kuwa, kana ganin zasu sake dani har in zama kamar da a zuchiyoyinsu? Ahmad Zubaina itace ta raba ni da kowa nawa, dukiyata ɗan wani abu ƙalilan iyayena da ƴan uwana suka samu. Amman Zubaina da makirar uwarta su naima aiki. Kuma sanadiyyarsu na rasa aikina na tsiyace. Dubi irin ɗiban albarkar da yau Zubaina tai mun a tsakar gida?" Daurewa nayi da ƙyar na mayar da wani irin kuka da yake ƙoƙarin amayo kanshi. Ahmad ya dafani yace. "Alhamdulillah babu abunda zamu ce da Allah sai godiya. Allah ya kuɓutar da kai daga hannun Zubaina. Ai mu tuni mun daɗe da sanin sihiri na yawo a jinin jikinka. Sabida hidima da kariyar da kake ba Zunaina da danginta yayi yawa. Ba Bakura kuma zasu yafe maka da ikon Allah. Suma suna kewarka kuma suna son ji daga gareka, fishi kawai suke yi da kai. Hakan bazai hana suima adda'a ba. Ba'a cikin fishin Hajja Gana tasa ɗan uwanta ya nema mana wannan aikin ba? Ai su iyaye duk yanda ɗansu ya kai ga lalacewa, wallahi burinsu a kullum rayuwarshi tayi kyau da albarka. Ita kanta Yahanasun wacce iriyar wahalarku ce bata ɗauka ba. Ka kuma duba yanda tai ta hidima da kai da iyalinka, a lokacin da kake buƙatar majingina. Amman ita Zubaina data gama tatikeka daka taɓata ba cewa take yi gini take yi ba? Da kuɗin wa aka sai filin? Da kuɗinka, ga gida ka siya ma uwarta, kai ko bulo yanzu baka dashi. Kayi haƙuri kar ka takurama zuchiyarka gudun gaiyato hawan jini, dame zamu ji, da talauci ko da ciwo? Gara mu ji da ɗaya dan Allah" haka Ahmad yai ta bani baki, bai barni ba har sai da ya ragemun kaso mai tsoka na damuwata." Yahanasu: Ina zaune a gaban teburin aikina,na duƙufa sai faman aiki nake yi. Dan zuwa sha biyun rana akwai program da zan gabatar, na gayyaci wata uwar marayu da mijinta ya mutu ya barta da yara tara. Ina aikin ina duba lokaci, Binta abokiyar zamana kuma ƙawata sai tsaki take zabgawa. Duk da dai ta girmemun sosai, dan babbar ƴarta shekararta goma sha ɗaya. Amman jinina da nata ya haɗu sosai da sosai, na kan ranci kuɗi a hannunta, itama takan ranta a hannuna. Har adashe ta kafa mana a ma'aikatar tamu, maza da mata. Hannu biyu na shiga, duk wata ina zuba dubu shida daga cikin albashina, saura mutum biyu ɗauka yazo kaina, nice ɗaukar ƙarshe. Lafiya Binta kike ta faman tsaki tun zamanki? Kinsan fa kina da labarai zuwa ƙarfe ɗaya, ya kamata ki mayar da hankalinki ki samu ki haddace, kar a samu matsala irin na jiya. Hawayene ya cika tab a gurbin idanuwanta, ta sauke wata nannauyan ajjiyar zuchiya tace. "Damuwar dake cin ƙasan raina ba zai barni in samu nutsuwa ba. Dole a cikin aikina aita samun kusa kurai iri daban daban Yahanasu. Wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, sai maƙociyata da matsalarmu tazo ɗaya. Dubi nan" Ta yaye mun hannun doguwar rigarta, naga wajan a ɗaye yayi jaja zur da halamar shatin bulala. Me zan gani haka Binta? Wannan ai duka ne. Murmushi tai mun tace "Da zan buɗa miki bayana ashe zaki daskare a nan wajan. Hmm duk wata mace da kika ganta da irin matsalolin da take fuskanta a wajan mijinta. Ke dai kiyi aikin ki kawai" Jikina ya mace mus, a fahimtata kamar mijinta ne ya doketa. Lallai gidan aure cike yake tab da ƙalubale iri daban daban. Ina nan ina tunani naga Binta na dube dube, kafin ta zaro wata allura a cikin jakarta. Ban ankara ba naga ta tsira allurarnan a saitin jijiyar hannunta. Tana gama janye ruwan allurar ta mayar jakarta, tare da kifa kanta a kan benci ta rushe da kuka." Binta allurar me kikai ma kanki, dama kin karanci fannin kiwon lafiya ne?" Ɗagowa tayi idanuwanta caɓe_ caɓe da ruwan hawaye, tai mun wani murmushi mai kama da kuka. "Yahanasu, kullum sai nayi ma kaina wannan allurar nake samun nutsuwa, kuma ita ke mantar dani abinda na baro a gida. Ada babu irin nau'in kayan mayen da bana sha. Daga baya ko na sha basa gusar mun da ƙishin ruwana. Maƙociyata ce ta ɗaurani a kan wannan hanyar, itama shi take yima kanta duk kwanan duniya." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Kema kina ta'amali da kayan maye ashe?" "Sosai ma, ai a wannan zamanin in baki yi ta'amali da kayan maye ba. Zaki yi ta'amali da likitan zuchiya, kona hawan jini kuwa. A gaskiya a garin Kano mata da yawa sun faɗa harkar shaye_shaye fiye da yanda kike tunani. Ba matan auren ba, ba ƴan matan ba. Matan aure da dama suna ta'amali da miyakun ƙwayoyinnan ne, dan su samu wata ƴar nutsuwa, sakamakon rashin dace da namijin arziki. Ƴan matan kuma sunfi sha sabida samarinsu, ko dan burgewa, naga ƙawata nayi nima sai nayi." Murmushi nayi mata, nima saina tuno da halin da nake ciki a gidan Bulama Babba. Yanzu haka ma bansan me zanje in tarar a gidan ba, dan na baro baya da ƙura. To Bintain akwai wata allurar a jakarki, ki siyarmun mana, nima sai in gwada ai. Dariya na bata, tace. "Allurarnan zata iya fin ƙarfin ƙwaƙwalwarki, ki ci gaba da afa ƙwayoyi ko maganin tari kawai." Binta kenan, kaina yana ɗaukar kaya fa sosai, ke dai bani in jarraba" Zaro wata allurar tayi a jakarta ta nuna mun, amman tace in bari inna gama program ɗina, sai ta mun allurar. Ai kuwa hakan akayi, ina gama program ɗina, Binta ta jani hanyar bayi tai mun wannan allurar a hannuna. Wallahi in ɗaga ƙafata a wajan na kasa, sai tsugunnawa nayi na soma rarrafawa, ko ina sai ya zame mun rafi, har kifaye na gani suna iyo. Binta kuma ba dan taso ba, ta wuce ta gabatar da labaranta, ni kuma ta sanar cewar banda lafiya, zata kaini gida. Muna tafe ina ganin garin na jujjuyawa, ita kanta Bintan ganinta nake yi kanta a ƙasa, ƙafafuwanta a sama. A haka ta shiga dani cikin gida, har zuwa ɗakina. A kwance ta barni bacci ya kwasheni. Hajara: "Baiwar Allah lafiya kuwa naga kin kawo Yahanasu a rurriƙe bata da lafiya ne?" Hajara ce ke tambayar Bilkisu wacce duk ta ruɗe. "E bata da lafiya ne, kanta ne yake ciwo mai tsanani da jiri. Bazai wuce wahalar aiki bace. Amman yanzu naga harma ta samu bacci" Hajara tace. "Ba dole ciwon kai na wahala ya rabketa ba, am mayar da'ita tamkar baiwa. Duk da dai ita Zubaina taga ƙarshenta yau" Duk wannan surutan Hajara uwar gulma ta zaci a zuchiya take magana. Sai da Binta tace "Ban gane me kike nufi ba fa" Hajara ta riƙe bakinta da hannayenta tace. "Au ance baki shi ke yanka wuya. Zancan zuchi ne ya fito fili." "To Allah ya bata lafiya, gobe zan dawo in duba jikin nata." Tana kaiwa nan ta fice a gidan. Maryam da Bawa kuwa, sai koke koke suke yi na yunwa. "Dalla ku rufama mutane baki, so kuke in kashe kaina ko me? Abincinnan yana wuta, ai sai kuyi haƙuri ko?" Zulai tace da Hajara. "Anty ni ina ga kamar kukan mamansu suke yi, bana yunwa ba. Kinga cincin ɗin da kika sai musu ma basu gama cinyewa ba, sun dawo dashi harda jus ɗin." Hajara dai bata ce komai ba, taci gaba da aikin abincinta. Shinkafa ce fara da manja, da yaji sai salak da tumaturi da albasa a yayyanke. Ƙarfe shida ta sauke tukunyar abincin. Sai da ta sallami yaran sannan tace. "Zulai ɗakko kular da Yahanasu take zuba ma Bulama abinci, in zuba mishi. Ita ba lafiya, abincin ma sai dai da safe mu dama kokko" Ɗakko mata kular Bulama tayi, ta zuba mishi a kularshi, bayan ta zuba na Ahmad. "In yarannan sun gama cin abincin, ki ɗan share gidan. Dama Yahanasu ce ke sharewa, gashi bata da lafiya, sai bacci take ta yi. Ki zuba wanda zai isheki kici." Ruwa taja a rijiya tayo wankanta tsab, data fito ta ɗauro alwala. Ta shiga ɗaki ta sanya kaya ta fito fes da'ita. Dadduma babba ta fito da'ita ta jera abincin Ahmad a kai, da ruwa da komai. Ta hau kan taburma ta soma sallar magriba. Zulai ma a gurguje ta ɗauro alwala ita da yara suka ta da tasu sallar a gefen Hajara. Bulama: Assalamu alaikum. Na yi sallama da ƙarfi a zaure, tunda ba matana bane kaɗai a cikin gidan ba. Ahmad ya kutsa ta bayana ya shiga, dan ya sanar ma Hajara ta suturta jikinta. Daga baya yace in shiga. Yara na ganina suka taso da gudu, duk suka rungumeni harda yaran Ahmad. Sai Baba oyoyo suke yi mun. Biskit ɗinsu dana saba siyo tsaraba na miƙa ma Zulai tare da ledar biredi da kayan shayi dana siyo ma Hajara. "Zulai raba musu biskit ɗinnan ko zasu barni in huta. Wallahi na gaji, kaina kamar zai fita. Wannan ledar kuma ki ajjiyeta da safe kwa haɗa tea ku da yaran. Hajara tace. "Angode sosai Bulama, sannu da ɗawainiya. Am Yahanasu tana ciki babu lafiya, ba yanda take. Dan ko ɗazu dana leƙata, saina samu tana ta firgita, harda surutai. Na dai tuttufa mata adda'a saita samu baccin ya kuma kwasheta." Ya Allah na furta a raina. A zahiri kuma tambayar Hajara na shiga yi meke damun nata. "Ban sani ba. Abokiyar aikinta ce ta dawo da'ita gidan a rirriƙe, ta dai ce ciwon kai mai tsanani da jiri ne ke damunta. A sakamakon yawan aiyuka da su kai mata yawa. Kuma fa hakanne, aiki yayi mata yawa, gana gida, gana wajan aiki, Zubaina fa ko tsinke bata taɓawa a gidannan komai Yahanasun ce ke aiwatarwa. To zubaina ɗazu kuna fita taja akwatinta da ɗanta ta fice a gidan, bayan ta ƙare mun tana di ni da Abban Anisa, wallahi sai da ta daka ni kamar wacce ta kama ɓarauniya kafin ta bar gidan." Da sauri nace. Ta fita da akwatifa kika ce?" Ahmad yayi carab yace. "Shiga kaga jikin Yahanasu fita batun Hajara. Banda gulma ba abunda yake damunta, daga dawowarmu ta tare mu da wannan maganganu haka. Kallon Hajara yayi yace. "Ke kam kinji daɗin halinki Hajara, wato ba zaki dena gulma ba ko?" Ban bi ta kansu ba, na faɗa ɗakin Yahanasu. Tana kwance a kan katifa tayi shame shame tamkar wata matacciya. Idanu na ɗauko na zuba mata, tare da ƙarema fuskarta da jikinta kallo. Ban taɓa tunanin akwai wani abu da zai iya ramar da Yahanasu ta zama haka ba. Sai gashi sanadiyyar aurena, da ƙuntata mata da mu kai ta yi ni da Zubaina, ya zugar da Yahanasu tashi guda, gashi har cutar da'ita da muka dinga yi yai sanadiyyar kwantar da'ita. Ni da wanne ma idanu zan ɗaga in kalli Ba Modu dashi? A lokacin da nine kaɗai ɗa a gabansu, na samu gata da kulawa a wajan Ba Modu fiye da kima. Har Ba Bakura ne yake mishi faɗa kan irin yadda yake ji dani ɗin yayi yawa. Shi ya dinga koya mun karatu tun kafin in soma zaman aji, hakan yasa na goge, ko da na shiga makarantar nafi duk ƴan ajinmu ƙoƙari. Shi yake riƙe hannayena ya kaini makaranta, ya ɗakko nera biyar ya bani a saman nera ukun da Ba Bakura ya bani. Banda carbin malam da gudi_gudi da yake sai mun a bakin makaranta. Kaina na dafe wanda yake shirin tarwatsewa. Zubaina ta cutar dani cutarwa mafi girma, gashi ta tsallake tayi yaji bayan cin mutuncina da tayi a bainar nasi. Ta faru ta ƙare wai anyi ma mai zani ɗaya sata. Wayata na zaro a ajjihuna, hannuna yana kakkarwa na rubuta ma Zubaina shika kamar haka. _Ni Bulama na sake ki matata Zubaina saki biyu_ Babu daɗi babu ragi na tura mata, na kashe wayata ɗib. MRS BUKHARI CE [31/07, 8:22 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 18 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* "Bulama ya yanayin jikin nata, ko sai mun kaita asibiti ne?" Na jiyo Ahmad daga ƙofar ɗaki yana magana. Fitowa nayi jiki a mace na same shi. To bata farka ba ma tukunna, ballantana inga yanayin jikin nata. Ahmad kai kaga yadda Yahanasu tayi wata uwar rama kuwa, anya yarinyarnan tana ma cin abinci kuwa?" Ahmad ya nisa yace. "Yanzu zo muje muyi sallah tukunna. Hajara zata kula da'ita kafin mu dawo. Ka samu kaima kaci abinci ka haɗiyi magani, kaima ba ishasshiyar lafiya ba" Sukuku haka nabi bayan Ahmad muka je muka yo sallah. Amman yayi yayi dani inci abinci ko in sha magani naƙi fur. Haka dole ya rabu dani, nayi musu sallama shi da Hajara na koma ɗakin Yahanasu. Nayi mata tashin duniya akan ta tashi taci abinci tayi sallah, amman sai wasu surutai take yi na zafin zazzaɓi. A daren ranar kusan raba dare nayi ina sallah, tare da roƙon mahaccina ya yafe mun a bisa wulaƙanta mahaifana da nayi ba'a cikin hayyacina ba. Yahanasu, sai baccinta take yi, ni kuwa banko rintsaba sam har garin Allah ya waye, da ƙyar na samu Yahanasu ta farka, Na taimaka mata zuwa bayan gida, ina tsaye a kanta alwala ma wannan ta kasa, ta ɗauki buta ta riƙe da hannayenta ya gagara. Dole haka na riƙeta na mayar da'ita ɗaki, mu kuma muka wuce masallaci. Badan naso ba haka dole na shirya dan fita aiki. Yaran kuma suna wajan Zulai tana shiryasu zasu tafi makaranta. Sallahu na ba Hajara. Hajara in Yahanasu ta tashi, ki kirani a waya ko Ahmad ki sanar damu, in ma zan dawo gidane muje asibiti sai in dawo. Kuɗi na zaro nera dubu ɗaya na miƙama Hajara, ta miƙo hannu zata amsa, Ahmad ya karɓe kuɗin a hannuna, yana hararar Hajara. "Haba Bulama kar ka kuma yi mun haka. Aika zarce komai a wajena wallahi. Su Maryam ai ƴaƴanane, Hajara zata kula dasu kafin Yahanasu ta samu lafiya, kila ma zuwa lokacin mahaifiyarsu ta dawo. Jana yayi muka fice. Ahmad ni fa tun a daren jiya nai ma Zubaina saki biyu. Ko kusa bazan iya ci gaba da rayuwa da'ita ba. Ina mai nadamar saninta ma da nayi a rayuwa. Na barta da Allah, yaro kuma tana yayewa zanje in karɓo abuna dan bazan bari yarona yai zaman agolanci ba. Kuma zanci gaba da adda'a Allah yai mun tsari da Zubaina da ire iren masu irin halayyarta ma. Iya cuta Zubaina ta cutar dani gaskiya, ka duba duk soyayyata da mahaifana da ƴan uwana, sai da Zubaina ta raba ni da kowa, kaine kaɗai ka jure aka tafi a haka Ahmad. Ni bansan da wanne ido zan kalli Yahanasu da Ba Modu ba ma wallahi. Shi kanshi Ba Bakura kasanshi da tauri fa. Tun jiya nake kiran wayarsu ba wanda ya ɗaga." Ahmad ya yi Murmushi yace. "Na gode Allah da yasa kayi tunanin shikan Zubaina, ni kaina naso in baka shawarar sakin nata. To amman bansan ra'ayinka a kai ba, nasan kana yima Zubaina wani irin so. Kuma tsakanin miji da mata nasan sai Allah. Alhamdulillah da ka saketa, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku baki ɗaya. A cikin zamantakewar da kuka gudanar a baya duk wanda ya cuci wani shi da Allah." Hakane Ahmad gaskiya ka faɗa. Ahmad yace . "Zancan su Ba Bakura kuma, ka bari zamu samu lokacine muje mu roƙi gafararsu, sai ka haɗa da yin ta'aziyyar Ba Baana bai ɗaya, Allah ya ƙara rufa mana asiri." Yahanasu: A hankali na soma buɗe idanuna ina jin kaina na juyawa dani, ina dai kwance bana ma gane kaina. Ina dai jiyo maganganu haka a kaina sama sama, can nesa nake jin maganar, kuma ji nake maganar tana amsawa. Na jima sannan na gane a inda nake, har na gane Hajara dake zaune tana karyawa, ta nai mun sannu. Dafe kaina nayi nace. "Hajara waya kawo ni gida, ya akayi na zo gida?" A jere nayi mata wannan tambayoyin. Ta bani labarin abinda ya faru tun daga lokacin da Binta ta kawo ni, har zuwa yanzu. A zabure na miƙe zaune, sai dai jiri ya mayar dani yib na koma kwance. Hajara tace . "Subuhanallahi yi a hankali mana, sabida in kula da ke ne yasa banje wajan aiki ba. Bari in taimaka miki, wanka ya dace ki soma yi sai ki rarrama sallolinki." Hawayene ya ziraro a gefen kumatuna. Da taimakon Hajara naje bayan gida. Sallah sai a zaune na yi ta. Abinci Hajara ta kawo mun, ta nemi waje ta zauna. "Hmm ci abinci in baki labarin gagarumin rikicin daya faru tsakanin Bulama da kofur Zubaina, ke ta yi yaji ma fa, bata kwana a gidan ba." Har wani rage murya can ƙasa_ƙasa Hajara take yi. Mamakin abinda ta faɗa ya kamani, jikina na rawa na yunwa na gama da duk abincin da Hajara ta kawo mun, na shanye ruwan ma tas, dana lumshe idanuna sai naji sabon bacci na kwasata.. Hajara kuma ta soma mun zuba, ta bani labarin tas abinda ya faru bayan zuwana aiki. Naji daɗin labarin da Hajara ta bani. Hamdala nayi a zuchiyata, Allah ya karɓa mun adda'ata, bayan shekara guda Alhamdulillah. A fili kuma nace Amman me yasa zata ɗau fishi har ta tsallake yaranta ta tafi, alhalin ba korarta yayi ba?" Hajara tace. "Ke meye naki ni da nayi tunanin zaki yi murna, wake ƙaunar kishiya in ba ke ba. Ko da yake ta asiriceku ne wallahi tallahi shi yasa ki kai ta mata bauta, da asirin ya karye ba gashi kin botsare ba. Harara na sakar mata naja bakina nayi gum. Hajara ni wani irin ƙauri nake ji, ko kin ɗaura girkine yake ƙonewa, ga hayaƙi yana shigowa daga tsakar gida. Hajara tace. "Wallahi ko ɗaya babu abinda na ɗaura, ina tunanin ko taya ake ƙonawa acikin layin, tun safe nake jin wannan ƙaurin. Kafin ta ida magana sai muka ji dam wani abu yayi ƙara. Muka soma jiyo ihun mata da yara suna ambaton gobara_ gobara. A zabure muka miƙe, duk da ina cikin jiri a guje muka fito tare da Hajara. Ashe a cikin gidanmu ne gobarar, a ɗakin Zubaina, wuta ce take ci ba ba ba ba, gashi harya kama kitchen ya kama zaure, babu wata hanyar fita. Sai ambaton Allah nake yi da ƙarfi, hawaye na fita a idanuna. Iyayena kawai nake tunowa, shikenan mun rabu kenan, dan izuwa yanzu wutar harta kama ɗakunan gidan kab, da mugun gudu na shiga cikin ɗakin na zari jakata wacce takadduna suke ciki, hankalina in yayi dubu to ya tashi. Sai watso ruwa mata da matasa suke yi ta katanga, amman a banza man kare, gashi ƙofar gidan da sakata. Mata sai ihu da kururuwa suke yi a waje, hayaƙi ya gama turniƙe mu sai tari muke yi. Da naga muna shirin halaka, ba shiri nayi kukan kura naja hannun Hajara muka shiga zaure. Tururin wuta da zafin hayaƙi duk ya kiɗimamu, numfashinmu na gab da ɗaukewa muka ji an ɓalle ƙofar, matasa sun fincikomu waje. Shanshar na faɗi a wajan, hayaƙi na fita ta hanci ta bakina. Haka ma Hajara. Gidan maƙota mata suka kaimu duk aka kewayemu ana kuka, wuta bata taɓa mu ba sam, amman kuma sai tari muke yi, muna fitar da kaki baƙi ƙirin. Wata tsohuwa tace. "Ga manja ku shanye, tun wuri ku samu kuyi aman wannan hayaƙin tun kafin ya halaka ku. An auna arziki tunda dai kun fito da rai, kuma wuta bata taɓa ku ba." Wallahi haka matannan suka dinga ɗura mana manja, mu ka dinga kwara amai baƙi ƙirin, muryoyinmu lokaci guda suka dashe dan maƙorona babu abinda yake yi sai zafi tamkar zai tsatstsage. Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun shi nake ta nanatawa ina hawaye. Wani ɗaki aka shiga damu, sai zuwa jaje maƙota suke ta faman yi. Anci nasarar kashe gobarar amman komai ya ƙone ƙurmus, har ya fara cin gidan maƙota. Hajara sai sambatu take yi. "Oh ni Hajara Allah na tuba. Shi yasa akace in zaka auri mutum ka aureshi domin Allah, ba dan abinda yake dashi ba. Yanzu jiba ƴan tsunmokaran da muke gadara dasu, da ma komai duk sun ƙone. Muƙami babba da Abban Anisa yake riƙe dashi, motocinshi biyu. Sutura kuwa yasa wancan, ya cire wannan, ya kyautar da wannan. Ni kaina wanne irin facaka ce banyi da dukiya ba. Kasuwanci nake yi, ina juya sama da million amman wata la'ananniya ta damfareni, komai namu ya ƙare sai ci baya da muke sake yi. Allah in wani laifin mu kai ma ka yafe mana. Wallahi ko a iya haka abin ya tsaya munga aya." Ita tana da bakin surutai ma, ni in banda addu'a babu abinda nake yi. Kwayoyi kawai nake burin gani na afa ko zanji sauƙin zugi da tashin hankalin da nake ciki. Ji nake yi tamkar in tsala ihu sabida hayaniyar masu zuwa jajanta mana, jinta nake yi a cikin ƙwaƙwalwata, tamkar zan zare haka nake ji. Wannan tsohuwar ce ta sake leƙowa ɗakin da muke tace damu. "An sa samarin gidan, sun kira mazajenku a waya, anyi musu bayani. Suna ma hanyar zuwa. Allah yasa da abinda gobararnan ta tare muku. Allah ya mayar muku da arziki. Ameen Baba mun gode" Shine abinda na iya cewa. "Ba komai, hakkin maƙwabtakan kenan. Kafin ɗan uwanka yazo kan ka, koma menene, maƙocinka shi zai soma zuwa. Shi yasa akeson a zauna da kowa lafiya. Cikin ku tsakaninmu daku girmamawa ce. Hajara kuwa nanne gidan hirarta. Yahanasu ce ma dai, tun lokacin da kuka shigo kuna sababbin dawowa layin, bata kuma shigowa ba. Abokiyar zamanki dama ita bata zo ba. Ni ina take ne ma tana wajan aiki ko? Oh kome ta bari a kunne a ɗakin sai Allah, daga ɗakinta wutar ta tashi Wuta ta lashe muku komai na tausaya gaya." Carab Hajara tace. "Ai tayi yaji. Bayan wannan hatsaniya data afku jiya Baba, bata kwana a gidan ba, ƙila wani abun ta bari a kunne kam" Kallon Hajara nayi ina mamakin gulma da munafurcinta, a cikin wannan tashin hankalin da muke ma sai tayi halin nata. Baba tace. "Kai ai wannan yarinya, jiya wuni nayi ina mamakinta, cin mutuncin miji haka ai babu kyau. Oh yanzu sai dai taji mummunan labari maras daɗin ji" Ni dai bana iya cewa komai. Hanya nake nema in fita ko bashi ne in ciyo na maganin mura in sha, tun kafin kaina ya hargitse asirina ya tonu. Gashi wayata na barota a can cikin gidan, inason inji muryar su Ba Bakura ko zanji dama dama, in sanar dasu halin iftila'in da kuma muka kuma faɗawa." Zubaina: Washe gari: Cikin ƙunci da zafin zuchiya na kwana. Bansan dalili ba nima. Yusuf ma haka ya raba dare yana kuka, nonon ma yaƙi karɓa, Nafisa sai faman tsaki take ja mun, mun hanata bacci. Gashi babu wuta haka mu ka ƙwan ba wuta, wayata a mace ta wuni ta kwana. Zama nayi a kujerar tsugunno, ina goge bakina, Mama kuma tana gaban wake tana wankewa. Daga bayan gida Sagiru ya fito, butar da nake amfani da'ita Sagiru ya saka ƙafa yayi boll da'ita. Ruwan ya tarwatse duk ya ɓata mu. "Wannan ƴar tashar kuma me take yi a cikin gidannan Mama?" Ni dai idanu na bishi dashi, dan ji nake yi zuchiyata na tunzurani akanshi. Mama tace "Shine zaka yi mata boll da buta, wannan butar ita kaɗai ta rage a cikin gidannan, sabida duk ka farfasa mana kayan ribobi. A zabura na miƙe tsaye, kokawa ta kaure a tsakanina da Sagiru, dukana yake yi sosai, nima ban tsaya raga mishi ba, na shiga yi mishi dukan manyan ɓarayi. Mama sai zage_ zage take yi, tana ta kiciniyar rabamu, mu kuma sai turka_turka muke yi. Musa da Nafisa ne suka raba wannan taƙaddama da ƙyar, dukkanmu mun daku sai huci muke yi. "Wallahi ba dan Mama ba saina kasheki har lahira, ko ba komai na rage mugun iri, amman a juri zuwa rafi wata rana za'a fasa tulu, in sanda na yawo, kai na yawo wata rana zasu haɗu. Karki kuskura in dawo in sameki a gidannan, la'ananniyar Allah, sai na zame miki silar ajali. Mama tace. "Tunda gidan na ubanka ne kai kaɗai ba, mitsiyacin yaro wanda baya ƙaunar dukkan wani farin cikina, Allah dai ya tsine maka akbarka, ita da gidanta ko ka mance mijinta ne ya sai mana gidan. Ubanku me ya mutu ya bar muku in banda riguna uku da rediyo sai tabarau da lofe." Harya soma tafiya ya juyo yace ma Mama. "Allah ya tsinemun albarka, to na nawa kuma? Tun ina yaro kike tsine mana ai, waye zaiga haske a rayuwarshi kin gama kwashe mana Albarka. Kinga wata rana sai inyi ajalinki. Gasu ɗan Mama su da suke yanka kare su gasa su ci, mahaifiyarshi da yake mai tarbiyya ce kullum albarka take saka mana. Amman mu Baba ya auro mana uwa ƴar buyagi babu abinda ta sani sai ashariya, Mama in ku kai wasa fa wallahi duk zan sa kawunanku gabas in yanka." Yana dasa aya ya fice yana gauraye hanya, sai zage _zagen rashin mutumci yake yi. Ni kuwa tsaki naja na wuce na ɗebo ruwa a kofi na ƙarashe brosh ɗina, na koma ɗaki goya Yusuf nayi, na fito tsakar gida. Mama maganar atampopin Tafarkiya zata siyanne ko in kai kasuwa kawai? Banason mabaruka tazo tai ta aukin jirana, ni kaina na tsagu inje ai mun maganin Bulama da matsiyaciyar ƙanwarshi, zasu ɗanɗanama aya zaƙinta wallahi." "To kinsan Tafarkiya inta faɗi kuɗin kamar saukar wahayi bata ƙara ko sisi akai, in kina ganin zaki siyar mata a hakan da tace, ai sai in kai yanzu ta caske miki kuɗinki, nima da kuɗaɗe a hannuna duk sai a gagganɗa, na aro miki dubu ɗarin ma da kika ce." Cikin juyayi nace To Mama akai mata banda zaɓi, biyan buƙata yadi dogon buri. Mama ta shiga ɗaki ta ɗakko ledar kayan, ta haɗa da robar niƙan waken da take son yin alala ta fita. Nafisa na kalla tana zaune a tsakar gida tana faman chartting ɗinta na jaraba sai dariya take yi tana buga ƙafa. Duk yanda naso in gyara rayuwarsu sunƙi su hau layin seti, duk sun watsar da karatun dana tsaya a kansu nake son ganin sunyi, kowa ya shiga aikin ɓel_ɓel kawai, kuɗine suke shigoma Nafisa faca _faca, gabaki ɗaya ta canja, kalarta ta sake fitowa, hutu da gigewa sun kuma bayyana a tattare da'ita. Ko ba'ace ba da ganin buɗewar idanun Nafisa da irin mazan da suke mu'amula da'ita, nasan tuni ta jima da sallamar musu da budurcinta, karenta take ci babu babbaka kawai. Musa kuwa, tun Mama na faɗan mata da yake kawowa cikin gida su kwana, harta zuba mishi idanu kawai, gashi har ta kai za'a ajjiye mana ɗan dakan kuka a cikin gidanmu. Sagiru kuwa tuni ya jima da gagarar kowa. Ina cikin wannan tunanin Mabaruka tayo sallama ta shigo, idanu na zuba mata ina nazartar yanayinta. Har wata ƴar rama naga tayi, tayi wani zuru zuru da'ita. "Ƙawata yauwa kin shirya ko? Muje maza dan mu samu mu dawo yau" Mabaruka ni ko ba zamu dawo yau ba, in dai buƙata zata biya ai an gama. Kuma ai boka gangaranne kafi gwani, Mama nake jira ta kawo mun kuɗi sai mu wuce, ni ko ishasshen bacci ban samu ba." Muna cikin mamana Mama tayo sallama ta shigo, Nafisa kuma ta miƙe da gudu kafin ta ƙarasa magudana ta shiga sheƙa amai, tamkar zata amayar da ƴan hanjinta baki ɗaya. Murmusawa nayi, ai dama da ganin zaki zaici mutum, irin canjawar da Nafisa jikinta yayi dole da walakin, ashe wake ta ciyo, dole kuwa tayi kumburin ciki. Salati da tafa hannaye Mama ta shiga yi tana jijjiga kamar beyerabiya, cikin hanzari nace. Kinga Mama sanlameni mu wuce, uzirin dake gabana yafi na Nafisa, ita daɗine yai mata yawa. Dama bata shiryaba ta soma" Mama taja ajjiyar zuchiya, tare da miƙo mun kuɗina, ta shiga ɗaki ta tarkatomun ƴan kuɗaɗen hannayenta da wanda ta ciyo mun bashi, ba laifi kuɗin sun tashi sosai. Daga gida kai tsaye muka wuce television garej anan muka hau motar Jos, masu bi ta kafancan. Bamu daɗe ba motarmu ta cika, kasancewar ɗaya a gaba uku a baya suke sakawa, amman kuɗin motar yafi na kawo tsada. Cikin awa uku da rabi muka iso Jos, kasancewar hanyar taana da kyau ba irin ta samunaka ba. Bamu muka isa ƙauyan boka ba, sai gaba da azahar, bamu ci komai ba, sai atile da muka siya da masara a bakin titin shiga Maza. Mun tarar da cincirindon layi sosai, maza da mata. Muna zaune wani Alh ya fito yana ɗingishi, jini face face a bayan malum malum ɗinshi, da ganinshi wani babban mai muƙamin ne. Bai jima da fita ba, sai ga Hama ta fito. Ah Hama ashe rai kan ga rai? Sama da shekara guda ba ɗuriyarki, number ki a kashe in na gwada" Hama ta kama haɓarta halamar mamaki da jin daɗin ganinmu, ta dubeni tace. "Masha Allah, haihuwa kika yi kenan Zubaina?" Dariya nayi duk da ina cikin damuwa da tunanin lalacewar da ƴan uwana suka yi. Haihuwa nayi hama na samu Yusuf gashi a baya" Daga nan muka ɓalle da hirar yaushe gamo, ita kanta Hama abubbuwa da dama sun caɓe mata fiye da tunani, gashi duk wani arzikinta ya ƙare, harma an sako mata ɗiyarta ɗaya tana gabanta tana zawarci. Nisawa Hama tayi bayan mun gama bata labarin halin da muke ciki, tace. "Shi zuwa wajan boka ko ƴan bori akwai biyan buƙata, sai dai bazaka taɓa yin arziki ba, sabida kullum a cikin matsaloli kake baka da aiki sai na samun biyan buƙata. Gashi bin bokaye tamkar sigari ko goro yake baka iya denawa, har sai kaga abinda ya ture ma buzu naɗi. Amman wannan karon tarwatsa gidan zanyi gabaki ɗaya, ni in zauna ni kaɗai ya fiye mun, na gaji da wannan yaƙin,na kashe kuɗi sosai yau, sabida aikin boka kullum a cikin ƙara farashi yake. Ƴan siyasa da masu neman duniya kullum kuma lalatashi suke yi, amman aikinshi ba dai yayi, baki samu abinda kike so ba. Mabaruka tace. "Sosai kuwa Hama shi yasa ni bana jin tsadar ma wallahi, tunda zaka samu biyan buƙata, bokayen ƙaryar ma ai tsada garesu, sai rashin biyan buƙata yadda kake so. Ai ni kaina Adam a wannan karon sakin Sagira zaiyi kawai in huta, na gwammaci in ɗauki ƴar aiki, ko da kuwa ni zan dinga biyanta. Da ƙyar Hama ta yakice hira tai mana sallama, tare da bamu sabuwar lambarta, dan waccan wayar tace sace mata ita akayi. Bamu muka samu shiga ɗakin Boka ba sai wajajan bayan la'asar. A gurfane muke a gabanshi, muna shigowa ya soma yima matarshi yare yana nunoni da ɗan yatsa, take naji jikina ya soma rawa dan bansan hau ɗin da zata hauni ba. Matar boka ta dubeni tace. "Yace a faɗa miki akan mijinki da kishiyarki kikazo, domun a lalata musu rayuwarsu. Sai dai abunda baki sani ba shine tun daren jiya ya turo miki da saƙon saki a wayarki ya sake ki saki biyu. Yau kuma suka wayi gari da gobara babu abinda suka ɗauka a gidan, dan haka sai dai in kina son komawa gidanki sai kiyi bayani" Zuface ta wankeni tas, wani irin duhu_ duhu nake gani, gabana sai harbawa yake yi. Ni Bulama zai saka haka kawai a kyauta? Tabb lallai na yarda da tsubbace_ tsubbacen Kanuri da ake faɗa yau, yarinya ƙarama lokaci ƙanƙani ta rushe mun duk ƙoƙarina na sama da shekaru. Tabb yau ake yinta ana dara ga dare yayi. Tunani na shiga mai mugun zurfin gaske, domun ina son yin nazari shin in koma gidan Bulama da ƙarfin asirine, ko in rabu dashi kawai in buɗe ma kaina wani kyakykyawan shafi na sabuwar rayuwane? Yanda nake da ƙuruciyata da dirinnan, kuma rayuwa ai yanzu na soma, naga zawarawa suna gara zarensu yanda suka so, har su kanyi dace da mijin daya kere mijinsu na baya ma. Yanzu Bulama ba koman komai bane fama da takauci yake yi, gandirobane ba wata tsiyar ba, ni ina ganin rabuwa dani da yayi tamkar wata ƙofa ya buɗa mun ta ginin sabuwar duniya. Ta wani fannin kuma ina gani tamkar na faɗi babu nauyi in har Yahanasu da iyayen Bulama suka samu abinda suke so. Wani shashe na lokon zuchiyata shi kuma sai hasko mun yarana yake yi. Yanzu haka zan tafi in barsu su kaɗai, zasu taso ba tare dani ba, yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu da mama ba lallai bane su Maryam su shaƙu dani fa ko? Daɗiin abun haushin shine, duk tarin tulin tsadaddun suturuna wannan matsiyaciyar ta bunka mun wuta sun ƙone, dan ina da tabbacin dan sabida ɗakina ya ƙone ta kunna wutar dama sun ƙone dukka gidan uban kowa ya rasa" "Zubaina meye haka wannan tunani haka har an kammalamun aikina amman sai faman karanta wasiƙar jaki kike yi. Ki faɗi abinda kike so mu tashi mu kama hanya" Mabaruka ce take yi mun magana, nisawa nayi na kalli uwar gidan boka nace. Bana buƙatar komawa gidanshi, tunda har ya sake ni. Amman inason a sashi yaita asara duk abinda ya taɓa ya lalace, dukiya ko nawa ya samu ya zama mai rariyar hannu, tunda ya yageni a jikinshi, yaita cin karo da bala'en iri daban daban kawai" Wawuyar ajjiyar zuchiya ce ta ƙwace mun wacce bansan dalili ba. Wata laya boka ya miƙo mun, Mabaruka ta amsa ta bani. Bai jima yana magana ba uwar gidan boka ta dubeni tace. "Wannan layar aikinta yana da laulayi sosai sai kin kula. Ki samu titi mai fuska huɗu ki tsaya a tsakiya, sai ki saki layarnan a tsaye ta faɗi, cikin dare amman zaki yi. In dai kika yi hakan shi da arziki sai dai yaga anayi. Kuɗinki dubu ɗari da ashirin" Kai wannan boka akwai shi da tsadar aiki gaskiya, sai dai fa akwai shi da aiki gaskiya. Dubu ɗari da ashirin ɗin na ƙirgo na miƙa mata. Muka fito daga cikin ɗakin. Wani irin ƙududun takaicine ya tokare mun maƙoshina da ƙyar nake haɗiyan kakkauran yawu. "Yanzu Zubaina shikenan yarinyarnan ta ƙone miki kaya ta ƙone banza kenan, babu wani hukunci da zaki ɗauka akan hakan?" MRS BUKHARI CE 😍🤍🤍🤍🤍 MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 19 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* murmushin ƙeta nayi ma Mabaruka, duk da zuchiyata zafi take yi mun nace. Habawa Mabaruka ai kowa yaci tuwo dani miya yasha. Duk hukuncin da zan ɗauka a kansu, ai a bayan wannan layar da boka ya bani ne. Babban burina shine inga Bulama tsiya na binshi, ya lalace rayuwarsu ta tagayyara ai shine kawai. Ƙaddara da rabon ƴaƴa shi ya haɗani da Bulama, da kuma ƴan canjin hannunshi, da maiƙon gidansu. In bacin wannan me zai haɗa kifi da kaska, baƙi mummuna dashi, fuskarnan tashi kamar tuwon dare, muni kuwa tamkar a yanka a ɓoye wuƙar. Yanzu kuwa ya bani damata da zan cashi zawarcina yanda yai mun, miji kuwa sai wanda ya isa zan aura, inda zan shiga in baza mulki na. Babban cutar da Bulama yai mun shine daya sake ni da ɗanyan jego sharab. Bansan ma ya idda ta zata kasance ba, tunda ni bana jini har sai nayi yaye ma." Mabaruka tace. "Tabb ai kuwa Bulama ya gama dake, dan wallahi naji fatawa akan haka a karatun Malam Aminu daurawa, cewar duk macen da aka saketa, sai sakin ya zamana tana da ɗanyan goyo, kuma in tana goyo bata jini, bazata ce ta ƙirga wata uku shikenan ta fita daga iddarta ba. Har sai ta jira ta soma jinin nan tukunna tayi jini uku sannan ne zata iya yin aure. Harma yayi bayani akan wata mace da ta rubuto mishi tambaya akan mijinta ya saketa, to ita kuma a shekara sau ɗaya take jinin al'ada, tana tambayar ne dan tasan ya iddarta take. Ya tabbatar mata dole sai ta jira wannan jinin tayi shi sau uku, shekara uku kenan sannan ta yi aure. Kinga kuwa Bulama ya cuceki, aini sona shine da zaran wata ukun iddarki ya cika sai yaji kinyi aurenki, amman kash, amman fa ƙawata gara da kika yanke hukuncin barin Bulama ." Dariya nayi. Haba Mabaruka ai babu komai a hakan ma, ƴan watannine ko shekara da da ɗoriya ai, kamar yaune. Tsugunne ai bata ƙare ba, tunda zanje wajan malamai su sanar dani hakkina daya rataya a wuyan Bulama a matsayina na mai shayarwa daya sake ni, inta kama ma sai in kaishi kotu in dai zai mun gardama. Ɗan tasha fa ɗaukar kaya kawai zai nuna mini." Haka mu kaita faman tattaunawa har muka fito daga wannan ƙungurmin dajin. Sannan kuma muka nufi tashar mota, sai magriba motar mu ta ɗauki hanya. Bulama: Da sallama muka shiga cikin gidan maƙotanmu, bisa jagorancin yaron gidan. Da Hajara mu ka ci karo tana zaune tana ba Anisa, da Maryam tuwo a baki, suna saye da kayan makaranta daga su har Zulai. Bawa da Mustapha suma tuwon suke ci. "Sannunku da shigowa ƴaƴannan" Cewar Baba tsohuwar gidan. Cike da girmamawa muka gaisa tare da yi mana jaje. Ni tunanina da burina bai wuce inga Yahanasu ba, idanuna suna kwaɗayin ganinta. Maryam ta miƙe ta faɗo jikina bakinta duk miya, sai ta saka kuka tana kiran sunan mamanta. Ƙur na ƙura mata idanu tausayinsu na huda ni. "Ina Yahanasu Hajara, ya kuma yanayin jikin nata?" Ahmad ya tambaya. Idanuna na lumshe a hankali. "Da sauƙi sosai, ai wani bala'in ya kan kori wani bala'in da gudu. Ta fita shago siyan magani, aron kuɗinma tayi a wajan Baba, kai Yahanasu bata jin daɗi, har tangaɗi take yi fa kamar wata mai shaye shaye." Muna cikin zancan sai gata tayo sallama a tsanaki. Idanu muka haɗa naji wani abu ya shigeni yar. Sannunku Yaya Ahmad kun dawo?" Ta faɗa a sanyaye, muryarta a dashe sosai. "Mun dawo Yahanasu, sannunmu fa, Allah ya auna mana arziki babu wanda ya jikkata, sai asarar dukiya da akayi kawai, wannan kuma dama nemota akayi, za'a nemo wasu da izinin Allah" Waje Yahanasu ta samu ta zauna kanta a ƙasa, da kyar na buɗe baki nace. Dukkannin wata ƙaddara da take samun bawa a rubuce take, wayo ko hikima ba zasu kuɓutar da bawa ba. Kuyi haƙuri a bisa yanda kuka tsinci kanku baku da ko zanen ɗaurawa, wata rana sai labari. Dole zuwa gobe zamu tattara mu je gida, ko da ku ɗinne mu kai ku, sai mu mu dawo, ɗan abinda aka gagganɗa muka kama muku haya sai kuma ku dawo. Karatun yaran ma dole zai tsaya tukunna." Babawo ne ya dawo inda muke a tsaye yace. "Bulama akwai ɗaki biyu a zaure na samarine zaku iya amfani da ɗakunan ku da iyalan naku, in yaso su yaran akwai ɗakin yara a cikin gida sai su kwanta, kafin kuma ku gama shawarwari a tsakankaninku. Muje ku ga ɗakin kafin mu wuce masallaci." A baya muka bi Babawo ya nuna mana ɗakunan harda katifu a ko wanne ɗaki, sai ɗan karen datti abunka da ɗakin samari. Komawa cikin gidan yayi ya sanar da iyalinshi ta taya su Yahanasu gyaran ɗakunan, mu kuma muka wuce masallaci. Bayan mun idar da sallar magriba kuma jama'a suka taru akaita mana jaje, masu taro masu sisi sai bamu suke yi. Harda masu suturu namu dana mata, da yara. Haƙiƙa musulunci akwai daɗi. Haka zalika zama da maƙoci cikin aminci da amana akwai daɗi, munga haɗin kai da soyayya irinta malam bahaushe mai ɗaukar damuwar wani tamkar tashi. Har bayan isha muna ta karɓar jaje daga manya da matasan anguwa, ni kuma zuchiyata tana wajan Yahanasu babu abinda nake son ji ko gani sama da muryarta, da ganinta a kusa dani. Tara saura muka samu shiga cikin gidan niƙi_niƙi da ledojin kayan da aka bamu. "Ahmad kai ka riƙe na hannunka ɗin, wannan ya ishemu." "Ah ba'ayi haka ba Bulama ai" Ban ce mishi komai ba na soma sallama a ɗakunannan dan sanin inda matayen namu suke. Ɗakin dake kusa dani shine ɗakin da na jiyo amon muryar Hajara tana amsa sallamarmu. Can inda Ahmad yake kuma kenan a nan Yahanasu take, duk da banji amon muryarta ba. Har zan shiga ciki Ahmad yace. "Aff ni na mance, iyayen Zubaina sun nemeka danjin ba'asin abinda ya faru har ta kai ku ga saki kuwa?" Tsaki naja nace. Ana ta kai wa yake ta kaya? Bana tunanin ko a mafarki zasu kira danjin me ya haɗamu, karfa ka mance ni gandirobane yanzu, mai ƙaramin albashin da bai taka kara ya karya ba. Akan me zasu kirani? Alhalin yanzu daga iyaye har yaran auren kwaɗayi kawai suke yi. Ahmad ni wallahi bana buƙatar da wasa iyayen Zubaina su kirani a waya ma, dan zan iya zaginsu" Dariya Ahmad yayi har yana girgiza kai. "Mai da wuƙar goga na kofur Zubaina ba da kan ka a sare kaje gida kace ya faɗi, sai da safe, ka gaishe da Yahanasu da jikinta" Yahanasu: Ina kwance shiru ina karanta wasiƙar jaki, duniya tayi mun ɗaurin lemar minti, al'amura sai caɓewa suke yi daga ɓangarena, bala'i ina cikin wannan sai wannan ya faru. Na yarda da ƙaddara, amman kuma ban isa ince bana cikin damuwa ba. Ba abu bane mai daɗi ace kayi gobara ka rasa dai dai da zanin ɗaurawa. Ni ina ganin bakin da Ba Bakura yai ma Bulama Babba akan dukiya da duniya shi yasa wannan abubbuwa suke faruwa damu a jejjere, dan fishin iyaye da zubar hawaye su masifa ce babba a garemu. Sallamar Bulama Babba na jiyo da sauri na shasshare hawayen dake zuba a idanuna. Yana shigowa ya zuba mini idanu cike da kallon tuhuma. Ni kuma da sauri na tashi naje zan karɓi ledojin hannunshi. "Ki barshi Yahanasu ke da baki da lafiya" Naji ya faɗa da wata muryar da bansan ya mallaketa ba, dan nasan muryarshi girma da kauri gareta. Dan bana mance sanda yake daka mana tsawa duk mu furgice tsabar kaurin muryarshi. A hankali na juya na koma inda nake. Shi kuma ya tattako ya zauna a kusa dani daf, jikinmu yana gugar na juna. "Kin samu kinci abincin, ko kuma akwai abinda kike buƙatar in nemo miki ki ci?" A'a bana buƙatar komai, naci abinci" "Maganin me kika fita siyowa da kika kasa bari sai na dawo na siyo miki? Ke da baki da kafiya haba Yahanasun Ba Bakura " Ɗan Murmushi nayi mishi kawai. Na jawo kwanon tuwonshi na dure a gabanshi. Ga abinci kaci" Kai ya girgiza mun "Abinci bazai samu gurbi a cikina ba Yahanasu. Bari ina zuwa kinji" Bai jira na amsa ba ya fice. Bai wani daɗe ba sai gashi da leda ya shigo. Balangu ya miƙo mun a ƙunshe a leda, shi kuma kunu naga ya ciro a leda ya soma sha. Da ganinshi a cikin tsananin damuwa yake sosai, idanunshi sun kuma rinewa sosai. Tsoka biyu naci balangunnan na ƙunshe shi, na adanashi a gefe guda. Kowa yayi shiru yana tunanin rayuwa, kowa da abinda yake saƙawa. Bulama Babba sai jan carbi yake yi daga zaune inda yake. Sannu hankali bacci ya gagari idanuna, a hakan ma na shanye kwalba guda na maganin tarin yara, na haɗa da ƙwaya guda biyu na haɗiye, amman idanuna tamkar an soya gyaɗa, kaina sai shirin tarwatsewa yake yi. Ina kwance Bulama ya ɗauki Qur'ani mai girma da ya gani a ajjiye, nan ya soma karatu da ƙira'ar alaramma Sulaiman sa'ed. Bashi da niyyar bacci, nima Allah nake ta ambato ina ta hailala. Ƙarfe ɗaya ƙarfe biyu, nima ba shiri na miƙe zan fita waje, yana kai aya yace "Ina zaki a cikin darennan Yahanasu?" Cikin rauni nace mishi. Alwala nake son in ɗauro, zanyi sallah. Bacci ya gagari idanuna, gashi kaina kamar zai tarwatse." Ƙur ya zuba mun jajayen idanunshi yana karantar yanayina. "Muje in raka ki to" Banyi jayayya ba, muka fito a tare, ya raka ni har ƙofar bayan gida na shiga bakina da adda'ar shiga ban ɗaki. Ina fitowa na ɗaura alwala, muka koma ciki. Hijabin matar Babawo data bani kyauta na saka, na ta da sallah, shi kuma yaci gaba da rera karatunshi a hankali cikin nutsuwa. Haka muka raya darennan da ibada, har zuwa asuba. Hannu na ɗaga na dinga ragargazo mana adda'a, mafi yawan adda'ata akan Bulama Babba take. Dan har ga Allah, tausayinshi na shirin fin ƙarfin zuchiyata, ni da na zauna tare dasu, nasan cewar ba banza haka Zubaina ta barshi ba, duk abubbuwan da yake yi baya cikin hayyacinshi domun ba haka halayyar shi take ba sam. Nutsuwa sam bata tattare dashi, wani irin suru_suru ta mayar dashi. Amman alhamdulillah Allah ya share mana hawayenmu, kuma ba zan gushe ba, wajan riƙon Allah ya shiga takaninmu da zubaina, da mugaye irinsu. Ina roƙon Allah ya kuɓutar dani in dena wannan shaye_shayen, nima ba a son raina bane. Amman nasan su ummu naheeba ba zasu fahimci halin da nake ciki ba. ( Note BARI IN YI MUKU TUNI, YAHANASU A CIKIN DEEPRETION TAKE KAR KU MANCE, SHI KUMA SHAYE_SHAYE BA KAMAR SHAN RUWA BANE DA ZAKA SHA A SANDA KA GA DAMA KA ƘI SHA A LOKACIN DA KA GA DAMA BA. WANNAN YANA DAGA CIKIN JARABAWAR YAHANASU, MATSI DA TSANANI YANA JEFA MUTUM A CIKIN MUMMUNAN YANAYI. KUMA MU SANI DEEPRETION CIWO NE WANDA YAKE IYA JUYARMA DA MUTUM ƘWAƘWALWA, KUGA MUTUM YA KASHE KANSHI, KO YA KASHE MIJI KO ƘAWA, KO YA FAƊA SHAYE_SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI. KUMS ABUNE WANDA IN AKA SHIGESHI FITARSHI YANA DA MATUƘAR WUYAR GASKE KUYI MATA UZIRI, NAJI ƘORAFE ƘORAFENKU) Kaduna Kofur Zubaina: Bamu muka iso Kaduna ba sai wajajen sha ɗayan dare. Mabaruka ta nufi gida, nima na dawo gida. A tsakar gida na samu Mama a zaune, ita kaɗai, cikin muryar bacci tace . "Zubaina kece da darennan me yasa baku kwana acan ba?" Zama nayi a kusa da'ita nace "Mama ke kiji ashe ɗan akuyarnan sakina yayi? Sai da muka je wajan boka yake faɗa mun. Ita kuma matsiyaciyar matarshi ta bunka ma gidan wuta, komai ya ƙone ƙurmus. Amman ina zuwa tunda akwai wuta bari in jona chaji in kunna wayar, inason ganin sakin ne" Nan na bar Mama tana ƙunduma ruwan zagi, tana tafa hannaye. Ɗakin babu kowa, da halama ma Nafisa bata gidannan. Wayata na saka a chaji, na sauke Yusuf dake ta faman bacci, a gado na shinfiɗeshi. Na dawo gaban wayar na kunna. Tana gama kunnuwa kuwa, sai saƙon Bulama ya shigo. Karantawa nayi, na ɗanyi Murmushi. Bulama kenan, zaka gane kuranka, sai kayi ɗan daka ce baka sake ni ba." Wajan Mama na dawo" "Hmmm Zubaina saki fa kika ce, yanzu abinda ja'irin yaronnan zai mana kenan, zawarci bagatatan haka?. Amman to ya kuka yi da bokan?" Ni bazan koma gidan Bulama ba dai na farko. Gara in yi zawarcina Allah ya ɓullo mun da wani mai maiƙon yayi wuf dani. Ni zawarci bazai bani wuya ba, ina aiki fa. Babban baƙin cikina goyon da nake dashi ɗanye ne, amman dai gobe zan shiga layin dutse makarantar sha rubutu, in mishi bayani ko akwai wata fatawa da zan samu mai sauƙi. Mama Bulama tunda ya rabu dani, ya dinga ganin masifu kenan, aikin da boka ya bani inyi, ban shigo gida ba sai da na aiwatar dashi tukunna." Mama tace. "Ina baki kina roƙa. Yanzu da wanne idanu zan kalli munafukan anguwarnan Zubaina in har suka fahimci zawarci kike yi? Gashi zawarcinma na tsiya tunda ko kayan kirki baki dashi, muguwar kishiya ta bunka miki wuta. Ga jarabar iyayen yarinyar da Musa yai ma ciki. Ko ɗazu sai da na kai kuɗin abincinta nera dubu ɗaya suka yanke za'a dinga biya kullum , in ba haka ba kotu ta raba mu. Na nemi ragi ma wallahi sun ƙi. Ga iskancin Sagiru abun ya'isheni kullum a cikin gaggayamun maganganu yake, ga Nafisa itama ko da mu ka je asibiti ɗazu cikine da'ita. Amman har an zubar mata, amman kinga harta fice yawo tana jinin raɓe raɓe. Yanzu ya zamanki zai kaya tsakaninki da Sagiru?" Ana cikin haka kuwa sai gashi ya shigo yana fito, hannunshi riƙe da adda tsirararta. Wani mugun kallo ya watsa mun yace. "Me wannan la'ananniyar Allahn take yi a cikin gidannan da daddarennan bata tafi gidanta ba? Ke dan uwarki me kike yi?" Mama ce tace. "To nan dai gidansu ne itama, kuma kasan mijinta ne ya siya mana gidan ko? Aurenta ne ya ƙare dan haka ta dawo gida da zama ne." Addar nan ya karta a ƙasa yayi ihu yace. "Arne Allah ya kuɓutar dashi daga sharrinku kenan? Ke kuma zaki girbe abinda kika aikata, sharri ɗan aike ne, kuma haushin kare ne, bayan mai shi yake bi. Gara ni bana cutar kowa, duk abinda zanyi tsakanina da mahaliccinane. Kuma ki kula da shiga harkata, dan wallahi in kika mun yankaki zanyi in soya" Dan baƙin ciki in yi magana na kasa, kallonsu kawai nake yi shi da Mama suna hargowa ta faɗa ya faɗa, daga ƙarshe ya wuce ɗakinshi ya sake kaya ya fice. Sai lokacin Nafisa ta dawo, ta tulin uban kaya leda leda, sai wani yamutse fuska take yi. "Ba kui bacci ba Mama, lafiya na ganku cirko cirko Anty Zubaina?" Mama ta taso mata da faɗa. "Dan ubanki daga cire miki ciki yau yau shine zaki fita ɓel ɓel, baza ki ma bari ki warke ba, so kike a sake yi miki wani cikin ko? Dan kinga ina baki kariya, ai ko babu komai ya kamata ki zauna ki warke ko?" Maganganu Nafisa ta soma yi ma Mama, dama mun saba a haka Mama ta tarbiyyantar damu tun muna yara, sai abinda mu ka ce "Haba Mama in ban fita ba a ina zan samu kuɗin da zanyi buƙata dashi, ke kanki daɗin da kike ci wa zai baki? Yaushe rabon Asiya data turo miki wani kuɗi ishasshe? Ta kanta kawai take yi. Dama mai ƙoƙarin Anty Zubaina ce, to ita kuma karayar arziki ya same su. Mama ki barni in nemo mana kuɗi kici daɗi in kai ki makka kinji?" Baki Mama ta washe tace. "Allah ya amsa Nafisa da kuwa naji daɗi, ni fatana ko wacce in ganta cikin farin ciki, dan ku nake yin komai. Asiya kuma ai tana ƙoƙari fa Nafisa, kuma in ita bata ƙoƙarin ai mijinta yana yi. Kuma tayi mun alƙawarin umara da watan azumi in sha Allah." Ni nama kasa ce musu komai, damuwar dake gabana itace a gabana. Ɗaki na wuce na kwanta, sai wasiƙar jaki nake ta faman karantawa, na kasa sa komai a bakina. Bansan sanda ɓarawon bacci ya sureni ba. Sai jin kiran sallar asuba nayi. Tashi nayi zaune wuf dan kwanciyar duk ta isheni dama. Bayan nayi wanka nai ma Yusuf ma wanka. Gari na yin haske na fito da goyo a bayana, na shirya tsab. Mama ni zan fita, inason inje office in sanar dasu dawowata nan, kwana biyunnan nayi wasa da aikina. Can dai Kanon na kira na sanar musu ina cikin wata ƴar matsala ne. Kafin in shiga office zan duba Malam sha rubutu a makaranta, ina da fatawane" "Amman Zubaina ba kya tsaya ki karya ba tukunna, ƙaramin goyo ne fa dake, aini nayi tunanin rabuwarki da Bulama bazai jefa ki a ko wanne irin halin damuwa ba. Sai naga saɓanin hakan" Rausayar da kai nayi nace. Yaran nake tunawa Mama, yanzu shikenan na haifi yara, wata banzar bazarace zata moresu harma ƙila asa su mance ni na haifesu? Ni kinji abinda ya dameni har ya hanani bacci mai daɗi. Amman ko ɗar bana ji dan na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda. Da sauran ƙuruciyata fa Mama, bari in gama goyo kiga motocin da zasu dinga mun sintiri. Ke dai sai na dawo, zan sai cin cin a layin dutse, ko in sai ƙosan wannan matar ta bakin layin sabo da Allah." Sallama nayi mata na fice. A zaure na haɗu da Sagiru ya bangaji kafaɗata ya wuce yana fito. Ba dan sauri nake yi ba, da zan tsaya muyi uwar watsi ni dashi, dan ba tsoronshi nake ji ba, a matsayina ta Kofur. Ina fita cikin layi,. Munafukai suka soma tambayata yaushe a gari, harda masu tambayar ina na baro motata. Babu wacce ta samu amsar abinda take son ji munafukai kawai. Ƴar ƙumbula na hau ta sauke ni a dai dai layin dutse dandali. Ta cikin layin na ratsa har zuwa makarantar malam sha rubutu. Almajirinshi yai mun iso har cikin gidanshi, wajan matanshi. Izini matar malam ta bani, na shiga ɗakinshi yana zaune akan buzu yana rubutu a jikin Allo. "Meke tafe dake yarinya? Ki yi mun bayani ina sauraronki." Zama na gyara tare ta bashi labarin sakina da Bulama yayi da ɗanyan goyo. Malam ni so nake in san yaya maganar iddata take, ni dai in ina shayarwa bana yin al'ada har sai yaro ya dena shan nono. To malam ya sake ni da ɗanyan jego ga shayarwa, yanzu yaya zanyi?" Malam sha rubutu ya dubeni da kyau yace. "Haƙiƙa bai kyauta ba da ya sake ki da ɗanyan jego. Dan gane da maganar idda kuma, a zahirin gaskiya tunda ke yarinyar mace ce kina yin jinin ba wai bakya yi ba. Dole zaki jira har zuwa sanda zaki yi yayen. Tunda kina yin jinin bawai kin wuce munzili bane. Sai kinyi wannan jini ukun sannan zaki yi aure. Sannan ratayayyen hakkine a wuyan shi uban ɗanki ya ciyar dake sabida yaronshi ta jikin ki yake cin abinci, in bashi da lafiya shi zai bada kuɗin magani. Dan da so samu ne a ɗakinshi zaki zauna kiyi iddarki kamar yadda Allah yace, har sai kinyi yaye kin kammala iddarki sannan sai ki tafi gidan iyayenki kuma" Wata sassanyar ajjiyar zuchiya na sauke, domin har na hango irin gara Bulama da zanyi dan wallahi sai na gigita rayuwarshi da bani bani. Bazan je gidanshi in zauna ba, gashin kaina nake son ci. Godiya nai ma malam, tare da kawo ɗan abun hasafi na bashi. Office ɗinmu na nufa, naima D P O bayanin mutuwar aurena. Ya jajanta mun matuƙa, kuma yaji daɗin dawowa da nayi, sabida ina bada gudunmawa sosai akwai ni da jajircewa akan aiki. A ranar dai ban shiga office ba, sai gobe nake son komawa bakin aikina, in D P O ya gama tattaunawa da na sama dashi kan batun transpa da akai mun da. Kai tsaye na wuce gidansu mabaruka. "Yanzu nake shirin kiranki a waya ƙawata. Hmmm aikin gama fa har ya gama. Yanzu na gama waya da Adam." Zama nayi daɓas a kujera babu kuzari sam a jikina, tunanina taya zan zauna a gida har na tsawon shekara ɗaya da rabi, ba tare da naji ɗumin namiji a kusa dani ba. Mabaruka tace. "Adam yana son ya mayar dani ɗakina. Amman na bashi sharaɗin sai ya saki matarshi, ya turo mun da copy na sakinta, sannan zan koma kuma ya shirya mun kayan ɗaki. Ai ƙawata a ƙasa zan jashi tamkar yanda kare yake jan mushen nama". Dakata Mabaruka naki duk mai sauƙine maganar kome kuke yi. Nifa sai na shekara ɗaya da kusan rabi zan yaye Yusuf sannan in jira in soma jini, shims Sai nayi wata uku, sannan kuma fa zan soma zance ayi batun aure. Ta yaya zan iya riƙe kaina na iya waɗannan lokutan ba tare da ana mun ban ruwa ba? Yanzu daga wajan malam sha rubutu nake, ina zuwa bari in kira Bulama in huce akanshi tukunna" Wayata na ciro a jakata na danna kiran layin Bulama amman harta tsinke bai ɗagaba, kuma kiranshi nayi ruri ɗaya zuwa biyu ya ɗaga wayar, ban jira yace komai ba nace. Na raina saki biyun da kayi mun. Da ace ka haifu cikin Bakura da Hajjagana da saki uku za kayi mun, kaga ba kare bin damo. Sannan ka sani hakkin ci da sha, da lafiyata yana hannunka har zuwa lokacin da zan yi yayen Yusuf in gama iddata. Dan haka nera dubu biyu zaka dinga turo mun a rana. Sannan naji ta'asar da matarka tai mun kishi yasa ta bunkama gida wuta, babu abunda zance sai abinda kukai mun Allah yai muku." Murmushinshi yayi mun cikin ƙatuwar muryarshi mai kama da sautin duro yace. Ke ma jahila kika san da wannan hakkin a kaina, ballantana ni mai sittin a kaina. Jahilci mugun ciwo, mai kashe rayuwa. Dubu biyu da kika yanka mun bazan ce zaki samu ba, dan ko kotu kika kaini sai alƙali ya soma da tambayar albashina. Zaki dinga ganin Alert na abinda ya sauwaƙa.... Ƙit ya kashe mun wayata, a madadin in bashi haushi sai shine ya cunkusamun baƙin ciki, yasa kwakwalwata ta cinkushe na rasa tunanin da zanyi. Kuka na fasa tare da ɗaura dukkan hannayena aka, kuka nake yi wi_wi tamkar zararriya. Da ƙyar Mabaruka ta dinga rarrashina harta samu kaina." Yahanasu: Misalin ƙarfe bakwai a tashar mota na anguwa uku yai mana. Bamu jima ba sosai motarmu ta cika muka ɗauki hanya. Kaina wani irin yam_ yam_ yam kawai yake yi mini, daidai da motsi ko hayaniyar Maryam da take cinyata, bugamun ƙwaƙwalwata yake yi. Kayan aiki kawai nake son in afa ko ƙwaƙwalwata zata barni in huta. Bulama Babba sai aikin sannu_sannu yake yi mun, a tunaninshi ciwo nake yi. Idanuna suna lumshe na jingina kaina a bayan kujerar mota, hannun Bulama Babba na gugann kafaɗuna, jikinmu a manne yake sosai, kuma naji zazzaɓi kau a jikinshi dan jikin yayi matuƙar zafi. Ana cikin haka wayarshi tayi ƙara. Ina jiyo duk abinda Zubaina ta faɗa mishi, da amsar daya mayar mata. Dukkan wannan abun da ke faruwa idanuna a lumshe suke. MRS BUKHARI CE MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 20 A cikin motar nan sai hira suke gudanarwa, yayin da wasu suke ta ciye ciyensu. Mu kuma a baya kowa yayi shiru tunani ya cika mana kayukanmu. A ɗan wani ƙauye muka tsaya dan gabatar da sallar azahar. Tun daga cikin mota na hango wani ɗan kemis ƙarami, ajjiyar zuchiya na sauke, dole in faki ido inje in siyo maganin tari. "Miƙo Maryam ki fito Yahanasu, ki bi su Hajara gashi can mata na shiga cikin gidan masallaci suna Sallah. Bulama Babba ke mun magana daga ƙasa. Maryam na miƙa mishi, ni kuma na sakko a hankali. Muna haɗa idanu ya sakar mun ɗan guntun Murmushi, duk da da ganinshi a cikin matsala yake. Bakina yana rawa nace Dan Allah in akwai kuɗi a hannunka ka bani" "Me zaki yi da kuɗi? Cikin inda_ inda nace dashi. Kaina ne yake ciwo zan sayi magani" Baice mun komai ba yayi tafiyarshi. Hannun Maryam naja nabi ayarin matan cikin motarmu zuwa cikin gidan masallaci. A zaune nayi sallah dan ji nake kaina kamar zai tarwatse mun. "A masha Allah, Yahanasu an shiga ayarin ƴan laulayin ciki kenan. Allah ya raba lafiya" Hajara ce take magana tana washe mun baki. Da kallon takaici kawai na bita, na kama hannun Maryam muka fito, hannuna dafe da kaina. Mota na koma na zauna, hannuna dafe da kaina me barazanar tsagewa. A haka Bulama Babba ya shigo ya tadda ni. "Ga nama da yogurt ki daure kici, sai ki sha maganin ciwon kan ko? Kawo Maryam ɗin Zulai ta riƙeta, kiji da kanki. Ɗaukar Maryam yazo yi, hannunshi ya gogi ƙirjina sosai. Wata guguwa ta taso mun daga kaina ta rufemun idanuna, sai kawai jin idanuna nayi a lumshe. Shi kanshi da halama baisan ya saki ajjiyar zuchiya mai nauyi ba. Zulai ya miƙa ma Maryam, sannan ya ɓare maganin ya bani na kora da yogurt. Bayan kowa ya shiga mota muka ɗauki hanya. Kowa a cikin motar nan sai da ya taɓa bacci, Amman ban da ni, dan idanuna sun bala'in soyewa har wani yaji yaji suke yi mun, duk sun ƙanƙance. Wajajen la'asar sakaliya muka shiga Damaturu, jefin shiddan yamma muka shiga cikin gida ni da Bulama Babba da yara. Ahmad yayi mana sallama zaije ya ajjiye Zulai da Hajara a gidan mamanshi. Ajjiyar zuchiya na sauke dana ji ƙafafuna suna taka farfajiyar tsakar gidanmu, zuchiyata cike da zabarin son ganin iyaye da ƴan uwana. Shi kanshi Bulama Babba naga wani irin annuri a fuskarshi, duk da dai akwai tsoro a tattare dashi, ni kaina inajin tsoro shin wacce iriyar tarba za'ai mana ne." Hango su Ya Innana nayi ko wacce tana zaune akan tabarma a ƙofar ɗakinta, suna wannan hirar tasu da suka saba, sai dariya suke yi. "Oyoyo oyoyo Yahanasu Bulama kune tafe da yamma sakaliya haka? Cewar Ya Bagulaji kenan. Da sauri duk matan gidan suka juyo kowa ya zuba mun idanuwa. Muryar Ba Bakura muka jiyo a bayanmu yana cewa. "Su waye nan a tsaye kamar Yahanasu?" Hantar cikina ce ta tattake ta kaɗa, da sauri muka juyo ni da Bulama Babba. Ba Bakura ne da Ba Modu, sai Hajja a gefensu, Bulama fari kuma yana riƙe da jakar Hajja da key ɗin mota da ganinsu unguwa suka fito. Kallon kallone ya shiga tsakaninmu dasu na wasu daƙiƙu. Bulama Babba yana kallon iyayenshi cikin so gami da nadamar duk abubbuwan da suka faru. Su kuma sunai mishi kallo mai cike da kewar ɗan nasu a kusa dasu. Ni kuma Ba Modu nake kallo, shima ni ɗin yake kallo, kallon tausayawa da lallashi. Ba Bakura ne ya katse shirun da cewa. "Daga ina haka bagatatan ba sanarwa, da kunzo bama nan fa uhmm?" Turus dukkanmu mu kayi, Bulama Babba take ya soma zubar da ruwan hawaye, Bulama Babba sau ɗaya na taɓa ganin hawayenshi sai kuma yanzu. Dan ko sanda Kaka Yahanasu ta rasu, shine kaɗai bai zubar da hawaye ba, sai dai shine ya kwanta ciwon rashinta. "Ku fice mun da gani, har Yahanasun. Tabi mijinta tayi biyayya, bana buƙatar sake ganinka. Modu ka tabbatar sun bar gidannan, ke kuma Hajjagana wuce mu tafi ciki." Jiki a sanyaye tabi bayan mijinta sumi_ sumi tana kuka. Ba Modu na kalla. Shima mu yake kallo a tsanake, matan gida kuwa kowa yayi tsit dan abun ba nasu bane." "Yanzu sabida Allah Bulama me ya kawo ku cikin gidannan, kai da baka ƙaunar ganin danginka sun raɓeka? Ku kama hanya ku fita tun kafin dare yayi muku" Da sauri Bulama Babba ya isa wajan Ba Modu. Tsugunnawa yayi guiwarshi a ƙasa, amman ya kasa furta komai sai hawaye kawai yake zubarwa, tun yana hawaye har ya shiga kuka mai sauti, da ƙatuwar muryarshi. Hakanne ya jawo hankalin surukan gidan suka soma baro shashinsu dan gani da jin abinda ke wakana." Jikina a sanyaye naja ƙafafuna zuwa cikin gida. "Ina zaki je Yahanasu, ba kiji abinda Babanku Bakura yace ba ko?" Ya Innana ce tayi maganar cikin sarewa. Inason inga Ba Bakura ne kafin mu wuce" Iyakar abinda nace kenan, na shige ciki da sauri. Ko da nayi sallama ban jira an amsa mun ba na faɗa falon. Ba Bakura yana tsaye sai zazzagama Hajjagana faɗa yake yi. Ita kuma sai kuka take yi, ganina ne yasa duk su kai shiru. Zubewa nayi a ƙasa na kama ƙafar Ba Bakura. Ba Bakura ka yafe mishi dan Allah, wallahi ba laifinshi bane sharrin azzalumar matarshi ne. Ba Bakura kai ka hore mu da yin haƙuri, tare da yin afuwa ga duk wanda ya nemi yafiyarmu. Bulama Babba wallahi yana buƙatar adda'arku, da yafiyarku ko dan yaga haske a rayuwarshi. Abubbuwa da dama sun faru damu. Yanzu haka gidan da muke ƙurmus ya ƙone bamu ɗauki ko tsinke ba a ciki, dai dai da suturar jikinmu ƴan uwa musulmai ne suka bamu." Ina kaiwa nan na kuma fashewa da kuka mai sauti, zuchiyata sai sake tunzura kukana take yi. Tsit babu wanda yayi ko da tari, sautin kukana ne kaɗai yake tashi a falon, na tsawon minti uku. Daga bisani Ba Bakura ya ja nunfashi, a sanyaye yace. "Yahanasu ke kinsan komai da yake gudana a cikin gidannan, da irin watsar da mu da Bulama Babba yayi. Ga uwarshi nan kullum sai ta yi hawaye sabida shi, har da hotonshi take kwana, ta zaci ko ban sani bane ba. Hatta aiki da Bature ya sa aka bashi na gandiroba duk ina da labarin komai. Matsawar Bulama yana tare da matar shi, to ba zan yafe mishi ba." Cikin sarƙewar murya nace. Ya saketa ma Ba Bakura, ko gobarar data faru bata gidan ta koma gidansu" Hajja ta miƙe da sauri tace. "Alhamdulillah Allah na gode maka daka ƙwato mun ɗa na daga hannun wannan makirar azzalumar yarinyar. Allah kana ganin irin rikici da damuwar data haddasa a cikin wannan ahalin, Allah ka saka mana abinda tayi mana" Ba Bakura ya wani kalleta, babu shiri ta zauna. Murmushi yayi mata tare da girgiza kai, kallona yayi yace "Na yafe mishi Yahanasu uwata amman da sharaɗi" sujudur shukur nayi a tsakar ɗakin ina kuka. Ba Bakura yasa hannu ya ɗagoni tsaye. "Kukan yayi haka uwata, na yafe ma mijinki, amman ki sanar mishi ni bani da buƙatar ganinshi, bana son yazo inda nake. Allah yayi mishi albarka, kema Allah yayi miki albarka uwata kici gaba da haƙuri, naso ace zan iya cire kuɗi in miki wasu kayan ɗakin, amman kash bazan iya kashe muku ko sisin kwabona ba. Kuma na haramta a baku kuɗi ko wani taimako, ai shi jajirtaccene nayi imani zai kula dake, mun yi na mu, a cikin gidannan kullum a cikin adda'a muke akan Allah ya kuɓutar dashi daga hannun azzalumar matarshi. Duk juma's kinsan anayin sauka ayi sadaka nan ma kuna cikin addu'o'in mu babu dare babu rana." Godiya nayi ma Ba Bakura sosai a bisa yafe ma Bulama Babba da yayi, duk da banso sharaɗin daya gindaya ba, amman dole inyi mishi adalci, Bulama Babba yayi musu abinda ya cancanci fiye da haka, duk da ba cikin hayyacinshi yake ba, amman fa akwai zafi. Kuma babu wanda yaci dukiyarshi, sai Zubaina da danginta. Hajja ta rungumeni a jikinta tana jin wani tsananin farin ciki. Hannuna taja muka koma tsakar gidan. Dai dai lokacin da Bulama Babba ya kama hannun Maryam da Bawa suka juya zasu fita. "Tsaya Bulama" Hajja ta faɗa da murya mai ɗauke da sautin farin ciki. "Bulama fari ka shiga da su Bawa ɗakin Innana ko Bagulaji. Shi kuma wanku ka buɗe mishi ɗakin ka na da dashi da Yahanasu su sauka acan." Murmushi Ba Modu yayi yai mun kallon na kyauta kuma na burgeshi. Farin ciki naji sosai da naga farin ciki shinfiɗe a fuskar Ba Modu. Kan ka ce me matan gida aka soma nannan damu, matan su Bulama ƙarami kuwa kowacce sai tace ɗakinta zan shiga. Ni kuma burina shine su barni tare da Ya Innana mu ɗanyi taɗi irinna ƴa da uwa. Hajja tayi dariya tace. "Yalewa ku barta da shiga ɗakin gyatumarta ta huta, duk zata biku ɗai_ɗai ku gaisa, uwata maza je kiyi wanka kizo ki kaiwa mijinki abinci" Kunya sai ta kasheni a wajan. Shigewa ɗakinmu nayi ina dariyar murna. Gyara naga anyi ma Ya Innana sosai an sake mata komai na ɗakin, ina tsaye ina santi sai ga bulama ƙarami, da Dala, da Wakil sun shigo suna tsokanata. "Mummunar gidanmu kune a tafe? Munyi kewa" Cewar Wakil kenan sai dariya yake faman yi mun. Dala yace. "Kunzo a dai dai ɗazu matar Wakil ta haihu mun samu me sunanki, suna asibiti ma. Daga wajansu su Ba Bakura suka dawo, sanda suka same ku a tsakar gida. Amman kowa yayi farin ciki da haƙurin da Ba Bakura yayi, wallahi muna kewar Bulama Babba sosai, ɓuya fa muka yi sanda yake kuka kamar ranshi zai fita." Bulama ɓaki yace. "Tunda fa Ba Bakura ya soma fishi da Bulama Babba gabaki ɗaya gidan ya dena ma kowa daɗi, to Bulama Babba ai shine uba a gidannan." In banda murmushi babu abinda nake yi ma ƴan uwana, maganganunsu daɗi yake yi mun. Bulama Babba abin so ne ga duk wani yaro daya taso a cikin wannan gida. Domun ko wanne yaro ɗan gata ne a wajanshi. Barkar haihuwa naima Wakil cikin sakin fuska. Sai jana da hira suke yi. Lokacin sallah ne yasa dole suka fice zuwa masallaci, lokacin kuma Ya Innana ta shigo, kallon juna mu ka yi mu kai Murmushi ko wanne yana farin cikin ganin juna. "Kin kyauta da kika kawo ƙarshen wannan turka turka, wanda duk a sanadiyyar aurenki kaso mafi yawa ya faru Allah yayi miki albarka. Ki shiga ki watsa ruwa sai kiyi Sallah. Harna wuce Ya Innana tace. "Gobe kuke da niyyar komawa ne na ganku ba kayan sawa, kuma har yaran baku ɗebo musu kaya ba?" A'a bansan yaushe zai koma ba. Ni dai yace mun zai barni anan tukunna kafin ya nema mana wajan zama" A taƙaice na ba Ya Innana labarin gobarar da mu ka yi, da rabuwa da Zubaina da Bulama Babba yayi. Ajjiyar zuchiya ta sauke tare da cewa. "Babbar magana, to Allah ya kyauta ya mayar muku da arziki. Ki je kiyi wanka ki yi sallah. Ga abincin mijinki yana ɗakin Bagulaji sai ki kai mishi, in sun dawo masallaci." Cikin farin ciki nayi wanka a bayan gidan Ya Innana mai ɗumbin tarihi a gareni, na ɗauro alwala na fito. Wadrope na buɗe na ɗakko wata doguwar rigar Ya Innana ta shadda blue na zura, na saka hijabin sallanta na ta da sallah. Ina kan sallaya a zaune na gama azkhar kenan na jiyo sallamar Ba Modu da Ya Innana. Zama yayi a bakin gado, muka gaggaisa cike da kulawa yake kallona. "Yaya kuka yi da Ba Bakura ne Uwata. Naji dai batun gobara, da batun sakin waccan sheɗaniyar yarinyar da Bulama yayi. To amma Bakura ya wakiltani in sanar ma yaran gidan dai dai da allura bai yarda a ɗauka a ba Bulama da sunan taimako ko wani abun ba. To inason jin yadda ya ce miki ke" Jikina a mace na bashi labarin abinda Ba Bakura yace mun. Ya Innana tace. "To amman ni malam ina ganin da anyi haƙuri an tausayama yaronnan, hannunka bafa ya ruɓewa ka yanke ka zubar." Ba Modu ya dubeta ƙur yace. "Kina son a taimaka musu kenan ko sabida Uwata yake aure ko?" "Bance a taimaka musu da kuɗi ba, amman ko da aikine a nema mishi wanda zai iya riƙe gidanshi dashi. A duba lamarin yaronnan fa, yaro mai tausayin kowa, mai hannun ungo. In hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi." "Ya isa Innana, ki bar yaro ya nema da kanshi kamar yadda ya samu a baya ya kula da iyalinshi. Bazan iya ja da Ba Bakura ba. Kuma ki sani duk irin so da ƙaunar da nake ma Bulama ba kamar yadda Bakura yake son shi da ƙaunarshi bane, kuma bazai ga abinda zai cutar da shi ya zuba idanu ba. Kaza tana taka ɗanta ne ba dan bata sonshi ba, tsawatarwa ne. Sau nawa Bakura yayi kuka ya kasa bacci akan Bulama? Harfa asibiti ya kwanta, meye Bulama bai yi ba a gidannan ba? Kema na baki umarni ban yarda ki ɗauki kuɗi ki ba Uwata ko Bulama ba. Na yarje miki ki bata sutura inma naki, inma ki ɗinka mata sababbi, ɗan zanin gado labule duk zaki iya taimakonta dashi, baya ga wannan ban yarda ki bata komai ba. Aiki take yi, shima yana aikin shi. Tayi ma mijinta biyayya su taru su rufama juna asiri, ni shine kwanciyar hankalina, duniyar guda nawa take Innana. Ke Uwata tashi ki je ki kaima mijinki abinci, sai ku tafi asibiti ku dubo matar Wakil. Kuma ki kwana tare da mai gidanki." Yana kaiwa ƙarshen maganarshi ya fita. Binshi Ya Innana tayi da sauri. Ni kuwa ina ɗago kaina na hango maganin tari a saman mirror ɗin Ya Innana. Ajjiyar zuchiya na sauke harda Murmushi, dan ji nake gabaki ɗaya kamar zan zautu. Zuƙe maganin nayi tas na jefa kwalbar a ƙarƙashin gado. Ina jiyo su Ya Innana da Ba Modu suna tattaunawa a kanmu. Sai da ya fita Ya Innana ta dawo. "Tashi Yahanasu ki je ki ɗauki abincin mijinki ki kai mishi. Kiyi haƙuri da jarabawar da kuka riski kanku a ciki. Ki riƙe adda'a, karatun Qur'ani, sallar dare, azumin litinin da alhamis. Ki dinga cire lokaci sosai kina ma mijinki adda'a Allah ya kare miki shi. Kar ki kuskura ki mishi iyaka da kuɗin albashinki, ki shiga cikin cefanen gida dumu dumu. Yaranki kuma karki bari suyi maraicin uwarsu, ki riƙesu fiye da yanda zaki kula da naki. Ki kasance mai sauƙi da sanyi a ko da yaushe. Kuma ki zama mace mai dabara gami da hikima. Zaki samu ɗaukaka a wajan mijinki, ki samu matsayi mai girman da ko da nan gaba zai ƙaro aure, to fa babu macen zata ture matsayinki a zuchiyar mai gidanki. Amman fa ki sani duk zaman lafiyan dake gidan aure, ba'a rasa jarabawa da saɓani a tsakani. Ki dai kasance mai mallakar kanki yayin da kike cikin fishi. Ki kasance mai tsawatar ma zuchiyarki, ba ita zata tsawatar miki ba. Tashi maza ki je ki same shi, ki kwantar mishi da hankali, yanzu ne dai dai lokacin da yafi buƙatar kulawarki fiye da ko yaushe. Karayar arziki fa bata da daɗi, shi yasa zaki ga waɗanda basu da tawakkali sai kiga sun haukace ma." Jikina a mace tulus na miƙe har zan fita Ya Innana ta dawo dani. Wani turare ta bani a cikin wata ƴar kwalba. "Ungo ki shafe duk jikinki da wannan turaren, kina Kanuri amman kin watsar da ƙamshi. Yahanasu ki kula fa. Ita zuchiyar ɗa namiji da kike gani, babu abinda take buƙata, sai sanyi, daɗi, laushi, sauƙi. Ai da ƙamshi zaki iya mallakar zuchiyar Bulama wannan ai babban sirrin matan ksnuri ne" Kunya duk ta rufeni ni kam. Shafe turarennan mai mugun sanyin ƙamshi nayi a jikina. Wasu garukan magungunane kwance a ƙasan kwalbar. Mayafi ta bani, na cire hijabin na yafa gyalen na fice." Ɗaki ɗaki na dinga bi ina gaishe da kowa. Har izuwa ɗakunan matan su Dala. A ɗakin matar Dala nayi sallar isha, sai da na tabbatar su Bulama Babba sun dawo sallah nayi mata sallama na fita. Ɗakin Ya Bagulaji na koma na ɗauki abincinmu wanda aka jera a babban tran silver na fito. Sai kunyarsu nake ji, kamar ba gidan da nayi rarrafe a cikinshi ba. A tsakar gida na tarad da Wakil da su Dala sun kewaye Bulama, sai hira suke yi a tsaye. Fuskokinsu cike da annuri. Idanu Bulama Babba ya zuba mun mu kayi kallon ƙuda na wasu sakanni, saini na zare idanuna a cikin nashi na sauke kaina. "Wakil karɓi trannan ka shigar mun dashi ɗakina. Sai kazo muje asibiti mu dubo madam ɗinka" Wakil ya karɓa ya shigar da abincin ciki, mu uku muka shiga mota zuwa asibiti. Ina baya shiru, Bulama Babba da wakil sai zuba hirarsu suke yi, har muka isa asibitin. A kwance muka samu me jegon amman ba bacci take yi ba. Yarinyar kuma tana hannun Yanunu. Yanunu tana ganinmu ta washe bakinta. "Kadunawa kune a tafe, lallai wannan yarinyar da halama zata yi goshi" Dariya nayi nace. Takwarata tayi kira ai dole inzo ayi shidimar suna dani. Yanunu ina wuni?" "Lafiya lau ƴar albarka, kun zo lafiya?" Bulama Babba ne ya gaisheta, faram_faram ta amsa mishi. Me jegon muka yi ma ya jiki, na ɗauki baby. "Kin ganta ko Yahanasu, takwararki ce" Yanunu tace. "Takwarar takwararta dai. Karma ka rufeta" Dariya mu ka yi dukkan mu. Bamu jima a asibitin ba, mu kai musu sallama. Idanuna a rufe suke zaune nake a bayan mota, babu abinda nake son sha sai ƙwaya, ita kaɗaice zata sauke mun wannan hayaniyar da taima kaina yawa, kwakwalwata har wani tsalle take yi mini. Muna shigowa gida, nayi tafiyata ɗakin Ba Bagulaji, inason in kwanta. Amman har ɗakin Ba Modu ya biyoni yace in fice in je in samu mijina. Yunwa kamar zata kasheni, amman bana sha'awar komai face in afa ƙwaya. Sum sum na fito, Ya Innana ce ta kirawoni, rigar bacci sabuwa ta yage ta bani. "Shiga kiyi wanka,ki zo ki sa ki je ku kwanta. Kinci abinci kuwa?" Sai kai kawai na iya girgizawa kunya ta hanani magana. Wanka na shiga nayi, na goge bakina da sabon brosh da na gani a bayan gidan. Rigar baccin na zura, bayan na shafe jikina da turaren humra. Rigar doguwace har ƙasa, hannun rigar yana da ɗan tsayi ba laifi, rigar tana da santsi sosai. Mayafi na saka na fita ina zunɓura baki. Ko da na je ƙofar ɗakin sai naji gabana yanata bugawa, daurewa nayi na shiga. A zaune yake hannunshi riƙe da ƙaramin Qur'ani yana karatu amman a zuchiya yake yi. Amsa mun sallamata yayi yana mun Murmushi, gefe na samu na zauna a takure, na kasa cewa komai "Kinci abinci?" Girgiza kai nayi halamar a'a. Baice komai ba ya matso kusa dani, tare da tran abinci. "Babu abunda zance miki sai dai ince miki Allah yayi miki albarka. Haƙiƙa na yaba da ƙoƙarin da kika yi a kaina wajan shawo kan Ba Bakura, har ya yafe mun. Nasan duk abinda suka faru a baya ba masu kyau bane. Wai nine da kaina na wulaƙanta Ahalina, iyayena ƴan uwana. Ina gani ruwa na dukan iyayena, hawaye na gangarowa a kumatun mahaifiyata, wacce bata iya bacci mai kyau a sa'ilin da nake ɗauke a cikinta, tai ta rainona cike da farin cikin son ganin na wanzu a duniya a matsayin mallakinta. Tasha zafin naƙudar haihuwata, kashi fitsari, kukana, hanata bacci. Amman wata mace tazo ta shiga tsakanina da'ita. Zubaina ta cutar dani wallahi. Hawayene ya shiga sunturi a kumatunshi. Ka dena kuka, ka yawaita istingifari, sannan ka dinga yawan kiransu, ka basu lokacinka domun kawanke musu zuchiyarsu, duk ɗan abun da ka samu ka tsakura musu duk da nasan cikin yalwa suke, amman naka na neman albarka ne. Ɗago jajayen idanunshi yayi ya zuba mun. Nima shi nake kallo, ƙare mishi kallo nayi, naji tausayinshi na ratsa ni. Hancinshi na kalla mai kamar gajeren wando dan faɗi da buɗewa, leɓenshi baƙi masu kauri ya buɗe na kalli baƙin dasashin shi. "Yahanasu. Kiyi haƙuri da abinda nayi miki a baya. Bana cikin hayyacina ne. Ni mai ƙaunarku ne dukkan ku, kina gani har su Ba Bakura ban kyale ba. Sannan bana son ki karɓi komai a hannun su Ba Modu, kuɗi ko sutura, ko wani abun. Ni zan kula dake zan nemi koyarwa in haɗa da aikina in dinga yi, dan in kula daku sosai. Ga su Maryam a hannunki ki riƙesu na baki su halak malak." Jikina ya mace mus, na kasa ce mishi komai. A kwano ɗaya mu ka ci abinci. Babu mai cewa da kowa komai. Bayan mun gama na fitar da kayan na dawo. A kwance na same shi daga shi sai gajeren wando. Saurin sauke kaina ƙasa nayi, ƙirjinshi sumul bako ɗigon gashi. Ba irin ƙirazan mazajen novels ba, dan ni ma'abociyar karatun littafinnan hausa ce. Kuma ni kaina ina hasaso irin kyawawan mazajen novels, da irin soyayyar da suke gudanarwa me daɗi. Duk da ni ban kasance kyakkyawa irin matayen Novels masu kama da larabawa ba, ni nasan ba kyakkyawa bace, Bulama Babba ma ba kyakkyawa bane sam, dan ba ko wacce mace bace zata yarda ta auri Bulama Babba ba, jajayen idanunshi kaɗai zasu iya firgitata, gashi da ƙatuwar murya, ƙaton hanci, da ƙaton baki. Amman Alhamdulillah ya kasance ma'abocin kyan zuchiya, mai addini, mahaddacin Qur'ani mai girma, kuma wannan shine cikakken so, dani da Bulama Babba mun dace da juna sosai. "Tunanin me kike yi Yahanasu, kizo ki kwanta kema ki huta mana." Motsi wannan na kasa yi balle in ɗaga ƙafata. "Zo ki kwanta, in kuma ba zaki iya kwana katifa ɗaya dani ba, bari in sakko in kwanta a ƙasa." Bai jira ta cewata ba, sai ya sauko. Nace dashi. Kayi haƙuri ka koma, zan iya" murmushi ya sakar mun. Nima na mayar mishi a kunyace. Mayafin jikina ya cire mun, kaina a ƙasa amman inajin kaifin idanuwanshi da suke yawo a jikina. Mrs Bukhari ce *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 21 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* Ajjiyar zuchiya naji yana ta saukewa, hannuna ya riƙe a hankali ya haɗamun wani shocking, danma hannun nashi ba mai irin taushinnan bane irinna mazajen littafi. Amman naji shigar riƙe hannun sosai, babu shiri na lumshe idanuna. Ahankali na dinga ɗaga ƙafafuna ina binshi tamkar raƙumi da akala, har izuwa bakin katifar. Ga katifar ba mai girma bace, ta gado waya shida ce. Zaunar dani yayi ta hanyar riƙe kafaɗuna. Nayi saurin shigewa can cikin katifar na juya baya, idanuna sai lumshewa suke yi. Amman dana tuno da azabar fyaɗen da akaimun, tuni na saki wani rikitaccen kuka mai dagula zuchiya, har wani firgita nake yi gani nake yi kamar abinda ya faru dani a baya yanzu ya faru, da rarrashi Bulama Babba ya bini, a tunaninshi taɓa ni da yayi ne yasa ni wannan kukan. Da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗaukeni zuchiyata fal da fargaba da tsantsar tsoron Bulama Babba. Bulama Babba kuwa, sai juye juye yake yi, cikin bacci naji ni a jikinshi ya rungumeni ƙam, gashi yana halin buƙata, amman bani da nutsuwar da zan iya bashi kaina, shima bai nema ba, sai shafo ƙirjina daya dinga yi dai. Sannan ko ina da nutsuwar bai dace ace a gaban iyayenmu zamu yi wannan aikin ba. Sai dai ban haramta mishi wasa da sassan jikina ba, kamar yadda naga yanayi, ni dai kunya da tsoro suka rufarmun, jikina har rawa yake yi babu nutsuwa tare dani sam. Sakeni yayi, ya ɗan matsa kaɗan. Bai kuwa jima ba bacci yai awon gaba dashi. Ni kuma ya barni da karanta wasiƙar jaki. Haka muka kwana tare, washe gari kuwa, na kasa haɗa idanu da kowa, sai sauke kai nake yi. Gashi a ɓarayin su Ba Bakura na wuni, tare da su Fanna, da Fanda, sai yaran ɗakin Marigayi Ba Baana, su biyu Sufaim, da Ya gaji. Kasancewar dasu nafi shaƙuwa sosai. Su Yabulu kuma tana gida tana fama da tsowon ciki. Hira me daɗi muke gudanarwa, Sufaim babba ce, dan itace Babba a ɗakin Ba Baana, amman mun shaƙu sosai, shi yasa kai tsaye daga wajan aikinta ta wuto gida, tunda labarin zuwan nawa ya bazu a dangi. Yau garau nake jina, sabida da safe na zari jiki na fita na siyo magungunan maye, duk da ban samu irin wanda nake sha ba, amman suma sun sani naji garau. A ƙarƙashin pillown Ya Innana na ɗauki kuɗin. Rabon da in ɗauki kuɗi ba tare da an bani ba, tun ina yarinya ƙarama irin na yarinta da ake yi. Amman sai gashi yau nice nayi sata, na siyo kayan maye. Bulama Babba yaso tafiya yau, amman kuma ya Ɗauki Amada, da Dala, da Ba'a kaka suka tafi gaishe da dangi, dan Ba Modu yace lallai yaje Yobe wajan Mama Gana itama ya bata haƙuri, tun safe suka fice a gidan. Nima cikin aminci na wuni tare da ƴan uwana, daga ɓarayin Ba Bakura muka wuce ɓarayin surukan gidan dan in gansu da kyau kuma in gane su. Abun sha'awa daga masu tsohon ciki, sai masu ƙaramin goyo, ga matar wakil itama an sallamota daga asibiti tun safe. Ina da tsananin son yara, ina son inga na haihu nima. Lumshe idanunta nayi, ƙwaƙwalwata ta shiga hasko mun abubbuwan da suka faru a daren jiya ni da Bulama Babba. Dana tuna sai inji jikina ya sauya, na rasa gane takamaiman abinda ke raina. Bani na samu hutu ba sai da daddare, bayan su Fandau sun koma gidajensu. Ina zaune akan sallaya Bulama Babba yayo sallama ya kutso kanshi cikin ɗakinmu. "Ya Innana kina ciki ashe?" Ya tambayeta yana ɗan sosa kanshi. Kallona yayi a fakaice. "Inanan Bulama Babba, shiga ka zauna, dama yanzu zanje wajan Baban naku ne." Tana faɗar haka ta fice abunta, ɗakin ya rage daga ni sai Bulama Babba. Sannu da dawowa, ina wuni?" Na furta a sanyaye. Sai da yaima kanshi mazauni a saman kujera sannan ya samu zarafin amsa gaisuwata. "Mama Gana tace in gaisheki, zata zo ta duba ku, tana mana jaje. Kai nasha faɗa yau a wajan Mama Gana, sai da tai mun tas da kika sani" Dariya nayi mishi, daman nasan ba zasu wanye lafiya ba sam. "Ina yaran ban gansu ba ko a cikin gidan?" Au Fanna ta kwashesu ta tafi dasu gidanta, mancewa nayi ban sanar maka ba" Murmushin farin ciki yayi. Na kawo mishi abincinshi, yaci anan, sannan ya tashi "Sai kin zo, ni zanje in dubo Ba Bakura da Hajja." Haka na wuce ɗakin Bulama Babba bayan na sake wanka, na bi jikina da turaruka masu jan hankali. Yauma a cikin jikinshi nayi bacci, sai dai cikin dare bansan yadda akayi ba, kowa ya saki ɗan uwanshi. Washe gari Bulama Babba yayi sallama da kowa ya tafi, akan zuwa ƙarshen wata zai dawo ya tafi damu. Sai naji ina kewarshi sosai, dan naji daɗin kwanaki biyun da mu ka yi tare matuƙa. Haka zamana a gida yaci gaba da gudana, yayin da shaye shayena yake ta gaba gaba, cikin sati guda na yi ɗan dumur dumur dani, hankalina a kwance yake sosai. Babbar matsalata guɗa ɗaya ne shine. In ban sha ƙwaya ba, sai inji kamar zan zautu, hakanne yake tursasamun wajan sha ala tilas, dan shine kaɗai kwanciyar hankalina. Ina zaune a ɗaki nayi zurfi a cikin tunanin yanda zan fitar da kaina daga cikin wannan rayuwar da damuwa, da kaɗaici ya sani a ciki, ina mai cike da nadamar jefa kaina halin shaye shaye da nayi. Ya Innana ta dafani. "Meya faru kwana biyu sai inga kin zauna kinyi tagumi kina tunani, lafiya kuwa in akwai wata matsala ki sanar dani, duk duniya baki da kamata" Inama zan iya buɗe baki in faɗa ma Ya Innana matsalata. Amman kash ko kasheni zata yi bazan iya buɗar baki in sanar da'ita nasa ƙafa nayi fatali da tarbiyyar da suka ɗaurani akai ba, bazan iya sanar da'ita na tambaɗar da mutuncina bane. Ga sace _sace da nake yi mata, jiya a ajjihun rigar Ba Modu na zari kuɗi masu tsokar gaske. Na siyo ƙwaya nasha, na adana kuɗin dan gaba. Na zama ƴar ƙwaya ƙarfi da ya ji, dama ina jin labari cewar ɗan shaye_shaye ko kuɗin wa ya samu sacewa zaiyi ya sai kayan maye dasu, ashe da gaske ne. "Wai ba dake nake yi ba kin barni ina magana, kan ki ɗaya kuwa? Baki na rawa nace mata. Babu komai bana jin dai daɗin jikinane sam, zazzaɓi ke damuna." Amon sassauci naji a muryarta, sai dai hankalina ya matuƙar tashi da naji ta kira Wakil. "Kana gida ne ko baka dawo ba?" Daga wayar Wakil yace. "Ban dawo ba Ya Innana, wani abunne ya faru?" "Babu komai, dama Yahanasu ce bata jin daɗi nake son ka kaita asibiti a duba lafiyarta kafin mijinta ya dawo" "Ina hanyar dawowan ta shirya, dana zo ƙofar gida sai ta fito mu wuce kawai" Ni dai ina jinsu su kai sallama, cikin dariyar yaƙe nace. Ya Innana da kin bari bafa wani ciwo bane sosai yake damu na ba" murmushi tayi "Ai gara a duba ki a baki magani, yanda mijinki ya kawo ki lafiya, ina fatan ya dawo sati mai zuwa ya tadda ki lafiya. Daga nan sai ki yi ma su Hajja sallama Wakil zai saukeki a gidan Yanunu, za tai miki gyare gyare, in ana gobe Bulaman zai tawo, sai ki dawo gida." Jikina har wani rawa_ rawa yake yi, tsorona Allah, tsorona kar asirina ya tonu a asibiti likitoci su gano ina shaye_ shayen ƙwaya ne. Ina zaune Wakil ya kuma bugo waya ya iso ƙofar gida. A ɗarare na haɗa kayayyakin da Ya Innana ta bani nake sawa, na zuba a jaka na naɗa lafayata, a hankali na fito Ya Innana tana zaune inda na barta. "To Allah ya ƙara sauƙi, ki gaishe da Yanunu ko? " Kai kawai na ɗaga mata. Cikin gida na shiga nai musu sallama, matayen su Wakil sai zolayata suke yi. Ni kuwa da yaƙe kawai nake binsu. Da muka isa asibiti cikin sa'a ni kaɗai na shiga ɗakin ganin likita. Na faɗa mishi ciwon kaine ke damuna, ya rubuta mun magani, nayi mishi godiya. A gidan Yanunu wakil ya ajjiyeni, na shiga ciki. Ko da kayan maye na ya ƙare, sai naji kaina na birkicewa, har na soma sambatu ni kaɗai. Ba shiri na lallaɓa ɗakin Yanunu na dinga bincike, a cikin kwanon samira na samu kuɗi, dukka na kwashe na fice da sauri sai bayan kango dan siyan kayan harka." KADUNA: KOFUR ZUBAINA: Dawowata daga wajan aiki kenan. Ina sanye da kayan ƴan sanda, riga da dogon siket, da ɗan ƙaramin hijabina. Yusuf kuma yana goye a bayan Zakiya, yarinyar maƙociyarmu dana ɗauketa take raka ni wajan aiki dan kula da Yusuf. Ina doso layinmu gabana ya faɗi ras. Matan layinmu sun fito ko wacce tana daga ƙofar gidanta a zaune suna hirar asara da suka saba. Suna hangoni suka soma zubar da habaici, wai har Raliya tana cewa ita tsoronta Allah, tsoronta kar a kaima matsiyacin mijinta farmaki. Mijin nata da ba miji ba, gadi yake yi a kamfanin giya can biriwuris na hanyar kakuri, Kai kawai na girgiza nayi wucewata, wasu munafukan sai son kulani suke yi, amman ganin babu fuska dole suka haƙura. Wata tiƙeƙiyar mota na gani a ƙofar gidanmu fara sol sai walƙiya take yi, Nafisa da wani ƙaton Alh mai ƙaton ciki na gani a jingine. Murmushi nayi, Yarinyarnan ko ina take samo zuƙa_ zuƙa kifi haka ohon mata. Su kuma mazan sun zama tamkar ƙudaje, dan kwaɗayi. Wucesu nayi banko kalli inda suke ba. Mama tana tsakar gida sai faman kaye kaye take yi. Asiya data dawo wankan jego kuma tana zaune a tabarma tana cin farfesun kifi, wayarta maƙale a kunnenta tana waya da mijinta. Mama ina abincina yunwa nake ji, Zakiya shiga ki shinfiɗeshi uban ƴan rigima. Mama tace. "Dama ke da Nafisa nake jiran ku dawo a samu a gagganɗa kuɗin cefane, tunda mijin Asiya dai ya jibge mana komai na abinci a wadace, to kuɗin cefanen kayan miya kuma ai sai ku ku bayar ko?" Kallon Mama nayi waini yau take faɗama haka, ta mance ni sanda nake siya musu komai hatta kayan miyan nike basu kuɗin saye. Ɗari biyar na zaro a jakata na miƙa mata. Gashi nan, na yau dana gobe, kinsan wata ya raba bani da kuɗi, nayi ɗinkuna da kuɗina, dan bazan zauna babu kayan sawa ba ina zawarci ba. Mama ta karɓi kuɗin tace. "Ba wancan baƙin yana turo miki da kuɗin abinci kullum ba?" Yana turowa, ɗari biyar ce yake turomun, amman yanzu ma so nake in huta in naci abinci zan kirashi in faɗa mishi Yusuf ba lafiya ko zan samu wasu kuɗaɗe masu kauri. Ina kaiwa nan na miƙe na shige ɗaki bayan na banka ma Asiya uwar harara ji nake yi na mugun tsananta. Tuɓewa nayi, na ɗan watsa ruwan ɗumi. Nafi minti goma ina kwalliya, na fito ɗas dani gwanin ban sha'awa, doguwar rigar bubu na saka ƴar kanti wacce take zuwa da babban mayafinta, nayi kyau sosai. Fitowa nayi tsakar gidan, na tarar Asiya ta gama wayar da take yi, ta miƙe tsaye tana wani ihu. Da harara na bita, danni yanzu kowa haushi yake bani, musamman ma masu Aure, kai zawarci fa babu daɗi sha'awa tai ta damunka, sai dai ka shiga bayan gida da ɗan kendir ɗinka, ko ka biya ma kanka buƙata da hannu. In bakai ɗayan biyunnan ba, to tabbas sai dai in maza zaka nema. "Mama albishinki" Da gudu Mama ta ƙaraso har tana murjemun yatsuna, da sauri na janyesu. "Goro fari gangariya, menene Asiya?" "Alh yace ya biya mana Umara dani dake dashi, da zaran nayi arba'in zamu wuce." Ihu suka shiga yi ita da Mama dole nima na shiga taya su murna cikin dariyar yaƙe. Haka fa al'amura sukaita garawa, kullum a cikin gantalin bin gidan ƙawayena nake, dan zaman gidan baya mun daɗi sam. Sai tatsar kuɗi a hannun Bulama nake yi, dan kullum Yusuf a cikin ciwo yake a wajena, dan kawai in dinga samun kuɗi, yana iya bakin ƙoƙarinshi har mamaki ma nake yi." Bulama Babba. Motarmu ce ta fice daga tasha ta ɗauki titi zuwa Damaturu. Ahmad ya dubeni yace. "Yau ka kira kaji ya jikin Yusuf kuwa? Kuma ya kamata in muka dawo, mu je Kadunan mu dubo shi ai" Idanu na lumshe a hankali. Nima nayi tunanin zuwan, amman ganin Zubaina bana son yi. Ɗazu na kirata a waya, tana asibitin ma a lokacin dana kiratan." Ɗan hira muka taɓa ba mai yawa ba, naja bakina nayi shiru. Inata tunanin yanda zamu yi rayuwa a ɗaki ɗaya jol gamu da yara . Ni nafi jin Yahanasu ma, naso ace yanzu ne nake da kuɗin da zan iya kulawa da'ita. Gashi kullum ita ke warwaremun gajiyar aiki, da kalamanta sauƙaƙa, masu sauƙaƙa mun zuchiyata in na kirata ta wayar Ya Innana. A cikin wannan wata gudan da nayi ba tare da Yahanasu ba, sai nake jina wani iri. Amman wannan ɗan tsukukun shi ya bani damar wanke kaina a wajanta. Ta hanyar bata lokacina, kulawa da'ita, yawan kiran waya dan jin lafiyarta. Sai mu kai sabon shaƙuwa, bacin wancan da muke dashi. Kullum kuma ina sanar da'ita ta shirya tarbata, dan a ranar dana iso bazan iya raga mata ba, dole ta mallakamun kanta. Dana faɗa mata haka sai tace. A shirye nake in faranta maka ranka a cikin ko wanne yanayi. Ai ni gonarka ce." Da ƙishin ruwan abunda nake tafe kenan, da so samu ne ma dashi zan so in soma arba. Haka mota tai ta lulawa damu a titi, yayin da zuchiyata tayi zurfi a cikin tunanin Yahanasuna. Zuchiyata sai zabarin son ganinta a kusa da masoyiyarta take yi. Allah ya sani ban iya soyayya ba, domun in inason abu sonshi nake yi da dukkan rayuwata, in ƙin mutum nake yi shima haka hakanne yasa Zubaina cutar dani, dan taga na jarabtu da sonta. A yanzu ina jin motsin son Yahanasu fiye da na Zubaina a da. Duk da Zubaina itace irin samfurin macen da nake da burin ƙare rayuwata da'ita. Ni ba kyakkyawa bane, za'a iya kirana mummuna kai tsaye kuwa, dan bani da wani abu dake sawa ayi kyau. Kuma ni baƙine wulik irin baƙaƙen kanuri ɗinnan. amman ina son mace mai kyau, kuma fara, hakan ne yaja ra'ayina akan Zubaina, dan tana da kyau dai dai irin kyawu na hausa fulani, kuma fara ce ɗas, ga gayu ga diri, tafi Yahanasu takota ina, gata da zati. Amman ina mamakin yanda lokaci guda na jarabtu da son macen da ban taɓa kawowa zan iya auren wacce ma ta ɗarata a kyau ba. Gashi banason mace mai ƙiba, Yahanasu kuma mai ƙiba ce, yanzu ne tayi rama a sakamakon halin dana sakata a ciki. Amman motsin sonta da sha'awarta ba ƙaramin taɓani suke yi ba. Lallai cikakken so na tsakani da Allah mara algus, ba ruwanshi da muni, ko kyawu, kuma babu ruwanshi da launin fatar mutum, balle jinsi, ƙabila. Haka naita lulawa duniyar tunani, har muka iso wani ɗan ƙauye. Anan mu ka yi sallah sannan muka sake nausar hanya, yunwa da ƙishirwa duk sun dame mu, mu ba wani wadataccen kuɗi ba, balle mu sai abinci kamar yanda ƴan cikin motar suka siya." YAHANASU: Tun sha biyu rana nake tsaye a kitchen ɗin Anty Aisa matar Wakil, ina girke_girke. Dan can na gudo sabida kunyar da nake ji. Gashi so nake in gwangwaje Bulama na da girke girke masu gamsarwa. Burabusko nayi mishi da miyar gyaɗa wacce taji naman kan saniya. Sai kuma nayi mishi kunun gyaɗa, da funkasau, sai jus ɗin tsamiya wanda yaji kayan ƙamshi. Dukkan abincin da nayi ma Bulama na, nasan sune abincin da baida tamkarsu. Ina cikin gyara kitchen sai na jiyo sallamar Fanna. Murmushi nayi kawai, uwar gulma nasan tazo ne dan taga wacce tarba zanyi ma Bulamana, ranar dana kwana a gidanta, kusan raba dare mu kayi muna waya da wayarta, tana jin yanda muke ma juna musayar kalaman ƙauna, da yanda Bulamana yake fasalta irin kewata data yara da duk ta addabeshi. Ina cikin tunaninnan naji Maryam ta riƙeni ta baya tana gwalan gwalan. Dariya nayi mata, nasa hannu na ɗauketa, itama sai dariya take yi mun. Tayi kyau sosai, Hajja ce tayi mata kwalliya da sababbin kayan da Ba Bakura ya sai musu ita da Bawa. Tasha jan ƙunshi da kitso, kamar yadda nima jiya muka raba dare ana mun lallen salatab da kitso ƴan yis yis irin na Kanuri. Ƙamshin da jikina yake yi a wannan lokacin sai wanda yaji. Kinyi kyau maryama na, ina Bawa yake?" Sai nuna mun hanyar fita take yi tana gwarancenta. A haka Fanna ta shigo ta same ni, ina sauraron shirmen Maryama. "Uhm su Yaya Yahanasu sai shirye_shiryen taran Bulama Babba akeyi, anata zumuɗin zuwan mai gida, an sha kewa." Hararar wasa nayi mata, nayi ƙasa da muryata nace mata. Kar kiga laifina, yayan naku ne ya iya soyayya da shagaltar da mace." Baki ta kama. "Au Yayanmu mu kaɗai kenan ke kin fita sahu? Hahaha lallai Bulama Babba ya samu gurbi mai kyau" Dariya nayi mata, na sauke Maryama. Ungo kulolinnan fitar mun dasu ki jera mun a daining ɗin Anty Aisa, ki dawo ki kai mun waɗannan kwanukan." Dariya take ta faman yi mun, ni kuwa banza nayi da'ita naci gaba da gyaran kitchen, tare da wanke duk abinda na ɓata. Ana kiran sallar la'asar na shiga wanka a ɗakin baƙi dake cikin falon Anty Aisa. Na jima ina kuɗe jikina da sabulun gyaran jiki da Yanunu ta haɗa mun. Ina fitowa na shiga aikin shafa turarene, kulaccar jiki data gashi ne, turarukan mai ne, na shafa turare kala biyar a jikina, kaina kuma kala biyu na shafa,. Na saka turaren turara gashi a cikin gaushin dake cikin kasko, wanda nasa Fanna ta ɗebo mun tun kafin in shiga wanka. Na turare gashina da turarennan, na yi turaren jiki, dana tsugunno, kusan minti arba'in na ɗauka ina gyare_gyare. Na zura rigar material a jikina kenan Fanna ta bango ƙofa da sauri gulma na cinta. "Bulama Babba ya'iso yana cikin gida" Ajjiyar zuchiya na sauke, gabana ya shiga harbawa, duk sai kuma naji na dibibice ma. Gyara zaman rigata nayi, na ɗaura ɗan kwali, na feshe kayan da turare mai taushin ƙamshi. Na dawo falon Anti Aisa nayi zamana, amman zuchiyata tana can wajan Bulamana. Anti Aisa sai dariya take yi muni, tana zaune tana ba jaririyarta nono, ni dai sai Murmushi kawai nake yi. Wakil ne yayo sallama ya shigo, dawowarshi daga wajan aiki kenan. "Au wai dama kinanan, Bulama Babba naga ya tura a kirawoki a ɗakin matar Ahmada." Wasa nake da zoben hannuna, wata kunyace take ta fisgata. Anti Aisa tace. "Yana ina ne Bulama Babban Abban Yahanasu?" "Yana ɗakin Bulama ƙarami na samartaka, sai nemanta akeyi fa ashe nan tazo ta ɓuya" "Ai itama sai jiranshi take yi, kaga abincinshi ta jera mishi a daining, anan ɗin taso tarbarshi. Amman Yahanasu kije ki haɗa mishi ruwan wanka, in yayi wanka ya huta sai ki kawoshi yaci abincin. Zan bar miki falon a buɗe, ni zamu fita da Abban Yahanasu." Miƙewa nayi na fice, ajjiyar zuchiya na sauke. Cikin bin bango nake tafiya, banason in haɗu da kowa, ai kuwa cikin sa'a babu da wanda na haɗu, da sauri na shige ɗakin tare da mayar da ƙofar na rufe. Yana tsaye a filin tsakar ɗakin. Sanye yake da wata shadda kalan sararin samaniya, mai sauƙin kuɗi, ɗinkin jikinta ma mai sauƙin kuɗi, kanshi saye da hula zanna wacce ta dace da shaddar jikin nashi, yanata ƙamshin turarenshi na farar humra. Ɗago da kaina nayi muka zuba ma juna idanu cikin kallon kuɗa, soyayyarshi sai wani fisgata take yi, yayin da naga halama jazbiyyata tana janyoshi tamkar yanda mayen ƙarfe ke jan ƙarfe.( Daku nake maman Yasser da ummu nabeeha, da Fatima Zara, da A.A 🤣) Hannayenshi ya ware mun tare da gyaɗa mun kanshi halamar in tawo. Cikin sassarfa na isa gareshi, a maimakon in afka ƙirjinshi sai naja tunga, wata kunya ce ta durarmun. Jawoni yayi da ƙarfi na faɗa jikinshi, kewayeni yayi da hannayenshi, nayi lub a ƙirjinshi, sai ajjiyar zuchiya yake ta faman saukewa, yayinda hanayenshi suke shafar jikina a hankali. Tsaiwa ce ta soma gagararmu, babu shiri muka afka kan katifar dake ƙasa a ɗakin. Ɗago mun da kaina yayi, nayi saurin runtse idanuna, kunya na shirin hallakani, ban aune ba naji tuɗun manyan leɓɓanshi a saman nawa, cikin ƙwarewa yaima bakina riƙon alewar yara. Wata sabuwar babbar duniyar ma'aurata muka lula, bana iya gane komai. Gabaki ɗaya Bulamana ya canja mun, ya dawo tamkar mayunwacin zaki. Da ƙyar na ƙwaci kaina a hannunshi, ban bari ya cinma burinshi ba. Ka bari kayi wanka kaci abinci tukunna." Hannayena ya riƙo dukka biyun yana ɗan murzasu a hankali. "Da kin bari na gama da wannan tukunna, Yahanasuna nayi kewarki sosai." Nima nayi kewarka, gabaki ɗaya zaman gidan sai naji ya hau kaina." Ranar ni naga fitina, Bulamana ya hanani saƙat. Da ƙyar na lallaɓashi yayi wanka, muka je yaci abinci, sai uban santi yake ta yi mun na kirawo mishi su Bawa. Bayan ya shiga cikin gida ne wajan Hajja, ni kuma na samu na gudu. Amman abunda nake gudu sai da ya faru da daren ranar da yazo ɗin. Munji ɗumin juna a wannan daren, a ranar Bulamana ya mayar dani cikakkiyar matar aure, tare da yi mun adda'ar Allah yasa yayi ajjiya a marata. A daren naci kuka sosai, ba kukan kasancewa da mijina ba, kukan keta mun darajata da wani banza yayi. Gani nake yi tamkar ban gamsar da Bulamana ba, domun banga yayi irin wannan abun da nake karantawa a littattafan hausa ba. Asalima sai da ya barni naci kukana na ƙoshi sannan ya bani haƙuri. Dama Hajja Fati ta faɗamun duk wannan rubutun first night da marubuta suke yi yaudarace kawai. Dududu a cikin minti goma Bulamana ya gama jin daɗinshi dani, saɓanin su da suke rubuta gabaki ɗaya daren aikin da akeyi kenan. Da asuba da zan shiga wanka, bayan Bulamana ya fito, na ɗauka bazan iya tashi ba sai ya tallafamun. Abun mamaki a kan ƙafafuna ras na shiga bayi, nayo wankan tsarki, sannan nayi wankan soso da sabulu na fito." A tsaye na same shi yana goge jikinshi da towel. Haɗa idanu mu ka yi, a tare muka sakarma da juna murmushi, inajin sonshi na sabunta kanshi a zuchiyata, Aure kenan mai sa duk girman namiji ka ganshi babu wando. Mai sawa duk ƙanƙantar mace ta ɗauke babban namiji. MRS BUKHARI CE 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 22 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* "Zan tafi masallaci, ki yi ƙoƙari ki shirya da wuri, ƙarfe bakwai mu ka yi da Ahmad zamu fito. Inason zanyi magana dake inna dawo masallaci, naso tun jiya muka tattauna, amman ganinki ya susutamun tunanina bamu samu zama ba balle mu tattauna komai. Amman inna dawo kafin mu fita sai mu tattauna, saina dawo ko mai daɗi" Kunya da daɗi yasa nayi saurin rufe fuskata da tafukan hannayena. Dariya ya sakar mun ya fice. Bayanshi nabi da kallo har sai da na dena ganinshi. Ajjiyar zuchiya na sauke, ina mamakin kaina akan sabon son Bulamana da yake bijiromun. Yau nice namiji yake rawar kai a kaina duk rashin kyauna, har na kai macen da zata susuta mijinta harma ya rasa gane kan nutsuwarshi? Lallai rayuwar aure sirri ce, soyayyar gaskiya babu ruwanta da muni. Ni kaina nayi mamakin yanda Bulamana ya dawo a idanuna, ganinshi nake yi tamkar yafi ko wanne namiji kyau a duniyarnan, duk wani muninshi da jayayen idanunshi bana gani yanzu, idanunshi har wani narkomun da sha'awarshi yake yi inna kalla. Allah kenan, Allah na gode maka daka bani ɗan uwana a matsayin abokin rayuwata. Jina nake yi tamkar nafi ko wacce mace kyau a duniyarnan. Daurewa nayi na mayar da kayana nayi sallah, ina kan sallaya Bulamana ya shigo da sallama. A kusa dani ya zauna jikinmu na gugar na juna. Idanunshi ya zuba mun, nima shi nake kallo zuchiyata cike da sonshi. "Meye sirrinne naga kin sake yin wani kyau, har haske kika sake yi fa uhm" Ya kafeni da jajayen idanunshi, sai wani lumshe su yake yi. Lallai Bulamana ya iya soyayya, da tarairayar mace, ba banza ba ashe Zubaina ta mallakeshi ita kaɗai. Kaine sirrin ai, kulawar dana samu a wajanka shine ya kwantar mun da hankalina, baka ga na ciko bane?" Hannayena ya kamo yace. "Na gani sosai ma kin ciko sosai. To bani labarin yanda sona yake a cikin zuchiyarki, sannan da fatan na gamsar dake, na kore miki ƙishin ruwanki, kamar yadda nawa ƙishin ruwan ya koru ko?" Sake sunne kaina nayi, zuchiyata sai tsalle take yi mun, daurewa nayi na faɗa mishi kalamai masu kwantar da zuchiya, amman da ƙyar nayi yaƙi da kunya. Nan muka shiga fallasama juna asirin zuchiyoyinmu, kamar zamu koma ruwa dai, da ƙyar na samu na lallaɓashi ya barni, amman bai rabani da jikinshi ba, yana kwance ni ina gefen kafaɗarshi "Yahanasu na" Yanayin muryar da yayi amfani da'ita wajan kiran sunana, yayi tasiri sosai a gangar jikina, ayau sai naji sautin babbar muryarshi na neman rikirkitani, saɓani da da in yayi Magana nake shiga taitayina. Na'am Bulamana " na furta a sarƙe. "Mun samu gida mun kama a can wata anguwa, to amman gidan gidan yawane sosai, mata zasu kai ashirin in ma basu fi ba. Kiyi haƙuri a yanzu iya abinda zan iya kenan, sabida ina buƙatarki a kusa dani, da yara ma su samu su koma makaranta, kema ki koma bakin aikin ki. Na je ma'aikatar taku na sanar dasu abinda ya faru, na kuma faɗa musu kin tafi gida amman ɗaya ga sabon wata zaki dawo bakin aikin ki. Gemunshi na kamo ina wasa dashi nace. Haba Bulamana, ni banji daɗin yanda kake bani haƙuri ba. Nifa matarka ce, duk inda kaga damar ajjiyeni ai anan zaka ajjiyeni, dolena ne in yi biyayya a gareka, ai babu komai" Kwanciyata ya gyara mun ya ɗaura da cewar. "Ina kuma baki haƙuri akan ɗaki ɗaya na kama a ciki zamu zauna harda yaran, sakamakon rashin lafiya da Yusuf yake fama dashi, duk kuɗaɗen nawa sun ƙare akan maganar lafiyarshi, sannan na ɗan siya mana katifa da ɗan abunda ba'a rasa ba......" Hannu nasa na rufe mishi baki. Shishsh.. baka da buƙatar yi mun dogon bayani, mu ci gaba da adda'a Bulamana. Bari inje in haɗo kayana, kaga ƙarfe shidda, kuma bakwai zamu tafi" Ƙoƙarin sauka nayi a jikinshi, da sauri ya dawo dani, gam ya riƙeni a ƙirjinshi. "Allah yayi miki albarka. Bani da kuɗi, bani da kyan da zan burgeki, anma zan baki kulawa da soyayyar da sai kinyi alfahari dani." Nima bani da kyau, bani da diri, bani da hasken da zan burgeka. In sha Allah zan yi maka biyayya, zan zame maka tamkar baiwa." Ina kaiwa nan na miƙe na fita ba tare da na waiwayo ba." Ina shiga ɗakinmu na taradda Ya Innana ta gama haɗa mun kayana tsab a jakarta, kayayyakine nata ta bani, sai sababbi kala uku da Ba Modu ya ɗinka mun. Wakil ya siya mun zanin gado, Dala ya siya mun labulaye ƙofa huɗu, Fanda ta siyamun lafiya guda uku, fanna ta bani takalmi ƙafa biyu. Ƴan uwana suka haɗa mun goma sha tara na arziki. Babu dai wanda ya bani ko sisin kobo, sai Ba Bakura daya bani, yayi ma su Bawa ɗinki, harda ƴan kanti duk ya sai musu. Hajja ta kuma ta haɗoni da kayan ƙamshi, dana gyaran jiki. Kowa dai da abunda ya bani. A tsaitsaye muka karya ni da yaran. Na ɗauki na Bulamana na kai mishi. Yana gamawa muka fito, ƴan uwa da iyaye sunata mana addu'ar isa lafiya. Wakil ne ya ɗauke mu, muka biya gidansu Ahmad muka ɗakkosu, wannan karon an bar Zulai a gida wajan Baba. Wakil bai bar tasha ba sai da yaga motar mu zata tashi, hannu yasa a ajjihu. Yana zarowa ya kamo hannun Bulama Babba ya damƙa mishi ya juya. Da idanu Bulama Babba ya bishi, har idanunshi na cika tab da ruwan hawaye. Motarmu ce ta fita da gudu a tashar, wakil sai ɗaga mana hannu yake yi, har sai da muka dena ganinshi muma muka sauke hannayenmu " KOFUR ZUBAINA: Ina zaune a tsakar gidanmu ina daddanna wayata, Nafisa na ɗaki tana baccin asara. Yau bani da aiki ina hutu. Su Mama kuma yau kwanansu biyar da tafiya Umara, sai jiya ne ma suka samu damar kiranmu. Mabaruka ce ta shigo gidan a birkice kamar an jefota. Hawaye caɓe_caɓe a fuskarta, gashi naga bakinta a kumbure. "Ƙawata Adam ya yaudareni ace munafukine ban sani ba?" Zama na gyara nace. Yi mun bayani dan Allah dena kukannan akan wani banzan namiji, wanda ƙila yana can yana sheƙe ayarshi ke kina nan kina kururuwa" Cikin kuka tace. "Ashe Adam yana kwanciya da Sagira baibai kawai suke ninkeni? Yau naga kilakanci sai ga Sagira da ciki, harya soma fitowa ni banma sani ba. Kuma dan bura ubanci Adam ne yazo yake shaidamun wai zai kaita asibiti zata soma awo. Wallahi ƙawata bansan sanda na cukume Adam na dinga narka ba, na haɗa da makira, kar ki so ganin buyagin da nayi yau. A take Adam ya cikace mun saki, a taƙaice dukka igiyoyin auren sun ƙare" Ido na zare waje nace. Ya sakiki fa kika ce, kuma kika ce Sagira na da juna biyu, wanne irin sakaci kika yi haka Mabaruka? Kinga irin abubda nake faɗa ko" "Ke dai bari, tunda na koma gidan Adam, ban sake kaima boka ziyara ya sabunta mun aiki ba. To bani da kuɗin Zubaina, duk kuɗaɗen aikina akan mallakar Adam suke ƙarewa, ban tara komai ba, gashi ya sake ni a banza. Sai dai zan kunna mishi jafa'i da masifar da bazai iya fita a cikinta ba. Dafata nayi. To meye na kuka ke da kina yin jini uku shikenan, kina da damar da zaki yi aurenki kwaf ɗaya. Ga Alhazai suna shaƙawata a gari. Kinganni fa duk sha'awa sai tsotseni take yi, a hakanma dan nakan ɗan rage ma kaina zafi. Zawarci masifa ne ƙawata, ni da'ace wata uku zanyi da naji daɗi, wani hamshaƙin Alhaji zaki cabke ki shige ki baza mulkinki. Ki duba Asiya yadda take tsula tsiyarta a gidan mijinta, gabaki ɗaya uwar gidan, da yaranta Asiya ta shafe su. Kinga haihuwarnan da tayi? Yanda kika san Asiya ce ta soma yi mishi haihuwa. Suna Umara fa yanzu haka Harda Mama. Me zai dame ki to dan Adam yayi ma Sagira ciki? Su je can su ji da talaucinsu, zaki samu babban rabone, kuma ki bar mata yaranki ta gama shan wahalarsu dan ubanta. Kamar yadda na tafi na barma jakar matar da Bulama ya auro rainon yara" "Wallahi ƙawata kuma hakane. Wato Mama ana makka? Oh ma'aikin Allah na madina ni Mabaruka. Muma Allah ya koro mana wani ƙusan, ƙawata yayi wuff damu, za'ayi zawarci fa mai lafiya, ko dan samun mai maiƙo ma. Tare da Mabaruka muka wuni a gida,. Sai da yamma lis muka fita nasha wanka da ɗan ƙaramin mayafina, ga Yusuf na riƙeshi a ƙuguna, shima naci mishi ado. Gidansu Mabaruka muka je. Ta zaiyanema mamanta cewar Adam yai mata duka ya sakota. Nan mamansu ta shiga sababi, tana ɗure_ ɗuren ashar manya manya. Duk jirgi ɗaya ne ya kwasosu da su Mama. Zuwa bayan isha na ɗau haramar gida. Ko a haka zawarawa suna latsani, sai dai irin waɗandan nake son su zo basu bane suke zuwa ba. Nakance musu iddata bata ƙare ba, kuma goyo nake yi ɗanye. Haka dai kwanaki su kaita tafiya. A tafiyar su Mama Musa kullum sai ya shigo da ƴan mata a ɓoye sun kwana a gidan, sai da asuba nake ganinsu wani sa'in. Sagiru kuwa, tun kafin Mama ta tafi yayi mata sallamar ya tafi Lagos, zasu bikin wani abokinsu. Tun daga ranar bamu sake sakashi a idanunmu ba. Nafisa kuwa, sai ta ga dama take kwana a gida, in kuwa bata ga dama ba, a waje take kwana abunta, dana yi mata magana ta nemi zagina, sai na fice a harkarsu duka daga ita har Musa. Tunda Mama ma data haifemu babu yadda ta iya damu dukkanmu, kuma ita ta sabar mana duk abinda muke son yi dai dai ne, ita ta koyar damu rashin ganin girman na gaba. Haka dai naci gaba da gwagwuyar zawarcina. Da kuma renon Yusuf. Wata rana in samu dubu ɗaya a hannun Bulama, wata rana ɗari biyar, kuɗaɗen albashina baya isata yima kaina hidima sam, dan duk wata ina sayen sutura kamar biyu, da takalmi da mayafi, harda ɗankunne da sarƙa fashion haka. Gaye nake ɗanɗasawa sosai. Bulama Babba: Muna tafe a cikin mota, jikina na gugar na Yahanasuna, hannuna na kan ƙugunta na tallafota jikina gabaki ɗaya, dan naga bacci take shirin yi. Ahmad ne ya zungureni dake shine a kusa dani "Wallahi baka da kunya, ji yanda ka ƙwaƙwube ƴar mutane a cikin motar haya, ko kunyar Hajara ba zaka ma ji ba?" Murmushi nayi mishi nace. Ai ban hana ka ka jawo taka matar ba, kowa ya biya allonshi sai ya wanke" Dariya mu ka yi dukkanmu, Ahmad yace. "Naji daɗin yanda hankalinka ya koma kan Yahanasu sosai, na kuma ji daɗin yanda kayi fatali da son da kake yima Zubaina. Duk da nasan baka haɗa komai da iyayenka." Ahmad aini yanzu nake ganin ma nasan meye soyayya, in da na auri Zubaina sabida haskenta, da cikar halittarta. To ita Yahanasu son so tsakani da Allah nake yi mata. Kuma a idanuna ina ganin kyanta fiye da kyan Zubaina, ina son matata sosai" Ni da Ahmad mu kaita tattauna halin rayuwa, a haka har muka iso garin kanon dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika. Bayan mun fito daga tasha, Ahmad ya tare mana ɗan sahu zuwa na'ibawa cikin layin S P. Anguwace wanda kai tsaye zamu kirata da anguwar talakawa, domun masu rufin asirin cikin unguwar baifi a ƙirga ba. Unguwace mai cike da datti, hayaniya, da hargowar yaran geto da ake sakinsu suna damun mutane da fitintuninu. YAHANASU: A bakin ƙofar wani kwaraɓaɓɓen gida mai ɗan sahun ya tsayar da ɗan sahunshi. Gidan ko ƙofa babu sai wani cinyayyen labulen buhu fari, wanda tsabar datti ya dawo ruwan ƙasa. Kayayyakinmu muka sakko dashi. Hajara tace. "Abban Anisa wai wannan ƙazamin gidan shine gidan da kuka kama dama?" Ahmad da gani baiji daɗin maganar Hajara ba sam, shi yasa ya amsa mata a daƙile. "Shine in baiyi miki ba, sai in mayar dake gidanku tunda yafi wannan tsabta ko?" Bakinta ta tsuke tayi shiru. Ni dai hannun yara na kama nayi gaba. Da sallama a bakina na shiga cikin harabar gidan. Cunkus ɗakin tsumma kenan. Babban gidane sosai mai cike da ɗakuna a jajjere hagu da dama, sai filin tsakar gida, da wata doguwar kwatar data kai tun daga farkon gidan har ƙarshe. Ko wacce mace da kurfot ɗin girkinta a bakin ƙofar ɗakinta, kasancewar yamma ne ko wacce tana bakin ƙofarta tana faman kacaniyar girki. Yayin da yaran cikin gidan wasu ke guje gujensu, wasu ke wasan gare gare abinsu. Datti takota ina a tsakar gidan kamar gidan gwagware. Assalamu alaikum sannunku da gida" Na faɗa ma matan gidan. Da fara'arsu kuwa suka tarbemu, nace. Mune sababbin zuwan da muka kama ɗakuna" Hajara tana bayana sai ƙarema gidan kallo take yi. Bulamana da Ahmad kuma bayan sunyi sallama, ko wanne ya nufi ɗakin daya kama da kayayyakinmu. Mu kuma muka tsaya aka gaggaisa da matan gida. Wata mata wacce ake kira maman Sabeer tace. "Ga can ban ɗakunan gidan, sune daga ƙarshen gidan, na wanka biyu, na ba haya ma biyu. Amman babu kitchen kun dai gani ko wacce dai a ƙofar ɗakinta take girkinta. Mu matan aure dai mun kai mu Ashirin da uku ko Uwa? Ta tambayi matar dake tuƙa tuwon dawa a ƙofar ɗakinta. "Mu ashirin da biyu dai, kin mance Hauwa zaman idda take yi, data gama zata kwashe kayanta. Sai masu zaman kansu mutum takwas, mu dai talatin ba ɗaya in an cire Hauwa da zata tashi." Mamakine ya kamani da naji sun ambaci masu zaman kansu. Hajara tace. "Au a cikin gidan harda masu zaman kansu kuma ya kuke ƙarewa da mazajenku?" Matar da aka kira Uwa ta yi shewa tace. "Waye ma Hajiya Dumba ba zata saka ba a gidanta, matar da bata san mutunci ba, kuɗi kawai ai tasa a gabanta. Ai kuwa da masu zaman kansu muke zaune, amman ai kowa harkar gabanshi yake yi, babu ruwan matan aure da masu zaman kansu. Maman Sabeer tace. "Abun takaicin ma sai kuna zazzaune, za'a shigo muku da ƙaton gardi, baku da yanda kuka iya, wani ma da wando iya cinya yake shigowa, gida ya kaure da hayaƙin sigari. Gidan haya makaranta." Ni dai jikina a sanyaye na wuce su a tsaye, Hajara na jin kanun labarai. A tsaye na samu Bulamana, da halama jiran shigowata yake yi. Shi nake kallo. "Kinga irin gidan ko? Kiyi haƙuri mu lallaɓa, in sha Allah ba zamu wuce shekara guda ba. Wallahi rashin kuɗine yasa na kama wannan gidan, bani da kuɗin da zan kama ɗaki in biya shekara, shi kuma wannan duk wata dubu uku ake biya shi yasa. Idanu na lumshe nace. Ai ko dokar daji ka kaini ni mai zama ce, ballan tana nan gidan na mutane. Karka damu kanka, Allah ya hore mana sai mu sake gida." "Ameen Yahanasu na. Inason in fita yanzu zan dawo amman." Tausayinshi ne ya kamani, dana tuna gidanshi na Kaduna, da irin motar da yake hawa, gadon da yake bacci akai ma mai shegen kyau. Adawo lafiya Allah ya tsare." Da "Ameen" Ya amsa yasa kai ya fita. Ɗakin na ƙarema kallo, ɗakine madaidaici, shi ba babba can ba, amman ba za'a kirashi ƙarami ba. Ga ƴan katifu madaidaita guda biyu ya siyo, ɗaya tamu ɗaya ta yara. Mayafina na zare, na shiga kaye kaye, dadduma na shinfiɗama su Bawa a gefe suka zauna. Ni kuma na fito tsakar gidan ina neman ɗan dogon abu da zan iya hawa in kafa labule. Maman Sabeer tace. "Bari in ɗakko miki kujerar ɗinkina inaga zata kai miki, labule zaki buga?" E kawai nace mata. Ta shiga ɗaki ta miƙo mun kujerar, nayi godiya na koma ɗakina. Amman ko da na hau kujerar tsayina bai kai ba, sai da na ɗaura jakar kayanmu sannan tsayina ya kai. Labulen ƙofa na saka, na saka labulen windo. Ragowar labule biyun da suka rage, nayi dabarar raba ɗakin biyu da labulayen, kuma yayi kyau. Dakatawa nayi dan naji an soma kiraye kirayen sallar magriba. Ruwa na ɗiba a butar da na gani a kusa da wata ƙaramar randa ta wajan bayan ƙofa. Na shiga ƙyanƙyami da tashin hankali sosai sanda na shiga bayan gida, da ƙyar na samu gefe guda na tsugunna, a tafin hannuna nayi fitsarin dan gudun Infection (sanyi) ya kamani in shiga ukuna. Kamar zanyi amai haka na fito, nayi alwala a tsakar gida na koma ɗakina. Bawa na zuba ma ruwa nace ya fita ƙofar ɗakinmu yayo alwala yazo mu yi sallah, dan naga kowa a gefen ɗakinshi yake komai, naga wasu ma a tsakar gida suke sallah. Ina idar da sallar magriba, na ci gaba da gyare _gyare, nice har bayan isha ina abu ɗaya. Cin cin da kilishin da Hajja ta bani na fito dashi na ba Bawa da Maryam su ka ci. Na ɗiba da yawa na miƙa ma Hajara. Shinfiɗe Bawa da Maryam nayi a katifarsu, ina zaune a cikin duhu. Sai tunane tunanen rayuwa nake yi. Sallamar Bulamana na jiyo a bakin ƙofa, da sauri na taso na nufi ƙofar. Kurfot da kwatan buhun gawayi ya ajjiye mun a gefen ɗakina kamar yanda na kowa yake, ledar hannunshi na karɓa na shigo ciki, ya biyo bayana. "Subuhanallahi na mance a duhu na barki ke da yara ai." Yai maza ya kunna wayarshi, a lokacin ne yaga yanda na gyara ɗakin yayi tsab dashi, murmushi ya mun tare da cewa. "Allah yai miki albarka matata Ameen mijina. Nace ina dariya dan in ƙarfafa mishi guiwa, amman a zahirin gaskiya ina tausayin rayuwar da zamu yi a gaba, ina fatan Allah ya shiga cikin lamarin namu ya taɓa." "Ga taliya na siyo leda biyu, akwai mai da maggi,da kayan miya duka, sannan akwai ƙosai da biredi a cikin ledar, ki tashi yaran sai kuci, in yaso da safe kya dafa taliyar ko?" Hannunshi na kamo, na ɗauki ledar, yana biye dani muka shige uwar ɗakin da na haɗa mana. A bakin katifa na zaunar dashi, na taimaka mishi ya cire rigar jikinshi wacce ta jiƙe da zufa sai warin rana yake fitarwa. "Ka zauna ka huta, yara sunci abinci kafin suyi bacci. Amman ni banci ba ina jiranka. Amman ko zaka ɗan watsa ruwa kafin muci abincin?" Murmushi yayi tare da lumshe mun idanunshi. "Nagode da kulawarki a gareni. Mu ci abincin tukunna bana son ki yi ta zama da yunwa." Bana son inyi jayayya dashi shi yasa na buɗe mana ledar ƙosai da biredin, muna ci muna korawa da pure water, muna hira harda dariya. Bayan mun gama, na zuba mai ruwa a bokiti ya ɗauka, na zuba wani a buta na bi bayanshi dashi. Matan gida ko wacce ta baje a tsakar gida da iyalanta, wasu na cin abinci da mazajensu da yaransu, wasu kuma firarsu suke yi, wasu a zaune, wasu a kwance. Duk inda muka wuce Bulama na yi ma mazan sallama kafin mu wuce. Ruwan butar hannuna na kora dan rage dattin bayan gidan kafin ya shiga, ni kuma na dawo na sake cika ruwa a buta na koma. Ina komawa yana fitowa, nima wankan na faɗa nayo yana gadina, dan babu ƙofar kirki a bayan gidan. Bayan mun gama muka tawo tare muna ɗan taɓa hira har muka shiga ɗaki. "Akwai brosh da man goge baki, daure ki ɗakko mana mu goge bakinmu." Buɗe ledar da ya shigo dashi nayi na ciro sabon brosh ɗin dana gani, na haɗa da nashi brosh ɗin da man goge bakin. Shi kuma ya ɗebo mana ruwa a buta muka fito mu ka yi brosh a bakin kwatar data raba gidan biyu, hatta wanke wanke a bakin kwatar naga sunayi, yara kuma a wajan suke tsula fitsarinsu. Mun raya wannan dare da soyayya mai wahalar goguwa, rungume da juna mu kai baccinmu cikin farin ciki sosai. Da asussuba ina bacci Bulamana ya tashi ya buɗe ƙofa ya fice. Zare sakatar da yayi shi ya tasheni daga bacci, a hankali na miƙe na mayar da doguwar rigar baccina, na yafa mayafi na leƙo. A gaban kurfot na samu Bulamana yana ta kiciniyar hura wuta da leda ya kasa. Murmusawa nayi, bai ankaraba yaji na karɓi ashanar a hannunshi. Bansha wuya ba wutar ta kama, a hankali ta ruru na ɗaura ruwan zafi. Shi kuwa da ruwan sanyi yayo wankan sallah, dana soso da sabulu. Ƙarfe huɗun dare ne, amman mata har sun soma fitowa domun hura wuta. Allah sarki dama haka marasa ƙarfi suke gudanar da rayuwarsu abun tausayi? Allah sarki, ni ban taɓa ganin irin hakan ba, kasancewar gidanmu akwai rufin asiri babu laifi. Juye ruwan zafin nayi a bokiti nayi wanka na fito, a tsaye na samu Bulamana ya soma sallah. Kayan jikina na sake, na fita da kayan jajjage gashi banda turmi ko gireta. Leda na ƙulla a hannuna, na yayyanka kayan miyan da wuƙa. Bani na gama haɗa sanwa ba sai bayan sallar asuba, lokacin gidan ya ɗauki haramin kacaniyar yara da iyayensu, anata gaishe _gaishe. A ƙofar ɗakina nayi ma su Bawa wanka kamar yadda naga matan gidan nayi. Ƙarfe bakwai na gama girkina tsab, na zuba gaushi a kaskon turaren wuta na shiga dashi. Turaren wuta mai daɗin ƙamshi na zuba a wutan. "Su Bawa zasu ci gaba da zuwa makaranta, amman wata makaranta ce mai suna Zainab Acadamy na sanya su. A cikin layinnan take, in zamu fita zan nuna miki. Sai ki kaisu, ƙarfe uku suke tashi a makarantar, tunda 2 ki ke dawowa gidan sai ki dinga ɗakkosu." To in sha Allah, Allah ya basu nasarar karatu. Bawa to maza a gamakaryawa ko za'a koma makaranta. Bawa ya dubi Abbanshi yace. "Dady ina momy take?" Bulama Babba ya dubeshi da kyau, yayi ɗan jim kafin daga bisani da bashi amsa da cewa. "Momynku tayi tafiya kaji Bawa, ba yanzu zata dawo ba, ka kwantar da hankalinka kaji?" Abunka da yaro kai kawai ya gyaɗa. Yana gama cin abincin ya miƙe yana kallon agogon hannunshi. "Madam bakwai da rabi harta wuce, ya kamata ki taso mu fita, kar Ahmad ya soma ƙorafi" Dama a shirye nake tsab cikin farar lafaya mai taushi, takalmi kawai na saka na rataya jakata, na kama hannun Maryam, shi kuma ya riƙe hannun Bawa, a jere muka fito, dai dai fitowar Ahmad da yara shima. MRS BUKHARI CE [06/08, 4:26 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 25 *INA MIƘA SAƘON GODIYA GA ƊUMBIN MASOYANA. NAGA SAƘONNIN KU NA YA JIKI, NAGODE SOSAI, NA SAMU SAUƘI ALHAMDULILLAH AMMAN HAR YANZU INA KAN MAGANI, ZAMU LALLAƁA IN SHA ALLAH. ƳAN BATI ASHE SUNA DA YAWA, WASU SUNYI ƘARFIN HALI SUN KIRANI SUJI JIKINA, KUMA FA BASU SAI LITTAFIN BA BANSAN MA DAGA INA SUKE BA. AMMAN WALLAHI NAJI DAƊI TUNDA NASAN SO NE, AI AKWAI LITTATTAFAN KYAUTA MA DA KO SAURARENSU BA'AYI. NI BANYI ALLAH YA'ISA BA, ƘOFA A BUƊE TAKE KOWA YA KARANTA, ABUNDA ZAN SAMU IYA SHI ZAN SAMU. INA ALFAHARI DA RUBUTU, INA SONKU MASOYANA* Mabaruka ta dube ni tace. "Zanyi miki baya ni ƙawata daga baya, kafinnan bari in kwafe number motarshi" Wuce mu yayi a hankali baya wani gudu. Nan da nan Mabaruka ta ɗauki number motarshi a hoto. Ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Ni nafison ɗan bana bakwai, so nake in gwangwaji romon soyayya da yaro matashi mai jini a jika. Wani sa'in sunfi daɗin sarrafawa ki mallakesu hankalinki kwance. Ƙila baifi ace matarshi ɗaya da ƴan ƙananan yaranshi da basu wuce biyu ba. Kinga basu girma ba, balle suma suita cin kuɗinki ta hanyar kai sunayensu wajan boka dan ai musu farraƙu su da uban, tanan kuɗina ya huta, sai inji da ubansu da uwarsu kuma. Wannan shine dabarata ƙawata, gobe sai Jos in Allah ya yarda " Baki kawai na taɓe bance da'ita komai ba, ra'ayinta ta faɗamun, nima da nawa. Washe gari da duku _duku muka kuma ficewa, ba mu muka dawo Kaduna ba sai bayan isha. Amman aikin gama ya gama, boka ya bata kwallin da zata sa a idonta, da misalin ƙarfe biyar na yamma, taje kan titin isa kaita ta tsaya. Wannan matashin zai ganta, zai tsaya ya ɗauketa" Ai kuwa yanda boka yace hakanne ya faru, komai ya tafi dai_ dai irin yanda Mabaruka take so. Abunka da sihiri Salisu ba ƙaramin rikicewa yayi akan Mabaruka ba. Bayan ya kaita gida, su kai musayar number, tare da alƙawarin zai dinga kiranta, kuma zai yi ƙoƙarin fahimtar da iyayenshi kafin ta gama idda. Sabida wai bai jima da auren ba, ɗan shi ɗaya ne, matar tashi tana gidan iyayenta tana wankan gida. Wannan kenan, haka rayuwa tai ta tafiya, komai na tafiya yanda ake son shi. An kawo sadakin Nafisa da kayan na gani ina so na garari, biki ƙarshen watan da muke ciki za'ayi shi, Amarya zata tare a Abuja. Kwana biyu da bikin zasu wuce ingila. Shirye shiryen biki ya kankama sosai, Alhn Nafisa sai ɓarin kuɗi yake yi mana tamkar mara hankali, ko da yake duk wannan abunda yake yi bai san yana yinsu ba, dan an juyar mishi da tunaninshi ne, kuɗin da yake jibga mana bama amfana da komai, malamai ke morarsu dan kullun a cikin kawo kaza, za'ayi miki kaza, sai an kace bakin wane, haka dai karatun yake kullum. Ana cikin haka Sagiru ya dawo, ya sake zama abun tsoro, ya kuma riƙa a iskanci, har karya ya ajjiye mana a gidan mai ciki ma, kuma a dole Mama take zuba ma karyannan abinci da ruwa. Ni kuwa dashi ko ga maciji bama yi." YAHANASU: Cikin raɗa Bulamana yake mun magana. "Kukan ya isa nace ko? Taya raina bazai ɓaci ba uhm Yahanasuna, kinsan irin sonki da kishinki da nake yi kuwa?" Cikin shessheƙar kuka na ɗago kaina muka haɗa idanunmu waje guda. Kayi haƙuri bazan sake ba, nayi hakanne dan in samar maka sauƙi" "A'a wannan sauƙin bana buƙatarshi sam Yahanasuna. Wannan ai aikin maza ne ni zanyi abuna. Na barki da girki da kulawa da yara." Banyi aune ba naji ɗumin leɓenshi akan nawa yayi musu riƙon alewar yara. Nuna rashin gajiyawa nayi, na ba mijina kulawar da duk ta dace. Cikin minti goma na faranta ranshi. Kanshi na saman pillow yayi baccinshi, ni kuma na shiga sosa mishi kai. Cikin baccin yasa hannunshi ya cire mun hannuna daga sosa kanshi da nake yi. "Allah yayi miki albarka, ya faranta miki kamar yadda kika faranta mun kiyi baccinki. Idanuna na lumshe wasu zafafam hawaye suka gangaro kan kuncina. Tausayinshi ya kama ni sosai, naso ace na kawo ma Bulamana budurcina, amman kash ƙaddara ta riga fata. Yanzu ne na gane hikimar Ba Bakura daya haɗa aurenmu. Tun a baya da Bulamana ya ci mun mutunci akan ƙarya ma nake yi ba fyaɗen da akaimu. Bayan wannan bai sake yi mun maganar ba, ko a fuska bai nuna mun ya ji zafin jina ba cikakkiyar mace ba. Da wannan tunanin nayi baccina, bani na farka ba sai huɗun asuba. Akan sallaya na tarar da Bulamana yana tulawar Qur'ani. Muna haɗa idanu yayi murmushinshi yace. "Kaddai karatunane ya tayar dake a baccin? Nima murmushin na mayar mishi. A'a baccinne ya ƙare mun, da yake na saba tashi Sallah. "Hakane, ruwan wankanki yana wuta, ki yo wanka ki dawo, ko raka'a biyu sai kiyi nafila ko ƴar albarka?" Kallon tuhuma nayi mishi, inason tambayarshi waya hura wutar? Amman sai ya girgiza mun kai halamar A'a. Bakina na rufe bance komai ba. Zani na ɗaura a ƙirjina na zura hijabina na fita tsakar gidan. Maman Hassan ce kawai take ta faman wankin wake, tana yin alalar siyarwa da safe, dan jiya da zan fita naga an yi layi sai saye akeyi. Gaisawa mu ka yi, na wuce ta zuwa bayan gida. Duk sammakona wasu sun riga ni. Sai da na jira aka fito sannan na shiga, nayi wanka biyu, dana sallah, dana soso da sabulu. Nafila nayi, tare da shafa'i da wuturi. Qur'ani nima na ɗauka, nayi karatu kamar na minti goma haka, kafin na soma ragargazo roƙon Allah, buƙatun duniya dana lahira, arziki mai amfani ta hanyar halali babu wanda ban roƙama mijina ba. Kafin na tashi kuma na shiga ɗan kaye kayen ɗaki. Ƙarfe biyar na tashi yara nayi musu wanka, a lokacin matan gidan kusan rabi duk sun fito, ko wacce na hidimar dake gabanta. Biyar da kwata su Bulamana suka wuce masallaci, harda Bawa. Kafin su dawo na gyare ɗakina tsab sai ƙamshin turaren wutan dorot yake yi, ina ɗaura ɗumame na gabatar da sallar asuba. Na dama kokko na gama ɗumamen shinkafa da miyar da muka ci da daddare. Sai ƙarfe shiddan safe suka shigo. A tsanake kowa ya shirya, cikin annashuwa muka gama karyawa Tsab. Na ɓararraka ma su Bawa taliya da miyar jiya wanda zasu yi break dashi a makaranta. Tare muka fice yauma. Sai da na shiga ɗan sahu Bulamana yace. "Aff madam na mance yau ba sai kin biya ɗakko yara ba, Hajara zata dinga ɗakkosu tunda tana gida. To shikenan ranka shi daɗe sai kun dawo" Mu kai sallama na kama hanya. Rayuwa haka tai da yin tamaule da da mu, muna rayuwa cikin farin ciki da soyayya, harma mu kan mance a ɗaki ɗaya muke rayuwa, amman rayuwar ta maneji sosai muke yi, cikin sati guda shaƙuwata da Bulamana ta ƙara yin ƙarfi sosai. Kuɗin adashen dana ɗauka da kuɗin tallafin dana samu, na tarkata da ɗan kuɗaɗen da Ya Innana ta bani a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, duk na haɗa na tarkata na siya mana ƙaramin fili a gandu, wanda baifi a gina ɗaki biyu da bayan gida da kitchen ba. Da sunan Bulamana aka cike takaddun, Binta ce ta shige mun gaba, da ƙaninta har aka gama komai, aka damƙa mun takaddun filin nazo na adanasu, ba tare da sanin Bulamana ba. Ɗan kuɗaɗen da suka saura a hannuna su nake son in soma juyawa amman inata tunanin me zan dinga siyarwa. Kamar wasa muna maganar da Bulamana yace me zai hana in dinga yin meat pie ina kaiwa wajan aiki. Ai kuwa munyi wannan hira da kwana biyu na soma yin meat pie. Na dubu ɗaya na yi, babu laifi duk ya ƙare har ana nema, sabida na yi shi da arha, ban bi babbar riga ba. Rayuwa sai daɗi take yi mana, kusan kullum sai mun yi waya da gida, iyaye da ƴan uwa. Bani da damuwar komai, sai shaye_ shayen miyagun ƙwayoyi da kullum a cikin sake dulmiya nake. Har cikin zuchiyata inason in dena shan komai. Amman abun ya ci tura, in nayi kwana ɗaya bansha ba, ko rintsawa bana yi, sai inji kaina kamar zai rabe gida biyu. Ko da na kira Hajja Fati a waya nake yi mata ƙorafi akan hakan, cemun tayi bazan taɓa komawa kamar da ba, kuma bazan taɓa samun sukuni ba in dai ban sha ba. Gaba ki ɗaya abun duniya duk yabi ya dame ni. Kamar ko da yaushe ina zaune nayi rashe_ rashe a tsakar ɗakina, labulen ɗakin yana rataye a saman ƙofa, kuɗi nake ta faman shiryawa, ina yi ina kora laka mis ɗina. Bawa ne ya biyo Maryam a guje zai doketa, ta faɗo kaina da hanzari. Nayi carab na riƙeta ina jin son yaran sosai, gani nake tamkar ni na tsugunna na haifesu. "Umma kinga Maryam na tsokanata ko?" Cewar Bawa. Hannunshi na riƙe nace. Ka yi haƙuri kaji Bawa? Maryam ƙanwarka ce banda duka. Ke kuma ja'ira banda tsokana, riƙe hannunta ku je ɗakinsu Anisa ku yi wasan ku. Hannunta kuwa ya riƙe suka fita, da kallo na bisu ina ganin cikakkiyar wautar uwarsu data kasa fauwala ma Allah lamuranta, ta tsugunna akan yaranta. Ina cikin tunanin nan sai na jiyo muryar Bulamana yana gaisawa da Hajara dake tsakar gida, sai kwankwatsa hira akeyi a ƙofar ɗakinta, gulme_ gulme kuwa kullum a cikinshi suke, suce mijin wannan kyakkyawa, suce mijin wance mummuna, ko ita matar ace mata mummuna. Kamar ni kam da Bulamana ina jin yaran da suke zaman kansu a gidan suna gulmarmu. Gamu baƙaƙe munana, wai in muka haihu yaranmu ba zasu ganu ba dan muni. Ni kuwa hamdala nayi da yasa iyakar munina a iya fatar fuskata da ƙirar jikina yake, amman zuchiyata mai kyauce, tunda zaman aure nake yi, ba dandi ba. Kuma na gode Allah da Allah ya bani miji mummuna mai kyakkyawar zuchiya ma'abocin addini da sanin darajar mace. Da sallama ya shigo yana washe mun baki "Kaga Hajiyan kuɗaɗene kike lissafawa haka, iye" Dariya mu ka yi dukkanmu. Waje ya samu nesa dani ya zauna, kasancewar labulena a ɗage yake. Me ka siyo mana ne naga leda har bibbiyu?" "Kaji me bakin kwaɗayi ko? Sabulu da omon wanki na siyo, ki fito da kayanki dana yaran da nawa duk zan haɗa in wanke, ke kuma sai kiyi kwalimar da kika ce kinason kiyi. Wannan kuma naman kan saniya ne, nasan kina so shine na siyo miki ayi mana farfesu da farar shinkafa. In Allah ya kaimu sati me zuwa in an yi albashi zan siyo mana gado. Akwai wani gado da katifa dana taya, naji yayi mun sauƙi, amman fa kiyi haƙuri ba sabo bane na hannu ne" Murmushi nayi nace. Allah ya saka da alheri Bulamana ina godiya sosai. Batun siyan gado da ka ɗan jinkirta ba yanzu ba tukunna, banyi ƙorafin yanda nake ba, Alhamdulillah. Akwai abubbuwan da suka fi gado da katifa mahimmanci a gabanmu, lokacin da ya dace ayi za'ayi. Kace yau zamu goge wuya da farfesu. Amman nasan ba'ayi biya ba ina ka samu kuɗi?" Dariya yayi yana nuna ni da yatsa. "Dama nasan sai kin tambaya. Fito mun da wankin waje, zamu yi maganar." Tashi nayi na haɗo kayan wankin basu da yawa kala bibbiyu ne, sai zanin gado guda ɗaya. A waje na same shi akan turmi yana kaɗa kumfa. A gabanshi na dure kayan wankin. Gidan cike da mata harda na maƙota anata sharara gulma, sabida rashin abun yi. Ƙazanta tayi musu katutu tun safe in suka fito, babu abinda suke in banda gulma da shewa, tsakar gida duk datti, bayan gida duk zarnin masifa. Ɗakunan biyu dana shiga da suka haihu kuwa, abun ya matuƙar bani mamaki. Wasu tsunmokarai da annakiyoyin datti ne zai soma maka maraba, ga wani hamamin tsami da warin datti da ɗakunan suke yi. Ko da yake da dama a cikinsu ko tsabtar jikinsu basu san ya zasu yi ba. Ɗai ɗai ku a cikin gidanne masu tsabta, dan ko ƙofar ɗakinsu ka kalla kullum fes fes dashi. Kullum sai na share ƙofar ɗakina, kuma kullum saina karkaɓe tokar kurfo ɗina, har mopping ƙofar ɗakin nake yi da tsumma kullum. Wayar Bulamana ce tayi ringing harna juya zan shiga ɗakko naman kai zan ɗaura a wuta tunda akwai ragowar gaushi a kunne. Sai naji inason tsaiwa inji wake kiranshi, dan kwana biyunnan Zubaina na yawan damunshi da waya, jiya sha ɗayan dare ta kirashi a waya. Zaro wayar yayi a aljihunshi ya kara a kunne. Idanu na ƙura mai ƙur ina jin motsin kishinshi a ƙirjina. "Hello Zubaina ya jikin Yusuf ɗin to?" Bansan me tace ba na dai ji yace "Subuhanallah abun yayi tsanani haka harda ƙarin jini, amman sun faɗa miki abunda ke damunshin kuwa tun jiya nake tambayarki. Ni dai tsabar kishi ma shigewata ciki nayi, na juyo naman kan a tukunya na zuba ruwa na wanke shi tas, na girgije kurfo ɗina na ƙara gawayi na mayar da naman wuta. Har zuwa lokacin bai daina waya da Zubaina ba, suna maganar kuɗi ina dai jin ana ambaton dubu goma. Jajjayen kayan miya na soma yi. Yana gama wayar ya shiga kallona. "Kinga jikin yaronnan yayi tsamari fa har jini aka ƙara mishi yau. Inaga dole gobe zan kama hanyar Kaduna in duboshi. Allah ya kaimu, shi kuma Allah ya bashi lafiya" Iyakar abunda na faɗa kenan na tsuke bakina. Sai da na gama haɗa farfesuna tsab na koma ciki dan soma kwalima. Biyoni Bulamana yayi. "Haushi kike ji sabida ina waya da Zubaina ko? Kishi kumallon mata. Ai matsayinki ya kere matsayin ko wacce mace a zuchiyata. Zubaina kuma dole zamu dinga waya sabida akwai ɗana a hannunta, amman kinsan ko yarona baya hannunta zata iya kira ta wayata tace abata yaran zasu gaisa ko? To kiyi haƙuri ki dena fishin, Ahmad zaije ya dubo Yusuf ɗin in ya kama ni kuma ina manne dake. Haka yaita jana da wasa harna sake, daga baya ma na dinga jin kunya. Bulamana yana wanki ni kuma inata share share, matan gida aka kafa dabarshi sai zuwa wucewa akeyi dan a tabbatar da wankin yake yi mana ni da yaran. Shi kuwa bai san anayi ba. Ni da na sani sai janshi da hira nake yi muna dariya, yana aikinshi ina girkina, yara kuwa sai wasan gare gare suke a tsakar gidan. Shanya kayan yayi a igiya, ya zari bokiti ya tafi ɗebo ruwa. Nan fa surutu ya ɓalle, daga masu cewa ba banza na barshi ba, sai masu cewa ya basu mamaki, sai masu cewa Kanuri gidan asiri. Ni dai duk wacce tai magana sai in kalleta kawai. Yana gama jidan ruwan yayo wanka. Cikin shirin fita ya fito. "Zanje makaranta sai bayan isha zan shigo." Da adda'a na bishi, har sai da yayi nisa na yi shiru. Wayata ce ta soma ringin a ɗaki. Ko da na shiga sai naga su Dala ke kirana. Mun kuwa jima anata waye_ waye, suka sanar dani matar Dala ta haihu yanzu. Cikin jin daɗi da taya murna nayi ma Dala murna, bayan mun gama waya dasu na kira su Ya Innana da su ya Bagulaji nayi musu barka, na kuma kiran su Ba Modu nayi musu barka, hakan akeyi a gidan namu in aka samu ƙaruwa. Ba Modu yace. "Amman kiyi haƙuri ki yi zamanki tunda baki daɗe da komawa ba. In wani sha'anin ya taso kwa zo, sha'ani baya ƙarewa a gidannan ai" Naso zuwan, amman inna tuna bani da suturar mata da zan fita taro dashi, da wasa bana fatan aga gazawar Bulamana a kaina. Tunda yana bakin ƙoƙarinshi, ko farin ciki daya bani ya fiye mun duniya da abinda ke cikinta. Damuwata shaye shayennan ne da ya zamemun ƙarfen ƙafa, ina tsoro gami da jimamin ranar tonon asiri, bansan da wanne idanu zan kalli mijina da iyayena, da ƴan uwana ba. Bansan da wanne ido zasu dinga kallona ba, ƙila ma igiyar auren da nake alfahari da ita ta samu targaɗe, astagarufullah." Da haka mu kai sallama dai _dai ana kiraye kirayen sallar Magriba. Kulolin tuwo da miya na fito dashi tsakar gidan. Na zuba ma mijina nashi shinkafa da farfesun, yarama na zuba musu nasu, suka zauna a tabarma suna ci, kwanon Hajara na karɓa na zuba musu nasu, sai fara'a take yi da taga farfesun. Ruwan wanka na mayar, bayan na ɗauro alwala na shige ɗakina na yi sallar Magriba. Ina idarwa nayo wanka. Kasancewar garin zafi zafi akeyi bansa wasu kaya masu nauyi ba doguwar rigar bacci na saka har ƙasa, bayan na cakuɗe jikina da sassanyar Humra. Bawa yana zaune sai gyangyaɗi yake yi an sha gagamniya. Bawa tawo kayi sallar isha sai ka kwanta ko? Maryamana taso muyi Sallah. Muna idar da sallar isha duk yaran su kai bacci, laka mis ɗina na ɗaga na shanye rabin gora, kafin minti goma na soma jin network ɗina yana kawowa, da ya ɗan sauka ƙasa. Zuchiyata fes da'ita. Na daɗe da lura kwanciyar hankalina shine in sha kayan maye, sai in dinga jin wani farin ciki mara yankewa. In kuwa ban sha ba na wuni guda, sai in dinga jin tamkar an ɗauramun gingimemen dutse a kaina. Hayaniya a kunnena kuwa kamar kasuwar kurmi. Ina ninke kayayyakin wankin mu, Bulamana yayo sallama hannunshi riƙe da ƴar leda baƙa. Ledar na karɓa tare da yi mishi maraba da dawowa. Lemo ne guda uku a cikin ledar ya siyo mana. Murmushi nayi mishi, shima ya mayar mun. Muna hira muna cin abincinmu, har muka gama na raka shi yayo wanka, mu kai brosh a tsakar gida, nan muka bar Ahmad da Hajara a zaune a waje suna hirarsu suna shan iska. Maman Hassan ma suna ƙofar ɗakinta ita da mijinta, suna hira suna shan rake. Bayan mun yi mu'amala aure mun nitsa ne, Bulamana ya zo mun da wata magana." "Yahanasuna, ni ina ganin zan jona mastas a B.U.K badan komai ba sai dan in samu aiki me kyau. Ko da lecturing suka ɗauke ni ina laifi duk da na jarraba hakan ma ya gagara, amman ƙila in nayi mastas dasu zasu bani koyarwar Kinga kullum fa sai mun fita neman aiki ma'aikatu_ma'aikatu, duk inda muka je sai ace babu aikin. Ni na yanke shawarar bazan sake zuwa neman aiki ba. Hajja ma ta ɗan tuntuɓamun a wajan yayyunta, aikin bai samu bane. Amman shawarace me kika ce?" Gyara kwanciyata nayi a jikinshi, ina wasa da gemunshi nace. Wannan magana taka tayi Bulamana, amman ka sani yanayin karatu yanzu ya zama sai adda'a kuɗin registration anan matsalar take, in ka samu gurbin karatun dame zamu biya registration?" Ajjiyar zuchiya ya sauke ya ce. "To ni ina gani zan shiga adashe hannu biyu, akwai wanda akeyi a gidan yari. A kwai wanda malaman makarantar da nake koyarwa zasu kafa sati mai zuwa. Ina ganin duk zan sa hannuna ayi tare dani. Bani kaɗai zan koma makaranta ba Harda ke kema, gara mu shiga tare kawai." Dariya nayi mishi tare da muskutawa nace. Wasa kake yi dai, in yi yaya da aikin nawa da yaran?" Pa time zaki dinga zuwa makarantar, gara mu shiga tare kawai Yahanasu na. Ko koyarwarne ai sai mu yi tare ko ya kika ce?" Hakane Bulamana, zamu ci gaba da shawara a tsakaninmu kafin zuwan lokacin, duk da dai watannine ya rage, Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkhairi" Da "Ameen" ya amsa, muna ta taɓa hira har bacci yai awon gaba damu." Haka al'amura suka ci gaba da turawa, har yanzu Ba Bakura bai gama sakewa da Bulamana ba, amman yana ɗaga wayarshi, yana amsa gaisuwarshi harma ya tambayeshi lafiyarshi da tamu lafiyar. Ni kuma haka naci gaba da kasuwancina ina jijjuya kuɗi, duk da ba wani mai yawa nake yi ba, amman babu laifi ina samun alkhairi sosai, kayan fulawa akwai riba sosai. Kuma ina bama yara su tafi dashi makarata, ina ƙunsama Bulamana da Ahmad suma su tafi dashi, duk da haka sai dai hamdala. Wannan watan ina ɗaukar albashina, na cire nera dubu biyar muka sai bulo ni da Binta, itama ta sai ƙaramin filinta a kusa da nawa. Harma mun kira magina sun haƙa: ginshiƙi, ko wacce ta zuba bulo ɗinta a filinta ƙanin Binta na kular mana da wajan. Ragowar kuɗin kuma na yo cefane, na siyo ma yara da Bulamana takalmi. Ni kuma na siyi wata atamfar roba na ajjiye, dan ko kuɗin ɗinkin bani dashi, sai dai in jira wani watan. KOFUR ZUBAINA: Gida ya cika ya batsa tab da jama'ar biki. Yanzu aka gama ɗaurin auren a can gidan kawu Tanko. Mu kuma a cikin gida muna ta fama shirye shiryen halartar walima abokan ango suka haɗa. Na fito nayi wani irin mugun kyau da murjewa na sha make up rantsatstsiya, ina saye da wani tsadaden farin lace, da farin takalmi mai tsini. Mabaruka da Hadiza Aliyu, da Mariya Buba da su ka zo mun biki ko wacce saye take da farin leshi mai tsada, dan Mariya wani hamshaƙin Alhaji take aure Haka zalika Hadiza Aliyu itama mijinta me akwai ne. Mota Alh Liti ya ɗakko a ciki ya ɗebeni da ƙawayena, Mariya Buba tana biye damu da yaranta a cikin tata motar. Ni na kasance mace mai mugun baƙin ciki, nifa bana son a fini nafi son ace ni nafi kowa. Amman naga halama ƙawayena kamar duk sun kere mun, dan ko irin kuɗin da Salisu yake kashe ma Mabaruka Alh Liti baya kashe mun irinsu, duk da yana mun ɓarin kuɗi sosai, dan ko a hidimar bikinnan dubu ɗari da hamsin ya ba Mama, banda buhunhunan shinkafa biyar da yasa aka turo gidan, yace ayi abincin biki dasu, ni kuma dubu ɗari biyu nayi mishi total bai yi musu ba ya bani. Amman naga yanda Mariya Buba ta zama wata hajiyane, gashi tace mun zata sake komawa hajji wannan shekarar ita da mahaifiyarta, duk da shekara biyu kenan da dawowarta, taje Dubai, ta je Qatar, amman ni iyakata Najeriya. Hadiza Aliyu ma tayi aikin hajji tayi umara. Ohhh zuchiyata wani zafi naji tana yi mun, munfashina ya shiga bazaranar tarwatsewa. Bansan mun kawo holl ɗin ba, sai da naji fitar su Hadiza Aliyu daga cikin motar tukunna na ankara. Alh Liti na ƙura ma idanuna da suka rune tsabar baƙin cikin da nake yi da ƙawayena da ƙannena. Wai da gaske kuwa Alh Liti kana sona, kuma zaka aure ni a hakan?" A rikirkice ya kalleni, babban abunda ya tsana a duniya bai wuci ɓacin raina ba. Dan ko a waya ya ɓata mun rai, ba ƙaramin birkicewa yake yi ba, sai ya kira Mama ya dinga roƙonta akan ta bani haƙuri. Magana yake yi, amman ni hankalina ya koma wajan Asiya dana hangota ta sake zama wata wayayya, harda ƙawayenta biyu tazo bikin, wasu wayayyu matan alhazai, sun sha kwalliyar gwalagwalai. Tsaki naja a fili, na dubi Alh Liti a tsawace nace. Kai nifa na gaji da baƙar rowarka, Allah ya haɗa kowa da rabonshi. Ina kaiwa nan na ɓalle murfin motar na fice, harara na sakar ma Asiya da ƙawayenta na shiga na samu su Mariya Buba a ciki" MRS BUKHARI CE [07/08, 9:42 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 26 Da ƙyar na daidaita fishin fuskata, na zage mu kaita hira da su Hadiza Aliyu. Alh Liti sai faman kiran wayata yake yi, data katse daya kuma danna mun kira. Kashe wayar nayi dan dole. Ba shiri ya shigo buguzun_ buguzun da ƙaton ciki a gaba, malum_ malum ɗinshi cike da iska. Shaddace mai tsada fara sol a jikinshi. Agogon hannunshi, takalminshi da jar darar hularshi ita ta sake fito da tsantsar haskenshi. Gefena ya tsaya ya dinga magana dani, sai da su Mariya Buba suka sa baki sannan na biyo bayanshi zuwa waje, muka jingina a jikin motar da ya kawo mu. "Wai ni kam Gimbiya lafiya me ya birkita mun ke haka, yanzu ni me nayi miki da har zaki ce kin fasa aurena? Wallahi haɗari zan shiga mai girman gaske, ashe baki san girman sonki a zuchiyata ba ko, me kike so, waya taɓaki?" A yatsine na soma magana. Nifa in kwanciyar hankali kake nema wallahi ka game mun ginina kawai so nake in zuba ƴan haya, kaɗan ma ya rage . Sannan inason zuwa umara da zaran munyi aure, kuma ka siya mun mota." Murmushi yayi yana dubana da mitsimitsin idanuwanshi kamar an ƙwantali kabewa. "Shikenan abinda kike buƙata ai miki Gimbiya?" E ai kaji na faɗa ma yanzu" Wayarshi ya ciro a aljihu ko wa yake kira oho. Na dai ji suna maganar aje a duba ginin nawa ayi mishi estimet na kuɗin da gidan zai ci, komai a zuba masu tsada, dama damuwata kayan tails da kayayyakin cikin bayangidun, da wayaring sune suka rage kuma ba ƙaramin kuɗi zasu lashe ba. Wani farin ciki naji a cikin zuchiyata, amman a zahiri sake haɗe rai nayi. "Gimbiya a saki ran mana uhm ko so kike dai ki sukurkutani a wajannan ne? Ki bani nan da wata guda za'a kawo miki key ɗin gidanki, za'ayi miki komai, ɓangaren da kike son saka Mama kuma za'a zuba furniture masu tsada, Maganar umara in munyi aure wannan ai baki da buƙatar sai kin ce. Zamu zagaye ƙasashe sosai in kai ki yawo buɗe idanu. Mota kuma sai kin zaɓi wacce tayi miki, amman da direba zan haɗaki ya dinga kai ki ko ina. Ki yi haquri dan Allah a saki ran mana inji daɗi uhm?' Haka yaita faman lallaɓani da ƙyar na sakko, muka ɓalle da hirar soyayya. Haka dai aka gama walima duk muka watse. Washe gari akayi yinin biki, a ranar muka wuce Abuja gidan Nafisa, ni dai da ƙyar nake shaƙar nunfashi dan ji nake yi kamar zan zautu dan baƙin ciki. Sai cikin dare masu kawo Amarya suka iso. Washe gari da sassafe muka tattare ina mu ina mu muka nufi Kaduna. Nafisa kuma ƙarfe sha ɗayan rana girjinsu zai tashi zuwa ingila. Al'amura sukai ta garawa dai. Yanzu zaman gida ya sake yi mun rashin daɗi, daga ni sai Mama. Dan ma ina zuwa aiki shi yasa abun yazo mun da sauƙi. Maginan da Alh liti ya ba kwangilar ginin gidana suna ta aikinsu. Harma na kai Mama da Musa munje mun ga gidan, sai santi Mama take yi. Ni kuma sai jin daɗi nake yi. Burina in gama wannan idda data riƙe mun wuya in zama mallakin Alh Liti ya huta, in huta nima. Yahanasu: Yau tun dana tashi nake jin kasala sosai a jikina, a ciccije na kammala aikina, Bulamana sai tambayata yake yi abunda ke damuna. Na samu dai na lallaɓa naje wajan aiki. Sai bacci da bin sanyi a haka na wuni har muka tashi. Binta ta kalleni tace. " Ki sai P T ki yi awon ciki, gaskiya cikine dake. Wani farin ciki ya lulluɓeni, nayi murmushin jin daɗi. In kuwa hakane nasan Bulamana zaifi kowa farin ciki. Haka ƴan Damaturu zasu yi farin ciki." Zan siya kafin in shiga gida. Amman ba kince zamu je sabon gari siyan kaya ba?" Binta tace. "Aji garau zaki ce. Yanzu kuwa can muka nufa muje ko?" Muna cikin ɗan sahu Binta tace. "Matar da zaku je gidanta ku tattauna, a kurna take, zan baki lambarta in kunje kurnan sai ki kirata. Nima gobe zamu halarci wani taron ƴan siyasa da za'a gudanar a cikin gari. Zamu je ayi damu mu kwaso rahoto." Kallon Binta nayi nace. Uhm aikin jarida akwai wuya, wallahi aikin ya fice mun a kaina, musamman program ɗin nan da yake hannuna, rana ɗai ɗai ne fa bana zubar da hawaye a gaban matan da naje tattauna dasu fa. Sabida labaran nasu gwanin ban tausayi. Duk da labaran wasu matan gwanin ban ƙaye. Ki ga dai labarin mai shari'a Hajiya Turai. Gaskiya matar ta burgeni yanda ta tsaya a kan yaranta, ki gani kuma mijin ya rasu. Dole a buga misali da wannan baiwar Allah, ga masu zagin yaran mace. Ita kam gashi yaranta suna bautama ƙasa. Daga soja sai likita, sai lauya. "Kai Yahanasu nima labarin matar nan ya burgeni. Dama wanda suka kalla na tabbatar. Mun samu kiraye_ kirayen waya akan labarinta ba adadi." Muna cikin tattaunawa muka iso sabon gari. Sakkowa mu ka yi, ni na biya mai ɗan sahu kuɗinshi muka nufi gidan magajiya. A ɗaki muka same ta a zaune tana ƙirgama wata mata wasu kayan maye masu kama da ganyen shayi. Da ganin matar itama tsohuwar kilaki ce. Magajiya ta kalli Binta tace. "A Binta mai yar shaye_ shayen ƙwaya kenan baki da aiki sai shan ƙwaya. Nayi miki tayin ganye kinƙi, sai allura kika fi faɗawa dasu. itama ganyen fa duniya ce, sauke nauyin kai take yi sosai. Ja biyu kyawawa in kika yi ya wadatar dake, zaki ji hayaƙin ya wanke miki kwanya. Fatima basu labarin ganye" wannan tsohuwar kilaki ta dube mu ta watsar tace. "Ai kinsan shaye_shaye ra'ayine. Kuma ganye yafi dacewa da ƴan mata ko masu zaman kansu irinmu. Ihu muka jiyo daga tsakar gidan su magajiya. A guje muka fito dan gane ma idanuwanmu. Wata karuwa ce take wannan ihun, ta faɗa kwata jikinta ya lalace ga ciwuka taji a fuskarta da hannunta. Magajiya tace. "Nifa na gaji da wannan mahaukaciyar, ina Jumman Lokoja take, ita ta kawo mun yarinyarnan lokacin da hankalinta, amman yanzu tunda ta zama taɓaɓɓiya gara ta tafi titi karta hana kostomominmu shigowa. Jiya ta Hana Bala aci bulus wuce wa, sai zagi da ashariya take yi. Yanzu kuma jibeta. Wacce aka kira da Jumman Lokoja tace. "Magajiya yarinyar nan, inaga sai dai in sata a mota a yi hanyar barin gari da'ita sai mu saketa, tabi jeji tai ta haukarta. Tun da hankalinta nake jan kunnenta shaye_ shayen da take yi yayi yawa, karta kashe rayuwarta a banza. Da yake ƙadangarun bariki sun ɗaure mata baya, ai banza tayi dani. Ta dinga yin allurai, gashi da ƙuruciyarta zata ƙare a bola. In hankalina dubu ne yau ya tashi, da naji dalilin daya haukata wannan baiwar Allah. Na shiga ruɗani da tashin hankali mai yawan gaske. Hasaso kaina nake yi a cikin irin yanayinta na hauka. Ko wannan dalilinne yake sawa in ban sha kayan maye ba nake jin kamar zan danna ihu, ga wasu surutai da hayaniya da nake ji a kunnena kamar zan zautu" magajiya kamar tasan tunanin abunda nake yi, dafa ni tayi tace. "Karma ki sama ranki komai. Wannan ɗan kurɓe_ kurɓen da afe_ afen ƙwayoyin da kuke yi, babu abunda zai saki. Ke baki isa ki sha kwatan_ kwatan abinda matsiyaciyar yarinyar nan take sha ba. Har giya da koken sha take, alluran doki take yima kanta, itace shaƙar kashin ƙadangare. Ai wannan naku shaye _shayen na rage matsalolin yau da kullum ne, shi yasa nafi ciniki a wajan matan aure. Dan kaso saba'in bisa ɗari na kostomomina matan aure ne, masu ƙoƙarin cire takaicin mazaje ƴaƴan kunama, sun waye da ciwon zuchiya ko hawan jini ya kashe su, shine sai su kora harka" Ajjiyar zuchiya na sauke ina dafe da ƙirjina nace. Da har hankalina ya tashi wallahi, har nake jin kamar bazan sake shan komai ba. Amman wallahi ba iyawa zanyi ba, sai fa na kora nake jin daɗin komai. Siyan abunda ya kawo mu muka yi tare da ficewa a gidan, mun barsu anata dambarwar kama matashiyar mahaukaciyarnan. Kemis na shiga na siyo P T. A wajan mu kai sallama da Binta. Ina zaune shiru a bayan Ɗan sahu nayi mugun zurfi a cikin tunani da tashin hankali. Maganganun Jumman Lokoja dana magajiya sai karakaina suke a kaina. Haka ƙwaƙwalwata sai hasko mun hoton matashiyar mahaukaciyarnan yake yi. Idanuna na lumshe, tare da shafa cikina da nake tunanin kamar jinin Bulamana ya samu wajan zama a mahaifata. Hakan ya sanyaya mun raina, har guntun murmushi ya sufce mun. Amman tunanin wannan yarinyar ya kasa goguwar mun, a haka na shiga gida da sallamata, hannuna riƙe da ledar cefanen dana tsaya a bakin hanya nayi mana. A guje su Bawa da Anisa suka nufoni, maryam na biye dasu itama a guje tana kiran. "Umma umma umma" Maman Hassan da su Maman Iklima mai kitso sai dariya suke ma Maryam. Tsugunnawa nayi na ɗauketa na rungumeta ina faɗin. Yarinyar ummanta, kinga su Maman Iklima sai dariya su ke yi miki ko? Maman Sajida ta dubeni tace. "Umman su Maryam anya ba cikine dake ba kuwa?" Tana gama faɗar haka ta saki kan matar da take ma kitso ta matso kusa dani. Ni dai sai dariya nake yi mata ina jin wani farin ciki. "Gaskiya cikine dake babu makawa, Allah ya raba lafiya, zamu sha sunan kanurai. Maman Hassan tace. "Ah za'a gwangwaje sunan kanuri a cikin gidannan. Sai dai wannan ƴa ko ɗa zai zo da baƙi kamar bawa, koma yafi bawa tunda Hajara tace mahaifiyarsu farace kamar tsada. Turus nayi na bi Hajara dake tsintar wake da ido. A tunanina matan gidannan basu da masaniyar bani na haifi su Bawa ba. Ashe aku mai bakin magana tuni ta fesa musu, harda haɗawa da suffanta uwarsu. Ko da yake nima nayi kuskure da nake tunanin Hajara ba zata basu labari ba. Allah kaɗai yasan me suka sani a kaina. Ɗan Murmushi na ƙaƙaro nace. Kaji mun maman Iklima da gani na sai kice cikine dani? Ke kuma Maman Hassan sannunki da kushe mun mijina. Ko da yake kun saba ai, kullum yazo wuce wa ina ji kuna cewa wannan miji na Yahanasu ba dai baƙi da jan ido ba, ga muni ko? Nagode sosai." Ba da faɗa na faɗa ba, asalima dariya ce a fuskata, amman na ɗauresu da jijiyoyin jikinsune, kuma sunji kunya ainun. Basarwa nayi na dubi Maman Iklima wacce ta juya sum_ sum zata koma bakin aikinta na kitso. Maman Iklima inna gama girki zan zo ki mun kitso." Cikin dariyar kunya da dibibicewa tace. "Mu fara kitson mana kafin ki ɗaura sanwar, in dai ba abu mai wahala zaki dafa ba, maman twins" Murmushi nayi nace. To bari inyi sallah, naji ana kiran sallar la'asar. Bawa muje ko?" Na ja hannun yaran nayi gaba, na barsu da kunya. Itama Hajara da muka haɗa idanu na bita da kallon kin kyauta, sai wani borin kunya take yi, sai labarin yara take bani. Ni kuwa na bagarar da'ita a gefe nayi alwala na ƙule ɗakina. Na daɗe a zaune a kan sallaya ina tunane _tunanen da bansan meye mafita ba, ni dai har ga Allah na kaɗu da ganin wannan yarinyar. Wata zuchiyar tana faɗi mun. "Anya ba zaki dena shaye shayennan ba tun kafin wankin hula ya kai ki dare?" Wata zuchiyar kuma sai zugani take yi da cewa. "Amman su ai ba kalar abu ɗaya kuke sha ba, kuma bakya shan giya da koken. Da ana haukacewa da Hajja Fati da Binta sun daɗe da yin hauka tuburan. Ga mata nan birjik da suke shaye shayensu basu haukaceba sai ke?" Da yake aikin shaiɗanne sai naji hankalina yafi rinjaya akan zuchiyar da take ƙoƙarin sake dulmiyar dani. Take na jawo jakata na ɓalle haɗin laka mis ɗina na kwankwaɗi abuna, na miƙe. Kallon ɗakin nayi babu wani gyara da yake buƙata, dan kafin in fita nake gyara ko'ina. Humrar gashi na jawo a gefen katifarmu, na bulbula a gashina, na sake lakutan KULACCHAM na gashi na shafe kaina dashi. Dama kan a tsefe yake tun jiya, ya kuwa sake danƙarewa. Kum na ɗauka, na fice na samu matan gida an kafa daba anata gulmar masu zaman kansu na gidan. Ni dai nawa idanu kawai, Mama Iklima tana kitso tana tofeni da yawu, tsabar gulma na cinta. Ni kam ki yi sauri ki gama mun kitso, bana son mijina ya shigo ban gama girki ba." Dungure mun kai tayi tana dariya tace. "Masu miji manya, ai ni nawa mijin ba miji bane ko, sabida baya mun wanki ko?" Nan fa maganar ta dawo kan maza. Maman Nuratu tace. "Ni ko sanda nake da tsohon ciki ma, Baban Nuratu bai taɓa mun dai_ dai da juye ruwan wanka ba." Maman Hassan tace. "Hana ƙarya Baban Hassan ya taɓa ninke mun kayan su Hassan sau ɗaya tak, lokacin suna jira jirai" wannan tace wannan, wannan tace wancan. Ni dai sai dariya kawai nake yi, ina ƙara godema Allah daya bani miji irin Bulamana. Alhamdulillah da munin nashi, da baƙin nashi a hakan nake bala'in son shi. Shima duk baƙi da rashin dirina bai hana shi tsantsar sona ba. Babu abinda kyakkyawar mace zata nuna mun, ta fannin soyayyar miji. Wallahi wata kyakkyawar bata samu kwatan son da Bulamana yake yi mun ba, a wajan mijinta. Kuma wata kyakkyawar mai gashi bata fini jin daɗi da kwanciyar hankalin aure ba. Me zan ce ma Ba Bakura? Sai adda'ar gamawa da duniya lafiya. Maman Binta ce ta katsemun tunanina tace. "Yahanasu a bamu laƙanin muma mana, kinsan fa Kanuri, da Shuwa basa barin mazajensu haka, akwai wasu asiri _asiri da ake haɗa musu a gida" Da sauri na tare ta da cewa." Wannan duk ƙaryace kawai sauran ƙabilu suke jifan ƙabilarmu da'ita." Hajara tace. "Umman Maryam kina nufin Kanuri basa asirin mallakar miji?" Na kalleta nace. Bazan ce muku kanuri basa asiri ba. Kamar yadda bazan ce, fulani, Hausawa, Yarbawa, Inyamurai, Ibira, Igala, arago da sauran ƙabilu da dama basa asiri ba. Ko wacce ƙabila nayi. Ni abinda na sani shine. Tunda na taso ban taɓa ganin wani abu daya jiɓanci asiri ba. Mahaifiyata da dadduma da Qur'ani, da carbi na santa. Kuma nima guzirin data bani kenan. Abunda na sani da matan Kanuri suna da tsantsar biyayyar aure, da tsantsar tausayin miji. Ƙamshinmu da tsabtarmu ke lashe zuchiyar mazajenmu. Amman ba komai ba. Allah yasa kun fahimci bana cikin Kanuri masu mallake miji ta hanyar asiri, kamar yanda kuma bakwa ciki ko?" Ɗankwalina na ɗauka na karkaɗe jikina dashi. Na ajjiye ɗari biyu a cinyar maman iklima. Nagode da kitso, bari in je in ɗaura girki" Nan na barsu suna ta tattaunawa. Gaushi na ɗiba a kurfot ɗin Hajara na zuba akan gawayina. Sai na zauna na soma gyara kayan miyana. Farar kuskus na dafa da miyar tankwa, wacce na saka mata ɓararren kifi. Na mitstsike tsamiyar dana dafa tun safe da kayan ƙamshi a ciki. Na tace na zuba ɗan gishiri da suger. A ƙatuwar gora na juye, na miƙa ma maman Kaula ta ɗan samun a gidan ƙanƙara. Abincin kuma na zuba a kula, na ɗaura a faranti da fileti da cokali, da cokalin ɗiban abincin, na shige dashi ɗaki. Na bunke ɗakin da turaren wuta. Sannan na shiga shara, da wanke wanken Kayan dana ɓata. Ina fitowa wanka aka soma kiran sallah. Naga wucewar Ahmad masallaci. Bulamana nasan sai yayi isha zai shigo gidan. A gajiye tulus yake shigowa ga yunwa. Abinci na zuba ma yara, na je na karɓo jus ɗina, na sai ruwa mai sanyi a wajanta. Ina zaune na tuno da P T ɗin dana siya. Ai ba shiri na ɗauka nayi bayan gida. Fitsari na tsula a kanshi bayan na ɓare. Cikin saƙanni sai ga jan layi biyu sun fito ɓaro_ ɓaro. Lumshe idona nayi. Lallai yau akwai goron albishir kenan Bulamana?" Ina shiga ɗaki na tarad dashi a zaune a gaban abinci yana ta kiciniyar zubawa. Da sauri na riƙe cokalin zuba abincin na idasa zuba mishi. Sai da na tura mishi abincin da kofin dana tsiyaya mishi jus ɗin gabanshi, sannan nace mishi. Sannu da shigowa, ka dawo ina bayan gidane" Fuskata ya shafa yace" "Inata sallama ai, da naji shiru sai na shigo naga bakya nan, nayi tunanin Sallah kike yi. Bari dai inci abinci akwai labari me zafi yau." Yana cin abincin ina mai fifita, nima inaci, muna ɗan taɓa hira jifa jifa. Bayan ya fito wanka ne yake bani labari. "Ina wajan aiki da safe Wakil ya kira ni. Yana ƙorafi akan matarshi Maman Yahanasu, akan ta fiye ƙazanta, gashi bata yi mishi biyayya kwata_ kwata. A taƙaice dai har tayi zuchiya ta tafi gidansu. Iyayenta basu duba dangantaka ba, tunda duk dangin junane, da ta tafi, mai makon su kira Wakil ɗin suji ta bakinshi. Sai ba su yi hakan ba. Kawai suka turo ƙannenta suka ɗibar mata kayan sawarta da kayan ɗiyarta Yahanasu. Kinji halin da ake ciki yanzu haka, tafiya Damaturu ta kama ni gobennan" Shiru nayi ina tuno Maman Yahanasu. Zancen gaskiya ƙazama ce, nima na gani, dan ɗakinta har wani tsami yake yi, kaima ai ka shiga ɗakin. Babu ƙamshi irinna matan Kanuri sam. Amman Ba Hamma bai dace ace sun bar Anti Aissa a gida ba. Ya dace su tuntuɓi Wakil ɗin." "Kinsan wasu iyayen a kwaisu da goyon bayan yaransu. Ba Bakura kuma ya hana Ba Modu zuwa, yace Ba Hamma ya dace ya tuso Aissa a gaba ta dawo ɗakinta, ba wai a turo a ɗebi kayanta ba Ko kuma ya kirasu a waya, tunda ƙani yake a wajanshi, da kakan Ba Hamma, da Hajja Yahanasu, ƴaƴan wa da ƙani suke, kuma Ba Bakura ya taimaki Ba Hamma sosai a rayuwa. To tunda nine babba shine Wakil ɗin ya kira ni ya faɗa mun halin da ake ciki. Na kira Ba Modu ma a waya mun tattauna. Gobe zamu haɗu da wakil ɗin a Pataskum ɗin, sai mu je tare" Yana gama wannan jawabin ya jawo ni jikinshi, ya kai hancinshi zuwa kaina ya shinshina. Hannu yasa ya zame mun ɗan kwalina, a hankali ya shafa kitson nawa, da ɗan gashina da jelarshi bata wuce kamu ɗaya ba. A kunne ya raɗamun. "Kitso yayi kyau, mai kitson ma tayi kyau" Bakinshi ya ɗaura akan nawa, lumshe idanuna nayi, tare da cabke leɓenshi. Sai da muka samar ma da juna nutsuwa, sannan na ɗago da kalla na kalleshi, inason yi mishi albishir. Amman ina yayi bacci, sabida a gajiye tulus yake shigowa gidan. Sai da safe bayan ya gama shirin tafiya Tsab na tsaida shi a bakin ƙofa. Sai kuma na shiga kame_kame da ƙyar na faɗa mishi ina da ciki." Murmushi yayi, tare da saurin kamo hannuna ya kafeni da jajayen idandunanshi. "Da gaske ko zolaya Yahanasu na, shine baki faɗa mun tun jiya ba, asibiti kika je ko yaya kika gane kina da ciki?" Wannan tambayoyin nashi a jere su suka sani darawa. Gwadawa nayi da P T amman inason zani asibiti tunda bamu da aiki yau" "Alhamdulillah Allah na gode maka. Ki kula sosai Yahanasu, kinsan cikin fari sai da lallaɓawa. Allah ya raba lafiya, Allah ya bamu masu albarka" Da Ameen na amsa mishi. Dubu ɗaya da ɗari biyar ya bani, nasa hannu na karɓa. "Ga wannan kije asibiti, sauran canjin ki riƙe a hannunki duk abinda kika ga kina son siya sai ki siya. Kuɗin cefanenki na saka miki a bankaɗen katifa, dubu ɗaya ne, ki jalauta zuwa yau ko gobe. Akwai saƙo da Ahmad zai kawo miki da yamma. Ni sai na dawo." Nan mu kai sallama na bishi da fatan alkhairi. Yara sunata ɗaga mishi hannunsu, har yayi mana nisa, sannan muka koma ɗaki. A tsanake na shirya tsab, na fito rataye da ƙaramar jakata. Hajara na miƙa ma Su Bawa, na mata sallama akan zanje kasuwa, dan nasan dana ce mata asibiti zani zata baza ni a wajan matan gidan. Ban wani samu layi sosai ba can, duk da asibitin gwamnati ne. An gwadani, ƙaramin ciki ne har na sati Takwas, wata biyu kenan. Sun ce nan da wata biyu sai in dawo na soma awo. Murna a wajena ba'a magana, ina fitowa na yi ma Bulamana saƙon karta kwana ta wayarshi, na faɗa mishi satittikan yaron nashi. Kai tsaye na wuce sabon gari, a ƙofar gida na samu Magajiya tana faman ciniki. Ga matan aure nan suna ta siyan kayan maye. Wasu ma da goyo a bayansu, wasu kuma masu ciki ne. Sai mamakin yanda shaye_shaye ya zama ruwan dare a wajan matan aure nake yi. Magajiya ta miƙo mun laka mis gora biyu. Ni kuwa Magajiya ya ku ka yi da wannan matashiyar mahaukaciyar da rannan muka tarar ana artabu?" Shewa tayi tace. "Tuni Jumman Lokoja tasa manyan maza suka cabketa aka fice da'ita bayan gari aka wullar." Baki na buɗe da mamaki nace. Kuma iyayenta ba zasu zo nemanta nan ɗin ba?" "Karuwa ce fa Yahanasu, wa yasan daga inda ma tafito balle har azo wani nemanta. Kai naci gaba da jinjinawa, ina tsaye ina jiran canji na, in yi gaba, dan kullum nazo wajannan bana samun nutsuwa har sai na bar wajan. Sai inga kamar idon sani zai ganni asirina ya tonu. Wata matace tazo itama siyan abun mayen. Ni naga sai wani fisge fisge take faman yi, tana dafe kanta. Kwalba biyu na maganin tari Magajiya ta bata, a take ta shanye. A cikin minti biyar ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "Haba sai yanzu na dawo duniyar mutane. Da ji nake kamar za'a zare mun ƙwaƙwalwata daga ƙoƙon kaina. Wallahi kwana biyu na shiga halin rashin kuɗine Magajiya. Sai da na faɗa ɗakin matar gidanmu na aro kuɗaɗe. Ƙaro kwalba biyu, ki haɗa mun da laka mis gora biyu. Na yi maneji zuwa kwana biyu. Canji Magajiya ta miƙa mun na wuce. Hankalina yafi tashi yau fiye da wannan mahaukaciya dana gani. Dan Magajiya ce mana tayi, har giya da koken take sha, shi yasa ta haukace. Wannan matar da na baro a wajan Magajiya ai naga ita maganin tari da laka mis take sha. Amman jibi yanda ta fice a hayyacinta, wannan babu wani sauran hankali a jikinta, zaucewa ne kawai bata yi ba. Wasu hawayene suka sulalo kumatuna masu ɗumi. Wata nadama ce ta shigeni sosai. Mrs Bukhari ce [07/08, 9:42 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 27 *UmmuAffan Collection* _DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_ Royal jelly big Royal jelly 30 pieces Royal jelly small one 60 pieces inside the pack Vitamin C-100, Vitamin E big Pesona Dara Cantik ayu GLUTA white Khusus ibu Sugar wanita Majakani 3 in 1 Eve Care Juliet eve Phyton buster Phyton collegen Glute sparkling days ginger oil for hair Papaya oil for breast Garlic oil for hips Vitamin C serum Vitamin E serum Busty blend Gluta prime Collegen+C *Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144* Tare da taraddadin in na mutu a cikin wannan halin me zan ce ma Allah, ya iyayena zasu ɗauki wannan abun, daga ranar da asirina ya tonu, ya Bulamana zai kalleni daga ranar da wannan ɓallin zai ɓalle, yarana da wanne ido ni zan kallesu? Ƙila ma a haukace zan ƙare, duk wannan abubbuwan bazan gansu ina cikin hayyacina ba. "Hajiya mun zo fa" Muryar mai ɗan sahun da nake ciki ta doki dodon kunnuwana. Cikin rashin kuzari na fito na zaro kuɗinshi na bashi. Duk wanda ya kalle ni yasan nayi kuka. Da na shiga gidan babu wanda na yarda na haɗa idanu dashi. Hajara na bakin ƙofar ɗakina a gaban wani deepfreeza babba, mai ruwan toka, amman da gani na hannune kuma ya sha jiki, dan har tsatsa ne a ƙasan shi." "Kin dawo kenan Yaha? Ai ina nan tun tuni ina ƙarema wannan firji kallo. Gaskiya Bulama ya gwngwajeki, Allah ya baki miji mai zuchiya ba mai dukiya ba." Wani farin ciki ne ya lulluɓeni kamar wacce aka biya ma umara. Nan na shiga washe bakina ina dariya. Matan gidan duk suka rufu ana taya ni murna. Ahmad ne ya shigar mun da shi ɗaki, na kuwa yi sa'a da wuta. Mintuna kaɗan da shigar mun na kunna, na jejjefa pure water a ciki. Allah sarki Bulamana akwaishi da ƙoƙari dama shi haka yake tun yana ma yaro, yana mugun son ɗan uwa, ballantana ni da na zame mishi uku a ɗaya( 3 in 1 ) Ƙanwa, ƴar uwa, mata. Gahi ina shirin zama uwar ƴaƴanshi. Cikina na shafa ina farin ciki, na kalli tumbina a raina nace. Yanzu nasan ina haihuwa tumbina zai ƙara girma, ƙila har ƙiba in ƙara tunda ni mai jikin ƙiba ce. Sai na tuno da Fanna sanda ta haihu, sai da ta ninka ƙibarta ta da sau biyu, ga tumbi, ga kumatu. Har yanzu kuma tana nan da ƙibarta bata sauka ba. ( Amman ina tunanin in kira Maman Amal in sai constifree tea na kamfanin G H T maganin rage tumbi sadidan, harma da ƙibar. Sannan ta haɗamun da female care domun ya tado mun da komaɗata, tunda in mace ta haihu tana rasa abubbuwa da yawa. Kuma magungunan G H T ingantattun magungunane da aka samar dasu daga itatuwa. +234 703 777 8458 ga number ta ga me buƙata.) Duk da nasan irin tanadin da Kanuri suke ma mai jego wajan gyaran matantakarta abun sai son barka. Amman hausawa suka ce kogi bai ƙi daɗi ba. Da rana garin kwaki da ƙuli na jiƙa mana da ruwan sanyi. Na shinfiɗa mana tabarma a tsakar gida, dan zaman ɗakin bazai yiwu ba sabida zafi aka shiga, kuma ya sauka da ƙarfinshi sosai. A tsakar gida nayi sallah, nan na kishingiɗa bacci yai awon gaba dani. Sai la'asar Hajara ta tasheni tana zolayata. "Shi kuma wannan na sa bacci ne kenan, tun ɗazu sai sharara baccinki kike hankali kwance." Murmushi nayi mata. Na yunƙura na miƙe. A nan na kuma yin sallar la'asar, daga nan na soma haramar ɗaura abincin dare. Ina tsaka da yin girkin ne Bulamana ya kira ni. Da sauri Bawa ya ɗakko mun wayar. Karawa nayi a kunnena bayan na ɗaga. "Hello barka da gidan Yahanasu Maman Hajja, yaya gidan da fatan saƙo ya iso miki ko?' Dariya nayi nace. Yauwa barka da hanya, ina fatan ka sauka lafiya?" "Ah lafiya ƙalau ina tasha ma ina jiran isowar Wakil, kinga yanzu na gama cin burabusko a tasha. Ya kinje asibitin, wata nawa suka ce?" Sai da na kyalkyale da dariya sannan na bashi amsa. Sati takwas suka ce dani. Naji ma har an sa mata suna, to in Namiji ne kuma wa zaka saka?" Cikin dariyar farin ciki yace. "Ba Baana zan saka in dai namiji ne, nima in yi mai takwaran da zan dinga tunashi da shi. To ya kika ga firji? Hmmm firji yayi matuƙar kyau, harfa na kunna dan zumuɗi, kuma gashi yana aiki da kyau. Naji daɗi sosai Bulamana ubangiji Allah ya yauƙaƙa hannayenka duk abinda ka taɓa ya zama mai albarka. Nagode sosai " Da jin yanda yake murmushi na tabbatar adda'ar ta sanyaya zuchiyarshi. "To sai a soma yin su kunun zaƙi da jinja ɗin da akeson a soma siyarwa. Rannan ina jinki kuna hira da matan gida kina cewa da zaki samu hali da kin sai firji dan cin kasuwar lokacin zafi da aka shiga. Shine ƴan kuɗaɗen da nake tarawa sabida komawa makaranta duk na ƙundume na siyo miki" Ji nayi Bulamana ya mayar dani tamkar sarauniya. Hausawa sunyi gaskiya a hikimar zance da suka ce, gaya ma mai zuchiya ba mai dukiya ba. Daga jin hirarmu a tsakar gida shikenan sai ya aiwatar da abunda yaji inason? Madallah da samun miji mummuna, mai kyakkyawar zuchiya, mai sauƙi, da faram faram. Godiya da adda'a na dinga kwararo mishi, har sai da ma ya gaji da amsawa ya kashe wayarshi. BULAMA BABBA: Girgiza kaina nayi, ina mamakin irin godiyar da Yahanasuna ta dinga ragargazo mun, tamkar wacce aka biya ma aikin Hajji. Allah ka hore mun in biya ma Yahanasuna aikin Hajji, in siya mata dalleliyar mota" Ina cikin wannan taɗin zuchin na hango Wakil a cikin motarshi 4.0.7, miƙewa tsaye nayi, na biya yarinya mai abinci kuɗinta, Wakil ya iso inda nake ya karɓi ƴar jakata. Cikin sosa kai yace. "Bulama Babba kayi haƙuri, wallahi kasan ƙarfen nasara bashi da tabbas, motar ce ta samu ɗan matsala, sai da na tsaya a gefen hanya na gyara." Hannuna na ɗaura a kafaɗarshi na ɗan jijjiga irin na wa da ƙaninshi. Ba komai Wakil, ya ka baro su Ba Modu?" Tafiya muka soma yi dan kama hanyar gidansu Aissa. Sai bayan da motar mu ta hau kan titi wakil yace. "Ba Modu suna lafiya dukkansu, kafin ma in fito sai da muka yi magana dashi, yana cewa in kai zuchiyata nesa duk abubda Aissa zata ce in dai ba'a bani damar magana ba karma ince komai. Sun ɗauki abun da zafi har Ba Hamma ya kira Ba Modu wai ranar litinin zasu turo mota ta kwashe kayan Aissa ɗin." Da sauri na kalli Wakil ɗin. Har matsalar ta kai haka ashe, to wai meye yayi zafi haka a tsakaninku, ko dai ya wuce maganar ƙazanta ta yawan gantali ne?" Na tambayi Wakil tare da tsatstsareshi da idandunana. "A'a Bulama Babba, akansu ne kawai. Kuma ni gajiya nayi da ƙazantar tata. Hatta ɗan kanfanta fa sai ta ajjiyeshi a bayan gida kaca kaca da jinin al'ada. Haka data haihu, kusan kullum sai na ga jinin biki, har amai nake yi, amman nayi mata magana taƙi gyarawa. Mu da muka saba da ƙamshi amman Aissa ko wacce kusurwa a jikinta tsami. Data haihu sai abun ya haɗe da ƙarnin nono. Ni gani nake yi ƙawayenta na wajan aiki suke hure mata kunne" Tsahirta maganar mu ka yi, dan mai gadi ya wangale mana get ɗin gidan su Aissa. Ba Hamma yana zaune a kan kureja a cikin baranda, ga shinfiɗu anyi da lallausan kafet a wajan. Cikin girmamawa muka isa gareshi. Rai a murtuke ya amsa mana gausuwarmu, ya nuna mana wajan zama, sai daddanna waya yake yi. Wayar ya kara a kunnenshi yace. " ki tawo da Aissa ga Wakil da Bulama Babba sun iso. A kawo musu ruwa" Iyakar abunda yace kenan ya kashe wayarshi. Jim kaɗan sai ga wan Aissa Bukar da ruwan gora a tire. Hannu ya mimmiƙa mana aka gaisa kadaran kadahan. Bayan mun sha ruwa, sai ga Ya Hewa da Aissa sun ƙaraso. A kan idona ta watsama Wakil wata uwar harara, yayin da yake miƙa mata hannu akan ta bashi Yahanasu ƙarama. A cinyarshi ta dangwarar da yarinyar. A taƙaice aka gaisa, na soma magana. Ba Hamma dama munzo ne game da batun Wakil da Aissa. Domun a sasanta tsakaninsu ta koma ɗakinta." Ba Hamma yace. "Bulama Babba kenan, shi Bakuran ne ya aiko ka ko kai ka kawo kanka?" Kallonshi nayi a mamakince. Ni nazo da kaina a matsayina na babban wa a gidan. Koma me ke tsakaninsu ayi haƙuri dai ta koma ɗakinta, ga zuria sun soma shiga tsakani, gudun kar zumunci ya samu tangarɗa." Gyaran murya yayi irin ta manya. "Zumunci ya riga da ya taɓu. Domun nayi mamakin yanda Bakura a gabanshi Wakil yake horar da Aissa da yunwa, harma da duka in yaso. Amman ace ya kasa ɗaukar mataki akan Wakil. Ko ranar da yarinyarnan tazo mun cikin gidannan ga Bukar gashi, fuskarta a kumbure duk shatin yatsunshi sun kwanta a kan fuskarta. Kuma ta tawo Modu ko Bakura aka rasa wanda zai taso yazo cikin gidannan sai kai. Ai ko baiwace ita a gidannan bazan bari ta koma ba. Litinin za'a kwaso mata kayan ɗakinta aure a tsakankaninsu ya ƙare. Tunda kazo sai ka rubuta mata takaddarta ai." Cike da mamaki na dinga rarraba idanuna a tsakankanin Ba Hamma da Wakil, harma da Aissa ɗin." Duka da yunwa a cikin gidan namu? Amman Ba Hamma aba shi Wakil ɗin dama ya faɗi abinda yasan ya haɗasu, ni nasan Wakil bazai doki Aissa ba, balle yai mata horon yunwa ba. Domun hatta maƙotanmu da suke da buƙata Ba Bakura bai barsu haka ba. Har gobe yana ɗaukar ɗawainiyar karatun marayun yara da marasa galihu da yawa. Aissa ai ƴa take a gidan." Bukar yace. "Aissa ba zata yi mana ƙarya ba muma Bulama Babba, domun babu maƙaryaci a cikin gidannan. Nine babba a cikin gidannan kamar yadda kaima kake babba a naku gidan. Aissa ba zata koma gidanku ba, mu mun haƙura da wannan auren duka da yunwar. Dai dai da famfas bai san ya siyama ƴarshi Yahanasu ba, sai dai ita ta siya da kuɗin aikinta. Ko kuma ni in siya mata wata rana." Iya wuya na kai wuya sosai. Amman duk wuyan da na kai bai kai na Wakil wanda jikinshi har rawa yake yi ba. Idanuwanshi sun cika da hawaye tab. Na rasa ta cewa ni kam kaina ya ɗaure, nayi mamaki da iyaye basu cika bincikeba da zaran yara sun haɗo ƙarya da gaskiya sun ɗaura iyayensu a kai sai su hau. Soyayyar iyaye da yara sun rufe musu idanu, gani suke yaran basu iya ƙarya ba ma. Ni wanne kalan maɗe da munafurcin mace ne ban gani ba?" "Na sake ta saki ɗaya. In ni na cuceta Allah ya saka mata. In ita ta cuce ni Allah ya saka mun. Bulama Babba muje" Furucin Wakil sun yi tsauri amman sunyi dai dai, ƙila a sasanta bayan wani lokaci in zukata su ka ɗauki sanyi" Ba Hamm ya nunfasa yace. "Za kaci gaba da ciyar da Aissa da kula da lafiyarta har zuwa lokacin da zata yaye maka ƴarka. Zan turo a ɗebi kayanta." Jikinshi sai naga yayi sanyi, ita kanta Aissa ta yi laushi. Sai nayi amfani da wannan damar nace. Ba Hamma, a bisa tsari na musulunci Allah yayi magana akan zaman iddar mace a ɗakinta, da fa'idar hakan. Gashi Aissa goyo take yi. Ni ina ganin ku daure ta koma ɗakinta ta zauna har sai in ta yaye ɗiyarta sai ta dawo. In kuma sun dai dai ta kansu falillahil hamdu. Kar mu ƙetare maganar Ubangiji dan baza mu ga da kyau ba. Wasu matan ma basa yin jini a yayin da suke shayarwa har sai sun cire yaro a nono. Wasu ma bayan sun cire yaro a nono su kan jima basu yi jinin ba. Kuma in dai mace ba ta wuci yin jini bane, dole sai ta yi wannan jinin uku shine ta fita idda. In Aissa tana daga cikin irin matan, tofa har sai ta yaye Yahanasu tayi jini uku shine ta kammala iddarta. Ratayayyen hakkine akan Wakil ya kula dasu." Jikin kowa yai sanyi a wajan. Ni kuma banma kuma cewa komai ba, na zuba ido in ga zasu sa ƙafa su shure gaskiya ne ko yaya. "Aissa ki shiga ciki ki haɗo kayanki ki bisu, kije ɗakin ki ki yi idda acan. Umarnin Allah ne." Kuka ta fashe dashi wiwi. Mu kuma mu ka yi sallama dasu akan muna jiranta a mota." Me yasa kayi saurin sakinta baka da hankali ne? Kasan in Ba Modu yaji zai ɗau fishi da kai, ni meye amfanina to?" "Ba haka bane Bulama Babba. Aissa maƙaryaciyace wallahi ko kallon banza ban taɓa yi mata ba. Balle duka, ko barinta da yunwa. Store ɗinta a cike yake da kayan abinci fa." Barta ai ta yaba ma aya zaƙinta. In kana son matarka a zaman iddarta sai kayi ƙoƙarin ku sasanta kanku. In kuma baka sonta shikenan in ta gama iddar sai ta tafi gidansu. Ba Hamma ya bani mamaki matuƙa," Wakil yace. "Iddarta zata gama ta koma gidansu, ni kafin ta gama iddarma zanyi aure. In naci gaba da zama da'ita ƙila zumuncinmu ya rushe da ƴan gidansu ta sanadiyyarmu. Babban abunda Ba Bakura ya tsana kenan, shi yasa ya fi son ayi auren zumunci. Sai dai yana zuwa shima da nashi matsalolin. Ƙila ƙannenmu mata suma suna can suna fuskantar tasu matsalar a wajan mazajen nasu, ko mazajen na fuskata a wajansu." Aissa ce ta ƙwanƙwasa glass ɗin motar. Wakil ya fita ya saka mata kayansu a both. Ta shiga gidan baya sai runtuma kuka take yi. Ya Hewa na bata baki. "Ki dena kuka kamar yau zaki gama iddarki ai ki dawo gida. Ƴan uwanki zasu dinga leƙo miki, in Zaina ta dawo hutu zan turo miki ita. Ki dena kukan hakanan" Da yare take mata magana, sai da ta matsa a jikin motar, naja motar mu ka fice a gidan. Ni nake tuƙin motar dan Wakil yana cikin damuwa mai girman gaske, dan yana son matarshi, auren soyayya su ka yi." Babu wanda yace da ɗan uwanshi wani abun. Na mayar da hankalina kan tuƙin da nake yi, Wakil kuma sai ajjiyar zuchiya yake saukewa kawai. Take Zubaina ta faɗo mun a raina. Nasan yanzu tana can tana jiran jini ya soma zuwar mata, domun ta gama iddarta, wani mai ƙarar kwanan shima ya kwasa. Gata da daɗin baki da yaudara, halayyarta ɗaya da mahaifiyarta. Su Nafisa na tuno dana dinga yi musu dawainiya, da kaisu manya manyan supermarket, in danƙaro musu siyayya, dan kawai in faranta ranta. Take naji inason ganin Yusuf, nasan yanzu yayi wayo sosai. Ɗan guntun murmushi nayi kawai na girgiza kaina. A haka muka isa Damaturu, na shiga gareji na ajjiye motar, muka nufi ɓarayin Ba Bakura, Aissa kuma ta wuce ɓangaren surukan gidan fuu da jakarta a hannunta, da ɗiyarta. A falo muka samu Ba Bakura da Ba Modu suna shan shayi suna hirar kasuwanci. Ganina yasa Ba Bakura ya gimtse fuskarshi, yayin da Ba Modu ya faɗaɗa murmushinshi. "Bulama maraba da zuwa, har kun kammala kun dawo, ince dai an sasanta ko?" Cikin biyayya na gaishesu. Ba Bakura kadaran kadahan ya amsa mun gaisuwata. Anan na labarta musu duk yanda akayi. Salati suka ɗauka dukkansu, har da Hajja data shigo yanzu. Waje ta samu ta zauna tace. "Yanzu yarinyarnan ƙazafin da za tai ma yaronnan kenan, a gidannan ai ko ƙadangarun da suke shigowa cikin ƙoshi suke, ballantana ita, meta nema ta rasa? Kuma shi Hamma haka akeyi babu bincike ba komai, yarinya ta faɗi magana ku hau ku zauna haka akeyi ne?" Ba Bakura nan ya shiga zazzaga ruwan faɗa akan sai da yace dama kar aje ai, amman Ba Modu ya goyi bayan lallai aje ayi sasanci. "To ai shikenan, ni bazan ce komai ba. Kuma Hamma ya kyauta wulaƙancin da yayi mana. Yarinya in ka sasanta da'ita kaji zaka iya sake yin zaman aure da'ita to. In kuma ka haƙura shikenan daka nutsa sai ka tafi can gidan kawunku Bature, akwai ƴaƴa mata guda uku acan sai ka zaɓi wacce tayi maka. Ka aureta ku zauna. Yarinya kuma ta ajjiye maka abunka, iyayenka mata zasu riƙe. In ta tafi da'ita shikenan sai abar mata can ma gidane, sai kayi ƙoƙarin sauke nauyinta a kanka, ka kula da rayuwarta. Hukuncin daka yanke a wajan na sakin yayi dai_dai, dan sai an tauna tsakuwa aya ke jin tsoro. Dan Dala ya kawo mun ƙorafin matarshi kan irin zaman da suke yi. In tana son mijinta ta shiga taitayinta dan gudun kar abinda ya faru da Aissa ya faru a kanta. Ina mai horarku da kuji tsoron Allah ku riƙe matayenku babu cuta babu cutarwa. Ku duba kuga irin zaman mutumci da muke yi da iyayenku, kuma ku kwatanta akan matayenku. Ku ji ƙansu ƴan uwanku ne, ku tausaya musu. Kuma ko bayan babu ku, sai Allah ya haɗa yaranku da masu jin ƙansu. Ko bayan ƙasa ta rufe idanuwanmu ku daure ku riƙe gidannan, kuma a dinga auren zumunci domun haɓaka zumunci. Dan mutanen wannan zamanin sun yi ma zumunci riƙon sakainar kashi. Hamma da Hewa sun matuƙar bani mamaki, amman babu komai." Tarin shi na tsufa ya soma yi, Ba Modu yana yi mai sannu. Gabaki ɗaya jikinmu duk ya mace, dan duk ranar da Ba Bakura ya yi batun mutuwa, duk sai mu shiga tashin hankali. Hajja tace. "Modu kwana biyunnan ɗan uwanka baya samun bacci ishasshe, numfashinshi sai inji yana fita sama_ sama. Tunda Bulama Babba yazo, ya kamata a kaishi asibiti a duba lafiyarshi. Ni kaina duk na bi na shiga damuwa, da irin halin da yake ciki. Ba Modu yace. "Bakura akwai inda yake yi maka ciwo a jikinka ne" murmushi yayi kawai yace. "Sai ciwon tsufa wanda ko wanne tsoho ke fama dashi, shi kuma mutuwace kawai maganinshi. Baya ga wannan babu abunda ke damuna. Sai rashin baccin dai da ban samu ba, shekaran jiya zuwa jiya, shine kawai. Amman ina haɗiyar ƙwayar bature kullum, ko rabi ma ban sha ba. Yaushe_yaushe muka je ka kaini asibitin.?" Dubana yayi yace. "Kai ya Yahanasu da yaran suke?" Kai na sosa ina ɗan murmushi nace. Suna lafiya, amman ita bata ji daɗi ba, taje asibiti amman yau. Ina hanya ma ta kira ni. Wai ciki ne da ita" Kaina na sauke ƙasa. Gabaki ɗaya falon suka yi kabbara, zukata su ka ɗau sanyi. Ba'a daɗe ba kab gidan ya ɗauka Yahanasu na da juna biyu. Ni dai ina faɗa na gudu masauki. Bayan sallar Magriba, Dala ya raka ni muka zagayo ƴan uwa, aka gaggaisa, bani na shigo gidan ba sai wajajen sha ɗayan dare. Washe gari da sassafe na shiga haramar tafiya. Wani ƙunshin baƙar leda Hajja ta bayar tace a ba ma Yahanasu. Haka ma Ya Innana ta bani ƙatuwar keda itama tace a kaima Yahanasun. Ni kuma na ba Ba Bakura dubu ɗaya, ba Modu dubu ɗaya. Iyayenmu mata na bisu da ɗari biyar biyar. Matan ƙannena na bi ko wanne ɗaki da ɗari bibbiyu nace a sayi omo ai ma yarana wanki. Ba'akaka da Wakil ne suka raka ni tasha, har sai da motarmu ta tashi sannan suka tafi suma. YAHANASU: A daren jiya, bacci kasa ɗaukata yayi fur, sakamakon bansha komai ba, idanuna na jisu a soye, sai zafi da ƙaiƙayi da suka dame ni dashi. Haka naita faman juye_ juye, yanda naga rana haka darenma ya kasance mun. Da asuba kuwa na tashi da matsanancin ciwon kai, ko idanuna bana iya ɗagowa. A daddafe nayi aikace aikacen yau da kullum wanda suka zame ma ko wacce mace jiki. Muna gama karyawa, na zura ma Maryam kayan makarantarta, Bawa ya saka nashi, ya ɗaukar musu lunch box ɗinsu. Nima na ɗauko jakata na rufe ɗakina, naima matan gida sallama muka fita. Sai da na biya ta makaranta na ajjiye yara, ni kuma na wuce wajan aikina. Haka dai aikin ya kasance mun babu daɗi. Har na baro office muka nufi ɗorayi gidan wata uwar marayu domun tattaunawa da'ita. A daddafe dai muka gama program ɗin, ya ɗauke mu awa guda. Office muka sake komawa. Sai ƙarfe biyu muka tashi. "Yau na ganki sukuku, idanunki sunyi jawur, akwai wata matsala ne Yahanasu?" Kai na girgiza nace. Ba komai kaina ne kamar zai tarwatse dan ciwo. Gabaki ɗaya komai kika ga inayi ƙarfin hali ne kawai." "Kina da laka mis ɗin shine har ciwon kai ya addabeki kuma? Yau tunda kika zo aiki banga kin kora komai ba" Shareta nayi bance da'ita komai ba. Ɗan sahu ɗaya muka hau da'ita dan itama zata je kasuwa cefane. Ni kuma zan siyo kayan meat pie da kunun zaƙi. A kasuwar muka rabu bayan mun gama siyayyar da zamu yi. Ina shiga gida na shiga aikin kunun zaƙi bayan na haɗa niƙa na miƙa cikin gida, sai na leƙa gidansu Uwatale ƙawata, tana siyar da goruna. A tsakar gida na sameta tana ƙirga ma wata mata goruna. "Umman Maryam yau kece a gidan namu? Lallai za'ayi ruwa da ƙanƙara yau" Dariya nayi ma Uwatale inayi ina dafe kaina da nake ji kamar zai faɗi ƙasa. Uwatale ta soni sosai da ƙawance, takan shigo wajena da yamma haka. Amman ni sau ɗaya na taɓa zuwa gidanta, data haifi yarinyarta, shima tare da matan gidanmu muka shigo, sai kuma yau dana shigo. Tun tana ƙorafin harta dena. Kai Uwatale, wato za'ayi ruwa da ƙanƙara ma ko? " Itama dariya tayi mun tace. "Sau ɗaya kika zo gidannan, shima tare da su Maman Hassan. Ni har Abban su Fatima na sanarma, nace mishi na lura kamar cusa kaina nake yi gareki, ke bakya so. Shi yasa kika ga kwana biyu na ja baya dake" Baki na buɗe nace. Wallahi ba yanda kike tunani bane Uwatale, abubbuwanne sai adda'a kawai. Ga hidimar iyali, ga zuwa aiki. Yanzun ma niƙa kunun zaƙi na miƙa cikin gida shine fa nace bari in zo wajan ƙawata in sai goruna" Hararata tayi tace. "Ba wani aiki ke dai baki yi niyyar yin zumuncin dani bane" Hararar nima na mayar mata nace. Naji ƙorafinki, zan gyara in sha Allah. Yanzu dai ki bani robobi dozin biyu, dozin ɗaya manya, dozin ɗaya ƙananu." Sai da ta sallami matar da take ƙirga ma gorunan, sannan ta ƙirga mun nawa gorunan ina daga zaune. Sai da muka taɓa hira kafin nace. Zan tafi gida sai na sake shigowa" Tace dani. "Ai kuwa nagode sosai, duk da ba takanas danni akazo ba, amman nagode. Kuma zan sa Khalifa ya shishshiga maƙota ya sanar musu kina kunun zaƙi Muma kullum in Abbansu ya dawo yana aikawa can shagon ɗan fulani a siyo mana. Kinga ma dinga siye a wajanki, matan gidannan namu ma, da zaran yamma tayi zaki ga suna aikawa a siyo musu abun sanyi. MRS BUKHARI [07/08, 9:43 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B) 28 Sai da Uwatale ta raka ni har zaure, mu kai sallama na koma gida. A lokacin ne naji kaina kamar zai tsage mun, wani irin amai na taso mun. A guje na ƙarasa kwatar data raba tsakar gidan, na dinga amai, ina jin kaina da tsigar jikina suna bubbuɗewa. Matan gidanmu suka taru a kaina. Daga masu cewa ta tabbata ciki ne dani. Sai masu yi mun sannu. Da ƙyar na tashi na shige ɗaki, bayan na tace ƙullin kunun zaƙi na. Laka mis na buɗe na shanye gora guda na yar da gorar a tsakar ɗakin, a wajan na sulale ina kuka. Ke nan haka rayuwata za tai ta tafiya, duk ranar da ban sha wani abun ba, babu zaman lafiya?" Na kai kamar minti talatin a zaune a wajan, a hankali na dinga jin kaina yana daidaituwa. Jin hakanne yasa na fita a ɗakin na ɗauro alwala nazo nayi sallar la'asar. Sannan na koma tsakar gida bakin aikina. Ina haɗa kunun zaƙi, ina girki. Ina gama haɗa kunun zaƙin na kai firji dan yayi sanyi sosai, na dawo naci gaba da aikina. Shida da hamsin na fito wanka a gurguje, dan Bulamana ya kira ni, sun shigo gari, yana hanyar dawowa gida. Sai da aka kirayi sallar isha ya shigo niƙi _niƙi da kaya. Da sauri na tarbeshi, yara suka isa gareshi a guje, ya rungume Maryam tsam a jikinshi, yana shafa kan Bawa da ɗayan hannun nashi. Ni kuma sai Murmushi nake yi ina musu kallon sha'awa. "Bulama ka shigo ne?" Muka jiyo Muryar Ahmad a ƙofar ɗakinmu. "E yanzu na shigo, kaya na shigo ajjiyewa, naji ana kiran Sallah." Dubana yayi yace. "Bari in je masallaci, kafin in dawo ki zuba mun ruwan a bokiti zanyi wanka" Yana faɗar haka ya sauke Maryam ya fice shi da Bawa. Taburma babba na baza mana a tsakar gida gefen ɗakinmu, dan ɗakin in ba wutar nefa bane akwai, baya iya shiguwa a zauna a ciki. Gashi tunda aka shiga wannan zafin suka soma hanamu wuta. Kayan abinci na ajjiye, ina shirin zama kamar wasa aka soma shigowa siyan kunun zaƙi, kowa na son jiƙa maƙoshinshi da abun sanyi, dama Hajara ta aika yara sun shisshiga maƙota sun sanar. Haka masu sayen pure water ma sai shigowa suke suna siya a wajan maƙociysta Wani yarone yazo siyan kunun zaƙi na shiga ɗakko mishi kenan Bulamana suka dawo daga masallaci, ganin kayan abinci akan tabarma yasa ya zauna. Ina fitowa naga ashe sun dawo. Yaron na miƙa ma kunun zaƙin da canjin shi. "Kice har an soma cabkar kuɗi?" Dariya nayi mishi, na nemi waje na zauna nace. Har nayi ɗari uku da hamsin, ga kunun zaƙin har wasu sun soma yin ƙanƙara, firjin yana da ƙarfi sosai, ni har mamakin ƙarfinshi nake yi, a haka kuma yaji jiki sosai. Muna cin abinci, yana labarta mun yanda akayi da Ba Hamma. Nayi mamaki matuƙar mamaki. Bulamana yace. "Ai wannan mamakin kowa ne yayi shi, ba mu kaɗai ba. Amman ita Aissan ta gaji da Wakil ɗinne, gara data nuna mishi halinta tun wuri, yarinya ɗaya ce a tsakaninsu. Da yayi wannan maganar sai na tari numfashin shi da cewa. Yauwa dama ina son in tambayeka, yaushe zaka je ka dubo Yusuf ne? Ya kamata ka je kaga lafiyarshi, tunda su basu zo sunga lafiyar su Bawa ba, kuma ko a waya ba wanda ya taɓa kira da zummar yanason yaji muryarsu. Ƙanwar mahaifiyar tasu da take nan Kano itama bata taɓa zuwa ba" Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya ɗaga kofin dana zuba mishi kunun zaƙi ya kafa a bakinshi, bai cire ba har sai da ya shanye tukun. "To nima jiya nayi tunanin zuwa ganin Yusuf, kawai sai naji ya faɗo mun inason in sa shi a ƙwayar idanuna. Mu bari zuwa ƙarshen wata in anyi biya sai in je in dubo shi. To ya Baby na yana lafiya ko?" Dariya nayi mishi, na shafa cikina tare da numshe idanuna, ina jin son cikin sosai a zuchiyata, ashe dama haka iyaye suke ji a lokacin da suke ɗauke da ciki?" "Kin shiga tunani, kinƙi amsa ni ko?" Kafin in yi magana, Hassan ɗin Maman Hassan yazo siyan kunun zaƙi na nera ɗari. Bulamane ne ya shiga ya ɗakko mishi. Ahmad ya tuntsure mishi da dariya, dake suma suna zaune a ƙofar ɗakinsu. "Ka zama me sayar da kunun zaƙi kenan kaima, gaskiya wannan ƙanwar tawa ta shanyeka da yawa Bulama" Dariya yayi mishi yace. "In ban kula da'ita ba, dawa zan kula, ka mance laulayi take yi ne?" Dariya Ahmad yayi yace "Ban isa in mance ba, kuɗin rago na wuyana ai. Kuma ina yi ma Walid kamu in macece ce" Haka dai sukai ta zolayar junansu. Kafin daga bisani Bulamana ya fuskanceni yace. "Ga kaya Hajja, da Ya Innana suka ce in kawo miki, ni bansan ma kayan meye ba. Babbar ledar shine na Ya Innana" Allah ya saka musu da alkhairi, ai kasa duk sun kirani, sai murna suke yi, ni kuma Kamar in nitse dan kunya wallahi, ai da baka faɗa musu ba." Murmushi yayi mun kawai, ya kakkafeni da idanunshi. Haka mu kai ta hirarmu gwanin sha'awa, kafin mu tashi a wajan kunun zaƙi ya ƙare har ana zuwa nema, kasancewar da sanyi sosai, kuma nayi shi da kauri dan ban bi riba mai yawa ba, albarka nake nema. Haka dai rayuwar tai ta turawa ahankali. Wata ranar juma'a na dawo gida a gajiye, gashi nasha wata ƙwaya da ban taɓa sha ba, kaina sai juyawa yake yi da ni, da ƙyar na iya kawo kaina gida. Ina shiga ɗaki jini ya ɓalle mun, take marata ta shiga jujjuyawa tana murɗewa. Tsugunnawa nayi ina nishi da ƙyar, hankalina ba ƙaramin mugun tashi yayi ba, take na shiga kuka wiwi domun na fahimci ɓari nayi. Da ƙyar na iya tashi na gyara jikina, maganin mayen da nasha yana kuma ɗibata. Kintsa jikina nayi na koma kan katifa na kwanta hannuna dafe da marata, hawaye sai bin kuncina yake yi. Wasa wasa ciwo yaci gaba da tsananta. Dole na kira Hajara da ƙyar nake magana. Hajara ki taimaka ki kira mun Rabi nose da naga matan gidannan na kiranta. Marata zata fashe ki taimakeni". Ina kaiwa nan na fashe da sabon kuka. "Sannu Yahanasu, subuhanallahi, Allah yasa dai ba ɓari kika yi ba. Bari in kira Maman Iklima ta zauna dake kafin in dawo" Da sauri ta fita. Bata jima da fita ba Maman Iklima ta shigo. A lokacin na kusan fita daga hayyacina bibbiyu uku_ uku nake ganinta. Daga hakan ban sake ma sani inda kaina yake ba. Farfaɗowa nayi cike da matsanancin ciwo, da zubar jini sosai. Rabi nose ta dubu Hajara tace. "Cikin jikinta ne ya zube, ga jini na zuba a jikinta ni ina ganin kuje asibiti mafi kusa zaifi. Ko Asibitin Dr Bala ku kaita." Basu yi wata wata ba, suka taimaka mun na miƙe suna riƙe dani, jini duk ya ɓata katifar da nake kwance a kai, ya ɓata mun jikina. Hijabi na zura a jikina na tuɓe kayan daya ɓacin na sake wasu, tare da yin ƙunzugu. Jikina sai wani ɓari yake yi,sanyi na ratsani. Haka suka riƙe ni muka je ɗan kemis ɗin Dr Bala inda anan matarshi take duba marasa lafiya, harma ta basu gado in ta kama, amman ba'a kwana a wajan. Sun buɗe wajanne domun taimakon marasa ƙarfi. In sun dawo asibiti sai su buɗe kemis ɗin dan duba marasa lafiya da siyar da magani. Kwanakin baya ma a nan Uwatale ta haihu. Muna isa Dr Hauwa tana ganinmu ta riƙe ni. "Lafiya me ya same ta take zubar da jini haka?" Hajara a tsorace tace. "Rabi nose ce ta turo mu nan, tace ɓari tayi jini ya ɓalle mata." Dubana ta yi da kyau. Bata ce komai ba ta shigar dani ɗan ɗakin da a ciki suke kwantar da marasa lafiya. Gadaje biyu ne jol a ciki. Taimakon gaggawa tayi mun, tamun wasu allurai, tare da bani wasu magunguna nasha. Take jinin da nake zubarwa ya dai dai ta sai dai cikin har zuwa lokacin yana murɗa mun. "Nace akwai wata ƙwayar bature da kika sha wanda ba likita bane ya rubuta miki, misali maganin ciwon kai, maganin mura, da sauransu? Domun irin wannan jinin da kike zubarwa yayi yawa. Ko dai maganin zubar da ciki ma kika sha ne, ko ƙwayar maye. Ina mijinki inason yin magana dashi gaskiya" Hankalina in yayi dubu ya tashi, a tsorace na dubeta, itama ni ta zubama idanu tana karantar yanayina. Likita babu abunda nasha wallahi. Ki rufa mun asiri dan Allah, wallahi ban sha wani abu dan cikina ya zube ba, inason abuna ƙaddarace wacce ta riga fata" Wani kallon banza tayi mun, ba tare da tace komai ba ta fita a ɗakin. Kuka na fashe dashi, hankalina a tashe yake ainun. A cikin wannan halin barci yaci ƙarfina. Bani na farka ba sai wajajen goman dare. Bulamana yana zaune a bakin gadon da nake, ya zabga tagumi ni kawai yake kallo. Ina buɗe ido dashi na soma tozali. Hawaye ya soma bin gefen fuskata. Hannayena dukka biyun Bulamana ya riƙo cikin ƙasa da murya yace. "Haba Yahanasu menene ma abun kuka dan kinyi ɓari, ina kuma ga masu renon cikin tsawon wata tara su yi naƙuda, amman ɗan yazo babu rai fa, su me zasu ce? Addu'a ya kamata mu yi akan Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu. Allah ya bamu wanda ya fi wannan" Ƙarfin guiwa naji sosai, kuma na tabbatar likita bata faɗa mai wani abun ba. Ajjiyar zuchiya na sauke a hankali nace. Su Ya Innana sun sani?" Kai ya gyaɗa mun yace. "Sun sani, tun ɗazu Ba Bakura yake kira yaji ko kin farka ma. Bari in yima Likita magana, dan tace kina farkawa zamu koma gida, ina zuwa ko?" Fita yayi da hanzari, na bi bayanshi da kallo, ina fargabar kada likita ta faɗa mishi wani abun da zata jefa zuchiyarshi a doron zargina. Amman abun mamaki har muka baro kemis ɗinnan wannan likitan bata faɗi wata kalma guda ga Bulamana ba, dangane da tambayoyin data mun farkon zuwan mu. Ahankali nake tafe Bulamana yana riƙe da hannayena. Matan gidanmu duk a tsakar gida muka tarar dasu, yayin da wasu ke hira, wasu kuma bacci ya kwashe su. Muma a tsakar gidan muka ya da zangon mu. Sai gaisheni da jiki suke yi, tare da yi mini adda'ar samun wani rabon da gaggawa. Su Ya Innana ne suka yi kiran waya, haka na dinga amsa ya jikin iyayena da ƴan uwana. Sai hawaye kawai nake sharewa dan fitar cikin ya mun ciwo, sakamakon shaye _shayen muyagun ƙwayoyi ya salwantar mun da farin ciki na. Nayi matuƙar nadamar shaye _ shaye a rayuwata. Kuma nayi ma kaina alƙawarin da zaran na samu ciki zan jingine komai a gefe ko da hakan na nufin tonon asirinane, inason nima inga jinina. Babban abinda ya fi komai tada mun hankali shine labarin da Hajara ta bani bayan ta kawo mun abinci da ruwan Tea, tayi mun ya jikin. "Ki ci abinci gashi nan Yahanasu, ruwan wankan ki yana bayan gida in kika gama cin abincin sai ki watsa da zafin shi." Murya a dakushe nace. Nagode sosai Hajara, sannunku da ɗawainiya, ina yaran fa?" Ɗan Murmushi tayi tace. "Haba ai mun zama ƴan uwan juna Yahanasu, yara gasu can a tabarma sunyi baccinsu. Sai kika ji labarin an sallami su Abban Anisa daga wajan aiki ko? Hummm abun yayi mun ciwo. Kinsan ɗaukarsu akayi ba tare da sun shiga shashin horaswaba, to an sake musu shugaba, shine fa akayi bincike aka sallami mutane sama da ashirin, suma abun ya faɗo ta kansu." Da sauri na dubi Bulamana wanda shima idanu ya zuba mun. Hawaye tuni suka wanke mun fuskata, cikin rawar murya nace. Da gaske ne abinda Hajara ta faɗa an sallameku a aiki?" Kai ya gyaɗa mun baice komai ba. Ahmad ya ƙaraso inda muke yace. "Sai da na kwaɓe wannan bakin naki mai shegen surutu akan kar ki faɗa ma Yahanasu halin da ake ciki, ki barta ta ji da jikinta. Amman taurin kai yasa sai da kika sake sanya zuchiyarta a damuwa ko? Dame kike son taji to?" Kuka nake yi mai ɗan sauti kaɗan, Bulamana ya kasa rarrashina ya kasa magana. Hajara kuma Ahmad ya tusata a gaba suka koma ƙofar ɗakinsu, sai balbaleta yake da ruwan faɗa. "Ki share hawayenki, Allah yasan da mu, shi zai kawo mana ɗauki. Daure ki sha ko da tean ne sai ki yi wanka zaki fi jin daɗin cin abincin naki. A wannan daren da ƙyar bacci ya ɗebe ni a bisa tursasawa da rarrashin Bulamana. Shi kuwa a kan dadduma ya kusan kwana, sai jefin assalatu bacci ya ɗebeshi a tsakar ɗakinmu, dan wajajen sha biyun dare da garin ya ɗan yi dama dama sai muka shiga ciki. Washe gari haka muka wayi gari cikin rashin walwala da kuzari. Bayan mun gama karyawa nasha magunguna, da misalin ƙarfe bakwai da rabi Bulamana ya kama hannun yaran yace. "Zan kaisu makaranta, daga nan zamu fantsama gari neman aiki, ko na ƙarfi ko na abinda muka karanta. Kinsan yadda ƙasar ta dawo, aiki yayi wuya kafin a ba mutum ofa sai fa ya sauke kuɗaɗe masu yawan gaske. Digree ta zama abun banza a ƙasarnan. Amman Allah zai rufa mana asiri, zan dage ko ni ɗinne in jona mastas, in yaso inna gama kya jona naki. In sha Allah zamu samu sauƙi. Akwai abinda kike buƙata in siyo miki in zan dawo ne? Naso in zauna in yi jinyarki ma, amman zama ba aiki bai taso ba. Sannan ka da ki sake ki sanar ma kowa rashin aikina, kar mu ɗaga musu nasu hankalin, Allah zai mana mafita." A raunace na kalleshi, gurbin idanuna tab da ruwan hawaye nace. Ubangiji Allah ya baku abunda kuka fita nema, Allah ya bada nasara. Babu abunda nake buƙata face kayan kunun zaƙi da meat pie ɗina babu, kuma ya kamata ayi, sabida kasuwanci bai gaji yau akwai gobe babu ba. Zan kira ma'aikatarmu in sanar dasu halin da nake ciki, ko sati guda ne su bani in zauna a gida in yi jinya. Sallama yayi mun suka fice da yaran, bayan ya karɓi kuɗin kayan haɗin kunun zaƙi da meat pie. Cikin sati guda yawon neman aiki su Bulamana suka share suna yi. Amman ba wani labari, hatta koyarwa a makaranta, sun nema a makarantu da dama, amman aikin bai samu ba. Masu digiri da damansu da koyarwar suka ta'allaƙa, samun koyarwar a wannan lokacin shima sai sa'a. A cikin sati na biyu ne suka yanke hukuncin karɓar hayan ɗan sahu, zasu dinga kabu_kabu. Shima da ƙyar suka samu wani bawan Allah mai bama samari lon ɗin ɗan sahu, ya siya musu ta hannu ko wanne ɗaɗɗaya, zasu dinga kai balans ɗin dubu biyu da ɗari biyar kullum har su gama biyan kuɗin ɗan sahun, sai ya zama nasu. Ni kuma shaguna biyu yanzu nake kaima kunun zaƙi da meat pie, banda wanda nake tafiya dashi wajan aiki, ga kuma masu shigowa saye a gida. Har kunun aya da ƙanƙarar madarar kuka nake yi yanzu. Al'amuran sai dai godiyar Ubangiji, ni nake biyan kuɗin haya duk wata, hatta kuɗin makarantar yaran kusan ni nake biya, ga gini a hakan ina taɓawa duk wata ina warar wasu kuɗaɗe in zuba a ginin, adashe nake yi hannaye birjik. Ana cikin wannan rayuwar Bulamana ya samu gurbin karatun mastas a jami'ar bayaro dake Kano, ni kuma na samu ƙaramin ciki. Al'amuran suka sake ɗaure mana sai hamdala kawai, iyaye da ƴan uwa babu wanda yasan halin da muke ciki. Cikina na da wata uku na sake yin ɓari, a sakamakon shaye _shayen muyagun ƙwayoyin da na kasa dena shansu. Ban fi wata ɗaya da yin ɓari ba na samu wani cikin. Watan shi biyu shima yabi rariya. Nayi kuka kamar raina zai fice, nayi nadamar soma shaye _ shaye a rayuwata. Haka lamuran rayuwa su kai ta gudana. Munje gida mun yi zumunci, mun zagaya dangi, har gidan Hajja Fati Bulamana ya kaini. A cikin halin matsanancin ciwo na je na iske Hajja Fati. Ta lalace ta komaɗe in banda sambatu babu abunda take yi. Bata ma iya gane ni ba, shaye _ shayen miyagun kwayoyi ya jirkita mata ƙwaƙwalwa. Ranar na kuma jin tsoron Allah, gami da buwayarshi. Kwana nayi ina kuka tun Bulamana yana rarrashina, har abun yaci tura, ya juya bayanshi yayi watsi dani. Nafi sati guda a cikin tunanin hanyar da zan bi dan ganin na dena shaye shaye, amman duk yanda nayi tunani abun yafi ƙarfina, da naji ina shirin zaucewa dole na sake komawa ruwa tsundum. BAYAN SHEKARA GUDA Abubuwa da dama sun faru. A ciki akwai samun ƙaruwa da akayi a can Damaturu. Kusan kab surukan gidan sun sake haihuwa, Aissa kuma ta gama iddarta. Ba Modu yayi ciwon da har an cire rai da ci gaban rayuwarshi, amman daga bisani ya samu lafiya. Ciwon siga ne yai mishi mummunan kamu mai zafi. An ɗaurashi akan magani, sannan su Ya Innana suna ƙoƙarin su wajan bashi abincin masu irin lalurarsu. Dangin wake, jar dawa, alkama, acca, tamba, basmati rice, marvel madarar masu ciwon siga, Tropicana silm (suger shan tea ta masu ciwon suger) da duk wani abinda masu ciwon siga suke ci. Duk wata ana mayar dashi asibiti dan a duba yanayin hawa da saukan sigar. Ta ɓangaren mu kuma rayuwar sai sake tsauri take mana, duk ƴan kuɗaɗen aikina dana sana'a ƙarewa suke yi tas a hidimar gidan. Bulamana kuma yanata aiki da ɗan sahunshi, ɗan kuɗaɗen da yake samu, dasu yake ɗaukar jigilar karatunshi. Kullum a cikin bani haƙuri yake. Ni kuma kullum a cikin ƙarfafa guiwarshi nake, domun babu abinda yake dauwamamme face ƙudurar Ubangiji, bayan wuya sai daɗi. Muna cikin wannan halin kwatsam wata ranar lahadi da misalin ƙarfe takwas na dare. Ina zaune a tabarma ni da yara a tsakar gida, Bulamana ya tafi aikin kabu _kabu, bai dawo ba, sai goma da rabi yake shigowa gida. Wayarshi daya bari a gida ake kira. Ina jawowa naga sunan Zubaina ɓaro _ɓaro ya bayyana akan kwalbar wayar. Sai da gabana ya faɗi, dakewa nayi na ɗaga wayar. Assalamu alaikum wake magana?" Jim muryata yasa tayi jim kafin daga bisani ta saki tsaki. "Kwatancen inda kuke zaki yi mun, inason in zo ganin yarana tsohuwar munafuka algunguma" Cije leɓena nayi nace. Za'a turo miki adireshin a rubuce" Ban jira naji me zata ce ba, na datse wayar. Adireshin gidan na tura mata. Naci gaba da shige da ficen ɗakko kunun zaƙi ma masu saye. Kamar minti goma sha biyar da kiran waya da Zubaina tayi. Sai ga Bulamana ya shigo gidan, ya nemi waje ya zauna a taburma. Tagumi ya zuba. Na dubeshi jiki a sanyaye nace. Lafiya meke faruwa Bulamana, wani abunne ya faru na ganka haka, gashi yau ka dawo da wuri?" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Ai kasuwar sai godiya, tun fitar da nayi nera ɗari biyar kacal nayi. Gashi jiya ban bashi balans ba, yau kuma ga yanda abun ya kasance. Gashi zazzaɓine ma yake damuna sosai Yahanasu" Bance mishi komai ba, na shige ɗaki, na buɗe bankina na ƙirgo dubu biyar na fito. Bayan na zauna ne na miƙa mishi kuɗin. Ƙin karɓa yayi ya bini da jajayen idanunshi. "Wannan kuɗin na meye kuma Yahanasu? Ina bazan ma karɓa ba. Komai na nauyin gidannan kan ki ya dawo fa, ke kike yin komai. Balans kuwa na biya da kaina, sai kace mara tausayi" Murmushi nayi nace. To in banyi maka ba wa zan yi ma to? Kai dai ka karɓa kawai ka je ka kai mishi. Wata rana sai labari, kar ka mance karatu kake yi, in sha Allah da zaran ka kammala zaka samu aikin yi. Muna fatan kafin ma ka kammala ɗin. Ai ko a gidan wani nake aure, zanyi ma duk wannan abubbuwan, ballantana kai nake aure, dan Allah karɓi ka kai mishi" Karɓa kuɗin yayi, ya dinga shi mun albarka. "Kai in nayi kuɗi sai kin soma hawa mota kafin in hau, ke zan soma siya ma. Banda suturu da zan ta jibgo miki, duk shekara kuwa a Saudiyya zaki yi Azumi. Dariya mu ka yi dukkanmu, har muna tafawa duniya tayi mana daɗi. Ban da dai cika baki, azo kana yin kuɗi ka danƙaromun Amarya, ƙila ma ta riga ni tarewa a cikin sabon gidan da zaka gina mana" Dukan wasa ya kawo mun. Nayi wuf na kauce. Kiran wayarshi ce ta katse mana nishaɗin da muke ciki "Zubaina ce yau take kira na? In ma batun kuɗine bani dashi gaskiya nima" Sai da ya gama surutanshi kana ya kara wayar a kunnenshi. "Ina bakin layin naku, ko za'a iya zuwa ai mun jagowa zuwa gidan, in fa da hali kenan?" Da mamaki ya zare wayar a kunnenshi dan ya tabbatar shin ko gizo idanunshi ke mishi, amman daya duba sai yaga itance, kafin ma yayi magana ta katse wayar. Da yake wayar tashi na da ƙara sosai, raɗau abinda Zubaina ta faɗa a kunnena. Ɗazu ta kira, ni na bata adireshin gidanma. Ka je ɗin ka shigo da'itan" Ran shi a dagule ya fice a gidan. Ni kuma wani irin kishin mijina ne naji yana nuƙurƙusar raina, ji nake tamkar in bishi in ce inason raka shi, dan gani nake kamar biko Zubaina tazo , ba wani ganin yara. Shekara ɗaya da wata biyu da rabuwarsu, sai yau ne ta tuno da akwai yara a tsakaninsu da zata tawo ganinsu. BULAMA BABBA: Ina tafe ina mamakin zuwan Zubaina wai ganin yara. Shekara ɗaya da wata biyu ta kwashe ba tare da tazo duba yaran ba, sai yau ne zata zo. "Malam Bulama Bakura Bukar bismillah shiga gidan baya mu ƙarasa gidan ko?" Zubaina ce a kame a gaban wata jibgegiyar baƙar mota. Tayi wani irin kyau da mugun haske, fuskarta sai sheƙi take yi. Tsanarta naji ta kuma yi mun dirar mikiya a zuchiyata. Kallon shirgegen mutumin dake tuƙa motar nayi, shima ni ɗin ya zuba ma idanu, yana wani irin murmushin da shi kaɗai ya barma kanshi sanin dalilin yin shi. Kar ki damu, ku bini a baya kawai gidan ba nisa." Ina faɗar haka na shige gaba ina tafe ba guiwa. Ni kaina bansan dalilin daya sarar mun da guiwata ba. Gabana sai faɗuwa yake yi. A ƙofar gidanmu na tsaya, ina jiran su gyara tsaiwar motarsu. Tafi minti biyar kafin ta fito daga cikin motar nan. Idanu na zuba mata ƙur. Mrs Bukhari ce [08/08, 7:26 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 29 Ƙamshinta ya daki salansar hancina. Sanye take cikin shigar atampa ɗinkin doguwar riga, ya kamata tsam, duk wani diri da cikar halittarta ya bayyana. Ga wasu takalma masu tsinin gaske a ƙafafunta. Tasha kwalliya tamkar wacce ta fito dan zuwa wajan zaɓen sarauniyar kwalliya. Sai wani annuri fuskarta ke fesarwa, ta yi mul_ mul abunta. Yusuf ta fito dashi daga mota, shima yaci uban ado yayi kyau ainun. Kamarshi sak da Zubaina har ma ya zarce ta fari da yake yarone. Tana takowa inda nake, na tsugunna na ɗauki Yusuf a jikina, na lumshe idanuna na buɗe su a kan Zubaina dake tsaye a gabana tana dariya. "Malam Bulama Bakura Bukar, a wannan ƙazamar anguwa da ƙazamin gida kuke rayuwa haka? Wow kace talauci yaci uban na da, ko da yake ba abunda ya kawo ni ba kenan." Murmushin cusa haushi na mata nace. Mu je ki aiwatar da abunda ya kawo ki Zubaina, kin bar bawan Allah shi kaɗai. Wucewa ta nayi ciki, tana biye dani har ƙofar ɗakinmu. Yahanasu na kalla muka haɗa idanu, murmushi ta sakar mun, nima na mayar mata da murmushin. Ga baƙuwar mu, ki bata wajan zama, ga kuma ɗanki Yusuf. Na tsugunna na ajjiye mata shi a jikinta. Yahanasu ta nuna ma Zubaina kujerar tsugunno tace "Bismillah Kofur ga waje, maraba da hanya, bari a kawo abun sha." Da sauri Yahanasu ta miƙe ta shiga ciki. Sheƙeƙe Zubaina tabi bayanta da kallo. Yaranta ta zuba ma idanu suna kwance a tabarma, duk sun rame sun yi duhu, sun dawo yaran malo. Kai ta jijjiga kawai. Ahmad da Hajara ne suka fito tsakar gidan. Zubaina ta buɗe bakinta data gansu. Hajara ta iso wajan da saurinta tana yashe baki. "Kaga manya_manya maganin ƙanana ƙanana. La'ilaha_illallahu Zubaina kece kika zama babbar mace haka, kinga yanda kike haske kamar wata ɗan daren sha biyu? Tubarakalla kai farar mace alkyabbar mata, Kai ya sa, ji Yusuf yanda yaro ya zama ɗan turawa wallahi ba kya ce Bulama Babba bane gyatumun shi ba" A yatsine Zubaina ta dubi Hajara tace. "Hajara kina nan a yanda na sanki. Ya yaran kema a cikin jagwalgwalon gidannan kuke, aminci daɗi?" Ahmad ne ya ja ni gefe can. "Me ya kawo wannan maras tarbiyyar gidannan kuma Bulama?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Tace dai ganin yaran tazo. Ita da wani ne ya kawota." Kai Ahmad ya jijjiga. Muna jiyo Hajara sai ɓarin zance take yi, har abinda ba'a tambayeta ba sai da ta faɗa ma Zubaina. Hatta rasa aiki da mu ka yi, sai da ta fesa mata. A fusace Ahmad yayo kan Hajara rai a dagule, ba shiri ta gudu ɗaki tana tambayarshi ita me tayi. Yahanasu ce ta fito da kunun zaƙi jiki a sanyaye, ranta a dagule bazai rasa nasaba da surutan Hajara ba. "Yaronku na kawo muku dama, domun na kammala iddata har an sa mun ranar aure. To ba'a ƙasar zan zauna ba, shine nace bari inzo in ga yaran shi kuma Yusuf in dawo dashi gidansu" Baki na washe mata nace. Kai masha Allah, Allah ya sanya alkairi, Allah yasa gidanki ne. Ina taya Yusuf murnar dawowa cikin ahalinshi. Yahanasu tashi su Bawa su ga mamansu." Tashinsu Yahanasu tayi, Bawa ne kaɗai ya gane mahaifiyarshi, amman Maryam ta mance da'ita. Ɗan jim tayi ta saka hannu a ajjihu ta zaro dubu ashirin ta ajjiye mana "Ga wannan a yima shi Yusuf ɗin siyayya, tunda banzo da kayanshi ba. Sunan Asiya nazo sai kuma nayi amfani da damar kawai nace bari in kawo muku shi kawai. Tana kaiwa nan ta miƙe ta tafi. Bayanta nabi da kallo, ina juyowa Yahanasu ta gallamun harara tace "Ka mayar mata da kuɗinta, bata isa raina mana arziki ba, tunda gidanmu yafi nasu nesa ba kusa ba." Ran Yahanasu ya ɓaci ainun, ga kishi ina hangowa ƙarara a idanunta. Ba shiri nabi bayan Zubaina, tana shiga mota, ni kuma ina isa wajan. Ƙwanƙwasa ƙwalbar tagar motar nayi. Tana yin ƙasa da kwalbar na ajjiye mata kuɗinta a cinyarta, bance da'ita komai ba na juya na dawo wajan ƴar matata me kishina. A daren ranar naga rikicin Yahanasu, dan da ƙyar ta ba da kai bori ya hau, nasan ta wannan hanyar kaɗai zan rarrashi abata. Ahmad kuwa muna jiyo rikicinshi da Hajara, sai tafi da ɗaga mishi murya take yi, kamar wata ƴar tasha, duk da a hakan ma ta rage abubbuwa da daman gaske. KOFUR ZUBAINA: Bayan Bulama na bi da kallo, na dawo da kallona ga kuɗin daya ajjiye mun a cinyata. Alh Liti yace. "Amman wannan tsohon miji naki akwai shi da girman kai, da ganinshi talauci ya gigita rayuwarshi, ni tausayin Yusuf ne ma ya kamani. Jikina a mace na dubi Alh Liti nace. Su kansu su Bawa kar ka so ganin yanda duk suka lalace, cikin gidan ma kaɗai ya isa ka tausayama Yusuf da yayyenshi. Amman ni naji daɗin ganin Bulama cikin rashin daraja, da kasan wulaƙancin da yayi mun sabida dukiyar daya samu ai kare bazai ci ba ma alhakina ne ya talautashu." Motar shi yai ma key muka koma gidan Asiya. Washe gari da safe Alh Liti ya ɗauke mu zuwa Kaduna. Kwanan mu biyu da dawowa daga Kano, Alh Liti ya tura magabanshi zuwa gidan Kawu Tanko. Mazan su kai sadakin, matan kuma suka shiga cikin gida da akwatunan aure na alfarma. Mama ma tana gidan tare da Mama Rakiya ƙanwarta da Mama Zakiya, Musa yana waje tare da su Kawu Tanko. Kaji goma Mama ta soya musu akai musu pepper kickhen, sai kayan fulawa dangin cincin, meat pie, fish roll. Abun sha katon biyu, ruwa katon biyu. Dangin Alh Liti sun samu tarba ta mutunci. Ina daga ɗakin Goggo Safiya ina leƙensu. Tsofaffine, amman ƴan gayu cikin sutura mai daraja. Kayan akwati da su katon katon na sweet, biskit, cingam, ruwan gora, da lemun roba, sai da suka kusa cika falon Goggo Safiya. Dubu ɗari Mama ta zaro ta miƙa ma Goggo Safiya ta basu a matsayin tukuici, domun hausawa suka ce yaba kyauta tukuici, tuwon girma miyar nama" Zuwa bayan Isha suka yi musu sallama suka fita. Da sauri na fito daga cikin uwar ɗakin Goggo Safiya. Baki na kama da naga yawan kayan abun ya matuƙar bani mamaki. Ban tsure ba, sai da aka buɗe akwatunan naga nagartattun haɗaɗɗun tsadaddun kayan da Alh liti ya loda mun. Sai son barka ƴan uwa suke yi mun. Ana cikin haka Hajiya Mabaruka ta shigo da sallama da ɗan ƙaramin cikinta daya ƙara yi mata kyau. Dubanta nayi naga ta sake zama wata Hajiya, da gani hutu da nutsuwa sun samu waje a jikin Hajiya Mabaruka. Baki ta shiga washewa da ta ga irin kayan da Alh Liti ya lodo mun, da irin dukiyar daya narkar. Ita kanta da Salisu ke ji da ƙuruciya da tashen dukiya, bata samu rabin abunda na samu ba. "Ƙawata kinyi goshi gaskiya, irin wannan kayan alatu haka. Kiyi haƙuri naso zuwa tun tuni ayi komai dani. Amman Salis ne ya ɓata mun lokaci yace sai na jirashi shi zai kawo ni." Dariya nayi nace Ai babu komai ƙawata, baga ki kin zo yanzu ba" Kawu Tanko da Musa ne suka shigo da sallamarshi. Waje ya samu ya zauna a sama ya yi gyaran murya. "Jummai ga sadakin Zubaina nan nera dubu ɗari da hamsin nan na karɓa. Kamar yanda wanda ya ba da sadakin ya faɗi yace shi ƙanin mahaifin Alh Liti ne" Kuɗin ya miƙo ma Mama, tana washe baki ta karɓi kuɗin ta adana a jakarta. Kawu Tanko ya ɗaura da cewa. "Sati mai zuwa in Allah ya nuna mana juma'a da safe misalin ƙarfe bakwai safe za'a ɗaura auren a ƙofar gidannan. Zuwa ƙarfe goma da rabi jirginsu zai tashi zuwa Ghana in sha Allah, kuma ta Lagos zasu tashi, daga nan zasu hau jirgi zuwa Lagos. Duk wani biki a can za'a gabatar dashi tare da danginshi wanda su kai tsaye Ghana zasu wuce. Yaso daga shi sai Zubaina zasu tafi. To ganin rashin dacewar hakan yasa na roƙeshi akan za'a tafi da iyaye ko da mutum biyu ne, dan bai dace ace daga shi sai ita zasu kama hanya ba. Kuma tunda yace acan za'a gabatar da biki tare da danginshi ai ya kamata ace itama wani nata yana kusa. Da Safiya, da Rakiya sai ku shirya daku za'a tafi. Ƙawayenta sai su yi haƙuri waje ba kusa ba." Ni dai haushi ma Kawu Tanko ya bani, naso ace mu yi tafiyarmu mu mu biyu daga ni sai Alh Liti, sai Mabaruka da mijinta zai biya mata kuɗin jirgi. Amman sabida shishshigin ace matarshi ta taɓa hawa jirgine yasa ya roƙeshi. Mama tace. "Ashsha Tanko naso da ka bar Alh Liti yayi yanda yaso ɗin ya tusa matarshi sun tafi ni ina ganin da zaifi. Amman yaya zanyi tunda ka roƙeshi ya amince maka mutum biyu zasu bisu ai shikenan" Kawu Tanko yace. "Jummai kenan. Ai ni abunda duk kika ga nayi, ko nayi magana akai yana da matuƙar mahimmanci ne. Gani nayi in dai Zubaina da gatanta ai bai dace ace an ɗaura aurenta ta bi miji sun tafi wata ƙasar su su biyu ba. Ko banza yana da kyau ko da mutum ɗaya ne su bisu domun ganin muhallinta dan gudun afkuwar wani abun. Ni dai ta ɓangarena banyi bincike a kan Alh Liti ba. Amman ai ke kince ba'a buƙatar bincike sabida abokin mijin Asiya ne. Kinga dani da ku du bamu san halinshi ba, abun hannunshi kawai aka duba. Toh yace matarshi baza tayi aiki ba, tama ajjiye aikin ɗan doka da take yi. Amman akwai albashi da zai dinga biyanta duk wata na kimanin nera dubu ɗari biyu a kuɗinmu na najeria. Inaga iyakar abunda zance kenan. Allah ya nuna mana lokacin, zan je ƙauye gobe in sanar da su, zamu dawo tare da Isiya ma, da jama'ar ƙauye da zasu zo ayi biki tare. Sai Zubainar ta kasance a nan gidan da safe, dan daga nan zasu wuce." Haka dai mu kai ta shirye_shiryen biki. Ni da Mama mun so ayi bikin a sabon gidana dana zuba haya. Dan akwai ɗakina dana Mama a cikin gidan dana ware mana babu kowa a ciki. Amman kawu Tanko ya buƙaci ayi bikin a gidanshi kamar yadda aka saba. Ƙawayena kowa na son zuwa, wasu nisan ke kashe musu jiki amman ba dan basu da kuɗin jirgi ba. Wasu kuma basu son tafiya mai tsayi sosai. Haka dai naita aikin gyaran jiki da gyaran gashi, na tsawon kwana huɗu. Supplement na kamfanin G H T nasha na gyaran fata, nasha na gyaran al'aura duk wani na gyara babu wanda ban sha ba. Na sai majakani ma, da wani supplement mai ɗankaren kyau na matsi nera dubu tamanin na siye shi, na sha pesona ma shima ƙarshe ne. Maman Amal ita ta haɗamun kayan kamfanin G H T Cikin ƙanƙanin lokaci na canja na sake, ni kaina ina jin sha'awar kaina sosai. Kaya kala goma na ɗinka daga cikin kayan akwatina na cin bikin da za'ayi a Ghana, ɗinkuna masu tsadar gaske na sa akaimun sosai. Ran alhamis na yi taron bikina ni da Mama. Ƴan uwa da abokan arziki duk sun halarta, babban fili na kama akaci aka sha, aka yi rabon sobeniya na kasko da turaren wuta wanda MRS BUKHARI ke yi domun aure, ko bikin suna. Washe gari da sassafe muka kulle gida zuwa gidan Kawu Tanko. Dangin mahaifinmu cike da gidan maza da mata anzo daga ƙauye. Ɗaki guda aka ware mun ni da ƙawayena. Ina zaune nasha kwalliya da wani dafaffen farin lace, wanda yasha ɗinkin doguwar riga, stone work akai mun a jikin lace ɗin sai walwali nake yi. Takalmin ƙafata ma fari ne sol, haka fashion ɗan kunne da sarƙa na suma fararene sol. Sai ƙamshi nake ta fitarwa tamkar fulawar Queen of the night. Su Hajiya mabaruka sai zuba akeyi da kawayenmu. Nafisa ce ta shigo cikin shigar atampa super tasha adon gwalagwalai tace. "Anti Zubaina Mama na nemanki, tana wajan bayan ɗakin Kawu Tanko. An ɗaura auren ma yanzunnan" murmushi nayi wani farin ciki ya saukar mun, tare da faɗuwar gaba, da sanyin jiki wanda bana ce ga dalili ba. A sanyaye na bi bayanta muka fito, nan take sanar dani itama zata bimu ita da Asiya. Naji daɗi sosai, ko ba komai nima aga ƴan uwana suma masu kuɗine. Mama na samu a can bayan ɗakin Kawu Tanko ita da Mama Rakiya. Kasancewar nan ɗin shine ba jama'ar biki. "Yauwa dalilin da yasa na kira ki Zubaina shine. Aure an ɗaura yanzu, har ma Alh Liti ya turo a sanar muku nan da minti talatin za ku tafi filin jirgi. Ga wannan hayaƙin, da kun shiga ga Rakiya ta turare miki ko ina da shi. Ga gawayin kanti tafi da gidanka, dan nasan ko a maƙota ba zaku samu gaushi ba. Zubaina sai fa kin tashi tsaye sosai akan kishiyarki da yaran mijinki. Ki dinga turo kuɗi ana kaima bokanku tunda Mabaruka tana nan, kar ki je ki miƙe ƙafa, in ba haka ba zaki dawo najeria dan wallahi matarshi ba zata zauna ta miƙe ƙafa ba ke kin fi kowa sani ai. Kuɗin hayar gidanki kuma ya za'ayi miki dasu?" Dariya nayi guntuwa. Ku dinga amfani dashi. Zan turo kuɗaɗe ɗan abun da zan wawuro na amarci a sake sayen wani filin a rangaɗa ginin gidan sama babba. Amman kafin nan ina samun kuɗi zan sa a rushe gidanku a gina gidan sama mai lafiya,yanda ƴan anguwa zasu san e mai kuɗi nake aure. Zan sa Alh ya zuba muku komai sabo. Kuma zamu aikin Hajji harda Mama Rakiya da Musa da Sagiru ma in sha Allah. Nan mu ka yi sallama, ina fitowa naga su Mabaruka cirko cirko a tsakar gida. "Yauwa dama yanzu zan zaga in kira ki sai ga ki. Alh yace mu fita waje, zamu tafi Airport tun yanzu." Sallama na shiga yi da ƴan uwa da ƙawayena. Mu bakwai muka fita zuwa waje. Alh Liti yana jingine a motarshi muka fito, ya dube mu yace. "Ya nagan ku har ku bakwai, duk ina zaku je?" Mabaruka ce ta soma yi mishi bayani. "Ni da su Nafisa mun biya ma kanmu kuɗin jirgin. Su kuma iyaye su biyu kai zaka biya musu" yace. "To babu laifi muje ko?" Mota biyu ce ta kwashemu ƴan uwa sai hannu suke ɗaga mana. Kai tsaye muka wuce Airport mu ka hau jirgin Lagos. Ƙarfe goma da minti goma muka shiga Airport na na Lagos. Kai tsaye bayan an gama bincikar kayanmu, muka sake shiga layin da zai sada mu da harabar filin, dan shiga bus da zata ƙarasa damu wajan jirgin. Ƙarfe goma da rabi muna zazzaune a cikin jirgin ko wanne ɗaure da bell, na'ura sai magana take yi akan, kowa ya gyara zamanshi, nan da minti biyar jirgi zai ɗaga. Lokacin na cika jirgi ya shiga haramar tashi, cikina take ya bircike, dan ji nake kamar kaina zai fita a jikina. Bani na dawo dai dai ba har sai da jirgi ya dai dai ta a sararin samaniya, ajjiyar zuchiya na sauke mai ƙarfi. Na dubi Alh Liti yai mun Murmushi yace. "Matsoraciya, a haka zaki tafi yawon buɗe idanun kina shirin sume mun a jirgi gimbiyar mata. Yau gamu a matsayin ma'aurata, na tabbatar gidana zai baki farin ciki da nutsuwa, yanzu ne zaki san kin yi aure." Murmushi na mayar mishi nace. Ni kaina na san yanzu ne nayi aure. Kuma na tanadar maka farin ciki da nishaɗi a cikin wannan rana mafi girman daraja" "In kuwa hakane, na tabbatar daren yau babu abunda zai zo ya ture miki shi a zuchiyarki. A shirye nake dan dandalar zuma mai garɗi, wadda na daɗe ina tanadi, sai yau Allah yasa ta zama mallakina" Haka mu kai ta musayar narkakkun kalaman soyayya mai daɗi. Haka jirginmu yai ta gudu a sararin samaniya. Awa ɗaya da minti hamsin da huɗu jirginmu ya sauka a KOTOKA international Airport Accra" A hankali muka sakko daga cikin jirgin, zuwa cikin wata ƙofar glass. A cikin wannan falon muka jira akwatunan kayanmu da suke tawowa cikin wani abun sulu. Mu kuma duk muna tsaye, in akwatinki ya sulo sai ki ɗauka ki fice ta wata ƙofa, in da anan masu jiran ƴan uwansu suke jiransu, masu motoci da babura ma duk iyakarsu wajan. Wasu manyan motocine suka ɗebemu zuwa gidan Alh dake Nima anan cikin Accra. Mrs Bukhari ce [08/08, 9:04 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 30 . A hankali na buɗe idanuna ina kallon ƙasar Ghana, farin cikin dake cikin zuchiyata ba abu bane wanda zai musaltu ba. Babu abunda nake yi sai Murmushi. Cikin wata anguwa naga motarmu ta sulale ta shiga. Anguwace wacce take cakuɗe da masu kuɗi da talakawa. Amman gidajen masu kuɗin kamar yafu yawa, dan manya manyan gidajen sama su suka fi yawa ma a anguwar fiye da gidajen ƙasa. A wani katafaren gidan ƙasa muka tsaya gari guda. Gidan yasha zane irin na gidajen sarautun Arewa, amman gidan ya fi mun kama da irin zanen gidan sarkin Bauchi. Get biyu ne a gidan, tsakankanin ko wanne get akwai tafiya. Wani matashi ne mai tsantsar kama da Alh Liti ya taso ya nufo motar mu. Alh Liti ya sauke kwalbar jikin tagar motar ya dubi wannan saurayi ko magidanci zance yace dashi. "Buɗe mana get ɗin ɓarayina can, ta can zamu shiga." Yaron Alh Liti cikin hausarshi irinta hausawa mazauna Ghana yace. "Su Hajiya Kubra suna ta wanga ƙofa suna jiran isowarku Baba" Idanu Alh Liti naga ya runtse yace. "Nace ka buɗe mun wancan get ɗin ko Adamu, shin ko kayi hauka ne ban sani ba" A zabure wannan yaro ya wuce zuwa ɗayan get ɗin gidan. Mu kuma muka bi bayanshi da mota, mun yi tafiyar kimanin minti uku kafin mu iso bakin ɗayan get ɗin. Tura hancin motar mu muka yi zuwa cikin gidan, wanda yake cike da shukoki kala daban daban. Gidan nake ƙarema kallo sosai. Babban gidan sama na hango a ware a gefe ɗaya, anyi mishi gini irin na alfarma. Tsakar gidan an shinfiɗa intalok tako ta ina, ga wata baranta da aka ƙawata ta da kujerun kaba masu kyawun gaske. Jibga_jibgan motocin Alh Liti guda uku suna adane a rumfar adana motoci na farfajiyar gidan. Daga hannun dama na na hango wata ƙatuwar ƙofa wacce da dukkan halamu itace ƙofar da zata sada mutum da ɗayan ɓarayin, ba sai mutum ya fita waje yayi doguwar tafiya zuwa get ɗin farko ba. Da dukkan halamu ɗayan ɓarayin na uwar gidan Alh Liti da ɗiyoyinta ne, in kuwa hakanne zanci karena babu babbaka kuwa" firfitowa muka yi daga cikin motar. Alh Liti yana gaba muna biye dashi a baya. Key yasa ya buɗe wata ƙofa. Falone gabjejen gaske, wanda ya lamushe kujeru kusan saiti biyu da rabi. Ga wasu tum tum da aka barbaza a kafet ɗin dake tsakiyan falon, kalan kujerun, falon ya tsaru iya tsaruwa. Hotunan mata na hango cike da wani bango, ciki harda hotona, hoton Alh Liti yana tsakiya yafi na kowa girma. "Goggo Safiya ku shiga can ɗakin, zan sanar ma da mata isowarku a kawo muku abinci." Cewar Alh Liti kenan. Ni kuwa tsabar daɗi kamar in tashi sama haka nake ji. Ɗakin da ya nuna mana muka shiga, shi kuma ya haura matattakalar dake cikin falon dan hawa sama." Ɗakin baccine mai kyan gaske, komai na cikin ɗakin baƙi ne da ratsin silver, tun daga kan gado, wadrope, santa kafet, labulaye, komai da komai dai. Ɗakin babu wani kayan hayaniya, amman dake kayan ciki masu tsada ne, sai suka fito da ɗakin sosai. A bakin gadon na zauna, su Goggo Safiya kuma su ka yi rashe rashe a ƙasa suna ta kallon waje. Mabaruka da su Nafisa suka ɗane tsakiyar gadon suna yabon kyau da tsari, gami da girman gidan Alh Liti. Mabaruka tace. "Ƙawata a gaskiya gidanki yayi kyau babu ƙarya, kuma da halama ɓarayinki da ban, na uwar gida ma daban, in kuma ba a saman da Alh Liti ya hau take ba. Amman falonnan naki shararshi da tsabtaceshi sai ƴan aiki ba ma ƴar aiki ba, naga yana da girma sosai. Murmushi nayi mata nace. Gida kam yayi kyau, abun ma ba'a cewa komai gaskiya. Haka zanyi kane_ kane a cikin gidannan inta zazzage ƙwayayan da suke mahaifata a cunkushe, in giwa ta faɗi mu ci nama" Hannu ta miƙo mun muka tafa, tare da yin dariya ƙasa ƙasa, dama cikin raɗa_raɗa muke maganar daga ni sai ita. "Yanzu in Alh Liti ya tabbatar miki nan ɗakin shine naki, sai in sassaka miki layun da boka ya bayar ko?" Hakan data faɗa yasa na tuno da hayaƙin da Mama ta ba Mama Rakiya. A hankali na isa gareta a kunne nayi mata magana dan gudun kar Goggo Safiya taji mu. Ba shiri Mama Rakiya ta miƙe tsaye, nan ta shiga binciken ashana ko laita. Kab ɗakin dai bata samu ba, falo ta fita bata jima ba sai gata da laita ta shigo. Gawayin ta kunna, ta saka a ƙaramin kaskon ƙarfe da yake jakarta. Nan ta yi ma gidan hayaƙi har zuwa falo." Ina sallah na jiyo sallamar mace. Su Goggo Safiya ne suka amsa sallamar, ta turo ƙofa ta shigo. "Sannunku da zuwa lale. Ina yininku, kun zo lafiya?" Kafin su amsa na sallame, Amman ban juyo ba. Har suka gama gaisuwarsu. "Ni ɗiyar Alh ce, nazo ganin Amarya ne, sannan Hajiya tace in sanar muku a shirya Amarya, zuwa bayan la'asar akwai biki a ƙofar gida da za'ayi, in kun ci abinci, Ni sunana Hadiza" Gaggo Safiya tace. "To madallah Hadiza, kinga Amaryar gata can akan sallaya tana sallah ne. Zuwa dare ma zamu zo cikin gidan mu kawota, sannan zaku ganta a wajan bikin." Dariya tayi ta fice, naja guntun tsaki na takaici. Hadiza bata daɗe da fita ba, aka kawo mana abinci. Jallof ɗin shinkaface da kaza, sai coslo, da lemon gora da ruwan gora. Kowa yaci abinci ya goge wuyanshi. Daga bisani kuma, muka shiga shirin biki. Zuwa bayan la'asar kowa ya shirya tsab dashi. Ina sanye cikin wani net mai duwatsu masu walwali orange, ɗinkin riga da siket wanda suka ainihin zauna a jikina das, nayi kyau sosai, takalmin ƙafata mai ɗan karen tsini na saka mai ruwan madara, sarƙar wuya na itama mai ruwan madararce, na fito shar dani. Ƙarfe biyar dai _dai wasu mata su kai sallama a ƙofar ɗakin da muke. Mama Rakiya suka amsa musu, suka shigo. Su biyu suka shigo. Wata matace fara sol mai haƙorin makka a bakinta na azurfa dan sai ƙyalli yake faman yi, ita ta soma magana da cewa. "Sunana Hajiya Kubra nice uwar gidan Alh Liti. Wannan kuma ɗiyarshi ce, Maryam. In Amarya ta shirya zaku iya biyo bayanmu mu je." Kallonta nayi da kyau, itama ni ta saki baki galala tana kallona. Siririyace sosai, fara sol da'ita dan ta kereni fari, amman bata da hanci, kuma idanuwanta fici fici suke kamar fincen ƙuma, gata da ƙaton leɓe, duk da nima laɓɓana suna da girma, amman nata sunfi nawa girma. Atampa Chiganvy ce a jikinta ɗinkin riga da zane, sai wani ɗan mitsitsin gold a kunnenta, mayafin jikinta na nera dubu huɗu ne, takalmin ƙafarta bazai haura nera dubu uku ba. Fuskarta ba kwalliyar komai sai kwalli, duk da ta manyanta kaɗan. Baki na taɓe, naji wani sanyi a raina. Ita Maryam ɗin da akace ɗiyarshi ce, wani ƙoɗaɗɗen tsohon lace ne a jikinta, wanda tuni aka daɗe da dena yayin irinsu, in ba idanuna ke mun gizo ba ma, har ƙuraje leshin jikinshi yayi, hatta gyalen jikinta tsohon yayine irin na gyatumarta. Wani kallon banza na watsa musu kuma dukkansu sun gani. Goggo Safiya tace. "Dama muma yanzu muke shirin ɗakko Amaryar mu kawo muku ita, sabida gobe zamu juya in Allah ya yarda. Hajiya Kubra tace. "Ai Babu komai Baba kar ku wahalar da kan ku wajan kawota ma, Alhn zai kawota da kanshi, haka doka da tsarin gidanshi yake. Kuma da ace kun kawota ba tare da sanin nashi ba, ranshi ka iya ɓaci da hakan, mu janku ko?" Tana gama faɗar hakan suka fita ita da Ɗiyarta. Bayansu muka bi, tiryan_tiryan har zuwa ƙofar gidan. Inda ya cika ya batse da maza da mata, ana zazzaune a kujerun robar da suke cikin rumfar da aka kafa ƙatuwa. Ga makaɗa a fili sai tattakawa tsirarun mata suke yi. Wani irin biki ne wanda mu dai bamu gane kanshi ba sam, haka dai akaita abu ɗaya, gashi ba abinci, ba ruwa har aka tashi ba'a bamu komai ba. Iya ƙula na gama ƙumewa sosai. Muna dawowa na siga aikin kiran wayar Alh Liti dan in sanar mishi ba'a bamu abinci ba a wajan biki, kuma ba'a kawo mana abinci ba. Amman nayi kiranshi yafi sau goma, dana sake gwadawa ma sai naji wayar a kashe. a cikin jirgi Alh Liti ya bani sim na ƙasar Ghana na sanya a wayata .Mama Rakiya tace. "Kar ki ɗaga mishi hankali Zubaina, duk wannan abun bazai wuci sharrin uwar gidanshi ba. Amman tunda ba wata yunwa muke ji ba, ki bari mu tari gobe, sai ki yi mishi bayani cikin lumana bayan mun tafi." Haka na kwana cikin zafin zuchiya, da tunanin dalilin da yasa Alh Liti yaƙi ɗaga wayata. Washe gari da sassafe shi ya tashe mu. Ina buɗe ƙofar muka haɗa idanu dashi, kallona yayi ƙur kamar mai nazari, rannan nashi a murtuke, sai naga duk ya sauya mun, fuskarshi ta zama kamar ba tashi ba. "Kice ma su Goggo su shirya ƙarfe takwas zamu kai su filin jirgi" Tunda nake dashi ban taɓa jin muryarshi a kaurare haka ba, nayi mamaki sosai, amman sai na ɗaura alhakin hakan akan ƙila uwar gida ce ta murɗa kambunta, nace dashi. Dama suna so, su shigar dani cikin gida wajan Hajiya Kubra kafin su tafi" "A'a ni da kaina zan kai ki, bama sai sun wahala ba, ke dai kice su shirya." Yana gama maganarshi ya wuce. Ni kuma ina tsaye ina ganin ikon Allah, ban bar wajen ba har sai da na ga ƙulewarshi sama, sannan na juya cikin ɗakina jikina a sanyaye sosai. Kafin takwas kowa ya shirya tsab. Amman babu abinci ba dalilin abinci, har Alh Liti ya zo yayi mana sallama akan su Goggo Safiya su fito. Mabaruka ta ɗan jani gefe guda "Ga layunnan gudun kar a samu matsala, in zo in saka su a ɗakinnan, ya zamana ba a ciki zaki zauna ba, kyayi aikin da kan ki kawai. Kinga sharrin kishiya ko? Harta kaɗa miji mijinki ya sauya miki, tun jiya da yamma rabonmu da abinci" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Ni gabaki ɗaya naga Alh ya canja mun, kinga yanda yake harhaɗe fuska kuwa, yanzu yana nufin ba zaku karya ba zaku tafi?" Mabaruka tace. "Kar ki damu da wannan, ke dai ki shawo kan mijinki Zubaina, irin wannan gidan zaman cikinshi sai anyi da mugun gaske yake yiwu fa." Muryarshi muka jiyo yana kwaɗamun kira da sunana. "Ke Zubaina Zubaina ku fito mana" Tsurewa na kuma yi. Da sauri muka fito falon suna tsatstsaye mu suke jira. Amm Alh basu karya ba fa, kuma jiya da daddare ba'a kawo abinci ɗakinmu ba, inajin Hajiya Kubra ta manta ne." Agogon hannunshi ya kalla yace. "Yanzu in suka ce zasu tsaya cin abinci zasu iya rasa jirgi. In sun isa lagos sa ci abinci." Mama Rakiya tace. "Ai babu komai Alh" Goggo Safiya tace. "Amman munso mu miƙata cikin gida, wajan uwar gidan. To amman hakan bai samu ba. Alh dan Allah ayi haƙuri da duk halayen Zubaina. Kaga Zubaina yarinya ce, duk abunda tayi ba dai _ dai ba, a dinga nusasheta dan Allah " Murmushi yayi ya kwantar da murya yace. "Wannan ba komai Goggo, za'ayi ƙoƙarin hakan. Muje mu kaisu filin jirgin ko Zubaina?" Tare mu ka kaisu filin jirgin, muka yi sallama da juna, sai naji lokaci ɗaya jikina yayi laushi, har nake jin tamkar in bisu mu koma. Amman babu dama, mota na shiga mu ka bar filin jirgin izuwa gida. Tunda muka soma tafiya, babu wanda yace da wani uffan, kowanne da abunda yake saƙawa a cikin ranshi. Taka maimai in za'a shaƙeni bana ce ga abinda nake tunawa ba. A get ɗin farko muka dakata, Alh ya dube ni yace. "Fita ki buɗe mun get in shiga da motata." Kallonshi nayi cikin tuhuma, shima ni yake kallo, sai zazzare idanu yake yi. "Dallah fita ki buɗe mun get in shiga da mota, dan bura'ubanci kin kakkafeni da mayun idanunki" Wata uwar tsawa ya daka mun, sai da hantar cikina ta kaɗa, ba shiri na ɓalle murfin motar na fito a hargitse. Da sauri na tura ƙaramar ƙofar dake jikin get ɗin, na shiga cikin gidan. Turus na tsaya cak, ina ƙarema gidan kallo, wanda nake gani kamar mafarki nake yi, in kuwa ba mafarki bane, to tabbas wannan shafar aljanune" Mrs Bukhari ce [08/08, 11:24 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR (,DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 31 YAHANASU: Sai da na shafe kusan kwana huɗu ina fishi da Bulamana. Shi kuwa yaƙi sam yayi fishi dani, sai lallaɓani da yake faman yi. Yusuf kuwa rashin sabo yasa kullum a cikin ɗan karen rikici yake, musamman in dare yayi, sai yai ta kuka, wata rana in na bashi ruwa ya karɓa yasha, wata rana ya botsare mun. Yau kwanan Yusuf biyar da dawowa hannuna, Bulamana ya siyo mishi ƴan kayan gwanjo kala uku. Nima yau na ɗan biya kasuwa bayan na tashi aiki na tsinto mishi kala uku, na ƙaro ma su Bawa kala bibbiyu. Bulamana ma na siya mishi wandon jins guda biyu da ƴan t shirt kala biyu, dan kayan nashi duk sun soma jemewa, gashi har zuwa yanzu ƴan Damaturu basu san halin da muke ciki ba. Kullum muna kiransu a waya a gaggaisa, amman muna sa ran zuwa sati mai zuwa bikin Wakil. Ina zaune a tsakar gida sai faman aikin kunun zaƙi nake yi, yara sai shigowa saye suke yi, a yanzu a iya cikin gida ma ina yin dubu biyu da ɗari biyar, banda wanda nake kaiwa shaguna, ga meat pie shima yanzu ina cinikinshi a gida, banda wanda ake kaiwa shaguna. Uwatale ce ta shigo wajena, baki na washe mata. Uwatale baki yi fishi dani ba, wallahi naso in shiga miki jiya, amman sai naga mashin ɗin Baban Maryam a ƙofar gida, nasan yana ciki, kinji dalilin rashin shigowar tawa. Ga kujera zauna mana" Zama tayi tana hararata tace. "Har akayi azumi, aka sallace bamu haɗu ba, ke da an taɓa ki kice bakya zama aiki, ni nama gaji da wannan ƙawancan gaskiya." Dariya mu ka yi duka, meat pie da kunun zaƙi na kawo mata. Bismillah ƙawata, muna hira kina korawa ko, kin ganni girki nake son maza maza in kammala, zamu je dubiya ni da Abban Bawa ne asibitin murtala, shi yasa kika ga inata sauri" Uwatale ta kalli Yusuf dake zaune a bakin ƙofa yana cin meat pie tace. "Ƙawata wannan yaron fa, baƙi kika yi ne?" Au Yusuf wai? A'a ƙanin Maryam ne, mamanshi zata yi aure ne shine ta kawo shi" Zama Uwatale ta gyara tace. "Ƙawata ashe jita_jitan da nake ta ji a cikin layi gaskiya ne, cewar su Maryam ba yaranki bane, yaran mijinki ne?" Baki na riƙe nace. Tsegumi daɗi, wato har wani jita_jita akeyi a anguwa? Zancen duniya baya ɓuya" "Hmmm ƙawata, Hajara ce take ta yaɗa zancan duk inda ta ɗaura ɗuwawu ta zauna, sai ta yi hirar. A wajan matan gidanmu nake ji, suma itace ta fesa musu." Take jikina yayi sanyi kamar an watsa ma kaza gishirin, rashin samun haihuwa ya sake dukan zuchiyata, nayi shiru na wasu daƙiƙu. Uwatale tace. "Ƙawata ina adda'ar kema Allah ya baki naki yaran ki rainasu da hannunki. Kuma dole a yaba miki yanda kika riƙi su Bawa, duk da dai kince auren zumunci kuka yi ke da Abbansu. Daɗin auren zumuncin kenan, ai duk kishinka baka cutar da yaran ɗan uwanka ba" Haka dai mu ka yi hirar inata daurewa, sai da na gama girki na zuba mata, da taci ta ƙoshi ta mun sallama. Magriba na gama duk aikace _aikacena, har nayo wanka. Abinci na zuba ma yaran, ni kuma na ƙule ɗaki abun duniya duk yabi ya isheni, kwaɗayin son samun ciki ya sake shigata. Doguwar riga ƴar kanti na zura a jikina, wadda Bulamana yai mun da ƙaramar sallah. Sallar magriba nayi, ina zaune a kan sallaya na zuba tagumi bulamana ya shigo da sallama. Ciki _ ciki na amsa sallamar tashi, dan tun ranar da Zubaina ta tako ƙafafunta zuwa cikin gidannan nake ta aikin fishi dashi, yayi rarrashin, yayi magiyar, amman fur naƙi daina fishi. Tun ranar ban sake bashi hakkinshi ba, duk da inna kalleshi yana bani tausayi, domun nasan baya iya zura mun idanu na kwana biyu ba tare da ya huta dani ba, sai dai in al'ada nake yi, shima kwana uku nake yin wanka. Amman yau kwana biyar rabonshi dani. Wannan shine karo na farko da nayi fishi mai tsawo dashi, tun bayan daidaituwar zaman aurenmu. Nima kuma ina kewarshi sosai. "Gashi, zaki ga ƙunshin naki yafi girma, ƙaramin na yara ne, ki shirya ina dawowa masallaci zamu tafi" Yana gama faɗar haka ya fita, dan kiraye kirayen sallar isha aketa yi. Sai da nayi sallah, sannan na buɗa ledar da Bulamana ya turo gabana. Balangune gashin ruwa ruwa, yaji kayan ƙamshi sai turiri yake yi. Murmushi nayi, dan nasan so yake yi dai in sakar mishi mu dawo yanda muka saba, ni kaina duk na bi na takura, amman wani sa'in ɗan adam yakan wayi gari cikin jin haushin kowa da kowa ma, wannan ɗabi'ace ta ɗan adam. Musamman ma'aurata sunfi shiga irin wannan yanayin. In ba'a kai zuchiya nesa ba, akan iya samun gagarumar rikici akan ɗan abun da bai taka kara ya karya ba. Kiran yaran nayi suka shigo. Kasafta musu nasu balangun nayi, na ba kowa nashi. Kunun zaƙi na ɗakko mai sanyi inaci ina korawa. Kai Allah kai mana arziki mai albarka. Rabi naci na ƙunshe mishi rabin. Da sallama ya shigo. Na amsa mishi. Cikin yaranshi ya shiga ya zauna, sai biyema shirmensu yake yi. Wasu siraran hawayene naji suna surnanowa daga gurbin idanuna. Ni sai yaushe zanga nawa jinin Bulamana yana wasa dashi, kamar yadda yake wasa dasu Bawa?" Bansan Bulamana yana kallona ba, ji nayi ya riƙo hannayena yana murzasu a hankali. Jikina murza yatsun da yake mun yake shiga sosai, kasancewar nayi kewar hakan. "Menene ya saki kuka Yahanasu na, haba masoyiyata. Me nayi ne kike ta faman azabtar mun da ruhina?" Da sauri na fisge hannuna na tashi a guje, na shige wajan katifarmu dana raba da labule.ina shiga na kife a katifa sai na raushe da kuka, wanda nake jin ciwonshi daga ƙasan zuchiyata" Da sauri ya shigo. Ji nayi ya kamoni gabaki ɗaya ya sani a jikinshi yana rarrashina. Jina a jikinshi yasa na kuma rushewa da kuka mai taɓa zuchiya" "Wani abunne ya faru bayan fitata ko menene Yahanasu? Dan Allah kiyi shiru ya'isa haka yara suna jiyo kukan ki fa" Haɗiye kukan na shiga yi, amman hawaye bai dena sunturi a kumatuna ba. Zaunar dani yayi muna fuskantar juna. "Menene yabi ya dameki Yahanasuna, yau tsawon kwana biyar kina ƙunci, ko zuwan Yusuf ne baiyi miki ba? In kina ganin hidimar tayi miki yawa sai in kai shi wajan Hajja, ko Ya Innana, zuwa kafin ya soma......" Da sauri na katseshi. Ko kusa in yaran daka haifa da Zubaina sun kai goma, ni zan riƙe maka su, in basu tarbiyya har suyi aure. Kawai kishinka ne ya dinga nuƙurƙusan zuchiyata, ganin Zubaina ya famamun abubbuwa da suka faru a baya. Sai idanuna suke nuna mun kamar kallon so kake yi mata, zuchiyata tai ta rura mun abun. Wannan shine abunda yasa nake ta ƙunci, amman ba dan zuwan Yusuf ba. Yau kuma na shiga damuwa a sakamakon rashin samun haihuwata, ko Ya Innana abun yana damunta ko da yaushe a cikin yi mun magana take" Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya dubeni cikin zolaya yace. "Au kishina ashe kike yi, ɗan duƙununu dani, mummuna dani?" Kafi mun ko wanne ɗa namiji kyau a duniya. Ka sani kyawun zuchiya shi ake biɗa, ba kyawun fuska da zubin halitta ba. Wannan baƙar fuskar, da wannan jan idon su ke sa in sake jin lallai kana da wani matsayi babba a zuchiyata." Dariya mu ka yi, na faɗa jikinshi, ina share hawayena da bayan hannuna. "Kai yau naji daɗi, sai yau na samu nutsuwa. Amman zan rama, irin wannan wuya da kika bani, in na kamaki anjima a shinfiɗa, sai na fanshe duk ƙullewar marar da kika haddasamun, dan yau fyaɗe nayi niyyar yi miki" Kalmar data dakatar da nishaɗi da walwalar dake shinfiɗe a fuskata, na sake rikicewa da hawaye. Shi kanshi na lura yayi nadamar furta wannan kalmar. Da ƙyar ya shawo kaina nayi shiru. Kwalli na murza ma idona, na naɗa lafaya ta muka fito. "Ki yima Hajara magana ta ɗan dinga jiyo miki motsin Yara, da masu zuwa neman kunu" Tsaƙi nayi guntu na harari wajen da Hajara suke zaune da Ahmad" Dan Allah daure ka faɗa ma Ahmad ɗin, ya sanar mata" Ana cikin haka Ahmad ya taso ya iso wajanmu. "Sai yanzu zaku je dubiyar, aini na ɗauka tuntuni kunje har kun dawo" Cewar Ahmad" Bulamana yace. "Kaga ƴar rigimar data tsai damu nan, amman yanzu zamu je mu dawo. Ƙofar a buɗe take madam ta dinga duba mana yaran, sai mun dawo" Sallama su ka yi, ina jiyo Hajara na ce mun sai mun dawo, banza nayi da'ita. Nayi kamar ma bansan me take cewa ba. Muna cikin ɗan sahu ne nake ba Bulamana labarin abinda Hajara take ta yaɗawa a anguwa a game da yara. Shima ranshi ya ɓaci sosai yace. "Ai Ahmad bai yi sa'ar matar aure ba sam. Yarinya ba kamun kai ba nutsuwa sam. A hakan ma ai ruwa ya daki babban zakara, a lokacin da Ahmad yake da abun hannunshi, meye Hajara bata yi ba. Rayuwar ƙarya iri iri. Yanzu ne fa ta nutsu talauci ya saitata." Har muka isa asibitin Murtala muna ɗan taɓa hirarmu. Alhn daya basu lon ɗin ɗan sahu ne ba lafiya, shi muka je muka duba a asibiti. Daga nan ya wuce dani sahad mu ka siyo chocolate nawa dana yara, a gajiye muka shiga gidan tulus. A cikin wannan dare, mun murji junanmu sosai, Bulamana zame mun yayi tamkar mayunwacin zaki. Rungume da juna muka yi baccinmu mai daɗi. Haka mu ka wayi gari cikin walwala da farin ciki. Takwas Bulamana ya fita, suna da jarabawa a makaranta. Ni kuma dai a hankali yau na kammala komai, sai wani jiri da tashin zuciya nake ji. Sai wajajen tara da rabi ma na isa office. Haka dai wunin na yi shi sukuku. Kamar wasa da zan shiga gida na sai p t. Ai kuwa ina gwadawa ya bani ina da ciki. Jan layi biyu suka fito ɓaro ɓaro. Murna a wannan ranar ba'a cewa komai, duk da a kwance na wuni, amman ina Allah _Allah Bulamana ya dawo in yi mishi albishir. Girki ma na kasa, sai inji amai na taso mun. Sai Uwatale na kira tazo ta ƙarashe mun, ta yi mun wanke_wanke. Hajara sai suntiri take yi mun, so take taji abunda ke damuna, ni kuwa nace mata mura ke damuna, hancina yoyyo yake yi, shi yasa na kasa yin girki. Sai Magriba Uwatale ta yi mun sallama ta tafi. Ina kwance Bulamana ya shigo da ƴar guntuwar sallama ɗauke a bakinshi. A hankali na amsa mishi ina kallon idanunshi, wanda suka ƙanƙance tsabaragen wahalar aiki, ga kuma karatu ma. "Ba lafiya ne na ganki a kwance a ƙasa?" Hannu yasa ya ɗauki Yusuf daya tawo wajanshi, amman hankalin shi yana wajena. Lafiya lau, ciwon daɗi da farin ciki ne ya kwantar dani" Zama yayi yana murmushi yace. "Inna canka dai _ dai ciki ne dake kenan ko?" Dariyar da nayi ta bashi tabbacin abinda ya faɗa dai _ dai ne. Hamdala yayi tare da kallona yana dariya. "Kuka ya ƙare kenan ko? Sai ki nutsa ki kula da kanki, meat pie da kunu ni zan dinga yi miki, aiki kawai na yarda kije, kuma in muka tafi bikin Wakil, ina tunanin zan ajjiye Yusuf a wajan Ya Innana, ke ma ki kula da kan ki, in yaso in lokacin shigarshi makaranta yayi, sai ya dawo. Zuwa lokacin abunda kika haifa shima yayi ƙwari. Allah ya raba lafiya" Ameen nagode. Amman dan Allah kar ka faɗa ma ƴan Damaturu, ka barsu kawai, in na juye abunda ke cikin nawa sa sha mamaki. Tunda a baya kaga abunda ya faru. Muita adda'ar Allah yasa mai zama ne" Yace. "In zaman nashi shine mafi alkairi ba. Ai dukkan abinda kika ga ya samu bawa, to da sanin Allah, kuma shi kaɗai yasan dalilin faruwar hakan. Sau da dama zaka so abu, kaga Allah ya hanaka. Ƙila ba alkhairi bane a cikin rayuwarka wannan abun da kake ta so. Ki dogara da Allah kawai" Ghana: ZUBAINA: Abunda idanuna yayi tozali dashi ya firgita tunanina. Da sauri na leƙo waje domun tabbatarma da kaina anya nanne gidan Alh Liti kuwa inda uwar gidanshi take ciki? Nan ɗinne kuwa. Jikina na rawa na ɓalle sakatar dake jikin get ɗin na wangale mishi, domun wani irin gigitaccen hon ya soma yi mini. Kunno hancin motar tashi yayi izuwa ciki, da ƙyar na mayar da get ɗin na rufe. Wani irin kwaraɓaɓɓen gidane, mai cike da yara yingu_ yingu, da ƴan madaidaita, harma da ƴan mata da samari. Filin tsakar gidan ba ko filasta, rairayine a tsakar gidan, wasu ɗakuna guda shiga na hango a jejjere kamar gidan aladu, dan basu da tsayi sosai, ginin ya galabaita, haka kwanon da a ka yi rufin ɗakunan a ratattake suke, wannan ana samun ruwa da iska, zai kwashesu yayi awon gaba dasu. Wata mata na gani a gaban tulin tarin uban wanke_ wanke, tana ta aikin wankesu, yayin da nake hango ƙyallin wutar murhu na itace a cikin wani gini ɗan guntu yana tashi, irin kitchen ɗin ƴan ƙauye, ko ince na mutan da. Ƙatuwar tukunyace akan murhunnan, wata mata mai goyo sai iza wutar murhun take yi, hayaƙi na buleta ita da yaron bayanta idanunta tab hawayen da hayaƙin itacennan ya haddasa mata. Hajiya Kubra kuma tana zaune gefe guda tana yima wata ƴar matashiyar budurwa kitso. Kowa dai na harkokin gabanshi, suna cikin wasu irin tsummokarai, yara_yaran kuma wasu ba riga fuskokinsu a mugun bushe kunatukansu duk waskane, manyan kuma a yamushe suke. Kaina yayi wani irin mugun ɗaurewa, anya ba mafarki bane kuwa, to ko dai aljanune suka shafeni?. A tsaye Alh Liti ya sakko ya same ni. "Kubra banga Rumaisa'u ba, ina fatan ta tattare iya kar kayanta ko? Ga Zubaina zata maye gurbinta" Hajiya Kubra tace. "Tana cikin ɗaki, tun safe Rumaisa'u take kuka a cikin gidannan, babu kalan rarrashin da ba'ayi mata ba, wallahi bata kula ba" Da mamaki Alh Liti ya kalli Hajiya Kubra yace. "Dan bura'ubanci nine zan bada umarni, wata ƴar iska ta ketare karar dana gindaya? E lallai Rumaisa'u karanta ya kai tsaiko" Malum_malum ɗin shi ya tattare, ya kutsa kai ɗakin da yake kallomu. Ni dai gabaki ɗaya kaina ya kulle, ikon Allah kawai nake son gani. Ghana most go Alh Liti ya jefo tsakar gidan, tare da jefo wasu tsunmokaran kayan sakawa. Ban gama rufe baki ba naga wata mata ta faɗo gabana Alh Liti ya jefo ta. Kuka kawai take yi tana faɗin. "Kai mun rai Alh Liti ina son zama ko dan goben yarana. Gidannan babu wadatacciyar tarbiyya, yaro mahaifiyarshi ma na tsugunne a gidan ya ya cika, balle bata nan. Ni inma ba zaka barni in zauna ba, ka bani su in tafi dasu" Huci naga Alh Liti yana yi, gabaki ɗaya ya sauya ya zama abun tsoro. "Ni zaki tafi ma da yara? Buyagi, to na baki nan da mintuna goma ki bar farfajiyar gidannan, tunda babu kuɗin ubanki a ciki, kwaɗayayya, ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi, yasan a tashar wulaƙanci motar nan zata ajjiyeta. In kika sake na dawo na tarar dake anan zaki fita da gudu, ƙila ko arzikin sutura ma bazaki samu ba. Ke kuma daga yau wannan shine ɗakin ki, zaki soma zuwa kwana turaka daga daran yau." Fuuu ya nufi babbar ƙofar da zata sada shi da ɓangarenshi. Ni kuwa da kallo na bishi, idanuna suna tsiyayar ruwan hawaye masu ɗumin gaske. Mata da yaran gidan ko wacce kanta a ƙasa da dukkan halamu Alh Liti boss ne a cikin gidanshi, kowa tsoronshi yake yi. Hajiya Kubra ta matso kusa da Rumaisa'u da take ta kwashe kayanta tana turawa a Ghana most go ɗinta tace. "Rumaisa'u da kin bi shawarata da duk haka bata faru dake ba. Domun irin wannan korar karen a gabanki anyi ma mata uku, kuma kinsan Alh bazai sauya ba. Ke da zaki yi hamdala kin rabu da ƙwallon mangoro kin huta da ƙuda, yara Allah zai raya su, zasu neme ki a duk inda kike." Wannan mata mai goyo, wacce take aikin girki ta fito tace. "Wallahi ni naso ace ta kaina sakinnan ya zagayo, domun inda kika san a kan ƙaya haka nake. Danni wallahi babu zaman iddar da zanyi a wannan ƙaddararren gidan ma. Amman nasan sakin ki da Alh yayi, shi ya bani damar matsowa layi, ana tafe za'a isa." Wannan mata mai goyo na kalla, ruwan jiri na shirin ɗibata in faɗi tsabar yanda nake ji jikina takota ina rawa yake yi. Alh Liti to matan aurenshi nawa ne, ni da yace mun matarshi ɗaya tilo da ƴan ƴaƴayenshi shida. Sai gashi nazo na ga saɓanin abunda yace mun. Ga ni, ga Hajiya Kubra, ga Rumaisa'u, duk da dai a iya fahimtata na fahimci aurensu ne ya ƙare ita da Alh liti, ga kuma mai goyo. Kuma Hajiya Kubra tace an kori mata uku a gaban Rumaisa'u, ɗaurewar da kaina yayi yafi gaban misali. Wannan wanne irin gidane na kawo kaina" Haka nake ta maimaitawa a zuchiyata, ban gama ta'ajibi ba, muka hango Alh Liti da ƙaton gora irin ta bugun ɓarawo ya nufo mu gadan gadan da wani irin mugun gudu, iska cike da malum_malum ɗinshi. Habawa kowa take ya dare, yayi ta kanshi mata da yara sai rige_rigen gudu suke yi. Ɗakin da Alh ya nuna mun yace in shiga, nan na faɗa da mugun gudu ba shiri, harda tura ƙofa A jikin bango na jingina, hannuna na dafe da ƙirjina, a firgice nake ainun, idanuna suna zubar da ruwan hawaye. Har izuwa yanzu gani nake yi tamkar ba ni bace. Ina tsaye ina jiyo yanda Alh yake kutumtumo zagi ɗuma_ ɗuma irin na Sakkwatawan Shehu. Gidannan yayi tsit tamkar babu ƙwayar halitta mai rai. Abubbuwan da suka faru a tsakar gidan, tare da maganganun da suka faffaru, su kaina ƙwaƙwalwata ke ta juya mun, a ƙoƙarinta na son ganin gano bakin zaren. Ni dai abunda na fahimta shine. Alh Liti matanshi uku banda Rumaisa'u daya saka, yaranshi kuma suna da yawa naga halama, domun ko iyakar waɗanda na gani a tsakar gida za su kai dozin uku in ma basu fi ba. Kaina na dafe wanda yake saramun, ahankali na sulale akan ledar tsakar ɗakin, na saki kuka mai gunji. Tuni na shiga hasashen makomar rayuwata a cikin ƙasar da banda kowa, gidan da kamar kowa ta kanshi yake yi. Me yasa ma tun farko na aminta da Alh Liti ne? Wata zuchiyar tace mun. "Zaƙin bakinshi, da abun hannunshi su suka rufe miki idanuwanki" Ni sai yau ne na sake ganinshi da kyau, na kuma gane lallai ko kusa bamu dace da juna ba." Nafi awa biyu a zaune ina aikin karanta wasiƙar jaki, ni kaina bana ce ga abinda nake tunanowa ba. Kiran sallar azahar da na soma jiyowa daga masallacin cikin unguwane ya dawo dani kan doka da oda. Ajjiyar zuchiya na sauke, na sa hannu na shasshare hawayen dake ta faman sintiri a kumatuna. Sai a lokacin na shiga karema ɗakin kallo. Gadone ƙarami a ɗakin, sai wadrope mai ƙofa biyu shikenan abunda yake cikin ɗakin, ƙaramine sosai ɗakin, filin tsakar ɗakin bazai wuci mutum uku su zauna su miƙe ƙafafuwa ba, hatta windon ɗakin ƙaramine sosai, hakama ƙofar shiga ɗakin itama ƙarama ce. Har aka idar da sallah a masallaci ina zaune dirshen bani da guiwar da zan iya miƙewa tsaye, jikina yayi mugun sanyi kamar wacce aka watsa ma ruwan firji. Da ƙarfi naji an doko ƙofar ɗakin, a zabure na miƙe tsaye nima, dan na gama tsorata da sha'anin Alh Liti. Wannan matashiyar yarinyar ce da Hajiya Kubra ke ma kitso ɗazu. Hannanunta riƙe da kwanon silver da kofin silver na ruwa. Ɗan Murmushi tayi mun kaɗan, ta ajjiye mun kwanon da kofin. "Ga abincinki nan Anti Amarya, Hajiya ce tace in kawo miki." Harta juya zata fita da hanzari nace. Dan Allah inane bayan gida inason zan kama ruwa in yi alwala?" Bata juyo ba tace. "Muje to in nina miki bayan gidan" A tsorace na biyo bayanta muka fito. Su Hajiya Kubra duk suna tsakar gidan, abinci suke ci, a manya manyan tire. Hajiya Kubra tace. "Kin fito yin alwala ba Amarya" E" Shine amsar daya fito a bakina, wata ɓagurarriyar buta wannan matashiyar ta ɗakko ta cika mun ruwa a ciki, ta bani. "Ta lungunnan bayan gidan yake, da kin shiga zaki ganshi" Wuce wa nayi lungun da take nuna mun, bayan nayi mata godiya. Bayan gidan babu laifi a tsabtace yake, yasha sumunti sumul sumul, sai ɗan zarni da baza'a rasa ba. Ina hawaye na kama ruwa na fito. Ni da nayi tunanin bayan gidana sai ya zama abun kallo, sai gashi na lalace a shiga bayan gida mai daɓen siminti. A tsakar gida nayi alwalar inda naga wata ƴar yarinya da bata wuci shekaru uku ba tana alwala. A kusa da su Hajiya Kubra na tsaya nace. Dan Allah Hajiya inane gabas?" Da fara'arta tace. "In kika shiga ɗakin ki, ƙofar shiga zaki kalla nanne gabas ɗin" Godiya nayi mata na koma ciki, sai gauraye hanya nake yi. Yaran gidan kuma abun kallo na zame musu, sai uban hayaniya da sowa suke yi, wanda wannan kaɗai ya isa birkita ƙwaƙwalwa. A zaune nayi sallar, dan tsaiwar ta gagara babu guiwa a tare dani. Cikina sai murɗamun yake yi, rabon da ya samu loma tun jiya da yamma. Kwanon abincin da aka kawo mun na jawo. Ina buɗewa naci karo da farar shinkafa sol da manja da yaji, sai albasa ɗanya da aka yayyanka a saman abincin. Ina hawaye ina tura abincinnan a bakina, loma huɗu nayi na sha ruwa, na ture kwanonnan gefe. Tunanin hanyar guduwa na soma yi, domun bazan taɓa iya rayuwa a cikin irin wannan gidan ba, in ma na zauna tamkar na kashe rayuwata ne baki ɗaya. Tunano ƙannena da ƙawata Mabaruka na shiga yi, da su Hadiza da duk suke auren masu sukuni, suke fantamawarsu, babu ma kamar Mabaruka a cikinmu. A wannan ƙaddararren ɗakin na wuni, tunani ya kaini har bayan magriba. Duhu dilim a ɗakin, amman kasancewar gangar jikinane kaɗai a cikin ɗakin ruhina baya wajan yasa banga duhun ba. Turo ƙofar akayi da fitilar ƙwai a hannun mai shigowar. Hasken haƙorin makan Hajiya Kubra na gani tana yi mun Murmushi, hannunta riƙe da kwanon abinci. A gabana ta dure kwanon, ta nemi waje gefen gado ta zauna. "Baiwar Allah kina ta zaune sai wasiƙar jaki kike ta karantawa ko? Tun ɗazu nake ta jiran fitowarki domun in faɗa miki ƴan ƙa'idojin gidan namu wanda ya kamata kiji a bakin nawa, sauran kuma Alh zai faɗa miki domin shi dake ya shafa kai tsaye. MRS BUKHARI CEMAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 32 Amman kafinnan inaso in soma da baki shawara. Abu mafi sauƙi da zaki yi shine ki kwantar da hankalinki, karma tunanin tawaye, ko guduwa ya zo zuchiyarki, in kika watsar da komai, kina zaune haka a cikin ɗakinnan, in dai Alh ne zai leƙo ya ce ya sake ki, in ya samu wata. Kamar yadda ya saki Rumaisa'u daya same ki, haka ne yake gudana a cikin lamarin rayuwar Alh, sake mace yafi mai sauƙi fiye da cire hula a kanshi. To dokokin gidan sune. Alh ƙarfe takwas na dare yake shigowa cikin gidannan, yana so kafin ya dawo wacce take da girki ya zamana ta kasance a bakin barandar turakarshi domin tsaiwar jiranshi. Ƙin yin hakan ka iya sawa ki fuskanci fushinshi, fishinshi kuma babu kyau a gareki. Sannan in ya buɗe kofa kuka gaisa, saiki zo ki gabatar mishi da abinci, wanda dama tun magriba abincinshi zai kasance a ɗakin wacce take da kwanane. Girkin gidannan yana da matuƙar yawa da wahala hakan yasa ko wacce mace bata da wani hutu a cikin gidan kullum. Wacce take da girki ita zata yi girki ita kaɗai, mu kuma zamu kama shara, wankin bayi, da wanke wanke. Yaran gidan kuma aikinsu shine ɗibo ruwa da ɗan aike da dai abunda baza'a rasa ba. Abincin gidan kullum iri ɗaya ne. Da safe abunda ake dafawa shine dai, haka ma da rana, da daddare ma haka. Ranar juma'a ne kaɗai ake yin tuwon shinkafa da miyar kabewa da rana. Baya ga wannan rana babu wani sauyi a abincin gidan.Sai da sallah ƙarama ko babba ake dafa shinkafa da jar miya wato miyar sutu, Ina ganin abunda ya kamata kiji daga gareni kenan, sauran bayanan shi zai miki, in ma da abinda na mance ban sanar miki ba, sannu a hankali zaki gane ki fahimta. Hawaye na bin fuskata nace da'ita. Na gode da bayananki, amman da kin adanasu zasu yi ma wacce Alh zai kawo gaba amfani. Domun Allah ko kwana bakwai bazan yi a cikin gidannan ba, ƙasarmu zan koma" Wani murmushi taimun mai fassara, ta miƙe tsaye. "Irin wannan taurin kan, da ikirarin nayi a shekaru Ashirin baya da suka wuce, kuma wannan dalilinne ya bani lasisin zaman dirshen a gidan Alh Liti. Da ace ban yi rigima dashi ba, da tuni nafi shekara goma sha tara da rabuwa dashi, na tafi wani gidan na gina kyakkyawar rayuwa mai inganci. Sakin da yaga shine kaɗai abunda nake nema yasa shi kuma ya ƙi sakina dan tsabaragen muguwar mugunta. Kuma wannan shawarar na kan ba duk wata Amarya da Alh zai kawo ta cikin gidannan." Miƙewa tsaye nayi, nayi tsaiwar daka a gabanta nace. Kema yaudararki kenan Alh Liti yayi ya baroki da ƙasarki da danginki?" Murmushin da na lura ya zame mata jiki ta kuma yi mun. "Yarinya, son zuchiya da kwaɗayin abun hannun Alh shi yai sababin shigowar duk macen da Alh ya auro, da waɗanda zai auro nan gaba ma. Dukkanmu kwaɗayayyune daga mu har iyayen namu ke kin sani nima na sani, Alh Liti hatsabibine ki kiyayi jayayya dashi. Ɗakina yana jikin naki, in Alh ya dawo ko sai ki zo ki karɓa mai abincinshi, takwas saura kwata yanzu" Tana kaiwa nan ta fita, ta bar mun fitilar ƙwan. Ko kallon abincin data kawo mun banyi ba, kan gado na faɗa, wani mugun wari da zarni ne yasa na tashi da sauri. Zirga _ zirga na shiga yi a harabar ɗakin, na dunƙule hannuna na dama, yana nausar na hagu, ina neman mafita da tunanin dabarar da zanyi ma Alh ya sauwaƙe mun cikin ruwan sanyi. In kuma yaƙi sauwaƙe mun, in gudu da auren nashi a kaina, in shige duniya." Agogon hannuna na duba da sauri, takwas saura minti biyar. Mayafina dake ƙasa na ɗauka na fito tsakar gidan. Matan gidan da yaran gidan duk suna tsakar gidan, suna shan iska, kowa da sha'anin da yake yi. A yanzune naga tulin bataliyar yaran nashi, manyan maza da manyan mata, waɗanda bamu haɗu ba, sai gaisheni suke yi, yayin da mata _ matan suke ƙunshe dariyarsu. Tsakar gida kamar anacin kasuwar monday ta Kaduna, ace duk wannan bataliyar yaran na mutum ɗaya ne, kuma kai zaka yi musu girki kai kaɗai su ci? Tab wannan daka gama ai sai mutuwa. Ƙara tsurewa nayi sosai. Salalab_salalab na wuce su, na nufi ƙofar da zata sadani da ɓarayin Alh. Ina shiga cikin ɓarayin, naga hasken wutar mota, sai hon ake dannawa da ƙarfi, a jajjere kuma. Ni kuma ina jinjine ina kallon ikon Allah, Ƙaramar ƙofar shigowa cikin gidan aka buɗe da Alh mu ka haɗa idanu, yana huci yace. "Dan bura'ubanci kina jin ina hon, uban wa kike tunanin zai buɗe mun get in ba ke ba, bauta kika zo yi gidannan, dolenki kuma kiyi bautarnan, dan igiyarki tana hannuna." Kai na gyaɗa kawai, ƙafafuna na rawa na isa bakin get na buɗe mishi ya shigo da gudu. Mayar da get ɗin nayi na rufe, na nufoshi, fitowarshi daga cikin motar kenan, idanu na ƙura mishi ina mamakinshi, shima ni yake kallo bakinshi a yashe, har yana wani lashe leɓe. "Amarsu ta ango, farar mace alkyabbar mata" Ni dai na kasa cewa komai, a baya na bishi zungui_ zungui, har zuwa sama. Muka shiga wani haɗadɗen falo a sama wanda ya take na ƙasa. Ƙasan kafet ya nuna mun da hannunshi. "Zauna a nan ki kijira ni ina fitowa ko?" Har ya juya nace. Abincin ka fa?" Wata dariya yayi, wacce ta ƙara mishi muni yace. "Ai kece abincina a cikin wannan daren, yau zan fanshe wahalar da kika dinga bani. Hidimar yarana kuma zata fanshe dukiyar da kike tunanin bani da hankaline shi yasa na dinga ɓarnatar miki. Yaro _ yaro ne ko da ɗan giwa ne." Da wata mahaukaciyar dariya ya kece, ya shige wani ɗaki ya barni da sakakken baki da hanci. Kaduna: Mama tana zaune a tsakiyar su Mama Rakiya, da Nafisa, suna mayar mata da yadda akayi" "Aini Yaya Jummai da ganin abubbuwan da suka faru ko, wallahi ba lafiya ba. Bawan Allahnnan fa, jirgin Lagos kaɗai ya sako mu aka kawo mu. Da ba dan Mabaruka, da yarannan namu ba, in dan ni da Safiya ne, wallahi da sai dai muyi bara a ƙarƙashin gadar Lagos, har zuwa lokacin da zamu haɗa kuɗin motar da zai dawo damu Kaduna. Yaya Jummai tunda muka ci abincin tarar baƙi, bamu sake sa dai _ dai da ruwa a bakinmu ba a cikin gidannan. Nafisa tace. "Aini Mama tunda aka kawo bushashshiyar jollof ɗin, jikina ya mutu. Domun a yanda Alh yake da mashahurin kuɗi, bai dace ace ma abincin gida zamu ci bana hotel ba. Ki duba fa lokacin da Asiya ta haihu, ba hotel babba Alh ya kama akayi hidimar suna a ciki ba, duk abinda muke so muyi oda kai tsaye daga Kitchen ɗin hotel ɗin. Wallahi na zaci hakan Alh Liti zaiyi mana. Nifa jikina yana bani akwai matsala babba gaskiya." Asiya wacce tayi tagumi tayi jigum tace. "Matsala kam akwaita. Kuma wallahi ko da na tambayi Alh akan me ya sani game da Abokinshi. Ni fa Mama ce mun yayi bai san komai a game dashi ba, yasan dai mashahurin ɗan kasuwane, kuma yana da kuɗin daya ninka nashi, harkar kasuwancin zuwa ƙasashene ya haɗasu har suka zama abokai. Amman baisan kowa nashi da komai nashi ba. Ni sai naji duk jikina yayi sanyi gaskiya." Mama duk tabi ta ruɗe sosai, ta rasa ta cewa, dan tana tsananin son Zubaina, dan ita bataƙi duk abinda ta samu ta kashe akanta ba, ita kuma zuchiya tana son mai kyautata mata ne. "Ku kira mun layin Zubainan dai ko Allah zai sa ta ɗauka, muji tana dai lafiya ko?" "To ai Yaya Jummai tun a Lagos muke kiran wayarta ba'a ɗagawa, har shi mijin mun kira bai ɗauka ba. Abunda ya sake kashe mana jiki kenan" Mama tace. "Rakiya ku sake kiranta, hankalina bazai kwanta ba, in banji daga Zubaina ba. Ni na shiga uku, karfa son zuchiya ya kaimu tsakar rana. Ni na ɗauka mijin Asiya yasan komai a kanshi. Shi yasa ko da Tanko yayi magana, nace mishi daga ɓangarenmu munyi duk wani bincike" Sun ta kiran wayar Zubaina data mijinta shiru kake ji malam yaci shirwa. Gabaki ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, an rasa me bacci, gashi ba gari ɗaya ba, balle gobe ai musu dirar mikiya sassafe. Yahanasu: Bulamana na juyo na kalla, sai sauke numfashi yake yi, hankalinshi a kwance, amman ni bacci ya ƙauracema idanuna, ga wani irin nauyi da nake ji a kaina tamkar kan nawa zai fashe. Nayi alƙawari a wannan cikin, bazan sha komai daya danganci kayan maye ba, ko dan ganin na samu haihuwa nima, ina nadamar wanda nasha a baya, kuma ina roƙon Allah ya yaye mun wannan bala'in. Kuma babban abunda Bulamana yake so bai wuce ƴaƴa ba. Ko ba komai nima inga jinina, iyayena ma kullum a damuwar rashin haihuwata suke, dan har Ya Innana ta ce in nazo bikin Wakil, zata kaini wajan wani mai magani, in soma shan maganin hausa, ko Allah zai sa a dace. Ga kaina yana barazanar fashewa. A daddafe na miƙe tsaye, nayi alwala a cikin bahun, dan dare ne sosai tsoro bazai barni fita ba. Sallar nafila na tayar, amman wallahi abun gagara yayi, inyi karatun sallah na kasa, sai wani irin ƙara da hauragiya nake ji a kaina da kunnuwana. Zama nayi daɓas, nayi shiru ina tunanin yanda na lalata rayuwata a banza da wofi, har ta kai ta kawo bana iya gudanar da komai, har sai nasha abubbuwan maye. Gashi sallah na kasa karanta ko wacce sura, ni da nake da sittin a kaina. jin kaina nake tamkar ban haddace ko alif ba. Qur'ani na jawo na buɗe, rubutun kawai nake bi da kallo, na kasa haɗa baƙin in karanta, sakamakon ciwon kai da ruwa da idanuna ke fitarwa. A wajan na kife na saki kuka mai gunjin gaske, wanda yai sanadiyyar farkawar Bulamana. Da sauri ya iso inda nake, ya sa hannu ya ɗagoni, na faɗa jikinshi kukan nawa ya sake tsananta. Sai kalmar la'ilaha illallah nake ambato, ina haɗawa da lahaula wala ƙuuwati illabillah, astagarufullah astagarufullah astagarufullah. Ina yi ina kuka muryata na rawa. Bulamana duk yabi ya kiɗime, yana tambayata menene damuwata, ko cikin ya zube ne. "Haba Yahanasu, me yasa kike haka, dan cikin ki ya zube shikenan sai ki ta rusa kuka tsakar dare, ƙarfe biyun dare ne fa yanzu. Ki jini da kyau, Allah yana sane dake, kuma ai ya baki bai zauna bane. Kinsan adadin matan da suke son ko ɓarin ne ace sunyi, dan a dena kiransu da juya kuwa? Ke ki godema Allah da yake baki ya amshe. Ni baki ga canji daga wajena ba, kinsan kuma ai baza ki gani a wajan iyayenmu ba, dan haka ki share hawayenki, kizo muje ki kwanta" Miƙar dani tsaye yayi, ina jikinshi muka isa kan katifar, ya kwantar dani, shi kuma ya zauna yana mammatsa mun jikina a hankali. Rufe idanuna nayi kamar mai bacci. A ƙasan zuchiyata kuma tausayin kaina, da tausayin Bulamana ne fal cikina. Ina tausayin kaina a ranar da asirina zai tonu, ƙila hakan yai sale salin ruguza dukkan farin cikin gidana, dama farin cikin dangina. Kab gidanmu babu ɗan shaye_shaye sai gashi an same ni, ina mace, macen aure da shan miyagun ƙwayoyi har yayi sale salin zubewar ciki a jikina har sau huɗu. Nayi ma kaina alƙawarin na dena shan komai, ko dan lafiyata, da lafiyar yaran da zan haifa. Bugu da ƙari ina cikin saɓon Ubangiji, nabi ruɗin zuchiya, idanuna ya rufe ni nitsuwa kawai nake son samoma kaina tsiya tsiya. Na mance dukkan nutsuwa yana ga karatun Qur'ani mai girma, sallah, da tasbihu sune kaɗai ke yayema mutum damuwa, su maye ma da farin ciki. Gani da haddar izifi sittin cib a kaina, musabaƙa naci ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Amman nayi fatali da sanina, na nema ma zuchiyata salama ta hanyar shan miyagun ƙwayoyi, gashi sun kaini sun baro. Ya iyahil alamin, Allah na tuba." Kwanciya bulamana yayi a hankali a gefe na, a tunaninshi na samu baccine. Buɗe idanuna nayi, hawaye sai cika su suke yi tab, suna sulalewa ta gefe da gefen idanun nawa. Bacci kuwa babu dalilin wanzuwarshi" Ghana: Ni dai a zaune a inda Alh ya barni, bansan mintuna nawa na share ba. Har ya shigo ban san ya shigo ba, sai da na jiyo amon shegiyar muryarshi, da lalatacciyar hausarshi ta mutan Ghana a kaina yana faɗin. "Ke ko tunanin me kike yi a rana irin ta yau? Kin mance da tarin alƙawarurrukan da kikai mun a wannan darenne? Ni ko fes suna ƙwaƙwalwata tun daga ranar da kika furtasu kawo i yanzu. Yanzu dai zo mu shige daga ciki ko?" Kallonshi nayi, daga shi sai gajeren wando, da singlet, tumbinnan nashi yayi wani uban tsoro, gashi da nonuwa kasancewarshi mai ƙiba. Ni dai a kiɗime na bi bayanshi muka shiga ɗakin baccinshi. Ɗakin baccin ya haɗu, ga gadonshi babba 6 by 7 katon gaske, yasha lallausan farin zanin gado, sai ƙamshi ɗakin yake fitarwa. "Zauna a kan gadon mana, ai ranarki ce yau, a gadonnan zamu ci uwar sabada" Idanu na zare, na zama kurma dai. Wutar ɗakin ya kashe duhu ya gauraye ko'ina a ɗakin. Muryarshi na jiyo yana cewa. "Ki cire komai na jikinki ki hayo mana, naga kina ta yin wani abu kamar wacce aka zare ma laka a jiki ne" Ƙululu cikina ya ba da ƙara, kuka na sakar mishi mai gunji. Wutar ɗakin ya kunna muka haɗa idanu, babu komai a jikinshi, miƙewa nayi da sauri zan gudu, hannuna ya riƙo ya yarɓani a kan gadon ji kake yib ya bugani a katifa ya kashe wutar ɗakin. Gauramun mari yayi, yana huci. "Baki da hankaline dan ubanki, ni zaki haramta ma kanki, duk maƙudan kuɗin dana kashe a kanki, zaki tuɓe ki kwanta ne, ko sai na banƙare miki ƙafa kamar yadda ake banƙare kazar gidan gona?" Jikina na rawa na shiga kiciniyar cire kayan jikina, tsoron Alh take ya ɗarsu a zuchiyata, dan daga marin daya wankeni dashi, nasan in nayi wasa zansha jibga a darennan. Jikina na rawa na haye gadon kusa dashi, ina runtse idanuna. Mirginowa Alh Liti yayi, kawai ya danneni, banyi auneba naji yana neman hanya, ba tare da ya taɓa komai na jikina ba, sai kace wata jaka ya hauni. Da sauri nace. Dan girman Allah, Alh kayi wasa dani, kar ka afkamun haka kamar jaka." Idanu na runtse tsabar tsoronshi, gashi Mabaruka tasa naje asibiti an ɗinkeni. A wannan daren Alh ya majigani sosai, ko tunkuza bata kaini shan matsa ba, nasha azaba sosai. Shirim Alh ya sauka a kaina, yana mayar da numfashinshi. Ni kuma ina kwance ina kuka mai ƙarfin sauti, dan wallahi ko kasheni zaiyi yau ni sai ya sake ni a darennan. "Ke wannan wanne irin bura'ubanci ne haka, zaki tusani gaba kinai mun kuka kamar wacce akai ma fyaɗe. Ko so kike dole ki sani in koyi iskanci ƙarfi da yaji. Shikenan kinaso in sha miki nono, in shafa miki mazaunai sai kace wani ɗan bakiri, ko ƙaramin yaro, ko an ce miki ni ɗan iska ne? To ni ban taɓa yin hakan ba akan ki kuma bazan yi ba, kija bakin ki ki mun shiru ni dallah" Dan Allah Alh ka rufa mun asiri, ka sake ni in koma ƙasarmu. Wallahi bazan iya rayuwar aure dakai ba, na roƙe ka da Allah ka sake ni" shiru naji yayi, ina juyowa naga baccinshi ma yake yi ashe, sai gwarti yake sha. Ihu nayi tare da bubbuga gadon, dole ya buɗe idanunshi ya kalleni. A zabure ya tashi yana ƙoƙarin wawuroni, banci nasarar guduwa ba, dan zafin nama ne dashi. Danneni yayi ya sakarmun nauyinshi yace. "Kin ɗauka ni irin ɗan iskan mijinki na baya ne ko, ƙila kin saba yi mishi rashin daraja yana ƙyaleki ko? In na kuma jin muryarki saina baki mamaki a cikin darennan, kinsan koni waye ma kuwa? Oh son duniya ya rufe miki idanu ke da kilakin uwarki, shi yasa kuka kasa bincike a kaina. Gidannan kuma kin shigoshi kenan, babu saki, babu yaji." Da ƙyar nake numfashi sabida nauyi ya sakar mun, sai da yaga fuskata ta dawo jazur sannan ya rabu dani. Ya mirgina ya kwanta, ko minti biyu baiyi da kwanciyar ba yayi baccinshi hankalin shi a kwance, sai gwarti yake sakarwa. Ni kuwa ina kwance ko ƙwaƙƙaran motsi tsoron yi nake yi, dan gudun kar Alh ya farka, bansan irin buyagin da zai tare ni dashi ba. Tun ina hawaye a wannan dare, har hawayen nawa ya ƙare, kaina ya ɗau caji, tashin hankali ya ziyarceni, mafita kawai nake nema koma wacce iri ce in dai zata fitar dani a wannan ƙaddarennen gidan. Idanuna biyu aka yi kiran sallar asuba. Lumshe kumburarrun idanuna nayi, na sakko daga kan gadon, jikina yayi mugun tsamin gaske. Ban ɗakin dake manne a cikin ɗakin na shiga, na tari ruwan zafi a bokiti na gargasa jikina, ina jin wani jirin yunwa, da zazzaɓi a jikina. Na gargasa jikina sosai, sannan nayi wankan sallah na fito. A ƙasa na tsince kayana na mayar jikina. Na soma sallah kenan Alh ya sakko daga kan gadon. Dariya naji yayi. Ko ta meye ohon mishi. Ina zaune a inda nayi sallar ya fito ɗaure da tawul, a gurguje ya zura jallabiyarshi ya fice. Fitarshi ke da wuya na ji wayarshi ta shiga kuka, ko in kula ina zaune ƙwalam, da naji kiran yayi yawa ne dai na miƙe na isa bakin gadon. Jummai naga an rubuta, dana kalla da kyau sai naga kamar number Mama. Baki na riƙe dana tabbatar numbern ne. Da sauri na kara wayar a kunnena, kafin tace wani abun na ɓalle mata da gigitaccen kuka, duk na tashi hankulansu, dan ina jiyo Asiya tana cewa. "Kinga ni ba, ai ni nasan ba Lafiya jikina ya bani" Inyi Magana ma na kasa cewa komai. "Zubaina akwai matsala ko? Ki buɗe baki kiyi mun magana ko zan samu sassauci, dan jiya ko runtsawa banyi ba. Cewar Mama, cikin shessheƙar kuka nace da Mama. Alh Liti azzalumine macuci maha'inci ya yaudareni. Gidanshi yafi kurkuku muni da wahala. Mama ki tawo ki tafi dani dan Allah, dan Allah Mama kizo, dan in kika wuce kwana biyu baki zo ba, wallahi zan kashe kaina kowa ya huta" Motsin shigowarshi ne yasa na zabura naja baya, tare da datse kiran Mama. Tinƙis tinƙis ya iso gare ni, yana wani zazzare mun idanu. "Na lura kina da taurin kai ko? Ko da yake Rumaisa'u tayi hauka a cikin gidannan na sama da kwana biyu, babu wanda bata kutuntumama ashariya ba, amman daga baya ai kinji roƙo take yi ma in barta ta kula da ɗiyoyinta, kar su zama ƴan tsakar gida kamar sauran. Ni kuma baiwar da Allah yai mun, sau ɗaya nake kwanciya da mace ta samu ciki. Zubaina inaso ki kiyayi shiga gonata, ki kiyayeni bani da daɗi" Tsugunnawa nayi ƙasa, akan guiwowina ina roƙonshi ya sauwaƙe mun aurenshi. Dariya yayi mun yace. "Ki shirya ki caɓa ado, yau lahadi rana ce ta musamman da nake ganawa da kab mata da yaran gidana, in gansu su ganni, waɗanda suke da ƙorafi duk yau suna da dama. Ki shirya ki same ni a falon ƙasa an kawo abun kari." Wayarshi ya karɓa a hannuna, ya harareni kafin ya fice. Ina hawaye na biyo bayanshi har zuwa falon ƙasa. Inason in duba kayana yana can ɗakin" Na nuna mishi ɗakin da hannuna" "Ki shiga ki sake kaya, kayan akwatunan kuma kar ki taɓa su, ki barsu a ɗakin. Kayan da kika tawo dasu daga gidan iyayenki, sun isheki kiyi amfani dasu, danni ba almubazzari bane. Akwatunan kuma na kaima ƙanwarki da zan auro ba da jimawa ba, domun kayan akwatunannan da kike ganinsu na cizo ne, waɗan da kika ɗinga Allah ya ci dake, sauran kuma a cikin ɗakin zaki barsu, dama daga ɗakin aka fitar dasu. Tunda na shigo gidannan nake ganin abubbuwan almara iri daban_ daban. Inason yi mai tambaya, amman bata da amfani, ni da ba zama nazo yi ba ma. Shigewa nayi ɗakin, hawayen idanuna da halama sun ƙare tas, doguwar rigar leshi na saka, na shafa mai na na MAKARI, na fito falon. Da idanu ya bini, yana lasar bakinshi, ni kuma na sake haɗe raina tamau. Kujera na nufa zan zauna ya dakatar dani. "Baki da tarbiyya ne, ina kujera zaki zauna a kujera, in ubanki ne a zaune a kujera ai bazaki zauna a kujerar ba. Bake ba ko wacce matata a ƙasa take zama in ina gabanta. Na lura dake tun jiya kamar baki horu da tarbiyya ba, amman zaki samu tarbiyya a nan gidan." Ji nake kamar in kutuntuma mishi ashar, in yi fashe _ fashe a falon, ko in mutu ko in yi rai. Dannewa nayi, na zauna a ƙasa. "Ga abun karyawarki nan, ki karya kafin iyalan gidan su zo" Muguwar yunwa nake ji dama, kofin silvern daya nuna mini na jawo, na buɗe wani ruwan kokko na gani tsararo a ciki, sai ƙuli ƙuli mai suger, irin masu faɗinnan guda uku, da mazar ƙwaila rabin_ rabi, wato kwata. Ɗagowa nayi na kalleshi, yanda yake shan kunun yana kallon labarai. In ya gutsiri kuli kulin, da mazau ƙwailar sai ya guntsi kunun. Kasa yin hakan nayi, iya kar ruwan kokkon nasha kawai na rufe. Kallona yayi yace. "Bakya cin ƙuli ƙuli ne?" Kamar in zageshi haka nake ji, da ƙyar na daure nace. Ina ci" Kai ya gyaɗa yace mun. "Kinga dukka matan jikin hotunannan? Matanane dana auresu, dukkansu munyi rayuwar aure dasu, wasu sun haifamun ƴaƴa, wasu kuma ɗaya suka haifa. Biyu daga cikinsu ne Allah yayi musu rasuwa, a wajan haihuwa, suka mutu tare da abinda ke cikin nasu." Kallon hotunan na shiga yi, ina ƙirga yawansu a zuchiyata. Mata rai goma sha shida na ƙirga cib harda nawa hoton da aka kafe a kusa da wata kyakkyawar matashiyar bafulatana mai ƙuruciya. Kafin in fita daga mamakin lamarin Alh Liti, su Hajiya Kubra su ka yo sallama, su uku suka shigo. Da idanuwa na bisu, yanda naga sun durƙusa suna kwasar gaisuwa a wajan Alh, sai kace wani adalin sarki. Ya ɗauke kanshi shi kuwa gogan kallo wannan basu isheshi ba, amman ya tambayesu ya yaran suke, sannan a cikinsu wacece bata da lafiya" "Nice Alh bani da Lafiya, juna biyu gare ni, sai dai yazo mun da ciwon mara sosai, kwana biyu kenan bana runtsawa" Sai lokacin ya juyo ya dubeta, baice da'ita komai ba. Dawo da kallonshi yayi gareni yace. "Waɗannan sune abokan zamanki Zubaina, Kubra, Nabila, Zakiya, sai ke cikwaton ta huɗun. MRS BUKHARI[09/08, 11:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 33 Da idanu na bi matan Alh Liti gasu nan a zaune su su uku. Al'amarin gidan Alh Liti da shi kanshi mai gayyar ƙoƙarin tarwatsa mun zuchiya yake yi. Dukan yayi mun yawa tako ta ina. Wato gadar zare Alh Liti yai mun, ni kuma kwaɗayin abun hannunshi yasa na zurma wannan gadar, gashi gadar na shirin halakar dani. Amman nasan da zaran Mama tazo ƙasarnan ƙafarta_ ƙafata, in ma bata zo ba a cikin kwana biyu, to tabbas zan shiga duniya, da in zauna wahala da takaicin gidan Alh Liti ya hallaka mun rayuwata, ya sukurkuta ƙuruciyata, na gwammaci in fantsama duniya a neme ni a rasa. Alh Liti ya ce. "Kubra ina yaran suke to?" "Suna waje suna jiran ai musu iso. Sai dai mummunan abu ya faru da Rashida, mijinta ya sake ta yai mata korar kare, har da yaran ya hadota suka tawo. Bari dai in musu iso su shigo waƙa a bakin mai ita yafi daɗi" Murmushi Alh kiti yayi yace. "Ai saki ba mummunan abu bane masalahane akan duk namijin da yayi saki, dama ita macen da aka saka. Yaranne dai ubanshi yayi kaɗan in ciyar mishi dasu, ita kanta uwar yaran ina mai takaicin sanwarta da za'a ƙara." Ni dai ina raƙuɓe ina kallon ikon Allah, zazzaɓine kau a jikina, zafin zazzaɓin sai hawa kaina yake sake yi. Yara da matasa, maza da mata, ne su kaita tittiɗowa babban falon Alh Liti, sunfi rai talatin, harda magidanta, ga wasu yungu_yungu suma daga gaba gaba abun tausayi. Dukkansu babu mai kyan shiga, da gani rayuwa matsarsu take sosai, duk wanda ka gani a komaɗe. "Am da fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya ko?" Cewar Alh Liti. Nan suka shiga rige_ rigen gaisheshi, hayaniyar muryarsu duk ya cika falon na ɗan lokaci. Wasu ƴan mata ne su su biyar kansu ɗaya suka miƙe tsaye, da halama magana zasu yi. "Baba mu dai akan batun makaranta ne. Dan Allah Baba kar kayi mana aure mu karatu muke son muyi, ko dan mu taimaki kanmu da iyayen mu mata" Wacce ta wakilcesu take magana Alh Liti ya kafama idanuwanshi yana kallonta ƙur, har sai da ta dasa aya sannan ya numfasa yace. "Batun aure babu fashi, yanda ban ɗauki nauyin ko wanne yaro a cikin gidannan yayi karatu ba, haka kuma ba ku isa kunyi karatu ba. Aure babu fashi magana ɗaya nake yi. Nan da sati guda duk wacce maneminta bai fito ba, to zan aura mata wanda raina yake so. Masu jawabi na gaba" Wasu gungun maza ne riɗa _ riɗa su takwas suka miƙe, mutum guda ya wakilcesu, kamar yadda ƴan matannan su ka yi, shima ina tunanin wata doka ce, tunda ko kotu na lura bata kai gidan bin doka da oda ba. "Mu Baba aikin yi muka rasa, ɗan dakon kaya da muke yi a kasuwar Nima kuma, jama'a sun sa ido da yawa, surutai tako ta ina tashi suke yi a cikin kasuwar. Baba shagunanka sunfi goma a kasuwarnan, banda store_store ka taimaka ko yaran shagunanka ka mayar damu, wallahi daga mu har iyalanmu, da sauran ƙannenmu maza muna cutuwa, ya kamata ka taimaka ka dubemu da idanun rahama ka samar mana da abun yi. Ka tsundumamu a harkar kasuwancinka, mu kula da harkokin tunda dukiyar dan mu kake tarawa. Azabar dake cikin gidannan tayi yawa. Duk gari sai zancan matsolancinka ake yi, wasu kuma sunce kuɗin lukudi kake dashi......." "Kace ubanka Sani, nace kaci gidanku. Wannan maganar sama da shekaru goma sha, duk sati sai kun zo mun da'ita gabana, nine zan ɗaura ku akan kasuwancina ku karyani, kunsan ma da yaya na tara dukiyar nan kuwa? Da kunsan irin yawon fataucin da nayi baza ku ɗauka zan rayu har in kai yanzu ba. Ku ma maza ne, ku fita ku nemo, ku shiga ƙasashen duniya ku samar ma kan ku mafita" Cikin ɗaga murya da buyagi yake maganar tamkar zai cinye wanda ya kira da Sanin. Wani daga bayan sanin yace. "Wai Baba kuma da gaske ne kai ka haifemu dan Allah? Ni naga muguntarka tayi yawa, baka jin tausayin kowa." A zabure ya miƙe ya nufi wanda yai maganar da nufin rufeshi da duka. A guje ya fice, Alh Liti ya rufa mishi baya shima a guje, ko nauyin cikinshi da jikinshi baya yi. Sani da yasan Alh ya fice a falon yace. "Ai gaskiya Dauda ya faɗa, mutum sai rashin mutunci, Allah ya ɗau ranka uban kowa ya huta. Mutum ya tara uwar dukiya, yaƙi ci ya hana kowa yaci, sai auro ƴan shila, daga tattaraba sai kanari" Cikin masifa Alh Liti ya shigo. "Ɗan nema, dana kamashi da yaji tsohon hannu. Sani ku fice mun a falo, kuma kar ku sake halartar wannan taron daga yau sai yau. Kamar yanda su Nasiru suka zuƙe jikinsu suka dena shigowa nan kuma haka nake so kuyi" Sani yace. "Baba kayi haƙuri dai, sannan su Yaya Nasiru da Yaya Rabo ba zuƙewa su ka yi ba. Basa ƙasar ne, sun shiga birkinafaso ci rani. Su kan dai yi ma iyalansu aike" "To kaji, kuma ku fantsama mana da zai fi muku, kun tsaya jiran dukiyar ubanku. Kai ka sani inajin duk surutan ku akan cewar in mutu ku huta. Wallahi duk mai jiran saina mutu zai yi arziki, to walaha da yunwa su zata riga halakawa" Ficewa su kayi suna ƙunƙunni, ragowar matasan da basu tashi sunyi nasu jawabin ba, suka mara musu baya, suna surutan banza. Ɗakin ya rage sai yaranshi mata, da kuma ƴan yungu _ yungun yaran gidan. "To Rashida tayi kiyi naku jawabin ina jinki, shegiya kulllum in kika zo taronnan a cikin kuka kike." Wacce ya kira da Rashida ta tashi tsaye tana sharar hawaye. "Baba mu kukanmu ɗaya ne ko da yaushe. Shine dan Allah ka rufa mana asiri ka dena wannan auri sakin da kake yi. Wallahi Baba ko ina a gari zaginmu akeyi harma da kai ɗin. Hatta mai gidana motsi kaɗan sai ya zagar mun kai, a dalilin haka ne ma ya sake ni, nima na gaji da cin zarafinka da yake yi... "Ya isa haka ƴar ƙundun uba kai. Ku tashi ku fice mun da gani. Babu uban da ya isa ya sani in dena auri saki, ko yau na samu wacce ta yi mun, saina saki wata cikin waɗannan na auro wata. Ai ni gidannan in kinga na dena aure da saki, to rayuwata ce ta zo ƙarshe, amman ko a gadon mutuwa nake zan iya saki in auro kuma. Tunda mata in dai kana da kuɗi ba cancanta suke nema ba" Suma haka ya kaɗasu suka fita, duk yawancinsu kuka suke yi. Ɗakin ya rage daga mu sai yungu_ yungun yaran gidan. "Kubra su kuma fa waɗannan?' "To su kuma duk basu da lafiya, wasu ƙurajene suka fiffito musu a jikunansu, jikinsu da zazzaɓi dukkansu." Kallonsu yayi yace. "Ke Hauwa, da Ummu Kulsum ku tawo inji jikin naku" Na yi matuƙar mamaki da naji ya ambaci sunan yarannan. Wallahi ko kusa banyi tunanin zai iya tantance sunayensu ba, naga yaran nashi yawa garesu kamar fari. Jikin yaran daya kira ya tattaɓa. Ya girgiza kai yace. "Kubra kenan, ke wato a kullum baki da hankali, haka kike tunda na sanki. To me kike son ayi ma yarannan dan Allah?" Hajiya Kubra ta yi Murmushi, yanzu ne na gane murmushin da take yawan yinshi meye ma'anarshi. Na baƙin ciki ne da tsantsaryar takaici, gami da dana sani maras amfani. "Na ɗauka za'a kaisu asibiti, tunda abun yazo da ƙurairaji. Kuma Alh ko bacci ma yaran basa iya yi. Kwana biyunnan Zakiya ke kwanciya dasu a ɗakinsu. Yarannan ka tausaya musu, su yarane sosai, gashi babu iyayensu a gidan balle su su tallafesu" "Uwar zaƙin baki kenan Kubra. Magana kamar wacce ake rubuta mata ta haddace. To kiji da kyau, ni in ba magashiyan naga yaro rai a hannun Allah ba, bafa za'a sani asarar dukiya ba. Ku basu sabara su sha, zan shigo da ganyen gwanda a dafa musu. Ƙurajen jikinsu kuma a shafa musu toka zasu baje" Ɗayar daga cikin matan Alh mai goyannan tace. "Haba Alh ka ji tausayin yarannan mana. Duk wani jiƙo wallahi an basu, amman da zazzaɓin suke kwana fa. Ya kamata a kaisu asibiti a duba lafiyarsu" "To in kuna da kuɗi ni ban hana ku kaisu asibiti ba , ai kuma yaranku ne. Amman ni da kuka ga na rayu har zuwa kawo yanzu, babu wata ƙwayar bature dana taɓa haɗiya. Ni a ƙauyenmu ma babu asibitin, da magungunan gargajiya na rayu. Kuna maganar ƙuraje, mu da mu ka yi ƙazzuwa, da sosa gaye tun kafin asan ma zaku zo wata duniya" Shiru kowa yayi a falon. Ni kuwa lamarin Alh Liti ya dena bani mamaki ma, dan na fahimci baduniye ne shi sosai, asalin tantiran ƴan ƙauyannane jahilan da basu san komai ba, Allah dai ya azurtashi ne, ya samu dama shi kuma yake ɓarar da mata makwaɗaita irinmu. A haka dai wannan taro ya watse, suka fita suka barmu a zaune daga ni sai shi. Miƙewa tsaye nayi nace. Zan iya ɗaukar wayata in ci gaba da amfani da ita?" Dariya yayi ya kalleni yace. "Kofur Zubaina kenan, har bakin tsiwar taki ta mutu ne haka, naji muryar tayi sanyi gwanin daɗi" Murmushi nayi mishi kawai na wuce ɗakin daya sauke mu da muka zo. Na tattare kayan sawana, na bar mishi akwatunanshi nan. A hanyar fita falon muka haɗu. "Ni zan fita Nima market, sai takwas zan dawo. Da daddare zaki gyara falo da sama, yanzu ki samu ki huta ke amaryace." Bance dashi ci kan ka ba muka fito tare. Ni na buɗe mishi get ya fice ya barni a tsaye ina cizon yatsana. Barayin matan gidan na shiga, jama'ar gidan sai hada hadar aikace_ aikace suke yi, gidan kuwa ya haɗe yayi kace_ kace, ko ina ruwa. Haka na tsatstsallake na shiga ɗakina. Kwanukan abincin jiya aka turo wata ƴar lukutar yarinya ta fita dashi. Zama nayi a bakin gado, na saki kukan nadama da dana sani, wacce hausawa sukaima laƙabi da ƙeya. Wayata ce ta shiga ruri da sauri na rarumeta na kara a kunne na. Kuka nake yi a hankali. "Ya'isheki haka kukan mana Zubaina. Ke kan ki kinsan in dai ina numfashi bazan bari ki wulaƙanta ba. Jibi zanzo, yau zanje wajan malam ya haɗo mun wasu magungunan mallaka masu zafin gaske, zan tawo miki dasu, ki kwantar da hankalinki, dukiyarshi wallahi sai fa munci" Da sauri na katseta da cewa. A'a Mama, karma ki wahalar da kan ki akan wani zuwa wajan boka. Wallahi Allah bazan zauna a wannan gidan ba. Sannan wanne irin maganin mallakane banyi amfani dashi ba? Bokan daya raba Bulama da iyayenshi, ya haɗa Mabaruka da mijinta na yanzu shi yayi aikin fa. Kuma yanka wuƙane, ni gani nake Alh Liti ba'a zaune yake ba, yana biye_ biyen muggan malamai. Ni dai kixo ki tafi dani kawai, kuɗinshi ba masu cuyuwa bane kuɗin cizo ne dashi. Wallahi yaranshi ma taimako suke buƙata, abun a taimakesu ne. Mama asibiti wannan na fahimci sai Alh Liti yaga mutum na gargarar mutuwa yake bari a kaishi asibiti. Katseni Mama tayi da cewa. "Yanzu ba zaki bari mu sake jarabawa ba, ko Allah zai sa mu yi dace uhm? Ki duba fa bawan Allahn nan irin miliyoyin daya kashe a kanki, dan ya mallakeki kawai. Ni ina ganin in da zaki bi sannu _ sannu, cikin laluma da kissar mu ta mata, kamar zaki iya shawo kanshi ko? In kuma kina ganin inje in samu Mabaruka ta raka ni wajan bokan naku ai sai inje mu tafi tare. Ki daure mu jaraba, in yasan wata ai bai san wata ba. Ki bar mun komai a hannuna, ko tsirara zanyi yawo ni kuwa sai na samar miki da fada a wannan gidan, sai kin mulki kowa, mukullin taskarshi sai ta zama a tafin hannayenki. Maza kira Mabaruka kice mata gani nan zuwa gidan nata" Da waɗannan kalaman Mama ta shawo kaina, har na ɗanji nutsuwa ta faɗa mun. Kiran Mabaruka nayi a waya. "Ƙawata ta kaina. Yanzu nake shirin kiranki ai, amman sai nace bana kira Amarya da safe ba." Tsaki naja nace. Wacce Amarya kuma? Hmmm Mabaruka ai ina cikin tashin hankali mai girman gaske. Alh Liti fa kallon kitse ashe nai ma rogo. Mai kuɗin lukudine, kab ƙasar Ghana kowa yasan hakan, gashi da auri saki. Mabaruka matsalolin Alh Liti sunfi ƙarfin in tsaya faɗa miki duka, sai dai in tsakura miki kaɗan." Labarin kaɗan daga cikin hali da gidan Alh Liti ya kasance na bata. "Ni ai tun daka kan abincin da aka tare mu dashi. Wallahi na san akwai matsala gagaruma. Amman kinyi amfani da waɗannan layun da boka yace ki saka a ƙarƙashin gadon baccinku, da pillow?" Kai na dafe nace . Na sha'afa shab tsabaragen tashin hankalin da nake ciki. Sannan Alh Liti turaka yake dashi, a ɗakina zan sa ko a ɗakin nashi?" Mabaruka tace. "A ƙarƙashin gadon da kuke hawa kuyi kwanciyar aure zaki saka, da pillown da yake ta da kanshi. Ki kula sosai, wannan maganin da kinyi amfani dashi tun jiya ai da kakarki ta yanke saƙa." Ajjiyar zuchiya na sauke wani daɗi ya ratsa zuchiyata. Mabaruka ai wallahi na mance shab da wannan layu, zan yi duk ƙoƙarina inga na aiwatar da wannan aikin. Ni da harfa nace mama tazo ta tawo dani ni bazan iya da wannan ƙaddararren auren ba. Da har tace zata zo gidanki ki rakata gidan boka fa. Bari in kirata in sanar da'ita tayi zamanta, ba sai ta zo Ghana ba, kuma ba sai ta je gidanki ba." "Gaskiya kam, kema dai Zubaina kin mance da aikin boka ne. Ya taɓa yi miki aiki bai ci bane?" Mabaruka ke bazaki gane irin halin dana shiga tsakanin jiya zuwa yau ba. Wai ke kinga yanda Alh ya hayeni kamar wata doki, ya shiga sukuwa kuwa? Ga matsaloli masu tayar da hankali, yaranshi da matanshi duk a yamutse, ga wani abinci da suke ci kamar a firzin" Mun dade muna tattauna maganganu da Mabaruka, daga baya muka yi sallama. Na kira Mama na sanar mata abunda ke tafiya, itama taji daɗi sosai. Jigum nayi a zaune ina karanta wasiƙar jaki. Anya kuwa wannan hanyar zata ɓulle dani kuwa, matan Alh kab da ya dinga aura yana saki, su basu san hanyar gidan boka bane, ko su ba sa son dukiyar tashi ne? Tsorona kar in je garin neman wajan zama a gidan Alh Liti, inje ta zaune mun, sai dai inji kiɗa a magwan. Na ɗau lokaci mai tsawo ina aikin tubka da warwara. Zakiya ce ta yi sallama a ƙofar ɗakina ta ɗaga labule. "Amarya ki fito mu yi wanke_ wanke" Dubanta nayi na kuma, ina nanata kalmar a zuchiyata. Wanke_ wanke, wanke_wanke ina Amarya? Ni da nayi tunanin ƴan aikin ɓarayina zasu fi uku ma, kowa da aikinshi, sai gashi daga yin kwana ɗaya ana jirana in soma bautar bataliyar yaran kishiyoyi. Miƙewa nayi na fito. Wanke_wanken da na hanga himili guda a tsube, shi ya kashe mun jiki. Kut wai ni ce zanyi dukka wannan uban wanke _wanken, sai kace wata jakar da aka cire kuɗi aka siyo?" A cikin zuchiyata nake maganar, Zakiya ta nuna mun kujera, da ruwan ɗauraya, da kwandunan kife wanke wanken, naga ta shiga aikin iza wuta. Hajiya Kubra tana zaune a ƙofar ɗakinta tana yin sukola. Motsi wannan na kasa yi, sai kallon tarin wanke_wanken dake jirana nake yi" "Umma zamu tafi, ki bamu kuɗin makaranta" Cewar ƴan matasan da suka fito daga ɗakin dake kusa da kitchen ɗin gidan. Kayan islamiyya ne a jikinsu, kayan duk sun jeme,sun dafe. "Toh Rauda, kuje ɗin kuce da malamin naku za'a haɗa mishi dana wancan watan a biya." Wacce aka kira da Rauda tace. "Yace in babu kuɗin kar ma muzo wallahi, ni na haƙura ma da karatun duka, kullum a cikin shan wahala kike Umma, Baba yana da dukiyar da zai iya biyan kuɗin makarantar yara sama da dubu, amman mu yaranshi ko islamiyya yaƙi samu" Wucewa tayi cikin ɗakin data fito tana kuka. Ɗayar budurwar dake saye da kayan makarantar tace. "Ni na gaji wallahi da rayuwar gidannan, kullum cikin talauci. Ni zan nemi ƴar uwata Jamila in koma nima zaman kaina kawai in huta, ni wallahi bazan zauna ba." Wucewa tayi tana bubbuga ƙafafunta. Duk wannan abin dake faruwa ina tsaye a gaban kwanukan wanke_wankennan ne" "Hajiya yarannan su fito da miji kawai a aurar dasu muma mu huta. Kina jin abunda Kaula take cewa fa. Zata je ta zauna da Jamila, itama tayi zaman kanta. Wannan masifa da bala'i dame yayi kama. Mun jefa rayuwar ƴaƴanmu, da tamu rayuwar a cikin wata iriyar rayuwa, duk a sakamakon son abun duniya. Ina soyayyata da Jabir kamar mu haɗiye junanmu, lokaci ɗaya Alh ya shigo rayuwata ya yaudare ni, ya yaudari magabata na. Mu kai fatali da maganar Auren Jabir, saurayin daya shafe shekaru goma yana mun hidima, kaico na. Ya Allah ka kawo mun ƙarshen zaman gidannan, ya Allah ka kare mun yarana, Allah na tuba." Hawayene suka ciccika guraben idanuna, na tsaya ƙyam a tsaye ina kallon Zakiya. Hajiya Kubra tace. "Hmmm ina jiye ma Alh ƙarshenshi, domun ƙarshenshi bazai yi kyau ba. Ya cutar da mata da yawa, ya haifo yara birjik ya kasa ɗaukar nauyin komai nasu, mu ya barmu da wahalar renon mishi yaranshi. Allah zai saka mana. Kuma mu ɗauka auren Alh da rayuwa tare dashi yana daga cikin jarabawar rayuwarmu. Muyi ƙoƙarin cin jarabawar kawai. Rashida gata a zaune, zamanin da suke ƴan matancinsu wanne irin lalacewa ne basu yi ba. Sune hotel, sune shagunan maza, suna ba da jikkunansu ana basu kuɗi, ko sutura, ko abinci mai kyau. Gabaki ɗaya sai da suka gama tambaɗewarsu kafin su kai aure gata. Duk kuma wa yaja in ba Alh ba? Duk da mu matan mu muka fi kowa laifi, bari inje in shawo kan yarannan" Harta miƙe Rashida tace. "Hajiya barshi, bari inje in same su. Su yi haƙuri komai tsawon zamani Baba dole ya mutu, abunda ya shuka shi zai je ya tarar, mu kuma bai isa ya hana a rabe mana kuɗin lukudin daya tara ba" Miƙewa tayi ta bi bayan su Rauda. Daɓas na zauna zaman ƴan bori akan kujerar tsugunno, domun ƙafafuwanane suka gaza ɗaukata. Ina zancan zuchi ina faman aikin wanke _wanke, hankalina baya ma cikin gidan baki ɗaya. Tuno gidana na Kaduna nayi, da irin tsantsar so, da kulawar da Bulama ya bani a rayuwarshi. Da irin martaba ɗangina da yake yi, da irin sarrafani da yake yi a gado, cike da tsantsar so, da nuna muradinshi a fili. Ohh ya ilahi. Na sake tuno lokacin da nake juyashi sai yanda nayi dashi, da raba shi da iyayenshi, da danginshi da nayi, babu abunda ban tunoshi a yau ɗinnan ba. Ban ankaraba har na gama wanke tulin kwanukannan tas, nasa hannu zan ɗauki kwano naji wayam, ina kallon gabana naga kwanukan sun ƙare, saura ƙatuwar tukunyar tuwo da miya. Kai na girgiza lallai na shafe awanni ina faman aikin tunani. Tashi nayi na dinga kankarar tukunyar tuwonnan, na tara ƙanzon a wani kwandon roba, sama sama na wanke tukwanen, na mammatsar da kwandunan gefe. "Ki bar sharar yara zasu su fito su yi. Rashida a ba yarannan maganinsu su sha" Cewar Hajiya Kubra kenan, bayan ta mun magana ne, ta juya kan Rashida. Alwala na ɗaura na shige ɗaki, a ledar tsakar ɗakin na yi zaman dirshen dan na gaji ainun, ga zazzaɓi sai sake lulluɓeni yake yi. Kafin la'asar har bana iya gane wanda yake kaina ma, tsabar azaba" MRS BUKHARI CE [09/08, 11:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 34 YAHANASU: Daren ba ƙaramin nisa yai mun ba, da ƙyar asuba tayi a wajena, ina kwance lamo, kaina kamar zai fashe tsabaragen ciwo, haka idanuwana in na buɗesu tamkar zasu faɗo ƙasa tsabaragen zafi da zugin da suke yi mun. "Yahanasu, ki daure ki tashi kiyi sallah, in yaso sai ki koma baccin, ki sanar a wajan aiki baki da lafiya" Da dabara na buɗe idanuna, muna haɗa ido da Bulamana ya sau mun Murmushi, take idanuna su kai ƙwalƙwal. Da taimakonshi na miƙe zaune, kaina na dafe a hannuna na fita a ɗakin. Da dabara nayo alwala na shigo ɗaki. Sallar ma a zaune nayi, ina idarwa na koma na kwanta, take na shiga rawar sanyi. Duk Bulamana ya rikice ya ruɗe, sai da ya lulluɓeni da bargo babba na samu sassauci, shi kuma ya samu zarafin shirya yara zuwa makaranta. A yanzu Bawa da su Anisa da kansu suke zuwa makaranta su dawo da kansu. Bayan sun tafine ya fitar da wanke_wanke da wankin kayanmu, kan kace me ya gama aikace _aikace, shine harda sharar ɗaki. "Tashi ki je kiyi wanka, in kika fito ga dumame nan ki daure kici. Ni bari inje in siyo miki magani" Nagode sosai da kulawarka a gare ni. Nace yau baka da jarabawa ne?" Murmushi yayi yace. "Akwai, saura pepa ɗaya ya rage mana, yau zamu kammalata, ƙarfe biyu zan fita. Kafinnan har abincin rana kinga na gama" Yusuf ya riƙe ma hannu suka fice, nima je bayan gida na watsa ruwa da zafi zafi na fito. "Umman Maryam jikinne har yanzu dai?" Cewar Maman Gaddafi kenan. Cikin muryar rashin lafiya nace. Wallahi kuwa, jikin yaƙi daɗi" Maman Hassan tace. "Bari in ɗan rarrage aiyukana, sai inzo in kama miki wani abun. Naga Baban Maryam ya yi muku wanki sassafe." Hakane kam. Amman ya gama aiyukan dukka ma, na gode Allah ya bar zumunci" Nan dai su kai ta mun sannu. A bakin ƙofar ɗakina naci karo da Hajara itama tazo yi mun ya jiki. Ahmad ma ya leƙo daga cikin ɗakin nasu yai mun ya jiki. Ina zaune ina ɗan cin abincin kaɗan kaɗan, bulamana suka dawo daga siyo magani. Harda kayan shayi ya siyo mun. A kofin roba ya haɗamin tea mai kauri ya miƙo mun. "Sha maza sai ki haɗiyi magungunan, ki samu ki rama baccin daren jiya ko? Banyi mishi musu ba na karɓi tea ɗinnan na dinga kurɓa, nasha fin rabin kofon, sannan ya bani magunguna na haɗiya tare da korawa a tean, ragowar kuma na ba Yusuf. Sai da na kwanta na kira ma'aikatarmu na sanar musu ina kwance a gida banda lafiya dan haka bazan samu damar zuwa ba. Abu wasa ne gaske ne, bacci fur yaƙi ɗaukata, har bulamana Ya shirya ya tafi makaranta bayan ya ɓararaka mana taliya. Hajata tayi tayi ya barshi zata ɗaura girki damu, amman fur yaƙi, kasancewar yasan fama suke yi, tunda a hakan mun fisu wadata tunda ni sa'ata ta karɓu ina ciniki sosai. Ita kuma bata daɗe da soma sana'ar siyar da kayan yara ba. Carbin malam, hanjin ligidi, alragis, soyayyar kwakwa da siga, kwakumeti, da dai sauran ƙwalam na yara, ta na ɗan fita dashi ta kai makatantar yara. A mugun galabaice na kai yamma, kaina kuwa ji nake kamar ana tsittsikara mun allura haka nake ji. A ranar Bulamana ya zo mun da kyakkyawan labari mai daɗin sauraro. Bayan ya shigo ya zauna, ya tambayi jikin nawa, sai ya ɗaura da cewa "Addu'ar da muka daɗe muna yi akan Allah ya bamu aiki. To kusan zan iya ce miki na samu koyarwa a Jami'ar Bayero, kinga a baya na je neman koyarwar a can ban samu ba, da yake ba lokacin rabon yake ba. Amman yanzu da rabon ya tsaga kinga ina dab da haɗa mastas ɗina koma in ce na haɗa tunda mun zana jarabawar ƙarshe sai jiran sakamako, na kuma samu koyarwar. Amman ba yanzu zan soma karantarwar ba,sai lokacin da za'a ɗebi sababbin ɗalibai, a lokacin zan soma koyarwar, wani abokin karatuna ne kamal yai ma mahaifinshi maganata, shine fa aka sama mun koyarwar, kinga ikon Allah ko? Komai na duniya yana da iyakarshi." Cikin murna da zumuɗi na miƙe zaune ina dariya nace. Wannan babban labarine sosai. Kai Alhamdulillah naji daɗi sosai Bulamana, Allah ubangiji ya taya ka riƙo, ka kula dan Allah da aikinnan naka. Ka sanar ma da Ahmad kuwa?" "Ahmad baya gida. Amman dama ke ya dace in soma sanarma,tunda su Ba Bakura basu da masaniyar na rasa aikina na gandiroba, da su zasu soma ji, sai ke. kinga da izinin Allah komai zai warware mana, zamu tashi a wannan gidan in kama mana me dama, da zaran na karɓi albashin farko. In sha Allah zan cika miki ɗakinki da kaya. Murmushi kawai nayi mishi, sai na ɗan ji ƙarfin jikina sakamakon wannan kyakkyawan labari mai ɗan karen daɗi. Amman zuwa bayan isha ba sai tashin hankali ya same ni ba, nice harda ihu ina bige_bige. Bulamana ina jinshi yana ta karatu yana tofa mun yana cewa. "Zaku fita da ƙafafuwanku, domun kuwa kun taɓo gidan rina, ashe ku kuka shafeta ko?" Sai adda'a yake yi yana tofa mun, kaina sai wani zungurata yake yi, jikina kamar ana sossoka mun allurai. ( Subuhanallah shaye_shayen miyagun ƙwayoyi masifa ne mai girma) A hankali naji abun ya na sassauta mun kaɗan kaɗan. Sai kuma na shiga kuka ina mai nadama da dana sanin soma shan miyagun kwayoyi a rayuwata sai nayi kamar in faɗa ma Bulamana halin da nake ciki amman sai tsoro ya hanani. " Ghana: Adda'a duk wacce tazo baki na cabkarta nake yi, kafin in kai ƙarshe ta dubce mun, domun asarar kuɗin tara akayi. Sai da aka kira sallar isha na daure na tashi da ƙyar na fita tsakar gidan. Wani irin abinci naga suna ci a cikin ɓawon masara abun yake kamar tuwo mulmulallu. Zakiya tace. "Zubaina yanzu nake shirin tura yara su kira ki kici abincin dare, kinga shinkafarki ta rana ma tana kitchen baki je kin ɗauka ba" Fuskata a kumbure nace mata. Bana jin daɗi ne, ko sallar magriba ban yi ba." Nan matan suka shiga yi mun sannu. Yayin da yaran kuma suka bini da idanunsu, Rashida ce kaɗai ta mun sannu. Har samarin gidan ba wanda na isa kallo. Kwata_kwata yaran gidan Alh Liti basu da tarbiyya, kasancewarsu yaran tsakar gida, kuma yaran ido iyayensu mata basa gidan balle su kwaɓesu. Mata_ matan kuma na lura haƙuri akeyi dasu kawai, dan da ƙyar suke aikuwa, aikima ba yi suke ba, in banda ɗebo ruwa da suke yi a gidan. Alwala na ɗaura na koma ciki na yi sallar magriba da isha. Ina idarwa na miƙe dan takwas saura, ina tsoron kar Alh Liti ya dawo bana wajan, dan nasan zan sha tujara." A gurguje nake tafiya har ina harɗewa domun ina jiyo hon ɗin motarshi yanda yake matsawa da mugun ƙarfi. Da ƙyar na buɗe mishi get ɗin ya shigo, yana faka motar ya fito ko rufewa bai yi ba. Cikin jaraba da ƙanƙance idanu yake nunoni da yatsa. "Wannan bura'ubancin ya isheki haka yarinya. Kar ki ga ina sassauta miki dan ke amarya ce, nan da kwana bakwai in akace miki kiyi hakan ma, sai kin gwammaci mutuwarki, ki kiyaye ni bazan ɗauki sakarci ba" Wani kududune ya tokare mun wuya na, bance komai ba nabi bayanshi, juyowa yayi ya kalleni yace. "Wa zai rufe miki motar, ni kike jira inje in rufe miki ko, in ubankine zaki bari ya rufe da kanshi ne?" Tsaki yayi ya shige ciki yana sababi. "Aikin banza aikin wofi yara sai rashin kunya, da rashin sanin darajar aure" Kai na girgiza kawai na je na tura ƙofar motar na bi bayanshi, ina cike da tsantsar zafin zagin ubana da yake yi. Ko da na shiga ɗakin baccin nashi har ya shiga wanka. Layar da boka ya bani na zaro a bireziyata, na jefa ɗaya ƙarƙashin gadon Alh Liti. Ɗayar kuma na ɗauki pillown da yake ta da kai dashi na zare rigar pillown, a ɗinke pillown yake, da baki na dinga cisgar daren ɗinkin har na samu bakinshi. Ɗan waje kaɗan na ɓarka na tura layar nan da sauri. Ina kan mayar da rigar pillown Alh Liti ya fito. Da kallo ya bini yana mun murmushi, take tsoro ya kama ni ina tunanin anya kuwa bai ganni ba. Wata zuchiyar tace mun, ko kuma asirin ya soma aiki ba. Ajjiyar zuchiya na sauke. "Ya naga baki sake kayan jikin ki ba, ko baki yi wanka bane? Kinsan fa kwalliyarki ba ƙaramin sukurkutani take yi ba. Yana yin magana yana kallon ƙwayar idanuna. A tausashe nace. Da zazzaɓi na wuni, ban sake wanka ba tun na safe, amman yanzu zanyi" Ina gama faɗar hakan na shige ban ɗakin Alh Liti ina murmushin muguntar yazo hannuna, zanyi tamaule dashi" Alh Liti: Zubaina na shigewa Bayi, ya saki murmushi tare da girgiza kanshi. Sai da yaji zubar ruwa halamar wankan ta soma, sannan ya miƙe ya isa bakin gadon. Da wayarshi ya haska ƙarƙashin gadon ya hangon layar bata ma shiga can ciki ba, hannunshi ya zura duka a ƙarƙashin gadon ya zaro layar. Kai ya kuma girgizawa kawai, ya jawo pillown ya cire layar data cusa. A cikin durowarshi ya adana layun, ya dawo ya zauna kamar ba shi ba. "Yaro baisan wuta ba sai ya taka. Turnuƙu faɗan ibilisai, yarinyarnan ni zata yi ma asiri a wautarta da ace ba da idanu ɗaya nake bacci ba da yanzu ba'a kassarani ba? Ai ko matan da na saka kaɗai sun isa su jefe ni. Zanyi maganinta, ni da ita babu saki, mutuwa ce kaɗai zata raba mu. Hatsabibiya kawai. Miƙewa yayi tare da nufar durowar gefen gadonshi, ya zaro wani magani a baƙar leda. Ya barbaɗa ɗan kaɗan a cikin nama, bayan ya raba naman gida biyu kenan, yasa hannu ya cakuɗa naman yana kwashewa da dariyar mugunta" ZUBAINA: Cikin walwala na fito, duk da zazzaɓine kau a jikina. Rigar baccin dana tawo da'ita a leda na zare na zura a jikina, nabi jikina da turare na fesa sama_sama. Kayan dana cire kuma na ninkesu na mayar cikin ledar da na cire rigar baccin. Sai kallona Alh Liti yake yi yana murmushi. Nama ya buɗe cike da takadda ya ji yaji da albasa, take yawu ya soma gudana a bakina, dama banci komai ba tun safe cikin fara'a nace dashi. Abincinka fa baza kaci ba yauma? Da wai so nake yanzu in je in ɗakko maka ai" Hannuna ya riƙo ya zaunar dani a saman cinyarshi yana shinshinar ƙamshin turarena. Cikin muryarshi ta yaudara yace. "Ai ko kusa bazan so kiyi nisa dani ba, in ce dai kema baki ci abinci ba ko? Ga nama na kawo mana shi zamu ci mu kwanta. Wannan doguwar rigar taki ta tado mun da sha'awarki ainun" Far nayi da idanuna nace. Ai kai da kaya duk mallakar wuya ne. Abinci kuma banci ba sabida da zazzaɓi na wuni sosai" Zamewa nayi na zauna a gefenshi. Naman ya soma ci yana kallona. "Kici nama ga fura in kina son sha ki sha." Zamana na gyara cikin kissa da kisisinar dana ƙware a kai nace Dama Alh Liti inason muyi magana ne akan inason ka bani jari in soma gudanar da kasuwanci, tunda kaga baka son aikin mace, ni kuma ina kulawa da Mama, da ƴan uwanta. Duk da nasan su Asiya ma suna iyakar iyawarsu." Shiru nayi ina kallonshi tare da karantar yanayinshi. So nake in gani maganin boka ya soma aikinne, duk da na ga halamar ya soma aikin, tunda har yayi mun tayi nama da fura" "Hmmmm kamar nawa kike ganin zai isheki yin kasuwancin, sannan wacce sana'a kike sha'awar somawa ke da baki san kan Ghana ba tukunna?" Wani sanyin daɗi naji a raina. Lallai duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba. Wato irin garaɓasar da Mama ta hango mun kenan, shi yasa tafi son in yi haƙuri in kwantar da hankalina in dandali arziki." Ko miliyan biyar ma in ka bani zan soma juyawa mu gani" Ƙwarewa yayi da nama, take ya shiga tari ƙwatol_ƙwatol. Ruwan roba daya shigo dashi ya ɓalle sai da ya sha rabi sannan ya sauke robar. Ya dubeni ƙur, ni kuma sai sannu nake yi mishi cikin muryar yaudara. Dariya yayi mai ɗan tsayi kafun yace. "Miliyan biyar zai miki dai ko ai naga kamar ba yawa?" Cike da azarɓaɓi na gyaɗa mishi kaina halamar E zai ishenin" "To shikenan, in Allah ya kaimu gobe sai in ƙirga in baki. Kinga waccan durowar? Shaƙe take tab da kuɗi harda na amurka" Idanu na zare, na bi durowar da kallo ina murmushi. Muna hira jefi jefi, muna cin namannan, ko wanne cikinmu da abinda yake saƙawa a ranshi. Furarshi yasha ya rage mun nawa, ya dubeni yace. "In kin gama cin naman sai ki share gidan kiyi mopping ɗinshi. Da safe ya kamata kiyi, ganin ke ɗin amaryace yasa na ɗaga miki ƙafa." Cikin fara'a na amsa mishi da. Ba matsala dana gama zanyi" Zama na gyara na dinga cin namannan sai da na cinye tas, na kora da fura. Sannan na tashi na shiga aiki. Hmm aikin babu sauƙi domun sai da na share sama da awa biyu ina abu ɗaya, bayana da ƙafafuna duk sun ƙaƙe. Da ƙyar na hauro sama, a zaune a kan gado na samu Alh Liti, yana daddanna waya yana murmushi. Wanka na shiga nayo, a yadda na barshi a haka na fito na same shi. Ina hawa kan gadon, ya murgino ya hayeni kamar doki, nan ya shiga sukuwa yana nishi. Ni kuma wani baƙin ciki ne ya turniƙeni, babu ko ɗigon sha'awar Alh Liti a tattare dani, banjin zan iya sha'awarshi kwata_ kwata. Haka yaita matsata kamar kayan wanki. Yana sauka a kaina ya soma sakin munshari. Kallonshi nayi inaji kamar in shaƙeshi ya mutu kowa ya huta. Da ƙyar bacci ya kwasheni na wahala, dan ko ina a jikina ciwo yake yi mun. Gabana kuwa ina tunanin ya tsagene, dan raɗaɗin da yake yi mun bana wasa bane. YAHANASU: A gaba Bulamana ya tusa ni, tare da yin tagumi. Ni kuma ko ina babu daɗi a jikina, ji nake yi kamar mutuwa zanyi. Gashi inason cikin dake Jikina ya zauna, nima ace ga nawa ɗan, shima Bulamana zai ji daɗin faruwar hakan, da ma su Ba Modu baki ɗaya. Idanuna haka su kaita fitar da ruwa. Sai na samu nutsuwa, zuwa can sai in kama kaina ina rishin kuka. Dan ji nake yi tamkar kaina ya ragargajene. A taƙaicen taƙaicewa yadda Muka ga rana haka darennan ya kasance mana. Bulamana idanuwanshi sun ƙanƙance sosai. Ko da asuba tayi sai da ya kira Hajara ta zauna dani kafin suka tafi masallaci. Ni kuma da taimakonta na samu nayi sallah a jingine a kan katifa, dan bazan iya zama akan sallaya ba. Bulamana yana shigowa ya shiga aikin hura wuta, kunu ya dama mana. Ya aiki Bawa ya siyo ƙosai a cikin gidan. Ni dai da ƙyar na yarda na sha kununnan, babu abunda nake son sha sai caka mis. Wannan baiwar Allahn na tuno wacce muka taɓa haɗuwa da'ita a wajan magajiya, tazo a birkice a ruɗe. Idanu na runtse gabana na tsananta faɗuwa, gani nake yi tamkar watan tonon asirinane ya tsaya. Ka yafe mun Bulamana, ka yafe mun dan Allah. Ko da na mutu ka samu Binta zata nuna maka fili......" Kaina na riƙe ina salati da ƙarfin gaske, a ruɗe Bulamana ya kama kaina ya shiga yi mun tofi. "Ki zauna bari in ɗakko ɗan sahu muje asibiti, duk da ina ganin ciwon kamar makarai ne suka shafeki, amman muje dai asibitin. Ki kwanta ina zuwa yanzu" Yana fita na miƙe a zabure. Jakata na zara ko mayafi babu a jikina, haka ko takalmi ban saka ba na fice da sauri. Matan gidan sai tambayata inda zani suke yi. Ina zuwa, mantuwa Abban Maryam yayi" Na fice da sauri ina waige. Ina fita na samu ɗan sahu na faɗa da sauri hannuna bibbiyu riƙe da kaina. Malam kai ni sabon gari. Ko nawa ne zan baka" "Durob kenan Hajiya?" Ya jefo mun tambaya. Kaga nace ko nawa ne zan biya ka, kayi sauri zan mutu wallahi" Ɗan sahun yaja fiii muka zo muka wuce Bulamana a guje. Tafiyar bata zame mun mai sauƙi ba, domun kaina sake birkicewa yake yi, harma na soma fisge fisge kafin mu iso. Muna isowa sabon gari na sakko da hanzari. Dubu biyu na jefa mishi a cikin ɗan sahun na tsallake a guje, ban tsaya ko ina ba sai gidan magajiya. A tsakar ɗakinta na zube ina nishi. Wayyo Magajiya mutuwa zanyi. Ki taimaka ki mun allura, ki bani benelin in sha, zan haukace in na sake muntuna" Ihu na saka a cikin ɗakin magajiya. Ba shiri magajiya ta riƙeni dam. Inajin shigar ruwan allurar cikin jikina. Benelin ta ɓalle ta bani. Zuƙa biyu nayi na shanye, na fasa kwalbar, nasha laka mis roba ɗaya. Sai da na kwashe sama da minti talatin na soma jin dama dama. Amman sai na tsinci kaina a halin jiri, ɗakin Magajiya ma tamkar zai rikito mun nake gani. Fita nayi a guje, Magajiya ta rikeni dam. "Ke karamar karuwa, ƙaramar ƴar shaye_shaye baki bani kuɗina ba, kuɗinki nera dubu biyar" Cikin muryar maye nace. Ki cire a jakaaataaaa" Da ƙyar na haɗa maganar, harshena wani irin kakkarwa yake yi. Sai da Magajiya ta cire kuɗinta sannan ta sake ni na fice. Bazan iya tuno abubbuwan da suka faru dukka ba. Na dai ganni a cikin layinmu, ina tafe ina layi, yaran anguwa suna ihu suna jefana. "Ta yi marisa, tasha kabso, tayi marisa tasha ƙwaya" Haka su kai ta bina suna faɗe" MRS BUKHARI [09/08, 12:55 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 35 BULAMA BABBA: Ina isowa ƙofar gidanmu na tarar da Hajara da Ahmad a waje suna dube_dube. Sai naji gabana ya yanke ya faɗi ras. Kafin in kashe ɗan sahun Ahmad da Hajara suka shiga gidan baya. "Hanzarta mu bi sahun Yahanasu, yanzu Hajara take faɗa mun wai ta fita a firgice ba ko mayafi a jikinta" Subuhanallah subuhanallahi, Yahanasun ce ta fita ba mayafi, a cikin kuma halin da take ciki?" Ban jira amsarsu ba, domun ba nayi maganar bane domun ina bukatar amsar daga garesu ba. Juya ɗan sahun muka yi, nan mu kai ta karaɗe layin, amman babu Yahanasu ba dalilinta. Nan muka shiga tamabayar matasa masu zaman banza na anguwa, amman babu wanda yace damu ya ga dai _dai da gilmawarta. Zama nayi a cikin ɗan sahun na dafe kaina wanda yake sarawa da zafi_zafi. Ahmad ne ya dafa ni, da sauri na ɗago kai muka haɗa ido. "Ka kwantar da hankalinka zamu ganta in sha Allah. Ni bansan ma ka fita ba ina cikin ɗaki a kwance zazzaɓi ya rufe ni ne." Babbar damuwata shine kar aljanun su kaɗata ta shige inda ba zama a ganta ba, ko kuma wani mummunan abun yaje ya sameta, ga ƙaramin yaron ciki a jikinta. Ahmad ya zanyi, me kuma zance ma manya?" "A'a kar kace haka Bulama, in sha Allah zamu ganta, mu yanka can anguwar ko zamu ganta. Ke Hajara shiga mu je" Ahmad ne ya tuƙa ɗan sahun, ina gaba a gefenshi, Hajara tana gidan baya ita kaɗai. Muna zuwa bayan layinmu muka hango dafifin yara a bakin wata kwata suna ihu suna jefa duwatsu. Har mun karya kan ɗan sahun mu zamu juya, wani matashi yazo wucewa ta gefenmu yana faɗama abokinshi cewar. "Wata ƴar ƙwaya ce ta faɗa kwata fa, shine yara suke ta jifanta" Inajin haka jikina ya bani anya ba Yahanasuna bace? Ahmad tsaya bari in leƙa kwatar can in gani dai, ku jirani ina zuwa" Da sauri na fice, na tutture yara na samu damar kutsawa da ƙyar. Dam gabana ya yanke ya faɗi, zuchiyata ta karye, idanuna suka soma zubar ruwa, yayin da jikina ya shiga kakkarwa a sakamakon tozali da Yahanasuna da nayi a cikin wani mummunan yanayi. Kwance take tsamo_tsamo cikin ruwan kwatami, baccinta take yi rai ɗaya, goshinta da gefen bakinta sai jini suke zubarwa, yarannan su suka fasa mata da tsuwatsu. Ahmad ne ya ƙaraso da sauri, yaran ya soma kora tare da hanasu jifan Yahanasu. Ni kuwa idanu kawai na zuba mata ina tunanin garin yaya tayi gamo da Aljanu, yaushe, kuma a ina ko dai abun maye tasha kamar yadda matashin saurayinnan ya kirata da ƴar ƙwaya?. Kai Yahanasuna bata da halaƙa da shaye_shaye, sai dai shafar alhanun gaskiya" "Daure mu cirota mu kaita asibiti Bulama, kayi haƙuri nasan kai musulmine cikakke mai yarda da dukkan ƙaddarar data sameshi." Ahmad ne ya dawo dani daga zancen zuchin da nake yi, tare da ƙarfafeni, dole ba dan naso ba Ahmad ya kama ƙafafuwan Yahanasu, ni kuma na kamata daga hammatarta. Sharaf _sharaf da ruwan kwata muka sata a cikin ɗan sahun, Hajara tayi mata matashi da cinyarta. Kallo guda za kai mun ka gane ina cikin ɗimuwa. Malam Aminu Kano muka wuce kai tsaye, a guje Ahmad ya shiga cikin asibitin, zuwa kamar minti goma sai gashi da gadon ɗaura marasa lafiya yana turowa. Akai muka ɗaura Yahanasu, Ahmad ya dubi Hajara yace. "Ki koma gida ki ɗakko mata kayanta kala ɗaya, dole za'a buƙaci sake mata kaya tunda wannan ɗin ya jiƙe" Hajara jiki a mace tace. "Babu ko ficika a hannuna Abban Anisa" Ahmad ya laluba aljihunshi bashi da sisi, haka nima babu kuɗi a jikina. "Ki shiga ɗan sahu ki jirani, in aka bata gado in sha Allah sai in fito muje mu ɗakko kayan nata" Cikin ganzari na dinga tuƙa gadon da Yahanasu take ciki har zuwa bakin wani ɗaki da ma'aikaciyar jinya ta nuna mun akan in shigar da'ita. Shigar da'ita nayi ga majinyata nan a kwakkwance gado_gado. Ma'aikaciyar kiwon lafiyar dake tsaye a kan Yahansu wacce take sanye da farar lab kot ta dubeni tace. "Malam kai wanta ne, ko kuwa mijinta?" Mijinta ne likita" "Amman meye ya sameta haka jikinta duk rauni, sannan jikinta duk warin kwatami garin yaya hakan ta faru" Wallahi likita fita tayi daga gida muka nemeta muka rasa , kuma dama ko bacci bamu samu damar yi ba, shafar aljanu take fama dashi, a cikin kwata muka tsinceta kai tsaye muka nufo asibiti da'ita" Kai likitannan ta girgiza tace. "To Allah ya bata lafiya, muna buƙatar kayan sawarta, sannan in tana da kati ka ba nurses su duba, in kuma bata da kati sai ku yankar mata kati ko? Ka jira mu a waje, mu kammala gwaje_gwajen daya dace" Jikina a mace mus na fita a ɗakin ina waigen Yahanasu wacce wannan likitan ta soma duba lafiyarta. Ahmad na samu a tsaye a bakin ɗakin, yana ganina ya nufoni. "Yaya ake ciki Bulama?" Cikin ƙarfin hali nace. Zan je in yanko mata kati ne sabida bata dashi. Suna buƙatar kayanta domun a sake mata na jikinta, Ahmad ku tafi ku ɗakko mata kayan." Numfasawa Ahmad yayi yace dani. "To shikenan bari muje ba zamu daɗe ba zamu dawo, ka kula da kanka, ka kuma yi haƙuri sai mun dawo" A tsaye a bakin ƙofar ɗakin Ahmad ya tafi ya barni, da ƙyar naja jikina zuwa bakin teburin yankan kati na yankar mata kati na kaima nurses ɗin da likita tace in basu, sannan na nemi waje na zauna nayi tagumi ina tunanin halin rayuwa, jarabawa daga wannan sai wancan, Allah dai ya bamu ikon cinye dukkannin jarabawar da zai jarrabemu da'ita domun gwajin ƙarfin imani a garemu. Ina zaune ina zancen zuchi har Ahmad da Hajara suka dawo. Sun kwaso kaya harda tabarma da flask ɗin ruwan zafi da kofi. "Ga kayan Bulama ka shiga ka basu sabida a cire mata masu jiƙan kar sanyi ya shigeta kuma. Karɓar ledar da kayan Yahanasu yake ciki nayi na shiga ɗakin, wanna likitan tana zaune a gefen gadon, wani likita namiji yana gaban Yahanasu yana dubata. Wannan likitar na miƙa ma ledar kayan Yahanasun. "An yanka mata katin ne?" Ta tambayeni. E an yanka mata, na ba nursses ɗin da kika ce in ba katin" "To shikenan ka jira mu daga waje, zamu nemeka da zaran mun kammala dukkannin bincikenmu" A sanyaye na fice ina duban fuskar Yahanasu, sai naga tayi wata muguwar rama ta sake yin duhu sosai. A kusa da Ahmad na zauna jigum ina tunani. "Bulama ya kamata ka kira su Ba Bakura ka sanar dasu rashin lafiyar Yahanasu, domun kaga ciwon dake damunta babbane ba ciwo bane da za'a ce zamu ɓoye ba. Ni a ganina kayi gaggawar sanar. Musu ko babu komai za'a turo wanda zai zauna da'ita Yahanasun domun ba zasu bari kai kayi jinyarta ba, Hajara kuma zata dinga komawa gida da daddare sabida yara." Wayata na zaro a aljihuna na danna number Ba Bakura. Kuka uku wayar tayi ya ɗaga. "Bulama lafiyar Yahanasu kuwa inata kiran layinta bata ɗauka, kwana biyu bata kira kowa a waya ba?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Ba Bakura bata da lafiya ne, yanzu haka ma muna asibitin Aminu Kano a kwance bata ma san inda kan nata yake ba" Ba Bakura nan ya shiga sallallami daga bisani yace. "Subuhanallah meke damunta Bulama?" To Ba Bakura ciwonta ina tunanin makarai ne suka shafeta, dan yafi kama da hakan, da safennan a waje muka tsintoto wallahi babu ko mayafi balle takalmi, a kwata muka zarota" "Innalillahi wa'inna ilaihil rajiun, Yahanasun ce makarai suka rabketa? To to yanzu bari in sanar ma Modu sai mu ga wa ya dace a taso yanzu_yanxu su tawo, in dai makarai ne, ai ba asibiti ya kamata a kaita ba, Damaturu ya kamata ku wuto da'ita ayi mata tsakani dasu kuma a bata jiƙe_jiƙen magungunan sheɗanu, amman da mamaki ace iska ya ka da Kanuri fa. Bari zan sa Modu ya kirawoka yanzu. Ba Bakura DAMATURU: wayar ya sauke a kunnenshi yana salati Hajja Gana ta dubeshi tace. "Malam iska naji ana batun ya bige Yahanasu iskokai a cikin zuriyarmu anya kuwa?" Ba Bakura yace. "Ni kaina tunanin da nake yi kenan. Amman bari in kira Modu a duba mutum biyu zuwa uku daya dace su je ayi komai a gaban idanunsu, inta kama su tawo da'ita Damaturun ne sai su tawo da'ita, tunda makarai ke damunta sai muji me suke so." Hajja Gana tace. "Ƙila ma sabida zalunci su suka hanata haihuwa suke ta faman ɓarar mata da juna da zaran ta same shi. Baice komai ba yasa kai ya fita har zuwa ɓarayin Ba Modu. A dokin ƙofa suka ci karo da Ba Modu shi da Ya Innana da halama fita zasu yi zuwa wata ƴar anguwa. "Bakura kaine da kanka baka sa anyi kirana ba?" Ba Bakura yace. "Babu komai dole ce tasa na taso ai Modu, wannan yaro BULAMA BABBA ya kira ka a waya kuwa?" Cikin fargaba Modu yace. "A'a ni rabona dasu tun shekaran jiya, har kaima kace kwana biyu su basu kira ba, muma bamu kira ba. Bakura lafiya dai ko?" "To lafiya ba lafiya ba zamu ce" Ya Innana da jin haka ta dafe ƙirjinta, tayi zuru tana sauraren me Ba Bakura zai ce. "Yahanasu ba lafiya, suna asibiti yanzu haka ma. Bulama yana neman ƴar uwa wacce zata zauna da Yahanasu kafin jikin ya warware, ni kaina inason zuwa in ganta ɗin ba dan jikina ba kuma gobe zan koma asibiti, amman suwa za'a tura musu kana ganin, mace biyu da namiji da zai tuƙasu?" Ba Modu jikinshi duk yayi mugun sanyi, yasan in ba gagarumin ciwo ba, mai zai sa har sai an ɗebi majinyata daga nan Damaturu har zuwa Kano? Ya Innana tuni ta shiga tashin hankali, sai Allah take ambato a fili tana sauke haki. "To Bakura Bagulaji da da Aissa ta wajenka sun isa, sai Gunsum ya tuƙasu ya kaisu ko shi ko Bukar" Ba Bakura yace. "To shikenan ka kira mijin Aissa ka sanar dashi, in yaso in sun fita sai su ɗauketa in ya amince, Bagulaji ta shirya, Gunsum sai ya kaisu, ka basu dubu ɗari su riƙe a hannunsu, Bagulaji zaka ba, Gunsum kuma duk wani abu daya taso zai biya a aljihunshi tunda Bulama bashi da ƙarfi. Allah ya bata Lafiya Innana a taya mu da Adda'a, kya sanar ma sauran matan gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci labarin rashin lafiyar Yahanasu ya karaɗe babban gidan. Bagulaji kuma tuni ta fito, Gunsum take jira ya fito, fitowa yayi cikin sauri. Gareji ya shiga ya fito da mota suka shiga. Ba Modu ya matso jikin tagar direba yace da Gunsum. "Duk halin da take ciki kayi ƙoƙarin sanar damu da wuri Gunsum, sannan kul aka kira Bakura a waya aka sanar dashi wani abun, kaga a haka ma jikinshi na son tashi. Bagulaji ku kula sosai, Allah ya tsare hanya ko?" Sallama su ka yi, anata musu adda'ar isa lafiya tare da adda'ar Allah ya ba Yahanasu lafiya. Kowa yana son ace dashi akaje. Wakil ya kalli Ya Innana wacce take sharar hawaye yace. "Ya Innana ki dena kuka in sha Allah zata warke. Kuma in aka kwana biyu ni da kaina zan ɗaukeki muje ki dubota mu kwana ɗaya mu juyo." Sai da yace haka ta ɗan ji dama_dama." MRS BUKHARI CE[11/08, 7:03 p.m.] +234 708 194 6843: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 36 .. Ghana: Kofur Zubaina: Da kyar na lallaɓa jikina na faɗa bayan gida nayo wanka, na gabatar da sallar asuba. Jigum nayi a kan sallayar inata tunane_ tunane barkatai. A wajan Alh Liti ya shigo ya same ni. Yana saye cikin doguwar farar jallabiya, tumbinshi ya fito titsitsi a gaba kamar mai cikin wata tara, sai wani munafukin murmushi yake yi mun. Ina kwana Alh?" Na faɗa a taƙaice. Cike da fara'a ya dube ni yace. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Kin tashi lafiya ko?" Kaina na sauke ƙasa ina jin wani iri a jikina. "Motata tana jiranki ki wanke mun ita. Jeep ɗin zaki wanke mun zan fita taron ƴan kasuwa a tamil." Da mamaki na dubi Alh Liti da yayi kicin_ kicin da fuska kamar bashi yake dariya yanzu ba. Abun mamaki sai na tsinci kaina da kasa yin musu dashi, ba shiri na jini a tsaye cikin zabarin son cika umarninshi, jikina har rawa yake yi bana son in ɓata ranshi. Soson wanke motar fa Alh yana wajan motar ne? Na tsinci bakina yana furta hakan. Cikin ɓata rai Alh yace. "Yana daga jikin fulawowin da suke kusa da mota, zaki ga bokiti da brosh na gurje taya da car wash ɗin duk a wajan. Tsumman goge motar kuma yana cikin motar a buɗe take motar. Ki hanzarta ki gama maza" To in sha Allah yanzu zan gama. Ina faɗar haka na juya na soma gangarawa gudu_gudu. Ina jiyo yanda Alh yake sheƙa dariya yana faɗin. "Shegiya duniya mai ido a tsakar ka, wacce tafi bagaruwa jima. Tsakar gidan na isa ina jin wani ƙunci a zuchiyata mara musaltuwa zuchiyata sai tafarfasa take yi. Ina hawaye haka na soma wankin motar Alh, nice wai yau a durƙushe ina durje ma Alh tayar motarshi, kuma a cikin zuchiyata ina fatan ya yaba mun. Anya kuwa lafiyata ƙalau kuwa, to meke faruwa dani haka? Kuka na sake rugujewa dashi mai ƙarfi nafi minti biyar ina rera kuka. A durƙushe a bakin motar Nabila ta zo ta wuce ni da kwanukan abinci, sai kallona take yi cikin tausayi, ni kaina da idanu na bita. Gata a ido yarinyace mai ƙuruciya, amman tana saye cikin jemammun kaya, fatarta duk ta yamushe, harda kaushi a ƙafarta fara ce sol, abinda na nura Alh Liti yana mugun son farare da dukkan halamu. Harta fito daga ɗakin Alh ina durƙushe na shiga cikin zurfin tunani. "Zubaina wankin mota kike yi ne?" Ta yi magana tana fara'a. Ɗaure fuskata tamau nayi nace mata. E ina kwana?" Ban bi ta kan amsarta ba na zabura naci gaba da aikina. Na gaji iyakar gajiya mara misaltuwa, ina kan goge motar na jiyo ƙamshin turaren Alh. Shine ya fito yana saye cikin wata farar shadda mai kashe idanu. Yayi kyau sosai cikinnan nashi shirim a gaba sai tafiyar ƙasaita yake yi. Murmushi ne ɗauke a fuskarshi wayarshi na kare a kunnenshi, ya zagayo ya zauna a mazaunin direba. "Ai kinfi haka gimbiyar mata, raina fansa ne gareki. Ina kammala mitin ɗin dana faɗa miki, zan dawo gida in kintsa sai jirgin Lagos, daga Lagos zan hau jirgin Sokoto da yardar Allah. Ki yi mun tsaleliyar kwalliyarnan taki mai jan hankalina." Shiru yayi yana jan numfashi. Hawayen dake kwarara a idanuwana na share ina kare ma Alh Liti kallo. Ya samo wata budurwar kenan yana yaudareta a waya sai ya kawota cikin gidan tasha azaba. Akwai yiwuwar mace ɗaya zata bar cikin gidannan kenan, dan mu huɗune a halin yanzu matan Alh. Wata zuchiyar tace mun. "Ke ma ba sai da aka saki Rumaisa'u kafin aka auroki ba, sai da akai mata korar kare kika samu ɗakinta" Kai Alh Liti mugun mutum ne sosai. Dariya yayi shi da budurwarshi ta waya. "Duk abinda kika girka mun ai mai daɗi ne, na baki wuƙa da nama ki yi duk yadda kike ganin kin soni dashi. Rayuwata da taki a waje guda suke. Zan kira ki dana shiga Lagos I love You" ƙit ya kashe wayar ya barni da sakakken baki, hawaye sai makanta ganina yake yi, ni kaina bansan kukan me nake yi ba. "Ke ki shiga ki fito da kwanukan dana karya, sannan ki fito da ledar kayanki, ki jirani a bakin get zaki buɗe mun, inason in shiga cikin gidan." Nan ya fito daga cikin mota ya nufi cikin gidan ni kuma ya barni da sakakken baki. Alh Liti: Yana tafe yana wani murmushin mugunta, hannu yasa da karfi ya tura ƙyauren da zai sada shi da barayin iyalan nashi. Kasancewar gidan tabkekene mai yalwar tsakar gida babu ma wanda yasan da shigowarshi. Tun daga nesa ya hango Jamilu ya cukume Fa'iza suna rikici Hajiya Kubra ce a tsakankaninsu tana ta kiciniyar kwatan Fa'iza a hannun Jamilu. Nabila tana gaban murhu tana haɗa wuta, Zakiya kuma wankin kayan yaranta take yi, da goyonta a bayanta. Ƴan matan gidan kuma sun fita jidon ruwan da ya zame musu tamkar idaba domun babu fashi kullum sai sunyi, wasu daga cikin ƴan matan suna waje suna taɗi da samarinsu, wasu kuma suna zazzaune a tsakar gidan a hautsine. Matasan gidan kuwa masu fita nema sun fita, masu fita bin yawon majalisa suna can, ƴan maula sun tafi sana'ar tasu. Halifa ya fita kasuwa saida maganin basir. "Jamilu ka saketa nace dan ƙundun ubanka baka da hankali ne zaka cukumeta kana tuhumarta?" Cewar Hajiya Kubra kenan. Jamilu yace. "Tare da abokina suka kwana a ɗakunan hotel ɗin cikin lingun gidansu Mafi fa, waye bai san Zazu ɗan iska bane bashi da aiki sai na ɓare mata. Dan ubanta tun a wajan nayi mata maganar meya kaita ɗakinshi shine take mun rashin kunyar data saba." Hajiya Kubra data saba da irin wannan kes ɗin in dai akan yaran gidanne tace. "Yanzu Fa'iza kema bin mazan kika soma bakya ko jin tausayin mahaifiyarki kullum in tayo kiran waya a cikin yi miki nasiha take, ashe bata isa dake ba ko?" Cikin rashin kunya da tsiwa irin ta yaran da idanuwansu ya buɗe suka san maza tace. "Kashe kaina zanyi to Hajiya, a gidannan ko asibiti ba'a kai mutum a duba lafiyarshi, zancan abinci ma ba'ayi sam dan wallahi abincin gidannan bashi da maraba da guba. Sutura daga shekara sai shekara akeyi mana, wanne namijin ne zai kulaka a wulaƙance, ga kuɗi a gidan ubanmu amman kuɗin lukudi" Alh Liti yace. '"Kinci abu kazan ubanki shegiyar yarinya" Take kowa ya sha jinin jikinshi, takalmin ƙafarshi ya cire ya nufo su, daga ita har Jamilun darewa suka yi, suka ari na kare. Da mugun gudu ya bisu har ƙofar gida yana kutuntuma manya_manyan ashariya. "Ƴan iskan yara, na haifa sun zame mun masifa da jaraba" Yafi minti biyu yana ƙunduma zagi. Harya juya zai shige cikin gidan, ya hango su Barira da Aina'u suna taɗi a dakalin kusa da gidan nasu. Faram_fararam ya isa wajan da takalminshi a hannunshi. Da samarin da yaran nashi duk suka miƙe tsaye. "Aurensu kuka zo yi, ko rage lokaci kuke yi?" Mai ƙarfin hali daga cikinsu yace. "Aurensu muke son yi Alh" Alh Liti yana zazzare idanu ya mazarin tsire yace. "Nan da kwana bakwai ku tawo da sadakinku a hannu, bayan sallar isha za'a ɗaura muku aure dasu. Sai ku sanar ma magabatanku ku yi shiri. Ba'a akwatin aure a gidana, a madadin akwati zaku yi musu kayan ɗaki, da gara. Ni su zan baku gayatan ɗinsu da an ɗaura aure su fito ku tafi. Su waye iyayen naku?" Suna soshe_soshe suka yi mishi bayanin kansu, duk yasan iyayen nasu. Yarane na talakawan anguwa masu lallaɓowa suna son haɗa zuriya da Alh Liti ko banza komai daren daɗewa zai mutu, kuma za'ayi rabon gado, matayensu Allah kaɗai yasan abinda zasu mallaka. Alh Liti ya kora yaranshi gida suka shiga ya rakasu da gudu har ciki. A cikin wannan zage_zagen ya saki Zakiya. "Ayirirririiiii Alhamdulillah Allah na gode maka daka kawo mun ƙarshen wannan wahalar, ku kuma inai muku fatan alkhairi. Yara Allah shike riƙe dasu dama. Yaron bayanta ta kwance ta kwantar dashi a ƙasa ta shige ɗakinta tana kukan da ya zame ma mata al'ada, duk yanda su ka kai da son saki, da zaran anyi musu sai su fashe da kuka. "Aikin banza aikin wofi, tunda baki da mutunci ki tattare inaki inaki ki bar mun gidana. Ke Kubra ɗauki yaronnan ya rayu a tsakankanin cinyoyinki da kafaɗun Nabila. Yarannan ƴan matan su goma ne cib ko?" Hajiya Kubra tana kuka ta ɗauki yaron Zakiya ta rungume, tama kasa amsa tambayar da Alh Liti yayi mata, har sai da ya daka mata uwar tsawa. "Ba magana nake yi dake ba, kike faman yi mun kukan iskanci ba" "E e su goma ne" Ta amsa a kiɗime dan tasan ba ƙaramin aikinshi bane ya tsinkata a gaban yara ba. "Duk su fito da mazaje sati mai zuwa zan aurar dasu, in basu da samarin kuma, zan bada su kyauta ga ƴan ciranin da muke sallah dasu, na faɗa muku dan haka su zauna cikin shirinsu daga yanzu zuwa sati guda." Cikin kuka Hajiya Kubra tace "Alh kaji tsoron Allah ina jiye ma ƙarshen rayuwar......." "Dakata Kubra, baki faɗama iyayenki suji tsoron Allah ba, sai ni kike faɗama jin tsoron Allah? Da kina jin tsoron Allah bazaki butulcema mai ƙaunarki da gaskiya kibi son duniya ki zaɓeni ba. Alhalin dashi nazo na tarar kuna soyayya. Duk matar da zan auro son duniya ne yasa ta aureni ai" Yana gama faɗar haka ya wuce fu ya barsu a wajan suna jimami. Zubaina: Ina tsaye naga shigowar Alh Liti fuu kamar kububuwa da sauri na buɗe mishi get ya fice da mugun gudu fuuu" kwanuka da ledar kayana na ɗauka na shiga cikin gidan. A tsattsaye na samesu suna ta jimami. Tambayarsu nayi meke faruwa. Rashida ce tace. "Anty Zakiya Baba ya saki. Kuma nan da wata uku zaki ga ya sake auro wata matar. Wannan abun kunyar mu da wanne zamu ji?" Tana kaiwa nan ta fice a gidan tana faɗin. "Gara naje gidan abincin Mari in huta da takaicin cikin gidannan namu, Allah ya ɓullomun da bazawari dana gama idda ya aureni. Jikina a sanyaye na ajjiye kwanukan abincin Alh a wajan wanke_wanke har zan shiga ɗaki Nabila tace. "Ga abincinki can a rufe ki je ki ɗauka. Sannan ki dinga fitowa cikinmu kina ɗan hira kar ciwon zuchiya yai ajalinki ba tare da kowa ya sani ba. Muma da haka duk muke zaune a gidannan. In kaje ganin gida aita ma tambayar ciwo kayi ne. Ciwon cikin gidannan ai baya warkewa har sai ranar da zaka karɓi takaddar sakinka a hannunka. Ni dai bance komai ba na juya na ɗakko kokkona da kulikuli na shige ɗaki. Kaina na haɗa da guiwa na shiga rera kuka, ina cikin kukan sai ga kiran Mama ya shigo wayata" Bulama Babba: Ina tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Yahanasu, babu nutsuwa a tattare dani sam. Nafi minti talatin a tsaye, jama'a sai kai kawo suke yi a cikin ɗakin, wasu su shiga, wasu su fito, a haka Ahmad ya dawo. Ledar kayan ya miƙo mun "Ka kai musu kayan a samu a sake mata ta rabu da wannan kayan dattin?. Bance mishi komai ba na shiga ɗakin a katange gadon Yahanasu yake, da halama har zuwa lokacin dubata akeyi, a gefe na tsaya nayi musu magana. "Malam ko zaka taimaka mana wajan sake mata kayan nata nauyi gareta tun ɗazu muke kiciniyar saka mata mun kasa, dan transpa zamu rubuta muku ma yanzu, mu mun gama namu. A rikirkice na isa bakin gadon da Yahanasu take kwance, fuskarnan tata tayi fiyau da'ita, taji ciwo sosai a fuskarta, har gefen hancinta naga bandeji. Da taimakon wannan likitar mace na sake ma Yahanasu kayan jikinta, sauƙinta ma gashinta bai jiƙe ba. Wannan likitar ta dubeni tace. "Ina mai baka haƙuri cikin dake jikinta an rasa shi. Sannan nayi maka batun Transpa ko? Zamu turaku asibitin DAWANAU ne, ka biyo ni muje zan ɗanyi ma bayani kaɗan." Dam naji gabana ya yanke ya faɗi, zargina ya sake tabbata cewar da jinnu Yahanasu taci karo suka jirkita mata ƙwaƙwalwarta. Take zufa ta shiga yayyanko mun, ƙafafuwana da harshena su kai mun nauyi, na kasa tafiya, haka zalika na kasa furta ko wacce kalma, idanuwana suka kawo ruwan hawaye, sai ambaton Allah nake yi kawai a cikin zuchiyata wacce take bugawa" "Bawan Allah kayi haƙuri, ka biyoni inyi magana da kai, kafin ka karɓi takaddar transpa" Naji wannan likitar dana manta ma ni take jira tace. Bance komai ba na bi bayanta ina waigen Yahanasu har sai da na fice a ɗakin tukunna. Ahmad yana ganinmu ya taso ya riƙe hannuna. Baice mun komai ba, nima bance mishi komai ba, mu kaita bin likita a baya har izuwa ofishinta. "Ku zauna ga waje" Ta nuna mana benci, bani da guiwa haka na daure na zauna na ƙurama ƙasa idanu. "Kamar yadda dai na faɗama shine, cikin dake jikinta ya zube, sannan tana cikin wani irin hali a sakamakon shan miyagun ƙwayoyin maye ta samu taɓin hankali, kuma bincike ya nuna mana magani tasha mai ƙarfi ya salwantar mata da cikinta. Amman bai kamata a matsayinka na mijinta ka kasa kula da'ita ba harta faɗa ƙangin shaye_shaye. Ko ma naga shaye_shayen ya zama tamkar ruwan dare ga matan aure. A cikin sati biyu mun samu keses ɗin matan aure masu shaye_shaye bakwai harda matarka ta takwas, duk mun aike dasu dawanau, uku daga cikinsu an basu gado, huɗu kuma suna zuwa karɓar magani." Ajjiyar zuchiya likitannan ta sauke, ni kuwa in banda rawa babu abunda jikina yake yi, kaina kamar zai tarwatse haka nake jinshi, duniyar baki ɗayanta juyawa take yi dani. "A'a likita bana jin Yahanasu zata faɗa ƙangin shaye_shaye kamar yadda kika faɗa, ni nafi alaƙanta wannan lalurar tata da shafar aljanu amman ba shaye_shayen muyagun ƙwayoyi ba, meye matsalar Yahanasu da har zata yi ta'amali da kayan maye? A baya ma da abubbuwa da dama suka faru da'ita bata sha komai ba, sai yanzu da take cikin walwala da farin ciki." Ahmad ne yake wannan maganar a kausashe, har suna shirin yin rikici da likitan. "Kana nufin zaka nuna mun aikinane, ko kana nufin bansan me nake yi bane, waye ma kai a wajanta da zaka hayayyaƙomun? Kabar mijinta yace wani abu mana" Ahmad ya zabura zai mayar ma da likitarnan amsa, nayi saurin cewa. A'a dan Allah Ahmad. Muyi haƙuri muje dawanau ɗin a duba ta, amman ba wanna sa'insar ba. Likita kiyi haƙuri, a bamu takaddar transpa ɗin, ni dai a iya sanina in banda lakasera babu abunda Yahanasu take sha Dr, kullum sai ta sha wannan lakasera" Zama Ahmad yayi sai muzurai yake yi, ita kuma wannan likitar ta shiga rubutu a wata ƴar takadda. Takaddar ta miƙomun tare da katin mu. " Wannan lakasera da kake magana akai, ƙwaya suke narkawa a ciki suita sha hankalinsu kwance, yanzu mai gari ya waya? Ƙwaƙwalwarta gabaki ɗaya ta jirkice. In kuka je DAWANAU ku nemi Dr Halima ta dubata, ku sanar da'ita Dr Ruƙayya Shehu ce ta turo ku. Zan kirata ma in sha Allah kafin ku isa. Zaku biya kuɗin gado, da kuɗin gwaji kafin ku wuce. Sannan ina mai baka shawara kai a karan kanka ka yi tunani da kyau, shin baka taɓa kama matarka da wata ƙwayar magani, ko kwalbar maganin yara ba, iyakar wannan lakasera kawai ka taɓa kamawa tana sha kullum? Da sannu ƙila ka tuno wani abun. Ga takaddar biya nan kuje ku biya" Godiya nayi ma likitannan muka fito. Ahmad ka je ka biya kuɗin, ni kuma bari in sakata a cikin ɗan sahu kafin ka fito" Ahmad ya bini da idanu yana son ya karanci yanayina. Da sauri na wuce ɗakin da Yahanasu take kwance. Bacci_bacci ido biyu na sameta, tana ɗan surutai sama_sama bana iya gane abunda take cewa. Yahanasuna kin farka ne? Na faɗa a hankali, kallona tayi da idanuwanta da suka rine suka zama wasu kala. ",Na farka, naganmu a jeji me muke yi ne haka? Ni tsorona ma ɗaya kar zaki ya cinye mu" Da sauri nasa hannu na rufe mata bakinta hawaye na shirin zubo mun, da ƙyar na yaƙesu basu zubo ba, na shiga dube_duben ɗakin ko wasu na jinmu, amman kowa harkar gabanshi kawai yake yi. Miƙar da'ita nayi tsaye na saɓa hannayenta a kafaɗata na tallafi ƙugunta sosai. A hankali muke tafiya, tana sulalewa ina tarota, wata nurse ce ta taimaka mun muka kai Yahanasu har cikin ɗan sahu. A wajan zaman direba muka tarar da Ahmad yana jiranmu. Haka muka nufi hanyar Dawanau babu mai cewa da kowa komai hankali da nutsuwata basa tattare dani sam. Adda'a nake yi Allah yasa ba dai_dai bane abinda Dr Ruƙayya ta faɗa akan Yahanasu. Ɗan sahun mu har cikin harabar asibitin Dawanau muka shiga da'ita. "Bulama ina ganin ka zauna bari in soma shiga ciki in kira nursses su taimaka mana, ina zuwa ko?" Kai kawai na ɗaga ma Ahmad, ina zaune ina tunani Ahmad suka iso gabana ban sani ba. "Malam ka fito mu shigar da'ita ciki" Naji muryar wata mace. Sai lokacin na ɗago kaina wanda yake sarawa na kallesu, a sanyaye na sakko daga cikin ɗan sahun. Ni da wannan nurse muka kama Yahanasu ta gefe da gefe zuwa cikin asibitin. Marasa lafiya mu kaita wuce wa, har zuwa wani babban ɗaki na majinyata mata. Babban abunda ya tsoratar dani, bai wuci yanda na ga ɗakin cike da mata ba, wasu ma hannayensu ɗaure da kaca an sagale a jikin gadajen nasu. Wasu na bacci, wasu kuma suna shirme, harda masu zage_zage. Take ruwan jiri ya ɗebeni nayi kata_kata zan zube Ahmad yayi saurin taroni. Gam ya riƙe ni yana faɗin. "Ka mallaki kanka mana Bulama meye haka? In sha Allah ba abunda yake damun Yahanasu daya danganci taɓin hankali, mu basu dai dama su gama bincikensu, zasu sallame mu ne. Zaunar dani yayi a farar kujerar roba, na zuba ma Yahanasu ido tana kwance a gadon, bakinta yana motsi amman idanuwanta a rufe suke. "Dan Allah muna neman Dr Halima ne. Dr Ruƙayya ce daga Asibitin Murtala ta turo mu nan." Ahmad ne yake magana da wannan nurse data taimaka mana. "Okey kai ka biyo ni in kai ka office ɗinta, yanzu ma zata tafi gida dan night tayi. Amman muje, shi sai ya zauna da'ita. Ina jiyo su suna tafe tana tambayarshi mun taɓa zuwa nan ne. Ni dai tagumi na gasa ina kallon fuskar Yahanasu kawai. Wayata ce tayi kuka, da ƙyar na zarota daga ajjuhuna. Ba Modu ke kiran wayar tawa, gabana ya faɗi ras. Cikin mazantaka na ɗaga wayar tare da karawa a kunnena. Assalamu alaikum barka da rana Ba Modu" Ya amsa mun sallamata a sake "Yaya jikin Yahanasun, Innana ta damu da yawa, na shiga ɗaki na same ta sai aikin kuka take yi, kasan mata da rauni. Shine dai nace bari in kira ka in Yahanasun ta farka a bata wayar taji muryarta" Cikin dauriya na ƙwaƙwalo murmushi nace. "Bata farka ba, anyi mata allurar bacci ne, sai gobe zata farka. Jikin da sauƙi sosai Ba Modu" "To to shikenan, su Aissa suna hanya tun wuri duk inda suke ma sun kusan isowa, anata kiran wayar tasu ma bata shiga." Nan dai muka rabu lafiya da Ba Modu. Ina ajjiye wayar Ba Bakura ya kira ni. Shima yadda nace da Ba Modu haka nace dashi muka yi sallama. Ahmad ne ya shigo shi kaɗai, dubanshi nayi nace. Yaya dai Ahmad, ina Dr Haliman take na ganka kai kaɗai?" Ahmad yace. "Uhmm Dr Halima ta tashi a aiki Bulama, sai ƙarfe shiddan yamma zata dawo bakin aiki, amman akwai nursses ɗin da zasu kula da ita Yahanasun kafin ta dawo. Ina ofishinta ma Dr Ruƙayya ta kirata tayi mata maganarmu. To ta dai ce zata biyo ta ganta kafin ta wuce." Yana cikin yin magana wata farar dattijuwa ta iso bakin gadon da muke. "Wannan itace Yahanasun ko?" "E Dr itace kin ganta" Ƙur ta zaba ma Yahanasu idanu, ta matsa kusa da'ita ta gwale mata idanu, tare da juya kanta ya dawo gefen dama. "Allah ya bata lafiya, zuwa ƙarfe shidan yamma zan dawo, zan duba ta in sha Allah. Iyalaina suna jirana a gida, tun 8 na safe ya kamata in tafi gida amman nice har goman safe. Amman ƙila har in dawo ma bata farkaba, ƙwayar data sha mai ƙarfin gaske ce, ina tunanin allurar doki ma tai ma kanta gaskiya, dan shi ke zaburar da ƙwaƙwalwa kai tsaye, ba kamar laka mis ba. Ba nan kusa zata sake ta ba. Ni zan tafi, nursses zasu dinga zagayowa dubata. Sannan a samo mace da zata zauna da'ita, sabida ward ɗin mata ne. Ahmad ne yayi mata godiya har yana rakata. "Bulama bari in je gida in dawo, dan nasa Hajara tayo girki, ta dafo ruwan zafi. To zanje in tawo da abincin, itama Hajaran sai tazo ta zauna da ita Yahanasun" Har Ahmad ya fita sai kuma ya dawo. Ya ka dawo Ahmad?" "Bazan iya tafiya in barka a wannan halin bane Bulama, na kira Hajara zata kamo hanya." Wata nurse ce ta ƙaraso inda muke tace. "Dan Allah ku je daga waje, maza basa zama a ɗakinnan in ba masu dubiya bane" Hannun Ahmad na riƙe muka fita waje. Mrs Bukhari ce [11/08, 7:03 p.m.] +234 708 194 6843: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B 37 GHANA ZUBAINA: A sanyaye na ɗaga wayar tare da karawa a kunne. "Yaya ake kici Zubaina, ince dai ke kaɗai ce ko?" Kukan dake shirin turniƙeni na haɗiye da ƙyar murmushi na ƙaƙaro nace. Ni kaɗai ce Mama yanzu Alh ya fita ni kuma na shigo cikin gida kenan ina ɗakina" Ƴar dariya ta saki tace. "Kin yi abunda boka ya ce kiyin, ya yanayin abun yake kuma, kinsan da zafi_ zafi ake dukan ƙarfe?" Aiki yaci Mama babu wata matsala, kuma Mama ni yanzu ma naga gidan zama, bansan ina son Alh ba ma sai yau, wani bala'in son shi nake yi sosai." Ni kaina ji nayi zancen ya subce a bakina ba tare da na shirya ba. Duk da dai a yanda nake ji a yanzu, sai naji lallai inason zaman gidan Alh ji nake zan iya rasa rayuwata in bana tare dashi. Ba tare da wani dalili ba, dan babu komai a gidan Alh in ba baƙar azaba ba. Amman ina ganin gara in haƙura kawai in zauna. ( Asirin Alh Liti yayi tasiri a jikin Zubaina. Wannan wani babban darasine, asirin mallaka yayi mata, da soyayya Kamar yadda tai ma Bulama) Mama ce ta katse ni dariyar murna da naji tana yi gami da hamdala. "Alhamdulillah Zubaina sai yanzu naji abunda ya tokare ni ya faɗa. To kinsan da zafi _ zafi zaki yagi abunda zaki yaga. Ki dinga turowa ana siya miki filaye ana gina miki, ke har tirela ma sai ki siya abunki, ko ki buɗe shago a kasuwa, ko daga ghanan ki dinga turo kaya. Ko Musa sai ya kula miki da shagon. Amman kar kiyi sake, tun kafin gishiri ya fice daga kan kaza zaki haɗa balance ɗinki." Kukan yarinya na ji a kusa da Mama. Ajjiyar zuchiya na sauke ina tunanin yanda zan ɓullo ma zaman gidan Alh. Mama kukan ƙaramin yaro nake jiyowa, ko su Rauda ne suka zo?" "Wace Rauda? Hmmmm ƴar dakan kukannan aka zo aka diremun da sassafennan, wai yarinya an yayeta. Ni nama rasa yadda zan tsoma kaina ta ina zan soma renon wannan yarinyar ƴar ƙararrama da'ita? Ke fita ma bazan iyayi ba. Sagiru nake ta aikin nema tun jiya yazo mu tattare mu koma can sabon gida, nima in huta da wannan ƙaddararriyar anguwar." Baki kawai na taɓe abunda yake gabana yana da yawa. "Mancewa nayi ban sanar dake ba Zubaina Asiya tana son a rushe wannan gidan, wai gidan sama take son tayarwa mai hawa uku ma. In yaso ko haya a zuba." Tana haɗiye yawu ta sake cemun. "Ba wani abu da zaki turo mana ne Zubaina?" Kai kawai na girgiza nace. Mama ni yanzu bani da kuɗi, kuma turo kuɗi daga Ghana zuwa Najeriya akwai wuya. Shi yasa fa nace kuɗin hayar gidana in kun karɓa ku dinga amfani dashi kawai Mama." Yarinyar Musa ce ta hana mu ƙarashe wayar, sai kuka take yi. Ƙit Mama ta kashe wayar ina ji sai ƙundumama yarinyar zagi take yi. Ɗan latse_latse nayi a wayar na ɗan shiga whatapp ɗina. Saƙonni barkatai na tarar. Da yawan saƙonnin na murnar aurenane, dan su Asiya da Mabaruka sun watsa zafafan hotunana kafafen sada zumunta. Wani sabon group naga an adding ɗina mai suna MATSALOLIN MU, wata tsohuwar ƙawata Bilki ce ta adding ɗina. A hankali na soma bin saƙonnin cikin group ɗin. Sai na fuskanci gidan shawarwari ne, zaka turo da matsalarka, ko na wanin ka, sai ka nemi shawara a baka. Idanuna na runtse hawaye suka sulalo mun. Kokkonnan na ɗaga na soma sha a hankali ina gutsurar ƙuli_ƙulinnan, sai kawai na fashe da kuka. Tunanin gidan Bulama na soma yi. Da farfesun naman rago, ko kan saniya dashi nake karyawa. Rana ɗaɗɗaya ne nake karyawa da kakkauran tea da biredi, da wainar ƙwai harda bota a jikin biredin. Amman yau nice kokko da ƙuli _ƙuli ya zama abun karyawata. Ɗaga kaina nayi na kalli ɗakin nawa, ɗakin da kishiyata ta gama zamanta ta haifi yara har biyu. Nima gani a ɗakin a kan gadon. Ɗakina na gidan Bulama na sake tunowa, yanda gadona yake babba gashi da tsadar gaske. Bayan ya auro Yahanasu ya sake sake mun kayan ɗaki harda fenti. Na sake tuno da kayan ɗaki daya ciyo bashinsu ya samun a ɗaki a lokacin da na haifi Yusuf, dan kawai yaga walwalata Oh Allah rayuwa kenan duk da hakan kuma sai nake jin inason zama da Alh, bana fatan abunda zai rabani ma dashi. Ni bansan ina sonshi ba, sai yau dana ga ya fito cikin kwalliyar nunawa sa'a. Amman wajan wata budurwar ma zashi, na tabbatar itama aurota zaiyi, shine dalilinshi na sakin Zakiya. Ina cikin wannan tunanin na jiyo sallamar Zakiya zata tafi Najeria. Fitowa nayi tsakar gidan tana tsaye da akwatin kayanta. Tana sanye da wata jemammiyar atamfa shuɗiya, da wani farin ɓulallen mayafi, takalmin ƙafarta ma ƙarewarta a tsinke yake ta ƙulle da wani jan zare. "Zubaina ni kam zamana ya ƙare, abunda naita nema yau yazo kaina, a gabana an saki wasu matan. Ina muku fatan fitowa da wuri ba ma sai kun kaini jemewa ba. Ga yara nan na barsu." In yi magana ma na kasa, wani irin hakine yake taso mun, ina jin wani jiri na ɗibata. Wannan wacce iriyar rayuwa ce na shigar da kaina? Ina zaman_ zamana. Manya da yaran gidan sai sallama suke ma Zakiya, ɗan yaronta da bai wuce shekaru uku ba yana tsaye ba wando sai zandara ihu yake yi. Goyon da Zakiya take yi kuma yana hannun Nabila, ita kanta sharar hawaye take yi. Nima hawayenne yake zuba a kumatuna. Haka rayuwa taci gaba da garani. Uƙubar da nake ciki ko maƙiyina bazan so ace ya faɗa ba. Wayata ma baki ɗayanta kasheta nayi na jefa a jakata, dan katin cikin wayar ya ƙare, kuma haushin kowa nake ji. Musamman Asiya da Nafisa da in suka kirani suke mum wani shegen iyayi da feleƙe. Wanka a ƙyanƙyame nake yi, sabida ƙyamar da bayan gidan yake bani. Rashin Alh Liti a gari ya sanyaya mun zuchiyata. Ina kwance a kan gadona ina cikin duniyar tunani, tare da tausayin yarinyar da naji Alh Liti yana waya zaije wajanta. Ko kurkuku yafi gidan Alh Liti daɗin rayuwa. Bulama ne ya faɗo mun a raina, wanda hakan sai da yasa ni murmushi. Bawa da Maryama na na tuno saina fashe da dariya, ina dariya ina share ƙwalla. Nasan duk talaucin da Bulama zai tsinci kanshi, babu abunda zai sauyashi wajan bautawa matarshi. Kaicona da na bar gidan Bulama, da zamana nayi muka rayu rayuwa mai daɗi. A ranar dai tunanin Bulama da zugin zuchiyane suka hanani bacci, sai wajajen asuba ɓarawon bacci ya ɗebeni. Asibiti. Bulama Babba. A wasu dogayen binci muka samu waje muka zauna. Babu mai cewa da kowa komai. Ward ɗin a cike yake maƙil da masu kawo ziyara, lokacin shiga suke jira kawai ya cika su shiga su duba majinyatan da suka zo dubiya. Hajara ce ta iso inda muke kici_kici da kaya da sauri Ahmad ya miƙe ya karɓeta ga goyon Yusuf a bayanta. "Abban Anisa akwai filo da tabarma da bokiti na ajjiye su a wajan mai gadi kayan sunyi mun yawa." Cewar Hajara wacce ta zauna tana mayar da numfashinta. Ahmad baice mata komai ba ya nufi hanyar dogon falon. "Sannu Bulama yaya me jikin? Kun samu ganin likita kuwa naga har azahar ta kusa?" Cikin tawakkali nace mata. A'a sai zuwa shiddan yamma likitar da zata dubata zata shigo. Amman dai ta samu gado. Sannu da ɗawainiya ga Yusuf ma yayi bacci." Kafin tace wani abun muka jiyo ihu da dambarwar wata baiwar Allah ita da nursses da halama itama mai taɓin ƙwaƙwalwarce, sai ƙunduma ashariya take yi, wani dattijo kamar mijinta yana riƙe da'ita yana. "Hauwa kiyi shiru dan Allah, a asibiti muke fa" Amman wannan matar taƙi yin shiru sai naushi take kaiwa nursses ɗinnan. Allura wata nurse ta fakaiceta ta tsira mata. Kafin ma a zare allurar tuni tayi laushi sai ido. Da taimakon wannan dattijo aka shige da'ita ɗakin da Yahanasu take ciki. Ni dai nayi tagumi ina kallon ikon Allah. In baka je asibiti ba, ba zaka gane ana fama da cuta ba. "Ohh ni Hajara ji wannan lamari abun tausayi ya Allah." Ahmad ne ya iso da kaya a hannunshi. "Ungo Hajara ki shiga ki ajjiye a gefen gadon da Yahanasu take kai. Sai ki zauna a gefenta, inta farka ki kira mu." Karɓan bokitin da tabarmar tayi, ta shige ɗakin da saurinta har tana bige wata nurse. "Gunsum sun kira ni yanzu ina hanyar shigowa, suna dab da shigowa cikin garinnan da Gunsum, da Bagulaji, sai Asissa tamu ba tsohuwar matar Wakil ba. Na dai ce da zaran sun shigo su kira ni sai in yi musu kwatancen asibitin da muke, gudun kar in ɗaga musu hankali in nace muna dawanau." To Allah ya kawo su lafiya. Leɓena na lasa wanda ya bushe kamar zai tsage. "Bulama muje masallaci lokacin sallah yayi, na baro maza anata alwala." Miƙewa nayi muka jera ni da Ahmad, babu Mai cewa uffan. Ko da mu ka idar da sallah a wani ɗan masallaci a tsallaken titi. Zaune nayi ina tasbihi a hankali. Bayan na gama na nufi durowar Qur'anan masallacin na ɗakko Qur'ani na dawo na zauna. Karatun Qur'ani na shiga yi domun in samu ƴar nutsuwa dan zazzaɓi ne yake shirin kayar dani, ko yanzu da likitoci zasu yi aune_aune a jikina na tabbatar zasu bani gado a matsayin mara lafiya. Wayar Ahmad dake ajjiye a ƙasan kafet ɗin masallacin ta shiga kuka, ƙarfe biyu dai_dai na rana. "Gunsum kun ƙarasa shigowa gari kenan? Cewar Ahmad dake waya. Bana jin me Gunsum yake cewa, na ji Ahmad yace. "To kayi amfani da map ya kawo ku asibitin Dawanau, in kuka iso sai ku kira ni" Kallon Ahmad nayi naga yayi jim ga wayar a kunnenshi da dukkan halama magana Gunsum yake yi mishi. Numfashi yaja yace. "Gunsum ba abunda kuke tunani bane sam. Daga asibitin Murtala aka turo mu yin wani gwaji, kai dai sai kun ƙaraso kawai." Ya sauke wayar yana girgiza kanshi. A sanyaye nace. Tambayoyi ya shiga yi maka ko Ahmad?" "Wallahi kuwa kai dai ka bari, ina jiyo muryar Bagulaji da Aissa suna rabka salati. To amma tunda sun shigo garin ai dole su san koma me ake ciki ai. Mu dai fatanmu shine Allah yasa da zaran Dr Halima ta gama gwaje_gwajenta ta mayar damu asibitin Murtala." Ameen Ahmad" Na ce a raunace. Mun shafe kamar minti talatin muna jiran su Gunsum, suna kira muka fice a masallacin muka koma cikin asibitin. Sai dube _dube muke yi ko zamu hangosu, can wajan ajjiye motoci naji muryar Gunsum yana kirana. "Bulama Babba gamu nan" Juyawa nayi nayi ido huɗu da ƴan uwana, naji sassauci sosai dana gansu, saidai ganinsu ya sake haifarmun da mutuwar jiki ainun. Wajansu muka nufa, suma tawowa suke yi, a hanya muka ci karo . Bagulaji ta zuba mun idanuwanta tana karantata, ni kuma na sauke kaina ƙasa ina murmushin dole. Aissa tuni ta soma shessheƙar kuka. Gunsum yace. "Nifa dama nasan halinki muguwar raguwace, ni banso akayi tafiyarnan dake ba ma. Bagulaji ce ta katseshi da cewa. "Ahmad yaya mai jikin? Cikin inda_ inda Ahmad yace. "Jiki da sauƙi Bagulaji, ya hanya, ya kuka baro mutan gidan kuma?" Tsugunnawa nayi a guiwowina na gaishe da Bagulaji cikin tsantsar mutuntawa. Jikinta a sanyaye salab ta amsa mun, idanuwanta cike da tsantsar tausayina. Miƙewa tsaye nayi, muka yi musabaha da Gunsum, Aissa tana kuka ta gaisheni ni da Ahmad da yake gaisawa da Gunsum. "Muje ku kaimu muga Yahanasun ko zamu samu nutsuwa" Cewar Bagulaji kenan. Gaba mu ka yi mu uku, su suma su Aissa suna biye damu, har zuwa dogon falon da zai sada mu da ward ɗin da Yahanasu take. Babu cinkoso yanzu a falon, sai ɗaiɗaikun mutane da suke zaune a kujera wasu ma a tabarma suke zaune. Ɗakin na leƙa naga masu zuwa dubiya suna ciki. Bagulaji mu shiga ga ɗakinnan" Gaba na soma yi suka mara mun baya har zuwa gadon da Yahanasu take kwance. Hajara bata zaune a kusa da Yahanasu kamar yadda Ahmad yai mata umarni. Tana can gadon ƙarshen ɗakin inda muka ga an cika, wata baiwar Allah sai ihu take yi. Bagulaji da su Gunsum idanu kawai suka bi Yahanasu dashi, kowa jikinshi ya sake macewa mus, babu wanda yayi magana duk suna tsaye jigum dasu. Ahmad wucewa yayi wajan Hajara a fusace, ya finciko hannunta suka dawo inda muke. "Taka_ mai_mai me ke damun yarinyarnan wai, kuimun bayani. Ni duk na ganku a rame ne sosai" Inji Bagulaji wacce tayi Maganar a tsanake. Bani da zaɓi, labarta mata yanda abun ya soma nayi, harxuwa tsintarta a cikin kwata da mu kayi, zuwa kaita asibitin Murtala da mu ka yi, da abunda Dr Ruƙayya ta faɗa a kanta, da batun lakasera da take sha kullum." Salati Bagulaji ta shiga rerawa tana tafa hannayenta, idanuwanta suka cicciko da hawaye. "Yanzu Yahanasun ce ake zargin tana ta'amali da kayan maye, harma ita likitar tace muku waɗannan kwaya suke zubar mata da juna in ta samu? Shine kuka tattagota kuka kawota asibitin mahaukata sabida kuma mahaukatanne ko? A cikin zuriyarmu maza ma ba sui shaye_ shaye ba, sai mace za'ace tana shaye_shaye? Ni nafi danganta lamarin da shafar jinnu gaskiyar magana." Duk dai shiru mu kayi muna kallon Bagulaji sai faɗa take yi. Gunsum yace. "Amman Ya Bagulaji ni ina ganin kiyi haƙuri mu bar likitoci su gama dukkan bincikensu a kanta kafin mu yanke hukunci, tunda shi ma Bulama Babba yace tana shan lakasera kullum, a cikin lakaserarnan samari suke narkar da ƙwayoyi fs suna sha. A koda yaushe halin ɗan adam ka iya canjawa da irin halinshi da kuka sani na baya. Kuma shaye_shaye ya zama ruwan dare a cikin wannan zamanin da muke ciki. Kar ku manta Dr Ruƙayya likitace wacce ta shafe tsawon shekaru tana karatu a fannin ilimin jinya. Kuma ƙila ta daɗe tana aiki, Asibitin Murtala, babban asibiti ne shima, banyi tunanin zasu yi binciken da ba dai _dai bane. Kuma cikinmu babu wanda shaiɗan ba zai iya cin nasara a kanshi ba. Mu yi haƙuri mu ba likitoci dama su gudanar da aikinsu." Wata nurse ce ta ƙaraso inda muke tace. "Lokacin dubiya ya ƙare, zaku iya fita daga waje dan Allah, mutum ɗaya muke da buƙatar gani a nan. Sannan ɗaya daga cikinku ya biyo ni domun yankan kati." Ya Bagulaji ce ta ja kujera ta zauna tana sharar hawaye. "Kuje ni zan zauna da'ita. Yaran du suna gida kenan" Nace mata. E suna gida, ga Yusuf a bayan matar Ahmad Hajara." Hajara ta matsa suka gaisa da Ya Bagulaji ta shafa kan Yusuf, idanshi biyu sai kallonta yake yi. Fita waje mu ka yi, mu ka bar Ya Bagulaji ita da Yahanasu. Gunsum da Ahmad kuma suka je siyan kati. Tabarma Hajara ta ɗakko a ciki ta shinfiɗa musu, ta koma ta kawo musu abincin data dafo. An ɗiba ma Ya Bagulaji abincin ? Na tambayi Hajara. "Na zuba mata amman kaɗan tace in zuba mata. Ga naku kaima ka daure kaci abincin tun safe rabonka da abinci. Aissa ta dubeni cikin yare ta dinga yi mun nasiha. Dole na zauna ta zuba mun abincin, kaɗan naci na sha ruwa. Ina zaune su Ahmad suka dawo. Abincin suma su ka ci. Ana kiran sallar la'asar Hajara ta soma azamar tafiya. Mu kuma muka nufi masallaci mu ukun. Misalin ƙarfe shidda Dr Halima ta shigo asibitin. Muna zazzaune jigum ta shiga ɗakin da Yahanasu take, tana saye da kayan likitoci. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da roƙon Allah yasa ba taɓin hankali Yahanasuna ta samu ba." Fitowar Ya Bagulaji muka gani, dukkanmu muka tashi muka nufeta, sai sharar hawaye take. "Da gaske fa Yahanasu kamar shaye_shaye take yi. Dan yanayin muryarta tafi kama da muryar ƴan maye ba wanda Jinnu suka shafa ba. Amman in dai hakanne wannan yarinya ta ɗakko hanyar tarwatsa mana sunan gidanmu wallahi, zaku ma ta ci ubanta a wajan iyayenta maza. Tunanina yanda za'ayi ma su Ba Bakura jawabi har tunaninsu ya ɗauka, kar Ba Bakura ciwonshi ya tashi nake jin tsoro." Dam gabana ya yanke ya faɗi, kuka Aissa ta fashe dashi tana ambaton Allah. Nima Allah na shiga ambatowa, dan wani irin harbawa xuchiyata ta shiga yi ba ƙaƙƙautawa. Hankulanmu duk ya sake tashi ainun. Da ƙyar muka rarrashi zukatanmu muka nemi waje a benci muka kafa muka tsare, muna jiran fitowar Dr Halima. Su Ya Bagulaji suna zaune a tabarma tana amsa wayar matan gida da suke ta faman tambayarta jikin Yahanasu." MRS BUKHARI CE[13/08, 9:33 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI) 38 Sama da mintuna arba'in Dr Halima ta fito daga cikin ɗakin. Da sauri na miƙe na isa gareta. "Ka same ni a office yanzunnan" Tana gama faɗar haka ta wuce. Ya Bagulaji tace. "Muje mu sameta, su kuma su jira mu, Aissa ta koma wajan Yahanasun. Gunsum yace. "Ya da kin zauna mu muje." "La ba haka mu ka yi da Babanku ba. Yanzu ni suke jira in kirasu in sanar dasu halin da ake ciki. Bulama muje" A sanyaye nayi gaba, tana biye dani a bayana har zuwa ofishin Dr Halima dan muna hangota ta shige wani ɗaki da muke kyautata zaton nanne ofishin nata. Da sallama muka shiga ofishin. Bayan ta amsa sallamarmu ta bamu wajan zama tace. "Mama kece mahaifiyar Yahanasu?" Ya Bagulaji murya a sarƙe tace. "E likita Yahanasu ƴata ce." Kai ta jinjina tace. "Akwai wani abu daya taɓa faruwa da'ita mai firgitarwa ne, ko kuma mutuwar wani na kusa da'ita?" Ni dai nayi ƙuri ina kallon Dr Halima. Ya Bagulaji tace. "E likita shekaru uku da suka wuce an taɓa yi mata fyaɗe. Ina tunanin wannan shine gagarumin abun da zance ya taɓa faruwa a famili baki ɗaya mai firgitarwa ." "Okey an kaita asibiti a lokacin da abun ya faru, ko kuwa a gida aka barta ne" Muƙut Ya Bagulaji ta haɗiyi yawu. "An kaita asibiti, ta samu kulawar duk daya dace ta samu likita. Dan iyayenta maza tsayayyune kuma ƴan boko ne." Dr Halima tace. "Yaya kuma Rayuwarta taci gaba da tafiya bayan ta dawo gida, sannan ya al'umma suka ci gaba da kallonta?, Ta shiga wani hali na tsangwamane" "Sakamakon ta firgita ainun da lamarin daya risketa, ko a asibiti da aka kaita tayi ta fisge _fisge, da yawan firciki, da taimakon Allah da kulawar da likitoci suka bata sai ta samu lafiya, amman an yi ta sauke mata Quri'a. To ko da ta dawo gida sai ya zamana bata son fitowa waje, cikin ƴan uwanta ma bata son shiga. Tayi rama sosai, to ana cikin wannan gaɓar mahaifinta yai mata aure da shi Bulama Babba wannan, dama ɗan uwanta ne." Shiru Dr Halima tayi tana nazari, tayi jim tana kallona, ni kuma duk na gama dibibicewa, tausayin halin da Yahanasuna ta tsinci kanta a ciki a baya ya tsirga mun ainun dan ban taɓa jin wannan labarin ba, tunda dai Mama Gana ta sanar dani an yi mata fyade a lokacin da suka kawo ta gidana, ban sake tayar mata da zancan ba. Dr Halima ta dube ni tace. "Yaya Yahansu ta kasance a cikin gidanka?" Cikin faɗuwar gaba na zaiyana mata ɗan abunda ya kamata ace na sanar mata,na halin ko in kula data tsinci kanta a ciki, kwanciyar hankalin data samu baifi na shekara ɗaya da ɗoriya ba. Shiru kake ji a cikin ofishin ko wanne cikinmu da abunda yake tunani. Haƙiƙa na muzanta a cikin wannan ofishi sosai, duk da nasan ko a lokacin da nake cusgunama Yahanasu ina jin zafi da raɗaɗin ganinta a cikin damuwa. Amman ƙarfin asirin da Zubaina tayi mun yayi mugun tasiri a jikina. Kuma bana wasa da sallolin nafila dana farilla, bana wasa wajan tilawar Qur'ani da azkhar. Wannan ya farune sabida shine ƙaddarata ni da Yahanasu. Allah ka yafe mun, ka bawa baiwarka lafiya ka dubeni. Haka nai ta tattauna maganganu a zuchiyata, amon muryar Dr ne ya sa na ɗago kaina wanda yake baranar ƙonewa tsabar tsantsar chajin daya ɗauka. "To ina ganin sakamakon fyaɗen da akayi mata a baya, shi ya jefata a cikin wannan halin data tsinci rayuwarta a ciki. Sakamakon rashin kulawa da bata samu ba, ko kuma ince tarairaya. Ta kamu da cutar damuwa wacce a turance muke kiranta da (Deepretion) Amman ku baku fahimta ba, sai akayi mata aure, ta jima wannan cutar tana cinta, wanna raɗaɗin na fyaɗen da akayi mata shi ya jata ta soma shan miyagun ƙwayoyi domun ta samama kanta nutsuwa da hutun ƙwaƙwalwa. Tana cikin wannan halin aka kuma yi mata Aure, ta fuskanci matsi a gidan aure, hakan ya ƙara sake jefata a matsananciyar ciwon damuwa, ta yanda ba zata ma iya sarrafa kanta ba. Ciwon damuwa ciwone mai girman gaske, da yake buƙatar a tarairayi dukkan wanda ya kamu da wannan cuta. A dinga kawo shi asibiti yana karɓar magunguna akan kari, likitanshi na bashi kalma mai daɗi. Amman mutane da yawa suna tare da cutukan damuwa ba'a sani ba. Matan aure da yawa sun faɗa cikin harkar shaye_shaye tsundum a sanadiyyar ciwon damuwa, wasu kuma gudun kar su kamu da hawan jini ne. Gasu can duk a cikin ɗakin, kaso saba'in duk shaye _shaye ne ya haukatar dasu, kuma a cikin kaso saba'in ɗinnan kaso hamsin matan aure ne, kaso ashirin kuma yawanci ƴan mata da suka tsinci kansu a cikin jarabawar fyaɗe ko wata tsangwama. Kaso goman daya rage kuma masu shafar aljanune duk muna dasu." Ajjiyar zuchiya ta sauke ta kakkafemu da idanuwanta. Har ga Allah sai naji na muzanta ainun. Lallai Zubaina ta cutar dani da yawa. Yahanasu a cikin irin halin da dama aka kawo ta gidana kenan, amman na kasa bata kulawa balle in san a wanne hali take? Kaico, Allah kana gani ba acikin hayyacina na aikata komai ba, Allah ka kawo mana ɗauki ka dawo mun da nutsuwa da tunanin matata." "To yanzu dai ƙwaƙwalwar Yahanasu ta gama birkicewa tuƙuru. Sakamakon wani magani ko allurar doki da suke yi ma kansu masu ƙarfi, hakanne yasa cikin dake jikinta ma ya fita. Zamu riƙeta a nan asibitin mu bata kulawa tare da ƴan uwanta masu taɓin ƙwaƙwalwa, har zuwa lokacin da zata warke, shekara guda ko ƙasa da hakan. Ku yi haƙuri nasan da ciwo, kuma duk abubbuwan sun faru ne a bisa rashin sanin ita a wanne halin take bayan fyaɗen da akayi mata. Ciwon damuwa cutace da ita ke sarrafa mutum, itama tana kamanceceniya da taɓin ƙwaƙwalwa. Da yawan matan da kuke jin labarin sun soka ma miji wuƙa, sun kashe kishiya, sun ƙona miji, yawanci ciwon damuwa ke ɗawainiya dasu, ya taɓa ƙwaƙwalwarsu ba'a sani ba, ko sun aikata zaku gansu a kafafen yaɗa labarai suna ba da labarin yanda suka yi kisan. Mai hankali ai bazai yi irin wannan aikin ba mata da aka sanmu da taushi. Shaye_ shayen mata ya ta'azzara a wannan ƙasar tamu, musamman a garin Kano ( kuyi haƙuri wannan zancan gaskiya ne. Shaye_shaye yayi yawa a Kano, musamman na mata) Kuka Ya Bagulaji ta fashe dashi, ni kaina hawaye nake zubarwa dan zuchiyata ta riga data tsinke sosai, na kasa sarrafa kaina bansan sanda na soma zubar da hawayen ba. Dr Halima ta ja fasali tace. "Ba kuka zaku yi ba. Ku bita da adda'a dan ƙwaƙwalwata ta taɓu sosai, ta jima tana ta'amali da waɗannan miyagun ƙwayoyin, a hankali _ a hankali har suka ƙarashe rikita mata ƙwaƙwalwarta. Kamar yadda na faɗa muku zamu riƙeta a nan muci gaba da bata kulawa, zata samu kulawa daga ƙarƙashin ofishina in sha Allah. Mutum biyu zasu zauna su yi jinyarta mata, sabida jinyar masu taɓin ƙwaƙwalwa akwai wahala sosai. Sannan akwai lokuta da aka ware na zuwa dubiya, bama son ana yawan zuwa ana ganinsu, sabida hakan wani lokaci ka iya sake rikirkita mana majinyatanmu. Ga wannan takaddar ka fita ka samo mana wannan allurar, bamu da ita ta ƙare, kuma muna buƙatarta da gaggawa, in ka kawo ta sai ka kawo mini. To Allah ya bata lafiya, maman Yahanasu ayi haƙuri." Ina riƙe da hannun Ya Bagulaji muka fita, dan tama kasa tashi sam. Zaunar da'ita nayi a benci, sai faman haki take yi. Ahmad da Gunsum suka shiga tambayata me Dr tace. Sun fahimci ta tabbata Yahanasu na ɗauke da taɓin ƙwaƙwalwa duba da yanda suka ga duk na fice a hayyacina. Takaddar allurar da Dr ta bani na miƙa ma Gunsum. Ka fita ka nemo wannan allurar, bazan iya tafiya ba Gunsum." Da sauri ya amshi takaddar ya fice. Ahmad ya zaunar dani dan ya lura da yanda jikina yake ɓari. Haƙiƙa Zubaina ta cutar da rayuwata. Ta zalunci kowa nawa, amman nasan Allah zai mun sakayya, fit duniya wal akira. Ina dafe da kaina na ji Ya Bagulaji tana waya, na dai ji ta ambaci Wakil, tiryan_tiryan ta soma yi mishi jawabi, take na soma haki, ina ambaton Allah a fili, saitin zuchiyata na dafe bugawa yake yi kamar zai Burma mun kirjina. "Kasan yadda za ka sanar ma Babanninku musamman Innana, wacce daman na barota a cikin damuwa. A taya mu da adda'a. Sannan a sanar ma da Mama Gana halin da ake ciki, in yaso in zaku tawo ku tawo da'ita sai mu zauna mu kula da ita Yahanasun kafin mu ga abinda hali zaiyi." Bana jin abunda Wakil yake faɗa mata. Da haka ta ajjiye wayar tata. Cikin ƙanƙanin lokaci aka dinga kiran wayar Ya Bagulaji, duk ƴan gidane tun tana ɗagawa har ta gaji ta maka wayar a silent, dama ni tuni na" kashe wayata, wayar Yahanasu kuma tana gida. Minti talatin da fitar Gunsum sai gashi ya dawo da ledar allurar ya sayo. Tare dashi muka kaima Dr. Allurar tazo taima Yahanasu da bata ko motsawa. Kallona tayi tace. "Ina ganin ku kam zaku iya tafiya gida, ba kasafai muke son ganin mutane ba. Masu kula da'ita kaɗai zaku bari. Gobe kwa dawo da misalin biyun rana ne kaɗai zaku iya ganinta." Ya zanyi dole haka mu ka yi ma su Ya Bagulaji salllama. Gunsum ya ciro kuɗi ya miƙa mata taƙi karɓa. "Akwai kuɗi a hannuna Gunsum. Ku je abinku. Bulama Babba abunda zan faɗa maka shine ka daure karka bari ciwo ya kwantar da kai, dukan yai mana yawa, dan naga jikinka har rawa yake yi. Ka yi hakuri. Ba Bakura yasa anyi mata sauka jiya. Yau ma za'a kuma yi. Gobe wasu zasu tawo daga can Damaturun, harda Innana. Da mahaifiyarka. Hankulan ƴan Damaturu ya tashi ainun. Mata matam da suke gidan miji duk kowa so yake sai ya zo. Amman Ba Modu yace mota biyu kawai za'a zo dubiya, washe gari su koma. Ku tafi Allah yayi albarka. Ahmad Allah ya bar zumunci sannunku dukkanku da ƙoƙari. Ka gaishe mun da Hajara inai mata ban gajiya." Sallama mu ka yi muka fita. Ahmad ya ja ɗan sahu, mu kuma muna biye dashi a mota har zuwa na'ibawa. Muna shiga layin ana kiraye_ kirayen salla, sai da mu ka yi sallar magriba, mu ka zauna a masallacin ƴan anguwa suna tai mun jajen ashe Yahanasu ta samu lalurar taɓin ƙwaƙwalwa. Nasan aikin Hajara ne uwar kusasu. Ahmad ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba dannewa kawai yayi. Sai da mu kai sallar isha muka kuma nufi gidan." GHANA: ZUBAINA Allah yayi dare gari ya waye. Tun duku_duku hayaniyar bataliyar yaran gidan ta tashe ni a nannauyan baccin da ban daɗe da samun shi ba. Yau da bala'i da masifa ƴan matan gidan suka farka. Wai akan wata tayi ma wata ƙwacen saurayi a cikinsu. Shine suka kaure da damben mafisa, wanda dama a cikin kwana biyun da nazo kullum sai yaran sunyi rikici. Da naji ihun yayi yawa ne na fita a guje. Abunda na gani ya razanani. Walida kamar yadda naji ana kiranta a gidan na gani da wuƙa a hunnunta jini na ɗiga. Yayin da wata farar budurwar da ban san sunanta ba, na hangota a ɗurƙushe dafe da kunnenta jini na zuba. Dan ba duka yaran gidan na san sunansu ba, Allah yayi yawa dasu. Hajiya Kubra da Nabila sai salati suke zabgawa. "Baki da hankaline zaki yanki ƴar uwarki da wuƙa sabida ɗiban albarka. Ashe har yanzu baki dena wannan harkar daban ba. Nabila duba muga kunnen nata." Hajiya Kubra ce tayi waɗannan maganganun a zafafe. Walida tace. "In kika ga na dena daba sai dai in raina ne ya tsaya. Nifa babu matar data isa dani a gidannan danni nake yi ma kaina komai, zaman kaina nake yi. Kullum mahaifiyata tana samun albarka a waya." "Hajiya Kubra, kunnen shingin kaɗan ya fice daga jikinta, ga jinin sai tsananta zuba yake yi dole a kaita asibiti. Amman walida baki kyauta ma ƴar uwarki ba." Walida ta katse hanzarin Nabila da cewa. "Ita da tayi ƙwacen saurayi ba a ce bata yi dai_ dai ba. Sai ni dana hukuntata shine banyi dai_dai ba? Ko da yake dama ba wacce taƙe ƙaunata a cikinku. Kafin ta rufe baki Rashida ta zabgeta da mari tace. "Ki shiga taitayinki wallahi kin gane ko? Akan wani ɗan iska zaki raunata Yayarki dan ba ciki ɗaya kuka fito ba? Nan faɗa ya dawo kan Rashida, faɗan da sai da suka dangana da ƙofar gida, filin tsakar gidan yayi musu kaɗan. Mazan gidan daga masu tsaki, sai masu cewa su kashe kansu talauci da Babansu ya sasu a ciki ne sanadi. Nabila da Bala kuma suka kama wacce aka jima rauni suka nufi asibiti. Ni dai ina riƙe da haɓa ina kallon ikon Allah. Wannan wanne irin ƙaddarren auren ne haka? Gida sai kace gidan kazo nazo gidan karuwai.? Ina cikin wannan tunanin muka jiyo muryoyin maza a waje, sai magana akeyi. Babu shiri muka nufi ƙofar gidan, Rashida ce ta shigo da mugun gudu ta bangajeni na faɗi akan hannuna ɓaras na karye a tsintsiyar hannuna. Wan Rashida ne ya shigo da shegen gudu shima hannunshi riƙe da wuƙa. Yaran gidan suma suka shigo. Duk suka tumurmisheni suka wuce. A wajan Hajiya Kubra ta tafi ta barni ina riƙe da hannayena. Ihun kuka na saka ina faɗin. Ni Zubaina na mutu na lalace ina zan tsoma kaina ne a cikin wannan tsinannen gida, tun asubar fari mun tashi da jarfa.? Miƙewa nayi da ƙyar kafin kace me hannuna ya suntuma har ƙyalli yake yi. Ƙurar faɗan kuma ya lafa. Har wan Rashidan yazo ya fice, ko kallon banza ban isheshi ba, ballantana yai mun sannu. Ɗaki na koma nayi zaman ƴan bori tim a ƙasa ina kukan fitar rai. Ji nake Inama ace mutuwa tazo ta fige mun rai na ko zan huta. Hannu ciwo sai gaba _ gaba yake yi, na rasa me ke mun daɗi. Da ƙyar muryata take fita, sai kiran Hajiya Kubra nake yi da muryata wacce ta dashe sabida yawanta kuka. Labule ta ɗaga tana cewa. "Ni bana mance ma na ganki a yashe a ƙasa ba ɗazu." Bata hadiyi yawu ba taga hannuna yana reto. Ba shiri ta shigo tana duba hannun. "Karyewa kika yi Zubaina?" Wani kukane ya tunkudo mun, ban iya bata amsa ba. "Ki taso mu je gidan madori ya ɗoraki. Amman kina da kuɗi ko kayan kuɗi ko?" Kallonta nayi da mamaki. Murmushi tayi mun tace. "Nasan baki fahimce ni ba, kasancewar ke sabuwar zuwa ce a gidan. Ai Alh iya ci da shayarwa, da kwanciyar aure shine kaɗai yake shiga tsakaninshi da matanshi. Da sallah zai bi matanshi da yaranshi mata da atampa ko yadi kala ɗaɗɗaya. Sai kuma in kin haihu kuma. Amman ko haihuwa a asibiti ba'ayi anan gidan. Duk yawan yarannan iyayensu a cikin gidannan sukai naƙudarsu, wasu sai da suka fi kwana biyu suna naƙuda da taimakon unguwar zoma ta gargajiya. Yace a haka shima mahaifiyarshi ta gama haife_,haifenta. Dan haka in kina da abun siyarwa faɗa mun inda yake in ɗakko miki, in munje ma ba mai ɗorin a madadin kuɗin." Hawayena na share, na nuna mata ƙaramin akwatina da hannuna. Akwai atampata me ruwan ɗorawa ki ciro mun a cikin ƙaramin akwatinnan. Sai mayafina kuma yana kan gado." A gurguje Hajiya Kubra ta ciro, ta taimaka mun ta samun mayafi muka fito. Rashida ta bama izinin kula da yaran gidan da kokkon karin kumallo, kafin mu fita. Munsha ɗan karen tafiya mai nisan gaske. Sakamakon nera biyar da Bama magani, nayi tafiya har ƙafata nayi mun zugi. Gashi ko sallar asuba banyi ba. Muna isa gidan ɗorin muka tarar da layi har mutun uku. Da wata dattijuwa ɗaya, sai yara uku duk suna zaune a wani ƙaton falo suna jiran izini. Mu na zaune aka kawo mana fanke da ruwan lipton. Ni da Hajiya Kubra cin nama mu kai ma fankennan kafin kace kwabo mun lamushe muna siɗe man dake hannunmu. Muna zaune har layi yazo kanmu. Har fitsari sai da nayi a zaune dan azaba. An ɗorani irin ɗorin gargajiya wanda ake jera karere, ya bani wasu garin magunguna na sha, yace bayan sati biyu mu dawo a kwance mini. Godiya mu ka yi mai, muka dire mishi atampar da muka tawo da'ita. Da zazzabi kau a jikina muka shiga gidan, ina shiga na kwanta na shiga rawar sanyi, kafin kice kwabo na soma suma kala_kala. Ciwo nake har bana iya gane wanda yake kaina. "Hajiya Kubra ki kira mun Mamana in zan mutu in mutu a kusa da wani na." Wayata Hajiya Kubra ta kunna tai ma Mama flashing, ba a jima ba kuwa ta biyo kiran. Hajiya Kubra tayi mata bayanin halin ciwo da nake ciki da karyewa da nayi. Mama tace sha Allah gobe zata biyo jirgin safe ta tawo." MRS BUKHARI CE [13/08, 1:11 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (,DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI) 39 Kaduna: Mama. Zirga_zirga Mama ta shiga yi a tabkeken falonta na sabon gidan da suka koma. Tana goye da Maryam yarinyar Musa a bayanta. Ta gama jibgar yarinyar kenan kiran Zubaina ya shigo wayarta. Dama kwana biyu cir tana kiran wayar tata sai ta ji ta a kashe. Wayarta ta ɗauka ta kira Nafisa. Ringin ɗaya biyu wayar ta shiga. "Nafisa so nake ki biya mun jirgin Lagos, daga Lagos in hau jirgi zuwa Ghana. Zubaina bata da lafiya ta samu karaya a hannunta, ko magana bata iyayi, kishiyarta ce tai mun bayanin halin da take ciki. Mijinsu kuma ya tafi kasuwanci." Nafisa tace. "To shikenan Mama bani nan da awa ɗaya zan sa a gama miki komai. Zuwa gobe sai ki tafi. Allah ya bata lafiya, zan kira inji jikin nata. Muma muna shirin tafiya misra kenan, akwai wani semina da Alh zashi can. Uwar gidanshi ma taso ta kunno wuta, kan cewar sai dai itama wannan karon a tafi da'ita. To da yake na samu wajan zama a zuchiyar Alh Mama kar kiso kiga diban albarkar da yayi mata. Har wanke ta da mari yayi a gabana." Shewa Mama ta saka tace. "Shegiya ba, ai gwanda daya nuna mata matsayinki. Kar dai kiyi sake da bin malamai.duniyar ba'a zama haka. Ita kanta Zubaina zanje wajan sabon malamina yai mun aiki in kai mata, in yaso in na dawo na biya shi." Haka dai hirar tasu ta ƙare. Mama na kashe wayar ta saɓi tsadadden mayafinta, da tsadadden takalminta ta rufo ɗakinta, a ƙofar fita suka ci karo da Musa ya fito saga ɗakinshi da yake hanyar waje saɗab_saɗab da budurwarshi yana riƙe da ƙugunta. "Hiye ba shakka Musa. Kai amman wannan yaro kwai kwashasshe. Wato so kake ka cika mun gidannan da yaran shegu ko?" Ta dubi yarinyar data yi tsuru_ tsuru ta nunata da yatsa tace. "Ke kuma inna kuma ganinki a cikin gidannan. Wallahi saina sa Sagiru yayi gunduwa_ gunduwa da namanki ya watsar dan ubanki. Ku kuke lalata mun yaro ko? Fice ki bani waje, kai kuma muje ka rakani wajan malam" Da sauri yarinyar ta fice a gidan. Musa kuma ya bi Mama suka jera. "Musa da kai da Sagiru so kuke in faɗi in mutu ku huta. Jiya_jiyannan fa ƴan sanda har cikin ɗaki suka zo neman Sagiru. Zarginsu ake wai sun shiga Kasuwa sun fasa shagon Alh muttaƙa sun yi sata. Tun jiyan rabon da in sashi a idanuna, ƙila ma yana police station. Shi nemo jafa'i kai nemo fitna. Gashi gobe zan tafi Ghana Zubaina ba lafiya ta samu karaya. Inna dawo zamu zauna ka faɗa mun yarinyar da kake so, sai inje da kaina in nemo maka auren, ko in tura kawunku" "Ni Mama har yanzu ba'a ma haifi matar da zan aura ba. Ki barni kawai aure ba yanzu ba. Kiyi haƙuri zan shiryu. Sagiru kuma ko ɗazu na ganshi a saman katangar gidanmu, harma yace in gaisheki, dama lafiyarki yazo dubawa." Da wannan hira har suka isa gidan Malam, kai tsaye akai musu iso suka shiga. Malam yana zaune a kan buzunshi. Ta kwararo mishi bayani akan Zubaina da mijinta. Da kuma Musa da ɗabi'unshi. "Jummai babu matsala, akwai rubutu mai zafi da zanyi mata a allon ƙarfe, za'a wanke da ruwan gawa. Da daddare ki turo Musa ya karɓa miki, sai ya karɓi nashi shima." Mama na yashe baki tace. "Godiya muke Malam Allah ya ƙara girma. Sai dai malam kafin alƙalamin sai in na dawo zan bayar dai." "Haha Jummai ai babu komai an riga da an zama ɗaya" Sallama su kai mishi, suka fito, daga ƙofar gidan Malam kowa ya kama gabanshi dan ba gida zasu ba dukkansu. BULAMA BABBA: Tunda mu kai sallama muka shiga cikin gidanmu. Matan gidan su kaita tambayata yanda na baro mai jiki. Gunsum kuwa sai ƙarema gidan kallo yake yi yana faman jijjiga kanshi. Tsaya bari in shinfiɗa mana tabarma, ko in ɗakko mana katifa muyi kwanciyarmu a tsakar gida, ɗakin ba shiguwa yake yi ba. A tsaye cike da ta'ajibi na bar Gunsum. Ahmad ma ya wuce ɗakinshi, ina jiyoshi yana rangaɗama Hajara kira. Leƙowa cikin ɗakin namu Gunsum yayi. Hawaye naga yana sharewa. Ni kuma na ɗaga katifa zan fitar mana. Hannuna Gunsum ya kama cike da rauni yace. "Bulama Babba, yanzu a cikin irin gidannan da ɗakinnan kuke rayuwa harda yaranku. Dama haka rayuwa tayi da ku Bulama Babba, aikin gandirobar da kake yi ka dena ne, naji Ahmad yace ɗan sahunnan naka ne kake tuƙawa ka nemi kuɗi? Meye amfanin zumuncinmu, meye amfanin dukiyar da muke dashi? Dukkanmu muna cikin rufin asiri, amman jibeku a cikin damuwa da ƙunci, da talauci. Bayan mu ka bamu kulawa da soyayya, ka bamu kariya dukkanmu. Me yasa Ba Bakura ya ɗauki zafi da kai haka har ya kasa yarda mu tallafa muku?" Idanuna na ƙura mishi ina nazarinshi. Ni kaina kukan nake son dama da hali inyi ko zan ji daɗi amman ni babba ne. Dafashi kawai nayi nace. Haba Gunsum, ai baku bane gaba dani, nine gaba daku, ni yafi cancanta in tsaya muku ba ku zaku tsaya mun ba. Batun aiki kuma, mun jima da aka sallamemu a aiki, lone muka ɗauka na ɗan sahu muna fita aiki, muna cin abinci. Yahanasu tana zuwa aiki, sannan tana sana'ar sai da kayan ruwa kaga firjin dana siya mata. Kusan ita tai ta ɗaukar nauyin komai na gidan, har sutura ita ke siya mini. Ni kuma saina koma makaranta nayi mastas ɗina, yanzu haka jarabawar ƙarshe muka zana. Kuma harna samu gurbin koyarwa a Jami'ar Bayero. Dai_dai lokacin da na samu nutsuwar da zan kula da Yahanasuna wannan abun ya kunno kai. Gunsum Ba Bakura yana da gaskiya kuma ya fiku sona. Nayi imani a hanya yake son ya ɗaurani mai kyau, ba gashi munata rayuwarmu ba. Ai ni iyakar yafemun kura_kuraina da yayi wallahi Alhamdulillah" Gunsum yace. "To amma Bulama Babba!. La kar kace amma, fitar da katifarnan bari in ɗakko maka kunun zaƙi" Katifar ya ja ya fitar, ni kuma na ɗebo mana kunu gora biyu na fito. Hayaniyar Ahmad na dinga jiyowa daga ɗaki yana rikici da Hajara. Ba shiri na isa ƙofar ɗakin nace. Ahmad kaima Allah ka rabu da'ita kayi haƙuri haka nan ya isa." Leƙowa yayi yana kumfar baki yace mun. "Daga shigowata dan nayi mata maganar me yasa tai ta yayata lalurar data samu Yahansu. Sai fa kawai ta dirarmun, har tana mun tafi sai kace muna Lagos, bansan me yasa surutun Hajara yayi yawa ba munafukar yarinya" Kai na girgiza nace Bai kamata ka biye mata ba. Kayi haƙuri maganar ta wuce hakanan kar ku tashi yaran a barci." Hajara ta iso inda muke tana sababi kamar zata ari baki. "Baka isa wulaƙantani akan wata banza ƴar shaye_shaye ba. Waye bai san shaye_shaye take yi ba. Kullum cikin narka ƙwayoyi a lakasera take. Ahmad ni na gaji da aurenka ka sake ni in huta." Shiru nayi ina nazarin maganganun Hajara. Sai naji take na gasgata maganarta kullum Yahanasu a cikin shan lakarera take, babu ranar da bana ganin gorar lakasera a jakarta, kenan Hajara tasan Yahanasu tana shaye_shaye kenan? Jikina a mace na dubi Ahmad wanda yake shirin marin Hajara. Ga matan gida har sun soma zuwa ban haƙuri. Haba Ahmad ka rabu da yarinyar nan dan Allah, karka damu da abunda take faɗa." Wucewa nayi na barsu nan na shige ɗaki. Nan na shiga binciken kayayyakin Yahanasu, ban samu komai ba, jakunkunanta na bincikesu babu komai a ciki. Jiki ba ƙarfi na fito na samu su Ahmad a waje yana zuba musu miyar tuwo. Kallona Ahmad yayi yace. "Ya dai kar dai maganganun Hajara ne yayi tasiri a jikinka? Zo ka zauna kar kace komai kaci tuwonnan kasha magani tukunna" Zama nayi Ahmad ya tusani a gaba sai da naci tuwonnan da yawa, ya bani magani nasha. Gunsum dai baya cewa komai in banda tagumi da yayi yana kallona. Ahmad yace. "To Alhamdulillah naji daɗi daka daure kaci abincin. Gunsum muci tuwo, abincin namu sai haƙuri babu kifi ba nama, sai daddawa da tafarnuwa." "Yaya Ahmad baku kyauta mana ba, da kuka ɓoye mana halin da kuke ciki. Yanzu munanan cikin wadata ku kuna cikin rayuwar ƙunci. Jibi gidan da kuke zaune, da anguwar da kuke shi kaɗai tashin hankali ne mai girma." Dariya Ahmad yayi ya saka lomar tuwo a bakinshi, sai da ya tauna ya haɗiye, yana lasar baki yace. "Gunsum kenan, ai rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki sai dai muce Alhamdulillah. Tunda bamu taɓa barin iyalanmu cikin yunwa ba. Yaranmu kuma suna zuwa makaranta ta dai_dai ƙarfinmu. Gunsum ita rayuwa ai juyi_juyi ce, mu kanmu bamui tsammanin zata juya damu haka ba, khairan in sha Allah. Bismilla kaci tuwo da zafinshi kasha kunu. Mijin tace ne yayi kunun zaƙin fa. Har goruna shi yake wanke mata a tsakar gidannan, mata suita zinɗensa. Murmushi kawai nayi musu, Allah sarki Ahmad aminin arziki kenan ( KAMAR AMINU DA SAMINU) Bayan sun gama cin tuwon Ahmad yace. "Ya batun kwanciya fa Bulama, a ɗakin zaku kwanta ko a tsakar gidan? Naji cikin da zafi, ga ba wuta" A tsakar gidan zamu kwanta Ahmad. Shi ya kwanta a katifar, ni wannan daddumar ma ta isheni." Ni dai a cikin wannan daren, babu wani bacci dana samu damar yinshi. A sallaya na kwana ina nafilfili da adda'ar samun lafiyar Yahanasu. A cikin kunnuwana akayi kiran sallar farko na assalatu. Ahmad da Gunsum na jira su kai alwala muka nufi masallaci. Bamu muka baro masallaci ba, sai da rana ta fito mu kai nafila raka'a biyu, mu kai addu'o'i sannan muka fito. Ahmad kayi ƙoƙari ka tafi aiki yau, ni kuma zan kai kekena wajan parking. Nagode matuƙa gaya." "Bulama ka wuce haka a wajena. Akwai abinci a gidan wanda zasu ci yau. Zan tsaya tare da kai zuwa gobe, muga yanayin farkawar tata. Kuma kaga yau ƴan Damaturu zasu iso, nasan dole kana buƙatata a kusa da kai. Muje wajan mai waina mu siya ko?" Gunsum yace. "To muje sai a siya harda yaran. Wainar dubu biyu Gunsum ya siya mana. Muka koma gida, Ahmad ya kaima su Hajara da yaran nasu. Mu kuma muka ci namu. Ni da Ahmad ne mu ka yi wanka, muka sake kaya. Gunsum yaƙi yin wanka, nasan bazai iya ba dan yana da ƙyanƙyami. "Yaya Ahmad ga dubu biyar ɗinnan aba Anti Hajara tayi ma su Mama Gana girki dan Allah. Karɓar kuɗin Ahmad yayi ya koma ɗaki. Mu kuma muka fita dan jiranshi a cikin motar Gunsum. Bai jima ba, sai gashi da filas ɗin ruwan zafi. A hanya Gunsum ya saima su Ya Bagulaji lafiyayyen abinci a restaurant muka kai musu. A barandar kusa da ɗakin da Yahanasu take ciki muka samesu. Ya Bagulaji tana kwance a tabarma. Aissa tana waya ganinmu yasa ta kashe wayar ta miƙe ta karɓi ledar hannun Gunsum na take away ɗin su, da filas ɗin tea ɗin hannun Ahmad. "Sannunku da zuwa Yaya Ahmad, Bulama Babba, Gunsum. Kun tashi lafiya?" A tare duk muka amsa mata. Jin muryoyinmu yasa Ya Bagulaji ta tashi. Cikin ladabi muka gaisa tare da tambayarta mai jikin. "Hmmm jiya munga tashin hankali sosai Bulama. Yahanasu ta farka misalin ƙarfe ukun dare. Tai ta bige_bige tana dariya, da wasu irin sambatu marasa daɗin ji. Tana ta batun cikinta wai bai zube ba ko, tana tambayata. Bafa ta dena surutai ba, har sai da akayi mata allura bacci yayi awon gaba da'ita. Ko abinci bata samu taci ba, sau biyu Aissa na zuba mata abincin tana ɓararwa. Haka ɗai ɗakin ya kasance, kowa naji da ƴan uwansu marasa lafiya. Kai wannan yarinya ta bani tausayi. Yanzu haka zamu zuba idanu muita kallon Yahanasu a asibitinnan?" Kaina ne ya sara mun, dama ciwo yake yi mun kamar zan zauce ni kaina. Wannan mummunan labarin ya sake rikirkitani ainun. Magana wannan na kasa. Sai binsu da idanuwa nake, suna ta mai da zance. "Ya Bagulaji ga abincin kari nan ku karya. Su Wakil sun taso ne?" Cewar Ahmad. Ya Bagulaji tace. "Ai hankula yaƙi kwanciya, tun kafin asuba tayi suka ɗakko hanya, sallar asuba ma a hanya zasu tsaya suka yi. Ku je ku ga Yahanasun. Ya kamata ka kawo mata kayan sawa ko?" To Ya Bagulaji za'a kawo. Miƙewa nayi su Ahmad suka mara mun baya. Da wata nurse muka ci karo, kamar wajensu Ya Bagulaji zata je. "Yauwa bawan Allah kamar kaine mijin Yahanasu ko?" Cikin sauri na ɗaga mata kai. E nine lafiya?" "E lafiya dama ta farka ne, ya kamata tasa wani abun a bakinta, kuma za'ayi mata allura da bata magunguna, dole sai da nata a kusa, dan duka take yi sosai. Juyawa tayi muka bi bayanta. Tun daga bakin ƙofa nake jiyo ihun Yahanasu tana. "Ku rabu dani, juna biyu ne fa dani, ku barni ni bazan sha komai ba, banason nayi ɓari. Sauri_sauri gudu_ gudu na isa bakin gadon da Yahanasu take nasa hannuna na riƙeta, na kalleta ta canja kamar ba ita ba. Sai surutai take yi, can kuma tayi shiru hawaye na kwarara a gurbin idanuwanta. Sai da ta samu nutsuwa nace Gunsum kira Aissa ta tawo da abincinta maza. Tashi ki zauna Yahanasuna" Tana kuka tace. "Nifa lafiyata ƙalau me yasa aka kawo ni nan?" Tambayata take yi. Zasu sallameki yanzu. Kici abinci tukunna." Kai ta ɗaga mun halamar to. Aissa ce ta iso da take away da kofin tea mai madara. Zama nayi na dinga bata jallof ɗin shinkafar wacce taji kayan lambu. Tas ta cinye, shayinma tas ta shanye shi. "Na gama a sallameni to?" Ta faɗa tana ƙara kafe ni da idanu. Sai kuma ta fashe da kuka. Maganin na narka a cikin kofi na ɗura mata. Nurse kuma tayi mata allura guda biyu. A hannuna tayi bacci, na gyara mata kwanciyarta, na rufeta. Tsuru nayi ina sauke ajjiyar zuchiya, baccin magani take yi mai nauyin gaske. Kowa yayi shiru da abunda ko wannenmu yake ƙissimawa a zuchiyarshi. Haka nursses ɗinnan su kai ta bi gado_gado suna bama marasa lafiya magani, wasu da allura wasu babu allura. Sai da suka gama tsab, suka ce mu fita mu basu waje, su samu su huta a tsanake, basa son hayaniya. Haka muka dawo wajen Ya Bagulaji muka zauna. Gama karyawarta kenan. "Yanzu nake son in biyoku, Yaya akayi, taci abincin kuwa?" Taci Ya Bagulaji, ni sha'anin jikin nata ya tsorata ni. Ni ina ganin a sake mata asibiti zaifi. Amman bari su Ba Modu su iso muji wanne hukunci Ba Bakura ya yanke a kan lamarin." Ya Bagulaji tace "Hakane nima zuwan iyayen naku nake jira, inji me zasu ce. In sunce a barta ai shikenan, in kuma suka ce mu sake mata asibiti shikenan. Suma Dawanau suna iyakar ƙoƙarin su, tunda daga gari_gari suke amsar marasa lafiya. Da dama sun warke an sassallamesu. Yanzu jiya wata baiwar Allah da take jinyar mahaifiyarta gadonsu na kallon namu. Cemun tayi sanda ta kawo mahaifiyarta daga Jigawa har ɗaɗɗaureta akeyi a jikin ƙarfen gado. Makarai ke damunta. Amman baka ga jikin nata yanzu yanda yayi kyau ba. Watansu huɗu yanzu suna jinya. In kaga uwar ba kace ma marar lafiya bace. Sai in hira kuka soma zaka ji tana sakin layi a wasu wajajan. Mu yi ta adda'a." Haka mu Kai ta zama a asibitin. Ana dab da azahar su Ba Modu suka iso. Muna zaune sai muka gansu tafe. Ba Bakura da Ba Modu suna gaba. Ya Innana da Hajja, da mana gana suna biye dasu. Sai su Dala da wakil, da da Yanunu da Fandau, da Yurom babban ɗan Mama Gana. Da sauri muka tashi muka nufesu. Ko wanne ka kalla a cikinsu suna cikin damuwa. Musamman Ya Innana idanuwanta duk sun koɗe. Ba Bakura ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Kuyi mana jagora zuwa ɗakin da Yahanasun take." Ahmad yace. "Ba Bakura da saura kaɗan kafin aba masu zuwa dubiya izinin shiga. Ku zauna ku huta kafin lokacin yayi. Da zaran anyi azahar zasu buɗe ƙofa." Zama matan su ka yi a tabarma. Mazan kuma muka zazzauna a benci. Nan aka shiga gaggaisawa. Ba Bakura yace. "Naji duk abunda Dr tace akan Yahanasu. Nayi mamakin yanda Yahanasu ta tsinci kanta a cikin wannan yanayin. Shaye_shaye a cikin zuriyar gidanmu. Kuma ma ba namiji ba mace. Ina ɗumbun ilimin da muka ba Yahanasu ya tafi? Qur'ani shine maganin dukkan wata damuwa, me yasa bata riƙe kanta ba. A kanta aka fara fyaɗe ne ko a kanta aka soma shiga ƙunci? Ta tabka kuskure babba yarinyar nan, kuma ta kasa sanar ma da kowa halin da take ciki har sai da wankin hula ya kaita dare. Shikenan ai yanzu gashi abunda ta jawo mana ta gama zubar mana da kima da darajar gidanmu." Haki ya soma yi, idanuwanshi na zubar da hawaye duk yabi ya rikice yana shirin fita a hayyacinshi. Ba Modu yace. "Bakura kayi haƙuri ka dena wannan hawayen ya'isa haka. Ni ina ganin adda'a ya dace mu yi ma Yahanasu, tunda abunda ya faru ya riga da ya faru. Ta shafa mana baƙin fentin da bazai taɓa gogewa ba, wallahi ji nake kamar in haɗiye zuchiyata in bar muku duniyar ko zan samu sassauci. Ka duba duk tarbiyyar da muka bata sai ta ɓige da shaye_shaye. Ace Ɗiyata aka samu da shan miyagun ƙwayoyi masu gusar da hankali?" Ba Bakura ya riƙe hannun Ba Modu gam yana sharar hawaye yace. "Duk abunda ya samu Yahansu wannan yaron shine silar komai daya kwaso mana bare ya cakuɗa mana ita da zuriyarmu. Da ace sanda muka hanashi auren Zubaina ya haƙura ya janye duk haka ai bazata faru ba laifin Bulama Babba ne, ya azabtar da Yahanasu ainun. Yarinyar da muka aura mishi ita tana cikin ciwon damuwa, da ace ya kula da'ita da mance komai zata yi. Allah kaɗai yasan irin azabar daya gana mata harta tsunduma kanta harkar shaye_shaye, ya ba zata shiga mummunan hali ba? Muma fa yaronnan sai da yasa mu rama da rashin bacci, ballantana Yahanasu yarinya muma harda laifinmu Modu da muka ɗau dokin zuchiya." Ƙasa nayi da kaina nayi shiru gabana na dokawa. Mama Gana ta sake ruruta lamarin ta hanyar dawo da bara bana. "Shine kam sila. Muma ya wulaƙantamu balle Yahanasu. Zubaina waye bata mulkaba a cikinmu. Yaronnan a ranar da zamu dawo Damaturu sassafe ya fice a gidan ya barmu. Ya ba mai gadin gidanshi kuɗi ya bamu. Tunda ya ɗaukemu ƙwaɗayayyu kamar dangin shegiyar tsohuwar matarshi mai idon cin nera. Bulama ka cucemu mu kam gaskiya. Aurenka da Yahanasu bai amfana mana komai ba, sai baƙin ciki da ci baya da aka samu." Kuka ta fashe dashi har tana buga ƙafa. Da idanu kawai na dubeta an rasa wanda zai rarrasheta. Hajja naga ɓacin rai sosai a fuskarta amman bata ce da kowa komai ba. Ya Bagulaji tace. "Haba ku tausayama yaronnan kar kusa ya zauce mana. Ku duba yanda ya rame ya fice a hayyacinshi. Ku dubi shigarshi mana. Wancan abinda ya faru ai ya farune a bisa ƙaddarar da babu makawa sai ya faru. Ku sani Allah shi ya shirya ma Bulama Babba rayuwa. Har ya shinfiɗa aurenshi da Zubaina da zuriyar da suka tara tare. Yaronnan yarone mai cikar kamala da hankali. Gashi da son ƴan uwa da dangi baki ɗaya. Cikinmu babu wanda baiyi alfahari da Bulama Babba ba. Wannan yana daga cikin ƙaddararshi. In ba'a rarrasheshi ba, bai kamata a ga laifinshi ba ni a tunanina. Ba Bakura kayi haƙuri ku bi su da adda'a, zancen tuna baya ma bai taso ba" Jikin kowa ya mace mus, da dukkan halama zantukan Ya Bagulaji ya shigesu, nan suka shiga ƙaremun kallo cike da tausayi. Ina hango sona da ƙaunata a idanun Ba Bakura, ya jima bai mun irin wannan kallon ba. Ni kuwa jikina rawa yake yi na zazzaɓi sosai. Ana cikin haka aka fara kiraye_kirayen sallah. Tare mu ka yi sallah dasu a masallaci. Muna dawowa muka samu an bada izinin masu dubiya su shiga. Kai tsaye ɗakin muka wuce tare da su Ba Bakura. A cikin ɗakin muka tarar da su Ya Innana suna tsaye. Yahanasu tana kwance idanunta biyu, sai kallon kowa da kowa take yi. Ba um ba um um. Ba Bakura ya isa kusa da'ita ya dafa kanta a hankali yana ƙare mata kallo. Murmushi tayi mishi bayan ta kalleshi. Shima sai ya sakar mata murmushi, ga hawaye na bin kuncinshi. "Ku bani ruwa a kofi inyi mata tofi." Ya faɗa yana duban su Aissa. Ya Innana ce ta matso da kofi a hannunta ta bashi. Jigum tayi tana kallon Yahanasu, sai hawaye take sharewa kawai bata iya magana sam. Tofi Ba Bakura yayi mata a cikin ruwa ya ɗagata zaune ya bata ta sha. Wanda yai ragowa ya shafa mata a fuskarta da hannayenta, har cikin gashinta. Kallon kowa yayi ɗai _ɗai yace. "Salati goma ga Annabi. Ku ɗaga hannayenku muyi ma marasa lafiyar dake ɗakinnan adda'a Allah ya yaye musu lalurar dake tattare dasu." Dukkanmu kowa ya ɗaga hannayensa muka soma amsa addu'ar da Ba Bakura yake ragargazowa. Dukka ƴan ɗakin suma suka ɗaga hannu sukai ta amsawa da ameen Ameen. Yafi minti sama da talatin yana adda'a kafin daga bisani ya sauke hannunshi bayan mun ƙare da salatin Annabi kamar yadda muka soma dashi. "To mu kam zamu koma gida. Amman ya yanayin kulawar da ake basu yayi dai_dai ko kuma zamu tafi da'ita can Damaturun ne ayi mata magani acan?" Ahmad ya amsa da cewa. "Ba Bakura ga abinci can Hajara ta kawo yanzu naku ne. Dangane da batun kulawa kuma, agaskiya likitocin suna iyakar bakin ƙoƙarin su wajen kulawa da marasa lafiyansu. Kuma ana samun ci gaba sosai. Kasan sha'anin ƙwaƙwalwa sai a hankali. Amman ni ina ganin a barta a nan ɗin in sha Allah, addu'arku muke nema." Ba Bakura yace. "To shikenan Allah yayi muku albarka ya haska gabanku da bayanku baki ɗaya. Ya raya muku zuriyarku. Ku kula da zumunci da haɗa yaranku auren zumunci. Ko bayan ƙasa ta rufe mun idanu Bulama ka riƙe Yahanasu da daraja. Ka kula da ƴan uwanka ka kula dasu Bulama. Modu Hajja sai mu kama hanya ko? Mama Gana da Bagulaji zasu ci gaba da kulawa da Yahanasu, ku kuma duk zamu koma tare zaman bai da amfani azo a tare a asibiti. Kuɗi ya zaro rafa biyu ya miƙa ma Mama Gana. Nima ya miƙo mun rafa ɗaya, ya ba Ahmad rafa ɗaya. "Duk abinda ake buƙata ayi a cikin waɗannan kuɗaɗen. Bulama zan sa ƴan uwanka su turo da nasu taimakon ta asusun bankinka, maza da matansu. Ku da kuke nan zan soma daku, gwargwadon abunda Allah ya hore muku ku taimakawa ɗan uwanku. Na janye daga maganata ta baya. Ku haɗe kanku, kuci gaba da shawartar ɗan uwanku a kan duk lamarinku dan ni tawa ta ƙare bana jin zanga wannan abun kuma in ci gaba da nunfashi, Yahanasu ta karyar mun da zuchiyata. Modu kaima ka saka idanu sosai akan sha'anin zumunci ko bayan babu ni. Muje su matan suci abincin sai mu kama hanya." Mrs Bukhari ce [13/08, 3:52 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 40 Ba Bakura sai da ya zagaye duk marasa lafiyan dake cikin ɗakin ya gaishesu tare da basu dubu goma_ goma. Sannan muka fito baki ɗaya, Mama Gana kuma ta zauna tare da Yahanasu tana bata abinci a baki, lokacin shan maganinta na rana yayi. Kayan sawarta da Hajara ta kawo mata na shigar musu dashi. Ga kayan sawarta, zan siyo hita ko kettle sai a jona mata ruwan wanka tayi, ko zata ji daɗin jikin nata." Karɓan kayan Mama Gana tayi, taci gaba da ba Yahanasu abinci. Ni kuma na koma wajan su Ba Bakura. Yusuf yana kan cinyarshi yana mishi wasa. Kallona Ba Modu yayi yace. "Zamu tafi da Yusuf a rage ma Ahmad da Hajara ɗawainiya. Sai nake ganin tunda mijin Fandau ya fita ƙasar waje yin cous ina ganin itama a barta ta zauna tare da su Bagulaji tunda bata da goyo. Zan faɗa ma mijin nata. Ko girki da shirya yara ta taya Hajara. Sai su dinga yin aikin gidan tare. Su kuma su Mama Gana su dinga kulawa da Yahanasun. Ko me kace Bakura?" "Hakan ma yayi, tunda ba yanzu mijin nata zai dawo ba, sai nan da watanni shida. Yaran kuma dama a ɓangaren kakanninsu suke zama. Amman kirashi yanzu muji daga gareshi tukunna." Ba Modu baiyi wata_wata ba ya doka ma mijin Fandau waya. Bayan ya ɗaga suka gaisa ya tambayi mai jiki. Sai ya shigo mishi batun zaman Fandau dan ta taya su Balaguji jinyar Yahansu. Nan take ya amince ma Ba Modu da buƙatarshi. Godiya yayi mishi su ka yi sallama, Ba Modu ya ajjiye wayar. "To ya amince Bakura. Sai mu barta ɗin ta dinga yi musu girki tana taimakon Hajara." "To shikenan Allah yayi albarka duka. Mu zamu tafi sai in an kwana biyu zamu sake zagayowa in sha Allah. Allah ya bata lafiya." Dukka muka ɗinguma wajan motocinsu domun musu rakiya. Ba Bakura sai nasiha yake yi mana mai kama da wasiyya. Yana hawaye motarsu ta soma tafiya, sai albarka yake shi mana yana share hawaye. Ni kaina a take naji hawaye na zuba a kan kumatuna. Gani nake kamar bazan kuma sa Ba Bakura a idanuna ba. Ahmad yaja hannuna muka koma ciki su Fanda suna biye damu a baya. Cikin ɗan lokaci na dinga samun Alert daga ƙannena, ko wanne yayi iyakacin ƙoƙarinshi. Kai kawai na shiga girgizawa ina ambaton Allah. Haƙiƙa ƴan uwana suna ƙaunata ƙauna mara algus. Allah ya isa tsakanina da Zubaina data shigo rayuwata ta tarwatsamun. Ktile muka siyo da bokitin wanka. Nan da nan Mama Gana ta jona ruwan zafi, ta taimakawa Yahanasu ta tsabtace jikinta tas. Suna fitowa Mama Gana ta taimaka mata ta sake kayanta. Wanda ta cire ta saka a bokitin ta fito ma da Fanda ta wanke. Haka dai muka kuma wuni a asibitin cir sai magriba mu kai ma Mama Gana da Ya Bagulaji sallama muka tafi da Fanda. Ko da Fanda ta shiga ɗakin ƴar uwar tata sai ta saki kuka. Haƙuri na dinga bata kawai dan bani da wani ta cewa. A waje na kwanta, Fanda kuma suka kwana a ciki ita da yaran. Da sassafe ta tashi da aikace_ aikacen ɗakin Yahanasu itace harda kwalima. Fita nayi na barta na fita inyo cefanen abincin da za'a dafa ma ƴan asibiti. Ahmad kuma sassafe ya fita aiki yau. Fanda: Tana bakin ƙofar Yahanasu tana shafa ma Maryam mai, Matan gidan suka iso inda take aka gaggaisa tare da tambayar mai jikin. Maman Hassan tace. "In zaku tafi asibiti muna son zamu biku muje mu duba Umman Maryam. Uwatale ƙawarta ma tace in zamu je muyi mata magana zata bimu. Fandau tace. "Sai dai ko zuwa azahar ku tawo tare da Anti Hajara, sabida ƙarfe biyu ake iya shiga dubiyar. Ni kuma yanzu zan kammala in koma asibitin. Maman Iklima tace. "Iko sai Allah. Muryarku ɗaya da umman Maryan. Ke ƙanwarta ce?" "E uwa ɗaya uba ɗaya ma." Nan suka shiga ɗan mata tambayoyi a fakaice. Ganin ta haɗe raine yasa suka watse a ƙofar ɗakin. Shirya su Bawa tayi tsab suka saka kayan makaranta, suna zaune a tsakar gidan. Bulama Babba ya shigo kici_kici da kayan cefanen abinci. Bulama Babba: "Fanda ga kayayyakin abinci nan na siyo. Sai ki yi abunda kika ga ya dace. Ban samu nama ba yayi safiya, amman na siyo ɗanyan kifi kiyi amfani dashi. Bari in yo wanka kafin ki gama." Ɗaki na shiga na ɗebi ruwan sanyi cikin bokiti naje na watsa ruwa na fito. Ina ɗaki ina sa kaya naji Fanda na kiran sunana wai ana nemana. Kayan na ƙarasa sakawa na fito tsakar gidan. Wata mata na gani a tsaye. Gaisawa mu ka yi take shaidamun ita abokiyar aikin Yahanasu ce. "Allah ya bata lafiya. Dama akwai maganar data kawo ni dangane da gidan da Yahanasu take ginawa ne dama. Ganin wannan lalurar ta sameta shine nace bari in zo in sameka, tunda kaine mijinta sai in danƙa maka takaddun gidan a hannunka, da takaddun suna hannunta ma, daga baya kuma ta kawo mun tace in adana mata." Da mamaki na dubi matarnan. Ganin Hajara ta dena aikin da take yi tana kallonmu yasa nace. Fanda ki shigo da'ita ciki muyi maganar a zaune zaifi" Komawa ciki nayi, su kuma suka shigo tare. Nan wannan baiwar Allah ta zayyanamun komai dangane da siyan fili da Yahanasu tayi, da gama ginin da tayi, buga rabta da ƙofifi ne kawai ya rage mata. Takaddun ta miƙo mun. Nasa hannu na karɓa jikina a mace, ina jinjina girman tunanin Yahanasu. Allah sarki baiwar Allah, ashe gida take gina mana a ɓoye ba tare da ni na sani ba. Allah yai miki albarka ya baki lafiya ki dawo muci gaba da rayuwarmu mai daɗi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace da wannan matar. "Nagode sosai baiwar Allah. Ko zan iya sanin a inda ginin yake dan Allah. Sannan meye sunanki?" "Zaka sani sosai ma. Ko yanzu ai sai in rakaka muje. Sunana kuma Binta." Godiya mu kaima Binta mai yawa. Nasa Fanda ta karɓi number ɗan uwanta da tace shi ke kula da ginin. Nace zuwa yamma zamu je muga wajan. Sallama tayi mana ta tafi. Fanda kuma ta gama girkinta ta zuba na ƴan asibiti ta zuba mun nawa, ta zuba na yara . Ni abincinma ba shiga yake yi ba. Bakina ba daɗi sam,ko bacci bana samu, babu kwanciyar hankali da nutsuwa a tare danu sam. Haƙiƙa Yahanasu ta zama wani ɓangare na rayuwata, ina mata son da bashi da iyaka. jiya cike da mafarkan Ba Bakura na kwana. Wayata ce ta shiga kuka ina ɗagawa naga number Ba Modu ne. Da sallama na soma. Sai naji muryar Ba Modu cikin tashin hankali. Ras gabana ya faɗi, jikina ya riga daya bani mai afkuwa ta afku akan Ba Bakura. Ai kuwa hakanne, abunda Ba Modu ya kira ya sanarmun kenan. "Allah yayi ma Bakura cikawa yanzu Bulama. Sai kayi hanzarin tawowa. Su kuma iyayenka zasu zauna su kula da Yahanasu, amman anan muna buƙatarka." Salati na soma yi, hawaye na wanke mun fuskata, jikina take ya shiga rawa. Fanda ta shigo a dibibice, ganin halin da nake ciki ne ya tilasta mata fasa ihu. Tana faɗin. "Shikenan Ba Bakura sa'i yayi. Dama ni nasan wasiyya kake bamu. Jikina ya bani mutuwa zakayi shikenan." Lokaci guda Fanda ta tara mana mutane, matan gidan duk suka tawo suna tambayar abunda ke faruwa. Ahmad na kira na sanar dashi halin da ake ciki, yace mun gashinan dawowa zamu tafi tare. Cikin minti goma sha biyar Ahmad ya dawo. Sallamar Hajara yayi da kuɗin cefane. Muka kama hanyar asibiti. Har muka isa asibitin Fanda kuka take aikin yi. Su Bagulaji ma a irin halin da muka tarar dasu kenan an rasa me ba wani haƙuri. Ni kuwa kukan nake son inyi, amman ya ma ƙi zuwa. Bakin gadon Yahanasu na tsaya na shafi fuskarta, sai lokacin hawaye ya zubo mun. Sumbatar bakinta nayi na fita a ɗakin, sai baccinta take yi. "Mama Gana mu kam zamu kama hanya. Jirgi ma nake son mu hau zuwa Yobe sabida mu samu jana'izar. Ku dena kuka ku yi mishi adda'a." Sallama mu ka yi musu a gaggauce muka isa filin jirgi na malam Aminu Kano Airport. Ghana: Zubaina. Cikin raɗaɗi da azabar da ban taɓa jin kwatankwacinta ba na kwana. Tsabar ciwo har zabure_zabure na dinga yi. Rashida ce ta kwana dani. Da safe Nabila ta shigo hannunta riƙe da kofin kokko ta dure a ƙasa, ta nemi waje ta zauna. "Sannu Zubaina ya kufan jikin naki. Naga hannun kumburin yayi yawa." Rashida tace. "Ai tana jin jiki, wallahi bamu ko rintsaba haka na kwana a zaune. Itama ta kwana wash_wash. Amman mahaifiyarta tana Lagos ma yanzu haka zata hau jirgin Ghana, bata daɗe da kiran waya ba. Tama kasa ɗaga wayar sai dani tayi magana. Na kira wayar Baba kiran duniya yaƙi ɗagawa, daman in sanar mishi halin da take ciki ne." Nabila tace. "Rashida ho kamar baki san halin uban naki ba. Inya tafi fataucinshi ai baya ɗaga wayar kowa. Allah dai yasa mahaifiyar tata ta iso da wuri a samu a kaita asibiti ko ta rabu da azaba. Hanun sai sake kumburi yake yi. Ni dai ina jinsu sama_sama azaba ta isheni. Fuskata tayi wani irin mugun kumburi sabida tsabar kukan dana kwana cur inayi. Kokkon da Nabila ta kawo mun ma kasa sha nayi, in tashi zaune ma abu ya gagara. Sai wajajen jefin azahar Mama tayi kiran waya, ta ari wayar wata mata da suka sauka a jirgi. Kwatancen layin da muke Rashida taima matar. Basu fi awa ɗaya da rabi ba sai ga Mama na jiyo muryarta a tsakar gida tana gaisawa da yaran gidan, da su Hajiya kubra da basu jima da fita a ɗakin nawa ba. "Bismilla ga ɗakin nata nan tana ciki" Cewar Hajiya Kubra kenan. Godiya Mama tayi mata ta shigo ɗakina, salati ta shiga rabkawa tana tafa hannayenta, cikin ta'ajibi take kallon ɗakin da nake kwance a ciki tace. "Me zan gani ɗuwawu ya mutu ya bar zani. Zubaina inane nan kuma?" Cikin rishin kuka nace. Mama ki yi haquri ki kaini asibiti mutuwa zanyi. Ku bar zancen komai Mama " Sai lokacin idon Mama ya sauka a kan hannuna cikin kururuwar kuka ta soma sakin salati a jejjere. Yaran gidanne suka nemo mana mori har cikin gidan ta shigo. Mama da Rashida ne suka rirriƙeni na shiga mori ɗin. Tare da Rashida da Mama muka je wani prive asibiti mafi kusa damu. Daga nan suka turamu general asibiti, domun suke da ƙwararrun likitocin ƙashi. Da isarmu aka shigar dani wani ɗaki, likitoci biyu ne suka rufu a kaina, Mama tana gefena tana sharar hawaye. Ɗayan likitan ya dinga faɗan danme zasu yi mun dorin gargajiya, saida hannu ya suntuma zasu kawo ni. Ɗayan yace. "Allah yasa hannun bai ruɓe ba, dan yanda ya aune haka, in infection ya shiga cikin ciwon dole mu yanke mata hannun. Dajin haka daga ni har Mama muka tsure. Tashin hankalin dana shiga yafi gaban misalin da za'a rubuta. Allura sukaimun, ban sake sanin inda kaina yake. Sai wajajen bayan isha na farka a wahalce. Hannuna na kalla a tsorace, ajjiyar zuchiya na sauke dan ganin hannun yana jikina ba'a yanke mini ba. Yana sagale a wuyana an ɗaure da farin zaren asibiti. Fuskata a ciccike dan kumburi. Da Mama muka haɗa idanu ta zabga uban tagumi ta shiga wani irin zurfin tunani. Mama. Na ambaci sunanta da sanyin murya. Ta juyo muka haɗa idanu, ajjiyar zuchiya ta sauke tace. "Kin farka Zubaina, sannu da jiki kinji ƴannan." "Kinci abinci Mama, yunwa nake ji ni." "Naci abincin dana saima cikina. Allah ya auna mun arziki tun a Airport nayi canjin kuɗi daga nera zuwa cedi. Zubaina naga rayuwa ni kaɗaice zaune a ɗakinnan ina kula dake. Na kashe kuɗi fin dubu ɗari a kuɗinmu na Najeriya. Na ƙosa ki farka ki bani labarin duhun dana ganki a ciki. Kaina ya ɗaure ainun. Yanzu muka gama waya da Rakiya ta wayarki nasa kati na nemeta. Bari ina zuwa in siyo miki abinci a bakin asibitinnan." Bayan Mama nabi da idanu, ina hawaye. Lokaci yayi da zan bar Ghana ko ana ha maza ha mata. Tunda dai har na riga na fito daga gidan Alh Liti. Da wannan tunani likita ya shigo ya ganni idona biyu. Dubani yayi tare da duba yanayin hannun nawa, yai mun tambayoyin abunda yake yi mun ciwo a halin yanzu. Hannun yana mun ciwo sosai, sai kuma zazzaɓi dake damuna shikenan. Likita yace. "Dole hannun yayi miki ciwo sabida yayi tsami sosai. Da ace kun kai gobe baku zo asibiti ba da sai dai kina ji kina gani zamu yanke hannun. Dan nama da ƙashin wajan har sun soma laushi. Hakan yasa ko da hannun ya warke bazai yiwu kiyi aikin ƙarfi dashi ba. Allah ya ƙara sauki. Nurse zata kawo miki magani, in kika ci abinci sai ki sha kafin ayi miki allura. Ina Mama?" Ta fita yanzu zata dawo" Kai ya gyaɗa yayi ficewarshi. Yana fita Mama ta shigo hannunta riƙe da ledar abinci da pure water ɗaya a saman robar abincin. Fried rice ce koriya fatau, sai kaza a saman da coslow a gefe. Hannu baka hannu ƙwarya nake cin abincin, Mama ta zuba mun idanu nan da nan na cinye abincin nasha ruwa. Nurse ce ta shigo taimun allura ta bani magunguna na haɗiya. "Ke Zubaina bani labarin kab abunda ke faruwa. Kar ki yi gangancin ɓoye mun komai. Dan ko baki faɗa mun ba Alh Liti yaudararki yayi da kalamai na ƙarya. Na firgita da yanda na ganki a wannan ƙazamin ɗakin mara daraja." Hawaye ya soma zubo mun. Labarin halin dana tsinci gidan Alh Liti, da halinshi kab babu wanda ban ba Mama labari ba. Kai ta jijjiga tace "Ciɓiri nannagi azumi ta dahu. Ai wallahi kinji na rantse ba zata saɓu ba bindiga a ruwa. Ƙafata ƙafarki dole mu koma gida najeriya, wallahi sai ya sake ki. Kuma saina yaga mishi rigar rashin mutumci matsiyaci. Ashe kallon kitse mu kai ma rogo. Ke kuma dan ubanki dana tambayarki asirin yaci, sai kika ce mun E. So kike kici gaba da yi mishi bauta kome?" "Mama wallahi Alh Liti hatsabibine, wayar gari kawai nayi naji na jarabtu da matsananciyar soyayyarshi. Kuma shakkarshi nake yi Mama. Bana jin zan iya rayuwa ba tare da Alh Liti ba. Shi yasa na ɓoye ma kowa komai. Wallahi Mama ina sonshi. Ni dai kisa ya sake mun gida kawai." "La'ilaha illallah mahammadun rasulillah sallallahu alaihi Wasallam. Zubaina kece da bakinki kike faɗar kina sonshi a hakan, da mata huɗu da bataliyar yaran? Ohh kin fi son har sai layi yazo kanki yayi miki sakin wulaƙanci sannan zaki dawo Najeriya baki ga tsuntsu baki da tarko ko?, ke wallahi Alh Liti ɗan tsubbu ne, in ba tsubbaceki yayi ba meye abun daɗi a gidanshi da har kike mafarkin kici gaba da zama har sai yayi miki korar kare, irin yanda yaima sauran matan daya saka ko, ko kuma yaranshi su kasheki a banza da wofi, tunda da badan nazo da hanzariba yanke miki hannu za'ayi ki zama nakashashshiya. Kuma ya danna miki saki. To wallahi baki isa ba. Mama na cikin sababinnan Alh Liti yayo sallama ya shigo ɗakin, sai muzurai yake yi. Ƙamshin turarenshi na mallaka ya daki hancina, muka haɗa idanu dashi. Fararen idanunshi sun sha kwallin idonki idona na ƙifil. Take naji na sake jarabtuwar da soyayyar Alh Liti, tsoronshi ya kuma shigata. Hatta Mama da suka haɗa idanu sai da ta shiga taitayinta. A madadin ta jira ya gaisheta, itace ta gaisheshi tana washe baki. Sai da yai mata wani kallon ƙasƙanci, da rashin girma sannan ya soma magana cikin cin magani. Ba tare daya kalli inda Mama take ba yace. "Lafiya Jummai kece dama, to maraba lale." Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna. Naji zafi da raɗaɗin yanda Alh yake ma Mama magana cikin rashin daraja. Mama ta saki bakinta tana kallonshi, kalmar Jummai sai nanata kanta take yi a kunnuwanta. DAMATURU. BULAMA BABBA: Da misalin ƙarfe goman safe muka isa Damaturu. Tun daga kwanar layinmu muke cin karo da motoci, layin cike da mutane, wasu na alwala wasu kuma isowar tasu kenan kamar ni. Ganin jama'ar ya sake rikita lissafina. Dam Ahmad ya riƙe hannuna mu kaita kutsa kai cikin mutane. Waɗanda suka Sanni sai nuna ni suke yi suna faɗin. "Wannan ai shine Bulama Babba, babban ɗanshi kenan" Ni dai bana ko iya ɗago kaina a haka muka shiga cikin gidan. Koke_ koken mata na al'ada ya sake firgita tunanina. Take hawaye ya soma wanke mun fuskata. Ƙannena maza da mata naita cin karo dasu. Ko wanne cikin zubar da hawaye. Wakil ne ya riƙe hannun haguna suka shiga dani falon Ba Bakura. Inda na tarar da Ba Modu, da yurom, da Ba'a Kaka. Ba Bakura yana shinfiɗe a cikin makara an gama suturceshi. Hajja tana gefe tare da sauran ƙannena waɗanda suka samu damar shigowa. Naga ƙannena da muke ciki ɗaya dukkansu. Gefen Ba Modu naje na durƙusa jikina na rawa, hawaye ya kafe a idanuna, bakina sai ambaton Allah kawai yake yi. Adda'ar samun rahamar Allah nayi ma Ba Bakura. Na shafa jikinshi ina jin zuchiyata na ɗaci. Gawar muka cicciɓa muka fito. Mata nan suka shiga kururuwa. Allahu Akbar Ba Bakura mutum na mutane, baya goya marayu. Ya samu jama'a sosai. A tsohuwar maƙabarta aka birneshi, maƙabartar da aka birne Hajja Yahanasu, da Ba Baana da sauran danginmu da suka kwanta dama. Bayan mun kai Ba Bakura gidanshi na gaskiya, sai muka ɗinguma zuwa cikin gidan dan yima iyayenmu ta'aziyya. Ba Modu kuma ya tsaya tare da jama'a yana shaida musu Ba Bakura ya daɗe da yin wasiccin in ya mutu kar ayi mishi zaman makoki. Kowa yayi gaisuwa ya kama gabanshi kawai. Nan jama'a su kai ta ma Ba Modu gaisuwa suna watsewa. Biyo bayanmu yayi zuwa cikin gidan. "Innana a sanar ma maƙota dan Allah ko wacce tayi gaisuwa ta koma gidanta. Marigayi baya son zaman makoki, ko a rasuwar mahaifinmu, da Hajja bai bari anyi makoki ba. Suma yara yaran zuwa yamma ko wacce ta ja hannun ƴaƴanta su koma ɗakin mazajensu. Bulama Babba sai bayan uku zasu goma, domun a tattare kan dukiyar Bakura a rabe musu. A sauke mishi nauyin dake kanshi." Ni dai ina bayan Ba Modu ina jinsu. Falon Ba Bakura muka nufa. Mu kai ma Hajja ta'aziyya sai faman kuka take yi. Ƙannenta nata bata haƙuri. Zuwa yamma gidan kamar ba gidan mutuwa ba, kowa ya watse sai surukan cikin gidan kawai. Sai da na samu ƴar nutsuwa na kira su Ya Bagulaji dan inji jikin Yahanasun. Amman sai naji labari mara daɗi, cewar da ƙyar aka taro Yahanasu taso ta fice daga asibitin, tana ihu da kururuwar zata sha lakamis. Wannan labari shi ya sake susutani. Ambaton Allah kawai nake yi. Take na ɗauki karatun Qur'ani na soma rerawa domun samun nutsuwa. Ba Modu kuwa sai faman ganawa yake da manyan baƙi, masu hulɗar kasuwanci da Ba Bakura. Ni dai ina ɗaki ni da Ahmad, bana ƙaunar son ganin kowa. Damuwar dake kaina ma ta isheni." MRS BUKHARI CE[14/08, 9:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 41 GHANA ZUBAINA: "Lallai Alh Liti, zahiri ka bani mamaki. Ta wanne dalili zaka je har najeriya ka auro mun ƴa ka kawota inda bata sani ba ka shiga gana mata azaba. Nazo na sameta a cikin wani irin hali wanda da banyi gaggawar zuwa ba, da sai dai a yanke mata hannunta, kai ba asararka bace. Yaron da yayi mata wannan aikin ya kamata a ɗauki matakin shari'a dashi dan kasheta yayi niyya. Alh Liti maganar gaskiya ni bana son tashin tashina, ka saki Zubaina kawai mu kama hanyarmu, bazan iya barinta a cikin wannan halin ba." Kallon Mama nayi ta gefen idona a tsorace nake sosai da Alh, in na ganshi gabana har kakkatsewa yake yi. Gyaran murya yayi yace. "Hummm Jummai lashe money kenan. Kin ɗauka rabuwa da Zubaina wani kayan gabas ne a wajena? Bari kiji na auro ƴan mata waɗanda ni na yage ledarsu, ma'ana ni na karɓi budurcinsu, na sauwaƙe musu, ballan tana wannan fankon da ko ɗanɗano bata dashi. Rabuwa da'ita kamar in tuɓe takalmin ƙafata ne, kinga kuwa cire takalmi ai ko yaro baya yima wuya balleni da a girme na girme miki. Amman bari kiji in so kike da gaske in rabu da Zubaina, sai kun biyani dukkan kuɗin dana narkar muku dashi, komai da taci tun daga farkon haɗuwarmu kawo i yanzu yana rubuce. Itace mace ta farko a cikin rayuwata data lashe kuɗi tsabarshi sama da million bakwai, dan ko a ƙarashen ginin gidanta da kayan dana zuba mata a cikin gidan yayi million biyar. Ke karan kanki nawa kika ci? Million ɗaya da rabi na kashe miki babu amfanin kuma da zaki yi mun. Kuɗaɗena sun kama jimilla million tara da dubu ɗari huɗu da ashirin da biyar. Banda kayan maƙulashe fa da nake siyo muku ku lashe, A cake mun su, kuga aiki da cikawa. In kuwa ba'a cake mun ba, ni da Zubaina mutu ka raba dan bata cikin jerin matan da suke jiran layin saki ya zagayo kansu. Sannan Jummai inason in ja kunnenki karki kuma yi mun kutse cikin harkar data shafi iyalina, abinda yasa bazan yi ƙararki kotu ba sabida wannan shine karon farko, amman ina mai gargaɗinki da ki kiyaye gaba. Ke kuma Zubaina, ki shirya da yamma za'a baku sallama sai Jummai ta mayar dake tunda dai ita ta ɗakko ki. Yana dasa aya ya juya ya fice yana saɓa malum_malum ɗin shi. Idanuna na tsiyayar hawaye nabi bayanshi da kallo. Mama na kalla jikinta yayi sanyi ainun idanunta sun cicciko da ruwan hawaye. "Ni Jummai wannan mutumi kwai tambaɗaɗɗe, Zubaina dama haka Alh Liti yake, ashe gogaggen baduniye ne bamu sani ba ƙwallon shege?, kallon kitse mu kai ma rogo ashe? Tabɗi jan ni Jummai tawa ta ƙare." Ni dai sai hawaye kawai nake zubarwa, ina tuno lokacin da Bulama yake gurfana guigowinshi a ƙasa, kanshi na kallon ƙasa yana gaishe da Mama cikin girma da karamci. Na sake tuno yanda yake ganin girmana da girman ƴan uwana. Nayi imani da Allah da ace a gidan Bulama na samu wannan karayar da yanzu yana gefena yana aikin yi mun sannu da jiki. Muryar Mama ce ta katseni tana faɗin. "Dole zaki bar gidan Alh Liti in kina son ki tsira da rayuwarki. Zan haɗa kan ƴan uwanki su samo wannan kuɗaɗe a biya Alh Liti ya sauwaƙe miki. Tunda matsiyacine shi. Da sauri na dubi Mama kaina na saramun nace. A'a Mama karki nemo kuɗi a wajan kowa ki barshi kawai" Shessheƙar kuka naci gaba dayi. Mama ta riƙe ƙugunta tace. "Me kike nufi da kar in nemi kuɗi a wajan kowa Zubaina, baki da hankali ne, ko kuwa asiri Alh Liti kema yayi miki ne?" Wallahi Mama ban sani ba. Amman ko asirinne sai yayi mini. Ni dai kawai inason in zauna a gidan mijina, sabida bana jin in na rabu da Alh Liti rayuwata zata ɗaure. Mama wallahi ina sonshi." Kuka mama ta saka tana salati tare da kutuntumama Alh Liti ashariya iri _ iri akan ya rabasu dani. Ni dai ina kwance ina kukan baƙin ciki da takaici, tare da tambayar kaina me yasa nake son zama a gidan Alh Liti ne? Sai dai kash bani da wannan amsar, wanda zai bani amsar ma ban sanshi ba. Haka mu kai zaman kurame ni da Mama a asibitinnan, ina ji Asiya tana cema Mama ta bani wayar zamu gaisa, amman Mama fur taƙi sai ce ma Asiyan tayi ina baccine. Kallonta nayi, itama ni take kallo, harara Mama ta sakar mun tana ƙwafa. Da yamma aka bamu sallama muka tattaro muka dawo gida. Nan su Hajiya Kubra suka shiga tambayar jikin nawa. Mama kuwa tagumi tayi tana kallonmu dukkanmu, hawaye take ta aikin sharewa da gefen mayafinta. Da daddare aka kawo mana dukunu da miyar tanƙwa da soyayyun kayukan kifi. "Me zan gani ɗuwawu ya mutu ya bar zani ni jummai, Zubaina meye wannan haka a ɓawon masara?" Ajjiyar zuchiya na sauke na kalli Mama itama ni take kallo tana tsaye a kaina. Dukunu ne Mama, wani irin tuwone na gargajiya anan Ghana." "Kuma ake cinshi da romon attaruhu da kayukan kifi, sai kace wasu kuliyoyi? To bada ni ba gaɗa a makwantai, inci zawo ya hanani tafiya gobe. Tashi zaki yi ki kira mun wata yarinya nan in aiketa ta siyo mun abunda zan iya ci." Cikin ɓata fuska nace. Haba Mama ni da ba lafiya gareni ba shine zan tashi in kira miki yaran aike? Yaran gidannan ma ba aikuwa suke yi ba Mama." Ai daga faɗar haka Mama tace ina wuta ta sani. Ta inda take shiga ba tanan take shiga ba, zagi kuwa a wannan ranar nasha zagi iri _ iri. Matan gida na jinmu, sai kuka nake yi. Fuuu mama ta fice abunta ina kiranta ma tayi banza dani. Bata jima ba ta dawo da take away na indommie da soyayyen ƙwai sai coke mai sanyi. Ina kan gado na soma cin dukunu kenan ta shigo, ko kallon inda nake batai ba. Nima bance mata ci kanki ba. Har dukkanmu kowa ya gama cin abincinshi. Alwala na fita na ɗauro na dawo na rama sallolin da ake bina. Mama kuwa ni take kallo ƙur da halama tunani take yi mai zurfin gaske. Mama kiyi haƙuri in nayi wani abun daya ɓata miki ranki. Wallahi Mama inason inci gaba da zama a wannan gidan. Kuma Mama ni ina ganin kamar alhakin Bulama da iyayenshi ne ya soma bibiyata tun kafin aje ko ina. Mama wanne surƙuƙune bamu shiga mun gurfana a gaban bokaye ba? Mama kin taɓa ba da jikinki ga boka duk dan sabida biyan buƙatarmu. Mun samu komai a yadda muke son ya tafi mana. Amman aurena da Alh Liti ina ganin kamar shine sakamakon dukkan aiyukan sharrin da muka shuka a baya. Ni dai Mama na zubar da wasu makaman yaƙina. Kuma zan ta yin istigifari Allah ya yafe mun kura_ kuran dana aikata a baya. Wallahi Mama Alh Liti yafi ƙarfinmu ne shi yasa kika ga na sallama." Kallona Mama take yi sosai tana nazartar yanayina tare da jujjuya kalamaina. Ajjiyar zuchiya Mama ta sauke ta kira sunana da sassauƙar murya. "Zubaina dukkan maganganunki akan hanya suke. Tun kafin in yi aure nake biye_ biyen bokaye, gashi har yanzu aikin kenan guda ɗaya sama da shekaru talatin da doriya. Ban huta ba kuma har yanzu bata sauya zani ba. Kuma har gobe a cikin matsaloli muke, daga wannan sai mu faɗa wannan. Yanzu haka ko jarabar Musa da Sagiru aka barni dashi wallahi ta isheni. Ƴan uwanki dai ko wacce lafiya sumul take zaune a gidan mazajensu. Ke da kika faɗa jarabawa sai dai ince miki Allah ya fitar dake, zan ci gaba da taya ki da adda'a. Amman ni kaina yawon bin malamannan ya gama isata wallahi, na riga dai na shiga ne, in banje ba sai inga kamar rayuwar tawa ba zatai dai _dai ta ba. Amman a hankali zan dinga rage zuwa har in dena. Kici gaba da zaman haƙuri in ki kai ta adda'a Allah zai kawo miki mafita." Cikin muryar kuka nace. Dama Allah ya barmu ne da iyawarmu, yanzu kuma sai yaso ya nuna mun ikonshi ta hanyar jarabtata da Alh Liti. Mama nayi kaicon barin gidan Bulama Kamar yadda nayi kaicon cutar da mahaifanshi da nayi. Nayi kaicon biye _ biye bokaye maƙaryata da na dinga yi Mama. Mama ki nemi Bulama ki dubo mun su Bawa dan Allah, nayi watsi da yarana da yawa. Ina gudun kar dangin mahaifinsu su rabani dasu baki ɗaya." A daren ranar munfi ƙarfe biyun dare muna tattaunawa da Mama. Dukkanmu tsoron Allah da dana sani ya ratsa jikkunanmu sosai. Washe gari sassafe Mama taimun sallama ta tafi. Ta barmun ragowar kuɗaɗen Ghana data canja anan. Haka naci gaba da jinyar hannuna, hannu dai kullum babu daɗi kwata _ kwata, ina cikin jinyarnan akayi bikin yaran gidan su goma, bikin daya tara tarin jama'a, dan ko wacce yarinya mahaifiyarta ta samu halartar taron, a bisa jagorancin dangi. Maƙotama sun cika gidan fam, bikine dai akayi shi kadaran kadahan, dan iyayen amarennan kusan su suka ɗauki nauyin abincin ranar yinin biki, Alh Liti na ranar ɗaurin aure kawai ya bada cefane, tuwon shinkafa da miyar kabewa, babu ishasshen kayan miya, balle nama ko kifi haka akayi bikinnan aka kai amare gidajen aurensu. Sati biyu na zagayowa na koma asibiti dan a kunce mun hannuna kamar yadda suka ce. Tashin hankali wai hannun bai ɗauru ba sai an kuma mun sabon ɗori. Haka aka kuma karya hannuna akaimun sabon ɗauri, sai da nayi kashi tsabar azaba. BAYAN WATA UKU MRS BUKHARI CE [14/08, 9:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 42 DAMATURU: BULAMA BABBA: Ranar addu'ar uku akayi mana rabon gadonmu. Inda mu mazan muka tashi da gidaje bibbiyu masu ɗakuna goma sha bibbiyu da shaguna uku a jikin ko wanne gida,dama gidajen haya ne. Matan suka tashi da gidaje ɗadɗaya. Muka yi taraiya a kamfanin pure water mallakin Ba Bakura wanda bai jima da buɗewa ba, amman kamfanine babban gaske, akwai motoci goma sha biyu masu jigilar fitar da ruwa, har ruwan gora suna yi a wannan kamfani. Banda kuɗaɗe da aka raba mana masu tsokar gaske da ƴan kadarori dai irin filaye da gonakai. Adda'ar uku akayi, ni da Ahmad muka kama hanyar komawa Kano dan ci gaba da kulawa da lafiyar Yahanasu na. Watanmu ɗaya a Dawanau amman babu wani canji da zan ce mun samu babba. Abu ɗaya ne dai, Yahanasu ta dena ihu da fisge _ fisge. Amman kullum a cikin fargaba muke da damuwa. Wata ranar asabar da yamma na shigo duba Yahanasuna, na tarar da Mama gana tana waya tana. "To shikenan Modu ni gobe ma sai mu kamo hanya kawai. Kana ji ko Modu? Mu haɗu daku ɗin kawai a Dauran. Yanzu Bulama Babba ya shigo zan yi mishi magana a shirya daga yanxu zuwa gobe kawai. Ka kashe wayarka in muka gama tattaunawa zai kira ka." Wayar ta sauke a kunnenta ta dubeni tace. "Bulama Babba. Modu ne ya kira ni yake yi mun wani batu. Ni dai na gamsu da batun daya kawo mun, kuma ina fatan ku gamsu domun ko baku gamsu ba babu wanda ya isa ya tanƙwarashi." Ina jinki Mama Gana me Ba Modun yace ne?" "Dangane da batun lafiyar matarka ne Yahanasu dama. Yace akwai wani rehab da aka bashi labari a can Daura garin su Baba Buhari. Kuma ya tura Dala ya dubo mishi wannan rihab acan Daura. Duk sun gamsu da wajan shine yake bada umarnin akai Yahanasu can domun a kula da'ita yanda ya dace. ( Bawai dan sun raina ƙwazo da ƙwarewar likitocin Dawanau bane, wannan ra'ayinsu ne) Dan haka sai ka shirya mata kayanta cab gobe in sha Allah sai mu ɗauki hanya. Tunda Allah yasa ka sayi mota ma tazo mana da sauƙi ai. Ni dai hankalina bai kwanta da batun ɗaukar Yahanasu daga asibiti zuwa Rehabilitation center ba ( gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shaye na gargajiya) dan akwai wani labarin daya taɓa faruwa a ɗaya daga cikin ire _ iren gidajennan labarin mummunane. Ana azabtar da mazauna irin wannan gidan azaba mai tsananin gaske. Duk da nasan ba duka aka zama ɗaya ba. Muryar Ya Bagulaji na jiyo tana faɗin. "Kayi shiru baka ce komai ba Bulama Babba, baka ji abunda Mamanka tace bane? Mama Gana nan ta sauke mun kwandon jarabar dana rasa dame ma zanji. Naji Ya Bagulaji ina dai tauna zancenne a raina kawai." Buɗar bakin Mama Gana tace. "Dake ba Bakura bane ya yanke hukuncin ai dole ya tsaya tattaunawa. Da uwarka Hajja Gana wannan koɗaɗɗiyarce ke magana ai da saika bata amsa kafin ka tauna duk abinda kake son ka tauna." Haƙuri na basu dukkansu nace. Shikenan zanje in samu Ahmad muyi magana kafin goben. Sabida dama a satinnan nake son shi Ahmad ɗin ince mishi ya koma Yobe ɗaya daga cikin gidajena ya zauna da iyalanshi, kafin in gyara mana gidan da zamu zauna. Wannan sha'anin jikin na Yahanasu ne yasa komai ma ya dakata. Amman ba damuwa Allah ya kaimu goben." Ban jima a asibitin ba na fito. Neman Ahmad nayi a waya muka haɗu dashi, a gefen hanya ya ajjiye keken nashi a cikin keken muka zauna. Halin da ake ciki kab na zaiyane mishi, shima yaji girman abun. Ni Ahmad hankalina bai kwanta da rihab ɗin gargajiya bane kawai, duba da irin tarin matsalolin da ake samu. Amman dole inbi umarnin Ba Modu. Ka taya ni da adda'a Ahmad. Sai batun komawarmu Yobe kuma. Ina ganin ko zuwa jibi ai sai ku wuce ko? Kasan gidan, nasa an tashi ƴan hayan ɗakin da zaku zauna a ciki. 3bedroom flat ne. Ku zauna a ciki kafin in gyare mana ɗayan gidan sai mu haɗu duka muci gaba da zamanmu dan sake haɓaka zumuncinmu. Wannan kamfanin pure water ɗinnan kasan dole sai ka taimakamun da aiki, tunda kaga babbane kamfanin. Ita kanta Hajara ba zata rasa aikin da za'a bata ba, a ƙalla itama zata taimakama iyayenta. Na tura maka nera dubu ɗari da hamsin a account ɗinka naka ne ku ɗanyi siyayyar kayan ɗaki. Wannan million ɗayan kuma kuɗin gidan Yahanasunane dana siyar na tura cikin account ɗinka ka Ajjiye mun." Mun daɗe muna tattaunawa kafin daga bisani muka tafi gidan tare. Kekunan da muke tuƙawa na biya mana ragowar balance ɗin daya rage mu game lone ɗinmu. Munyi da Ahmad zai tura da kekunan Damaturu aci gaba da kabu_ kabu dasu. Washe gari nayi ma mazan gidan sallama na nufi asibiti. Su Bawa Ahmad zai tafi dasu Yobe. Ina zuwa asibitin na tarar da su Mama Gana har sun gama haɗa kayanmu. Takaddar sallama suka miƙamun naje nayi duk abunda ya dace. Dr Halima har gaban motarmu ta rakomu tana ɗaga mana hannu. A hankali nake tuƙin motar ina kallon Yahanasuna ta mudubi, tayi shiru tana kallon gefen taga. A haka batai kama da masu taɓin hankali ba sam. Sai kayi mata magana ta kasa baka amsa ta sako shirme ne mutum zai fahimta. Ko kuma in abun ya motsa ta soma fiffisga tana ihun a bata laka mis in ba haka ba mutuwa zata yi. Ina jin su Mama Gana suna ta hirarsu da Ya Bagulaji. Ni dai hankalina yana wajan tuƙi, zuchiyata kuma tana wajan Yahanasuna. Haɗa idanu muka yi ta mudubi. Murmushin soyayya na sakar mata mai taushi. Abun mamaki itama murmushin ta sakar mun tana mai kafe ni da idanunta. Can kuma sai ta soma zubar hawaye. Haka dama Yahanasu take a koda yaushe tunda wannan lalurar ta same ta. Tafiyar awa hudu ne ya kaimu garin na daura can wani ƙauye, tambayar gidan malam Rilwanu mu ka yi aka nuna mana. A ƙofar gidan muka ga motar su Ba Modu halamar sun iso suma kenan. Malam Rilwanu ne yai mana iso har cikin gidan nashi. Yana gaba muna biye dashi a baya. Gaisawa su Mama Gana suka tsaya yi da matan gidan, ni kuma ya jani zuwa cikin turakarshi inda anan na tarar da Ba Modu da Ba'a Kaka da Ya Innana sai Fanna. Gaggaisawa muka shiga yi, a cikin haka su Mama Gana suma suka shigo a bisa jagorancin wata dattijuwar farar mace. "Nazifa a kawo musu ruwa da abinci, baƙine daga Kano wadannan kuma daga Damaturu, marar lafiya suma suka kawo." Wannan dattijuwar tace. "Marabanku lale da zuwa. Me jiki kuma Allah ya bata lafiya, jiya ma wasu bayin Allah suka kawo ɗansu daga Kaduna can hayin rigasa." Tafiya tayi bata jima ba sai gata da ruwa cikin kofunan silver. Da dambun rama cikin wata ƙaramar kwalla. Godiya Ya Innana tayi mata, sannan ta dube mu tace. "To bismillah muci abinci ko, sai mu sa haramar komawa." Ni dai loma biyu nayi na ajjiye cokalina, cike zuchiyata take tab da tsantsar alhinin rashin Yahanasuna. Ita nake kallo, sai kama kanta take yi, tana wata iriyar zabura. Suna kammala cin abincin malam Rilwanu yace. "Sai muje can bayan gida in nuna muku inda muke ajjiye marasa lafiyanmu ɓangaren mata. Da kuma nasarorin da muka samu na warakar wasu daga cikin waɗanda aka kawosu suna hauka tuburan. Duk da naga taku marar lafiyarma tana jin jiki, ƙila ta jima tana shan miyagun ƙwayoyi masu cutar da ƙwaƙwalwa." Yana gaba muna bin bayanshi. Bamu fita waje ba, ta cikin gidan nashi muka shiga wata ƙofar, munyi tafiyar kimanin minti goma sha biyar kafin muka iso wata ƙofar. Muna shige wannan ƙofar muka soma ganin guggun mata a zaune a wata baranda ana koyar dasu darasin lissafi wato Maths. Matane manya da matasa. Ɗakunan da suke kwana ya shiga nuna mana ɗakuna, ko wanne ɗaki mutum shida ke rayuwa a ciki, katifar yayi ce ƙanƙana a shisshinfiɗe a cikin ɗakunan ko zanin gado babu balle matashi. Babu ƙazanta dai a wajan amman kuma babu wata tsabda ta azo a gani. Wasu ɗaure suke a mari, yayin da wasu suke a sake. Kana ganin wasu da halamar haukar sosai ta bayyana a jikinsu, yayin da wasu kuma tabarallah kamar irin waɗanda muka samu a can baya suna karatu. Wani godon ɗaki malam Rilwanu yasa wata malama Fahiƙa ta shigar damu. Keken ɗinki muka gani, da keken saƙar setin kayan sanyi na jarirai. Sai kuma katakwaye irin dai na haɗa gado kamar kafinta dai zance. Shi kuma wannan ɗakin na koyon sana'a ne, wanda ya zama wajibi akan ko wanne marar lafiya. Amman da halamar kamar ana ɗan azabtar dasu, dan na ga manyan dorinaye. Kuma duk ɗakin da muka leƙa sai inga ƴan ɗakin sun zabura da zaran sun ga malam Rilwanu. Daga ɗakin koyon sana'a kuma ana nuna mana wajan da suke motsa jikinsu atisaye, sai ɗakin shan maganin bature, inda wani matashi yake zaune a gaban teburi shi da wata dattijuwa. Gaggaisawa mu kayi, yai mana ɗan bayani a taƙaice na irin gudunmawar da suke basu ta fannin ilimin likitanci, su ɗin likitocin ƙwaƙwalwa ne. Duk wannan zagayen da muke yi Yahanasu tana riƙe gam a hannuna, sai matse mun hannu take yi tana shigemun. Da muka zo rabuwane ta fashe da kukan da sai data raunata zuchiyoyinmu dukkanmu. Matan suma kuka suke yi, tuni idanuna suka sake kaɗawa su kai jawur dasu. "Dan Allah karka barni anan wajan. Nifa lafiyata ƙalau. Kar ku barni su cutar dani." Sake rushewa da kuka tayi ta faɗa jikina tana kukan fitar rai. Da sauri na cireta a jikina sabida su Ba Modu. Tsugunnawa nayi a ƙasa ina mata magana ƙasa_ƙasa. Zan dinga zuwa dubaki kinji? Ki dinga shan maganinki, sannan duk abunda akace miki kiyi, kar kiyi musu gaddama kiyi kinji? Zan dinga zuwa. Da dabara na share hawayen daya zubo kan kumatuna. Yahanasu ta rungume Mama Gana tsam ta dinga kuka. Da ƙyar na ɓanɓareta a jikin Mama Gana na damƙata ga malama Fahiƙa nace. Amanarta tana hannunki, ki kular mun da'ita dan Allah." Malama Fahiƙa tace. "Amanoninsu duk a hannuna suke. In sha Allah bayan wata ɗaya in kuka kawo mata ziyara zaku yi farin ciki a bisa sauyin da zaku gani daga gareta. Allah ya basu lafiya. Dan Allah kubi doka. Talatin ga ƙarshen ko wanne wata ne yake zama ranar zuwa ziyartarsu, in ba dai kunji kiran gaggawa daga garemu ba kar kuzo." Sallama mu ka yi musu muka fito tare da malam Rilwanu. A bakin motacinmu muka tsaya. Bayana na juya ina share hawaye dake zubowa a idanuna. "To Malam Modu nagode sosai. Zuwa nan da wata uku ina tunanin kuɗin hidima da'ita zai iya ƙarewa, in ma ya wuce wata ukun duk zan sanar muku. Nagode da kayan abinci da aka sauke mana, ku sauka lafiya, sai ƙarshen wata in Allah ya kaimu cikin rayayyu.' Sallama su kai mishi muka shiga mota. A wannan karon bani da kuzarin da zan iya tuƙi. Zama nayi a gefen mai zaman banza, Dala ne ya riƙe motar. Mama Gana da Ya Bagulaji suna baya. Ba'a Kaka kuma ya tuƙa Ba Modu da Ya Innana. A jere muke tafiya, a masallacin daura mu kai sallar azahar kafin muka ɗauki hanya. Sai magriba muka isa Damaturu, kowa jikinshi a mace mus. Ɗakin Dala na samartaka na shiga na keɓe kaina, bayan na zaga iyayen nawa mun gaisa na ƙara musu ta'aziyyar Ba Bakura. A ranar baccin kirki ban samu damar yi ba. A sallaya na raba dare ina roƙon Allah ya bama Yahanasu lafiya. Haka dai al'amura su kai ta motsawa. Ahmad sun shiga Yobe sai da ya ajjiye Hajara da yaran acan sannan ya tawo damaturu. Kwana biyu mu ka yi a Damaturu muka koma Yobe. Gadan_gadan na shiga gyaran gidan da zamu zauna, bayan ƴan hayan gidan duk sun tashi. Fasali me kyau nasa akema gidan. Duk wannan aikin ƙarfin hali kawai nake yi, babu nutsuwa a tare dani. Na rame sosai, ko da yaushe inna je Damaturu sai Ba Modu yayi mun faɗa tare da nasiha. Cikin kwana ashirin da biyu da Yahanasu tayi a Daura, kullum na kwanta sai nayi mafarkinta. Ranar juma'a ya kama talatin ga wata, a daren da washe gari zamu tafi Daura, bacci ɓarawone ya ɗaukeni. Tun asuba kuwa na shirya tsab harda yaran da Ahmad muka nufi Damaturu. Acan ma mun same su a shirye tsab. Hajja ta bada cincin da alkaki tace a kaima Yahanasun. Ya Innana kuma tayi mana lafiyayyen buski da miyar kuka da taji kaza. Sallama mu ka yi musu muka kama hanya. Wannan karon da su Yabulu, da su Gunsum muka tafi, sai Fanda. Mun isa Daura dab sallar juma'a. Sai da muka gabatar da sallar juma'a sannan muka ƙarasa ƙauyansu malam Rilwanu. Motoci da dama muka riske a ƙofar gidan Malam Rilwanu. Da halama motocin iyaye masu zuwa ziyartar yaransu ne. Kai na jinjina, ina biye da Ba Modu a baya har zuwa cikin gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shayen. MRS BUKHARI CE[15/08, 11:55 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA (DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 43 GHANA ZUBAINA: Yau gidan mun tashi da hidimar abincin masu kawo Amaryar Alh Liti daga sokoton Shehu. Kaji bakwai ya kawo, da shinkafa forin kwana biyu, ruwan roba katon hudu da lemun gora katon biyu. Tun asuba da mu ka yi sallah muka duƙufa aikin. Hannuna har zuwa wannan lokacin bai warke ba, bayan sake ɗaurani da akayi a asibiti, sai da aka sake yi mun ɗaurin gargajiya dan dana koma asibitin cewa su ka yi hannun bai haɗeba sai an sake karyawa an dorani. Gashi ba kuɗi a hannuna, na roƙi Alh Liti roƙon duniya ya taimaka mun, amman yace mun bashi da kuɗi. Hajiya Kubra ce ta sake raka ni gidan wani mai ɗori acan wata anguwa mai nisan gaske. Takalmi da jakata wanda naci bikina dashi, shi na bayar a matsayin kuɗin gyaran karayan. Ina cikin jinyar hannuna na shiga laulayin ciki, gashi wannan karon cikin ba ƙaramin jigatani yake yi ba. Duk wanda ya sanni a lokacin da nake kofur Zubaina, ko mrs Bulama sai ya sha mamaki, domun ba ƙaramin lalacewa nayi ba, nayi baƙi na wani ƙanjame kamar ba ni ba. Mama kuwa kullum a cikin yi mata filashin nake amman bata kirana. Asiya da Nafisa suna kirana jefi_jefi mu gaggaisai. Mabaruka kuwa tana ƙasar ingila ita da mijinta ta rakashi wani aiki. Amman tayi mun alƙawarin zata zo ta ganni kafin su koma Najeriya. Kullum a cikin mafarkin gidana na da nake da yarana da Bulamana, ina da number Bulama a kaina, amman kona danna da zummar in mishi filashin in ya kira ince ya bani yara mu gaisa, dan gudun karsu mance wacece uwarsu, sai in fasa kiran sabida kunyar jin muryar Bulama nake yi, tare da taraddadin in Alh Liti yaga na kira wayar Bulama bansan wanne hukunci zai mun ba." "Yauwa masha Allah, Zubaina komai ya kammala, Nabila sai wanka kuma, mu tsimayi jiran manyan baƙi. Cewar Hajiya Kubra kenan, tana riƙe da tsintsiyar data gama share wajan girkin tsab. Rashida wacce take gaban kular da aka zuba kaji tace. "Wannan rayuwa ta ƙaddara, Baba bashi da aikin daya wuci Aure da saki sai kace mai bakin uwa, ko kuma wanda akaima asiri. Taya ma mazajenmu zasu riƙemu da daraja? Ai ko alhakin matan da yake aurowa ya gana musu azaba, bazai sa mu mazajenmu su tarairayemu ba." Tsaki ta dinga jerawa. Mu dai babu wanda ta tanka mata, a cikinmu ko wacce ka kalla a cikin ƙunci take da yawan tunani. Wanka mu ka yo ko wacce ta shirya tsab dan sauraran isowar baƙi. Ai kuwa dab magriba sai ga Alh Liti ya shigo ɓarayinmu faram _ faram da farar shadda ɗinkin malum_ malum, hula a karkace, sai kwaɗa mana kira yake na rashin daraja. Ina kwance na jiyo kiran da yake yi mana, babu shiri na miƙe a zabure dan ba ƙaramin tsoronshi ya ɗarsamun a zuchiyata ba. Har bana ƙaunar kwanana ya zagayo dan ina gurzuwa kamar babban bargo. Gashi sai ya gama yai ta mun mita wai shi bai gamsu ba, babu ni'ima sam a tare dani, ai aurena asanar kuɗine, babu irin maganganun da baya yaɓamun. A tare muka firfito ko wacce kanta a kasa. "Dan bura'ubanci ina kiranku kunyi kunnen uwar shegu dani, kunfi son inyi rashin daraja baƙi su jiyoni ne ko yaya? Ai wannan iskancine da daƙiƙanci irinna mata." Kallonshi nayi kalmar daƙiƙanci da iskanci daya faɗa ya huda zuchiyata zafin. A zuchiyata nace. Ai uwarka ma ƴar iska daƙiƙiyace tunda macece." A zahiri kuma jikina har rawa yake yi wajan ba Alh Liti haƙuri, kamar ingizashi muke yi, haka ya tusamu gaba yai ta ɗebe mana albarka, inda sabo mun riga da mun saba. Wata iriyar rayuwa Alh Liti yake gudanarwa ta rashin jinƙai da tunani. "Sai ku kwashi kayan abincin ku kai ɓangarena wajan baƙi. Ban yarda kowa ya gabatar da kanshi ga dangin Amarya ba. Ni da kaina zan gabatar daku a wajenta, tunda dukanku zamana kuke yi. Ƴan iska a haka kamar na Allah. Cikinku ba wacce bata cuceni ba lokacin muna nema, kun ɗauka irin santolon namijinnanne, wasu ma har romiyo suke kirana a waya in na kira wayarsu." Ya gama buyaginshi ya wuce buuu kamar kububuwa. Numfashi naja tare da share hawayen idanuna, kaina na jinjina kawai. Na duƙa na ɗauki babbar kular kajin, su Hajiya Kubra da Nabila, da Rashida suka ɗebo ragowar kayan muka bi bayan Alh Liti zuwa ɓarayinshi. A ɗakin da aka saukeni a lokacin da aka kawoni a nan ya ajjiye Amaryar tashi da danginta. Ko da muka shiga, dangin Amarya sai wani gani _ gani suke yi mana, sun ganmu hajaran majaran. A raina nace. Kwana nawa ne maye yayi Amarya zai lashe abunshi." Da ƙyar suke amsa gaisuwarmu, Amaryar ma bamu samu ganinta ba wai tana sama tare da Alh Liti. Wata dattijuwace tace. "Ammm nace dan Allah a cikinku wacece uwar gidan Alh Litin?" Murmushin da Hajiya Kubra ya zame mata jiki a wannan karon ma shi tayi tace. "Nice uwar gidan nashi, sunana Hajiya Kubra" Nan kallo ya dawo wajenta, amman babu wanda dai yace wani abu. Muka jawo tsumman rayuwarmu muka dawo ɗakunanmu. A daren ranar nayi kukan marar iyaka, kukan da bansan me yasa nake yinshi ba nima. Haka naita tubka da warwara da ƙyar bacci ya ɗebeni. Da sasafe na fito na haɗa itacen dama kokko, yau nice da aiki, ga ciwon hannu ga lallauyin karamin ciki, amman babu mai taimakamun in ranar aikina ta zagayo duk abunda yake a wuyana saina yi shi. Babu babban tashin hankali irin dafa dokunu/ kenke. Wani irin tuwone mai azabar wuyar aiki. Da farko garin masara ake jiƙawa a ruwa ya kwana biyu a jiƙe, sai a juye ƙullin a tukunya rabi a barshi yaita dahuwa, in ya dahu sai a juye a ƙaton bahun, a sake zuba ɗanyen jiƙakken ƙullun masarannan a cikin dafaffen aita gaurayawa har sai ya haɗa jikinshi, sai a samu ɓawon masara a dinga zuba wannan tuwon a cikin ɓawon ana nannaɗewa, Ana mayarwa cikin tukunya akan wuta, bayan an gama za'a zuba ruwa a tukunyar abar tuwonnan yaita dahuwa har na tsawon minti arba'in. ( Da soyayyan kifi ake cin tuwon a ƙasar ghana, da ƴar miyar jajjagen attahuru da albasa) Amman a gidan Alh Liti kayukan kifi ake siyowa na ɗari biyar a watsa a jajjagen, kowa ya dinga lasawa. Hajiya Kubra ce ta fito tana salati tsakar gidan, har tana hawaye. Da ƙyar na miƙe bayana a kantare na dubeta nace. Lafiya Hajiya Kubra kike rabka salati haka sassafe?" "Zubaina wannan yarinyar Rabi naƙuda take yi fa, domun duk halamun naƙuda sun baiyana a tattare da'ita, har faya ta fashe." A razane na dubeta inason yin magana Rashida ta fito tana rabka salati. "Shikenan Rabi ta mutu ta huta da rayuwar cikin gidannan. A guje muka shige ɗakin da Rabi take kwance male_male a cikin jini. Duk wani mai tausayi in ya ga Rabi a cikin wannan halin sai ya zubar mata da hawaye. Muna cikin alhinin mutuwar Rabi Alh Liti ya buɗe labulen ɗakin da muke yace. "Ohh sabida gidajen iyayenku babu arziki baku gajeshi ba, shine zaku yi mun almubazzaranci da dukiyata ko? To acikinku wacce ƴar iskarce ta bar kokko akan wuta yake ta amai?" Jin ya ambaci kokko na zuba jikina ya hau rawa, muryata ta shiga karkatsewa. "Ba magana nake yi ba dan ubanku kunyi mun kunnen uwar shegu, ko sai na kawo hannu?" Jikina na rawa nace. Nice Alh dama, Rabi ce Allah yayi mata rasuw....." Tas ya zabga mun mari lafiyayye ya tokareni da ƙafa na faɗi a gefen gadon ɗakin bakina ya daki katakon gadon. Take jini ya hau zuba daga bakina. Wani kuka gigitacce na saka domun zafin kau ya karaɗe jijiyoyin kaina ya dinga tartsatsi ta ciki. "Zaki tashi kije ki sauke mun kokko a wuta ne ko saina illataki?" A guje na fice a ɗakin ina waiwaye. Ina ji yana tambayar garin yaya Rabi ta mutu, kuma ya ya ganta a cikin jini male_male. Bansan amsar da Hajiya Kubra ta bashi ba, hankalina na wajan sauke tukunyar kokkonnan. Ina saukewa na zubar da jinin daya cika mun bakina tab. Haƙorin ƙasan bakina na gefen dama ya biyo jinin. Ina ganin haƙorin a ƙasa kukana ya sake tsananta, bakina ya suntuma him, harshena na soka a wajan dan in tabbatar shin da gaske ne ko gizo ne. Sai naji wajan wawalo. Yau ni duniya ta juya ma baya, yau ni da nake juyawa ni ake juyawa, yau ni da nake wulaƙanta dangin mijina, yau ni miji yake wulaƙantawa harda arzikin duka da fasa baki, da cire haƙori? Duniya mai ido a tsakar ka. Duniya budurwar wawa, duniya zancan banza. Bani na samu kaina ba sai dare, kafin daren fuskata ta kumbura tayi suntum, dan ko shagalin bikin Amaryar Alh ban samu damar fita zuwa ƙofar gida inda akeyin bikin ba. Zazzaɓi da ciwon baki ya far mun. Inda haƙorinnan ya fice har numfashi yake yi mun tsabaragen azaba. Washe gari muka rankaya zuwa ɓarayin Alh Liti. Yaranmu da manyanmu, mata da ƴaƴa. Harda magidantan yaranshi dake zaune da iyalansu a waje duk sun zo. Na lura suna mutunta wannan ranar ta ganawa, domun a ranar kowa ke da damar shigar da kokensu. Ni a ganina wannan ranar ta ganawa bata da wani amfani a wajena. Domun babu wani koke da Alh Liti ya taɓa saurara ya biya ma mai koken buƙatarshi. Da zage_zage yake korar kowa, wasu ma tashi yake ya mugun rufesu da mugun duka, ko ya bisu a guje, dan na fahimci baya jin nauyin jikinshi sam." Amaryar Alh Liti tana cikin ruɗun da tashin hankali ganin mun mamaye wawakeken falon Alh Liti, kuma yana gabatar damu a matsayin matanshi, bataliyar jama'ar data gani kuma ya gabatar mata a matsayin yaranshi. Amaryar Alh Liti mai suna Zarah tayi kuka harda birgima a falon Alh Liti. Sai daya daddaka mata tsawa ya miƙe kamar zai daketa. Ba shiri ta maƙale a bayana har tana riƙe mun hijabina. Sai da hankalin kowa ya nutsa, sannan aka soma gudanar da abunda ya taramu. Amman jiya dai i yau. Korar kare Alh Liti yai mana. Ba shiri Zarah ta miƙe da zummar binmu. "Ke Kubra! Ki nuna mata akurkinta ta shiga na lura ta tsorata dani. Dokikin daya kamata ta sani na cikin gidan a sanar da'ita, ragowar aikin nawa ne." Cewar Alh Liti, yayi maganar ne cikin zolaya. Hajiya Kubra ta girgiza kai tace mishi. "To shikenan. Amarya muje ko?" Amarya Zarah ta riga Hajiya Kubra ma fita. Ni kuwa ina tafe ina tsaki abun duniya duk yabi ya isheni. Gashi wannan laulayin cikin ya haifarmun da wani irin mugun kwaɗayi mara misaltuwa ji nake kamar in gutsiri hannuna dan masifa. Ina shiga ɗaki na soma laluben abunda zan iya ɗagawa in siyar, hatta ƴan zinarai na duk na kaɗar. Hatta ɗan karamin dana sako a kunnena nazo gidannan dashi, na kaɗar dashi kuɗin duk sun ƙare a asibiti lokacin da aka sake ɗora mun hannuna. Tagumi nayi ina zaune a ƙasa jigum. Ihu da bige_bigen Zarah na dinga jiyowa sama_sama. Baki na taɓe ina ƙara tsinema Alh Liti a zuchiyata. Wayata ce tayi kuka, ina ɗagawa naga baƙuwar lamba. Jikina har yana rawa na ɗaga wayar. Mabaruka mutanen turai" Ta cikin wayar tace. "Ƙawata yaya naji muryarki a haka kamar ba ke ba? Ko da yake ba wannan ba, gani a Airport na Accra, ki turomun da Adireshin gidanki dan ba ganewa zanyi ba." Nan da nan na ruɗe ma mabaruka da ihu. A guje na shiga ɗakin ƴan matan gidan. Rashida na zaune yaranta sun kawo mata ziyara suna hirarsu. Sauran yaran gidan kuma wasu na zaune, wasu na kan cinyayyun katifunsu. Rashida na sama wayar a kunne ina murmushi nace. Ga ƙawata dan Allah kwatanta mata gidannan namu, suna Airport ɗin Accra." Riƙe wayar Rashida tayi, turyan_turyan ta kwatanta ma Mabaruka gidannan ta miƙa mun wayata. Hello ƙawata sai na ganku, tare da oga zaku shigo ne?" Mabaruka tace. "Ban isa ba, zamu soma kama hotel in nayi wanka ni zan tawo inzo mu wuni, da daddare zai zo saimu koma hotel. Naso in kwana miki ƙawata amman bazan iya barinshi shi kaɗai a hotel haka nan aimun sakiyar da ba ruwa ba. Sai dai nazo kawai." Ƙit ta kashe wayarta. Rashida na gode fa?" "Lahh babu komai Anti Zubaina" Fita nayi ko kallon ragowar yaran ɗakin banyi ba, dan riƙaƙƙun marasa mutunci ne, dan su zageka ba komai bane, a gabanka, a dakesu yayyensu maza riƙakƙun ƴan tauri suzo har tsakar gida suna karta adda, suna maka barazana da rayuwarka. Ɗaki na koma na kasa zaune in kai mari in kai gwauro, ina tunanin kalar kunyar da zanji in Mabaruka ta shigo taga ɗakina. Duk da tasan halin da nake ciki, amman ko kusa bata san abun ya kai haka ba. Hankalina yabi ya tashi, abincin da zan bata ma tunani nake yi akanshi, amman nasan bani da wata mafita. Awa ɗaya awa biyu sai ga wayar Mabaruka. "Ƙawata get ɗin farko kikace zan shigo ko?" E Mabaruka, bari in fito in tarbeki ma." Da sauri na saka mayafi na fita tsakar gidan. Sannu naima Nabila dake gaban murhu kace_kace. "Ina zuwa da sauri haka Zubaina ke da baki da ishashshiyar lafiya?" Murmushi nayi mata nace. Baƙuwa nayi zan shigo da'ita. Aminiyata ce tazo" Ban jira me zata ce ba na wuce, mabaruka harta shigo cikin gidan da sallama a bakinta. Idanuwanta ta zuba mun cike da maɗauƙaƙin Mamaki" MRS BUKHARI CE [15/08, 11:55 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA ( DUNIYA) GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 44 Kallon ƙuda mu kai ma juna ni da Mabaruka, bansan sanda hawaye ya soma gudana a fuskata ba. Mabaruka shar da'ita tana cikin kayan alfarma sai ƙamshi take yi, ga cikinta ya amsheta yayi ɗas a jikinta. Kai da ganinta kasan ana lalatata da gata. "Kofurr Zubaina wanka, kece haka ko gizo idanuwana suke yi mun? Ina wanka, da kwalliya, ina hasken fata, da glowing. Ke kinga yanda kika koma kuwa?" Numfashi mai ƙarfi naja na ɗanyi Murmushin nadamar rayuwata, duk da nasan Mama itace ummul aba'isin dukkan halin dana tsinci kaina a yau. Dan uwa itace makwafin yaranta. Ya rage naki kiyi me kyau, ko akasin hakan. Amman a matsayinki na uwa ki dinga hangen goben ƴaƴanki. Mabaruka maraba da zuwa ƙawata, nayi farin cikin ganinki kafin in mutu in huta. Hawayene suketa turereniya a kan kumatukana. Daga bayanmu muka jiyo tashin zage_zage da tashin muryoyi. Alh Liti ne da Amaryarshi Zarah suke cin uwar sabada. Akwatin kayanta take ja tana cewa ita sai ta tafi . Yayin da shi kuma ya caɓe akwatin yana faɗin. "Ai wallahi Zarah in da uwarki kike yawo baki isa ki bar gidannan ba, ai tunda kwaɗayine ya kawoki cikin rayuwata, saina gurje kuɗina na mori gyaran jikin Amarci, da laushin fata. Ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi, yasan sunan tashar da za'a saukeshi, sannan duk ƴan iskan da kika zo kika tarar da badan na kafesu a cikin gidan ba, baza ma kizo ki samu kowa ba, ba'ai macen da zata iya fita a cikin gidannan da zummar guduwa ba. Kinga can inda Zubaina take, baki isa kin wuce wajan ba, in kika ga kin wuce wajan to tabbas ba gudu zaki yi ba. Fita ce kawai ta jeki ki dawo." Zarah ta dubeshi tace. "Ba dai uwata ba, sai dai uwarka ɗan kutumar...." Bata rufe baki ba, ya naushe bakin nata sai jini, ya zuzzuba mata wasu irin gigitattun maruka. Nan yayi baya yana neman madoki. Muciya ya ɗakko da gudu ya bi Zarah, ganin ya nufota gadan_gadan yasa ta ari na kare, rufa mata baya yayi nan suka shiga wasan tsere. Yaranshi ƙananu da manya duk suna gani, harda ƴan mazan ma. Haka su kaita zaga tsakar gidan a yunƙurinshi na ganin ya cin mata. Mabaruka tace. "Innalillahi wa'inna ilaihil rajiun Zubaina haka gidanki yake? Danƙari maƙari sunan kare a lahira. Hannunta naja kawai. Zo mu tafi Mabaruka, sauran tattaunawar ta cikin ɗaki ce. Ko da muka shigewarmu ɗaki, muna shiga Mabaruka ta soma zabga salati, tana tattafa hannayenta gami da riƙe haɓarta. "Na shiga uku Zubaina wannan akurkin mai kama da fursuna kuma inane?" Kuka na fashe mata dashi mai ƙarfin gaske, dama dannewa nake yi kawai gudun kar in kunyata kaina a gaban yaran Alh Liti. Na jima ina kuka kafin daga bisani na tsokatama Mabaruka kaɗan daga cikin halin da nake ciki, ragowar kuma na barma kaina, ciki ba dan tuwo kaɗai aka yishi ba, ko Mama da su Asiya bana sanar dasu halin da nake ciki. Dan Mama tace bani ba ita, in dai bazan bari ta turo mun wata laya data karɓo a wajan bokanta dubu dari uku ba, wannan layar tace dana matsa Alh Liti zai sauwaƙemun. Ni kuma a halin yanzu da'in kuma bin ruɗin bokaye na gwammaci wahalar gidan Alh Liti tai sanadina. Wanda nayi a baya ma ina ɗan daka ce banyi ba, kuma har gobe a cikin istigifari nake. Abunda na shuka ne nake girba, yanzu nasan zafi da raɗaɗin a mallake mutum, ana cutar dashi bashi da abunda zai iya aikatawa, sai dai zuchiyarshi tai ta mishi suya kawai. "Zubaina to me kike tsarama kanki da baki koma Najeriya ba, sannan naga halama ƙaramin cikine a jikinki, ya zaki bari kiyi ciki a gidannan, zaki tsallake kema ki bar abunda kika haifane tunda kince bai bari mace ta tafi da yaro? Ga hannunki a jone har yanzu karayar bata warke bane, ga bakinki a suntume, haƙorinki ma naga ya faɗi, kenan jibgarku Alh Liti yake yi kamar yadda naga yana bin matarshi da muciya suna zagaye gidan? Zubaina ya kamata kiyi wani abun domun samarwa da kanki mafita. Kin ganni nan? Ni yanzu haka a cikin tashin hankali da matsalolin dangin miji nake wallahi, kuma nabi malaman duniya dan in mallakesu abu yaci tura. Suma mugayen ƴan biye_biye ne. Yanzu haka rikicin da ake ciki, hajiyanshi taje can gidanmu ta ɗauki uwar gidan ta mayar da'ita gidanta, akan tana jiran dawowarmu ayi wacce za'ayi. Duk abinda na tara na dukiya a gidan Salisu na kaɗar dashi a wajan bokaye, da abun da na tsira bazai wuce gyara mana gidanmu da Salisu yayi ba." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. "Yaya batun yaranki na wajan Adam, ince dai kina jin ɗuriyarsu ko?" Mabaruka ta gyara zamanta tace. "Bana jin ɗuriyarsu wallahi Zubaina. Amman a cikin kwanakinnan sai na yawanta mafarkinsu, inason dai in dubosu da kaina. Amman Mama na zuwa dubosu. Nabila ce ta katse mana hirarmu da yin sallama. Shigowa tayi hannunta riƙe da kwanon silver da kofin silver na ruwan sha. "Ga abinci aba baƙuwa" Ta dubi Mabaruka tace. "Sannu da zuwa, ina yini?" "Lafiya lau, nagode sosai" murmushi Nabila tayi kawai ta fice. Mabaruka ta jawo abincin ta buɗe, ina ganin sanda tayi turus tana kallona, kai kawai na sauke inaji tamkar ƙasa ta tsage in faɗa tsabaragen kunya. Numfashi naji tana ta saukewa tana ɗauka. Ni dai ban ɗago kaina ba balle mu haɗa ido. "Zubaina wai shin kin zaɓi zama a cikin wannan uƙubarne har kika amince da zaman harma da ƙaruwar juna biyu a tattare dake? Ko ko so kike in kika haihu lafiya ki cika ma rigarki iska ko ya abun yake? Dubi wata jagalgalalliyar shinkafa fara sol da wani mitsitsin yaji a gefe, ke kanki kin ganki kuwa, amman kina duba madubi kuwa?" Ina dubawa Mabaruka, amman inaso ki sani, Allah kamar ya kawoni cikin gidannan ne domun ya ramama Bulama da mahaifansa abinda na aikata a kansu. Mahaifiyar Bulama ta jima tana yin adda'ar Allah ya saka mata. A gaban idona a Damaturu ta faɗa, a wata ziyarar bazata da mu kai musu, ziyarar da bazan taɓa mance ta ba. Ni wacece da Allah bazai azabtar dani akan hakkin bayinshi dana ɗauka ba. Babban abunda yafi mun raɗaɗi shine, nisa da nayi da yarana. Yanzune na gane girman abunda na aikata, mabaruka duniya makaranta ce, mai cike da ɗumbin ajujuwa, ko wanne aji da irin darasin da ake koyarwa. Ni kam ko Alh Liti kasheni zaiyi, na yarda na aminta inyi bautar Allah, wataƙil hakan kankarar zunubine a gareni." Ina kaiwa nan naci gaba da sharar hawaye. Mabaruka tayi tsuru_tsuru nan take ta soma tunanin makomarta da kuma gobenta, bata san ya zata kasance ba. Dan Mabaruka azzalumace, tayi ma Adam da Sagira zalunci mai girma. Ita kanta tasha jinin jikinta sakamako yananan fitowa a kanta. Abincinnan kuwa bata ci ba, rufewa nayi abuna, da daddare naci, in huta da cin dokunu yau. Tana sallah na fita na karɓo abincina, a tsakar gidan na tarar da Zarah a bakin ƙofarta, sai harare_harare take yi. Ni kuwa banbi ma ta kanta ba, damuwar da take nuƙurƙusan zuchiyata ma kaɗai in aka barni dashi, a kwana a tashi zai iya zama sanadin ajalina. Sai da daddare Salisu yazo ɗaukar Mabaruka, da kwatance ya kawo kanshi har ƙofar gida, a bisa jagorancin dan lori daya ɗauko. Zuwa wannan lokacin zazzaɓin dake kaina ya wuce gaban misali, bakina kuwa ya aune ya suntuma. Mabaruka babu yadda batai dani ba, kan muje asibiti, amman fur naƙi, sai maganin zazzaɓi taimun alƙawarin zasu kawo mini. Har ƙofar gida na rakata, mu ka gaisa da Salis, sannan na dawo gida akan zasu je su siyo mun magani su dawo. Ina shigowa cikin gidan na ji Hajiya Kubra na fama da Zarah akan taje ta buɗe ma Alh Liti get ɗin ɓarayinshi. Da ƙyar ta tashi ta tafi fuu. Da idanu kawai na rakata, haka kurum sai naji jinina sam bai haɗu da Zarah ba. Dan na fuskanci irin yarannanne masu buɗaɗɗen idanu, masu ido a tsakar ka, bakina na taɓe, na nemi waje a gefen Nabila na zauna, sai cin Dokunu take yi, Amman ranta a jagule yake ainun. Lafiya kuwa Nabila?" Ajjiyar zuchiya ta sauke. "Daga gida aka kirani, mahaifiyata rai a hannun Allah, to inason zuwa gidane dan in dubata, shekarata uku rabona da gida. Kinji duk abinda yabi ya damu raina kenan. Alh Liti nasan ba barina zaiyi ba ko da na faɗa mishi uzirina. Kuma dole saina jira lokacin ganawa ta zagayo, ko kuma in kwanana ya zagayo. Bazan iya ɗauke har kwana biyar ban gana da mahaifiyata ba." Hawayene ya sulalo mata a kumatunta, ni kaina sai naji kamar in zubar mata da hawaye. Hajiya Kubra dake jinmu tace. "Ki daure lokacin kwanan naki ya zagayo sai ki sanar mishi, tunda baki da wani zaɓi. Ba zamu gushe muna adda'ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan halin da muke ciki ba. Har gaban abada bazan dena dana sanin Abinda na aikata har yai silar shigowata gidannan ba. Allah yasa ya zama izina ga mata masu shegen son abun duniya. Domun Alh Liti cikakken mayaudarine, wanda duk wayonka baka isa ka ganeshi ba. Yayi amfani da dukiyarshi, da kwaɗayinmu, dana iyayenmu ya ɓarar damu." Muna cikin wannan maganar muka jiyoshi yana rangaɗama Nabila kira a ƙagauce. Kanmu yazo ya tsaya "Munafukan Allah ta'ala an kafa taburmar zagina da tsine mun ba?. Ke kuma iyayenki sun kirani da yamma suke sanar dani rasuwar mahaifiyarki. Dan haka sai ki shirya gobe a saki a mota zuwa Lagos, daga can sai ki nemi motar garinku. Kwana bakwai dai_dai na baki. In kika wuce hakan zaki gane kuskurenki." Fuu ya koma, Nabila kuma ta sau kuka harda kururuwa, sai mune mu kaita tunasar da'ita adda'a ya dace ace tayi, ga ciki a jikinta tayi haƙuri. Muna cikin wannan halin Mabaruka ta dawo. Na ganta da ledoji niƙi_niƙi a hannunta. A tsakar ɗakina ta dure. "Ga kayannan na tabbatar zasu yi miki amfani. Akwai suturu kala uku a ciki, nawane dana siya a Dubai, kya yi fitar suna dasu. Akwai kuma kayan ciye ciye, irin su yogot, chocolate, cincin, da dai sauransu. Ga kuma wannan kuɗin da maganin Salis yace in baki. Zubaina ni kaina da da hali wlh da na dena bin bokaye. Ga Mama ba lafiya sai sunturin asibiti muke yi. Ni gabaki ɗaya na tsinke da wannan lamari." Haka dai mu kai sallama da Mabaruka ina hawaye. Maganin zazzaɓin da su ka siyo mun na ɓalla nasha. Komawa nayi wajan Nabila, sai faman kuka da sambatu take yi. Washe gari sassafe Alh Liti yasa ɗanshi ya kaita tashar mota aka sata a motar Lagos. Cikin alhinin taima kowa sallama ta tafi. Rayuwa haka tai ta garawa damu, kullum ba daɗi, bala'in yau daban na gobe daban. Zarah kuwa Alh Liti ya ladabtar da'ita ta dena yi mishi tsiwar da take yi mishi. Sai dai na lura Zarah kishi take yi dani sosai. Dan ko wucewa nazo yi sai ta ja tsaki. Ni kuwa sai dai inyi mata murmushi kawai, lallai kura tayi lafiya. Da dane Zarah bata isa mun haɗa mijibaa, balle harta samu ƙwarin guiwar yi mun tsaki a tsakar gida. MRS BUKHARI CE [15/08, 2:50 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: 45 GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) . BULAMA BABBA. Sai karo muke ci da iyayen yara masu shige da fice. Ni dai Allah Allah nake yi inga Yahanasuna, da kuma yanayin lafiyar jikinta. Muna shiga cikin asalin inda ɗakunan nasu yake, muka hangota tana zaune a bakin baranda, tana kallon ƴan uwan zamanta masu ganawa da iyayensu. Idanunta carab ya shiga nawa, take naga ta shiga sharar hawayenta. Ji nake ni kuma tamkar in je in rungumeta tsam a jikina in rarrasheta, kuma in tusata gaba mu dawo gida. Rashin Yahanasu ba ƙaramin giɓi yai ma rayuwata ba. Malam Rilwanu ne ya taryemu da fara'arshi. "Alh Modu barkanku da shigowa, maraba lale an sha hanya. Tsaiwa gaisawa suka yi. Ni kuma na wuce wajan Yahanasu da take ta kuka. Ina isa ta miƙe tana son rungumata, nima abinda nake so kenan. Amman ana barin halak dan kunya, baya nayi da sauri sai ta faɗa jikin Yanuna tana mai kuka kamar ranta zai fita. "Me nayi muku kuka kawoni wannan gidan azabar, gidan da kullum sai an dakemu, kashemu suke son yi. Dan Allah Bulama Babba kace a tafi dani gida. Wallahi na tuba bazan sake shan ko ruwan shayi ba balle wani abun maye." Zuru nayi ina kallonta cikin tausayawa. Ba Modu ne suka iso dasu Gunsum. Ƙasa Yahanasu tayi da kanta, kunya take ji da ganin yanayinta. Lallai akwai nasara fiye da ta baya. Sai dai muguwar ramar da tayi ya bani tsoro, ta sake yin baƙi sosai, kamar ba Yahanasu ƴar lukuta dana sani ba. Ba Modu ya ƙura mata idanu ƙur, sai kuka take faman rerawa. Kai kawai ya girgiza, nasan dole yana tausayin Yahanasu amman girman abunda ta aikatane yasa yake danne tausayinta da yake ji. "Yanunu kuje ke da Fanda wajan Malama Fahiƙa kuji yanayin jikin nata. Kai kuma Gunsum muje gefe inason magana da Malam Rilwanu. Watsewa suka yi suka barmu mu kaɗai. Kallona take ta yi. Hankali da halama ya soma dawowa jikinta, amman ba wani sosai ba, sai dai naji daɗin yanda ta gane mu dukkanmu. Amman yanayin ramarta ya ɗagamun hankalina. Zo muje mu zauna ki samu kici abinci Yahanasuna" Hannunta na kamo, ɗayan hannun kuma na ɗauki basket ɗin abincin. A wata tabarma kusa da wasu suma kamar mijinne ya kawo ma matarshi ziyara da yaransu. Bawa da Maryam suna biye damu. Muna Zama Yahanasu ta ɗauki maryam a cinyarta, Maryam kuwa tayi lub a jikin Yahanasu. "Ina Yusuf shi?" Da mamaki na dubeta da har ta iya tuno Yusuf. Bawa ne ya bata amsa. "Yana wajan Ya Innana, yana shan kunu da ƙwai" Murmushi nayi musu. Na buɗe abincin na zuba mata a plate. Hannu baka hannu ƙwarya ta dinga cin abincin tana shaƙewa, dan biski baka isa ka mai cin gaggauwaba. Ruwa na ɓalle zan miƙa mata, ta warce da sauri sai da ta shanye tas. Cikin raɗa tace. "Dan Allah zaka bani laka mis in ɗan kora, ko ƙwaya zaka bani in zuba in kora da kodin? Sai kuma ta sau kuka dai, tana ambaton kayayyakin mayen data saba sha a koda yaushe. Lallai akwai aiki ja a gabanmu, na ganin Yahanasu ta dawo hayyacinta. Gashi Hajja tace tana son ta tattauna dani in na dawo, bansan mai take son mu yi magana a kai ba. Alkakin da Hajja tace in bata na damƙa mata a hannunta, na soma share mata hawayenta. Ki dinga ambaton Allah a duk lokacin da zuchiyarki ta bijiro miki da wani abun maye da kika sha a baya kinji ko? Muma ba'a kwance muke ba, adda'a muke miki Allah ya yaye miki wannan ciwo. Ki yi haquri kukanki na dagula mun zuchiyata kinji ko?" Kai ta gyaɗa mun, bata ce dai komai ba, sai daga baya ne inta ɗebo zancan arziki ringiɗi_ringiɗi sai kuma ta kasa ƙarashewa, a mugun sanyaye take magana tamkar mai raɗa. Yanunu da Fanda ne suka iso inda muke, Yanunu ta zauna kusa da Yahanasu tana sharar hawaye. "Oh Yahanasu Allah ya baki lafiya ki rabu da zaman gidannan. Nifa Bulama Babba da ace Modu zai ji shawarata da mun koma da Yahanasu asibiti. Gabaki ɗaya wajan bai kwanta mun ba, amman naga Modu a wannan karon ya ɗauka da zafi. Innana tayi mishi zancan a dawo da Yahanasu Babban asibitin Yobe amman fur yaƙi. Baiwar Allahnnan ko rintsawa bata yi, duk tabi ta ƙare sabida fargaba da tunanin me kaje kazo." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To Yanunu Ba Modu bazai yarda da wannan zancan ba, kwanaki dana matsa mishi da zancan, cemun yayi in batun dawo da Yahanasu ne zai dinga kawoni Damaturu to kar in kuma zuwa in yi zamana a Yobe. Yanzu dubi duk yanda ta lalace fa, ni bansan ma ya zanyi ba. Bani da sukuni da kwanciyar hankali kwata_kwata. Duk wani kula da kamfani da wani gyaran gida da muke yi. Ahmad ke yin komai, Hajara kuma ke kular mana da yaran duka." Muna cikin haka Gunsum da Ba Modu suka iso inda muke. "To inaga ya isa haka, sai ku taso muje ko? Amman kafinnan Bulama likita yana buƙatar ganinka." Miƙewa nayi na nufi ofishin likitan, yana zaune yana rubuce_rubuce . Gaisawa mu ka yi, ya bani kujera na zauna ina fuskantar shi." "Yahanasu tana samun sauƙi sosai, duk da tasha manya_manyan ƙwayoyin maye kuma ta jima a cikin rayuwar. Duk sanda nazo dubata ina ganin sauƙi tattare da'ita. Kuci gaba da yi mata adda'a. Amman har yanzu bata dena kiran abata ababen mayen ba, har ihu take yi duk ta birkita kanta, in abun ya motsa mata. Shi yasa ake ɗan dukansu domun a dawo dasu haiyacinsu. Duk da hakan ya saɓa ma doka, amman ana samun ci gaba ta ɓangaren yi musu barazanar duka, ko a dake sun. Sannan kullum ana basu rubutu suna sha. Ga sana'ar ɗinki da jiya ta soma shiga koyo, duk da hankalinta baya kai. Babu walwala a tare da'ita sam, amman in aka dage da adda'a ba zata wuce wata shida ba ƙila a sallameta. Dan ko yau mun sallami mata bakwai sun koma cikin iyalansu." Ajjiyar zuchiya na sauke, ina jin ɗacin dukan da likita ya faɗa mun ana ma Yahanasu. Amman nasan Ba Modu ba saurarena zaiyi ba. Gunsum ne ya leƙo. "Bulama Babba Ba Modu yace ka fito mu tafi, suna mota kai ake jira." Jikina a mugun mace na miƙe, musabaha mu kayi da likita na fita zuchiyata a raunace. Ko da na fito na samu duk an mayar da su ɗakunan su. Cikin gidan ya kaure da iface_ifacensu. Malam Rilwanu kuma sai sallamar iyaye, da ƴan uwa yake yi, kan cewar lokacin su ya ƙare dan Allah suje. Ficewa nayi ba tare da nayi sallama dashi ba. Baya na shiga kusa da Fanda, na jingina bayana a jikin kujera, idanuna a lumshe kaina mugun saramun yake yi. Ko a mafarki ban taɓa tunanin zanyi mafarkin Yahanasu a irin wannan mawuyacin yanayin ba. Ina zan tsoma raina ne, wajan wa zan kai kokena dan ai ma Ba Modu magana ya yarda a dawo da Yahanasu gida? Tunowa nayi da umman Ahmad nasan Ba Modu yana matuƙar ganin girmanta, shawara na yanke zanje in sameta in faɗa mata buƙatata. Da tunane_ tunane barkatai naita hira a zuchiyata. Ina jin su Yanunu suna zancan basu ji daɗin ganin Yahanasu a halin da suka zo suka isketa ba. Kowa na tofa albarkacin bakinshi. Ni kuwa sun ɗauka ma bacci nake yi, dan idanuwana a lumshe suke. Haka mu kaita sharara gudu a hanya. Bamu muka isa Damaturu ba sai taran dare. Ɗakin Ya Innana na zarce dasu Maryam na ajjiyesu, anan naci abinci kamar yadda na saba. A ɗakin Ba Modu ya shigo ya tadda ni, ina kallon labarai. Sannu da zuwa Ya Innana tayi mishi bayan ya zauna ne take tambayarshi yanayin jikin na Yahanasu. "Jiki kam da sauƙi sosai, danni naga sauƙin jikin nata fiye da asibitin. Ki yi ta mata adda'a bazai faɗi ƙasa banza ba." Ya Innana tace. "Amman ni da za'a daka ta tawa da an mayar da yarinyarnan asibiti. Ire_iren gidajennan fa ba ƙaramin mugunta da azabtar da mutane suke yi ba. Ga yawan mafarkai da suka addabeni duk akanta." Take Ba Modu ya gintse fuskarshi yayi kicin_kicin yace. "Ko kasheta zasu yi sai dai su kasheta. Da ace Yahanasu ta riƙi adda'a batai watsi da tarbiyyar gidannan ba, da bata cikin halin da take ciki yanzu. Tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa ka duka, kar ku kaini bango akan batun Yahanasu" A tausashe nace. Ba Modu ko wanne bawa baya wuce ƙaddararshi. Ciwon damuwa ciwone da babu abunda baya sa mutum ya aikata. Tunda waɗanda suka tsinci kansu a irin wannan halin, har kashe kansu da kansu suke yi" "Ita adda'a ai ta game komai. Da ace tabi koyarwar ma'aiki arrasul S A W da bata tsinci rayuwarta a cikin gidan mahaukata ba. Uwarta gata nan kullum a cikin damuwa take, cikin da take samu yaƙi zama, kullum a cikin yi mata adda'a take. Ashe ita ke zubar da cikin da gangan dan samun wani farin ciki na rayuwarta. Ku barni haka da batun yarinyarnan haka ya isheni. Na san da ƙaddara, sannan nasan adda'a na iya sauya ƙaddara daga mummuna izuwa kyakykyawa. Sanadiyyar yarinyarnan na rasa Bakura amini, kuma uba, wa a gareni. Baƙin cikin Yahanasune ya buga mishi zuchiyarshi. Ya bazan damu ba." Hawaye ya soma zubarwa, a wajan ya fita ya barmu, jikkunanmu a sanyaye. Ni kam abun duniya ya haɗu yai mun yawa. Yanzu ne na gane dalilin Ba Modu na nuna halin ko in kula akan lalurar Yahanasu, da kuma irin gidan da yasa aka kaita dan neman lafiya. Shi gani yake sabida ita Ba Bakura ya mutu. Alhalin ko Yahanasu bata aikata komai ba, Ba Bakura zai mutu da zaran wa'adin zaman duniyarshi ya ƙare. Nunfashi na fesar mai zafi. Ya Innana tace. "Ka samu ka shiga cikin gida ka huta Bulama Babba. Babanku ya ɗauka da zafi sosai. A tunaninshi Yahanasu ce tasa yayi rashin ɗan uwanshi. Bashi da laifi dan ya ɗauki fishin da yafi wannan a kanta. Kaje, nasan Modu ya fini,ya fika son Yahanasu, kuma in Yahanasu ta cutu, sai ya fini ya fika cutuwa, ai shine mahaifinta, ba dan rashin so yake yin hakan ba. Sai dan tsoratar da ƴan gaba, su shiga taitayinsu. Tunda wannan shaye_shayen ya tashi daga hula ya dawo ɗan kwali. Babban abunda ya sani a damuwa yau ɗin nan, shine labarin rasuwar ƙawarta hajja Fati, sakamakon haɗarin mota data samu. Wanda ya bigetan yace wai a bige ta shige mai gaba a titi. Kuma ko da aka bincike jakarta wallahi Bulama Babba cike da kayan maye aka tarar da jakar. Ɗazu da na shiga yima mahaifiyarta ta'aziyya ne take labartamun wannan zancan, dan labarin haukacewar Yahanasu ya karaɗe anguwarnan dama kewayenta." Shiru nayi ina nazarin maganganun Ya Innana, ina tunanin ko dai Yahanasu ta koya ma Hajja Fati shan muyagun ƙwayoyi, ko kuma ita Hajja Fatin ta koya ma Yahanasu, domun amintarsu tayi kama da amintata da Ahmad, Ahmad kuwa babu abunda muke iya ɓoyema junanmu. Allah ya kyauta, ita kuma Allah yai mata rahama. Zuwa gobe kafin in wuce zanje in musu ta'aziyya." Miƙewa nayi na fita. Sai da na zaga iyayenmu mata duk na gaishesu, na ba kowacce ɗan kuɗin kashewa, ɗakin Hajja ne ƙarshen shiga. Tana zaune akan dadduma hannunta da carbi tana ja, da sallama na shiga na zauna a gefenta nesa da'ita ba sosai ba. "Yaya mai jikin kuka sameta?" Ɗagowa nayi muka haɗa idanu da'ita. Naji muryarta babu daɗi sam, na kasa karantar yanayinta. Jikin Alhamdulillah, da muka je ta gane mu, harma tace sai dai mu tawo da'ita. Kuma acan ma ance mana jikin nata da sauƙi." "To Allah ya ƙara sauƙi. Kaci abinci a wajan Innana ko?" Kai na ɗan sosa nace mata. E nan na soma shiga ma, na kai mata yaranne." "Maganar da dama nake son yi da kai shine. Me zai hana tunda kana da lafiyarka, kuma yanzu kafi ƙarfin ciyar da mutum ɗari ma, me zai hana kayi aure? Ai ba zaka zauna haka ba, tunda ita matar taka bamu san yaushe zata warke ba ko." Dum gabana ya buga, kuma na sha ruwan mamaki da naji irin wannan kalamin a bakin Hajja. Domun nayi tunanin ko ni nazo mata da irin wannan zancan ba zata yarda ba. Sai gashi daga rasuwar Ba Bakura komai yana son sauyawa, duk wasiyyar daya dinga jaddadawa akan muyi riƙo da zumunci, kar muyi sake zumuncinmu ya tarwatse. Ya Ba Modu zai fassara wannan maganar in ya jita, Ya Innana me zata yi tunani?" "Kayi shiru nayi magana baka iya cewa komai ba." Ba haka bane kiyi haƙuri Hajja. Bani da ra'ayin haɗa matsayin Yahanasu da ko wacce mace a zuchiyata" "Har dani dana ɗauki cikinka nayi naƙudarka? Ko da yake ai barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafeba. Innana ma ai ta riga data shanye Modu. Da badan tasan wanshi yafi ƙarfinta ba, ƙila da harshi zata mallake. Yanzune Bagulaji ta dena zuwa falonnan kawo ƙarar Modu bisa fifita Innana da yayi akanta. Zubaina ma ta mallakeka balle Yahanasu jinin Kanuri gabanta da bayanta" Kaina ne naji ya buga. Ni bansan mahaifiyata da haka ba, ban taɓa ganinta a cikin irin yanayinnan ba, to wa yake zugata, ko dai ƴan uwanta da suka zo ta'aziyya ne suka zugata. Bani da mai bani wannan amsar, baki na kada nace Ko kusa, aike matsayinki da banne, baki a cikin jerin abinda nake nufi. Amman Hajja Yahanasu ƴarki ce, ko bani take aure ba nayi imani ba zaki so ta ƙuntata ba. Kuma tayi mun dukkan alkhairi. Bata da wani laifi a wajena, face wannan jarabawar data sameta. Ni bani da sha'awar mata biyu. Kiyi haƙuri, sannan bani da wacce na gani naji inaso" Na ƙarashe maganar har ina haki, tsabar yanda ƙirjina ke bugawa. "Yayi tabbatacce. To naji, kai in baka da wacce kake so, ni akwai wacce na gani kuma nake so. Bazan sa aima ƴar mutane Auren dole ba. Amman kaje ku daidaita. In ma ka nuna mata baƙin rai dan ku kasa daidaitawa, to fa ka rubuta ka ajjiye zan yi ma Auren dole, kamar yadda aka yi maka akan Yahanasu, bayan ta saryar da mutuncinta, dan ba wani fyaɗe da akayi mata biri boko kawai akayi mana, ƴan uwanta ƴan maye ta bama jikinta suka yagalgala. Tashi ka bani waje, kuma gobe kafin ka wuce ka tabbatar ka je ka ga Yalewa ɗiyar ƙanina Bature." Da sauri na kalleta da naji sunan wacce ta ambata, amman ganin a hasale take, ga takaba tana yi sai nace mata. To Allah ya nuna mana, mu kwana lafiya" Na miƙe jikina har yana rawa_rawa na fice. Ko da na shiga ɗakin masaukina. Kasa nutsuwa nayi. In kai mari in kai gwauro. Hajja ta jefa ni a cikin tsaka mai wuyar fita. Ina jin tsoron ƙiris abunda zai sa in zama silar ɓacin ran iyayena, ina tsoron kuma lalacewar zumunci. Amman taya zan yi aure, alhalin zaman lafiya muke yi da Yahanasu. Ita kaɗai ya cancanta tayi rayuwa a ƙarƙashina, taji daɗin dukiyata. Dole tun wuri Ba Modu yaji wannan labarin, duk da nasan ba labari bane me daɗi. Amman shigarshi cikin lamarin yana da kyau. Ahmad ne yake kirana a waya. Numfashi na fesar me zafi, na ɗauki wayarshi. Hello Ahmad ba kai bacci ba?" Ahmad ya amsa daga ɓangarenshi da cewa. "Wane bacci zanyi banji daga gareka ba. Na kira wayarka yafi sau a ƙirga, amman network bai bani damar samun naka ba. Kana Damaturunne, yaya kuma jikin ita Yahanasun?" Ahmad jikinta ba laifi da sauƙi. Harma ta gane mu. Amman Yahanasu ta zube ta lalace sosai ba ma kace ita bace. Na sake shiga damuwa sosai dana ganta Ahmad" Ahmad cikin sigar rarrashi yace. "Dama ai dole ta lalace Bulama, ciwo take yi fa na rashin hankali. Amman tunda sauƙi yana samuwa ai abunda muke nema kenan. Cikin kwana bakwai kake yin sauka, kuma kayi sadaka tare da tawassali cewar Allah zai bata lafiya. Kayi haƙuri kar kaima ka jefa kanka a cikin deepretion, ayi ƴa kwance uwa kwance, kaga an ɓata goma ɗaya bata gyaru ba." Ahmad Hajja tazo mun da wata magana mai tayar da hankali ainun, a wannan halin da nake ciki in ba'a rarrasheni ba, ai ba'a ɗaga mun hankali ba. Aure fa Hajja take so inyi. Kuma ta rasa da wacce zata haɗani sai Yalewa ɗiyar Kawu Bature, yarinyar da tsabar boko take ganin maza ma ba a bakin komai suke ba. In ƙi aurenta Ba Bature yace naƙi jininshi, in aureta Yahanasu taga kamar nayi mata butulci." Ahmad ya fi minti talatin yana rarrashina tare da tunatar dani girman iyaye, da fa'idojin adda'a, dana istikara. Madallah da abokin ƙwarai irin Ahmad. Ko babu komai ya kwantar mun da kaso hamsin cikin kaso ɗarin damuwata. Ban gushe ba sai da nayi sallar nafila tare da roƙon Allah ya bani mafita, bacci nayi mai nauyin gaske. Washe gari na tashi da niyyar kama hanyar Yobe dan komawa bakin aiki. Ko da nayi ma Hajja sallama sai da ta tuna mun da batun zuwa gidan Kawu Bature, Yalewa na nan tana jiran isowata. To kawai na iya ce mata na ajjiye mata dubu ɗari a gabanta na fita. Su Bawa na turo mata nace suyi mata sallama in sun fito su sameni a garejin mota. Da wakil naci karo a tsakar gida yana nufar hanyar turakar Ba Modu. Tare muka jera dashi yana tambayata jikin na Yahanasu. Yaran gidan sai kallona suke yi, kafin in wuce sai da na rabama yaran gidan dubu ɗaɗɗaya, iyayensu kuma na basu dubu bibbiyu yaran suka kai musu. Wani irin girma na musamman matan ƙannen nawa suke bani, kuma hakan na da nasaba ne da yanda ƙannen nawa suka ɗaukeni da mahimmanci. A turaka muka samu Ba Modu shi kaɗai yana lazimi. A kusa dashi daf na zauna kamar yadda nake yi da a lokacin da bana auren Yahanasu. Kallona yayi cike da so da nuna kulawa yace. "Ji yanda ka rame akan Yahanasu, ya kamata ka sassauta ma kanka, na ganka a cikin sabuwar damuwa" Bansan sanda na fara yi mishi bayanin yanda mu ka yi da Hajja ba. Murmushi kawai naga Ba Modu yana yi, yana girgiza kanshi. Wakil kuwa miƙewa yayi yanason ya bamu waje. Dubanshi nayi jikinshi duk ya mace nace. Dawo ka zauna Wakil" Baiyi musu dani ba, domun ba tarbiyyar gidan bace. Ba Modu kallonmu yake yi yana karantar yanayinmu dukkanmu, can yace. Mrs Bukhari ce[16/08, 9:05 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 46 "Dama da ganin take _ taken Hajja nasan wannan abunne zai biyo baya. Tunda Innana ta sanar dani kowa ya shigo mata banda Hajja. Duk da nasan tana takaba ne, amman ai Yahanasu tata ce, ko babu aure daya gibta a tsakaninku nayi imani zata damu da halin da Yahanasu take ciki. Ballantana kuma kai ke aurenta. Danginta na ɓangaran mahaifinta su suka zugata kan wasu al'amura bayan rasuwar Bakura. Wanda dani da'ita da Kawunku Bature muka zauna harda ma Hamma. Kan batun gidanmu da ake haya a ciki na waccan anguwa. To ni dai nasan gidan namu ne mu biyu da Bakura. Amman gudun matsala yasa na bar muku ku magada, domun Hajja tace bata amince ba, sabida babu shaida, kuma takaddun gidan da sunan mijinta aka saka. Ba zaku san anyi dukkan wannan abun ba, kuma abunda na lura Bature shine yake mata ingiza mai kantu ruwa. Dan rankatakab dukiyarta ta tuminin takaba, gidajen Bature ke kular mata dasu. Ni dai na ɗakko idanu na zuba, Bature ya kai mari ya kai gwauro a cikin gidannan. Hatta mata dake cikin gida basu da masaniya kan komai. Ni dai abunda zance maka kayi mata biyayya dan a zauna lafiya. Ko kusa bana fatan zumuncin gidannan ya tarwatse. Wannan dalilin yasa matan Baana na hana ko waccensu tafiya nace su share waje su zauna. Toh Bakura ya jaddada wasiyyarshi a gareni kan, lallai lallai in haɗesu dukka biyun in auresu. Nima da nayi wannan tunanin tun rasuwar Baanan, amman ganin cikinmu babu wanda ya samu nutsuwane yasa ban fitar da zancan mata sun sani ba. Amman yau nake shirin tunkararsu da zancan, in muka sasanta kanmu dasu, sai kuma iyayenku su samu labari. Ko bayan raina Bulama Babba ka kasance jajirtaccen uba a Cikin zuriyarnan. Kar ka bari ayi wasarairai da zumunci. Ashirin ga wata akwai taron ƴan uwa da aka saba yi, zamu ɗaura daga inda aka tsaya. Ku tashi ku tafi, Allah ya tsare maka hanya. Kai kuma Wakil sai ka dawo." Jikkunanmu a sanyaye muka fito dukkanmu. Sallama nayi da kowa, na samu su Bawa a gareji su da Ba'a Kaka, sai zabga mishi surutu suke yi. Shi kuma ya biyesu sai dariya yake faman yi musu. Hannu na miƙa ma Ba'a Kaka, cikin girmamawa ya miƙo hannunshi muka gaisa. Yaya iyalan naka kowa lafiya ba wata matsala ko?" Kai ya sosa yace. "Ba komai Bulama Babba, kowa yana lafiya. Yanzu ma aka kwashe kab yaran gidan zuwa makaranta, shine na tsaya a wajan su Bawa muke hira. Murmushi gajere nayi mishi, kana na shiga mota. Kowa ya ganni yasan ina cikin matsananciyar damuwa babba. Wakil ne ya tura su Bawa mota, dubu bibbiyu Ba'a kaka ya basu. Wakil kuma ya basu ɗari biyar biyar. Har sai da na ɓace na daina ganin hannayensu da suke mun adabo dashi. Cike da tunane_tunane kala_kala na ƙarasa ƙofar gidan Ba Bature, nama mance da zancan zuwa gidan umman Ahmad kan batun Yahanasu. Kaina yayi zafi da yawa, sai dai in na gama da nan in koma baya. A gefen kwatar gidan na ajjiye motata na fito, su Bawa suka fito muka shiga baki ɗaya. Suna tsakar gida dukkansu karyawa suke yi da kokko da ƙosai. Ba Bature yana ganina ya shiga washe bakinshi. Goggo Bulu tace. "Me gidan da ba cefane yau kaine a gidannan? Rabonka da gidannan tun sanda uwarka ta zo da goyonka, sai yau kuma da Bulama Babba ya kawo ka. Ga kuma kishiyata Maryama ba. Dariya mu ka yi duka, kan ƙaton kafet ɗin da suke nima na hau. Kokko da ƙosan dake gaban Ba Bature ya turo mun, bakinshi cike da kokko yace. "Bismilla sha Bulama Babba. Su kuma saji da yaran. Banyi musu ba naja kwanon ƙosan gabana naci biyu, na kora kunun. Sannan muka shiga gaisuwa. "Zaina yaushe kika shigo Damaturu? " Zaina yar Yalewa ce, itama batai aure ba. Ma'aikaciyar banki ce a bankin FCMB dake hijar Yobe. Acan take da zama ta kama gida, sai dai ta kawo musu ziyara. Mai sunan Hajja kuma tana karatun mastars dinta a jihar Borno, ƙanwarsu ce itama batai aure ba, sai ƙaramarsu Yana ita kuma digree take haɗawa a fannin kasuwanci. Zaina tace. "Jiya nazo, yau da yamma zan wuce. Ya jikin Yahanasu kuwa? Kwanaki dana zo Ba Bakure yake sanar dani taɓin hankalinta." Yaƙe nayi nace. Ayya, jikin da sauƙi, jiya ma muka je dubota da yaran duka. Goggo Bulu tace. "Allah ya bata lafiya. Ka shiga daga falo Yalewar wanka take yi, inta kintsa zata sameka a ciki" Bance uffan ba na miƙe nabi umarninta zuwa cikin madaidaicin falonsu, wanda yaranta suka cika mata tab da kayan alatu. Zama nayi a saman kujera ina karanta wasiƙar jaki. Nafi minti talatin a zaune kafin Yalewa ta buɗe labule ta shigo. Idanu muka haɗa, ta wani yamutse fuskarta kamar taga kashi, ko wani mugun abun. Doguwace Yalewa sosai, fara sol da'ita kamar ba Kanuri ba, gata da gashi irin na matan Kanuri, maganar diri kam in yana yawa to yayi mata yawa, akasarin matan ƙabilar Kanuri Allah ya azurtasu da kyakkyawan zubi da tsari ta ɓagaren jikinsu dama fatarsu, sai dai basu cika kyau ba, kuma da wahala kaga farin Kanuri. Gogaggiyace sosai riƙaƙƙiyar mace wacce ta zama minista a gidansu tsabar girma. In ban yi kuskuren lissafi ba Yalewa zata kai shakara talatin da bakwai shekarun haihuwa. Sanye take da baƙar lafaya mai adon jan zare. Tayi kitson gaba irin na al'adunmu. Waje ta samu nesa dani ta zauna. Ƙur na zuba idanuna a nata ina ƙare mata kallo, gami da karantar yanayinta. Da dukkan halama ita kanta tursasa mata akayi saurarata kamar yadda nima a kaimun. Ni ina ma zan kai wannan tsohuwar guzimar. Tunda baki da bakin gaisheni ni bari in gaisheki. Ina kwana?" Kallona tayi rai a haɗe tace. "Baƙin gaisheka nayi ba, ina shirin yin hakan ka katse mun hanzari." Kinsan dalilin zuwan nawa ai, dan nasan Ba Bature yayi miki bayanin abinda suke son ƙullawa. Duk da ni bani da ra'ayin haɗa matsayin Yahanasu da kowa. Amman sabida iyaye da gudun rushewar zumunci dole in amsa umarninsu. Amman ke ta ɓangarenki meye ra'ayinki game dani da kuma auren? Kar ki cuci kanki ta hanyar kasa faɗin abunda ke ƙasan zuchiyarki. Ki sani Aure ba abun wasa bane. Kuma Hajja tace babu mai yi miki dole, in banyi miki ba ki sanar tun kafin tafiyar tayi nisa." Zuba mata idanu nayi ina karantarta. "Zahiri ni ban taɓa jin ina ra'ayin ƙulla wata alaƙar data wuce ta zumunci a tsakaninmu ba. Da ace kayi mini, ko kana daga cikin zubin mazajen da nake buri. Tabbas da ita kanta Yahanasu da bata same ka ba, tunda a gabanmu suka taso. Tun a jiya da Hajja ta kira tana sanarma da Ba Bature zuwanka. Ban ɓoye musu komai ba, ba kai mun ba. Kar azo ayi abunda duk rai bazai yi daɗi ba. Aini a ganina aurena sai babban mutum sosai wanda ya ƙara rabi akan shekarunka. Kuma ina nan akan bakata, babu wanda zai mun auren dole. Ina da wanda muka gama maganar aure dashi, da zaran ya dawo umara zan gabatar musu dashi." Wani daɗi da farin ciki ne ya ziyarceni, harma ya kasa ɓoyuwa a fuskata. Zama na gyara na dubeta ina ɗan dariya nace. Kin kyauta, lallai kina son zumuncinmu yaci gaba da ɗorawa, nima zan yima Ba Bature bayani ta yanda zai fahimceki, suyi haƙuri ki auri wanda kuka yi alƙawari kawai. Na kuma gode da baki yi wani rufa_rufa ba." Dariya itama tayi mun tace. "Haba da wayewata zan tsaya a tauye mun hakkinane? Ai aure dole hatta a addinance bai dace ba, ballantana a zamana ce. Mastas gareni fa, ma'aikaciyace ni tsawon shekara goma ina cin gumina." Hakane kam. To Allah yasa mu dace. Ni kam zan kama hanya, sai in na kuma shigowa garin kuma" Tare da'ita muka fito faram_faram. Ganin mu hakan ya ƙara ma Ba Bature ƙarfin guiwa. Sai bayan da muka keɓe a waje nayi mishi bayanin da ita Yalewa tayi mun, nan kuma ya gintse fuskarshi, har yana dakatar dani a zafafe. "Kar ka faɗamun maganar banza Bulama Babba. Ita uwar taka abunda ta turoka kenan kayi, jin ra'ayin Yalewa? Alhalin ni mahaifinta na zaɓa mata mijin da yafi dacewa da'ita. Ko so kake ka nuna ma duniya modu ne kaɗai yafi kowa a duniyar ka mutunci?" Kaina na sauke ina jimamin wannan sabon lamari dake shirin yi mana kutse cikin zuriyarmu. Haƙiƙa Ba Bature shike zuga Hajja kamar yadda Ba Modu ya sanar dani. Bazan taɓa auren Yalewa alhalin nasan ba sona take yi ba, gata da buɗaɗɗen idanu. Mace me buɗaɗɗen idanu ta shani harna warke." A fili kuma nace dashi. To ni zan koma Ba Bature, duk yanda kuka yanke da Hajja ni mai yin biyayyane a gareku." Murfin motata na buɗe na shiga, su Bawa suna bayan mota a zaune. Ficewa nayi daga anguwar na dawo da baya zuwa gidansu Umman Ahmad. A gindin bishiyar mangoron dake tsskiyar gidansu na sameta a zaune a tabarma. Ta tarbemu cikin girma da karamci, Mahaifiyar Ahmad akwai kirki da son mutane. Harna tuno sanda nake biyo ma Ahmad zuwa makaranta. Kullum sai ta ƙulla mana gyaɗa a leda ta bamu nera bibbiyu. Bayan mun gaisa ne na sanar da'ita maƙasudin zuwana wajanta. "To Bulama Babba, sha Allah zanje yau ba sai gobe ba, zanyi magana dashi Modun. Duk yanda mu ka yi zan bugo maka waya. Yaya jikin na Yahanasun amman?" A jikin da sauƙi, tunda har ta gane mu ma da muka je. Banji ɗuriyar Zulai Amarya ba Umma." Umma tace. "Au Zulai ai tana Yobe jiya taje, Hajara tace taje ta zauna a wajanta, satin bikin sai su rankayo su dawo. Zan sake yi maka godiya da kayan ɗaki da kayi ma Zulai Allah ya saka da Alkhairi. Haba umma Zulai ai ƙanwata ce, me yasa zaki ta godemun ne, ni banaso Umma. Sai anjima ma." Dariya tayi tace. "Ɗan nema kamar ba jiya_jiya kake shigowa neman Ahmad hanci du majina ba, ga hawaye kullum a idanka." Dariya nayi sosai. Kullum sai Umma ta yi wannan maganar, sai dai in banzo dubata ba. Kuɗi na ajjiye mata a gabanta, nayi mata salllama. Tuwon madara ta ƙullowa yara a leda muka yi mata sallama muka fito. Gidan mahaifiyar Hajja Fati naje nayi musu ta'aziyyarta kamun na kama hanyar Yobe kuma. Yaran kawai na ajjiye a gida, na juya na samu Ahmad a kamfani. A kujera na kwanta hannuna dafe da kaina. Da sauri Ahmad ya iso inda nake yace. "Kai karfa kaje ka halaka kanka a banza, ka sassauta ma kanka. Zama yayi a kujerar dake gefena yace. "Ya kuka ƙare da Yalewa?" Labarin yanda muka yi na bashi. Cikin zolaya yace. "Yaushe Yalewa zata yarda ta aureka baƙiƙƙirin da kai, ga shegen jan ido, kai hatta dasashinka fa baƙine" Dariya mu ka yi dukkanmu, duka na kai mishi ya kauce a hanzarce. Wallahi nima a zuchiyata haka nace. Gata kyakkyawa son kowa. Ina ni ina samun irinsu, ai wannan sai mijin novel. Yanzu da a novel ne, ina zuwa zata ruɗemun. Allah na tuba mummuna dani yaushe zan ruɗa Yalewa, ai ni ɗin na Yahanasu ne kawai. Ko Zubaina son duniyane yasa ta aure ni, har ga Allah nasan kyanta yafi ƙarfin ace nine mijinta. Shi yasa ma ta garani." Ahmad yayi dariya harda buga ƙafa yace. "Kai dai ka tsorata da mata masu kyaune kawai, amman Zubaina bata fi ƙarfinka ba tunda kaga har ta aureka. Da iliminka da degree dinka kace ƴar talakawa tafi ƙarfinka? Haba kar ka ba da maza mana. Gara Yalewan in kace tafi ƙarfinka kana da hujja mai ƙarfi." Nan mu ka shiga hira muna dariya kamar ba ni ba. Ahmad ya rage mun zugin abubbuwa da dama. Ƙarfe huɗu da rabi muka bar kamfani. Kai tsaye muka nufi ɗayan gidan namu da akeyin gyara. Saura kaɗan ya rage a kammala gyaran, komai yayi kyau. An farfasa ɗakunan an jonesu. Ɗakin Yahanasuna ciki da falo, da bayan gida. Nima nawa haka, sai ƙaton falo a tsakiya wanda anan kitchen yake da ɗakin yara, da ɗakin wasansu. Ɓangaren Ahmad ma haka tsarin yake. Ga filin tsakar gida yalwatacce. Ta baya akwai babban B Q, sai sai wani ɗan fili da aka malala jan kafet. "Kaga nan yara nake son a zuba ma kayan wasan yara su lilo da sulu haka." Na dubeshi nace. Banda ɗakunan wasan da suke dashi a ciki?" "Wancan ɗakin karatune haɗe da wasa ai. Zasu fi sakewa a tsakar gidan ai" Haka mu kai ta zagaye a cikin gidan. Abinda ya rage filasta ne, sai fenti, da kuma kayayyakin cikin bayan gida da tails ɗin ɗakunan da za'a sake. Haka lamura su kai ta tafiya. Umman Ahmad taje ta samu Ba Modu tayi mai magana. Amman haƙona bai cimma ruwa ba. Dan Ba Modu kirana yayi a waya yai mun tas. Ta ɓangaren Hajja kuwa ta buɗe mun wuta sosai akan batun Yalewa tace dole ko muna so ko bama so sai anyi bikinnan. Sannan ta bani umarnin in dinga zuwa gidan Yalewa zance. Al'amura duk suka bi suka cuɗe mun. Har wata uwar rama nayi. Ranar da naje Damaturu ɗaurin auren Ba Modu da matan Marigayi Ba Baana, ranar Hajja ta tusani gaba ta inda take shiga ba tanan take fita ba. "Ni dama na san dole Modu ya mallakeka kamar yadda ya mallake mahaifinka. Komai ya kwaso Modu, Modu dai. Ko kai baya maka son da yake ma Modu. Kuma ai auren Yahanasu da aka baka da biyu ne. Wata munaƙisa Modu ya ƙulla shi yasa. Dan haka baku isa ba daga kai har Modu, ina dai _ dai da kowa a cikin gidannan. Aure dai sai an yi shi". Haka na koma Yobe cikin damuwa. Har kwanciya nayi a gadon asibiti jinya mai mugun tsanani ta kada ni. Hankalin ƴan Damaturu duk ya bi ya tashi. Na jima ina jinya kafin daga bisani aka sallameni. Nanma ban tsira a wajan Hajja ba. Bugomun waya tayi take cewa dani. "Da ace ka yarda kayi auren ai da ba Ahmad, da Wakil bane zasu dinga kwana da kai a asibiti ba. Ka sa sun baro matansu sunzo sun tare a asibiti. Na ji likita yace hawan jinine yake son kama ka. Sabida wannan dalilin zan sa Bature ya ɗan jinkirta batun aurenka da Yalewa zuwa wasu ƴan watanni. Amman kafa sani babu wani makawa aure babu fashi." Idanu kawai na lumshe na sauke wayar a kunnuwana. A hankali jikina ya soma warwarewa harna koma bakin aikina. Kullum inna farka naga babu Yahanasu a gefena, da damuwa nake ƙarashe wunin ranar. Duk da dai alhamdulillah jikin nata da sauƙi nima na gani. Allah _Allah nake yi watan ya kai ƙarshe, dan inga Yahanasu in kuma nuna mata gidanta yanda aka gama komai hatta da sutura na jibge mata a wadrope, na sai mata dogayen abayoyi na ijib da aka kawo mana tallarsu har kamfani. YAHANASU: GIDAN FARFAƊO DA RAYUWAR MASU SHAYE_SHAYE: Idanuna na runtse hawaye na ambaliya a kumatuna. Haƙiƙa zuchiyata cike take tab da nadamar rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Ni kaina bazan iya cewa meye mafarin abunda yasa nayi watsi da tarbiyata ba, na faɗa cikin kogon da babu mai iya fiddani ba. Yau nice a gidan mahaukata, kullum a cikin uƙuba da duka nake, bayana duk ya farfashe da bulala, ko zaman kirki bana iyayi tsabar irin yanda ake azabtar damu. Ba kayan maye bane suka fice mun akai kaɗai ba. Hatta rayuwar da nake yi ta fice mun a raina, bazance ire iren gidajennan basu da amfani ba, domun na zauna tsawon wata biyar, kuma na samu lafiyar ƙwaƙwalwata na gane kaina, har nazo a fahimci a inda nake. Na koyi darasi masu yawan gaske, na haɗu da mutane mabanbantan ra'ayi. Da a ɗakinmu mu goma ne, amman yanzu mu huɗu muka rage, da sannu sannu anata samun lafiya. Na koyi sana'ar ɗinki. Kuma ni malamace ina koyar dasu ilimin Hadith, sai matan ɗakinmu da nake yi musu ƙarin Qur'ani. Bani da wani buri daya wuce inga na bar cikin gidannan na koma ɗakin mijina, na shinfiɗa kyakkyawar rayuwa mara algus. Ina tausayin Bulamana fiye da yanda nake tausayin kaina. Ina jin tsantsar kunyar haɗa idanu da Ba Modu, da Ba Bakura, da Ya Innana sosai. Ina fargabar yanda zan fita in shiga cikin al'umma da irin tarbar da zan samu. Idanuna na buɗe na dubi ƙawayena ƴan ɗakinmu ko wacce na kalla sai inga tana zubar da hawaye irin na nadamar masifun da muka jefa kawunanmu. Murmurshi nayi na ƙarasa garesu na zauna ina fuskantar su. Mrs Bukhari ce [16/08, 9:21 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI) 47 Ga wani hadisi zan karantar daku ko hakan zai kawo sanyi da haske a cikin ƙirazanmu. ( An karɓo daga Abu Malik, Harith bin Asmin Al_Ash'ariy yace, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace. "Tsarki rabin imani ne, faɗin Alhamdu lillaah tana cika mizani, faɗin Subuhanallaah wal hamdulillah, su biyun suna cika, ( ko kuma kowacce ɗaya daga cikindu tana cika) abin da yake tsakanin sama da ƙasa, kuma sallah haske ce, sadaka kuma hujja ce, haƙuri kuma haske ne, AlQur'ani kuma hujja ne gare ka, ko a kanka, dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa ya sayar da kansa, ko dai ya ƴantar da kansa, ko kuma ya halakar da kansa" Muslum ( #223) ya yawaito. Idanu na zuba musu hankulansu da nutsuwarsu duk sun miƙa mun. Sai naci gaba da bayani na. Da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, tsarki rabin imani ne, magana mafi inganci dangane da tsarki, shi ne abin da hankula yake zuwa gareshi da zarar an ambaci kalmar tsarki, kamar alwala, da wanka, da taimama. Waɗannan su ne ake kira da suna tsarki, cewar tsarki rabin imani ne, akwai maganganu da yawa a kan hakan. Ko dai mu fassara imani mu ce shi ne sallah, sai ya zamanto tsarki ne rabin sallah. Masu wannan magana suka ce, saboda sallah an sa mata suna imani a cikin AlQur'ani. ( ... Da ɗai Allah ba ya nufin ya tozarta imaninku ( Sallarku).... Suuratul Baƙara: 143) Imani a cikin wannan aya ana nufin sallah. Don haka Bukhari ya kawo wannan hadisin a cikin babin da yake nuna cewa sallah tana daga cikin imani. Sai suka ce tsarki, wanda tsarkin nan wanda ya danganci wanka ne, alwala ne, duka biyun ne, taimama ne, sai dai da tsarki ake yin sallah, sai fa in wani uzuri ya hana ka dukkan waɗannan. Waɗansu kuma suka ce a'a, al_imaan yana nan a bisa ga yadda muka san imani. Tsarki shi ne rabin imani, imani kuma shi ne wanda ta'arifinsa ya riga ya gabata, tun can a baya. Suka ce abin da ya sa muka ce haka, saboda imani shi ne ƙudiri kyakkyawa a cikin zuchiya dangane da kaɗaitakar Allah da manzanni da sauran duk abin da ake faɗa. To ɗan Adam , wato ɓangare biyu gare shi, ɓangaren jiki da ɓangaren zuchiya. Imani zai tsarkake ɗaya ɓangaren na ɗan Adam, wato zuchiya, shi kuma tsarki wanda ya danganci alwala ko wanka zai tsarkake ɗaya ɓangaren na ɗan Adam, wato gangar jiki. Sai ya zamanto da imani da tsarki kowanne ya ɗauki rabi kenan! Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, yawan maimaita lafazin Alhamdulillah yana cika mizanin awon ayyukan mutum a ranar tashin ƙiyama. Wannan misali ne Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yake bugawa. Ma'ana da a ce waɗannan kalmomi za a yi halitta da su, da wannan za ta iya cika mizani in an zo auna ta a kan mizani a ranar tashin ƙiyama. Ko kuma ka ce lada da mutum zai samu sakamakon faɗin Alhamdulillah yana cika mizani. Sai kuma manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, faɗin ....subhanallaah wal hamdu lillaah, su biyun suna cika, ( ko kuma kowacce ɗaya daga cikinsu tana cika) abin da yake tsakanin sama da ƙasa..... Wato ladansu kenan. Wannan mai wannan riwayar hadisin ne ya yi shakka, imma dai Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ce su biyun ko kuma ya ce kowanne ɗaya daga cikinsu. Sai kuma manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce .....sallah haske ce, sadaka kuma hujja ce... A nan ana nufin sadaka ta wajibi, wato zakka. Ma'ana hujja ce bisa ga cewa mutum yana da imani, hujja ce bisa ga cewar mutum ya amsa umarnin Allah , hujja ce bisa ga cewar yayi yaƙi da zuchiyarshi. Sai kuma ya ce, ........ Haƙuri....." Ma'ana yayin da duk ka tashi kafa hujja a musulunci, to ya zamanto ka kafa hujja da AlQu'ani ko hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, in ba haka ba kuwa ba kabi Allah da ma'aikinsa ba, AlQur'ani ya zama hujja a kanka. Sai kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ......dukkan mutane suna jijjifi da safe..." Suna wayar gari da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa ya sayar da kansa, ma'ana ya wayi gari wajen mummunan aiki kenan, akwai kuma wanda zai ƴantar da kansa. Mutane kala biyu ne, wanda zai wayi gari cikin aikin ɓarna, to shine mai sayar da kansa, ko wanda zai wayi gari cikin aikin alheri, to wannan shi ne mai ƴantar da kansa) Yawu na haɗiya ina mai sauke numfashi zai zafin dake tokare mun munfashina tamkar mai ciwon asma. Ƴan uwan zamana na kalla, ko wacce cikinsu ajjiyar zuchiya kawai take saukewa. Amina tace. "Madallah dake Yahanasu. A zamanmu dake mun ƙaru sosai. Dariyar ƙarfin hali nayi nace. "Ai gidannan makarantar rayuwace mai ɗauke da ajujuwa zamani_zamani. Zaman gidannan ya ƙara wangalemun idanuna na gane ainihin menene haƙiƙanin rayuwa. Na koyi darasi mai ɗunbun tarin yawan da bazan iya mancewa ba har ƙarshen rayuwata. Ni daku inason mu zamewa kanmu ƴan uwa majiɓantan lamuran juna." Maman Amira tace. "Da yardar Allah ai mun riga da mun zama dangin juna. Zan baku labarin abunda ya jefa ni cikin duniyar masu shaye_shaye yanzu." Zaman mu muka gyara cike da zabarin son jin labaran juna. "Asilin iyayena fulanine gaba da baya mazauna jihar Gombe. Kiwo ne ya dawo da mahaifana garin katsina cikin anguwar masanawa. Ƙannena biyar dukka maza nice ɗiyar farko a wajan iyayena. Munyi aure da Baban Amira yardar juna soyayyar gaskiya. Sani talakane sosai, ya gama karatun digri ɗinshi aiki bai samu ba. A haka muka ganganɗa mu kayi aurenmu, daga bisani yaci gaba da yawon neman aiki, shine kullum a tafe. Ɗaki ciki da falo Sani ya kama mun can gangarar layin gidan iyayenshi. Kullum in nayi girki ina zubama mahaifiyar Sani a bisa kyautatawa, dan bai sani ba. Wata ran inje in kai mata da kaina, wataran kuma ƙanwarshi Adawiyya ce take zuwa ɗaukar musu. Duk bayan sati na kanje in yi ma mahaifiyata wanki, inna dawo sai in tsaya a gidansu Sani in ma Goggonshi nata wanki, da share_share, duk da yaranta matane, inayi mata ne dan in ƙara siye zuchiyar Sani. Na samu fada sosai a wajan mahaifiyarshi da ƙannenshi, harma da yayyenshi. A lokacin da garata ta ƙare ne muka soma shiga taskun rayuwa, gani da cikin Amira ƙarami a lokacin. Haka Sani yai ta faman faɗi tashin ganin ya rufa mana asiri. A wannan halin na haifi Amira a cikin gida. Ba mu yi taron suna ba, Sani bai samu kuɗin yanka mata haƙiƙa ba. Ni kuma duk ban ɗauki wata damuwa na ɗaura ma kaina ba. Tunda dai baya barinmu da yunwa yana ƴan bige_bigenshi. Amira na da shekara ɗaya na samu cikin Mujibul Rahman. Cikin yazo mun da laulayi ainun, dan har sai da na tafi gida jinya na tsawon wata biyu. A dawowar da nayi ne gidana gabaki ɗaya ya sauya. Domun Sani kullum a cikin ƙunci da tsaki yake in dai ya ganni. Na yi mishi tambayar duniya ya faɗa mun laifina, amman Sani yaƙi ya faɗamun inda matsalar take. Ga sabon wulaƙanci daya samo, in yasa ƙafa ya fita tun safe, sai isha yake sake waiwayena. A lokacin ne zai shigo da cefanen abincin dare ya miƙa mun. Shi kuma yayi wanka ya fice, bashi zai dawo ba sai wajajen ɗayan dare ko fin hakan. A cikin wannan halin na haifi Mujib. Bayan suna kamar da sati biyu na kwashi ƙafata naje na samu Goggo nake faɗa mata halin da Sani ya tsiro dashi. Tai ta rarrashina, tana bani magana masu daɗi. Nasan Sani yana matuƙar son mahaifiyarshi. A cikin kwana biyu Sani ya dena mun duk wannan sabon halin. Ya sake muka ci gaba da rainon yaranmu. Anyi haka da sati biyu wata ranar talata da daddare, ina zaune muna hira da mata a tsakar gida, sai ga Sani ya shigo jikinshi a mace mus. Tsallakeni yayi ya shige ɗaki. Ba shiri na bishi. A falo na tarar dashi ya kai mari ya kai gwauro, idanuwanshi sunyi jawur. "Sani lafiya kuwa, me ya faru naganka ka dawo a haka? Na dai ga babu leda a hannunka, bazai wuce dan baka samo kuɗin da zaka yo mana cefane bane yasa ka shiga wannan halin ko?" Kallona yayi tare da yin jim, sai ya fesar da iska daga bakinshi kana yace. "Naja'atu wani taimako nake so kiyi mun. Ki taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeki uwar ƴaƴana." Da kyau na kalleshi, bance komai ba na kama hannunshi muka zauna a kujera. Yi mun bayani Sani. Ai ko raina kace in zare in damƙama da akwai halin yin hakan kasan ni mai yi maka ce." Jin na faɗi haka yasa Sani washe bakinshi yace. "So nake yi ki siyar da komai na dakinki ki bani kuɗin a hannuna, zan buɗe shagon provision ne, sannan zan sai P O S in dinga harkar. Ana samun kuɗi sosai. Zan mayar miki da kuɗinki wallahi." Jim nayi ina tunanin wannan maganar ta Sani. Amman sai da Sani yasan kalmomin daya dinga yi mun a wannan dare, har sai da na amince mishi. Washe gari kuwa mota tazo ta kwashe kayana tas aka fice dashi. Labule da katifa sai sutura da kayan kicin kawai na tsira. Cikin sati guda provition ya haɗu tsab aka saka kaya ga P O S duka dai. Rayuwa ta warware mana. Sai dai sai Sani ya kai Sha biyun dare bai shigo ba, da nayi ƙorafi sai yace ciniki yake yi a shago ai bazai bar ciniki ya tawo gidaba. Duk fa wannan labarin mahaifana basu sani ba, sai ranar da Mamana tazo duba Mujib ba lafiya. Sai taga ɗakun wayam, haɓa ta kama tace. "Me zan gani Naja, kayan ɗaki Sanin sai sauya miki ko yaya?" Cikin sosa kai nace. A'a Mama siyarwa nayi na ba Sani kuɗin. Ya buɗe shago yana kasuwanci, amman zai mayar mun da kayan, harma ya shiga adashe hannu biyu, duk dan ya dawo da kayan ɗakin. "Ba shakka" Shine kaɗai abunda umma tace, tayi dubiyarta ta tafi. Haka al'amura su kai ta juyawa, har shekara guda ta sake zagayowa. Sani ya karya jarin shago tas, gashi bai mayar mun da kayana ba. Naci kuka na gode Allah, rayuwa ta sake tamke mu. Sai ƙannena maza ke taimakanmu da abinci. Wannan yai mun_wannan yai mun. Kullum a cikin babu nake, suturar arziki ta fita kunya bani dashi. Wata ranar juma'ar da bazan mance da'ita ba Sani ya zo mun da wani babban al'amarin daya jijjigani. "Naja, kinsan kuwa ashe matar Umar Saudiyya ta tafi ashe tana aikatau? Ke kinga tamfatsetsen gidan data gina ma Umar kuwa? Ga kayan alatu ta zuba musu, ta sai ma Umar mota yana kabu_ kabu. Bata dawo ba tukunna tace sai ta kuma gina musu wani gidan tukunna. Baki na riƙe nace. Shi Umar ɗin ya bar matarshi ta tafi aikatau har ƙasa mai tsarki, to yaran fa Yaya su ka yi dasu?" Sani yace. "Yara suna wajan Umar ɗin. Mai aiki na kulawa dasu, amman da kafin Umar ya gama ginin gidan, yaran na wajan mahaifiyarshi. To yanzu da ginin ya kammala ne suka koma gidan. Makatanta mai tsada maman ta sa su." Mamaki na dinga yi. Mu kai ta hirarmu da lokacin kwanciya yayi muka yi baccinmu. Ashe tsugunne bata ƙareba. Da rana fatse_fatse ina kwance ina ƙailula sai ga sallamat Sani. "Naja tashi abun arziki ya same mu. A gigice na tashi ina mistsike idanuna. Sani lafiya kuwa na ganka duk a rikice?" Zama yayi kusa dani. "Uhm gidan Umar na koma Naja. Harma ya ban matarshi a waya mu ka yi magana ta fahimtar juna. Babban abunda yafi ƙayatar dani shine yanda ta sa Umar ya bani number Hajiya Kati, wacce take tura mata Saudiyya aikatau, in kayi aiki ka biyata kuɗinta. Gobe zamu je wajanta muma." Cike da mamaki na dubeshi da kyau nace. Kana nufin nima saudiyyan zaka turani aikatau dan in gina mana gida?" "Ƙwarai kuwa harma da mota, in kika ji gida ɗaya kenan gidaje zaki gina mana ai" miƙewa nayi fuu na barshi a nan yana ƙwalamun kira. A fusace ya biyo ni. Mun sha rikici da Sani sosai. Baiyi zaton zan yi mai kafiya ba. Tun yana ruwan masifa, har ya sakko ya shiga lallaɓani. Amman ya kasa gane kaina sam. Kullum a cikin rikici muke ni dashi. Tunda yasan babban abunda yake jagulani shine kaiwa dare a waje. Sani in ya fita wataran a waje yake kwana, wataran kuma ya dawo gida ukun dare ko biyun dare. Na yi zaryar kai ƙarar Sani gidansu amman bata sauya zane ba. Na kai ƙararshi gidanmu. Hmm abun mamaki mamanmu ta lulluɓeni da faɗa, wai matan aure nawa ne suke saudiyya dan rufa ma kansu asiri? Nima inje tunda mijinane ya yarje mun. Ƙannena maza suka nuna su atafau basu yarda ba, Mama tayi ruwa tayi tsaki akan ita ba ruwanta kar inje in kaso aurena in ɗaura mata jakar tsaba a wajan dangin Babanmu. Haka dole na yarjema Sani zani saudiyyan. Jiki na rawa ya kaini gidan Hajiya Kati. Cikin wata ɗaya da zuwanmu jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki, ina kukan rabuwa da yarana da nayi. Sani kuwa bakinshi tamkar gonar audiga. Bari in taƙaice muku shekarata biyar a Saudiyya ina bautama Sani. Sabida tsabar sha'awa data dame ni a matsayina na mace mai lafiya, na faɗa harkar shaye_shaye kamar da wasa har ya zame mun jinin jikina. Kullum in na ce ma Sani ni zan dawo sai yace mun a'a in ƙara lokaci. A lokacin gidaje biyu Sani ya gina, kuma ya sai mota, Mama ma na sai musu gida, na buɗe ma ƙanina Anas shagon sai da takalma da jakunkunan mata. Ranar dana gaji kuwa na hau shirin dawowa gida Najeriya. Ina dira kai tsaye na wuce gidan da Sani ya gina mana ni da yarana, dama ya sanar dani layin. Har hoton gidan akwai a wayata da number gidan. Hmmm abin mamaki da shigata." Kuka ne yaci ƙarfinta, mu kuwa munyi jigum muna jin labari mai taɓa zuchiya. MRS BUKHARI CE[17/08, 12:05 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 48 Ci gaban labarin Maman Amira: Sai da Maman Amira tayi kukanta mai isarta sannan ta share hawayenta, ta ɗan yi murmushin da yafi kukan data gama ciwo ta ɗaura da cewa. Wata mata na gani fara sol tana zaune a falo tana shan jus ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya. Ga A c na hurata, tashar Arewa 24na aiki a ƙaton talabijin ɗin dake manne a ɗakin. Tana ganina ta miƙe tace. "Baiwar Allah ke kuma daga ina zaki shigo ma mutane kai tsaye cikin falo ba sallama?" Sai da ta yi magana na tuno da banyi sallama ba ashe. Zuchiyata ta kwaɗaitune da son ganin Sani da yarana. Yi haƙuri baiwar Allah, na sha'afane shi yasa banyi sallama ba. Assalamu alaikum" A taurare ta amsa mun, tare da watso mun tambayar. "Daga ina na ganki da akwati?" Zama nayi ina kallon wannan yarinya dake gabana, ni dai ban santa a dangin Sani ba. Ba tai kama da ƙyar aiki ba, to wacece ita?. Bani da amsa, ɗago da kaina nayi muka haɗa idanu da'ita. Na kalli bango na hango hotonta da Sani a jikin wani ƙaton agogon bango, da rubutu kamar haka a jiki ( happy married life) da date da komai. Anan naga sunanta harma da inkiyarta. Wani ruwane ya shiga kai kawo tsakankanin jijiyoyin idanuna da jijiyoyin kaina, zuchiyata ta shiga tsalle a ƙirjina. Yarinyarnan mai suna Husna tana tsaye a kaina ƙerere sai magana take yi. Kukan dake tunkudo kanshi na haɗiye nace. Wajan mai gidan nazo, in yana ciki aimun magana dashi, in baya nan kuma zan iya jiranshi dan Allah?" Baki ta taɓe tace. "Honey baya nan, amman ba jimawa zaiyi ba. Zaki iya jiranshi." Tana faɗar haka ta fita ta barni a falon. Kwayoyi na afa a bakina cikin tafin hannuna, na kora da ruwan faro dake kusa dani. Na lumshe idanuna ina tsiyayar da ruwan hawaye, zuchiyata da ƙwaƙwalwata sun kasa aika ma da juna sakon komai. Sai jini da zuchiyata take watsawa gangar jikina wanda ya wuce kima. Ina zaune har bayan la'asar ko azahar ban yi ba. Sai ga hon ɗin motar Sani. Na gane hakanne ta dalilin fitowar matarshi cikin sabuwar shiga tana busa ƙamshi tayi waje taran Sani. Ji nayi kamar in jawota in hauta da duka, amman babu ƙarfi a jikina ƙwayoyin dana afa sun soma tasiri a jikina. Ina jingine Sani ya shigo saye da farar shadda, da wani yaro a kafaɗarshi. Idanu na zuba mishi ina karantar yanayinshi. A madadin inga tsoro da firgici a tare dashi, sai naga ganina da Sani yayi bai ɗaga mishi hankali ba. "Mutan Saudiyya yaushe a gari inji maƙi baƙo?" Da fara'a ya nufoni ya zauna a kujera mai fuskantata. Saukar kenan nace bari in sauka a gidana, inga mijina da yarana" ƙur nayi mishi inason inji mai zaice. Sai naga yayi murmushi yace. "Mutan Saudiya kenan, hmmm ke a tunaninki zaki je saudiyya tsawon wannan shekarun ki dawo kuma muci gaba da aure?" Sai ya kalli matarshi yace. "Honey wannan itace tsohuwar matata, maman su Amira. Maman Amira wannan itace Husna sabuwar matata dana aura bayan na sake ki saki uku" A ruɗe na kalleshi nace. Saki kuma Sani, giyar wake kasha ko me? Anya a hayyacinka kake?" Dariya yayi yace. "Wallahi ras nake, ai baki ga halamar hauka tattare dani ba. Cewa nayi na sake ki saki uku, zai fi miki ki tattare ki koma gidan iyayenki." Nan na miƙe dama a buge nake, munci uwar sabada ni da Sani. Dan rufeshi da duka nayi tako ta ina, inayi yana yi. Ihu nake kurmawa dan ƙaramin zaucewa nayi. In muku a gurguje da ƙyar aka fito dani daga gidan Sani. Da ƙyar na gane gidanmu na kai kaina. A cikin kwana goma na haukace tuburan, sai na wayi gari na ganni a gidannan. Ina shirin maka Sani a kotu. Wannan shine labarina, amman kes ɗin yana hannun wata lauya mai zuwa dubani tare da su Mama. Duk abunda na ke turama Sani a lissafe yake, kuma saiya biyani abuna." Rarrashin maman Amira mu ka shiga yi, labarinta ya taɓa mu baki ɗayanmu. A daddafe na basu labarin kab rayuwata da yanda akayi na tsinci kaina a gidannan. Haƙiƙa sun jinjina mun, sun kuma sake jin girman Bulamana a zuchiyarsu, sun tausayama halin dana shiga ainun. Zainura ce tace. "Labaranmu suna da taɓa zuchiyoyi, ni na haƙura da bada nawa labarin sai zuwa dare in Allah ya nuna mana. Duk sai mu ka tsaya a matsaya ɗaya kan cewar a bari sai da daddaren sai mu ci gaba da jin labarin ɗaya daga cikinmu, ko babu komai zamu rage ma kanmu dare." Misalin ƙarfe taran dare muka sake haɗe kawunanmu domun sauraron labaran ƴan uwanmu. Zainura ce ta soma da cewa. Ni nawa mijin shi ya sani a cikin masifa da tashin hankalin da nake ciki a yanzu. Auren soyayya mu ka yi, soyayyar da sai da kab dangina suka sanshi. Muna zaune cike da so da Amana, yaranmu biyu. Kwatsam rana tsaka yace shi Aure zaiyo. Har ga Allah a lokacin ni ban ɗaga hankalina ba. Dan bazan mance ba har gidan iyayen yarinyar da zai aura a lokacin ya kaini. Da yamma ina aiki a kitchen ya shigo, yara suka taryeshi, sai da ya gama wasanshi da yara kafin ya same ni a kitchen ɗina a falo. "Maman Hafsa baki sauke sanwar ba, bacin tun jiya na sanar dake zamu fita?" Ranshi ya ɓaci sosai. Ni kuma cikin rarrashi nace mishi. Kayi haƙuri, gas ɗinane ya ƙare, sai da na fita na sawo. Amman abincin yanzu zai tsotse, ni kuma ai kaga a shirye nake tun ɗazu yaranma na shiryasu. "To kiyi sauri dan Allah." Yace dani. Cikin minti goma abincina ya tsotse, na zuba wanda zamu ci a kula, sauran na barshi a tukunyar. Mayafina da jaka na shiga ciki na ɗakko. A kan mashin ɗin roba robanshi na sameshi. Hafsa na gaba ita dashi. Musina tana tsaye a ƙasa kusa da ƙafarshi. Gidana na kulle kafin na hau mashin ɗin, na ɗaura Musina a cinyata. Ya ja ni fuu sai gidan budurwarshi, bai tashi sanar dani ba sai da muka tsaya a ƙofar gidan, ina gefe ni da yara ina jiranshi. Parking ya gyara kafin ya nufoni. "Nanne gidansu Nana, ta jima tana mun ƙofarin ita tana son ganinki. Shine fa yau dai nace bari in kawo ki. Dum naji gabana ya faɗi, na bi Sunusi da idanu ina mamakin wulaƙantani da yayi. Tunda itace take son lallai sai ta ganni ina laifin ita ya kawota gida ta ganni? Sai ni ce marainiyar wayonsu. Ban samu zarafin cewa komai ba, domin in nace zanyi magana to zagine zai fito a bakina. Nana ce ta fito cikin kwalliyar kece raini, sai masifaffen ƙamshin Humra take yi, wanda Mrs Bukhari take siyarwa, mai inganci da riƙe jiki. ga me buƙata sai ya neme ni. "Allah ya taimaki ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Barka da zuwa shingena. Cewar Nana wacce ta yi banza dani kamar bata ganni ba. Shi kuwa Sunusi sai wani yashe baki yake yi kamar gonar audiga. "Barka da fitowa tauraruwa, kai kwalliyarki abun yabawace, ƙamahinki mai daɗin shaƙane" Jikina sai rawa yake yi mun. Zuchiyata na ingizani kamar in jawo Nana inta jibgarta. Sai da Sunusi ya gama dibar albarka kafin ya dubeni yace. "Maman Hafsa ga Nana, Nana ga Maman Hafsa yau na cika alƙawari dai ko?" Nana ta washe baki tace. "Barka da zuwa uwargida ran gida. Gaskiya Baby ka cika alƙawari. Maman Hafsa mu shiga ku gaisa dasu Mama." Kamar raƙumi da alaka haka na bi bayan Sunusi dake bayan Nana. Mune har cikin gidansu. Nana ta gabatar dani ga ƴan uwanta. Muka gaggaisa da iyayenta. Kafin muka shiga ɗaki. Hmmmmm nan naga kwanukan abinci da abubbuwan sha ratata wai duk namu ne. Ni dai ruwa kawai na iya kurɓa, wallahi da ƙyar ya wuce. Sunusi da yara dai sai da suka take cikinsu. Har Nana tana ce mai. Baici dayawa ba yau, ko dan ya ganni ne. Ni dai banza nayi dasu. Daya gama taɗinshi da Nana muka kamo hanyar gida. Nana ta cika yara da su sweet da biskit. Ni kuma ta bani takalmi da jaka. Tun daga wannan ranar na soma kwasar baƙin ciki. Ashe banga komai ba. Sai da Nana ta tare ne, na gane waye Sunusi. Ƴan uwa tunda Sunusi ya shiga ɗakin Nana bai sake waiwayena ba. Nayi kukan, nayi zuchiyar, na kai ƙaran amman wallahi sai sabon wulaƙanci kawai da Sunusi yake sake tata mun. A hankali Sunusi ya dena bamu abinci. Sai dai in je inyi aikatau in samo ma yarana abinci. Na nemi ya bani takaddata ni na haƙura da auren. Sunusi ya je ya sanar da iyayena. Mahaifiyata da bulala tazo ta zane ni a gaban Nana. Kuma tace muddin na kashe aurena basu bani. Rayuwa ta yi tsanani, hawan jini na son halakani. Ranar wata maƙociyarmu ƙawatace take bani shawarar in samu ɗan maganin tari in dinga kurɓa, zai mantar dani halin da nake ciki. Ita kanta in takaicin ɗa namiji yai mata yawa, maganin tari take sha tai ta bacci. Kamar wasa na soma sha, sai naji ashe da gaske yana sauke matsaloli, ya rage cunkushewar zuchiya. Wannan dalilin ne yasa na faɗa harkar shaye_shaye haiƙan.shine silar shigowata wannan gida. Bayan na samu taɓin hankalin, ina cikin wannan halin, Sunusi ya aiko mun da takaddata, kuma ya turo su Hafsa suka dawo gidanmu. Wannan shine labarina a taƙaice. Hadiza ta share hawayenta ta kallemu tace. Ni zafin zawarci, da irin tsangwamar da ƙabilar hausawa ke ma bazawarane yasa na faɗa hidimar shaye_shaye. Amman alhakin mijina ne ya bibiyeni, dan babu irin rashin ɗa'ar da banyi ma Bala ba. Asirceshi nayi, na dinga tamaule da rayuwarshi. Hatta albashinshi in akai musu biya sai dai ya ɗakko A T M card ɗin ya bani. A taƙaice babu irin zaluncin da banyi ma Bala ba. Bayan asirin da nayi mishi ya karyene ya sauwaƙe mun. Ya kuma hanani ɗaukan ko yaro ɗaya. Wannan shine iya abinda ya dace ku sani. Amman ina cike da nadama, da zabarin ganin na roƙi Bala yafiya, ko hakan zai zame mun matattakalar shinfiɗa rayuwa mai kyau a gaba." Ranar a cikinmu banyi tunanin ko akwai wacce ta runtsa ba. Domun cikinmu ko wacce ta fama wani mikine dake zuchiyarta. Ni dai da naga kwanciyar ba zata kaini ba. Sai na tashi na ɗaura alwala na shiga raya daren da nafilfili. Bayan na idar na shiga istigifari domun neman yardar Allah maɗaukakin sarki. Ghana: Zubaina: MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE [17/08, 12:06 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 49 Zubaina: Haka rayuwa tai ta shurawa dani. Lalacewar da nayi tafi ƙarfin gaban a kwatanta sai wanda ya gani kawai. Ga Zarah ta sani a gaba zagi da habaici babu irin wanda bata yi mun. Ni in Zarah na tsakar gidan ma shakkar fitowa nake yi, sabida gudun fitina, dan hatta yaran gidan duk rashin kunyarsu Zarah bata ƙyalesu ba. Alh Liti kawai take jin shakka a cikin gidannan. Sati na zagayowa Nabila ta dawo. Watan ta guda da dawowa ta suntulo ɗiyarta mace mai tsananin kama da'ita. Ni dai sai tura nawa cikin nake yi, yau ciwo gobe lafiya, har yanzu hannuna bai idasa warkewa ba, gashi inaji ina gani na zama me giɓi a bakina. Oh duniya mai ido a tsakar ka. Duk wanda yayi sake duniya da abun duniya su ka ruɗeshi, zai mutu a wulaƙance yana cike da dana sanin rayuwa. Cikina watanshi takwas da kwanaki amman ban taɓa zuwa awo ba, ba abinci mai kyau, ba ruwan sha mai kyau, na dawo kamar ƴar lambu. Ƴar babbar wayar da nake ɗan hawa whatapp in rage ma kaina zafi, na siyar a lokacin da nayi wani rashin lafiya, kwanana huɗu a asibiti a kwance. Rashida ce tayi jinyata, Alh Liti baya ma ƙasar ya tafi fataucinshi daya saba, da biye _ biyen matanshi da baya rabo dashi. Dan kullum kaje kwanan turaka ka ji ya raba dare yana hirar soyayya da mace a waya. Ni dai a kullum roƙona shine, Allah ya shiga lamarina ya taɓa ya kawo mun ƙarshen wannan zaman rashin ƴan cin da nake yi. Ina bakin murhu na gama naɗe tuwon dokunu a ɓawon masara kenan na mayar wuta, na ji hon ɗin Alh Liti a get ɗin ɓarayinshi. Da sauri na tafi dan buɗe mishi, da ƙyar nake ɗaga kumburarrun ƙafafuna, amman a hakan har gudu_gudu nake yi, dan kar in yi gagarumin laifi. Ina jin Zarah tana tayi tsaki tace. "Aikin ɓur in ji tusa, dan Allah jibabta" Ni kam ban ko saurareta ba, na je na buɗe ma Alh Liti get ya shigo a fusace kamar zai taka ni da mota, sai ƙara raɓewa nayi a jikin get ɗin ina sauke ajjiyar zuchiya. Da ƙyar na mayar da get ɗin na rufe, na nufi Alh Liti da sauri dan karɓar jakar hannunshi. Dawowarshi daga tafiya kenan. Sannu da dawowa Alh " Kallona yayi a wulaƙance yace. "Menene haka ya sameki naga kin aune, fuskarki ta kumbura idanuwanki sun nutse kamar an huda saƙwara?" Ni kaina ban sani ba, wayar gari nayi na ganni na kumbura takota ina, jikina har ƙyalli yake yi. Gashi bani da kuɗin zuwa asibiti" Tsaki yaja yace "Ku da an magana sai batun asibiti. Ki kwaɓa toka mai zafi ki shafe jikinki dashi, zai saɓe anan gidan haka akeyi. Ko kin ɗauka ni lusarin kanurin mijinki na da ne da kika maidashi soko? To ni ba haka nake ba. Yau ko mutuwa kika yi su Jummai take kowa? Su ke da asara amman ba ni ba. Kafin ki rufa kwana uku zan maye gurbinki da tiya leda. Wuce ni dallah ki shigar mun da jaka" Sum _ sum na wuce ciki ya bi bayana yana faɗin. "Um um hum su Zubaina wanka, an zama Zubaina ƙazanta. Naga ƙafarki har kaushi ta soma yi. Da an samu dama sai faman damawa akeyi, ana lanƙwasa tamkar ba'a kashi, yanzu jibeki yanda kika dawo guzuma." Hawaye kawai nake yi. Key yasa ya buɗe ɗakin muka shiga. A sama na ajjiye mishi jakar, a kan matattakalar sakkowa muka haɗu dashi, yana haurowa yana waya, sai kalaman ƙauna masu daɗi yake faman zabgawa. Har na wuce yasa hannu ya jawoni baya. Daɓas na zauna akan matattakalar ina haki, dan jawoni da yayi, baya nayi zan faɗi. Numfashi na sauke, ban ko iya tashi ba, ina zaune har ya gama lallaɓa budurwarshi da halama fishi tayi. Nima sai ya tuna mun da fishin da na taɓa yi mishi lokacin bikin Nafeesa, wanda a Wannan ranar ne nace sai ya ƙarashe mun ginin gidana, inason mota, kuma inason zuwa aikin Hajji. Murmushi nayi dana tuno amsar daya bani a wannan lokacin. "Ke dan bura'ubanci shine zaki wuce ni kamar kinga buhun dawa? To ki hauro sama in murje kuɗaɗena da aka ci mun ko?" Da sauri na kalleshi nace. Kai mun rai. Wallahi bazan iya ba. Ba daɗi nake ji ba, tun jiya marata take faman ciwo" "Ni ne zanyi miki rai? Allah ne kaɗai ke ma ɗan Adam rai. Ki taso ni dallah. Ke kin isa kici tuwo ki kwanta getsetse ba tare da an banbasha ki ba." Sahunshi bani da kallo yana haure bene. Da ƙyar na kai kaina ɗakin Alh . Irin wannan kwanciyar dai da hausawa ke mata laƙabi da ( salamatu kwanta ko kuma Ci ka rufe) Ita yai mun. Ya hau yai ta sukuwa tamkar ya samu tsowon jaki. Babu abunda nake ji sai raɗaɗi. Marata kamar zata dare haka nake ji. Dan mugunta Alh sai da ya kai kusan minti ashirin yana ƙurzata. Sai da ya ƙoƙeni tas ya shige ban ɗaki ya barni a yashe a gadon ina cizon yatsana. Da ƙyar na yunƙura na miƙe, na ja zanina ya rufe mun ƙafafuna. Da bin bango, da zaman hutu na sauka ƙasa. Ina komawa cikin gidan naga Nabila na raba ma yara dokunu, harta sauke ta mayar da tukunyar ruwan wankan jegonta. A gidannan ko haihuwa kayi ɗaga ƙafar kwana bakwai akeyi maka. Da kan ka kake yima kan ka komai. Gefe na samu na zauna naci gaba da rabon abincin ina share zufa da bakin zanina. Bangajeni Zarah tayi sai da na kusan faɗuwa ƙasa. Da sauri na ɗago ina kallonta, sai jijjiga take yi a kaina. "Malama tun tuni kin tafi wajen miji kin bar mutane da yunwa, dallah ni ki zuba mun abinci." Da yatsa na nuna ta nace. Kinci alfarmar abunda ke cikina, amman wallahi da yau na nuna miki waye Zubaina. Zarah baki sanni bane, ruwane ya daki babban zakara, kin samu kura tayi lafiya, ni ɓarayi nake masga da manyan ƴan iska wanda suka fiki riƙa da gashin fiffike. Hmmmm Allah ya shirya ni banga abun kishi a cikin gidan da kowa ta kanshi yake yi ba.'" Robar hannunta na fisge na zuba mata dokunu ƙulli biyu da kan kifi ɗaya, na dangwarar mata a gefen ƙafarta. Ai kuwa ashe na taɓo tsuliyar dodo, nan Zarah ta shiga kutuntume_kutuntumen ashar, har su Hajiya Kubra da Rashida suna rirriƙeta wai sai ta tattakani. Ni kuwa sai haɗiɗiyar zuchiya nake yi bakina yana ambaton Allah. Gabana sai faɗuwa yake yi, dan nasan ko lafiyace dani a dake zan sha duka a wajan Zarah, dan hausawa sunce halamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Ana cikin wannan sowar Alh Liti ya shigo cikin gidan buguzun_buguzun da malum_malum yana tafe yana saɓawa. "Wai menene ne haka gida sai jaraba, sai kace ku kaɗaine kishiyoyi a cikin gidannan?" Ya dubi Zarah da aka rirriƙeta yace. "Ita kuma wannan mahaukaciyar masifaffiyar meya faru da'ita na kada ta haune ko barhazs?" Hajiya Kubra tace. "Ba wani na kada. Zarah bata son zaman lafiya sam tunda ka aurota kullum a cikin tarar masifa da bala'i take. Ni bansan me take ma kishi a cikin gidan ba. Koma meye ya kamata ka sanar mata mu tazo ta samu a gidan, Zubaina tana gaba da'ita" Kwafa Alh Liti yayi, ya wuce kamar bazai yi komai ba, ace satar Zarah yake son yi. Ƙafarta ya ja ta faɗi rub da ciki ta saki ƙara. Igiyar shanya a tsinke a bango. Ya hau jibgarmu baki ɗayanmu harda yara da suke faman kallo. Kowa ya watse ya barni da ƙyar nake ɗaga ƙafafuna, ɗakin Hajiya Kubra na kutsa kaina da sauri. Yafi sama da mintuna goma yana bol da kwanuka yana wani irin kutuntume_kutuntumen ashariya. Ajjiyar zuchiya na sauke ina ambaton Allah. Sai da ya gama buyaginshi ya bar tsakar gidan, kana kowa yaci gaba da aikinshi. Ƙarashe rabon abincin nayi. Nabeela na juye ruwan wankan jegonta na mayar da nawa. Kafin magriba nayi wanka Sallah na ɗan gargasa jikin nawa. Ina zaune jigum akan sallaya tunani yabi ya addabeni ƴar Nokia ta raka ni kashi ta soma ruri. Mama ce ke kirana, da sauri na ɗauka. "Yaya yanayin jikin naki da sauƙi dai ko, ciwon marar fa?" Numfashi naja nace. Kayya yau kam da ƙyar nake ɗaga ƙafafuna, cikin kuwa a kan guiwata nake jinshi Mama. Haihuwarnan tazo fa, bana tunanin zan wuce gobe ban haihu ba. Mama kiyi mun rai ki taso ki zo, wallahi gani nake yi kamar mutuwa zanyi ma. Bana son in haihu ba wani nawa a kusa Mama al'amarin gidannan tsoro yake bani wallahi" Tsaki Mama tayi tace. "Ban kira ki dan ki faɗamun labarin gidanki ba. Zubaina ke kike sha'awar zama da Liti, babu wanda yai miki tilas, ke ba dai kince kin dena bin bokaye ba, kin ja hannu kin naɗe ko? Kuka yanzu kika soma. Mijin Asiya yayi mun burking jirgi, sati mai zuwa sai in tawo. Amman in kina jin halamun haihuwar a kusa ko jibi sai in kamo hanya ai. Asiya da Nafeesa dai sai ana gobe suna zasu tawo. Musa kuma ya samu matar Aure, har ma yaje ya samu kawunku da maganar, yau da daddare zasu je gidan su yarinyar. Sagiru kuwa ban faɗa miki bane sabida kar abun yayi miki yawa. Yau ɗinnan aka sakoshi daga fursuna watan shi hudu a gidan ɗan kande. Wata gagarumar sata suka tabka a wani kamfani, shine aka kamasu. Ai mun sha sintirin zuwa kotu. Musa kuwa hmmm wallahi yanzu haka ma dadironshi bata daɗe da barin gidannan ba, munfi wata biyu muna tare, tun ana boyewaa har aka dena. So suke su kasheni su huta, ga Asiya bata jin daɗi a kwance ma take." Kuka Mama ta fashe dashi mai ciwo. Shiru nayi ina sauraren amon kukanta. Bayan duk ita tai sanadiyyar ɓalɓalcewarmu, ita ta ɗauramu bisa mummunar turba. Ga tsinuwa bisa abunda bai taka kara ya karya ba. Yaya ba zamu gamu da iftila'i ba?" Kiyi haƙuri Mama Allah ya shiryesu baki ɗaya. Asiya wanne irin ciwo ke damunta to?" Mama tace. "To mijin dai yace kamar makarai take yi. Tunda ya kaita ƙauyansu ziyara suka dawo yarinyarnan a kwance take fa, ko bacci basa iyayi da daddare. Amman ana mata hayaƙi, da wankan magani. Ni dan ina fargabar yadda haihuwarki take ne ma, da bazan zo Ghana ba, itan zan sa ya kawo mun ita muyi jinyarta a gida. To kema ina duba yanayin da kike ciki. Rakiya kuma bata nan." Haka dai Mama ta kashe wayarta ta barni da jimami, kullum mu kai waya sai naji abu maras daɗi wanda bazai barni bacci ba. Bayan isha na kulle ɗakina na wuce turaka. Haka naita tura cikin zuwa kwana biyu. Mama tun asuba ta kirani tana Airport na Kano zuwa Lagos, sai da taje ta dubo jikin Asiya tukunna. Nima jikin nawa tun bayan hantsi nake jina sama_sama dai. Zuwa sha ɗayan rana ruwa ya soma bin ƙafata, sai uban wanke wanke muke yi ni da Zarah. Tun ranar da Alh Liti ya kayar da Zarah a tsakar gida, ta dena tsiwa, sai harara da tsaki da zaran kun haɗa idanu. Baya nane yayi wata iriyar ƙagewar da bansan sanda na ɗan saki salati da ƙara ba. Dafe ƙuguna nayi ina cije leɓena. "Zubaina ko naƙudarce ta tashi? Nabeela goya ɗiyarki ke da Rashida ku kaita ɗaki. Tun jiya naga halamun naƙuda take yi a tsaitsaye." Rashida da Nabeela ne suka rirriƙeni, a daddafe muka isa ɗaki, a kan cinyayyar tabarmar ɗakin na durƙushe ina shan yaji ina cije bakina. Abu kamar wasa fa naƙuda ta rabkeni sai fama nake tata yi. Unguwar zoman dake karɓar haihuwar matan Alh Liti ce a kaina sai faman bubbugamun baya take yi tana faman yamutsamun cikina. Awa uku ina abu guda duk na galabaice, sai aikin sannu Hajiya Kubra da Nabeela suke jeromun. Ni kuwa bana ma iya amsawa sai cin kwakwa nake yi. Wani nishi ne naji yana tunkudo kanshi min indillah, ina yin wata ƴar ƙara sai ga kukan jariri ya faɗo a hannun unguwar zoma. Numfashi na shiga mayarwa ina ganin yanda yaron yake ta wiltsil_wintsil. Wani sabon naƙuda ne ya sake turniƙe ni, baifi na minti talatin ba na kuma haihuwa, ko wanne jariri da mahaifarshi, bansha wuya ba mabiya ta fito. Sai rawar sanyi dana soma yi. "Kai masha Allah, Allah ya kawo mana ƴan biyu kyautar Allah cikin zuriya. Duk aure aure da Alh yaita zabgawa babu wacce ta taɓa haifar biyu sai ke Zubaina. Ni dai sai yaran kawai nake kallo ina tausayama rayuwar da zasu taso su ga kansu. Wani irin ƙauna ta mahaifiya da ƴaƴa ta shiga hudani. Zani Nabeela ta miƙo mun na ɗaura, na zame wanda ke jikina, gado na hau na lulluɓa na shiga rawar sanyi. Kafin kace me sai zazzaɓi ya rabkeni. Ana cikin yi ma jariran wanka sai ga Rashida da akwatin Mama da jakarta. Tare suka shigo. "Au ta sauka ashe? Wooo ƴan biyu muka samu? Allah ya raya mana ku yara" Cewar Rashida. Mama kuwa babu wani fara'a a ranta sam. Tsallakewa tayi ta same ni a kan gadon. Jira _ jiran kuma an saka musu kayan gwanjo, wanda sai da na siyar da ɗankakkun kayana kala biyu na je kasuwa na ɗan tsinto kwashe. "Zubaina lafiya lau kike dai ko?" Magana wannan na kasa. Mama duk tabi ta ɗaga hankalinta. Babu shiri ta tattagemu daga ni har jariran sai asibiti. Gado aka bani, kafin mu je asibitin ma duhu ya mamaye mun idanuna. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE [17/08, 12:06 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. 50 Asibiti: Mama: Tana zaune a ɗakin ganin likita yanai mata bayanin halin da kofur Zubaina take ciki. "Mama hawan jini ne ya rafketa mai ƙarfi. A binciken da muka gudanar Zubaina tana cikin matsananciyar damuwar da in ba kwantar mata da hankali akeyi ba. Komai ka iya faruwa da'ita. Kinga hawan jini babban ciwone wanda a shekarunta bai kamata ma a sameta da wannan ciwon ba. Ga ciwon damuwa da a yanzu yake jefa mata a cikin fitintinu iri daban _ daban. Ya kamata a ririta mata lafiyarta ne. Gashi ta galabaita sosai a haihuwarta, basu samu wata kulawar daya dace ba." Kuka Mama ta fashe dashi tace. "Mugun kafiya ne da Zubaina, ita ta jefa rayuwarta cikin rayuwar da take a yanzu. Allah na gode maka dame mutum zaiji ma to wai? Ta dubi likitan tace. "To yanzu likita menene abunyi? Ka ganni babu wani ishasshen kuɗi a hannuna, zamanmu a asibitinnan ba yiwuwa zai yi ba. Likita ya dubi Mama yace. "Zan iya sallamarku in ta farka daga baccin da take yi zuwa gobe. Amman kar a barta ta zauna ita kaɗai tana da buƙatar masu ɗebe mata kewa. Sannan a guji abunda zai jawo mata ɗacin zuchiya, Allah ya sauwaƙe" Mama tayi jin kafin tayi ma likitan godiya ta fita a ofishin. Jiki a mace ta koma ɗakin da aka kwantar da Zubaina, Rashida ce zaune a gefen gadon. Jariran dake bayan Rashida a jere duk su biyun Mama ta ƙura ma idanu. Ƙaddarar ƴaƴannan ce ta kawo Zubaina Ghana aure. Amman tana tunanin ƙaddarar ita ce dai zata sa ta rabu da Alh Liti ta bar mishi yaranshi, ta bi Mama su koma gida najeriya. Washe gari Zubaina: A hankali na buɗe idanuna ina ƙarema Mama kallo wacce take zaune a kujera tana ba jariran ruwa a karamin kofin filas na yara. Mama maza ne ko mata? Na tambayeta cike da son na son me na samu." Idanu Mama ta kafa mun tace. "Ba shakka Zubaina, wato da zancan daya dace ki tareni kenan a naki rashin hankalin ko? To mata kika samu duka, bayan wannan sai me zaki tambaya kuma uwata?" Idanu na lumshe ƙwallar data taru a guraben idanuna suka gangaro. Lokaci ɗaya Mama ta sakko ta shiga rarrashina. "Ki dena kukan haka Zubaina ya'isa haka nan. Kinga yaranki farare sol kamar ubansu." Matso mun dasu tayi na kallesu da kyau har ina ɗan murmushi. Alh Liti yazo kuwa Mama, ke kaɗai ce a nan ɗin?" "Ki ture waɗannan tambayoyin ba lafiya bace dake, yanzu dai ki tashi ki sha tea, kafin in siyo miki abinci. In kika gama ci mayi magana. Sai da Mama ta haɗa mun tea kakkaura sannan a ajjiye yaran a gefena ta fita siyo mun abinci. Soyayyar taliya da soyayyan kifi ta siyo mun. Zagewa nayi na cinye take away biyun data dure mun, nayi gyatsa an daɗe ba'a haɗu ba. "To likita ya bamu sallama da safennan. Dama ke kawai nake jira ki farka sai kuma mu kama hanyar komawa firsina ko? Taso bari in taimaka miki." Sai da mama ta goya ƴan biyu a bayanta ɗaya ta gaba ɗaya ta baya, sannan ta taimaka mun na miƙe, kaina kamar zai fice ga ruwan jiri yana dibata. A haka muka shiga ofishin Likita. Shawarwari masu yawa ya bani. Mu kai mai godiya muka fita a asibitin. Lori Mama ta tarar mana zuwa gida. Ni dai ina zaune ne a motar, amman tunanin dana saba shi nake yi dai. Ina tunanin yadda zanci gaba da zaman uƙubar gidan Alh Liti. Da kuma tunanin yanda zan bar yarana a tsakar gida in yau Alh Liti yaga wata macen yazo ya tafa mun takaddata a hannuna. Oh ya Allah kaimun mafita, Allah na tuba kaine majiɓancin lamurana. Juyowa nayi na kalli Mama nace. Mama kuna zuwa dubo su Maryam a Kano kuwa, ko Asiya ta taɓa zuwa?" Harara Mama ta zabga mun. "Babu wanda ya taɓa zuwa, banjin akwai kuwa wanda zaije. Ke dai tunda yaranki ne in kika samu damar zuwa Najeriya kinga sai ki je ki dubosu. Bulama sai yaga lalacewar da kika yi, kinga sai yayi miki dariya. Yahanasu tayi miki Allah shi ƙara. Zubaina wallahi ba dan likita yace a lallaɓaki kin kamu da hawan jini ba, kuma ciwon damuwa zai iya kamaki a ko da yaushe ba. Wallahi da kinci ubanki da duk maganganunnan. Ke nifa wallahi ko mutuwa zaki yi in baki bini mun tafi najeriya kin rabu da ƙaddararren mutuninnan ba, to Zubaina sai dai fa in kika mutu a burne gawarki a Ghana, ƙila ƙasarki ce take nan. Ke kinga yadda kika koma kuwa kamar wata dodanniya? Ko sha'awar rayuwa bakya yi, da ƙuruciyarki da kyanki, da kuma lokaci, amman sakarcii kina son ki bari ya dakusar miki da hasken tauraruwarki. Alh Litin da daya sake ki, kina haɗe idda ƙila wani hamshaƙin ɗan kasuwan yazo yayi wuf dake, muma mu dangwali arziki daga gareki." Murmushin takaici kawai nayi. Waɗannan tunane_tunanen na Mama shi ya jamu zuwa ga wannan rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Allah ya kiyasheni taɓewa. Bance mata komai ba, har muka shiga cikin gida Mama tana sababi. Dan ko da Nabeela tazo da saurinta zata karɓi kayayyakin hannun Mama cewa tayi. "Ƴarnan basshi kinji, da lafiyata ras bana buƙatar taimakon kowa a cikin wannan jarabben gidan mai cike da jarabawar rayuwa." Ta ja hannuna muka ƙule ɗaki. Kwanciya nayi ina lumshe idanu. Mama kuma ta kunce goyon tagwaye a bayanta, zata fita kenan Hajiya Kubra ta shigo da sallamata. Ni na amsa mata, Mama kamewa tayi a jikin bango tana jiran ƙiris. "Mama ayi haƙuri bamu samu zuwa dubiyar Zubaina ba. Wallahi mai gidanne ya hana mu zuwa. Dan yace ba'a nemi izininshi ba aka fita da Zubaina ba. Amman munso zuwa, yanzu dama Rashida take shirin kai muku abinci. Umman ƴan biyu ya ƙarfin jikin?" Da sauƙi Hajiya nagode." Nabeela ce ta shigo da kwanon abinci da kofin ruwa ta ajjiye a gefen gado. "Umman ƴan biyu yaya ƙarfin jikin? Kinga bamu samu zuwa ba ko? Hmmm buyagin da Alh yayi a tsakar gidannan ranar da kuka tafi ai bata wasa bace. Shi ya hana mu zuwa ma. Mama ayi haƙuri" Ni dai a ido_ido nake kallon Mama tsoro na Allah, tsorona karta tsinka ni a gaban kishiyoyi. Sai cewa tayi. "Hmmm Allah ya kyauta. Ai kuwa ina ji ina gani bazan bar ƴata a cikin haɗari ba, da har saina tsaya wani neman izininshi ni da ɗiyata. Am bayin Allah, zata samu ruwan wankanta dana yaran ne, ko shima ruwan ya hana?" Banji daɗin kalaman Mama ba, amman su kansu sun fahimci a halin da Mama take na fishi. Hajiya Kubra tace. "Zata samu, akwai ƙatuwar tukunya a wuta, Zubaina ki shirya za'a kai miki ruwa. Nabeela zata kawo ruwan wankan yan biyu." Fita su ka yi tare. Haba Mama, dan Allah...... "Kinci ubanki, Zubaina in baki bini a sannu ba, sai in ɗaga miki nono kinga sai ki ƙara miƙe ƙafarki a duniya. Ni zaki ma ƙorafi dan na caccaki kishiyoyinki. Au yanzu ke nan har kishiyoyi kin ɗaukesu ababen shawara ko kuma ababen yarda kenan? Tana cikin sababi Nabeela ta shigo da ƙaramin bokitin ƙarfe, da ruwan zafi rabi. Harda sabulun salonta da take ma jaririnta wanka dashi. "Kawo ɗaya in soma yi mata" Cewar Nabeela. Mama tayi carab tace. "Mun gode, jeki abunki" Nabeela bata tanka ba ta fita abunta. "Haka kawai a je a kashesu a banza, kishiyoyi da muguntar tsiya, yau ni naga tsiya da wasali ƙasa, a bokitin zanyi wa yaran wanka Zubaina?"" Ni dai tsabar haushi banko kalleta ba na yafa fallen zani na fita a ɗakin ina bin bango, da zagi ta bini. Sai da na sake surka ruwan wankan, dan likita yayi mun gargaɗi kan ruwan zafi. Naji dama dama sosai dana yi wankan. Ƙunzugu nayi da ɗan kwalin atamfata na yafa zani na fito. Na shiga ɗakin na tarar Mama na gasa ma ƴan biyu cibi, har ta kunna turaren wuta a ɗakin. Ina zama wayata ta shiga ruri. Mama ta jawo wayar tace. "Rakiya ce ko lafiya?" Wayar ta ɗaga ta sa a handsfree taci gaba da gashin cibi. "Rakiya kin dawo ne daga tafiyar?" Mama Rakiya tace. "Na dawo babu shiri Musa ne ya kira ni jiya wai mijin Asiya ya dawo da'ita gida. Jikin nata ya tsananta ainun. To shine na dawo ba shiri Yaya. Jikin babu daɗi, gashi wuyanta yayi wani irin mugun kumburi. Nifa ina ganin ko garin biye biyen ƙauyukan bin bokayene tayi gamo da jinnu. Dan ciwon yafi kama da hakan. Sambatu iri_iri. Yaya ba ma wannan ba, mijin yarinyarnan fa tunda ya zo ya ajjiyeta wallahi bai sake kiran waya ba. Daga cikin danginshi babu wanda ya kira mu, kuma bai ba da ko sisi ba. Akwai matsala." Daga ni har Mama dukkanmu mun shiga cikin damuwa ainun, hankalina ba karamin mugun tashi yayi ba. Mama tace. "Rakiya ni nama rasa me zance, na shiga ukuna asirina yana dab da tunuwa, ko aikin da muka yi akan Alh ya samu tangarɗane. Ƴata kuwa wallahi duk wanda ya taɓa mun ita da asiri ya tono tsuliyar dodo. Gobe zan kamo hanya, yanzu ku kuna ina? "Yaya muna gidanki. Ina wani tunani ko dai abokiyar zamanta ce tayo mata wani agumun? Ke kinga yanda Asiya ta canja lokaci guda kuwa, sai dai kin zo Yaya. Zubaina me ta samu?" Sai da Mama ta taɓe baki tace. " Ƴan biyu mata, yanzu muka dawo asibiti ma, hawan jini ne ya kamata, sakamakon uƙubar azabar da take ciki. Rakiya komai ya kwaɓe mana. Ita fa kanta Nafeesa a cikin ƴan matsaloli take, yarinyarnan ko bacci bata iya yi. Rakiya sai dai na dawo kawai." Ƙit Mama ta kashe wayarta, ta rushe da wani kukan baƙin ciki. Nima kukan nake yi. Dama nasan tunda dai su Mama suka ƙi tuba, ƙarshen ba kyau zaiyi ba. Ai duk bawan da yayi fito na fito da ƙudurar Ubangiji, to ƙarshenshi taɓewace, tare da shiga fitintinu iri_iri. Ina nema ma dangina sassauci. Muna cikin wannan halin Alh Liti ya shigo cikin ɗakin ranshi a taurare. Gabana ya yanke ya zube, Mama ya tsallake ya matso bakin gadon ya ƙura ma yaran idanu, nima ya dubeni da kyau yace. "Yanzu ba anjima ba ki same ni a sama, ki kwaso yaran naki kizo dasu" A ɗarare nace mai. Ina jin jiri da yawa, banjin zan iya hawa sama. Ga Mama Alh ku gaisa" Sai cewa yayi. "Oh wai Jummai?, dole ne sai na gaisa da uwarki dan tazo wajanki? Wancan zuwan nayi mata gargaɗi akan yi mun kutse cikin lamarina bata ji ba." Ni da Mama baki muka sake muna kallonshi. Tsallake Mama yayi, har yana take mata yatsun ƙafa. "Jummai daga yau sai yau karki kuma zuwar mun gida, ƴarki nake aure, baku kuke aurena kamar yadda kuka saba ba, ko Alh da kuka tabkeshi da asiri yanzu kanshi ya fito a tukunya, in kin koma najeriya kya ji mummunan labari. Ita kanta ƴarki alhakin mijinta na baya da iyayenshi ke bibiyarta, a hakan ma nata yayi kyau, bari mu jira naki, ƙila kafin ki mutu haushin kare zaki soma" Alh Liti...... Karka kuma kallon mahaifiyata ka dinga faɗa mata kaifafan maganganu irin wannan....." Bansan sanda na miƙe tsaye ba, cikin ɗaga murya da dakiya nake magana dashi. Mari ya gaura mun, ya kai hannu zai ƙara mun Mama ta shiga tsakani, marin a kan kumatunta ya sauka tau, Alh Liti ya ɗaga ƙafa ya tunkudo mama ta faɗo jikina duk muka zube a ƙasa muna kukan baƙin ciki." "Yan iska, wallahi ni ba ƙaramin aikina bane in muku fitsari a ka ba. Ni babu wata tsohuwar ƴar iskar data isa juyani. Na fiku bin bokaye, mahaifina tsohon ɗan tsubbune. Kuma wallahi gobe_gobe ki tattara ki bar mun gidana kar ki kuma zuwar mun. Ke bake ma kaɗai ba har waɗannan karuwan ƙannen nata karsu sake su tako inda muke. Ke kuma ki taso dan ubanki ki kawo mun yara in yi musu huɗuba" MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE[18/08, 9:16 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 51 Wani gigitaccen kuka na kuma saki mai ƙarfin sauti, nayi imani duk wanda ke tsakar gida ka iya jiyo kukana. Wani irin duhu ne yake mamaye mun idanuna, kaina ya sake tsananta ciwo ainun. Adda'a dukkan wacce tazo bakina cabkarta nake yi. Bin bokaye masifa ne, da badan naƙi bin Allah a baya ba, da yanzu ina rayuwa dai_ dai data mutane. Wannan bala'i da mai yayi kama ace mijinka ya mari mahaifiyarka yasa ƙafa ya shureta, ya zageta. Innalillahiwainnailaihilrajiun, Allah ka kawo mun agaji, haka nasa Bulama yai ta wulaƙanta iyayenshi. In yaga wayarsu sai yayi tsaƙi ya dubeni yace. "Su Ba Bakura sun fiye naci kamar ni kaɗai ne ɗa a cikin gida" Ni kuwa a lokacin ji nake yi kamar an yi mun bushara da gidan Aljanna dan tsantsar daɗi. Ina zaune daga ni har Mama a inda Alh Liti ya turemu. Kawai sai muka ganshi a mugun fusace hannunshi riƙe da igiyar wuta. Ihu muka shiga yi ni da Mama, Alh Liti ya shiga zane ni ciki da waje. In mama ta miƙo hannu dan ta tareni haka zai zuga mata bulalarnan. Da mama taga dai da gaske kasheni zaiyi gadan_ gadan ta nufoshi ta cukumeshi. Cizo ta gasa mishi a kumatunshi. Zafin cizon ne yasa ya fyaɗar da Mama a ƙasa ya taka mata ƙafarta. Idanunane suka rufe ruf dukkansu na dena ganinsu ma, sai sautin ihunta kawai nake ji. Sai farkawa nayi naga Hajiya Kubra a kaina. Mama kuma ban ganta a ɗakin ba. Hajiya Kubra ina mahaifiyata take, ba dai tafiya tayi ba ko?" "Bata tafi ba Zubaina. Nabeela da Rashida sun raka ta gidan ɗori, kamar ta samu tsagewar ƙashi ne a ƙafa. Abinda nake so dake shine. Muje in raka ki ɗakin Alh yana sama yana jiranki. Sannan zan faɗa miki in kina son kan ki da arziki karki sake tankama Alh balle har yai miki irin wannan dukan." Kaina na sauke hawaye na shatata a kuncina. Da taimakon Hajiya Kubra, da taimakon Nasiba ɗiyar wajanta muka isa ɓangaren Alh. Naci sa'a yana falon ƙasa. Yaran Hajiya Kubra ta bashi yasa hannu ya karɓesu. Rannan nashi a murtuke, ni dai ina ƙasa na ƙume da haushi kallonshi ma bazan iyaba. Ina ji yana mis mis da baki yana ma yaran adda'a. Can ya miƙa ma Hajiya Kubra da Zainab yaran. "Nasa musu suna Fatima da Aisha. Wannan itace Fatima, wannan Aisha, ai musu inkiya da Hassana da Usaina. Sannan gobe ina da zama da ku a cikin gidannan. Dan naga raini da rashin ɗa'a ya soma damunku ina son zanyi ma tubkar hanci. Ke kuma ki ƙara jaddada ma uwarki, gobe ta tattare ta bar mun gidana. Duk ranar dana sake ganinta a gidannan, saina zauna a ruwan cikinta nayi mata fitsari. Ƴar iska maras tarbiyya, wacce bata gaji tarbiyya ba, masu abun faɗe. Ko Alh da ƴar uwarki ta dabainayeshi da asiri, Asirinku ya tonu, ya sake ta saki uku ya huta, ga lalura data kamu dashi, wallahi baku ga komai ba ma. Ni kaina da ɓarnar da zaku yi mun sai tafi ta Alh tunda na fishi ƙumbar susa, ke da kwanciyar hankali har abada, aurena dake ba saki, babu yaji. Na zame miki ɗuwawu dole ki zauna dani. Ku fice mun da gani." Hmmm da taimakon Hajiya Kubra muka bar shashen Alh Liti. A tsakar gida muka tarar da Zarah tana hararwa, tunda na haihu Zarah ko barka bata leƙo tayi mun ba. Yanzun ma tana ganina ta saka dariya. "Ahayye, an dai yi abun kunya. Faɗa da mijin ƴa har da cizo, kila dangin mayu ne ku wa ma ya sani" Damuwar dake damuna tafi ƙarfin in tsaya tanka ma Zarah. Jikina har rawa yake yi, maganganun Alh Liti akan saki ukun da mijin Asiya yayi mata ya gigitani. Na shiga tambayar kaina. To ya ma akayi Alh yasan Asiri akayi mishi?" Ina zama a bakin gado Mama suka dawo ita da su Rashida. Ƙafarta tayi suntum, gefen idanunta ya tara jini, ga ciwo a bakinta. Ajjiar zuchiya kawai na sauke, na dinga bin kowa da idanu, kaina kuwa riƙewa yayi gam, jirine ya kwasheni na faɗa gado luu. Dole haka Mama tasa aka kwasheni zuwa asibiti, gado suka bani dole, sabida jinina ya hau sosai. Washe gari Mama ta kama hanyar Najeriya, ko sallama da juna bamu samu damar yi ba. Rashida ke zaune dani a asibiti. KADUNA: Misalin ƙarfe shidan yamna Mama ta sauka a tashar mota daga Kano zuwa Kaduna, dan jirginta na Kano ne. Da sallama ta shiga ɗakin ta iske, Rakiya da Naja'atu ɗiyarta. Asiya kuwa tana kwance a ƙaramin gado kamar babu rai a jikinta. Wuyanta ya kumbura yayi suntum dashi himm. "Rakiya haka jikin na Asiya ya tsananta? Innalillahiwainnailaihilrajiun, Alhn kuwa ya dawo ko tunda yazo ya ajjiye mun ita bai waiwayo ba?" Rakiya tace. "Yaya haɗarin mota kika yi ne, naga kin shigo harda sanda, ga fuskarki duk ciwo" Zama Mama tayi tace. "Ke dai Rakiya bari. Mijin Zubaina ne ya haɗa ni da itan yai ta jibgarmu, kinga ƙafata targaɗe da tsagewar ƙashi na samu. Ita kanta fa Zubaina ciwo take yi mai tsananin gaske. Amman wallahi yaƙi ya barni in zauna da'ita, tana asibiti babu mai kulawa da'ita sai kishiyoyi. Ni rayuwarma ta fice mun a kai" Salati Rakiya ta shiga rabkawa ita da Naja'atu. "Yaya duka fa, yau ni naji tsiya da wasali ƙasa, amman wannan miji na Zubaina kwai tambaɗaɗɗe. Ki duba yanda Bulama yake haba_haba damu, in munje gidansu, ya hadomu da goma sha tara na arziki, ya ɗakko mota ya kawo mu har gida. Abinci da Azumi muma sai dai mu taimakawa maƙota, sallar laiya fa ki duba Yaya har ni yake yi ma laiya, ga atamfar sallah da takalmi da yake aikoqa Zubaina dashi. Ohh duniya kenan, ni na ɗauka yanzu ne Zubaina zata huta ashe kallon kitse mu kai ma rogo?" Mama ta share hawayenta da yake zuba tace. "Ke dai bari tuna mun wannan yaro Bulama Rakiya." Rakiya tace. "Kinga Naja'atu ma uwar miji ta hanata zaman auren fur, tasa mijin ya korota gida, amman bai bata takadda ba. Yaya Alh fa ya saki Asiya saki uku. Hmm Yaya da yazo ma ƙin shigowa yayi wallahi, kishiyarta ya turo uwar gidanshi kenan da takaddar ta shigo ta kawo, tana wani taƙama. Ni bama wannan ba, gidajen da yarinyarnan ta giggina aka zuba haya, duk ya ƙwace gidajen, sannan yace duk wanda ya taka gidanshi da sunan kwasar kaya, ko ganin yara to kotu ce zata rabasu. Shi yasa nake zargin kishiyarta ce ta tabka mata wani asirin." Mama kuka wi_wi ta fashe dashi har tana birgima, sai faɗi take ta shiga uku ta lalace, asirinta ya tonu. "Yaya bafa kuka bane mafita, yanzu meye abun yi? Wajen wanne mai magani zamu kai yarinyarnan?" Mama ta miƙe da ƴar sandarta a hannu tace. "Rakiya mu soma zuwa gidan Malam Babba. Naja'atu ki fita ki taro mana Ɗan sahu, tunda gidan ba wani nisa." Naja'atu ta fita ta dawo da me ɗan sahun. Ita da Mama Rakiya suka kinkimi Asiya zuwa ɗan sahun. Mama ta rufe ɓarayinta ta biyo su. A bakin ƙofar gidan Malam Babba suka tsaya, sun kuwa ci sa'a yana ciki, dan sun hango layin mata. Mai ɗan sahun suka sallama, aka sake tarairayo Asiya zuwa rauren gidan malam Babba. A benci suka zauna suna riƙe da Asiya. Mama da mama Rakiya kowacce tayi jigum abun duniya ya ishi waɗannan bayin Allah. Mama ta ɗaga wayarta ta kira Musa. "Halo Musa, kazo nan gidan malam Babba ka same ni, mun kawo Asiya ne" Musa ya amsa mata da cewar shi baya ma garin, yaje wajan wata yarinya a Jigawa. Da tsaki Mama ta datse wayarta tana tsine ma Musa" Mama Rakiya dai bata ce komai ba tana riƙe da Asiya. Sannu kan hankali har layi yazo ya iskesu. Haka suka kuma tattagar Asiya zuwa cikin ɗakin malam Babba. A gefen wata tabarma ya nuna musu yace ta a shinfiɗe Asiyan. Umarninshi suka bi suka shinfiɗeta. "Jummai lafiya wannan ba Hajiya Asiya bace?" Mama na share zufa tace. "Itace ka ganta nan kishiya ta sabauta mun ita, miji ya saketa, duk wasu kadarorin data tatsa a jikinshi komai ya kwace. Malam kai mun rai" Miƙewa malam Babba yayi ya tsugunna a gefen Asiya ya kama kanta yana dubawa. Ya daɗe yana nazari kafin ya ɗago da kanshi yace. "Jummai an fa yanka ta tashi. An samu gagarumar matsala dangane da aikin da nayi ma Hajiya Asiya. Dan kinga wannan ciwon nata? Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya aka turo mata, da yanzu kishiyarta ce a cikin wannan lalurar" Mama tasa hannu a ka tace. "Shikenan Jummai ƙaryarki ta ƙare alkadarinki ya karye Jummai. Malam to yanzu menene abun yi, sannan wacece tayi mata irin wannan mummunan aikin" Kasar da yake duba da'ita ya soma zanawa, ya jima yana zanawa yana gogewa, daga bisani yace. "Ƙasa bata nuna mana wanda yayi ƙaiƙayi koma kan masheƙiyar ba. Babbar matsalar shine, maganin makarinshi ne babu Jummai. Yarinyar nan ku mayar da'ita gida mutuwa zata yi. Aljanu sunfi dubu a jikinta. Jummai ku tashi ku tafi." ( Tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana. Dama ƙarshen masu bin bokaye ba ƙarshe bane mai kyau. Komai daren daɗewa wata rana zasu zama ababen tausayi) Nan su Mama suka ɗauki Asiya suka nufi gida. Washe gari suka kuma zazzagaye bokaye da ƴan borin da suka sani, duk inda suka je cinye musu kuɗi kawai akeyi a banza amman babu wani canji wuyan Asiya sai kumbura yake sake yi, Mama bata da zaɓi dole taje gidan kawu Tanko ta zayyana mishi halin da Asiya take ciki da kuma wulaƙancin da Nafeesa take fuskanta a wajan mijinta dama danginshi, da irin yanda suka kwashe da mijin Zubaina,tana yi tana kuka. Shiru Kawu Tanko yayi yana nazari tare da jinjina ƙudurar Allah da yanda yake kama mai laifi duk abinda ya shuka ya girbe abunshi. Ya ji daɗin faruwar hakan ba dan baya son su Asiya ba, sai dan ya zame musu izina dama masu karatu baki ɗaya. kwatancen wani ƙauye yayi musu a Bauchi yace su tafi can ko Allah zai sa a dace. Sai dai fa babu kuɗi a hannayensu. Haka dole su Sagiru suka sa gidan gadonsu a kasuwa suka siyar, aka tarkaka kuɗin Mama da Nafisa da Goggo Safiya, ne aka shirya tafiyar dasu, Ita kanta nafisa a cikin tsangwama da hantara take a wajan mijinta, ya ɗauke mata wuta, bata jin daɗin zaman dashi sam. Tayi baƙi tayi muni, duk ƴan kadarorinta sun salwanta a hanyar bin malaman tsubbu da bokaye, da komai nata ya ƙare ne tayi haƙuri ta zuba ma sarautar Allah idanu zanen ɗaurawa wannan bata da na kirki,ga ciki na biyu a jikinta. Halin da Mama ta bata labarin Zubaina tana ciki, da halin data ga Asiya a ciki, da irin yadda Mama ƙafarta take mata mugun ciwo shi yasa ta saduda tabi Allah ta bi koyarwar ma'aiki arrasul Sallallahu alaihi Wasallama. Ko wannan malamin da zasu je wajanshi. Malamine na gaske ba mishiriki ba. Zubaina kuma suna waya da'ita babu laifi kwananta uku a asibiti aka sallamesu suka koma gida. MRS BUKHARI [18/08, 9:45 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 52 BULAMA BABBA: Yau ya kasance ranar asabar, wanda yai dai_dai da ashirin ga watan da Ba Modu ya tsaida ranar meeting na gida. Tun sassafe na gama shirina a gurguje, dan Mama Gana tun asubar fari take jaddadamun in zo ta gidanta mu tawo tare, domun su Ya Ari basa nan duk sunyi tafiya. Ina fitowa na samu Bawa a falo yana aikin gida wanda makaranta ta basu, domun kar a barsu a ranakun hutun haka. Bawa ina Maryam take, me yasa baka je ɗakin karatunku kayi karatun a can ba, ina su Aneesa fa?" Bawa yace. "Suna ɗaki dasu Maryam Abba. Yanzu umman Aneesa tayi mata wanka." To maza tashi zamu je Damaturu yanzu." "Abba muna da islamiyya, kuma jarabawa zamu zana" kai na dafe dan na sha'afa da batun jarabawar sam. Hannunshi naja zuwa ɗakin yaran na hado kansu muka fito, sai da na kulle shashen, sannan muka nufi Shashen Ahmad muka nufa, a guje suka shige suka barni a tsaye. Hajara ce ta leƙo. "Bulama ina kwana" Lafiya Hajara, ya hidima, amma Ahmad fa?" "Ai ya fita tun safe, yace akwai aikin da zai gudanar a kamfani." Sallama nayi mata kawai na wuce, bayan na bata key. Ko da naje gidan Mama Gana ta gama shiri ta jima tana jirana. Ai kuwa ina shiga ta dirarmun da masifa. Ni dai sai haƙuri nake bayarwa. Muna hanya ne Mama Gana tace. "Wai ni Bulama Babba baka ji halamar sauyi a muryar uwarka ba tunda Bakura ya rasu ba?" Gabanane ya faɗi ras na dubi Mama Gana nace. A'a wani abun kika ji Mama?" "O'o kawai dai ni inna kirata sai in ji tana sha mun ƙamshi. Duk da nasan mutuwar miji akwai ɗaci, amman ai ba mu muka kashe BaKura ba, sa'inshine ya cika. Ni naga kamar ta sauya." To ƙila dai sabida rashin mijinta da tayi ne, kinsan Ba Bakura da barkwanci." Mama Gana ta taɓe bakinta kawai. Ni kuma na shiga tunanin me yasa Hajja zata ɓullo da wannan ɗabi'un a yanzu da gidan babu abunda suke buƙata sai haɗin kai, da sake riƙo da zumunci. Lallai ta ɗakko hanyar wargaza zumuncin cikin gidan. Amman in sha Allah ba zata samu wannan nasarar ba. Haka nai ta aikin tunane_tunane, hirar ma jifa_ jifa muke yi da Mama Gana, daga baya ma bacci ne yayi awon gaba da'ita." Kai tsaye falon Ba Bakura muka harhaɗu kamar yadda aka saba. Wannan taron shine taro na family na farko da aka gudanar babu Ba Bakura. Kowa ka kalla da ɗan guntun hawayenshi a idanunshi. Mama Gana ma na shigowa ta fashe da kalan nata kukan. Ni dai hawaye kawai nake sharewa da bayan hannayena. A kusa da Gunsum na zauna. Ba Modu ne ya yafito ni da hannunshi ya nuna mini kusa dashi. Dawowa nayi na zauna a kusa dashi. "Allah ya gafartama iyayenmu, da ƴan uwanmu. Ya gafartama dukkan muminan duniya baki ɗaya, in tamu tazo Allah yai mana cikawa da kyau da imani. Bulama Babba a matsayinka na shugaba kuma jagoran gidannan tashi ka buɗe taron da adda'a domun mu gudanar da abunda ya tara mu a nan, wasu nasan suna da uziri." Umarnin Ba Modu na bi ta hanyar miƙewa na buɗe taron da adda'a mai tsayi daga bisani na zauna kaina a ƙasa. "Na tara wannan taronne a bisa dalilai. Na farko inaso zan soma da sake jaddada maganar zumuncinmu. Sannan inaso ƴaƴayanku tun yanzu ku zaɓa musu matayen aure, maza_ mazan kenan domun a sake cakuɗuwa, ta hakane zumuncin zai sake yin ƙarko da yardar Allah. Muyi haƙuri da kayukan mu, mu yi haƙuri da ƴan uwanmu. Banda riƙo duk da nasan ba'a yin wannan halin a cikin wannan ahalin. Amman duk wanda yake da abun faɗe yayi bayani. Duk wanda aka yi wani abun da ranshi ya sosu ya sanar kafin in ɗaura daga bayanina." Shiru Ba Modu yayi yana sauraren ko da me ƙorafi. "To ni dai Modu ƙorafina biyu ne kacal kuma dama irin wannan ranar nake jira in faɗi abinda yake raina. Hajja Gana tunda BaKura ƙasa ta rufe idanuwanshi shikenan mata ta soma cika tana batsewa, in an kirata a waya sai kaji tana magana kamar wata ƴar tauri. To ta fito fili tayi bayanin in akwai abunda yake damunta sai mu ji. In kuma rabon gadon da aka gudanar ne baiyi mata ba sai tayi bayani a gaban kowa. Ƙorafi na biyu akan Yahanasu ne Modu. Ni dai fishi da yarinyarnan da kake yi ya isheka haka nan. Tunda dai tana iya banbance fari......." Ba Modu ya dakatar da Mama Gana ta hanyar ɗaga mata hannayenshi. Gum tayi da bakinta. Kallonshi ya mayar kan Hajja. "Kinji abunda Mama Gana ta faɗi, kina da abinda zaki ce dangane da wannan tuhumar da take yi miki" Kallonta nayi rannan nata a mugun ɗaure tace. "Babu wani abun da kowa yayi mun. Damuwar mutuwar mijina itace ta dame ni, ya kamata aimun uzirin. Batun rabon gado ai nasan ba da ka akayi ba. Asalima Bature ne yazo da malaman da suka yi rabon gadon." Ba Modu yace "To Mama Gana kinji amsarki. Akwai wani mai ƙorafin?" Shiru babu wanda ya tanka, hakan ya nuna babu kenan. Sai Ba Modu ya ɗaura bayaninshi da cewa. "Sai magana akan Yagaji da Yana iyalan Baana. Ni da su mun dai_daita tsakaninmu zan auresu su zauna a ƙarƙashina, domun faɗaɗa zumuncinmu. Sai ko wacce taci gaba da zama a ɗakinta. Na tabbatar yara zasu yi farin cikin hakan" Nan falo ya ɗau sowa sai hamdala akeyi. Bayan an nutsu yaci gaba da magana. "Yau za'ayi ɗaurin auren in sha Allah. Sai maganar mata_ matan cikin gidannan surukai da muke da su, da namu yaran da suke gidajen wasu. Na ba ko wacce nera dubu ashirin_ ashirin, ba dan komai ba, ba dan mazajen sun gaza ba, kyauta ce daga baban yaran. Bulama Babba ga kwali nan tun jiya nasa Dala ya wauware dubu ashirin_ ashirin ka miƙa ma matan, surukan gidan in an gama taro sai a basu nasu." Miƙewa nayi na bibbisu da dubu ashirin_ ashirin dinnan sai godiya da washe baki suke faman yi. Sai da falon ya kuma nutsuwa sai Ba Modu ya ci gaba da Magana. "Na samu ƙorafe_ ƙorafe masu tarin yawa akan gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye_ shayen muyagun ƙwayoyi da na miƙa Yahanasu. Har mijinta yana kai kokenshi wajan mahaifiyar Ahmad nashi. Tazo ta same ni, hatta dattawan anguwa sun tare ni da zancan. Haka dangin Innana su kai ta sintiri duk dai akan batun. To ku sani ba ƙin Yahanasu bane yasa na miƙata wannan gidan ba, kuma ba wai bansan gidan suna azabtar da marasa lafiyar ciki bane. Asalima irin labaran duka da azabtar dasu da akeyi ne yasa na yanke hukuncin kai Yahanasu can. Hannunka baya ruɓewa ka yanke a kar. Ana iya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Daga cikin ku wasu sun kai ma Yahanasu ziyara, sun dawo da kuka, wasu an basu labarin irin rama da duhun da Yahanasu ta sake yi, duk kowa ya shiga tashin hankali. Wallahi _ wallahi tashin hankalin da nake ciki yafi na ku, yafi na Innana, yafi na Bulama. Ban sake yin bacci mai kyau ba tun ranar dana yi tozali da Yahanasu a Dawanau. Wannan hukuncin dana yanke a kanta shine hukuncin daya dace da'ita. Kuma shine zai faru akan duk wanda ya kasa rungumar ƙaddara ya faɗa hidimar shaye_shaye mace ko Namiji. Babu ragiya a tsakanina da duk wanda zai ɓata mana suna ya lalata rayuwarshi, ya saɓi Allah domun wani biyan buƙatarshi. Tun wancan watan malam Rilwanu yace zamu iya dawowa gida da Yahanasu aci gaba da sa mata idanu. Ni kuma nace ya barta ta sake dakuwa tukunna. Iya duka Alhamdulillah ta daku, tasha rubutu, ba dare babu rana adda'a nake mata dan samun lafiya. Jiya malam Rilwanu ya sake kirana yace Yahanasu ta warke sumul kamar ba wannan Yahanasun ba. An kawo mata laka mis ɗin ma, ta fashe da kuka tana ambaton Allah. Alhamdulillah zuwa ƙarshen wata Yahanasu zata dawo cikin iyalanta." Idanu na lumshe ina jin wani irin farin ciki na fisgata. Sai hamdala ƴan uwana suka shiga yi, suna jinjina maganganun Ba Modu. "In da mai abun faɗe ya faɗa ni kam na gama, ƴan ɗaurin aure suna jirana a waje" Cewar Ba Modu. Hajja ce tace. "Ina da maganar da nake son isar muku nima, naso ko da babu taronnan in haɗa iya taron cikin gida." Tunda ta soma magana gabana yake faɗuwa. "Sati biyu masu zuwa in sha Allah ɗaurin auren Bulama Babba, rana irin ta yau. Zai auri ɗiyar wajan Bature Yalewan gidan" Gabaki ɗaya falon babu wanda wannan batu bai jijjigaba, ni kaina na kaɗu da jin wannan batun. Mu yaran gidan mu kai tsuru_ tsuru, matan gidan kuwa kowa ya saki baki . "Akan wanne dalili zaki ce Bulama Babba ya auri Yalewa, yarinyar data riƙe ita zaki haɗa da Yahanasu su zauna tare? Yarinyar da ta kasa zaman gidan Bature, tana can Yobe tana yawonta kwararo_kwararo. Wallahi baki isa ba Hajja. Ohh yanzu na gano ki shi yasa kike ma mutane gani_gani ko? To wallahi bazai yiwu ba. Modu kana jin abunda wannan matar take cewa ko?" Mama Gana ce ke magana cikin zafi. Ranta har ya gama hargitsewa ta miƙe tsaye. Ya Bagulaji tace. "To duk da dai baki sanar damu meye manufarki na son haɗa auren Yalewa da Bulama Babba ba. Amman da dukkan halamu yaron ba so yake yi ba. Ni ina ganin in dai baya so da anyi haƙuri an bar yaronnan da matarshi" Ya Innana uwar kawaici tace. "Akan me zaku ce haka? In akayi haka ai tamkar ba'ai ma Hajja adalci bane. Tana da damar bama Bulama Babba duk matar da take ganin tafi dai dai da rayuwar ɗanta. Fatanmu Allah ya basu zaman Lafiya." Nan fa Mama Gana ta dire a ƙasa tana kuka. "Ohh sabida anga BaKura baya nan ƙasa ta rufe idanunshi za'a kawo mana rabe_raben kai? To a matsayina na ya a cikin gidannan ina da ƙarfin faɗa aji dole wallahi ko kuna so ko bakwa so. Nari ga na gane take _ taken ki. Tun lokacin da Yahanasu ta faɗa jarabawarnan kike cikin fishi da kowa. Ke kin mance sanda naki ɗan wata ƴar iska ta raba ku dashi ko waya baya iya muku. Ince ba Yahanasun bace tayi uwa tayi makarɓiya wajan dawo dashi saiti ba? Duk abunda ya faru da Yahanasu Bulama Babba da tsohuwar matarshi su su kai mata sila, ita kuma tsantsar biyayya yasa ta ci gaba da zaman. Yanzu daga yaro ya samu dukiya shine Bature yake ƙoƙarin ganin ya shiga tsakaninmu? A lokacin da shi Bulama Babban yace cikin ukun da tsohuwar matarshi ta sashi. Ai a lokacin ya dace Bature ya sadaukar ya ba Bulama Babba Yalewa su je su gwabza da Zubaina, tunda dama duk ƴan duniyane dukkansu" Duk wannan maganganun cikin zafi Mama Gana take fesar dasu. Dukkannin abinda take faɗa gaskiya ne kuma. Hajja ta miƙe tsaye tace. "A hir dinki Mama Gana, dan kina ƙanwar mijina ai baki isa kin taka ni na ƙyaleki ba. Yahanasun ba sai da ta rasa darajarta bane aka liƙa ma Bulaman ba? Me yasa tun da darajarta ba'a aura mishi ita ba. Sannan da kike zancan Yalewa ƴar iska ce, amman kinsan ba'a taɓa kamata tayi ma iyayenta ƙaryar anyi mata fyaɗe ba ko? Yahanasu kuwa shaye_shayenta taje tayo, ƴan iska abokanta ƴan iska suka tare ta su kai mata fyaɗe. Modu yasa BaKura ya rurrufa aka ba Bulama ita. Dan haka a wannan karon sai ya auri Yalewa ko kuma ya saki Yahanasun" Ƙasa tamkar ta tsage in faɗa nake ji tsabaragen kunyar Ya Innana da Ba Modu. Hawaye sosai Ba Modu yake zubarwa kuka kuwa harda shessheƙa. Abinda ya ja hankalin kowa kenan har hayaniyar ta lafa. Sautin kukanshi ya cika falon tab. Dukkanmu mazan muka isa gareshi muna rarrashinshi, amman sai ɗaga mana hannu yake yi akan mu barshi yayi kukanshi. Mama Gana tana kuka tana faɗin "Ku barshi ya koka Bulama Babba. Hajja Gana na son kawo rikici da gaba a tsakanin iyalan Modu da BaKura. Kinci amanar ɗan uwanmu, ashe lumbu_lumbu kikai mishi sabida kinsan zai iya haƙura da ke sabida farin cikin danginshi." Hajja ta shigewarta ɗakinta tana fesar da maganganu masu kaifin gaske. Ba Modu ya daure yace. "Kar kowa ya ɗauki wannan abinda ya faru a matsayin komai. Wannan nasan shine na farko daya taɓa faruwa a wannan zuriyar. Ina mai baku haƙuri. Hajja Gana tana nan a matsayin uwa a cikin wannan gidan. Kuma matsayinta yana nan dam. Aikhairanta zamu kalla ba wannan abun data aikata ba. Nasan a cike take da zafin mutuwar BaKura ta dalilin halin da Yahanasu ta jefa rayuwarta. Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka. Kai kuma Bulama Babba da kaina zan kai kuɗin aurenka zuwa wajan Bature. Allah yayi muku albarka. Mama Gana ki dena kukan ya'isa kiyi haƙuri kar ki sake cewa komai." "Wallahi tallahi Modu baka isa ka tursasa Bulama Babba ya auri Yalewa ba. Akan wannan lamarin zan iya yin fito na fito da kowa. Na faɗa ma, wannan shine karon farko da mukai gaddama da juna. Kar ka bari in hassala in yi abunda zan ƙarashe rayuwata a firzin." Miƙewa tayi ta fice tana share majina. Komar kowa jira yake yi sai aka soma firfita. Matan duk suka yi shashen iyaye mata, su Aissa kuma suka shiga ciki wajan Hajja. Mu kuma ƙofar gida muka nufa, dan gudanar da ɗaurin auren Ba Modu. MRS BUKHARI CE[19/08, 9:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 53 YA INNANA: Sunturi take yi a farfajiyar falonta. Kanta yayi matuƙar ɗaukar zafi sosai. Taji zafin maganganun Hajja Gana matuƙa gaya, har tana ji kamar ba zata iya mancewa da wannan lamarin ba. Wannan ranar ranace wacce ba zata gogu a tarihin rayuwarta ba. Kuma tana ji kamar ƙarshen zaman Bulama Babba da Yahanasu yazo. Ya Bagulaji ce ta shigo jikinta a sanyaye ta dubi Ya Innana wacce idanunta ya kaɗa ya zama jawur dashi. "Innana kinga wani sabon al'amari da ya ɓullo cikin gidan kuma. Daga rasuwar Ba Bakura al'amura sun soma jagulewa. Ga can Mama Gana ta sake komawa ɓarayin Hajja Gana sai rikici suke yi. Kinsan mama Gana ba ƙanwar lasa bace. Gashi mazan gidan duk suna wajan sha'anin ɗaurin aure. Su Fanna dai da surukan gidan nasa suke kwashe tuwon ƴan ɗaurin Aure. Muje dan Allah mu same su gudun kar ayi ɓatacciya. Gashi hankulan surukan gidan duk ya koma falon Hajja Gana. Ya Innana bata ce komai ba tasa kai ta fita. Ya Bagulaji tabi bayanta har zuwa cikin falon. "Waye bai san Innana ta gama mallake Modu ba? Hatta Bagulaji sau nawa tasha kawo ƙarar Modu kan fifita Innana da yake yi. Ai barewa ba za tai gudu ɗanta yai rarrafe ba" Itace kalmar data dira a kunnen Ya Innana. Ji tayi data sani da bata shiga falon ba balle har ta ji wannan kaifaffar maganar. Mama Gana tace. "Amman kin cika butulu Hajja Gana. Zaki sha mamaki kinsan Allah sai Bulama Babba ya saki Yahanasu tunda bashi bane autan maza ba. Ni sai yanzu naji daɗin yanda Zubaina ta dinga hanaki bacci, ke da ɗanki baki da matsayin da zaki kira wayarshi ya ɗauka. Allah ya bamu lafiya" Fuuu Mama Gana ta fita tana ihun kuka. Ya Innana ta ƙura ma Hajja Gana idanu tana mai cike da mamakin yanda dukiya ta rufe mata idanu, har take ƙyashin Yahanasu ta ci wannan dukiyar. Har ta buɗe baki zata yi magana, sai ta tuno maganar bata da amfani kwata_kwata fita kawai tayi. Ya Bagulaji ta biyo bayanta. A tsakar gida suka iske Mama Gana tana burgima. Shigowar su Ba Modu kenan suma, an gama ɗaurin aure, ana kan yin walimar cin abinci. Fanda ta je ta kirawosu, zuwa wannan lokacin surukan gidan sun fahimci inda aka dosa. Sai dai mazajen nasu sun musu umarni da ko wacce ta wuce ɓarayinta. "Modu Bulama ya saki Yahanasu shine abunda nake so. Wallahi ba zata ci gaba da zama dashi ba, yaje yai ma uwarshi biyayya. " Bulama Babba: Dam naji gabana ya faɗi jin furucin Mama Gana. Ba Modu yace. "Ki dena wannan maganar Mama Gana a tsakar gida gaban yara. Ke sai yaushe zaki girma ne? Ni kaina da kika ga nayi shiru zan ɗau matakin da zai kwanta ma kowa a rai. Ko wacce ta shirya ta koma gidan mijinta. Bulama ka ɗauki Mama Gana ku koma ka kwashi yaran." Wakil ka je gareji ka fito mana da mota zamu yi wata ƴar tafiya. Kai Dala ka je ka sallami jama'ar dake waje." Ni dai gabaki ɗaya sun gama rikirkitamun lissafina. Na ma rasa yanda zanyi. Gashi Ba Modu ya tsorata ni dangane da batun matakin da zai ɗauka, tunda bansan wanne mataki bane. Sannan ina zasu je yanzu? Innalillahiwainnailaihilrajiun Allah ka kawo mun ɗauki ya iyali. Mama Gana ce tace. "Ga yaranka Bulama wuce mu tafi ka mayar dani gida. Amman kafinnan zaka kaini gidan Bature. Ni dai ko magana wannan na kasa yi. Ina gani su Ba Modu suka fice a mota shi da Ya Innana sai wakil dake tuƙi. Fita motarmu tayi a cikin gidan muma. Na baro yan uwana a cikin tulin baƙin ciki da damuwa. Kai tsaye gidan Ba Bature muka nufa. A ƙofar gida naso tsaiwa amman Mama Gana ta tusani a gaba muka shiga. Abinda muka tarar yana faruwa a gidan yai mun daɗi. Yalewa ce riƙe da akwati tana rantsuwar in suka matsa mata dole sai ta aureni zata iya shiga duniya a nemeta a rasa. Ita me zata yi dani mummuna baƙi dani. Mama Gana dake tsaye a bakin ƙofar shiga ko sallama ba tai ba sai jin maganarta suka yi a bayansu. "Kinyi dai_dai yarinya. Wake yayin auren dole a wannan zamanin. Kai kuma Bature wallahi ka faɗi ƙasa tim babu nauyi. Oh sabida Hajja Gana ta miƙa maka dukiyarta a hannunka shine kake son ka haɗa auren ɗiyarka da Bulama Babba ko? Kaga in Hajja Gana ta mutu dukiya ta zama ta Bulama Babba shi kuma Bulama Babba sirikinka ne, kaga kuɗin ya koma hannunka. In lissafina yayi dai_dai to kaine kai ma Hajja Gana famfo, ta sauke mana atilarar rashin arziki a gida." Nan sa in sa ya ɓalle a tsakankanin Ba Bature da Mama Gana, sai ni ne na zama mai rarrashinsu. Sai da tayi ma kowa tas sannan ta fita, matan gidan da Yalewa babu wanda yace komai. "Ba Bature ayi haƙuri. Rikicine sosai ya ɓalle a gidan, ni kuma tace in rakota bani da ikon yi mata musu. Kuma Ba Bature tunda Yalewa bata son aurennan, nima ba so nake yi ba. Ni ina ganin ayi haƙuri kawai zai fi alkhairi. Sannan Ba Bature dan Allah ka samu Hajja ka tausheta, yau tayi maganganu a gidan marasa daɗi".... Katseni Ba Bature yayi ta hanyar cewa. "Fice mun a gida kaji Bulama Babba, ba dai kafi fifita ƙanin mahaifinka sama da ƙanin mahaifiyarka ba? Ka fifita ƴar shaye_shaye sama da Yalewa" Ban bari ya ƙarashe ba na fice da sauri a cikin gidan, idanuna cike tab da ruwan hawaye, na fahimci so suke su haukatani, kowa sai garani take yi kamar tayar mota. Mota na shiga muka kama hanyar Yobe" Tun daga Damaturu Mama Gana take jaraba har muka iso gida na sauketa. Ban ko shiga ba na juya na nufi gida. Ɓarayin Ahmad na isa dan in karɓi key. Hajara ce ta miƙa mun key ɗin na wuce ɓarayinmu ba tare da yaran sun biyo ba. Sallah nayi da shigata, ɗakin dana rufe na Yahanasu na buɗe na shiga ina ƙare ma ɗakin kallo yanda ya tsaru sosai. Ba tarkace aka cika a ɗakin ba, amman komai yana kan tsari da matsuguninshi mai kyau. Bakin wadrope na isa na wangale murafan wadrobe ɗin na shiga kallon kayayyakin dana siya na loda mata a cikin wadrope ɗin. Tun daga kan atampa zuwa leshi, material shadda, lafayoyi, dogayen riguna ƴan yayi iri iri. Wasu kayayyakin ma ɗikkakku na sai mata irin ɗinkin hajiyoyinnan. Naci burin Yahanasu ta samu lafiya ta dawo mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai ni'ima in riritata taji daɗin aure, wahalar hidima dani da yara da tai ta yi in fanshe mata. Duk a cikin wannan hidimar da tai ta fama dashi, har muhalli take ta ƙoƙarin taga ta gina mana duk dan asirinmu ya rufu. Na tuno sanda take shiga ƴan gwanjo ta tsinto kaya ta siyo mun dani da yara. Na sake tuno sanda nace mata in nayi kuɗi zata ji daɗi ita zan soma siyama mota kafin ma in hau. Kuma na cika mata alƙawarinta wannan motar da nake hawa tatace, da sunanta na siya, kamar ta san mai zai faru tace. "Allah yasa in kayi kuɗin ka barni in mora, ƙila ma tare da Amarya zamu tare a sabon gida, koma ta rigani tarewa." Ya ilahi ka kawo mun mafita. In sha Allah in ta dawo ta samu lafiya, zan kaita umara in kaita aikin Hajji ta sauke farali itama. Kuma aurena da Yahanasu babu wanda ya isa ya kashe mun shi, ni da ita mutuwa ce kaɗai zata iya rabamu. Wayata ce ta shiga kuka a ajjihu. Ina zarowa a ajjihuna naga Hajja Gana ce kira na. Sai da gabana ya faɗi ras kafin na ɗauki wayar. Kuka take yi sosai, kukan da take yi a yanzu bata yi kwatanshi a rasuwar Ba Bakura ba. Cikin shessheƙa tace. "In dai ni na tsugunna na haifeka, to inci darajar naƙuda da rainon ka da nayi. Zan baka umarni ka saki Yahanasu, kar ka ce zaka yi mun musu dan zan iya yima baki a kanta. Naji ɗiban albarkar da ka raka Mama Gana tayo a gidan Bature. Ashe zaka iya rakota ta zazzageni nima? To yayi, ka sani aurenka da Yalewa babu fashi. Ina jiran ka ka kawo mun takaddar sakin Yahanasu"" Kaina ya shiga jujjuyawa dani, duniyar tai mun zafi da duhu. Allah kawai nake ambato dan shine abun ambato. Idanuna na lumshe wasu hawaye suka zubo mun mai zafin gaske. Sallama na jiyo anata dokawa, da ƙyar na lallaɓa na fito falon. Ahmad na gani a tsaye da basket na abinci. Ganin halin da nake ya girgizashi ainun. Da sauri ya iso inda nake. "Lafiya Bulama rasuwa akayi ko me?" Ahmad rayuwata Hajja take neman ta raba ni dashi. Ahmad kaji fa wai sai na saki Yahanasu. Kuma umarni take bani. A cikin masifa take son ta jefa ni Ahmad, tace zata mun baki in na ƙi sakinta. Wannan jarabawar da nauyi take." Zaunar dani Ahmad yayi a kujera yace. "Bulama ka kasance mai dauriya. Ka nutsu kai mun bayanin menene yake faruwa. In yaso sai mu je mu samu Mama mu yi mata bayani. Ni da ita zamu je mu samu Hajja mu yi mata magana" Cikin haki na bashi labarin duk abubbuwan da suka faru, na ɗaura da cewa. Yanzu haka shi kanshi Ba Modu yace zai yanke hukuncin da zai ma kowa daɗi. Bansan wanne irin hukunci bane. Kuka Ba Modu da Ya Innana suke yi suka fita. Ahmad bansan inda zasu je ba. Ita kanta Mama Gana tayi kuka yau sosai. Ba Bature ne yake son wargaza mana kan gidanmu, sabida dukiyar da Ba Bakura ya rasu ya bar mana muka gada." "Ya'isa haka Bulama, na fahimci abubbuwa sun kwaɓe ba lallai a halin yanzu lallami ko aike yayi tasiri ba. Duk da haka ba zamu zauna ba. Ga shawara me zai hana a halin yanzu tunda a cikin fishi da dokin naƙi take, ga takaba tana yi, ga abubbuwa da suka faffaru a baya. Ka saki Yahanasu saki ɗaya, in yaso daga baya ka mayar da matarka ta dawo maka. Nasan zaka ji nauyin abun. Ina guje maka fishin mahaifiya, ga baki da tace zata yi maka. Yanda Ba Bature ya jagwalgwala al'amurannan zaiyi wuya mu samu abunda muke so..." A'a Ahmad mu nemi wata mafitar rabuwa da Yahanasu gangancine Babba." Ahmad cikin fishi yace. "Kamar yadda bijire umarnin Hajja yake da haɗari babba ba. Bulama duk wannan nasan bazai wuce sanadiyyar mutuwar Ba Bakura da Hajja take tunanin halin shaye_shaye da Yahanasu ta shiga shi yai silar mutuwar mijinta. Ai mata uziri ba lallai ta fahimci komai yanzu ba, iyaye ka sani a kullum duk abunda kaga sunyi ba suna yi dan son zuchiyarsu bane, sanmu ne yake sawa su yi wannan abun. Ka saketa kawai ta samu kwanciyar hankali in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Bani wayarka bari in kira Ba Modu mu tattauna ban fito da tawa wayar ba." Wayata na miƙa mishi ya dailing number Ba Modu. Ringing biyu ya ɗauki wayar, bayan sun gaisa da Ahmad sai Ahmad yai mishi bayanin halin duk da ake ciki. Murmushinshi yayi yace. "Ka bani Bulama Babban in yi mishi magana" Ahmad ya miƙo mun wayar dukkan illahirin bakina rawa yake yi, ina ji Ba Modu yana kiran sunana amman na kasa amsawa. "Bulama Babba iyaye girma ne dasu. Ni bazan so kaina in hana ka bin umarnin mahaifiyarka ba. Tunda har tayi wannan furucin to ya fa zama dole ka saki Yahanasu domun ɗorewar farin cikinta, da dorewar zumunci. Ni kaina matakin da nake faɗa ma Hajja zan ɗauka kenan a kan aurenku. Akwai abubbuwa masu tarin yawa da Hajja Gana ta riƙe ya zame mata hujjar raba ka da Yahanasu. Kabi umarnin mu ka saki Yahanasu nima na baka wannan umarnin kar ka kuskura ka kuskure a bisa umarninnan dana baka. Kar ka bari akan mata ka dinga saɓawa da iyayenka. Bawa da kake gani baya wuce ƙaddararshi, ƙila dama Allah ya haɗa aurenka da Yahanasu ne na tsawon wani lokaci ba mai yawa ba. In kuma akwai rabon ku sake gudanar da rayuwa a gaba sai kaga daga baya an sasanta. BaKura ya barmun wasiyya masu nauyi a kan zumunci. Kuma yace ko bayan ranshi kar a raba aurenka da na Yahanasu kamar yana duba yasan wannan rikicin zai afku bayan ƙasa ta rufe idanunshi. Amman mahaifiyarka a yanzu zata iya maka baki rayuwarka taƙi yin albarka. Bakura shi kuma baice bai yafe maka in ka rabu da Yahanasu ba. Ka rubuto takaddar saki a rubuce gobe ka kamo hanya ka kawo mata takaddar irin umarnin data baka. Mu muna hanyar Zuwa ɗakko Yahanasu ne zamu dawo da'ita gida mu ci gaba da bata dukkan kulawa." Ƙit ya datse wayarshi. Kaina yaci gaba da jujjuyawa ina jin kamar numfashina na fusga. Haki nake yi tamkar mace mai ɗauke da juna. Bansan hawaye na zuba daga guraben idanuna ba sam. Ciwon da kaina yake yi baya musaltuwa. Allah shine shaidata akan kuɗirin ba Yahanasu farin ciki da nayi a rayuwata. Allah nake roƙo ya kawo mun mafitar dukkan abunda zai zama shine mafi alkairi a gare mu baki ɗaya. Alwala na ɗauro na dawo na ɗauki Qur'ani na soma karantawa. Ahmad yana zaune jikinshi a matuƙar mace sosai. Ni kuwa a hankali na soma dawowa dai_ dai. Kiran sallar magriba ne yasa na dakatar da karatun na ɗaga hannu na dinga ragargazo adda'a kafin kuma na miƙe naje na ɗauro alwala na samu Ahmad a zaune. Mu je masallaci Ahmad." Idanu ya zuba mun yana karantar yanayina. Murmushi nayi mishi nace Kar ka damu Ahmad khairan in sha Allah" Fita mu ka yi tare, ina ganin kiran wayar ƴan ɗakinmu. Su Gunsum ne, amman ban samu zarafin ɗaga wayoyinsu ba." Yahanasu: Ina zaune a ɗakinmu muna taɓa hira, kewar gida da kewar mijina kwana biyunnan duk ta isheni. Malama Fahiƙa ce ta shigo da sallama. Muna ganinta muka shiga cuccurewa a waje guda, kowa na kakkare jikinshi, jikkunanmu duk a farfashe sabida tsabaragen duka. Wata tsawa ta daka mana duk muka nutsu. "Ku rufa ma mutane baki. Wani ne yasa ku shan abunda zai gusar muku da hankali har a kawo ku nan? Ƴan cin uwa. Ke Yahanasu ki shirya ki mayar da kayanki na gida suna durowa, iyayenki suna cikin gidan malam Rilwanu sun zo tafiya dake" bansan sanda nayi sujudur shukur ba, tsabar farin cikin dana tsinci kaina a ciki. Ina dingishi na miƙe zuwa bakin lokar ɗakin, na buɗe lokar na ciro rigata na nufi ban ɗakin ɗakin namu na mayar da rigar tawa, sururu nayi a cikin rigar tamkar rigar aro. A hanzarce na fito bakina yaƙi rufuwa. Muna kuka nayi sallama da su maman Amira, akan in Allah ya yarda zan kawo musu ziyara har garuwawansu tunda muna da adireshin juna. Kuma wa'adin zaman gidan nasu ya kusan zuwa ƙarshe. Cikin ɗakinmu babu wacce hankalinta bai dawo dai_dai ba. Malama Fahiƙa ta tusani a gaba zuwa gidan malam Rilwanu. Ina tafe ina ɗingisa ƙafata, ciwo ne babba a cinyata wanda malama Fahiƙa ta ji mun shi sati guda kenan. Muna shiga cikin gidan na tarad da Ya Innana a tsakar gidan tana gabatar da alwala. A guje na isa gabanta ina zubar da hawaye. Ƙirjinta ta dafe tana kallona. "Hukunci sai mai tsaga ido. Yahanasu kece kika zama haka? Innalillahiwainnailaihilrajiun." Durƙushewa nayi a gabanta ina kuka. Tasa hannu ta ɗagoni. Tana share mun hawayena. "Dena kuka Yahanasu ya isa haka" hannuna ta ja muka shiga ɗakin da aka saukesu. Matan gidan ƙila sun saba da ganin irin wannan lamarinne dan naga su ko a jikinsu. Zaunar dani Ya Innana tayi tace. "Bari in yi Sallah kafin su Babanku su fito masallaci zasu wuce cikin Katsina ne a can zamu kwana washe gari kuma mu ɗau hanya." Ina zaune ina kuka har ta idar da sallar. "Ki fita ki yo alwala ki zo kiyi sallar kema" Miƙewa nayi ba musu na fice ina dingishi. Ban jima ba na shigo ɗakin da sallama. Lafayarta ta warware ta keta ta gida biyu. Ta miƙo mun rabin tace. "Yafa kiyi Sallah" Yafawa nayi ina sallah ina kuka a haka na idar. Ina sallamewa matar malam Rilwanu ta yo sallama a dokin ƙofa. "Hajiya me gidan yana jiranku a waje, wai ku fito ku tafi. Nace ma ku dakata kuci tuwon gero, amman yace sauri kuke yi. Ya Innana tace. "Wallahi mun gode Allah ya saka da Alkhairi." Miƙewa mu ka yi, muna tafe matan malam Rilwanu suna yi mana Allah ya tsare hanya, har muka fice. Mota muka shiga, Ba Modu dake gaban mota ya juyo muka haɗa idanu. Sai hawaye shar_shar ya gangaro a idanuna. Shima shiru yayi yana Kallona, hankalinshi a mugun tashe ainun. "Uwata kece kika zama haka? Allahu Akbar" Shiru yayi ya ƙura mun idanunshi, ni kuma sai kuka nake yi. Wakil yace. "Ki dena kukan kar ki jangwaloma kanki wani ciwon mana" Ba Modu yace. "Wakil tuka muje gidan Alh Shitu can anguwar alƙali maza. Na kirashi ma suna tsumayar zuwan namu." Jingina nayi a kujerar motar, ina jin wani tsantsar farin ciki. Tafiya mai tsayi muka yi kafin na ganmu a wellcome to katsina anguwar Ɗanɗagoro. Tiryan_tiryan sai ga mu a anguwar alƙali mun iso gidan Alh Shitu abokin Ba Modu da su ka yi jami'a tare. A harabar gidan muka samu iyalan gidan suna jiran isowarmu. Wakil ya parka mota a wajan ajjiye motoci. Ya Innana tace. "Ki sakko a hankali naga kina ɗingishi, ciwo kika ji ne?" Kai na girgiza mata halamar a'a ba ciwo bane. "Hmmmm" kawai tace dani. Na fito a motar a hankali. Su Ba Modu har sun isa wajan su Alh Shitu. Can muka samesu "Hajiya Innana zumunci ya yanke, saduwa tayi wuya" Wata farar mace ce ke magana da fara'arta har tana ɗan rungumar Ya Innana. "Ke dai Hajiya Kati ki bari kawai. Hidindimu sunyi yawa, girma na ta hawa kanmu. Alh Shitu barka da dare" Cikin fara a ya amsa ma Ya Innana. Nima da ladabi na bisu na gaishesu, kafin daga bisani muka shiga zuwa babban falon gidan. Nan muka zazzauna su Ba Modu suka ɓalle da hirar yaushe gamo. "Muje masallaci Modu, Wakil taso muje" Cewar Alh Shitu kenan. Masallaci suka nufa. Mu kuma Hajiya Kati ta shige damu haɗaɗɗen uwar ɗakinta. "Hajiya Innana ga ɗaki ga ɓan ɗaki kuyi sallah kafin su dawo sai muci abinci. Har zata fita Ya Innana tace. "Dan Allah Hajiya Kati Kaya nake so ki bani Yahanasu zata yi wanka sai ta sake na jikinta." Sai lokacin Hajiya Kati tace. "Amman yarinyar nan jinya tayi ko? Ni naga duk ta zabge, ba ita bace wannan ƴar lukutar ba?" "Itace fa. Jinya tayi na sama da wata biyar. Yanzu haka daga gidan magani muka ɗakkota, shi yasa nake son ta gasa jikinta ko zata ji daɗin jikin." Kai ta girgiza ma Ya Innana tace. "Hmm Allah ya bata lafiya. Ta shiga tayo wankan bari in kawo mata kayan ummina zai yi mata, ummi na haka take ba auki" Tana faɗar haka ta wuce. Ya Innana tace. "Bari in yo alwala sai ki shiga ki gargasa jikin naki ko?" To" Shine abunda nace mata. Ina tsaye har Ya Innana ta fito. Ban ɗakin na shiga na soma taran ruwan zafi a bokiti. Wanka nayi da sabulun ruwa mai ƙamshi, jikina duk ciwuka wani wajan ma bana iya wankewa, dan ciwon yayi ɓawo ɓawo. Shampoo na zuba a kaina na wanke tas, kitson kaina bai wani sha jiki ba. Dan ana mana kitso duk bayan wata. Alwala na ɗauro na fito ɗaure da mayafin lafayar Ya Innana. Iska da ni'ima na shigata ta ko wanne gaɓa. Hamdala nayi a zuchiyata. Ina jina tamkar baiwar da iyayen gijinta suka ƴantata, baka sanin kana cikin ni'ima sai ni'imar da kake ciki ta kufce ma a hannunka. Ko maƙiyina bana mishi fatan ya faɗa ƙangin shaye_shaye. Hajja Fati da Binta ƙawata ne suka faɗo mun a zuchiya, harma da gidan magajiya mai kodin. MRS BUKHARI CE [19/08, 9:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 54 Numfashi na ja, na koma bayan gida na saka kayan, rigar ta ɗanyi mun yawa kaɗan, zani ne da riga, zanin na ɗaura na fito ina ɗaurin ɗan kwalin nawa. "Zo maza kiyi sallah Yahanasuna" murmushin jin daɗi ne ya subuce mun, na saka hijabin da Hajiya Kati ta ajjiye saman kayan, da ganin mahaɗin atamfar ne. Sallah na tayar. Har na idar Ya Innana sai adda'a take ragargazowa. Ni kuma ina gefe ina jan carbi. Da aka yi kiran sallar isha, muka tashi muka gabatar da sallar isha. Hajiya Kati ce taa leƙo. "Hajiya Innana bismilla kuzo mu ci abinci, Alh Modu sun shigo. Ya Innana na gaba ina biye da'ita a baya har zuwa falon gidan. Akan daining muka tarar dasu. Nan aka shiga sake sabuwar gaisuwa. Cikin ladabi na gaishe da wasu maza wanda da gani babu tambaya ƴan biyu ne. Dan tsananin kamar da su kai da juna. Abinci muka shiga ɗiba, kowa na ɗibar wanda zai ishi tumbinshi. Dashishi ne da miyar ganye. Dashishi abincin katsinawa ne, wanda akeyi da ɓarjajjiyar alkama, anacinshi da miyar taushe, ko mai kabewa ko mai gyaɗa. "Alh Modu Yahanasu ciwo tayi sosai ko? Ko ba ita bace wannan ƴar lukutar dana sani ba?" Cewar Alh Shitu. Ba Modu yace. "Itace ka ganta. Jinya tayi ta tsawon sama da wata shida ma. Kaga duk ta zuge ko? Ciwo babu daɗi" Kafin Alh Shitu ya tambayeshi ciwon me nayi yayi saurin kawar da zancan ta hanyar tambayarshi. "Niko Alh Shitu ina Ɗan Filato yake ne, yana katsinannan taku kuwa?" Dariya yayi yace. "Ina yana Dubai shi da iyalan nashi dukka. Yana aiki a ƙarƙashin wani kamfanin sutura. In ga ganshi a katsina sai dai ziyara. Kwanakin baya dai da mu kai waya yake mun magana akan yana son su zo shi da iyalan. Kuma kafin su koma yana son yayi ƙarin aure, ya gaji da zaman Dubai ɗin. Kasan katsinawa da son mata hudu. Nima shashatau Hajiya Kati tayi mun fa" Dariya suka kwashe dashi. Mu kuwa kowa ya mayar da hankali ne akan cin abincinshi. Bayan mun kammala kuma, aka raka mu ɗakunan da zamu yi bacci. Ni ɗakin da aka kaini ba kowa a ciki, da halama ni kaɗai zan kwana. Ina kwance ina cikin murna da zabarin ganin gobe. Babu wanda idanuna ke son yin tozali dashi sama da Bulamana. Naso in tambayi Ya Innana dalilin rashin biyosu da bai yi ba. Amman ina jin kunya da tsoron kar suga nayi rashin kawaici. Murmushi nayi tare da lumshe idanuna ina tuno gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shaye. Gidan ukuba da azaba. Bazance ire iren gidajen basu da amfani ba. Domun na samu lafiya ta dalilin gidan. Da dama an kawosu cikin hauka tuburan, kuma sun samu lafiya. Saƙona ga irin wannan gidajen shine. Su ji tsoron Allah, su sani mu ma ƴaƴane, kuma babu wanda yafi ƙarfin faɗawa irin halin da muka riske kawunanmu a baya. Kuma su sa tausayi cikin lamuransu. Daga ƙarshe ina godiya a garesu bisa kulawa da lafiyar ƙwaƙwalwata da su ka yi. Ta hanyar bani rubutu, da ƙwayoyin bature, da koyar damu sana'a domun dogaro da kai. Da tunanuka masu dama bacci yayi awon gaba dani. WASHE GARI: sassafe muka kamo hanyar Damaturu, dan ko karyawa bamu tsaya mun yi ba, sai dai Hajiya Kati tasa masu aiki su kai mana abincin karin mota, tace ko a hanya maci. A cikin motar ma bacci na dinga yi sosai, domun ba samu lafiyayyen bacci mu ke yi ba sam. Misalin ƙarfe biyun rana muka shiga Damaturu. Kai tsaye babban asibiti Ba Modu yasa muka wuce. Ni dai har muka shiga ɗakin ganin likita gabana bai bar faɗuwa ba. Wajan Likitan ƙwaƙwalwa Ba Modu ya kawo ni domun a duba lafiyar ƙwaƙwalwata. Alhamdulillah kyakykyawan labarin sa farin ciki. Shine lafiyar ƙwaƙwalwata ras, sai dai zazzaɓi cizon sauro, da tiyfot da nake fama dashi, sai kuma raunuka da suka samu a jikina. Ya rubuta magunguna, Ba Modu yai mishi godiya muka fito, nan muka nufi gida." Bulama Babba: Bamu muka shigo gidan ba, sai da mu ka yi sallar isha tukunna. Sukuku haka nake tafiya kamar zakaran daya taka wuƙa. Ahmad kuwa ya kasa tafiya ɓarayinshi. Abinci ya tusa ni a gaba, sai da ya tilasta ni, na ɗan tsakura na sha ruwa. Gunsum ne ya kira wayata, naga kirare_kirayen ƴan Damaturu da yawa, naƙi fur in ɗaga wayar kowa. Ahmad ne ya ɗaga wayar Gunsum. "Gunsum yaya akayi, kana lafiya?" "Yaya Ahmad lafiya lau, tun ɗazu inata kiran wayar Bulama Babba baya ɗauka, na gwada taka kuma a kashe take." "E hakane wayata tana kashe tun safe ma. Yaya akayine?" Gunsum yace da Ahmad. "Hajja ce ba lafiya, muna shirye_shiryen kaita asibiti ne ma yanzu haka. Muna ta kiran wayar Ba Modu bata shiga wayar, Wakil ma wayarshi tana gida bai tafi da'ita ba. Kuma Hajja sai ambaton sunan Bulama Babba take yi. Wai ya kawo mata takadda, mu bamu san wacce takadda bace, shine nace bari in kira in sanar mishi." Duk tattaunawarnan ina ji dan Ahmad ya ƙara ƙarfin jin magana. Numfashi naja kafin nace. Gunsum ka kwantar mata da hankali, zan kawo mata takaddar, in jikin ba mugun tsanani yayi ba ku jira zuwan Ba Modu tukunna. Ya je Katsina ne. Da sassafe zan tawo, duk abinda ake ciki ka tabbatar kana sanar mun." Wayar Ahmad ya katse. Ni dashi an rasa me cewa komai, muna zaune har sha ɗayan dare. Da ƙyar na roƙi Ahmad ya tafi wajan iyalinshi. Kan sallaya na hau na dinga karatun Qur'ani babu ƙaƙƙautawa shine kaɗai ke saukar da sanyi da salama a ƙirjina. Misalin biyun dare kuma na shiga raya daren da nafilfili, ina roƙon Allah ya kawo mun ɗauki. Sai wajan huɗun asuba na samu na runtsa. Ana assalatu na miƙe. Wanka nayi na goge bakina, na ɗauro alwala. Na nufi masallaci. Ban fito a masallaci ba sai da rana ta fito, nayi nafila ra'aka biyu, nayi azkhar. Sannan muka fito ni da Ahmad. "Yaya jikin Hajja?" Jikin da sauƙi dama ciwon na ƙiyaryar Yahanasu ne, kuma na ba Gunsum saƙon zan kawo takaddar yau in sha Allah. To tunda ya faɗa mata jikin nata yayi sauƙi,munyi waya da Gunsum cikin dare sau biyu. Babu wata matsala. Yanzu inason in kama hanyar Damaturu, kafin nan zan je wajan Mama Gana mu tattauna tukunna." Ahmad jikinshi ya mace mus. "Hmmm Allah yasa mu dace, Allah yasa rabuwar itace mafi alheri a gareku baki ɗaya. Allah ya hadaku da madadin alkhairi. Nima wanka zanyi in zan wuce office sai in kai yaran makaranta. Su basu san a gidan ka kwana ba ma" Da haka mu kai sallama da Ahmad kan cewar sai na dawo, kowa ya nufi ɓarayinshi. Takadda da biro na ɗauka, gabana sai dokawa yake yi da ƙarfi, rubutu nayi da bai wuce layi uku ba, na nannaɗe takaddar nasa a ajjihun rigata. Na kulle ko ina, na shiga mota na fice a gidan. Gidan Mama Gana dana so zuwa ma, fasawa nayi, hanyar Damaturu kawai na nufa abuna. Tafiya kawai nake sukuku kamar bazan kai ba. Tunani da tausayin halin da Yahanasu zata tsinci kanta a gaba yafi koma azalzalar zuchiyata. Ina gudun kar in jefa kaina a rijiya gaba dubu, da badan haka ba babu wanda ya isa ya sa in saki matata, na sani komai zai iya faruwa dani in har na rasa Yahanasu, domun ta gina zuchiyata ta ƙarfafa jijiyoyin jinina da soyayya zalla mara algus..... Ƙiiiiiii naji wani abu ya tokare ni, a dai_ dai wani ɗan gauye dake gefen titi, da dukkan halama kasuwar ƙauyen yau take ci. A guje na fito na kukkutsa tsakiyar mutanen da suka rufe abunda na bige. Wani dattijone a kwance ƙafarshi na fitar da jini. Kaina na dafe inaji tamkar zuchiyata zata faɗo. Subhanallaah sannu Baba. Dan Allah kayi haƙuri Baba tsautsayine" Nan fa jama'ar da suka zo kasuwar ƙauyaa nan suka nemi su dake ni, sabida tsabaragen rashin hakuri, gidadanci, da rashin ilmi. Sai wannan tsohonne yace. "Ku dakata kar wanda ya doke shi." Shine fa Allah ya kwace ni. "Naci sa'a ma daya bige ni ya tsaya. Da wani marar imanin aka samu, sai dai ya ari na kare ai. Yaro kaini kemis a wanke mun, su ɗan bani magani, domun bani da ko sisi da cewa zanyi kayi tafiyarka." Jikina a mace nace. To Baba zaka iya tashi ko in ɗaukeka? Ku kuma wani yai mun jagora zuwa kemis ɗin da za'a duba shi" Baba tsoho yace bazai iya tashi ba, dan yaji rauni sosai. Wasu samari biyu ne suka taimaka mun muka sa Baba a mota. Suma suka shiga dan su nuna mun kemis ɗin, yana can cikin ƙauyan ne. A nan na ɓata lokaci sosai, bani na baro wannan ƙauyen ba sai wajajen sha biyu da arba'in na rana. Sai da na kai Baba har gidanshi, kuma a ƙauyen gaba yake kuma can ciki, kasuwa ce yaje ci a ƙauyen dana bigeshi. Nera dubu goma na danƙa mishi, yai ta bina da adda'a har sai da na ɓace ma ganinshi. Misalin ƙarfe biyun rana na shiga cikin layin mu. Ina shan kwana na hango motar Ba Modu a gabana. Suna tafe, gabana ne ya sake tsananta bugawa, ina jin nauyi da kunyar ganin Yahanasu da shi kanshi Ba Modu ɗin, uwa uba Ya Innana. Motarsu na shiga cikin garejin tawa na biye a bayansu. Jim nayi a cikin motata, har sai da naga fitowar Ba Modu da Ya Innana, ban gushe ba sai ga Wakil da Yahanasuna suma sun fito. Sai murmushi take tana kallona. Babu guiwa na fito daga mota, ƙurama juna idanu mu ka yi na wasu lokuta. Kifiyoyin so sai sossoke mun zuchiya take yi. Idanu na lumshe tare da ɗaga hannuna sama. Allah na gode maka daka bama Yahanasu lafiya, ubangiji ka kareta daga faɗawa wata fitna, ka kare ƴan baya." Da Ameen dukka suka amsa. Da murmushi na ƙarasa garesu, Yahanasu ta kalleni tana murmushi, nima murmushin nake mayar mata, tayi muguwar rama bata wasa ba, Yahanasu abar a tausayama ce. "Bulama sai yanzu kake tafe, me yasa baka zo tun wuri ba" Cewar Ba Modu daya katse mana hanzari ni da Yahanasu wacce ta cike ni da kallon soyayyar nuna yabawa. Kai na sosa nace. Wallahi na ɗan samu hatsari a hanya ne na bige wani dattijo. To hidimar kaishi kemis ne ya tsayar dani. Amman ba wani rauni bane yaji mai yawa ba. Ya Innana barkan ku da dawowa" Wakil ya matso yana tambayata. "Amman Bulama Babba baka ji ciwo ba kai ko?" Murmushi nayi na dafa kafaɗarshi kawai. Ba Modu yace. "Allah ya taƙaita ka dinga kula sosai Bulama, rayuwa ita ba lalle bane farin ciki ya ɗore ba. Dole yau aji sanyi gobe kuma a busa zafi. Muje ciki mun kwaso hanya." Gaba su Wakil su ka yi da Ya Innana, Ba Modu ya mara musu baya, Yahanasu na shirin bin bayan Ba Modu, na jawota ta dawo da baya. Idanu na zuba mata, ina jin sonta da tausayinta na nunkuwa a cikin zuchiyata. A jikina na mannata dukkanmu muka sauke ajjiyar zuchiya. Mun jima a haka, har sai da muka soma jiyo kororoton ƴan cikin gida, masu murnar dawowarta, ala dole na zareta daga jikina ina kallonta. Har gaban abada bazan mance alkhairinki ba, kuma bazan dena sonki ba, da sonki zanta rayuwa" Gunsum ne ya shigo cikin garejin motar yana kiran sunan Yahanasu. Dole muka fito zuwa cikin gidan. Yanyame Yahanasu mata su kai a tsakar gidan, su Dala sai washe baki suke yi. Ya gaji ta kamo hannunta tana. "Ya'isa ku barta ta huta tukunna, sannu Yahanasu an sha jinya" Ni kuma bin bayan Ba Modu nayi da naga ya nufi hanyar turakarshi. "Bulama Babba, maza jeka ka cika umarnin mahaifiyarka, in ka dawo mayi magana ka same ni a ɗaki. Ka zama mai juriya da dangana Bulama Babba, ka zama mai gaggawar bin umarnin iyayenka kaji ko?" Je ka maza Allah yayi ma albarka A sanyaye na juya na nufi hanyar falonmu." Ba Modu: Bayan Bulama Babba ya bi da kallo, ya na ji da yana da iko da ya hana afkuwar wannan saki. Tuno ɗan uwanshi gudan jininshi yayi. Hawaye suka gangaro daga idanuwanshi i zuwa kuncinshi. Yana jin kamar ya dawo da agogo baya, amman ina abunda ya riga ya wuce ya wuce kenan" Turakarshi ya buɗe ya shiga. Amman ya kasa zama tamkar wanda ya haɗiyi taɓarya. Yanzu shikenan Auren Yahanasu mutuwa zaiyi? Ita kanta ya zata ji wannan lamarin, da wacce siga za'a sanar mata da wannan mummunan labarin? Zama yayi a kan gado, ya zare malum malum dinshi, tare da cire kularshi zanna. Kai ya dafe yana tuno fuskar Bulama Babba a lokacin yana da shekaru goma a duniya. Da irin tsantsar so da kulawar daya dinga bashi, har Ba Bakura yana ganin kamar son yayi yawa kar yaje ya sangarce. Da kuɗinshi Bulama Babba yayi karatu, a ƙarƙashin kulawarshi Bulama Babba ya girma. Dan wajen Ba Modu kaɗai Bulama Babba ya ke kai buƙatarshi. Kowa a cikin family ya shaida soyayya da shaƙuwar dake tsakanin Bulama Babba da Ba Ba Modu. Shi kanshi Ba Bakura ya yarda Bulama Babba ya fi son Ba Modu fiye dashi mahaifinshi" lumshe idanuna Ba Modu yayi wasu hawaye zafafa suka zubo mishi. Take kanshi ya ɗauki ciwo, zazzaɓi ya lulluɓeshi sosai. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CEGAWURTATTU UKU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 55 BULAMA BABBA: Jikina na ɓari na shiga falon, bakina da sallama. Tana zaune a kan kujera, Gunsum da Aissa suna ƙasa a gabanta. Aissa hawaye naga tana zubarwa, Gunsum kuwa jikinshi duk yayi sanyi. Waje na samu a gefe na zauna. A sanyaye na gaisheta, bata amsa gaisuwar tawa ba. Gunsum da Aissa ne suka shiga rige_rigen gaisheni. A sanyaye na amsa. Ya jikin naki Hajja " na faɗa a hankali. Cikin dakiya tace. "Ciwo ai kaine sale_salin tayar mun dashi. Amman tun a jiyan da saƙonka ya iso gareni na samu lafiya. Kazo mun da takaddar sakin a rubuce?" Numfashi naja nace. Na rubuta amman kafinnan Hajja ki rufa mun asiri ki barni in rayu da Yahanasu, yarinyarnan ba ta yi komai ba, kuma ta samu lafiya gata can an dawo da'ita ma. Ina gudun lalacewar zumuncinmu ta dalilin wannan sakin. Nayi imani da Ba Bakura yana da rai wannan maganar ma ba zata taso ba. Ki mun rai" Hawayen dake shirin zubo mun nayi kokawar mayar dashi. "Ka gama, nace ka gama dai ko? Kaga ƙannenka sunfi awa ɗaya suna mun magiya. Babu wani sauyi da zaku samu. Miƙon takaddar in gani " Hannu nasa a aljihu na ciro takaddar na miƙa mata. Hannu tasa ta karɓa. Murmushi naga tana yi. "Allah yayi maka albarka bisa umarnina da ka bi. Ungo ka kai mata takaddarta maza, sannan ka dawo zamu yi maganar kuɗi dangane da batun aurenka da Yalewa". "To Hajja" Abunda bakina iya furtawa kenan. Fita nayi a ɗakin ina gauraye hanya. Dala yana hangoni ya iso inda nake. Dala kira mun Yaha kace ta same ni a ɗakin ka na da, ka bani key ɗin ɗakin" Dala yace. "Bari in ɗakko key ɗin tukunna." Har zai wuce nace. Dala in ka buɗe ka kirata kace ta jirani, zanje in ga Ba Modu" Ina faɗar haka na wuce, mota na koma na ɗebo takaddu na wuce ɗakin Ba Modu. Sallama nayi yai mun izinin shigowa. Da ganin fuskarshi kasan yana cikin damuwa. A gabanshi na zube ina kuka kamar mace. Duk na gigice kunya nake ji sosai. Takaddar hannuna Ba Modu ya zare ya ajjiye a gefe. "Bulama kuka ba naka bane. Duk inda aka samu biyayya akwai nasara. Yahanasu kayi mata fatan alkhairi ina ganin zaifi. Kaima ina maka fatan alkhairi, Allah ya haɗaka da mata ta gari. Ka share hawayenka" Hawayena na shiga sharewa, da ƙyar na auro jarumta na yafa. Ga takaddun ɗaya daga cikin gidajen dana gada Ba Modu na mallaka ma Yahanasu duniya da lahira. Kuma zan tara ƴan uwa su zama shaida. Wannan key ɗin motar ma gashi. Motar tatace dama da sunanta na siya, a baya motar dana karɓa a hannunta tafi wannan ma tsada. Sannan na tura maka da million ɗaya kuɗin gidanta ne da take gina mana kafin lalurar data sameta ta same ta. Ba Modu ka yafe mun, ka taya ni ba Yahanasu haƙuri." "A'a Bulama Babba shi gidan da motar na meye kuma haka? A'a ka ɗebe kayanka, babu buƙatar hakan, kana buƙatar gidan da motar dukka, Yahanasu maccece gidan wani zata je." A'a Ba Modu, ko ubangiji yace in zamu yi sakin mu kyautata sakin. Haka kurum ma ana sakin mace a haɗo ta da mota ko check. Wannan na bata duniya da lahira" Sai da Ba Modu yayi jim ya ƙura mun ido kafin yace. "Allah ya saka da Alkhairi. Yahanasun tasan me ke faruwa kuwa?" Da sauri na girgiza mishi kaina halamar a'a" "Kar ta ji a bakin ka. Zan sa a kira mun ita, dole da sigar lallashi da hikma za'a yi mata bayani. Kana da damar da zaku zanta a tsakaninku. Tashi kaje Allah ya baku haƙurin rashin juna. Allah bai ƙaddari Yahanasu zata haifa maka ɗa ko ƴa ba, sakamakon muyagun ƙwayoyin da tai ta ta'amali dashi." Bance komai ba na fita. Sai haɗe hanya nake yi, da ƙyar na isa ɗakin Dala. Yahanasu tana zaune a bakin katifa na shigo. A jikin bango na jingina ina daga tsaye nake ƙare mata kallo, ina jin wutar sonta da kewarta na ruruwa a zuchiyata. Tasowa tayi tana shirin shigewa jikina. Idanu na runtse da naji ta rungume ni ƙam, sai nunfarfashi nake fitarwa. Sake ni muyi magana " Jin kaurin muryata ne yasa ta ɗago kanta a firgice. Idanu da muka haɗa ne ta fahimci ina cikin matsala. Hannuna ta jawo ta zaunar dani a gefen katifa, ita kuma ta zauna a ƙasa. "Haba Bulamana, menene yayi zafi haka wanda har ya sa idaniyarka zubar hawaye, kaddai a bisa laifin shaye_shayen da nayi a baya ne, ko a bisa cikin jikina da yai ta zubewa ne? To in ma a kanshi ne, da izinin Allah an sha ni kuma na warke. Yanzu nake shirin zuwa ɗakin Hajja, ita da Ba Bakura ne kaɗai ban gani ba." Idanu na lumshe kawai bance komai ba. "Meke faruwa ka sanar dani dan Allah" Babu damuwa Yahanasu. Ki koma ciki ki huta, dan kina buƙatar hutu sosai. Zanje in samu Hajja tana jirana." "Wanne hutu, ai in hutun akeso in yi, sai a kaini ɗakin mijina kai tsaye ai dan nayi kewarka sosai, kuma kaima nasan kafi son mu kasance a tare. Ɗazu na ganka a mota kuma ba motar gida bace ta wanene?" Miƙewa nayi da kuzari nace. Zan je in dawo zan neme ki kinji, ki kula da kan ki Yahanasu ƴar lukutar Bulama" murmushi mu ka yi dukka, jikinta dai a sanyaye ta fice. Ni ma na nufi ɓarayin Hajja. A falon na tarar da Ba Bature suna tattaunawa da Hajja. "Gashi nan ma ya shigo" Cewar Ba Bature. Gaisheshi nayi, ya amsa cikin fara'a. Waje na samu na zauna. Hajja ta shiga mun lissafin maƙudan kuɗin da bikin zai lashe. A sanyaye nace. Zan turo da kuɗin in sha Allah. Sannan inaso ku shaida, na mallaka ma Yahanasu ɗaya daga cikin gidajen dana gada, sai motar da nake ja na mallaka mata a madadin motar ta da Ba Bakura ya siya mata, wacce na kwace a baya, suturu dana loda a wadrope da sunanta na siya, zan turo mata dasu suma Domun Allah subuhanahu wata ala shi ya faɗa cewar in zamu yi saki mu kyautata" Hajja kamar zata ari baki dan masifa, dukanane kawai ba ta yi, amman har tana kukan wai Ba Modu ya cuceta. Ni dai sallama nayi musu na bar garin ma baki ɗaya" YAHANASU: Ina fitowa kaina ya shiga sara mun. Da ganin Bulama Babba nasan akwai gagarumar matsala sosai. Da Ya Innana naci karo, hannuna ta ja mu ka shiga turakar Ba Modu. Rabona da shiga wannan ɗaki tun ina yarinya ƙarama. Zaunar dani tayi a ƙasa a kusa da ƙafarshi. Tana ajjiyeni ta fice ta barmu. "Wanne irin darasi kika koyo a duniyar masu taɓin ƙwaƙwalwa?" Kalmar ɗaya soma jifana dashi kenan. Jikina na rawa, muryata na sarƙewa nace. "Na koyo darrusa masu tarin yawa. Hakan ya ƙaramin tsoron Allah, da kuma tsoron duniya, ya koyar dani ilimin rayuwa wanda ba'a aji ake koyo ba. Nayi nadama, na sake gode ma Allah a bisa ni'imar lafiyayyar kwakwale daya bamu har muke tunani. Haƙiƙa na tabka kuskure mai girma, kuma nayi nadamar dukkan abubda na aikata, na ɗaukeshi a matsayin ƙaddarar da bawa bai isa ya shure ba." Ƙur Ba Modu ya zuba mun idanunshi. Ni ko ɗari _ ɗari nake yi dashi. Domun nasan sai ya hukunta ni, a bisa ɓata mishi suna da nayi" "Toh zan ɗaura miki sa nasiha" Nan ya shiga yi mun nasihu da kalamai masu sanyi. Yafi awa biyu yana nuna mun yadda rayuwa take da yanda ake kore damuwar duniya. Nayi kuka sosai. A cikin wannan nasihar tashi ne ya sanar dani rasuwar Ba Bakura. Nayi kuka sosai, dan Ba Bakura jigo ne. Ba Modu ya sanar dani aurenshi da su Ya gaji, da abubbuwa da suka faru ban sani ba. Bayan ya samo nutsuwata ta hanyar karanto mun wasu hadisai sai yace. "Shi aure, rai ne dashi kuma ina so ki rungumi dukkan jarabawar da Allah zai jarabceki dashi. Ki sani gwajin imanine, kuma hakan nasara ne ga duk wanda ya cinye, ubangiji yana kallo. Yahanasu na yarda na gamsu Bulama Babba yana tsantsar sonki. Kamar yadda ƙaddara ta ƙadarto miki shaye_shaye da taɓin ƙwaƙwalwa, kuma haka ƙaddara ta ƙadartoma Aminiyarki Hajja fati ajalinta a sakamakon ta'amali da miyagun ƙwayoyi. Haka ƙaddara ta ƙara ƙadarto miki mutuwar aurenku da Bulama Babba. Ki sani wannan baya nufin ƙarshen rayuwarki ne, ki ɗauka yanzu zaki soma rayuwa, kuma kice Allah yasa hakan shine alkhairin, ki rungumi ƙaddara kinji ko uwata? Dole akaima Bulama tare da barazanar tsinuwa kar ki kama shi da laifin komai" Jikina babu ta inda baya rawa, Allah na shiga ambato a fili, idanuna naji suna mun yaji_yaji. Ba Modu ya tare ni da hadisai masu kashe jikin ɗan Adam. Ajjiyar zuchiya na shiga saukewa, a hankali ina ambaton Allah sai naji na samu salama, idanuna basu zubo da hawaye ba. Labarta mun dalilin sakin da Ba Modu yayi, yafi sakin girgiza ni, kuma yafi sakin bani mamaki. Murmushi kawai nayi nace. Babu komai Ba Modu, Allah yasa rabuwar mu shine mafi alkairi. Ka kwantar da hankalinka, bazan sa komai a raina ba, kuma bazan riƙe kowa ba." Yawu na haɗiye, wani malolone ya tokare mun maƙoshina, bai wuce ba, bai fito ba. "Ga takaddun gidan da Bulama Babba ya baki. Sannan ga mota, kuma ya turo mun da million ɗaya kuɗin gidan da kika soma ginawa a Kano. Gasu." Hannu biyu nasa na karɓi takaddun nace. Allah ya amfana, nagode sosai. Allah ya jiƙan Ba Bakura. In sha Allah zan shiga in yi ma Hajja ta'aziyya da sauran iyaye." Sallamata Ba Modu yayi yana shi mun albarka. Ni kuwa ina fita naji duniya na juyawa dani. Gefe na samu na dinga ambaton Allah, sai da na samu sassauci sannan na nufi ɗaki. Su Fanna na tarar a ɗakin, suna ta hira. Suna gano ni suka soma murna. Ai ina ganinsu na soma kuka mai gunji, cikin ɗimuwa na sanar dasu Bulama Babba ya sake ni. Ya Innana ta saki kuka itama. Cikin ɗakinnan wakil da Bulama fari ne kawai ba su yi kuka ba, amman sun kasa rarrashinmu. Sai da nayi kuka mai yawan gaske sannan nayi shiru a kan ki kaina. Rarrashin su Ya Innana na shiga yi. Kuyi haƙuri, wannan duk abubbuwan da suke samu na Allah ne yake jarabtata, ku ƙarfafeni dan Allah. Ku yi mun adda'a dan Allah." Jin na fadi haka ne yasa Ya Innana tace. "Madallah da tarbiyyar da muka baki Yahanasu. Kin yi biyayya a lokacin da aka aura miki Bulama Babba, kinyi tawakkali a lokacin da Bulama ya sake ki. Allah ya kawo miki sauyi da haske a cikin rayuwarki." Fanna ku je ɗaki da ita." Kafin dare kab ƴan cikin gida sunji labarin abunda ya faru. A kan sallaya na raba dare ina sallah ina roƙon Allah ya cire mun son Bulama a zuchiyata. Washe gari muka wayi gari da labarin rashin lafiyar Bulama Babba yana asibiti. Babu shiri Ba Modu da Gunsum suka kama hanyar Yobe. Mama Gana da Ahmad ne a wajanshi. Ni dai ina ɗaki jigum, da naga shirun yayi yawa, sai na soma karance karance littattafan Hausa, da wasu littattafan addini da ban karanta ba. Wasa_wasa ciwon Bulama Babba yayi mugun tsananin gaske, Ba Modu dai ya dawo, amman Wakil da Ba'a kaka sun tafi jinyarshi. Hajja ma ta je ta dawo, har ta kwaso su Bawa ta dawo dasu gabanta. Sai dai in shiga ɗaki in ci kuka in gode Allah, Ya Innana bata barina in keɓe kaina kwata_kwata tsoro take kadda in koma gidan jiya, kullum a cikin adda'ar samama Bulama Babba lafiya nake. Ranar da ya cika sati guda a asibiti. Da safe ina ɗaki a kwance Ya Innana ta shigo tace. "Ki shirya zaku Yobe da Babanku ki je ki ga jikin Bulama, ance jikin ya tsananta sosai. Ki ɗan ɗebi kayanki kamar kala goma sai ki sauka a gidan Mama Gana ki ɗan huta. Banda sa damuwa a rai, komai yai tsanani zai yi sanyi da izinin Allah." Jikina a mace na tashi na sake kaya. Na haɗa kaya kala goma kamar yadda Ya Innana ta umarceni. Lafaya na naɗa na zari ƙaramar jakata. Sai na dawo Ya Innana" "Allah ya tsare hanya. Ki gaishe da Mama Gana" Kai nasa na fita. Gaisawa na soma yi da matan yayyena, wasu suna haramar tafiya wajan aiyukansu, wasu sun riga da sun tafi tun sassafe, domun akwai likitoci, Nurses, da malaman makaranta. A bayan mota na zauna ni da Ya Bagaji, Ba Modu yana gaban mota, sai Bulama baƙi na ɗakin Ba Baana shi ke tuƙin motar. Ni dai ina zaune lamo a bayan mota ina kallon jejuna da jama'ar ƙauye, masu wucewa da masu cin kasuwa. Ohhh yau nice zanje duba Bulama Babba a matsayin ƴar zuwa dubiya, Allah mai iko kenan. Gashi a cikin gida ina ji ana batun an sake matso da bikin Bulama Babba, yanzu haka saura kwana huɗu a ɗaura aurenshi da Yalewa, harma an fitar da angon milk ɗin lafaya na ƴan cikin gida, da kamfalar kanuri wacce take sananniya a ko ina. Da waɗannan tunanin muka iso Yobe, kai tsaye muka wuce babban asibitin na Yobe, ɓangaren maza. A baranda muka tarar da Mama Gana, Hajja, Aissa ta ɗakin su Bulama Babba, Wakil, da Mainam yaron Mama Gana. Sai Ba Bature da Yalewa Amarya suma da halama isowarsu kenan. Idanu na zuba mata lyakkyawa da'ita san kowa ƙin wanda ya rasa, gata doguwa jiki duk madara. Wani zazzafan yawu na haɗiye mai ƙuna, tsugunnawa nayi na soma gaishesu ɗaya bayan ɗaya. Hajja a daƙile ta amsa mun, tunda na dawo ban sake ganin sakin fuskarta ba, ta'aziyya da na shiga ɗaki nayi mata ma, ƙarshe zageni tayi tas, ta kirani da fasiƙa. Amman ban faɗama kowa ba, ɗaki na shiga nayi kukana sosai." "Uwar masu gida, zo uwata ki zauna ki sha Mama?" Cewar Mama Gana, tana magana tana yatsina, nasan da Hajja take yi. A kusa da ita na zauna, muka haɗa idanu da Yalewa ta yi wuf ta ɗauke idanunta daga kaina. "To mu je mu duba jikin na Bulama Babba, mu kam ba zama zamu yi ba hanya zamu sake kamawa" Ba Modu ne yake Magana. Tare dukka muka ɗunguma zuwa ɗakin da Bulama Babba yake kwance. Ɗakin gado ɗayane a ciki, da bayan gida, ga tv da firji. Ahmad da Ba'a Kaka ne a cikin ɗakin. Bulama Babba yana zaune ya jingina bayanshi a fullo yana cin ayaba. Idanu ya zuba mun, nima shi nake kallo ina mamakin ramar da yayi tashi guda, da ganin yanayinshi kasan yana cikin jinya sosai. Hawayene suka cika gurbin idanuna suna shirin zubowa, kai ya girgiza mun halamar kar inyi kukan gashi ya cike ni da kallon soyayya. "Bulama Babba ya jikin da sauƙi dai ko?" Ba Modu ne ya katse mana kallon ƙudan da muke ma juna. "Da sauƙi Ba Modu, gobe ma zasu sallame mu suka ce. Sannunku da zuwa" Nan aka shiga gaishe_ gaishe. Yaya jikin naka Bulama Babba?" Bai ji kunya ko nauyin su Ba Modu ba yace. "Bazan amsa ba, sai yau kika ga damar zuwa dubani, bacin kinsan sabida ke nake kwance a nan wajan" Kai na sauke ina jin kamar zan fashe da kuka. Hajja na kalla, naga ta sake murtuke fuska. Ahmad ma yace. "Gaskiya kam umman Maryam muna fishi kuma ba zamu amsa wannan gaisuwar ba. " Murmushn ƙarfin hali nayi musu kawai. "Yalewa zuba mishi burabiskon da ki ka yo mishi ya samu ya ci" Cewar Hajja kenan. Ni dai bance komai ba. Duk a tsaye muke, Ba Modu yana kusa da Bulama Babba sai kallonshi yake yi, cikin so da nuna kulawa." Yalewa kuwa kiciniyar zuba burabisko take ta yi. Tana buɗe burabuskon ƙamshi ya cika ɗakin. Burabiskone mai hanta da kayan lambu a ciki, sai farfesun kaza mai ɗan kaurin romo. Zuba mai tayi ta ƙarasa kusa da Ba Modu, tana son cewa ya matsa, amman naga ta kasa. "Yau ga tsiya da wasali ƙasa. Baiwar Allah tureshi zaki yi sabida fitsara ko yaya? Ko da yake kin saba da fitsara da goyayya a cikin ƙattai" Cewar Mama Gana wacce ta isa inda Yalewa take ta fisge plate ɗin abincin. "Rashin kunya, a baki kike so ki bashi ko me? Ko da yake ba mamaki ai tunda an saba cuɗanya da masu buɗewar idanu" "Ya'isa Mama Gana. To mu kam zamu wuce Allah ya ƙara lafiya Bulama Babba. Mama Gana ki zo mu tafi gidanki mu ɗan zanta mana" Da dariya yayi maganar. Nan mu ka fice mu ka bar su Hajja da Ba Bature, da Ahmad dan ba'a kaka ma biyo mu yayi. Mu muka shiga motar Ba Modu da mu ka zo a ciki. Su Mama Gana kuma suka shiga motar Mainam, muka nufi gidan Mama Gana. A falo mu ka ya da zango. Ita kuma ta shige ciki sai gata da alkali da nakiya cikin faranti. Da tuwon shinkafa miyar taushe a ƙaton tran silver. Gwanin sha'awa dukkanmu mu ka sa hannu a cikin abincin muna ci. Dana ɗago sai in ga Mainam na kallona. Hakan ya mugun takurani sosai, ba shiri na tsame hannuna a abincin nace Ni na ƙoshi. Dama ba wani na azo a gani na ci ba. Ganin Bulama Babba ya fama mun mikin dake cikin zuchiyata. Ɗakin Mama Gana na wuce da akwatina. A kan gadonta na kwanta ina sharar hawaye tausayin kaina da tausayin Bulama Babba ya kamani. Ba Modu: "Mama Gana ga Yahanasu nan ni da kyatumarta mun yanke hukunci ta dawo wajanki ta kammala iddarta. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin na nemo mata aikin gidan TV in sha Allah, tunda nasan tana so. Na tura miki kuɗi wadatattu ki kula da'ita sosai, kin san dai halin da take ciki da wanda ta fito a ciki, kar a sake a barta ita kaɗai a ɗaki. Bana son kowa yasan tana gidanki. Ki tuntuɓeta ya take son yi da kuɗinta da Bulama Babba ya bata? Ga waya nan Wakil ya siya mata. Mu kam zamu koma sai kun zo biki." "Wa babu wani biki ni kam da zanje. Su je su yi biminsu can da su gada." Cewar Mama Gana tana magana tana huci. Ba Modu yace. "Assha Mama Gana, ai wannan bikin mune akan gaba gaba. Ita kanta Yahanasu ya zame mata dole ta halarci bikinnan. Abunda ya faru ya riga da ya faru kuma ya wuce ai. Fatanmu Allah ya haɗa kowa da abokin zama na gari. Mu kam zamu wuce." Nan suka tattara suka kama hanyar komawa Damaturu. Ba Modu yana zaune a mota yana tunanin al'amuran da suka faffaru." BULAMA BABBA: Kaina na sauke ina jin zuchiyata babu daɗi sam. Hajja kuwa ta inda take shiga ba tanan take fita ba. "Ka kiyayeni akan Yahanasu wallahi Bulama Babba, kar ka bari in yi fishi da kai. Yalewa ki zauna ki bashi abincin har sai kin tabbatar ya ci tukunna. Muna jiranki a waje, in kin gama sai mu tafi. Bature mu basu waje" mamakine sosai ya kama ni jin Hajja tace a bamu waje, sai kace mata da miji. Ina gani suka fice a ɗakin har da Ahmad, ɗakin ya rage daga ni sai Yalewa da take zaune a kujerar roba tana fuskantata. Ƙur ta zuba mun idanu tana karantata. Abincin ta ɗebo a cikali ta nufo da cokalin bakina. Carab na riƙe cokalin ina kallon ƙwayar idanunta nace. Al'adarmu da addininmu sun koyar damu kunya. Ita kunya adone a gun duk wata ƴa mace. Sabida wayewa jibi shigar jikinki, gashinki da ƙirjinki a bayyane. Kayan jikinki sun kama miki jikin ki, kin bayyana ma mazan waje adonki, kina tallata musu surarki, dan Allah ya baki kyau, da kyan fata, da kyan diri ta hanyar daya dace kiyi amfani dashi kenan....?" "Dakata Bulama Babba. Kar ka ɗauka aurennan da za'a ɗaura mana ko ina sonka ne, balle ka samu damar ci mun fuska. Ka dubi kyau da tsarina wallahi nafi ƙarfin talaka irinka. Kuma jikina haramun yake a wajanka baka isa ko yatsan hannuna ka taɓa ba. Ka ɗauka zan zauna a gidanka ne a matsayin baƙuwar da ka ba ma wajen kwana" Tana kaiwa nan ta ja tsaki tare da dangwarar mun da plate ɗin abincin a saman cinyata rabi ya zube. Ta kama hanyar fita, na bi bayanta da kallo, babu shiri na kawar da kaina. Dan duk wani lafiyayyen namiji in yai tozali da irin shigar da Yalewa tayi, dole kwaɗayinshi sai ya motsa, balle irinmu da mu kai tsatsa. Idanu na lumshe fuskar Yahanasu ta shiga yi mun yawo, ina hango tausayina da kewata a tsakiyar idanunta. Shigowar Ahmad da Ba Bature ne yasa na buɗe idanuna. "Bulama Babba Allah ya ƙara sauƙi sai ka zo taron ɗaurin auren Allah ya ƙara lafiya" Ameen Ba Bature nagode sosai. Yana fita Ahmad yace. "Wallahi Bulama Babba Yahanasu tana cikin tashin hankali da damuwa mai tsanani. Ina tausayinta sosai. Yanzu likitan ma yace zamu iya tafiya gida ya sallame mu, na gama komai. Sai ka taso mu tafi Dala yana waje yana jiranmu, wannan abincin fa zubewa yayi?." A sanyaye na sakko muka wuce gidan ba tare da na iya cewa komai ba. Amman kullum a cikin kewa da tunanin Yahanasu nake, ashe haka soyayyar gaskiya take, jibi yanda duk girmana soyayya take sani fitar hawaye, da kasa bacci, rashin walwala da rashin sukuni. Oh ya Allah, ban taɓa mafarkin Yahanasu zata iya zamewa sanyi ga idanuna ba, sai gashi a kanta nake fama. Haka dai lokacin yai ta tafiya ana gobe ɗaurin Aure na shiga shirin tafiya Damaturu da safe dan Hajja ta dame ni da waya akan ya kamata in zo, anata gudanar da bukukuwan al'ada babu ango. Babu yadda zanyi haka na shirya na fito. Ina fitowa Mama Gana ta kira ni a waya. "Bulama Babba kana Yobe ko Damaturu?" Ina Yobe yanzu kinga fitowata kenan zan je can Damaturun." "Yauwa shikenan ma. Biyo ta gidan ka ɗauke mu a sabuwar motarka muma mu ɗana" Ɗan murmushi nayi nace. Ke da waye Mama Gana?" Ɗan dariya tayi mun itama tace. "Ni da Uwata ne." Dam naji gabana ya ba da wani irin bugu. Idanuna na ɗan rintse kaɗan, ina jin motsin son Yahanasu wanda nayi imani dashi zan game rayuwata. Gani nan zuwa Mama Gana" ƙit na datse wayar wajan motata na nufa. A wajan na tarar da Ahmad da Hajara da yaran suma sun fito tsab Damaturun suka nufa, amman a tashi motar daya siya zai tuƙa su. Zan biya gidan Mama Gana in ɗaukosu ita da Yahanasu sai dai mun haɗu a Damaturun kawai" "Ohhh Yahanasu tana cikin garinnan shine ko ta ɗan leƙo mana. Kuma Bulama itama bikin zata je? Allah sarki Yahanasu" Kallonta nake yi kawai Ahmad ne ya daka mata uwar tsawa. "Dalla shige mota jo. Baki ba matari duk maganar data fito bakin ki sai kin fesar" Da sauri taja yaran suka shiga mota. Ahmad ya dafani yace. "Bulama kayi haƙuri ka cire Yahanasu a cikin rayuwarka ko dan ka zauna lafiya. Kayi ta adda'a in da rabon ku sake yin zaman aure a gaba wallahi sai kaga komai ya zama kamar tarihi. Kaje ka ɗakkosu suna jira" MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE[20/08, 10:01 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 56 GHANA: Kofur Zubaina: Kwanan mu uku a asibiti aka sallamomu muka dawo gida. Matan gida sai sannu su ke yi mun, ni kuma ina binsu da um hum. A bakin gado na zauna ina ba ƴan biyu nono ko wanne ya kama sai ja suke yi abinsu. Idanu na zuba musu hawaye na shatata a kuncina yana ɗiga a kayansu. A haka Nabeela ta shigo cikin ɗakin da kofin ruwan zafi a hannunta. Ganin halin da nake ciki ne yasa ta zauna tace. "Sai yaushe zaki dena zubar da hawayenki a game da lamarin Alh da gidanshi ne Zubaina? To wallahi gara ma ki dena dan Alh yana nan yana dakon dawowarki cikin gidannan ya sauke miki buhu_buhun ɗiban albarka sabida katsalandan da mahaifiyarki take yi mishi akan ki. Ni dai babu abunda zance damu duka sai haƙuri. Duk abunda ya samu shamuwa watan bakwai ne, in da kwaɗayi da wulaƙanci, motar kwaɗayi a tashar dana sani take tsaiwa. Kuskure ne mun riga mun tabka, jarabawa kuma bamu isa tsallakewa ba, sai mu yi haƙuri mu rungumi ƙaddara. Ga ruwan zafi nan na ɗebo miki ki dan kukkurɓa ya warware miki hanji tunda kunu ko shayi bazai samu ba. Nima a haka nake nawa jegon. Ke bama ni kaɗai ba harda waɗanda zasu shigo gaba ma." Hawayena na share jikina ya sake yin laushi, dama ashe haka sakayya take, ashe haka ƙaddara take juya akala? Allah na tuba ka yafe ni ya Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Nabeela nace. Nagode ƙawai Nabeela" fita tayi ta barni a zaune ina karanta wasiƙar jaki. Muguwar yunwa nake ji, ji nake uwa ana yashe mun hancin cikina, ga ƴan biyu sai tsotso suke yi, ruwan nononma guda nawa ne. Bayan sun yi bacci na shinfiɗesu, sai na shiga buɗe buɗe ko zanci karo da wani abun ci. Ledar da Mabaruka ta bani na hango a can ƙarshen gado, hannu nasa da ƙyar na zaro, na zazzage ko Allah zai sa in dace. Amman wayam babu komai a ciki duk na cinye komai, ala tilas na kafa kai na kwankwaɗi ruwan ɗuminnan, ina sha ina jin ƙarar gangarawarshi cikina tamkar ana zuba ruwa a buta. Abun duniya ya game yai mun yawa, hankalina ya dawo kan ƴan uwana da halin da Asiya take ciki. Gashi bani da ko sisin kobo balle in kira in ji yadda ake ciki. Mun dai yi waya da Mama kafin a sallamoni daga asibiti take sanar dani zasu tafi wani ƙauye domun nemama Asiya magani ko Allah zai sa a dace. Nayi kuka kamar fitar rai, tausayinmu da tsoron Allah ya sake shigata ainun. Jiƙewar da ƙunzugun jikina yayi da jini shi ya tilastamun tashi domun neman fallen zanin da zan yayyanka in yi ƙunzugun dashi. Wata atamfar chiganvi na kakketa na ɗauki falle ɗaya na fito tsakar gida da zummar zuwa banɗaki in gyare jikina. Ina fitowa wani sanyi ya shiga kaɗani jirin yunwa da rashin ƙarfin jiki na jinya suka saukar mun. Alh Liti na hango buguzun_buguzun yana tawowa ɓarayinmu. Sunana ne a bakinshi yana rakaɗa mun mahaukacin kira. Tsumman hannuna babu shiri ya faɗi ƙasa jikina babu ta inda baya rawa. In kada baki in amsa kiran nashi na kasa. Yara da manyan gidan kowa ya shiga taitayinshi sun zuba idanu suna shirin kallon ikon mai sama. Da ɗan yatsa ya nuna ni. "Wallahi duk ranar da kika kuma fita da sunan zuwa asibiti a cikin gidannan sai na wulaƙantaki ƴar iska ƴar gidan maras tarbiyya. Bazai yiwu Jummai ta dunga zuwa tana fita mun dake ba. Kin ci sa'a da ba dan nayi alƙawarin bazan sake ki ba wallahi da kinga tsiyar da zan tabka miki da ɗanyan jegon nan. Da sai na birkita ma Jummai ƙwaƙwalwa ta ganku jibge ku biyu a gabanta kuna zawarci." Ni dai tunda na sauke kaina ban dena zubar hawaye ba, har sai da ya gama buyaginshi ya tafi, kana na samu zarafin tsugunnawa in ɗau tsummana. Bayan gida na isa da jan ƙafa har yanzu a kumbure nake ban saɓe ba. Ƙunzugun jikina na cire na mayar da wani. Ba sabulu ba omo haka na wanke tsumman jinin nan, na fito dashi. Ɗaki na koma na kwanta numfashina na fita sama_sama. Haka nai ta wannan jego na wahala ruwan nonon ma baya isar jariran sam. Ranar suna da asuba Alh Liti ya leƙo ya jefo mun wata leda kan gadona ya saki labulen. Ledar na jawo atamface ɗinkin doguwar riga atamfar roba, sai rigar yara guda biyu, sai omo ɗaya sabulun wanki ɗaya, shikenan abunda ke cikin ledar nashi kayan sunan kenan a matsayinshi na uba wanda aka haifa mishi ƴan biyu. Idanu na runtse ina kaico a zuchiyata. Na tuno lokacin sunan Bawa. Irin hidimar da Bulama yayi abun har ya wuce misali. Daga ni har jaririn sai da yayi mana akwati ko wanne da nashi. Kayan fitar suna kuwa kala bakwai na ɗinka tsadaddun kaya haka ma ɗinkin shima mai tsadar gaske. Raguna biyu tiƙa tiƙa ya yanka. Banda kaji guda goma sha biyar da aka yanka, abincin suna kuwa sai da mu kai kala uku, ga sobeniyas da muka raba. Murmushi kawai nayi na ɗakko yaran na saka musu kayan da babansu ya kawo musu. Zuwa goman safe yaran gidan suka soma hallara, tuwon shinkafa miyar kabewa akeyi na suna. Babu wani ko wata daga maƙota da suka shigo da zummar taya mu suna. Mu kaɗai ma gayyane bana jin abincin da ake dafawa ma zai wadaci kowa da kowa a gidan. Kuma a Ghana naga rumfa suke kafawa maza da mata a haɗu ayi bikin suna, ana cin abincina ana raye_raye kamar dai yarbawa. Abun haƙiƙa kuwa Alh bai yanka ba haka mu ka yi sunan mu lami washe garin suna na koma bakin aikace_aikacen gida. Ko bacci bana samu ishasshe sabida kuka da tsotson ƴan biyu, nonon ba issarsu yake yi ba to nima banci na ƙoshi ba balle su samu. Yanayina kuma ya koma na bagidadawa fatata ta dafe ta yamushe, ƙafata kuwa duk faso, kaina harya soma furfura dan masifa bansan da me zan fasalta muku zaman gidan Alh Liti ba, su Hajiya Kubra ne kaɗai zasu fahimceni domun tare dasu muke ɗanɗanawa. Ga Zarah data sakoni a gaba, dan tsabaragen jarabarta na dena fitowa tsakar gidan ma in ɗan sha iska, sai dai in ni ce da girki. Mama ƘAUYEN YADAGUNGUME DAKE ƘARƘASHIN ƘARANAR HUKUMAR NINGI TA BAUCHIN NAJERIYA" Isar su Mama gidan mai magani kenan. Ko a iya hanya sun jigata, jigata bata wasa ba, dan a mashin suka ƙarasa cikin ƙauyen da kwatance suka isa gidan mai maganin kasancewar sanannene sosai a fannin bada magunguna irin na gargajiya, fitar da aljanu, dama fitar da maita wannan dalilin yasa ake mishi inkiya da dodon mayu, maye daya haɗa idanu dashi yake soma bubburwa. "Sannunku da zuwa maraba baƙi. Ga can ɗakin jira ku je ku kama layi, duk waɗanda ke cikin ɗakin layi baizo kansu bane. Ku shiga bari a kawo muku ruwa" Cewar wata dattijuwa dake bakin murhu tana talge. Mama da Goggo Safiya da suke riƙe da Asiya suka shiga wannan ɗaki da wannan baiwar Allah ta nuna musu. Mutanene sosai a cikin ɗakin, ga kuma gadajen kara a jejjere da marasa lafiya a kai. Wasu suna kwance yayin da wasu suke a zaune. Wasu suna sambatu da dariya, yayin da wasu kuma suke shiru, amman kallo guda za kai musu kasan lallai babu lafiya. "Bayin Allah ga gadon kara can ku shinfiɗe maras lafiyar a kai. Barkan ku da zuwa" Ɗaya daga cikin matan ɗakinne taima su Mama magana. Shinfiɗe Asiya su kayi a gadon kara, wuyanta a goce ya suntuma sai walƙiya yake yi. Hawaye Mama ta shiga sharewa, ɗingisawa tayi da ƴar sandarta wanda take dogarawa tun sanadin Alh Liti. "Sannun ku baayin Allah mun same ku lafiya ya masu jikin kuma?" Goggo Safiya ce take gaishe da jama'ar da suka samu a ɗakin, bayan sun nemi tabarma sun zazzauna. Nan aka shiga gaisuwa da tambayar masu jiki. Wannan dattijuwar ce ta kawo ma su Mama ruwa a kofin silver. "Dan Allah muna son zamu kama ruwa zamu yi alwala kuma" Inji Goggo Safiya dan Mama da Nafeesa sun kasa cewa komai, ko wanne cike yake da dana sani a rayuwa. Bayan sun rama sallolinsu ne suka koma ɗakin jira. Goggo Safiya tace. "Nafeesa taimaka ki ba Asiya ruwa kar ƙishi ya dameta." Nafeesa a sanyaye kamar ba'ita ba tace "Goggo ko an bata ruwan ƙwaranyewa yake yi, wuyanta a karye yake sosai." Mama cikin muryar kuka tace. "Ni ban taɓa ganin irin wannan ciwon na Asiya ba. Amman wallahi ba da ban na tuba na koma ga Allah ba da sai na yi shari'a da Alh Jafar da matarshi, dan su suka nakasa mun ɗiyata. Allah ya isa bazan yafe musu ba mugaye kawai" Goggo Safiya ta dubi mama tace. "Jummai kenan wanzami dama ance bai son jarfa. Wannan duk abubbuwan da suke ta faruwa akufi_akufi girbine na abunda kuka shuka. Ai adda'a zaku yi Allah yasa ya tsaya a haka. Kuma a dage aita tuba zuwa ga Allah, an yi kusa kurai masu tarin yawa, suma mazan Allah ya shiryar dasu baki ɗayansu. Rayuwa kenan duniya juyi_juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi." Mama da Nafeesa sai share hawaye su ke ta faman yi. Suna dai wannan gidan har bayan sallar isha. Da dama an dubasu sun tafi majinyata biyar suka rage a ɗakin, sai ƴan Rakiya. Wannan dattijuwar ce dai ta shigo hannunta riƙe da katon trai mai murtala da tasosi a kan tran na tuwo dana biya. Durewa tayi a tsakar ɗakin, ta fita sai gata da wani tran ta sake direwa. "Bayin Allah ga abinci, tire ɗaya na marasa lafiyan ne. Ɗayan kuma naku ne. Zuwa gobe da safe malam zai duba ku in sha Allah." Godiya su kai mata, Goggo Safiya ta ce. "To bayin Allah ga fa abinci nan. A samu aba marasa lafiyan tukunna. Mu tamu ko ruwa aka bata dawowa yake yi baya zama. Nafeesa ke da kike fama da juna maza ci abinci. Adda'a zaki dage da yima ƴar uwar taki, ba wai kita tagumi ba Allah zai bata lafiya in sha Allah." Haka su ka ci tuwannan na dawa da miyar kuka ko maggi babu sai gishiri, tako ji daddawa sosai sai ƙamshin kalwa take yi. A zazzaune suka kwana wasu kuma a kan taburmin suka shinfiɗe. Da safe aka tare su da ɗumamen tuwonnan da ruwan kokko. Misalin ƙarfe sha biyu layi ya iso kan su Mama. Zuwa wannan lokacin jama'a sun sake cika ɗakinnan da marasa lafiya." Da Goggo Safiya da Nafeesa ne suka tattagi Asiya, Mama na biye dasu tana ɗingishi tare da cije lebɓa dan kullum ƙafarnan sake yin ciwo take yi mata a ko da yaushe, gashi sai kumburi take yi, rashin nitsuwa dangane da ciwon Asiya ne ya hana Mama zuwa asibiti domun a duba ta. A falon malam suka shinfiɗe Asiya suka zauna daga gefe. Malam ja'e ya ƙura mata idanu sosai ya taso ya dubi wuyanta yanda ya kumbura yai suntum gashi a gefe. Addu'a ya soma yi yana tofe ta dashi tub_tub. Daga bisani ya ɗakko wani garin magani ya kwaɓa da wani irin kitse ya shafe mata wuyanta dashi, ya yayyafa mata wani ruwa a ƙwarya. "Allah ya bata lafiya, amman dole zamu riƙeta anan domun ace za'aita tiri_tiri abun bazai yi muku kyau ba jikin nata zaiyi laushi. Akwai magunguna da zan sa mata su dafa, akwai na sha da na wanka in sha Allah. Ga wannan shi kuma sau uku za'a dinga shafa mata a rana. Allah yasa mu dace, ku ɗauketa in kun shiga cikin gidan kuce Hanne ta nuna muku ɗakin jinya zata nuna muku. Akwai masu kawo abincin siyarwa dandali zaku iya sayen duk abunda kuke so, dan ba lallai bane abincin namu yayi muku ba." Da godiya suka kinkimi Asiya zuwa ɗakin jinya da Hanne ta nuna musu. Akwai majinyata har guda biyar a cikin ɗakin. Goggo Safiya tace. "Nafeesa zuwa gobe sai ki yi azamar komawa ɗakin ki, kya dinga zuwa dubiya lokaci zuwa lokaci tunda bamu san yaushe zamu bar nan ba" Nafeesa sai ta fashe da kuka tace. "Wallahi Goggo Safiya ko bacci bana iya yi a cikin gidan, firgita nake yi sosai. Sannan shi kanshi mai gidan kar ki so ki ga irin tsawar da yake daka mun ni bazan koma ba" Mama ta yi wuf tace. "Ki ma kan ki Alam nashara ki koma ɗakin ki bakin ki a likkafa Nafeesa, da kinga halin da Zubaina take ciki da yanda ta zama kuma kice me?" Nan su kai ta lallaɓata washe gari ta kama hanya ta koma. Su kuma su ka ci gaba da zaman jinyar Asiya, babu dai wani canji, abinci da ruwa ɗura mata akeyi, baya wani shiga, ba um ba um _um haka dai take kwance kamar gawa bata dai sauya zane ba. Mama kuwa ƙafarta kullum a cikin ciwo take sai da malam Ja'e ya ɗaurata itama akan magani, dan magashiyan ta kwanta jinya, bata ko iya motsa ƙafarta guda ɗaya balle har ta takata. Oh Duniya mai ido a tsakar ka kenan, ku dubi yanda rayuwa take juyawa wannan kaɗai ya ishe mu jin tsoron rabbil sama wata wal ardi. Ubangiji ka bamu dama da ikon cinye jarabawarmu. Mrs Bukhari ce [20/08, 10:01 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI IBRAHIM B4B GIDAN ƘAMSHI 57 GHANA: ZUBAINA: Haka na ci gaba da rainon ƴan biyu na, ga jego ga aikin gida, gashi ko ishasshen bacci bana samu. Gabana kuwa duk ya ɗaɗɗaye tsumman ƙunzugu ya cinye mun wajan sosai, a tattale nake tafiya. Rashin kyan abinci da rashin lafiyayyen abinci yasa na sake ficewa a hayyacina, suma yaran ruwan nonon babu maiƙo baya isan su sam, shi yasa kullum a cikin tsala kuka suke, ni kenan a cikin rarrashinsu, in abun ya isheni in ta faman kuka nima. Musa ne ya kira wayata, tun shekaranjiya nake mai filashin sai yau ya kira. Musa ya ake ciki ne wai, wayar su Mama bata fa shiga kwata_kwata ranan kace zaka je can ƙauyan ka dubo jikin na Asiya tunda Nafeesa ta maka kwatance ko, to baka je ba?" Musa yace. "Gobe zan je in sha Allah tare da Kawu Tanko zamu je da Kawu isiya zai tawo daga Rano yau, gobe sai mu wuce. Wallahi Zubaina rayuwar na gama tsorata da'ita kin ganni ina nan ina istigifari wallahi bani ba zina, wallahi duk waɗanda naga suna aikatawa ma zan musu faɗa ni islamiyya ma zan koma ko da ta dare ne, bazan so abunda naima yaran wasu nima ai ma yarana ba. Yanzu ga Sagiru yana firizin kuma rayuwarshi zai gama gaba ki ɗaya a can. Rai suka kashe, kuma ran yana da gatan shi. Sati guda kenan da aka gama zaman kotu, har Kawu Isiya ma ya tawo daga Rano. Amman an yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai, ni faɗa miki ne banyi ba, kuma kuji da musibar dake gabanku, Mama ma sai mun je ƙauye zamu faɗa mata. Ba network ne a garin" Da kuka na ajjiye wayar, na sake shiga wani mugun tashin hankalin sabo. Ji yanda rayuwarmu ta dawo abun tausayi kamar ba damu ake damawa ba a da. Ni nawa ma da sauƙi dubi Asiya da Sagiru yanda rayuwarsu ta juye cikin ƙanƙanin lokaci. Oh Allah na tuba ka gafarta mun, Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar. Ƴan biyu na haɗe a bayana su biyun na goya su na dawo bakin aikina. Zarah sai zage_zage da habaice habaice take ta faman yi. Ina gaban murhu ina iza itace Alh Liti ya shigo yana ihun kiran sunan Nabeela, sai uban sauri yake yi. A guje Nabeela ta fito. " Na sauwaƙe miki aure na, Zarah kema ki je na sakeki tunda baki da ciki, kwanaki dai naji labarin kin yi ɓari. Ku tattare ku bani fili zanyi sabbin zubi" Salati muka shiga zabgawa, saki shi bashi da daɗi sam, duk buyagin gidan Alh Liti in ya saki mace sai ta ci ɗan banzan kuka, ko dan sabida yaranta da zata tsallake ta barsu. A ranar Nabeela ta kama hanyarta, ni ina kuka ita tana kuka, yaron da take goyo ta miƙo mun, hannuna yana rawa na amsa. "Gashi dan Allah ki haɗa ki shayar dashi shima, nono yana da matuƙar hamimmanci ga jikin yaro, watan shi biyu zaki dinga haɗa mishi da kokko. Hajiya Kubra saduwar alkhairi, Allah ya ƙaddara saduwarmu, ya haɗa fuskokinmu da Alkhairi" gidan gabaki ɗaya a ranar hautsine mana yayi ni da Hajiya Kubra. Washe gari sassafe Zarah ta tattare inata inata itama tayi gaba. Abubbuwa suka sake cakuɗe mun, ga yara har uku, ga aikin gidan ya ƙaru mana ainun. Da yamma ina zaune a ƙofar ɗakina nayi jigum yaran yanzu na gama basu nono duk sun yi bacci. Sai ga wayar Musa. Ina ɗagawa na jiyo muryar Mama cikin rishin kuka. Gabana ya yanke ya zube hankalina ya tashi ainun cikin kakkarwar murya nace Ta mutu ko? Innalillahiwainnailaihilrajiun kaico har ga Allah banso Asiya ta mutu ba tare data yi istigifari da aiyukan alkhairi dan wanke laifukanta a wajan Allah ba" Ina gama faɗar haka na ƙule ɗaki da wayar a kunnena. "Bata mutu ba Zubaina amman dole ki tausaya ma Asiya in kika ganta, duk da dai muna ganin canji sosai dan ta soma karɓar abinci. Sai dai ba um ba um um. Jiya Zakiya da Rakiya suka koma sun zo dubamu, Nafeesa ma tana nan tare damu, mijin yayi mata kafurin duka ya korota, amman bai saketa ba dai. Mun yi kiran wayarshi kiran duniya ya ƙi amsa kiran namu. Ga ƙafata ciwo take yi. Ni dai ku yafe mun dan Allah duk ni na sa ku a wannan ukun na tuba na tuba." Idanu na lumshe wani hawaye mai zafin gaske ya yanko mun. Tausayin kanmu dukka ya kama mu, a hakan ma bata san abinda Sagiru ya aikata ba. Mama ki gode ma Allah daya ganar damu, lokaci bai ƙure mana ba. Muita roƙon Allah gafara, shi ɗin mai yawan afuwa ne. Bani Musa " Mama ta miƙa ma Musa waya. Musa so nake ka kira wayar Bulama kaji ya su Bawa suke, in da hali kaje ka dubo mun su. Wallahi kwana biyunnan sun tsaya mun a raina. Ban ma yaran adalci ba yanda nayi fatali dasu, kai mun wannan taimakon." Ya amsa mun akan zai kira duk yanda su ka yi zai sanar mun. Ya ba Goggo Safiya mu ka gaisa, Nafeesa ma muka gaisa, nayi mata ƴan nasihu a matsayina ta babba, daga haka mu kai sallama dasu. Rayuwa tai ta kulawa watan su Mama biyu a gidan mai magani, hatta da gidana da suke ciki sai da aka siyar da ɓangaren da aka zuba haya, ɗakin mama da ɗakin Musa kawai ya rage. Ni kuma ina da wannan ɗanyan goyon, bala'i na yau da ban na gobe da ban. Kwatsam na tsiri laulayi, ga yara uku, ga ƙaramin ciki ga fargaba, ga bautar gidannan abubbuwa suka sake dagule mun. Ɗan sauƙin dana samu shine yaran suna shan kunu sosai, kuma ina mamula musu tuwon dokunu suna kuma karɓa. Bayan tafiyar su Nabeela da wata uku Alh Liti ya fello Amarya zuƙeƙiya kyakkyawa yarinya shatab da'ita. Ni dai baya gabana ina fama da laulayina. Asiya jiki da sauƙi sosai, mai maganin ma yace musu sati mai zuwa zai basu sallama, harma an bani ita a waya mun yi waya na ji muryarta sai naji sanyi a raina. Musa kuma ya sanar dani yayi waya da Bulama, amman yace mishi sun koma Yobe da zama. Take hankalina ya kuma tashi sosai, sai Musa ne yai ta kwantar mun da hankali akan da zaran su Mama sun dawo shi zai je Yobe ya gano mun su, shine na samu dama dama. Yobe: Yahanasu Ina zaune a kan kujerar falon Mama Gana, ga akwatina, da jakar kayan Mama Gana a kusa da ƙofar shigowa. Sai mu ka jiyo sallamar Bulama Babba. Gabana naji ya harba, dama sukuku nake jin kaina yau tunda na tashi, dan da ƙyar nayi wanka na kintsa ko karyawa Mama Gana tayi_tayi in karya naƙi, nace mata in naje gida zan karya. Carab muka haɗa idanu da Bulama Babba, yaci ado dama can shi gwanin adone gaskiya rayuwace ta mayar dashi baya talauci babu abinda baya haddasawa. Sannu da zuwa Bulama Babba " na katse kallon ƙudan da muke ma juna. Bai kai da amsawaba Mama Gana ta fito daga ɗaki ta cokara ɗan kwali tayi shar da'ita." "Au kazo ashe? Ke taso mu tafi karmu ɓata ma ango lokaci." Shi dai kai ya sosa ya zube ya shiga gaishe da Mama Gana, nima na gaisheshi muka ɗunguma cikin motarshi. Mama Gana ce ta shige gaba abunta ni kuma ina baya na lumshe idanuna ina ambaton Allah hawayene ke shirin tsinke mun ni kuma sai daddaurewa nake yi kar hawayennan ya zubo in kunyata. Dan Mama Gana ba ƙyaleni zata yi ba. Zama yayi a kujerar direba bayan ya zuba mana jakunkunan mu a bayan but. "Masha Allah mota tayi kyau rangaɗi kenan, a kashe lafiya, ango mijin Yalewa kenan. Ni ko Ahmad da matarshi fa ba za je bikin bane?" "Zasu je, suna hanya shi da iyalan nashi." Ya bata amsar a taƙaice, ta sake jefo mishi tambaya. "Tare zaka tawo da Amarya bayan an gudanar da hidindumun bikin ko, iyayenta ne zasu kawo maka ita" Sai cewa yayi. "Ni fa ban san komai game da tsare_tsaren su ba. Kinga ina gadon asibiti suka tsara koman su. Duk yadda ku ka yi dai_dai ne." Mama Gana tace. "Ni kaza duk yadda uwarka tayi dai. Kai Hajja tayi ƙarkon kifi daga ruwa zuwa wuta wallahi, kuma ta tsinka Modu. Duk irin so da kulawar da Modu ya baka a rayuwa yau shine zata tozarta mishi ƴa. Allah ya bamu lafiya, za ku sha mamakin irin mijin da Uwata zata aura." Tai ta surutu ratatata, mu dai kowa yayi shiru kamar ruwa ya cinye mu. A haka muka isa Damaturu gida batse da jama'ar biki kowa ka gani cikin lafaya, tsakar gidan sai ƙamshi turare yake zabgawa. Da halama gagarumin biki Hajja ta shirya bana wasa ba. Ni dai na shige cikin ƴan uwana, amman babu walwala ko kuzari a jikina sam, amman haka nai ta daddaurewa anata sha'anin bikin Bulama Babba da wakil da zai auri ƴar wan Ya Innana da suke zaune a Biu. Biki aka gudanar cancaɗeɗen gaske, Hajja tayi ɓarin kuɗi sosai. Ba Bature suma ba ƙananan kuɗi suka kashe wajen haɗa akwatin ango ba, wasu irin tsadaddun yaduna da shaddajo aka zuba mishi, agogon hannu ma sai da suka zuba hannu bakwai, banda turaruka da sauran tarkace. Irin yanda muke gudanar da bikin al'ada haka akayi wannan biki shina. Zuchiyata sai suya in na ga Bulama Babba cikin adon kece raini, duk da baya cikin walwala Amman sai nake ganin ai yana son matarshi. Ni kuma fa a cikin taron bikinnan sai nuno ni akeyi, daga masu kaɗa kai sai masu nuna sun tausaya mun. Hankali ya tashi ainun. Ranar da za'a kai Amarya Yobe Ba Modu ya kirawoni har ɗakinshi, na zauna a ƙasa kaina a ƙasa ina sharar hawaye. Allah shine masanin tsantsar son Bulama Babba dake raina. "Uwata kiyi haƙuri ki nutsar da zuchiyarki waje guda. Kifa tuna da baya ko a mafarki na tabbatar baki taɓa mafarkin zaki auri Bulama Babba ba. Ki koma wajen Mama Gana da zama uwata, ki tafi da motarki sabida in kin samu aiki ki dinga tafiya da motarki. Kuɗinki kuma uwata na ƙara miki dubu ɗari biyar akwai. Yayyenki maza suka haɗa miki dubu ɗari shidda suma. Uwata ki soma sana'a kina haɗawa da aikin ki na jarida. Sai ki ga kin samu nutsuwa. Kije kiyi tunanin abunda zaki yi na sana'a. Mama Gana zata kai ki wata ma'aikatan talabijin na kan tauraron ɗan adam zaki ci gaba da aikin ki. Kiyi haƙuri duk ke kika jawo ma kan ki, ban yi tunanin zan iya jin na tausaya miki ba, da baki yi wannan shaye_shayen ba ba lallai bane Hajja ta bijiro da wannan halin ba. Amman ina baki haƙuri." To Ba Modu nagode sosai da kulawarku gareni. A gaskiya na cuci kaina a bisa halin dana jefa kaina a ciki. Ƙaddarallah. Kuma inaso zan buɗe babban shagon gyaran jiki da gyaran kai irin na Kanuri, da su ƙunshi, da turarukan wuta da humra. Abinda nake son yi kenan" Ba Modu yace. "To kinga ta kwana gidan sauƙi, gidan da Bulama Babba ya baki akwai shaguna kinga har uku a jere. Sai ki sa a haɗe miki shagunan, a gyara miki shi tas. Sai ki soma gudanar da harkar kasuwancin naki. To amman aikin naki zai baki damar yin wannan sana'a naga sana'ar tana buƙatar lokaci " Zan ɗebi ma'aikata Ba Modu, sabida babban shago nake son buɗewa. Amman zan bari in shekara ta zago na karɓi kuɗaɗen hayata, sai in haɗe da kuɗin wajenka in yi duk abunda ya dace." Baki Ba Modu ya riƙe. "Uwata shagon kuɗi zai lashe haka" Da zolaya a muryarshi sosai. Murmushi nayi mishi kawai. "To ga shawara Dala zai taimaka miki da Mama Gana ku tsara komai, a duba nawa shagon yake buƙata na kuɗi. Sai in ara miki ai uwata ki soma yi, shekara ɗaya ai yayi yawa." Nayi murna sosai, shi kanshi Ba Modu yaji daɗin yanda yaga na kasa rufe bakina ma tsabar murna. Ya Innana na je na labartama da su Fanna. Kowa ya taya ni murna sosai. Fanda ce ta taya ni na kwashe ƴan ragowar suturuna da basu da wani yawa. Na ba Fanda key ɗin motata ta kai mun kayan mota. Muka bi ayarin tawagar Amarya. Har zuwa Yobe. Har dani aka je gidan Bulama Babba. Gida ya zuga kyau Tubarakalla. A ɓarayin Hajara na zauna, ƴan uwanta sun cika falon. Sai uwar ɗaki ta kaini jikinta sai rawa yake yi. Zance kuwa ta soko wannan a cikin wancan haka ta dinga sokiburutsun zancenta. Hajara ya'isa kaina ciwo yake yi" Ala dole ta barni, anan nayi kwanciyata har zuwa magriba Mama Gana da Fanda suka shigo ɓarayin Hajara kirana. Fitowa nayi zazzaɓi ya gama rufeni. "Yaha sai mu tafi gida ai tunda biki an gama. Bance musu komai ba na nada lafayar ankonmu na fita, suka biyoni a baya. A dai _dai in da na ajjiye motata muka haɗu da Bulama Babba da Ahmad, dasu Dala ne Wakil ne, Ba'a Kaka ne. Duk ƴan maza_mazan duka dai. Idanu Bulama Babba ya ƙura mun, ni kuwa nayi saurin shiga mota na zauna a mazaunin direba na runtse idanuna ina hawaye. Su Mama Gana kuma sai hirarsu suke yi. "Yahanasuna kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayenki. Wannan damuwar da nake gani tattare dake yana azabtar dani. Ban taɓa tunanin zaamu rabu ba Yaha" Idanuna na buɗe tar a kan fuskar Bulama, idanuwanshi sun kuma yin ja sun ɗan ciccika da hawaye. Na rasa me zan ce mishi, shi kuma ya cike ni da kallon soyayyar daya saba yi mun. Tsigar jikina da tsigar kaina sai zullo suke yi mun. Kishi ya sake turniƙeni ina hango Bulama Babba yayi ruf da ciki akan Yalewa. Idanu na kuma runtsewa nace. Kaje dan Allah bana son ina ganin ka. Ka dena fama mun mikin da dashi zan koma ga Allah Bulama Babba. Allah ya baku zaman lafiya a tsakaninka da Yalewa." Saurin goge idanuna nayi, da naji motsin su Mama Gana. A daren ranar bacci wannan ya gagari idanuna. Amman ya zanyi bani da tudun dafawa. Dole na sake naci gaba da gudanar da rayuwata zuchiyata maƙale da son Bulama Babba. Bayan sati guda da Auren Bulama Babba na soma aiki a gidan talabijin dake kan tsuraron ɗan Adam. Nike gabatar da labaran safe, da wani program sabo da ni na soma gudanar dashi. Domun tattaunawa da manyan ƴan kasuwa. Dala kuma bashi Damaturu bashi Yobe muna ta tsare tsaren maganar shago. Mama Gana kuma ta tafi maidugurin domun saron mun buhunhunan itatuwan turaren wuta iri daban_daban. Da kayayyakin gyaran jiki da duk abinda ya dace. Mun bada aikin stiker, da sainbot ɗin shagon nawa. An yi fenti an yi duk abinda ya dace ayi ma shago. An fitar da ɗakin gyaran jiki, ɗakin gyaran gashi da gasa shi, da ɗakin ƙunshi, harma da office ɗina. Amman ba'a zuba kayan aikin ba tukunna. Mama Gana na dawowa muka shiga aikin haɗa turarukan wuta, dana jiki, da na gashi. Da su humrarori nau'i daban_daban. Haka dai mu kai ta shirye_shirye tsawon wata biyu. A iya tsawon watannin nan ban sake sa Bulama Babba a idanuna ba. Kuma yana zuwa gidan. Amman duk sanda zai zo ina wajan aiki. Ko kuma yazo nayi bacci da daddare. Haka rayuwa tai ta garawa, da son Bulama Babba nake kwana kuma da son nashi nake tashi, har ƙarshen rayuwata bana jin zan iya dena son Bulama Babba" MRS BUKHARI CE[21/08, 9:35 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 58 GHANA: Bayan wasu watanni. Ina durƙushe a bakin murhu ina hura wuta, ga zungureren cikina haihuwa ko yau ko gobe. Amaren Alh Liti suma suna tsakar gidan tare da Hajiya Kubra. Yarane ƙanana ya auro, suma yarannan sun yi bore a tsakar gidannan kamar ba zasu dena ba. Daga ƙarshe ne suka dangana tare da zuba ma sarautar Allah ido. Duk wanda ya ganni bazai gane ni ba, gashi Mabaruka Mama ta kira ni jiya take sanar dani bata da lafiya tana cikin ciwo mai tsanani mijinta ya dawo da'ita gida da takaddar saki. Naci kuka sosai, dan na jima ma banji ɗuriyarta ba, to nima ta kaina nake da ta ƴan uwana. Ga Nafeesa ta haihu itama sai da su ka yi wata uku a asibiti ɗan ba lafiya, kuma mijinta yaƙi biyan ko sisinshi. Sai Mama da Musa ne su kai ta jigila, sai Kawu Tanko daya ke sa musu hannu. Daga baya yaron ya koma. Abubbuwa dai da dama sun faffaru. Ɗazu nan mu ka yi waya da Mama take sanar dani zasu je dubo yaran Asiya a Kano daga nan kuma zasu biya ta Damaturu su dubo su Bawa. Na ji daɗi sosai, da a kwance nake ma jikin ba daɗi amman bayan mun gama wayar ne naji dama_dama shine har na samu damar fitowa iza wuta. Ƴan biyu suna tsakar gida sai ta_ta_ta suke ta faman yi. Dan watan su biyu a duniya na shiga laulayin sabon ciki. "Ahuwanku dai masu gidan" Muka jiyo muryar wani bawan Allah a tsakar gidan, yana saye da ƙananun kaya da ƙatuwar jaka a bayanshi. Hajiya Kubra ce ta tashi tsaye tana nuna shi tace. "Wa nake gani kamar Jaba dama kana duniya baka mutu ba? Shekarun baya aka aiko mana da takaddar mutuwarka a cikin kogin lokoja" Dariya ya sheƙa mata kawai ya ƙaraso kusa da in da muke. Kamarshi ɗaya da Alh Liti tamkar kara aka tsaga, kuma shima ya manyanta sosai. Hajiya Kubra ta nuna mishi tabarma ya zauna. "Jaba ashe baka mutu ba, to mai ya dawo da kai cikin gidannan bayan kasan halin Alh sarai. Yana nan fa a yadda ka tafi ka barshi. Kaga waɗannan yaran du matanshi ne. Waɗannan yaran kuwa du ƙannenka ne, sama da guda talatin ma suna gidan mazajensu. Jiya aka gama bikin Rashida da ƙannenta su biyar. Ni da kaji shawarata da baka dawo ba, domun Alh zai iya makaka a kotu Jaba" Ni dai da mamaki na dubi Hajiya Kubra nace. Hajiya shima wannan yaron Alh ne wai? Murmushi tayi tace. "Shine ɗanshi na farko a duniya. Wata tataɓurza ce a tsakaninsu mai girma, dan abun yafi shekaru ashirin da faruwa. To Jaba dai ya tsallake ya gudu. Sai takadda aka turo mana cewar ruwan lokoja ya cinye shi, sai kuma gashi." Baki na taɓe kawai ina kallon ikon Allah, jaba kam kamarshi ɗaya da mahaifinshi ba maraba. Gaggaisawa mu ka yi dukka. "Ai Hajiya Kubra ni kwana ɗaya nazo yi gidannan ba zama zanyi ba. Wani aikine ya kawo ni, dana gama aikina cikin dare ba lallai mu yi sallama ba ma." Ƙasa_ƙasa yayi da murya yace. "In tambayeki mana har yanzu Liti yana nan a Litin dana sani mai ajjiye maƙudan kuɗaɗe a ɗaki?" Dariya tayi mishi tace. "Babu inda kai kam ka baro uban naka wajan son abun duniya. To mai za'a fasa. Ghana most go_ghana most go yake shiga da kuɗi turakarshi ai. Sai dai na cizo ba." "To ni zan je masauki Hajiya Kubra dama zuwa nayi in gaisheki. Ina su Halifa kuwa duk sun girma" "Halifa yana kasuwa yana sai da maganin basir, su Bala kuma cima zaune kenan." Murmushi yayi yana zare ido yace. "Zan biya wajan Halifa ya zagaya dani in ga ƴan uwana, dan gobe duku_duku zan wuce." Ya zaro dubu biyar ya ajjiye a gaban Hajiya Kubra ya juya, yana tattale ƙafa kamar agwagwa." Ni dai naci gaba da aikina ina jan ƙafa. A haka na gama abincin rana, na kuma rabama kowa da kowa. Na zubo mana namu a ƙaton faranti. Duk muka sa sannu muna ci ana taɓa hira, zuchhiyar kowa babu daɗi sam. Ni yanzu bana ƙoshi sam duk abinda naci bana ƙoshi sai dai in haƙura. Ƴan biyu na kalla suna ta cin nasu abincin, rabi a ƙasa. Kamarsu ɗaya sak har bana iya banbancesu da kamanni sai dai ta gashi. Gashin Hassana yafi na Usaina baƙi, shine kawai banbancinsu. Rayuwa kenan, da tsohon cikinnan nayi tuwon dare na sake rabawa. Ina fitowa wanka ana kiraye_kirayen Sallah. Sai da nayi sallah mu ka zauna zaman cin abinci da hirar tsakar gida. Takwas saura na kinkimi tran Alh na wuce ɓarayinshi. Ƴan biyu suna hannun Mariya Amarya a ɗakinta ma suke kwana Allah ya mata son yara, duk da dai itama ta kusan juyewa, duk ciki ne dasu riƙi_riƙi. Ina shiga ɓarayin Alh, motarshi ta iso bakin get. Kafin yayi hon na wangale mishi get ɗin ya shiga. Ya futo a cikin mota, ya buɗe buth ya ciro wata ƙatuwar jaka ya shige ciki abunshi, baiko kalleni ba. Kai kawai na girgiza ko kuka yanxu na dena zuchiyata ta riga data dake. Tiran abincin na ɗauka na bi bayanshi. Da dabara nake hawa saman cikina ya tsufa sosai. Na shiga na same shi yana waya. "E Alh ga kuɗaɗennan yanzu na shigo dashi. Nera million Arba'in ne. Cikoton kuma sai yaushe, kasan ni bana wasa da kuɗi. Shanu ko guda dubu kake so zaka samu fa, lafiyayyu ƙosassu ma kuwa" Ni dai ajjiye tiran nayi na zauna da ƙyar a bakin gado ina cije leɓena, anya ba naƙuda na ke yi a tsattsaye ba ma tukunna?" Ya dai gama wayarshi, bayan nayi mishi sannu da zuwa na gabatar mishi da abincinshi. Sai loma yake yi. "Daɗina dake hannunki ya iya miya sosai, sai kiji kan kifin yayi wani mugun taushi gwanin daɗi." Ni dai bance komai ba, dan ba iya mishi akeyi ba. Yanzu zaka yi magana in baka ci sa'a ba ya ƙare da zagin maka iyaye. Alh dan Allah inason daga yau in barma su Hajiya Kubra kwana, cikina ya tsufa gashi ƙafafuna du sun kumbura, ko awo ban taɓa zuwa ba. In na haihu na yi arba'in na ci gaba. Kayi haƙuri " "E babu shakka Kofur kinzo da iskanci. To in ke ɗin nake sha'awa shikenan sabida a kan ki aka soma ciki sai bazan huta dake ba? Wai me yasa baki da hankali ne wai?" Kayi haƙuri Alh......" "Ya isa dallah bana son magiya" Shiru nayi ina zaune har yayo wanka ya fito. "Ki cire kaya ina buƙatarki" Ba damar musu haka dole nayi yanda yake so. Nasha azaba a wannan daren bana wasa ba. Ina zaune nayi tagumi ina tunano rayuwa. Alh Liti kuwa sai munshari yake yi babu ƙaƙƙautawa, ƙarfe ɗayan dare ƙarfe biyu idanuna biyu. Tashi nayi na faɗa ban ɗaki dan yin wankan sallah, inason in yi sallar dare. Ina fitowa ɗaure da zani a ƙirjina naci karo da wani mutum a tsaye haka. Da baƙaƙen kaya a jikinshi, fuskarshi a rufe. Take jikina ya soma rawa na soma ja da baya. Alh Liti bai san abunda ake ciki ba sai bacci shi yake shatatawa. "Kar ki sake kiyi ihu ba wajanki nazo ba. Nazo ne in raba kowa da wahala" Ni dai ina maƙure a ƙofar bayan gida jikina na kakkarwa. Wuƙa ya zaro ya yanki babban yatsan ƙafar Alh Liti. Da sauri ya tashi. "Wani ɗan abu ta kazan ubane haka?" Ya furta, ganin mutum a gabanshi bai bashi tsoroba sam. "Wane mai ƙarar kwanan ne ya shigo mun turaka, yaro ba dai sata kazo yi ba?" Cewar Alh Liti. "Kashe ka nazo in yi kamar yadda na lashi takobi." Yana kaiwa nan ya cire hular kanshi, da ƙyallen daya rufe fuskarshi. Wannan jaba ɗin da yazo da rana ne yaron Alh. Ba Alh kaɗai ba har ni sai da na razana da ganin Jaba." "Jaba baka mutu ba dama? To yau wallahi zaka mutu ko ni ko kai" Alh yana faɗar haka ya miƙe yana ƙoƙarin dafa bango Jaba ya saurin cukuikuyeshi nan dambe ya kaure a tsakaninsu. "Baka kayi layar zana ba yau, kwananka ya ƙare a duniya". Ni dai ina tsaye ina kallon tashin hankalin wanda ba'a sa mishi rana. Bansan yanda akayi ba na gansu jina_jina dukkansu. Alh Liti ya faɗi ƙasa tim kayan cikinshi na motsi, Jaba ya farke mishi tumbi, Wannan abun dana gani shi yasa na soma naƙuda, bani da ko kuzarin da zanyi ihu, jinin Alh Liti harya gangaro inda nake. Jaba kuwa ya kinkimi jakunkunan kuɗi guda biyu ya arce, juyowa yayi ya kalleni "In kika sanar ma wani ni na kashe Liti duk inda kika shiga saina bincikoki na farkeki, hatsabibine ni fiye da tunaninki" Yana kaiwa karshe ya fice. Sai lokacin na zunduma ihu gigitacce ina jiyo tashin motar Jaba. Daga wannan ihu da nayi ban sake sanin ina kaina yake ba. Ni dai na farka na ganni a ɗakina anata faman yi mun fifita, haske har ya fito. Hajiya Kubra na kalla nace. Jaba ya kashe Alh Liti Hajiya shi ya kashe shi" Bakina ta rufe tace. "In kina son kan ki arziki ki ja bakin ki kiyi shiru, karki sake ki ambaci sunan Jaba. Jaba hatsabibine na ƙarshe zai iya dawowa ya kashe ki kema. Alh Liti dai ya mutu sutura ma akeyi mishi za'ayi jana'izarshi zuwa goman safe, lokacin shine yayi babu makawa" ciwon naƙudane ya murɗeni na cije bakina ina ruwan hawaye da ruwan jiri. Ba kowa a ɗakin daga ni sai Hajiya Kubra. Sai da aka kira mun wani malami ya dinga mun tofi, dan jini ya hau kaina. Gani nake yi tamkar mafarki nake yi wallahi, ni naga bala'i ganin idanuna." Hijabi na saka muka fito tsakar gida sai ta'aziyya ake mana tare da yi mana jajen ashe ɓarayine suka shigo sata suka kashe Alh Liti. Ni dai bana ko iya magana a cikin ɗimuwa nake sosai, jina nake kamar zautacciya, ashe haka Hajiya Kubra tace ma mutane ɓarayine suka shigo sata suka kashe Alh. Yaran Alh Liti mata_matan sai gasu gungu_gungu sunata shigowa, ko wacce in ka ganta kasan kukan munafurci take yi. Maza_mazan kuwa ba wanda yayi kuka ma sam, fuskokinsu cike da fara'a. Ni dai ciwon naƙuda sai ɗan mintsinina yake yi sama_sama. Kafin ƙarfe goma gidan ya cika dam da mata. Mu kuma aka kirani muje mu yi ma Alh adda'a. Duniya ba komai bace, duk wanda ya bari duniya ta ruɗeshi yayi wawa. A falonshi na ƙasa muka samu gawarshi shinfiɗe, daga sama aka sakko da gawar falon ƙasa, Hajiya Kubra tasa aka rufo saman. Dan a saman dukiyarshi take. Adda'a mu ka yi mishi, muna kuka. Ba kukan rabuwa dashi na tabbatar muke yi ba. Ni dai kukan farin ciki da annashuwa nake yi har ga Allah bazan ɓoye ba. Nayi imani sauran ma babu mai kukan mutuwar Alh Liti. Yaranshi ne suka riƙo makarar aka fito da'ita zuwa ƙofar gidan. Mu kuma Hajiya Kubra tace mu zauna karɓar gaisuwa a falon Alh tunda babbane. Nan muka zauna ƙwanmu da ƙwarƙwatarmu, ni dai sai ciwon mara sama_sama. Aisha kuwa ana fita da Alh ta soma naƙuda zanga_zanga sai su Rashida su ka yi da ita ɗakinta. Wayata aka miƙomun Mama ce take kirana. Ina ɗagawa na sanar mata da batun mutuwar Alh Liti, kuma nace ko bashi ne su ciyo ita da Asiya su zo su zauna dani, dan ni gani nake nima Jaba zai zo ya kasheni. A haka muka gama magana da mama cewar gobe zasu taso. Jama'a kuma aka barsu akan ɓarayine suka shigo har gida suka kashe Alh." Muna zaune maza ƴan raka gawa saka dawo. Nan akaita shigowa yi mana ta'aziyya. Hajiya Kubra ce take da kuzari ita take ta amsawa dama ita aka sani gaskiya, yaran Alh Liti kuwa basu kareba sai shigowa suke yi, wasu ma ban taɓa ganinsu ba ni dai. Auwal ne ya leƙo yace. "Hajiya ji mana ke da matan Baba" mu uku muka miƙe muka fito, tsakar gidan cike da al'umma. "Hajiya batun abun da za'a girka fa. Kinga mutane an cika kowa yana jiran me za'ayi, ni dai na tura su Halifa nace su ɗakko Saniya guɗa ɗaya azo a yanka ƙatuwa. Ku kuma ku ɓalle store a fito da shinkafa da mai Hajiya, ayi lafiyayyen girki kowa yaci ya goge wuya, wala Allah ya samu adda'a ko?" Hajiya Kubra tace. "Kasan komai ya shiga gado fa Auwal kubi a hankali, kar a kuma ɗakko Saniya gaskiya, duk da nasan anan Ghana gidan mutuwa yafi wani gidan bikin ma, amman abi a hankali " Dariya yayi yace. "Haba Hajiya, giwa fa ta faɗi ai sai cin nama. Gayennan ya fa tara dukiya wallahi bana wasa ba, kuma mun gasu. Ai ni da an yi rabon gadonnan ƙasar zan bari ma" Harara Hajiya Kubra ta zabga mishi ba shiri yayi shiru. Haka kuwa akayi, aka kada ƙatuwar Saniya aka yanka. Aka shiga gidan maƙota aka shiga girkin shinkafa da miya da nama sutu_sutu. Rayuwa kenan yau ina wanda ya tara? Babu shima bai ciba, gashi yanzu za'aci ba lalle bane ya samu masu yi mishi adda'a ma. Kafin yamma Mariya ta haifi yaronta namiji tubarkallah. Ni kuwa a tsaitsaye nake naƙudar tawa. Bamu muka samu kanmu ba sai da daddare. Ina ɗakina ina cin tuwon shinkafa miyar egusi, taji naman kan saniya, ta yi mugun daɗi sosai. Ni dai a daren ban yi bacci ba, ina zaune a kan sallaya ina addu'a. Ciwo yana ta tsikarata, a haka har gari ya waye, da nayi Sallah kuma muka koma falon Alh Liti da zama. MRS BUKHARI CE [21/08, 3:16 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 59 Muna zaune a babban falon ƙasa da masu zuwa gaisuwa, aka soma shigo da dumamen tuwon shinkafa da miyar Egusinnan, mutane sai ci suke ana hira kamar ba gidan mutuwa ba. Auwal ne ya leƙo yake sanar mana dangin Alh Liti suna hanyar zuwa daga Sokoto, tsofaffin matan Alh ma sunata kiran ƴaƴansu suma fa suna hanya. Shaguna da store_store na kayan masarufi na Alh dake kasuwa duk aka bada umarnin a rufe. Da rana taliya da bushasshen kifi akayi ma baƙi, mu kuma akayi mana jallof rice mai daɗi taji soyayyen naman saniya. Da misalin ƙarfe ukun yamma naƙuda taci ƙarfina dan ko iya tashi na kasa yi. Ana cikin wannan halin su Mama suka iso. Sai mata_ matan da suka cika falonne suka firfice, su Mama da Hajiya Kubra suna kaina, ni kuwa sai kwakwa nake faman ci, cikin ikon Allah a cikin awa guda na haihu, tunda kwana biyu kenan ina naƙudar a tsattsaye dai. Ai kuwa sai ga ɗana namiji sunkucecen gaske na haifa. Mama ce tayi ma jaririn komai, Asiya kuma ita ta kwashe ƙazantarnan ta haihuwa ta zuba a bokiti ta fita tsakar gidan. Ni kuma Hajiya Kubra ta raka ni ɗakina. Ni dai ina kwance ƙwalam sai ga Mama ta shigo da jaririn a hannunta ta naɗeshi da hijabinta. "Zubaina ashe ciki ne dake shine ƴannan baki faɗa ma kowa ba? Iko sai Allah, wai Alh Liti naji anata zancan wai ɓarayine suka shigo har ɗaki suka kasheshi. Kwana ya ƙare ya bar baya da ƙura wannan bataliyar yara daya tara haka, amman zaku kwashi dukiya. Hmmmm ni dai naji daɗi da Allah ya yanke miki wannan wahalar, ya sake dubanki ya yanke miki takaba kuma. To Allah yasa ƙarshen wahalar kenan, Zubaina muna ganin rayuwa wallahi, abinci fa wannan da ba dan kawunku Tanko ba wallahi da bamu isa munci ba. Sai Asiya da take son ta soma aiki a gidan wata mata, dan mu rufa ma juna asiri. Matar Musa ta gama mallakeshi nera biyar Musa sai dai ya bamu a ɓoye, ke wata rana sai dai ya siyo mana dafaffen abinci ya zuro mana ledar abincin ta taga fa." Hawaye Mama ta shiga sharewa kawai tana jin zafi a zuchiyarta na rabata da ɗanta da suruka tayi. Haƙiƙa na cuci mahaifan Bulama dana raba su da ɗansu, irin wannan kukan da Mama take yi a gabana Hajja tayi irinshi da yawa a gabana. Mama kiyi haƙuri, a hakan ma mun samu da sauƙi, fatanmu Allah ya yafe mana dukkan kura_kuranmu. Zan je in samu Bulama da iyayenshi, da Yahanasu su yafe mun cutar dasu da nayi ko zanga haske a gaba." Asiya ce ta shigo da bokitin ruwan zafi a hannunta. "Mama ga ruwan wankan yaron, Anty Zubaina Hajiya tace kije kiyi wanka an kai miki ruwan wankan. Kuma wai dangin mijinku sun iso, in kin gyara jikinki sai kije ku gaisa" Da ido na bita, ta rame sosai, idanta zuru_zuru dasu, kamar ba Asiyar dana sani ba. Amman naji daɗin ganinta akan ƙafafuwanta. Fita nayi tsakar gidan. Kai tsaye ban ɗakin na nufa na gargasa jikina na fito. Na fito na samu su Mama sai cin haɗama suke ma taliya. Wasu siraran hawayene suka surnano akan kuncina. Koɗaɗɗiyar goduwar rigar wani lace na zura, na fito da wani koɗaɗɗen hijabina na saka. Mama ko zamu je tare mu gaishe da dangin Alh?" "To sai mu je ai Zubaina, Asiya taso muje." Tare muka fita zuwa falon Alh. Ƴan uwanshi daka gansu ba sai an baka labari ba, sun yi kama kusan su takwas su ka zo. Maza huɗu mata huɗu. Nan muka shiga gaisuwa, tare da ma juna ta'aziyyar Alh. Na dubi Mariya nayi mata barkar haihuwa, itama taimun. Kafin mu fito tsofaffin matan Alh Liti suka soma hallara suma Allah yayi yawa dasu, kuma ko wacce da ƙwanta a gida gadon ɗanta tazo ma. Bani na samu kaina ba sai bayan isha. Ina zaune ina cin abinci a ɗaki, muna taɓa hira dasu Mama. Asiya sai ƴan biyu take ba abinci a baki. Haka dai zaman makokinnan yaci gaba da gudana, sai tattaro dukiyar Alh Liti aketayi, dan ance ranar sadakar arba'in za'a raba gado. Ranar sadakar bakwai Amaryar Alh Liti ta haifo ɗiyarta mace itama. Ranar da Alh Liti ya cika kwana goma kowa ya saki jikinshi, har ana taɗin yanda za'a fantama in anyi rabon gado. Duk yaran Alh Liti sun dawo gida, har da waɗanda suka tafi karuwanci duk sun dawo domun karɓar gado. Tsofaffin matan Alh da danginshi ba wanda ya tafi, kowa ya kafa ya tsare, Nabeela kuwa hannu da hannu na danƙa mata ɗanta da yake mun kallon uwa, sai godiya take zuga mun. Ranar ko da Alh Liti ya cika arba'in a ranar malamai suka soma rabon gado bayan anyi adda'ar arba'in da sadakar su cincin da waina. Rabonnan aketatayi, har zuwa la'asar kafan aka kammala, a ranar naga wasu irin mahaukatan kuɗi da suka sa tsigar kaina su kai ta tashi, gasunan buhu_buhu jaka_jaka. Mu matanshi mu aka soma cirema kasonmu, aka kididdiba mana bayan an cire bashin da ake bin Alh Liti wanda ya kusan lashe rabin dukiyar daya mallaka, amman fa duk da haka dukiyar batai rawa ba, dan akwai gidaje, filaye, garke_garken shanu duk suna rubuce a hannun malamai. Bayan an raba mana namu, Sannan aka raba ma yaran gidan ihu maza da matan suka saka sabida tsabaragen miliyoyin da suka samu, burin mazajen yaran gidan ya cika, dan dama ance duk dan sabida dukiyar Alh Liti suke zaune da yaran, irin wannan ranar suke jira. Dangin Alh dake jahilaine suma jira suke ace ga nasu. Da ba'ace ba, nan tarzoma ta tashi sai waje aka fitar dasu. Mu mata_matan Alh duk mun yarda a siyar da kadararmu data yaranmu a bamu kuɗaɗenmu. Amman mata_matan da suka yi aure an basu shawarar kar su siyar suci gaba da juyawa. Dama maza_maza ba'a maganarsu dan zasu ci gaba da kasuwancin da mahaifinsu yake yi ne. A cikin sati guda aka siyar mana da komai aka danƙa mana kuɗaɗenmu, naga miliyoyin kuɗi cike da jaka. Washe gari ni da Mariya muka fito dan tafiya gida. Hajiya Kubra zata ci gaba da zamanta tare da yaranta a Ghana amman ba'a wannan gidan ba, dan gidan bai fito a gadon yaranta ba. Ni dai nai ma kowa sallama muka kama hanya. Kuɗaɗennan muka samu jakunkuna muka rarraba kuɗin muka bisu da tsummokarai a sama. Mama na goye da Hassana, Asiya ta goya Usaina, ni kuma ina goye da mai sunan Alh a bayana, babu abunda na ɗauka a gidannan duk tsummakaran kayana da su kai ragowa anan na barsu. Motar wani malamine ya rakomu har Airport yai musu bayani ni dai bansan mai yace musu ba, anan yai mana sallama. Sanda na zauna a kujerar jirgi kuwa idanuna a rufe suke ina kukan farin ciki, wani irin daɗi nake ji. Da muka sauka a Lagos sai daɗi ya kuma shigata ina jiyo ƙamshin arewa. Kai tsaye tashar mota muka nufa dan muna tsoron kar a tuhumemu dangane da kuɗaɗen da muke tafe dasu, Najeriya macuta sunyi yawa. Motar tare muka faɗa abinmu. A mota muka kwana cur,. Da na ganni a ɗakin Mama sai da nayi sujudur shukur, ina ɗagowa na yanke da kukan da ni kaina na kasa tantance na daɗine ko akasin hakan. Nayi farin cikin ganin dangina sosai, har kawu Tanko shima yazo yi mun ta'aziyya da shi da Goggo Safiya. Su Mama zakiya duk kowa yazo. Bayan na nutsa ne yau na shirya inason zanje in duba Mabaruka a asibiti. Liti na saka a baya na fito. A tsakar gida na samu Mama a zaune tana gyara kayan miya, Asiya kuma tana hura gawayi. Matar Musa kuma tana tsakar gidan tana wanki sai yarfo ma Mama ruwa take yi. Ayi magana ta nemi zagin mutane, ko Mama tace mu barta duniya ce. Mama zanje asibity in duba mabaruka bazan daɗe ba" "To Zubaina dan Allah ki gaisheta da jiki" Sallama nayi musu na fice. Ganin Mabaruka ya ɗaga mun hankalina sosai, tana kwance da robar lumfashi a fuskarta da wasu na'urori suna aiki a jikinta. Bata sanin ma wanda yake kanta. Ina sharar hawaye sai ga Adam ya shigo shida yaran Mabaruka da matarshi Sagira. Sun zama masu kuɗi gasu nan gwanin sha'awa. Ni kuwa a mugun kunyace na gaishesu, Sagira kuwa da fara'arta ta gaisheni, ina bani da guiwa anan suka tafi suka barni jikina a mugun mace. Dubu ɗari biyu Adam ya ajjiyema mamansu Mabaruka suka fice." Yobe: Yahanasu Fitowata daga ma'aikata kenan inason zan nufi shago akwai Amaryar da zan yi ma gyaran jiki. Sanye nake cikin wata baƙar abaya wacce take daga ire_iren kayan da Bulama Babba ya sai mun. Sabida son Bulama Babba yasa na soma ƙaunar baƙaƙen kaya nima. Motata na shiga ina sauke nunfashi, na sa hannu zan murza keyn motar kenan Alh Nura ya ƙaraso bakin tagar motar. "Haba Yahanasu yanzu kenan ba da ban ina hangoki ba da shikenan tafiya zaki yi ki barni kenan? Na ɓata lokaci sosai ina jiranki, kwanana nawa ina baro office ina zuwa wajanki, amman kin ƙi bani dama" Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Alh Nura nayi jim. A zahiri yana da kamala gashi yana da kyanshi dai_dai shi gashi da haske. Ni har mamaki nake yi to mai yake nema haka wai a wajena da har ya nace mun? Duk da ni kaina nasan munina ya ragu, sabida gogewa babu abinda bata ɗaukewa kuma ina yin gyaran jiki ka'in da na'in, girman shekaru ya sake murje munina, kuma ina gaye fiye da yanda nake a baya, dan shima yana shafe munin ɗiya mace, kwalliya wani babban jigone na ɓoye munin mace mata ku kula da wannan, baƙar fatata har wani walƙiya take yi tamkar jikin kulɓa sabida tsabaragen gyaran da nake yi duk sati, da wata irin haɗin dilka ta bare bari mazauna sudan ( nima ina da ita duk mai buƙata ya tuntuɓeni, in kina amfani da'ita babu ruwanki da shafe_shafen mai, ko wani sabulun gyaran fata mai so ta tuntuɓeni) Ajjiyar zuchiya na sake saukewa, ni tsoron bama wani namiji dama nake yi, gani nake kamar zan koma ɗakina. Duk da naji labarin Yalewa matar Bulama Babba ta kusan haihuwa, kuma na ji labarin yadda take azabtar da su Bawa, duk abinda yake faruwa dasu ina jin labari a bakin Mama Gana. Alh Nura kayi haƙuri wallahi har ga Allah na mance kana jirana. Kuma gashi sauri nake yi ana jirana a shago ko zamu bari gobe ma yi maganar?" Da sauri Alh Nura ya tari nunfashina yace. "Ni sai in biki a baya in kin ban dama, inaso yau mu kawo ƙarshen komai" naso in samu in kubce amman fur Alh Nura yaƙi. Ni kuma ban iya musu da babban mutum ba, tsakaninmu da manya girmamawa ce" Motarshi ya shiga ya dinga bina a baya. A hankali na dinga tafiya gabana na faɗuwa nasan ma cewa zaiyi yana sona. Wasu hawayene suka shiga tuntiri akan fuskata. Shikenan abu kamar wasa shekara guda da rabuwata da Bulama Babba, yana ganina ina ganinshi amman sai dai in mai kallon wa, yai mun kallon ƙanwa? Innalillahiwainnailaihilrajiun Allah ka iya mun, ka sassauta mun soyayyar wannan bawa naka, shima ka sassauta mai irin wannan so da yake mun, Bulama masoyine na haƙiƙa. Da waɗannan zantuka na iso shago. A gefen shagon na yi parking motar Bulama Babba na gani a ƙofar shagon, sai da gabana ya yanke ya faɗi, ji nake kamar nayi laifi ina kallon bakin shagon muka haɗa idanu da Bulama Babba mu kai ma juna kallon ƙuda. Alh Nura ne ya buɗe mun murfin motar tawa, harda murmushin shi. Da sauri na kalli Bulama Babba naga yana rarraba idanu a tsakankanina da Alh Nura. Jikina a sanyaye na fito, ya rufe motar. Ƙafafuwana har rawa suke yi sanda nake nufar cikin shagon. Kafin in ƙarasa bakin shagon Bulama Babba ya shige ciki abunshi. Tare muka shiga da Alh Nura cikin in da baƙi maza suke zama, dan wasu su ke kawo matayensu, ko ƴaƴansu, ko budurwayensu. Bismillah ka zauna ga waje" Na nuna mishi kusa da Bulama Babba. Zama yayi ni kuma cikin dakiyar zuchiya na kalli Bulama Babba da Ahmad nace. "Yau Bulama Babba kune a shagon nawa, ko madam kuka kawo mun in mata gyaran jiki?" Bulama Babba ya haɗe ranshi tamau, bai ko kalleni ba saima juyawa da yayi ya miƙa ma Alh Nura hannu. Ahmad ne yace. "Ai Khairat muka kawo gyaran jiki amaryata kenan ai. Ba dai ke kin watsar damu ba, ko irin zuwa duba yara sam bakya yi kin zama Hajiya, ko wanne gida son kasancewa tare dake suke yi a telebijin ɗinsu." Ɗan murmushin yaƙe nayi nace. Ba haka bane, yanayin aiyukanne basa bani damar in samu lokacin kaina. Ko Damaturu ina jimawa ban shiga ba. Ashe Khairat amaryarmu ce ai ban sani ba." Alh Nura na kalla, shima naga fuskarshi ta nuna rashin jin daɗi, sai kuma naji babu daɗi sam sai nace. Alh Nura waɗannan yayyenane" Sai lokacin ya saki fuska suka sake sabuwar gaisuwa. Nima na gaishe da Bulama Babba, a daƙile ya amsa, yana gama amsawa ya miƙe tsaye. "In an gama mata kyaran jikin ma dawo mu ɗauketa, Ahmad muje ko?" Musabaha suka sake yi da Alh Nura kafin su tafi. Shi kuma nasa aka bashi tea kafin in shiga ɗakin aiki. A ciki na samu Khairat harma an soma rage mun aiki. Ban yi wata wata ba, na saka kayan aiki na hau dirzarta ina shafe mata jiki da dilka haɗin ƴan sudan. Bayan na gama na sata a burƙha domun in turara mata jikinta. Duk wannan abunda nake yi, zuchiyata tana wajan Bulama Babba, banji daɗin yanda ya tafi yana fishi dani ba sam. Hannu na wanke kafin in shiga ɗan ofishina naima ɗaya daga cikin ma'aikatan shagona magana nace, ina da baƙo a ɗakin baƙi, ai mai iso office ɗina kafin na wuce. Ban daɗe da zama ba sai ko gashi ya shigo da sallamarshi. Waje ya samu ya zauna a 2 sitter yana fuskantata. Ina jinka Alh Nura, ina bakin aikine na sake nace bari in baka lokaci. Kyaran murya yayi. "To Yahanasu dama ba goduwar magana bace, ni dai ma'abocin sauraren shirye_shiryenki ne a ko da yaushe bana missing program ɗin ko sau ɗaya. Daga haka sai naji na soma jin kina burgeni. To sai nasa a ka ɗan mun ƙaramin bincike aka tabbatar mun baki da Aure. Hakanne ya bani damar zuwa inda kike. Ba wani abun bane sonki nake yi har ga Allah da Aure. Kinga ni ba yaro bane, aurenki nake son yi in kin amince, ina da mata da yarana biyar" Sai ya yi shiru yana mai da yawu. Nima nayi shiru kamar ruwa ya cinyeni shurun yayi tsayi sosai. "Kaddai na ɓata miki ranki ne Yahanasu naji kinyi shiru?" Sai lokacin na ɗago raina a dagule nace. Kayi haƙuri ni ban shirya faɗawa wata soyayyar ba gaskiya, sannan a gidanmu auren zumunci muke yi, bazan iya auren wani bare a waje ba. Nagode da soyayya sosai, amman kayi haƙuri " Tarar numfashina yayi da cewa. "Mutum baya ƙin ta mutum ance da ɓarawo ya ruga. Abunda nake so dama ce kawai. Ki taimaka ki bani dama in ɗan kutsa kai cikin rayuwarki, in sha Allah bazan cutar dake ba, ba zaki yi kaicon rayuwarki dana shiga ba. Ko gaisuwa ma dinga yi" naso yin musu, danni sallamarshi naso yi baki ɗaya. Amman sai ya dinga magiya sai kunya ta kamani, dole na bashi number wayata ko dan mu rabu lafiya. Cikin jin daɗi ya yi mun sallama. Nima na koma bakin aikina, ina ta tunane_tunane. Kafin yamma khairat ta sake ta sake yin wani irin haske. Kai Amarya gaskiya kinyi kyau, yau dai mun gama da ke, sai kuma gobe in Allah ya kaimu. Ashe wana zaki aura? Ai Ahmad yayanane, ni bansan kece Amaryar Hajara ba" Ɗan murmushi tayi tace. "Nagode sosai Anty, barin in kira baby yaxo ya mayar dani gida" Kai na jijjiga yanda naga tana wani irin gwalangwaso nasan za'asha cabta da Khairat da Hajara. Office nayi komawata na zauna, ina duba takadda dan ganin gobe aiki nawa muke dashi. Ina cikin wannan aiki naji an turo ƙofar office ɗin. Bulama Babba ne ya shigo yaima kanshi masauki. "Wato har kin soma kula samari bakya fatan mu sasanta da Hajja ki dawo ɗakin ki ko, duk fafutukar da nake yi ashe ke soyayyarki kike sha abunki. Banyi tunanin zaki mance dani ba. Jibi yadda na zama duk dan sabida ke, dame kike son inji da jarabar Yalewa ko da kishinki? Kullum fa saina ba Hajja haƙuri kuma ina san zaki goma ɗakin ki" Idanu na ƙura mishi har ya gama maganarshi tsab, nama rasa me zance mishi sabida gani nake yi kamar ma ya raina mun wayau. Shi yana can da matarshi harya ɗirka mata ciki, amman ni so yake in tsofe a gida inta jira har sai sanda Hajja zata ce ta amince mu dawo da aurenmu, taya ma hakan zai yiwu?. Hmm Bulama Babba kenan. Oh so kake inta zama ina jiran tsammanin zan koma ɗakinka? Ai tuni nayi haƙuri da kai daga lokacin dana ga Yalewa da titsetsen cikin ka a jikinta. Kaga halamu sun nuna kuna shan romon soyayya ni kuma kana son cika ni da romon baka ko? Kaga ina mugun ganin girmanka kuma kana da babban matsayi a rayuwata, ka riƙe wannan matsayin dan Allah, bazan taɓa iya komawa gidanka ba na riga na gama jinyar sonka" A fusace ya mike tsaye yana nuna ni da yatsa kamar zai mare ni. "To ki sani baki isa ki kawo mana bare ba, gara tun wuri ki sallameshi dan ba zamu aura mishi ke ba in dai nine a matsayin wa a gareki. Ɗakin ki zaki koma, ya kamata ki tausayama yaran ai ko Yahanasu suna bukatarki nasan kin san komai, so kike sonki ya halaka ni, a gabana kike ma wani namijin kallon soyayya, ko dan kin zama tauraruwa shine kike ganin kamar kin fi ƙarfina ko, sabida kinga al umma ke suke son ji da gani?" Fuu ya fice, da sauri na bi bayanshi amman kafin in fita Ahmad ya ja motar fuuu sun bar ƙofar shagon. Kaina na dafe da yake mun mugun ciwo, to ni ya akeso in yi da raina ne, Hajja bata sona kallon ƴar iska ƴar shaye_shaye take mun, gashi tana ganin kamar ni na kashe mata mijinta, har abada bana jin zata dena mun wannan kallon gara in yi aurena nima in huta kawai" Haka kwana biyu na kasance sukuku, Mama Gana sai aukin tambayata take yi inai mata ƙaryar aikine yai mun yawa a wajan aiki. Shi kuma Bulama Babba ya shiga aikin sintiri a tsakanin shago da gida ya hanani yin saƙat, ko yaita kira na a waya, da yaji number busy shikenan zai ta turo tesa_tesai na soyayya. Ga Alh Nura shima kullum a cikin tarairayata yake a waya, duk da dai bamu sake haɗuwa ba, amman kullum yana kirana sau biyu a waya, bama waya mai tsayi sai dai yana zube mun kalamai masu tsaiwa a kahon zuchiya. Ko bikin Ahmad ban je ba, Hajara dai tazo ƙunshi da gyaran jiki shago. Bayan bikin da sati uku Yalewa ta haifi ɗanta Namiji, ban je barka ba, amman na kira Bulama Babba nayi mishi barka, na kira ƴan Damaturu suma nayi musu barka, Hajja da ƙyar take amsa gaisuwata tsabar jin haushina da take yi. Ranar suna na fito cikin sauri inason fita wajan aiki na tarar da Mama Gana a falo tana zuzzuba mun turarukan wuta a kwalabe. "Har kin fito agogo sarkin aiki? To zo ki zauna mu ɗan tattauna Bulama Babba ne ya kawo mun ƙararki." Gabana ya yanke ya faɗi dawowa nayi a sanyaye na zauna. "Yahanasu nace ashe samari kike tarawa a shagon naki dama ni banda masaniya?" Da sauri na ɗago na dubeta da mamaki nace. Samari kuma Mama Gana, ni wallahi bana tara samari" "To Bulama ne ya ce wai kina tara samari a shago, ya kamata in miki faɗa, shi shine maɗaurin aurenki bazai bari ki auri bare ba. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba kamar zai yi mun kuka anan. Kishi ya gama rufe mai idanunshi ainun. To mu dai ba zamu hanaki auren bare ba, amman mu munfi son ki auri ɗan gida zancan gaskiya kenan. Akwai maza a cikin gidannan, ga wasu a Damaturu ya kamata ki basu dama su bayyana kansu. Sabida zaman haka bazai yiwu ba ni kuma ko Hajja ta sakko tace Bulama ya mayar dake. Wallahi Allah bazan yarda ba ni, sai dai ayi duk abunda za'ayi ai taci mana mutunci ƙiri_ƙiri muna gani. In akwai wani bare da yake zuwa wajanki ki dakatar dashi kawai tun wuri zai fi miki, anan gidan nawa ma kina da miji ai kin sani sarai yana sonki. Ki tashi ki tafi. Bazaki sunan matar Bulama bane ko kema kishin ne? Ƴan Damaturu suna hanya" Ɗan dariyar yake nayi kawai nace. Zan zo in na baro ma'aikata labaran safe kawai yau zan gabatar." Adda'a ta bini dashi harna ƙule. Ina tafe a mota ina mamakin Bulama Babba, so yake in ta zama kenan ni kar in yi aure haka yafi so ko? Da ace yau daya rabu dani bai yi wani auren har yayi ma mace ciki ba, da nima sai in zauna in iyaye suka ga zamu tsofe ba auren sa dawo mana da aurenmu. Ni nasan wannan itace ƙaddarata a sakamakon ƙin karɓar ƙaddarata da nayi, ya Allah bazai jarabceni ba? Da banyi shaye_shaye ba nayi imani da yanzu ina gidana ina farin ciki, da yanzu nice na haifama Bulamana yaro. Kukane yaci ƙarfina. MRS BUKHARI CEGAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 60 Sai da nayi kuka ishasshe sosai sannan na share hawayena na shiga ma'aikata domun gabatar da labaran hantsi. Haka dole na ɓoye damuwata na soma ragargazo labarai ina yi ina jinjina irin yadda ƙasarmu ta lalace da tsadan abubuwa, masara wannan kuɗinta ya ninku, ga kayan miya yayi tashin gwauron zabi, al'umma sunfi ta'amali da bushasshe a halin yanzu fiye da ɗanye. Minti arba'in na ɗauka ina labarai kafin na ƙarƙare na fito. Yau ban tsaya ɓata lokaci ba sam shago na wuce bayan nayi cike_ciken takaddu a wajan aiki. Wata mai jego nai ma gyaran jiki, zuwa azahar muka kammala, na bar shagon za'ayi mata ƙunshi da kitso, ni kuma na nufi hanyar gidan Bulama Babba. Tun safe su Fanna suka kirani suna sanar dani isowar tasu. A bakin wani kanti na tsaya na durzarma jariri kaya masu kyau guda uku da takalmi, nera dubu arba'in da hudu na kashe musu sannan na kama hanya. A babban falon gidan na tarar da ƴan uwana an baje anata tiƙar hira. Ƴan uwan mai jego sai kai komo suke a tsakankanin ciki da falo. Cikin ƴan uwana na ƙule na saki jiki muna ta hira kamar bani da damuwar komai. Amman a baɗini ji nake kamar in fasa ihu. Ana cikin haka Ya Bagulaji ta fito falo in da muke, zamanta ke da wuya aka biyota kici_kici da abincinan suna. Fried rice su ka yi da coslo, sai tuwon shinkafa miyar egusi da ganda, sai kuma biski da miyar taushe, banda lemukan gora da ruwan gora, ga sobeniya da suka yi na jaka shaƙe da tarkace, buhu ɗaya aka bamu an san yawa ne damu ga haɗin kai, ɗaya bazai yi amfani dashi ba in ɗan uwanshi bai samu ba. Sai da aka ƙirgemu tas. Ni dai ruwa kawai nasha, banci wannan abincin sunan ba. Bayan sun kammala na ja Fanna ta raka ni wajan mai jego. Hamshaƙiyar dana ganta tsurewa nayi, har wani mugun zazzaɓine ya rabkeni lokaci guda. Tayi kyau gaskiya sai dai maƙiyi gata fata irin ingarmun matan Kanuri, tasha adon lace da ɗan ƙaramin gwal a wuyanta. A daddafe ta amsa gaisuwata ni dai nayi barka muka fito, sai wani harararmu take yi tana yatsina. Ni dai nasan a yanzu nafi ƙarfin yatsinar fuskar wata mace, danni a cikin kanurin ma ƙamshina ya fita daban, ƙamshina ya na kwana biyu a waje in dai na shiga na zauna ƙyan fata kuwa baza'a nuna mini ba, sai dai a fini farar fata. Kayan dangin miji muka soma haɗawa a falon. Sai da akayi mata turamen zani kala arba'in, kayan yaro kuwa ba'a magana, sabulu omo jingim haka famfas ma. Surukan gidanmu ne suka ɗauka Ya Bagulaji da Ya Gaji suka jagorancesu wajan kai kayan ciki, a hannun manya suka danƙa kaya sai son Barka. Muna zaune su Bulama Babba suka shiga tare da su Bulama ƙarami, da su Ahmada. Tsakiyarmu suka shige anata hira. Ni da Bulama Babba sai kallon_kallo muke aikama da juna na tsantsar soyayya. In nace bana tausayinmu nayi ƙarya, Bulama Babba ya rame sosai a kullum baya cikin walwala da nutsuwa sam, baya rasa nasaba da rashin zaman lafiyar da suke yi da matarshi, da kuma rashina a kusa dashi. Haka dai mu ka gama suna aka watse, wajen motata Bulama babba ya biyoni yace. "Yahanasu wallahi sau ɗaya tak na kusanci Yalewa shima rabon yaronnan ne yasa har na kusanceta, a daren da abun ya faru ji nayi kamar in ban kusanci mace ba mutuwa zanyi. Sai naga ai bani da zaɓi daya wuce in kusanci Yalewa ko ba komai ai matatace. Amman naga kin ɗauki fishi dani, babu macen da ta'isa kai ki matsayi a rayuwata. Na soki kuma da sonki zan koma ga mahaliccina. Ki ma Allah ki dena ƙona mun zuchiya ta hanyar sauraron Alh Nura. Ni dai ban iya ce mishi komai ba, a wajan na tafi na barshi ya saki baki yana mamakina. Ni da Alh Nura abu sai gaba yake yi, tun bana damuwa dashi harna soma, tun bana jin sonshi har na soma ji dai, daga haka soyayya ta ɓalle a tsakaninmu. Ana cikin haka muka tashi da mummunan labarin Bulama Babba yana asibiti Yalewa ta farke mai ciki da wuƙa ta tsallake ta gudu gidansu, shi kuma yana babban asibiti rai a hannun Allah. Ranar munji tashin hankali bana wasa ba. Kan kace me ƴan Damaturu suka ɗau motoci suka nufo Yobe. Ni da Mama Gana da yaranta mu muna asibitin, anƙi barinmu ma mu ganshi. Ahmad ne da Hajara suka kawo shi asibiti, sai da suka kira ƴan sanda tukunna aka yadda aka karɓeshi. Har dai su Ba Modu suka iso ba'a shiga ɗakin da Bulama Babba yake, bamu san a wanne halin yake ba. Ba Modu yana hawaye yace. "Wakil kaini ɗakin ganawa da likita muji shin mutuwa yaronnan yayi ne suke ɓoye mana ko yaya? Ke kuma Hajja ki sani sai nayi shariya da wannan yarinyar ke in ma ta kama harda ke zanyi shari'a baki isa kin ka an kashe mun yaro ba.." Wakil ya kama hannun Ba Modu suka tafi ganin likita Ba Modu sai haki yake yi. Nan Mama Gana ta dinga ma Hajja jaraba ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Ana cikin haka Ba Bature ya ƙaraso shi da Hewa. Muna nan jigum muna jiran me kaje kazo. Su Ba Modu ma basu samu damar ganawa da likita ba. Ni dai adda'a kawai nake yi. A firgice wani Dr ya fito daga cikin ɗakin da Bulama Babba yake. Gabaki ɗaya shi muke kallo, Ba Modu kuwa harya ƙarasa in da yake. Buɗar bakin Dr yace. "Baba ayi haƙuri" Wani irin zabura nayi na isa gaban likita nace. Me kake nufi da ayi haƙuri mutuwa yayi ko me?" "Ku kwantar da hankalinku, aiki zamu shiga dashi yanzu, Baba kaine zaka sa mana hannu ko waye? Amman fa sai kun taya shi da adda'a dan da ƙyar bawan Allahn nan yayi rai" Ajjiyar zuchiya na sauke, hajja kuma tana gefe sai kuka take yi Ba Bature na rarrashinta. Ba Modu ya shiga yasa hannu a takaddar aiki suka fito. "Wakil inaso kai tsaye ayi magana da lauyoyi a shigar da kara kotu, dole mu ɗau matakin shari'a, da yanzu wannan abun yazo da tsautsayi shikenan yaronnan da mutuwa zaiyi lokaci ɗaya? To wallahi bazan yarda ba, yanzun ma ai kunji abunda likita yace, cewa fa yayi ba lalle ya tashi ba." Ba Bature yana jin haka yace. "Modu kai mun rai dan girman Allah. Wallahi ni bazan so hakan ta faru ba wannan abun duk na gidane, yarinya bata kyauta ba kuma zamu ɗau ƙwaƙƙwaran mataki akan hakan. Ku yi haƙuri. Hajja kuyi haƙuri dan girman Allah ban taɓa tsammanin ƙiyayyar da Yalewa take ma Bulama ta kai rabin haka ba." Da haka dai magana ta mutu da ƙyar duk da Ba Modu yace sai an ƙwato ma Bulama hakkinshi, haka muka wuni a asibitinnan, bayan an fito da Bulama Babba daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu, nan aka buƙaci za'ayi mishi ƙarin jini. Wakil da Ahmada ne suka ba da jininsu aka ƙara ma Bulama Babba. Ba Modu yai ta hidima da Bulama Babba, dan karewarta shi ke jinyar shi. Hajja kuwa sai kuka take tana roƙon a yafe mata a bisa sawa da tayi Bulama Babba ya sake ni. Ita tayi nadama, ita sai dai a dawo da aurenmu kafin ma Bulama Babba ya farfado. Ni kuwa nayi fur nace ai ina na riga nayi ma wani alƙawari na bushe idanuna. Ba Modu shi kuma yace babu mai yi mun dole a karo na biyu. Mama Gana tace nayi mata dai_dai , sai an ga Bulama Babba a cikin wani hali akeson ni in raɓeshi dan ayi amfani dani kamar yadda akayi a baya. Haka dai akaita jinyar Bulama Babba, yana farfadowa ya rubuta ma Yalewa takaddar sakinta, Wakil aka wakilta ya kai musu har Damaturu. Satin Bulama Babba shida a asibiti aka sallame shi, kai tsaye Ba Modu yace a wuce mishi dashi damaturu. Hakan ko akayi muka ɗunguma sai Damaturu, a turakar Ba Modu aka ajjiye Bulama Babba, sai nan nan Ba Modu yake yi dashi. Kunyar duniya ta ishi Hajja. Gashi Ba Bature ya turmushe mata kuɗaɗenta, wasu kadarorin ma ya sasu a kasuwa ya karɓi wasu kuɗaɗe daga ciki. Sai Ba Modu ne ya biya kuɗin kadarorinta suka dawo hannunta. Wallahi kunyar wannan abun yasa ta kwanta jinya zanga _zanga, a lokacin Bulama Babba ya warke fes yana shirin komawa Yobe, ni kuma soyayya muke ci da Alh Nura sosai. Rashin lafiyar Hajja ya ɗagama kowa hankali dan harta soma barin wasiyya." MRS BUKHARI CE[23/08, 12:00 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: Gawurtattu uku 61 Kaduna: Kofur Zubaina: Yau da safe na shirya na koma asibiti domun duba jikin Mabaruka. Jikin babu laifi na same ta a zaune tana shan tea. Bayan mun gaisa da Mama sai ta bamu waje, a gefen gadonta na zauna. Ya jikin Mabaruka inata zuwa amman kina halin da baza ki iya gane wanda yake kan ki ba" Buɗar bakin Mabaruka tace. "Ki matsa Zubaina kar in shafa miki cutar ƙanjamau ƴan uwana ciki ɗaya ma ƙyamata suke yi. Kinga yanda rayuwa ta mai dani ko? Naki mai sauƙi ne Zubaina, ni ciwo yaci ƙarfina ba lallai bane in rayu. Zubaina ki nemi Bulama ya yafe miki da danginshi. Adam da Sagira sun yafe mun jiya da suka dawo dubani, naci albarkacin yarana." In banda kuka babu abunda nake yi, tsoron Allah ya sake shigata sosai na sake tsinkewa da lamarin duniya ainun. Ina asibitin har yamma, sallama aka basu tare dani muka je gidansu bani na baro gidan ba sai bayan isha. Ina komawa gida na jawo jaka na soma haɗa kaya. "Wannan jakar fa Zubaina" Mama ta tambayeni. Inaso gobe in Allah ya kaimu ne in je Damaturu gidan su Bulama in roƙi gafararsu da su yafe mun Mama, in da hali Mama ku raka ni dan Allah." Mama na share hawayenta tace. "Zamu je dukkanmu Allah ya kaimu goben. Amman wannan kuɗi na gadon yarannan me kike ganin ya dace ace anyi dasu Zubaina kinga muna ta zara?" Jim nayi mata nace. Ina ga kawu Tanko zan je in danƙama ya dinga juyawa ana tarama yarannan riba, in ma bazai yi ba zai bamu shawara mama. "Hakan yayi gaskiya dan Tanko mutum ne harda ɓari, to shikenan" Washe gari. Sassafe muka fice a gidan ko sallama ba mui ma Musa ba balle matarshi. Tasha muka nufa muka shiga motar Damaturu. Mun sha tafiya sosai, wajajen bayan azahar muka isa cikin layin su Bulama. Gabana sai faɗuwa yake yi, ji nake kamar ƙasa ta dare in faɗa ciki dan kunya. A mugun kunyace muka shiga cikin gidan. A falon mahaifiyar Bulama aka saukemu, muna zaune Bulama ya shigo da Sallama idanu muka haɗa dashi gabana ya yanke ya zube. Idanu ya bimu dashi kamar bai sanmu ba, shirin shigewa ciki yake yi Mama tace. "Bulama wajanka muka zo dan Allah ka tsaya ka sauraremu" Cak ya tsaya, amman fa bai juyo ba. Ba Modu ne yayo sallama ya shigo falon, dan jiranshi akayi akan yana da baƙi. Waje ya samu ya zauna, Bulama ya juyo ya samu waje a ƙasa ya zauna. Yahanasu ta shigo da sallama hannunta riƙe da Bawa da Maryam Yusuf ne ya soma shigowa da gudu ya je wajan Ba Modu. Idanu na ƙura musu su ukun dukkansu. Itama ni take kallo ta kasa motsa ƙafarta ma. " Uwata zo ki zauna. Bawa ga mahaifiyarku kuje gareta maza " Sakin yaran tayi suka zo wajena yace ma Yusuf ma yazo, ita kuma ta nemi waje ta zauna kanta a ƙasa. Ba Modu yace. "Hajiya ina saurarenku" Mama tace. "Yafiyarku mu ka zo nema a bisa kuskuren da muka aikata, ko kuma in kirashi son zuchiya. Domun duk wani alkhairi Bulama yayi mana. Mu kuma da sharri muka nufeku. Amman munga rayuwa, ku da ganinmu ba sai ance muku ba. Bulama ku yafe mana dan girman Allah. Mahaifinka da mahaifiyarka duk muna neman gafararsu a taimaka a yafe mana" Hawaye nake tsiyayarwa sosai. Ba Modu yayi gyaran murya yace. "To babu komai. Dama ko da yaushe anason mutum ya gane kurenshi sai ya gyara. Naji daɗi da kuka tako zuwa neman gafararmu, domun kun yi mana zalunci sosai. Ta sanadiyyar auren ƴarki abubbuwa da yawa sun faru a cikin wannan zuriyar. Ni dai ta ɓangarena na yafe. Bulama uwata ku yafe musu kuma, ubangiji yana son masu yafiya da afuwa" Yahanasu tace. "Ban riƙe kowa a zuchiyata ba Ba Modu. Amman duk da haka na yafe musu Allah ya yafe mana baki ɗaya. Nima in a zaman mu na zalunceki ki yafe mini" Bulama shima yace ya yafe mana. Mun nemi ganin mahaifiyar Bulama da Ba Bakura. Anan Ba Modu ya sanar mana rasuwar Ba Bakura. Hajja kuma bata da lafiya tana kwance a ciki. Da kanshi yai mana jagora har inda Hajja take muka roƙi gafararta ta yafe mana itama ba tai ko musu ba. Zuchiyata tayi sanyi sosai, sai naji kamar an sauke mun wani gingimemen dutse a kirjina. Kwana ɗaya mu ka yi a gidan washe gari muka yi azamar komawa. Ba Modu yace mu tafi da su Bawa su je su yi mun hutu tunda ana hutun makaranta, yai mana goma sha tara na arziki, har tasha yasa aka kaimu a mota akan in hutu ya ƙare Bulama zai je ya kwaso yaran." Yahanasu: Ina kwance a ɗakin Ya Innana wayata tayi ringin. Da sauri na ɗaga na yi tunanin Alh Nura ne, dan tun jiya ni dashi muke abu ɗaya. Wai Ba Modu ya kirashi ya bashi haƙuri akan zan koma ɗakina. Shine fa hankalinshi ya mugun tashi, sai kirana a waya yake yi yana cewa. "Ya zanyi da sonki Yahanasu, yanzu kema kin yarda a rabamu?" Ire_iren kalaman da yake ta jifa na dasu kenan duk yabi ya rikice. Ni kuma bansan ma ina sonshi ba, sai da aka sa ranar ɗaurin aure na da Bulama Babba tukunna. Ina kara wayar a kunne sai naji muryar mace. "Hello Yahanasu Maman Amira ce, kin ganni a Damaturu." Da murna na tareta nace. Da gaske Maman Amira, kina ina yanzu haka?" Cikin fara'a tace. "Ina tasha saukata kenan" Ba shiri na zari mayafi na wuce gareji da mugun saurina mota na shiga na fice fuu a gida. Sai tasha, a zaune a wata rumfa na sameta tana jirana. Rungume juna mu ka yi da murna, sai hawaye kuma sai kuka mai sauti ya ƙwace mana. Yana da nasaba da irin rayuwar da mu ka yi a rihab mun ci wuya iya wuya. Janta nayi muka shiga mota. Sai da muka share hawayenmu tas sannan na ta da motata mu ka bar tasha. "Sai yau kika kirani. Kinsan ku baku bani numbobin wayoyinku ba, sai dai adireshi,. Ina Zainura kuna zumunci dai ko tunda garin ku ɗaya?" "Muna zumunci sosai ma, ta yi alƙawarin zata zo itama sai mu koma tare in sha Allah. Kin ga yadda kika koma kuwa Yahanasu Bulaman ki ya tsaya miki" Dariya kawai nayi mata nace. Ke ma kin yi shar dake Maman Amira. Ina Sani ya kuka ƙarke?" Dariya ta kwashe dashi tace. Labari yana gaba, bari in samu in watsa ruwa in ci burabusko zaki ji labari filla_fillah. Da haka muka iso gida. Motar Alh Nura na gani a cikin gareji yazo kenan. Muna fitowa daga mota ya karaso in da muke. Idanu na ƙura mai naga ya rame ainun. Ɗan murmushi nayi mishi carab a idanun Bulama Babba wanda fitowarshi daga gida kenan da halama fita zaiyi. Kallona yayi naga idanunshi sun cicciko da ruwan hawaye. Na shiga tashin hankali sosai. Ƙarasowa yayi in da muke ya ba Alh Nura hannu suka gaisa, jikin Bulama Babba yayi wani irin mugun sanyi. Maman Amira ta gaisheshi na gabatar mishi da'ita. Ya ma kasa magana sai ɗan guntun murmushi yake yi. Yana shiga motar shi, nace ma Maman Amira ta jira ni ina zuwa. Anan na barta ita da Alh Nura. Murfin motar Bulama Babba na buɗe na shiga gaban motar. Kanshi ya ɗago daga kan tiriyarin motar. Idanunshi sun ƙanƙance sun kuma yin ja, take jikina ya mutu. Haƙiƙa nasan Bulama Babba yana sona so na haƙiƙa so mara mis a cikinshi, Alh Nura tausayi yake bani, amman zallar soyayya Bulama Babba nake yi ma. Domun a zaman mu Bulama ya soni, ko da aka tursasashi ya rabu dani sai da ya bini da Alkhairi. "Na lura ni kaɗai nake ƙwaɗayin yin rayuwa dake a karo na biyu Yahanasu. To bazan miki dole a karo na biyu ba. Tunda kin fi tausayin Alh Nura to ni na haƙura. Inai muku fatan alkhairi Allah ya baku zaman lafiya, zan sanar ma Ba Modu na janye" Hawayene suka gangaro a kumatunshi. Take na rushe mishi da kuka dan bansan mai zance mishi ba. Nasan baya son kukana, kukan kaɗai zan yi ya tsaya ya saurareni. "Kukan na menene shin ba haka kike so kiji nace ba?" A'a kaima kasan babu wani ɗa namiji da zai iya ture matsayinka a rayuwata balle har ya maye gurbinka. Shin kasan irin ƙunci da takaicin da zuchiyata tai ta shanyewa a kan ka kuwa, kasan yadda naji a karon farko da naga Yalewa da cikin ka kuwa? Ina sonka kaima ka sani, ina farin cikin wannan komen da zanyi, ai yanzu ne zamu yi auren soyayya kayi haƙuri. Alh Nura baza ka sake ganinshi ba. In ƙawata bata da wani tsayayye zan haɗa su in sun amince" Idanu muka haɗa yayi murmushi ya sauke ajjiyar zuchiya. Nima murmushin nayi mishi nace. Shikenan ƙasusuwan jikin ka sun kwanta ko?" Ido ya kashe mun yace. "Za dai su kwanta sarauniya in na ganki akan shinfiɗata ina gurzarki" Da sauri na fice a motar ina dariya. Wajan su Alh Nura na nufa. "Alh ai mun afuwa na barku ku kaɗai. Yanzu dai kaga ina da baƙuwa zamu yi waya ko kuma da daddare mu haɗu" Sallama mu kai ma juna muka shiga ciki. Nuna Maman Amira nayi a cikin gida mu kaita zagaye zagaye. Kafin muka ya da zango a ɗakina. Bayan tayo wanka tana cin abinci ne tace. "Ni fa kaina duk ya ɗaure Yahanasu. Ni na ɗauka zan ganki a gidan mijinki sai naga saɓanin haka. Kuma naji anata ce miki Amarya meke faruwa ne?" Na ɗauki Maman Amira ƙawa Aminiya. Labarin komai daya faru na bata, tace "Amman gaskiya na tausaya miki sosai. Hajja bata kyauta ba, amman ta gane kuranta ai da taga za'a hallaka mata ɗa. Hmm ni ai ko ƙuda ya kasa shinshinata, duk wanda yazo wajena ɗaya biyu shikenan baya kuma zuwa, kinsan hausawanmu abu baya wuce musu. Ni kuwa rayuwata nake yi a nitse, ina juya kuɗaɗena bani da matsalar komai. Ai baki sani ba. Ina komawa gida da sati muka soma zurubtun zuwa kotu da Sani. Kinsan sha'ani na maganar kotu mun kai wata takwas ana abu ɗaya. Kab dukiyata ta dawo hannuna harda bashi da nake binshi. Yanzu haka yana gidan kyaran hali zai ɗan yi aiki na wata huɗu haka. Na ji labarin ma ita yarinyar daya aura sun rabu, tun muna sintirin zuwa kotu da ta tabbatar da gaske fa dukiya zata dawo hannun mai ita" Nayi farin ciki sosai da jin wannan labari. Da wannan damar nayi amfani na shigar mata da zancan Alh Nura. Alhamdulillah tayi na'am, ta ɓangarenshi shima ban samu matsala ba, dan maman Amira kyakkyawar mace ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Kwanan Maman Amira uku Zainura tazo itama. Bulama Babba ya dinga zaga garin Damaturu damu. Har Yobe mu ka je suka ga gidana da zan zauna. Bulama Babba sai sake gyara gidan yake yi." Naji daɗin wannan zumunci sosai. Bayan wata biyu muka shiga shagalin bikina, da bikin Wakil wanda sabida rashin lafiyata aka ɗaga. An yi shagali sosai, Hajja ta yi bajinta ainun a wannan biki namu. Bayan an gama duk shagali kuma muka nufi Yobe, amman Ya Innana tace abar mata yaran dukka su dawo Damaturu da zama baki ɗaya. Gida daga ni sai Bulama Babba. Wata iriyar rayuwar soyayya da jin daɗi muke gudanarwa tamkar zamu haɗiye junanmu. Lallai Bulamana yayi kewata kewa mai yawa, ni kuma na saki jiki na faranta mishi ranshi sosai. Shi kanshi yayi mamakin yadda na zama ƴar duniya ƙarfi da yaji, yanzu ne muka san munyi aure a baya wasa muke yi na yiyyi amfani da maganguna ingantattu da wani haɗin turaren tsugunno ina na matan Kanuri wanda yake maida tsohuwa yarinya, wannan turare ko wacce matar Kanuri da matan shuwa dashi suke bugun ƙirji, yana tattare da wasu irin surruka na musamman ne. ( Me so ta tuntuɓeni 08179523215) Kasancewar ni kaɗaice a ɓarayina, kullum cikin shigar ƙananun kaya nake, gyaran jiki da kwalliya sun sa na zama mai kyau, mata da yawa sai suke sha'awar fatata. Kullum gidana a cikin ƙamshi mai ni'ima yake, ƙamshi mai kwantar da hankalin mai gida, asalin ƙamshi na manyan mata, wasu irin turarukan wuta na al'adar Kanuri na haɗa masu dogon tarihi da surrukan kwantar da hankalin mai gida kana da kara danƙon soyayya ( shima akwaishi mai so tayi magana) Bayan wata guda da aurenmu muka tafi umara ni da Bulama Babba. Rayuwa ta warware na sake zama Hajiya ƙarfi da yaji. Aikin gidan TV ɗinma Bulamana ya hana, sai na mai da hankalina kan shagon gyaran jiki. Bulamana ya sake ƙawata mun shagona ya zama shahararren shago, turarukan wutanmu, da asalin ɓakar Humra mai taushin ƙamshi ta kabilar Kanuri ba ƙaramin cinikinsu muke yi ba, gyaran jiki mukam samu a ƙalla mata ashirin a rana, goma, takwas, in kamar ranakun Alhamis ne aikin kacame mana yake yi sosai. Maman Amira kuwa Allah yayi Alh Nura ta aura aka kawota Yobe zumunci ya saƙe karfi, muna zumunci sosai da su Zainura da Hadiza ma. A Damaturu kuma surukan gidan sunata hayayyafa, yara kullum sai cika gida suke yi. Fanna yaranta uku yanzu haka, Fandau kuma yaranta bakwai. Jikoki a cikin gidannan ba dama. Duk wutu in an samu Bulama yana kaima Zubaina yara su yi mata hutu. Muna waya da'ita muna zumuncinmu kamar babu abinda ya faru ma, rayuwa kenan. Tunda nakoma gidan Bulama Babba ban ko yi ɓarin wata ba, abun duniya duk yabi ya isheni, duk inda naji mai magani sai na karɓa, kuma a asibiti sun ce lafiyata ƙalau. Tun ina nema harna haƙura da naga shekaru nata shurawa, saina fauwalama Allah. Wata ƙila iyakar ƴaƴan nawa kenan waɗanda na zubar dasu a sanadiyyar shaye_shayen muyagun ƙwayoyi. Yalewa kuma har zuwa wannan lokacin batai aure ba babu ma wanda yake ko shinshinarta. Hajja wani irin so da kulawa take nuna mun, kullum saita kira ni a waya mun gaisa, in kuma ta samu masu zuwa Yobe zata aiko mun da saƙo. Mama Gana tun tana fishi harta sakko rayuwa ta dawo dai_dai zumunci yaci gaba da tafiya kamar Lokacin da Ba Bakura yake raye. Hankalin kowa a kwance yake sosai muna rayuwarmu cikin aminci gwanin sha'awa. MRS BUKHARI CE [23/08, 12:00 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: Gawurtattu uku 62 Ƙarshe. Zubaina: Tunda dai na roƙi gafarar su Bulama Babba suka yafe mun sai naji sanyi a raina. Yaran dana tawo dasu naji daɗi sosai. Suka gama hutunsu aka turo mota aka tafi dasu. Haka rayuwa tai ta shurawa. Kawu Tanko ya sai mun gidaje manya guda biyar na haya, aka zuba ƴan haya duk shekara ana karɓar kuɗaɗe masu yawa, sai ya bamu shawarar zuba hannun jarin wani kasuwanci. Shima na cire million uku na zuba. Anata dai juya ma marayu kuɗinsu. Muma nu na ci muna sha. Yarona na da wata tara sai ya yaye kanshi ya dena karɓar nonon kwata_kwata. Sai na yaye shi. Mabaruka ta samu ƙwari jikinta babu laifi, sai magani da take zuwa karɓa. Muna zumuncinmu dai dai yadda muka saba. Ana cikin haka wani ɗan kabu_kabu ya fito neman auren Asiya. Dake Allah yayi mijin nata ne cikin wata uku aka gama komai muka ɗau amarya mu ka kaita hayi. Itace ta uku a gidan, ɗakuna ɗaɗaɗaya ko wacce mata take dashi, sai falo wanda a cikin dalon ɗakunan suke. Ashe wannan bawan Allah baya iya ciyar da matanshi da abinci, su suke sana'a su ke ciyar da kansu da ƴaƴansu. Kuɗi na ware dubu hamsin na ba Asiya nace taja jari karta zauna haka. Bai fi wata ɗaya dana ƙarama Nafeesa jari ba itama sana'ar take yi, ita ke ciyar da ƴaƴa. Ko rabon kwana bayayi da'ita amman Mama tace tayi haƙuri komai mai wucewa ne tayi ta adda'a tana istigifari. Haka dai mu ke ta gurgura rayuwar. Musa ma yanzu babu aiki sam a hannunshi, kullum yana gida, matarshi kuwa a gaban Mama sai ta cukume shi, mu dai bama ce musu komai. Da shekara ta zago sai na cire dubu ɗari huɗu na sai ɗan sahu na ba Musa nace ya dinga kabu_ kabu dashi, ya kula da iyalanshi. Ana cikin haka Mama ta kwanta jinyar da ashe bana tashi bane. Kwananmu arba'in da shida a gadon asibiti. Wata ranar juma'a da safe Allah yai ma Mama rasuwa. Shikenan maraici ya ganmu ba uwa ba uba. Amman Kawu Tanko ya zame mana makwafin iyayenmu, shi ya tsaya a kanmu. Ya haɗani da wani almajirin gidanshi da ya yaba da hankalinshi. Mu kai aurenmu na tare a ɗaya daga gidajena, yana da mata tana rigasa da yaranshi huɗu. Ni kuma ina gidana da yarana. Ni ke musu komai, ƴan biyu sun kai shiga makaranta, na samu makaranta mai kyau na saka su a ciki. Nafeesa cikin amincin Allah mijinta yayi mata afuwa sun dawo suna zaune lafiya, yaci gaba da rabon kwana da'ita. Asiya kuma ta kama sana'arta tana ta jujjuya kuɗi. Har kasuwannin ƙauye take sarin kayan masarufi. Abun ya kankama sosai tana juya kuɗi. Ko data haihu ita da kanta ta dinga yi ma kanta hidima. Nima haka dana haihu ni na ɗauki nauyin komai hatta ragon suna ni nayi ma kaina, Auwal babu ruwanshi, sai dai ran kwanana yazo yaci abinci ya kwanta dani. Amman muna zaune lafiya na rungumi ƙaddarata kuma na gode Allah. Har wani rawar kai yake yi in kwanana ya zagayo,dan nafi matarshi nesa ba kusa ba, ko banza yazo yaci abinci da nama ai, to da kuɗina gaskiya muna cin abinci mai kyau ni da yara. Nayi ɓul_ɓul abuna, sai dai haskena ya disashe yaƙi dawowa sam. Mu kan kai ma Sagiru ziyara gidan yari. Shima ya shiryu ya zama kamar ba shi ba, sai karatu yake yi na addini a gidan yarin. Ni ma ina zuwa islamiyyar matan aure ina karatuna, kuma Alhamdulillah ina fahimta Auwal ma yana ƙaramun Quri'a a gida duk sanda yazo, rayuwar auren ina jin daɗinta gaskiya. Matar Musa ta sake ana zumunci da'ita tunda yanzu ko suna ko biki in ya tashi na family da'ita ake komai. Ko wancan satin Mama Zakiya ɗanta yayi aure da'ita mu kai ta jigilar komai. Hajiya Kubra Ghana muna waya sosai da'ita, haka Nabeela, ita kam har Zariya naje gidan da take aure. Muna zumunci sosai, dana sake haihuwa ma da'ita akayi hidimar suna tsab har aka gama kafin ta koma Zariya. A bakin Hajiya Kubra nake jin labarin Jaɓa ya haukace tuburan bola ma yake bi, sauran yaran Alh Liti kuma duk dukiyar da suka samu ta galgance ta hanyar neman matan banza. Wasu kuma sun gaji mahaifinsu ta fannin shahara a kasuwanci. Rayuwa kenan in kaga ta wani sai kace taka da sauƙi. Wasu in suka ga yadda muke rayuwa tausaya mana suke yi. Mu kuma sake godema Allah muke yi a ko da yaushe. Dukiyar marayu sai sake burunƙasa take yi, ni kuma inata hidintama karatunsu da wannan dukiya, da ƙannensu wanda suke uwa ɗaya. Na dawo nayi fes dani kamar bani ba, haskena ya dawo nayi ƙiba sosai sabida cin daɗi. Bana dani za'ayi aikin Hajji in Allah ya nufa, na biya mana ni da Auwal. Mabaruka ta samu wani mai irin lalurarta ta rufa ma kanta asiri tana zaune lafiya dashi suna shan maganin akan ka'ida. Mu kan ziyarci juna, amman ƙawancan namu ya ja baya sabida sungulloli da su kai ma kowa yawa. Yahanasu: Ina tsaye hannuna riƙe da kaskon turaren wuta sai na jiyo sallamar Bawa da ƙannen nashi. Da gudu yazo ya rungume ni. Ya girma sosai shekararshi goma sha uku yanzu, yana SS 2 a fannin boko, a fannin islamiyya kuma yayi sauka. Daga ina kuke haka ƴan samari? Na tambayesu shi da Yusuf. Maryam ce ta shigo ita da Ba'a kaka. Ba'a kaka ashe tare kuke, anyi hutu sai Kaduna ko?" Muna cikin haka Bulamana ya fito daga ɗaki yana sanye da jallabiyya yau Sunday ne yana gida. Yaran ya kira su ka je suka same shi. Ni kuma na shiga fito da abincin karyawa. Sai da na gama nace. To ku sakko mu karya dukkanmu." Bulamana yace. "Wai yaranki fa wannan karon su baza su je gidan uwarsu ba, a wajanki zasu zauna. Wai Babansu Maryam ƙarama baya son kulasu, kuma in suka je kullum shi Baban a cikin rikici da uwar yake" Haɓa na riƙe nace. To Allah ya kyauta. Kasan wasu haka su ke yi. Ku dai sakko mu ci abinci, sai mu fita siyayya ko?" Nan suka soma murna muna cin abinci da yara ina jansu da hira. Su kuwa sai surutu suke faman yi mun. Ashe Bulamana mu yake ta kallo ko ƙibtawa babu. Murmushi nayi mishi na soyayya. Bayan mun kammala karyawa sai Bawa yayi wanke wanke, Maryam kuma tayi shara na fito na sameta tana sake turaramun falon da turaren wuta. Ɓarayin su Hajara na nufa. A bakin kofa na samesu suna yankan nama, anayi Hajara na ma khairat jaraba. Dariya nayi dan Hajara ba zata sauya halinta ba sam, ba karamin chabta suke yi ba, ita Khairat akwaita da gwalangwaso, shi kuma Ahmad sabida wanna gwalangwason ma kamar yake jin ya kara sonta, Hajara kuma kullum a cikin rikici ake da'ita. Yanzu ne data nutsu na bata wasu surrukan turaren wuta, na ɗaki dana tsugunno, dana turara kaya, da humra uban ubansu. Tana ganina ta shiga yashe baki. "Hajiya Yahanasu ni dai bazan dena mamakin irin wannan kyau da ado da kike zugawa ba. Kinsan Allah kamar canja ki akayi. Ki ganki fa a Kano lokacin muna gidan su maman Hassan" Ahmad ne ya fito ɗaga ɗaki yace. "Faɗi ba'a tambayeka ba kenan tazo ko ki barta ta zauna kin tareta da soki burutsun zance" Ni dai dariya nayi kawai. Muka gaisa da Ahmad kana nace. Fita zamu yi da yamma zuwa park mu ɗan huta sai ku shirya zuwa bayan la'asar da yaran duka. A kunnen Hajara nayi mata raɗa" Ki tabbatar kinyi amfani da wannan humrar dana baki."Nan na bar su, Aneesa anata murna. Da yamma kuwa muka shirya tsab, na soya mana kaji, nayi mana babban cake da fried rice ƴar kaɗan sai drinks. Yara suka saka a mota da dadduma duk suka fice suka barmu cikin ado Bulama Babba ya fito. Rungumeni yayi yana mun raɗa. "Kece farin cikina sanyin idaniyata uwar ƴaƴana" idanu na lumshe hawaye suka gangaro kan kumatuna. Allah na gode maka daka barni da raina da lafiyata, da Bulamana kuma. Rashin haihuwa Allah yasa hakan shine mafi alkairi a gareni." Fita mu ka yi mota biyu. Na gaiyaci Maman Amira ma acan muka same su. Yau ɗaya Hajara ta ɗauki shawarata tayi mugun kyau, taci wani lace mai mugun kyau, fuskarta tayi sawai, gashi ta saka humrar dana bata. Ahmad sai wani kallonta yake yi yana murmushi yana wani liƙe mata ( in kema kina son mijinki ya dinga niƙe miki ya zamar miki ɗaye manna to ki neme ni) ita kuma sai sakar ma Khairat harara take yi. A wajan mu ka ci mu ka sha akayi hirar nishaɗi. Yara su ka ji daɗin su. Dab magariba muka nufi gida. Washe gari har daki Hajara ta biyo ni tace. "Jiya na tsugunna a kan turaren tsugunnon nan da kika bani Yaha, hmmm in ana sallah ba'a magana wallahi har kyautar dubu goma Ahmad ya bani, ke a liƙe muka kwana ko ya na motsa zai dawo dani jikinshi, na yi amfani da wannan turaren kwanciyar da humrar matan Aure. Gaskiya wannan setin duniya ne, ya kamata ko wacce mace ta mallaki nata. Shi yasa ku Kanuri da shuwa mazaje suke liƙe muku aita ɗaukar hakkin ku ana cewa asirine, ashe gyaran shedkwata kuka fimu iyawa" Dariya ni ta bani ma sosai. Ƙarin bayani na yi mata ( kina son mallakar naki setin? To ki tuntuɓeni ki yi booking naki) Da daddare ina kwance lamo a bayan Bulamana na yi matashin kai da gadon bayanshi. Hawaye nake tsiyayarwa wannan rashin samun rabo yana damuna ainun. Amman ita rayuwa bata taɓa rabo da ƙalubale. Idanu na lumshe bacci yayi awon gaba dani cike da maharkan jarirai baƙaƙe masu kama da Bawa . Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen wannan labari. Sai Allah ya sake sadamu a cikin wani sabon littafin zaku jini ba da daɗewa ba in sha Allah. Masu siyan setikan turare kuma ina maraba daku nagode sosai masoyana. Yahanasu tana miƙo saƙon gaisuwarta ga masoyanta tana barar adda'arku Allah ya bata rabo da Bulamanta. Ba Modu kuma har yanzu yana nan gadagau dashi cikin ƙoshin lafiya