KUDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI GWARAZAN JIYA BABI NA ƊAYA Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta. Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!. Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu. Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne, Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi. Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi, Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa, Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi, Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa. Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba, Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske, Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin. A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya, Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa, Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi ba. Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo daga cikin keken dokin, Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa. Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya, Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba. Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari, Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da ke gudana ba, Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya aka sakata a cikin wannan akwatu? Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan. An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin akwatin? Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin, Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen, Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi, adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu. Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen keken dokin, Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice. A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu. Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar bata raye a halin yanzu. Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat? Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne". Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat. Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa sama. Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin dawakansu suka koma izuwa cikin dajin. Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar jaririyar? Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?. Dalilin faruwar hakan kuwa shine. Babi na biyu A ƙarni na biyu a yankin ƙasashen yammacin duniya anyi wani ƙasaitaccen birni da ake yiwa laƙabi da Madinatul-kusuf. Birnin Madinatul-kusuf ya bunƙasa a noma, kiwo kasuwanci da tarin al'umma, Daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan mayaƙa masu juriya a filin daga. Sarkin da ke riƙe da sarautar birnin yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa DANDAZON JARUMI a filin fama, Yana da tarin dukiya, kuma ya shahara ainun a fagen sanin ilimin tsafi, Bisa wannan dalili ya sanya ya zamo gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu a tsakanin sarakunan nahiyar. Ana yi ma shi laƙabi da Sabrul-Marhut, Ya na da matar aure guda ɗaya wata kyakkyawar gaske mai suna Hunaisat. Sun kai shekara goma da yin aure amma Allah bai basu Haihuwa ba, Al'amarin da yake matukar dugunzuma hankalin sarki Sabrul-Marhut kenan, Duk sa'adda ya gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sai ya ga cewa tabbas zai samu haihuwa amma sai a nan gaba. Shin yaushe zan samu wannan haihuwa bayan cewa a ko da yaushe shekaruna na daɗuwa girma na kamani? Anya kuwa halarar tsafina gaskiya ta faɗi cewa zan samu Haihuwa? Tambayoyin da sarki Sabrul-Marhut ke kasa bawa zuciyarshi kenan. Wata rana sarki Sabrul-Marhut na zaune a cikin ƙasaitacciyar turakarshi bisa kujera ta alfarma sanye da tufafin barci marasa nauyi, A wannan lokaci dare ya tsala babu abin da kunne keji face haushi karnuka da kukan gyare tsilli-tsilli. Duk da kasancewar akwai gajiya a tare da Sabrul-Marhut yana buƙatar rintsawa, Amma sai ya ji ko da gyangyaɗi bai yi ba sai dai ya saƙa wannan ya warware waccan. Yana cikin wannan hali ne sai ya ji alamun motsi a harabar turakarshi, kawai sai ya miƙe tsaye zumbur ya fita zuwa wajen amma sai yaga wayam bai ga komai ba, kuma gaba ɗaya dakarun dake ɓangaren sun ɓingire ƙasa suna sharar barci, Al'amarin da yayi matuƙar ɗaure mashi kai Kenan kuma ya bashi mamaki. Nan take ya fahimci cewa tabbas akwai aikin wani Ma'abocin sihiri a wannan al'amari, Nan fa ya sha jinin jikinshi har ya buɗi baki da nufin ya furta waɗansu ɗalasiman tsafi. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wani Dattijo ya bayyana gareshi ma'abocin ƙaurin jiki, ya na da ƙirar mutanen birnin Sin, gashin kanshi, Gemu da kasumba farare ne sol ko da ɗigon baƙi ɗaya babu, Yana sanye da tufafi na jemammiyar fatar damisa tun daga ƙasa har sama, A hannunshi yana riƙe da wani ƙwagiri na sihiri. Kallo ɗaya za ka yiwa mashi ka tabbatar dacewa ya yi shura a halarar tsafi, Sa'adda sarki Sabrul-Marhut ya yi arba da mutumin sai yaji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun, Amma saboda ƙi faɗi irin ta manyan sarakai sai basar ya dubi mutumin ya daka ma shi tsawa yace "Shin wane ne kai kuma mene ne nufin ka a gare Ni?. Ko da jin wannan batu daga bakin Sarki Sabrul-Marhut sai mutumin ya taƙarƙare ya bushe da dariya mai kama da haniniyar doki, sai daga bisani ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da wasiƙar mutuwa ya buɗi baki cikin kakkausar murya "Yakai Sabrul-Marhut ibn saiban ka yi sani cewa ba na zo gare ka domin na cutar da kai ba sai domin na taimaki rayuwarka. Amma kafin hakan akwai buƙatar na sanar da kai wane ne ni kamar yadda ka buƙata. Babi na uku Kimanin shekaru ɗari biyu da ɗoriya a birnin Romaniya mahaifinmu sarki Raziban shi ne ke riƙe da Sarautar birnin, Sarki Raziban yakasance gwarzon mayaƙi kuma JARUMIN JARUMAI gawutaccen matsafi wanda masu bincike da hasashe suka tabbatar da cewa a ƘARSHEN ƘARNI na uku bayan shuɗewar boka Shuyuɗan mai taskar ANNOBA DARI ba a samu wanda ya kai mahaifinmu ƙarfin sihirin tsafi, Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan nahiyar ke yi masa mubaya'a bisa dole, Wasu ma na kiran mahaifinmu da Amirul-Sihir ma'ana Sarkin bokaye. Duk da irin ƙasaitar mulki da mahaifin mu ke da shi amma giyar mulki ba ta ja shi ba yakasance mutum adali ma'abocin tausayi da afuwa, Mahaifinmu ya na da 'ya'ya guda bakwai, Yarima Zafiyar shi ne babba dai gimbiya Rumailat, Yarima Hasanul-Mausur, Sumaiyat, Laswil, Rukaisu, Zaidar sannan kuma ni Matawus na cikon bakwai ɗin su. Kowannen mu na samun kulawa daga soyayyar mahaifinmu, duk da irin matsananciyar gaba da ƙiyayyar da ke tsakanin mu wacce ba kowa ba ne ya haddasa hakan ba face bakin kishin da ke tsakanin iyayen mu mata. Wata rana mahaifin mu na zaune a fadarshi bisa karagar mulki, fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da idanu ba su taɓa gani, Fadar ta cika maƙil duk inda mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke. 'Yan majalissar sarki na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma A kowa ce kusurwa a fadar dakaru ne na jinsin MUTUM DA ALJAN shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar gwarjini da ban tsoro ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro. A wannan lokaci idan ka ɗauke iskar da ke kaɗawa a fadar babu abin da kunne ke ji face sautin fitar numfashin ɗaruruwan jama'ar fadar. A na cikin wannan hali ne kwatsam sai a ka ga sarki ya faɗo daga kan karagar mulki yana amai na jini kuma tari mai tsanani ya turnuƙe shi, Cikin kaɗuwa gaba ɗaya 'yan majalissa suka yi ca akan mahaifina, da hanzari dakaru suka shigo fadar ɗauke da wani ƙayataccen gado suka ɗauki sarki suka fice da shi kai tsaye suka kai shi turakar shi suka shimfiɗe shi bisa gadon sarauta suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar shi. A can gidan sarauta kuwa labarin abin da ya faru da sarki ya riske mu don haka ni da 'yan uwana sai muka ɗunguma muka nufi turakar shi hankulan mu a tashe, Ya yin da muka iso ne sai dakarun da ke tsaron ƙofa suka dakatar da mu cewa sarki ya ce kada a kyale kowa ya shiga har sai ya yi umarni. Ko da jin wannan batu daga bakin dakarun sai yarima Zafiyar ya fusata ainun ya daka masu tsawa ya dube su ya ce "Shin mene ne matsayin ku da har zaku hana mu ganawa da abbanmu ina so ku gaggauta buɗe mana ƙofar tun kafin KAIFIN TAKOBI na ya tsara ruhikan ku". Da jin hakan daga bakin yarima sai hankalin dakarun ya dugunzuma ainun, daƙyar aka samu wani mai dakakkiyar zuciya ya buɗi baki da nufin ya furta wani abu, kawai sai aka ji ƙarar zare sakatun dake dake kofar, jim kaɗan sai ƙofar ta buɗe sai ga boka Jauwad ibn Ramli ya bayyana a gare su. Boka Jauwad yakasance dattijo mai kimanin shekaru saba'in dogo ne kakkaura yana da gashin gemu da ƙasumba farare sol ko ɗigon baki babu, fuskarshi doguwa ce mai ɗauke da dara-daran idanu jajajur! tamkar garwashin, yana da faffaɗan hanci mai ɗauke da ƙofofi tamkar mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar bakin rijiya mai ɗauke da wargatsattsun haƙora marasa kyawun gani, yana sanye da baƙaƙen tufafi tare da guraye da layu na sihiri tamkar wani tsohon mahaukaci, kallo ɗaya za ka yi boka Jauwad ka tabbatar da cewa ya cika hatsabibi a fagen sarrafa alƙalumman sihiri. Duk da kasancewar mahaifinmu mashahurin matsafi da babu tamkar shi a nahiyar amma bisa al'adar masarautar mu akwai bokan da ya ke gudanar da dukkan wani sha'ani na lafiyar iyalan masarauta, da kuma jagorancin abin bauta. Ya yin da muka yi arba da boka Jauwad sai dukkanin mu muka risina gare shi muka kwashi gaisuwa cikin girmamawa, boka Jauwad ya dube mu ɗaya-bayan-ɗaya, sannan daga bisani ya buɗe tafkeken bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa wannan jinya da ta samu mai martaba cuta ce mai matuƙar haɗarin gaske, wacce za ta iya zamowa ajalin shi baki ɗaya, Ba wani abu ba ne ya haddasa mashi cutar ba face wani sihiri da abokin gabar shi boka Bazzagul-Nadiyar ya yi mashi, an binne sihirin ne a cikin wata tsohuwar rijiya dake cikin fadar sarkin bokayen aljanu na duniya, Kafin mutum ya isa inda fadar sarki bokayen take akwai haɗdura masu yawa gami da miyagun dazuka. A halin yanzu bincike ya tabbatar mani da cewa a kaf duniya yanzu babu wani waje mai tattare da haɗari tamkar shi, Daga nan zuwa can ɗin tafiyar shekaru huɗu ce amma bisa Saurayin aljani mai tashen balaga za a iya isa cikin watanni shida. Sa'adda boka Jauwad yazo nan a jawabin shi sai hankulanmu ya dugunzuma ainun, wasu daga cikin'yan uwana cikinsu ya ɗuru ruwa, saboda fargabar kada sarki ya rasa rayuwar shi a halin yanzu ba tare da ya sanar da su mabuɗin taskar dukiya ba. Boka Jauwad ya katse shirun da ya wanzu tsakanin su ta hanyar buɗe baki a karo na biyu ya ce " Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa a halin yanzu babu abin da ya ke gaban ku face shiga duniya domin ku isa fadar sarkin bokaye ku karya sihirin da aka yi wa sarki, Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan har kuka yi jinkiri sarki ya rasa rayuwar shi tamkar kun rushe birnin ku da hannayenku ne, domin abokin gabar abban ku boka Bazzagul-Nadiyar zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA na wannan birni, kun ga kenan shi ne zai gaji KARAGAR MULKI ta mahaifin ku. Jawabi na ƙarshe a gare ku shi ne mai martaba sarki ya ce na faɗa maku cewa dukkanin wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yi masa shi ne zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA. Ko da boka Jauwad yazo nan a zancen shi sai ya rikiɗa zuwa wani baƙin hayaƙi ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Jiki a sanyaye ni da sauran 'yan uwana kuma juya muka fice daga harabar turakar mai martaba. Kamar yadda boka Jauwad ya faɗa haka al'amarin yakasance bayan kwanaki biyu da kwanciyar mai martaba jinyar rashin lafiya sai dukkan 'ya'yan tare da ni mu ka hallara a fada domin gudanar da tafiya karya sihirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu, lokacin da mu ka shigo fadar sai mu ka tarar ta cika maƙil da jama'ar gari tare da 'yan majalissar sarki a gefe guda boka Jauwad ne tare da magajin gari mai suna Shuraih wanda yakasance ɗan uwa a wajen sarki uwa ɗaya uba ɗaya, bisa dokar masarautar duk sa'adda sarki ya kwanta jinya ko kuma wani uzuri ya same shi sai a damƙa sarauta ga magajin gari, A iya sanin da nayi wa magajin gari shuraih nasan babu wata matsala tsakanin shi da sarki don haka koda wannan jinya ta sarki ta faru ban zarge shi da wani abu ba, Bayan kowa ya hallara a fadar kuma an samu nutsuwa sai sarki Jauwad ya miƙe tsaye daga kan kujerarshi ya fuskanci al'umma ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku jama'ar wannan faɗa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne 'ya'yan mai martaba sarkinmu za su tafi izuwa fadar sarkin bokayen duniya domin su tone sihirin tsafin da aka yiwa sarki wanda abokin gabar shi kuma maƙiyin wannan ƙasa tamu ya yi mashi wato sarki Bazzagul-Nadiyar. Bisa Wasiyyar da sarki ya bayar cewa dukkanin wanda ya tone wannan sihirin tsafi ya zo da shi nan shi ne zai gaji karagar shi ya mulki. Sa'adda boka Jauwad yazo nan azancen shi sai fadar ta kaure da cece kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi, tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani Jauwad ya ɗaga hannunshi sama fadar ta yi tsit a karo na biyu sannan ya cigaba da cewa "Yanzu dukkan wani abu na guzuri da abin hawa an tanadar masu abin da ya rage yanzu shi ne za a ɗora Magajin gari a bisa KARAGAR MULKI, sannan bayan 'ya'yan mai martaba sun yi bankwana da mahaifinsu mata za'a yi masu rakiya izuwa bakin ƙofar gari. Lokacin da boka Jauwad yazo nan azancen shi sai wani badakare ya matso daf da shi ɗauke da wata akwatun baƙin ƙarfe ya ajiye a gaban shi ya buɗe ta ya ɗauko wani kambun Sarauta ya miƙa mashi shi kuma ya ɗora kambun a bisa kan magajin gari da ke zaune a daf dashi a kan kujerarshi, badakaren ya sake zira hannunshi a cikin akwatun ya ɗauko wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta ya risina cikin ladabi ya miƙa wa Boka Jauwad shi kuma sai ya damƙa a hannun magajin gari, Sannan shuraih ya miƙe tsaye ya je ya zauna a bisa KARAGAR MULKI take jama'ar dake fadar suka risina da kawunansu a gare shi dake nuna mubaya'a a gare shi. Koda kammala bada riƙon sarauta sai ni da 'yan uwana muka shiga zuwa gidan sarauta domin yin bankwana da mahaifanmu kamar yadda boka Jauwad ya tsara, Lokacin da na Kaɗaita da mahaifiyata a cikin turakarta sai na dube ta cikin alamun matuƙar damuwa na ce "Ya ummina na ji a jikina cewa wannan gasa da aka sanya mana ita babu tabbacin zan yi nasara domin duk abin da zai kai ga a samu nasarar 'yan uwa sun ɗara ni wato jarumtaka da ƙarfin sihiri". Koda jin wannan batu daga bakina sai murmushi mai taushi ya suɓucewa mahaifiyata al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan na dube ta nace "Ya ummina shin ina dalilin wannan murmushi na ki?. Dajin wannan tambaya sai mahaifiyata ta yi buɗe baki ta ƙura mani idanu ko kiftawa bata yi ta fara magana a karo na farko "Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa haƙiƙa bani da wani buri da huce naga cewa kai ne ka gaji sarki ba 'yan uwanka ba, kuma dukkan maganar da ka faɗa tana kan gaskiya, Abin da ya sanya ni murmushi kuwa shi ne kana tare da abin da yafi na 'yan uwanka kuma matsawar ka yi riƙo da shi zai zaka samu nasarar cinye wannan gasa", Cikin matuƙar mamaki na dubi ummina na ce "Ya ummina shin ina dalilin wannan furuci na ki kuma wane abubuwa ne nake d su wanda idan na riƙe su zan samu nasara?, Ummina ta ce "Ya ɗana ka yi sani cewa tun da na mahaife ka na tabbatar da cewa na haifi yaro nagari kuma mai nasara a rayuwa, tun kana yaro ƙarami na fahimci halayen ka masu kyaune saɓanin 'yan uwanka, Ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya komai kake taƙama da shi akwai wanda ya huce ka domin masu iya magana na cewa "Kamai sammakon ka wani a hanya ya kwana" Wato idan jarumta, sihirin tsafi ko ƙarfin mulki kake taƙama da su cewa sune zasu bada nasara a cikin 'yan uwanka akwai waɗanda suka shafe ka, Abin da kake da shi wanda 'yan uwanka basu da shi da idan ka rike su zaka samu nasara su ne kamar haka, Gaskiya, Tausayi, Amana da hakuri waɗannan sune halaye mafi daraja da dukkan wanda ya riƙe su zai cimma nasara a rayuwar shi kuma babu wani abu da zai sanya a gaban shi face ya samu nasara, Gaskiya dai zata ƙara maka daraja da ɗaukaka a cikin dukkanin harkokin rayuwa kuma ita ce ke bayyanawa jama'a darajar da mutumtakar ɗan Adam, Tausayi kuwa na sanya soyayyarka a cikin zukatan al'umma har da maƙiyan ka, Amana kuwa na ƙara wa maka ƙima da daraja a cikin kowacce irin al'umma ka shiga,Hakuri kuwa zai sanya ka cimma nasara a dukkan abin da ka sanya a gaba, domin duk kyawun abu idan baka yi hakuri ka cimma karshen shi ba to abu biyu zai faru, Da farko shi ne zaka rasa wannan abun, sannan ka yi asarar lokaci da lafiyar da ka ɓata a kan shi, Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa waɗannan halaye sune sinadaran shaharar duk wani tauraro a duniya, Na so a celokaci bai kure ba da baka tsakure daga hikayar jarumi Masnur ibn Abdullah da wani fasihin marubucin hikayoyin wannan ƙarni wato Sufi ya tattara kuma ya sanya littafin suna KUNDIN HIKAYA, Tabbas da zaka ƙara tabbatar da batu na kuma ka ƙara ƙanƙame halayen da kyau". Lokacin da na ji wannan dogon jawabi daga bakin ummina sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ban sa'adda na rungume ta ba ina mai cewa haƙiƙa na aminta da ke ummina ɗari-bisa-ɗari, da yardar abin bauta ba zan ketare wannan wasiyya ta ki ba, kuma zan samu nasara bisa abin da na fita nema fatana na dawo na same ki cikin ƙoshin Lafiya". Sa'adda da na zo nan azance na sai mu duka biyun muka fashe da kukan farin ciki, dakyar da siɗin goshi muka rabu da juna suna masu zubar da hawayen baƙin ciki na shaƙuwa da juna. Lokacin da na isa fada sai na tarar dukkan 'yan uwana sun hallara ni kaɗai ake jira domin haka ina isowa sai aka ɗunguma izuwa wajen fada muka kama dawakai muka haye dake dauke da abin guzuri, kai tsaye boka Jauwad tare da magajin gari Shuraih haɗe da sauran mutanen gari suka yi mana rakiya har zuwa bakin iyakar gari suna masu yi mana fatan samun nasara, Lokacin da muka nausa zuwa cikin daji sai muka cigaba da tsala gudu a bisa dawakai sai da muka shafe tsawon sa'a ɗaya muna tafiya babu sassauci lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta cika a dai-dai wannan lokaci ne mu ka iso wata mararraba a dajin da ta kasu gida huɗu, Sai yarima Zafiyar ya durfafi hanyar yamma, Laswil kudu, Rumailat arewa sai ni kuma na yi gabas, dukkan 'yan suna kallon juna cikin matuƙar ƙiyayya amma ni sai na dunga sakar masu tattausan murmushi a haka har mu ka ɓacewa juna da gani. Lokacin da cigaba da tafiya a cikin dajin sai na wanzu ina tsala azababban gudu a bisa dokina ta hanyar ratsa duwatsu, ƙoramu, bishiyu da sarƙakiya, Sai da na shafe tsawon sa'a biyar ina wannan tafiya a dai-dai lokacin ne na fahimci cewa dokina ƙarfin gudun shi ya ƙaru ainun domin haka sai na ja linzamin shi na tsaya cak! na sauka ƙasa na zauna a ƙarƙashin wata itaciya na fito da abin guzuri na domin na yi kalaci shi kuma dokina ya shiga yin kiwo yana cin ciyayin da ke dajin, Ina cikin yin kalacin ne kwatsam bazato babu tsammani sai na ji kwantsama wata tsawa gami walƙiya cikin ƙankanin lokaci sararin samaniya ta canza launi izuwa baƙi, Cikin wani irin baƙin zafin nama na miƙe tsaye zumbur gami da mayar da abin kalacin izuwa cikin jakar guzuri na gami da zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayana, Kwatsam sai na ga dokina ya faɗi ƙasa ƙasa yana shure-shuren mutuwa, Cikin kaɗuwa na ruga zuwa inda ya ke kafin na isa har rai ya yi halin shi, cikin matuƙar takaici na tsugunna a gaban shi cikin alhini a lokacin ne na lura cewa wani irin baƙin ruwa mai yauƙi na fitowa daga bakin shi, koda na shin-shina ruwan sai na ji alamun akwai guba a cikin shi hakan ya sanya na fahimci cewa tabbas ciyawar da ke dajin ita ce ke ɗauke da wannan guba, Cikin matuƙar fushi na miƙe tsaye zumbur gami da kwarara wawan ihu, faruwar hakan ke da wuya sai duhun da ke sararin samaniya ya washe tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Kwatsam! sai wani ƙaton kai mai ɗauke da kawo biyu da fala-falan kunnuwa irin na Zomo haɗi baki irin na jemage ya faɗo tim, sannan hannaye, kafafuwa, gangar jiki suka biyo baya, ko da ganin hakan sai na ƙara riƙon takobina ina zuba idanun, Sannu a hankali sai sassan jikin suka dunga haɗuwa da 'yan uwan su har sai da halittar surar ta kammala, kafin na ƙarewa surar kallo wani sulken yaƙi da makamai sun bayyana a gare ta, A lokacin ne na fahimci cewa tabbas surar aljani ne ba bil'adama ba saboda waɗansu fuka-fukai da suka bayyana a gwiɓin hammatarsa guda biyu, Tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin halitta mai kwarjini da ban tsoro tamkar halittar ba domin haka sai yanayin tsoro ya kama ni har gumi ya fara tsattsafo mani a fuska amma saboda ƙi faɗi Irin ta 'ya'yan sarakai sai na basar. Ko da aljanin ya lura da hakan sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, Sai da ya yi dariyar ta ishe shi sannan ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da Saƙon mutuwa, Kawai sai ya zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje ya yi ɗauki izuwa Kai na yana ihu da kururuwa mai firgitarwa, Ko da ganin hakan sai nima na ruga gare shi domin tarar juna muna haɗuwa muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, Muka wanzu muna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama, Idan ka ɗauke sautin kaɗawar iskar dake sanya rassan bishiyu rangaji babu abin da kunne ke ji face ƙarar karafniyar makaman yaƙin mu da ke haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara mara daɗin saurare, Sai da muka shafe tsawon rabin sa'a muna wannan baƙin artabu babu sassauci a lokacin ne na fahimci cewa tabbas na gamu da gamo na, Domin ƙarfin saran aljanin ya nunka nawa sau uku, A wasu lokutan idan ya kawo mani hari idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa sannan na taso sama na mayar da martani, A cikin wannan artabu ne aljanin ya kawo mani wani nagartaccen sara da nufin ya tsinke mani wuya, cikin zafin nama na sunkuya makaminshi ya sari iska, Kafin ya sake wani yunƙuri ya sake kawo mani wani harin a kwaɓin cinyata ta hagu duk ƙoƙarin da nayi domin naga na kaure amma sai da makamin ya yanke ni a cinya jini ya yi tsartuwa na kurma ihu sakamakon raɗaɗi da zugin da na ji. Kafin cikar daƙiƙa ashirin ya samu nasarar yi mani raunuka biyar ɗaya a cinya biyu a kafaɗata ta dama sauran biyun a damtsen hannuna na hagu kowanne rauni na zubar da jini, Nan fa wani irin zazzaɓi mai matuƙar zafi ya kama ni, jiri ya fara ɗiba ta ina faɗuwa ƙasa, amma saboda da JURIYA DA JARUMTA irin ta MAZAN JIYA sai na miƙe tsaye a haka na ci gaba da kare kaina ba tare da mayar da martani ba. Lokacin da rabin sa'a da daƙiƙa ɗari biyu da hamsin ta shuɗe ana wannan artabu kwatsam! Bazato babu tsammani sai na wata hikima ta faɗo mani a rai, koda jin hakan sai na yi wuf na dunƙule hannuna ya kirɓawa aljanin naushi a kwiɓin hammatarshi saboda ƙarfin naushin sai da ƙashin hannun ya karye ya yi ƙara ruƙus! Aljanin ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji. Koda na fahimci cewa ashe sam makami ba ya tasiri akan shi nan take na yi jifa da takobina na shiga kai mashi bugu da naushi hannu da ƙafa. Wohoho haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canja, nan fa yazamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci na yi mashi jini-jina baya iya mayar da martani, kawai sai na yi wuf na kama wuyan shi na murɗe da ƙarfin tsiya, nan take na jefar da gawarshi gefe guda ko shurawa bai yi ba. Koda samun wannan gagarumar nasara sai na cika da matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa na ɗauki takobina na ci-gaba da tafiya ina takawa daƙyar bisa ƙafafuna na durfafi wata hanya, tafiyar daƙiƙa ɗari kacal nayi na iso wata ƙorama da ruwan cikinta yakasance garai-garai gwanin ban sha'awa, cikin matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa ya sanya hannayena biyu ina kamfatar ruwan ciki ina sha. Sannan na miƙe tsaye na durfafi wata bishiyar tuffa na tsinka na ci na ƙoshi. A sannanne na ji ƙarfin jikina ya dawo kuma sanyi da zazzaɓin da nake ji sun rabu da ni. Nan take na ci gaba da tafiya ina sake kunna kai izuwa cikin dajin ina tafiya cikin hanzari. Tsawon kwanaki uku na shafe ina tafiya a ranar kwana na ukun ne na iso izuwa gabar wani ƙaramin tsibiri mai ɗauke da bukka guda ɗaya jal, a gaɓar tsibirin wani makeken kogi ne mai tsawon gaske da ba a iya hango ƙarshen shi. Nan take na fahimci cewa ba zai yiwu na iya ƙetare wannan kogi ba face na ha samu kwale-kwale, don haka sai na isa izuwa bakin wannan bukka na yi gyaran murya har sau uku. Jim kaɗan sai ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wani dattijo dogo mai matsakaicin kaurin jiki ma'abocin kamala da haiba sanye da jajayen tufafi a hannun shi yana dogare da wani kwagiri. Sannu a hankali ya tako da ƙafafuwanshi har yazamana ya iso daf da ni ya ƙura min idanu. Fuska ta cike da annuri na dube shi na yi gyaran murya na ce "ya kai wannan dattijo ma'abocin kamala ni matafiya ne hanya ta biyo da ni domin nemo wani abu mai matuƙar alfanu gare ni, ina so ka taimake ni da jirgin ruwan da zan iya ƙetare wannan kogi, kasancewar na rasa abin hawa na? Koda jin wannan tambaya sai dattijon ya buɗi baki ya yi gyaran murya cikin kakkausar murya ya ce "ya kai wannan matashi ka yi sani cewa idan har ka amince da wasu sharuɗɗa da zan gindaya maka to zan ƙetarar da kai daga wannan kogi. Sharaɗi na farko shine zaka zauna da ni na tsawon mako takwas domin ka taya 'yata noma da kiwo. Sharaɗi na biyu kai ne zaka dinga nemo mana abin kalaci na nau'in dabbobi, Sharaɗi na ƙarshe shine duk kaine zaka bamu tsaro a duk lokacin da muke barci. Waɗannan su ne sharuɗɗan kuma ka yi aiki bisa amana to ina mai tabbatar maka da cewa zan haurar da kai akan wannan teku kuma zaka cimma nasara akan abin da ka fito nema. Sa'adda na ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin dattijon sai nayi shiru ina mai zurfafa cikin kogin tunani. Abu na farko da ya faɗo min a rai shi ne "shin yanzun kana ganin cewa idan ka ɓata tsawon mako huɗu 'yan uwanka ba za su cimma nasara ba. To amma kuwa shin akwai wata hanya da mutum zai iya isa gidan boka Bazzagul-Nadiyar batare da ya ƙetare wannan kogi ba, Kenan hakan ya tabbatar cewa dukkanin 'yan uwana sun iso wannan waje ko kuma za su iso anan gaba. Kaga kenan a cikin su babu wanda zai iya amincewa da sharuɗɗan dattijon". Lokacin da nazo dai-dai nan a tununi na sai na dubi dattijon na ce da shi na amince da dukkan sharuɗɗan ka kuma ina mai tabbatar maka da cewa ba za ka same ni mai cin amana ba"; Koda jin wannan batu sai dattijon ya yi murmushi mai taushi ya ce "zuwa gobe da safe bayan ka huce gajiyar dake tattare da kai. Daga wannan batu ne dattijon ya juya ya kunna kai izuwa cikin bukkar yana mai yafito ni da hannu yana nuni da na biyo bayan shi. Lokacin da muka shiga izuwa cikin bukkar sai na tarar ta kasance mai girma da faɗi kuma tana ɗauke da ababan more rayuwa abin da ya haɗar da gadaje biyu, shimfiɗu da sauransu, bayan na zauna a bisa shimfiɗar sai dattijon ya yi gyaran murya da ƙarfi jim kaɗan sai ga ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wata budurwa ta shigo ɗauke da Alhaji da salkar ruwa, budurwar takasance mai matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ne ba gajere ba, fatar jikinta takasance mai tsantsi luwai-luwai tamkar ta jariri sabon haihuwa, ƙugunta mai faɗi ne da tudu ta yadda koda kofin lemo aka ɗora zai zauna daram daga gaba kuma ya tsuke, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, fuskarta rufe take da baƙin yanki idanunwanta kaɗai ake gani waɗanda suka kasance dara-dara farare ƙal masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu baƙin cikinsu yakasance ɓaƙi siɗik, gashin kanta baƙi ne mai sheƙi ya zuba har izuwa kan kwankwasonta. Sanye take cikin tufafi masu yalwa na fatun dabbobi. Koda na haɗa idanu da budurwar sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi wani abu ya ɗarsu a zuciyata. Budurwar tana takawa a hankali cikin ƙasaita irinta JININ SARAKAI ta iso daf da ni ta tsugunna ta ajiye wannan akushi da salkar ruwa sannan ta juya ta nufi ƙofar fita har ya sanya ƙafarta ɗaya a waje sai dattijon ya dube ta ya yi gyaran murya ya ce "ya sha'afa ban faɗa miki sunan baƙonmu ba da abin da ke tafe dashi, amma magana a bakin mai ita tafi daɗi bari ki ji daga gare shi. Koda jin hakan sai na buɗi baki na ce da farko dai suna Matawus ibnu Sahibul-Sihir, kuma na fito ne tare da 'yan uwana domin zuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar duk wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yiwa mahaifinmu shine zai gaji karagar mulki. A wannan tafiya tawa ne hanya ta biyo da ni ta nan, kuma zan zauna tare da ku wani lokaci kafin na samu damar haye kogin dake gaɓar wannan tsibiri. Sa'adda nazo nan a jawabi na sai kyakkyawar budurwar ta juyo ta dube ni tare da ƙura min idanu ko ƙiftawa ba ta yi, sai daga bisani ta gyaɗa kai sannan ta juya ta fice batare da tace ƙala ba". Dattijon ya dube ni ya ce "ya kamata nima na sanar da kai sunan mu ni da 'yata, ni suna na Abu-Raudat 'yata kuma ana yi mata laƙabi da Raudatul-Abyad. Daga wannan batu ne kowa ya yi shiru na buɗe wannan akushi da aka kawo min na shiga kintsa cikina. Babi na huɗu Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan mun kammala kalaci sai muka yi ɗauki kayan aiki muka nufi gona tare da Raudatul-Abyad, yau ma kamar kullum fuskarta rufe take da rawani kuma tana sanye da baƙaƙen tufafi a gadon bayanta tana ɗauke da wata zabgegiyar takobi, shigar da ta yi matuƙar yi mata kyawu. Tafe muke cikin hanzari ta gaba ina biye da ita a baya, tsawon daƙiƙa ɗari biyu muna cikin wannan hali babu wanda yace ƙala. Sannu a hankali har muka iso wata makekiyar gona mai ɗauke da alkama mai tsawon hetta goma. Koda muka iso ɗin sai Raudatul-Abyad ta miƙa min fartanyar dake hannunta gami da lauje na karɓa sannan ta yi min nuni da na fara aiki batare da buɗi baki ta ce min uffan ba, kawai sai ta durfafi gindin wata itaciya ta kwanta bisa wata tabarmar kaba mai haɗe da matashi, kawai sai na duƙufa na fara aiki, wasa-wasa sai ga shi na shafe tsawon sa'a ɗaya a cikin wannan yanayi, koda na ɗaga kaina na duba aikin da na yi sai naga ashe bai huce kunya goma ba, a wannan lokaci hasken rana ta fito ta fara zafi ainun. Al'amarin da ya sanya kishi ya fara damuna, kuma gadon bayana ya fara ciwo. Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ina cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai na ga waɗansu masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, cikin wani irin zafin nama na dinga zillewa kibbau ɗin tare da falfalwa da azababban gudu izuwa inda Raudatul-Abyad ke kishingiɗe domin na bata kariya, a wannan lokaci barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, koda ya rage saura taku biyar na isa daf da ita kwatsam ba zato babu tsammani sai waɗansu irin samudawan dakaru suka yi fitar burgu daga duhuwar dajin, Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, fuskokinsu a rufe suke da hulunan ƙarfe, a hannayensu suna ɗauke da miyagun makamai dangin Gatari, sungumi, majaujawa, al'amudi da sauran su. Adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya, kafin nayi wani yunƙuri sun yi min ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu. Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakaninmu sai na lura wani badakare ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad. Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo, daga can sai wani narkeken ƙato ya fito daga cikin su, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa shine shugabansu saboda hular kwanon da ke kanshi da takobinshi da ta kasance ta musamman, Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har iya isa daf! Da inda Raudatul-Abyad take ta yadda suna jin numfashin juna. Kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba, daga bisani kuma sai ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da SAƘON MUTUWA, sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya dubi Raudatul-Abyad ya ce "ya ke Raudatul-Abyad 'ya ga tsoho Abu-Raudat kiyi sani cewa dama na faɗa miki in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za su haɗu, kuma rabon kwaɗo baya hawa sama koda ya hau zai sakko. Yau ga shi kin faɗa tarkona wanda ya za ki iya tserewa ba, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan kashe wannan baƙo naki a gaban idanuwanki sannan na tafi dake a matsayin sabuwar amaryata…". Kafin narkeken ƙaton ya gama rufe bakinshi ya gama rufe bakinshi Raudatul-Abyad ta tari numfashin shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "Dawazul-kiryan kayi sani cewa haƙiƙa ka tafka babban kuskure da rafkananniyar zuciyarka ta yaudare ka cewa za ka ci galaba a kaina, ka sani cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA ba za su taɓa zamtowa abu guda ba, ni MURUCIN KAN DUTSE ce ban fito ba sai da na shirya. Kuma ni ƙadangaren bakin tulu ce.. Shawarar da zan baka ita ce ka gaggauta miƙa wuya gare ni wata ƙila ka samu tsira da ruhinka"; Dawazul-kiryan ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya ce "haƙiƙa ƙi faɗin ki tana matuƙar burgeni domin masu iya magana na cewa wai matsoraci baya zama gwani. Amma kar ki manta cewa alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, kuma koda ba a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza. Kuma dai SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI. "Haƙiƙa ka makara wajen cimma wannan burina naka, amma ko ba komai an ce ba a ƙwacewa yaro garma. Kuma inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa" Raudatul-Abyad ce ta yi wannan furuci cikin matuƙar fushi. Dawazul-kiryan ya ce "ai zuwa a makare yafi zuwa a makara, kuma duk mai nema yana tare da samu". Koda gama faɗin hakan sai yaran Dawazul-kiryan suka yi wuf suka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa sannan suka yi ɗauki izuwa kaina. Yayin da naga hakan sai na zare takobina ya ruga gare su domin tarar juna, Lokacin da aka haɗu sai a kayi KARON MAZA, aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, ana fara wannan artabu ne na fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba. Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje ta cika dodon kunne, duk sa'adda na kaiwa dakarun hari sai ka ga sun kare tare da mayar da martani, in da ba don ina da matuƙar zafin nama ba da tuni sun murƙushe ni saboda yadda suka yi min rubdugu tamkar yadda dandazon ƙudade ke yanyame ƙwallon mangwaro. Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi kuma na fahimci cewa idan aka cigaba da wannan artabu a haka wankin hula zai kai ni dare kuma dakarun za su samu nasarar kashe Raudatul-Abyad. Koda na zo nan a tunani na sai na fusata ainun na sake dage damtse ina kai sara da suka cikin matuƙar zafin nama, gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canja dole rawa ma ta canja, faruwar hakan ke da wuya sai na fara samun galaba akan dakarun, yazamana cewa duk inda na sanya a gaba sai dai kaga fili fetal dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga. Al'amarin da ya fusata sauran mayaƙan kenan suka sake yin ɗauki izuwa kaina, kafin shuɗewar daƙiƙa ɗari kacal na kashe fiye da rabin dakarun. Nan fa JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda. Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan artabu na zubar da dukkan mayaƙan a ƙasa hatta badakaren da ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad, illa shugaba Dawazul-kiryan ne kaɗai a tsaye fuskarshi a murtuke tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakani na da Dawazul-kiryan na wani lokaci daga can sai ya dube ni cikin kakkausar murya mai tattare da fushi ya ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin taurin kai da shisshigi kayi sani cewa zaki koda ya mutu gawarshi abar tsoro ce, KARO DA GOMA kalacen safe in ji masu iya magana, kuma masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yanka wa ba ne. Saboda haka idan ka miƙa kan ka izuwa gare ni, zan yi maka kisa mafi sauƙi ta hanyar datse gaɓoɓin jikinka ɗaya-bayan-ɗaya ba tare da kasha wahala ba. Idan kuwa ka ƙi to zaka gwammace wa aya zaƙin ta"; Kafin ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka mishi tsawa na ce "ya kai wannan tsohon AZZALUMI kar ka manta cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Kuma shi zalunci baya ɗorewa a doron ƙasa, don haka sai ka shirya ga maza nan bisa kan ka. Koda gama faɗin sai na ɗaga takobina na durfafi inda yake tsaye ina kururuwa koda ganin hakan sai Dawazul-kiryan ya yi wuf ya zare wani zabgegen gatari a gadon bayanshi ya yi ɗauki kaina, muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Koda fara wannan artabu sai Raudatul-Abyad ta koma gefe guda ta harɗe hannaye tana kallon yadda gumurzun ke wakana. Nan fa muka wanzu muna kai wa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA. kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, kuma idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu wanda yake yin fito-na-fito da ita face GWARZON ƘARNI. Kuma masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne ma fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Ga wanda ke kallon yadda gumurzun ke wakana zai fahimci cewa Dawazul-kiryan ya nunka ni a ƘARFIN DAMTSE sau uku. Domin kuwa duk ya kai min hari da gatarinshi idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci na fara galabaita ya zamto ba na iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kaina, ana cikin wannan hali ne Dawazul-kiryan ya shammace ni ya makamin ƙotar gatarinshi a akaina saboda ƙarfin dukan sai dai kan ya tsage jini ya yi tsartuwa, saboda matuƙar zugi da raɗaɗi ban san sa'adda na kurma ihu ba na yi taga-taga zan faɗi amma sai na turje, sai dai kash! Kafin na dawo cikin hayyacina ya sake samun nasarar makamin a wuya. Nan take na sulale ƙasa magashiyan ina nishin wahala. Koda samun wannan gagarumar nasara sai Dawazul-kiryan ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska ya dube ni ya ce "ai da ma na faɗa maka a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe" kuma komai tsananin duhun dare gari zai waye". Yanzu ga shi kana kusa da baƙuntar barzahu za ka yi mutuwar wulaƙanci, alfarma ɗaya zan yi maka ita ce ka rubuta wasiyyarka kafin na zare maka ruhi daga gangar jiki". Duk wannan abu dake wakana sai Raudatul-Abyad na tsaye a gefe guda tana kallo. Dawazul-kiryan na gama faɗin hakan sai ya durfafi inda nake kwance ya raba ƙafafuwanshi biyu a kaina yana mai yi min murmushim mugunta, kawai sai ya ɗaga gatarinshi domin ya datse min wuya, kawai sai wata hikima ta faɗo min na damƙi ƙasa a hannuna na watsa mashi a fuska. Kafin ya wartsake na miƙe tsaye zumbur na sanya takobina na sare mashi wuya take kan yi fitar burgu jini ya yi feshi gami da tsartuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica!. Nan take na faɗi ƙasa bisa gwiwoyina cikin matuƙar galabaita. Cikin matuƙar kaɗuwa Raudatul-Abyad ta rugawa izuwa inda nake ta rungume a ƙirjinta tana mai fashe da kuka mai tsuma zuciya duk da kasancewar ina cikin mawuyacin hali sai da naji sanyi a raina gami da farin ciki. Bisa jin Raudatul-Abyad a daf da ni. Sannan daga bisani ta janye jikinta daga gare ni muka fuskanci juna cikin alamun matuƙar tausayi ta dube ni kana ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai ɗan-karen daɗi tamkar alagita ta ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin sadaukantaka haƙiƙa na yaba da sadaukantakar ka kuma ma yarda cewa kai mai amana ne, kai ne irin namijin da ya dace ya zamto abokin rayuwata. Ina mai matuƙar farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara. Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa. Daga wannan furuci ne kuma ta shiga bani kulawa inda ta tashi tafaɗuna muka isa ƙarƙashin itaciya ta zaunar da ni sannan ya ɗauko salkar ruwa ta buɗe murfin ta ta sanya hannunta ta tallafo wuyana ta kafa min a baki na shiga kwankwaɗar ruwan har na ƙoshi, kana ta buɗe wata jakar fata dake sanye a kwiɓin cinyarta ta buɗe ta ɗauko wani gashasshen naman barewa ta shiga bani a baki ina ci cikin matuƙar tsantsar soyayya da tausaya wa. A iya tsawon rayuwata ban taɓa sanin cewa haka so yake da daɗi ba. Haƙiƙa so shine sinadari mafi girma dake sanya zuciya da ƙarfafa garkuwar jikin ɗan Adam. So shi ne linzami da yafi ƙugiya ƙarfi wajen sarrafa bil'adama a doron ƙasa. Haƙiƙa so kan sauya duniyarmu daga kowanne ƘARSHEN KARNI izuwa SABON ƘARNI mai cike da abubuwan ban mamaki. Tabbas so shine ni'ima mafi daraja a cikin dukkanin wata al'umma. A wannan rana haka muka kasance tare da Raudatul-Abyad tana ba ni kulawa mai cike da tsantsar bege da soyayya. Sai da la'asar sakaliya sannan muka nufi komawa izuwa gida, da yake a wahale nake sai ya zamana daƙyar nake iya takawa domin haka kafin mu isa gida duhun dare ya kawo kai. lokacin da muka samu nutsuwa sai Raudatul-Abyad ta kwashe dukkan labarin abin da ya faru da damu ta zayyanawa mahaifinta Abu-Raudat daga farko har ƙarshe. Koda jin wannan labari sai farin ciki ya turnuƙe shi bai san sa'adda murmushi mai taushi ya suɓuce mashi ba ya dube ni cikin murya mai tattare da dattijantaka ya ce "ya kai Matawus kayi sani cewa kai ne matashi na arba'in da biyar da suka zo gare ni domin na bayyana masu hanyar da za su haye tekun dake gaɓar mu domin su isa izuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar. Babu wani mahaluki ɗaya a cikin su da ya samu nasarar cinye jarabawar da na yi masu sai kai, 'ya ta Raudat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai yi tozali da ita face ya kamu da matuƙar sha'awar ta, amma gashi ka keɓance da ita ba tare da ka haike mata ba, Sannan kana da halin da za ka ƙi ceto rayuwar 'yata a lokacin da dakarun sumame suka farauce ta. Tsawon lokaci ina jiran zuwan jarumin da zan damƙawa amanar 'yata a hannun nagartaccen namiji, kuma GWARZON ƘARNI amma sai a yau na cimma burina. Kasancewar a halin yanzu shekaru na sun ja tsufa ya kamani kuma cutar da nake fama da ita a koda yaushe rai zai iya yin halin shi, domin hakan dole na miƙa ragamar abar kaunata kuma farin cikina ga wanda zai bata farin cikin rayuwa har abada. Ina mai farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara akan abin da ka fito nema". Lokacin Tsoho Abu-Raudat yazo nan a zancen shi sai ya sanya hannunshi ya ɗaga gefen shimfiɗar da yake zaune ya ɗauko wata jemammiyar fatar barewa ya miƙa min sannan ya ci gaba da cewa "wannan ita ce taswirar da zata kai ka izuwa fadar boka Bazzagul-Nadiyar da dukkan bayanan kowacce ƙofa da dokokin shiga fadar. Sannan ina mai damƙa maka amanar 'yata ka riƙe min ita cikin aminci, bana sa rai za ku dawo ku same ni a raye. Zan haɗa ku da hadimin da zai yi maku rakiya a cikin wannan tafiya har ku cimma nasara. Koda gama faɗin hakan sai Abu-Raudat ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar fita daga bukkar cikin hanzari ni da Raudat muka rufa mashi baya. Ya yin da muka fito ne sai Abu-Raudat ya buɗe bakinshi yana mai karanto waɗansu ɗalasimai da shi kaɗai ya san me ya ke furtawa. Yana gama rufe bakinshi sai ga wata shirgegiyar halitta tana keto wa daga cikin gajimare sannu a hankali wata irin iska mai ta karaɗe wajen, wacce ta haddasa kaɗawar rassan bishiyu sai da halittar ta sauka a bisa turba sannan komai ya samu dai-daituwa ita dai halittar takasance wani narkeken ƙaton aljani mai girma da munin tsiya, yana rusheshen kai mai ɗauke da 'yan mini-minin idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshi mai girma ne ƙofafin masu faɗi tamkar mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar ƙofar gari mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora babu kyawun gani. Yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda goma a kowanne kwiɓin hammatarshi, gaba ɗaya jikinshi cike yake da wani irin baƙin gashi buzu-buzu. Babban abun da ya ƙara mashi muni shine wani zabgegen gemun shi mai tsawon kamu shida. Kaico! Haƙiƙa babu wata halitta mai numfashi da za ta yi tozali da wannan aljani face ta yi nadamar wanzuwar ta a doron ƙasa. Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Abu-Raudat, Sannan ya buɗe bakinshi a karo na farko ya fara magana cikin wata irin kakkausar mai kama da saukar aradu, kanshi a sunkuiye ya ce "ya shugabana yau fiye da shekaru hamsin rabon da ka yi min wannan kiran, tun lokacin kana samartaka. Me kake da buƙata gane gare ka ya ubangidana". Abu-Raudat ya dube shi ya ce "ya kai Jauharul-layal kayi sani cewa na kira ka nan domin ka yi wa 'yata Raudat rakiya tare da wannan saurayi izuwa fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar. Koda jin wannan batu daga bakin Abu-Raudat sai Jauharul-Layal ya risina cikin ladabi sannan ya dube shi cikin matuƙar damuwa ya ce "ya shugabana kana ganin cewa zamu cimma nasarar shiga fadar Sarkin bokaye kuwa kar ka manta cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai ɗauke da musiba da annoba tamkar fadar Bazzagul-Nadiyar". Koda jin wannan batu sai Abu-Raudat ya dube shi ya ce "haba sarkin matasan aljanu kai ne fa ANNOBA ƊARI mai share TAWAGAR MAYAƘA kai ne hadari mai shayar da RUWA DA ISKA na musiba. Faɗuwar gaba asarar namiji, shin har akwai wani mahaluki da zai razana ka". Koda jin wannan kirari daga bakin Abu-Raudat sai jikin Jauharul-Layal ya kama tsuma tamkar nazari, ya ɗago da kanshi cikin ladabi ya ce "ya shugabana na rantse da ƙabarin kakana Marganun-uƙub ba zan dawo gare ka ba face na samu nasara shiga fadar bokaye. Koda gama faɗin hakan sai Jauharul-Layal ya shimfiɗe gadon bayanshi, Nan take Raudatul-Abyad ta ruga izuwa inda mahaifinta yake ta faɗa kan ƙirjinshi tana mai fashe da kuka, Abu-Raudat ya rungume ta, na wani lokaci daga bisani ta janye jikinta daga nashi ta dube shi cikin alamun matuƙar tausayi lokacin da idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta ce "ya abbana haƙiƙa na shaƙu da kai ainun tsawon shekaru tun ina yarinya ƙarama, ban san kowa ba sai kai, yau ga shi zan tafi nayi nesa da kai inda bana da tabbacin zamu sake saduwa da juna ba"; Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai mahaifinta ya dube ta lokacin da ƙwalla ta cika mashi idanu ya dube ta ya ce "ya farin cikin rayuwata kuma sanyin idaniyata kiyi sani cewa na fi ki jin zafi da raɗaɗin rabuwa dake, domin a halin yanzu na rasa komai na jin daɗin rayuwa, dukiya, mulki da SADAUKANTAKA. A halin yanzu yanzu shekaru na sun ja a Kowa ne lokaci ajali zai iya riskata, domin koda a halin yanzu bamu rabu ba, tabbas akwai mutuwa. Kin ga dole na zaɓa miki abin da zai inganta rayuwarki kuma ya ba ki farin ciki. Wasiyya ta a gare ki ita ce duk sa'adda rai da rabo suka kai ki izuwa birnin Madinatul-Aswaj ki cika burin zuri'armu na ɗaukar fansa akan sarauniya Jauharat. Lokacin da tsoho Abu-Raudat ya zo nan azancen shi sai duk biyun suka fashe da kuka mai tsuma zuciya suka sake ƙanƙame juna. Al'amarin da ya sanya na ji ƙwallar tausayi ta zubo min, domin rabuwa da masoyi babu daɗi, duk da dake War zuciya irin ta aljani Jauharul-Layal sai da ƙwalla ta zubo mashi. Tsawon daƙiƙa hamsin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Raudatul-Abyad ta janye jikinta daga na mahaifinta ta nufi inda nake, ba tare da wani ɓata lokaci ba ni da ita muka hau bisa Jauharul-Layal muka zauna. Jauharul-Layal ya yunƙura cikin zafin nama irin na GWARAZAN JIYA ya buɗe manyan fuka-fukan shi ya tashi izuwa sararin samaniya ya fara keta giza-gizai. Tun Abu-Raudat na iya hangen mu har muka ɓace mashi da gani, ana fara wannan tafiya sai na cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin matsanancin gudun da Jauharul-Layal ke yi, domin a iya tsawon rayuwata ko a tarihi ban taɓa jin aljani mai matuƙar gudu a sararin samaniya tamkar shi ba. Sai da muka shafe tsawon sa'a bakwai a sararin samaniya muna tafiya babu sassauci ba tare da mun yada zango ba, lokacin da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ne, Jauharul-Layal ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a bisa turba. Inda aka saukar ya kasance daji mai tattare da dogwayen bishiyu, duwatsu, ƙoromu da sarƙaƙiya. Ko iya shirun da ya wanzu a dajin ya isa ya jefa razani a zukatan duk wata halitta. Cikin alamun matuƙar damuwa na dubi Raudatul-Abyad na ce "ya sarauniyar kyawawa shin bakya ganin cewa yada zango a wannan daji a haɗari sosai, ki duba ga ki ga yadda yanayin shi yake ? Har Raudat ta buɗi baki da nufin ta furta wani abu sai sarkin matasan aljanu ya yi caraf na tari numfashin ta ya ce "ai an kare zai yi cizo ake siyo shi a kiwata. Domin koda akwai abubuwa masu cutar a wannan daji dole ne mu yada zango domin mu samu ƙwarin jikin da zamu tunkari fadar Sarkin bokaye". Raudatul-Abyad ta ce "kwarai kuwa zancen ka dutse ya sarkin matasa, domin haka sai mu kasance cikin shirin ko ta kwana". Koda gama faɗin hakan sai muka nufi wata itaciya, bayan mun zauna a ƙarƙashin ta sai muka fito da abin guzuri muka shiga kimtsa cikinmu, bayan mun kammala ne sai muka kishingiɗa domin mu huce gajiyar dake tattare, shi kuwa Jauharul-Layal sai ya shiga yin rangadi a wajen domin tabbatar da cikekken tsaro. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a wajen. Budurwar ta kasance doguwa mai kyawun diri da sura. Hancinta dogo ne mai lankwasa da kyawu a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta mai kyawu ne dogo tamkar na barewa, kirjinta cike yake kuna a tsaye ƙyam! Ba su ranƙwafa ba, sai sheƙi suke tamkar nunanniyar gwanda, gwanin ban sha'awa, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya buɗe ya yi tudu ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi da fatar su ta kasance luwai-luwai tamkar ta jaririya sabuwar haihuwa, sanye take cikin tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama da suka kama jikinta ainun duk wata sura da zata ja hankalin namiji ta bayyana. Wohoho! Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kwaɗaitu da sha'awarta Sa'adda muka yi arbda da wannan kyakkyawar sura sai muka miƙe tsaye zumbur! Aka fara kallon-kallo tsakaninmu, a iya tsawon rayuwata ban taɓa ganiko jin wata 'ya mace mai kyawu tamkar budurwar ba. Duk da irin kyawun diri na Raudatul-Abyad amma budurwar ta zarce ta matuƙa ainun. Tsawon daƙiƙa hamsin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne kyakkyawar budurwa ta buɗi cikin wata irin zazzaƙar murya tamkar ana busa sarewa ta ce "yakai Matawus ibn Raziwan tare da Raudatul-Abyad bintu Abu-Raudat ku yi sani cewa tsawon shekaru huɗu ina jiran dakon samun ku domin na mallaki taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar domin cimma burina na ɗaukar fansar ran mahaifina a hannun sarakunan duniya huɗu na kuma mulki duniya baki ɗaya. Fatana na cikawa abbana burinshi na mulkar duniya baki ɗaya, Saboda haka kira na a gare ku ku gaggauta damƙa min taswirar fadar cikin ruwan sanyi, idan kuwa kuka ƙi ta lumana azabar KAIFIN TAKOBI na zata tabbata a gare ku". Koda jin wannan batu daga bakin kyakkyawar budurwar sai na dube ta cikin matuƙar fushi na ce "ya ke wannan AZZALUMA kiyi sani cewa haƙiƙa rafkananniyar zuciyarki ta yaudare ki da ta bayyana maki cewa za ki iya yi mana fashi da makami, wato ƙura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Kuma ina so kiyi sani cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza" kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Zamu ga yadda za ki karɓe taswirar daga hannunmu." Koda jin wannan daga bakina sai kyakkyawar budurwar ta fusata ainun, idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur, har ƙwalla ta zubo mata ta dube mu ta ce "haƙiƙa rashin sani ne ya sanya har ka amba ce ni da azzaluma, amma akwai buƙatar na sanar da ku labarina a takaice. Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan kayataccen littafi. Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi 08137237071