GWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part A Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey AI'amarin jaruma Ilaila kuwa ko da ta ga an harbo kibiyoyi an kashe abokan tafiyarta guda shida nan take sai ta yi wuf ta suri garkuwarta da takobinta ta shammaci mai hular karfe ta gabza mata naushi a ka da garkuwar dake hannunta. Saboda karfin naushin sai da mai hular karfen ta hantsila baya ta rinka mirginawa a kasa izuwa can inda koramar nan take. A lokacin ne aka ci gaba da harbowa Ilaila kibiyoyi amma sai ta dunkule jikinta waje daya ta kare jikinta da garkuwarta. Sai da ta ji kibiyoyin sun daina dira akan garkuwar tata sannan ta mike tsaye zumbur ta falfala da masifaffen gudu i zuwa cikin dajin Hairil Salas sakamakon ta fita daga cikinsa ta bi hanyar da Nazima ta bi! Haka dai ta cigaba da gudu ba waige amma saita ci gaba da ganin ruwan kibiyoyin wasu suna wucewa ta samana wasu ta gefenta. Kawai dai tsananin sa'a ne da nisan kwana suka sa ko kibiya daya ba ta soke ta ba. Ba ta daina ganin ruwan kibiyoyi ba masu kawo mata hari har sai da ta shafe sama da rabin sa'a tana gudu. A wannan lokacin ne ta yi tuntube ta fadi kasa, ta dinga mirginawa a kasan da gudu ba ta ankara ba sai ji ta yi a fado kasa cikin wani rami mai tsananin zurfin gaske don haka sai ta kurma uban ihu lokacin da ta saddakar da cewar ajalinta ya zo. Ba zato ba tsammani sai ta ji fanjam ashe cikin ruwa ta fado. Ko da tai nutse izuwa karkashin ruwan sai kanta ya bugu a jikin wani dutse nan take ta suma. Hakika mai rabon ganin badi ko ana daka shi a turmi sai ya gani, maimakon Ilaila ta cigaba da nutsewa i zuwa kasan kogon da ta fada sai gashin kanta ya nannade a jikin jelar wani katon kifi da ya zo giftawa da gudu. Ai kuwa sai ya janyeta ya tafi da ita yana ta gudu har sai da ya iso gabar kogin sannan gashin kan nata ya warware daga jikin jelar kifin kuma sai ambaliyar ruwan ta hankadota wajen cikin rairayi. A wannan lokaci alfijir ya keto an fara wata irin iska mai karfi da sanyi, wannan iska ce ta sa Ilaila ta fartado daga dogon suman da ta yi ta mike zaune a matukar firgice sannan ta dubi gabas da yamma kudu da arewa. Ko da ta liga inda take ta tund lokacin da tuntube ta fado kasan rami ta kalli kogin dake gabanta kuma ta hango hisan dake tsakanin gabarnkogin da can saman ramin da ta fado sai ta cika da tsananin mamaki Ya ya aka yi har na iya ketare wannan kogin na iso nan? Amsar da Ilaila ta kasa bai wa kanta kenan amma sai wani abu ya fado mata a rai ta ce duk yadda aka yi suma na yi sa'adda na fada cikin kogin nan kuma akwai yiwuwar cewa wani ne ya kawo ni nan ko kuma wata dabbar ruwan ce ta janyo ni nan. Gama ayyana hakan ke da wuya Sai ta hango kyallen wuta a can nesa sosai a bayan wani kogon dutse, da yake har a sannan gari bai|yi gaske ba sai Ilaila ta mike tsaye ta kama sanda ta nufi inda wannar hasken wuta yake. Sannu a hankali ta kusance wajen sai ta fara jiyo sautin muryar mutane da yawa suna a hira. Sai da ta matso daf da su sannan ta labe a bayan kogon dutsen ta kasa kunne tana sauraron hirar da suke yi. Kawai Sai ta gane cewa ai wadannan mutane ba wasu ba ne face rukunin dakarun $umame na চiyu, kuma Shugabansu ne yake cewa "Ya zama wajibi mu yi shiri, mu bi bayan mayakan nan mata wadanda suka rage ba su mutu ba. Kun sani dai labarl ya riskenmu cewa a cikin su akwai wata shaidaniyat da ta fi shugaban yan rukunin farko iya yaki har ma ya ajiye mukaminsa ya bar dajin nan. A halin yanzu yaransa sun kashe mutum $hida daga cikin mayakan matan, an harbi daya da kibIya a kafadarta amma tsere an nemeta an rasa. Ita ma Wannan hatsabibiyar cikin nasu ta gudu ba a ganta ba. Barita ce ta kawo mana wannan labarin kuma tanal cikin dajin nan tare da wasu daga cikin dakarun rukuni na uku suna farautar ta hatsabibiyar jarumar. "Lallai duk inda take sai sun cimmata. Yanzu tun da mun yi kalaci sai ku tashi mu hau dawakanrnu mu ruga 1 zuwa can wajen dajin nan domin mu cimma mayakiyar da aka harba a kafada kafin ta isa birmin Misira saboda Sarki Marhat ya ce lallail kada a bar a ta fita a raye. Za mu bar mutum daya jal ya yi gadin komai namu da ke cikin wannan kogon dutse." Gama fadin hakan ke da wuya sai shugaban dakarun sumame na biyu ya mike tsaye suma sauran yaran nasa sa Suka mike gabadayansu. Nan take Suka debi makaman yakinsu suka hau dawakal suka bi hanyar da za ta fitar da su daga cikin dajin gabadaya Suka bar badakare guda daya jal zaune a kofar kogon dutsen yana gadi. Sai da Ilaila ta tabbatar da cewa wadannan dakaru sun yi nsia da tafiya sannan ta cigaba da tafiyar sanda har ta iso bayan wannan badakaren da aka bari gadi bai ji motsınta ba, kawai sai ta hannayenta biyu tal kama kansa ta murde masa wuya, ta yar da gawarsa kasa. Ckin anzari] ta cire tufafin Badakaren ta sauya da nata, kawai sai ta dauki gawar ta jefa bayan wasu duwatsu yadda babu mai gani ta. Nan take Ilaila ta dauki makaman yakin badakaren da ta kasheh ta kwance dokinsa ta hayenkuma tajuya da baya, ta nufi hanyar da yan'uwansa suka bi! Maimakorn laila ta bi sawun dawakan dakarun sai a bi wata hanyar daban wacce za ta iya shan kansu ta ci gaba da yi wa dokinta Kaimi. Ashe wannan hanyar da ta bi anan ne ragowar rukuni na hudu na dakarun Sumame suke kuma kowane rukun sansaninsu daban. Tabbas zakaran da Allah ya nuta da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Da gudu bisa doki Ilaila rinka wuce sansanin dakarun sumamen har guda hudun sa dai kawai ta daga musu hannu su daga mata amman babu inda aka tsayar da ita. Dalili kuwa shi ne tana sanye da kakin dakarun sumame na biyu da kuma irin kayan yakinsu ajikinta. Da yake gabadaya tukuni su shidan sun san junansu kuma sun san kalar tufafinsu da makamansu wannan yasa ta tsallake bincike. Haka dai Ilaila ta ci gaba da gudu bisa dokinta ba sassauci har sai da rana ta kwalle. A daidaı lokacin ne ta iso iyakar daji da birnin Misira, kawai sai ta hango Nazima a guje bisa kafafunta ga dakarun sumame bayanta bisa dawakai su ma a guje suna kokarin cimmata amma saboda karfin gudun nata sun kasa cimma ta. Har i zuwa wannan lokaci akwai kibiya soke a kafadar Nazima ba a cire ta ba, amma saboda juri ya da jarumtaka ta kk yarda dakarun Sumamen su ¢immata. Saura bai taku biyar ba wani Badakare ya cimma Nazima har ma ya kai mata sara da takobinsa ta sunkuya ya sari iska sai ta daka tsalle ta tsallake iyaka ta fada cikin yankin birnin Misira ta fadi Kasa da ruf da ciki. Ko da ganin haka sai Dakarun Sumamen Suka kada linzamin dawakansu suka juya da baya suka koma inda suka fito. Duk wannan abu da yake faruwa Ilaila ta buya cikin duhuwar ciyayi tare da dokinta tana kallo. Har dakarun sumamen suka zo suka wuce ta kusa da ita amma ba su ganta ba. Ita kuwa Nazinma ko da ta ga dakarun sumamne sun hakura sun koma da baya ízuwa cikin daji sai ta yunkura da nufin ta mike sayc ta nufi cikin birnin Misira. Kawai sai ji tayi an maketa ta baya. Nan take ta sulale kasa sumammiya. Ba wani ba ne ya maketa ba face jaruma mai hular karfe. Kawai sai ta sunkuya ta dauketa ta dora ta a kan wani doki da ta zoda shi sannan ta hau dokin ta kada shi ta nufi hanyar da za ta kai ta inda kurkukun mata yake na birnin Misira Lokacin da Ilaiia ta ga abin da ya faru ga Nazima sai ta kada dokinta ta nausa wani bangaren dabaru na dajin. A can cikin daji ne ta rabu da dokin kuma ta cire tufafin da ke jikinta na dakarun sumame ta sanya nata kuma ta rufe fuskarta, sannan ta sake dawowa kofar birnin Misira ta shiga cikin gari. Sai da Ilaila ta shafe kwanaki goma sha úku tana boye cikin birnin Misira sannan ta yi shiri rana daya ta yi kundumbala ta haura gidan Sarkin Misira da tsakar dare domin ta kashe shi. Wannan shi ne sanadin da aka kamata aka jefa ta cikin keken doki aka ka ta kurkukun mata na birnin Misira. Daga wannan rana Ilaila ta ci gaba da rayuwa a cikin kurkukun birnin Misra. Duk bayan kwana bakwai sai Sarki Marhat ya kawo nata ziyara har kurkukun. Abin da yake gaya mata kawai shi ne, "Kin tuno inda mahaifinki ya boye littafin sirrina?" Idan ta ce 'a'a" ko kuma ta girgiza kai alamar cewa bata sani ba to ko kallonta ba ya yi sai kawai lya juya ya yi tafiyarsa. Sau uku Ilaila tana guduwa daga kurkuku amma shugaban dakarun kurkukun Gadaraz yana bin ta ya kamota, ya dawo da ita kuma duk sa'adda ya dawo da ita sai an yi mata azaba ta tsawon sati guda. Akaro na ukun ne da ya kamata suka yi kazamin artabu wanda kowannensu ya jigata ainun kuma ya kasa amfani da karfin sihirin tsafinsa a kanta sakamakon a ranar ya manta bai dauko kambunsa na tsafi ba ya daura karfin ya biyo sawunta. Sa'adda suka yi kare jini biri jini suka zube akasal suna haki da numfarfashi a yanáyin da dayansu ba zai iya mikewa ba sai ya dubeta ya ce Wai ke mene ne dalilin daya sa ba za ki daina kokarin guduwa daga wannan kurkukun ba? Ilaila ta dube shi ta ce "Saboda na san cewa wata rana zan iya tuna inda mahaifina ya boye littafin sirrin sarki kuma da wannan littati ne kadai zan iya daukar fansa a kansa. Kai kuma mene ne dalilin da ya sa ka tsaya kana bata lokacin ka kana bautar tsaron kurkuku alhalin käna da wannan karfi da jarumtaka kuma da sihirin tsafi haka" Lokacın a Gadaraz yaji wannan tambaya sai ya yi ajiyar numfashi sannan ya dago kai ya dubi Ilaila ya ce 'Matsalata da taki kusan iri daya ce. Asalin masarautar garin han ta Kakannina ce, kakan Sarki Marhat ne ya kashe Kakana na biyu ya gaje karagar mulkinsa. Ba ni da wani buri a duniya wanda ya wuce naga na dawo da Wannan masarauta hannun zuri'ata to amma na san cewa abu ne wanda ba zai yiwu ba cikin kankanin lokaci. Bisa wannan dalili ne nima tun ban fishekara tara ba a duniya na rinka bai wa kaina horona yaki da jarumta kuma na rinka bin bokaye ina yi musu bauta, ina samun sihiri a wajensu domin na yi gagarumin shirin yin juyin mulki a kasar nan. A zaton sarki Marhat babu nutum daya da ya yi saura daga cikin zuri'ata alhalin bai san cewa ni ina raye ba. Ke ma kin yi ganganci kuma| kin yi gaggawa da ki ka bayyana kanki a a gare shi domin ba za ki ya samun nasara ba al yanzu. Yanzu idan na mayar da ke kurkuku za aci gaba da gana miki azaba ne irin wacce ta fi ta baya ni kuma ba zan iya jurar ganin hakan ba. Ko da jin haka sai mamaki ya kama Ilaila ta dube shi tace "Mene ne dalilin da yal sa ba za ca ya jure ganin yi min azabar ba?" Gadaraz ya ce "Saboda yanzu na gane cewa ciwo na irin naki ne don haka idan ana yi miki azabara cikin jikina zan rinka jin ta. Baya ga haka tun ranar da kika fara guduwa daga kurkukun nan na biyo ki muka yi artabu na ga irin jarumtákarki sai ta burge ni kawai na ii ina kaunarki. A tsawon zamanki a kurkukun na wata tara kullum idan na ganki sai naji kina dadđa shiga raina, Ayau din nan da na san wace ce ke sai na ji na kamu da tsananin tausayinki gami da matukar kaunarki a zuciyata. Zan so a ce ki zamo abokiyar rayuwata tun da mundace da juna a jarumtaka da kuma kaddarar rayuwa". Sa'adda Gadaraz ya zo nan a jawabinsa sai |laila ta kur amasa idanu nan take hawaye ya xubo mata Sannan take ta rungume hi tare da fadawa kan kafadarsa suka rungume juna. Daga can saj Ilaila ta janye jikinta daga cikin nasa ta dube shi ta ce Yanzu mene ne abin yi?" Gadaraz ya ce "Báza mu koma kurkukun birni Misira ba birnin Kisra za mu tati Sau uku sarkin Kisra yana yi mini tayin na je na kula da kurkukunsa zai rinka biyana albashi mai tsoka ninki ukun wanda Sarkin Misra ke ba ni amma naki saboda mafarkin dake raina na yin juyin mulki. Yanzu zanje na karôi wannan aiki, idan kin amince sai mu yi aure amma burinmu na nan na daukar fansa a kan Sarki Marhat kawai dai za mu cigaba da yin.bincike a kan yadda za mu sami nasarar cika burinmu." Wannan shi ne asalin haduwan Ilaila da Gadaraz har suka yi aure a birnin Kisrai suka cigaba da rayuwarsu a wannan kurkuku. Aranar farko da aka kawo jarumi Insam Gadaraz na yin arban da shi sai ya ga ai kamanninsa iri daya ne sak da na Sarki Marhat tamkar an tsaga kara. Hatta tsayinsu da kaurin jikinsu iri daya ne, abin da ya kara daure masa kai shi ne Insam na yin magana sai ya ji muyarsa ma irin ta Sarki Marhat ce. Nan take wani tunani ya fado a zuciyar Gadaraz ya ce "Wannan mai laifin zai iya zama makamin da za mu ya cika burinmu hi da Ilaila a kan Sarki Marhat. Lokacin da aka shigo da Insam cikin wannan kurkuku na birnin Kisra har Gadaraz ya zo wajensa ya gan shi Şuka yi magana ya tafi sai ya sami Ilala ya ba ta labarin Insam da ya gani yanzu kuma ya gaya mata cewa za su yi amfani da shi wajen cika burinsu. Nan take farinciki ya turnuke Ilaila ta daka tsalle ta fada kan kirjinsa suka fada kan gado anan barci ya sace su. Karar wannan kaho da aka busa ne ya tashe su daga barcin. Lokacin da Gadaraz ya fito daga bangarensa na gidan kurkukun dauke dal makamansa na yaki yana mai falfalawa da gudu sai ya nufi inda ya ga dakaru na tafiya al guje, a hanya ne ya yi ta tsallake dakarun da su Insam suka banbanke zube a kasa fululu, wasu ma sun sami raunuka a sassan jikinsu sun kasa nikewa tsaye. Kuyi hakuri kwana biyu shiru in sha Allahu ba zamu kara daukar long time irin haka ba fatan alheri gareku masoya masu bibiyar wannan littafin. Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799GWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part B Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Insam da Barsad suka ci gaba da watsar da dakaru a kasa suna ta falfalawa gudu. Wani lokacin har tsalle suke yi sama suna hayewa kan katangu da rufin dakuna suna dira kasa. Kafin Gadaraz ya riskesu tuni sun iso inda rariyar gidan take wacce aka rufeta da shafen sumunti, cikinta kuma karfe ne na gorar ruwa mai kamar bututu, dogo ne mai tsawon gaske, gami da kauri kuma ya hade da wata korama dake bayan kurkukun. Ko da su Insam suka iso inda wannan rariya take sai Insam ya dako tsalle sama daga inda yake ya dira a kan malalan sumntin wanda shi ne murfin rariyar sai ya zage iya karfinsa gabadayal ya naushi murfin rariyar. Wohoho! Wanda duk Allah ya bai wa karfi to sai dai Allah ya isa. Insam na naushin wannan malalen sumuntin sai wajen ya burme ginin ya fashe suka fada cikin rariyar wacce ruwa ke gudu a cikinta. Nan fa suka yi ta tafiya suluiu a cikin rariyar har zuwa karshenta inda ta watsosu cikin| wannan Korama dake bayan kurkukun. Ko da suka fado cikin koramar sai suka ga wani kwale-kwale karami daure a gabar koramar, ai kuwa sai suka y iyo izuwa wajen kwale-kwalen suka haura cikinsa suka kwance igiyar da ta tsai da shi suka tuka kwale- kwalen da sandunan tukinsu suka yi gaba. A daidai wannan lokaci ne Gadaraz da dakaru suka fado cikin koramar. Ko da suka hango su Insam a cikin kwale-kwale sun yi nisa sai Gadaraz ya kwarara uban ihu. Kawai sai ya ga Ilaila ta fado cikin koramar daga cikin rarriyar itama. Ilaila ta dago kai ta hango su Insam a can nesa cikin kwale-kwale sannan ta dubi Gadaraz ta ce 'Maigida yanzu mene ne abin yi?" Maimakon ya ba ta amsa sai ya juya ya dubi mataimakinsa tare da saurar dakarun dake biye da shi ya ce "Ku koma kudauko dawakai ku je ku Sha kansu a can dajin Farwas. Ni da matata za mu haye koramar nan mubi sawunsu. Ko da jin haka sai mataimakin gadaraz wato Saduaki Bartus ya dube shi çikin alamun damuwa ya ce, "Ya shugabana ni fa ina ganin cewa akwai lauje cikin nadi. Ta ya ya aka kawo kwale-kwale aka ajiye a nan.wurin alhalin ba a kawowa kuma a koyaushe dakarunmu na gadin har wajen amma yau babu ko mutum daya daga cikinsu. Ga su can ma kwance ga dukkan alamu kashcsu aka yi. Duk yadda aka yi wadannan fursunoni guda biyu da suka gudu sun sami hadin kan wasu murafukai daga cikinmų wadanda suka taimaka masu. Ko da jin haka sai Gadaraz ya ce "Yanzu ba mu da lokacin yin wani bincike kawai ku je ku zartar da abin da na umarce ku da yi." Bartus bai yi gardama ba sai ya juya, ya fice daga cikin koramar sauran dakarun na biye a shi suka koma cikin kurkukun domin dauko dawakai. Gadaraz da Ilaila kuwa sai suka ýi iyo izuwa can gabar koramar $uka riski inda su Insam suka bar wannan kwalc-kwale. Da fitowarsu daga cikin koramar sai suka bi sawur su Insam suna masu falfala uban gudu. Al'amarin Insam da Barsad kuwa tun da suka iso gabar koramar $uka fito daga cikin kwale-kwalen sai suka ruga izuwa cikin daji. Sai da suka yi gudun sa'a guda ¢ur sannan suka zube kasa bisa guiwoyinsu suka kama haki da numfarfashi sakamakon tsananin gajiya da suka yi a kokarinsu na fitowa daga cikin kurkukun da kuma gumürzut da suka yi da dakaru. Barsad ya dubi Insam ya ce, "Yanzu dai ga shi mun $ami nasarar fitowa daga cikin kurkukur nan amma daga yanzu zuwa kowane lokacin dakaru za su ya isowa nận su cimmana ka ga kenan duk wahalar da muka sha a baya ta zama ta banza, domin ba za mu iya tserewa ba. Insam ya ce Kamar yadda na baka nmamakl na cire rodunan tagar dakin da aka kulle mu kurna na gaya maka ta hanyar da za mu bi mu ficc daga cikin kurkukun wacce kai baka taba tunaninta ba a zuciyarka haka ma yanzu zan shirya mana yadda zamu kubuta. Za mu gaba da yin gudu na tsawon rabin sa'a kacal sannan mu tsaya. Shi inda za mu tsaya din anan gaba bishiyoyi ne a wajen ko kuwa duwatsu ne? Ka fi ni sanin haka tun da kai mutumin daji ne". Barsad ya jinjina kai ya ce, "Bishiyoyi za mu riska masu tsawo da duhowoyi". Insam ya ce "Da kyau" faduwa ta zo dadai da zama. Lallai a iya Tsawon gudun abin sa'a ne dakarun kurkuku za su riske mu domin a kan dawakai zasu biyo mu. Yanzu dole ne mu hanzarta mu isa inda bishiyoyin nar suke kafin su rigamu zuwa domin mu hau kan bishiya mu buya inda zamu dinga yi masu daukar daidai. Abin da nakc so ta kal ১hine da zarar mun isa wajen, duk abin da ka ga na yi kai ma ka vi shi.! Gama fadin hakan ke da wuya sai Insam ya falfala da gudu izuwa cikin dajin, ai kuwa sai Barsad ya yi koyi da shı. Haka dai suka gaba da gudun babu waiwaye babu tsawa har tsawon cikar rabin saa sai ga shi sun iso wannan wuri mai dauke da dogayen bishiyoyi wadanda suka haifar da duhuwoyil sakamakon fadin ganyayyensu da yawansu. Da isowarsu wannan wuri sai lnsam ya yi trujiya shi ma Barsad sai ya tsaya cak lokacin da Insam ya kurawa dajin idanu yana kallon gabas da yamma kudu da arewa sannan ya dubi kasa. Ko da ya daga kansa sama sai kawai ya hango raga ta taho kansu. Kafin su yi wani yunkuri tuni ragar ta lullube su sai kawai suka ga dakarun Gadaraz suna firfitowa daga maboyansu rike da masu da takubba kimanin su dubu sun kewayesu. Gashi raga ta kanannadesu kuma g6 shi babu makami a hannunsu ko guda daya Insam ya dubi Barsad cikin alamun takaicj da bakin ciki ya ce Mun yi latti tunda sun rigamu isowa nan. A daida wannan lokacin ne mataimakin Gadaraz sadauki Bartus ya fito daga inda yake boye yana kyalkyala dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa ya dubi Insam da Barsa ya ce, Mene he amfanin gudun da ba tsira. Ku sani cewa hukuncin kisa ne a kan duk wani fursunan da ya yi kokarın guduwa. Yanzu za mu kasheku a nan don haka inda kuma da wata wasiyya ku fada kafin taku ta kare' Ko da jin wannan batu sai Barsad ya dubi Insam ya ce Yanzu wace dabara ta rage mana?" Insam ya ce "Ba ni da sauran dabara mutuwa za mu vi kawai tunda in dai muna cikin ragar nan ba mu da wani tasiri". Barsad ya ce "Amma dai ka cuce ni. Ni ina da buri a duniya ka janyo min mnutuwa a lokacin da ba ta kamacc ni ba. " "Ta ya ya za ka cika burin naka alhalin an yanke maka hukuncin daurin rai da rai?" Barsad ya ce Kullum tunani nake yi a kan hanyar da zan bi na tsere cikin nasara amma kai naka wannan gajere ne mara nasara." Kafin Insam ya kara fadin wani abu sai Bartus ya dubi dakarunsa ya ke "Ku zuba musu kibiyoyi mu ķwashe gawarsu mu kai gidan sarki. Da jin haka sai dakaru suka zaro kibiyoyi suka dana a kan baka suka tabe da nufin sakin harbi. |Kwatsan sai aka ga wasu wasu kibiyoyin a sama cikin iska suna fadowa kan dakarun suna zubewa kasa matattu. Ba shiri Bartus ya vi wuf ya đauki garkuwa ya rufe jikinsa, kibiyoyi suka ci gaba da zuba akan garkuwar tasa. Sai da Bartus ya ji shiru alamar cewa kibiyoyin sun kare sannan ya mike saye Kawai sai ya ga gabadayan dakarunsa a kwance kasa sun zama gawarwaki. A sannan ne kuma ya hango wadansu dakarun yaki a cikin shigar bakaken tufafi sun rufe fuskokinsu da makamai sun durfafo lnda yake. A guje Bartus ya nufi inda dokinsa yakc ya yi tsalle ya haye shi, ya zabure shi da gudu ya nufi hanyar da za ta mai da shi cikin birnin Kisra. Su kuwa wadannan dakaru masu bakaken tufafi sai mutum daya daga cikinsu ya dana kibiya da nufin ya harbo Bartus amma sai shugabansu ya rike hannunsa ya yi masa nuni da ya kyale shi. Insam da Barsad kuwa mamaki ya turnuke su kawai suka kurawa bakin dakarun idanu suna tambayar kansu a cikin zuciya suna cewa wadannan Kuma su waye kuma a kan wane daliii suka ceci rayuwarmu?"Amsar da ba su sani ba ke nan bar Dakarun suka iso daf da Su. Danna shugabar dakarunne a kan gaba tare da mataimakinsa Da isowarsu dafl da su insam sai shugaban dakarun da mataimakinsa suka kwance rawanin da ya rufe fuskokinsu koda su Insam suka yi arba da su sai suka kara kamuwa da tsananin mamaki. Ba wadansu ba ne wadannan mutane biyu face Gadaraz da matarsa Ilaila. Gadaraz ya dubi Insam da Barsad cikin murmushi ya ce "Ni ne na taimaka muku har kuka sami nasarar isowa nan wajen domin ni ne na sa aka ajiye muku kwale -kwalen da kuka hau kuka ketarc wannan babbar korama ta buyan kurkuku. Na kubutar da rayuwarku ne domin ku yi mini wani aiki. Ku sani yanzu ba mu da lokacin tattaunawa, dolene mu fice daga cikin yankin kasar nan kafin Sarkin Kisira ya turo mana dakarun da za su fikarfinmu. Kowa a hau doki mu bar nan wajen. Yana gama fadin haka sai ya zaro wuka ya farke ragar da ta lullub su Insam. Cikin hanzari kuwa suka fito daga çikin ragar. Kafin cikar dakika dari da tamanin kowa ya kama doki daga cikin dawakan Dakarun kurkuku ya haye, nan da nan suka zabure su izuwal cikin daji. Sai da su Gadaraz suka shafe sa'a shida suna gudu kan dawakai su ratsa wannan daji su fita wancan har dai suka samu suka ficc daga cikinnyankin kasar Kisira $annan suka yada zango a wani daji gaban wani katon tsauni. A wannan lokaci rana ta fadi gari ya soma duhu. Nan take aka kafa tantuna Sannan aka kunna wuta kashi-kashi domin jin dumi sannan aka debo abinci aka fara bawa kowa ya sami nasa. Insam Barsad! Gadaraz da Ilaila na zaune a wajc guda gaban wuta suna ji dumi kuma suna cin abinci, sai Gadaraz ya dubi Insam da Barsad ya kyalkyaie da dariya ya ce, Tabbas duniya juyi-juyi ce, dazu kuna cikin kurkuku a tsare babu yanci amma yanzu ga ku a sake cikin walwala har kuna cin abinci mai kyau da dadi ba irin na kurkuku ba. Sa'adda Insam ya ji wannan batu $ai ya tsaya ga barin cin abincin ya dubi Gadaraz cikin nutsuwa ya ce "Wace bukata ka kaso mu biya maka wacce har ta sa ka hakura da aikinka na shugaban dakarun kurkukun birnin Kisira kuma ka aikata laifi na kashe abokan aikinka wanda idan har aka kama ka hukuncinka kisa ne?" Lokacin da Gadaraz ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi ya ce, Ya kai Insam dan Hashman jikan Damrus na sani cewa kai bawa ne kuma dan bawa a cikin gidan sarautar Sarki Zamral na birnin Kisira. Ảna zarginka da laifin yin alakar soyayya da matar Sarki, bisa wannan dalii ne aka yanke maka hukuncin dauri rai da rai. Tabbas wannan zalunci ne domin kai ba Sonta kake ba, ita ce take sonka saboda kana kama da masoyinta. Hakan ya samo asali ne a ranar da aka kawota gidan sarautar tana amarya a lokacin da kuka yi wasan nuna jarumta kai da 'yan'uwanka bayi don taya sarki murnar bikin aurensa. Ko da jin wannan batu sai Insam ya fada kogin tunani. Da yanmaci ne aka shigo da amarya Sulaisa a cikin wani keken doki na alfarma cikin gidan $arautar birnin Kisira. A wannan lokaci dakaru dubu ne suka rako Gimbiy Sulaisa wacce ta kasance| ya ga sarki Zarkam na birnin Sadyas A gaban tawagarta akwai kuyangi dari biyu bisa dawakai dauke da kaskwayen furanni suna ta watsa furannin sama suna zubowa kasa a cikin harabar gidan sarautar. Har sai da aka iso.tsakiyar gidan sarautar sannan aka tsaya! Sarki Zarkam na zaune bisa wata kujcra ta alfarma fadawansa da dakaru da hadimai sun kewaye shi. Tsayuwar keken dokin amarya Suiaisa ke da wuya sai Sarki ya mike tsaye fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki saboda doki gami da farin ciki. A wannan lokaci su Bawa Insam na tsaye a gefe kimanin su goma sha shida sun yi shiga iri daya domin debewa amarya kewa. Ko da aka bude keken doki amarya Sulaisa ta zuro kafafunta waje suka taba kasa sannan ta zuro kanta waje kowa ya yi arba da kyakkyawar fuskarta sai jama'a suka rude kuma suka dimauce saboda ganin tsananin kyawunta. Sulaisa ta kasance matashiya budurwa yar shekara goma sha takwas. Doguwa ce kuma fara kal mai madaidaicin kaurın jiki. Tana da dogon hanci, dan karamin baki, manyan idanu gami da siririn wuya. Gashinta baki ne sidik yana sheki da walwali tamkar madubi kuma ya zubo har kasan kwankwasonta. Tana sanye da wata doguwar farar riga mai tsadar gaske irin tasu ta sarakai. Tsayin bezar rigar ta daga baya va kai kamu sittin kuyangi ne ke rike da ita suna tattareta. Kallo daya mutum zai yi wanwannan amarya ya gane cewa ba ta son wannan aure da aka yi mata saboda murmushin yake take yi kawai. Fitowarta ke da wuya daga cikin keken dokin sai sarki Zamral ya mike da sauri daga kan kujerar da yake zaune ya je ya taro ta, inda ya mika mata hannunsa ta kama sannan ya jawota suka zo inda yake zaune suka zauna. Shi dai jarumi Insam tunda ya yi arba da Gimbiya Sulaisa sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi kuma wani irin tsoro ya shige shi wanda bai san dalilin faruwar hakan ba. AI kuwa sai Gimbiya ta waiwayo ta hada idanu da Insam ai kuwa sai ta kura masa do ta kasa kawar da kai har sai da Sarki ya lura da abin da ke faruwa ya kamo hannunta sannan ta daina kallon Insam. A daidai wannan lokaci ne mai gabatar da taro ya mike tsaye ya yi dan jawabai sannan aka gabatar da bayi wadanda aka shirya musu gasar fada domin fitar da gwani. Mutum na farko da aka fara kiran sunansa daga cikin bayin shi ne bawa Insam. Insam ya fito daga cikin yan'uwansa bayi yana sanye da dogon wando buje da kuma riga falmaran ya shiga cikin wata daira dake tsakiyar |wannan fili. Kuyi hakuri kwana biyu shiru in sha Allahu ba zamu kara daukar long time irin haka ba fatan alheri gareku masoya masu bibiyar wannan littafin. Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799GWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part C Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Ita dai wannan da'irar an kewayeta ne da wasu karafa da kuma igiyovi akan wani gini mai tudu wanda duk jama'ar da ke wajen ke iya hangota. Bayan an budewa Insam da'irar ya shiga ya tsaya sai aka jcho masa sanda ya cafe sannan aka kirawo bawa na biyu wanda shi ne abokin gwaminsa mai suna Janas. Janas wani katon Bawa ne dogo kuma kakkaura domin ya ninka Insam sau biyu 2 girma da kwarjini, kuma fuskarsa babu annuri ko kadan. Janas na shigowa cikin da'ira gasa sai shi ma áka jeho masa tasa sandar ya cafe sannan ya gyara tsayuwarsa suka fuskanci juna. A wannan lokaci ne jamaa suka rude da shewa gami da tafi. Kawai $ai aka buga gangar fara wasa. Jana ya ruga da gudu i zuwa kan Insam ya kawo masa wawan bugu da sanda a kai, cikin zafin nama Insam ya kare dukan suka ruguntsume da azababben fada ya zamana cewa Şuna kai wa junansu duka ta sama da Kasa. Sai da suka shafe dakika dari da tamanin suna kai wa junansu hare-hare ba tare da dayan su ya $ami wata nasara ba, sannan suka ja da baya suka gyara tsayuwa suna tunanin irin sabon salon fadan da kowannensu ya kamata ya yi don ya samu nasara. Lokaci guda suka ruga da gudu a karo ha biyu suka kacame da sabon masifafien fada. A wannan lokaci kowannensu ya zage damtse yana fadan ne da iyakar karfinsa da kuma kwarewarsa. Tun a farkon fara wannan gumurzu tsakanin Insam da Janas sarki Zamrall na lura da Gimbiya Sulaisa Duk sa'adda ta ga an kai wa Insam wawan hari har yana neman faduwa sai hankalinta ya tashi alamar fargaba ta bayyana karara akan fuskarta amma da zarar ta ga cewa Insam ke da alamu nasara sai fuskarta kama annuri da murmushi. Ganin hakan ne kishi ya turnuke Sarki Zamral ya ji kamar ya bayar da umarnin nan take a kashe bawa lnsam. Ba wani abu ba ne ya sa Gimbiya Sulaisa ta ji tana son bawa Insam anganin farko face yana tsananin kama da masoyinta wanda ta so ta aura akanhanata wato Sarki Marhat na birnin Misra. Sai da aka yi gasa ta dukiya a tsakanin sarakuna goma sha daya sannan aka fitar da gwanin daya sami damar auren Gimbiya Sulaisa kuma ba wani ba ne ya lashe gasar face Sarki Marhat amma a ranar da za a kai amarya birnin Misra aka nemeta aka rasa ashe Sarki Zamral ne ya tura aljanu suka sato ta. Sai da aka shafe shekaru uku ana nemanta ba ganta ba har masoyita Sarki Marhat da nahaifinta suka hakura suka rungumi kaddara, Duk irin karfin tsafin Sarki Marhat na birnin Misra bai ya gano inda Sulaisa take ba. Bayan shekara.uku ne Sarki Zamral ya shirya bikin aurersa a Sirrance a gidan sarautarsa ba tare da ya gayyaci Sarki ko guda daya a Nahiyar ba. A ranar da amarya za ta tarc aka shirya wannan gasa ta jaruma tsakanin bayin gidan sarautar. Ko da fara wannan artabu karo na biyu sai fadan ya sauya ya zamana cewa insam ne yake kai wa Janas mugayen hare-hare wadanda da kyar yake iya kare su kuma baya iya mayar da martani. Ana ciki haka ne lnsam ya shammaci Janas ya doki kafafunsa da sanda Janas ya sama kafin ya fado kasa lnsam ya sake doka masa sanda akan kirjinsa, take Janas ya fado kasa tim, bisa gadon bayan sa ya furzo da gudan jini daga cikin bakinsa kuma ya kasa mikewa tsaye. Nan fa yan kallo suka rude da shewa gami da tafi Gimbiya Sulaisa kuwa ba ta san sa'adda ta mike tsaye ba, tana yi wa lnsam ta fi sai da Sarki Zamral ya riko hannunta sannan ta koma ta zauna. Daya bayan daya sai da jarumi.Insarn ya yi fadan sanda da wadannan bayi guda goma sha shida kuma ya yi nasara a kansu, đayansu bai sami nasarar koda dukan jikinsa ba sau daya. Ana gama wannan gasa ne Sarki Zamral ya ja amaryarsa suka shiga cikin gidan sarautar, taro ya watse kowa ya kama gabansa. Lokacin da bayi da kuyangi suka raka amarya Sulaisa cikin turakarta suka fito suka bar ta ita kadai jal a zuane gefer gadonta na alfarma sai ta fashe da matsanancin kuka na bakin cikin wannan auren dole da ta yi. Ga shi an rabota da kasarta ta haihuwa iyayenta ma ba ta san ranar da za ta sake ganinsu ba, kuma ga shi an rabata da masoyinta Sarki Marhat To wai shin jarumin da na gani yanzu mai kama da masoyina Marhat waye shi? Anya kuwa ba shi da wata nasaba da Sarki Marhat domin kamannin nasu ya yi yawa matuka. Tana cikin yin wannan tunani ne da kuka Sarki Zamral ya shigo cikin turakar. Koda ta ga ya durfafota gadan-gadan sai ta sauko daga kan.gadon da gudu ta nufi kan tebur da aka ajiye ya'yan itatuwa da wuka Kawai sai ta dauki wukar ta đoral a kan wuyanta ta dube shi ta ce, Idan ka kara yin tafiya taku d'aya izuwa gareni na rantse da darajar iyayena sai na kashe kaina.' Ko da in wannan batu sai hankali Sarki Zamralya.dugunzuma ya yi taku biyu sannan ya dubetal ya |ce, "Ni ma na rantse da darajar nawa.iyayen daga yau ba zan sake kusantariki ba har sai kin bukace ni da kanki Amma ki sani cewa wannan bawa da ya lashe gasar jarumta mai kama da tsohon masoyinki duk anar da kika kusance.shi ko kuka yi magana da juna ba ki sake ganinsa ba domin kurkuku zan kai shi a yanke masa hukuncu daurin rai da rai." Gama fadin hakar ke de wuya sai Sarki Zalmar ya juya da baya a fusace cikin bakin ciki ya fice daga cikin turakar. Kashegari da safe kuwa aka nemi.amaryal Sulaisa sama da kasa aka rasa a cikin gidan sarautar. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Zalmar kenan ya baza dakarunsa a nahiyar aka yi ta nemanta amma ko duriyarta ba a ji ba a tsawon kwanaki bakwai. Bisa wannan dalili ne Sarki Zalmar ya zargi Bawa Insam a kan cewar akwai sa hannunsa a batan Gimbiya Sulaisa don haka ya sa aka kama shi aka yi ta gana masa azaba iri-iril har tsawon kwanaki goma sha daya inda Sulaisa take. Bayan an gano cewa babu sa hannunsa a 6atan Sulaisa sai kuma aka yanke masa hukuncin daurin rai da tai aka kai shi kurkuku. Sau uku yana guduwa ana kamo shi daga karshe aka kai shi babbar kurkuku inda Gadaraz ke shugabancin dakaru. Lokacin da Insam ya gama tunanin wannan al'amari da ya faru a baya sai Gadara ya dafa kafadarsa ya ce "Na san yanzu ka gama tuno komai. Shin ka san ko waye ya sace amarya Sulaisa kuwa?" Insam ya ce, Ya za a yi na sani sai zargi da aka dora mani aka zalunce ni bada hakkina ba. Gadaraz ya ce "Haka ne to ba wani ba ne ya sace ta face ni di nan, kuma na mayar da ita gidan sarautar Sarki Marhat nd babban abokin gabata domin na dawo masa da farin cikinsa sannan kuma yanzu daga baya a na same ku kai da Barsad zan je na rushe dukkan farin cikinsa da arzikinsa kuma na cika burina a kansa. Hadin kanku kadai ya rage mani yanzu na cimma burina. Ku sani idan wannan buri nawa ya cika har abada kun tsira daga sharrin kowane $arki a wannan nahiya kuma zaku zama manyan Sarakai na manyan biranc a wannan nahiya ta mu." Sa'adda Insam da Barsad suka ji wannan batu sai suka kamu da farin ciki amma sai Insam ya dubi Gadaraz ya ce, To yanzu ta ya ya zaka iya rushe farin cikin Sarki Marhat kuma ya zamu yi da barazanar Sarki Zamral tunda dole ne ya cigaba da farautarmu saboda ya san cewa kai ne ka taimaka mana muka sami nasarar guduwa daga kurkuku?" Gadaraz ya yi ajiyar zuciya ya ce "Duk abubuwan da ka ga nayi yanzu a lissafe suke kuma a shirye tun shekaru uku baya da suka gabata. Sai da na auna komai na tanadi komai da sannan na fara aikina, hatta kai a Barsad kana cikin mutanen da na tanada don cika wannan burni nawa. Abin da na ke bukata da ku kawai ku daukar mini alkawarin cewar duk wuya duk tsanani kuna tare da ni ba za ku ci mini amana ba. Idan kun amince ga hannuna kowannenku ya dafa shida hannunsa na dama. Sa'adda Insam da Barsad suka jii wannan batu sai suka dubi junansu sannan suka tsaya suna tunanin abin yi. Insam ne ya fara dora hannunsa a kan na Gadaraz sannan shima Barsad ya dora nasa a kan na Insam. Koda ganin haka sai ita ma llaila ta.đora hannunta a kan na Barsad ta ce, Ni ma ina tare da ku dari bisa dari." Wannan shi ne abin da ya faru ga su jarumi Insam bayan shugaban dakarun kürkukun birnin Kisira wato Gadaraz ya taimaka musu suka sami nasarar guduwa. A can baya kuwa lokacin da Gadaraz ya sace Gimbiya Sulaisa, sai da ya kai ta har kusa da gidan sarautar birnin Misira amma ba ta san wane ne ya satota ba. Kawai ta san cewa ta kwanta ta yi barci a can birnin Kisira amma sai farkawa ta yi ta tsinci kanta a kan doki wani mutum na rike da ita a gaban dokin yana tsala gudu. Ko da ta waigo sai ta ga fuskarsa a rufe take za ta yi magana ke nan sai ta ji ya ja linzami takc dokin ya yi turjiya gami da daga kafatuwansa na gaba sama yana haniniya sannan ya ajiye su kasa. A sannan ne suka sauko daga kan dokin. Sulaisa ta dubi gabas da yamma, kudu da aewa kawai $ai ta hango gidan $arautar masoyinta wato $arki Marhat. Nan take ta kamu da tsananin mamaki gami da dimbin farin ciki ta dubi mahayin ta de "Wane ne kai kuma saboda me ka sato ni daga wajen wancan azzalumin sarkin ka dawo dani hannun masoyima?" Lokacin da mahayin ya ji wannan tambaya sai ya kwaye fuskarsa. Ko da ta yi arba da shi sai ta sake cika da mamaki saboda ba wani ba ne face Gadaraz. Gadaraz ya yi murmushi ya ce, "'Na san za ki yi mamaki domin kin sanni a matsayin amintaccen hadimin sarki Zamral amma kuma ga Shi naci amanarsa, ki sani na yi haka ne domin na cika wani buri nawa. Ina so ki sani cewa shi ma wannan masoyin naki azzalumi ne ya cutar da rayuwar mutane da yawa amma ba ki sani ba Shawarar da zan ba ki ita ce ki yi bad-da kama ki.shiga gidan sarautar a matsayin.baiwa domin ki gano ainihin wane ne Sarki Marhat sannan ki yanke shawara a kan za ki iya ci gaba da rayuwa da shi ko a'a." Gadaraz na gama fadin hakan sai ya kama dokinsa ya haye sannan ya dubi Sulaisa va ce "'Sai mun sake haduwa a wani karon. Yana gama fadin hakan sai ya juya da dokinsa baya ya zabure shi da gudu ya nufi hanyar da suka fito. Ita kuwa Sulaisa hankalinta ne ya dugunzuma ta rasa abin dake mata dadi domin ta tsinci kanta acikin wasu-wasi ákan shawarar da Gadaraz ya bata. Ga shi dai yanzu tana farin cikin rabuwa da Sarki Zalmat wanda yake kokarin aurenta bisa dole kuma gashi ta dawo garin masoyinta Sarki Marhat wanda ta ba wa amanar Zuciyarta da ámanar rayuwarta. Idan abin da Gadaraz ya gaya mata gaskiya ne to ai kuwa ba ta ga amfanin zama da azzalumi ba gwara ta goge Sonsa daga cikin ranta har abada. Gama ayyana hakan ke da wuya sai Sulaisa ta nufi wannan hanya wacce za ta kai ta gidan sarauta. Sai da ya rage bai fi tazarar tafiyar dakıka dari biyar ba sannan Sulaisa ta rabe bayan wata bishiya daidai mararraba hanya mai zuwa cikin gari. Dama Sulaisa ta rufe kanta da mayafi da duk jikinta, kuma ta sunkuyar da kanta kása. Da vake Sulaisa ta san duk iri abubuwan dake faruwa a cikıa gidan sarautar Sarki Marhad a kowane lokaci sam ba ta da wata damuwa domin da ta dubi lokacin da ake ciki yanzu sai hankalinta va kwanta saboda nan ba da dadewa ba wata amintacciyar kuyangarta zata fito daga cikin gidan sarautar domin zuwa kasuva yin siyayya. Haka dai Sulaisa ta ci gaba de jira |har tsawon yan dakiku, kwatsam sai ta hango baiwa ta fito daga cikin gidan sarautar kuma aka yi Sa'a ita kadai ta fito tana rike da wani kwando. Sai da kuyanga Rasimat ta gifta wannan bishiya wacce Sulaisa ke rabe sannan Sulaisa ta kira sunanta. Cikin firgita ta waigo har tana sakın kwandor dake hannunta ya fadi kasa. A zaton Rasimat gamo ta yi. Ko da ta vi arba da Gimbiya Sulaisa sai ta kamu da tsananin mamaki ta rugo da gudu izuwa gareta suka rungume juna. Rasimat ta janye jikinta daga na Sulaisa tana murmushin cikin farin ciki ta ce "Ya $hugabata wai su waye suka sace ki, kuma ya ya aka yi kika dawo nan yanzu? Sulaisa ta ce "Duk wannan wani abune mai tsawo sai na nutsu, abin da nake so da ke shi ne mu tafi kasuwar tare amma a can zan batar da kamannina na dawo a matsayin baiwa saboda ina son na gano wani al'amari a tare da sarkil Ina bukatar ki rufa nin asiri kuma kada ki bari Kowa ya gane ni. Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta yi nmurmushi a ce Ya shugabata ai wannan abu ne mai sauki a wajena tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai, A matsayina na shugaba kuyangin gidan nan zan iya yin abin da ya fi hakarn, muje kasuwa kawai." Nan take Rasimat da Gimbiya sulaisa suka jera suka nufi kasuwa.suna hira abin su tamkar baiwa da ৮aiwa. Bayan sun hattama duk siye-siyen da ya kamata ne sai Rasimat ta kai Sulaisa shagon wata mace inda take siyen kayan Sawa na bayi da kuma kayan shafe-shafe na mata. Anan ne aka zabowa Suiaisa kayan da suka yi mata daidai, sannan aka yimata wani irin gyaran gashi gami da shafe-shafen fuska wanda ya canja kamanninta gabadaya. Duk irinn sanin da mutum yai mata bai isa ya gane ta ba. Daga nan ne suka kama hanya suka koma gidan sarautar. Ba su sami matsalar komai ba, tun daga kofar farko ta shiga gidan suka yi ta kutsawa suna wuce dakaru, bayi, fadawa da hadimai har suka iso bangaren da turakar Rasimal takc Rasima ta sa mukulli ta bude kofar dakin har ta sa kafarta guda ciki Sulaisa na biye da ita kawai sa suka ji muryar Sarki Marhat a bayansu ya ce Yau kin dade a kasuwa tun dazu nake neman ki." Kuyi hakuri wallaahi exam muke yi ne shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, yanzu ma space na samu yi maku wannan posting din saboda yadda kuke a cikin zuciyata. Daga karshe ina mai neman Addu'arku yan uwa na gode 🙏🙏🙏GWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part D Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Take zuciyar Rasimat da ta Sulaisa suka buga da karfi Rasinat ta juyo ta dube shi tana murmushin karfin hali ita kuwa Sulaisa ba ta dago kanta ba Rasimat ta ce Ai ba ya kasuwa na je ba, na je dakin bauta ne." Sarki Marhat ya dubi Sulaisa wadda ta rufe kanta da mayafi ya ce "Yau kuma kın siyo sabuwar kuyanga ne?" Rasimat ta ce E yanzun nan na taho da ita daga kasuwa. Marhat ya ce "To dama neman da nake miki kenan ina son a canja mani kuyangin dake kula da turakata saboda ba sa yin aikinsu yadda ya kamata, sai ki hado da wannan sabuwa a cikinsu don na ga kamar zata kasance mai nutsuwa da sanin ya kamata. Rasimat ta risina ta ce "An gama Shugabana." Da jin haka sai Sarki ya juya ya koma hanyar da zaa ta mai da shi turakarsa. Tafiyarsa ke da wuya sai Rasimat da Sulaisa juna suka dafe kirjinsu suka sauke ajiyar Zucıya, sannan suka shige cikin turakar suka kulle kofar. Bayan sun zauna ne Rasimat ta kawowa Sulaisa abinci da abin sha ta ci ta koshi sannan ta dube ta ta ce "Tabbas idan kika kảl ni cikin kuyangin dake yi wa Sarki hidima da zarar ya kalli idanuwana zai shaida ni, ni kuma a ƙalla ina bukatar kwana bakwai kafin na gano abin da nake son na gano." Sa'adda Rasimat ta ji wannan batu sai ta kyalkyale da dariya ta ce "Kwantar da hankalinki ya shugabata. Dabara ba ta karewa mai neman tsira. Na san yadda zan yi ke dai kawai ki zuba ido ki sha kallo." Kafin sa'a guda ta cika Rasimat ta zabo kuyangi guda goma sha daya sai ta yi musu ado iri daya da na Sulaisa sak, sannan kafin ta fito da Sulaisa daya cikin furakarta sai da ta sauya mata launin gashin kanta na ainihi daga baki zuwa ruwan kasa yadda babu wanda zaigane cewa launi aka sauya masa, sannan ta bata wani abu ta sanya shi cikin kwayar idanunta. Take kalar idanunta suka sauya Sulaisa ta fito daga cikin turakar Rasimat ta jero acikin kuyangi goma sha daya suka tsaya reras a sawu guda Rasimai ta zo ta tsaya á gabansu sannan ta sanar da su yadda za su tafiyar da ayyukansu a turakar Sarki daga nan ne ta wuce gaba suka bi ta abaya har cikin turakar sarki. Sarki Marhat na zaune bisa wata shimfida ta alfarma a tsakivar turakarsa sai ga shi an shigo da kuyangi guda goma sha bivu suka jeru a gabansa suka risina suka kwashi gaisuwa sarki Marhat ya mike tsaye ya fara kalonsu daya bayan daya yana matsowa gaba a hankali har ya zo daf fa Sulaisa wacce ita ce ta biyun karshe a layi. Ya dubeta da kyau amma sai ya wuce gaba ya kurawa ta karshen idanu sannan ya juyo ya dubi Rasinat ya ce "Aikinki ya yi kyau su fara nasu aikin." Ba tare da bata wani lokaci ba Rasimat ta raba kuyangin gida uku ta nuna musu irin ayyukan da za su gabatar. Shi kuwa Sarki Marhat sai ya koma kan shimfidarsa ya kishingida aka kawo masa kayan ciye-ciye da na shaye-shaye amma ko kallonsu bai yi ba sai ya daga kansa Säma yana kallon rufin falon. Ga dukkan alamu dai tunani yake yi, kuma yana cikin damuwa mara misaltuwa. Ku da ganın haka sai Rasimat ta taho gareshi ta zauna a gefen hagunsa ta dube shi ta ce, Ya shugabana kamar kana cikin damuwa da rashin walwala, shin akwai wata matsala ne?" Sa'adda Sarki Marnat ya ji wannan tambaya sai yayi murnushin yake ya ce 'Ya ke shugabar| kuyangi ki yi sani cewa tun daga ranar da aka nemi masoyiyata Sulaisa aka rasa a cikin gidan nan sai farin ciki da walwala suka kaurace mini. Na tura yan leke asiri izuwa duk biranen dake nahiyar nan su gano min ko wane ne ya Saceta amma ko duriyarta ba ajii ba. Nayi amfani da karfin sihirin tsafina don gano inda take duk a banza. Ni dai zaton da nake yi wanda ya saceta ya kasance gawurtaccen matsafi kuma babban makiyina." Lokacin da Rasimat taji wannan batu sai ta yi ajiyar numfashi ta ce Ya shugabana ga yadda soyayyarku ta kasance ta gaskiya kai da Gimbiya Sulaisa babu wani mahalukin da ya isa lya raba ku face mútuwa." Da jin haka sai Sarki Marhat ya bushe da darıya al'amarin da ya yi matukat baiwa Rasimat mamaki kenan Kawai sai ta ga $arki Marhat va murtuke fuskarsa ya dubeta ya ce, "Ba ki san sharrin makiya ba. Yanzu haka wanda ya saceta ya gaya mata gaskiya da karya kuma ya nuna mata hujjojin da zai sa ta gamsu cewar ni ba mutumin kirki ba ne, don haka za ta iya tsanata a rana kuma a lokaci guda." Rasinat ta ce Haba ya shugabana ai ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi, kuma so ba karva ba ne." Cikin fushi sai Sarki Marhat ya mike tsayesayd zumbur ya dubi Rasima ya ce Tabbas So gaskiva ne amma yana |ya juycwa ya zama kıyayya. A halin vanzu Suiaisa ta daina sona tunda har ta amince da maganar da makiyi na Gadaraz wanda ke shirin daukar fansa a kaina ya fada mata.' Ko da jin wannán batu sai zuciyar Rasimat ta buga da karfi jikinta ya kama tsuma. Ita ma Gimbiya Sulaisa da ke cikin bayi ta yi bad-da-kama tana ta aiki såi Zuciyarta ta kama daka. Kawai sai suka ga Sarki Marhat ya baro inda yake ya durfafo inda Suiaisa take, Yana zuwa sai ya cafkk kevarta ta baya da hannunsa, ta kurma ihu sannan ya dube ta kuma ya waigo ya dubi Rasimat ya ce, "Ke munafuka kina zaton za ku iya yaudarata ne? Na karfinku kuma na fi karfin makiyana. Tabbas ni azzalumi ne, na kashe talakawan da ba su da laifin komai, haka ma attajirai da masu mulki don kawai na mallake abin da suke da shi, ko kuma domin jin dadina da nishadina. Ke Sulaisa ki sani cewa Babanki ma yaudararsa na yi da batun neman aurenki ba shirya gasar dukiya ta hakan ne na sace dukkan dukiyar da aka tara a wajen gasar da kuma ta 'sa wacce ya boye a įnda ya ke zaton babu wanda ya sani. Yanzu na mai da shi matsiyacin Sarki bai sani ba. Aurena da ke kuma ya zama wajibi gobe-goben nan za a sha shagalin bikinmu." Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa sau biyu Nan take wasu dakaru guda biyu suka shigo Cikin falon, ya dube su ya ce, Ku kama munafuka Rasimat ku kai ta kurkuku, gobc bayan an gama shagalin bikina da Sulaisa za a yanke mata hukuncin rataya." Ko da jin haka sai Rasimat ta kurma ihu, ai kuwa sai dakarun suka kamata da karfin tsiya suka fice da ita daga cikin falon, Ita kuwa Sulaisa sai ta doke hannun Sarki Marhat daga jikin keyarta ta waigo, ta dube $hi a fusace ta ce Tabbas abin da Gadaraz ya fada mini a kanka gaskiya ne. Ka tabbata azzalumi kuma butulu, ma ci amana To ka $ani zalunci baya dorewa kuma ina mai tabbatar maka da cewa sai dai ka zauna da gawata a gidan nan." Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya ya ce "Duk abin da na shiryawa rayuwata shi ke faruwa. Ba a sarrafa ni sa dai ni na sarrafa wanda na so." Nan take Sulaisa ta yunkura cikin zafin nama ta ciro wata takobi da ke rataye a jikin bango ta daga sama da rufin ta caka a cikinta amma sai hannunta ya kame a saman ta kasa motsa shi. Sarki Marhat ya kyalkyale da dariya sannan ya sa hannunsa va karbe takobin daga hannunta, ya dube ta ya ce "Ai jikinki namu ne sai dan haka babu wani abu zai same shi face da yardarmu. Şhige ki tafi turakarki ki kwanta ki huta. Ba zan zo miki ba sai gobe đa daddare bayanan gama shagalin biki." Ai kuwa sai Gimbiya Sulaisa ta juya ta fice daga falon Sarki ta nufi tata turakar kamar yadda ya umarca ta. Tabbas tsafi gaskiyar mai shi ne. Gabadayan kuyangi da hadirnan dake cikin wannan falo na Sarki Marhat sai da suka cika da tsananin mamakin karfin sihirinsa þisa yadda ya gano duk irin shirin da Rasimat da Sulaisa suka şhirya da kuma yadda vake sarrafa Sulaisa tamkar rakumi da akala. Wannan Shi ne abin da va faru a birnin Misira bayan Gadaraz ya mayar da amarya Sulaisal ainihin ga masovinta Sarki Marhat wanda a halin yanzu ya babban makiyinta a duniya. A can fadar Sarki Zarmal na birnin Kisira kuwa yana zaune ana tafiyar da harkokin fada cikin nishadi, wasu yan mata na rawa a gabansa ana buga wani kidan taushi sai ga Sadauki Bartus ya shigo da sauri fuskarsa cike da alamun damuwa Da zuwansa kusa da karagar Sarki sai va zube kasa bisa guiwarsa guda lokacin da masu kida suka dainab'yanmatan dake rawa suka tsaya cak, fadar ta yi tsit tamkar babu mai rai a cikinta. Sadauki Bartus ya budi baki kansa na sunkuye ya ce Ya shugabana. Gadaraz yaci amanarka. Ya kashe dakarunmu kuma ya taimakawa insam Barsad sun sami nasarar guduwa daga kurkuku. Koda jin wannan batu sai sarki Zamral ya bushe da dariyar farin ciki al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan a fadar, sannan Zamral va murtuke fuska ya mike tsaye daga kan karagarsa ya dubi sadauki Bartus ya ce ai dama wannan ranar nake jira ya kai Bartus kasance wa wani lokaci yazo wanda zan mallaki birnin Misra. A duniyar nan kaf bani da makiyin da yafi sarki Marhat na binin misra ni da shi munyi kunnen doki a karfin mulki arziki da kuma karfin sihiri tsafi. Kowannan mu so yake ya kawar da daya domin va mallake komai nasa, tun tsawon shekaru bakwai baya amma mun kasa Gadaraz shine mutumin da zai tai maka mini na sami lagon sarki Marhat, na sata amarya Sulaisa daga hannun sarki Marhat shi kuma Gadaraz va saketa daga hannunsa na mayar da ita wajen marhat matar Gadaraz wato jaruma Ilaila itace kadai wadda tasan inda littafin sarki Marhat yake kuma itama ta manta inda yake, amma zata iya tunowa idan wani abu ya faru makanancin wanda ya bata labari inda aka ya boye littafin. Ya zama wajibi nayi gagarumin shirin yaki nabi bayan su Gadaraz ba tare da sun san da cewar ina biye da su ba har sai sun đanko wannan littafin daga nan naje na yaki sarki Marhat na kasha shi na mallaki kasar sa, dukiyarsa dama amaryarsa sulaisa, matsala ta guda daya ce yanzu, gobe daura aurensa da Gimbiya Sulaisa lallai ina son na tsayar da wannan daurin auren domin bana son ya kwanta da ita kafin na gama dashi, lokacin da sarki Zamral yazo nan a jawabinsa sai fadar tayi tsit aka rasa wanda zai kala. Daga can sai wazirin sarki zamral yayi gyaran murya ya dube shi yace ran sarki ya dade ai wannan abu ne mai sauki, kawai rundunar yaki zaka tasa ta isa kofar birnin misra a gobe da sassafe a aikawa sarki Marhat takardar yaki, kaga kenan batun bikin aurensa ya rushe tunda tashin hankali va zo sannan kai da wasu dakarun daban sai kabi bayan su Gadaraz a sirrance. Koda jin wannar shawara sai sarki Zamral ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dubi wazirin sa yace tabbas duk wanda yariga ka kwana dole ne ya riga ka tashi wannan shine amfanin zama da manya, ga shi a cikin kankanin lokaci ka bani shawarar da itace kadai mafita. Sarki zarmal ya dubi sarkin yakin sa dake tsaye a gefe guda yace ya kai dirka birnin kisira maza kaje ka shirya dakarun yaki kaso biyu, kaso na farko kaine zaka jagorance su izuwa kofar birnin misra ku vaki Sarki Marhat kaso na biyu kuma ni zan jagoran ce su Mubi sahun su Gadaraz sarkin yaki Darkis yace angama ya shugabana. A can daji bayan su Gadaraz Sun gama yarjejeniya akan dayansu bazai ci amana ba sai Gadaraz ya dubi Ilaila yace lokacin da kina yarinya karama wane abu kika fiso, kuma wane abune yafi baki tsoro? Koda jin wannan tambaya sai mamaki va kama Ilaila ta dube shi tace saboda me kayi min wannan tanbayar? Gadaraz yace dole a cikin wannan abubuwan guda biyu zaki iya tuno labarin da mahaifin ki ya baki dangane da inda aka boye Iittafin sirrin sarki Marhat. Ilaila tayi shiru tana tunani har izuwa tsawon yan dakiku sannan tace a rayuwa ta ina son hawa tsauni da shiga cikin kogon duwatsu abin da yafi bani tsoro a cikin wannan duniya shine nayi arba da aljani ko dodo mummuna. Gadaraz yace da kyau mun sami mataki na farko na ga0e inda zamu sami wannan littafin, dole ne muje inda kogon duwatsu suke da kuma tsaunika mu shigesu mu kuma hau kansu, wannane kawai hanyar da zai sa ki tina inda aka ajiye littafin sirrin da muke nema, tabbas inda aka ajiye littafin aljanu da ko dodanni ke gudinsa. Ku sani bamu da wani isashen lokaci don haka kuzo muyi sauri mutafi izuwa wannan wurare. Gama fadin hakan keda wuya sai Gadaraz ya mike tsaye ya kama dokinsa ya hau, cikin sauri sauran yarana masu shigar bakaken tufafi kimanin su dari suka yi koyi dashi, ai kuwa sai Insam, Barsad da Ilaila suka mike suka kamo nasu dawakan suka hau aka dunguma gaba daya aka nausa cikin daji. Gadaraz ne akan gaba yana yi masu jagora. Al'amarin sarki Marhat na binin misira kuwa ashe kifi na gani ka mai jarkoma. Duk abubuwan da suka faru a fadar sarki Zamral da wanda suka faru a daji tsakaninsu Gadaraz sarki Marhat ya gani a madubin tsafinsa, don haka sai ya kyalkyale da dariyar farin ciki. Lokaci guda sai yace ai ni murucin kan dutsene ban fito ba sai da na shirya, tabbas sarki zarmal yayi kuskure da kake tunanin cewa zaka iya yaudarata da yaki sannan ka tafi izuwa inda littafin sirrina yake ka dauko shi, duk da cewa nima kaina bansan inda littafin yake ba amma ai gashi a saukake za'a kaini inda yake, naga ta yadda ko su Gadaraz zaku iya mallakarsa alhalin ina wajen. Koda gama wannan batu sai sarki Marhat ya tura aka kirawo sarkin yakin birni nasa mai suna sadauki Inzan ya dubeshi ya ce ya kai Inzam dama ka kwana biyu baka motsa jiki ba. AlhamduLillahi naga addu'o'inku yan uwa, kuma ina godiya matuka Allah Ya saka maku da alheri ga karin kumallo nan. Allah Ya cika mana burikanmu na alheri 🙏🙏🙏 GWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part E Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey To ka sani abokin hamayarka sadauki Darkin na birnin kisira ya đebo dakarun yaki sun taho izuwa nan birninmu domin su yake mu, so suke su iske mu has nan kofar gari, abinda nake so da kai shine kaima ka debi dakaru masu yawa kaje kutaresu a can daji kuma ku dana musu mugayen tarkuna da zasu hallaka kafin ku hada jiki dasu, ma'ana kuyi musu yakin sumame da mamayar bazato, koda jin wannan koda jn wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki Inzanu saboda damá ya dade yana so yayi ramuwar. akan sadauki Daskin na kisira bisa dan uwansa uwa daya uba daya daya kashe a wani yaki da akayi shekaru biyar baya, don haka ya dubi sarki cikin murna ya ce ya shugabana ina mai tabbatar maka da cewa zan shiryawa dakarun birnin kisira tuggun yakin da dayan su bazai tsira ba kuma wannan sine karo na karshe da zamu yi yaki dasu domin birnin nu ya zama namu. Koda jin haka sai sarki marhat ya bushe da dariyar farin ciki yace maza kaje ka fara shiri nima.yanzu Zanyi nawa domin bin bayan $arki Zamral izuwa inda littafinsa na sirri yake domin kawo karshensa gaba daya. Sadauki Inzam ya risina yace angama ya shugabana, nan take ya juya da sauri ya fice daga cikit dakin. Sarki Marhat sai ya fara kira sunayen wadansu aljanu, kwatsam sai ga wasu zaratan matasan aljanu acikin shigar yaki dauke da makamai masu ban tsoro, suna ratsowa ta saman gini suna sauka a gaban sarki Marhat suna masu kwasar gaisuwa. A can sai da su Insam suka shafe kwanaki biyu da yini guda sannan suka iso wannan daji mai dauke da manyan tsaunika da manyan kogunan duwatsu, da iso warsu wannan waje sai sai suka tsayar da dawakansu suka sauko suka daure su a jikin bishiyoyi, faruwar hakan keda wuya sai suka ga Ilaila ta kama kallon wani guri ta hanga can ta kalli nan, daga can kawai sai ta durfafi wani tsauni kai tsaye, koda ganin haka sai Gadaraz yabi bayanta da sauri ai kuwa sai Insam da Bushrad ma suka biyo su, yayin da Ilaila taci gaba da tunkarar tsaunin sai kuma ta kara sauri | daga bisani ma ta fita da gudu hart a isa kan tsaunin suma su Gadaraz suna biye da ita, koda isa kan tsaunin sai ta tsaya cak ta kura wa wasu duwatsu guda biyu idanu wadanda aka ajiye a wajen nan take sai hawaye ya zubo mata ta tsuguna bisa gwiwoyinta ta shafa dutse daya a cikin duwatsun, koda ganin haka sai Gadaraz ya tsugunna kusa da ita ya dubeta yace shin kin tino da wani abu ne? Ilaila ta dubi Gadaraz lokacin da hawaye ya ci gaba da zubo mata tace ni da mahaifina mun ta6a hawa kan tsaunin nan har muka zauna a kan duwatsun nan guda biyu. Cikin murna Gadaraz ya ce ina son to ki kurawa duwatsunan biyu idanu ki yi kokarin tino da duk abin da ya faru tsakaninki da mahaifinki lokacin da kuke zauna a wannan wuri. Koda jin baka sai Ilaila ta dafa dutsen da mahaifinta ya zauna sannan ta rintse idanuwanta ai kuwa nan take tafada kogin tunani. Suna zaune akan duwatsun biyu sai mahifinta ya dauko salkar ruwa ya samata a baki ta sha, sannan shima ya sha sakamakon kishit ruwal da kuma da gajiyar tafiya da suka sha, sa'adda idanunsa suka ciko da kwalla yace yake yata ki sani inda zamų yanzu wajene mai hatsarin gaske, zan iya rayuwa kuma zan iya mutuwa amma bamu da wani zabi wanda ya wuce muje wajen, in ba haka ba wanda ke biye da mu zai riskemu koma yakashe ni ko ya rabani da wannan littafin, nan take mahaifin Ilaila va sa hannu cikin aljihun rigarsa sai ya dauko wani dan karanin jan littafi ya nuna wa Ilaila inda sarki Marhat ya boye dukiyarsa mai tsananin yawan gaske kuma yana dauke da sirrin sa na tsafi wanda dole saida shi da shi ne kadai za'a iya hallaka shi, kuma duk wannan dukiya daya tara nine sanadinta Hakazalika duk sihirin daya samu nine sanadi kuma nine kadai na sani a fadin wannan duniya. Bisa wannan dalili ne yake so ya kasha ni kema kuma kama ki zaiyi yanzu daga nan zamu je kogon badarel anwar inda zan boye wannan litattafin a gaban idonki idan kin rayu zaki iya zuwa ki dauki littafin domin ki kawo.karshen sarki Marhat bisa cin amanata da yayi, idan kuma baki rayu ba shikenan shi ma har abada ba zai sake mallakar littafinsa ba kuma sai ya mallaki littafin a hannusa sannan zai iya samun nasara akan abokan gabarsa har ya cika burikansa. Lokacin da mahaifin Ilaila yazo nan jawabinsa sai ta dube shi tace, Yakai Abbana to akan me kake fadamin cewar ba zaka rayu ba, alhalin gaka yanzu a raye ina tare da kai? Mahaifin Ilaila yace ka'idar wannan littafi shine duk wanda ya kai shi cikin kogon Hadara aswar ya ajiye shi indai ba mamallakasaba rmutuwa zai yi, kuma ba bu wanda zai iya sake daukoshi face jininsa. Amma ke zaki iya dauko shi nan gaba babu abi da zai sameki. Sa'adda mahaifin Ilaila yazo nan a jawabinsa sai Ilaila ta fashe da kuka kuma ta rungumeshi tana mai cewa ya kai Abbana saboda me zaka sallamar da rayuwarka don kawai kakai wannan littafi kogon Hadaru Aswar. Dajin wannan tambaya sai ya janye jikinsa daga ciki nata sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace nayi hakane domin ceto rayuwar miliyoyin jama'ar da sarki Marhat yake zalunta. Idan ban rabashi da wannan littafi ba to nan gaba sai ya mallake nahiyarnan gaba dayanta, kuma mulkin zalunci zai yi ta dorarwa kema ba zakiyi rayuwa mai kyauba. Kafin Ilaila ta budi bakin ta kara cewa wani abu sai kawai suka hango sarki Marhat bisa doki tare da wasu dakarun yaki acan nesa kadan sun darfafo wannan tsauni da suke kai! Nan take Mahaifin Ilaila ya mike tsaye zumbur ya suri Ilaila ya goyata a bayansa yasa Mayafi va daureta ta tamau sannan va falfala da gudu yana mai sakkowa daga kan tsaunin ya nufi wata hanya da tanufi çikin kungurimin daji mai dauke da manyan duwatsu, koda su sarki Marhat suka hango mahaifin Ilaila goye da 'yar sa ya tunkari cikin wannan daji a guje sai suma sukal karawa dawakan su.kaimi domin su cin musa, amma sai suka kasa saboda gudun nasa na sihirine. Ai kuwal sai shima sarki Marhata ya fara amfani da na shi sihirin na tsatin ya zamana dawakansu na iya tsallake duwatsu da bishiyoyi tamkar kibiyoyi ake harbowa, $ai da aka shafe rabin sa'a ana wannan tseren gudun tsakanin mahaifin Ilaila da sarki Marhat amma basu riske shi ba, gashi suna harbo masa kibiyoyi sai dai sun kasa samunsa har suka isa bakin| kogon| Hadari Aswad. Da zuwa sai mahaifin laila ya kunna kai cikin kogon ba tare da tsoron komai ba yana goye da Ilaila. Mutum na shiga wannan kogo zai ga wani katon rami a kasansa mai tsananin zurfin gaske dauke da wata gadace a saman ramin wacce aka yi ta da itatuwa, dole sai mutum yabi ta kan wannan gadar sannan ya wuce kana ya isa cikin wannan ainihin kogon dutsen inda aka ajiye kayayyaki na dukiya da sihiri marasa adadi, ba tare da shakkar komai ba mahaifin Ilaile ya wuce da gudu takan wannan gadar yana kallon kasa kuma yane tsalake wasu itatuwa wanda ba a takasu, domin idan mutum yayi kuskuren ta kasu zai subuto kasa gadar ya halaka saboda wata irin gagaruma wuta ce a kasan ramin take zabalbala har da narkeken dutse a cikin ta. Mahaifin Ilaila na cikin yin gudu akan wannan gada sai yaga sarki da dakarunsa sun shigo a guje sai suka tsaya a bakin gadar wace aka yi tada itatuwa, kuma itatuwan sun tsufa ga dukkan alamu baza suyi kwari ba, sai hankalinsu ya dugunzuma jikinsų va kama kyarma kawai sai sarki Marhat ya ratse gefe guda ya dubi badakaren dake bayansa sai yace maza ka ruga ka riske su ka kasheshi ka dauko min wannan yarinyar da littafin dake hannunsa, ciki tsoro bisa dole badakaren ya ruga kan gadar aikuwa taku na uku sai icen da ya taka ya karye ya sullubo kasan gadar yana mai kurma ihu. Koda ya isa can kasa cikin wutar nan sai suka ji kara soyewarsa tamkar anjefa nama a tafasashen man girki, nan fa saurar dakarur suka fisgita ainur suka fara Kokarin jada baya amma sai Sarki Marhat ya daka musu tsawa tare da cace duk wanda ya yi yunkurin guduwa zan kure masa kudunsa kuma in halakashi da hannuna, sajin haka sai dakarunsa suka tsaya kawai sarki Marhar ya ci gaba da umartarsu suna rugawa kan gadar har saida mutum tara suka hallak sannan ya tsayar da sauran ashe yana lurane da abinda yake sasu Hallaka, wani farin ice ne ba'a takawa daga cikin itace, idar kuwa mutum ya takashi take -zai sullulibo kasan ramin, nan take sarki ya sanar da sauran dakarunsa wannan matsalar sannan ya fara wuce wa da gudu ba tareda ya taka farin ice ba ya nufi inda su Ilaila suke, aikuwa suma sauran dakarun sukayi koyi dashi, koda mahaifin Ilaila ya hango su sarki Marhat sun biyo su sai yakara karfin gudun har ya įsa karshe gadar ya dira cikin kogon hadari Aswar. Yaci gaba da gudu a cikin kogon bai tsaya ba, ga tsubi tsubin dukiyoyi nan kamar su Zinare, luu u'u, jauhar da sauransu ko kallonsu bayi ba har $aida ya iso gaban wani teburi na karfe wanda a tsakiyar sa akwai wani dan karamin rami sannan ya tsaya ya kwanto Ilaila daga bayansa ya ajiye ta a gabansa ya kalleta kallon karshe a lokacın da hawaye ya zubo masa yace yake 'yata anan nake miki ban kwana domin ni nazo inda mutuwa zata rabamu da zarar kin ga na sa wannan littafi a wannan raminki gudu ki nufi can kudu karshen sa akwai cibiyar ruwa ta kogi kawai ki yi tsalle ki fada ciki, nasan tun kina yar shekara hudu na fara koya miki iyo a ruwa kiyi iya yinki har ki isa gabar rowan idan kina da rabon rayuwa zaki rayu har ki dawo nan ki dauki wannan Iittafi idan kuma baki da rabon rayuwa to shi kenan koba komai mun hana sarki Marhat cika babban burinsa a rayuwa, yana gama fadin hakan sai ya zura wannan littafin cikin wannan ramin dake kan wannan tebur din adaidai wannan lokacin sarki Marhat suka įso ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku hudu ba gama zura littafin a cikin ramin keda wuya sai mahafin Ilaila ya daskarc ya zama kamar kankara sannan ya dinga ruburbushewa yana zama gari. Koda ganin haka sai laila ta kurma uban ihu kuma ta fashe da kuka amma da taga Sarki Marhat ya nufota sai ta juya da gudu ta nufi inda mahaifinta ya umarceta saura taku daya ja! Marhat ya cafkota da hannunsa sai ta daka tsalle ta fada cikin wannan ruwan daya kasance cibiyar wani kogi kuma daga inda tayi tsallen ta fada kasa çikin kogin ramine mai zurfin gaske wanda ya firgita sarki Marhat ya kasa yin kundunbalar ya bita. Lokacin da llaila ta fada cikin wannan kogin tuni ta suma, cikin sa'a sai ta taso saman ruwa kuma igiyar ruwa ta nnga hankadota har ta isa bakin gaba indal wadandu masunta keyin su, anan sarkin masuntan kauye ya tsiceta inda yaga wata laya a wuyanta, koda ya bude layar sai vaga wata wasika a ciki, a cikin wasikar ne yaga wasiyyar da mahaifin Ilaila ya bari a gare shi daya ɗauki Ilaila sai ya kaita wajen wani mashahurin mayaki domin a bata horo ta jarumta da iya yaki Koda Ilaila tazo nan a tunanin ta sai ta fashe da kuka. Cikin hanzari Gadaraz ya shiga rarrashinta kuma ya rungume akan kirjinsa, daga can sai ýa janye jikinsa ya dubeta yace nasan yanzu Kin gama tino komai kisani yanzu bamu da warni isasshen lokaci don haka kitashi mu hanzarta muje inda aka ajiye wannan littafin sirrin mu dauko shi saboda shi babban makamin da zai kaimu ga nasara. Koda jin wannan batu sai Ilaila ta mike tsaye zumbur ta্|juya da baya ta sauko daga kan wannan tsaunin da gudu ai kuwa sai Gadaraz, Insam da Barsad ma suka yi koyi da ita suna saukowa daga kan wannan tsaunin kowannan su ya kama dokinisa ya haye suma dakárun Gadaraz masu bakaken tufafi sai suka bisu a baya aka sukwani dawakai da guda aka nufi kogon hadaril Aswad, dayake Ilaila ce akan gaba suna isowa gaban kofar kogon sai ta tsayar da dokinta ta sauko kowa ma sai ya tsaida nasa dokin ya sauko kai tsaye ba tare da wata fargaba ba Ilaila ta kunna kai cikin kogon ta tsaya a bakin wannan gadar ta itace har sai da su Gadaraz suka žo suka risketa sannan tayi musu bayanin yadda za'a haye gadar ba tare da dayansu va fadđa kasa cikin wannan gagaruma wuta ya hallaka ba, tana gama yi musu bayani sai ta wuce da gudu ta kan gadar kamar yadd mahaifinta ya wuce da ita tana goye abayansa shekarun da suka gabata sa'adda tana yarinya karama, hatta gwarzon sadauki wato Insam saida ya firgital da ya kalli wannan gada.wadda wannan narkakken dutse ke fasa acikinta da kuma nisa gami da zurfin dake tsakanin gadar da kasanta amma sai yavi ta maza yabi bayan Ilaila da gudu yana ma kiyaye taką wannan fararen itatuwan. Gadaraz ne ya zamo na ukun su sannan Bursad ya biyo su suma dakarun Gadaraz sai suka saida rai suka biyo su amma saida tsautsayi ya ritsa da mutum uku suka fada kasan gadar suke narke a ciki wutar ruwan dutsen, kai tsaye Ilaila ta nufi inda wannan teburin yake wanda mahaifinta yazura wannan jan littafin a cikinsa, da zuwanta sai ta iske littafina wajen kamar yadda suka barshi duk tsawon wadannan shekaru bai motsa daga inda yake ba amma kura da yana ta lullibe shi, batare da wani bata lokaci ba ta zura a cikin wannan ramin da littafin yake ta dauko shi, a wannan lokaci dakarun Gadaraz sun rude kuma sun Zauce bisa ganin Irın tarin dukiyar da ke cikin wannan kogon dutsea don haka basu san sa'adda suka fara bude rawaninsu ba suna zuba zinaren ba suna daurcwa gami da azawa a kansu, ilaila na gama zaro wannan littafin daga cikin wannan ramı da yake sai wasu irin munanan aljanu masu manyan bakuna da manyan jiki suka bayyana a gaban dakarun Gadaraz suka dinga yimusu hadiyya daya kamar mutum ya jefa gyada daya a bakinsa ya lunkume, kuma nan take dutsen ya fara tsatsagewa daga sama yana rushewa gami da zubowa kasa, da kyar da sidin goshi Ilaila, Gadaraz, Insam da Barsad suka ruga izuwa inda cibiyar ruwanan yake nan take, bayan duwatsu sun farfado musu sún sami raunika a jikinsu, suna isa wajen suka daka tsalle su fadawa cikin wannan kogi a matukar galabaice, nan fa suka yi yita iyo har suka kai gabar wannan kogin. Suna fitowa ne sai suka ci karo da sarki Marhat tare da dubunnan dakaru bisa dawa kai dauke da makaman yaki a gabansu. Sarki Mahat ya dubi Gadaraz da su insam ya bushe da dariyar mugunta sannan ya mikawa Ilaila hannu yace bani Littafina, tabbas duk wahalar da kuka kun sha ta zama a banza, domin nahiyar nan gaba daya ta zama tawa dan haka dukkanin ku kun zama bayina. AlhamduLillahi Yan Uwa da abokan arziki Allah Ya nufa mun kammala exam lafiya sai kuma jiran sakamako, ina matukar godiya da addu'o'inku a gareni Allah Ya bar zumunci da kuma kauna. Sannan wannan shine page na kusa da karshe inda daga next page Littafin Gwarzon Sadauki na biyu ya kare sai kuma mu shiga wani littafin amman kasancewar zamu shiga azumi sai mu bari sai bayan sallah sai na baku jerin Littattafan dake gareni sai ku zabi daya daga ciki. Na gode maku Allah Ya biya wa kowa bukatarshi ta alheri, AminGWARZON SADAUKI Littafi Na Biyu (2) Part F Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey Ilaila ta tari numfashinsa tana mai cewa idan kaga na baka wannan littafin to sai |dai idan bana numfashi a doron kasa. Sarki Marhal ya ce ai kuwa yanzu zaki daina numfashi. Tsulum sai Gadaraz ya shiga gaban Ilaila ya dubi sarki Marhat ya ce ba sai ka kashe taba da hannunka za ta baka wannan Littafin. Gadaraz ya dubi Ilaila yayi mata wata inkiya, batare da wata gardama ba sai ta nufi inda sarki Marhat ya ke rike da littafi da nufi zata mika masa, saura baifi taku uku kacal ta isa gareshi sai aka gaan harbor wata kibiya daga can samar wani katon dutse, kibiyar tazo ta cake a tsakanin Sarki Marhat da Ilaila take kowa ya dago kai ya dubi inda kibiyar nan fa suka hango rundunar sarki Zarmal bisa dawakai a sukwane sun durfafo su, babu wanda yayi wani motsi har rundunar ta iso kusa da su suka yi turjiya aka fara kallan kallo, daga nan sai sarki Zarmal va dubi sarki Marhat yace yau ne rańar raba gardama ranar da Karshen gaba zata zo, ranar da daya daga cikin mu zai mallaki wannan nahiya gaba daya, tabbas dole ne a yau daya daga cikinmu zai cika mafarkinsa, yanzu haka ana can ana yaki tsakanin sarkin yaki na da naka, kai a zaton kun shirya dabarar da zuku iya karar da mutanena cikin kankanin lokacin? To ina so ka dauko madubin tsafinka ka ga qbinda ke faruwa domin kare jin biri akeyi, duk tarkunan da dakarunka suka danawa dakaruna ba su afka ciki ba. Koda jin wannan batu sai sarki Marhat yayi sauri ya dauko madubin tsafinsa daga cikin aljihunsa ya shafeshi nan take yaga abinda sarki Zalmar ya fada shike faruwa, al'amarin daya daure masa kai kenan amma sai ya bushe da dariyar mugunta, sannan ya ce koda mayakanka da nawa sunyi ragas, to kayi sani cewa anan ni ne zanyi nasara akan ka, maza ku shiya ga maza nan bisa kanku. Nan take sarki Marhat ya zaburi dokinsa da gudu izuwa tawagar sarki Zalmar, ai kuwa sai sauran dakarunsa suka rufa masa baya, nan ta aka hade aka cakume aka kuma ruguntsume da azababben yaki, karar karafa da ihun mazaje gami da haniniyar dowakai ta cika dodon kunne, yayin da kura tatashi ta turnike sararin samaniya Ilaila, Gadaraz, Insam da Barsad kuwa sai suka dunga yaki da kowanne bangare saboda sukare kansu kuma su tsirar da littafn dake hannun Ilaila, nan fa suka fara kokari ficewa daga cikin taron yakin amma sai abu ya gagara, domin duk inda suka nufa sai suga ambisu du... ana yan yame su ana kawo musu sara da suka ta ko ina, idan da ba kowannensu ya kasance gawurtaccen jarumi ba da tuni an gama dasu, sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan bakin gumurzu sannan da kyar da sidin goshi kuma da karfin tsiya Gadaraz, Insam da Barsad suka budawa Ilaila hanya ta fita daga cikin taron dakarun da ake yakin dasu ta gudu tare da nausawa cikin daji. Koda sarki Marhat ya kyalla idanu ya hangota sai kawai ya tashi sama kamar tsutsu ya biyota, kwatsam sai yaga Sarki Zarmal ma a sama ta gabarsa, tare da tare masa hanya kai kace fuka-fukai ne da dasu, nan fa kowannansu ya daga takobinsa ta yaki suka hade a sama suna masu kai wa junan su sara da suka cikin bakin zafin nama da jarumtaka, duk sa'adda ta kubbansu suka hadu sai kaga tartsatsin wuta na tashi gami da Karar saukar aradu, kasa kuwa ta ringa jijjiiga tana tsawa saboda karfin sihirin tsafinsu, duk sa'ada da dayan su yayi kokarin yabi bayan Ilaila da gudu ya kamo ta don ya karbe littafin sihirin sai dayan ya sh gabansa suci gaba da yaƙi. Gadaraz, Insam da Barsad kuwa sai suka kara kaimin yaki suka ci gaba da bazaar da dakarun dake gabansu, a haka har suka samu suka kwace dawakai suka haye nan fa suka zaburesu da gudu izuwa inda Ilaila ta nufa. Ilaila na cikin gudu ne sai ta hango Gadaraz bisa doki a guje ya tabo garetal kawai sai ta tsaya tana jiiran isowarsa, koda ya karaso sai ta daka wanki wawan tsalle ta haye bayan dokin nasa suka cigaba da gudu su Insam na biye dasu haka suka baro rundunar yakin Sarki Marhal da ta Sarki Zarmal ana ci gaba da fatatatawa. Su Gadaraz basu dirfafi ko ina ba sai birnin Misira inda a hanyarsu ta zuwa sunzo wani dajı nan ma suka ga anata artabu gami dq azababben yaki tsakanin rundunar sadauki Darkis da rundunar sadauki Inzam, a wannan lokaci yakin ya dau zafi sosai babu abinda ido ke gani face zubar maza a kasa jini kuwa na malala tamkar idaniyar ruwa ce ta balle. Ba tare da jiran komai ba su Gadaraz suka ratsa cikin sansanin yikın da gudu bis dawakai suna masu kai sara da suka ga dakarun birnin kisira, take kuwa suka murkushe dakarun birnin kisira gaba daya ya zamana cewa babu mutum ko đaya da ya rage a cikinsu. Bayan kurar ta lafa ne sai aka zauna ana jiran dawowar $u sarki Marhat, ana cikin wannan jira ne kwatsam sai ga wani ragowar yaki ya dawo jina jina akan doki, yana mai fitar da numfarfashi da kyar, to daman a wannan lokacin da su Gadaraz suka kawowa su sadauki Inzam dauki, koda suka ga su Insam sai suka zata cewa sarkin sune Marhat ya kawo masu dauki kasancewar kammaninsu iri daya ne, don haka suna cike da kwarin gwiwa gami da farin ciki suka karasa wannan yaki, inda ba a dauki wani dogon lokaci ba suka murkushe dakarun birni kisira, da isowar wannan ragowar yakin sai ya fado daga dokinsa sa Inzam ya ruga gareshi tare da dago kansa ya dubeshi ya ce me ake ciki acan fiIin yaki? Ragowar yakin ya bude baki dakyar yace sarkin mu da sarkin birnin kisira sunyi ragas, sunyi ragas, sun zama gawa. Inzam ya dakawa ragowar yakin tsawa yana mai cewa shin kayi hauka ne, ai ga sarkinmu can ya dawo a raye zaka ce ya mutu. Ragowar yakin nan ya dubi Inzam yace wancan ba sarkin mu bane, kama dai suke yi da shi. Kafin Inzam ya juyo yayi wani abu tuni Gadaraz ya harbo masa kibiya ta sokeshi a wuya ta bullo ta keyarshi, take va fadi kasa matacce. Koda ganin haka sai ragowar dakarun Inzam suka mika wuya tare da zubar da makamansu na yaki. Batare da 6ata lokaci ba su Gadaraz su ka dunguma izuwa cikin birnin misira suna zuwa gidan sàrautar aka bude musu kofa suka kunna kai ciki, basu tsaya a ko ina ba har cikin turakar gimbiya.Sulaisa inda suka isketa tana ta faman sharar kuka. Ko da Sułaisa ta dago kai ta ga Insam, Gadaraz, Ilaila da Barsad tsaye a gabanta sai ta firgita kuma ta kamu da matukar mamaki. Da ta ga Insam ta zata Sarki Marhat ne amma kuma me ye gaminsa da wanda ya ci amanarsa ya gudu da me laifi Ilaila? Gimbiya Sulaisa tayi wa kanta tambayar da bata da amsarta. Ko da suka fahimci halin da take ciki sai Insam ya dubeta cikin murmush ya risina gami da girmamawa ya ce, "Ranki ya dade sunana Bawa Insam, kiyi sani cewa azzalumin Sarkin da yake son ya aureki tuni ya dadc da zama gawa a filin yaki. Sa'adda Sulaisa taji wannan batu sai ta murtuke fuska ta ce Ta ya ya zan aminta da ku, tun da babu mamaki kaine Sarki Marhat kana so ka yaudare ni ne kawai?" Gadaraz ya ce Ai ko zai yaudareki ba za iya tare da ni ba, tunda kin san ko wayel ni? Gaskıya ya gaya miki Shi ne Bawa Insam mai kama da Sarki Marhat wanda ya lashe gasar jarumtakar da aka yi a tsakanin bayin ranar da aka vi shagalin bikin aurenki a birnin Kisira. Yanzu zan nuna miki cikakkiyar shaidar da za ta tabbatar miki da cewa Sarki Marhat ya mutu". Yana gama fadin haka sai ya juyo ya dubi Ilaila ya yi mata inkiya. Nan take Ilaila ta zura hannunta a cikin aljihu ta dauko littafin sirrin Sarki Marhat ta nunawa Sulaisa. Nan fa Sulaisa ta kama yin murmushin farin ciki. A daidai wannan lokacin ne daya daga vikin amintattun dakarun Gadaraz ya shigo cikin turakar ya risinawa Gadaraz ya ce, "Ya shugabana komai ya kammala na zo da abin da ka umarce ni, kuma gabadayan 'yan majalisar garin nan ga su can sun taru a kofar fada ku kadai ake jira. Ko da jin wannan batu sai Gadaraz ya yi murmushi, sannan ya dubi su Insam ya ce Ku zomu je can." Nan take suka dunguma gabadayansu suka nufi kofar fadar birnin. Da zuwa suka iske gabadayan fadawan Marigayi Sarki Marhat da jama'ar gari a tsaitsaye an yi cirko-cirko cikin halin jimami da wasu-wasi. Wasu suna tunanin cewa Sarki Marhad ya mutu tunda labari va zo cewa gabadayan dakarun da va fita da su an kashe su babu daya a raye, amma kuma da aka ga Bawa Insam sai mutane suka shiga rudani. Nan take su Gadaraz kuka zo gaban jama'ar gari suka tsaitsaya. Kawai sai aka ga dakarun yakin Gadaraz kimanin su dari biyar a saman katangar gidan sarautar a tsaitsaye sun kewaye gidan gabadaya, kuma sun dana kibiyoyi a kan baka sun ritsa kowa. Kawai sai Gadarad ya dubi fadawan tsohon Sarki da kuma mutánen gari ya ce, "Ya ku jama ar birnin Misira kuyi sani cewa sarkinku ya dade yana tafiyar da mulkin zalunci a kasar nan. Yana sa muku haraji mai yawan gaske yana kuma kwace muku amfanin gona. Ya tara dukiya mai tsananin yawan da babu mai kamarta a nahiyar nan gaba daya. Amma wannan dukiya ba ta amfanarku da komai. To ku sani daga yau karshen wannan zalunci ya zo. Sarkinku Marhat ya mutu ga shaida zan nuna muku. Gadaraz ya dubi wani Badakare dake kusa da shi sai Badakaren ya miko masa wata jaka. Take Gadaraz ya bude jakar ya ito da abin da ke ciki ya daga sama kowa ya gani. Ba komai ne wannan abu ba face kan Sarki Marhat". Nan fa jam6aa suka dimauce aka kama ka-ce-na-ce. Gadaraz ya yi tsawa aka yi tsit sannan ya nuna Insam ya ce. Wannan shi ne Bawa insam mai kama da sarkinku Zuciyarsa ta adalci ce yana kuma da tausayi, ba shi da komai hakazalika shi ba dan kowa ba ne talaka ne kamar kowa. Daga yau shi ne Sarkinku, don haka Sabon sarki sabuwar rayuwa." Ko da jin wannan batu sai suka rude da shewa gami da tafi. Gadaraz ya daga hannu sama aka yi tsit sannan ya dubi fadawan Sarki.Marhat ya ce 'Duk wanda baya goyon bayan wannan sabuwar daula yana da zabi biyu ko ya hada kayansa ya bar gari ko kuma ya fito fili yana nuna adawarsa. Idan kuwa ya Munafurce mu hukuncin kisa ne a kansa. Da jiin wannan batu sai gabadayan fadawa gami da yan majalisar tsohon sarki suka daga hannayensu Sama suka ce "Muna goyon bayan wannan daula ta adalci." Nan take wuri ya hargitse da sowa aka fara kade-kade da raye-raye. Asannan ne su Gadaraz suka koma cikin gidan Sarautar suka Zauna. Gadaraz ye dubi Sulaisa ya ce, "Shin kina son sabon Sarinku a daura maku aure da shi" Sulaisa ta yi murmishi ta ce Ai yanzu șhi ke da zabi tun da shi ne Sarki. Insam ya yi murmushi ya ce, Tun ranar farko sa'adda aka kawo ki a cikin keken doki kika zuro santala-santalan kafafuwanki waje, sannan na yi arba da kyakkyawar fuskarki sai ji da ganina suka dauke, zuciyata ta kama bugawa da karfi yanayina ya sauya, na nemi yawun da zan hadiya a bakina na rasa. Ba komai ne ya haddasa hakar ba face tsananin sonki da na kamu da shi farat daya. Ina mai neman amincewarki da ki yardarki domin mu zamo miji da mata. Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye, yana mai kallon Sulaisa cikin murmushi kuma ya mai bude hannayensa. Kawai sai Sulaisa ta mike tsaye tana kallonsa daga can kuma sai ta ruga gareshi ta fada kan kirjinsa suka rungume juna. Take Gadaraz, Barsad da Ilaila suka kama yi musu tafi. Ana cikin haka ne Gadaraz ya kama hannun Barsad ya ja shi gefe daya ya dube shi ya ce "Birnin Kisra ya zama naka. Yanzu za ku tafi kai da dakaru kaje, ka kar6i karagarka. Bayan daurin auren Insam da Sulaisa da kuma bikin sarauatrsu za mu halacci bikın naka sarautar. Ka sani ba ka taba yin abin kirki ba a rayuwarka sai.wannan karon da ka yaki zalunci ka kafa adalci. Lalla adalcin za ka ci gaba da yi a kan karagarka idan kuma ka yi sabanin hakan ni da Insam zamu hada kai mu hambarar da gwamnatinka." Barsad ya yi murmushi ya ce "Ba zan taba kaucewa umarninka ba ya shugabana, tun da ba don kai ba har abada a kurkuku zan gama rayuwata. Yanzu ga shi ka mayar da barawo ya zama Sarki kuma adali. Ni da Insam duk ka mai da mu sarakuna kai kuma me ye makomarka?" Sa'adda Barsad ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi ya ce, 'Ni ba ni da sauran wata bukata a duniya tun da in tare da matata muna zaune lafiya. Burina daya ne jal daga nan har mutuwata na ga zaman lafiya da adalci ya tabbata a tsakanin al'umma a wannan nahiya. Duk sarkin da ya kau daga kan umarninmu zamu kawar da daularsa. " Ko da jin wannan batu sai Barsad ya yi murmushi ya ce "Na rantse da darajar iyayena da kakannina zan vi mulkina bisa gaskiya, adalci da tausayin talakawa". Cikin murna Gadaraz ya rungume Barsad suka yi bankwana. Sannan Gadaraz ya janye jikinsa daga cikin na Barsad ya juya wajen Insam shi ma ya rungume shi suka yi sallama yana mai dagawa amarya Sulaisa hannu. Nan take ya je ya kama dokinsa ya hau, dakaru dari biyu suka yi masa rakiya suka fice daga cikin binin Misira. Kashegari aka daura auren Sulaisa da Sarki Insam aka sha shagalin bikin aure gami da nadin sarauta. Kamar yadda aka yi wannan biki na sarauta a birnin Misira haka aka yi na Sarki Barsad a birnin Kisira cikin kwanciyar hankali da lumana. Daga wannan rana zaman lafiya, gaskiya da adalci ya wanzu a wannan nahiya gabadaya, har izuwa tsawon wadansu shekaru masu dan yawa. Daga bisani bayan shudewar dattawan kwarai irin su Sadauki Gadaraz sai al'amura suka sauya aka samu azzaluman Sarakuna suka fara hawa kan karagar mulki. A birnin Misira wani gawurtaccen sarki ne ya kwace karagar mulki da karfin tsiya ya kashe sarkin dake mulki da dukkanin ahalinsa sannan ya kashe gabadayan yan majalisarsa ya nada sababbi wadanda yake so, sannan ya fara tunanin hanyar da zai bi ya mallake manyan kasashen dake nahiyar. AlhamduLillahi Anan muka kawo karshen wannan littafin sai kuma mun hadu da ku a wani sabon Littafin na Abdulaziz Sani Madakin Gini Mai suna Birnin Sadaukai Ko kuma Taskar Tsafi zuwa bayan sallah idan Ubangiji Ya nufemu da kaiwa. Domin sauke cikakken Littafin a Wayoyinku na hannu ko kuma karantawa sau ku danna bulun Rubutun dake ƙasa ko kuma hoton 👇👇👇👇 https://aihausanovels.com.ng/litattafan-yaki/gwarzon-sadauki-littafi-na-1-complete-document-by-abdulaziz-sani-madakin-gini Ga masu son dauko Littafin Complete ga link dinsa nan a sama ko kuma ku tuntubeni ta wannan Number 08138873799 Ku huta lafiya Masoya 🥰🥰🥰