[9/14, 9:59 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM……. …….BIRNIN SA 1 Sunkuye nake a gindin famfon bayan gida ina wanke kayan kashin qanina Nazir. Safiya ce mai tsananin hazo, wanda matsanancin sanyin watan Fabrairu ya haifar.Ina sanye da ruwan bular siket mai fadi da farar suwaita mai dogon hannu. Kaina nade cikin hular sanyi mai fuska irin ta yaran-goye. Sanyin dake kadawa na karfe shidan safiya da sanyin ruwan da nake wankin da shi, shi ya hadu ya haifar min da toshewar hanci. Can anjima sai kaduwar hakora qaf-qaf-qaf! Kamar ana kada cokali a tsakaninsu, don haka na mike a galabaice na juya hagu da dama, kana na mai da raunannun idanuna da suka kankance cikin dan lokaci zuwa hanyar cikin gida. Na tabbatar babu kowa ba mai kallona, babu motsin su Ilyas ‘yan rahoton Mami, wadanda nake da tabbacin yanzu suka yi juyin farko a barcin su. Sai na tsame hannuna na koma karkashin bishiyar guava dake nan bayan gidanmu na kwanta, na cure na dunkule wuri guda kamar curin alkaki, jikina na kaduwa, hannayena biyu na hade na tura cikin rigata, hawaye na bilbila. Wani bangare na zuciyata ya ce, “Bai kamata ki yi kuka ba SAKINAH! Inda sabo ya kamata a ce kin saba........” To ana saboda wahala ne??? Rai dangin goro ne yana bukatar hutu, ko da kuwa a ce jikin na karfe ne. Balle jiki na jijiya da tsoka, wanda jinni ke zagayawa a cikinsa. Na tambayi kaina shin haka sauran yara tsararrakina da nake gani a makaranta suke rayuwa a gidan ubansu? Shin da gaske ne Abbanmu ne ya haife ni ko ko “Walagigi” ce kamar yadda Mami ke cewa? To idan ba Abbanmu ne ya haifeni ba, mai ya sa ake kirana da sunanshi a makaranta? Idan shi ya haife ni, mai yasa ake banbanta ni da sauran kanne na? Kwakwalwata ta cunkushe, tunanina ya yi zurfi, haka kukana ya tsananta. Hawaye ya hade da majina, har sautin kukan ba ya fita sosai. Watakila hakan ne ya yi sanadiyar da ban ji tahowar Mami ba, sai tsawarta da azababben rankwashinta mai shiga har cikin kwakwalwata, ya dusar mini da ji da gani na wucin gadi. Ta kama hannayena duka biyun ta murde tana ci gaba da rankwashina, na yi kara don azaba. Cikin kuka na ce, “Ki yi hakuri Mami ba zan sake ba.....”!. Ta ce, “Ko ubanki bai isa yau ya bani hakuri ba. Ashe gaskiyar Ilyas ne idan na saki aiki barci kike yi a gindin bishiya. A yi magana ki ce ayi hakuri. Da bana hakuri dake da tuni na kada ki duniya kamar yadda na kada uwarki. To dadin ta kina yi min amfani, don haka ya zame min dole in yi hakuri dake, amma ba zan dauki wannan sakarcin ba”. Ta sakar min kunnen ta hankadani iya karfinta, na bugu da bishiyar da nake jingine da goshina, kafin ki ce meye wannan goshi ya haye ya yi suntum. Na kai hannuna duka biyun na dafe goshin ina kuka mai ban tausayi. Kwalar rigata Mami ta ja keeeey……! Har jikin famfon, kana ta jawo kwandon kayan wanki ta karo, duk rabi na Nadiya da Ilyas ne, sai ‘yan kadan na Abba. Ta ce, “Mintuna talatin na baki ki wanke su fes! Ki dauraye ki shanya ki yi ta firfita su har sai sun bushe. Ga doya can a kicin ki feraye ki dora, idan ta dahu ki kirba mana sakwara a turmi kafin Adama ta zo ta yi miya, kina ji na ko ba kya ji?” Na daga kai da sauri, kamar in ce, “Mami makaranta fa? Yau ba za ni ba?” Na jiwa kaina tsoron al’amarin da hakan zai jawo, da rankwashin dake azabta ni, wanda ban san lahanin da yake yi min cikin kwakwalwa ba. Na dukufa wanki ba ji ba gani, na nemi sanyin da nake ji na rasa, zuciyata ta kekashe. Ina cikin shanya na jiyo hayaniyar su Nadiya suna fita don tafiya makaranta. Na zo bayan bishiyar goba na rabe ina lekensu, kaunata da makaranta na cigaba da ruruwa, hawayena na ci gaba da kwarara. Na kai bayan hannuna ina share idona. Daga inda nake rabe na jiyo Nadiya na cewa da Safinatu, “Yau su Walagigi an gamu da fushin Mami........”. Safina ba ta ce komai ba suka fita. Har suka gama ficewa ban gama dawowa hayyacina ba daga azabar zugin, rankwashin wadda take a matsayin Mamana. Na fara kirbar sakwara kenan Adama mai aikin Mami ta iso. ‘Yar kabilar ‘Itsekiri’, ba tun yau ba nake jin tsoron Adama. Ba don komi ba sai don munin halittar ta. Baqa ce wuluk! Guntuwa, amma ba (wada) ba. Mai nanannen hanci, idanunta miri-miri kuma jajaye. Ban san me ya kai Mami daukar Adama a matsayin mai aiki ba. Sai dai ga yadda na fahimta wani boyayyen aminci ne a tsakanin su, ba aiki kadai Adama ke yiwa Mami ba. Adama tana nemo mata asirai a tsibirin su da tsubbace-tsubbace kala-kala a garinsu Bayelsa. Wadanda ake dirkawa Abbanmu yana ci ina ji ina gani don ba tsorona suke ji ba, balle su boye wai don ganin idanuna. Ganin irin rikon sakainar kashin da wulakancin da Mami ke min, ya sa Adama jin tausayina, da son jana a jiki, wanda ban ga dalili ba a matsayinta dai na aminiyar Mami. A kullum in tana aiki na kan ganta da wani tsumma kunshe da wani abu wanda take shaka lokaci-lokaci. Idan kuma ta shaka za ta yi ta aiki da kuzari babu gazawa. Daga karshe in ta gama aikin, zubewa take a corridor din kicin ta yi ta barci har sai Mami ta tashe ta, ta ce ta tafi Baskwata. Ina tsoron Adama, ita kuma tana sona, ba don komi ba sai don ba ta yi min kama da mutane masu dauke da ALHERI ba. To yau ma kamar kullum, tana shigowa muka hada ido, ta yankwane fuska kamar zakanya wai ita a nufin ta murmushi ta yi min. Na yi saurin kau da kai. Ta ce, “Sakina, Sakinatun Abba”. Ban amsa ba. Ta soma kiciniyar dora sanwa tana cewa; “Yau muguntar Mami ko makaranta ba ta barki kin je ba?” Ni dai ban amsa ba, sai jibgar doya nake tun karfina kamar Allah ya aiko ni, har da hadawa da tsalle, wai don dai in samu sakwarar ta hada jikinta, amma yawan doyar ya sanya kamar ba jibgarta nake ba. Ta juyo ta dube ni ta yi dariya cike da tausayi, ta soma taku tana matsowa inda nake. Ta ja kujera ‘yar tsugune ta zauna, ta sassauta murya ta ce. “Da za ki bi shawarata da kin gudu wurin Mahaifiyarki kin huta. Dubi irin kyawun da Allah ya yi miki, wanda bai yiwa kowa cikin gidan nan ba, ki zauna matar uba tana azabtar dake a banza. Ai yanzu an daina wannan zamanin. Abu ne da ake yi a can wani karni a baya da ya shude, amma ba a wannan karnin na ‘yancin kai da muke ciki ba”. Na bi ta da kallo galala! Ina tunanin ko ba ta da hankali ne? Matar da ta tsige ni a nono, ta dankafar dani hannun matar uba, bata taba waiwayena ba koda da ziyara itace wacce zan bi?, Da dadi ba dadi na rayu da ita, har na kawo wannan munzalin. Shekaru goma sha biyu ba ta waiwaye ni ba, ita ce wacce zan bi? Alhalin ba ta kaunata? Tunda ta iya ta barni tun ina bakin nono, ba ta kara waiwayata ba! Nima zan ci gaba da hakuri, in ci gaba da rayuwata a haka. Tunda dai wuya ba ta kisa, da tana kisa da tuni ta kashe ni tun ina mitsitsiyata. Tukunna ma, ina na ga kudin jirgin da zan je Libya in nemo (Sakinah)? Libya a ina? A wane bangare? Wadda ta tafi ta barni tun ina shekara daya, yanzu haka ma ta manta da kamannina. Nima ban santa ba, ban san kamanninta ba. Sunanta kawai na sani a bakin Abbanmu, inda ya ce sunanta ne aka sa mini. Magana nake a zuci ni kadai kamar zararriya. Ban san cewa a fili nake yi ba. Adama ta kafe ni da jajayen miri-mirin idanunta, ta ce, “Zuwa Libya, da neman Mamanki ba wahala bane. Abbanki yana da adireshinta. Kudin jirgi kuwa sai in baki so ba. Ni din nan ba wani sirrin Mami da ban sani ba, idan kin lura duk ni nake kawo mata magungunan da take wa Abbanku amfani dasu tana biyana. To amma ai ba haka kawai nake mata wahalar ba, abin dari nake maidawa dari biyar. Ke baki san Mami kurciya ta yi mata ba ta koma kasarsu ta kuma dawowa da Abbanku sadakinshi???” Na saki baki ina kallon ta. Maganganunta sun girmi kunnuwa da tunani na, na bude baki da kyar na ce, “Ke wa ya gaya miki?” Ta yi dariya sosai ta kai hannunta ta bugi kirjinta, “Ni din nan ni na binne asirin da hannuna a makabarta. Sakina ki yi hakuri, Allah ne ya sanya min kaunarki, shi yasa nake gaya miki sirrin Mami. Ki yarda ina kaunar ki, ki tserar da rayuwarki ki tafi inda za ki huta. In ba haka ba Mami za ta lalata miki kuruciya, babu birbishin imani a tare da ita. Idan ba ta lalata ki ta hanyar azaba da wahala ba, za ta sabautaki da asire-asirenta kamar yadda ta sabauta duk wani da ya shafi Abbanku. Ta sha gaya min ba ta kaunarki....... Ke kadai kika rage mata, ba ta son ki samu gadon Abbanku. ‘Ya’yanta ne kadai ke da shi. Sakina ki nemawa kanki gata, ki tserar da rayuwarki. Zan ranta miki kudin jirgin zuwa Libya, in kin je sai ki aiko min......”. Cikin tashin hankali da tsorata, gami da tsanarta gaba daya ita da Mamin na ce, “Babu inda za ni, duk abin da ya faru da bawa da sanin Allah! Nan ne gidan ubana, don haka bani da wani gata da ya fi nan. Dabarata ko taki ba ita za ta fissheni daga abin da Allah ya hukunta a kaina ba. Kuma idan da rai watarana za ni ganta. Ki daina gaya min wani al’amarinku ke da Mami, babu ruwana, bana son ji. Can a tsakanin ku, bana neman taimakon kowa sai na Allah. Don haka rike kudinki, babu inda zani. Nan ne gidanmu, banida inda ya fishi. Don haka ki daina jin tausayina, ba akan qaya nake ba”. Ta yi murmushi ta mike ta karbi tabaryar daga hannuna, “Kawo sakwarar in karasa miki, ba zan daina tausaya miki ba Sakina, bari na karasa miki kafin ta zo ta kama kwarzabarki”. Ba musu na sakar mata, jikin cabinet na koma na jingina, na runtse idanuna. Tunanin abubuwan da na fahimta game dani kaina, ke dawo min filla-filla. Na fahimci ni SAKINAH ‘I am leading an incomplete life.’ Duk da ina tare da mahaifina yana kaunata sama da komi a duniya, to amma kaunar ba ta amfana ni da komi ba, tunda ba ta da power din da za ta fitar dani daga halin kuncin da nake ciki a gidanmu. Kaunar uba ba ta da tasiri musamman in babu uwa a tare da Da. Ita ce ta san ciwonka, ita ce za ta tsaya ta san me kake ciki. Ita ce kadai za ka iya gane your inner feelings, meye matsalarka, me ke damun ka? Ita ce za ta tsaya a kan tarbiyyarka da rayuwar ka wanda ni duk ban samu wannan ba. Ita ce kadai za ta yi maka soyayya mara algus, sai ko uban da ya haife ka. Ta yi aiki da karfi da lafiyarta. domin amfanin ka. Kenan ni Sakinah na rasa wani bigire ko-ko bango, kuma majingini mai muhimmanci ga dan adam, musamman diya mace........ *** *** [9/14, 9:59 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM.... Sunana Sakinatu, wadda mutane da dama ke taqaitawa da Sakinah. M.T Liman shi ne mahaifinmu, wato Chief JusticeMukhtari Tukur Liman (Alkalin alkalai na kasa baki daya). Sakinah M.T Liman, shi ne sunan da nake amfani da shi, kuma kowa ya sanni da shi a makaranta. Abbanmu dan asalin garin ‘Yan Leman ne ta jihar Jigawa, ya yi zuzzurfan ilimi a kan alqalanci, tun daga kuruciyarsa a gida da waje da taimakon gwamnati, har zuwa matakin da yake kai a yau. Tsohon Alkali ne fitacce, kuma shahararre wanda ya shahara kwarai a kan aikinsa, wanda ya sha gwagwarmayar rayuwa a kuruciyarsa, ya samu kudi da suna a shekarun girmansa. Abbanmu dan dangi ne gaba da baya, amma bamu sansu ba, domin babu mai kaimu, suma basa zuwa. Duk ba don komai ba sai don Mami da izayarta, duk wani talakan da ya san ciwon kansa ba zai kawo kafarshi gidan M.T Liman ba, ko da kuwa a ce a ciki guda suka fito. Mami (Lami) ta hana wannan, Abba nata ne ita kadai da ‘ya’yanta. ‘Ya’yan Mami guda biyar ne, idan ka hada dani ‘ya’yan gidan mun zama mu shida ke nan. Safina ita ce babba ‘yar kimanin shekaru goma sha hudu, sai Ilyas sannan Nadiya, Abba ke bin Nadiya, yayin da Nazir ya kasance autanmu, wanda Mami take goyo a halin yanzu. Mun zauna a garuruwa daban-daban, kusan duk manyan biranen Najeriya babu inda bamu zauna ba, kamin daga karshe mu dawo nan Abuja inda Abba ke aiki da (federal high court) matsayin Alkali na qololuwa da kasa ke tinqaho da shi, domin babu wani Alkali da ya sha gaban M.T Liman a Najeriya gaba daya. Zan iya cewa ban san dadin arzikin babana ba, tunda ba ci nake ba. Sitturuna kwata-kwata zan iya kirga su; goma. Wadanda Mami ke bani kala dai-dai da kowacce sallah da takutaha. Don haka mafi yawa sunyi min kadan haka nake sanya su a matse, suttura da kayan qawa na mata sai dai in gani a jikin su Safinah. A tasowata na ga Abba ya auri mata daban-daban har guda biyar, in ka cire mahaifiyata. Sai dai kowacce ba ta shekara take sa takalmanta ta fice. Ta karshen ce ma ta yi ciki har ta zo haihuwa ta haifi qadangare ya yi kanta ya shaqe har ta mutu. Tun daga nan Abba bai kara marmarin kara yin aure ba, Mami dai ita ce har yau babu wadda ta kama kafarta a zuciyarsa. Ita kadai ke mulkin wannan tangamemen gida namu. Mami ‘yar garin Bidda ce, sun hadu da Abba tun lokacin da yake karatu a jami’ar Legas (UNILAG). Ita da Mamanta suna sayar da abinci da lemo cikin jami’ar, kullum a ‘kiosk’ dinsu yake cin abinci har suka saba da Maman-Lami da Lamin kanta. Daga baya Maman Lami Allah ya ji qanta ta daina karbar kudin sa, a kyauta yake ci kullum safe da rana, saboda son da ta lura Lami na masa. Bai taba tsammanin zai so Lami ba, sabida kwatakwata ajin rayuwarsu ba daya bane, ko firamare bata yi ba, gata ba kyau ba ba fasali ba, ba’a zancen tarbiyya, gata girman Legas, a yayinda shi ya kasance dan Limami jikan Limamai, amma farat Daya ya ji ta shiga zuciyarsa, saboda ladabin da take mishi da yadda take nuna mishi kauna. Shikuma Allah yayi shi mutum mai girmama duk mai kaunarshi. Don haka ne da Mamanta ta bijiro da batun aure tun kamin ya kare karatu bai yi musu ba. Ya zo gida ‘Yan Leman ya kawowa mahaifinshi Liman bukatar shi na aje masa neman auren Lami a Bidda, ya manta da diyar wan mahaifinshi Suwaiba da aka yi musu baiko shekaru uku da suka wuce, an hanata kula kowa tana zaman jiransa ya kare karatu kamar yadda ya bukata, a lokacin yana kokarin hada (LLB) dinsa. Wannan shi ne abin da ya fara janyo masa sabani da iyayenshi, domin kafewa suka yi kan sam-sam basu amince ya auri Lami ba. Kai ko su biyu basu amince ya hada ya aura ba, don basu yarda da asalinta da tarbiyyar ta ba. Wannan ne ya sa ya tsallake ya bar gida ‘Yan Leman. Suka je garin su Lami Bidda suka yi aurensu, suka dawo Legas inda Mamanta ta kama musu haya a Surulere har ya karasa karatu. A lokacin ne Maman Lami ta rasu, wadda ita ce taqamarsu mai tallafa musu, tunda ba aikin komi yake ba. Dole suka tattaro suka dawo gida ‘Yan Leman. Abba ya ce min wannan shi ne babban kuskuren da ya tafka a rayuwarshi, wanda har gobe yake nadamar shi. Domin fata-fata mahaifinshi da mahaifiyarshi suka yi masa, suka ce ya tafi sun sallama shi sun barwa Lami da uwarta. Malam Sule mahaifin Suwaiba da ya ki aure kuma Baffansa, shi ne ya tsaya tsayin daka ya sasanta tsakanin shi da iyayenshi suka hakura suka karbi Lami a matsayin surukarsu kan ba yadda za su yi. Aka ware musu sassa guda a nan gidan mahaifinshi suka zauna. Nan ya bar Lami ya koma Lagos ya ci gaba da karatun shi. Bayan watanni uku-uku yake zuwa. Don haka Suwaiba ta hakura da shi ta auri wani malamin firamare a nan ‘Yan Leman. Allah bai bawa Lami haihuwa da wuri ba sai da Abba ya kammala karatun shi ya tafi (Law School) ya kare ya samu aiki da babbar kotun jihar Jigawa, aka dauki shekaru uku da fara aikinsa har ya samu ya kammala ginin da yake yi a cikin garin Dutse suka koma shi da Lami. A lokacin Allah ya karbi ran Liman Tukur wato mahaifinsa, sai mahaifiyarshi Inna Abu da qaninshi Tasi’u da sauran kannen shi mata Kubra, Dijah da Zainaba, wadanda duk an musu aure sun haihu a gidan mazajensu. Sun dade a garin Dutse kamin Abba ya samu damar fita qaro karatun Alqalanci a kasar Libya da taimakon Gwamnatin jihar Jigawa. Ya bar Lami da yaron ciki. Bayan watanni tara ta haifi Safina mai kama da Abbanmu sak, ashe rabon haihuwata ya kai Abbanmu kasar Libya. Inda ya fada a matsananciyar soyayyar wata abokiyar karatunsa “Sakeeinah” ‘yar asalin kasar Libya a garin Tripoli. Kusan duk abin da ya mallaka ya narkar ya auri Sakieenah sabida aurensu babu sauki, suka yi aurensu a Tripoli, ban da kanin shi Tasi’u da Baffanshi Malam Sule babu wanda ya sani, sai da suka kammala karatunsu tsaf suka tattaro suka dawo, Sakinah dauke da guzurin ciki na watanni biyu. Lami ba ta zata ba, ba ta tsammana ba sai ganin Abba ta yi da sankaceciyar Balarabiya wai a matsayin matarsa. Hauka ne kawai ba ta yi ba, tayi bala’in tayi masifar ta yi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita, tana murnar sabon gida katoton gaske ita kadai ranta, amma ashe abin da Abban zai yi mata ke nan. Don haka a washegari ta goya diyarta ta yi yaji ta koma Bidda gidan wan mahaifiyarta. Abba ya yi sintirin biko har ya gaji amma ta ce ba za ta dawo ba. Inda amarya Sakeeinah ta yi zamanta a Dutse tana rainon cikinta hankali kwance, har zuwa sanda ta haifeni. Saboda son da Abba ke yiwa Sakeinah ya sanya yasa mini sunanta. Kamana daya da Mamana, ko a farce ban yi kama da Abba ba. Sakienah ta kama dangin Abba ta rike cike da alheri, mutuntawa da kyautatawa. **** A can Bidda Lami ta fara shiga halin ni ‘yasu, a dalilin Baffan nata ba wani mai hali bane(Herbalist) ne wato mai bada magungunan gargajiya, ga shi dama ba ta san babanta ba balle danginsa, haka ta tashi ta ganta tare da mahaifiyarta, ba ta kuma taba tambayarta cewa wane ne babana ba balle danginsa. Ita ma kuma ba ta taba budar baki ta yi mata zancen ba. Hatta abin da za su sanya a bakinsu ita da diyarta ya soma gagararsu, sannan ga rashin arzikin da matan kawun nata ke mata, don sun gaji da zamanta tare dasu, babu gaira babu dalili ga shi ta ce mijin bai saketa ba balle su yi tunanin watarana za ta yi aure su huta. Babban tashin hankalinta yadda yaran gidan suke cin zalin Safina, ba ta isa ta rarrafo tsakar gida ba za ta jiyota ta tsandara kuka, dole kullum kuma ko yaushe ta goya ta don sama mata lafiya. Naira biyar wannan ta fi karfinta, tunda ita ba karatu ba balle ta yi aiki, ita ba jari ba balle ta yi kasuwanci. Gaba daya sun fige sun lalace ita da diyarta, yadda wanda ya sansu a Dutse da ‘Yan Leman ya kuma gansu a lokacin da kyar zai gane su. Ga Abban tuni ya yi watsi da al’amarinta ya kama Balarabiyar matarshi ya kulle a kofar zuciyarshi. Don haka ta soma bin soron malaman tsibbu wai a kado mata hankalinshi ya dawo da kanshi ya mai da ita. Sunyi iya yinsu har sun gaji, duk ‘yan gwala-gwalanta sun kare amma babu M.T Liman babu dalilinshi. Mahaifin Abbanmu mai rasuwa shi ne babban limamin garin ‘Yan Leman, don haka gidan kakanninmu ba boyayye bane a ‘Yan Leman. Babba da yaro kowa ya san gidan Liman Tukur. Sakinah ta bi duk kannen Abba mata dake gidan aure ta jari mai tsoka, kowacce ta kama sana’a. Dija na kiwon kaji (Poultry). Zainaba na dinki, Kubra na gashin gurasa. Sannan ta tsaya tsayin daka wajen ganin M.T Liman ya kula da karatun Tasi’u wanda ke karatu a jami’ar Maiduguri mataki na biyu, fannin aikin jarida. Don haka suma suka kamata suka rungume abin da basu samu daga Lami ba, sai bakin qyashi da rowa, sannan da rashin son kowa ya rabi mijinta. Wannan halinta ne tun M.T ba shi da komai. Watanni biyar ke nan da tafiyarta, a lokacin cikin Sakina ya shiga watanni bakwai, ta goyo ‘yarta babu ko biko ta dawo ‘Yan Leman gidan Baffa Sule ta ce gata ta dawo dakinta, ya bai wa M.T hakuri ya maidata. Baffa Sule bai yi la’akari da halayen Lami ba da kowa nasu ke kokawa ya sa M.T ya mai da ita dakinta, ba tare da wata tashin-tashina ko bin ba’asi ba. Ya ce, ai shi dama ba korarta ya yi ba ita ce ta kori kanta, amma idan ta san ba za ta zauna lafiya da matarshi ba, to ta koma inda ta fito. Tana kuka da al’ajabi ta ce, “Ta yarda za ta zauna da Sakienah”. Don haka ta bude dakinta ta share ta zauna, sai dai kuma ko maganar arziki wannan babu ita tsakaninta da Sakeinah, duk da yadda Sakina take ba ta girma. Zuwa lokacin Sakina ta zama ‘yar gari ta iya Hausa, sannan M.T ya samu promotion suka tattara suka koma jihar Lagos. A can ne Mami ta hadu da Adama take mata aikace-aikace tana biyanta, tana zaune tare da su har suka koma jihar Kaduna inda aka haifeni. Aminci mai tsanani ne tsakanin Mami da mai aikinta Adama. Bayan haihuwata ba da dadewa ba mahaifiyata ta koma kasarsu, bayan ta ajiyewa Abba ni ko yaye ni ba ta yi ba. Na girma na ganni a gidan mahaifina cikin wata irin rayuwa mai wuyar fassaruwa ta kunci da zalinci, har ma da rashin tsoron Allah cikin al’amarinsu. Sai kuma Allah ya sanyawa Adama tausayina, duk da kiyayyar da Mami ke min, take taimaka min a boye tun ina kankanuwa. Ta sha kwatata in Mami na jibgata, haka nan tana bani abinci a boye, a duk lokacin da muguntar Mami ta motsa ta hanani. A tasowata na ga Abbanmu ya yi aure har sau hudu bayan mahaifiyata, kowacce kuma ta fita ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Kamar yadda na fada a baya. Don haka ne Abba ya hakura da aure, sai Mami ita kadai ranta. Shekaru biyu ne tsakanina da Nadiya wadda Mami ta haifa a Kano, muna Porthearcourt aka haifi Ilyas, sai Abba (Muktar) sannan Nazir wanda aka haifa a nan Abuja. Mami gogaggiyar ‘yar duniya ce ta a buga a jarida, ta yi kawaye da yawa matan manya iri-iri a nan Abuja, masu ra’ayi da akida irin tata ta rashin hada mijinsu da kowacce mace ta hanyar asire-asire da tsaface-tsaface, musamman Hajiya Laila, uwargidan Justice Ribadu mataimakin Abbanmu, halinsu daya, akidarsu daya, sannan turbarsu daya na sun fi karfin zama da kishiya. Da dukkan alamu kuma suna cin nasara cikin al’amuransu, tunda dai an ce tsafi gaskiyar mai shi ne. Domin ita Hajiya Laila duk kishiyar da a kai mata sai ta rasa wani bangare na jikinta sannan ta fita, kamar ido, kunne ko kafafu. Wannan ne yake tsorata mata da auran masu mazaje. Don haka Mami (Lami) ta zamo BABBAR MACE a katafaren gidanta. BABBAR MACEN da mijinta ke shayinta. BABBAR MACEN da ta takurawa rayuwar mijinta, ta hana shi dandana kwanciyar hankalin aure da ni’imar da Allah ya yiwa sauran mata. Sannan BABBAR MACEN da ta yi sa’ar raba shi da farin cikin rayuwarsa (Sakeeinah), ya koma waina a tanda, sai yadda Lami ta juya shi. Don haka ne duk wani wanda ya san irin rayuwar da M.T Liman ke yi a gidansa, ya kuma ganshi a waje, cike da haiba da kamala, dole ya tausaya masa, har in yana da imani, to ya taya shi da addu’a ya kuma zubar masa da hawaye. **** [9/14, 9:59 PM] Asmau: To haka abin yake a gareni, kullum na yi sallah ina yiwa Abba addu’a, ko da nike yarinya karama, na san Abbana ba ya jin dadin zama da Mami. Sau tari idan ina son ganin shi, na leka ta tagar falonshi, na kan ganshi ya yi tagumi, kuma kullum cikin rama yake, abin da ya haifar mishi da cutar hauhawar jini, yake yawan ganin likita akai-akai, wanda yake zuwa har gida yana duba shi duk sati. M.T Liman mutumin kirki ne, kowa ya san haka. Wanda abin hannunshi bai rufe mai ido ba, wanda Allah ya halitta da yawan kyauta da alheri. Sai dai kuma duk yadda ya so da ya dinga tallafawa ‘yan’uwansa hakan ya ci tura, Mami ta bi ta kankane komi, komai zai yi sai ya yi shawara da ita, ta tabbatar masa ta amince. Tuni su Kubra suka dauke kafafunsu daga gidan dan’uwansu saboda wulakancin da Mami ke musu, duk dumbin arzikin Abba basa cin kwandalarsa sai dai su Nadiya. Dadinta da ya kasance Kawu Tasi’u ya kare karatunshi ya yi hidimar kasa ya samu aiki a can Dutse, shi yake tallafa musu. A da Daddy baya watanni uku bai je ‘Yan Leman ba gai da Baffanshi Sule da sauran danginsa, amma tun sanda muka dawo Abuja Mami ta san kissar da ta yi ta hana shi, don a cewarta Baffa Sule baya kaunarta, tunda a kanta ya ki auran ‘yarsa, wadda kuma mijinta ya rasu a wannan lokacin tana zaune gida. A cewarta so yake ya sake kakaba mishi. Har ga Allah Abba na son ya auri Suwaiba ko don Baffa Sule ya ji dadi, amma yana tsoron kara yunqurin yin auren, don ya san ba da dadewa ba wani mummunan abin zai faru ya saketa. Don haka ya yankewa zuciyarshi da muguwar rawa…... gwamma kin tashi. **** Yau ranar ta kasance asabar, don haka duka yaran gidan suna nan basu je makaranta ba. Abbama yana gida bai je ko ina ba. Ina bayan gida ina wanke-wanke, yayin da Adama ke gefena tana yankan salad. A can wani gefe daban Abba ne ke wasa shi da dan makotanmu Salim a kan kekunansu suna wasan tsere. A cikin gida kuma dakin su Safina ita da Nadiya suna kwance kowacce a gadonta suna cin biskit din digestive suna kallon film din Indiya a tashar tauraron dan Adam. Safina ta kau da idonta daga talabijin din cikin damuwa, ta ce, “Yanzu abin da Mami ke yi tana jin tsoron gamuwarta da Allah kuwa Nadiya? Tun asuba ta tashi Sakeeinah, diba har zuwa yanzu tana bayan gida tana aiki ba ci ba sha”. Nadiya ta ce, “To laifin wa? Laifin Abba da ya saki babarta. Da tana nan ai ba za ta yi mata haka ba, ya aura ya saki kamar na mamajo”. Mami ta shigo duk suka yi muqus! Ta dauki abin da za ta dauka a dakin ta fita. To haka ne, hatta ‘ya’yanta shayinta suke balle Abbanmu. Amma a zahiri akwai boyayyar kaunata ta ‘yan uwantaka a zuciyoyinsu wadda ba ta da tasiri tunda basu da karfin gwiwar da za su bayyanata a fili. Safinah na aji hudu na sakandire, ya yin da nake a J.S 2, sai Nadiya tana J.S 1, Ilyas da Abba duk ‘yan firamare ne. Abba ya zo wucewa ya ganni, takaicin duniya ya kama shi, wai kamar shi da arzikinsa da komi, wai amman a ce ‘yarsa ce ke wanke-wanken gidansa. Ya ce, “Sakinah!” Cikin wata murya mai rauni da rashin amo. Na dago kumburarrun idanuna wadanda ke cike da barci da gajiya na dube shi. Ya ce, “Tashi ki tafi daki”. Cike da tsoron abin da hakan zai haifar na tsame hannuna na dauraye na mike na nufi hanyar cikin gida, ina jinshi yana ce da Adama ta karasa wanke-wanken. Dakin da Mami ta ware min a gidan kusa da dakin su Safinah ne, da babu komi sai fallen tabarma da kayana cikin (Ghana must go), amma shi Abba bai san hakan ba, ya dauka daki daya muke kwana da su Safinah, don bai cika kwakkwafi ba. Daga nan inda dakina yake ina jiyo muryar Abba a dakin Mami, ya ce cikin tattausar murya, “Yanzu saboda Allah Lami ina kudin da nake biyan masu aiki suke yi miki aiki? Da za ki dinga sanya Sakinah cikin ayyukan gidanki masu tsauri? Naki ‘ya’yan kin killace su a daki suna kallon talbijin?” Mami sai ta fashe da kuka, cikin kuka take cewa, “Dadin ta dai ba za a yi min gorin haihuwa ba, har da bakinka za ka fada min cewa Sakina ba ‘yata ba ce don kawai ina yi mata horo na ‘ya mace. Uwar tata tana sonta ta ajiye min ita tun a bakin nono? Na yi rainonta har Allah ya rayata, don na dan sa ta aikin da bai taka kara ya karya ba shi ne za ta kashe min aure?” Mamaki ya hana Abba cewa komai, ya juya ya fita. Fakam-fakam! Ta yo dakina ta soma buga kaina da bango, na yi kara na sa kukan da ya jawo hankalin su Safinah, sai dai babu wacce ta yi gigin zuwa. Shi ma Abba yana ji amma bai kara juyowa ba. Yana isa daki ya kwanta numfashinsa yana hawa yana sauka da sauri da sauri, ya mike a three seater ya dafe kirjinsa da hannun dama. Kafin zuwan Dr. Saddiq ya galabaita matuka. Ya shigo da sauri ya bude lokar magungunanshi ya diba ya dora masa da gorar ruwan eva mara sanyi. Sannan ya yi masa B.P yasa abin awonshi kan kirjinsa ya girgiza kai cikin damuwa ya ce. “Justice I’m sorry to say, jininka ya kara hawa har ma fiye da yadda ba a so. Nayi-nayi in ji damuwarka a matsayina na likitanka ka ki gaya mini. Idan babu aminci da amana a tsakanin likita da patient dinsa sai mene ne?” Abba ya yi murmushi cikin karfin hali, ba tare da ya kawar da murmushin ba ya ce, “Ka yi hakuri Saddiq, ina iyaka kokarina wajen yakice damuwar nan amma na kasa. Ko na yi kokarin yin hakan bana cin nasara. Sannan baka da maganin da za ka maganta min damuwata, sai dai ka bani maganin da zan ji sauki a cikin gangar jikina, amma ban da a zuciyata”. Dr. Saddiq ya ce, “Yadda muke da maganin kowane ciwo dake cikin gangar jiki, haka muke da maganin kowacce damuwa ta hanyar counselling. Ta hanyar amfani da hankali da tunani wajen magance ita wannan damuwa. Ka yi hakuri Justice ka gaya min damuwarka cikin amana, insha Allah zanyi iya kokarina in ga cewa na taimaka wajen gushewar damuwarka”. Abba ya yi shiru yana dan tunani, ya yin da Dr. Saddiq ya ci gaba da kwantar mai da hankali ta hanyar gaya mishi tausasan kalamai masu sanyaya zuciya, har dai ya amince Dr. Saddiq mai kaunarsa ne, don haka ya yanke shawarar kwaye mishi bargon damuwarshi. “Saddiq matsala ce ta cikin gida, yarinyata Sakinah ke fuskantar matsin rayuwa a cikin gidan nan, saboda mahaifiyarta ba ta nan, mun rabu tun Sakinah na jaririya, don haka Sakinah ba ta san dadin uwarta ba. Na auro uwarta a kasar Libya, na kuma koma na neme ta a adireshinta ban tarar dasu ba, an ce sun dade da barin Tripoli sun koma wani gari daban. Ina so in samawa Sakinah kyakkyawar rayuwa, ban san ya zan yi ba, domin mai dakina ba za ta bari ba”. Dr. Saddiq ya ce, “Wannan har matsala ce da za ka dinga wasa da ranka a kanta Justice? Shawarata a nan shi ne, ka dauki Sakinah ka kaita makarantar kwana”. Abba ya ce, “Saddiq mai dakina ba za ta bari ba”. Dr. Saddiq ya maimaita kalmar, “Mai dakina ba za ta bari ba”. Da Abba yake yawan ambata. Which means yana shayinta, a matsayinsa na Alkalin-alkalai na kasa bakidaya, zai iya zartar da hukunci kan diyarshi ba tare da amincewarta ba. Abba ya ci gaba da cewa, “Ka ga ana zuwa hutu, dole Sakinah za ta zo hutu bayan kuma ni so nake kwata-kwata in nesanta ta da gidan nan. In kaita inda za ta samu hutu dauwamamme ba na wucin gadi ba. Don haka ne na so na sadata da mahaifiyarta, in roketa alfarmar ta rike min ita zuwa sanda za ta isa aure in aurar da ita, in yaso in dauki dawainiyarta. To ka ji yadda al’amarin ya kasance, wato sun bar garin da na sansu a nan sun koma wani garin daban wanda ban sani ba”. Dr. Saddiq ya ce, “To ka yi mata AURE!” Abba ya zaro ido cikin tsorata, kafin yace, “Wanene zai auri wannan ‘yar kankanuwar yarinyar da ko kirgen dangi ba ta fara ba?” Daga can bakin kofa aka ce dasu; “…..ARCH. ABDULHAKEEM RIBADU”. Cikin nutsattsiyar murya irin ta dattijantaka, kuma kamilalliya mai kwantar da hankalin mai sauraro. Abba da Dr. Saddiq suka juya a razane kuma a lokaci daya. Justice Ibrahim Khalil Ribadu ne tsaye a bakin kofar, aminin Abba kuma Alkalin da ke bin bayan M.T Liman a Najeriya gaba daya. Ya karasa shigo da gangar jikinsa gaba daya cikin falon yana murmushi, ya mikawa Dr. Saddiq hannu suka yi musabiha, ya mikawa Abban ma. Ya zauna a kusa da shi yan ninsa da ido cikin yannayi na tausayawa, ya ce, “Yanzu Ba don kunnuwana sun jiye min ba M.T Liman da haka za ka hallaka kanka a banza ka cucemu, ka cuci al’ummar Najeriya, ka cuci kotun koli a kan al’amarin da bai kai ya kawo ba! Duk hirar da kuke ina tsaye ina jinku, al’amari irin wannan M.T Liman ka kasa furta shi gareni sai ka barshi yai ta cinka a zuci? To za ni ce ta tadda muje mu, nima nan zuwa na yi idan kana da diya ka bani in baiwa Abdulhakim, jiya an yi min tozarcin da ban taba zata ba a kan auren Abdulhakim. Abdulhakim ya kai kayan aure da izinin yarinya iyayenta sun ce ta fi karfin ta auri dan Alkali, me na sama ya ci balle ya baiwa na kasa? A takaice dai an dawo mai da gayyar tsiyar shi (kayanshi). Yana nan kwance a daki ciwon so zai illata shi. Na ce da shi ya kwantar da hankalinsa cikin satin nan zan yi mishi aure a inda na ga ya dace, ba diyar masu kwadayi ba”. Abba ya girgiza kai ya ce, “Sai dai ko Safinah, ita ce mai shekaru sha hudu, tana shirin shiga sha biyar. Amma Sakinah shekarunta goma sha biyu, a matsayinka na likita bai kamata ka ba da shawarar ayi mata aure yanzu ba, ya zama child-abuse’ kashinta bai yi kwarin haihuwa ba”. Justice Ribadu ya ce, “Babu tantama Sakinah za’a bawa Abdulhakim. Nana Aisha (R.A) shekarunta tara Sayyadina Abubakar As-Saddik ya wanketa ya baiwa Manzo (S.A.W), ba ta mutu ba, ba ta yi yoyon fitsari ba”. Cike da kokonta Abba ya ce, “Shi Abdulhakim zai amince ya auri Sakinah a wadannan kananan shekarun, alhalin ka ce ga wadda yake so? Hana shi fa aka yi ba wai shi ya ce ba ya so ba”. Justice Ribadu ya ce, “Abdulhakim yaro ne mai biyayya, na tabbata ba zai bani kunya ba, kuma ba zai ki bin umarnina ba”. Dr. Saddiq ya ce, “Maganar Justice gaskiya ce, Sakinah ta yi kankanta da aure, ai ni na dauka budurwa ce”. Ribadu ya ce, “Duk yarinyar da ta yi shekara goma ai sunanta budurwa, ka bawa Sakinah shekaru uku kacal a gidan Abdulhakim za ka sha mamaki. Ka yarda da Allah Dr. Saddiq, ba aikinka na likita ba. Mu musulmi ne da muka yarda Allah ke yin komi, don haka ka yarda da hukuncin Allah mu taru mu taimaki ‘ya’yanmu mu kulla ALHERI! Jikina ya bani insha Allahu alheri muke shirin kullawa”. Abba da Dr. Saddiq suka gyada kai alamu ne na sun yi saranda sun yi amanna. Basu da ta cewa. Justice Ribadu ya nemi alfarmar su bar wannan magana a tsakaninsu, bai yarda mata su ji ba, suka bar asabar mai zuwa matsayin ranar daurin aure. **** MUHARRAM/HIJRIYYA Mutane goma da ke cikin babban falon M.T Liman, ciki har da Baffanshi Malam Sule, dan’uwanshi Tasi’u da likitanshi Dr. Saddiq. A bangaren Justice Ribadu akwai manyan alkalai ‘yan’uwansu guda uku, sai yayyensa maza biyu, suka gabatar da sadaki naira dubu goma kacal da huhunan goro ga Baffa Sule, aka gudanar da daurin auren Abdulhakim Khalil Ribadu da Sakeeinah M.T Liman kamar yadda shari’ah ta tanada. Shaidu sun shaida, iyaye sun karba. Saura da me? Abba ya shigo yana gyaran murya yana cewa, “Ina Lami ne? Ko ba ta gidan ne?” Ina duke a jikin famfo ina wanke kayan fitsarin Nazir na dago na dube shi. Ya bini da wani irin lallausan murmushin kauna, ban yi nawa ba wajen mayar masa da wanda ya fishi. A ransa ya ce, “Wahalarki ta kare Sakinah!”. Tasi’u ya biyo bayanshi rikle da huhun goro. Ta fito daga (store) tana gyara daurin kallabinta, ta fara da yankawa Kawu Tasi’u harara. Ya yi murmushi ya dauke kai kamar bai gani ba. Ta ce, “Lafiya ake yanka min kira kamar ana bina bashi?” Ya sa kai cikin falonta. Tasi’u ya bi bayanshi ba tare da ya ba ta amsa ba. Jikinta ya yi sanyi da ganin goro da alawa, Abba ya karkace ya zaro kudi daga aljihunshi ya mika mata ta ki karba. Ta ce, “Na mene ne?” “To ki karba tukunna sai in miki bayani”. A sanyaye ta karba tana jujjuya su. Ya ce (ba tare da wata fargaba ba) “Sadakin Sakinah ne, na aurar da ita. Gwaggonninta na nan zuwa su sadata da dakin mijinta”. Ta yi watsi da kudin suka tarwatse a tsakiyar dakin, ta mike tsaye tace, “Zancen banza, na ga mai fitar da Sakinah daga gidan nan, ban yarda ba ban amince ba, tunda ba a yi shawara dani ba”. Abba ya rausayar da kai ya mike, Tasi’u ma ya mike ya tura mata huhun goro don ya kara kular da ita, ta kuwa dauka ta watso su waje gabadaya. Abba ya ce, “Ni dai babu ruwana tunda na fita hakkinki na sanar dake. Don haka Sakinah ta fita daga ikonmu ta koma ikon mijinta. Kuma ubansa Alkali ne idan ya maka ki a kotu babu ruwana”. [9/14, 9:59 PM] Asmau: Na sanya kafa zan shiga motar kamar an ce dani daga kanki, na hango Abbanmu a bakin tagar falonshi yana kallona. Hawaye fal idanunsa. Na daga hannu na yi mishi bye-bye shi ma ya yi mini. Wasu hawaye suka shimfido a kundukukina, hakika ina son Abbana son da bana yiwa kowa a duniya!!! **** Kugin karshe da motar ta yi a harabar gidan Justice Khalil Ribadu ne a unguwar Maitama, Hajiya Laila da kanta ta fito ta kamani zuwa cikin gidan a hamshakin falonta. Bayan an gaggaisa anyi abin nan da ake kira amana, sannan suka tafi suka barni tare da Inna Ladiyo. Hajiya Laila da kanta ta rakamu gidan da zamu zauna wanda ke opposite din su. Har bakin gadona ta zaunar dani, sannan ta budewa Inna Ladiyo wani daki da ke can gefe ta ce ta zauna a can. Ta duba ko ina ko da abin da yake bukatar gyara ta ga babu, don haka ta yi mana sallama ta koma nata gidan. Sannan ta turo mai aikinta da abinci kala-kala na alfarma ta kawo mana. Inna Ladiyo na zaune a gefena ta soma bubbude kulolin abincin tana diba a faranti tana cewa, “Gara ma ki bar kukan nan, tunda ba kabari aka kawoki ba dakin aure ne, dakin kowacce mace”. Ta tura min farantin gabana, “Ajiye mayafin nan maza-maza ki cinye ki bani farantin”. Ganin ba alamun wasa a tare da ita na karbi farantin na soma ci, amma hawayena basu bar ambaliya ba. Ita ma ta zuba nata tana ci tana cewa, “Haba! Yarinya sai kukan tsiya, maimakon ki yi murna ki gode Allah, dubi irin dukiyar da ubanki ya shirya miki a gida. Ga surukar kirki Allah ya baki, in ba ki yi dariya ba to ba za ki yi kuka ba, kika kara yi min kukan nan bige miki baki zan yi, shashasha kawai”. Ta gama cin abincinta ta goge baki, ta kwashe kayan ta yi kicin dasu. Ta dawo ta dau filo ta jefa a kasa ta yi kwanciyarta, ba ta dade ba ta soma jan minshari. Na yi zaune a gefen gado, tunanin duniya ya ishe ni, duk da nake yarinya karama ban taba jin wani aure irin nawa ba. Ban san angon ba, shi ma bai sanni ba. Bai san za’ayi ba nima ban san za’ayi ba sai a labari. Har dare ya mika na kasa barci, ga minsharin Inna Ladiyo dake bani tsoro. Babu motsin wani mahaluki cikin gidan, sai haushin karnuka a makota. Na kankame jikina wuri daya na ci gaba da kuka a hankali ina roka wa kaina afuwa cikin ita wannan sabuwar rayuwar. **** Dogo ne baki, amma bakinsa mai kyau ne, saboda baki ne da ya hadu ya cakude da gogayya cikin zuzzurfan ilimin boko. Ma’abocin fadin kirji da alamun karfi ta ko’ina. Kyakkyawa matuka, abin alfaharin kowacce mace, har maza ‘yan’uwansa ba za su bar dakacen ina ma a ce su ne shi ba. A kan ce wai duk mutum tara yake bai cika goma ba, to amma ABDUL-HAKIM KHALIL RIBADU, ya kai 95% ma, a dabi’a, sura da halayya. Tunda iyakar kushen mai kushe, da iyakacin kwakkwafin mai kurullah, ba zai ce ga ta inda Allah ya rage shi ba. Duk wani dake tare da shi ya yi shaida a kan kyawawan halayensa na hakuri, rikon addini, juriya da kaifin kwakwalwa. Wata irin kwakwalwa kamar computer, wadda in ta zana maka gida, makaranta, titi, asibiti ko ma’aikata za ka yi tsammanin baturen Ingila ne ya zana su. Da daya kwal! Kuma jallin jal ga Alkali Khalil Ribadu da Hajiya Laila. Bayan shi kuma ba a haifi wani ko wata ba har inda yau ke motsi. Don haka shi din dan gata ne na karshe. Bayan karatu mai suna karatu a kan Quantity Survey daga jami’ar Ahmadu Bello. A halin yanzu ma’aikaci ne na ‘Julius Berger’ reshen jihar Lagos. Dan kimanin shekaru talatin da biyu. Abdulhakim ya tashi tare da Abdallah, dan Yayan mahaifin shi, duk wata dabdalar kuruciya tare suka yi ta, a cikin gida daya daki daya, ta yadda in baka san tarihin gidansu ba da wuya ka san cewa Abdallah ba Yayan shi bane na ciki daya ba. Domin kamar su daya, saidai hali kowa nashi daban. Abdallah mai harka ne sosai da faram faram da jama’a (jovial), ga son mata da son raha, inda suka sha bambam da Abdulhakim kenan Abdallah zai bai wa Abdulhakim shekaru biyu, shi kuma ma’aikacin DSTV ne a Kaduna, don haka duk karshen sati suna tare a gida Abuja, sai yammacin lahadi suke komawa garuruwansu. Saukar Abdulhakim ke nan daga jirgi, ya hada layi ya kira Abdallah ya sanar da shi isowar shi ya zo ya dauke shi. Cikin abin da bai haura mintuna sittiin ba, Abdallah ya iso airport din Abuja, suka hade a reception ya karbi jakar hannunshi bayan sun yiwa juna murmushi, suka doshi inda Abdallah ya yi parking. Sai dai cikin ransa yana matukar tausayawa dan’uwanshi halin da ya samu kanshi ciki, gaba daya ya rame ya rasa kuzari kamar ba Abdulhakim ma’abocin haba-haba da jama’a ba, fara’a da sanyin zuciya. Ya tabbata abin da Daddy ya yi bai kyauta mishi ba, don shi din shaida ne a kan son da yake yiwa Farida. Yiwa Abdulhakim AUREN HUCE HAUSHI ba dabara ba ce so-karbau (inji malaman Hausa) da za ta gusar mishi da azabar zuciya da soyayyar da yake ciki. Suna tafe babu mai cewa uffan, don Abdallah ya kame bakinsa, bai gaya mishi auren da Daddy yai mishi ba da sanin shi ba. Shi kuma dama ya dade da zama silent tun daga lokacin da ya rasa abin da yake so a rayuwarshi. Suna isowa gida Daddy ma na sanyo hancin motarshi cikin gate din gidan, don haka duk suka dakata har ya karaso. Abdallah ya bude mishi owner side tare da karbar brief case din shi, ya dafa kanshi ya ce, “Har kun iso?” Abdallah ya ce, “Shi ne dai sai yanzu ya iso, amma ni tun goma na safe ina cikin Abuja”. Abdulhakim ya karaso shi ma yana kwasar gaisuwa, suka rankaya falonshi dukkanninsu. Hajiya Laila ta shigo ta sha kwalliya cikin shadda da zinare, sai walwali take. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci tsantsar farin cikin da take ciki. Kafin dan lokaci ta cika dining da abinci, har da ita aka hau tebir. Tana kallon Abdulhakim wanda ke ta zuba ruwa a kofi yana daddaka, amma ko loma daya bai yi ba. Ta cika filet da abinci ta tura mishi, “Cinye maza ka bani kwanon”. Ya girgiza kai, “I’m o.k Hajiyata, ban jima da cin abinci cikin jirgi ba”. Ba ta ja da nisa ba sai ta kyale shi, amma kallo daya za ka yi mata ka tabbatar ta damu da yanayin da yaron ke ciki. Sai da suka kammala Daddy ya dube shi da murmushi ya ce, “Sai kuka ji kirana babu zaton ku ko?” Abdallah ya ce, “Ko baka yi kira ba Daddy dama zamu zo ne”. Ya ce, “In ce ko ka yi mishi bayanin abin ALHERIN da na yi mishi?” Abdallah ya girgiza kai, “A’a, ai nima zuwana ke nan Hajiya take gaya mini”. Ya daga fararen idanunshi yana kallon su da alamar tambaya a kan kyakkyawar fuskarsa, Abdallah ya juyar da kai, don haka ya mai da kallon shi ga Daddy. Daddyn ya yi murmushi ya ce, “Abdulhakim!” Ya amsa “Na’am”. Ya sake cewa, “Abdulhakim!!” Shi ma ya amsa. Ya ce, “Ka bani hankalinka magana ce zamu yi ba ta wasa ba”. Ya ce, “Ina jinka Daddy”. Ya ce, “Yauwa. Na tura a nema maka aure kamar yadda kake so, ka kuma neme ni da in yi, iyayen yarinya sun wulaqanta Baffana da ‘yan’uwana, sun yanka mana sadaki na rashin hankali da rashin neman albarka, tare da wasu manyan bidi’o’i na neman magana da son kure mutum, wanda ba sai an fito fili an nuna min cewa raina ni aka yi ba, da na ce a rage ya yi yawa aka maido min da kayana duka. Don haka na karba maka aure na mutunci, diyar aminina M.T Liman wanda ba sai na tsaya ina yi maka bayaninsa da matsayinsa wajena ba. Sai dai Sakinah yarinya ce karama da nake fatan ka yi mata riko na kanwarka kuma matarka. Na san na isa da kai, shi yasa na yi hakan ba tare da shawara da kai ba. Na san har kullum kai mai biyayya ne a kan umarnina. Na san ba za ka watsa min kasa a ido ba, ba za ka ki rike diyar M.T Liman da mutunci ba ko da ace bana raye”. Wata irin zufa ce ta ketowa Abdulhakim daga goshi har zuwa yatsun kafa. Ya dago a firgice ya dubi mahaifinsa, hankalinsa a kwance yake maganarsa, idanunsa suka kankance cikin tashin hankali. Cikin firgici da sarqewar murya ya ce, “Amma.......amma Daddy.....ai...”. Ya kasa karasawa don harshensa ya kasa daidaituwa. Ya ce, “Ai me? Fadi ra’ayinka na baka dama”. Ya ce, “..Ai an daina irin wannan auren yanzu, Daddy ban santa ba, ita ma ba ta sanni ba. Baka sani ba ko da wanda take so, nima da wadda nake so. Duk da cewa na hakura da Farida amma Daddy i’m sorry ban san ya zan yi da wannan auren da ka karba mini ba”. Daddy da Hajiya suka yi murmushi, Hajiya ta ce, “Ka kwantar da hankalinka Abdulhakim, Sakinah yarinya ce karama, ba ta san komai ba sai abin da ka sanar da ita. Ka zauna lafiya da matarka, yarinya ce sai girman kashi da manyan barage. Abin da nake so ka yadda da shi shine, Daddynka ba zai dauko maka mummunan abu ko abin da ya san ba zai amfane ka ba”. Sai juya kai ya yi kamar ya yi ihu, amma babu dama, ga yadda ya gama fahimta Daddy bazai taba sauraron uzurinsa ba, ko wace ce wannan yarinya ta ruguza mishi tsarin rayuwar da ya riga ya tsara ma kanshi. Ga shi suna ta ambaton wai yarinya ce, to yarinya kamar ya ya? Amsar da bai samu ba ke nan har suka fito daga falon Daddyn shi da Abdallah. Daddy da Hajiya na ta sanya masu albarka. Abdallah sarkin zolaya suna shiga daki ya juyo ya kama hannunshi ya ce, “Oya ango! Muje na rakaka dakin amarya”. Wata muguwar harara ya zabga mishi, ya ja bakinsa ya bame da makulli yana dariya kasa-kasa. Ya zauna gefen gadonshi ya kama kai, ya dafe da dukkan hannuwanshi. Idanunshi sun kada sun yi jawur, jijiyon kanshi duk sun fito rada-rada. Wannan shi ne alamun bacin ran Abdulhakim, amma ba kuka ba. Cikin ranshi yana cewa, “Gidan da na kwashe shekaru uku ina zanensa, na kwashe shekaru uku ina gininshi, shi aka sa matar da ban ce ina so ba! Ban san kalarta ba! Ban taba ganin ta ba!. Har zuwa wayewar gari barci bai ga idon Abdulhakim ba, tun Abdallah yana rarrashi, yana magiya a kan suje ya raka shi wajen amaryarshi, har ya koma ya mishi barazanar to zai gayawa Daddy. Ya nuna mishi hanya ya ce, “Have your way out.......Allah ya baka nasara”. Abdallah Ya ce, “To me kake nufi? Ka bar ‘yar mutane ta kwana ita kadai? Wallahi ka ji tsoron Allah”. Ya ce, “Ko me ya same ta ita ta jiyo, tunda ta ce ta ji ta gani, auren mijin da ba ta san ko waye ba?” Washegari ya tattara ya koma bakin aikinsa, ko Daddyn bai sani ba. Sai sallahu ya bar mishi a rubuce cewa ya koma Lagos ana kiransa a office da gaggawa. Daddyn bai kawo komi a ranshi ba, don a zatonshi Abdulhakim ya hakura ya karbi auren da ya yi mishi da hannu bibbiyu. *** Tashinmu ke nan da safe bayan komawa barcin asubahi, aka danna kararrawa misalin karfe takwas na safe. Inna Ladiyo na ta barci, don haka na nufi kofar na bude. Na zo na tsugunna har kasa ina gaishe su. Hajiya da Daddy ne da kansu, ta dora hannunta a kaina ta ce, “Kin kwana lafiya Sakinah? Yaya bakunta? Ina Innar?” Ladiyo ta fito tana cewa, “Gani nan barci ne ya sace ni daga lazumi”. Suka gaisa sosai, Daddy ya tambayeni ko inada matsala nace babu sannan suka tafi, mai aikin Hajiya ta kawo mana karin kumallo. Haka muka yi zamanmu lafiya ni da Inna Ladiyo, mu ci mai kyau mu sha mai kyau, mu zauna a mai kyau, mu daura mai kyau, ba abin da ya dame mu.Har satin da Abba ya debar ma Inna Ladiyo ya wuce. Hajiya Laila da kanta ta roki Abbana da ya kyale Inna Ladiyo mu zauna tare in har ba wani uzuri ne a kanta ba. Tunda Abdulhakim ba mazauni bane, sai karshen sati yake zuwa gida. Karshen wannan satin ko garin bai zo ba, ya sanar da Daddy ba zai samu damar zuwa wannan satin ba saboda an tura shi (surveying) ginin wani titi da suke yi a Akwa-Ibom. Alhalin a zahiri ba gaskiya bane, kawai yana gujewa Sakinar da har yau bai san wace ce ba, ba kuma ya bukatar ya sani. Nutsuwar zuciya da sauyin muhalli dana samu ya haifar min da murmurewa cikin ‘yan kwanaki qalilan. Babu aikin Mami na sassafe, babu fargabar jibgarta da rankwashinta. Ban damu ba wai don har yau ban ga angon ba, ni a wajena ma gara hakan. Sai dai makaranta da bana zuwa shi ne abin da ke damuna. Zuwa lokacin na saba da Daddy saboda yadda yake jana a jiki, tare da nuna kulawarsa gareni. Duk bayan kwana biyu ko uku yana shigowa ya ga lafiyata mu gaisa. Don haka yau litinin da ya shigo cikin shirin ofis da hularshi ta Alkalai a kansa, bayan mun gaisa sai na ja bakina na yi shiru. Ya ce, “Ya ya dai Sakinah? Na ga bakin yana ta motsi”. Na sunkuyar da kai na ce, “Daddy ina so in koma makaranta”. Ya ce, “Wacce kike zuwa?” Na ce, “Al-Amin International”. Ya ce, “Bari zan yi waya da Abdulhakim in ba zai samu zuwa ba wannan satin sai Abdallah ya mai da ke”. Na ce, “Daddy na gode”. Ya yi murmushi, “Babu godiya tsakaninmu Sakina, ni Babanki ne kin ji?” Na gyada kai. Daddy yana isa ofis ya kira Abdulhakim a waya, ya yi qasa da murya yana gayar da Daddyn. Ya amsa, ya ce, “Ya ya Abdulhakim za ka samu zuwa gida this week?” Don kada Daddyn ya dago shi a kan kin zuwa gida da yake yi ya ce, “Zan zo insha Allahu”. Ya ce, “To shi ke nan Allah ya yi maka albarka”. Karshen satin ya tattaro ya nufo gida Abuja. Wannan satin ya riga Abdallah sauka, wanda bai iso ba sai yamma lis. Tunda ya zo yana tare da Hajiya suna zancen tsarin filinta da za a soma gini, ta bar zancen gini ta dube shi sosai ta ce. “Abdulhakim”. Ya dago ido ya dube ta ba tare da ya amsa ba. Ta ce, “Fisabilillahi me kake nufi da auren ka? Ina lura da kai har yau baka je inda matarka take ba. Ba fa kare aka ajiye maka ba dan mutum ne mai kima da daraja. Idan har kana so mu shirya, to a yau nake so ka tattara komi naka ka koma gidanka, kada ka bari Daddy ya san halin da kake ciki ranshi ba zai yi dadi ba”. Haka ya taso ya fito duk jikinshi babu kwari. Ba ranshi ne ya baci ba, yarinyar ce kawai ba ya so. A ganinsa he is old enough da ya yi ma kanshi zabin abokiyar rayuwa tunda Daddy bai fi shi idon ganin mata ba. Ba kowacce mace ce ke da abubuwan da yake so a diya mace ba sai FARIDA. Ya soma tattare duk wani abu da ya san mallakinshi ne daga dakinsu da Abdallah yana sanyawa a katuwar jaka, ya kammala ya kira Sadi mai wankin Hajiya ya soma diba yana kaiwa gidanshi. Bayan ya ba shi mukullin dakin da zai sanya su. Ladiyo tana dakin da ya zama nata tana barci, ni kadai ce a falo kishingide a three seater, cikin doguwar riga kirar Bahrain baqa wuluk. Da ‘remote’ a hannuna ina kallon yadda sojojin Amurka ke ragargaza ‘yan’uwa musulmin Palastine da tankokin yaki. Hawaye shabe-shabe a idanuna don tausayi. Wata sassanyar murya mara amo, wadda ke dauke da rashin kuzari ta yi sallama a falon, mamallakin gidan ya bayyana zahiri yau a gabana. Ba sai an gaya min ba, kallo daya na yi mishi na gane shi ne dan Alkali Khalil Ribadu, kuma mijina, saboda tsabar kamannin su. Abdulhakim ya dade a tsaye hannunshi zube cikin aljihun sassalkar farar shaddar ‘getzner’da yake sanye da ita dinkin Mohammed, yana nazarin yarinyar da aka kira, SAKINAH, kuma MATARSHI. Kallo na rahama da salama, wanda bai san yaushe kwayar idanunshi ta rikide ta ke yi ba. A zahiri kuka take, tana kallon talabijin, amma bai taba ganin wadda hawaye ya yiwa kyau irin wannan yarinya ba. Duk wani kulli, fushi, bacin rai da ke cikin zuciyarshi sai ya ji yana bacewa. Ya ci gaba da kallon ta, kallon rahama, cikin dakikan da basu gaza biyar ba. Kafin ya yiwa kanshi mazauni a daya daga cikin kujerun da suka yiwa kayataccen falon qawanya. Da bayan hannu nake share hawayen kamin in sauko da gwiwoyina kasa ina gaishe shi, alama ya yi min da in koma in zana bisa kujera. Allah mai juya al’amura, a take Abdulhakim ya ji nan duniya ba abin da yake so irin Sakinah. “Ke kadai ce a gidan?” Ya tambaya cikin kallo na. Girgiza mishi kai na yi alamar “A’a, ba ni kadai ba ce”. “Kukan me kike yi?” Ya sake tambaya. Da dan yatsana na nuna mishi talabijin, “Suna ta harbin musulmi ne”. Ya kai ganin shi ga tashar CNN ya yi murmushi, “Ni a ganina addu’a ya kamata ki tayasu ba kuka ba”. Na sake share hawayen ba tare da na yi magana ba. “Kin sanni?” Ya tambayeni yana nuna kanshi da dan alinshi. Gyada mishi kai na yi alamar, “Eh, na sanshi”. Ya yi murmushi ya ce, “Kin sanni ke nan Sakinah?” Na ce, “Eh”. “Ya ya sunana?” Wannan karon girgiza kai na yi, wato ban sani ba. “Ashe mace tana manta sunan mijinta?” Ya tambaya with a low tune. “Ba mantawa na yi ba, ban sani bane”. Ya yi murmushi, “To daga yau in kin ganni na zo gidanki, sunana MIJIN SAKINAH”. Da sauri na dago na dube shi, “Mijin Sakinah?” Na tambaye shi cikin sigar tambaya. “Eh, mijin Sakinah”. Ya maimaita cikin tabbatarwa, dauke da siririn murmushi bisa siraran lebbansa. Nima sai na yi murmushi na ce, “Wannan ba suna bane”. “In ba suna bane mene ne?” “Inkiya ce”. “Ashe kina da wayo? Su Hajiya suke cewa Sakinah yarinya ce?’ Murmushi na yi, “Ni ba yarinya ba ce, ina da kannena ma Nadiya, Ilyas, Nazir da Abba, duk na girme su”. Ya yi dariya wadda ta fiddo wasu fararen jerarrun hakora kamar kankara, ya ce, “Ina ma nine ke Sakinah, ni bani da kanne”. Na ce, “Kai kadai ne a gidanku?” “Ni kadai ne Sakinah”. Na ce, “To ba gani ba an kawoni gidanku sai in zame maka kanwa”. Ya dara sosai, kafin ya ce, “I like you girl…., zo mu kulla abota”. Na rufe fuskata da tafukana ganin ya miko min hannunshi. Wanda ke daure da wani irin sassalqan agogo samfurin ‘swatch-blustery’. Ganin na rufe ido naki mika mishi hannun. Sai ya taso ya iso har gabana, ya kai hannunshi ya bude tafukan da na rufe fuska dasu. Na kuwa kyalkyale da dariya. “Kin ce fa ni Yayanki ne don me za ki ji kunyata?” Dariya ta kamani, na cigaba da kyalkyalawa sosai, bai katseni ba sai da na gama. Yana murmushi ya ce, “Wani ya taba gaya miki kina da kyau Sakinah?’ Kamin ince komi ya miko min dan yatsanshi na mika nawa, muka sarqe su, ya ce, “Friends…?” Na gyada kai cikin murmushi. Daidai lokacin da Inna Ladiyo ta fito daga daki ta ga mutum durqushe gaban Sakinarta ya kama hannuwanta ya cukuikuiye, ta saki salati mai razanarwa ta ce, “Wane ne kai?” Mikewa ya yi yana dariya ya russuna yana gaishe ta, amma ba ta amsa ba tambayar shi ta sake yi, “Wane ne na ce?” Ya sunkuyar da kai kafin a hankali ya ce, “Abdulhakim”. Ta ce, “Ba sunanka na tambaya ba, cewa na yi wane ne kai? Ko kuma don kana Abdulhakim sai ka shigo gidan matar aure ka cacumi hannayenta?” Dariya ya sake yi sosai kafin ya yi magana nayi hanzarin cewa. “Inna shi ne MIJIN-SAKINAH”. Ya kama baki yana mamaki, ya ce da Inna, “To kin ji Sakinah ta hutassheni”. Kunya ta kama Inna ta juya tana cewa, “Au maigidan ne? Ai ni fushi nake da kai tunda na zo gidan nan yau sati hudu baka kawo min kudin cefane ba”. Ya ce, “Ki yi min uzuri Inna, bana nan ne ina wajen aiki, amma tunda gani na dawo cefane sai kin ce ya ishe ki”. Ta koma daki ba ta kara magana ba. Aka danna kararrawa, ya isa ga kofar ya bude. Hajiya Laila da Abdallah suka bayyana a falon. Ta kalli kowannenmu, sannan ta yi murmushi cikin jin dadin ganin fuskar Abdulhakim da walwala. Ta ce, “Sakinah yau ga maigida ya zo, babu sauran damuwa ko?” Na yi murmushi ban yi magana ba. Shi kuma Abdallah sai ya tintsire da dariya ganin ‘yar kwailar matar Abdulhakim. Don haka Hajiya tana ba da baya Abdulhakim ya harare shi, “Uban me kake yiwa dariya?” Bai ba shi amsa ba ya ce, “Sakinah baki sanni ba ko?” Na yi murmushi. Ya ce, “Laifin angon ki ne da bai yi introducing dina (gabatar dani) ba. I’m Abdallah Ribadu”. Na ce, “Sannu da zuwa Abdallah”. Ya ce, “Kema sannunki da zuwa cikin family dinmu. Ga nan Abdulhakim shi ne angonki, yana ba da hakurin rashin ganinshi tun lokacin da aka kawo ki, wannan ya faru ne a dalilin ayyuka da suka sha gabansa. Abdulhakim mai kirki ne Sakinah, ki saki jikinki cikin gidan auren ki kike. Ai kina son shi ko?” Ya fadi cikin daga gira. Na rufe fuska da hular da ke jikin rigata, kafin in falfala da gudu in yi daki. Ina jiyo dariyar su da hirarrakin su, har aka yi kiran sallar magariba suka fita. Karfe tara na dare na fito falo saboda in ci gaba da kallon yakin Larabawa da nake son gani. Mijin-Sakinah ne a kan dining yana cin abinci. Ya ce, “Kawo min ruwa Sakinah”. Na nufi kicin inda firij yake, Uche (kukun gidan) ne yake wanke kwanukan da ya yi amfani dasu a sink, ya russuna yana gaisheni kamar kullum muka hadu a kicin din. Na dauko robar ruwan FARO da lemun Squashda kofi na dora a karamin faranti, na kawowa Mijin-Sakinah. Murmushi ya yi ya nuna min kujerar kusa da shi ya ce in zauna. Na zauna ina cewa, “Ina Abdallah?” Ya yi murmushi ya ce, “Shi gwauro ne, yana can dakin gwauraye yana cin nasa abincin” [9/14, 9:59 PM] Asmau: Abin ya baiwa Kawu Tasi’u dariya, har sai da ya murmusa a mamakance da abin da M.T ya yi mata a yau, ta figi waya ta yi kiran aminiyarta Hajiya Laila. A tare dukkansu suka hada baki suka ce, “Kin ji abin da M.T ya yi min ko?” Amma ita Lailar cewa ta yi, “Kin ji abin da Ribadu ya yi min ko?” Mami ta ce, “Wai ya aurar da Sakinah”. Hajiya Laila ta ce, “To ai nima haka yake gaya min yanzu, wai ya karbawa Abdulhakim aure, yaron da ke cikin halin jinyar zuciyarshi a kan rasa yarinyar da yake so?” Mami cikin tangardar harshe da matsanancin faduwar gaba ta ce, “To ko dai Sakinah ce ya aura mishi?” Hajiya Laila ta yi wata sassanyar ajiyar zuciya a ranta ta ce, “Allah ya sa!”. Amma a fili sai ta ce, “To wa ya sani ne? Ni aikin Na-dutse ban ga yana ci kamar na dan Ikko ba. Kwata-kwata na kasa gane kan Ribadu a kwanakinnan. Idan ya yi kamar ya zo hannu sai kuma ya baude ya dinga yi min abubuwa na gadara. Yanzu saboda Allah ya dace ya yiwa dana aure ba tare da sanina da yardata ba? Idan ke bake kika haifi Sakinah ba ai Abdul ni na haife shi”. Mami ta ce, “Na shiga uku ni Lami! Idan Abdulhakim ne mijin Sakinah na fadi ba nauyi, na tabbata daga Safinah har Nadiya babu wadda za ta yi sa’ar da ta yi. Wato Sai da ya daddage ya zabo miji na nunawa sa’a, ya tsallake ‘ya’yana ya ba ta.....”. Ta rushe da kuka. Hajiya Laila wadda ke ta hamdala a zuciyarta ta ce, “A’a, Lami kar ki kuka, babu abin kuka a nan”. “Ya ya ba zan yi kuka ba? Abdulhakim mijin Sakina........duk mugun burin da naci a kan yarinyar nan ya ruguza min shi, ya shammaceni, ya yi min bazata. Ni ina tutiyar na mallake shi, ashe har yanzu gangar jikinsa na mallaka zuciyarsa na kan Sakieenah da ‘yarta. Ki taimake ni Hajiya Laila kada ki bari auren nan ya je ko ina”. Hajiya Laila ta ce a ranta, me zai kaini yin surukuta da ke Da na ya zama M.T Liman? A fili kuma tace. “A wane dalili? Kina tunanin idan na raba auren zai yiwu ya auri Safinah ne?” Ta ce, “Na san ba zai yiwu ba, amma akalla duk sun rasa”. Hajiya Laila ta yi murmushi ta ce, “In gaya miki gaskiya? Irin auren da nake so Abdulhakim ya yi ke nan, ba wannan auren da ya je nema aka hana shi ba. Bana son Abdul da auren macen da yake so, don ni hoto zan zama, in zama kura da shan bugu gardi da amshe kudi. Don haka na karbi Sakinah a surukata, ba ya sonta kuma ita ma ba ta san komi ba, sai abinda muka koyar da ita, don haka ki sanya ranki a inuwa. Idan har Sakina ce surukata na karbe ta da hannu bibbiyu, ga kyau ga kyan hali. Ga shi ta fito tsatson mutumin kwarai irin M.T Liman. Ni kuwa Laila me zan nema a suruka tagari banda wannan?” Mami ta saki kunnuwa tana sauraron aminiyarta cike da mamaki, ta ce, “Haka za ki min Hajiya Lailah?” Ta ce, “To ya kike so ayi? Don Sakinah tana ‘yar kishiyarki cewa nake ita ma ‘yar M.T Liman ce?” Mami ta kara rikicewa da mamakin Hajiya Laila, ta kashe wayarta tana jujjuyata cike da zargin ko karya ta gaya mata? Ko kuwa mafarki take? Laila ta fi kowa sanin yadda ba ta kaunar Sakinah, amma yau ta zabi su bata a kan Sakinah. Karfe biyar na yamma Kubra, Dije da Zainaba kannen Abba da Suwaiba ‘yar Baffa Sule, da Innarta Ladiyo suka iso Abuja a 506 din Abba da ya tura a debosu daga ‘Yan Leman. Abba ya ce ba ya son wani bidi’a, su gyara ni washegari su rakani dakin aurena, kada su damu da Mami da duk abin da zatayi bata da cikakken hankali. Ban san abin da ke faruwa ba, ina bayan gida ina wankin kayan Mami. Nadiya ta lallabo ta rufe min idanu da hannunta ta baya, na soma kici-kicin ture hannunta ta rankwafa dai-dai kunnena ta rada min; “Albishirinki, wai Abba ya yi miki aure, wai yau za a kai ki gidanki, ga ‘yan ‘Yan Leman can ma sun zo tafiya dake”. Na dube ta galala! Ban damu da abin da ta ce ba na ci gaba da wankina. Ta ce, “Wallahi Sakinah da gaske nake, har goro da alawa mun ci”. Ta waiwaya ta tabbatar ba mai kallonmu, ta kara kaskantar da murya ta ce, “Har da kudin sadakin mun gani, Mami ta watsar dasu a falo”. Ba ta rufe baki ba Ladiyo da Zainaba suka shigo daga kofar cikin gida, ta kwasa da gudu ta yi ciki. Na cika da mamakin ganin ‘yan ‘Yan Leman yau a gidanmu, kada dai zancen Nadiya gaskiya ne??? Ba su ce min komi ba, Ladiyo ta kama jikakken hannuna suka nufi sashen baki dani, ta hada ruwan dumi cikin kwami ta yi min wanka irin wanda ba a taba yi min ba. Ta tsefe birkitaccen kitson da ke kaina ta wanke min da ruwan kumfar wanke gashi na (Fa). Ladiyo na cewa, “Mu a wurin mu ai har haihuwa Sakinah za ta iya yi tunda mai manyan barage ce, a haka wani sai ya ce ta yi shekaru sha biyar”. Zainaba ta ce, “Ni ba ina kamarta aka yi min auren ba? Me ya cini? In banda zamani da bature da ya lalata duniya ai haka ya kamata al’ummar musulmi su dinga yi don koyi da Manzo (S.A.W); $$# da zinace-zinace sun ragu, alfasha ta ragu, Allah ya yiwa Yaya Muntari arzikin duniya da lahira, ya dubi niyyarshi ta alheri ya shirya mishi zuri’arsa ya zaunar da Sakinah a dakin mijinta har abadan-abadan”. Sai na fashe da kuka da dai na tabbatar zancen Nadiya ya tabbata gaskiya. Gidanmu za a bari dani a kaini wani gida da ban sani ba. Duk da izayar da Mami take min daidai da rana daya ban taba tunanin in bar gidanmu ba, wai saboda wahala. Ni ina son ‘yan’uwana kamar yadda suke sona, bana fatan abin da zai rabamu. Ladiyo ta ce, “Daina Kuka Sakinah, aure dole ne a kan duk wata diya mace. Sai in lokacin bai zo ba, idan ya zo kamar habo yake, dole sai ya zubo, wato dole sai anyi ana so ko ba’a so. Don haka ki daina kuka, ki yi addu’ar Allah ya baki aljannar da ake samu a dalilin aure”. Kubra na tsane min dimbin gashin kaina da tawul ta ce, “Wannan ango ya more, gashi kamar a India, kyau kamar a birnin Omani. Allah ya sa ki yi hali irin na mahaifiyarki ba halin marikiyarki ba”. Suka sanyani a tsakiya, Yaya Dije ta sa kakkaifar kibiya tana yarfa min kananan kitso suna ta yi min fada, duk a kan zaman aure, wanda ban taba ji ba, ban taba kawowa wai nan kusa za a yi min ba. Kallon komai da jin komai nake kamar almara. Karfe shida daidai motocin daukar amarya suka iso. Wata daga cikin kawayen mahaifiyar ango ta kawo wasu kaya cikin (kit), ta ce su za a sanyawa amarya, lefe sai daga baya don ba lokaci basu kintsa da wuri ba”. Zainaba ta ce, “Babu komai”. Ta karba ta bude, wani lallausar farin cotton lace ne da yarfin ruwan kasar furanni da kananan (stones), a qalla kudin shi ya kai naira dubu saba’in, a dinke, dinki na alfarma da haiba. Sai wata laffaya ita ma ruwan kasa mai laushi da mannewa a fatar jiki. Yaya Zainaba ta sanya min da saitin Dubai da warawarai masu nauyi mahadin set din guda hudu a hannuna na dama. Tuni na fito a Sakinah ta, na yi kyan da ban taba yi ba. Ni kaina ban san ina da kyau ba sai yau. Duk abin nan da ake Mami ba ta fito ba tana daki tana fama da kuncin rai, ta nunawa duniya adawarta dani da bakin cikinta a fili, sannan ga bakin cikin ‘yan uwan Abba sun zo sun cika mata gida. Safinah ko ta yi nan ta yi can tana kara kawo kayan da za a yi min kwalliya. Bayan an gama shirya ni an fesheni da turaren (Avon) aka kaini falon Abbana, ya ce da su Zainaba su jira a waje yana son yin magana dani ni kadai. Abba ya dube ni ina ta kuka cikin yadin laffaya, kuka nake haikan kamar raina zai fita. Abba bai yi magana ba har sai da shesshekar kukan ta tsaya mini na yi shiru. Ya sauko daga kujerar shi ya dawo gabana ya zauna a kan gwiwoyinsa ya ce. “…..Sakinah ‘yar Sakina-ta, jikar Liman Tukur!” Na yi saurin dagowa na dubi Abba domin ji na yi yana magana da wata murya mai wani irin amo tamkar ba tashi ba. Sai na ga hawaye suna gudu a kundukukin shi, yana kuma murmushi duka a lokaci daya. Ya ce, “Yau ce rana ta biyu da zan kara dandanar wani bakin ciki da farin ciki duka a lokaci daya. Bakin cikina shi ne, zan rabu da Sakinah…. mai tuna min da Sakinah ta. A kan dole ba don na so ba, ba don ta kai munzali ba sai don hankalina da nata ya kwanta. Farin cikina shi ne, ban kai Sakinah mugun hannu ba ko hannun da za ta tozarta ba, na kaita hannun da nake da yakinin cewa da nawa da shi duk daya ne. Ko bayan rai na. Sakinah ki yi hakuri na yi gaggawar yi miki aure a lokacin da baki isa ba. Ban yi hakan don cutar dake ba, sai don hankalina da naki ya kwanta. Don kullum zan fita daga gidan nan cikin fargabar halin da kike ciki nake, wanda har hakan ya shafi lafiyata. Sakina na yi duk iya kokarin da zan iya in mai da ke ga Mamanki in ba ta amanarki, amma hakan ya ci tura, don haka ne a karshe likitana ya bani shawarar in yi miki aure don hankalina ya kwanta naki ya kwanta, wanda nake fatan ni da ke mu ci ribarsa a duniya da lahira. Na aurar da ke ga dan aminina Alkali Khaleel Ribadu. Ga nan sadakin ki”. Ya debo kudin da Tasi’u ya tattaro a falon Mami ya danqa min cikin hannuna, ya kara da cewa. “Ki yi abin da kike so dasu don hakkinki ne, ki zamo mace ta gari kamar mahaifiyarki Sakina. Halayenki na kwarai da na sanki dasu su zamo jagoranki a gidan aure. Allah ya yi miki albarka Sakinah, Sakinah Allah ya yi miki albarka. Na yafe miki duniya da lahira, nima ki yafe mini rayuwar kuncin da kika rayu cikinta a gidana na kasa daukar wani mataki a kai. Allah kadai ya san cikin halin da nake rayuwa, ina neman waraka daga gareshi, ki dinga sanya ni cikin addu’arki a duk lokacin da kika yi sallah, kin ji Sakinah?” Na gyada kai, na fyace majina da gefen laffayar. Ya ce, “To tashi ku je, ina kara cewa ALLAH YA YI MIKI ALBARKA!” Yasa murya ya ce, “Zainaba!” Ta shigo da sauri. Ya ce, “To ku je sai kun dawo. A bar Inna Ladiyo ta yi sati tare da ita don ta saba ni da kaina zan maidota ‘Yan Leman insha Allahu”. Cike da mamaki suka ce, “To”. Suka amince lallai ba abin da ya fi karfin addu’a. Addu’ar da suke kwana da yini yi a kan dan’uwansu, yau Allah ya karba ya fara juyo musu da hankalin dan’uwansu. Zainaba ta yi mishi murmushi, shi ma ya yi mata. Sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Don haka ta yi saurin kama hannuna muka fita inda motocin daukar amarya suke jira a harabar gidanmu. [9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ce, “Shi ba a yi masa aure ba?” Ya yi dariya, ga dukkan alamu Abdulhakim gwanin dariya ne, abin dariya bai da wuya a wajensa, ko kuma yarintar amaryar tashi ce ke ba shi dariya da sanya shi nishadi?Allah A’alam. A yadda ya fahimta ba ta san mene ne mijin ba, baya ga abokin hira, kuma yana jin dadin hakan. Gaskiyar Hajiyarshi ne Sakinah yarinya ce danya sharaf, ba ta san komi ba sai abin da zai koyar da ita. Ya ce, “Shi ba a yi mishi aure ba Sakinah, saboda yarinyar da yake so ya aura ba ta son shi”. Na ce, “Ba sai ya rabu da ita ya nemo wata ba?” Ya murmusa ya ce, “Gane min hanya dai matas, nima akwai wata wadda nake so mai kyau sunanta Farida, amma iyayenta basa sona saboda ni ba millonnaire bane. Da na hakura ba gashi Allah ya bani Sakinah ba? Wadda ta fi Farida kyau da komai?” Na dube shi sosai na ce, “Ba wanda ya taba gaya mini haka cewa ina da kyau, sai na dauka ni bani da kyau irin na Safina”. Ya yi murmushi ya ce, “Wace ce Safinah?’ “Safinah Yayata ce”. Ya ce, “Kin fi Safina kyau Sakinah, duk da ban ganta ba, don dai ita babba ce, ta san yadda zata gyara kyanta, kema in kika girma za ki kara kyau fiye da wannan da kike da shi”. Ya debo fried-rice a cokali ya ce, “Bude bakin matar Abdulhakim”. Na bude cikin murmushi ya saka min na tauna, ya lumshe ido yana kallon taunar matar shi very gently. Yana kallon wadannan kissable lips da ‘beauty point’ din da ke lotsawa ciki sosai ayayin taunarta. Ga uban gashi cunkus dunkule cikin tafkeken ribbon na larabawan usli. Wani al’amari ya soma zarya cikin wasu sassa na jikinsa da bai taba ji a rayuwarshi ba. To amma ya yi alqawarin rainon Sakinah ne, har sai ta zama mutum kamin ya mai da ita cikakkiyar matar aure. Ya ce, “Kin iya girki Sakinah?” Na daga kai, “Amma Mami ta ce jagwalgwalo nake yi”. “Ke kika yi wannan girkin?” “A’a, bani ba ce wancan kabilan da Hajiya ta kawo ne”. Ya ce, “To daga yau in zan zo zan yi miki waya in gaya miki ki yi min duk irin jagwalgwalon da kika iya shi nake so. Bana son na Uche, kina jina?’ Na daga kai. “Kin ga da kamin ki zo Hajiya ce take yi min da kanta, sai dai ki dinga yi a hankali kada ki kone. Ki daina kallon fadan Larabawa tunda kuke suke sa ki”. Na girgiza kai, “Ai Abba ya gaya min Mamana tana can, shi yasa nake son su”. Ya dube ni sosai ya ce, “Wace kasa ya ce miki?” Na ce, “A Libya”. Ya ce, “Na yi ta tunani tun dazu kan jinsin da matar Abdulhakim ta fito, ashe Sakina-ta babban tsatso ne. Na kara GIRMAMAKI, na kuma kara GIRMAMA zaben Babana. Haka na kara son sa, sannan na yi nadamar wautar da na so na yi a baya, na kuma yi alqawari Sakinah watarana zan kai ki Libya idan mun samu adires a wurin Abba...... Manzon Allah (S.A.W) yace “ku so larabawa sabida abu uku; na daya ni balarabe ne, na biyu Alqur’ani balarabe ne, na ukku harshen ‘yan Aljannah shine larabci”. Ban san sanda na kamo hannunshi ba ina murmushi, kamin hawaye su ballo su mirgino. Ba wanda ya taba gayamin kalaman da suka farantamin a duniya irin wadannan bayan Abbana, ya kai hannu yana share min ya ce, “Kada ki yi kuka, bana son hawayenki, tukuicin da nake so ki yi min idan na kaiki Libya shine, ki tsaya ki yi karatu, ki bani sakamakon da zan yi alfahari da ke. Dazu Daddy ya yi min zancen makarantarki, don haka zan kai Monday don in kai ki. Sai dai ina so ki kula da kanki Sakinah, ki sani da da yanzu ba daya bane, yanzu ke babba ce tunda kina da aure. Ba ruwanki da kawaye barkatai, ki mai da hankali kawai kan abin da ya kai ki, ki kawo min kyakkyawan sakamakon da zan ji dadi. Kina jina matar Abdul?” Na ce, “Ina ji Mijin-Sakinah, kuma na yi alqawarin zan yi abin da ka ce”. Ya shafa gashin kaina ya ce, “Na gode”. Har dakina ya rakani, Ladiyo tuni ta yi barci a dakinta. Sai da ya ga kwanciyata ya ja lallausan bargo ya rufe ni, ya kashe lantarki ya bar min na gefen gado mai raunin haske. Ya yi kamar zai sumbaci goshina, ko me ya tuna? Kuma ya fasa. Ya yi min murmushi ya ce, “Good night”. Nima murmushin na mayar masa, mai nuna jin dadi da kulawar shi. Da baya da baya ya fita daga dakin, ya maido kofar ya rufe. Na lumshe ido barci mai dadi ya fizge ni, cike da mafarkai masu dadi, duk rabi a kan Abdulhakim din da ya kirayi kanshi da mijin Sakinah. **** Agogon alarm da na saita shi ya tashe ni, na gabatar da sallar asubahi. Ina lazimi bisa darduma barci na dibana kadan-kadan, na ji an murda kofar an shigo. Mijin Sakinah ya bayyana a dakin cikin farar jallabiya da carbi a hannunsa. Wani lallausan qamshi ya bakunci hancina. Ya zo ya tsugunna a gabana, tuni barcin ya wartsake, na yi murmushi na ce, “barka da asubah an tashi lafiya?” Ya ce, “Ai ni ban yi barci ba matas sai tunaninki”. Na rufe fuska da hijabina, ya rike gefen hijabin ya ce, “Na roke ki, ki daina yi min wannan rufe fuskar, kinga ni da ke yanzu we are one. Tashi muje kicin mu yi abin karyawa kafin Baba Ladiyo ta tashi”. Na ce, “To, jeka waje in cire rigar baccin”. Ya ce, “To, na yi waje”. Ya fita. Na mike na canza rigar barci na da pakistan ruwan madara, na je toilet dina da ke manne a dakin na yi brush yadda na saba na kuskure bakina da ‘listerine’, sannan na cimmashi a kicin har ya soma firar dankali. Na ce, “Ai akwai na’urar fere dankali”. Ya ce, “To kawo”. Nan da nan ya kammala na zuba mai a ‘fryer’ na kunna. Nan da nan muka gama sassauqan karin kumallo. Soyayyen Dankali ne chips da plantain, sai soyayyen kwai da ruwan lipton, na kwaso na kai dining yana biye dani da flask din ruwan zafi. Daga nan muka yi daki kowanne ya nufi toilet dinsa don ya yi wanka. Cikin kayan da Hajiya ta bani matsayin lefe na zaro wata lallausar super ruwan kwaiduwar kwai da ratsin blue, na fesa turare ‘Azzaro Visit’, na taje sumata na hadeta waje daya a tsakiyar kaina. Sai ban daura dankwalin ba na kawo dan karamin gyale na nade kaina na matse da fil. Na fito dining na zauna ke nan sai ga Mijin-Sakinah ya fito, wannan karon cikin kananan kaya, bakin wandon jeans da shirt din Armani, sai qamshi yake. Ban taba jin wanda ke qamshin Abdulhakim ba, turarenshi na daban ne, haka komi nashi is special kamar yadda shi din ma yake na daban, da sauran al’umma dana saba gani. Ya ja kujera kusa dani ya zauna, kafadunmu na gugar na juna. Har yanzu ban daina kallon shi ba. Ya murmusa ya ce, “Wannan kallo haka matas?’ Na yi murmushi tareda saurin dauke ido a kanshi na ce, “Ka yi kyau ne”. Ya ce, “Allah ko matas?’ Na ce, “Allah da gaske”. Ya ce, “To ai ban kai ki ba”. Na ce, “Allah ka fini”. Ya ce, “A’a, ban da washi Sakina-ta”. Aka danna kararrawa ya je ya bude, suka shigo tare da Abdallah. Ya ce, “Wane irin sammako ne haka Abdallah?” Ya ce, “Don ka samu abokiyar hira ni sai ka manta dani bayan ka san ni bani da kowa”. Ya yi murmushi ya ce, “To ka yi zuciya mana? Kai ma ka samu mai tayaka hirar”. Bai ba shi amsa ba ya ce, “Amaryarmu wane delicious aka shirya mana?” Ya fadi yana bude filet din. Mijin Sakinah ya ce, “Ci ne fa da shi uwa rumbu, yanzu in kika yi wasa sai ya tashi da dukkan abincin nan”. Na yi murmushi na ce, “Ba zai iya cinyewa ba”. Ya ce, “To sa ido ki yi kallo”. Abdallah ya ce, “Ki dinga yin girki dani Sakinah in ina nan, gwauro sai da taimako. Don Hajiya ta hanani ta ce nima in yi zuciya in yi aure”. Na ce, “Ai gaskiya ta fada, in wadda kake son ba ta sonka, ni ina da kanwa mai kyau zan baka”. Ya hangame baki yana mamakin inda naji wannan zancen ya dubi Abdulhakim yana girgiza kai ya ce, “A’a, Sakina bana son ‘yar kwaila, ke kanki nawa kike balle kanwarki? Barni da Safiyyata in nan ina lallaba ta a hankali za ta so ni”. Na ce, “To Allah ya sa”. Mijin Sakina dai cin abincinshi yake bai sa mana baki ba. Uche ya zo ya kwashe kayan ya yi kicin dasu. Inna ta fito suka gaisa suka fita tare da Abdallah. Na kaiwa Inna abincinta har dakinta na zauna muna hira. Ta ce, “Tunda maigidan ya dawo ni ya kamata in koma ‘Yan Leman gobe insha Allahu”. Nasa mata kuka na ce, “Nima wallahi ba zan zauna ba sai dai mu tafi tare”. Kuka nake kashirban. Ta ce, “An taba haka Sakinah? Nima nawa tsohon angon jirana yake yi, muje mu lallaba tsufanmu. Ga mijinki yaron kirki mai son mutane da girmama su, auren ke nan Sakinah, kowacce mace haka ta gada”. Na sake tsananta kukana, “Ai ba zama zai yi ba, ya ce ran Monday in ya kaini makaranta zai koma”. Ta ce, “To bari ya dawo sai mu yi maganar ko wata ce ba sai a samo miki ba, amma ni zamana har yaushe?” Suna tafe cikin motar Abdulhakim, sanyin raba na ratsa su. Wani nishadi ne na musamman tattare da Abdulhakim Khalil Ribadu. Wanda dan uwansa Abdallah bai taba ganin sa cikin kwatankwacinsa ba. Abdallah ya dube shi yana murmushi ya ce, “Yar yarinya ta ci gari ga dukkan alamu”. Shima ya yi murmushin ya ce, “Kasar ta ci gaba daya ba garin ba. Abdallah, sai yanzu na gane son da nake yiwa Farida ba natural bane, burgewa ce da sha’awa. Ga son da nake ji har cikin kashi da bargo ba kuma don wani dalili ba, sai Allah da ya sanya mini. Abdallah na kamu da love at first sight na yarinyar da ba ta gama sanin kanta ba balle ta san ina yi”. Abdallah ya ce, “Nima na lura da hakan, shi yasa ake so mu zamanto masu biyayya ga iyayenmu, don ba za su taba yi mana abin da ba alheri bane a garemu. Na gode Allah da ya ganar da kai da wuri da ka zo kana dana sani wadda ba ta da amfani”. Daidai sanda suka iso ofishin Daddy cikin federal high court, kan wasu takardu da ya ce ya debo masa don ranar ta kasance lahadi babu aiki. Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci, shi kadai ya shiga ya dakko ya fito suka juya. Ya tsaya a wani kasaitaccen shago cikin wata Plaza suka shiga tare. Sayi banza sayi wofi duk bai san dalilinsu ba, duk saboda Matar Abdulhakim. Ya yi mata shopping mai yawa da tsada, sannan suka juyo gida. Ya tarar da ni na ci kuka na qoshi duk a kan sai Inna ta zauna da mu. Ya zauna dab da ni ya kama hannuna ya ce, “Ni ba kya son zama dani Sakinah?” Na yi shiru ina share ido. Ya ce, “Ki bi Inna tunda ni ba kya so na”. Ya fadi cikin alamun hushi, don lallashin karamin yaro. Inna ta ce, “Rabu da rigimar Sakinah, tafiya ba makawa gobe zan yi ta”. Ya ce, “A samo wata su zauna tare mana”. Inna ta ce, “Sai dai uwarta Suwaiba, tunda ita maigidanta ya rasu, idan na tafi gobe ita za ta zo jibi”. Abbana da kanshi ya zo daukar Inna, murna a wajena kamar-kamar me. Na kama shi na rungume abin da ban taba yi ba a rayuwata, saboda ban isa ba, ban kai wannan matsayin ba. Sai yau da ya zo da kafafunshi gidan aurena, inda nake da ‘yanci. Mijin Sakinah ya cika da mamakin ganin kukan da nake saboda ganin Abbana, maimakon in yi farin ciki. Abba Ya kawo kudi masu yawa ya bani, ya kuma godewa Abdulhakim makaranta da zai mai dani. Ya ce, “Suwaibar ma ba za ta zo ba rana ita yau daurin auren shi da ita, amma za a samo min mai aiki a can ‘Yan Leman su taho tare”. Da wannan suka lallaba ni suka tafi. Shi ma Abdulhakim fita ya yi tare da su. Bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. Ina falo ina sana’ar tawa (kallon Larabawa). Ya sa ‘remote’ ya kashe, na daga ido a hankali ina kallon shi. Ya karaso ya zauna gefena bayan ya ajiye ledojin da ke hannun shi. Ya juya min baya ya ce, “Fushi nake dake Sakinah”. Na ce, “Ai ina son Inna ne”. Ya ce, “Ni ba kya sona?’ Na girgiza kai, “A’a, ina sonka”. Dariya ta kama shi amma ya gintse, saboda yadda na fadi, “Ina sonka”, din kadai zaka karanta tsabar kuruciyata karara. Sannan ban san wane irin so ma yake nufi ba. Ya janyo ledodin dake gefe ya bude ya soma zaro tsala-tsalan kayan dake ciki riga da wando, siket da riga, dogayen riguna da abaya kala-kala. Ya ce, “Duba ki gani za su yi miki daidai?” Cikin murna nake karasu a jikina ina cewa, “Sosai ma kuwa, na wane ne?” “Na Sakinah ne, mijinta yana so ta dinga sanyasu a gida tana yi mishi kwalliya”. Na kyalkyale da dariya na ce, “Na gode, Allah ya kara budi”. Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kama tafukana ya rike cikin nasa ya ce, “Gobe zan koma Sakinah, I will miss you so much…., ko za ki bini?’ Na ce, “Makaranta fa?’ Ya ce, “Hup! Na manta ne, in ina tare dake sai in manta komai”. “Za ka dawo wani satin?’ Ya ce, “A’a, sai sati na sama saboda zan je Ibadan kan Shimfida wani titin jirgin kasa da zamu yi”. Na ce, “Titi kake ginawa?” Ya yi murmushi ya ce, “Ni magini ne Sakinah, ba abin da bana ginawa. Tun daga makarantu, jami’o’i, gidaje, ma’aikatoci da asibitoci kin gane?” Na daga kai. Ya ce, “Nima in tambaye ki, me yasa dazu da kika ga Abba kike kuka?” Na ce, “Saboda ban taba rungume shi bane a rayuwata sai yau”. Ya kwanta sosai cikin kilishi ya ce, “Bani labarinki Sakinah, kin ce Mamanki tana Libya, ga Abbanki kuma a nan, basa tare ne?” Na ce, “Basa tare, nima ban santa ba, Abba ya ce tun sanda ta yayeni ta tafi”. Ya ce, “To wace ce ta rike ki?” Na ce, “Mami matarsa”. Ya ce, “Hajiya Lami ke nan qawar Hajiyata?” Na ce, “Eh”. Ya ce, “Bana son matar nan ban san me ya sa ba. Bana son tarayyarta da Hajiyata, tun daga lokacin da Hajiya ta sani na kaisu wani qungurmin jeji tare a Bidda”. Na yi shiru ban ce komi ba, don ba zan iya zagin Mami a idon kowa ba. Na riga na yafewa Mami duk abin da ta yi mini, tunda dai ta rike ni da dadi ba dadi har na kawo munzalin da nake a halin yanzu. Na soma hamma, yana magana bana jin shi sosai saboda barci da ya ci karfina. Ya mike ya miko min hannunshi na kama, har dakin barcina. Na kwanta a gado, ya ja bargo mai laushi da taushi ya rufe ni, sannan ya dauki ‘remote’ ya rage karfin A.C “Sleep well matar Abdulhakim……!”. Na ji shi yana fadi sama-sama. Sabida tuni barci ya ci karfina. Ya fita ya ja min kofar. *** Washegari ma tare muka hada kalaci, sannan na shirya cikin ‘uniform’ dina. Na juya na dubi kaina a mudubi. Ni kaina na firgita da irin kyawun da na ga na yi cikin dan lokaci qalilan. Ya fito shi ma cikin shiri na dakakkiyar baqar shadda galila, sai maiqo take. Na ce, “Mijin Sakinah ka yi kyau”. Ya ce, “Allah Sakinah? Don baki ga naki kyan cikin uniform din nan bane”. “Ina uniform ya ga kyau Mijin-Sakinah?” “Yana yin kyau a jikin special people (mutane na musamman) irin Sakinah Abdulhakim”. “A’a, Sakinah M.T Liman nake, kowa haka yake kirana a makaranta”. Yace “tuni kika tashi daga Sakinah M.T Liman, kin dawo Sakinah Abdulhakim Khalil Ribadu”. Sai na yi murmushi ban ce komi ba. Muna tafe a hanya kira’ar Abdurrahman Sudais na tashi cikin (Suratul A’araf), har muka iso makarantarmu. Ya yi parking a inda aka tanada don adana motoci muka karasa ofishin principal, ya yi ta bata hakuri kan rashin zuwana makaranta na lokaci mai tsawo bana jin dadi ne, da kyar ta hakura.Ya ce dani, Daddy zai zo da kanshi ya daukeni in an tashi, daga gobe kuma akwai direba John da zai dinga kawoni yana dauko ni kullum”. Ya kara jaddada min in kama kaina ba ruwana da kawaye, kuma kada in dinga fada musu an yi min aure, kowa ya ce me ya sa bana zuwa in ce bana jin dadi ne. Shi zai wuce Lagos sai ya dawo. Ina yi mishi bye-bye har ya qule na daina ganin shi bai daina daga min hannu ba. Da aka fito break muka hadu da Nadiya muka yi ta tsalle muna labarin bayan rabo. Daga bayanmu Safinah ta daka mana tsawa.Ta ce, “Ke Sakinah yanzu fa ba daya kike da Nadiya ba da za ki biye mata kuna tsalle-tsalle. Girma ya hau ki, kada in kara ganinki kina wannan tsallen”. Karfe biyu Daddy da kanshi ya zo ya dauke ni. Na tarar da Sabuwa mai aikin da Abba ya dauko min daga ‘Yan Leman har ta rigani isowa, muka gaisa na wuce daki don in cire kayan makaranta. Zaman mu ni da Sabuwa gwanin sha’awa, Sabuwa mace ce mai tsafta da zafin nama, kafin in tashi barci ta rigani ta tsaftace gidan, kafin in gama wanka in yi shirin makaranta ta kammala kalaci ta zuba min wanda zan tafi da shi cikin flask, sai in ci in fito in tadda John mu wuce makaranta. Yau da aka fito break muka hadu ni da Nadiya muka nufi gindin bishiyar goba muna cin abinci, na Nadiya muke fara ci sannan mu ci nawa. Muna ci ta ce, “Sakinah ya ya sunan mijinki?’ Na ce, “Sunan shi Mijin-Sakinah”. Ta ce, “Mijin-Sakinah?’ Na ce, “Eh, shi ya ce min sunanshi haka”. Ta jinjina kai ta ce, “Uhm! Ban taba jin wannan sunan ba”. Na ce, “To haka ya ce sunansa”. Ta ce, “Kin san kuwa Abba ya auro Yaya Suwaiba ta ‘Yan Leman?” Cikin mamaki na ce, “Yaushe?” “Yau satinta daya, kuma Mami da Adama sun yi fada ta kore ta, don ta gane cutarta take, in ta aike ta wajen malamansu ba ta zuwa sai ta zuba kudin a aljihunta ta kawo mata magungunan karya. Yanzu gaba daya Abba ya watsar da Mami sai Yaya Suwaiba, kuma ya hanata zuwa ko ina. Mami har tausayi take bani”. Na ce, “Allah sarki Mami, gara ta rabu da Adama, don ba mutuniyar kirki ba ce, amma inda za ta gane ta zauna lafiya da Yaya Suwaiba don tana da kirki sosai”. Ta ce, “Abin da Yaya Safinah ta gaya mata ke nan”. Aka kada kararrawa muka koma aji. Har aka tashi yau ina tunanin hirar da mu kai da Nadiya. Gaskiya ne addu’a ba ta faduwa kasa banza, addu’ar da nake kwana da wuni ina yiwa Abbana a kan Mami, ba ta fadi a banza ba. Tunda gashi alqadarinta ya soma karyewa, Abba ya fara zama namijin duniya. Tunda Mijin-Sakinah ya tafi, bamu gaisa ba, don bani da waya. Ga shi ya ce in zai dawo zai sanar dani in yi mishi girki. Don haka na bi na damu, don ban san ranar da zai dawo ba. Sai na kintata tunda ya ce wannan satin ba zai zo ba sai sati na sama, don haka ranar juma’a ta sama na shiga kicin don ganin abin da ya dace in girka masa. Sakwara na fi kwarewa da yi, saboda yadda Mami ke son ta, take kuma yawan samu mu yi ni da Adama. Don haka da kaina na kirba doyar a turmi. Sabuwa na yankan alayyahun miya muna hira, sannan na fiddo kayan ciki a firji na wanke na dora sanwar farfesu. Ina gamawa na yi wanka na sanya daya daga cikin riga da siket da Mijin-Sakinah ya sayo min na fesa turare na dawo falo na zauna kallon mutanen nawa (larabawa) a tauraron dan adam. Shiru-shiru tun ina duban kofa har na soma mikewa ina leka waje, babu Mijin-Sakinah babu alamun shi. Har magariba babu shi babu Abdallah. Na dawo cikin kujera na yi zugum dani, damuwa karara ta bayyana a fuskata. Kamin ka ce meye wannan? Sai hawaye, wasu na korar wasu. Aka murda kofar falon a hankali aka shigo, na daga kaina a hankali don ganin mai shigowa. MIJIN-SAKINAH ne, rataye da falmaran din baqaqen ‘Italian Suit’ da yake sanye dasu. Ya yi tsaye a kofar yana kallona yana murmushi, hannayenshi duka biyu zube cikin aljihu, kafin ya bude min dukkan hannuwanshi da nufin in zo gare shi, na maida hannuwa na baya na sarqesu ina murmushin da ni kaina bansan irinshi ba. Murmushin farin-ciki indeed! Amma hawayen basu bar ambaliya ba. Da sassarfa ya karaso gareni, ya rage tsaho ya rankwafa ya kamani ya rungume, muka saki ajiyar zuciya mai nauyi a tare. Ya dago fuskata da hannun daman shi ya soma share min hawayen. Ya ce, “is O.K matas, na yi laifi da na dade ban iso ba, ba zan kuma ba, ban taso da wuri bane sakamakon dimbin ayyuka da suka tare ni. Ki yafe ni........ I’m terribly sorry….!”. Ya kai gwiwoyinshi kasa ya kama fatar kunnenshi, ya sake cewa, “I’m-sorry!” Na tuntsire da dariya duk da maqalallun hawayen da ke idona. Ya mike yana cewa, ‘Lemme take a shower, I’ll be back to you soon.... (bari inyi wanka ina zuwa gareki yanzu)” Ya wuce dakinshi yana cewa, “Biyoni da brief case din nan”. Na dauka na bishi a baya. Ban taba shigowa dakin Abdulhakim ba sai yau, makeken family bed ne dan kasar Italy, sai wardrove ta jikin bango, sittirun shi ne a jere reras saqale jikin ‘hanger’ wanda duk rabi suit ne kala-kala, baqaqe da rowan toka samfurin Tommy Hilfiger, Armani, Louis Vuitton, Dolce and Gabbana, Versace, DKNY gasunan dai barkatai wanda kallonsu kadai ya isheka kimanta tsadarsu, sun kuma isa su nuna maka cewa mamallakinsu dan gaye ne na karshe. Dakin shimfide yake da marbles farare sol har a jikin bango. Sai split mai kwararar da ni’imtaccen sanyi wanda ya gauraye da qamshin room-freshna respberry ya ba da wani nau’in sanyi da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya. Sai dai dakin a hargitse yake ko ina takardu da taswirar zane-zane. Don haka yana shiga shower na soma kintsa dakin. Na hada takardun wuri daya na adana komai a muhallinsa, na sa mopper ina goge marbles, nan da nan dakin ya hau sheki. Ya fito daure da tawul ya tsaya yana mamaki. Na dago ido na kalle shi na yi saurin dauke ido a kanshi, don ban taba ganin babba babu riga ba. Ya yi murmushi ya ce, “Haka kike da aiki Sakinah?” Ban amsa mishi ba, na soma kokarin fita ya riko hannuna na kuwa tamke idona tam! Ya langabar da kai abin tausayi ya ce, “Ni mijinki ne Sakinah, ki rage jin kunyata”. Na ce, “Ai fita zan yi kasa riga”. Ya ce, “To ai ni wai da tausa nake so ki yi min”. Na zaro ido. Babu bata lokaci na ce, “Ban iya ba”. Ya ce, “To zo in koya miki”. Ai kuwa na ce kafa……. me na ci ban baki ba…..na falfala da gudu na koma kichin. Ban kara dawowa ba. Ina jera abinci a dining ya fito cikin caftan na wata jiqaqkiyar wagambari deep green, sai sheki take saboda maiqo. Ya tsaya jikin tebir din yana kallona, na dukufa wajen shirya table, ya ce, “Dama kin daina wahalar da kanki, wajen budurwata dana gaya miki labarinta zan je in ci, kuma ta yi min tausa”. Da sauri na dago na dube shi, na kuma yi saurin sunkuyarwa don fuskarshi babu alamun wasa. Na ji wani haushi ya zo ya tokare ni a zuciya. Zai wuce na yi saurin shan gabansa, idanuna rau-rau suna niyyar zub da hawaye, “Don Allah kar ka je”. Ya dube ni sosai kamar yayi dariya amma ya dake, ya ce, “In ban je ba za ki yi min ne?” Da sauri na daga kai. “To amma kar ka cire riga”. Ya murmusa ya ce, “Ba zan cire ba, amma mu fara cin abincin”. [9/14, 9:59 PM] Asmau: Na ji dadi, na dau filet na soma zuba mishi. Ya soma ci ya ce, “Amma dai da inji kika daka sakwarar nan”. “A’a, da hannu ne, me ka gani?” “Ta yi kyau ne sosai, ga dadin taunawa, you are a good cook, na gode Sakina”. A kwana biyun da Abdulhakim ya yi wannan satin, na qware da yi mishi tausa, mun kara shaquwa, kauna ta musamman ta kara habaka a tsakaninmu. Har tsoro nake lahadi ta zo ta rabani da mijin Sakinah (kamar yadda ya kirayi kanshi) ya kuma ce min da hakan yake so in dinga kiran shi don yana jin dadi a ce shine mijin Sakinah. Ya koma ranar lahadi nima na koma makaranta ranar litinin. Jarabawar karshen zango na uku ta matso, wadda daga ita zan shiga aji uku na karamar sakandire. Mun samu hutu bayan kammala jarrabawa, Abdulhakim yana Lagos, sai karshen satin nan muke sanya ranshi. Na duba kicin na tarar duk naman da ke cikin freezer ya kare. Na kira Sabuwa na ba ta kudin cefane har da naman. Bayan ta kawo muna killace kowanne a inda ya dace, kararrawar kofar shigowa ta yi kara. Sabuwa ce ta je ta bude, sannan ta gaya min cewa ina da baki. Na wanke hannuna da sabulu cikin sink na fito, nan na yi arba da Abbana, Safinah da Nadiya da autanmu Nazir. Na yi tsalle na rungume su daya bayan daya, na rasa inda zan sa kaina don murna. Nan muka shiga hidimarsu ni da Sabuwa. Safinah da Nadiya suka ce, “Mami na gaishe ki”. Na yi murmushi na ce, “Ni kuwa?” Abba ya ce, “Mamin ku na gaishe ki da gaske, da tare ma zamu zo to sai ta yi baki”. Nadiya ta ce, “Baki san Mami bane ta sauya yanzu. Yaya Suwaiba ma tana gaishe ki, za su zo tare da Mami”. Na ce, “Duk ina amsawa Allah ya kawo su”. Mun kebe ni da Abba a karamin falon Abdulhakim, mun baro su Safinah suna ta ciye-ciye. Abba ya ce, “Babu matsala dai ko Sakinah?’ Ina murmushi na ce, “Babu Abba”. Ya gaya min cewa ya je Libya yana kara bincike har ya samu mutumin da ya gaya mishi sunan garin da su mahaifiyata suka koma a Egypt wato Qatar, yana nan yana fafutukar neman adireshin, da ya samu zamu je insha Allah. Da wannan daddadan labari suka tafi suka barni. Ko da Abdulhakim ya zo a wannan satin da labarin da na tare shi da shi ke nan, shi ma ya tayani murna. Ya sunkuce ni muka yi dakinsa yana cewa, “Ki yi min tausa..... I missed your tausa Sakinah….!”. Sai da nayi mishi tausar ya tausu, ya kama hannuwana ya rike cikin nasa, ya soma murza ‘yan yatsuna a hankali yanayinshi yana sauyawa a yau. Yana kallona da wani irin murmushi mai sanyi da sanyaya zuciya. Na kwace hannuna na ce, “Barci kake ji ne Mijin-Sakinah?” Daga can karkashin maqoshinsa ya ce, “Uh!” Na ce, “To bari in tafi ka kwanta”. Ya girgiza kai ya kara damke hannuna, damka sosai kamar zai ballani, nayi ‘yar kara nace “zaka karya ni” yace “bazan karyaki ba, amma Sakinah Mata da mijinta basa raba makwanci Sakinah, yau dai daya da zan yi miki sallama, ki tayani kwana!”. Cikin firgici na ce, “Ina za ka je?” Ya yi matashi da kafafuna yana ja min yatsu a hankali ya ce, “Wajen aikinmu sun zabe ni zan tafi wani course a Beirut (Lebanon) tsayin shekaru biyu...... ba don makarantarki ba da tare zamu tafi, amma zan ke zuwa akai-akai ina ganin ki...”. Kuka nasa sosai, “Ni ba zan zauna ba, wallahi sai dai mu tafi tare ko ka mai dani gidan Abbana”. Ya ce, “Gidan Abba kuma? Kina so Mami ta ci gaba da lakadarki ko?” Na ce, “To zan bika”. Ya ce, “Makarantar fa? Na gaya miki zan dinga zuwa ba zan yi watanni uku ban zo ba”. “To ka mai dani gidanku wajen Hajiya”. Ya ce, “A gidanki za ki zauna, ita ma Hajiyar a gidan mijinta take”. Na ci gaba da sharar hawaye yana lallashina. Washegari tunda muka yi sallar asubahi bamu koma barci ba. Nasihohi yake yi min a kan in kula da kaina, in kula da amanar aurenshi, in mai da hankali a kan karatu. Ya ce yana so kafin ya zo in dauko 1st position zai yi min babbar kyauta. Ya fada toilet ya yi wanka ya shirya cikin riga da wandon versace, yana kumbing kanshi, ya juyo ya dube ni na yi tagumi a gefen gadon shi, idona cike taf da kwallah. Ya aje matajin ya karaso ya tsuguna a gabana, ya kama hannuwana sannan a nutse ya ja ni cikin jikinshi, ya soma kissing bakina zuwa dogon wuyana bayan ya rike tufkar gashina da hannun hagunshi, cikin wani irin ‘passionate kissing’ mai tsirgawa har cikin kwakwalwa….. Da karfi na yi baya, na ce, “Wannan ai iskanci ne Mijin-Sakinah, meye haka? Sai kace wasu tantabaru?……”. Ya rufe baki yana dariya ya gyada kai ya danne dariyar ya ce, “To na daina iskanci, sallama ce nake miki matar Abdulhakim irin ta turawa, ko ba kya gani suna yi a talabijin”. Na ce, “Ina gani, amma kai ai ba bature bane, don me za ka kwaikwaye su bayan su ‘yan iska ne daman?” Ya kama baki ya girgiza kai yana so ya kara yin dariya amma ya dake, ya kama hannuna muka zauna a gefen gado. Ya jawo loka ya debo kudi masu kauri ya zube min a cinya. Ya ce, “Ku dinga yin cefane kafin in zo”. Sannan ya miko min kwalin waya yana nuna min yadda zan ke amfani da ita, na rike wayar nan ina murna. Ya kama hannuna ya lumshe ido ya ce, “Sakinah me za ki bani? Wanda zan ke tunawa da ke kullum?’ Na ce, “Me kake so in baka?” Ya rufe ido ya nuna min kuncinsa na dama, “Kiss me here........” Na zaro ido na ce, “Allah ba zan iya ba”. Sai ya kamoni ya rungume a kirjinsa yana saukar da numfashi da sauri da sauri. Ya ce, “I will miss you so much...... plz Sakinah kiss me....” Jin roqon ya yi yawa, ga shi yana ta bata lokaci, sai na runtse ido na yi yadda yake so. Nayi mishi sumba, mai tsayi, da zurfi. Ya kara kankame ni qam-qam tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya ni. Al’amarin ya soma kokarin sauya alkibla daga Abdulhakim a yau, gabadaya ya rikice mani, da wasu sabbin al’amura da ban sani ba, ban kuma taba tsintar kaina a ciki ba,ban sansu ba, cikin kananan shekaru na, wanda hakan ya haifar da matsanancin tsoro a gare ni. Sallamar Abdallah a falo ita ta katse duk wani hanzarinsa, ta qwaceni daga hannun mijin Sakina, wanda nake tunanin babballani yake so ya yi, na rufe ido saboda kunya, duk ya cukuikuiye min shaddata da ta sha guga. Ya ja babbar jakar na ja karamar muka fito falo. Abdallah ya ce, “Kana duba agogo kuwa? Ka san nisan airport din nan amma ka yi zamanka. Sakinah dauko mayafinki mu tafi su Daddy suna mota suna jira”. Ya ce, “Ba za ta je ba, don kuka za ta yi”. Yasa murya yai kiran Sabuwa, ta fito suka gaisa. Ya ce, “Ni zan tafi, don Allah ki kula da gida da Sakinah”. Ta ce, “Insha Allah Alhaji”. Ya fita yana waiwaye na ni kuma ina sharar hawaye. Tun tafiyar Mijin-Sakinah sai na zama wata irin sukuku ba kuzari, na saba da Mijin-Sakinah, matukar sabo kuwa. Ya shiga raina fiye da tunani, yau kwana bakwai da tafiyarsa amma har yau kewarshi ba ta sake ni ba, walwalata ta ragu, farin cikina ya taqaita. A makaranta ba na tsinana komai, sai tunanin Mijin-Sakinah da al’amuranshi, tareda tuna abubuwanda suke gudana a tsakanin mu, masu kara min kaunarsa. Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, da kirki na gasken-gaske, tareda biyewa kuruciyata, da karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa. Na samu kaina cikin wani sabon al’amari akan Abdulhakim. Na soma tambayar kaina shin me ke damuna ne? Ni ‘yar gidan Limamai? ‘Note’ ya taru ban yi ba, sai Nadiya nake kaiwa ajinsu idan ‘yan ajinmu sunyi ta yi min. Don haka da aka zo jarabawa na kwaso na talatin. Yau da dare Daddy ya shigo, bayan mun gaisa na nufi kicin na kawo mishi ruwa da lemu, na zuba mishi a tambulan ya sha. Ya dube ni sosai ya ce, “Wannan ramar ta mece ce Sakinah?” Na sunkuyar da kaina ina murmushi, na ce, “Mun yi jarabawa ne Daddy”. Ya ce, “Ina sakamakon?” Cike da tsoro na ce, “Yana daki”. Ya ce, “To kawon in gani”. Jiki babu kwari na shiga daki na fiddo mishi result din. Ya duba ya dago da sauri ya kalleni, “Na talatin Sakinah?” Na sunkuyar da kai cikin rashin jin dadi. Kamar ince da kasar ta tsage in shige sabida kunya. “Sanda kina gida na nawa kike dauka?” Muryata na rawa na ce, “Na goma ko takwas ko bakwai”. Ya ce, “Hakan na nufin kina da damuwa a yanzu, wadda ban sani ba? Fada min ko ta mece ce.....” Na ce, “Wallahi Daddy babu”. Ya ce, “To me yasa sakamakon ki bai yi kyau ba? Idan Abdulhakim ya ga wannan zai ji dadi ne?” Na girgiza kai ban yi magana ba. Ya ce, “To ki dage next term kada inga sakamako irin wannan”. Na ce, “Insha Allahu zan dage”. “Abdulhakim ya ce in tambaye ki, mene ne amfanin wayar da ya baki don ku dinga gaisawa kika rufe ba kya budewa?” Na ce, “Na manta da ita ne Daddy saboda exam, amma yanzu zan bude”. Ya ce, “Ki bude ki sata a caji, kada ki kara rufewa sai in za ki kwanta barci. Duk wata damuwarki ki sanar dani kin ji ‘yata Sakinah? Ki dauka ni da M.T duk daya ne, babu banbanci. Na samu malamin Islamiyya wanda zai dinga zuwa har gida asabar da lahadi ya dinga koyar dake karatun Alkur’ani da sauran litattafan addini, kina so?” “Ina so Daddy, na gode sosai”. “To Allah ya yi muku albarkar biyayyar da kuka yi mana, kuma ya baku masu yi muku kwatankwacinta, ko fiye da ita. Ni zan wuce, ba kya son komai?” Na ce, “Akwai komai, kuma akwai kudi, sai dai John ne ya ce yana tunin albashinsa”. Ya ce, “Babu damuwa, zan ganshi”. “A gai da Hajiya”. Ya ce, “Za ta ji”. Yana fita na yi daki na soma laluben lokas inda na san na ajiye wayata, na fiddota na hada na jona caji. Kafin a jima ta cika. Tun ina tunanin Mijin-Sakinah zai kira yau, gobe ko jibi har na hakura, na ci gaba da mai da hankali a kan karatuna na Islamiyya da boko. Watanni biyar ke nan da tafiyar Mijin-Sakinah, na dawo daga makaranta ko uniform ban cire ba, na shiga gidan Hajiyar Abdulhakim don na gaishe ta, kasancewar na kwana biyu ban shiga. Tun daga bakin kofar shiga falon Hajiya na soma jiyo muryar Mami, gabana ya fadi na juya zan koma sai gasu sun fito ita da Hajiya, ga dukkan alamu tafiya za ta yi. Daidai sanda na juya zan tafi Mami ta ce, “Sakinah, saboda na zo wajenki za ki juya?” Na juyo na tsuguna a kasa ina gaishe ta. Ta kama hannuna ta dago ni ta ce, “Ki yafeni Sakinah, kan duk abin da ya faru a baya. Na zo ne in ga dakinki, in kuma baki hakuri”. Na ce, “Ni baki yi min komai ba Mami”. Ta ce, “A’a, na yi miki, sai dai ki ce kin yafe ni”. Na ce, “To na yafe ki, muje kiga dakin nawa”. Har Hajiya muka je, Mami ta shiga ko’ina ta yaba, dakin Abdulhakim ne kadai a kulle. Na debo kayan shafa na (Neutrogena) cikin leda na ba ta. Da kyar ta karba, ta ce, “Ni ya kamata in kawo miki, ga shi ban kawo komi ba sai in amshe naki?” Na ce, “Na neman albarka ne Mami”. Ta ce, “To, Allah ya yi miki albarka”. Bayan fitar Mami da Hajiya na cire uniform na yi wanka na zuba riga da siket cikin kayan Mijin-Sakinah, na kunnawa gidan burner da turaren touch me. Na tadda Sabuwa a kicin tana kwashe abinci. Na ce, “Sannu da aiki”. Ita ma ta yi murmushi ta ce, “Sannu da dawowa”. “Yau kin yi lattin gama abincin”. Ta ce, “Gas ne ya kare, amma akwai electric da shi na yi, kin san kuma ba shi da sauri”. Muna haka Sadi ya soma shigo da jakunkuna manya-manya. Fitowar nan da zan yi na yi ido hudu da Abdulhakim a falon yana zaune yana amsa waya, ya mike dogayen kafafunshi sumul-sumul dasu a kan kilishi ya jingina da throw pillow. Fitowata ina murmushi bai sa shi ya daina wayar da yake yi ba. Na muttsike idona na tabbatar shi ne ba gizo idanuwana ke min ba. Ya kara wani irin kyau mai sanyin gani a ido, fatar jikinshi da sajenshi sunyi sumul sun kwanta sunyi lumm sai sheki suke, wani lallausar qamshi na tashi a falon wanda ban taba jin qamshi mai dadinsa ba. Da gudu na karasa gabanshi na zube daidai kafafunshi ina dariya. Ni kaina na rasa dalilin da yasa yau ban fada jikin shi ba kamar yadda na saba. Ya rufe wayar ya cillata kan kujera yana murmushi, “….This is not the kind of welcome I like....” Ya bude min dukkan hannuwanshi, na fada ciki a hankali, ya rungume ni yana rada min cikin kunnuwana cewa, “….Sakinah na yi kewarki!” Yinin ranar zungur, Abdulhakim ko masallaci bai je ba, duk inda ya yi ina naniqe da shi don tsoron, kada ya sake gudu ya barni. Yana tambaya ta abubuwan da suka faru a bayanshi. Ya ce in dauko result ya gani. Jiki babu kwari na dauko na kawo mishi. Ya karba ya duba, ya qura min ido cike da fushi ya ce, “Alqawarin mu dake ke nan Sakinah?” Na girgiza kai na sunkuyar da kaina. Ya ce, “Tunda haka ne tsarabar da na kawo miki na fasa baki su Nadiya zan aikawa, sannan kawo hannun ki maza mu kwance abotar tamu, daga yau bana yi da ke”. Na soma sharar hawaye ina cewa, “Ka yi hakuri ABDULHAKIM ba zan kuma ba”. Ya yi mamakin kiran sunanshi da na yi a yau, don ban taba yi ba. Ya ce, “To gaya min dalilin da ya sa ba kya mai da hankali a karatu”. Na sunkuyar da kaina naki amsawa, ya cigaba da nacin tambaya da kyar na iya na ce, “Tunaninka nake yi”. Ba karamin mamaki ya yi ba. Ya ce, “Kuma don kina tunanin mijinki sai ki ki yin karatu? Ba kya tunanin nima karatun nake yi? Nima ai ina tunaninki, amma bana bari ya hanani ci gaba, ya hana min yin karatun da zai amfane ni. Wannan shi ne kashedi na karshe, idan kika kara dauko sama da goma idan na tafi ba zan sake zuwa ganinki ba sai na gama duka. Ki yi ta tunanin nawa in kinga tunanin shi ya fi dacewa dake”. Ya cillar da report din ya mike ya nufi shower. Ganin yau Mijin-Sakinah ya yi fushi dani, duk sai na ji babu dadi, hankalina ya tashi. Yana fitowa na kama kafafunshi hawayena na diga akan tafukansa, na ce, “Don Allah ka yi hakuri bazan sake ba”. Muryarshi tayi sanyi. Ya ce, “Ni kam me kika yi min da za ki bani hakuri? Iyakaci in kin ki yin karatu in auro mai karatu wadda za ta koyar da ‘ya’yana karatu, ba wadda za ta koya musu tunanin miji ba.....” Na kara tsananta kukana na ce, “Don Allah kada ka auro kowa wallahi ba zan sake ba”. Ya juya baya yana dariya amma ya gintse, “Saboda me ba kya son a auro wata? Bayan hudu Allah ya ce in yi?” Na ce, “Ni dai bana so, don Allah ka bari”. Ya ce, “Ai ba zan bari ba, idan ba za ki yi karatu ba ni kuma ba zan fasa aure ba”. Don haka wannan zangon bayan komawar Abdulhakim na nade hannun riga da kafar wando na durfafi karatu ba ji ba gani, na bokon ne ko na Islamiyyar. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu na dauko na bakwai a ajinmu. Da Abdulhakim ya zo goyona ne kawai bai yi ba, don ya nuna min farin cikinshi.Har Daddy ma ya yi murna ya kuma sa min albarka. *** Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau muka samu hutu wanda daga shi in mun dawo zamu shiga aji daya na babbar sakandire. Abdulhakim ya gama course din shi a Beirut ya kuma samu qarin girma a ‘Julius Berger’. Yana daga cikin ma’aikatansu da suke ji dasu saboda fasahar da Allah ya ba shi. Idan ya tsara gini, ko bature albarka. Sai dai kokarin da yake na samun ‘transfer’ zuwa nan Abuja har yanzu bai samu ba. Shekaru biyu ke nan da aurenmu, wadanda suka yi daidai da cikata shekaru goma sha hudu a duniya. Zuwa lokacin na fara sanin kaina, na kuma fara sanin wane ne mijina Abdulhakim Khalil Ribadu? Dogo ne, ba shi da kauri sosai, kuma ba ya da rama. Wankan tarwada mai mikaqqen hanci, mai yawan sumar kai, ma’abocin yalwar fararen idanu masu sheki (oily eyes). Duk inda ake neman mutum ma’abocin kwarjini da kamala za a sanya Mijin-Sakinah a ciki. Babban abin da ke burge mutane dashi shi ne halayensa masu nagarta. Mijin-Sakina yana da saukin kai, sannan abin hannunshi bai rufe mai ido ba, kullum bayarwa yake, kuma kullum kara samu yake.Kin san dai ma’aikatan ‘Julius Berger’. Cikin shekaru biyu kacal da aurenmu Abdulhakim ya ce ya ga alhairori da budi kala-kala wanda yake da tabbacin falalar biyayya ga iyaye ne. Don haka yake kara rike ni Sakinah da amana da soyayya ta gaskiya, wadda bai taba tunanin zai yiwa wata diya mace ba. Har kuma inda yau ke motsi, bai taba daura min lalurar aure ba. Duk da hakuri yake yi, yana kuma tunanin Sakinah is too young....... har gobe ya dora mata bukatar auratayya. Rainona kawai yake tare da koya min soyayyarsa, don haka yake yawan yin azumin tadauwa’i, wanda ni ban san dalilinsa ba. Illa duk ranar da ya ce yana azumi, in ce azumin me kake? Ya ce na neman lada man Sakinah!”. Zan numfasa, muje ga littafi na 2, wanda tare yake da dan uwansa, maman Safah da Marwah ce……