NA MIJI K'UDAN ZUMA By maman Islam ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION Page 1 "Assalamualaikum maman Khalid yaudai gani a kar ki ciny...............d'if maganar ya d'auke sakamakon ido hud'u da sukayi da SAMAD dan haka tayi kicin kicin da rai yayin da taji aranta kamar ta juya ta koma sai dai ta san idan ta koma anty DEENAH bazata tab'a jin dad'i ba tunda sun riga sunyi da ita yau zata zo, sannan kuma tana yawan yi mata korafin rashin zuwan ta wanda hakan yana da nasaba da yadda tayi masifar tsanar Samad d'in. "Oyoyo mommy" yaron anty Deenah da fito yanzun wajen daddynsa ya kwala ihun murnan ganinta, saurin durkushe wa tayi ganin yayo kanta da d'an gudun sa ai kuwa yana zuwa ya fad'a jikinta ta rungume shi tsam tsam ajikinta tana mai jin dad'in ganinsa. Itama cikin murnan ganinsa tace "oyoyo my boy ina Momma?" Bai bata amsa ba yace "mommy ina tweets tin da titace a kawo min ya?" Ya tambaye ta cikin tsatstsamar hausar da bata gama kama bakin sa ba. Murmushi tayi ta d'an ja kumatunsa tace "kai my boy mai yasa baka mantuwa ne?" Ta fad'a tana d'ebo alwan a cikin Jakarta ta mik'a masa karb'a yayi da murnan sa na gode my mom ya fad'a yana barin wajen da gudu yayin da tashi da kallo har ya haye jikin daddyn sa wanda tun shigowar SUHANA yake binta da wani mugun kallo suna had'a ido itama ta galla masa harara karab sai a idon Deenah wacce ta fito yanzun. "A a SUHANA bana son iskanci meye haka wai Daddy sa'anki ne da kikayi masa irin wannn rainin?" Itama sak'on hararan ta aika mata kafin ta saki wani mugun tsaki ta mik'e da sauri ta juya. "SUHANA SUHANA SUHANA" Deenah ta bita da sauri tana kira harda d'an gudun ta, "SUHANA dan Allah karki tafi" Deenah ta fad'a da da d'an sanyi jiki, cak SUHANA ta tsaya tana goge hawayen da ya zubo mata amma bata juyo ba. "Haba SUHANA me yasa kike haka ne duk kin bi kin canja hali sam raina Babba ba halin ki bane me yasa yanzun kika canja haka da yawa?" Kuka ta fashe dashi tace "to anty me na masa da zai rik'a hantarana yana min kallon tsana da hararana?" "Ba hararan ki yake ba SUHANA abinda mutane suke zargin ki dashi shine shima yake tunanin hakan sam baya jin dad'in yadda mutane suke ya mud'id'i dake akan abinda ba haka bane" Kafeta tayi da ido tana kallonta yayin da wasu irin hawaye masu mugun zafi ya zuba mata tace "anty kema ZARGINA KIKE?" girgiza kai Deenah tayi tace "ko kad'an bana zarginki 'yar uwata tunda nike dake ban tab'a ganin wani abun assha atare da ke ba dan haka ban tab'a zargin ki ba SUHANA' amma kinsan cewa dole zargi ya hau kanki abisa abubuwan da kike aikatawa" "Ai kema kinsan dole ce tasani hakan bani da yadda zanyi ina samawa kaina nutsuwa ne amma wallahi bana aikata wani mugun abu" "Na sani SUHANA amma dan Allah ki rik'a taka tsantsan da rayuwa saboda kinsan yanzu kiwon mutum ake" "Naji kuma zan kiyaye ta fad'a tare da shafar fuskar ta tace"ni zan wuce anty" "Au bazaki shiga ba?" "Eh" "Me yasa?" "Saboda na tsani SAMAD kuma bana son ganin sa" Murmushi Deenah tayi tace "SUHANA kenan kedai wallahi rigiman ki yawa ne dashi" Itama murmushin tayi ta sumbaci hannun yayar tata tace "good by my ant" Ita ma hannunta ta d'aga mata jikinta a sanyaye aranta tanaiwa kanwar tata fatan samun sassauci abisa matsalar ta. Sanda ta koma d'akin tuni SUHAIL yayi bacci ajikin daddyn sa wanda yai kicin kicin da rai. Yadda ya had'e rannan tasan saboda ganin SUHANA ne dan haka ta d'an saki murmushi ta k'arasa ta shige jikinsa tana kafe shi da kallon ta mai sanya masa nutsuwa da gusar da duk wani fushin sa, a sanyaye yace "ki hanata zuwa gidannan bana son ganin ta" Kallon da tai masa shi da kansa sai da yaga rashin da cewar maganan sa,ko ba komai SUHANA yar uwarta ce kuma JININTA bai kamata ya rik'a nuna mata tsana karara haka a gaban taba. "Wa fa akan wa kake magana?" ne ta tambaye sa fuskar ta d'auke da wani murmushi mai CIWO, rungumeta yayi ya kasa ce mata komi domin tunda wuri ya gano kuskuren shi. "Dan Allah ka sassauta mata ka daina nuna mata baka sonta saboda idan BABU NI ITACE ZATA MAYE MAKA GURBI NA" "Allah ya sauwake min" ya fad'a tare da hankad'e ta daga jikinsa tayi wani irin baya zata fad'a kan tsohon cikin dake jikinta, cikin wani irin zafin nama ya fisgota ta dawo jikinsa kafeshi tayi da wani irin kallo kafin ta fusge jikinta ta tashi ta barshi anan. Ya k'ure ta Kennan? Ya ayyana hakan a ranshi take ya durk'ushe anan tareda dafe kansa cikin takaici sam Deenah bata ganewa batasan wacece SUHANA ba, batasan tantirancin SUHANA ba shiyasa har take iya fushi dashi dashi akanta tunda yake bai tab'a ganin mara mutuncin yarinyar sama da SUHANA ba bai tab'a jin tsanar mutum kamar SUHANA ba a rayuwar sa ya jima sosai a wajen yana saka da warwara. Niko ina fitowa daga gidan anty Deenah nasawa raina cewa nida gidanta har abadan saboda bana k'aunar ganin samad ko kad'an a rayuwata, ta fad'a tana hararan gidan kamar gidanne yayi mata laifin. Kanta tsaye gidan su Sameer ta nufa yana ganinta ya tare ta cikin farin ciki ya rungumeta tsam a jikinsa yana sakin wata ajiyar zuciya "SUHANA jiya kin barni cikin tashin hankali da damuwa dan Allah SUHANA ki taimaka ki AURENI wallahi zanyi miki duk abinda kike so" K'wace jikinta tayi daga nasa tare da galla masa wata katuwar harara tace "amma baka da hankali Sam, sau nawa zan fad'a maka cewa babu aure a tsakanin mu wannan ya zama na farko da k'arahen da zaka kumayi min zancen wani aure idan ba hakaba to wallahi saina yanke duk wata alak'a dake TSAKANINMU kaji na fad'a maka" ta k'arasa tana kuma galla masa wata hararan da tafi ta karko tare da sakin wani mugun tsaki ta zari mayafinta da jakkar ta da ya yasar mata anan gefe ta gaba ta barshi dafe dakai. Allah ya sani yana k'aunar yarinyar sai dai yarasa dalilin dayasa koda wasa bata k'aunar yayi mata batun aure baisan dalilin ta nayin hakan ba ko kuma shine bata k'auna? MAMAN ISLAM CE Yawan comment yawan typing insha Allah NA MIJI K'UDAN ZUMA BY MAMAN ISLAM BISMLLAHI RAHAMANIR RAHIM ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION☀️ 😘 Page 2 Ita ko SUHANA tana fita a gidan wayar ta yayi k'ara, tayi saurin d'auko wa a Jakarta tana dubawa taga hajiya cemahaifiyar ta sai da gabanta ya fad'i, sai kawai taki d'agawa ta maida wayar Jakarta ta bayan ta sakata a silent. "SUHA SUHA" ta tsinci muryarsa daga bayanta yana kiranta da sunan da ya saba kiranta da shi sai da ta daidaita nutsuwar ta kafin ta juyo fuskar ta a d'inke babu alamun wasa a cikinta, sam baya fushi da halinta hakanan Allah ya jarabta masa wata fitanannen SONTA sai da ita kuma sai jan sa take ak'asa iya son ranta sai yayi sa'ar gaske sannan zata kalleshi har ta tanka masa. "Hajjaju na daga ina haka?" hararan sa tayi tace "daga inda ka aike ni malam ban guri na wuce" "Allah ya huci zuciyar sarauniyar kyawawan matan duniya" bata san sanda wani murmushi ya k'wace mata ba sai dai bata yi ba ta barshi a zuciyar ta. "Haba kyakykyawata masoyiya ta bugun zuciya ta abar alfahari na tunda nake ban tab'a ganin matar da yanayi na yake sauyawa ba idan na ganta saike kece wadda idan ban ganki ba nake kasancewa cikin damuwa da tunani kuce farin ciki na dan Allah SUHANA ina rok'an alfarma ki taimaka ki tsaida ni amatsayin mijin ki, zaki farin ciki zaki alfahari da kasancewana mijinki abin Alfa"""""" dakata malam dan Allah" Ta fad'a cikin d'acin rai da wani mugun bak'in ciki,haka sauran ma suke fad'a mata haka suke riritata su tattala ta su nunawa duniya babu kamarta su rik'a ambatar itace duniyar su, saidai kuma da zaran ta shiga gidan ta zama nama ta zama wata irin baiwa mara gata da 'yanci ita ko ME ZATACE DA MAZA??????? Jin hawaye na shirin sauko mata yasa tayi saurin juyawa Khalil baya, bata so yaga raunin ta tayi alwashin babu wani D'A NAMIJI da zai k'ara ganin raunin ta bare ya mai da ita garaigaransa takawa tafara yi cikin takun ta mai tafiya da imanin duk wani na mijin dake tak'ama da isashiyar lafiya. Kafeta da ido Khalil yayi yana K'are mata kallo yayin da zuciyar sa yake wani mugun bugu damuwar sa fargabar sa tashin hankalin sa SUHANA tace bata sonsa bazata aure shi ba wannan ranan ya tabbatar saidai ya tsinci kansa agadon asbiti dan ya tabbatar da cewa zuciyar sane zai buga kowa ma ya huta. Yana ci gaba da kallon ta da mamakin ta har ta b'ace wa ganinsa, wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya d'aga hannunsa sama "Allah ka mallaka min wannan baiwar taka badan ni ko halina ba badan na'isaba dan fiyayyen halitta sallallahu alaihi wassalam. Hakanan taji kalaman Khalil sun b'ata mata rai wai me yasa MAZA suke haka ne me yasa suke da son kansu tana mamakin yadda na yaudara da son zuciya yake tasiri a zuciyar mata, tana tausayin duk wata yarinya da take rawan kai akan wani d'a NAMIJI wanda basu san cewa duk d'aya suke ba duk kurane da fatar akuya "Uku fa uku, uku" ta fad'a tana k'ara maimaitawa tare da d'aga 'yan yatsun ta guda ukun, sai kuma wasu irin zafafan hawaye suka zubo mata "Allah ka dubani Allah ka zama gatana Allah kazama gatana Allah kazama gatana haka ta rik'a maimaitawa cikin wani irin fitinannen kuka, kasa zuwa inda zata tayi kawai ta nufi gida duk da kasancewar bata so komawa gidan a wannan lokacin ba saboda gudun abinda zata tarar a gidan. Tana shiga babban falon ta ci karo da hajiya wacce take zaune a kujeran dake kallon k'ofar shigowa, ido hud'u sukayi da hajiya wacce ta kafe SUHANA da ido wadda har lokacin idanunta basu daina tsiyayar da ruwan hawayen ba, wani irin mugun fad'uwa gabanta yayi ganin irin kallon tsanar da mahaifiyarta take mata wanda yake haddasawa rayuwar ta bak'in ciki da tashin hankali wanda yasa sam take jin zuciyar ta babu dad'i har taji gwanda ta bar gidan ko zata samu sassauci abisa halin da take kasan cewa a ciki, duk kuwa da kasancewar halin ZARGIN da take kasancewa a idon iyayen nata sum sum tayi zata wuce, wata uwar tsawa da Yaya maleek ya buga mata batasan sanda ta tsinci kanta a gabansa tana hawaye ba " daga gidan uban wa kike?" Ya tambaye ta cikin d'aga murya, cikin inda inda tace "gid an anty Deenah "K'arya kike munafukan banza daga dai yawon iskancin da kika fi kwarewa akai kike" MAMAN ISLAM CE *NAMIJI K'UDAN ZUMA* Page 3 Ita ko SUHANA wani mugun kallo ta watsawa Yaya maleek tace "nasan abokin ka kake tayawa k'ina bazaka tab'a burge ni ba sai ka taya shi kun had'u kun hak'a rami kun binne ni da raina. "Ni kike fad'awa magana SUHANA?" "Eh Yaya da abinda zakayi ne?" "Kindai ci darajan hajiya da wallahi sai na taka kanki anan wajen" wani mugun kallo ta watsa masa ta wuce d'akin ta tana ci gaba da matsar hawayen ta. Tana barin wajen ya Maleek ya dafe kansa yana binta da kallo har ta shige "Allah ka bayyana mana abinda yake damun wannan baiwar taka, idan ma wanine yake jifan ta da wannan BALA'in Allah ka maida masa da abinsa kansa" ya shafa tare da sauke ajiyar zuciya sai kuma ya mik'e ya nufi d'akin hajiya yayi mata sallama ya wuce gidansa. Ita ko tana shiga d'akin ta, tayi wurgi da d'an kwalin ta da mayafinta da jakar duk anan tsakar d'akin sannan ta haye saman gadonta ta takarkare ta saki wani kafirin ihun da yasa hajiya dannowa aguje duk kuwa da ciwon k'afar da take fama da shi. Ganinta a zaune idanunta a soye dan tuni ta goge hawayen ta gyara fuskar tas, kallon ta hajiya tayi cikin takaici tace "kai SUHANA kai SUHANA Yanzun fisabilillahi SUHANA me nayi miki da zafi da yasa bakyason kwwnciyar hankali na?" Fashewa SUHANA tayi da kukan gaske tace "to ni nayi miki magana ne hajiya ko nace wani abu duk kukabi kuka tsaneni keda d'anki anty Deenah ce kawai tasan matsala na ita ta damu dani take amsar uzurina take jana ajiki take bani shawara a maimakon ke hajiya me nayi da zafi wanda yasa kika watsar da tarin k'aunar da kulawar da kike min ko dan kaddara ya giftawa rayuwa ta shine kike fushi da ikon Allah?" Ita kanta hajiyan bata san sanda hawaye ya zubo mata ba har ga Allah tana matuk'ar tausayawa autar ta sai dai kuma sauran yaran ta suna ganin ita ke d'aure wa SUHANA shiyasa take yadda taga dama, k'arasa wa tayi kusa da SUHANA tajata jikinta ta rungume tana d'an bubbuga bayanta tace. "SUHANA bazaki gane bane abinda kike aikatawa kina sa mana zargin ki da damuwa mai yawa dukanmu muna tunanin ko kina fita ki zubar mana da mutunci awaje ZARGIN KI MUKE SUHANA ba iya 'yan uwanki ba harda ni mahaifiyar ki" Kallo SUHANA tabi hajiya dashi wanda yake cike da wani k'unci da tsananin BUGUN zuciya tace "hajiya?" "Eh SUHANA haka ne ina ZARGIN KI domin abubuwan da kike dole a d'iga miki ayar tambaya" Take yanayin SUHANA ya sauya ta koma wani irin fitinannen mugun yanayi tareda k'arfin da yakanzo mata idan ranta ya b'aci cikin d'aga murya tace "cikani hajiya kar nayi miki illah" K'ara k'ank'ame ta hajiyan tayi tace "SUHANA ai ni bana tsoron kimin illah kuma a ko wane yanayin kike ni bazan gujeki ba amma ko wace uwace a matsayin Ni DA KE SUHANA dole ta zargeki dan haka SUHANA Deenah ne kawai ta yarda dake duk cikin mu" Wani irin kuka SUHANA ta fashe dashi tana tason kwatar jikinta daga hajiya ta k'arfin bala'i,amma ta kasa domin ba k'aramin rik'o hajiyan tayi mata ba sannan kuma ita d'in irin k'arfafan matannan ce dan haka duk sanda SUHANA ta shiga irin wannan yanayin ko Maleek baya iya rik'e ta sai dai hajiyar. "Ni ki cikani gidanki zan bar miki wayyo Allah na Abba na mai yasa ka tafi ka barni da wanda basa k'auna na, ni ki sakeni". Ta karashe da wani irin fitinannen kuka tareda wani irin fisge fisge, k'ara rik'e ta hajiyan tayi da kyau tana tofa mata addu'o'i, da k'yar ta samu bacci ya d'auke ta. Shiru hajiyan tayi tare da zuba tagumi tana kallon SUHANA cikin wani irin tausayin ta ta rasa abinda yake damunta tun bayan rasuwar ANWAR bata k'ara ganewa SUHANA ba. Tunda ta kama bacci bata farka ba sai bayan sallar magriba, sanda ta shiga ban d'aki saida ta fara wanka sannan ta d'auro alwala Bayan ta idar da sallah bata bar kan abin sallar ba saida ta gabatar da sallar isha kafin ta nad'e abin sallar ta koma, gaban merrow ta hau shafe shafen ta, kwalliya ta tsantsara ta gani a fad'a, ta bude' wadrop d'inta wasu irin k'ananun kaya ta d'auko ma asu masifar d'aukan hankali ta saka ta taje dogon gaahin kanta tayi donut dashi yai wani irin tumtum saboda yawa da tsayin sa, wani d'an siririn mayafi ta yafa kalar kayan ta k'ofar bayan gidan tabi ta fice batare da ta bi ta babban falo inda su hajiya ke jiranta dancin abincin dare ba MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION Page 4 Babu wani jinkiri ta fad'a cikin motar dake fake a k'ofar gidan wanda daman ita yake jira ya figa da wani irin mugun gudu. Tunda suka fara tafiya yake duban ta cikin tsantsar shi'awar ta sai dai wannan kadarar tafi k'arfin shi domin bala'in ta ya wuce da sanin sa ta wuce da tunanin k'ananun kwari irin sa. Ita kama bayan ta, ta kwantar jikin kujeran tana fesar da wata iska mai zafi har yau ranta a jagule yake ta rasa me ta tsarewa SAMAD da yai mata wannan tsanar tun tana daurewa har ta fara jin tsanar sa har ma fiye da yadda ya tsane ta, tasha alwashin ta daina raga masa ko kad'an duk sanda ya shiga hanyar ta sai taci mutuncin sa fiye da tunanin sa rashin mutuncin da zatai masa ko kare baya ci ba. Da haka suka k'araso club d'in da Na'im ya kawo su wanda kusan duk sanda SUHANA ta tsinci kanta cikin b'acin rai nan take zuwa tare da Na'im tayi mankas abinta ta koma gida a buge tatul. "Kai Annur maza je ka kira SUHANA tazo muci abinci" da sauri Annur ya nufi d'akin SUHANA, wayam babu ita take yaron yaji ransa ya b'aci muddun babu SUHANA a gida a irin wannan lokacin to bata da wajen zuwa sama da wajen tam bad'ewar ta dan haka cikin fushi ya koma ya sanar da hajiya. Dama tunda wannan abun ya faru tsakanin ta da Malik tasan za'ai haka itama ba k'aramin b'aci ranta yayi ba abincin da basu samu sunci ba kenan ita da Annur domin har yafi mahaifiyar tasu shiga damuwar halin da 'yar uwar tasa ta jefa kanta na banza. Acan club kuwa suna shiga Na'im yasa aka kawo musu kayan ciye ciye kala kala suka ci suka sha sannan ta kora da kayan da suke d'ebe mata kewa sosai yau ta bugu fiye da ko yaushe tun daga zaunen ta fara layi ganin haka yasa Na'im ya rungumeta a jikinsa suka shiga filin rawar, take filin yazama nasu ita da Na'im domin duk ranar da Na'im da SUHANA suka shiga filin rawa babu wanda ya isa ya shiga domin bala'in su ma ya ishi mutum. Wata irin rawa suke sunayi suna fad'uwa domin dukansu babu mai kwarin kirki sun riga da sun bugu da yawa. Yau kam bak'in cikin yafi na ko yaushe ga SAMAD domin ji yake kamar ana daddatsa zuciyar sa ganin SUHANA rungume a k'irjin wani k'aton d'an iska, cikin d'acin rai ya k'arasa wajen ya wani irin finci kota ta fad'a jikin shi yayi saurin janye ta tare da d'auke ta da wani bahagon mari, ta d'ago narkakkun idanunta ta watsa masa cikin muryan mashaya tace "Au ashe kaine jakin banza shine ka mare ni wallahi sai na rama SAMAD wai ina ruwan ka dani da kake zuwa kullum ka katse min jin dad'i ne Allah sai na rama mugu kawai" tana maganar ne tare da son d'aga hannun ta wanda yai mata nauyi tsabar buguwar da tayi duk irin yadda taso d'aga hannun ta kasawa tayi sai kawai ta fashe da kuka tace "Allah ya isa kawai mugu ka katse min jin dad'i na." Shi kansa bai san sanda wani irin zafafan hawayen da ya zubo masa ba ganin tana neman zamewa k'asa yajata ya rungumeta a jikinsa yayin da hawayen sa suke zuba saman kanta wanda dama tuni d'an siririn mayafin da ta yafa yayi nasa wajen. Kallon sa tayi da idanunta da sukayi mugun rinewa tsabar buguwar da tayi cikin muryan nan dai ta mashayan tace "dan nace Allah ya isa shine kake kuka? to na yafe daina kukan ta samu da k'yar ta d'aga hannu tana share masa hawayen, kasa magana yayi tsabar bak'in ciki ya d'auke ta cak ya nufi motar sa da ita ya sa ta a baya sai shirme take zuba masa ya figi motar da mugun gudu Pls manage bana gari yanzuma yakicewa nayi MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 5 A kuntace yake tuk'in cikin wani irin takaici badan yana gudun kar Deenah tayi masa wani fassara akan k'anwar taba da babu abinda zai hana yau ya mik'awa Deenah ita a wannan tambad'en taga yarinyar da akullum suke samun matsala da ita akanta sai dai baya fatan abinda zai daga hankalin salihar matar tasa musamman a irin wannan halin da take ciki. Ya rasa dalilin da yasaka ya kasa k'yale SUHANA taje tayi RAYUWAR ta kamar yadda take buk'ata take kuma jaddada masa ya rasa dalilin da yasa duk wani wajen lalacewar ta sai ya bita, daga yau yayi alk'awarin har abada bazai k'ara binta ba insha Allah. Nikam nace bazaka iya ba Samad domin baka da wannan zuciyar. Har suka kawo gidansu tana tunb'elan surutai, tace wannan tace wancen shi dai bai tankata ba tuk'in kawai yake cikin d'acin rai. Ta k'ofar da ta fita yayi faking dan baya buk'atar mai gadi ya ganshi, k'ofar kuwa tananan a yadda SUHANA ta barta babu wanda ya rufe domin sunsan tanan zata dawo, yanzu ma kamar d'azun kasa tashi tayi daga zaunen da take dole ya tallafo ta jikinsa. Yana bud'e k'ofar sukaci karo da Maleek ai kuwa yayi bala'in d'aure fuska dan baya buk'atar jin wani abu daga Maleek d'in, ganin yadda yai kicin kicin da rai yasa ya b'alla masa harara yace"wahalallen banza inda SUHANA ce kace zakasa abinta a ranka itace ajalinka wallahi" Shima wata muguwar harara ya wurga masa tare fa k'ara tamke fuskar yace "ina ruwanka inta kasheni ne waikai Maleek me yasa kake hakane SUHANA fa'yar uwarmuce idan akace muna juya maka baya irin haka rayuwar ta k'ara tan'arb'arewa zatayi" "Nidai ban maka alk'awarin shiga harkan wannan fetsararriyar yarinyar ba kai da kake ganin zaka gaka gata nan kaine ciwon zuciya zai kama a banza". Tsaki kawai yaja batare da ya tankaba ya tura k'ofar falon cikin fargaban karsu had'u da hajiya, anyi sa'a kuwa lokacin ta shiga raka Annur d'akin shi dan haka ya lallab'a ya kaita d'akin ta. Har ya juyo yaji ta rik'e masa riga, juyawa yayi yana kallon ta cikin buguwa tace "Kai Na'im ina koidin d'ina wallahi kasha sai munyi burauba dakai" wani irin runtse idanunsa yayi wani irin fitinannen abu na tsarga masa bai iya yace komai ba ya k'wace daga rik'on da tayi masa ya juya ya fice da sauri zuciyar sa na suya. Yanzun ma babu kowa a falon sai Maleek hakan yasa ya fice batareda ko kallon Maleek d'in ya kumayi ba. Allah sarki lokacin da yaje gida tuni Deenah tajima dayin bacci, dan haka shima wanka yayi ya kwanta a bayanta tare da rungmota jikinsa duk uwar yunwar dake damunshi bak'in cikin SUHANA bai barahi ya karb'i ko ruwa ba. Washegari da safe garas ta tashi kamar ba itace ta rik'a tunb'ele jiya da dare ba duk lokacin da ta yi shaye shayen ta to sai ta makara wajen sallar asbah yau ma hakance ta kasance dan sai k'arfe goma ta farka cikin sauri ta fad'a toilet wanka tayi da alwala sannan tazo ta gabatar da salla da karatun alkur',ani mai girma, tana cikin karatun cikin zazzak'ar muryan ta taji kamar motsi a bayanta, tana juyawa sukayi ido hud'u da ya Maleek dake zaune saman lokar gadonta yana binta da wani mugun kallo. Harara ta galla masa tare da had'e rai tana kai aya ta rufe k'ur anin ta mik'e ta fice falon gidan inda ta hango hajiya da Annur zaune saman kujera suna kallo, gaida haijyan tayi, ta amsa mata kadaran kadahan yayin da Annur ya gaidata shima babu walwala a tare dashi dan yana matuk'ar jin d'acin abinda yayar tasa take aikatawa. "Ke dan uwarki har ni zan shiga d'akin ki dan muyi magana ki wani hahareni ki fito ki barni sa'anki ne ni? Harara ta kuma galla masa harda murgud'a baki ta juyo tadubi hajiya tace "kiwa d'anki magana babu ruwan shi da harkana babu ni babushi idan ba haka ba wallahi saina d'auki matakin da sai ya girgiza kowa a gidananan" Har Maleek ya hayayak'o zai maketa Hajiya ta kalleshi take ya rissinar da kanshi k'asa yana bawa hajiyan hak'uri. Itako SUHANA dake wata azzalumar yunwa take ji kanta tsaye kicin ta shiga dan samawa kanta abinda zataci dan a cewar ta tadaina cin abincin Hajiya dan kar tayi mata asiri🤣🤣🤣(lallai SUHANA kina ruwa) Bayan ta gama cine ta dawo falon ta zauna tana wani ciccin magani "SUHANA" Hajiya ta kirata cikin raunin murya d'ago manyan idanunta tayi ta sauke akan Hajiyan batareda ta amsaba "kin kuwa san cewa nice na tsuguna na haifeki?" Kanta tsaye tace "ina tantamar haka Hajiya" Da madaukakin mamaki Hajiya da Annur suka kafeta da ido kafin Hajiya ta d'ora da cewa cikin raunin murya "tunda kike a gidan nan kin tab'a ganin mahaifin ki da wata matar bayan ni har ya koma ga mahaliccinsa?" "To Hajiya na sani ko tsinto ni kukayi yasa kike nuna baban banci tsakanina da'ya'yanki?" "Innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA ni kike fad'awa magana kanki tsaye?" "Duk yaran gidannan wa kikasa aka marya jaki sama dani kullum ayi ta dukana kamar jaka kiyi ta nuna banbanci tsakanina da yaranki" "SUHANA kema 'yatace JININA mafi soyuwa agareni" ."to in gani a k'asa ta fad'a tana mik'ewa ta shige d'akinta yayin da Hajiya da Annur suka bita da kallo kamar idanunsu zai fad'o. Wani zumbulelen hijab ta sako akan riga da wandon dake jikinta wanda ganin damarta nema yasaka ta sanya hijabin in bata ga damaba tana iya fita a haka. "Ina kuma zaki da safen nan SUHANA?" Ta tsinkayo muryan Hajiya a bayanta. Juyowa tayi ta d'an kalli Hajiyan tare da sakin murmushi kafeta nayi da ido sanda tayi murmushin ashe haka yarinyar nan take da masifar kyau idan tayi murmushi "Hajajju na kenan zanje wajen khaleel ne ko zaki bani aron Annur ya rakani?" Girgiza mata kai Hajiya tayi batareda ta iya magana ba tana kallon SUHANA ta fice daga gidan batare da wani damuwa tattare da itaba. Juyawa Hajiya tayi kawai sukayi kicib'us da Maleek wanda ya gama sauraron su tas harara ta galla masa cikin b'acin rai tana k'ok'arin tureshi ta wuce ya dafe ka fad'unta da kyau cikin tsantsar tashin hankali yace "dan Allah Hajiya ta kiyi hak'uri ki yafemin" Cikin rauni tace"Maleek kafasan duk wannan abun da SUHANA takeyi fad'a da hayaniya k'ara tunzura ta yakeyi amma ku bakwa ganewa duk cikin ku Deenah ce kawai take tausaya min akan halin da yarinyar nan take ciki" "Kiyi hak'uri Hajiya insha Allah daga yau nima na fita harkanta indai hakan zai faranta ranki" "Me kake nufi da hakan aikin banza kenan wato ku har kullum bakwa ganewa ko to Maleek idan ka fita a harkan SUHANA sai me Allah bazai tab'a barmin ita a hakaba dole wataran zata nutsu kamar ba itaba" "Kiyi hak'uri dan Allah Hajiya" daga haka ya juya ya fice daga gidan gaba d'aya. MAMAN ISLAM CE Ina k'ara fad'a muku yawan comment yawan typing By by NA MIJI K'UDAN ZUMA BY MAMAN ISLAM ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 6 SUHANA na fita gidan Deenah ta nufa inda ta iske Samad a haraban gidan suna buga kwallo dake lahadi ne baya fita aiki, da sauri Khalid ya saki boll d'in ya nufo SUHANA da gudu yana fad'in "yeeee ga mummy ga mummy saurin durk'usawa tayi tare da bud'e masa hannunta kamar dai yanda take masa, ya kuwayi saurin shigewa jikinta yana sakin dariya. "My boy ina mammy?" "Daddy ne yace mu k'yale mammy tayi bacci mu muzo tanan muyi wasa" "Ok maza jeka salallab'a a hankali kaga ko ta tashi amma fa kada kayi motsi me k'arfi dan kakar kasaka little babynka kuka" "To mammy"yaron ya fad'a tare da juyawa da mugun gudu Daddyn nasa na kiransa amma sai cewa yayi "bazan tasheta ba Allah kada little babyn da zaku siyo min yayi kuka" Wani irin mugun kallo ya watsawa SUHANA batare da b'ata lokaci ba itama ta antaya masa wanda yafi nata ta fara takowa inda yake cikin d'acin rai da mugun d'aure fuska har saida yayi shakkar hakan amma ya dake yana kallon ta tare da zura hannunshi cikin aljihun wandon jikinsa idanunsa kuma akanta yana son ganin iyaka gudun ruwanta, saida tazo dab dashi ta kuma sakar masa wani mugun kallo tare da sakin wani arnen tsaki abinda ya mugun b'ata masa rai kenan ya kafeta da wani mugun kallo cikin tsantsar damuwa sai dai bai tanka mata ba har ta bud'e baki dankanta ta fara magana tana wani yatsina kamar tanayi da kashi "Wannan shine karo na farko da k'arshe da zance ku fita a harkana Samad kaida abokin ka bana sonku bana k'aunar ku kamar yadda nima baku k'auna ta dan Allah ku barni inyi rayuwana yadda nake so tunda ai naga kabarin mu ba d'aya ba na fahimci kaike k'ara zuga abokin ka yana K'ara addabamin to ka sani wallahi ina da yan daban da zansaka suyiwa mutum kafirin duka" daga haka bata k'ara ba ta wani bangaje shi ta wuce tana wani shegen tafiyar da ka gani kuma kasan na shak'iyanci ne. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yana busar da wani zazzafan numfashi ya godema Allah dayasa bata gane shike maidota gida daga mashaya ba da tujarar nata sai ya ninka haka. Karo sukaci da Khalid ya danyi mata alamar ta kawo kunnen ta, ai kuwa k'asa k'asa tayi da kunnen ta dai dai bakin sa yace "mammy bata farka bacci take idan nataso ta bazaki fad'awa Daddy ba?" "Zan fad'a masa mana kuma little baby zaita kuka arasa mai rarrashin sa dominfa shi yake sata bacci" "Allah mummy?" ya fad'a yana zaro manyan idanunsa wanda suke matuk'ar kama dana SUHANA, dariya SUHANA tayi tare da sumbatar d'an k'aramin bakinsa tace "kaga wannan bakin naka ya rage magana maza muje nayi maka wanka" ai da gudu yayi d'akinsa tsab kuwa SUHANA ta wanke shi ta kimtsa shi cikin wasu fararen kaya Kal sun kuwa masifar yi masa kyau ya fita da gudu wai zaije ya nunama daddy, murmushi kawai tayi tare da girgiza kanta Allah ya sani tana matuk'ar k'aunar d'an 'yar uwartata hakanan duk cikin yayyenta tasu tafi zuwa d'aya da Deenah dan itama tana tsananin sonta, d'akin ta gyara Kal har band'aki ta wanke hakama falon sannan ta shiga d'akin Deenah ta gyara mata band'aki cikin nutsuwa dan gudun kada ta tadata ganin sha biyu tayi ta shiga kicin nanma ta gyara sannan ta hau dorama mata girki shinkafa da miya da salad a duniya Deenah tana matuk'ar son wannan abincin ko tuwon shinkafa miyar d'anyen kub'ewa, bayan ta gama takai dining ta gyara komai sannan ta koma ta kuma kimtsa kicin d'in ta fito falon tai karo da Deenah har tayi wanka harara ta galla mata ta fice batare da tayi mata sallama ba. Murmushi Deenah ta saki tare da addu'ar shiriya ga 'yar uwartata tareda yabama tsantsar tsabta irin na SUHANA domin ko yanzu ta gama gyaran gida tayima Khalid wanka muddun SUHANA zata zo sai ta sake. A haraban gidan ta had'u da Samad da Khalid yana ganin SUHANA yace"mummy zan biki"cikin d'aga murya tace "ba gida zani ba club zanje" "Ke SUHANA wannan wane irin bala'i ne haka Khalid d'in kike fad'a ma clubs zaki?" Harara ta juyo ta makawa Deenah da fad'in "to ki d'auki mataki mana idan kin isa" kafin ta bata amsa idanunta ya sauka kan Samad dake karatun jarida ko da wasa bai nuna yasan me suke tattaunawa ba, take Deenah ta gane inda SUHANA takeson tura sak'onnin ta hakan yasa bata k'ara tankawa ba gudun haifar da wata fitinar kuma. Tana kallo ta juya ta fice cikin wani irin taku Khalid yana kukan sai ya bita ko kallonshi batayi ba. Da k'yar Deenah taja k'afa ta k'arasa kujeran gefen Samad ta zauna tareda zuba tagumi tini idanunta suka cika da kwalla kallon ta Samad yayi shima zuciyar sa babu dad'i dan ya tsani ganin matar tasa cikin wani yanayin sai dai bai tankaba dan yanzu zata juye laifin akanshi Khalid yaja jikinsa yana rarrashin sa. Ita kuwa tana fita kanta tsaye gida ta wuce lokacin Hajiya ta shiga sallar Azhar itama d'akin ta ta wuce tayi wanka da salla sannan ta fito falon nan ta tarar da Hajiyan da Annur har da ya Maleek "sannu da gida Hajiya" SUHANA ta fad'a tana zama kusa da ita. "Dan Allah SUHANA ina kikaje kika bar wayoyin ki a gida?" Yanayin da Hajiyan tayi magana ya bala'in bata tausayi tace"Allah Hajiya ina gidan Deenah ki tambaye ta kiji" wata irin ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da lumshe kywawan idanunta wanda zance a gunta ne SUHANA ta koyi wannan tabi'ar murmushi SUHANA tayi tace Hajiya abinda kike tunani bazai tab'a faruwa ba tunda hakan bai tab'a faruwa daniba ko ga mazajen dana aura" a wani irin fitinannen rud'e Hajiya ta juyo ta rik'e SUHANA tana fad'in "me kike fad'a hakane SUHANA?" Gaba d'aya jikin Hajiya wani irin rawa yake tsabar rud'ani da tashin hankalin da SUHANA ta jefata shi kanshi Maleek mutuwar zaune yayi, tabbas yasan SUHANA bata k'arya bata b'oye komai ta aikata saidai in zasu kasheta ne su kashe amma sai ta fad'i duk abinda tasan tayi ko hakan yasa suke jin haushin tabi'ar tata duk da sun san cewa SUHANA muguwar fitinanniya ce tun tana mitsitsiyar ta. Maganar Hajiya ne ya katsewa Maleek dogon tunanin da ya fad'a hakan yasa baiji me Hajiyan taceba sai dai amsar da SUHANA tabama Hajiyar ta k'arshe ta masifar d'aga hankalin sa hakan yasa ya mik'e a mugun firgice jikinsa babu inda baya rawa ya juya zai fita a mugun fusace Hajiya tace "muddun naji ka d'aga zancen nan ban yafe maka ba Maleek domin hakan zai bawa mak'iyan SUHANA damar sake sabon shiri akanta". Dab'ar Maleek ya zauna a tantagaryan falon yana dafe kansa saiga hawaye"kinsan abinda yake sani kuka Hajiya?" Itama Hajiya kasa magana tayi sai girgiza mata kai da tayi, cigaba tayi da fad'in tsuntar kaina da nake a yanayin da bansan lokacin danake shigarsa ba Hajiya ki faramin addu'a ko zan daina abinda nake sannan ki fad'awa d'anki babushi babu ni da kuma surukin ki" ta fad'a tana hararan Maleek tare da mik'ewa tabar wajen saboda yunwar dake addabar ta da kallon tausayi duk suka bita cikin tsantsar damuwa da tashin hankali. Wai to me SUHANA ta fad'awa Hajiyan da ya firgita Maleek haka? Me Hajiyan ta fahimta game da matsalar 'yar tata? Shin SUHANA tana sani take aikata wannan abubuwan ko kuwa dai bata sani ba?" Shin meke tsakanin SUHANA da Abdul Samad mijin 'yar uwarta Deenah? duka wannanan amsoshin nima nake son nemo muku sai ku biyoni sannu a hankali dan samunsu Daga alk'alamin MAMAN ISLAM NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 7 "Hajiya dama kinsan da wannan amma kika k'yale yarinyar nan haka?" Girgiza masa kai tayi tace "ko d'aya Abdul Maleek duk dana san cewa SUHANA muguwar fitinanniya ce amma ina mamakin yadda al'amarin ta yake k'ara tan'arb'arewa amma yanzu akan wannan maganar na fara hango wani haske" Wani irin nannauyan numfashi Abdul Maleek ya sauke yace "Hajiya ko zamu sameta da maganar dan samo bakin zaren?" "Baka da hankali Abdul Maleek tayaya kake tunanin zamu tari mutumin da bamu tabbatar da abinba zargine kawai kaga duk ba wannan ba abinda nake so dakai kawai ka taya 'yar uwarka da addu'a insha Allah komai zaizo da sauk'i" Suna cikin tattaunawa SUHANA ta fito cikin shigar wasu matsatsun riga da wando ruwan kwanduwar kwai ta d'ora wata shara sharan a baya ruwan madara akan kayan ta d'an dubi Hajiyan kad'an tace" Hajiya ni zan wuce office ana nema" "Kai SUHANA dan Allah yaushe ranonki da office Abdul Maleek nefa kawai yake duka aiyukan naki danashi shine zaki tsiro da wannan?" "Nidai wallahi sai naje Hajiya"ta fad'a tana hararan Abdul Maleek da ya kafe ta da kallon tausayi, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "sai kin dawo SUHANA Allah ya tsare amma dan Allah karkiyi dare" Murmushi SUHANA ta saki tare da karasawa ta sumbaci goshin Hajiyan tace "amen Hajiya Allah ya tsone idon mak'iyan da suka shiga tsakanin mu" Itadai Hajiya bata tankaba tunda tasan dawa SUHANA take dan fitinar ta yawane da ita, Allah sarki shi wanda take dashi din ma bai nuna yasan dashi take ba domin kansa ma yana k'asa. Da gasken office d'in taje amma batayi cikakkiyar awa gudaba tabaro can gidan Hajiyan Anwar ta nufa kamar yadda take zuwar mata jifa jifa, yaudai Hajiyan ba fitina take jiba dan haka suka gaisa da SUHANA a mutunci suka d'an taba hira kad'an tana shirin fitane Na'im ya shigo ko kallonshi batayi ba bare ta nuna tasanshi hakan kuwa yayi masa zafi amma bai kula ba saima kallon Hajiyan tasa suka wani irin inkiya da sam SUHANA bata kula ba Na'im yasaki wani shegen murmushi ya juya ya fice kamar yadda Hajiyan tayi masa alama da ido. SUHANA kuwa bata baro gidan ba sai bayan sallar la'asar,a maikamkon tayi gida kamar yadda Hajiyanta ta rok'a kanta tsaye gidan su Sameer ta nufa tana zuwa taga d'akin sa a rufe sai ta juya da nufin komawa ido hud'u sukayi da Abdul Samad, batasan lokacin da ta dafe kanta ba aranta tace wannan wace irin masiface mutumin yake nema dani dan bala'i duk inda zani kana biye dani kamar wani jela wallahi sai nasa anyi min maganin ka tunda naga kana neman wuce matsayin ka dad'in abinma ba ni kake aure ba yayata kake aure bare ka hanani rawar gaban hantsi, azahiri kuwa wani mugun kallo ta watsa masa tare da sakin tsaki ta rab'a ta gefanshi har tana bangaje shi ta wuce abinta. Da kallo ya bita har ta fice daga layin zuciyar sa na wani irin tuk'uk'in bak'in ciki wayar sa ya zaro daga aljihun ya dannawa Deenah kira tana d'agawa yace "daga yau Deenah babu ni babu SUHANA kada ki k'ara sakani bin duddugin ta tunda ni ba d'an aikin ki bane" daga haka ya kashe wayar bai jira cewar ta ba ya juya a fusace ya bar wajen. Deenah kuwa dafe kanta tayi cikin damuwa a sarari kamar tana gabanta tace "kai SUHANA kai SUHANA dan Allah wai so kike sai kinga bayan mu?" Saiga wasu hawaye nabin kuncin ta. . SUHANA kuwa daganan kasuwa ta wuce tayi cefanen abinda zata buk'atar ta dan ta jima bata cin komai daga Hajiya ko sauran yan uwan ta wai kada suyi mata asari (nace ikon Allah SUHANA lamarin naki azimunne). Sanda ta shiga gidan babu kowa a falon sai Annur tace "kai Annur ina Hajiya?" "Tana kicin" daga haka sai ta juya kicin d'in inda Hajiya ke kad'a miyar d'anyen kub'ewa wanda tayi musu tuwon semo" Hajiya ki fad'awa Abdul Samad ya fita hanyana idan ba hakaba zan yaga masa rigar mutunci wallahi?" "Oh ni safiya naga ta kaina wai SUHANA dan Allah me yake damun kanki ne nidai na rasa wannan abu tsakanin ki da Abdul Samad wanda da sam babu wanda kuke shiri dashi kamarahi". "Da kikace Hajiya a yanzu babu wanda na tsana sama dashi wallahi" "To Allah ya kyauta" Hajiya ta fad'a tana ci gaba da aikin ta yayin da SUHANA tayi kwafa tabar kicin d'in MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 8 Tana shiga d'aki ana kiran sallar magriba dan haka tashige toilet ta d'auro alwala tazo ta tada salla, bayan ta idar bata ja wata doguwar addu'a ba saboda uwar yunwar dake sakad'ar ta rabon ta da abinci tun wanda tayi da safe taci hakane yasa ta nufi kicin ta d'ebi manyan kifin da ta suyo tazo jikin sink ta wanke da lemon tsami tasa wuk'a ta daddatsa sannan ta d'auraye tukunya ta saka kifin a ciki ta kawo albasa mai yawan gaske ta yanka ta d'auraye ta watsa ta daka tafarnuwa da masoro da cita ta saka indai takaice muku wannan kifin dafa du tayi masa saboda yunwar da take ji komai ta had'a daga k'asa kafin ta kunna gas ta d'ora tukunyar akai bata sa ruwa ko kad'an ba saboda tasan kifin mugun ruwa ne dashi, cikin mintuna kad'an ka'mshi ya gauraye kicin d'in sai ga Annur ya shigo da gudunsa "anty me ake dafa mana ne haka ka'mshi duk ya cikamu?" Harara ta galla masa harara tace "to akwad'aitu badai ci zakayi ba ware ta fad'a tana talle masa k'eya juyawa yayi zungwai zungwai yai waje. Binshi tayi da kallo cikin tausayin yaron Allah ma ya sani tana matuk'ar k'aunar Annur duk wata d'awainiya ta yaron kusan ita tayita sannan akwai shak'uwa mai k'arfin gaske a tsakanin su. Tana gamawa ana kiran sallar isha hakan yasa ta kashe gas din ta shige d'akin ta saida ta fara wanka sannan ta d'auro alwala tazo ta kabbara sallah bayan ta idar da gudu ta nufi kicin badan Hajiya tasan halin ta ba da babu abinda zai hana zuba da gudu itama saboda yadda ta fito d'in. Tukunyar ta d'auko gaba d'aya ta nufi dining da ita "Annur d'ebo min flats a kicin" babu musu yaje ya kawo mata ta zuba ta bashi "kaiwaya" ya d'auka ya mik'awa Hajiya har ga Allah tana k'aunar girkin SUHANA dan har mamakin k'warewar yarinyar wajen girke girke. "Annur taho muci" ta fad'a tana kai wanda ta d'auko bakinta d'auke kansa yayi yana girgiza mata kai alamun bayaci murmushi tayi bata kulashi ba Hajiya ma dake kallonsu tana cin nata kifin murmushi tayi dan taji abinda sukayi d'azu. SUHANA kam batabi takan Annur ba saida ta fara samun nutsuwa sannan ta mik'e ta kamo hannun Annur da yai wani kicin kicin da rai tace "dalla malam taso wai kai me yasa bakasan wasa ba tsokanar kafa nakeyi". Ta zaunar dashi tana tura masa kifin a baki tun yana kau da kai har ya fara bud'e bakin yana karb'a suna cikin cinne suhail ya shigo da gudunsa yana "momma momma gani daddyna ya kawoni da bakizo dani ba" ya fad'a yana hayewa jikin Hajiya "kaga ni d'aga ni kada karyani" "Hajiya nima kibani inci" "Na hanaka tafi ga uwarka can ta baka" "Ni ba yuwa na da ita tazu tak'i zuwa dani Nan" "Itaku babu ruwana da halinku" Suna cikin haka Deenah ta shugo turtsi turtsi da tsohon ciki Hajiya ta bita da kallon tausayi tace "oh ni safiya Deenah har yanzun bazaki hak'ura da fitarnan ba?" "Hummmm wallahi Hajiya suhail ne tunda SUHANA ta baro gidan ya hanamu sakat yana ta rigima shine Daddy yace mu kawo sa" "Kun kyauta ai" Hajiya ta fad'a tana hararan Deenah data nufi wajen SUHANA tana fad'in "me ake cine haka ba a ko kula mutane"harara SUHANA ta galla mata tareda d'auke kai dan tasan wallahi saita kaiwa mayen mijinta wannan kifin dan tafi kowa sanin yadda yake masifar son irin wannan kifin. Ilai kuwa bata bi ta kallon da take mata ba d'ebi tai waje dashi har suka gama suka bar wajen SUHANA ta shige d'akinta ta danna sakata, itama Deenah bata nemeta ba domin tasan bazata kulata ba tunda tasan tabawa makiyinta abinta MAMAN ISLAM NA MIJI K'UDAN ZUMA Page 9 Washegari babu inda SUHANA ta fita zama tayi a gida tayiwa Hajiya kwalema tsab ta gyare mata d'aki ta goge ya koma Kal Kal dan SUHANA akwai lafiyar tsafta. Ita kanta Hajiya tayi mamakin rashin fitar SUHANA musamman rana irin ta yau litinin wadda SUHANA ke k'aryar ta yafi office tayi tafiyar ta yawon d'aukar maganar ta amma yau sai taga ta kashe wayarta ma gaba d'aya ita dai Hajiya bata tanka mataba har rana ta d'an d'aga wajen sha d'aya taje tayi wanka ta dafa indomie ta d'an ci kad'an da bai dameta ba d'akin ta ta koma tayi kwanciyar ta bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba daita. Hajiya kuwa zama tayi a falo tana mamakin abinda ya hanata fita arana irin ta yau da ko mutuwa zatayi wajen ganin ta hanata fita muddun ta sanyawa ranta to wallahi saita fitan. Har Hajiya tagama abincin rana SUHANA bata farkaba saida ga lokacin salla na neman wucewa ne taje ta buga mata k'ofar ta d'an motsa tana addu'ar tashi daga bacci tayi mik'a gami da salati da gudu tayi bayi tayi wanka da alwala tazo ta kabbara sallah, Bayan ta idar bata ja wata doguwar addu'a ba tayi saurin k'arasawa gaban merrow ta hau shiri a gaggauce sam yau so tayi dama sai k'arfe biyu zata fita sai kuma gashi har biyu da kwata bata fitan ba. Cikin wani dandatsetsen less pink wanda yaji stone sai walwali yake ta shirya ba d'an k'aramin kyau tayi ba duk da kasancewar ta ba mai yawan son fenta fuska ba amma takanyi wani irin sihirtaccen kyau a duk lokacin da tayi iya abinda take ganin ta cancara kwalliya wato shafa powder da lipstick shikenan sai kuwa kwalli da yakewa idanunta masifar kyau. Afalo ta samu Hajiya tana duba wani littafin addu'o'i "Hajiya ina Annur?" Dag'owa Hajiya tayi jin fitinannen k'amshin dake tashi wanda hakan ke nuna mata SUHANA fita zatayi dan tasanta ko a gida take mayyar turarece tun tana'yar ficiciyar ta turarukan su suke shan bak'ar azaba a hannunta dan muddun ka bari suna taga turarenka to bashi kwana biyu ka dawo ka d'auki kwalbar. "Ina zuwa haka SUHANA?" Hajiya ta tambaya zuciyar ta na falfala gudu murmushi SUHANA ta d'an saki tace "Hajiya na miki tambaya baki bani amsa ba kuma kema kin tambaye ni, to ni office zani" ta fad'a tana d'agewa Hajiya gira "uhm to ga abincin ki ci mana kafin ki fita" Kallonta tayi kafin ta k'arasa kujeran da Hajiyan ke kai ta d'an rab'u da jikin Hajiyan tace "wallahi Hajiyata kina bani mamaki sau nawa zance miki ni bazanci ba gaskiyar magana ban yarda dake ba kada kije ki asurce ni" Idan akwai babban abinda yafi k'untata ran Hajiyan bai wuce kalmar asiri da d'iyar tata ke dangantata dashi amma kuma a d'an k'aramin bayanin da suka samu daga SUHANA shekaran jiya sai taji d'acin baikai na kullum ba dan haka ta d'an yi murmushi tace "ai shkenan SUHANA tunda kina tunanin har uwa mahaifiya zata iya cutar da d'anta" "Ni haifar tawama ina tantama wallahi yadda kuka tsane nin nan nasan ko kasheni akace kuyi keda yaya Abdul Maleek tsab zaku iya" ta fad'a tana hararan gefe kafin kuma ta mik'e tayi waje abinta. Dafe kai Hajiya tayi saiga wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata ta d'aga hannunta sama tace"ya Allah kanaji kuma kana gani babu wanda nasawa ko na zubarwa babu wanda na takawa balle ka kawo min mafita abisa halin da 'yata take ciki wanda nasan ba halin ta bane" ta k'arasa tana shafawa tare da zubowar wasu hawayen. Da gasken office d'in ta nufa tundaga bakin k'ofar sakatariyarta take sanar mata oga ya amshi makullin office d'inta wai zai gwada wani abu dashi' wani dan iskan kallo ta wulla mata tace"wane shegen ne ya baki umarnin bawa wannan banzan makullin office d'ina?" " Kiyi hak'uri ranki ya dad'e dama yana karb'a" "What dama kinsaba bashi kenan wacce irin dak'ik'iyace ke"? "Kiyi hak'uri ran"""''''dallah malama rufemun baki shaahasha kawai" ta fad'a tana aika mata da wani mummunan harara kamar idanunta zasu fad'o kafin a zafafe ta juya ta nufi office d'in Abdul Samad cikin k'unan rai * MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA Page 10 A zafafe ta tura office d'in babu ko sallama sannan sam bata kula da anty Deenah ba wacce tazo kawowa mijinta abincin rana da kanta dan wani lokacin da kanta takan kawo. "Ke SUHANA wannan wane irin haukane zaki wani shigowa mutane babu sallama kamar'yar kafurai?" Sai lokacin ma ta kula da anty Deenah saboda tsabar idanunta sun rufe da masifa harara ta dalla mata tare da jan wani uban tsaki ta d'auke kanta ta mayar kan Abdul Samad tana jifansa da wani mugun kallo ji kake tau Deenah ta d'auke SUHANA da wani mugun marin da shi kanshi Abdul Samad saida ya mik'e tsaye tsabar firgita da k'arfin marin Deenan ta fallawa SUHANA wanda ba komai yaja hakan ba sai tsakin da taja mata wanda kuma inda sabo yaci ace dukansu sun saba da halin SUHANA wanda ta arawa kanta shekaru kusan bakwai Kennan. Cirko cirko sukayi kamar wasu zakaru yayin da zuciyar Abdul Samad ta kama wani irin fitinannen bugu wanda har Deenah tana ganin irin yadda kirjinshi yake d'agawa sai ta d'an tsorata da hakan amma kuma sai ta dake tana fuskantar SUHANA da ta wani irin kafeta da idanunta da sukayi wani irin k'yallin hawaye "ni kika mara anty Deenah me nayi miki"? Harara Deenah ta galla mata tace na'ma"""'"""""ya isa dan Allah kuna damuna ku fita?" Ya fad'a cikin wani irin d'aga murya da tsawa Deenah kafeshi tayi da ido tana son gano wani abu tattare da mijin nata yayin da SUHANA itama cikin tsantsar damuwa da d'acin ran marin da 'yar uwartata tayi mata itama ta buga tebur d'in gabanshi tace "bai isa ba kuma baza'a fitaba me yasa ka amso min makullin office?" Makullin ya d'auko ya mik'o mata tasa d'ayan hannunta ta amsa d'ayan hannunta kuma har lokacin yana dafe da kuncin ta, hanyar fita ya nuna mata, ta galla masa harara da idanunta da sukayi wani irin ja tsabar b'acin rai shi kanshi ganin yanayin idanunta saida ya bashi tsoro amma ya dake yana jifanta danashi mugun kallon. "Wallahi babu wanda ya isa ya fitar dani daganan batare dana rama marina ba haka kawai uwatace ita da zata mareni" idanu suka zaro gaba d'ayansu suna mamakin furucin ta dan basuyi tunanin hakan daga gareta ba. Juyowa tayi kan Deenah a fusace batareda tayi la'akari da tsohon cikin dake jikinta ba ta d'aga hannunta da iyakacin k'arfin ta ta saita fuskar Deenah wacce ganin da gaske fa SUHANA take marin ta zatayi tayi saurin runtse idanunta jikinta na wani irin masifaffen rawa. Bansan ya akayi ba wane irin tsalle yayi ba me ya faru sai gani kawai nayi marin a sauka a saman tattausan fuskarsa ya wani irin runtse idanunsa da mugun k'arfi zuciyar sa na wani irin fitinannen gudu. Ita kuwa Deenah da sauri ta bud'e idonta jin K'aran tabbas anyi marin amma kuma bai iso gareta ba, ganin Abdul Samad agaban ta ba k'aramin girgiza ta yayi ba kenan shine ya tare marin? "Tunda kin rama jaki" ya fad'a da wani irin murya daya matuk'ar gigita Deenah yayin da SUHANA sam bata kula da hakan ba cikin hayaniyar da basu tab'a sanin ta dashi ba tace babu inda zani wallahi bazan fitaba naga duka kamfanin namune dan haka babu wanda ya isa yamin iyaka da inda zani a cikin sa" Duka da kallo suka bita har Abdul Samad d'in yana mamakin yadda take hayaniya yau d'in nan yasan SUHANA bataji amma kuma yasan bata da hayaniya hasalima idan aka cika hayaniya a waje barin wajen take. Juyawa yayi zai fita ya bar musu office d'in yaji Deenah na fad'in "SUHANA me yake damunki ne yau d'in nan" cak ya tsaya batare da ya juyoba "innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA" jin yadda Deedah ta saki salatin da k'arfi tare da kiran sunan ta yasa ya wani irin juyowa da k'arfi gani yayi SUHANA ta nufi Deenah da wani irin fitinannen yanayi ai da gudu ya shiga tsakanin su dan hannunta ta dunk'ule ta saita cikin Deenah dashi. Tana ganin shi a tsakanin su kawai ta fashe da kuka tana "ni wallahi bazan k'yaleta ba saina rama marina me na mata haka kawai dan sunga ba uwarmu d'aya ba sai su rik'a nunamin'yan ubanci" Fashewa Deenah tayi da kuka tace"la'ilahaillallahu Muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasalam SUHANA me zangani abinda Hajiya take fad'a innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA wa juya miki tunanin ki haka" kafin Deenah ta ankare ta kawo mata wani wawan naushi da sauri Abdul Samad ya tare naushin ya sameshi a gefen ciki tsabar azabar k'arfin naushin saida ya rik'e wajen yace achh kansa tayi da nufin tureshi ya rik'e ta da k'arfin gaske, Abinda ya bashi mamaki yadda ta rik'a k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da yayi mata da k'yar ya samu ya d'aga ta ya makata akan kujeran dake gefe ya turmshe amma duk da haka k'ok'arin tureshi take Deenah kuwa in banda kuka babu abinda take"kiramin Abdul Maleek yarinyar nan inaga aljanune da ita" "Kayi mata addu'a haka Hajiya take mata idan tayi bacci zata farka lafiya" shawaran Deenah yabi ya hau tofa mata addu'o'i tun tana k'ok'arin tureshi da mugun k'arfi har jikinta ya fara laushi daga haka kuma tayi bacci, Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Deenah da har lokacin kuka take yace"kukan ya isa haka madam maza jeki kawo mota bakin nan mu wuce gida da ita kafin ta farka" idanunta ta goge ta d'auki makullin motar tayi waje ta matso da motar bakin office d'in Abdul Samad ne ya d'auko ta ya sakata a bayan motar ya gyara mata kwanciyar sannan Deenah ta shiga gaba suka bar office d'in. "Mukaita d'akin ka dan kar suhail ya ganta a haka" k'ala baice da itaba ya nufi d'akinsa da ita ya shimfid'e ta a saman tattausan gadonsa ya juya zai fita Deenah tayi saurin rik'o hannayen sa tace "kada ka tafi ka barni da ita ni kad'ai dan Allah" duk da cewa zuciyar sa babu dad'i sai ya lumshe rinannun idanunsa ya bud'e akan matar tasa yace"ina zuwa" daga haka ya zare hannunta daga nashi yayi waje cikin motar ya koma ya d'auko takalman ta da mayafinta ya dawo. SUHANA kuwa bata farkaba sai daf da magariba tayi mamakin ganinta a gidan Deenah amma babu wanda ta cewa komai daga Abdul Samad d'in dake ta binta da kallon da ta kasa gane ko na menene har Deenah dake binta da kallon tausayi. Jitai jikinta yayi mata wani irin tsami yana mata ciwo sosai harara ta gallawa Deenah kafin tace"bayan kin gama cin zalina dan kinga a gaban mijinki ne shine ashe harda sumar dani kukayi keda mijin naki shine zaku wani kawoni wannan k'azamin gidan naku mai wari" ta fad'a tana cigaba da hararan ta tana d'aukar d'an kwali da mayafinta tayi waje tana mita babu wanda ya tanka mata acikin su har ta fice MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 11 Yanayin da taje gida sai da ya d'an tsorata Hajiya sauk'in da ta d'an samu Deenah ta kirata tayi mata bayanin abinda ya faru hakanan taji ranta ya kuma dugunzuma fiye da ko yaushe akan halin data ganta yau, dan haka ta yankewa ranta zata nemarwa yarinyar ta magani ko Allah zaisa adace dan taga abin nata kullum k'ara gaba yake, wayarta ta zaro ta kira Abdul Maleek tace maza yazo yanzun tanason ganinshi. Tana shiga d'aki tayi wanka tayi alwala bayan ta idar da sallar ne ta dawo falon nana ta tarar da Annur tace "dan Allah Annur d'an had'o min tea yunwa nakeji sosai" "Ga abinci idan kinsha shayin sai kici" "Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri nace miki duk sanda nake buk'atar abu zanyi da kaina" kafin Hajiya tayi magana Abdul Maleek yayi sallama hakan ya dakatar da Hajiyan daga amsar dataso bawa SUHANA. Bayan sun shiga d'aki Hajiya ta dubeshi "ya kukayi da malam Tijjanin?" "Wallahi Hajiya abinne ya mugun d'aure min kai ya kuma bani mamaki kwarai" Gaban Hajiya ne yai masifar fad'uwa tace "me yace maka Abdul Maleek kodai wani abun ne yasami SUHANAR?" "Kusan haka domin yace jifa ne akayi mata wanda kuma sanadin hakan idan ranta ya b'aci take tada iska wanda shima had'ata akayi dashi halinta nada shine kawai wanda ta had'u dashi wajen haihuwa amma baya ga wannan duk sauran abubuwan asiri ne" "Ya fad'a maka wanda ya aikatamin wannan abun Abdul Maleek?" Hajiya ta tambaya idanunta na cikowa da hawaye" haba mana Hajiya kada kiyi kuka kuma nima saida na masa wannan tambayar yace min ba fad'an ne me muhimmanci ba ayi mata maganin ta warke shine mai muhimmanci kuma yace duk sanda muka shirya aje da ita" "Yanzu zamuje Abdul Maleek" "To bari na fad'a masa" ya fad'a yana zaro wayarsa daga aljihu. Inda tabarta nan ta sameta har tagama shan tea ta d'an ka shingid'a idanunta a lumshe"ki shirya SUHANA zamu fita" idanun ta bud'e akan Hajiya ta d'an kalleta kamar tace babu inda zata sai kuma ta fasa ta maida idanun ta rufe kamar bazata tanka ba dan har Hajiyan ta sare sai kuma tace "ina kuma zama yanzu da dare haka?" Idan munje kya gani" Hajiyan ta bata amsa tana shigewa d'akinta "Allah yasa dai ba cutar dani za'a je ayi ba" ta fad'a da d'an d'aga murya yadda Hajiyan zataji, sai da Hajiyan ta d'an yi jim kafin ta saki murmushi mai ciwo ta shige ciki "kiyi hak'uri Hajiya insha Allah komai zai wuce Abdul Maleek ya fad'a yana duban Hajiyan da yanayin ta ya sauya. Batayi tunanin zata shirya ba Amman sai suka taddota tsab sanye da lafaya purple ta yane jikinta tsab haka suka wuce Abdul Maleek yana ta janta da hira tak'i tanka masa saboda haushin abokinsa kuma mijin yayarta da take ji. Lokacin da sukaje k'ofar gidan malam Tijjanin hakanan SUHANA taji gabanta yayi mummanan fad'uwa tayi masifar had'e rai tana dubansu "inane nan kuka kawoni Hajiya" "Mu shiga mana SUHANA"Hajiya ta fad'a tana kamo hannun ta"wallahi bazan shigaba ji muguwar mata ni zaki munafurta ki kawo nan?" Da matuk'ar mamakin gaske Hajiya ke duban SUHANA "nice munafukar SUHANA?" "Inba munafurci ba meye had'ina da gidan nan da zaki wani kawoni to wallahi banga wanda ya isa ya shigar daniba""""” saini ba" kamilar muryan malam Tijjanin ya daki kunnuwan su, shammtarsu SUHANA tayi zata d'iba da gudu Abdul Maleek yayi saurin fisgota ashe yana ankare da ita. Ta bayanta malam ya zagayo yace"muje"bata iya kallon idanun malam ba tace "dan Allah malam kayimin sassauci nine na kwanaki wanda"""''''ban buk'aci magana anan ba" "Dan""""""kai bana son zancen banza wuce muje" malam ya buga mata tsawa sum sum ta wuce tana hawaye. Tofa me yake shirin faruwa ne muje zuwa dai MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 12 Sum sum ta wuce tana hawaye suna zuwa bakin k'ofar ma saida ta tsaya ta kuma cewa "dan soyayyar dakakewa Annabi MUHAMMAD sallallahu alaihi wasalam malam ka tausaya min" "Ita an tausaya matane? malam ya fad'a a zafafe kunbar yar mutane tana walagigi a unguwa cikakken maida hankali waje guda batayi kullum ita kenan a gantale ga zargi da akasa tsakanin ta da kowa?" "Wallahi zan barta malam har abada" "To mu shiga muje"malam ya fad'a tareda nuna mata hanya da hannunsa. K'arshe dai ta k'arfin bala'i Abdul Maleek ya tura SUHANA wannan d'akin, suna shiga kuma kai tsaye ta nufi gaban buzun ta zauna ta tankwashe k'afa sai kawai ta kama kuka tun k'arfin ta. "Ku shiga muje dole idan abin yak'i sai an rik'eta saboda ga dukkan alamu wannan abin na kanta yana da k'arfin gaske" Jikin Hajiya a mugun sanyaye tabi bayan malam Tijjani da Abdul Maleek wanda sukayi gaba. Lallai kam Hajiya tasha kallon gwagwarmayar tsakanin malam da wannan iska da ya tabbatar da cewa turoshi akayi jikinta kuma saida akayi aikin gaske wajen rabata da ainihin na jikinta wanda suka kasance kariya ga SUHANA wanda a hannunsu aka haifeta duk kuwa da kasancewar wajen da aka haifeta ba wajene na aljanun kirkiba wajene na shed'anun aljanu wato toilet to amma kasancewar da addu'a Hajiya ta shiga sai suka kauce na kwarai suka amshi haihuwar SUHANA wanda suna suke d'an tab'ata take zuba fitina da rashin ji tun tana 'yar ficiciyar ta. Babu yarda malam baiyiba akan su fad'i wacce ta turosu da farko yak'i fad'a amma da yaga ruwan azaba yace zai fad'a amma sai Hajiya da Abdul Maleek sun bar wajen dan akwai Amana tsakanin su da uwar gijiyar tasu domin tana musu yadda suke so sai maganar k'in amsar abin hannun Hajiya shima sune suke sata dan gudun kada ta bata abinda zai rabasu da ita. Saida aka kai ruwa rana kafin yace zai bar jikinta saboda malam Tijjanin ya gane me mugun taurin kaine dan haka malam ya rik'e wuta wajen yi masa yadda bazai tab'a shi'awar dawowa inda take ba, ya kuwa yi alk'awarin zai barta amma yasan da cewa uwar gijiyar su zata kuma d'aukar wani matakin akan hakan dan ba k'aramin k'ullawa RAYUWAR SUHANA tayi, malam yace "wannan kuma ba damuwar ka bane kaidai shaida ne akan abinda zan iya dan haka idan akwai wanda yafika taurin kaima yazo zan iya dashi" bayan d'aukar alk'awarin bazai kuma tukaro SUHANA ba idan kuma ba hakaba ya amince malam yayi masa mafi munin hukunci sannan ta saki atishawa tareda kifewa a wajen. Magunguna malam Tijjani ya had'awa Hajiya wanda zata rik'a yiwa SUHANA amfani dashi sannan ya tabbatar mata zataga SUHANA ta daina wannan d'an banzan yawon mara dalili sannan kuma zata daina gayawa Hajiya magana dama bayin kanta bane, amma fa rashin jinta wannan a jininta yake. Bayan kwana biyu kuwa Hajiya taga matuk'ar sauyi tattare da SUHANA hakanan kuma ta daina wasu abubuwan sannan sai Hajiyan tagama kamar tafi da nutsuwa sai dai tana bata mamakin wani irin mugun miskilanci wanda kwata kwata bata san SUHANA dashi ba amma dai tana cigaba dayi mata addu'a dan Allah ma yasani kaf 'ya'yan babu ya SUHANA tanayi mata wani irin fitinannen so wanda duk abinda zatayi bata ganin laifinta sai dai takanyi k'ok'arin danne hakan har ta daure tayi mata fad'a idan rigima ta had'o ta da 'yan uwanta Wannan kenan Asalin labarin MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 13 Malam Garba wanda akafi sani da malam garbu shine kakan SUHANA mahaifi kenan ga alhaji Aminu mahaifin SUHANA asalinsu mutanen katsina ne a wani k'auye washi gurbin b'aure dukanin wasu dangi na malam garba sun rarrabu wasu suna zaune anan gurbin wasu suna cikin jibya yayin da wasu ke cikin katsina wasu kuwa sun tsallaka jamhuriyar Niger. Malam garba shi kad'aine a wajen mahaifinsa wanda akafi sani da Abdul Basi shi kuma Abdul Basi su goma sha d'aya ne a wajen mahaifinsu wato malam Muhammadu wanda asalinsu su mutanen yaman ne ta jihar Niger saidai suma basu gama girma da mahaifin nasuba duk cikin suma babu wanda yakai malam Abdul Basi sanin sa domin shine d'ansa na farko bayan shi sai mai bi masa Hajiya Rahane da Hajiya Gwaggo da Hajiya Fatima da Hajiya Inna sai da Hajiya Hadiza sai Hasan da Usain da Gambonsu dukansu maza sai kuma autar su Hafsu sai mata guda biyu da suka mutu tun suna yara. Duk da kasancewar malam Abdul Basi baiyi wani tsohon rai ba amma ya gina zuri'ar tasu abisa doron zumuncin wanda har yanzu da baya Raye zumuncin yananan yana gudana kamar yadda yake fata tun da rayuwar sa. Malam Abdul Basi ya rasune tun ba'a san da cikin malam Aminu ba wanda sai daga baya aka lura da hakan wanda ba k'aramin murna yan uwan sa sukayi ba dan da farko sunyi tunanin ya tafine batare da ya bar musu wani irin da zasu rik'a gani suna tunawa dashi ba. Bayan a haifi malam Aminu da shekara guda itama maihafiyarsa ta rasu sakamakon hatsarin mota wanda a lokacin tabar malam Aminu ne a wajen mahaifiyar ta taje gidan biki. Kafin auren malam Abdul Basi da Inna Shatu ta tab'a aure harda d'iyar ta Hadiza wacce sanda mahaifiyar su ta rasuma tuni ta isa aure dan haka aka aurar da ita a wani k'auye dake cikin Niger wanda su asalinsu yan wani k'auye ne washi duhun bara duk a yankin Niger yake amma yafi kusa da gurbin b'aure. Wannan dalilin ne yasa dangin malam Aminu suke da mugun yawa na ban mamaki dan sun tara zuri'a mai yawan gaske a yanzu haka maganar da nake muku mutum uku ne kacal suka rage a cikin wannan zuri'a Hafsu gambo da kuma malam Abdul wahab wanda yake zaune anan jibya yayin da Hafsu gambo su suna can gurbin da tasu zuri'ar. Mafarin zuwan babana kano ankawo shi karatu ne wanda shine asalin zamanshi anan d'in da farko a unguwar fagge ya fara zama har ya auri mahaiyata wato Hajiya Sadiya wacce mahaifin tane ya kaisu makka dukkan yayansu maza da mata babu wanda baikai makka ya mallakawa gidaba kasancewar sa babban attajiri a wancen lokacin. Kasancewar malam Aminu hayace ya Kama a faggen sai Hajiyan su Sadiya ta bata shawarar kawai su dawo gidanta da zama wannan shine asalin dawowar mu unguwar yakasai kuma duk anan aka haife mu banda mace d'aya wato nana Khdija. Mu goma sha biyu Hajiya ta haifa wanda wani irin zamane tayi da alhajin mu na tsantsar kawaici da hak'uri kasancewar malam Aminu fad'aci na gasken gaske hakan ne yasa wasu daga cikin yayyena sukan shaida irin wahalar da Hajiyan mu tasha da mahaifin mu. Saidai kuma mahaifin mu yana da wani rauni shine na tsantsar sonmu da Allah ya d'ora masa ko kallon banza babu wanda ya isa yayi mana babu kamar ni SUHANA Allah ya d'orawa alhaji tsantsar k'auna ta bayason ganin koda fushi nane bare kuma akai ga hawaye na hakan yasa sun sha samun matsala da Hajiya akaina wannan shine asalin rashin jituwana da yaya Abdul Maleek wanda ya kasance d'a na uku ga mahaifimu. Kamar yadda na fad'a da farko mu goma sha biyu cif Hajiya Sadiya ta haifo a cikin babbar yayarmu sunan ta aisha wacce sam ni bansanta ba kuma shine sunan da aka maidamun bayan an haife ni. Daga kanta saida Hajiya ta haifi Abubakar Umar Usman da Ali sannan Yaya Abdul Maleek sai yan biyu anty Khadija da Zainab sai Gambonsu wacce taci sunan Hajiya Hafsu hakan yasa yan gidanmu suke kiranta da gambo saboda kara wa k'anwar kakanmu sai aka haifi Ibrahim da Fatima wacce ta kasance sunan mahaifiyar Hajiya wato anty Deenah wacce kuma ana goyonta ne yayarmu wato wacce naci sunan ta Aisha ta rasu lokacin baifi saura yan kwanaki ayi bikin taba ba shekara biyu ko uku ne tsakani na da anty Deenah ba shekara d'ai d'ai ne har guda bakwai kafin a haifoni a wannan duniyar acikin band'akin gidanmu wanda Hajiya ta tabbatar min bata tab'a haihuwar sadaka irin tawaba domin jitai kawai tanajin bayan gida ta shiga toilet saidai kuma labarin ya sauya ashe ni Aishatul SUHANA nice zan duro doron duniya a cikin bayan gida. MAMAN ISLAM CE NA MIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 14 Hajiya tace bata tab'a fitinannen goyo irin nawa ba gani yar ficiciyar gaske sai fitinar tsiya gashi kuma duk abinda nace zanyi ko za a kasheni sai na aikata ga Hajiya da alhaji basa k'aunar a tab'a ni wannan ne yasa kaf ''yan uwana suka tsane ni banda Adda Deenah da Allah yasa mata tsananin k'auna ta kuma bata ganin laifina ko kad'an duk kuwa da cewa nafi takura mata fiye da kowa a cikin gidan baridai mubi labarin daki daki yadda zaku fahimci inda na dosa. Alhaji Aminu d'an kasuwa ne maisai da kayan masarufi da na aune aune yana da kusan shaguna guda uku na kanshi a cikin sunga sannan yana da kamfanin da ake sarrafa masa shinkafa hakanne yasa muke rayuwa cikin sukuni babu abinda muka nema muka rasa najin dad'in rayuwa harma da irin mutanan da suke rab'armu wato irin abokan su yayyanmu su Yaya Ali suna da yawan abokai wanda yawancin rayuwar su duk a cikin gidanmu sukeyin ta domin hakane ma alhaji ya samowa Hajiya masu tayata aiki har mutun uku saboda ana dafa abincin da ya fi k'arfin ta saboda yawan jama'ar dake shige da fice a gidan sannan kuma akayi sa'a daga Hajiya har alhaji mutane ne masu hannun kyauta basu da rowa ko kad'an. Bani da wayo sanda akayi bikin su anty zee wanda a yanzu haka suna da yara ita zee yaranta biyu yayin da anty Khadija ke da guda uku domin haihuwar ta ta farko yan biyu ta haifa hakanan tsransu kwanaki uku ne kacal wajen haihuwar farin saidai a ta biyun anty zee ta riga anty Khadija da kusan shekara biyu kasancewar kwanika tayi to masu karatu ku biyoni cikin gidanmu domin ganin irin yadda na gudanar da rayuwata tare da anty na wato Deenah. "Hajiya dan Allah kibar abincin nan kawai ki bani d'ari biyar nasai buscuet da lemo" babu musu Hajiya ta kama hannun zanin ta kunto kafin ta mik'omin anty Deenah tayi saurin karb'ewa tana hararana tace"wallahi Hajiya ki daina bawa SUHANA kud'i yaran mutane take tarawa tayi ta rankwashi ko gabzawa mutum mari tana bashi biyar ko goma" Baki Hajiya ta kama tace"hakane mamana?" Hajiya ta tambaya tana kallona nayi kicin kicin da rai ina hararan anty Deenah kafin na takarkare na saki uban ihun da duka hankalin yan wajen ya dawo kaina ashe dodona yana nan bak'in mugu maci zalina wato yaya Ali duk bala'i na ina masifar tsoron sa shine Hajiya ta sakawa duka ba ha'inci lallai duk ranan da Yaya Ali ya damk'eni sai nayi jinya saboda bana son duka ko kad'an. Ina can ina masifar d'aga murya da haniya wa anty Deenah saboda ta hana Hajiya tabani kud'i sai jinai Hajiya ta finciko ni tana fad'in "kada ka sake ka tab'a ta sokake kajamin asara yan kud'ad'e batareda na shiryawa hakan ba" ni sai lokacin ma na kula da shi hakan ne yasa na masifar maiaraice fuska ina hawaye saboda takaici duk da cewa Yaya Ali yayi mugun jin haushin abinda Hajiya tayi na hanashi fallawa SUHANA mari amma saida ya ta bambayi abinda yake faruwa babu musu SUHANA ta kwashe yadda akayi ta fad'a masa wannan dalilin ne yasa yake k'aunar SUHANA saboda ko za'a kashe ta bata k'arya. Sai da ya tallewa Deenah k'eya kafin ya ciro sababbin 'yan hamsi na d'ari biyar yabawa SUHANA yace "maza wuce ki tafi kuma wallahi kika sake na fito na sameki a waje sai na tattakaki. Duk da cewa raina baiso fita batare da na karb'i na wajen Hajiya ba ina nufin kud'in hakanan na fice inayiwa anty Deenah hararan gefe tareda tsatsare ta da idanuna Ina fita kuwa nayi karo da Marwa d'iyar malam sambo dama da safe tasa yayanta ya mareni akan kawai tayi kwanikan tab'o na rusa, tana gani na ta juya zata koma gida da gudu nayi saurin sa mata k'afa na maka da k'asa sannan na murje mata baki da takalmin k'afata, ta saki wani irin kuka kafin kice me b'at na b'ace kamar walk'iya dan Allah yayini da d'an karen gudu. Haka dana isa bakin makaranta naci karo da Balaraba 'yar kusa da ajinmu ce itama tak'ark'arewa nayi na d'urma mata dundu (k'ulli) agadon baya ashe shegiyar a taci yayi mata karo sai gashi ta kama kuza uban amai da sauri na shige cikin makaranta saboda hango malam Yahya wato duka ba ha'inci dan mugune na gaske danma har makarantar alhaji yazo yace kar malam Yahya ya sake ya K'ara dukana wannan kenan. A aji babu malamin da baisan da zaman Aisha Aminu ba akwai k'ok'ari akwai fitina wasu sukan lallab'a ni wasu kuwa sumin mugun duka wanda kuma hakan baya hanani abinda nayi niyya sannan bana fasa dukan duk d'an wanda tsautsayi yasa ya shiga hanyana hakanne yasa koda yaushe Hajiya cikin ganin 'yan kai k'ara take wuni take bada hak'uri MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 15 Ina ta zuba ido naga malam Yahya dan nayi tunanin Balaraba zata fad'a masa abinda nayi mata sai dai har aka tashi banga alamunsa ba ranan ma ko ajin namu bai shiga ba duk da cewa zai karb'i hadda dake mu duk sanda akayi mana k'ari anayi ne yadda ko kwakwalwar dusane dakai zaka d'auka sai kuma ace kaje gida gobe kazo da hadda. Na godewa Allah da irin baiwan da yayimin ta yadda indai aka biyamin karatu duk wahalar shi muddun za'a tusamin sau biyu ya zauna kenan akaina har abada. Bayan mun tashi na hango Balaraba ita da wata k'awarta suna tafiya haka kawai na tsargi kaina na kwalla mata kira, aifa tanajin murya na jikinta ya hau tsuma ta k'araso kusa dani harara na galla mata nace "shine kikaje kika had'a ni da malam Yahya ko?" K'irji ta dafe tace "lah wallahi babu abinda na fad'a masa ko barima banyi ya ganni ba dan kar ya tambayeni" kwafa nayi tare da k'ara mata hararan dayafi na farko nace "Allah ya ceceki yarinya da yau sai nasakaki aman mage" Daga haka ban k'ara bi takanta ba hankali na ya kwanta tunda bata had'a ni da malam zalimu ba. "Salamu'alaikum Hajiya ina abincina wallahi yunwa nakeji" "Jimun yarinya ina kud'in da Ali ya baki kikace zaki sai wani abun a hanya?" "Humum lallai wallahi bazan iya kashe wannan sababbin kud'ad'en ba dan haka zan had'a"""""""""maganar ya katse sakamakon ido hud'u da mukayi da Abdul Samad na kwasa da gudu na zube a gabansa tare da rik'o hannayen sa duka biyun nace"lah YAYANA yaushe ka dawo shine ko ka kirani a wayar Hajiya" Hannun nawa yakai bakinsa ya sumbata yace"haba TAWAN idan nace zan fad'a miki ai bazakiyi d'okin dawowane ba ko?" Ya fad'a yana d'age min gira, had'e rai nayi "nace shikenan babu ruwana da kai tunda haka kace" na fad'a tareda tashi zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN karkiyi min haka mana ina ta murna zanzo naga tauraruwata kuma sai tayi fushi ai sai kisa zuciyata ta buga" Murmushi nayi na koma na zauna tareda janyo kwanon gabanshi na bud'e ido hud'u mukayi da mutumina wato farfesun kayan ciki saida na had'iyi yawu dan ina masifar son kayan ciki d'aya kwanon na bud'e lafiyayyen tuwon shinkafa ne wanda ko ba'a fad'a min ba nasan miyar d'anyen kub'ewa ne ko zogale dan sune miyar da Hajiya da alhaji suka fiso. Zama na gyara a gabansa da nufin muci abincin tare Hajiya ta bugamin tsawar da ya gigitani na mik'e a zabure tace "wai dan Allah SUHANA meyasa baki da hankali ne bazaki jira na zubo miki nakiba zaki wani zo ki jagwal gwala masa abincin, kuma nasan ba tuwon zakici ba naman zaki tsince ki tashi dan bacin tuwo kike ba" wani irin fitinannen ihu na zunduma tare da kwanciya a k'asan kafet d'in falon ina birgima, da wani irin mugun mamaki yake kallona kafin ya kamo tattausan hannuna ya jawoni gefensa ya kwantar da kaina gefen kafad'arshi yana fad'in "Haba TAWAN dan Allah dama har yanzu baki daina wannan shirmen ba shekaran ki sha d'aya fa kina aji shida a primary gaki hazuk'a haddar izu talatin gareki shine kike irin wannan kamar wata karamar yarinya?" Harara na galla masa na mik'e zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace 'ina zaki zo muci abincin Mana?" Baki na tura nace "na fasa ci kuma idan alhaji ya dawo saina fad'a masa nace ba'a bani abinci a gidan nan" Hajiya ta fusata dajin abinda nace tace "dan ubanki idan ya dawo karki fasa fad'a masa shi kuma idan kin fad'a masa kar ya barni da rai?" Hajiya ta rik'a fad'a sosai yayin da Abdul Samad yayi ta bata hak'uri yace ta rik'a hak'uri dani kuruciya ce, ita kuma tace babu wani kuruciya iskanci ne" Bayan Hajiya ta gama sababin ta tabar wajen sai ya kama rarrashina nayi bala'in had'e rai, babu yadda baiyi dani naci abincin ba nace na k'oshi dan dole ya hak'ura yaci abincin sa shi kad'ai. Abdul Samad shima d'aya ne daga cikin yaran dake shiga gidanmu aboki ne ga ya Usman d'an Hajiya na hud'u hakanan d'ane ga mak'ocin mu malam Ibrahim wanda ya kasance malamin makaranta, a jama'ar BUK ta shi kad'ai ne dan daya rage musu a rayuwa amma kafinshi alh. Ibrahim yana da yara hud'u wanda Allah yayiwa rasuwa sakamakon gobara tare da mahaifiyar su shine ya auro mahaifiyar Abdul Samad Haj Aina'u mace mai tsananin kirki da hak'urin gaske dan zan iya cewama tafi Hajiyata hak'urin sannan aminai ne su na k'ud da k'ud baka tab'a jin kansu. Ana gaisuwar mutunci da girmamawa tsakanin alhaji Aminu da alh. Ibrahim amma sanadin abotar Yaya Usman da Abdul Samad alak'ar su ta soma k'arfi har sukayi wata irin shak'uwa har ya kasance idan d'aya zai aiwatar da wani abu sai ya nemi shawarar d'an uwansa. Abotar Yaya Usman da Abdul Samad ya samo asaline tun daga nussery har zuwa yanzun sunyi wata irin shak'uwa mai ban mamaki. Tun sanda aka haifoni Allah ya d'igawa Abdul Samad wani irin k'auna ta duk da kasancewar suna makarantar kwana nane shida Yaya Usman amma duk sanda akayi hutu yana mak'ale dani saboda ni Abdul Samad ya dawo gidanmu da zama duk da k'ulafucinsa da iyayensa sukeyi kasancewar sa shi shi kad'ai hardai suka hak'ura. Haka nataso da d'an banzan kiwa babu wanda nake yarda dashi sai NAWAN shine asalin sunan da ya koyar dani na rik'a kiransa shi kuma yace dani TAWAN kama har yau danake da shekara goma sha d'aya a duniya bamu daina kiran juna da hakaba wanda har yan gidanmu sun saba da hakan. MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 16 D'aki na koma abincin ma na fasa ci babu irin rarrashin da NAWAN baimin ba ya hak'ura k'arshe shima fasa cin abincin yayi duk da cewa Hajiya tasan za'ayi hakan shima sai ta rufeshi da fad'a ta inda ta shiga batanan take fitaba "eh tunda na tab'a JININ JIKINKA ai dole kace bakacin abincin tunda tayi masa yaji itama to dan Allah daganan har a busa k'aho kar ka k'ara ci" da dai yaga abin bana K'are bane shima ya lallab'a ya gudu dan Hajiya badai lafiyar mitaba. Ina fita gidan mommy na nufa, ina nufin Babar su NAWAN tana ganina ta hau fad'in "a a kaga sark' mai rikicin gangan daga ina haka naga kina ta wani cin maganin?" Kawai sai na fashe mata da kukan tab'ara nace "ba Hajiya bace take tamin masifa kuma ta hanani abinci" hannuna ta kamo tace "zonan yar lelena kinga yau danbun naman kaza nayiwa su Usman, muje ciki sauranki zasuci" aifa inajin abinda tace na k'wace hannuna ina bubbuga k'afa nace "wallahi mommy babu ruwana daku daga ke har Hajiyan fisabilillahi ace su yaya zasu dawo shine kuka barni natafi makaranta?" Dariya mommy tayi tasan rikici na yanzun sai na d'aga mata hankali dan haka ta rik'a lallab'a ni tana rarrashi tajani har falonta yadda ta gyara falon yana ta k'amshi yaja hankalina sai na samu waje na zauna ta kawo min k'atuwar samiran da ta zuba dambun naman a ciki taf ta cika kuma nasan an kaiwa Hajiya kuma nasan k'ulli na daban, murmushi nayi nace "mommy yau me kika dafa?" Kaina ta shafa tana murmushi tace "ai mutuniyarki na dafa shinkafa da miya da salad da kayan had'i" cikin jin dad'i nace "yauwa mommyna zubo min amma ni da manja da yaji nake so" mommy ta d'an had'e rai tace"waike SUHANA dan Allah mai yasa duk kinfi kauri wajen kwad'ayi ne?" Sanin halin Mommy yasa na rik'e ciki nace "wayyo Allah cikina ya k'ulle yunwa zata kasheni" ai kafin nakai k'arshe mommy ta tafi kawomin abincin, ni kuma na ciro leda daga jakar makaranta na dake goye a bayana na d'ebi danbun naman da yawa na maida jakata, ta kawo min abincin had'e da mai da kayan had'i, nace ta maida yajinta ina dashi a jakana tace"hakafa tsabar d'aurewa k'arya gindi harda guzurin yaji" ta bar wajen tana mita. Nidai ban tanka ba na zuba abincin dan gaske yunwar nake ji shiyasa ina gama zubawa NAWAN ya shigo "a a kice nan kika gudo kika barni da fad'an Hajiya" yana zama a kusa dani tare da jan flat d'in dana zuba abincin yasa hannu yana juya abincin yana fad'in "dole ki gudo wajen mommy tunda tana miki yadda kike so" harara na galla masa zan bar wajen yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN karkiyi min haka mana idan kika horamin kanki da yunwa bazan tab'a yafewa kainaba" "Ni daga yau bataka bace tunda har zaka iya gama makaranta ka dawo baka sanar min ba" marairace fuska yayi gabansa na fad'uwa yana matuk'ar tsoron fushin SUHANA dan bata da dad'i. Shiru yayi yana kallonta jafin yayi wani kalar tausayi ya mai da kansa yana kallon kafet d'in idanunsa suka d'an surka kad'an da sauri na k'araso kusa dashi na zauna ina kallon shi a rayuwata bana k'aunar ganin canjin yanayi a tattare da NAWAN hakan ne ma yasa na dawo na d'an lek'a fuskar sa har ta fara ja abunka da farin mutum ihu na fashe dashi tare da yunk'urawa zanbar wajen, a matuk'ar rud'e ya rik'o hannuna yana kallona yace "tunda kin fison d'aga min hankali shikenan kije kiyi abinda kikeso" "To ba kaine ka dawo baka fad'a minba ka barni na tafi makaranta" yasan za'ayi haka mitace zai shata danhaka yace "bari kawai na koma sai a maidani baya idan yaso randa zamu sabunta jarrabawa sai in sanar miki" ya k'arasa fad'a yana k'ok'arin tashi "ni bance ka koma ba idan ba hakaba yasin na daina kulaka" murmushi yayi tare da lakuce min hanci yace "ina matuk'ar k'aunar ki TAWAN" nima murmushi nayi nace "ai dai nafi sonka kuma nafika dauriya kai da wata rana da bani da lafiya ina kallonka kana matsar hawaye" na fad'a ina kwatanta yadda yakeyi a lokacin. Murmushi yayi tare da dungure min kai yace "wai yarinyar nan dan Allah me yasa baki mantuwa?" Dariya nayi nace "ai yasin bazan mantaba Kato dakai kanamin kuka ni haushi ma ka bani a lokacin" "Dan bakisan tsantsar k'aunar danake miki bane shi yasa kikemin d'an biki. Haka mukayi ta hira yana bani abincin a baki shima yanaci har muka kammala, dan koda mommy tazo taganmu tab'e baki tayi tabar wajen domin tasan halina yanzun zata ganmu muna abin arzik'i yanzun kuma zataga mun hau sama mun dawo. Mik'ewa yayi nace "ina kuma zaka"? "D'akina zanje na gyara mommy batasan da zuwana ba bare tasa a gyaramin" "To bari nazo na tayaka" hummmm"kidai tayani hira banda haka me kika iya" harara na galla masa na juya a fusace zan fita yayi saurin rik'o hannuna yace "haba TAWAN meye na d'aukar zafi ke da wata ranama duka wata d'awainiya ta ma ke zaki d'auka" fusge hannuna nayi zan fita yayi saurin rungumoni jikinsa take kuma yayi saurin sakina yana d'ago kaina muryan shi na d'an rawa rawa yace"kinaso nayi miki kuka?" Duk da hakan da yayi min ba wai sabon abu bane a wajena amma cikin yan kwanakin nan hajiya na yawan fad'a min indai ina barin na miji yana tab'a ni zan iya d'aukar ciki kuma har ga Allah na amince da wannan batun hakanne yasa naji gabana yayi wata masifar fad'uwa" na juya da gudu na fita tare da fashewa da wani fitinannen kuka. Mommy na tsakar gida taga wucewa ta, ta hau kwalamin kira sam ban saurareta ba ta yunk'ura da nufin zuwa tambayar abinda ya had'o mu dan nata tab'a ganin wannan fusatar a tare daniba sai taga shima ya fito a mugun kid'ime zai fita tace "kai Abdul lafiya?" dake haka take kiransa dashi"ina zuwa mommy kingafa fushi tayi take kuka dan kawai na rungumeta har dacemin d'an iska" jin abinda yace sai mommy taji dad'i a ranta kenan SUHANA tana d'aukar hud'ubar su tunda gashi har ta nunawa Abdul b'acin ranta akan abinda yayi Mata. Shikam bai saurari me mommy zatace ba ya fita da sauri. A falo na sami Hajiya harda anty Deenah ma ta dawo a makaranta wucesu nayi ina kuka tare da fad'in wallahi idan nayi ciki bazan yardaba Allah kuwa sai nayi shari'a dakai. Jin abinda nake fad'a Hajiya da Deenah suka kalli juna sannan suka kalleni Hajiya tace"me yafaru dake kkje wannan maganar banzan" fashewa na sakeyi da kuka nace ba NAWAN bane kawai ya rungumeni dan nayi fushi zan bar gidan tsabar iskanci kuma kince duk wanda ya tab'ani zanyi ciki" Kafin Hajiya tace wani abu sai gashi ai da gudu na afka d'akin mu da anty Deenah na b'amo k'ofar bugun duniya da magiya nayi masa banza Ina cigaba da kukana cikin tashin hankali MAMAN ISLAM NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 17 Cigaba yayi da bugun k'ofar cikin wata rarraunar muryan da saida naji jikina yayi sanyi to amma kuma abin kunyar da zai jaminfa ni yanzun idan aka ganni da ciki me zance da mutane dama gashi Hajiya tace duk sanda yaro zai aikata wani abu ko babu wanda ya ganshi tofa su iyaye suna gani an rubuta a goshinsa, wayyo Allah wallahi daga yau kai ba NAWAN bane na tsaneka tunda kakeso ka lalata min suna nima k'awayena su tsaneni haka na rik'a wani irin kuka mai cin rai. A kad'an Abdul Samad yakai mintuna hamsin a bakin k'ofar yana bugu kafin Hajiya tazo da k'yar tajashi sukabar wajen tace "kai kuwa me ya had'o ka da mutuniyar taka take wannan uban kukan, kai kuma gaka hankali a tashe saikace wanda akace yau alki'yamarsa zata tsaya?" Tayi masa tambayar duk da cewa ta d'an hasaso wani abin a zantukan da SUHANA takeyi hakan kuma ba k'aramin farin ciki ya sanyata ba kenan tsoratarwar da takewa SUHANA yana shiga kunnen ta kuma tana aiki dashi. "Idan tayi fushi dani ai alk'iyamar tawace ta tsaya Hajiya dan Allah ki lallab'a min ita wai daga na rungumeta shine take ta wannan tashin hankalin" Murmushi Hajiya tayi tace"kai da TAKAN wa ya isa shiga tsakanin ku ai kai da ka b'ata kaine zakaje ka gyara abinka da kanka indai SUHANA ce duk wanda ya shiga lamarinku shine zaiji kunya" "Dan Allah Hajiya kada kice haka b'acin ran SUHANA rashin kwanciyar hankalana ne domin ita d'in duniya tace" da mamakin furucin sa take dubansa tabbas Abdul ya zauce akan SUHANA duk kunya irin tashi yake iya fad'a mata haka, wani irin sassanyar murmushi tayi tare da fatan tabbatuwar hasashen ta akan Abdul Samad da SUHANA. Azahiri kuwa had'e rai tayi tace "lallai Abdul wato SUHANA duniyar kace kuma kake fad'a min saboda baka da kunya" Shifa sam yama manta da wata aba wai kunya fatansa kawai kada SUHANA ta d'auki wannan muguwar gabar tata dashi dan hakan yana nufin tashin hankali ga rayuwar sa "Hajiya"""""""jeka Abdul zan mata magana Hajiya ta katseshi dan ya k'yaleta ta lura bayan karatun bussiness da yayi harda naci ya koyo abinda ba halinsa ba ko kuma tace ya koya a wajen Usman dan shi kamar marok'i yake wajen iya naci. Sala lau sala lau haka ya mik'e ya fice Deenah ta bishi da wani irin kallo zuciyar ta na wani irin azababben bugu (off kumin afuwa nayi mantuwa wajen ce muku Abdul Samad da Usman candy sukayi a a NCE zance so kumin afuwa d'an Adam ajizine) Fatanta kada Allah ya tabbatar da abinda take zargi tsakanin ya Abdul da SUHANA idan kuwa har hakan ya tabbata to kuwa tana da yak'inin cewa rayuwar ta tana cikin garari.(to Deenah me kike nufi da hakan? To bari dai mugani) Yarda yabar mommy haka ya tadda ta zaune tana kallon labaran yamman a tashar NTA yanayin da ya shigo ya bata dariya da tausayi amma sai ta d'auke kai tana kallo ya zauna ya dafe kansa, sai kawai ta tashi tabar masa wajen Tun ranan da mukayi haka da NAWAN ban k'ara yarda mun had'u dashi ba haka kuma hakanan naji na tsane shi domin a ganina ai yana sane ya rungumeni dan kawai ya cuce ni. Haka har muka shafe kusan sati guda bai fasa zuwa ya bugamin k'ofa ba haka ban daina gudunsa ba bil hak'k'i da iya gaskiyata, idan zan tafi makaranta nakan yi wuf na riga anty Deenah fita sai dai ta taddani acen hakama idan mundawo ta baya nake biyowa. Yau dai ban rufe kaina kamar yadda na sababa muna ta shawagin mu nida Marwa kunsan dai fad'an yara yanzun ne za'ayi yanzu kuma an shirya hakan take nida Marwa saidai kuma tana mugun tsorona saboda nafi k'arfin ta mugun duka nake mata. Mun gama gararanbar mu a unguwar saboda wasu mutane da suke tarewa yau a kusa da gianamu hardamu ake shige da ficen saboda naga suna da yaran dabasu fimuba nida Marwa sai murna nake mun samu k'arin k'awaye MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 18 K'ishin ruwane ya kamani nayi saurin shigewa gida dama gidan jikin gidanmu yake. Turus nayi ganinshi zaune kusa da anty Deenah tanayi masa magana k'asa k'asa duk da bansan me take ce masaba saida naji wani irin ba dad'i araina, nayi bala'in d'aure fuska ina k'arasa shiga gabana yana fad'uwa. Daf da zan giftasu ya d'ago muka had'a ido ya wani irin kafeni da ido nima kallonsa nake ido cikin ido araina nike ayyana ko rashin lafiya yayine yayi wannan masifar ramar? Ganin da gaske wucesu zanyi yayi saurin tashi yasha gabana yana kallona sai naji wani irin abu yana tsargamin saboda yadda ya wani tsareni da kaifafan idanunsa sai nayi k'asa da kaina zan wuce yayi saurin rik'o hannuna "haba TAWAN dan Allah ya kikeso nayi da raina yayi maganar da rawar murya ga mamakina kuma har kamar kwalla na gani ta cika masa idanu zo kiji dan Allah" ya fad'a yana jana batareda yajira cewata ba nan Deenah tabimu da wani fitinannen kallo zuciyar ta na tsananta bugu. A soro muka tsaya ya kafeni da idanu yana bina da wani irin kallo idanunsa har sun canja launi"wai TAWAN me nayi mikine da zafi kike azabtar dani da fushin ki?" Harara na galla masa nace"daga yau ni ba taka bace na tsaneka tunda na gane jikina kakeso" idanu ya k'walalo gaba d'aya ya kafeni dasu nace "li'ilafi k'urraishi wallahi kurwata tafi k'arfin ka, daka wani tsareni da mayun idanunka babu abinda zaisameni" da ace ba a cikin wannan k'adamin suke ba babu abinda zai hana ya kwashe da dariya yadda tayi maganar tana wani marmar idanunta to amma sanin halin SUHANA ba'a biyo mata ta sauk'i yasa yace" nayi laifi amma ni kisani ni bada wata manufa na rungumeki ba amma zan kiyaye kiyi hak'uri ki daina wannan fushin dani zuciyata bazata d'auka ba" ya fad'a yana kai hannuna saitin zuciyar sa irin yadda naji tana bugawa da k'arfi abin ya matuk'ar bani tsoro wallahi ai tuni na manta da maganar wani fushi dan maganar gaskiya shak'uwa ta da NAWAN ya wuce tunanin duk wani mai tunani, cikind tsantsar amuwa nace"me yasameka NAWAN shine baka fad'a minba?" Na fad'a da rawar murya idanuna suna cikowa da kwalla ai ganin har sun fara zirara sai hankalinsa yai masifar tashi har zai rungumeni sai ya tuna ya fasa yayi saurin rik'o hannuna yace "dan girman Allah ki taimakeni kada kiyimin asarar wad'annan tsadaddun hawayen naki" Yayi maganar ne cikin tsantsar damuwa, sainaji ya bala'in bani tausayi bazan iya cigaba da fushi dashiba dalilin kenan dayasa nak'i amincewa mu had'u nasan cikin k'aramin lokacin zaisha kaina mu shirya, cikin muryan shagwab'a nace "ni k'ishin ruwane ya kawoni gidan" murmushi yayi yace? "da kina ina?" "Ina waje kasan yau mak'otanmu suke dawowa muna can nida Marwa muna tayasu aiki kaga babarsu kuma wallahi mai kirki ba'azo da yaran ba amma matar tace tana da yara kamar ni" murmushi yayi yaja hannuna zuwa cikin gidan har falon Hajiya sanda muka shiga anty Deenah tabar wajen hakan yamin dad'i dan haka nan naji kishin yar uwar tawa. Roban ruwan ya Ali ya d'auko nayi saurin rik'o hannunsa nace "kai rufamin asiri namu ya K'are kaga akwai pirewater a bani murmushi yayi shida kanshi yana shakkar Yaya Ali dan bashi da fara'a NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 19 A kad'an na kwashe kusan awa guda a bayan gida wannan ka'ida tane matuk'ar cikin yayyena akwai mai uzuri kuma yaga zan shigar masa bayan gida take suke korana suce karma na soma. Yanzuma hakan ne yafaru saida na kwashi cikakken minti talatin saman Masai kuma ma banyi kashin ba kawai tsigunon ne na jaraba da aka saba. Bayan na fito a wankan ma sai da na gama wasa da tsalle tsallena a gaban merrow d'akin Hajiya kafin na kimtsa na fito falon, bawan Allah yana nan yana jirana haka muka wuce muka tafi, a kuwa nasha lce cream kamar ba gobe sannan na dage saida mukaje wajen wasanni nanma mun jima kafin muka biya wata super market ya siyomin su alawoyi da buscuet kala kala masu mugun dad'i da tsada. Sanda muka dawo gida ana kiran magriba hakan yasa babu kowa a tsakar gidan sai anty Deenah tana alwala da sauri ya fita shima bayan ya ajiyemin ledar da muka shigo dashi. Tun anan naga anty Deenah tana binsa da wani irin fitinannen kallo bandai tankaba amma k'eyarta yasha harara, da haka nima nayi alwala na wuce d'akin mu lokacin har anty Deenah ta idar. Wata irin rayuwa muka shimfid'a da Yaya ABDUL SAMAD (NAWAN) tunda karancin shekaru na ya tabbatar min da yana sona zai aureni tun inajin haushin tsadaddun kalamansa har na dawo suna min dad'i tun inajin kunya har na dawo inajin kewa a duk ranan da wani abu ya gifta bamu zauna ya bani labarin yadda nake a zuciyar sa ba, duk kuwa da ya tabbatar min da cewa nice duniyarsa nice jin dad'in duniyarsa sannan babu wani babban uzuri da ya zartani a rayuwar sa. Ina matuk'ar jin dad'in hira da NAWAN ina matuk'ar k'aunar kasancewa dashi ya iya zantuka masu matuk'ar sanyi da sanya nutsuwa Ina da tabbacin duk ranan da na rasa NAWAN tabbas nima na rasa kaina domin shine farin cikina duniyata inaga dama da k'aunar juna aka halicce mu. A b'angaren tsokana da fitina kuwa harga Allah babu abinda na fasa musamman ma yanzu da su yazeeda mak'otanmu suka tare wayyo aiki ya dad'a lalacewa dan Hajiya da Babar su yazeeda kullum cikin bada hak'uri suke gashi muyi tabin gidajen tsofaffin unguwarmu muna kid'e kid'e da rawa Marwa har tafimu gashi bamu da wajen zama sai gefen wata bola dake bakin layinmu kuma duk sanda wani ya ganmu a cikin yan gidanmu ko gidansu yazeeda ko Marwa wallahi dukan mutuwa suke mana amma bamu fasaba ga Marwa da shegen kwalliyar aljanu a wani jagira asa eyeshadow eyelaner dama duk ciki nice bana wannan shafe shafen idan akaga nasa hodama to unguwa zamu fita da Hajiya. A gida kuwa halina yasa kullum kafin mu kwanta sai mun tik'i d'an banzan dambe da anty Deenah dan ta gaji da halina ta fara biyemin duk dacewa ni na iya fad'an yan China hakan yasa bata wani nasara akaina. Yau da dare muna tareda yazeeda dama Marwa ita wannan rik'on matar ubane ba'a damu da duk inda zataba in zatakai d'ayan dare babu mai cewa daga ina take kasancewar itace yar fari ga mahaifinta kuma matar babanta irin shashashun matan nanne da nasuma basu damu dasuba bare kuma d'an wani. Yanzu haka muna js 2 nida Marwa wacce tundaga primary har yanzun tare muke tafiya kuma ajinmu guda yazeeda dai kam ta wucemu kuma da alama ta girmemu halinne kawai yazo d'aya ake d'iga fitina. A gaskiyar magana ba d'an k'aramin hak'uri anty Deenah keyi damuba muna mata abu iri iri tun tana kirb'armu har tagaji ta daina saidai idan munyi mata wani abun tace Allah ka shiryamin wannan yaran Yau da dare muka shirya zamuje duba alhaji bawa mak'ocin mune shima bashi da lafiya aka kwantar dashi a asbitin malam Aminu Kano da farko Hajiya tace baza'a damuba mukace wallahi koda k'afa ne sai munje sanin cewa da gasken sai munje yasa tace NAWAN ya d'auko motar daddy yakaimu MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 20 Duk mukayi wanka muka shirya anty Deenah sai hararan mu take nace "na rantse da Allah idan kika k'ara hararana bazaki shigar mana mota ba saidai ya Ali ko ya habu sukaiki a motarsu" Sanin halina yasa ta daina hararanmu amma tayi wani kicin kicin da rai har zamu fita anty Deenah ta dubi Hajiya tace "Hajiya kijawa yaranki kunne muje lafiya mu dawo lafiya kada su ja mana wata fitinar" ai kafin ta k'arasa nayi kanta da hargagi da hayaniya nace kece fitinanniya wallahi au da marasa ji kika d'auke mu wallahi yau sai an banbance tsakanin nidake waye fitinannen" sanin zan iya kamata da kokawa yasa Hajiya ta rik'o hannuna tace haba autana akwai fitinanne irinta karki wani biye mata ai nasan yarana masu hankali ne" da wannan Hajiya ta lallab'a ni muka wuce muka tafi duba alhaji bawa. A mota NAWAN yana ta jana da hira ni kuma ina tunanin ta yadda idan munje zamu zame mutafi mutuware dan ganin shin da gaskene akwai gawa mai tafiya ko kuwa k'arya Nana ce d'iyar wata mak'otanmu ce daga ita har uwar idan suka shirga maka wata k'aryar yasin saika zuba da gudu tsabar kid'imewa. Muna zuwa muka duba alhaji bawa mun d'an kwaahi mintuna kusan sha biyar a wajen kafin mu mik'e ya Abdul yace mu rakashi ya duba wani abokinsa kafin mu wuce rad'a yazeeda tayi mana nida Marwa muka kuwa shek'e da dariya muka tafa da sauri anty Deenah da NAWAN suka juyo sai kuwa na had'e rai dan karma su tambayi dariyan da kukeyi ganin yadda nai da fuskar yasa anty Deenah ta juya shima kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya sukaci gaba da tafi mu kuma muka zame mukayi wata lungu da yazeeda tace mana ta hanyar ne mutuware yake. Ba d'an k'aramin nisane tsakanin inda muka baro zuwa mutuwaren ba wallahi gagarumar tafiyace sannan kuma hanyar babu mutane sosai sai tsilli tsilli ga hanyar ya d'anyi duhu dan ba ko ina akasa kwaiba amma tsabar fitina irin namu haka muka doshi wajen. Muna zuwa mukaga ana fito da wata gawa, sai mukayi saurin komawa baya muka lab'e ganin bayan likitocin harda yan sanda araina nace ko gawar waye wannan oho saida suka sa gawar a motar asbitin sukabawa mai gadi kud'i suka tafi sannan muka fito. "Sannu baba" nace bayan mun k'arasa wajen mai gadin munyi sallama ya amsa had'a baki mukayi muka gaidashi kamar wasu yan makaranta ya amsa yana kallonmu da mamaki a ransa kuwa yana d'ar d'ar anya ba fatalwowi bane dan wani zubin ana firgita shi amma ba muraran irin haka ba saidai daga nesa. Katse masa tunanin nayi ta hanyar fad'in "baba dan Allah munzo ganin mutuware ne" Jin abinda mukace ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace "aiata kungani sai ku wuce ku tafi kafin gawar d'aukar fansa ta mik'e ta fara ta kanku, ya fad'i hakanne dan yasamu ya koresu. Wallahi gabana ya fad'i amma tsabar fitina nace "dan Allah baba nuna mana ita munason ganinta". "Gawar d'aukar fansan?" Ya fad'a yana zaro ido da mamakin rashin tsorona. In takaice muku labarin duk ta inda baba mai gadin mutuware ya b'ullo muce ba hakaba ya d'auke wani katon katako ya bimu da gudu muka arce MAMAN ISLAM NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRTERS ASSOCIATION☀️ Page 21 "Nifa bazan tab'a barin wajen nan ba saina shiga mutuwaren nan" na fad'a ina kallon Marwa tace"nima gaskiya ina son gani, ta fad'a cikin d'ar d'ar dan har ga Allah tsoron SUHANA ne ya hanata nuna zahirin tsoronta a fili dan SUHANA muguwar fitinanniya ce wallahi. Ta bayan d'akin muka zagayo saiga wani window da alama ma ba'a bud'e shi dan duk yayi funfuna kalle kalle na farayi ko zan hango wani abun takawar idanuna ya sauka kan wani benci can k'ark'ashin wata bishi ga d'an irin abin treder d'in nan da alama wani ke saide saide a wajen da sauri na nufi wajen Marwa tayi saurin bin bayana ita kuma yazeeda ta tsaya tana d'an dudduba ta inda zamu samu sauk'in haurawa. Bencin Marwa ta tayani muka d'auko da k'yar dan yana da nauyi wallahi daidai window muka ajiye na taka sai dai ko kad'an ban ga alamar na doshi hanyar isa kusa da window ba dan yana da tsayi sosai. NAWAN kuwa bayan sun fitone suka nememu sama ko k'asa suka rasa da da farko sunyi tunanin wajen mota mukaje mu jira amma ganin bama wajen hankalin NAWAN yai masifar tashi a matuk'ar gigice ya dubi anty Deenah yace. "Yanzu fisabilillahi Deenah ina kike tunanin TAWAN zataje, ko kuma kinji suna hiran zasu duba wani anan d'in, ko akwai wanda suka sani sani a quarters d'in asbitin nan?" Yadda ya wani gigice ya rud'e yana faman jera mata tambayoyi sai taji wani irin mugun kishin kanwar tata dan haka cikin d'an zafi zafi tace "ajiyansu kabani bare ka isheni da tambaya kasan hali ai ka taho dasu" Da mamaki yabi bayanta da kallo to shi kuma me yayi mata take masa tsawa haka? lallai ma yarinyar nan, ransa ya d'an baci da abin da Deedah tayi masa saidai bai sa abin yayi nisaba may be wani abun SUHANA tayi mata shine ita kuma ta huce akansa. Saida muka samo bencina uku harda turmi wanda mu kanmu saida mukayi mamakin ganin sa acan wani d'an lungu turmin fa k'atone wallahi. Saida muka gama daidaitawa sannan rigima ya balle tsakanin ni da yazeeda tana ita zata fara hawa ina nice k'arshe dai Marwa tace tunda yazeeda doguwace sosai ko bata taka turmin ba tsayin ta zaikai kawai muhau tare haka kuwa muka hau tare ai kuwa hawan yazeeda yayi amfani domin k'ofar a rik'e yake k'am k'am munaja munajin kamar anaja daga ciki amma tsabar naci bamu hak'ura ba gashi duk gumi ya jik'amu "anya k'ofar nan zai bud'u kuwa? Na fad'a ina kallon yazeeda tace "ai wallahi duk bala'in sa munfishi ko ana muzuru ana shaho sai mun lek'a wajennan yau" ita dai Marwa tana daga gefe tana jinmu jira kawai take taga daga daga ta arce. "Kinga mu had'a k'arfin mu waje d'aya muja k'ofar nan da mugun k'arfi zai bud'e" na fad'a wa yazeeda haka kuwa mukayi muka had'a k'arfinmu mukaja da k'arfi maimakon k'ofar ya bud'e sai mune muka fad'o dukanmu ai kuwa mun bugu a mazaunen mu mun d'an jima a zaunen muna tunanin yadda zamuyi saijin wani k'ak'arfan sauti mukayi k'a k'a k'a k'a k'a yif muka kai dubanmu jikin tagar dan muna tunanin jan da mukai ta bud'e. Nida yazeeda muka kalli juna muka tafa nace "ashema k'ofar me sufurun ce kingama ta bud'e kanta" Yazeeda tace"wallahi kuwa May be da zamu fad'o ne muka danna wajen budewar" Marwa ce da tagama rudewa ta hau duba jikin windown taga dai babu wani madanni ajiki tace. Akwai matsalafa 'yan uwa wannan k'ofar babu wani madanni ajikinshi kila dai wani fatalwar ne ya bud'e" hararan ta nayi nace "dalla can matsoraciyar banza fatalwar lafiya ana zaune k'alau" nayi maganar ne hankalina akan k'afana danaji yana d'an min zafi kad'an a inda na buge. Ita kuwa Marwa idanunta k'ur akan k'ofar da ya bud'e kanshi tabbas tasan dole wani abin zai faru ilai kuwa tana kuma kai kanta santar k'ofar sai ganin hannu tayi dogo yana fitowa ta tagar gashi duk ya huda likafanin jiki "innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA shine abinda Marwa ta fad'a da azabar k'arfi kafin ta d'iba da mugun gudu. Ni kuma na d'ago naga ihun da Marwa take min kawai idanuna suka sauka akan abinda na tabbatar da cewa shi ya tsorata Marwa gawace tsaye agaban mu nida yazeeda idan ba gizo idanuna keminba kamar murmushi take mana tana mik'o mana hannunta da gashi ya huda likafanin "yazeeda fatalwar ce ashe" na fad'a a haukace tareda daka wani mugun tsalle na fita da azababben gudu tuni na manta da batun zafin da k'afana kemin ai atake yazeeda ma ta rufamin baya. MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 22 Duk da cewa Marwace ta fara tserewa amma fit nazo na wuceta kamar aljana idan ba idonane yakemin gizo ba sai nake ganin kamar dani kad'ai fatalwar ta jeru tana sakin wani mugun huci hakanne yasa na k'arfin guduna danaga abin bana K'are bane sai kawai na rufe idona naci gaba da gudun a half. "SUHANA" naji muryan NAWAN ya kwalla min kira inda naji muryan ya fito na nufa da gudu ina haki kuma har lokacin bandaina jin hucin koma meye yake bina ba, jinai an rik'e ni nayi tunanin NAWAN ne sai kawai na bud'e ido wani irin razannen ihu na saki lokacin da naganni kwance a jikinta take numfashi na ya d'auke na sume a wajen. Da gudu yazeeda da Marwa suka k'araso kusa dashi suka rirrik'eshi suna haki "mugudu Yaya Abdul fatalwace" Marwa ta fad'a cikin tashin hankali kafin ta yanke jiki itama ta fad'i a sume. Wani irin kuka Deenah ta fashe dashi tana kallon yazeeda dake tsaye tana makyarkyata fitsarin tsoro nabin k'afafun ta sai Deenah ta k'ara rikicewa dan tayi yak'inin ba d'an k'ananun abubuwane suke saurin firgita SUHANA ba bare kuma yazeeda ta dame SUHANA ta shanye a tak'adiranci "ina kukaje?" Deenah ta tambayi yazeeda da rawan murya tana kuka, cikin rawan murya yazeedan tace "MUTUWARE mukaje shine fatalwa ya biyomu" "fatalwar me kuma?" Deenah da Abdul Samad suka had'a baki wajen tambaya" wallahi anty Deenah a gabanmu ya tsaya nida SUHANA ita Marwa ta rigamu guduwa" ran Abdul Samad yai masifar b'aci yace "inba masifa ba uban me ya kaiku mutuware ai gashinan zakuje ku kashe kanku abanza da hofi" daga haka ya d'auki SUHANA yace yazeeda ta taimakawa Deenah su kamo Marwa. Daddy da Alhaji suna waje sunacin abincin dare wanda suka makara wajen ci saboda fitan da suka d'an yi, suka hango Abdul Samad d'auke da SUHANA yayin da yazeeda da Deenah suka d'auko Marwa "lafiya Alhaji ya tambaya a kid'ime ganin an rik'o shalelensa kamar gawa "MUTUWARE sukaje wai fatalwa ya biyosu" "Mutuware?" Alhaji da Daddy suka had'a baki wajen fad'a suna bin Abdul Samad dayai ciki da SUHANA yama kasa magana tsabar b'acin rai. Haka Hajiya ma ta rud'e jin abinda akace ya faru ta rik'a salati tana sallalami tace "banda fitina irin nasu mai zai kaisu ma'adanar gawa matattarar aljanu da daren nan ai dole a firgita su. Da k'yar aka samu Marwa ta farfad'o dan ta kanta aka fara saboda ta wuce gida gudun kada a nemeta duk da cewa sunsan zai wuya matar babanta ta neme ta muddun ba ubanne ya dawoba. Ni kuwa da gayya Yaya Ali ya watsa min ruwan roba dake hannunsa mai uban sanyi na kwalla wani razannen ihu nace "NAWAN fatalwa fatalwa zata kasheni wayyo Hajiya da Alhajina ku taimakamin shike nan na kai kaina makabarta" Fashewa Hajiya tayi da kuka tana fad'in"innalillahi wainnailahi raji'un SUHANA shikenan tayi gamo wallahi mai ya kaiki mutuware idan ba masifa ba na shiga ukuna ni Hansatu" "Wallahi Hajiya duk ku kuka lalata yarinyar nan ke da Alhaji badama tayi laifi ayi mata fad'a sai ku d'aure mata gindi" fad'a sosai Ali ya kamayi babu wanda ya tanka masa ganin irin zaburar danakeyi duk suka rufu akaina suna yimin addu'a intakaice muku dai a wannan dare saida Hajiya ta had'a da karb'o min taimako kafin na samu bacci ya d'auke Ni. NAWAN kuwa ranan a gidan ya kwana d'akin Abdul Maleek sabida yasan ko yaje gida bazai iya runtsawa ba ina cikin wannan halin Washegari ragal na tashi karad'ina nema ya tashi sauran yayyena Yaya Ali yana fitowa kuwa ya zubamin wani mugun rankwashi yace " shegiyar yarinya fitinanniya sai na karya wannan k'afar yawon" ihun dana zunduma ne yasa Alhaji aanya gudu dama ya fara sakowa daga samansa zaije masallaci "mamana kedawa haka nakejin ihunki?" "Ba Yaya Ali bane ya rankwasheni" na fad'a ina Sosa wajen dan da zafi wallahi Alhaji yace "haba Ali haba Ali dan Allah yanzu bazaka tausayawa yarinyar nan halin data shiga jiyaba shine zakazo kana cin zalinta banason mugunta Wallahi" ganin Alhaji zai fara sababin nasa na fama akan antaba yar gwal Ali yayi saurin ficewa batare da ya tankaba. Gari na gama wayewa saiga Marwa ta shigo dake yau lahadi ce babu makaranta sai muka samu waje muka zauna muna maida abinda ya faru jiya nace"wai jiya ninaga bala'in dayafi k'arfina ashe dai Nana da gaske take akwai fatalwa ni wallahi na d'auka sai a shirin film ake ganinta" Deedah ta shek'e da dariya tace "maganin marasa jin magana kenan" na galla mata harara nace "to ina ruwanki damu?" Marwa tace"uhmm ni kam na daina binki muddun asbitine dan nasan halinki duk da wannan abun kina iya cewa baki gani sosai ba sai kin koma" Hararan ta nayi nace "banza matsoraciyar banza ke wallahi kin shiga uku da tsoro" "Eh shiyasa naga saidana sha rubutu na farfad'o daga suman danayi" "Wallahi kika kawomin iskanci yanzu zanci ubanki ai gwandani nayi jarumta keda tun kafin fatalwam ya diro gabanmu kin kwasa da gudu banza matsoraciyar banza" nanfa muka fara raba halin dama wani lokacin idan Marwa tagaji da halina na masifa biyamin take muyi tayi muna cikin haka babban Yaya ya iso da d'an sa a fad'a da gudu na nufi wajensa na d'auki yaron nayi hanyar waje MAMAN ISLAM CE NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 23 A k'ofar gida muka had'u da yazeeda muka kalli juna muka tuntsire da dariya yazeeda tana dariyan tace "shegiya SUHANA dama akwai abinda zai firgitaki irin haka?" Nima dariyan nayi nace "kedai bari yazeeda ai ban tab'a ganin bala'i irin najiyaba tsabar masifa duk ta wuce ku ta jeru dani saboda ni kad'ai ta gani, Allah nefa ya taimaka ban had'iye zuciya jiyan nan ba"na fad'a ina cigaba da dariya Nan muka shantake da yazeeda a k'ofar gida tunda yau mun tab'a halin da Marwa nasan bak'in ran ya motsa ko na mata magana bazata kulani ba. Muna haka NAWAN ya fito a gidansu muna had'a ido ya galla min harara zai shiga gida nayi saurin tare k'ofar nima ina hararan sa dan bazan bari yaci bulus ba na lura tun jiya yakemin wani kallon raini. "Me na maka malam dazaka wani sani a gaba da kallon banza ko mutum na kashe maka ai sai haka" na fad'a ina murgud'a baki shi kam bina kawai yake da kallo yana mamakin yadda bandamu da zaman lafiyata ba Allah wallahi jiya saura kad'an zuciyarsa ya buga saboda halin data shiga amma ji yanzu tazo tana masa rashin kunya. Hannu yasa ya janye ni a hanya batareda yace min k'ala ba dan yadda yakejin sannan zai iya mammakeni kuma yajawa kansa wata fitinar daban. Ni kuwa yadda yayimin ba d'an k'aramin haushin hakan nayiba a take anan nasha alwashin babu ni babu shi tunda bashi da mutunci matsalar yarinta kenan abu kad'an ne yake zama laifi a wajen yaro. Mun jima da yazeeda saidai yanzun munbar hiran muna zaune ne kawai tunda NAWAN ya b'ata min rai ban k'ara maganar da mukeyi ba itama yazeeda sai taja bakinta ta tsuke dan tasan idan ta takuramin yanzun zamu damben bala'i. Can na sunkuci Affan nace wa yazeeda mu had'u anjima idan antaso a islamiyya, ta amsa da to tabar k'ofar gidanmu nima na shige ciki. Falon Hajiya na samesu duka suna hira abin ya bani mamaki ya Abubakar ya Umar Usman ya Ali ya Abdul Maleek anty Deenah, ni wallahi nayi tunanin ma wani abun ne ya faru wai ashe hira kawai suke. A cinyar Hajiya naje na d'ora Affan na wuce d'akin Hajiya ban d'akin ta na shiga nayi wanka na fito na shirya cikin riga da sket 'yan kanti har lokacin suna hira kaina tsaye wajen Yaya Ali na nufa dan duk bala'in sa yafi sauran yan uwana yimin abinda nake so. "Ya Ali dan Allah kabani dubu d'aya da d'ari biyar kaji"na fad'a a marairace, ya aiko min da wani mugun kallo yace "kiyi uban me dashi?" "Gidan anty Zainab zanje daga nan na biya gidan anty Khady zan amso sak'o" bai tanka minba saima ya Ibrahim ne yace "an hana dan uwarki" Harara na galla masa nace "to na kulaka ne kuma wallahi badai Hajiya ba" yi yayi kamar zai taso na daka tsalle na d'ane ya Ali dan shi yafi kusa dani"kaga karka sake ka tab'a autarmu ya Ali ya fad'a yana zaro kud'in ya mik'o min dad'i ya kamani harda kwaso shoki. Inda NAWAN yake ban kallaba har na wuce gidan anty zee baiwar Allahn nan tana shan wahala wajen mijin nan nata dan Wallahi duk yan gidanmu basa k'aunar mijin anty zee saboda mugun halinsa, gashi Allah ya d'iga mata mugun sonsa ranta har b'aci yake idan aka kushe shi mugun gashi abu kad'an zai had'a su zai hau mata horon yunwa idan zasuyi wata suna gaba to zaiyi wata bai bata abinci ba MAMAN ISLAM NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 24 Sanin halin Ma'ruf mijin'yar uwata yasa a hanya na siyi kayan wainar fulawa na siya mata d'anyen kifi na d'ari biyar dake nima kud'ina da nake tarawa duka na had'a dasu saboda nasan zuwa gidan anty zee kashe kud'i ne. Tundaga k'ofar gida nake jiyo hayaniyar ma'aruf yana surfa bala'i bansan sanda na saki wani mugun tsaki ba na afka cikin gidan a raina nake fad'in wallahi yau sainaci ubanka ma'aruf muddun ka sake ka zagi Hajiya da Alhaji. Yana ganina kuwa yayi muk'us na watsa masa wani mugun kallo na saki tsaki na shige d'akin ai ina shiga anty zee ta d'auke fuskata da Mari "dan ubanki Abban Annur sa'anki ne da zaki masa tsaki" mamaki kusan kasheni yayi na kafeta da ido ina mamakin yadda anty zee take fifita ma'aruf akan yan uwanta shiyasa yawancin su suka k'yale ta take shan bak'ar wahala. Bak'in ciki ne yasa na durk'ushe a wajen na fashe da kukan bak'in ciki yayin da anty zee ta koma tana bawa ma'aruf hak'uri waini yarinya ce innalillahi ganin yadda ma'aruf ya d'auke anty zee da mari wai ai dama dukanmu bamu da tarbiyya,wannan magana ta mummunan tafarfasa min zuciya tun ina yar yarinyata na tsani wulak'anci bana jurar sa yana d'aya daga abinda yake masifar k'untata min d'ago idon da zanyi kawai ya sauka akan wani dutsen wuta guda biyu mai d'an girma da kuma k'arami nasan aikin Annur ne da sauri na d'auka ma'aruf dake ta zagin iyayenmu cikin tsantsar wulak'anci da cin mutunci sai jiyai na sauke masa dutsen da yasa jiri ya wulwulashi da k'asa, kafin anty zee tayi wani abu itama na sauke mata nata kuma na had'a da fad'in "Kuma Allah ya isana muguwa kawai azzaluma ki zauna ya kasheki a banza ba kowa yayi asaraba sai 'ya'yanki dan bayan ni akwai anty Khady da anty Deenah kuma kinwa kanki abinda na kawo dagashi bazan baki ko sisina ba wahalalliya" daga haka na d'iba da gudu na bar mata gidanta ina kukan bak'in ciki da mamakin abinda yau anty zee tamin akan wannan tsinannen ma'aruf d'in. Yadda anty Khady ta ganni wurjanjan ido jazur yasa ta rud'e tana tambayana abinda ya faru ban b'oye mata duk abinda ya faruba na fad'a mata, itama ranta yai masifar b'aci ta rik'a zagin anty zee ni kuwa cewa tayi nayi daidai. A takaice sai bayan sallar isha Sulaiman mijin anty zee ya kawomu muna sa kai falon mukai ido hud'u da anty zee yaya Abdul Maleek sai zaginta suke tana kuka. "Ga munafukar nan ai sai ki shigo ki kwance k'ullin da kikaje gidan mace kika had'a tsakanin ta da mijinta" inji ya Ibrahim, kafin ma nace wani abu anty Khady tace"dallah malam dakata karka takura mata ni abinda tayi yamin daidai ta burgeni wallahi, ke kuma baiwar soyayya saikije yaci gaba bautar dake kamar jaka" Ta fad'a tana fincikar hannuna mukayi ciki MAMAN ISLAM NAMIJI K'UDAN ZUMA By MAMAN ISLAM ☀️ FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️ Page 25 Gaban ya Ibrahim ta tunkud'ani "gatanan kashe ta, kasheta nace dan ubanka akan me wannan shashashar zata zauna wannan banzan yana azabtar dake da alama wannan dukane kika sha" Ta fad'a tana nuna gefen kanta inda na jefeta da dutse ya fashe shi ya Ibrahim duk bak'ar zuciyarsa shiru yayi yana kallon ta yau tunda yaga tana zuba ruwan bala'i yasan da akwai dalili. Ni kam banyi mamakin ganin anty zee a gidaba dan ma'aruf bashi da aiki sai korarta gida abu kad'an zatayi ya koreta idan tazo kuma maimakon ta tsaya a karb'ar mata hak'k'in ta sai tak'i tayi ta damunsa da waya ba dole yayita wulak'anta taba. Gaban Hajiya da tayi zaune tanajin duk yadda anty Khady ke fad'a kamar zata ari baki amma bata kulaba dan Khadija bata iya fushi ba. "Fad'a musu abinda ya faru SUHANA" kafin ince komai saida na dubi Hajiya nace "nida gidan anty zee har abada kawai dan ma'aruf yana zaginta nayi tsaki shine ta gauramin mari tana zagina ma'aruf d'in yana tayata wai harda cewa bakiyi mana tarbiyya ba wai duk haka muke sakaka ba kwab'a ni kuwa nayi musu ruwan dutsina ita da ma'aruf d'in na gudu" "Kinmin daidai autarmu ni dama na tsani wannan mijin na zainab dan dai kawai ta nace masa ne kamar wanda yake bata wani abu ni daga yau kada a k'ara cewa na bada kud'ina ayi mata wani abun tunda bata san ciwon kanta ba" Take falon ya kauraye da hayaniya aka hau zagin ma'aruf ana tsine masa saboda tsabar haushin sa da sukeji gashi da d'an banzan bak'in hali ita kuwa anty zee kuka tasa ta shige d'aki dama hakace take faruwa ta tsani a zagi ma'aruf da azageshi gwara a zagi Alhajinmu. Wai ashe bayan na taho harda duka ma'aruf yaiwa anty zee sannan ya korota amma baiwar Allahn nan kwana biyu banzan ya lallab'a ta muka nemeta muka rasa ta koma gidanta. Irin hakane yake faruwa duk lokacin da akaso k'watar mata hak'k'in ta bata bada damar hakan shiyasa ma'aruf yake masifar gana mata azabar wahala ********* Rayuwa taja sosai yanzun mun shiga js 3 aji uku na lokacin kuma wani yayan yazeeda mai kirkin gaske ya dawo daga k'asar waje karatu ba d'an k'aramin kirkine da bawan Allahn nan ba cikin k'ank'ann lokaci mukayi wata irin shak'uwa dashi wanda yake haddasa mana yawan fad'a da NAWAN saboda d'an banzan kishin sa dan zuwa lokacin ya jima da sanar dani irin son da yakemin kuma nima ina tsananin sonsa wannan Kennan. Zaune muke nida yaya Marwan muna hira NAWAN yazo wucewa Marwan yana masa magana ya saki wani mugun tsaki ya wuce kawai Marwan ya saki baki ya bishi da kallo kafin ya maida kallonsa kaina "ikon Allah SUHANA kodai Abdul Samad baida lafiya ne kinga ina masa magana yak'i kulani" "Uhmm nima bansan me yake damunsa ba" na fad'a muryata na rawa matsalata kenan da raina ya baci sai muryata ya kama rawa "Allah ya kyauta" cewar Marwan na amsa da "amen daga haka nayi masa sallama na wuce gida. A soro na tadda NAWAN cikin fushi yace "ban hanaki kula wannan mutumin ba?" "Idan aurena kake to daga yau ka fasa na fad'a tareda shigewa cikin gida ai kuwa ba k'aramin fusata yayi ba ya wuce gidansu cikin d'acin rai. A k'alla saida muka shafe kusan wata guda bama magana kafin mu shirya dan gaskiya bawan Allahn nan yana mugun zuciya ga masifaffen kishi tunda ya nuna yana sona ban isa kula koda abokiba. Cikin wata gudan da mukayi bama magana da NAWAN wani irin shak'uwa mukayi da Marwan wanda har mutane da yawa suke tunanin soyayya muke nan kuwa yace yana sona na fad'a masa gaskiyar magana tsakanina da Abdul Samad. "Hadiza wannan ciwon zuciyar da ya kamani ba sanadin komai bane sai Abdul Samad wanda na lura yana tsananin son SUHANA ni kuma bazan iya jurewa ganin Hajiya da Alhaji a cikin wani haliba yasa nake b'oye musu duk lokacin da ya motsamin nake jinya b'oye" Cak na dakata da shiga d'akin namu jin wannan batun mai kama da almara mamaki ne ya kusa kasheni yar uwata tana son saurayin danake tsananin so kamar raina kai innalillahi wainnailahi raji'un MAMAN ISLAM CE