ƘARSHEN ZALUNCI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 BABI NA ƊAYA Wata mata ce mai shekaru talatin sanye da kayan fata riga da wando, ɗauke da juna biyu a jikinta ke ta faman tafiya babu sassauci, A wasu lokutan har tuntuɓe take yi ta faɗi ƙasa, amma sai ka ga ta miƙe tsaye da ƙyar ta ci gaba da tafiya a cikin kasaitaccen birnin ma'abocin dogayen gine-gine. Sa'adda ya zamana ta shafe rabin rabin sa'a tana wannan tafiya sai kishi ya addabeta sakamakon tsananin zafin rana. Duba ɗaya za ka yi mata ka fahimci cewa tana cikin matuƙar buƙata, domin ƙafarta ko takalmi babu. Lokacin da ya zaman ta shafe sa'a ɗaya cur tana wannan tafiya sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a dai-dai wannan lokaci ne wani saurayi ma'abocin kwarjini da haiba ya durfafo inda take, yayin da ya iso daf da ita sai ya durƙusa bisa gwiwoyinshi. domin ya ga mene ne ya same ta cikin alamun tashin hankali. Nan take ya lura cewa tsananin kishi ne ya addabe ta har ta yanke jiki ta faɗi, cikin matuƙar kaɗuwa ya ciro wata salka dake maƙale a kwiɓin cinyarshi ta dama ya buɗe murfin. sannan ya sanya hannunshi ɗaya ya tallafo wuyan matar ya kafa mata salkar ruwan a baki, take ta shiga kwankwaɗar ruwan har sai da ta sha ya ishe ta, tana kammalawa sai ta ja gwauron numfashi sannan ta yi ajiyar zuciya ta miƙe zaune tana mai ƙurawa saurayin idanu hawaye na zuba. Al'amarin da ya bawa saurayin mamaki kenan kuma ya ji ya kamu da matuƙar tausayin, ya dubata cikin damuwa ya ce “Ya ke wannan mata shin ina dalilin wannan zubar da hawaye naki? Koda jin wannan tambaya sai hawaye suka sake kwaranyowa daga idanuwanta kuma ta yi shiru ba tare da ta ce uffan ba. Daga bisa ne ta buɗi baki muryarta na rawa ta ce. "Ya kai wannan saurayi ma'abocin tausayi da jin ƙai ka yi sani cewa a halin yanzu ba zan iya baka amsar watdannan da ka yi mini ba. Kuma bani da abin da zan saka maka bisa wannan taimako da ka yi min sai dai kafin mu rabu ina neman wata alfarma guda daya a wajen ka.” Cike da mamaki saurayin ya ce, "Ke kuwa wace irin alfarma ki ke nema a gare ni?" matar ta yi murmushin karfin hali, sannan ta ce "Alfarmar ta farko da nake nema a wajenka ita ce, ina so ka taimake ni da abin hawa haɗe da guzuri, sannan ina so kar ka bayyana labari na ga wani domin matsawar wani ya sani tamkar ka rushe taimakon da kayi mini ne.” Da jin wannan batu daga bakin matar sai saurayin ya sake cika da tsananin mamaki, kuma hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo mashi a rai shi ne; "Mene ne dalilin da ya sanya wannan mata tace na ɓoye labarin ta? idan na ba ta abin hawa da guzuri shin ina za ta je?" Amsar tambayoyin da saurayin ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar wani gida ya shige ciki. Jim kaɗan sai gashi ya dawo gare ta janye da wani ingarman doki fari ɗauke da guzuri mai tarin yawa. Koda ya iso daf da ita sai ya taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya riƙe mata linzamin dokin ta kama ta haye. Sannan ta sakarwa dokin linzami ta ci gaba da tafiya tana mai waigen saurayin hawaye na kwaranya daga idanuwanta. Nan take ya ji ya ƙara kamuwa da tsananin tausayinta, bai san sa'adda kwalla ta cika mashi idanu ba, ya ji a zuciyarshi cewa tamkar zai rabu da ɗan uwanshi na jini. Har sai da ya zamana sun daina hangen junansu sannan saurayin ya juya ya fice daga unguwar zuciyarsa cike da tausayin halin da matar za ta kasance a ciki. Bayan kamar shudewar daƙiƙa hamsin da tafiyar ta sai aka jiyo ƙarar takun sawaye gami da haniniyar dawakai ta cika unguwar. Koda jama'a suka leƙo daga cikin gidajensu domin su ga mene ne yake faruwa sai suka ga a she waɗansu gabza-gabzan Samudawan dakaru ne su kimanin dubu biyu shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, hannayensu rike da zaratan makamai. Bawasu bane waɗannan dakaru ba face na Sarauniya Abidat da ke mulkin Birnin Sin. Duk wanda ya leƙo ya yi arba da su sai ka ga ya rufe tagarshi da kofar gidanshi, tamkar ya hango mutuwarshi. Ya yin da dakarun suka iso izuwa tsakiyar unguwar sai wani garjejen kato ma'abocin kwarjini da ya fi sauran kirar sadaukantaka, ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Sannan ya kama linzamin ya sakko. Kwai sai ya dakawa sauran dakarun tsawa, kafin ya gama rufe bakinshi duka sun shiga karya ƙofafin gidajen unguwar suna fito da mutanen, mata da maza yara da manya. Kafin cikar daƙiƙa arba'in an tara gaba ɗaya jama'ar unguwar a waje guda suka yi masu ƙawanya. Garjejen ƙaton ya tako tafka-tafkan ƙafafuwanshi har izuwa inda jama'ar suke ya yin da ya zamana tazarar tsakanin su bata wuce taku biyu ba sai ya ja ya tsaya ya zare wata sharɓeɓiyar takobia gadon bayanshi ya dubi gaba ɗaya jama'ar da jajayen idanuwanshi masu kama da garwashin wuta yana mai nuna su da tsinin takobin cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce, "Shin a cikin ku wane ne ya taimaki wata mata mai ɗauke da juna biyu? Ina so ku yi sani cewa rashin nuna wanda ya taimake ta dai-dai yake da rasa rayukanku baki ɗaya." Koda jin wannan batu daga bakin badakaren sai hankalin gaba daya jama'ar dake wajen ya dugunzuma ainun, kuma su ka kamu da tsananin tsoro da yawa daga cikin su ba su san sa'adda suka saki fitsari a wando ba saboda firgici, kuma aka rasa wanda zai ce ƙala. Da ƙyar aka samu wani dattijo mai ƙarfin hali ya buɗi baki ya ce "Ya shugabana mu a yau babu wani baƙo da muka sauka a wannan unguwa tamu.” Kafin dattijon ya ƙara she zancenshi shugaban dakarun ya sanya takobinshi ya datse wuyan dattijon, kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jikin, jini ya yi tsartuwa gami da feshi take gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica! Kawai sai badakaren ya dinga sanyawa aka dinga kawo mashi jama'ar unguwar ɗaya bayan ɗaya yana yi masu yankan rago kai har ƙanan yara, mata da tsofaffi bai ƙyale ba. Haƙiƙa komai rashin imanin mutum da rashin tausayin shi idan ya ga yadda waɗannan dakaru ke yin wannan ta'addanci, dole ne ya zubar da hawaye saboda matuƙar tausayi. Koda kammala wannan kisan gilla ne sai ya sanya aka cinnawa unguwar wuta. Al'amarin wannan mata mai ɗauke da juna biyu kuwa, tun sa'adda ta rabu da wannan saurayi suna zubar da hawaye sai ta ci gaba da tafiya babu sassauci. Ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni har ta fice da birnin baki ɗaya ta nausa izuwa cikin daji. Tana cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabi sai dokinta ya kama sassarfa a cikin wannan hali ne ta ji alamun na guda sun zo mata. Kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak ta kama ta sauko sannan ta durfafi kofar wani kogon dutse, kafin ta isa sai ta yanke jiki ta faɗi kasa, a cikin wannan hali naƙuda ta kamata ta haife abin da ke cikinta. Cikin matuƙar farin ciki maras misaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga ko mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar jaririya ce ta gaban kwatance, duk da cewa tana cikin halin laulayi ba ta san sa'adda hawayen farin ciki suka zubo daga idanuwanta ba. A dai-dai wannan lokaci kukan jariri ya cika dajin baki ɗaya, cikin azama ta ɗauki wani siririn itacen mai kaifi ta yankewa jaririyar cibiya. Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Ba zato babu tsammani sai ta hango waɗansu zaratan dakaru haye bisa dawakai sun rugo izuwa inda take. Kafin ta yi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗana bakanshi ya harbe ta da kibiya a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da zugin da ta ji ba ta san sa’adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta na ci gaba da tsala. kuka. Har badakaren ya sake zare wata kibiyar ya saka a cikin bakan ya ja ya taɓe da zummar ya sake harbawa matar. Kwatsam! Sai aka ga wata irin murgujejiyar zakanya ta yo fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse ta dako suma ta bangaji kirjin badakaren da dukkan ƙarfin ta. Saboda ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokinshi suka yi sama kamar an janye su da ƙugiya, sannan daga bisa suka faɗo ƙasa tim ko shurawa ba su yi ba. Al'amarin da ya firgita sauran dakarun kenan kuma ya fusata ainun su suka zare makamansu a kara fara kallon-kallo tsakanin su da zakanyar. Shin abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan mata ta fito kuma mene ne dalilin daya sanya waɗannan dakaru ke farautar rayuwar ta dalilin hakan kuwa shi ne. BABI NA BIYU Fiye da shekaru dubu uku da ɗoriya an yi wani ƙasaitaccen birni a yankin ƙasashen Larabawa da ake yiwa laƙabi da Nurul-Kusuf. Birnin Nurul-Kusuf ya bunƙasa a fannin noma, kiwo da ma'adan ƙarƙashin kasa. Sarkin dake riƙe da KAMBUN MULKIN birnin ya kasance dattijon mutum mai matsakaicin kaurin jiki kwarjini da haiba, yana da tausayin talakawanshi da son ganin ya kyautata masu. Ana kiranshi da suna Urwat ɗan Unaifa, yana matar aure guda ɗaya jal wata kyakkyawar gaske da ake kira da suna Suhaimat, sun kai shekara goma da yin aure amma ba su samu haihuwa ba. Al'amarin da yake matuƙar ci masu tuwo a ƙwarya, amma ba su taɓa yanke tsammanin cewa za su sami haihuwa ba. A iya wanzuwar birnin Nurul Kusuf ba su taɓa yaƙi ba kuma ba a taɓa kawo masu HARIN BAZATO ba. Bisa wannan dalili ne ya sanya biranen da ke maƙwabtaka da su ke tururuwar zuwa birnin domin yin aikin fatauci siye da siyarwa. hakan ne ya sanya a kowacce rana sai ƙarfin tattalin arzikn birnin ya ƙara haɓaka, har ya zamana sun zamto babbar cibiyar kasuwanci a nahiyar. Sai dai kash, wani abin takaici shi ne duk tarin arzikin da jama'ar birnin Nurul-Kusuf ke da shi ya tashi a banza, domin duk bayan wata guda suna bayar da haraji ga wata saruaniya da adadin shi ya kai dinare dubu ɗari shida. Wannan MULKIN ZALUNCI da Sarauniya Abidat ke yi masu yana matuƙar ci masu tuwo a ƙwarya domin a wasu lokutan da ƙyar suke samun ɗan abin da za su kai bakinsu. Wata rana da hantsi Sarki Urwat na zaune a bisa karagar mulki, sanye cikin ƙayatattun tufafi na alfarma, fadawanshi na kewaye da shi ana tafiyar a sha'anin mulki cikin walwala da jin daɗi. Kwatsam! Sai aka hango wani manzo ya durfafo fadar riƙe da wata doguwar wasika a hannunshi sanye da korayen tufafi irin na mutanen birnin Sin. Lokacin da rage saura kamar taku huɗu tsarkin shi da karagar mulki sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya miƙa wasikar wani bafade ya karɓa ya miƙawa magatakarda. Ba tare wani ɓata lokaci ba magatakarda ya warware wasiƙar sannan ya fara karanto abin da ke ƙunshe a ciki a fili kowa yana saurare. "Takarda daga Sarauniyar duniya uwar Hatsabibai Abidat bintu Hargal zuwa ga Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf ma'abocin biyayya a garemu. Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa ban rubuta maka wannan wasiƙa ba sai domin in ba ka wani umarni wanda amince da shi ne tsira a gare ka, saɓani shi kuwa na iya jefa al'ummarka cikin musiba. Na samu labarin cewa a koda yaushe tattalin arziƙin birninka yana daɗa bunƙasa, bisa wannan dalili ya sanya nake so ka nunka adadin harajin da kake kawo mani izuwa kaso uku, kuma kai da kanka na ke so ka zo ka kawo ba aike ba. Tabbas idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Daga Sarauniya mai cikakken iko, zuwa ga bawanmu Urwat Ibn Unaifa Sa'adda magatakarda ya zo nan a karatun wasiƙar sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake fadar ya dugunzuma ainun, kuma fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Daga can sai Sarki Urwat ya yi ƙarfin hali, fuskarsa cike da alamun matuƙar damuwa ya yi umarni da a tafi da ɗan aiken Sarauniya Abidat izuwa masauki, sannan ya fuskanci jama'ar fadar ya yi gyaran murya ya ce, “Ya ku Jama’ar wannan fada tawa mai albarka ku yi sani tabbas a halin yanzu rayuwarmu na cikin tsaka mai wuya, bisa wannan wasika da sarauniya Abidat ta aiko mana, don haka na sallami kowa zamu tattauna tare da 'yan majalisa domin samun mafita. Kafin Sarki Urwat ya gama rufe bakinshi jama'a sun tashi daga wajen zamansu suna masu fice daga fadar cikin kaɗuwa da tashin hankali. Shiru ne wanzu a fadar bayan sauran jama'a sun fice sai daga bisa ne Sarki Urwat ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar yin gyaran murya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya dubi 'yan majalisarshi ɗaya-bayan-ɗaya ya ce “Ya ku dattawan wannan birni namu mai albarka sanin kan ku ne cewa hanyar da muke biyan Sarauniya Abidat haraji muna fuskantar takura shin ta ya zamu iya riɓanya ukunshi? Sannan kun san cewa zamu iya yaƙar Sarauniya Abidat ba domin har abada linzami yafi ƙarfin bakin kaza ta ninka mu a yawan MAYAƘA. Koda jin wannan magana daga bakin Sarki Urwat sai hankalin 'yan majalisar ya dugunzuma ainu fiye da koyaushe, shiru ne ya sake wanzuwa. Waziri Samazan ya yi gyaran murya ya ce, "Ya 'yan uwana 'yan majalisa ku yi sani cewa, yanzu idan har muka bawa Sarauniya Abidat abin da ta bukata, tamkar mun rushe wannan birni namu ne da hannayenmu. Domin idan har muka bayar da kuɗaden tattalin arzikinmu zai durƙushe, baƙin fataken dake zuwa birnmu za su dai na zuwa, sannan a cikin muwane ne yake da tabbacin zamu iya mayar da abin da muka bayar kafin nan da cikar lokaci. Ina nufin a lokacin da zamu sake biyan wani harajin? Da jin wannan magana daga bakin waziri sai kowa ya ƙara shiga taitayinshi. Galadima Salmir ya fara magana a karo na farko da fara wannan tattaunawa ya ce, "Ya 'yan uwana 'yan majalisa hakika fa maganar Waziri abar dubawa ce, sai dai wani hanzari ba gudu ba, idan muka ce zamu yaƙi sarauniya Abidat rayuwar 'ya'yenmu da matayenmu tana cikin mawuyacin hali, sannan dole ne a samu hasarar dukiya da ba a san iyakarta ba, ina ganin kawai mu bi umarnin Abidat domin mu tserar da rayuwar jama'armu." Sa'adda 'yan majalisa suka ji wannan shawara daga bakin Galadima sai fiye da rabin su suka nuna goyon bayan su akan hakan. A inda aka tsaya akan cewa za a ɗebi dukiyar baitul-mali sannan kowanne magidanci zai bayar da dinare ɗaya. A ranar da mako biyu suka cika Sarki Urwat tare da wasu daga cikin 'yan majalisar da amintattun bayinshi suka shiga yin shiri domin tafiya birnin sin. Bayan Sarki ya kammala kintsawa ne sai ya nufi turakar uwargidanshi Suhaimat yana shiga ya tarar da ita zaune bisa kan ƙasaitacciyar kujera, kuyangi na kewaye da ita suna shayar da ita tacaccen ruwan inibi a kofin zinare, yayin da kuyangin suka yi arba da sarki sai suka fice daga turakar suna masu kwasar gaisuwa, ita kuwa suhaimat sai ta miƙe tsaye ta rugo izuwa inda maigidanta yake ta rungume shi. Daga bisa ne Sarki Urwat ya janye jikinshi daga nata fuskarshi cike da annuri ya dube ta ya ce. “Ya hasken ruhina ku yi sani cewa a yau ne zamu yi tafiya izuwa birnin sin domin aiwatar da umarnin sarauniya Abidat ta yi mana, ina fatan za ki yi mani fatan alheri har mu dawo lafiya.” Koda jin wannan batu sai fuskar Suhaimat ta canja daga Annashuwa izuwa tashin hankalin ta dubi maigidanta cikin alamun damuwa ta ce, "Ya Uban 'ya'yana ki yi sani cewa tabbas jikina ya bani wannan tafiya da za ka yi babu alheri a cikinta, shin me ya sanya za ka nisan ta da ni a lokacin da ya kamata a ce kana kusa da ni? Cikin alamun rashin fahimta Sarki Urwat ya dubi Suhaimat ya ce, "Ban fahimci abin da kike nufi ba ya farin cikina? Suhaimat ta yi tattausan murmushi ta ce, "ya farin cikin zuciyata a halin yanzu ina ɗauke da juna biyu har na watanni bakwai." Cikin matuƙar farin ciki da al'ajabi sarki ya ce, “Amma ta ya aka yi ki ka san hakan? Suhaimat ta ce "Na samu hakan ne daga baiwata kuma likitoci sun tabbatar mini da hakan." Koda jin hakan farin ciki ya turnuƙe Sarki Urwat har hawaye suka zubo daga idanuwanshi ya rungume Suhaimat suna masu fashewa da kukan farin ciki, sai da ƙyar da siɗin goshi sarki ya janye jikinshi daga na Suhaimat suka yi bankwana, suna masu karanto waƙoƙin baitoci. Dake nuna alamun tsantsar so da ƙauna. Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da waɗannan masoya biyu ke zubar da hawayen begen rabuwa da juna dole ne ya kamu da tausayin su ainun, ya tabbatar da cewa babu abin da yafi rabuwa da masoyi ciwo. Kai tsaye Sarki Urwat ya fice daga gidan sarautar ya nufi inda ayarin su suke yana isa aka kawo mashi doki ya kama ya haye sannan ya sakar mashi linzami ya ɗauki sauran ayarin suka mara mashi baya, sai da jama'a suka yi masu rakiya har izuwa bakin gari sannan su Sarki Urwat suka ɗauki hanya aka fara tafiya aka nausa izuwa cikin daji. Da aka fara wannan tafiya sai Sarki Urwat ya yi umarni aka sanya raƙuman dake ɗauke da dukiya da guzuri a tsakiyar, jama'a suka suka yi mata ƙawanya. Sannan dakarun rakiya suka rabu gida biyu, kaso ɗaya kewaye jama'a kaso na biyu suka sake rabuwa gida huɗu, suka tsaya a gabas, yamma, kudu da arewa, domin tabbatar da tsaro. Daga birnin Nurul-Kusuf izuwa birnin Sin tafiyar kwana biyar ce ba tare da yada zango ba, amma da yake su Sarki Urwat suna so ne su isa a cikin ƙanƙanin lokaci sai ya zamana ko yada zango ba a yi ba, kuma suna tafiya ne ba dare ba rana. A ranar kwana na biyu ne da La'asar sakaliya su Sarki Urwat suka iso ƙofar birnin sin, kai tsaye dakaru masu gadi suka wangame masu Ƙofar suka kunna kai zuwa ciki. Yayin da suka isa fada sai suka tarar fadar ta cika maƙil da jama'a duk inda mutum ya kai duban shi a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da bil'adama rututu, tamkar dandazon kiyasai. Fadar ta kasance tanƙamemiya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun more rayuwa iri daban-daban, wani abin ma mutum bai taɓa gani ko jin sunan shi ba, girman fadar ya kai na wani ɗan ƙaramin gari, kai tsayawa misalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce tunanin mutum sai dai abin da idanuwa suka gani kawai. Bisa kan wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta jauhari aka yi matattakala biyar da dutsen zubardaju. BABI NA UKU Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance. Tana da matsakaicin kaurin jiki ita ba doguwa ba ce ba gajera ba, fatar jikinta fara ce mai ratsin baƙi, tana dara-daran idanuwa farare ƙwal masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, ɗigon cikin su yakasance baƙi siɗik, tana da dogon hanci mai ɗaukar hankali, a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur. wuyanta dogo ne mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, saboda rigar dake sanye a jikinta har kana iya hangen sheƙin fatar su. Cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda koda kofin lemu aka ɗora zai zauna daram akai. Tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun hannuwanta da ƙafafuwa zara-zara ne, gashin kanta baƙi ne mai ƙyalli ya zuwa izuwa gadon bayan ta har zuwa kan kwankwasonta. sanye take cikin koriyar alkyabba mai ratsin fatsi-fatsi. sanye a kanta akwai kambun Sarauta da aka yi shi da zunzurutun zinare yana sheƙi da ɗaukar idanu. Wohoho! Haƙiƙa komai nisan gari da wani a gaban shi. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Komai hassadar mutum idan ya yi arba da wannan budurwa dole ne ya tabbatarwa da kanshi cewa ta kai maƙura a kyan diri da sura. Babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine duk sa'adda ta yi murmushi sai kyawawan fararen haƙoranta sun bayyana, fuskarta na fitar da sheƙin kyawu tamkar hasken farin wata. Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kamu da matukar kaunarta. Ba wata bace wannan budurwa ba face Sarauniya Abidat. Sarauniya Abidat Bintu Hatyal ta kasance gawurtacciyar Basadaukiya mai dakawa maza gumba a hannu, ta shahara ainun a sanin ilimin tsafi gami da tarin dukiya, daɗin daɗawa kuma ta tara zakwakuran MAYAƘA masu juriya a filin daga. Bisa wannan dalili ya sanya take kai farmaki izuwa ƙasashe da biranen da ke maƙwabtaka da ita domin ta faɗaɗa girman masarautarta. Tsananin zaluncin Sarauniya Abidat ya zarce tunanin mutum, domin babu wanda ta ragawa tsakanin talakawanta, attajirai har ma da fadawanta. Akwai wata rana da Sarauniya Abidat ke zagayawa cikin kasuwa domin ganin yadda al'amuran cinikayya ke gudana. Tafe take a bisa ingarman doki cikin ƙayatattun tufafi ta rufe fuskarta da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, waɗansu irin gabza-gabza samudawan dakaru ne ke take mata baya, hannayen su ɗauke da miyagun makamai sai muzurai suke yi tamkar za su ci babu, kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci cewa murmushi bai taɓa wanzuwa a kan fuskokinsu ba. Duk wajen da Sarauniya Abidat da dakarun suka durfafa a kasuwar sai dai ka ga yara da manya na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin ladabi, kuma suna darewa suna buɗa masu hanya tamkar sun hango mutuwarsu, ko ciniki ake yi da zarar su Abidat sun durfafo wajen sai ka ga masu siye da sayarwa sun zubar da kayayyakin dake hannayensu, sun faɗi ƙasa sun kwashi gaisuwa. Haka dai Sarauniya Abidat da tawagarta suka ci gaba da tafiya suna ratsa layuka da unguwannin kasuwa. Ana cikin wannan tafiya ne Sarauniya Abidat ta hango wani dattijo yana gyara waɗansu kayan marmari a cikin kwandon kaba, har ya zaman tazarar dake tsakaninsu bata huce taku shida ba amma dattijon bai daina aikin da yake ba ya zo ya kwashi gaisuwa. Koda ganin hakan sai Abidat ta fusata ainun zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta kone bisa ganin yadda dattijon ya nuna rashin ladabi a gareta. Cikin matukar fushi Abidat ta kama linzamin dokinta ta sauko ta yiwa dakarun ta inkiya da wutsiyar ido. Tamkar dakarun sun san abin da take nufi sai kawai suka je suka cakumo wannan dattijo suka gurfanar da shi a gaban ta Kawai sai Abidat ta zaro wata 'yar siririyar wuka a damtse ta yanke kunnen dattijon na dama, saboda tsananin raɗadi da zogin da dattijon ya ji bai san sa'adda ya kurma wawan ihu ba a lokacin da jini kezuba daga wajen, cikin alamun rashin imani Sarauniya Abidat ta sake yanke masa dayan kunnen na ɓarin hagu jini ya yi tsartuwa gami da feshi. Haka ta ci gaba da yankewa dattijon ƙananan gaɓoɓin da ke jikinshi. Haƙiƙa Sarauniya Abidat ta cika AZZALUMA ta gaban kwatance, domin komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda dattijon ke ihu da koke-koken neman agaji dole ne ya tausaya masa ainun. Da yawa daga ckin jama'ar da abin ke wakana a kan idanuwansu ba su san sa'adda ƙwalla ta cika muasu idanu ba suka fara zubar da hawayen tausayi. Koda Sarauniya Abidat ta ga cewar ta yanke duk wata gaɓa da ke jikin dattijon sai kawai ta takarkare ta bushe da dariyar mugunta. A dai-dai wannan lokaci ne numfashin dattijon ya sarƙe jikinshi ya sandare ya faɗi ƙasa, alamar dake nuna rai ya yi halinshi. Kawai sai aka jiyo ihu da kururuwa a tsakiyar jama'a, koda Sarauniya ta duba sai ta ga ashe matar wannan dattijon ce ta rugo izuwa wajen, tana mai rusa kuka, hannayenta riƙe da jariri ɗan shekaru biyu da haihuwa. Kafin matar dattijo Safwan ta iso wajen, Sarauniya Abidat ta zaro wani dogon mashi a jikin badakaren ta jefawa matar, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu a cikin iska ya soke a ƙirji, ya fasa ta gadon bayanta jini ya kwaranya gami da tsartuwa, take ta sulale ƙasa tana shure-shuren mutuwa, kafin wani lokaci idanuwanta sun ƙafe, komai na jikinta ya daina motsi, alamar ta baƙunci barzahu, amma wani abu da ya ɗaurewa Sarauniya Abidat da sauran jama'a kai shi ne, duk da kasancewar matar dattijo Safwan ta sheƙa barzahu babu rai a tare da ita, amma hannunta riƙe yake da jaririnta gam! Kuma fuskarta cike da annuri. Cikin matuƙar mamaki Sarauniya Abidat ta nuna jaririn da ɗan yatsan ta na hagu, take jaririn ya baro hannun mahaifiyarshi ya sauka a hannayenta biyu yana mai tsala kuka, koda ta ƙura wa jaririn idanu sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki, kenan ta ce a cikin ranta, "Me ya sanya da na haɗa idanu da wannan jariri zuciyata ta buga da ƙarfi alhalin hakan bai taɓa faruwa a gare ni ba?" Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta miƙawa wani badakare jaririn, sannan ta kama linzamin dokinta ta hau, ta zabure shi ta shige gaba dakarun ta suka mara mata baya, yayin da aka isa gidan Sarauta sai Saruaniya Abidat ta bayar da renon jaririn ga wata baiwarta mai suna Sunaifa, daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana face bincike bisa halarar tsafinta domin ta gano sirrin da ke tattare da jaririn dattijo Safwan. Sa'adda ya rage saura kamar taku huɗu tsakanin su Sarki Urwat da karagar mulki sai suka zube ƙasa bisa gwiwoyinsu suka kwashi gaisuwa ga Sarauniya Abidat, cikin matuƙar taƙama da BAKAR IZZA Abidat ta karɓi gaisuwar. Shiru ne ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai daga bisani ne Sarki Urwat ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "Ya shugabata gani na amsa kiran ki kuma tare da abin da ki ka buƙata domin FANSAR RAYUKAN jama'ata." Koda jin wannan batu daga bakin Sarki Urwat sai Sarauniya Abidat ta miƙe tsaye tsam! Daga kan karagarta ta tako matattakalar fadar ta sauko ƙasa, sannan ta taka da kafafuwanta har izuwa inda Sarki Urwat da jama'arshi ke duƙe ta shiga kewaya su tana mai bushewa da dariyar mugunta a lokaci guda kuma sai ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAKON MUTUWA ta dubi sarki Urwat ta ce "ya kai Urwat ka bi dukkanin wani umarni da muka baka sai dai a halin yanzu ina so ka umarci mutanen ka su fice daga birnin Nurul-Kusuf su nemi wajen da za su zauna." Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya Abidat sai idanun sarki Urwat suka zazzaro, cikin alamun matuƙar kaɗuwa da firgici ya dubi sarauniya Abidat cikin biyayya ya ce. "Haba ya sarauniyar duniya ta ya ya zan cewa al'ummata su fice daga birnin Nurul-Kusuf bayan cewa tun iyaye da kakanni suke zaune sannan fiye da rabin harajin da na kawo miki sune suka haɗa rabinshi ina neman alfarma a wajen ki da ki janye wannan ƙudiri na ki." Da jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu daga bisani ta haɗe rai ta ce, "Tabbas duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma rashin sani ya fi dare duhu" ya kai Urwat ka yi sani cewa, tun da nake a rayuwata kai ne mutum na farko da na taɓa faɗar magana ya ce ba haka ba, yanzu zan gindaya maka sharuɗɗa guda biyu dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki. Na farko shi ne ko dai kai da jama'arka ku fice daga birnin Nurul-Kusuf ko kuma ku bayar da ZARATAN MAYAKAN KU mutum hamsin." Sa'adda Sarki Urwat ya ji waɗannan sharudɗa daga bakin Abidat sai ya sake marairaicewa, yana mai yiwa yi mata magiya a kan ta janye waɗannan sharudɗa na ta. Al'amarin da ya jefa tausayi a zukatan jama'ar kenan kuma zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su kone, bisa ganin yadda Urwat ke ƙasƙantar da kanshi a gaban wacce bata huce 'yar cikin shi ba. Su kansu sauran jama'ar fadar sai da suka kamu da matukar tausayin shi. Ya yin da Abidat ta fahimci cewa Sarki Urwat ba shi da niyyar amincewa da ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ta gindaya mashi sai kawai ta yi wuf ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanta ta datse masa wuya, take kanshi ya yi fitar burgu gangar jikin ya faɗi ƙasa rikica! JINI ya yi tsartuwa haɗe da feshi tamkar an buɗe kan famfo. Kafin ɗaya daga cikin jama'ar marigayi sarki Urwat ya yi wani yunƙuri sarauniya Abidat ta afka masu da azababben yaƙi cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba gaba ɗaya ta sare kawunansu ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa ɗayan su bai tsira da rayuwarshi ba, nan fa jini ya dinga malala tamkar an ɓalle ƙorama. Sannan aka ga Abidat ta runtse idanunwanta ta karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai aka ga wani baƙin hayaƙi ya ratso daga cikin karkashin ƙasa ya tashi izuwa saman fadar ya ɓace ɓat! Kawai sai ta sake bushewa da dariyar mugunta tamkar ba za ta daina ba. BABI NA HUƊU A can birnin Nurul-Kusuf kuwa, shugaba Hushaib na zaune a fada bisa karagar mulki a matsayin halifan Sarki Urwat ana gudanar da sha'anin mulki cikin walwala. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! tamkar hadari ya gangamo, nan take gari ya kaure da guje-guje haɗe da iface-ifacen jama'a. Har shugaba Hushaib ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai aka hango sarkin yaƙi ya shigo fadar hankalinshi a matuƙar tashe, tun kafin ya iso inda karagar mulki take shugaba Hushaib ya je ya tare shi ya dube shi cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Ya dirkar birnin Nurul-Kusuf shin mene ne ke faruwa?" Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi Ikram ya dube shi cikin tashin hankali ya ce, "ya shugabana ka yi sani cewa tabbas yau ce rana ta farko da zamu fita yaƙi iya tsawon kafuwar wannan birni namu domin kuwa waɗansu irin halittu ne suka sauka a wannan birni namu, ni kaina tunda nake ban taɓa ganin irinsu ba ko a labari. Koda jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Ikram sai shugaba Hushab ya dube shi cikin kaɗuwa ya ce, "Haƙiƙa na ji a jikina cewa shugaba Urwat da tawagarshi na cikin halin tsaka mai wuya kuma waɗannan halittu da suka bayyana a garemu ba sa rasa nasaba da abin da ya faru da su a can birnin Sin ɗin saboda haka sai ka yi umarni a yi maza a je a buga kugen yaƙi domin a tari abokan gaba..." Kafin shugaba Hushaib ya gama rufe bakinshi sarkin yaƙi ya juya, ya fice daga fadar da sauri. *** A can fadar sarauniya Abidat kuwa sai da tayi dariya ta ishe ta sannan ta yi umarnin a kwashe gawarwakin sarki Urwat da jama'arshi kuma aka goge jinin da ya zuba a fadar, sannan ta koma kan karagarta ta mulki ta hakimce. Kawai sai ta zura hannunta a cikin aljihunta na hagu ta ɗauko madubin tsafinta wanda duka tsawonshi bai wuce girman faɗin tafin hannunta ba ta shafeshi da hannun hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai ga taswirar abin da ke gudana a birnin Nurul-Kusuf ya bayyana a kan madubin. Sa'adda sarauniya Abidat ta ga yadda waɗannan miyagun halittu da ta tura ke hallaka jama'ar marigayi Urwat ba ji ba gani tamkar suna kashe kiyasai, hatta dabbobin garin ba sa ƙyalewa ballanatana ƙananan yara. Koda ganin wannan al'amari sai farin ciki ya cika zuciyarta haka dai ta ci gaba da kallon yadda artabun ke gudana har kawo izuwa lokacin da halittun suka kammala kashe duk wata halitta da ke birnin kasancewar su ma su shugaba Hushaib ba karamar ɓarna suka yi masu ba. Jim kaɗan sai taswirar birnin ya ci gaba da canja launi har ya nuno taswirar wata mata tana gudu a bisa doki, a cikin daji waɗannan halittu na biye da ita a baya suna so su cimmata amma sun gaza. Ba wata ba ce wannan mata ba face Suhaimat matar marigayi sarki Urwat, Suhaimat na cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabai al'amarin da ya sanya gudun dokinta, ya ragu kenan, kuma ya bawa ɗaya daga cikin halittun dama ya samu nasarar mako ta daga kan dokinta. Kash! Hakika rashin sani ya fi dare duhu, ashe inda dokin Suhaimat ya durfafa wani ƙaton rami ne wanda a ƙarƙashin shi akwai ruwa, koda wannan halitta ta make Suhaimat daga kan dokin sai ta ci gaba da mirginawa a ƙasa ya yin da ta isa daf da ramin ta ga inda za ta afka sai kawai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu take numfashinta ya ɗauke. Sa'adda taswirar ta zo dai-dai nan akan madubin tsafin sarauniya Abidat sai ta bushe da dariyar farin ciki, ta mayar da madubin izuwa cikin aljihunta sannan ta sake miƙewa tsaye tsam! Daga kan karagar mulkin ta ta durfafi wata ƙofa da za ta sada ta da gidan sarautar dakaru na take mata baya. Nan take sauran jama'a suka miƙe daga wajen zamansu suka fice daga fadar suna masu faɗar albarkacin bakunansu bisa wannan tsantsar zalunci da Abidat ta yiwa Sarki Urwat da talakawansuhi, wasu har suna rokon abin bautarsu da ya a kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat. Lokacin da Suhaimat matar Margayi Sarki Urwat ta faɗa izuwa cikin wannan rami mai zurfi cikin halin suma sai igiyar ruwa ta ci gaba da tafiya da ita, sai da gari ya waye sannan igiyar ruwan ta kawo gaɓar tekun, kusa da wani daji ma'abocin tarin bishiyu da duwatsu da ƙoramu, kuma ya tara kayayyakin ni'ima, waɗansu irin kyawawan tsuntsaye na shawagi a sama suna fitar da sauti mai daɗin sauraro. Ya yin da hasken rana ya fito sosai sai Suhaimat ta farka daga dogon suman da ta yi tana mai jan dogon gwauron numfashi, kuma ta buɗe idanuwanta ta miƙe zaune koda ta ga a inda take hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanta. A sannan ne ta ji yunwa da kishirwa sun addabeta kuma raunikan da ke jikinta suna yi mata raɗaɗi da zugi, don haka sai ta miƙe tsaye da ƙyar ta shiga izuwa dajin domin ta samu abin da za ta yi kalaci. Daga wannan rana Suhaimat ta kasance a cikin dajin ba ta da abokan ɗebe mata kewa face tsuntsaye, a duk sa'adda ta tuna maigidanta marigayi Sarki Urwat da jama'ar birnin su sai ta fashe da kukan baƙin ciki. Amma da zarar ta tuna cewa tana ɗauke da juna biyu sai ta cika da matuƙar farin ciki domin ta san cewa za ta haifi abin da zai dawo mata da farin cikinta kuma ya kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat Sa'adda Suhaimat ta fahimci cewa juna biyunta ya cika wata tara. A koda yaushe naƙuda za ta iya kamata ta haife abin da ke cikinta, sai ta yanke shawarar ta ci gaba da tafiya domin ta samu wani birni a gaba da za ta haife abinda take ɗauke da shi. Sai da ta shafe tsawon kwanaki huɗu tana tafiya a ranar kwana na biyar ne lokacin da rana ta take ta yi tsananin zafi Suhaimat ta iso wani kasaitaccen birni tun da ta shiga birnin ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni a iya tsawon rayuwarta bata taɓa ganin birnin da ya ƙawatu kamarshi ba, tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wannan wane birni ne na shigo? Kuma a wace nahiyar nake. Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai ta ci gaba da tafiya a cikin birnin, tana cikin tafiya ne ta zo giftawa ta cikin kasuwa sai ta ji waɗansu dattawa guda biyu suna hira a tsakanin su a inda ɗayan ya dubi ɗan uwanshi ya ce, "Shin wai kuwa ka ji labarin abin da ya faru da Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf da jama'ashi na kisan wulakancin da Sarauniya Abidat ta yi masu." Ɗayan ya ce, "Kwarai kuwa na samu labari kuma na jinjina al'amarin matuƙa, fatana shi ne a samu wani GWARZON ƘARNI da zai kawo maka KARSHEN ZALUNCIN wannan sarauniya tamu." Sa'adda Suhaimat ta ji abin da dattawan ke tattaunawa a kai sai zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ta ji ta tsani sarauniya Abidat fiye da komai a rayuwarta. Kuma a sannanne ta fahimci wannan birni da ta shigo shi ne birnin Sin tana tana cikin wannan hali wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shi ne ya zama wajibi ki fice daga wannan birnin matsawar kina bukatar ki haife abin da ke cikinki, domin da dazarar Abidat ta ganki ba za ta bar ki a raye ba. Koda Suhaimat ta zo nan a tunaninta sai kawai ta ci gaba da tafiya da sauri domin ta fice daga birnin baki ɗaya. Wannan shi ne dalilin da ya sanya dakaru Sarauniya Abidat ke farautar wannan mata wato Suhaimat matar marigayi Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf. SHIN SUHAIMAT DA JARIRIYARTA NA TSIRA DAGA SHARRIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT! WACE IRIN ƊAUKAKA JARIRIYAR SUHAIMAT ZA TA SAMU A DUNIYA? SHIN INA LABARIN ƊAN DATTIJO SAFWAN WANDA SARAUNIYA ABIDAT TA BAYAR DA RENONSHI GA BAIWA SUNAILA? WANE IRIN AZABABBEN YAƘI ZA A YI TSAKANIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT DA WANNAN ZAKANYA? Mu hadu a KARSHEN ZALUNCI 2 na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.