TATTALIN SO Complete Hausa Novels by Surayya.txt

Author :  Surayya Category :  Home Of Novels

Chapter   14 / 18

39K to 42K   out of 51.6K words

yayi saurin bude musu bayan motar,
sukashiga ya rufe, zai shigo ya jasu Aliyu ya dagamasa
hannu, tare da cewar ba tafiya zamuyi ba.Yace ok sir, ya
tafi can wajen shuke-shuke yayizamansa.Ya dubeta, yace
zeeyra menene?Meya daga miki hankali kike hawaye?Ta
marairaice masa, tace yaya daman 'yan matane dakai?
Yace zeeyta wace irin magana ce wannan? Ainakika taba
ganina da 'yan mata?Yaya gani nayi ranar da muka zo,
wata tayomaka tes, tana yi maka barka da sauka,
yanzukuma gashi kuna ta hira da wata, tana tayi
makamurmushi.Oh! Sorry zeeyta, ya rungumota yana
rarrashinta,yayi murmushi wai zeey dinshi ta iya kishi.Ya
rada mata kunanta zeey kinsan bani dara'ayin tara mata,
da ina da ra'ayi shekarun damukayi da mansura a baya
danayi aure.To da yake bani da wani buri sai naki
shiyasawata 'ya mace bata taba burgeni ba, bare ta
banisha'awa. Shiyasa na zauna zaman jiranki HarAllah ya
kawomu na aureki, yanda kike auta agidanmu, to a wajena
ma kene autar mata, dominkece gimbiyar zuciyata ba wata
bayanke. Tasadariya Allah yayana?Allah zeeyta.Ta
rungumeshi tana dariya.Satinsu biyu a kano suka koma
abuja, kuma batasake haduwa da mansura ba, tun a wajen
fatinnan, bata kuma gayawa Aliyu cewar, ga abundatayi
mata ba.Tana kicin tana girki, ta rinka jin kanta yanajuyawa,
jiri yana dibanta, ta kasa hassala komaita zauna a kicin din
dirshan, ta matsa kararrawarkiran talatu ta shigo da
saurinta, tana fadin ganiaunty mami,halin data ganta ciki ya
bata tsorolafiya aunty mami.Ta rinka nuna mata kanta tana
lumshe idosaboda jiri.Talatu ta gigice ta daukota ta
shimfide a falo, kandoguwar kujera.Ta dauki wayan zainab
din ta laluba numbarAliyu, ta danna, tana ringin daya ya
dauka, hellozeeyta.Cikin dabir-dabir tace, ba ita bace talatu
ce, yacecikin rikicewa, talatu lafiya, ina zeey din tawa ne?
Tace bata jin dadi ne gata a kwance.Yayi zumbur ya mike
da wayan a hannunsa yafito, ya hau motarsa, bai tsaya
kiran direba bayayo gida cikin mintuna kadan.Talatu tayi
mamakin saurin zuwansa.Ya dagota zeeyta lafiya meya
sameki haka?Ta rinka nuna masa kanta, ya rike kan yana
yimata addu'a, ta rinka jin tashin zuciya, tanakokarin amai,
ta yunkura, tana so tabar jikinsa,
[7:59AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**2
Tana kokarin amai ta yunkura, tana so tabar
jikinsa, don kada ta bata shi, amma sai ya sake
rungumeta, ta rinka yunkurin aman kasancewar
bata ci komaiba sai ruwan shayi kawai data sha
ta amayar.
Ya rinka shafa kanta yana yi mata sannu, idonsa
shima yayi ja kamar yayi kuka don tausayin zeey
dinshi.
Saida ta gama aman ta kwanta luu a jikinsa
saboda rashin kuzari.
Ya dauketa ya kaita toilet ya wanke mata jikinta,
ya cire mata kayan jikinta, ya sake yi mata
wanka ya nadeta a tawul.
Ya cire kayansa yayi wanka ya canja kaya, yasa
mata wasu kayan, ya dauketa ya nufi mota, ya
sata ya figi motar da gudu.
Don du ta galabaita aman data yi ya rafkar da
ita.
Abunka da asibiti na kudi, na manya mutane, nan
da nan aka karbi zeey, likita ya fara yi mata
aune-aune da taimakon gaggawa.
Aka debi fitsarinta da jininta.
Suka jona mata karin ruwa da allura, tana ta
baccinta, Aliyu yana zaune gefenta, du ya damu
ganin yanda ta rame lokaci daya.
Bayan lokaci kadan likita ya dawo da gwaje-
gwajen tes din da yayi mata.
Ya mikawa Aliyu hannu cngrtln soja mata tana
dauke da cikin wata biyu.
Wani irin nishadi da farin ciki ne ya kwarara a
zuciyar Aliyu, ya washe baki yana murna ya daga
hannu sama yana godiya ga ubangiji.
Yace nagode likita, ka duba min madam sosai,
inaso ka kure tunaninka, ka rubuta mana
maganguna masu kyau, wanda zasu kara mata
lafiya da kuzari ita da baby.
Likita yayi murmushi yace, kada ka damu, du
maganin da nasan zai taimaka musu zan rubuta
muku, amma laulayi dole sai kunyi a hankali, da
cikin yayi kwari zata samu yanda kake so.
Ka rubuta min abubuwan da zata rinka ci da sha
da zai kara mata lafiya da babyn.
Ok zan rubuta muku, Allah ya kara sauki, amin.
Likitan ya fita Aliyu yayi waya ofis dinsa yake
gayawa sakatariyarsa du wanda yazo nemansa
yana asibiti, madam dinshi ba lafiya.
Ta jajanta masa tare da fatan Allah bata lafiya.
A hankali ta bude idonta tana kallon karin ruwan
da akayi mata.
Ya kashe wayar tare cewa sannu zeeyta.
Tace, yaya kasa akayi min allura, a cire min
wannan bana so.
Ya rinka shafa kanta yi hakuri barinsa su cire
miki,
ya dagota zaune, tana rungume a jikinsa, likitan
ya shigo Aliyu yace, yauwa cire mata karin ruwan
naga ya kare.
Tana noke hannun, tana wash-wash, tana
langwabe ajikin yayan nata, da haka likitan ya
zare mata allura yana tsokanarta raguwa me raki.
Aliyu ya rinka rarrashinta yana bata youghot da
kaza.
Kwananta uku a asibiti ta samu sauki, ta ware,
abokan Aliyu da matansu kullum suna turuwar
zuwa dubata, taji sauki an sallameta ta koma
gida.
Aliyu kullum yana manne da zainab har hutu ya
dauka, yake zaune a gida, don dai kawai kulawa
da ita, bashi da magana sai cikin dake jikinta
kamar bai taba haihuwa ba.
Tana kwance akan kujera tayi matashin da
cinyarsa yana karanta mata jarida.
Talatuwa ta kwankwasa kofar akayi mata iznin
shigowa.
Tace aunty mami, me za a girka miki?
Tace kiyi min pepper chicken, sai kiyi min hadin
salad. Shikenan
tace, to yaya fa? Tace a'a haba talatu girkin
yayan nawa zan baki kiyi?
Ki bari kawai na samu sauki zan mishi da kaina,
na hotel dinma an daina siye.
Talatu tayi murmushi, tace to uwar dakina, ta fita
Aliyu yace nifa bana son abunda zaki wahala ki
bari naci gaba da siyo a hotel din.
Tace, haba yayana kamarka ka rinka shiga hotel
siyan abinci.
Ni dai bana so, ka bari zan rinka yi maka nafa
samu sauki.
Ya shafa cikin nata, to ai ni babyn nawa kada
yazo yana kara saki amai, wahala kike yi zeeyta.
Bari dai nayiwa su Abba waya na gaya musu
albishir tunda kin samu sauki na gaya musu mun
samu ciki.
Tayi saurin damke wayar cikin shagwaba, nidai
yaya gaskiya kada ka gaya musu, so kake su san
abunda muke yi, da wane ido zamu kallesu? Nidai
kunya nake ji.
Haba zainab haka zamuyi ta zama bazamu gaya
musu abun farin ciki da ya samemu ba?
Um nidai yaya kada ka fada kunya nakeji.
To shikenan bazan fada ba.
Cikinta yana wata hudu aka karawa Aliyu girman
babban matsayi a soja, a lokacin ne kuma ya
gama musu tamfatsetsen gida da yake musu gina
a kano, ginin da aka farashi tun kafin ya auri
zainab.
Kowa da bangarensa fadin tsarin gidan bata
lokacine,
lokacin suka taho kano don zasu tare a sabon
gida.
Sannan zainab ta ciko tayi fresh, yaron cikin dan
wata hudu yayi mata kyau, yadan tasa kadan,
amma ba kowa ne zai iya ganewa da cikin ba, sai
me kula.
Lokacin da suka sauka 'yan gidansu sun
zagayeta kamarsa cinyeta, kowa dada sonta
yake, Abba da daddy sunfi kowa jin dadi da
alfaharin auren 'ya'yan nasu.
Umma kuwa kamar ta lashe zainab saboda
tsananin jin dadi, bama data hango dan matashin
cikin da yake jikinta, tana ganin kuma ta samun
jika daga wajen yaron kirki.
Ni'ima da sadiya suna zuwa suka rungumeta,
suka yi saurin cikata suna taba cikin, zeey ciki?
Ta kwalalo ido "bani da komai, suka yi dariya,
"um mun gani dai.
Ranar akayi walimar tarewansu a sabon gida,
kowa ya yaba da tsarin gidan da kyansa makeken
gida unguwa guda, ga wajen wasan buga ball,
wajen basket ball, lilina na yara, ga lambu da
swiming ful a ciki. Da dai abubuwan kawata gida.

TATTALIN SO 4**3
.
Yarinka lallaminta yana jijjigata kamar karamar yarinya,
harta koma bacci, sannan ya mike ya tafi. Be dade da jan
motarsa ya tafi ta farka da wani gigitaccen ciwon baya da
mara, ta farka tana salati, ta matsa kararrawar kiran talatu
shiru bata shigo ba ta tuna fa ashe tun dazu ta tafi gidan
yarta. Ta taso a hankali tana dafe da kugu, tana salati ta
fito babban falo. Mansura tana zaune tana kallo, ta jiyo
salatinta da nishinta, ta juyo tana kallonta, ta tabe baki ta
juya taci gaba da kallonta. Zainab ta durkusa a gabanta ta
daura kanta akan cinyarta, tana salati. Aunty dan girman
zatin Allah ki taimaka min ki tallafawa maraicina, ki dubi
girman Allah aunty kinsan abunda nakeji. Saita ji jikinta yayi
sanyi, taji tausayin yarinyar ta tuna irin gigicewar dayi
sanda tana nakudar Ahmad, da yanda yarinyar tai ta kuka.
Ta juyo ta kalleta, ta murkususu a jikinta, ta dauki waya ta
bugawa direban gidan, tace maza ya fito da mota. Ta
taimakawa zainab din, saida suka shiga direba ya dauki
hanyar asibiti data ke zuwa awo. Mansura ta fito da
wayarta tana neman layin Aliyu amma bata sameshi ba, har
suka isa asibitin, ana kokarin shigar da ita dakin haihuwa,
ta samu lambar Aliyu ta shiga. Ringin uku ya dauka, hello!
.
Aliyu muna asibiti da zainab ba lafiya. Kafin ta karasa cikin
kara yace mata what? Tayi saurin cire wayan daga
kunnenta, don jin yana barazanar tsorata mata dodon
kunne. Daga nan ya hawo motarsa ya nufo asibiti, ya tarar
da ni'ima da sadiya dasu umma sunata zarya a kofar dakin
data ke ciki. Yana zuwa bai tsaya ba ya banka dakin
haihuwar tayi wujiga-wujiga tana salati, wata likita tana
tsaye a kanta. A galabaice ta rinka miko masa hannu, tana
cewa wayyo yayana zan mutu, yaya ka yafemin, yaya haka
mamana tayi shiyasa ta rasa ranta. Yazo ya zauna a gefen
gadon ya rungumeta, yana rarrashinta kiyi shiru zainab, kita
addu'a Allah zai saukeki lafiya kinji? Ya rinka murza mata
bayanta, yana karanata addu'o'i ya tofa a ruwa ya bata
tasha. Taji ciwon ya lafa mata, ta bingire a jikinsa ta fara
bacci, can wani gigitaccen ciwo ya farkar da ita, cikin lokaci
kankani ta rikice da salati ta kankame Aliyu likitan tana
taimaka mata, katuwar 'yarta ta fado fara tas da ita. Wata
irin dariya Aliyu ya saka, tare da jerawa ubangiji kirari, yana
nuna godiyarsa ga Allah. Ya dauki 'yar ya rungumeta,
yanata aikin kallon babyn, likita tana gyara zainab, kamar
wanda aka mutsina yayo waje da gudu yana kiran umma,
mama, ummi, gaba daya suka yo kansa suna masu farin
ciki.
.
Ummi ta karbeta, kai tubarkallah masha Allah. Su ni'ima da
sadiya sai lekenta suke yi a hannun ummi, su naso su
dauketa, amma Aliyu ya hana, wai kada a jagwagwalaa, ko
ya manta suma sun a haihune. Likita ta fito cikin kalmar
turanci take ce masa likita baka tsoro bebyn tayi mura ne,
ka fito da ita take shakar iska? Aliyu yace ato ku kawota. Ya
karbeta da sauri yayi cikin dakin da ita. Su umma duk suka
bishi don ganin jikin zainab din. Zainab tana ganin su umma
ta rufe idonta wai kunyarsu take ji, ni'ima da sadiya sunata
yi mata dariya. Mansura kuwa tana tsaye a gefe tana
mamakin irin murnar da Aliyu yake yi, kamar wanda bai
taba haihuwa ba. Mansura ta fito daga dakin, don bazata
iya kallon takaici ba. Ya wani zauna dirshan a gadon zainab
din, jikinsa yana gogar nata, kamar zai rungumeta, sai wani
dariya yake. Ta dauko wayarta ta buga, hello yaya saratu,
yarinyar nan fa ta haihu yanzu, haba dan Allah meta haifa?
Um du wannan iyayi da akeyi ta bige da haihuwar mace.
Saratu tace "A me bambacin mace da namijin,kema ai yaya
saratu kinsan mace da namiji akwai bambanci.
.
Ai namij shine magajin gida bare ahmad shekara takwas fa
kenan, a hada da 'ya mace ta mintuna amma kinga yanda
shida kannensa da iyayensa yanda suke ta wani murna da
farin ciki. Saratu tace gaskiya mansura sai anyi miki uzuri,
wannan hali naki sai an taimaka miki da addu'a, ni kinga
bazan iya sauraran wadanan kananun maganganu naki ba,
ta kashe wayar. A ranar aka sallamesu saboda mai jego da
baby lafiyarsu kalau. Ummi itace a gun zainab. A ranar da
dare saida ta kori Aliyu bangarensa, da asuba talatu ta girka
garwa kan kuka gas, ruwan ya tafasa ta kwashe, ummi tayi
wa zainab cikakken wakan jego, tana zillewa tana wash a
haka aka gama. Zainab tana shiryawa ummi tana yiwa
baby wanka talatu tana goge lokaci daya du suka gama.
Me jego da baby sun fito dagwas shar dasu, gaba daya
bangaren nata ya rikice da kamshi me rikita zuciya. Karfe
takwas Aliyu ya shigo, ya durkusa ya gaida ummi, ya karbi
babyn a hannunta, yace ummi zeey din tana ina? Tana daki.
Ya mike da babyn a hannunsa ya shiga dakin , sai yaji
kamshin da dakin yake yafi na ko ina dadi. Tana zaune a
gefen gado ya shiga da dariyarsa, me jego kinsha kamshi.
Tayi murmushi yazo ya zauna kusa da ita. Ta durkusa kasa,
yaya ina kwana? Lafiya lau, yaya babyn ta kwana? Gata
nan ka ganta. Ya dago zainab din ta zauna a jikinsa, zainab
kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni?
.
Zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni? Saboda
me yaya? Wallahi tunani babyn nan tawa 'yar kyakywan nan
ta zauna min daram a rai, tunda na taso ranar da aka
haifeki, na ganki kika zauna daram a zuciyata, ban taba
tunanin za a samu abunda zai kuma shiga zuciyata ya
zauna min irin haka ba, sai gashi kin haifa min kyakyawan
diyata da tafi komai shiga zuciyata. Zainab ta kalleshi cikin
shagwaba tace, yanzu yaya kafi sonta dani? Yayi murmushi
ya shafi fuskarta, yace ai ke dabance zeeyta, kaunar
danake miki bata da misali, amma kinga bebyn nan tawa
ma ta maye ruhina gaba daya. Zainab kin gama min komai
da kika haifomin bebyn nan, bani da bakin da zan miki
godiya, bani da abunda zan baki. Babbar addu'a da zan
miki Allah ya miki tukuici da gidan Aljannah amin yayana.
Bebyn ta dan motsa, ya balle marfin swan water, ya tsiyayo
kadan a kofin azurfa ya bata tasha. Yace bata nononta
tasha. Yaya wallahi data kama jiya, baka ji zafi ba. Yi hakuri
ki bata a hankali zai daina zafin. Zainab din taba bata tana
cije baki tare da cewar wash. Lallabata yakeyi yana cewa,
yi hakuri zeeyta, tasha ta koshi, yauwa bata dayan. Da haka
babyn tasha ta koshi, ya karbeta ya dorata a kafada, yana
shafa bayanta har tayi gyatsa taci gaba da baccinta. Zainab
ta dora kanta akan cikinsa, yana tambayarta me da me take
so ayi shagalin suna? Suka jiyo karadin ni'ima da sadiya
suna buga kofa yace su shigo. Suka shigo, sadiya tace
yaya ka hade zeey din da bebyn du ka rikesu anan ga
jama'a ga jama'a can sunata zuwa barka ba me jego ba
beby. Yace nifa bana son yawan daukan nan fa, saboda shi
yake kawowa yara ciwon jiki. A fitar da kan gadonta falon a
sakata a ciki, a rufe da net din, du wanda yazo ganinta ya
ringa lekata kawai, a ganta haka basai sun dauka ba. Ranar
kwana hudu aka kawo kayan barka akwatuna shidda uku
na beby akwatuna uku na mai jego fadan kayan da suke
cikin akwatin bata lokacine.
.
Mansura ta mike fuu tayi bangare Aliyu, ta banko kofar
dakinsa, babu sallama ta tsaya masa tsegege aka, yana
kwance akan gado yana kallonta. Tace Aliyu nagaji da
wannan rashin adalci naka, ni bazan iya zama ba, kana
nuna min iyakacina, ka dubi uban kaya daka jibgawa zainab
da jaririyarta, ni wallahi bazan yarda ba saide kome zai faru
ya faru, ya daga mata hannu ki saurara kada kiyi min
hayaniya aka, fita ki bani waje. Ta fito ta kwashi akwatunan
daya bata ita da Ahmad tasa aboot din motar da ya bata da
akwatunan ta tafi gidansu. Mansura tana isa gida, tasa
kannanta suka shigo mata da akwatunan, iyayenta suna
falo da saratu da hauwa, suka tareta da lafiya? Tace
wallahi Alh na gaji da rashin adalcin mutumin nan, ka dubi
'yan kayan da ya bamu nida Ahmad, amma ita ya hada
mata akwatuna shidda ita da 'yarta kuma ya bata irin motar
da ya canja min. Saratu ta bude kayan tana gani, super da
holland da les da material da shadda ganila ga takalma
jaka da sarkar gwal. Akwatin Ahmad ma kananan kaya
masu tsada, sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki,
kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu kyau da
tsada, harda glas mai ruwan gwal suka gama gani, saratu
ta rufe kayan, hajiya tace mun gani Allah ya saka da
alkhairi, ubangiji ya kara buda masa. Mansura tace, hajiya
nifa na taho gida, ku kirashi kuyi masa fada bazan iya zama
da wannan rashin adalcin nasa ba.... Kafin ta rufe bakinta
Alh ya wanke mata fuska da mari, hajiya ta rufeta da duka.
Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya kawomin
makullin mota sabuwa kar. Ya aikowa da mahaifiyarki
katon injin kankara don ta rinka sana'a dashi shine kike
kokarin tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to du
ranar da kika sake zuwa gidan nan kika kawomin karar
mijinki, saina karyaki, bare kuma kiyo yaji, wannan kasheki
zanyi murus har lahira. Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje
da sauri,
.
kananta suka mayar mata da akwatunan cikin mota, taja ta
koma gida tana hawaye, fuskarta da yatsun babanta daya
mareta. Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu yana
zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta wuce bangarenta.
Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman zainab, suna
kiranta da ihsan. Taron suna yayi kyau angama lafiya aka
watse. Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba,
daga kawayenta, abokan Aliyu 'yan uwa da abokan arziki,
kayan kamar a bude sito dashi. Yaya ni'ima tace, kinsan
kuwa yau shekarar ku uku cif da aure da yaya. Shida yayi
alkawari saikin shekara uku sannan zai kusanceki, sai gashi
shekara uku tazo da 'yar diyarku ko? Zainab tace ke kika
jiyo, ni ba ruwana. Suka sa mata dariya. *** ***** kwanci
tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi arba'in, harta koma
abuja, taci gaba da karatunta. 'yar diyarta saida daddynta
ya nema mata tsari sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya
bude baki, sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take.
Ihsan watanta shidda kenan tayi 'yar kubibi abun sha'awa
da 'yan hakoranta biyu abakinta, tayi sabo da Aliyu du
sanda ya dawo gida, yana tare da ita, don haka data ganshi
tana bayan talatu zata rinka zillo. Ya karbeta ya rungumeta,
yana murnar ganinta...
[8:01AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**4
Tabbas badan tasan zafin zuciyar Aliyu ba, ba
zaiyi mata ta dadi ba, da sai ta barar da abincin.
Fuu! Ta tashi tayi daki, kamar kububuwa, su
kuwa basu kula da ita bama.
Sati yana cika suka koma Abuja, Aliyu yaci gaba
da rainon zainab da cikin da yake jikinta, taci
gaba da zuwa makarantarta, Aliyu shi yake dada
ganar da ita gun da ya shige mata duhu, don
haka kwakwalwarta ta sake budewa, take da
kokari sosai.
Don ma yanzu cikinta yayi nauyi, wani abun yana
yi mata wahala, tana daurewa ne, don saboda
Aliyu kokari yake ya hanata zuwa makarantar,
wai tana wahala.
Ga hajiya tanata damunsa da waya ya kawo
zainab ta haihu a gida, du sanda yazo wkend
hajiya ta sashi a gaba kenan tai ta mita.
Dole sai ya kawo zeey din ko kuma tasa a
kawota, har abujan ta taho da ita.
Yace hajiya kiyi hakuri, exam suke yi, yanzu saura
sati biyu su gama, suna gamawa zan dauki hutun
shekara saimu taho tare, tace to yanzu naji
magana.
Suna gama jarabawa kuwa, da sukayi hutun wata
biyu suka taho gida kano.
Du wata siyayyar haihuwa ta kayan baby da mai
jego Aliyu ya wuce dubai zaiyo musu acan.
Satinsa daya acan ya dawo ya tarar cikin zeey
dinshi ya kara girma, don komai a wahale take
yinsa, da kyar take daga kafa.
Har baya so yaga ta tashi don sai yaga kamar ya
ciro cikin ya dawo dashi jikinsa.
Da ta tashi zai dawo da ita, menene ne, ina zaki?
Yaya lemo zan dauko maka, ya kwantar da kanta
a kafadarshi yana lallaminta kamar karamar
yarinya, ki bari zan dauko da kaina, don Allah ki
daina wahalar da kanki, ni nake jin ciwon ajikina.
Sai kuma ta langwabe a jikinsa ta kama kuka ya
rinka jijjigata, yana rarrashinta, ya rada

14 / 18