Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Bookz
GUGUWAR ANNOBA
ABDULAZIZ MADAKIN GINI
08137237071
Nan take jikin Yarduza yai sanyi, shima ya
tsaya cak! Yana kallonsa, a lokacin da Sharlisa tsaye a bayansa ta zuba musu idanu kawai.
Kuraisu ya budi baki ya co, "Lale marhaba da dana mai kama da ubansa. Matso gareni na
dumin dan dan uwana wanda na rasa shekara d shekaru.
Koda yazo dai-dai nan a zancensa sai haway ya subuto masa. Ba tare da fargabar komai ba
kuw Yarduza ya ruga gareshi suka rungume juna kuma suka fashe da kuka a lokaci guda.
Sai da suka jima a kankame da juna sanna Yarduza ya junye jikinsa daga cikin na Kuraisu yı ce,
"Ya kai Abbana ka yi sani cewa zan kasanc mai tsananin farin ciki idan har zan zauna tare d kai
daga nan har izuwa sa'adda mutuwa za rabamu."
Sa'adda Kuraisu yaji wannan batu sai ya hannu ya share hawayensa sannan ya dubi Yardua
cikin alamun matukar damuwa ya ce, "Ya b dana, ai lokaci va vi karanci a gareni rayuwar das
rage min kankanuwa ce.
Kafin ku iso nan gareni na ga duk abinday faru a tsakaninka da kai da 'yata a cikin madu
tsafina. Na vi farin ciki da ka amince za kab bukatunmu amma ka sani cewa ba zan yarda kada
ni izuwa cikin gari ba face bisa kan sharadi uku
Sharadi na faro shi ne, sai kayi mana alkawari cewar ba za ka gayawa kowa ko ni waye ba,
domin a halin yanzu kai kadai ne ka san cewa ina nan a rayc
Sharadi na biyu shi ne, ina son ka yi mana alkawarin cewar za ka shigar da gunkin matata a
cikin wannan daki na ka na sirri wanda babu mai shigarsa sai kai kadai
Sharadi na uku shi ne, za kayi watsi da duk wata shawara wacce 'yan majalisarka za su kawo
maka a kaina ko 'yata a cikin tsawon kwana bakwai da zan yi a tare da kai a cikin gidan
sarauta."
Lokacin da Kuraisu yazo nan a zaneensa sai Sarki Yarduza yai shiru yana nazarin wadannan
sharuda guda uku a cikin zuciyarsa har izuwa lokaci mai tsawo. Daga can sai ya kawo gwauron
numfashi ya ajiye ya ce, "Shi ke nan na amince". Cikin tsananin farin ciki Sharlisa da Kuraisu
suka kama shirye-shiryen tafiya.
CAN fadar Birnin Kaluza kuwa, jama'a amma kowa hankalinsa akan bakin kofa yake
domin so ake kawai aga shigowar Sarki ya dawa farauta daga Ba komai bane ya daga hankalin
jama'a ba face lafiya ganin yadda ko sau daya Sarki bai zauna ba a fada tunda aka gama bikin
nadin sarautarsa, gani ake kamar rayuwarsa za ta iya salwanta a daji, sakamakon wannan
farauta da yake fiya
Koda yake mahaifinsa ma an sanshi akan wannan al'ada ta fita farauta daji shi kadai, amma shi
ba da safe yakan fita ba sai da yamma bayan an gama zaman fada.
Kwatsam! Sai aka ga Sarki Yarduza tare da bakin mutane guda biyu sun shigo cikin fada. Bakin
dai sun kasance mace da namiji.
Macen wata kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance wadda ta sa gaba dayan jama ar da ke
cikin fadar suka dimauce suka rude domin ko a wajen masana tarihi basu taba jin labarin an yi
mace mai ifin kyanta ba.
Shi kuwa bakon namijin, wani tsoho ne wanda ya rankwafa yai doro yana tafiya da kyar, amma
wani abin mamaki a tare da shi ne yana goye da wani katon sungumin ice wanda aka
nannadeshi cikin tsumma babu wanda ya san ko mene ne wannan abu.
Abin tambaya anan shi ne. "Ta ya ya wannan sohon mutum ya iya daukar wannan sungumi mai
nauyi a Bayansa alhalin sungumi ne mai girma da пацу
Idan mutum ya lura da kirar jikin tsohon wacce ta kasance irin ta samudawa zai iya baiwa kansa
amsa cewa nai karfi yana ga mai alamar kiba.
Kai tsaye Sarki ya nufi inda kujerar mulkinsa take tare da bakinsa mutum biyu. Koda ganin haka
sai 'yan majalisa suka mike tsaye don girmamawa. Da isarsu daf da karagar mulki sai Sarki
Yarduza ya kamawa tsohon wannan katon sungumi da ke bayansa ya ajiye a kas, sannan ya
tsohon ya yi masa umarni da ya hau kan karagarsa ta mulki ya zauna
Gaba dayan jama'ar da ke cikin fadar sai suka bude baki suka kurawa Sarki idanu cikin
tsananin mamaki, aka rasa wanda zai ce kala.
Sarki Yarduza ya dubi Sharlisa ya nuna ma ta wata kujerar da ke daf da karagar mulki ya ce
itama ta zauna. Sharlisa taje ta zauna sannan Sarki Yarduza ya tsaya a gabansu ya fuskanci
fadawansa da sauran jama'a ya ce, "Ya ku jama'ar Birnin Kaluza ku yi sani cewa wadannan baki
da nazo da su yanzu sun kasance masu matukar daraja a idanuna, saboda haka daga vau ina son ayi biyay ga wannan tsoho da ke zaune akan karagata
kam vadda ake vi mini har izuwa tsawon kwana bakws Duk irin abinda ake yi mini shi nake so a
dinga masa. Kada a rage masa abu daya".
Koda gama fadin hakan sai Sarki Yarduza koma gefe daya ya zauna a kasa dirshan kusa
karagar mulki tamkar almajiri, sannan aka ci ga da tafiyar da harkokin mulki.
Al'amarin da ya matukar baiwa gaba daya mutanen da ke fadar mamaki ke nan kuma
dugunzuna hankalin 'yan majalisa.
Daga can sai shugaban Majalisa yazo zauna daf da Sarki Yarduza yai masa rada a kunne ya
ce, "Ya shugabana wannan abu da kayi yanı bai taba faruwa ba a wannan masarauta tamu
tabbas abin kunya ne kuma abin gori zuri'arku". ne ga
Koda jin wannan batu sai Sarki Yarduza y dago kai ya dubeshi cikin tsananin fishi da fusat ba
tare da ya ce komai ba. Nan take jikin shugabe majalisa ya kama karkarwa, domin ya san coHE
shiru ma amsa ce.
Cikin sanyin jiki shugaban majalisa ya mik tsaye ya koma inda yake ya zauna.
Kuraisu ya kama kallon karagar mulkin da yake zaune a kanta tamkar dan kauye ya shigo Bimi,
sannan ya rinka kallon fadawa da sauran jama'ar gari da kuma sauran kayan kawar da ke fadar.
Daga can sai ya mike tsaye ya kama yawo a cikin fadar yana taba kayayyaki yana kyalkyala
dariya cikin tsananin farin ciki tamkar mahaukaci sabon kamu.
Daga can sai ya koma kan karagar mulki ya zauna. Kawai kuma sai aka ga ya fashe da kuka.
Koda ganin haka sai idanun Sharlisa da na Sarki Yarduza suka ciko da kwalla suka kama zubar
da hawaye, saboda tausayinsa, domin su kadai ne suka san dalilin dariyarsa da kukansa.
Sauran jama'a kuwa duk suka cika da tsananin mamaki bisa wannan bakon al'amari.
Kamar yadda Sarki Yarduza ya bayar da umarni, haka al'amarin ya kasance, wato sai da
Kuraisu ya kwana bakwai kullum yana zama akan karagar mulki yana shugabantar jama'ar
Birnin Kaluza, kuma yana kwana a gadon Sarki Yarduza,
yana sanya suturarsa da cin irin abincinsa. Babu abinda ya kara daurewa mutane kai face ganin
yadda Kuraisu ke tafiyar da harkokin mulki
dai-dai kamar yadda kowanne Sarki da ya shude ke yi, tamkar dama can a gidan sarautar ya
taso, san komai ba a koya masa ba.
'Yan majalisa kuwa, suka yi ta zunde da munafunci a tsakaninsu suna ta bincike akan su gano
ko wane ne wannan bakon tsoho da Sarki Yarduza ya zo da shi va daukakeshi five da kansa da
kuma dalilin yin hakan, amma suka kasa.
Abinda kawai suka iya ganowa shi ne, tsohon ya kasance uba ga wannan kyakkyawar budurwa
wacce Sarki ya zo da ita.
A daren kwana na bakwai ne tsoho Kuraisu ya kamu da tsananin zazzabi mai zafin gaske,
jikinsa ya kama tsuma, yana kwance akan gado a cikin turakar Sarki, 'yarsa Sharlisa na zaunc
daf da shi cikin tsananin dimauta da tashin hankali, domin a iya zamanta da mahaifin na ta bata
taba ganin sa ba a cikin irin wannan hali ba
Sharlisa ta Kurawa Kuraisu idanu a lokacin da hawaye ke zuba daga cikin idanunsu su biyun, ta
kama kafadunsa ta rike tana mai cewa, "Ya kai Abbana kayi sani cewa a tsawon zamana da kai
ban taba ganin ranar da ka yi koda ciwon kai ba, amma yau gashi zazzabi mai zafi ya rufcka,
kuma Likitoci sama da guda hudu sun shigo sun dubata yasun baka magani ka sha amma har yanzu baka sami lafiya ba, mene ne ma'anar wannan
rashin lafiva?" Sa'adda Kuraisu yaji wannan tambaya sai ya daga hannunsa da kyar ya kama
hannun Sharlisa ya cc, "Ya ke 'yata ki gafarceni, domin kuwa па боус miki wani babban alamari
a rayuwata.
Tabhas numfashina a duniya yau zai yanke, a yau ne mai rabawa za ta rabamu, domin wa'adina
ya cika.
Tun daga ranar da dan uwana Yarduza ya hau kan karagar mulkin kasar nan, wato mahaifin
Sarki Yarduza na yanzu, wanda ya kawo mu fadar nan, na bazama yawo wajen bokayen duniya
ina neman sihirin da zan iya hallakashi na yi masa juyin mulki da karfin tsiya a dare daya, amma
ban samu ba har izuwa lokaien da mabaifiyarki ta haifeki.
A ranar da aka haifcki ne na sadu da wani hatsabibin boka ya ce da ni har abada ba zan iyama
komawa cikin Birnin Kaluza ba sai bayan mutuwar dan uwana a zamanin mulkin dansa, kuma a
sannan din ma sai dai na dandani mulki na tsawon kwana bakwai kacal, kuma a daren kwana
na bakwan zan mutu.
Bokan ya ce da ni idan har na amince zai iya yi mini sihirin da wannan bukata tawa za ta biya.
Mu hadu a littafi na 6 don cigaban wannan labari
08137237071