Chapter 1 Reading GUGUWAR ANNOBA BOOK 7 Littafin Yaki By Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf Arewa Novels

GUGUWAR ANNOBA BOOK 7 Littafin Yaki By Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Bookz

Chapter   1 / 1

1 to 1.9K   out of 1.9K words

GUGUWAR ANNOBA
Littafin Yaki
08137237071


Ya yin da Dakarun sumame suka mace ce sai gaba dayansu suka bushe da dary mugunta.
Suka yi ta kyalkyalawa kamar baza daina ba.

Kwatsam! Sai suka ji Sharlisa ta daka tsawa, tsawar da ta cika filin wajen gabadays amsa
kuwwa.

Gaba dayansu sai da suka shiga taitay domin tsawa ce irin wacce manyan mazaje ko ya filin
daga, ka ga mutane sun dimauce sun k gudu suna neman maboya.

Sharlisa ta dubi Dakarun sumamen dayansu ta ce, "Ku kananan kwari, ku yi sani cev ni ce dan
hakin da kuka raina mai tsokane mub ido.

Tabbas yau kun yi babban kuskure, kum babban ganganci da kuka kawo hari nan Bimi domin
gwara ku je ku jefa kanku a cikin wutar ta shekara tana ci da ruruwa

Na rantse da darajar wannan takobi ta sar Birnin Kaluza da ke hannuna sai na zare mih ruhin
numfashinku gaba dayanku, dayanku ba tsira da rayuwarsa ba."

Koda jin wannan batu sai gaba dayu Dakarun sumamen suka sake bushewa da dariye
mugunta. Lokaci guda kuma suka tsuke bakinsu. Shugabansu ya dubi Sharlisa a wulakance
yace, "Ke! yarinya, shin baki da labarin GUGUWAR ANNOBA wacce tafi GOBARA DAGA
KOGI? To mu ne wannan GUGUWAR ANNOBA yanzu mun fara ta kan dabbobinku, da an jima
kadan zamu shiga har cikin Birnin naku mu rushe gidajenku duka mu kwashe dukkan
dukiyoyinku, mu maishe da garinku daji..."

Kafin shugaban Dakarun sumame ya gama rufe bakinsa tuni Sharlisa ta falfala da matsanaicin
gudu ta kutsa da karfin tsiva ta tsakivarsu tana bankesu, tana saransu da sukarsu.

Nan da nan wuri ya yamutse, kura ta turnuke a sama, ihun mazaje gami da karafkiyar karafa
suka cika dodon kunne

Sassan jikin bil'adama ya dinga shawagi a sararin samaniya. Jini kuwa ya rinka tsartuwa da
fantsama yana malala a kas tamkar ruwa ya yi ambaliya daga toku.

Wohoho! Yau fa ga MACE MAI KAMAR MAZA, ta zama shaidaniya kuma dodo, abin tsoro.

Nan take Dakarun sumame suka raina kansu,

domin jaruma Sharlisa ta zame musu annoba, saboda duk inda ta sa gabanta sai dai ka ga
maza na

zubewa kas tamkar ana sassabe a gona

Babu abinda ya kara firgitasu face ga tsananin zafin naman Sharlisa da kuam kari dantsenta
tamkar jikinta ba na jini da tsoka bane

Ko kadan babu alamar gajiya a tare da it kamar ma ko yaushe dada kara ma ta kuzari ake y

Duk sa'adda Dakarun sumamen suka yi mau rubdugu suka yanyameta sai ka ga ta tarwatsasu
da karfin sara, kuma ba da takobi kadai tai ragargazarsu ba, wani lokaci hannayenta kafafunta
ma sun fi takobin illah domin ta ko in tana kai naushi da bugu ne, karfin naushinta guà ya wuce
misali sai dai ka ga tana yin fatali kawunan mutane sama da biyar ko shida a loke guda tamkar
tana wasan tamola.

Kaico! Mai karfi sai Allah Ya isa! Haki Sharlisa ta sha sadaukantaka a nono, kuma ta ga
jarumtaka a jini, domin duk irin jarumake mahaifinta tana da ita, har ma tata ta ninka tasa uku.

Sharlisa ta ci gaba da ragargazar wadarsa Dakarun sumame ba ji ba gani.

Kai inda mutum yana nan a gefe daya yan ganin wannan mummunar barna da Sharlisa ke da
dole ne ya tausayawa Dakarun sumames
Mar Karamar zuciya kuwa fashewa zai yi da kuka musamman idan ya ga yadda sassan jikin
bil'adama suka zama tamkar tsummokara a sama da Rasa

Ana cikin wannan hali ne su Sarki Yarduza suka iso inda ake wannan bakin gumurzu.

Koda suka ga yadda Sharlisa ta ragargaji Dakarun sumamen ya zamana cewa sauran kadan
daga cikinsu sai duk suka ja linzamin dawakansu suka yi cirko-cirko suna kallon abin mamaki.

Babu wanda yafi cika da tsananin mamaki ma sama da Sarki Yarduza, domin ko a mafarki bai
taba zaton cewa Sharlisa tana da wannan karfi da jarumtaka ba.

Shi kansa sai ya ji ajikinsa cewa ko shi kansa baya zaton zai iya samun nasara akan Sharlisa
idan suka fafata yaki.

Tsayuwar su Sarki Yarzusa da fara kallon wannan yaki dake gudana, rabin sa'a bata shude ba
ya zamana cewa Sharlisa ta karar da gaba dayan Dakarun sumame saura mutum daya kacal a
cikinsu

Ba wani bane face Shugabansu kuma shima ta yi masa sara a sassan jikinsa, sun kai guda
bakwai,
sai jiri ne ke dibarsa sakamakon jinin da ke a jikinsa.

Har Sharlisa ta daga takobinta za ta fill kai sai taji an daka ma ta tsawa a bayanta

A fusace ta waigo, sai ta ga ashe tsaye a kan doki tare da masa baya su da yawa. wadansu
Dakaru masu

kamata ki kashe shi ba, gwara ki barshi ya zuwansa daf da ita sai va dubeta ya cc, "A Yarduza
ya saki dokinsa ya durfafeta labarin ki nahivarsu asan cewa MACE KAMAR MAZA ta baiyana a
wannan zamani."

Yarduza ya dubi shugaban sumamen "Bace daga nan wajen kafin na sauya shawara".

Koda jin haka sai shugaban Dake sumamen ya yi zumbur! Tamkar ba shi ba cikin mugun hali
ba, ya kama wani doki ya haye zabureshi da gudu izuwa cikin daji.

Sarki Yarduza ya sake duban Sharlisa murmushi ya ce, "Madalla da jaruma 'yar jan Hakika kin
gaji mahaifinki, ina ganin ma kin fre Ni kaina yanzu ina shakkar ja mtakata akan ak

Sa'adda Sharlisa taji wannan batu sai murmushi ta ce, "Ya kai mijina kayi sani cee babu
mamaki kallon kitse ka ke yiwa rogo.
Ka tuna cewa kaima ka gaji jarurmtakar nan kuma mahaifina ya taba gaya mini cewa
mahaifinka ya fishi dakewar zuciya.

Jarumin da yake da dakakkiyar zuciya kuwa mijintavana da vawan samun sa'a.

Na fuskanci cewa ka gaji dakewar zuciya a wajen mahaifinka, don haka ina matukar shakkarka
rarrabe tsakanin Ava da tsakuwa." akan hakan amma duk da haka zan so wata rana mu

Vitsalle ta haye bayan dokin Yarduza ta kwanta a Koda gama fadin haka sai Sharlisa ta daka ya
dokin ya juya da baya suka koma cikin Birmin bayansa ta kankameshi, shi kuwa sai ya zaburi
Kaluza.

Dakarun da suka ga wannan jarumtaka da Sharlisa ta yi ne suka yi ta bada labari a Birni da san
cewa Sharlisa jaruma ce ta gaban kwatance. kauye, labarin ya bazu ko ina a nahiyar kowa ya

Bayan wata uku ne da faruwar wannan al'amari Sharlisa ta fara laulayin ciki.

Koda Sarki Yarduza ya fahimci cewar matarsa na dauke da juna biyu sai ya cika da tsananin
farin ciki.

Daga wannan rana Sarki Yarduza ya daina fita ko ina ya zamana cewa dare da rana yana tare
da

Sharlisa yana kula da ita da kansa.

Kai sai da ya zamana cewa Yarduza ya dena fita farauta kuma ya daina zuwa dakin mankin
Salkar yana bauta masa har tsawon wala tan sa'adda cikin ya tsufa ya zamana cewa a ko yabe
za ta iya haihuwa.

Amma kafin cikar wata taran sau uku Sah Yarduza yana fita yaki.

Shi dai wannan yaki ba kowa ya haddasa ba face shugaban Dakarun sumamen nan Sharlisa ta
kashe jama'arsa gaba daya ya zamana cewa shi kadai ne yai saura.

Ashe lokacin da ya tafi ya yi jinyar jikinsa ha ya warke sai yaji babu abinda ya tsana a rayuwan
sama da kasar Kaluza, saboda haka ya kulla a ram cewa in dai yana raye sai ya ci kasar da
yakin yiwa su Sharlisa kisan wulakanci ya ya dukiyarsu kaf.

Bisa wannan dalili ne ya dinga hada kai gungun 'yan fashi yana kwadaita musu irin dumbe
dukiyar da ke cikin Birnin Kaluza, don haka suy gagarumin shirin yaki su zo a fafata, kuma da
zuwan da suka yi sau uku suna zuwa ne da muga yawa amma sai su Sarki Yarduza su
ragargazast fatattakesu ssu kashe na kashewa, saura su gudu Babban abinda ya yiwa Sarki Yarduza takaici shi ne, a duk yakunan da aka yi sau uku yana
ganin wannan shugaban Dakarun sumame, amma kafin a ama yakın sai ya sulale ya gudu ya
nemeshi ya rasa

Duk sa'adda ya dawo daga yakin ya baiwa Sharlisa labari sai itama takaici ya kamata har ta ce,
"Ai barin mugun iri a doron kasa ba karamar illa ba ce

Inda ka barni na kashe shi tun da farko da ba a sami wannan matsala ba, amma komai daren
dadewa ina fatan ya zamana cewa ni ce zan kashe wannan makiyi namu da hannuna.

da zan haifa ya kashe shi. Idan kuwa ni ban kashe shi ba ina fatan abin

A ranar da Sharlisa ta haifi santalcliyar aljanu ne Sarki Yarduza ya yi tsananin farin ciki
kyakkyawar 'ya ta gaban kwatance tamkar 'yar irin wanda bai taba yin kamar sa ba a
rayuwarsa, domin a ranar ne yasa aka saki dukkan fursunonin da aka tsare a shekarar komai
girman laifin da suka aikata kuwa.
Da ya fara kyautar kudi, sutura da kayayyakin kawa kuwa, tun safe har sai da magariba tayi, ba
shiri aka kamashi aka kaishi turakarsa aka kulleshi
a ciki domin idan aka kvaleshi zai ya kwana ya rabar da dukiyar bai gaji ba.

Da ranar suna ta zagayo sai aka nadra yarinya suna GIMBIYA LAMSIRAT. Nemato shiga sabon
bikin murna.

Sai da aka kwana ashirin da daya ana walina Baki kuwa da suka zo daga sauran kasa manyan
sarakai, attajirai da manyan bokaye sauran jama'a sai da aka rasa masauki.

A ranar kwana na ashirin da daya ne aka fie da jaririya, bokaye suka yi ta sa ma ta albarka, den
bayan daya.

Lokacin da wani gawurtaccen boka mai sa KIRBUZA ya zo kan gimbiya Lamsirat ya shi kanta,
kuma ya kura ma ta idanu, sai nan da te idanun nasa suka ciko da kwalla har hawayc zubo
masa.

Boka Kirzuba yai sauri ya share hawayen kada wani ya gani ya wuce gaba. Ashe S Yarduza ne
kadai ya ga abinda ya faru.

Bayan taro ya watse, boka Kirzuba ya im masaukinsa, sai ya fara shirin tafiya yana ha kayansa.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai yaa Sarki Yarduza ya shigo cikin dakin da yake.

Cikin kaduwa da mamaki ya risina ya ku
gaisuwa.
Sarki Yarduza ya karbi gaisywar sannan ya zauna akan wata kujera.

Shi kuwa boka Kirbuza sai ya zube kasa gabansa ya sunkui da kansa kas ya cc, "Ya
shugabana me kake da bukata a gareni?

Hakika na yi mamakin wannan ziyara taka a gareni?".

Koda jin wannan batu sai Sarki Yarduza ya kama kafadun boka Kirbuza ya tasheshi tsaye ya
zaunar da shi bisa wata kujera da ke fuskantar tasa, sannan ya dubeshi a nutse ya ce, "Ya kai
wannan babban boka mai daraja, kayi sani cewa ni kadai ne na ga abinda ya faru a gareka
dazu a filin fada sa'adda ka sawa jaririyata albarka.
Ina so ka gaya mini iyakar gaskiya kada ka rufe mini komai.

Mene ne dalilin da ya sa hawaye ya zubo maka sa'adda ka kurawa 'yata idanu?"

Koda jin wannan tambaya sai boka Kirzuba ya sunkui da kansa kas yai shiru kamar ba zai ce
komai ba, daga can sai ya dago kai ya dubi Sarki Yarduza cikin alamun tausayawa ya cc, "Ya
shugabana ba komai ne yasa ka ga na zubat da hawaye ba face ganin yadda rayuwar wannan
'yar taka za ta kasance anan gaba.

Mu hadu a littafi na 8
08137237071

1 / 1

Chapters