Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Romantic Hausa Novels
Guguwar Annoba
Madakin Gini
08137237071
Koda Dakarun su Sarki Yarduza suka gama fitowa gaba dayansu, sai suka zama tamkar an
ajiye 'yan tsaki a gaban Shirwoyi, saboda bambanci girmansu da yawansu akan Dakarun Sarki
Samiad
Sarki Samlad ya dubi tawagar su Sarki Yarduza ya ganusu yan kadan kamar ruwan aski sai ya
bushe da mahaukaciyar dariya, lokaci guda ya tsuke bakinsa sannan ya daga hannunsa sama
ya bada inkiyar a afkawa abokan gaba.
Wohoho! Nan fa aka zunguri cikin giwaue, suka zabura da gudu suka nufi rundunar su Sarki
Yarduza cikin matsanaicin gudu.
A wannan lokaci ne fa mutane suka sha mamaki, domin gudun da giwayen ke yi yafi na wanda
dawakai ke yi, abin kamar da sihiri.
Koda Sarki Yarduza ya hango tahowar wannan runduna ta abokan gaba mara adadi ta
durfafosu, sai shima ya daga hannu sama ya bayar da izinin suma su afka.
Nan fa aka sakarwa dawakai linzamai aka sukwanesu cikin azababben gudu. Koda rundunonin
biyu ta gwamutsa sai aka rugunisune da mummunan bakin yaki mara dadın kallo da tsananin
dugunzuma hankali.
Kaico! Sai dai ka ga giwa na tarmashe
dawakal da mahaymiku tan matsiltsikesu tankar dabbobi sun sawa kalmani wawa
Babu abinda zai baiwa mutum tausavi face yadda Dakarun fararen fatar ke murkushe na bakar
fata suna daddatsaso kamar yadda ake viwa nama filla-fitla a mahauta saboda Rarfin
dantsensu, zafin namansu da mramtakarsu ta ninka ta bakaken fatan sau goma
Mutum uku ne jal suke iya yaki da wadannan mutane, wato Sarkı Yarduza, Shariisa da gimbiya
Lamsirat. Sarki Yarduza da Sharlisa suna iya kaucewa harin abokan gabar har ma su mai da
martani, sai dai duk sa'adda suka sari abokan gabar ko suka sokesu ko gezau ba sa yi sai dai
su ji kamar karfe suka sara
Gimbiya Lansirat ce kadai take iya kashe abokan gabar ta hanyar harbinsu da wannan kibiyoyi
da wannan katuwar baka. Komai girman Kate idan ta dirka masa kibiyar sai ka ga ya fado daga
kan giwarsa ya baje a kasa matacce.
Koda Sarki Samlad ya hango barnar da Lamsirat ke yi masa kuma ya hango Yarduza da
Sharlisa sun zama alakakai sai ransa ya faci, ya
fusata ainun. Nan take ya bada umami ya ce a yiwa Lamsirat rubdugu a kamata da karfin tsiya,
kurna a rabata da wannan kwari da baka.
Ai kuwa sai Dakaru masu yawa suka yi caal akanta. Koda ganin haka sai ta sauya salon yakinta
ta dinga tsalle sama tana gudu akan abokan gabar da giwayensu tana ci gaba da dirka musu
kiboyoyi a hakan suna mutuwa.
A wannan lokaci tuni Sarki Samlad ya durfafi inda Sarki Yarduza da Sharlisa ke ta farman yaki
bai ma lura da irin mummunar barrar da Lamsirat ta ci gaba da yiwa Dakarunsa ba
Koda Samlad ya iso kan Sharlisa sai ya sa giwarsa ta daga kafarta guda ta talitse Sharlisa
tamkar ta talitse kitse akan dutse, gaba daya jikin Sharlisa ya dagwargwaje, kanta ya bare, sai
ga kwakwalwarta ta kwarara a kas
Kamar an ce da Sarki Yarduza ya waigo, nan take ya hango wannan mutuwar wulakanci da
matarsa tayi. Sarki Yarduza ya takarkare ya kwarara uban ihu wanda yarızana kowa a filin yakin
sannan yai tsalle sama ya dira akan grwar daya daga cikin abokan gaba yasa hanna ya
gabzawa na kan giwar naushi a ido. Take kwaya idon ta fashe, ya fado kasa
Kawai sai Yarduza yn sarrafa giwar ya zabureta da gudu ta tsakiyur abokan gabar yana
bankesu da karfin tsiya suna kawo masa munanan hare-hare yana gocewa da karewa har ya
isa inda Sarki Samlad ke tsaye akan gawar Sharlisa
Tun kafin ya isa gareshi ya daka tsalle daga kan giwar da yake zaune ya dira akan wuyan Sarki
Samlad tamkar dan biri ya gabza masa naushi biyu a lokaci guda.
Naushi na farko a makogwaronsa, dayan kuma a bakinsa. Saboda karfin naushin sai da hakori
guda yai fitar burgu daga cikin bakın Sarki Samlad hade da furzar da jini.
A gigice Sarki Samlad ya saki takobin bannunsa bai sani ba. Sarki Yarduza ya fado kasa daga
wuyan Sarki Samlad ya cafe takobin tasa, lafin taje Rasa ya cakawa Samlad a gefen Lirjinsa,
amma so ya yi ya cakata a tsakiyar kirjin sasa, sai Samlad ya goce.
Take takobin ta nutse a gefen kirjin ta balutso ta gadon bayansa wani gudan jini ya fallatso waje,
Surki Samlad ya kwarara uban ihu
amma sai yai wuf ya cafi makoshin Sarki Yarduza da hannu daya ya dagashi sama. Sai gashi
Yarduza yana kakarin mutuwa, kafafunsa na wutsil-wutsil a sama yana reto.
A haka Sarki Sanlad ya zare wannan takobi daga kirjinsa ya sokawa Yarduza a ciki ta faso ta
gadon bayansa.
Yarduza ya kwarara uban ihu irin wanda ya yi da farko. Samlad ya saki makoshin Yarduza ya
fado kasa kuma ya durkushe bisa guiwoyinsa a lokacin da idanunsa suke gani dishi-dishi, kuma
numfashinsa na sarkewa. Kawai sai ya dubi Sarki Samlad wanda shima yana layi a tsaye
sakamakon jinin da ke zuba a kirjinsa ya bushe da dariya ya ce, "Ko ba komai ba zan mutu rago
ba, tunda na bar maka shaidar rauni a jikinka wanda har abada tabonsa ba zai bata ba. Tabbas
mima Jarumi ne daga cikin Jarunan wannan zamani".
Koda gama fadin haka sai kan Sarki Yarduza ya langwabe kasa alamar cewa ya mutu. Sarki
Samlad yai sauri ya fisge rawanin da ke kan Sarki Yarduza ya daure kirjinsa don tsaida jinin da
ke zuba sannan ya dubi gawar Sarki
Yarduza cikin tsananın takaici ya tofa ma ta Yawu, har #wallar bakin ciki ta zubo masa saboda
tunda ya ke tsawon shekaru ashirin da biyar ko kwarzanar jikinsa ba'a taba yi ba, amma yau
gashi ya gamu da Jarumin da ya yi masa mugun rauni wanda inda da tsautsayi ma da tuni ya
hallakashi.
Abinda ya bashi mamaki shi ne, ya ya akayi Sarki Yarduza ya yi tunanin armfani da takobinsa
wajen kokarin hallakashi. Tabbas babu wata takobi ko makami da zai iya yin tasiri a jikinsa face
wannan takobi mallakinsa.
Sarki Samlad ya sa hannunsa ya zare takobinsa daga cikin Sarki Yarduza.
A dai-dai wannan lokaci ne gimbiya Lamsirat ta waigo ta hango gawar mahaifiyarta a
dagwargwaje sannan ta ga sa'adda Sarki Samlad ya zare takobinsa daga cikin mahaifinta,
gawar mahaifin na ta ta fingire kasa.
Koda ganin wannan al'amari sai gimbiya Lamsirat ta kurma uban ihu, ta juyo da baya da pudu
tana tafiya a sama bisa kawunan abokan pabe suna kaiwa kafafunta sara tana gocewa har aino
dal da Sarki Samlad dama tuni tun a saman
ta dana kibiya akan katuwar baka
Inda tayi kuskure shi ne, bata tabe bakanta ba sai da ta matsa daf da Sarki Samlad.
Kafin ta sakar masa harbin tuni shima ya dako tsalle sama tamkar an harboshi daga cikin
kibiya. Kawai sai ya mangareta da hannu daya ta fado kasa sumammiya amma tuni ta saki
harbin, hannunsa. don haka sai da kibiyar ta cake a cikin tsintsiyar
Sarki Samlad ya duro kasa bisa kafafunsa ko gezau bai yi ba, sannan ya sa daya hannun nasa
ya zare kibiyar da Lamsirat ta harba masa a hannunsa, sai ga jini na bulbula.
Cikin sauri wani badakarensa ya rugo ya dauyre masa hannun don tsaida jini amam duk da
haka sai da dafin kibiyar yasa ya kama jiri ya durkushe kasa bisa guiwarsa guda.
Cikin gaggawa aka kawo masa ruwan wani magani ya sha. Nan take kwarin jikinsa ya dawo ya
mike tsaye ya fara kalle-kalle yana duban miliyoyin gawar da ke kwance a filin yakin.
Koda yai nazari sai ya ga ashe Lamsirat ta kashe masa Dakaru sama da dubu dari uku.
Nan take bakin ciki ya turnukeshi ya bada
umarnın a fasa Rofar Birnin Kaluza da karfin kwashe dukiyarsu a kamo bayi. tsiya a shiga ciki a
kone gidajensu duka kuma a
Nan take aka cika wannan umarni. Kafin cikar wadansu sa'o'i Birnin gaba daya ya baje sai wani
daki guda daya jal da ya rage a tsaye wanda ya gagara rushewa da konewa.
A wannan lokaci ne aka fito da mata da samari matasa kimanin su miliyan biyu a daddaure cikin
sarka an kamosu a matsayin bayi,
wasu ma duk an yi musu rauni an fatattaka suturorin jikinsu suna kuka da bakin ciki.
Lokacin da Sarki Samlad ya hango wannan daki guda daya hal a cikin Birnin Kaluza wanda ba
a rusheshi ba kuma ba a koneshi ba sai ya
fusata ainun ya dakawa Sarkin yakinsa tsawa ya cc, "Saboda me baku rushe wancan dakin ba
kun Runeshi?"
Sarkin Yaki ya dubi Sarki Samlad cikin
matukar damuwa ya ce, "Ya shugabana wannan daki, daki ne mai dauke da karfin sihiri wanda
ya
wace dukkan tunaninmu.
Mun yi aya kokarınmu mu je kusa da shi na, amma mun kasa domin ji muke kamar zamu
jefa kanmu a cikin tafasasshen mai. Ya shugabana ko kai da kanka za ka jarraba"
Da jin haka sai Sarki Samlad ya dauki wata katuwar guduma wacce karti goma ma basa isa su
iya rabata da kasa ba sannan karbi ice mai ci da wuta ya durfafi wannan daki na gunki Salkar.
Koda ya rage saura taku biyar tsakaninsa da dakin sai yai sauri ya ja da baya cikin tsananin
razani da mamaki, domin shima ji ya yi kamar fatar jikinsa za ta babbake.
Sarki Samlad ya tsaya cak ya karanta wadansu dalasimai na tsafi ya sake durfafar wannan
daki. Ba shiri ya juya da baya a guje har yana faduwa kasa.
Kwatsam! Sai ya mike tsaye ya yi jifa da wannan katuwar guduma da icen wutar da ke
hannunsa ya kurawa dakin gunkin Salkar idanu cikin tsananin takaici da bakin ciki yana ciza
Іебе.
Nan take ya aiyana a ransa cewa, "Komai daren dadewa sai ya sake dawowa wannan Birni da
kansa ya rushe wannan daki ya koneshi bayan ya samo sirrin lalata sihirin da ke cikinsa."
Ba tare da bata lokaci ba aka tusa keyar
bayin da aka kamo gami da dukiyar Birnın Kaluza gaba daya aka tafi da su. Sarki Samlad da
Dakarunsa suna bayan wannan bayi da dkiya aka nausa cikin daji.
Wasu daga cikin Dakarun Sarki Samlad kuwa suna gaban bayin da dukiyar don tabbatar da
tsaro.
Wannan runduna bata yada zango a ko ina ba sai da tayi nisa ga barin dazuzzukan da ke cikin
nahiyar Birmin Kaluza.
Lokacın da gimbiya Lamsirat ta farfado daga dogon suman da tayi sai ta tsinci kanta a cikin
wani kejin ısafi kuma a daure tamau da sarkokin karfe hannu da kafa, kai ka ce wata muguwar
dabbar dawa aka kamo
Nan take Lamsirat ta tuno da irin mugun kisan wulakancin da aka yiwa iyayenta, sannan ta dubi
irin wannan wulakanci da aka yi ma ta, aka sata a nkin koi a matsayinta na 'yar Sarki, sai ta
fashe da
matsanaicin kuka na bakin cik Tavi ta rusa kuka kamar ba za ta daina ba har mada
SHIN GIMBIYA LAMSIRAT ZA TA
SHIRTACCEN KEJI DA AKA SANYATA KO KUWA SALAN JE DA ITA HAR IZUWA CAN
KUBUTA DAGA CIKIN WANNAN
BIRNIN MISRA KASAR SARKI SAMLAD?
TA YA YA WADANNAN KUYANGI DA BAYI ZA SU RAYU A CIKIN DAKIN GUNKIN SALKAR
HAR TSAWON KWANA BIYU?
SHIN GIMBIYA LAMSIRAT ZA TA DAUKI FANSAR MUGUN KISAN DA ΑΚΑ YIWA IYAYENTA,
KUMA SHIN BIRNIN KALUZA ZAI SAKE WANZUWA?
YAUSHE NE SARKI SAMLAD ZAI DAWO BIRNIN KALUZA YA RUSHE DAKIN GUNKIN
SALKAR?
IDAN GIMBIYA LAMSIRAT TA GIRMA TA CIKA BUDURWA WANE IRIN KYAWU ZA TA YI,
KUMA WACCE IRIN GAGARUMAR JARUMTAKA ZA TA SAMU?
MENE NE DALILIN DA YA SA SARKI SAMLAD YA KI KASHE LAMSIRAT YA SUMAR DA ITA
KAWAI?
Mu hadu a GUGUWAR ANNOBA littafi na biyu, don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.
Abdul’aziz Sani M/GINI
08137237071