TURABAR GASKIYA Part 1 Littafin Yaki By Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 1

1 to 2.3K   out of 2.3K words

TURABAR GASKIYA
Part 1 Littafin Yaki
Writing by
MADAKIN GINI

Lokacin da runduna ta nausa bakin birnin Baitul haural jama'a da suka yo musu rakiya basu
koma ba suna biye dasu suna daga masu hannu dan yin bankwana dasu, wasu na yin kuka
wasu kuma yin kabbara dan karawa tarin Dakarun karfin gwiwa. Shi kuwa Yarima Zaiyan har
zuwa wannan lokacin bai daina waigen wannan mai dara-daran idanuwa ba, ba komai bane
yasa ya damu da dubata sai tunanin da ya cika masa zuciya yana ganin cewar ba yau ya fara
saka wadannan kyakyawawan idanuwa ba a cikin nasa idanu.

Koda ya fuskanci runduna ta kara yawa nisa tsakaninsa da wadannan matan da suka biyo a
yarin likita Zuwad sun yi masa nesa domin tazarar dake tsakaninsu ya kai kimanin Runduna
uku, wanda yawansu ya kai kimanin dubu goma da doriya, wannan dalili yasa Yarima Zaiyan ya
hakura da waige ya cika gaba da sa kansa gaba tare da yin kabbara kamar yadda daukacin
dandazon mayakan kasar suke yi.

Shi kuwa Sarki Abu Zaiyan bai lura ma da halin da Yarima ya shiga ba, gabansa kawai yake
kallon yana kiran sunan Allah, da haka har aka zo bakin ganuwar garin, koda zuwa wannan
bakin ganuwar sai Sarki ya daga hannu yana mai bankwana da al'ummarsa wannan al'amari ne
yasa bake daya jama'ar kasar Baitul Haural suka kaure da kabbar suna masu yi masu fatan
samun nasara, da haka har aka fice daga birni aka mai da kofar birni aka rufe jama'a suka
koma gidajensu.

A wannan lokacin 'yanfashin da suke fakewa cikin dajijjikan da suke hanyar shiga birnin Baitul
Haural sai suka ari ta kare suka nausa cikin maboya domin ganin yanda Rundunonin mayaka
suka durfafo hanyar, abin da suke zargi shi ne yau ran Sarki ne ya baci da abinda suke
aikatawa dan haka ya yi wannan gagarumar hawa ya zo domin rushe su ya murkoshe su,
aikuwa zaman mafakarma sai ya gagari domin ganin irin yawansu suna ganin da an nufo inda
suka 6oye za'a riskesu dan haka suka ta shi

TURABAR GASKIYA-3

MADAKI

suka haye dawakansu suka nausa cikin dawa cikin tsananin firgici.

Kananun dambobi kuwa da tsuntsaye sai hankulansu ya dugunzuma cikin tsananin firgici suka
ta shi daga gidajensu suka arci ta kare.

Sawayan dawakai gami da kabbarar da Dakarun kasar Baitul Haural suke yi shi yake saka saka
faduwar gaba ga dukkan wani mugu da ya fake dan samun makafa ya cutar da wani.

Lokacin da Aka yi sa'a hudu da rabi ana wannan tafiya Sai Sarki Abu Zaiyan ya yi umarni dan a
tsaya a yi sallah kana a ci gaba da tafiya.

Koda aka saurara da wannan tafiya na kasa da dawakai da rakuma sai suka sauko nan fa aka
shiga naura alwala, cikin kankanin lokaci aka kira sallah rashin Ibin Haishan limamin kasar da
yake ba shi aka yi wannan tafiya yana gida, hakan ya sa Sarki Abu Zaiyan ya ja sallah. Bayan
an idar aka hayc dawakai aka ci gaba da tafiya.

Sai da aka kwana biyu ana wannan tafiya babu abinda yake tsaida su face yin sallah ko abincin
ba fara girkawa ba kowa da dan guzurin da ya taho da shi yake yin amfani

Lokacin da aka kwana biyar ne a cikin dokar daji ana wannan tafiya sai Sarki ya yi umarni da a
tsaya a lokacin ba su fi sa'a hudu ba da yin asuba bayan sun yi ta shi daga barci, sun yi sallah
sun ci gaba da tafiya.

Gurin da Sarki ya yi umarni a tsaya guri ne mai koramai da yawan sanyi, guri ne mai kyakyawan
yanayi duk da cewar guri ne mai hatsari gaske, domin kuwa ba'a rasa kuraye da zakuna a gun
mafi akasari gurin ne ma guri mafi son zaman wadannan dabbobi domin su shakata su huta,
amma jin doriyar jama'ar kasar Baitul Haural yasa suka arce suka nemi maboya domin suna zaton tashin alkiyamarsu ya yi, kamar yanda suka sani daga magabatan
iyayensu da kakanninsu, akwai ranar da zasu gushe ya zamana babu bakya daya.

Lokacin da Rudunoni suka ja daga suka tsaya sai aka hau kafatantuna domin dama a duk inda
aka samu kwana biyar ana tafiya cikin irin wannan tafiya to Sarki sai a irin lokacin yake bukatar
a huta musamman idan yaga guri mai yalwar nutsuwa da kuma ya kwanta masa, dan haka
suka sauka daga dawakansu.
Yarima Zaiyan da Sarki aka kafa musu tanti mafi kusanci da juna Sarkin yaki Safwan tantinsa
yana kusa da na Sarki ya zamana sun saka Tantin Sarki a a tsakiya.

Koda da wasu tsirarin dakarun da suke biye da shi suka nufo tantin sai Sarki Abu Zaiyan ya
dubi Tantinsa dake tsakiya kuma dubi Tantin dansa da na ya

Sarkin yakinsa a gefe da gefensa sai ya dubi Sarkin yaki Safwan ya ce.

"Ya kai Sarkin yaki Safwan ina dalilin saka tantina a tsakiya, alhalin kana sane da cewar ban yi
umarni da hakan ba.?"

Da jin wannan tambaya sai Sarkin yaki Safwan ya sadda kai kas ya dubi Sarki ya ce, "Ya
shugabana idan ban yi dai-dai ba ina fatan hưcewar zuciyarka, na kuma aikata hakanne dan
tsaron lafiyarka, kamar yadda Yarima Zaiyanu ya tsara ni kuma na ga daidai din hakan, ya
shugaba tsaron lafiyarka a gareni wajibi na ne, domin ba ni da wani aiki da ya wuce hakan."

Koda Sarki ya ji wannan ba tu daga Sarki yaki Safwan sai ya yi murmushi ya ce, "Kada ka
manta a lokacin da aka rantsar da kai a matsayinka na Sarkin yaki, ba ka dau alwashin kare
lafiya ta ba, ka dauki alwarin kare al'ummata ne iyaka gwargwadon ikon, ba ni ba, sanin kanka
ne bana bukatar tsoron kuwa face na Ubangiji da ya halicceni, dan haka ina son a dauke
wannan tantin a kai min shi can saman wannan tsauni ta yanda zan kasance ni kadai, kuma
cikin kula da al'ummata."

Koda Sarkin yaki Safwan ya ji wannan ba tu sai hankalinsa ya dugunzuma domin gurin da Sarki
ya nuna guri ne da baki daya mafaka ce ta mugayen dabbobi masu hatsarin gaske, dan haka
ya yi saurin rissana bisa Rafafuwansa ya ce.

"Ya shugaba ka yi sani wancan guri da kake nunawa babu komal a bisa saman tsauni face,
dabbobi masu hatsarin gaske, ka yi hakuri ka zabi wani guri ba can ba."

Sarki Abu Zaiyan sai ya dakawa Safwan tsawa ya ce, "Ka bami a can din ina sane na zabi can
din kuma ba dan komai na zabi gurin ba face na yi gadin al'ummata na tabbata idan muka

shagala cikin hutawarmu wadannan dabbobi zasu iya saukowa suka bi bayan wasu daga cikin
jama'ata su nemi cutar dasu, amma muddin ina gurin da zarar dabba ta fito ni kuma zan yi karo
da ita har sai lokacin da kowa ya gama hutuwa kafin cikar sala biyar cif da na dibar mana, dan
haka bana son ka kara wata magana yanzu take ka yi umarni a kai min tantina can.
Yarima Zaiyan dake zaune a gefe bai iya cewa komai domin ya san in dai Sarki ne akan
jama'arsa sai Allah, zai iya cewa yafi son su da shi kansa, dan haka ya ja bakinsa ya yi shiru
duk da bai son hatsarin dake gurin ba amma yana iya jiyo hargagin zakuna da kukan wasu
da'ikan dabbobin da bai san ko wane iri bane
Shi kuwa Sarkin yaki Safwan take ya yi umarni da wasu dakaru su je gurin su kafawa Sarki
Sansani kamar yanda ya bukata, amma ya yi umarni da kada su bar gurin su tsaya su yi gadin
sa.

A can kuma bangaren Likita Zauwad da jama'arsa sai su Shadilat da Lushmaira suka kasance
cikin tsananin farin ciki ganin har an kwashe kwanaki biyar a na wannan tafiyar dasu batare da
angano su ba, ganin haka sai suka sau jiki suka shiga harkokinsu San ransu amma duk da
haka fuskokinsu a rufe suke.
Shadilat ta dubi Gimbiya Lushmaira ta ce, "Ya ke 'yar uwata hakika na yi mutukar farin cikin da
na kasance cikin wannan tafiya godiyata ba zata kare ga Likita Zauwad sannan in Allah yasa
mun dawo cikin koshin lafiya zan yi masa kyauta ta musamman, sai dai abinda yake fadar min
da gaba shi ne, yanzu idan Yarima ko Sarki sun gano mu bakya ganin zasu iya sawa amai
damu gida.?"

Koda Lushmaira ta ji wannan ba tu sai ta yi murmushi ta dubi Shadilat ta ce, "Tabbas idan Sarki
ya ganmu zai iya daga mana kafa sai dai zai saka tsaro akanmug

sosai amma bana jin idan yarima ya ganmu zai barmu take batare da Sanin Sarki ba zai sa a
maidamu gida."

Da jin wannan ba tu sai gaban Shadilat ya fadi cikin tsananin bugun zuciya ta ce, "Ya ke 'yar
uwata aikuwa in haka ne ya zama dole na canza tufafi domin a lokacin da yarima ya dawo kaina
domin ya kara bincikena a yayarin da Sarki ya kira shi, ina ganin kamar ya so ya gane ni, domin
har muka baro cikin fada muka nufo hanyar waige yake yana dubana ganin baka yasa na sauya
gurin tsaiwa duk da haka ina kallonsa yana ci gaba da waigen kan layin da nake, tabbas na san
har yanzu bai aminta da zuciyarsa ba zai ci gaba da dubana, dan haka ya zama dole na sauya
kayan jikina da wata daga cikin matan da muke tare."

Koda Shadilat ta zo nan a cikin batunta sai Gimbiya Lushmaira ta dubeta da kyau ta ce,

TURABAR GASKIYA-J

MADAKI

"Tabbas duk wanda ya sanki bayan 6oye idanuwanki da kika yi, idan ya ganki cikin wannan
mayani na rufe fuska zai iya shaidake ba dan komai ba saboda launin idanuwanki ina mai
goyan bayan da ki sauya kayanki yanzu domin a wannan lokacin Yarima zai iya zuwa wannan
guri domin ya ci gaba da bincikensa, amma yanzu kada ki tunkari kowa daga cikin wadannan
matan bari mu nemo Likita Zauwad."

Nan take Shadilat ta amince take Lushmaira ta bi wata hanya ta nemo Likita Zuwad ta zo da shi
izuwa in da suke.

Batare da bata lokaci ba suka kadaita acikin Tantinsu. Lokacin da suka samu guri suka zauna
sai Gimbiyar Lushmaira ta kwashe duk abinda Shadilat ta sanar da ita da kuma bukatarta ta
sanar shi.

Koda gama jin haka sai ya yi shiru na tsawon lokaci daga bisani sai ya dago da kai ya dube su
sannan ya ce.

"Hakika kun saka ni cikin tsaka mai wuya, tabbas idan ban yi wasa ba sai kun sa Sarki ya yi
fushi dani, ina son ku sani shi Yarima Zaiyan mutum ne mai tsananin kaifin basira tunda har ya
dora zargin akanki babu shakka ko mai zaki yi sai ya nemo ki abinda zai hana ya gano ki kuwa
hanya daya ce, wannan hanyar ba wata hanya bace face, zaki kasance cikin tanti daga nan har
zuwa lokacin da za mu ci gaba da tafiya muddin zaki fito to babu shakka ko mai zaki sauya sai
ya gano ki domin ina da tabbacin zai zo nan a yanzu, idan kina cikin tantinki ba zai taba
shigowa ciki ba, amma in har kika fita to zai ganki kuma zai sa amai dake gida, alkawari daya
nake so ki daukar min koda ya gano ki dan Allah kada ki taba nuna masa cewa ni ne na
sanadinki zuwa nan."

Shadilat da jin haka sai ta yi na'am da batunsa take kuma suka mike ya koma bakin aikinsa ita
ma Lushmaira sai ta

TURABAR GASKIYA-3

MADAKI

fice tabarta cikin tanti lokacin da Lushmaira ta fita sai idanuwanta suka kan wata korama ta da
ruwa ki zuba farin ruwa ne fat mai sheki saboda tsananin haske dan haka sai nan take ta ji
sha'awa shiga ruwan ta yi wanka ya kamata.

Bata tare da ta shawarce kowa ba sai ta nufi bakin ruwan da yake ya yi baya da inda sansanin
jama'ar su suke, gadan gadan ta nufi gurin koda zuwanta bakin ruwa sai ta cire mayanin dake
rufe da fuskarta, ta kuma cire dogowar rigar da take jikinta ya zamana daga ita sai wani dan
bantai da rigar da ta rufe mata mama.
Kai tsaye ta daga tsalle ta fada cikin wannan ruwan tsundum.

Shi kuwa Yarima koda mahaifinsa ya tafi izuwa saman wannan tsaunin sai nan da nan tunanin
wannan da ya gani ya dawo masa nan take sai ya mike tsaye ya nufi sansanin matan da suka
taho da su dan yi musu girke girke da kula da lafiyarsu.

Tun daga nesa Likita Zauwad ya hango shi nan take sai ya nufo shi cikin dan murmushi "Barka
yarima da wannan lokaci."

Yarima Zaiyan ya dubi likita Zauwad da murmushi akan fuskarsa ya ce, "Barkan babban likita
da warhaka, ya jama'ar taka ina fatan dai komai lafiya?"

Likita Zauwad ya dubi Zaiyan cikin murmushi ya се,

"Ranka ya dade ai kowa lafiya bebu wani abu."

Da jin haka sai Yarima Zaiyan ya girgiza kai ya ce, "Haka ake so, amma akwai wani bincike da
nake son yi a cikin jama'ar da ka wo dasu ba dan ina zargi ka taho da wasu ba, a'a sai dan ina
zargin akwai wata da ta badda kama ta shiga cikin jama'arka batare da saninka ba."

Da jin wannan al'amari sai Jikin Likita Zauwad ya kama rawa bakinsa cikin rawa ya ce.

1 / 1

Chapters