Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Hausa Novels 001
TURABAR GASKIYA
Part 4 Littafin Yaki
Writing by
MADAKIN GINI
Dan haka babu wani annuri akan Fuskar Yarima Zaiyan tun daga farin tahowa har zuwa
wannan umarni na Sarki takaicensa biyu tafiya da Shadilat, da kuma Lushmaira, ga kuma
wannan tsayawar wacce ya fitar da rai da ita.
Hadiman da suke masa hidima suka hada masa Tanti, lokacin da suka hattama sai ya yi saurin
barin gun, ba ko ina ya nufa ba face Inda su Gimbiya Lushmaira da Shadilat suke.
Lokacin da ya isa sai ya same su, a cikin Tantinsu su biyu zaune, cikin nishadi da walwala,
akwai kuyangi biyu da suke masu hidima gabansu kayan marmari ne, sai ruwan inibi a cikin
tambula.
Koda gabatowar bakin. Tantin sai yarima Zaiyan ya yi musu sallama ya shiga cikin tantin koda
ganınsa sat suka ci ka da mamaki, Shadilat cikin ladabi da biyayya ta rankwafa ta ce, "Barka da
Yarima, garemu muna fatan zuwan samun duban goyan baya gareka."
Koda yarima ya ji wannan daga Shadilat sai ya nemi guri ya zauna, ya kuma dubeta ya ce,
"Barkan ki da warhaka, ina fatan komai lafiya.?"
Ta yi wani kayataccen murmushi ta kara dora dara-daran idanuwanta akansa, sannan ta ce,
"Komai lafiya babu fargaba tunda har Sarki ya ji kanmu ya barmu yin wannan tafiya."
Ita kuwa Lushmaira lokacin da ta gan shi cikin dakin sai ranta ya yi mutukar baci, da kyar ta iya
bude baki ta ce, "Sannu."
A sa'ilin da ya ji yanda ta yi furucin sai da ya dago kai ya dubeta, domin duk rashin jituwar da
take tsakaninsu bata taba nuna masa, a koda yaushe idan zasu hadu zata bashi girmansa
amatsayinsa wanda yake gaba da ita. Amma sai ya kanne bai nuna fushinsa ba ya dubi
Shadilat ya ce, "Kada ku cire fargabarku, domin a kowane lokaci zasu iya komawa gida, domin
ni ban lamunci da tafiya da mata ma'abota rauni a cikin irin wannan bakin yaki da zamu durfafa.
Koda jin wannan ha tu sai Shadilat ta yi shiru ita kuwa sai Gimbiya Lushmaira ta yarmatse fuska
cikin kunkuni ta ce, Babu rauni a tare da basadaukiyar mace da zata iya karo da karatan
Sadaukai sama da Ashiri kuma ta samu nasara dan haka, ka cire wannan batu a ranka babu
halin da zaka mai damu gida.
Koda jin wannan batu sai Yarima Zaiyan ya ji ransa ya baci da maganar Gimbiya Lushmaira
amma sai ya kanne bai bi ta kanta ba, har da dan murmushi ya cc.
"Sadaukai ko kuma ragwayc, kada ki yi tsammanin ganin kuna yaki a junanku na bajinta ki yi
tunanin cewar za ku iya yin bakin yaki da wanda ya taba halarta horon yaki na kwana guda ne,
dan koda
haka ki kiyaye kada ki dauki kan ki a bakin komai, duk bajintar da ku kai a bakin Ruwa na sani
bana bukatar ki sanar dani."
Koda Gimbiya Lushimaira ta ji wannan ba tu sai ta yi kayataccen murmushi ta ce, "Bana haufi
idan akwai jarabawa da zaka auna Sadaukantakarmu, muna saurarenka, in kuma babu abinda
zaka jarrabamu da shi, to muna son ka bamu sarari domin mu shaki iska,"
Cikin tsawa Shaidilat ta doka mata tsawa ta mike tsaye ta ce, "Ya ke Gimbiya kada matsayinki
ya dinga mantar dake waye Yarima Zaiyan, kada isa da iko ki manta da isar sa da ikonsa, lallai
furucinki haramtaccene a gareshi don haka ki yi biyayya ga yarima Zaiyan."
Koda Shadilat ta zo anan acikin zancenta sai ran Gimbiya Lushmaira ya tashi ainu cikin facin
ran ta dubi Shadilat ta nuna ta da yatsa ta ce, "Kada kwarjini
mulki ya rinjiyi ra'ayinki har ki dinga son farantawa wanda yake son bakantawa zuciyarki, ina
son ki sani Ina daukar kaina a matsayin Jaruma Basadaukiya 'yar na gada, dan haka babu wani
namijin da jarumtarsa bata taka kara ta karya ba da zai nuna min isa da iko, girman Mulki, kyau,
takama basa tasiri a gareni face kawai girman Sadaukantaka."
Lokacin da Lushmaira take sanar da
Shadilat wadan nan maganganun sai Ran Zaiyan ya yi mutukar baci zuciyarsa ta hau tafarfasa,
da sauri ya matsa kusa da ita ya kai mata wani bahagon mari, cikin bajinta Gimbiya Lushmaira
ta sunkuya hannunsa ya mari iska.
Wannan al'amarin ne ya kara jefa zuciyar Yarima Zaiyan cikin tsananin bakin ciki, ya saka
yatsansa a baki cikin tsananin takaici ya ma kasa cewa komai.
Ita kuwa Gimbiya Lushmaira sai ta fashe da dariya ta ce, "Ko aljani ya san
kaidin dan adam yafi nashi, haka bana ko shakka, akwai shakkar mata a zuciyar maza, don
haka ka kula da kanka, ruwa ba sa'an kwando bane."
Da fadar haka sai Lushamaira ta doka tsaki ta bar cikin tanti, ita kuwa Shadilat sai mamaki ya
cika mata zuciya ita kanda bata taba tunanin rashin jituwar Yarima Zaiyan da Gimbiya
Lushmaira ya kai haka ba. Da kyar ta samu ta daure damuwarta ta matsa kusa da shi ta ce.
Ka yi hakuri Ya kai Yarima Zaiyan hakika zuciyar Gimbiya a kekashe take, ba wai bata nuna
biyayya akan ka bane don rashin tarbiya a'a tana haka ne kawai don ta nuna maka cewar ita
ma jarumace tamkar, har kullum daukar kanta take kamar kai."
Sa'adda Shadilat ta zo nan a cikin zancenta sai Yarima Zaiyan ya dubeta koda ya tsura mata
idanu sai kuma ya bushe da dariya, wannan al'amari shi
ya jefa zuciyar Shadilat cikin tsananin mamaki har sai da ta yi tsammanin Yarima Zaiyan ya
kamu da ciwon damuwa wanda har ya haifar masa da matsala ciwon hauka, amma kafin ta yi
aune da tunaninta sai taga ya yi shiru kuma ya kara dubanta ya ce, "Ki je ki kirawo min Gimbiya
Lushmaira yanzu ina son zan yi magana da ita."
Batare da Shadilat ta tambaye shi dalili ba, ta juya ta fice daga cikin Tanti, jim kadan sai ga su
sun shigo ciki Gimbiya Lushmaira ta nemi guri ta zauna bata ko kalle shi ba, ita ma Shadilat ta
zauna a inda take zaune.
Koda ganin haka sai Yarima Zaiyan ya dubi Lushmaira ya matsa kusa da ita ya dan sunkuya
dan rage tsaye sannan ya ce, "Wutar daji, tafi kama da masifar da za'a kirata da suna
KUBUBUWAR AJALI, sunan mai tarwatsa mazaje, a filin daga Sadauki, ya yinda sunan
makashin
dabba, mafarauci, dan haka kada yaki da dabba ya sa ki girman kai har ki dinga daukar kanki, a
matsayin jaruma, koda ganin kashe dabbar da kukai, ban yi tunanin dama ke jaruma ce, na yi
tunani kamar haka, ashe dama makaminki mai kaifi ne."
Koda jarumi Zaiyan ya zo nan a cikin batunsa sai tsananin fushi da takaici ya kama Gimbiya
Lushmaira kai ba ma ita ba har Shadilat wato duk irin abin da mu kai nasara tana daga kaifin
tsinin masukanmu da takubbanmu, tabbas, ya ma raina musu hankali.
Lushmaira ta dago da kai cikin bacin rai ta ce, "Ku ido da ido da Zakanya sai na mijin gaske,
duk wannan maganganun da kake na riga na sani kana yinsu ne domin hassada, ina son ka
sani ita hassada tana tauye aikinka na alkari, na aminta da duk irin gwajin da kake tunanin za
ka yi min in har haka zai tabbatar maka da cewar mai hannu ɗaya baifi gurgu ba.
Mu hadu a part 5