TURBAR GASKIYA Book 6 Littafin Yaki by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf

Author :  Abdulaziz Sani M Gini Category :  Hausa Novels 001

Chapter   1 / 1

1 to 1.1K   out of 1.1K words

TURBAR GASKIYA
Part 6
MADAKIN GINI
08237237071

Lokacin da Gimbiya Lushmaira take duban wadannan Zakuna miji da mata sun yi mata
kawanya sai nan take ta shiga cikin tsananin ta shi hankali

Cikin 'yar sarsaría suka dinga matsuwa inda take, tana masu wani hargitsantsan gurnani mai
zaranar da zukatan ma'abota saurare.

Nan ta tsaya ita ba abin ta zura da gudu ba, ba kuma abin ta yi yaki dasu ba domin ko ba
gwadaba linzami ya fi karfin bakin kaza, amma lokacin da ta ga sun yo kanta cikin fushi sai ita
ma hankalinta ya dugunzuma domin ta aiyana a ranta cewa, idan ta tsaya tabbas za su sami
nasara akanta idan kuma ta ta shi tsaye ta kare kanta, watakila ta samu ta yi nasara akanta.
Nan take tunanin irin jarumtakar da mahaifinta ya yi a lokacin da macijiyar Burukul Kursum ta
shi go birninsu ya fado mata a lokacin da mahaifiyarta take bata labarin irin namijin kokarin da
ya yi har ya soke idon macijiya a yanda aka siffanta mata macijiyar loma guda
zata yi wa wadannan Zakuna ta gama da su, tabbas idan ta kasa karo da wadannan Zakuna
babu shakka ko inda ake yaki da Macijiya ba za ta iya zuwa ba, in kuwa hakane Kudirinta ba zai
taba cika ba.

Wannan tunanin shi ya yi tsananin karawa Gimbiya Lushmaira karfin ta ji wani sabon karfi ya
shigeta bata san lokacin da ta kwarara Kabbara ba. Ta tunkari Zakunan kamar yanda suke
tunkarota.

A tare suka yi sufa kanta, ita ma sai ta daka tsalle ta yi kansu a ka wata babagoyar haduwa a
cikin sararin iska, su duka suka gauro, wani taimako da Allah ya yi mata, a lokacin da aka ta shi
sama da niyar ta yi karo da wadannan Zakuna sai suka fita ta shi sama, dan haka su biyu suka
gauro suka zube kasa bisa faduwar rashin tsammanin domin dukkanin su basu fadi akan
kafafunsu ba kamar yanda ita ta fadi a kan nata kafafun.

Kafin su yi yunkuri mikewa sai ta yi azama ta yi kan Namijin Zakin da yake Rokaritt mikewa a
cikin tsananin fushi.

Tun daga inda take ta yi alkafira ta fada
TURBAR GASKIYA4

MADAKIN GINI

kan Zakin ta mai da shi, ya kara wani yunkuri zai mike ta saka kafa ta taka wuyansa iyaka
Karfinta.

Nan take ya kama kakarin mutuwa itu kuwa sai sa kara dagewa tana cikin haka hata ankara ha
ta ji an sureta an doka ta da kasa.

Cikin rashin bazata ta dubi wannan Zakanyar ce ta kara yunkuruwa cikin ta shin hankali ta kara
hiyota zata kara turmesheta.

A wannan lokacin karfin Gimbiya ya gama karewa amma ta ta kwala wata Kabhara domin ta
riga ta san idan wannan Zakanyar la turme sheta to sai dan Buzunta, ai kuwa yin wannan
kabbara sai ta yi sama tamkar wacce aka saka kugiya aka shillata, koda ta ta shi fadowa sai ta
sauko a kan kafafuwanta
Ai kuwa tana faduwa Zakanyar nan ta Kara yin kukan kura ta yo kanta. Irin mahaukacin gudun
da take yi yusa Gimbiya Lushmaira ta fahinci dan ta samicia za su yi muguwar ragwabza, ar
kuwa sai ta falfala da gudu. Ita ma Zakanyar ta bi bayanta suka kasa tsire cikin Isananin gudu,
wata dabara ta fadowa Gimhiya Lushmami lokacin da ta ga Zakanyar ta Kara tsananta, wajen
ne man ranta, dabarar da ta fado mata ita ce wata dogowar bishiya ta taku gabanta, suna cikin
gudun sai kawai Gimbiya Lushmaira ta kara azama dan ta nuli jikin bishiya tana kuwa isa sai ta
kama tattaka bishiyar tamkar wata 'yar biri, sai da ta yi nisa a saman bishiya a lokacin da
Zakanyar ta dako tsalle da niyar ta cafkota sai kawai Gimbiyar Lushmaira ta wultsila da haya,
Zakanyar ta dake bishiyar.

Saboda karfin da Zakanyar ta yi wajen dokan bishiyar sai da Bishiyar ta karya biyu rabi ya zubi
kasan jijjigen bishiyar ya kuma ya tumboko amma bai gama tumbukewa ba, amma rabin
bishiyar ya cire sun yi tafiyar ruwa da zakanyar, Zakanyar ta fadi kasa ko shuruwa bata yi ba

Aikuwa ganin wannan nasara da Gimbiya Lushmaira ta yi sai ta yi sauri zuwa inda jaririn Zakin
nan yake ta dauke shi ta kara falfalawa da gudu domin kuwa duk Zakunan ta lura basu mutu ba,
domin kuwa sai motsi suke.

Koda ta yi nisa sai ta fara tafiya a hankali domin wata shu'umar gajiya ta sarketa haka nan bata
san lokacin da ta zube kasa ba amma saboda tsananin naci irin na gimbiya Lushmaira bata saki
wannan jaririyar Zakin ba.

Al'amarin su Yarima Zaiyan da sauran tawagar su Sarki kuwa lokacin da suka kara nisa a cikin
tafiyarsu, har ya zamana sun shigo cikin dajin da 'yan sumamen daga bangaren Su Sarki
Madham suka boye cikin ciyayi suke. Koda Suka shi go wannan gurin sai tafiyarsu ta koma
sassarfa kuma da yawa daga cikin mayakan da suke kan gaba sun zare makamansu.
Ba komai ya sa haka face, kawai sun lura cewar akwai alamar wasu halitton a gun, ba dan
komai suka gane haka sai ganin da yawan Tsunsayen dajin sun ta shi sama, sannan kananun
namun dawa sun komo wajen dajin idanuwansu na kallon cikin korayen ganyayyarki

Lokacin da suka isa tsakiyar dajin basu gushe ba suna kara falfalawa da gudu suna kabbara
tare da daga makamansu sama.

Haka nan suka wuce wannan dajin batare da maboyan Dakarun sun yi illar komai a gare su ba

Lokacin da Ayarin Dakarun suka gama wucewa sahu-sahu, su ka yi nisa sai Dakarun suka firfito
suka taaya su ka yi cirko cirko suna numfarfashi. Domin wani irin tauro ne ya cika misu zuciya
har ya haifar musu da kasa aiwatar da koman

Su ka fito daga cikin mañoyar Sadauki Aksar ya tsaki gami da doka kafarsa a kasa, ya co.

"Tir da wannan jarumtakarmu da har kwarjinin wasu zai hanamu mu siwatar da abinda
shugabanmu ya umareemu, yanzu mai kuke zaton za mu je mu sanar da Sarki.

Wani mai bi masa da ake wa lakabi da Kuffuru, ya numfasa ya co, "Ya shugaba ni kaina abinda
yake raina ke nan, kuma na tabbata idan har muka komawa Sarki da labarin wannan ragwanta
da mu kai ba mu da hukunci da ya wuce harshensu ya karce kasa, ma'ana kaifin takohinsu ta
datsa wuyanmu, sai dai ba za mu talia barın haka ta faru kuma aikata hakan ba ya na nufin mun
gama asarar aikinmu hane, yanzu ma skwal dama tunda yanzu muna bayan wadannan Dakaru
abu na farko da za mu yi saurin yi yanzu shi ne mu bi bayansu tun kafin su Isa Sansanin da za
a yi wannan gumurzun mu


Mu hadu a part 6 don cigaban labari

1 / 1

Chapters