Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : New Hausa Novels 2026
TURBAR GASKIYA
BOOK 10
MADAKIN GINI
Koda Sarki Abu Zaiyan ya zo nan cikin natunsa sai jama'arsa suka kaure da kabbara. Lokacin
da sarakan uku da kuma manya dakaru da aka ware sai farin ciki ya mamayesu domin suna
gani sun samu nasara sun gama da haka suma sai suka barke da ihu.
Koda aka natsa da ihu da kabbara na kowane sansani sai Sadauki fangaren su Tarmas da
akewa lakabi da Mukanu, ya ei gaba da girgiza yana wani motsa sassan jikinsa yana daga
makami.
Nan da nan sai kowa ya ja da baya Sarki Tarmas da Sarki Husaka, Sarki madhman suka koma
kan kujerunsų suka zauna suna kallon wannan al'amari, cike da farin ciki domin sun san nasara
ta samu.
Shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya dubi gabas ya yi sujjada ga Allah sannan ya mike ya daga
hannu yı yi addu'a kana ya shafa ya dubi Sadauki Mukanu.
Hakikanin gaskiya banda Sarki Abu Zaiya bashi da tsoro kuma bai san tsoro ba da babu shakka
sai ya ji tsoron Makanu domin ku Kumburi jikin Sadauki makamu abin sa faduwar gaba ne, da
yanda damatsansa suke rawa 6ul-bula kai kace wata bijimar Mesa ce take kwance take
numfarfashi, wannan kadai dole yasa Babban Sadauki faduwar gaba, musamman irin makami
na kare dangi da yake hannunsa.
Amma shi Sarki Abu Zaiyan ko lura da haka ba i yi ba fatansa kawai su ja daga aikuwa sai
wanan katon ya shammaci Sarki Abu Zaiyan ya wullo masa katuwar garkuwarsa da niyar ta
ballawa Abu Zaiyan baya.
Koda Sarki Abu zaiya ya ga tahowar wannan garkuwa tamkar an saka kwari an harbota saboda
tsananin gudun da take har wani tashin kura take, amma kafin kuwa
ya ankara tuniSarki Abu Zaiyan ya tafi ga garkuwar nan sai da ya kusa isa gareta sannan ya
daka tsalle ya takata ta kowa Kara masa karfin ta shi sama koda ya tafi cikin iska tamkar an har
ba shi bai sauka ako ina ha da kafafuwansa biyu ya doki Kirjin Sadauki Makanu.
Sarki Abu zaiyan ya fado kasa baya da taku biyar saboda tsananin bugun da ya yiwa Makanu
shi kuma Makanu ya yi amfani da karfin kirijinsa ya yi cille da Sarki Abu Zaiyan.
Koda Sarki ya gansa a kasa ga kuma Sadauki Makanu a tsaye tamkar ba shi ya yiwa wannan
dukan ba, sai ran Sarki ya baci, kafin ya yi aune Makanu ya ta so masa haikan da niyar ya
rugaza shi da katuwar gudumar duke hannunsa.
Gudun da Makanu yake shi ya tsorotar da zuciyar su Yarima Zaiyan da sauran jama'a domin
tun kafin Sarkı ya
farga ga shi kurma ya fargar, amma bai vi wani yunkuri ba duk da cewar sauru/kiris Makanu ya
isa gam shi abinda basu sani ba Kofar ragowa ya yi masa sai da Makamu ya gama, bada
karfinsa guri guda sannanne Sarki Abu zaiya ya yi katantanwa ya fille Kafafuwansasu una alue
ise sammA
Aikuwa sai ga Makanu ya tashi sama tamkar wanda aka saka kugiya ta shilla sama da shi, kana
ga gudumarsa, ita ta yi sama Ganin haka Sarki ya yi sufa ya dauki Gudumar kafin Su iso kasa,
sai ya saita tsakiyar kan Makanu ya buga masa ita ai kuwa sai jini aka gani ya yi isartuwa a filin
gurin, gawar Makanu ta silalo kasa sai ga shi jini sai zuba yake ta ko'ina yana shuri-shiru
mutuwa.
Nan take bangaren Sarki Abu Zaiyan aka hau tafi da shewa ana kabbara da kiran sunan Allah,
shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya shiga zarya yana jiran wani mai
Karar kwanan a tsakiyar fili
Wannan al'arnari ba karami mamaki ya bawa kowa ba a cikin sahun sahun kafurai da manyan
adawan da aka tanada dan maganance musulunci da kautar da TURBAR GASKIYA.
Amma sai suka sauri suka turo wani Narkeken kato wanda ake masa lakabi da suna Jaura, shi
dai wannan Sadauki an haife shi a na lokacin da ake muku-mukun sanyi wanda kuma saboda
tsabar haihuwarsa da a ka yi da abubuwan al'ajabi a wannan lokaci haka ya kasance har sai da
Lokaci ya wuce sannan aka saka masa riga da wando kai sannan ne ma aka fara gasa masa
cibiya, wannan dalili ne aka saka masa suna Jaura, kuma a duk lokacin da wannan Sadauki ya
fi saukaka al'amuran al'umma shi ne lokacin Jaura, baya fada ko mai ka yi masa.
Dan haka Sai Jaura ya fito a cikin
hargitsantsan gudu da niyar ta take Sarki ya yi tamole da shi. Kowa dake filin sai da ya ji
faduwar gaba da fitowar Jaura domin girmansa ya yi Makanu sai biyu sannan kumarinsa ya
ninka na Makanu ga shi baki wuluk ko dan haske rahma babu a fuskarsa uwa uba ga irin
makamın da yake rike da shi, wani dogon mashi ne amma bakinsa mai tsini ne da shi wani
fataitane mai baki shi da wanda idan aka su ke ka da shi babu mamaki sai ya zaftaro duk wani
abu da yake cikin cikinka.
Koda ya nufo Sarki Abu Zaiyan da wannan makami cikin tsananin gudu wanda yasa kasa
girgiza, koda ya rufo Sarki sai Sarki abu Zaiyan ya juya da baya ya fita da gudu kamar ya ji
tsoro wannan al'amari ya saka su Sarki Tarmas dariya suna ganin Sarki tsorata ya yi, koda
Suka zuba tsare tsakanin Sarki Abu Zaiyan da Jaura sai suka ci gaba da falfalawa Sarki yana zagayawa da Jaura a fili har kusan rabin sa'a a wannan lokaci kuwa sai Jaura ya tsaya
yana haki, shi kuwa Sarki Abu zaiyan sai ya tsaya a gabansa ya ce
"Yanzu ne ya kamata mu yaki juna ni da kai."
Kafin Jaura ya yi wata magana tuni Sarki ya yi kansa nan take suka kauri da hargitsantsan yaki
suna kai sara da suka babu ji babu gani, dukka wani sara da jaura ya ke kaiwa Sarki sai Sarki
Abu zaiyan ya kauce, a haka nan ma Sarki ya kara wahalar da Jaura har ya zamana jaura ya
fara yin laushi da kai sara da suka, amma saboda tsananin taurin rai da karfin hali bai fasa ba,
shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya tikirkire ya dunkule hannu ya shammace Jaura ya dokan
masa mukamuki da hannun nasa
Sadauki jaura ya shamye dukan tamkar sauro ne ya cije shi ya kawowa
Sarki cafka da niyar ya daga shi sarma ya jefar da shi sannan ya bi shi da suka, aikuwa sai
Sarki ya kauce jaura ya kara kai hannu nan take ya yi sa'ar damkar Sarki Abu Zaiyan ya daga
shi sama sai ya daga shi ya dankara Sarki da kasa, maimakon Sarki Abu zaiyan ya fadi kasa ya
ji ciwo ko ya karkarye sai kawai aka ga Sarki ya dirga akan kafafuwansa daram, ganin haka
Jaura ya kawo suka, Sarki ya rike mashi da hannunsa tamau.
Jaura ya ja mashi da iyaka karfinsa mma sai ya ji ya kasa kwace, dan haka sai ya kawo
mangari da Garkuwarsa, shi kuwa Sarki Abu zaiyan sai ya yi matattakala da Garukuwa ya tafi a
sama ya doke Jaura a fuska, wannan dalili ne yasa Jaura sakin Mashin ya tafi taga taga zai fadi
nan take Sarki Abu zaiyan ya loma masa wannan mashin a ciki, ya kuma zaro Mashi lokaci
guda, Sai ga Jaura yana ihu, 'ya'yan
hancinsa hanta kuda da sauran kayan ciki sun yi fitar burgo
Koda faruwar Wannan al'amari sai kuwa da ihu ya cika gurin baki daya aka kama Kabbara,
mamaki irin Sadaukantakar Sarki Abu Zaiyan ta cika zuciyar Yarima Zaiyan da Sarkin yaki
Safwan da Kuma Lushmaira da kuma Shadilat da sauran jama'ar da suka taho dan yi jahadi.
Su Sarki Tarmas kuwa sai suka ji kamar su fashe da matsanancin kuka saboda ganin barnar da
Sarki ya yi musu a dan kankanin lokaci ya karar musu da sadaukan da idan da fadan Yamutse
akai da tuni sun kashe ya kai Dubu goma amma sun salwanta batare da sun ji gabata Sarki ba,
nan take Sarki tarmas ya dubi Sarki Madham ya ce, "Ai kuwa ba wuka muka dauka muka
dabawa kanmu ba ya ya kuke ganin zamu samu nasara alhalin a cikin
majiya karfin talatin da muke ji da su, biyu sun tafi, ta hanyar Sarkinsu kadai. Kada ku manta a
kwai Sarkin yaki Safwan mun san kwazonshi ba tun yau ba, ga kuma Yarima Zaiyan wanda
labari ya zo mana cewar shima tsakwakurine."
Koda ya kawo nan a cikin batunsa sai Sarki Husaka ya ce, "Haba ya kai Sarki Tarmas kada ka
manta, da waye Sarki abu Zaiyan ai ku da za a samu lagonsa ba yanzu ba, kai da ka zuba ido
akwai ribar a nan gaba
Kafin su ankara sai suka ji ihu wani Barden ya fito ganin wannan katon da ake Kira Rislalu sai
hankalinsu ya kwanta domin kuwa shi kuma bai da wani lokaci da aka taba nasara akansa, duk
irin yaki da ya yi a duniya wanda a kalla ya yi yakukuwa dari biyar, ba'a taba samun lokacin da
aka lakuci koda yatsansa ba, saboda tsananin masifarsa a filin daga ko