Author : M.Shakur Category : My Hausa Novels
soyayya har lokacin shiga paper yayi takashe wayan ta shiga.
Kwance tashi asaran mai rai, kwanaki sai ja suke, kullum soyayyar shukra karuwa take aran thariq amma baitaba fadamataba, saidai kullum kokarin nisantar ta yake, ta hanyar kin dawowa daga asibiti da wuri duk yana hakane saboda ya kula da amanan ta dake kanshi.
Yayinda shukra soyayyar Nazir tai zurfi aranta kullum intaje school sai sunsha fira kafin ta shiga paper. Wanan kenan.
Mum din shukra kam kullum saita kira thariq dan taji ya lafiyar yarta dakuma exam din datakeyi.
Maman shakur ๐
[10/11 9:03 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
4โฃ9โฃ
Ayaune shukra ta kammalla waec dinta dama tarubuta jamb tun kafin sugama waec, sunyi waya da Nazir yace gobe zaizo. tace amma kabari sai wuraren 11 lokacin yaya ya dade da tafiya aiki, yace mata to.
Suna gama paper thariq yazo ya dauketa sai murna take, suna kaiwa ta shiga dakinta dan ta chanza kayan makaranta, tana shiga maizata gani wani abu anyi raping dinshi, sanan sai wani katon box shima anyi raping dinshi, zuwa tayi tabude karamin taga laptop mai kyau na dell sai dan karamin paper ansa a gift 4rm thariq, tabude box din shikuma kayan sawa ne masu shegen kyau fita falo tayi da gudu taga thariq zaune taje ta dane jikinshi tana murna janyeta yayi yace mai haka?? Hawaye ya zubo daga idonta ta rikemai hannu Nagode yaya, wlh ina sonka sosai babana nabiyu, Allah baka mata tagari, azuciyarshi yace gaki nan. sai godiya take mishi yace naji jeki chanza kaya sanan ta mike tatafi.
Washe gari tun Wuraren 4 aka kira thariq daga asibiti akwai emergency hakanan yama shukra sallama yatafi, itakuma shukra takoma baccinta, dasafe Wuraren 10 tai wanka taci uban kwalliya kaman ba gobe tazauna jiran sahibinta NAZIR.
Maman shakur ๐
[10/11 9:21 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ0โฃ
Wuraren 11 yakirata yace mata gashi nan ya iso, tashi tayi takara fesa turare tafita, tana fita abunda yabata mamaki shine motoci biyu tagani daya wanda yake ciki, saikuma tagefe wata sabuwar benz ce baka sabuwa dal, karasawa tayi ta shiga mota tanamai murmushi, Nazir wani miyau ya hadiye da kyar yace yarinyar nan badai kyauba ga diri.
Riko hanunta yayi yace baby na kinyi kyau, da sauri ta janye hanunta ta ballamai hararan luv kafasan babu kyau rike hanun mace ko, yace sorry wlh inna ganki bana iya kama kaina, ranan sunsha firan soyayya saidai talura kallon da Nazir yake mata yau ya banbanta dana kullum dan wani zubin saiya kalleta ya lashe lebe, sai Wuraren 1 tacemai yakamata katafi fa, ya kalleta yace baby na wlh banason nisa dake, ke TAWA CE, fari tayi da ido tace karka damu nakusa fadama yayana maganan ka kaga saiya mana aureko. Aiko yay murmushi tana kokarin bude kofa tafita yace mata jimana,
Tajuyo ta kalleshi wasu keys ya dauko yabata ta tsaya tana kallonshi tace name?? Yay murmushi yace kinga wancan benz dinchan nakine, gift dinki ne nagama exam, ido tazaro waje jikinta yafara rawa, tace kanason katonamin asiri ne?? Mota ina zankai mota wlh banaso.
Ya kalleta yace shukra kinasona?? Tace eh, yace inhar kinasona to wlh ki karba, girgiza kai tayi tace aโa tawuce tafita, shima fitowa yayi daga motar har zata shiga gida ya damko hanunta yasamata keys din yakoma motarshi ya shiga yabar gidan, yabar shukra awajen hankalinta atashe yake.
Daki tawuce tashiga tai tagume yanzu in yaya yaxo maizata cemishi, ko 20 min baโayi da fitar Nazir ba thariq ya shigo dakin, direct dakinta yawuto, da sauri ta boye key din karkashin filo, yace shukra naga wata mota a compound ta wacece munyi baki ne??? Jikinta ne yafara rawa ko ina, tace uhmm uhmm โฆ.
Maman shakur ๐
[10/11 9:52 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ1โฃ
Jikinta rawa yake sosai kallo daya yamata yasan bata da gaskiya, dan lokacin dayashigo quarters din yahango wata mota na fitowa daga gidanshi, yakara Kallonta yace bakiban amsaba, bata bari sun hada ido ba tace yaya niban saniba, ni banma fita tsakar gida ba, Kallonta yayi yace ok, yajuya yabar dakin ranan bai kara fitaba.
Washegari dasafe yafita, Wuraren 11 taga kiran Nazir ta dauka, yace baby nasan ban fada miki zanzo ba amma dan Allah kifito muyi sallama kano zan koma kinji, fita tayi basu wani dadeba dayake sauri yake yabata kudi yan dubu 100, taki karba fitowa tayi yabiyo bayanta zata shiga ciki yakamo hanunta dai dai lokacin motan thariq ta shigo cikin gidan.
Shukra kokarin fizge hanunta take amma Nazir yaki saki kanshi na kallon motar thariq, saida thariq yafito hannunshi a aljihu, jijiyoyin kanshi duk sun fito sanan yatako wurin yana taku kasaita sai alokacin shukra tasamu daman kwace hanunta ta shige gida da gudu.
Nazir yay murmushi yace yayanmu ina wuni, thariq yay mishi wani kallo batare dayace komiba, Nazir yajuya zai tafi thariq yace kafita harkan kanwata, TAWA CE, stay away 4rm her. Nazir yajuyo yace karya kake malam, saina auri kanwarka wlh dan TAWA CE! Inaba hakaba duk kudin dana kashe mata sai anbiyani, yajuya yashiga mota yabar gida, thariq azuciye yafada cikin gidan direct dakin shukra yawuce.
Tana ganinshi tamike tafara kuka tana ihu, harda dan guntun fitsari a wando, ya tsaya dai dai saitinta har tanajin numfashin shi cikin muryan tsawa yace motar waye a gidanan??, ki gayamin gaskiya kona saba miki yau, jikinta yafara rawa tana hawaye tace na..na..w.. Kafin takarasa maganan taji tass afuskantaโฆ
Maman shakur ๐
[10/11 10:20 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ2โฃ
Ta dafe kuncinta tana kuka sosai, cikin wani irin muryan fushi yace a ina kuka hadu, ta kuma ina kuke communicating?? Wlh inkikamin karya shukra yau saina zaneki, kuka take sosai tace dan Allah karka zaneni, bazan karaba wlh natuba, yace a ina kuka sake haduwa?? Tana kuka tace yaya lokacin da nafara zuwa school akano, yace ta ina kuke magana?? Murya na rawa tace tawaya, Kallonta yayi yace dan baki da kunya shine kike amfani da wayan nan, shukra ke amanata ne, ban karbi wayan nan lokacin bane saboda na lura kinaso, and all i want is 4 u to be happy, nabar miki, but banace miki banason kiyi waya da kowaba? Ta girgiza kai yaya Allah bazan karaba dan Allah kayakuri wlh natuba yaya.
Yace ina abubuwan dayake baki?? Tanuna mai yaje yafito dasu babu abunda ta taba tabawa, har kudaden, su biscuit din duka duk sunanan yanda suke, yadawo gabanta mesa kikamin karya? Dama shiyabaki mota shine kika ki fadamin, harda bashi address din gidanan kinkosan waye nazir shukra?? Did u have any idea who dat man is?? Ta girgiza kai yayakaya kuri, wlh ina sonshine, wani wawan mari taji abakinta nan da nan lebenta yafashe yana jini, yace ni kike cema kina sonshine?? Abunku da yarinya, takara fashewa da kuka yay dan Allah kadena dukana wlh natuba, Allah dan inason shine, kuma ina tsoron karabamu saisa ban fadamaba,wlh ina son Nazir.
Mari yakaimata yaciro belt din jikinshi ya zaneta sosai ranan sai ihu take babu mai ceto, dan kanshi ya kyaleta ya daka mata tsawa ina key din mota ta dauko tabashi jikinta na rawa, yace ina wayan ta dauko tabashi yawuce yabar dakin, harya fita yadawo yace Nazir yataba cemiki ki cire riga?? Tace aโa, yataba kaiki wani waje?? Tace aโa. Hamdala yayi dan yasan Nazir dan iskan ne, ga shukra kuma rashin wayau.
Dawowa dakin yayi yadau duka kayan dayaba shukra yaje yasa a motan, yadau waya yakira wani driver yazo, yarubu tamai address din Nazir yakai mishi kayan gidansu. Dayake tun tuni yayi bincike kan Nazir, tun lokacin da Nazir ke binsu.
Maman shakur ๐
[10/11 10:40 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ3โฃ
Shukra tasha kuka sosai, duk hankalinta yatashi yau babanta na biyu na fushi da ita, tashi tayi jikinta duk yay tsami ta shiga bayi ta wanke bakinta dake jini, ta dawo kan gado tacigaba da kuka sosai daga baya bacci ya dauketa.
Thariq ya shiga dakinshi duk ranshi abace, Nazir ya cuceshi, ya koyama shukra sonshi, daga baya kuma saiya fara blaming kanshi, tokai mekakeyi?, har yarinya tafara soyayya, tafara kawo saurayi gida, tana magana da saurayi a waya, duk baka saniba, Thariq baka iya rike amana ba, inda yanzu lalacewa ne da yanzu shukra ta lalace, ta baci batareda kasaniba, u just dedicated ur whole lyf to asibiti, yakamata koda kana aiki suma gidan ka sa ido akansu, ka kula da iyalinka, shukra tafara soyayya amma wlh ba laifinta bane laifi nane, bansa ido dakyau a alโamurantaba, ban kula da ita dakyauba, bayan cewa ita responsibility nane, godiya yayima Allah dayasa yagane tun yanzu kafin Nazir yakai ga bata shukra, yakuma kara daura dammaran kula da ita, saโido a kanta, dan shukra TASHI CE kuma amanarshice.
Nazir yana zaune a dakinshi akai sallama dashi koda yafita driver harya ajiye mota yamika ma mai gadi key aba Nazir yatafi, Nazir ya karbi key din yaduba motan yaga duk abunda yabama shukra bata taba komiba yay mamaki, amma daga baya yay murmushi, yacema kanshi dole nagano wanene wanchan guy din ( thariq) arayuwan shukra, anya kuwa yayanta ne?? Dan naga sonta a idonshi, yay murmushi yace inkunsan wata bakusan wataba, shukra TAWA CE, wlh ko ban auretaba, saina sha zumanta, idan kuma hakan bai samuba to zanba shukra tabon da harta mutu yana jikinta. yay wani saurayin murmushi yajuya yashiga gida.
Masu karatu wani tabo yakeson sawa shukra??? Wanda harta mutu yana tare da ita?? Ina jiran comment naku.
Maman shakur ๐
mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
โ TAWA CE!!! 47 to 53TAWA CE!!! 60 to 63 โ
TAWA CE!!! 54 to 59
Posted on November 11, 2015 by mamanshakur
[11/11 7:51 PM] Aishat muhโd: [11/11 8:26 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ4โฃ
Da yamma shukra ta fito bataga thariq a falo ba tashiga kitchen ta dafa musu abinci. Coconut rice da stew, amma kwata kwata takasa ci, ta zauna akasa tai shiru tai tagumi, gashi cikinta har ciwo yake saboda yunwa.
Wuraren 10 yashigo gidan, yaganta zaune a falo idonta arufe tarike cikinta, da sauri yakarasa yarikota yana shukra lpy?? Ahankali ta bude idonta ta kalleshi tace yunwa nakeji, tashi yayi yashiga kitchen yadebo abincin yabata tace bazan iyaba kabani abaki, yafara bata yaki bari suhada ido, saida sukaki last spoon yazo zaisa abakinta ta daura hanunta kan nashi ta kalleshi hawaye ya zubo idonta tace yaya dan Allah kayakuri plz, bazan karaba kaji, ajiye spoon din yayi yamike yatafi dakinshi, binshi tayi ta tsaya bakin kofa tana kuka sosai amma thariq bai budeba har bacci ya dauketa a wurin yafito ya kaita dakinta.
Adaren thariq baiyi bacci ba, karshe ya yanke shawara zaikai shukra wajen mamanta, kota kara wayau tasan rayuwar ya mace.
Washegari da safe yakira hajara sukai maganan, tace Thariq gwara muhadu a kano kaga yakamata su baffa ( dad Thariq) da mum dinka susan wacece shukra, kaga hakan zaisa mum dinka da baffa su daidaita kansu ko?? Yace hakane anty, tace duk muhadu a kano yau, bari fadama honey mu shirya, sukai sallama suka katse wayan.
Dakin shukra ya shiga yaga tai zuru zuru ta balaโin bashi tausayi amma dole ya share, yace kihada kayanki zamuyi tafiya, murya kasa kasa tace yaya ina zamu?? Yace zankaiki wurin mum dinki, tace yaya nafison wajenka wlh, ya ballamata harara kiwuce kihada kayanki nace.
Maman shakur ๐
[11/11 9:17 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ5โฃ
Thariq basu shiga hanyar kano ba sai Wuraren 4 saboda yadanje asibiti, hajara sai kiranshi take dayake su harsun dade da isowa.
Wuraren 6 suka isa kano, shukra tana ganin sun shiga gidansu thariq tafara kuka yaya dan Allah mukoma wlh mum zata dakeni, yanda yaga hankalinta yatashi yasa yace mata babu abunda zata miki i promise u. Side dinshi yafara kaita saida suka salla sanan suka fito hanunshi ta rike gam suka shiga falon da sallamnsu.
Kowa na falo, dad,mum, Hj amina, hajara,Alh tafawa, twins dakuma imran. Dad shiya fara mikewa tsaye yace shukra baby kece kuwa?? Dama nace ke TAWA CE nasan zaki dawo gareni, ya kalli mum wanda haryau fada suke basu shiryaba yace kinga tadawo gareni saidai ki mutu da bakin ciki.
Mum ta mike tana nuna shukra da yatsa wanda tarike thariq gam jikinta na rawa mekika dawo yi?? Bar gidanan kafinโฆ
Hj Amina ne tamike tsaye itama da murmushi a fuskanta ta kalli dad tace yaya (dayake haka take kiranshi tunda kanin mijintane late Alh Muhโd,). tace yaya, hj ku zauna yanzu ba lokacin fada bane, tajuyo ta kalli thariq tace likita samu wuri ku zauna yazauna shukra ta zauna kasa ta rike kafanshi gam.
Hj Amina itace tafadi masu ko wacece shukra garesu, shukra kam kuka take sosai yanzu dad na matsayin kakanta ne?? Yaya thariq dan uwanta?? Ashe maganan yafito fili, hj Amina tace kwarai kuwa, marigayi Alh muhd mijina yayan dad din thariq neโฆ.
Maman shakur ๐
[11/11 9:59 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ6โฃ
Dad da jikinshi yay sanyi, yace ashe duk abunda nakeji game da shukra baโa banza bane, ashe ke jikata ne saisa Allah ya dauramin sonki. yace yaya na marigayi Alh muhโd yarigani aure danni banyi aurebama saida nakai shekara 45, saisa har Alh yay aure suka haifi hajara ni banyi aureba, kafin hajara tai aurene nazo nai aure ba dadewa alh ya albarkacemu da thariq.
Bayan haihuwan thariq dakusan shekara 15, akai bikin hajara inda itakuma bata samu ciki da wuriba, lokacin data haihu Alh yafadamin amma lokacin muna makka, Alh yacemin yasamu jika mai suna shukra nataya yayana murna sosai, muka dawo mukazo mukaga shukra sanan muka koma kano dayake ni achan nake aiki.
Bayan rasuwan yaya dayan watanni, hj takira waya wai baban shukra da shukra duk sun mutu.
Kowa jikinshi yay sanyi shukra yau taji inama babanta na wurinan, ashe ba laifin maman tabane, mum din thariq tazo wurin shukra tace kiyafemin dan Allah, shukra ta share hawaye tace mum na yafe miki bakimin komiba, hj Amina ma tazo shukra tace kaka nayafe miki wlh. shukra ta dagakai ta kalli ummanta hajara dake kuka sosai ahankali ta mike taje ta tsugunna agabanta tace umma na plz kiyafemin abunda namiki ranan, hajara tace bakimin komiba suka rungume juna yan biyu ma suka taso suka hadu suka rungume umman su.
Shukra tamike taje gaban alh tafawa da shima yay dan guntun hawayen tausayi, tace babana na uku ina wuni, kowa yay dariya adakin, yay murna yaji dadi yanda shukra takirashi babanta, shukra ta mike taje ta rungume dad din thariq ya kankameta yana jikalle ta ya isa haka kukan kinsan banison ganinki a damuwa ko, ta mike tajuyo ta kalli thariq, gudu tayi ta isa gareshi wani irin runguma ta mishi tana kuka sosai tace kaine Babana ne nabiyu, kai yaya nane, kaikuma dan uwanane, kaine gatana, u are my everything yaya thariqโฆ
Maman shakur ๐
[11/11 7:51 PM] Aishat muhโd: [11/11 10:23 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐ ๐ฟ๐ฟ๐ฟ
5โฃ7โฃ
Yanda yaji tana kuka ajikinshi saita karyamai zuciya, ya dagota yace shii, kukan ya isa haka karkiyi ciwo kinji shukra, ya share mata hawaye takoma kasa ta zauna ta rikemai kafa gam.
Ranan dai ankusa raba dare a wurin sai fira ake, dad da mum sun yafi juna sun shirya, hajara ma tayafema mahaufiyarta hj amina, kowadai murna yake. shukra, twins,da imran awurin suka bingile da bacci, yayinda dad Alh tafawa, thariq, mum,hj amina,da hajara sai fira suke suna dariya, hajiya na kara basu labarin yanda dad yadinga cewa zai aure shukra suna dariya. Mum ne ta kalleshi tace alh abu daya ne ya tsayamin arai har yanzu maiya kaika dakin shukra da daddarenan harna ganta akan cinyan ka?? Kowa yay shiru yana sonjin abunda dad zaice.
Dad ya sauke ajiyan zuciya yace bayan nagama abunda nake naji kukan shukra tana zafi zai kasheta ina shiga na kunna mata A.c. shine na zauna bakin gado ina shukra dena kuka na kunna miki A.c., kallona tayi tace babana sai ta daura kanta ajikina tacigaba da bacci, tausayi tabani sosai shine yasa ban cireta daga jikinaba ina shafa mata kai dan nasan yada da yakeji inbaida iyaye, dan nima narasa iyayena tun muna yara.
Kowa ya sauke ajiyan zuciya. Sai Wuraren 1 nadare suka gama fira, dad da mum suka tafi dakinsu, alh tafawa yadau hassan, hajara tadau hussain, ta kalli thariq tace dan kawo mana shukra side dinmu thariq yace to anty.
Ahankali ya janye hanunta daga kafanshi, ya daga kanta dake kan cinyanshi, ya dauketa chak kaman jaririya yabi bayansu Anty, dakin hajara ya kwantar da ita kan gado sanan yay musu sallama yatafi part dinshi.
Maman shakur ๐
[11/11 10:48 AM] Aishat muhโd: ๐ฟ๐ฟ๐ฟ TAWA CE!!! ๐
๐