MACIJIYA CE Book Complete By Garkuwar Jarumai.docx

Author :  Oum Sharifa Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   1 / 5

1 to 3K   out of 13.9K words

*MACIJIYA CE*

Book 1

Na

Oum sharifat (Garkuwar jarumai ce)

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION

بسم الله الرحمن الرحيم

Mutane ne cike cikin Wata ƙasaitacciyar fada wadda aka ƙawata ta da abubuwan burgewa wanda ke nuna isa da mulkin masarautar, sarkin dake mulkin garin wani ƙaton basamude ne ma'abocin girma da kwarjini,

yana zaune kan wata ƙasaitacciyar kujera cikin shiga ta alfarma wacce ke nuni da tsantsar mulki da kuma izza irin ta sarautar gargajiya, gefen sarkin wata matashiya ce wacce ba zata gaza shekara ashirin da biyar ba cikin shiga ta alfarma,

rabin fuskar ta a rufe da mayafi, rabi kaɗai ake gani saidai rabin bai rufe tsananin kyawun da take da shi ba.

Sarkin garin da wasu daga cikin mutanen garin suna bauta wa tsohon sarkin su wato kakan sarkin su na yanzu wanda akayi gunkin sa suka gina masa ɗaki inda suke bauta masa a matsayin ubangijin su.

suna kiran abn bautar da baduuhu shidai wannan abn bauta dk shekara ana yanka masa mata guda uku maza uku a bashi jinin shine hidimar da suke masa kuma anayin kuria ne dk wanda ta fada kan sa shine wanda jinin sa zai zama abn hidima ga baduuhu,

Akwai ma'abota addinin musulunci a garin saidai basu da yawa sakamakon dk sanda aka tashi yin ƙuria tafi faɗawa kan su.

wannan kenan,

Gyaran murya sarkin yayi cikin ɓacin rai yace ""ba zamu lamunci cin zarafi daga wata dabba ba, ba zamu juri wata dabba ta dinga kashe mana manyan fada ba" saboda haka mun yanke hukunci gobe dk wani wanda yake jin ya isa a kira shi mafarauci ya fito za'a tafi nemo wannan macijiya da ta dame mu domin masu magani sn gano dafin macijiya ɗaya ne ke kashe mutanen mu,

Yana gama faɗa ya tashi tsaye rike da hannun matashiyar dake kusa dashi bayi suka miƙe suka musu rakiya zuwa fada.

sauri sauri take ta bar wajan a guje ta ƙarasa gidan sh ko sallama bata yi ba ta kutsa kai cikin gidan, tsohuwar dake zaune tsakar gidan ta kalle ta da sauri tace

"" boɗɗi lfy kuwa? menene?""

bata kalle ta bare ta bata amsa ta shige dakin da yake mallakin,

ta tana shiga ta zauna kan katifar ta ta fashe da kuka tana toshe baki a fili ta furta

" bani bace" bana kisa kuma bazan aikata ba" wacece ke? meyasa kike kashe su ? wane zunubi suka aika ta a gare ki?

wani zafi take ji a zuciyar ta ga wani ɗaci ɗaci da take jin sa a harshen ta, fatar jikin ta ce ta fara tattarewa cikin tashin hankali tahade hannayen ta biyu alamar roko tace "ya rabb"

wasu zafafan hawaye ne ke sakkowa daga idonta

Kafin wani lokaci daga kugun ta zuwa kafar ta ya sauya zuwa wata katuwar macijiya mai tsaho da kauri,

tana hawaye haka ta dinga nanna ɗo jelar t cike da tashin hankali tana tsoron kar wani ya shigo,

tayi iya kar ƙoƙarin ta dan ganin takoma mutum amma abn yaƙi wani irin kukata fashe dashi tana jin zafi cikin zuciyar ta,

" tabbas ni musulmace kuma mai karɓar ƙaddara mai kyau ko mara kyau

"wai da can haka nake? wacece ni? suwaye iyaye na? me ya kawo ni cikin mutane?

ya Rabb ta fada tare da hade hannu alamar roko ta ba kallon sama,

ta ɗauki tsahon lokaci a haka kfn ta jiyo sallama a tsakar gidan,

hankalin ta bai ƙara tashi ba sai dataji mai sallamr yana tambayar ta,

"" tana ciki naga ta shigo da sauri tayi ɗaki shine abnda tsohuwar tace,

alamar tafiya take jiyowa tndaga tsakar gidan tagane gurin ta ya taho, wata dabarace tazo mata da sauri tadauki wani babban zani gado ta lullube jikin ta gaba daya dashi,

daidai lokacin kuma aka shigo d

ɗakin da sallama a hankali ta amsa tare da cewa ""hamma sannu da zuwa"

bai amsa ba sai kallon yanda ta lullube jikin ta yake yi yasan bata son zafi kuma a yanayin zafin ta lullube jikin ta.

Daf da ita ya ƙaraso ya kai hannu sa da niyayar janye zanin gadon caraf yaji an rike masa hannu babu wani alamun hannu sai shi da yake jin hannun a jikin sa,

da mamaki yake kalle kalle cikin ɗakin amma babu komai sai ita dake kwance,

addu'a ya fara karantowa a zuciyar sa yana nazarin abubuwa da dama acikin ɗakin,

nan da nan ko aka sakar masa hannu yayi bismillah ya yaye mata zanin,

rintse ido tayi dn tasan yau B

babu makawa sai sn gane ita macijiya ce, koya zasuyi daiya ? daidai nan ya gama cire zanin jin shiru bai ce komai ba yasa ta bude idon ta ta sauke su akan kafafunta wanda suka sauya daga jelar macijiya zuwa suffar bil adam,

a fili ta sauke wata nannauyar a jiyar zuciya tana ƙaƙalo murmushi

""ki ƙara addu'a boddi sannan ki dage da karatun Qur'an wannan ɗakin naki sai da addu'a Allah ya ƙara tsaremn ke kanwa ta""

da murmushi a fuskar ta ta amsa da "amin hamma na"

wacece boɗɗi?

dagaske ba itace me kisan ba?

to wacece?

domin jin amsar waɗannan tambayoyi dama wasu wanda banfaɗa ba ku kasance da garkuwar jarumai domin nishaɗantar daku cikin littafin macijiya ce.

YAWAN COMMEN YAWAN TYPHING.

*MACIJIYA CE*

page 2

NA

OUM SHERIFAT

( GARKUWAR JARUMAI CE)

📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚

بسم الله الرحمن الرحيم

Ficewa yayi daga ɗakin yana sakar mata murmushi,

yana fita ta sauke ajiyar zuciya ta zuba tagumi tana tinanin rayuwar ta, ganin tnanin bazai mata ba yasa ta mike ta fito tsakar gida,

""Inna sannu da aiki tace da tsohuwar dake hura wutar kara,

yauwa boɗɗi wai ni kam me ya dame ki ne ? kika shigo ɗazu a firgice?

numfashi boɗɗi ta sauke tace ". Inna dama fa hankali na ya tashi ne saboda yanda ake kashe mutane a garin nan bansan gaba wa za'a kashe ba.

ajiye aikin inna tayi ta dawo kusa da boɗɗi ta zauna yace

" ki kwantar da hankalin ki boɗɗi na dk wanda ki ka ga ta kashe shi kwanan sa ya ƙare ita sila ce kawai,

amma babu Wanda ya keda ikon yiwa bawa wani abu harsai ya kasance ƙaddara sa,

dk nasihar da inna ke yiwa boɗɗi hankalin ta baya wajan inna

tana tinanin ranar da zasu gane ita macijiya ce tasan babu wanda zai yarda ba itace ke aika ta wannan kisan ba,

Hawaye taji yana zubowa kan kyawawan kumtun ta cikin damuwa da tausaya wa inna ta shiga share mata tana rarrashin ta har tayi shiru,

daga baya ta koma tsokanar ta da mai tsoron mutuwa,

yaƴe kawai boɗɗi keyi azuciyar ta ko cewa take ""ai nice mutuwar inna ni ba alkairi bace agareki ni musiba ce a gare ki.

Sarki bahar da gimbiya diyanah tare suka shiga cikin gidan sarautar hannun su cikin na juna,lokaci lokaci sukan juyo su hada ido,

dk sanda suka hada ido Diyanah ke sakar wa sarki bahar tsadadden musmushi wanda ke ƙara narkar da zuciyar sa, yana jin zai iya yaƙi da duniya a kanta.

Turakar sarki bahar suka shiga su kuma bayin suka tsaya a bakin ƙofa,

suna shiga DIyanah ta shiga rage kayan jinin ta ta haye kan makeken gadon dake ɗakin ta kishin giɗa tana kallon sarki bahar wanda ke shirin shiga wanka .

da murmushi ta raka shi har ya shige bayin,

bayan mintuna kaɗan sarki bahar ya fito daga wanka suna hada ido suka sake sakarwa juna murmushi har ya ƙarasa gaban wani tafkeken mudubi wanda ke kallon gadon da diyanah take,

cak ya tsaya da abnda yake yi a razane ya juyo.ya dubi diyanah sannan ya maida kallon sa ga mudubin,

wata ƙatuwar macijiya yake gani a cikin madubin ta kanannade jikin ta a kan gadon ta fasa Kai tana fitar da dafi tana mayar wa,

da zarar kuma ya juyo sai yaga diyanah kwance tana sakar masa murmushi

A matuƙar firgice sarki bahar ya ƙwalawa bayin sa kira,

da sauri suka shigo dn amsa Kiran shugaba,

madubin ya nuna musu ta re da cewa "

" me kuke gani a ciki?

ido suka ƙurawa madubin sannan suka juyo suka rusuna da sarki bahar cikin hadin baki suka ce "" baduuhu ya baka nasa gimbiya ce aciki sake kallon madubin yayi shidai macijiya yake gani a ciki a fili kuma gimbiya,

haka ya dnga kiran bayin sa da barori dk wanda ya kalli madubi gimbiya yake gani a zahiri ma haka .

Bokayen garin sarki bahar ya aikawa da sakon kira kafn cikar wasu mintina tuni turakar sarki bahar ya cika da manyan bokaye kowanne da shirgin kayan bokancin sa ,

Gyaran murya sarki bahar yayi sannan ya basu lbrn abnda ya gani,

tsahon lokaci babu wanda yace ƙala kawunan su a kasa,

gajiya yayi da jiran su dn haka ya daka musu tsawa gaba daya jikin su na rawa suka fara kame kame,

Guda ɗaya daga cikin su ne yayi hanzarin cewa

""baduuhu ya baka nasara bincike na ya nuna mn cewa kaine wanda wannan shedaniyar macijiyar take hari saidai""

ba tare da ya ƙarasa ba sarki Bahar ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa daga ƙugun sa ya cire kan wannan bokan ya wullar da shi gefe a fusace yana huci yace

"" ƙarya ne ƙarya kake sai ka riga ni mutuwa.

Kaduna

Kiɗa ne ke tashi daga wani madaidaicin daki tndaga perking space ake jiyo sautin kiɗan kowa dake gidan ya toshe kunnuwan sa saboda takura musu da kiɗan keyi saidai babu damar magana,

budurwa ce zata kai a ƙalla shekara goma sha takwas sanye take da riga da wando wanda sukayi matukar kama jikin ta gashin kanta har kugunta sakamakon attachment da akayi kitson dashi ja da blue,

rawa take sha kamar ba zata dena ba

ta ɗauki lokaci mai tsaho tana rawar kfn ɗakin da take ya fara rawa kamar zai fadi,

hankalin ta ya fara tashi da gudu tayi hanyar fita tana taba kofar taji ta gam a rufe baya tayo tana kallon yanda dakin ke rawa taji ana bude ƙofar da windowa ana rifewa,

wani irin duhu ne ya mamaye ɗakin sai sautin dariya mai kama da kukan jaki dake tashi a dakin,

tsuguna wa tayi ta toshe kunnuwan ta da hannun ta ta fashe da kuka tana kiran momy,

hasken ɗakin ne ya dawo sannan ɗakin ya tsaya cak ya dena rawa dariyar ma ta ɗauke a hankali ta bude idon ta ta mike tsaye inda ta kai duban ta ga kan katon gadon ta

A matuƙar razane ta fara ja baya sakamakon ganin wata ƙatuwar macijiya fara sol mai matukar kyalli ta yi gammo tana fito da dafi....

Macijiya ce

Page 3

Na

Oum sharifat

( Garkuwar jarumai ce)

📚📚Jarumai writter's association📚📚

بسم الله الرحمن الرحيم

Wani gigitaccen ihu ta saka wanda ya jawo hankalin mutanen gidan gaba daya

Da gudu suka yo sama daidai kofar dakin ta suka tsaya suna buga kofar tare da kiran sunan ta ,

""" Meemah ! Meemah ! Na shiga uku na meyafaru ? ki bude mana kokarin bude kofar meemah keyi amma gam gam take jin ta taki buduwa ga macijiyar tana sakkowa daga kan gadon ,

a jikin kofar meemah ga tsaya ta rufe idanun ta tana cigana da kukan ta, macijiyar na zuwa daf da meemah numfashin ta ya dauke ta fadi kasa, daidai nan kuma aka bude kofar dakin da sauri su momy suka shigo dakin, ganin halin da meemah take ciki ya dagawa momy hankali inda ta dora hannu aka tana ihu da fadin tashiga uku,

ba kiran sunan Allah bakomai sai ihu, masu aikin gidan ne suka yi tnanin dakko ruwa suka fara yayyafawa meemah saidai shiru babu alamun motsi saida suka juye mata ruwa roba biyu meemah bata farfado ba haka aka kira driver aka saka meemah a mota,

momy Babu ko dankwali haka ta shige motar suka nufi asibiti,

Suna isa aka karbi meemah aka shiga da ita special room, su momy suka zauna a reception likitoci sun dauki tsawon awa biyu suna kan meemah ba tare da ya farfado ba a cikin na'ura kadai ake ganin numfashin meemah.

Haka suka gaji aka fito da ita aka bata daki a cikin asibitn.

Gari na wayewa aka fara busa algaita ana kirari a kofar gidan sarki Bahar nan fa mafarauta suka fara fitowa.kowa tsumin sa ya tashi

Suka shiga fitowa daga gidajen su kowa cikin shiri,

Tnda Boddi ta tashi kanta yake sarawa tn tana daure wa har ta fara hawaye, tana kwance a cikin dakin ta ta fara jiyo busar da ake yi a gidan sarki Bahar da kirarin da ake wa mafarauta,

kamar an tsikare ta haka ta mike ta fara layi kamar wacce tasha ta bugu rawa take sosai akan katifar ta kafn ya fadi kamar wacce aka yar ta shiga wani irin nannauyan bacci mai dadi....

Manage please

Comment & share plz

*Macijiya ce*

Page 4

Jarumai writer's association

Katifar da take kai ce ta fara sama kamar ansa hannu ana daga ta karkashin katifar wani katon rami ne da babu wanda yasan da shi a wajan daga ciki wata katuwar macijiya ce ta fara fitowa daga ramn fara ce soll tana kyalli sai da ta gama fitowa sannan ta tsaya daidai kan boddi ta fesa mata wani bakin abu daga bakin ta nan da nan jikin boddi ya canza launi zuwa wata macijiyar golden color kallon juna sukayi suna huci suka nannade jelar su waje daya a tare suka bace,

Can cikin daji suka bayyana cikin suffar mutane masu matukar kama da juna kowacce tana haki take kallon yar uwar ta cikin bacin rai boddi tace diyanah ki fita harka ta wai Ina ruwan ki dani ne mugun kallo diyanah ta watsawa boddi tace bazan fita ba boddi mekike yi cikin su me suka miki meyasa zaki cutar da su,

Ja da baya boddi tayi tace ai gara ni ko mutm daya ban taba kashe wa kuma bana fatan kashe rai koda nan gaba Wanda ya cutar danj shi nake cutar wa Amma mutanen nan basu mn komai ba akan ne zan cutar da su ke dai tnda ba zaki jiba kije ki tta yi Amma ki fita daga wayuwa ta

Tana gama fada tayi tsalle ta fada ruwa ta shige cikin jeji itama diyanah bace wa tayi daga wajan,

Manyan mafarauta suka shigo jejin cikin shigar su ta kama macijiya sai da sukayi doguwar tafiya cikin dajin ba tare da snga koda almar kyallin maciji ba .

Suna cikin tafiya auka iske wani karamin yaro cikin dajn yana ta kuka hancin sa dk majina sai ajiyar zuciya yake sauke wa har sun wuce sai kuma shugaban su ya sawo da baya ya dubi yaron yace lafiya Ina zakaje ba magana sai wani waje me cike da duhuwa yaron yake nuna musu ba tare da shakkar komai ba suka bi bayan yaron dn ganin abnda ke faruwa .

Bishiyoyi ne masu matukar tsaho wajan Babu haske ko kadan haka suka shiga ciki yaron na gaba sna binsa a baya saida suka zo tsakiyar wajan sannan hasken dake wajan ya kara yin kasa yanda ko tafin hannu baka iya gani kafn dajin ya fara girgiza haka aka shiga hada kawunan su ana gwara su tare da azababbun maruka masu zafi.

Hankalin momy a tashe ta dauki waya ta fara neman layin dady ,

Dady dake zaune a dakin hotel shida wata kwararriyar karuwa cikin wani kazamin yanayi baisan ana Kira ba har saida aka kira sai biyar kfn ya samu damar dauka what yace Yana mikewa tsaye meemah karya ne wllh Babu Wanda ya isa ya sabauta mn yarinya nasan Wanda ke da hannu cikin wannan aikin kuma wllh bazan barshi akan meemah wllh zan iya kashe koma waye

Aa dadyn meemah karfa ka kara tafk kuskuren da muka tafka a baya momy ta fada hawaye na sintiri a kumatin ta tace nasan wannan masifun suna da alaka da

Ai bata karasa ba dady ya katse ta ta hanyar cewa king Aisha na fahimci kema yanzu ba kaunar meemah kikeyi ba to wllh zan samo me kula mn da ita .



Sake hade jelar sukayi suka kaure. Da kokawa kowacce tana kaiwa yar uwar ta duka da jelar ta a fusace diyanah tace ni ba irin ki bace boddi Ina kisa amma Wanda ya cancanci kisa nake kashewa

Macijiya ce

Page 5

Free Page ya kare

Wanda zasuyi payment suyi mn mgna

Garkuwar jarumai ce

📚Jarumai writter's association📚

Kafin momy tace wani abu tini dady ya kashe wayar sa ko kallon wacce suke tare bai yi ba ya tashi ya shige toilet wanka yayi ya fito yana goge jikin sa fuskar nan babu annuri ko kadan itama batayi gigin yi Masa magana ba saboda tasan waye alh sa'id kuma tasan iya abnda ze iya aikata wa akan meemah,

Yana gama shirya wa ya dauki keyn motar sa da wayoyin sa ya fice da kallo ta bishi tana tabe baki Yana fitowa harabar hotel din tn tafin ya karaso ya danna remote control car ta bude Yana karasowa ya shiga ya kunna ta da gudu ya fice daga hotel dn

Direct wata unguwa ya wuce yanayin unguwar kadai zaka kalla ka gane unguwa ce talakawa akofar wani karamin gida yayi perking ya fito.yana huci ya tsaya kofar gidan ya fara buga kofar kamar zai balla ta cikin

1 / 5