Author : Ameera Adam Category : Aysha Cool Novels
[23/11, 21:00] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA ƊAYA
DAULAR JABAL
Shekara Ɗari Biyu Baya (1825)
Daular Jabal ta kasance ƙasaitacciyar daula, da ke ɗauke da dubban al'umma. Sunan Jabal ya samo asali daga yawan tsaunikan da yankin yake da su, mafi yawa suna zagaye da daular bakidaya. Daular Jabal tana kewaye da tekun Farjum, wanda yake da tsofaffin tarihi mabambamta masu cike da ban tsoro zuwa almara. Yankin yana ɗauke da tarin ƙabilu, waɗanda suke da bambamcin harshe a ƙalla sama da ɗari. Kuma yanki ne da yake da tarin arziƙin noma, kiwo da kasuwanci.
Tsaunin Jaddum shi ne katafaren tsaunin da ya fi kowanne tsauni girma a Daular Jabal, kuma tsauni ne mai matuƙar tsoratarwa da munanan al'amura suke faruwa a kansa. A labarin kunne ya girmi kaka, an ce a shekarun da suka gabata. Tsaunin matattarar wata ƙabila ce ta Gussum, wasu kuma suka ce sunan ƙabilar Hadira. Waɗannan ƙabilu da ake tantama a kansu, an ce sukan yanka duk jaririya macen da aka haifa ranar Alhamis, su shayar da jininta ga abin bautarsu da ke jingine a jikin tsaunin. Da matar shugabansu ta haihu a ranar Alhamis, sai suka nemi da a yanka jaririyar. Shi kuma Shugaban ya yi tsalle ya dire a kan hakan ba za ta kasance a kan jininsa ba, kuma da yake ya fi su ƙarfin dukiya da iko sai suka haƙura. Tun daga ranar, duk wanda ya hau kan tsaunin sai dai a ga ƙoƙon kansa ya gangaro ƙasa ya faɗi, kuma ba za a sake ganin gangar jikinsa ba.
Wasu kuma suka ce, bayan da aka yi wa shugabansu haihuwar mace ranar Alhamis. Da labarin ya bayyana, bai yi sallama da kowa ba ya tattara iyalinsa da jaririyar da aka haifa suka bar garin. Tun daga wannan ranar suke fuskantar mummunan hukunci ga duk wanda ya hau kan tsaunin da sunan bauta, domin abin bauta ya yi mummunan fushi da su.
Sai dai duk yawan tarin addininan da ke cikin daular, manyan addinai uku ne suke da tasiri a cikinta. Addinin Musulumci, addinin Kiristanci da kuma addinin gargajiya.
Addinin Musulumci
Addinin Musulumci addini ne da Musulmai suke bauta wa Allah Shi kaɗai, ba tare da waninSa ba. Wanda musulmai suke bin doron koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W), wacca take ƙunshe cikin littafi mai tsarki (Alƙur'ani) da Allah (S.W.T) Ya yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) wahayi, ta hanyar Mala'ika Jibrilu. Tare da bin Hadisansa, waɗanda suke tafe da sunnar yin aiki kyakkyawa da guje wa saɓon Allah.
Addinin Kiristanci
Addinin Kiristanci, addini ne na kiristoci da suke bautar Yesu Almasihu. Wanda mabiyansa suka ce yana koyar da ƙauna, gafara da aminci. Kuma sun yi imani da an gicciye Yesu, har ya tashi daga cikin matattu bayan kwana uku sannan ya hau sama. Kiristoci suna amfani da littafin Bible, daga rubutu daban-daban a cikin harsuna kamar Ibrananci, Aramaic da Girkanci.
Addinin Gargajiya
Addinin gargajiya, addini ne da mabiyansa suke amfani da koyarwar abubuwan bauta tun daga kan iyaye da kakkanni. Sun yi imani da tsafi, bokanci, sihiri da camfe-camfe, musamman a wasu ƙayyadaddun abubuwa kamar wurare, ranaku da sauransu. Addinin gargajiya, yana da bambamci da addinin Musulumci da na kiristanci. Saboda mabiyansa suna da abubuwan bauta kala-kala, wasu sukan bautawa ruwa, wuta, dutse, gumaka, rana, bishiya, kabari da sauransu. Kuma sun yi imani da taimakon aljanu, tare da ruhin kanninsu da suka gabata. Haka zalika ba su da littafin da suka amfani da shi a wurin bauta.
Sai dai kuma a Daular Jabal an samu dubban mabiya addinan gargajiya, sun yi haɗuwar tsintsiya wurin samar da littafi guda. Wanda aka sassaƙa bangon jikinsa da fatar wata tsohuwar damisa, wanda suka ajiye sirrikan kiran aljanu da kirarinsu. A silar haka ne aka samar da kundi ukun da mabiya addininan yankin suke amfani da shi. Sai dai kuma wani al'amari da ya faru a waɗansu shekaru ya sa bayyanar Kundin ke barazana, cimma buri da jefa kokonto a zuciyoyin Sarakuna ukun da ke rayuwa a cikin Daular.
Masarautar Kajjura (Sarki Gambo)
Masarautar Judala (Sarki Giɗaɗo)
Masarautar Zulwara (Sarki Dikko)
Sune masarautu da sarakunan da ke kewaye da Daular Jabal, kowannensu yana shimfiɗa mulki cike da isa, ƙasaita da izzar mulki. Domin gabaɗaya duka sarakunan babu wanda yake ga maciji da ɗan'uwansa, ba don komai ba. Sai don wasu munanan al'amura da suka gifta a tsakaninsu a lokautan da suka shuɗe.
MASARAUTAR KAJJURA
Zaune yake a kan lallausar kujerar da ta ƙayatu da kayan alatun gidan sarauta, fadawan da ke zagaye da shi gabaɗaya kawunansu a sunkuye yake suna jiran umarninsa. Daga gefe Shamaki ne ya sake russunar da kai, har zai fara magana. Daga jikin bangon gabas, suka ga fatar zakin da ta sha ado mai ɗauke da rubutun tsafin masarauta ta dare gida biyu. Kakkaifan takobi, kuma tsafaffan da ke saƙale a jikin fatar ta fitar da kanta daga cikin gidanta. Kamar walƙiya haka ya yi tsalle ta dira a daidai maƙoshin Sarki Gambo, duk yadda ya so matsawa sai ji ya yi ya manne da jikin kujerar da yake zaune.
Da ido ya dubi fadawansa domin su kawo masa ɗauki, amma ga mamakinsa sai ya ga sun bushe da dariyar ƙeta. Yana cikin wannan yanayin ya ga farin dattijon ya ratso daga bangon da ya dare. Ya ƙaraso gabansa yana sakin murmushi, kafin Sarki Gambo ya yi wani yunƙuri tsohon ya saka wannan takobin ya datse kansa ƙasa.
Firgigit! Sarki Gambo ya tashi zaune a razane daga mummunan mafarkin da ya yi yana shafa wuyansa, gumi ya shiga keto masa cikin tashin hankali.
"Allah Ya taimake ka, Allah Ya ba ka yawan rai..."
"Fulani akwai abin da yake shirin faruwa."
Sarki Gambo ya katse matarsa cikin damuwa, ajiyar zuciya Fulani Sadiya ta sauke ta ce.
"Ina fatan wannan ya kasance tuntuɓen fahimtarka ne ranka shi daɗe."
Bai amsa mata ba, ya miƙe jiki babu ƙwari. Don haka ita ma ta miƙe fuska ɗauke da damuwa ta ce.
"Ranka shi daɗe ina za ka je a tsohon daren nan?"
"Zan je na ga Malami!"
Ya furta mata yana naɗe fuskarsa da baƙin ƙyalle, cikin shigar ɓatar da sahu. Ganin har ya je bakin ƙofa ya sa ta bi shi da sauri ta ce.
"Amma ranka shi daɗe me zai hana ka bari zuwa safiy..."
"Idan har muka kai wannan lokacin, mummunan abu zai iya faruwa da mu. Kin san Bahaushe ya ce, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe."
Ya furta yana fita, ba tare da ya waiwayo ta ba. Ta ɓoyayyar ƙofar da ke cikin ɗakin ajiyar kayan sirrinsa ya shiga, yana tafe cikin duhu yana haskawa da itacen da yake ci da wuta har ya ƙarasa. A bakin bukkarsa ya tsaya, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kutsa kansa cikin bukkar.
Kamar bai ji motsinsa ba, haka Malami ya cigaba da shafa yashin da ke kan faifan gabansa. A gefensa Sarki Gambo ya zauna, bayan da Malami ya ƙarasa sannan ya dube shi ya ce.
"Tun da na ganka da kanka ba aike ba, na san banza ba ta kai zomo kasuwa."
Sarki Gambo ya warware rawanin fuskarsa sannan ya ce.
"To ai zuwa da kai ya fi saƙo ne Malami, kuma tun da kuka gan mu yanzu ai kun san akwai gagarumar matsala."
"Ita na kwana ina duba maka, domin niyyata zuwa safiya na zo har ɗaki na same ka da maganar." Malami ya furta yana tsare Sarki Gambo da ido, cikin ƙaguwa ya ce.
"Amma me yake faruwa malami? Haka kuma muna fatan wankin hula ba zai kai mu dare ba."
"Najibullah Bn Muhammad Bn Najibullah Dogaran bulukiya!"
Jin sunan da Malami ya ambata ya sa Sarki Gambo miƙewa zumbur! Nan take jikinsa ya shiga karkarwa kamar wanda ya ji kiɗan gangi.
"A wayewar garin gobe jinin Najibullah wato Najibullah zai shigo masarautar nan, kuma idan har ba ka dakatar da shi ba shukar da ka jima da binnewa za ta bayyana. Domin zuri'arsa za ta bankaɗa maka labulen sirrin da babu wanda ya san da shi daga ni sai kai sai amintacciyarka." Malami ya ƙarasa maganar yana kallon Sarki Gambo, kamar zai yi kuka sarki ya dafa gwiwoyin Malami ya ce.
"Don girman Allah, da matsayin abin bautar da na fi aminta da ita ka taimaka mini Malami." Murmushi ya yi masa ya ce.
"Zan taimaka maka Gambo, kamar yadda na rife sirrin addinin da kake bautawa, saɓanin na Musulumci da kake yaudarar talakawanka da shi." A fili Sarki Gambo ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido, Malami ya cigaba da cewa.
"Lokacin tashin alƙiyamarka ya zo Gambo, matuƙar ba ka hallaka jinin Najibullah ba. Kuma lokacin mallakar Kundi ukunka ya bayyana, domin kuwa Za a kawo Najibullah tare da aminin kakansa tsoho Sulaimanu. Wanda a shekarun baya na ce maka duk duniya daga marigayi Najibullah, sai tsoho Sulaimanu ne suka san maɓoyar ragowar kundi biyun cikin masarautun nan.
Ɗaya dai na san yana cikin masarautar nan, amma a ina? Ban sani ba, kuma duk shaiɗanun aljanun da ke yi mini aiki ba za su iya bayyana inda suke ba..."
"Yaya kamannin Najibullah yake? Haka shi ma tsoho Sulaimanu?"
Murmushi Malami ya yi ya ce, "Amma me kake ci na baka yana zuba Gambo? Ai duk gaggawarar amarya ta bari a kai ta ɗaki."
"Sanin a bari ya huce shi ke kawo da rabon wani, ya sa nake son ka yi gaggawar warware mini zare da abawa. Domin ko babu komai za mu aika Dogarai su bincika mana inda suke."
Da yake murmushi ya zama ɗabi'arsa, a wannan karon ma murmushi Malami ya yi ya ce.
"Ka gode wa Dogaran da suke farmaki yankin Baɗiya, domin a wani ƙasurgumin dajin da tsoho Sulaimanu ya ɓoye su a can suka farmake su. Idan da hali ma ka ƙara musu matsayi, ungo wannan turaren."
Malami ya miƙa masa wani garin baƙin magani, sannan ya cigaba da cewa.
"Ka yi shelar dakatar da bayin da za a shigo da su, sannan ka saka garwashi ka turara ɗakin da za ka killace su. Wannan aikinka ne ba na bayi ba, abu biyu zuwa uku ne zai faru a wannan lokacin."
Sarki Gambo ya damƙe maganin kamar wani zai ƙwace masa, ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙosasshan ƙadangare.
"Na farko idan har jinin Najibullah yana wurin take zai fara haɓo ya bayyana kansa, daidai wurin da suke tsaye ƙasar wurin za ta yi ja kamar wuta. Har da za ka saka hannu za ta iya babbake ka, sai dai kuma na bincika Najibullah ne kaɗai ragowar jinin zuri'arsa a doron ƙasa, amma kuma zuciyata tana yi mini wasu-wasi. Yana tafe da iyalinsa mai ɗauke da tsohon ciki, ka tabbatar da ka kashe shi. Ka killace matarsa har zuwa lokacin da za ta haihu, shi ma ɗa ko 'yar da za a haifa ka kashe su..."
"Dole sai mun jira ta haihu? Me zai hana mu hallaka su lokaci ɗaya?"
Sarki Gambo ya furta a harzuƙe, Malami ya girgiza kai ya ce.
"Matarsa za ta yi mana amfani, ko ba ka san jininsa da ya gauraya da nata zai zame maka takin da kowanne manomi yake burin samu ba? Idan har ka kashe ɗan da ta haifa ka kawo mini ita nan, ragowar bayanin zan yi maka daga baya."
Godiya Sarki Gambo ya yi masa, Malami ya cigaba da karanta masa bayanin duk abin da ya dace ya yi. Sai gabannin asuba, sannan ya yi masa sallama ya koma turakarsa.
A yadda ya bar Fulani Sadiya a haka ya koma tana zaune jigum, har ya koma ya same ta ba ta koma bacci ba. Dafe kai ta ga ya yi, cike da kulawa ta dafa jikinsa ta ce.
"Tun bayan fitarka zuciyata ke ɗamfare da tarin damuwa da tashin hankali."
Sai da ya janyo ta jikinsa, sannan ya sumbaci goshinta ya ce.
"Tarin alkairai ne suke ƙwanƙwaso mana ƙofa Fulani, dangane da tsofaffin kundun da na taɓa baki labari. Sai komai ya tabbata zan sanar da ke yadda aka haihu a ragaya."
Dam! Ƙirjinta ya buga, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta.
'Na yi alƙawarin bankaɗa maka labulen kowanne irin sirrin Sarki Gambo, kada wani abu ya dame ka. Na tabbata yana yi mini kallon kitse, ina yi masa na rogo ne.'
Fulani Sadiya ta tuna kalaman da ta furta wa Sarki Giɗaɗo, a lokacin da suka yi wata ɓoyayyar tattaunawar sirri. Amma a fili sai ta saki murmushi ta ce.
"Ina tare da kai Sadaukina, haƙiƙa kai ɗin mai sa'a ne."
Sarki Gambo ya saki murmushi, jin ana ƙoƙarin shiga sallar Asuba ya sa shi fita ya ɗaura alwala ya nufi masallaci.
Asubar fari Sarki Gambo ya sanar wa da Shamaki, da a kulle duk ƙofofi huɗun da ke cikin masarautar. Sannan ya ce a tsaurara tsaro a ƙofar Yamma, domin ta nan ne ya bada umarnin idan Dogaran da suka tafi farautar bayi sun dawo za su shiga.
Har sai da rana ta fara fitowa sannan labari iso wa Mai martaba, kan dawowar babban dogari Sale. Don haka zuciyarsa fal farinciki, ya shirya cikin baƙar alkyabba mai rashin jajayen duwatsu. Daga saman kansa akwai wata hular azurfa, ya ɗaga kansa yana kallon zabgegiyar takobin da ya yi mafarkin an datse kansa da ita.
"Da ita zan datse kanka Najibullah."
Ya furta cikin izza, isa da ƙasaita. Sannan ya ɗauko ta ya saƙala a wuyansa, kai tsaye fadawa suka ba shi hanya. Nan take aka fara busa sarewa da algaita, fadawa suka shiga zabga masa kirari. Yayin da maroƙa suka fara bambaɗanci suna wasa shi tamkar babu gobe. Duk da bai furta musu koda kalma ɗaya ba, amma irin murmushin da yake yi ya sa suka fahimci yana cikin tsananin farinciki. Sai dai kuma a ɓangare ɗaya, suna mamakin wannan umarni da Sarki ya bayar. Domin ba ya daga cikin hali ko ɗabi'arsa, duba bayi a duk lokacin da aka kawo su masarauta.
Tun da aka killace su ƙirjin Najibullah yake dukan uku-uku, gumi ya shiga karyo masa. Ganin yanayin da yake ciki ya sa tsoho Sulaimanu ya girgiza masa kai, duk da hannu da ƙafafuwansu a ɗaure suke hakan bai hana ya yi masa inkiya da ya lulluɓa wa kansa mayafin jarumta ba.
"Tsoho Sulaimanu, haƙiƙa zuciyata ta gama tsinkewa. Tun da nake numfashi a doron ƙasa, ban taɓa jin yanayin da yake kassara ƙwarin gwiwar gangar jikina ba sai yau."
Tsoho Sulaimanu ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Ƙwarin gwiwarka ita za ta assasa tawa ƙwarin gwiwa Najibullah. In Shaa Allahu sai mun cimma nasara, domin Ubangiji ba ya zalinci."
"Kai kaɗai ka rage daga cikin zuri'armu Najibullah, kuma a kanka nake saka ran za ka dawo da ƙima da martabar gidanmu. Haƙiƙa a baya an riga da an ci mu da yaƙi, amma ina son na nuna wa zuri'ar jininmu ba za ta ƙare a banza ba. Don haka nake umartarka da ka yi aure a cikin kwanaki ƙalilan, domin ta haka ne za mu cigaba da yaɗuwa a doron ƙasa."
Najibullah ya tuna kalaman mahaifinsa na baya, a lokacin da yake yi masa wasiyyar bankwana. Hawaye masu ɗumi suka zubo masa, sakamakon ido biyu da ya yi da matarsa Zainaba mai ɗauke da tsohon ciki. Yana shirin yin magana, ƙaurin turaren da ke hannun Sarki Gambo ya daki hancinsa. Lokaci ɗaya ya ji kansa ya sara, daga gefen hagunsa ya ji an ce.
"Ka gafarce ni Najibullah, a wannan karon na gagara ba ka kariyar da ta dace." Juyawa dattijuwar matar ya ga ta yi, sai ta ratsa ta jikin bango ta fita tana zubar da hawaye. Lokaci ɗaya ya ji abu mai ɗumi yana fita daga hancinsa, yana sauke idonsa ya ga jini yana zuba. Ɗago idon da zai yi suka haɗa ido da sarki Gambo, da yake jifansa da murmushin ƙeta mai cike da zallar rashin imani.
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[23/11, 21:33] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA BIYU
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
🛍️Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce!
Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃
📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida
✨ Kayan ado da kyalliya
✨ Kayan mata da maza masu kwalisa
✨ Kayan kitchen masu kyau da karko
🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi!
📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! 🙏
Maza ki shiga group ɗinmu yanzu:
👉
📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari!
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
Kamar yadda ƙirjin Najibullah yake dakan lugude, haka tsoho Sulaimanu ya shiga matsanancin tashin hankali. Najibullah ya runtse idonsa cikin sarewa, da wata irin raunanniyar murya ya fara yi wa tsoho Sulaimanu magana mai kamar wasiyya.
"Haƙiƙa ajalina ya gabato tsoho Sulaimanu, don haka zan damƙa ragamar duka wannan yaƙin a hannunka, duk da a yanzu shekaru sun cimma maka. Don Allah ka kula da Zainaba idan har ka samu