QURUCIYAR JUMMAI Hausa Novels By Halimatu Sadiya Muhammad.txt

Author :  Halimatu Sadiya Muhammad Category :  Aysha Cool Novels

Chapter   1 / 22

1 to 3K   out of 64.1K words

ο»Ώ[06/01, 21:03] β€ͺ+234 812 140 7930‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*πŸ’ž

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION*πŸ“šβœπŸ»


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*GARGADI*
*wanan littafi ban yishi dan cin zarafin wata ko wani ba,suna ye,da wurare da ke cikin duk ansa ne domin ya kayatar da masu karatu*

*TUNASARWA*

*a guji juya littafin ko ta wane irin tsiga ne,domin malakin marubuciya ne*


*SADAUKARWA*

*na sadaukar da wanan littafi gare Ku iyaye na a bisa namijin kokarin da kukayi wurin tarbiyarta dani,bani illimi both western and Islamic educationa,ina alfahari daku a duk inda Nike,without u am nothing confia to who I am today.jazakallahu fil jannah*

*JINJINA*
*GARE KU*-

*MEMBERS NA AMEENCI WRITERS*

*AMEENCI FANS 3*

*WRITERS ONLY*

*WATA RAYUWAR FANS GROUP*

*COMMENT NOVEL'S*

*MY NOVEL GROUP*

*SURBAJO 4 LYFE*

*R&A KITCHEN*

*MACE KYAUTAR ALLAH GROUP*

*CHIEF'S CORNER*

*YAN MATAN HUTU NOVEL GROUP*

*ABOVE ALL ADMINS NA WATA RAYUWAR FANS;MOPOL,RUKKY,MEELAT AND LEEMA JAZAKALLAHU FIL JANNAH*

*DA SAURAN GROUP DIN DA BAN SAMU RUBUTA SUNA YENSU BA*

*ALLAH BAR ZUMUNCI AMIN*





*1-2*




Dan dazo yara ne akkala sun kai su goma,suna biye da wata yarinya wadda bara ta wuce shekaru goma ba,sai waka suke rere wa,kamar haka;

Wata ke fadin;jummai, jummai,jummala,,,,,,,

Sauran yaran na amshi,kamar haka;mai jagwalin ido ba karfi sai tonan fada.

Jummai ce ta juyo ta murguda masu baki,tana cewa dana tona,na tone June.

Wata yarinya ta amshe,jummai mai kan kwakwa,cibike mai katon cibi

Sauran suce eyeeerr mai katon cibi.

Haka suka yita mata waka har suka rakota kofar gida.

Ita ko sai shan majina take, hanunta guda na baki yana tsutsar babban yatsarta,guda na kanta tana faman Susan dumbujin sumar kanta wanda yayi jajawur saboda tsabar dirty da kasa da yara suka tula mata a wurin wasa, domin duk yadda a ka daura mata dan kwali sai ta yar dashi,haka takalmi.


Umman suce ta leqo data Ji hayaniyar yara.

Ta riqe kunen JUMMAI.
Tace me kuma kika barkato yau?

Wata bakar yarinya,gajeruwa Wanda ta fisu kiba,tace umma jan MU tayi gidan sale mai lesson, wai muje leken shi ta ramin get din gidan shi yana wanka.

Shine aka kama mu, yasamu kama kune, bayan yace mu wuce ta fara zagin shi cikin waqa.
Sale sale salele

Bakin kwarto
Salele

Amalala
Salele

Kullum sai ya shanya katifar shi
Salele

Mai gadin gidan alhaji ammany
Salele

Barawo kaji
Salele

Axxalumi
Salele.......

Shine yasa aka kamo ta ya zane ta,yasa rabe ya mata ature da kasa,muko yace mu rakata da waqa har gida.

Umma tace ya mata kyau ai, jubeta kamar mahaukaciya.
Kuje gida Alawiyyah.
Ke kuma wuce ciki kiyi wanka.

Daga murya tayi tace allawiya mu hadu gurin mai masara bakin titi....

Umma tayi mata wanka, ta wanke kan nan sosai da gaban ta Wanda yake cike da qasa.

Vaseline umma ta shafe ta dashi ta Saka mata purple riga yar kanti, sai black hulla.

Tace ci abinci kije ki tsare ma yayar ki masara ta dawo tayi sallah.

Da yake bai fi taku goma ba daga gidansu zuwa bakin titin.
Tana zuwa daga gefe ta tsaya.

Aysha ko kallon ta bata yiba tana ta aikin gasa masaran ta.

Wani yazo yace nawa nawa masarar?
Aysha tace qarami naira talatin
Babba naira hamsin.

Jummai tai caraf, karya take Mallam.
Karami naira goma
Babba Naira ashirin.

Yace ya akayi haka.
Jummai tace gidan mu daya, haka nan aka kasa mata,ita ke qara kudi Dan tsabar keta da bakin ciki,kada ya qare da wuri, ta koma tayi aikin gida...

Mutumin yace tunda haka ne bai saya.

Aysha da mamaki take kallo jummai.

Haka mutane suka yita zuwa sayan masara jummai na korar su, wasu su saya, wasu su wuce.

Aysha ido cike da hawaye tace,haba jummai menene dalilin ki nayin haka,masarar nan fa kwanar sa uku a gida ba a sai da ba,yanzu idan umma taji labari kin San bara taji dadi ba.
Tace oh yanzu ma zanyi kashin kasuwar da tushe,tunda cutar mutanee ake yi,masarar kwana uku ake sayar wa a matsayin na yau.


Tace wai me ma ya kawo ki ne?
Tace sallah akace kizo kiyi

Aysha tace shine bakyi fada min ba tun dazu?

Jummai tace yanzu ai kin sani ko?""tana zarey mata idanu.

Tashi tayi tace gashi nan sai na dawo.

Zama tayi ta budea lema ta rufe fuskar ta""wai kada a ganta tana gashin masara""
(Oh ni halima,da magrib ake shiga lema,ba ruwan sama, ba rana)

Wuta taba masarar sosai ya babake,yadda ba wanda zai saya, sai data gasa da yawa, ta kashe wutan duka.

Sai tsaki take tana duban hanya har yanzu aysha bata dawo ba

Gashi su Alawiyyah sunki fita wasa.

Can sai ga dan dazo yan wasa maza da mata, ai da gudu tabar kujerar masara ,tayi wurin su.

Tace rabe samo kwali mai karfi,salama SAMo bakar leather.

Bayan sun samo ta yayanka,ta shirya cikin ledan, yayi kamar damin kudi, sanan ta nade shi,tace alawiwi aje gefen titi.

Gefe suka koma,suna jira suga wanda zai dauka.

Aka ci sa'a kuwa sai ga sale mai lesson, yasha wanka, sai kumbo yake""as fa babban yaro""....

Wai wai gawa yayi,yaga ba mai kallon shi,ya dauka cikin style...
Jummai tace yau zaka ci ubanka a hannu na.........


*L££MA*πŸ’ž
[07/01, 14:41] β€ͺ+234 812 140 7930‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*πŸ’ž


*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION*πŸ“šβœπŸ»




*3-4*




Fuska a murtuke ta isa wurin sa,cikin daga murya tace Mallam bani kudi na daka dauka.

Yace wane kudi.
Tace na cikin bakar leather.

Yace kina haukane,ni ban san me kike fadi ba.

Tace yanzu zan nuna maka kaidin mu na mata(tau)

Rike masa riga tayi,ta aza kuka,wayyo Allah Mallam ka bani kudi na.

Mutane suka fara taruwa.
Aka tambayeta lfy?

Tace kudi ta aje saman kujera cikin Leda shine ya dauke.

Wani dattijo yace,dan samari k ba yarinya kudin ta,idan da gaskiya ka dauka.

Yace baba qazafi tayi min,ni van dauki komi ba.

Wani saurayi ya taso""da ganin sa Dan shaye shaye ne""yace walai Allah,idan baka bada kayan nan ba xan farke maka ciki"yana yi yana yamutsan fuska""

Da yake sale nada rabon shan duka,ya kafe bai San maganar kudi ba.
""Bawan Allah,a tunanen shi kudi ke cikin ledan""

Su alawiyya suka yi Dan dazo suna qara zuga wa.
Da mutane suka ga yana bata masu lokaci,duka suka fara kai mashi ta ko ina, masu mari nayi.

Ko ni ya bani tausayi.

Da yaga ana batun halaka shi,yace Ku tsaya zan fitar.

Dattijon yace Ku dakata,zai bayar.

Da jummai taga haka,ai kafa mai naci ban baka ba,taja zugarta suka sulale,sai gangaren subahana.

Ko da aka bude Leda,tulin kwalaye ne ciki.

Haba kowa sai sallati da mamaki dauke a fuskokin su.

Suna takaicin yadda Yar kankanuwar yarinya ta bata masu lokaci,tasa suka zalunci bawan Allah.

Dan shaye shayen nan yace alqur'an na kama yarinyar nan sai dai uwarta ta haifi wata.

Sai lokacin Aysha ta iso wurin, taji abunda ya faru,gashi anyi masu watsi da kayan Masara cikin kwata.

Hakuri taba sale,ta kwashi sauran kayan zuwa gida

Da umma taji lbr tace yau mai hana inba Yar banzar yarinyar nan kashi sai Allah.

Baban su yace adu'a shine kawai mafita ba duka ba.
Sai dana hana ki daurawa yaran nan talla amma atafau kin qi bari...

Ya shige dakin shi.

Suna haqi suka isa gangaren subhannah.
Tace yauwa amina yanzo wurin wayan can zamu mu hanasu hira,daga gani dan iska ne, Baku ga yana kokarin rungumeta ba,shege qaton banza,azzalumi.

Tsaya sukayi kusa da masu hiran,gashi yana son making love da yarinyar,amma shegun yaran sunqi wuce wa.

Can yace kai Ku wuce inda aka aike Ku.
Jummai tace wasa muke yi

Dole ya hakura suka canza wurin hira.

Allawiya tace sai ina zamu kuma qawali

Tace yauwa muje Satan apple, dama yau ake sauke wa.

Babban wuri ne,kamar store inda yan company ke sauke apple domin yin juice.

A hankali suka lalaba.
Rabe yace yanzu ya zamuyi MU diba kunga akwai wutar nepa.

Jummai tace na Iya kashe meter, audu daura ni saman wuyar ka.

Tace Ku matsa kusa Dana kashi kwali guda zaku sunguma.
Suka ce tau.

Duka wa audu yayi ta haye wuyar shi,ta kashe meter ai da sauri suka dau kwali guda suka sheka

Sai kwanan gidan su.

Rabawa akayi,kowa ya kwashi nashi, akayi sai da safe.

Sai lokacin jummai ta tuna da aika aikan data wa umman su.

Tsaye tayi a zauren gidansu har ta fara gyangyadi,taji an hasketa da tourch light.
Da sauri ta bude ido.

Baban su yace ke me kike yi anan?

Tace ba umma bace zata Zane ni.
Yace da kika mata laifin me?
Ta tura baki oho mata.

Yace wuce ciki ki kwanta,ni rufe gidan zan yi.
Dakinsu ta wuce ta haye gado ta kwanta,da dirty,qura da kazantar data kwaso wurin jan fada.

Da safe,umma ta tada su sukyi sallah.
Aysha ta share gidn, tayi wanke wanke,umma ta Dama masu kunnun tsami ya.
Da yake jummai bata aikin komi.

Umma tace dauki kunun ki kisha ki kama hanyar makaranta ko sisi bazan baki ba yau domin ke kika jamin asara jiya.

Tace ni dai umma ban shan kunun gaskiy ki bani kudi na sayi masa.

Tace ki mutu da yunwa.


Jakar buhunta ta dauk buuuu.
Tabar gidan.

Gidan su allawiya ta shiga da sallama.
Tace ina kwana Maman MU.

Tace lfy lau, yasu umma?
Tace lfy.

Allawiya ce zaune saman carpet na Leda tana kallon NTA.

Jummai tace kan uban can.
Yanzu ke ko shiryawa bakyi ba?

Mun fa yi lattice""duk iskncin nan na jummai tana tsoron bulala""

Tace ke ba wanka zanyi ba,bara na wanke jiki muje, domin ko tea bazan sha ba"kullum ita Maman mu tea tea""
Ni duk ya isheni.

JUMMAI tace tab ke kin ma samu har kina yan ga,gamu nan kullum kunu.
Ni vari nasha kafin k shirya.

Shanye tea tayi tas da zungureren buredin ta.

Wanke hannu da kafa allawiya ta yi,ta lafta vaseline, ta dauko yamutsatsen uniform dinta cikin kayan wanki (milk and marron colour)
Sawa tayi,ta dau littafi kwara gida bako penc,tace muje.

Maman su ta mika mata naira hamsin""gashi kudin tara inji Baban Ku""
Sanan ina jakar ki?

Tace mama yau juma'a fa komi bama yi sai wankin allo.

Tace Ku dawo lfy.


Suna tafe suna wasa.
Allawiya tace ina hijabin ki.
Tace yana cikin jakka.
Tace kin dai San halin mal.ali mai IRK,gara kisa.
Dama uniform din karamin riga ne milk colour mai guntun hannu,sai na saman marron zuwa guiwa mai hannun vest,sai karamin hijab milk.

Wani babbban get suka nufa a sama an rubuta""IBB PRIMARY SCHOOL MINNA""

ko da suka shiga an gama assembly.
Uncle poul ne bakin gate ya tara yan latti.

Jummai tace kin ga abunda kika ja mana ko?

Allawiya tace yanzu mene ne abun yi?
Jummai tace kawai mu gangara masallacin juma'a mubi layin sadakar nono da naira goma goma.

Ta zaro idanu,akwai nisa fa, yaushe zamu kai?

Jummai tace shiyasa nace mu kama hanya yanzu,koda zamu is a,a dai dan mu.

Haka suka kama hanya basu isa ba sai 12:00pm""kasan cewa akwai nisa.

Wata dattijuwa sanye da fararen uniform""daka gani Yar agaji ce""
Yace yarana idan sallah zakuyi ku shiga daga cikin massalaci,nan bakin hanya ne.

Alla wiya tace wayyo Allah jummai ga malla'akar mutuwa.

Tace dallah can bakauya,kece bakuwar zuwa nan,almajira ce fa.

Ta kalli Matar ta murguda baki, ba sallah ya kawo mu ba.


Koda aka iddar da sallah,suna gaba cikin layi,su aka fara ba sadaka,suka sake bin layi,sun amsa yakai sau uku,sanan aka gano su,ka kuresu.

Haka suka koma gida da nono cike da leda.

Kodata koma gida, baban su na kasuwa,umma kuma ta Shiga makwabtan su""gidan su allawiya""

Aysha ce zaune ta dawo daga schl,da uniform nata""white Riga, white hijab da wando blue"""(government technical schl minna kenan)

Dumamen tuwun masara da miyar busasan kubewa na jiya take faman ci.

Tace jummai kin dawo?
Da ban dawo ba raki ganni.

Uhmm ga abincin ki can a kitchen.

Yadda jakar buhun da hijabi da takalmi tayi wurn, ta shige dan madaidai cin kitchen din nasu, tana bude marfin kwanun,zazafen tuwo ta gani.

Tace lalai ma Aysha yanzu wanan ne abincin?

Tace eh.

Tace ai shinkafa ce abinci, wannan kam tuwo ne""ta karkato kwanun har miya na zuba.

Ko uniform bata cire ba,ta Saka slippers tana fita taga allawiya zaune waje tana kuka.

Tace alawiwi mai jagwalin ido,ba qarfi sai to nan fada,,,,

Waya bubuge gigin yar kan nan?

Tace ba yaya nafi'u bane,wai dun ban dawo da wuri ba shine ya zaneni.


Kin ci abinci halan?

Tace A 'a

Tashi muje gidan yan karas.

Tace ahhh bakin kasuwa nefa?

Jummai tace sai Me,haaka zamu zauna da yunwa.

Kama hanya sukyi sai gidan yan karas, saman bola suka hau sunata tsintan rubabun karas, lemu da mango.

Sai da suka cika leda,jummi tace mu biya wurn babana.

Tsalaka titi sukayi sai rumfar shi,inda yake kasa kayan koli.

Gaishehi sukayi,yace daga ina?
Jummai tace gida.

Yace barin maki cefanan.

Sugar ya saya kulin murtala,kanwa,omo, maggi sai gishri duk kullin murtΓ la.

Yace yauwa gashi,ga naira goma Ku sayi alawa,Ku duba hanya.

A hanya sukaga wasu yara na yar cabal, zama jummai tayi tace zanyi,sukace Yar cin hannu ne
Tace ta amince.

Allawiwi tausaywa yaran tayi
Sai jummai ta cilla dutsen sama tacabe, haka ta canye duwatsun ta dandaki hannun yara.

Aka mai da duwatsu yaron shima ya fara,ai tana ganin ya kusa cinye wa, ta mike tana na waqa; Allah ya hana carafke,annabi ya hana carafke,shedan yace sai anyi, nidai nace bana yi,Ku kuma kunce sai kunyi.

Hanya gida suka kama, suna shiga umma tace daga inna?

Tace naje daukan cefanai ne..


Tace badan baban Ku ya hanani bugunki ba,da sai jikin ki ya fada maki.

Allawiya je gida,kema tube uniform din kiyi wanka...

Washe gari Saturday, umma ta shirya ta,tace kada a tsaya wasa ki tafi islammiya kinga Antyn ki tun dazu ta wuce.

Tace wai Aysha.

Umma tace bana hanaki kiran ta kai tsaya ba?

Tace ah in tana sun nce mata anty tayi aure mana.

Umma tace tana jss 2 din zan mata aaure?
Ke Yar primary 6 kiyi auren mana.

Ta tura baki ai niba yar iska bace,tayi waje.

A lungu taga allawiya,tace sai ina.
Islamiyya mana
Jummai tace yanzu zuwa kayiyi da gaske.

Allawiya tace
Kin manta yadda satin can mallama hadixa takai qarar mu,mallam babba ya AIkO a kama mu?
Nidai yau zanni.

Naji yanzu tsaya mudan yi Jan fada sai mu wuce.

Kofar gidan wasu Yar bawa suka tsaya.

Iche jummai ta miqa ma Alawiyyah, yita buga gate din yanzu zan rera waqa.

Bugun gate ta fara yi
Zabiya kuwa ta fara aikin ta;

Yar bawa masu kwallo kwallo da duwawu suke tuqin tuwo,,,,,,

Babu komi cikin miyar yar bawa sai tankwa,,, ,,

Wani saurayi ya lalaba ya kama allawiya..

Dutse jummai ta kwalla mai ya sake ta da sauri.

Suka sheqa,jummai tace shegu masu fitsari a tsaye jikan oduduwa.

Zama sukayi su huta, sukaji jiniyar motar yan sanda..
Jummai tace wata sabuwa, me nene ke faruwa kuma?

Allawiya tace ke manta yaune auren Aysha babangida""diyar former president general Ibrahim badamasi babangida""

Jummai tace muje.

Alawiya tace saman tsauni nefa gidan, ta yaya ma zaa bari mu shiga

Jummai tace bakar makaryaciyar banza, gidan dake London street..
Tace walahi saman tsauni ne, inda kunada TV da kingani ana nunawa.

Tace nadai Ji,muje.

Da kyar suka hau tsaunin,security ne birjik, rike hannu sukayi suna tafia wani sojar yace"hey where are u going?

Jummai tace mamata na ciki, tana kokarin wuce wa

Yanka mata mari wani yayi.

Ihu tayi,ta zube kasa.

Allawiya ta aza hannu aka wayyo ya kashe ta ..................


















*L££MA*πŸ’ž
[07/01, 20:50] β€ͺ+234 812 140 7930‬: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*QURUCIYAR JUMMAI*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*HALIMATU SADIYA MUHAMMAD*
*L££MA*πŸ’ž

*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION*πŸ“šβœπŸ»



*5-6*


Sai jijigata allawiya keyi,amma shiru kake ji.

Sojojin kuwa basu bi ta Kansu ba.

Wata black Prado jeep ce tazo wuce wa, ganin yara biu""guda na kwance kamar matata,guda na duqe tana kuka.
Yasa motar tsayawa.

Wasu hadadun guys ne,zaune a back sit orners corner, sai driver a gaba.

""Muhammad babangida kenan da Al-ameen BABANGIDA""
Diyan general Ibrahim badamasi babangida yara masu class,masu tarbiya da sanan darajar dan Adam...

Chief security ya sheko,yace sir.

Sauke glass din akayi.

Muhammad yace"what's wrong with those children.

Cikin pijin English nashi yace;Sir they are trying to get in, when we stop them, DAT sturbon 1 get down.

Al-ameen yace "Bros let's go and see""

Fita sukayi cikin natsuwa.

Shadda ce a jikin su fari sai aikin wuta da akyi mata blue sai black shoe dake kafar su..

Muhammad yace sannu yarinya.
Alawiyyah tace uhm.

Yace meya faru ne.
Ta bashi lbr duk yadda akayi tunda ga tura su islamiyya har zuwan su wurin""da take Matsoraciya CE""

Duk suka fashe da dariya hadda securities din.

Yace dama bata da lfy ne ko tana da wani ciwo b
Ne da yakan taso mata akai ta asibiti?

""Dajin haka gaban jummai ya fadi,domin kuwa lafiyar ta kalau""

Adu'a take cikin zuciyar ta kada allawiya tayi kwaba.

Allawiya tace eh
Iskoki gareta(aljannuh)

Al-ameen yace "I think these children are putting up an act.

Muhammad yace""ya I know there is nothing wrong with that girl""

Yace sergeant SANI
Ya amsa yes sir..

Pray for her..

Karatu al-Qur'ani mai girma ya fara..
Nanauyar ajiyar zuciya tayi..
Tace ka bari,ka bari,zamu wuce,mun zo taya Ku murna ne...

Yace Ku suwaye
Tace aljannu
Har Ku NAWA?

Dubu saba'in...
Daga ina kuke..

Kasar misra...

Zaku fita ko sai na kona kuuuuuu..

Tab taya zamu zo buki mu koma gida hannu rabbanah..
Sai an bamu abinci,lemu da kayan rabo...

Shine bukatan kawai?
Ehhhhhhhhhhh

Ku fita sai a baku.

Wayau kuke mana,mun San halin ku yan Adam da saba alkawari..

Muhammad yana murmushi yace munyi alkawari zamu Baku,ku rabu da diyar mutane..

Al-ameen babu abunda yake sai dariya har da riqe ciki.....

Attishawa tayi,ta bude idanu a hankali..

Allawiya tace sammu Yar uwa..

Su muhammad suka ce Allah tsare gaba,suka koma cikin motor, driver yaja.


Manyan Jakuna guda biu aka basu mai photo amarya,shake da kayan ciye ciye..
Chief security ya daura su saman bike yace su fadi gidan su..

Alawiyyah tace anguwar kaje,wurin new market...
Har kofar gida aka sauke su..

Koda ta shiga, umma taje kasuwar kwadabe,Aysha ce a gida, tana shirin fita wurin gashin masarar ta..

Tace daga ina kike jummai?

Tace ban sanni ba,Yar sa ido..
Yanzu ke kenan kullun jan fada;baki bar kowa ba a unguwar nan?
Ba Yar bawa ba,ba hausawa ba,ba inyamurai ba ba nupawa ba.

Kullum sai an kawo qarar ki,keba ga boko ba,baga islamiyya ba,sai yawo kamar wadda taci kafar kurege..

Wane irin *QURUCIYA NE HAKA JUMMAI*?

tace eh din,ba ruwan kowa dani, lokacin naki waya San irin ta'asar da kika barkata.
Ai an ce quruciya Dan gin hauka....

Kiyi sauri nidai ki kwashi kayan wahalan ki,ki fita.

Masara kusan sati guda, yaqqi qarewa, amma dan tsabar zallunci kullum sai an gasa...
Aysha tace Allah shirye ki,ta kama gaban ta.

Zama tayi ta bude jakar,fried rice with chicken ne cikin take away,sai babban kwalin 5 alive.
Sai meo,BUK,babban calender mai photo amarya.
Tace wai su komi photo amarya,bana ango?
Was ya sani ma ko tsoho ne,mumuna..

Hankali kwance tace duk kayan nan buye su zanyi sai Monday inje makaranta dasu,in nuna ma yan class dinmu,Susan nima naje auren, hadda abincin duka zan aje cikin jakar kayana...
""Allah sarki quruciya dangin hauka""'lol


Umma ce ta dawo niki niki da kaya..

Tace yanzu ke umma dan tsabar rashin sanin abun yi da kudi,ga jibgin masara can ba ta sayar ba kin qara jibgo wani, hadda buhun danyar gyada...

Tace Mara kunyar banza rufe min baki..

Wanan masarar dafa mata zan rinka yi da rana taje talla kasuwa, wan can kuma ta rinka gasawa da dare....

Gyada kuma da yawon banzar da kike yi cikin unguwa, dafa maki zan rinka yi,kina zama bakin titi, duk gwango naira biyar...

Tace haba umma, talla fa haramun ne a musulunce""mal.babba ya fada muna..

Ai ba yawon talla zakyi ba,sanan shi m.babban uban wa ya fada mashi, ko shine zai ciyar damu ko ya biya maku kudin makaranta?


Tau ai Baban mu ya hana a daura mana talla..

Walahi dole ki min

1 / 22