Author : Abdulaziz Sani M Gini Category : Hausa Book Store
Kundin Tsatsuba 7
Littafin Yaƙi
By Abdulaziz Sani Madakin Gini
07032707179
wadanne iri'ne,? ivie ye abin takamarsu har da suka gagare ka?"
Nargaz ya ce "Wadannan mutane ma'abota wani addini ne da na jia vi masa lakabi da Musulunci. Ya kai Gulzum ka yi sani cewa a duk duniya babu wani gari a halin yanzu da zaka sami irin wadannan mutane face birnin Bahazin, wete....anan kasa kenan inda na yi bautar shekara dubu biyu. Birnin Bahazin na can tsakiyar duniya, ka san cewa daga birnin Sin zuwa can, tafiya ce ta shekara dari uku da arba in da uku bisa sadaukan aljanu kamata."
Gulzum ya ce "Kash! Ai ba don nisan tafiyar ba, da na je na ga irin wadannan hatsabiban mutane wadanda suka iya fatattakar ma'abota tsafi da karfin sihiri."
Nargaz ya ce "Hmmmm......., ai in dai kana tare da wadannan hatsabiban yaran biyu, wato Jafar da Yelisa, wata ran sai sun kai ka birnin Bahazin."
Daga wannan batu Gulzum yayi shiru bai kara cewa komai ba, suka bar hirar haka.
Al'amarin Gimbiya Sima da Waziri Kaddaru kuwa, duk hirar da ta wakana dazu tsakanin Jafar da Yelisa sun ji, lokacin da ya ce sai yayi mata rakiyar mike kafa. Lokacin da Jafar da Yelisa suka nausa cikin jeji, sai su ma suka bi bayansu. Da yake su Sima na tare da sihirin hijabin bata su Jafar ba su san cewa ana biye da su ba.
Jafar da Yelisa na tafe suna hira, inda ya ba ta labarin abin da ya faru a gidan nan na dodanni, da kuma batun Gimbiya Sima da Wazirinta Kuddaru, wadanda suka bace masa da gani ya neme su sama ko kasa ya rasa bayan ya ceci rayuwarsu.
Ko da jin wannan labari, sai Yelisa ta cika da dimbin mamaki, ta karbi Kundin Tsatsuba daga hannunsa ta yi masa kallon kurilla sannan ta ce "Lallai akwai ababan al'ajabi da yawa tattare da wannan littafi, kuma ina kyautata zaton ko su kansu manyan bokayen duniya ba su san iyakar abin da ke ciki ba. I yanzu ba ni da burin da ya fi mu samun nasarar bude littafin nan, don mu ga iya sirrin da ke cikinsa."
Ko da Yelisa ta zo nan a zancenta, sai suka ga wata guguwa ta faso waje daga karkashin kasa ta kama katantanwa da su, kafin su ankara tuni su biyun sun sume, Da karfin tsiya guguwar ta janye su izuwa cikin karkashin kasar. Take wajen ya dawo daidai kamar yadda yake a da, kai ka ce babu abin da ya faru. Wannan al'amari gaba daya ya faru ne a kan idanun Gimbiya Sima da Waziri Kaddaru.
Cikin tsanani tsoro da firgita Kaddaru ya dubi Sima ya ce "Ranki ya dade, zo mu kewaye mu bar wajen nan, kada abin da ya faru ga su Jafar ya faru garemu."
Yayin da Gimbiya Sima ta ji haka, sai ta dubi Kaddaru cikin fushi da harara ta ce "Amma ban taba sanin cewa kai butulu ba ne sai yau. Ashe ka manta da lokacin da Jafar ya ceci rayuwarmu a cikin gidan dodanni? Taimakon mai taimako wajibi ne, dole ne mu shiga inda suka shiga don mu kai musu dauki, ko da kuwa za mu rasa rayukanmu."
Kafin Kaddaru yayi wani yunkuri, tuni Sima ta kama hannunsa ta ja shi da sauri izuwa wannan wuri. Ai kuwa suna sa kafafunsu a daidai wajen, sai guguwar nan ta bullutso waje ta zuke su izuwa karkashin kasa.
Suna kwance a sume ba su farka ba sai bayan dakika dari da ashirin. Yayin da suka farfado daga dogon suman da suka yi, sai suka mike tsaye da kyar, kawai sai suka tsinci kansu a gaban wani gabjejen gunki.
Gunki ne mai siffar mutum a zaune rike da wani abu mai kama da abin saka littafi, ko dorawa a kai don karantawa. Wannan gunki na ajiye ne a tsakiyar wani katon daki mai manyan turakan gini masu tsayin gaske ga kaurin tsiya. Gaba daya yanayin ginin wajen irin tsarin mutanen Misra ne, wato irin gininsu na gado tun zamanin sarki Fir'auna.
Bayan Jafar da Yelisa sun mike a gaban wannan gunki, sai suka ga kwayar idanunsa sun kada, kuma sai bakinsa ya bude ya ce da su "Lale marhaban da Jafar bin Ruziyal, tare da Yelisa bin Jinshan. Ku yi sani cewa wannan littafi da ka ce hannunku bai dace da ku ba, da ni ya dace, saboda haka na umarce ku da ku dora shi bisa mazauninsa da ke hannuna, in ba haka ba kuwa, yanzun nan zan dandana muku azaba daga cikin irin azabobina guda dubu."
Yayin da su Jafar suka ji wannan batu, sai Jafar ya dubi wannan gunki a fusace ya ce "Kai kuma waye, har da zaka ce mu baka Kundin Tsatsuba? Alhali mun sha wahala a baya kafin mu same shi, sannan kuma ga shi yanzu ba mu san iyakar wahalar da zamu sha ba nan gaba kafin mu iya bude shi, lallai karyarka ta sha karya, idan har ka ga ka raba mu da wannan littafi, to ka tabbata ba ma iya numfashsi a doron kasa."
Ba zato sai suka ji gunkin ya bushe da mahaukaciyar dariya, har wani îrin farin hayaki ya irinka bulbulowa ta
cikin kunnuwansa. Take hayakin ya rikide ya zama igiyar karfe. Ita kuwa igiyar sai ta kanannade Jafar da Yelisa ta matse su da karfi, suka yi ta ihu saboda tsananin zafin da suka ji tamkar kasusuwan jikinsu za su rugurguje. Bayan sun galabaita, sai igiyar karfen ta sake su, a lokacin da idanuwansu sun yi jawur sun cika da kwalla, jikinsu yai laushi kamar ba su da laka.
Gunkin ya dube su ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, sannan ya ce "Na umarce ku da ku sanya Kundin Tsatsuba bisa wannan mazaunin nasa da ke gabana."
Duk wannan azaba da su Jafar suka sha ba ta sa ya saki Kundin Tsatsuba ba, har yanzu yana makale da shi a hanımata. Lokacin da gunkin nan ya ba shi umarni, sai ya mike tsaye ya taka da kyar ya je ya aza Kundin Tsatsuba a bisa wannan abu da ke gaban gunkin. Yana dora shi ya ga ya zauna daram kamar dama can sai da aka auna abin daidai da fadio Kundin tsatsuba. Faruwar hakan ke da wuya kuma sai gaba daya fitilun daki suka kama, wadanda adadinsu ya kai dubu. Gaba daya wajen ya haskake da matukar haske, yadda ko da allura ce ta fadi za a iya ganinta. Shi kuwa wannan gunki, sai ya rikide ya zama wani gajeren mutum tsoho tukuf, wanda tsayinsa bai fi rabin na waziri Kaddaru ba wato ba zai fi kamu guda ba, ko kwando aka aza masa rufo shi zai yi ruf.
Kankanin mutumin ya dubi Jafar yayi murmushi ya ce "Na ji dazu ka tambaya ko ni waye. Yanzu zan sanar da kai matsayina, da kuma dalilin zamana a wannan jejin. Da farko dai, sunana Boka Hafsil Habar. Ni mutum ne kamar ku, amma na fi aljani shaidanci. Na sami shekara hamsin ina
bauta karkashin mulkin sarki Zurkilu na birnin Mazdur. A duniya kaf babu wani sarki mai karfin sihirin tsafi kamarsa. Na fara bauta a karkashin wannan sarki a lokacin da nake shekara goma da haihuwa, bisa alkawarin zai yiwa mahaifina sarautar waziri, kuma zai raba dukiyarsa gida biyu ya ba ni rabi bayan na taimaka masa ya biya wata muhimmiyar bukata. A wannan lokaci mahaifina ya tsufa sosai, domin shekarunsa sun haura casa'in, haka, dai na dukufa kan aikin sarki Zurkilu dare da rana, ina ta kokarin ganin bukatarsa ta biya, amma ban samu nasara ba sai bayan shekara arba in da bakwai, sannan wannan bukata ta biya. Na sha wahala mai tsanani a cikin wasu dazuzzuka guda bakwai, kafin na samo abin da na tafi bida don bukatar sarki ta biya. Kai a wannan tafiya ne na yi asarar yatsun kafafuna gaba daya."
Ko da Hafsil Habar ya zo nan a zancensa, sai ya janye doguwar rigar da ke kirjinsa, su Jafar suka ga gundumin kafafuwa. Hafsil Habar ya ci gaba da cewa "Bayan na kawowa sarki Zurkuki muradinsa, sai ya cika da farin ciki ya ce na tafi gida gobe da safe na zo fada don ya cika alkawarin da ya daukar mini. Nan take na yi sallama da shi na tafi gida cikin tsananin farin ciki, ina ta sauri na je na sanar da mahaifina yadda muka yi da sarki. Ko da na isa gida sai na wuce zuwa dakin mahaifina kai tsaye. Ina shiga na tsaya kyam jikina ya hau karkarwa, idanuna suka ciko da kwalla na kama kuka. Ba komai ne ya janyo haka ba, face ganin mahaifin nawa kwance kan gado an yi masa yankan rago. Gaba daya gadon ya malale da jini. Mamaki da bakin
ciki suka rufe ni. 'Wane ne ya aikata wannan danyen aiki ga mahaifina?" Tambayar da ban san amsar ta ba kenan.
Kawai sai na juya a fusace na ruga izuwa gidana don na shiga dakin tsaifina na yi bincike na gano wanda ya kashe mahaifin nawa. Tun kafin na karasa unguwarmu na harigo gidana na cin wuta, nan fa na kurma ihu na kara-gudu. Ina zuwa na iske gawar matata da ta 'ya'yana biyu Hazirtu da 'yar'uwarsa Luswal kwance a kas, wuta ta kone su kurmus Jama'a sun yi dandazo an kewaye gidan, kowa na fadin albarkacin bakinsa. Nan fa na haukace na rinką dukan jama'a ina tambayarsu waye ya bankawa gidana wuta? Jama'a kuwa suka tarwatse aka bar ni ni kadai ina ta bambamina. Ina cikin haka ne, dakarun Sarki Zurkilu suka zo gare ni. Da zuwa suka afka mini da duka. Na yi iya kokarina akan na hallaka su da karfin tsafi, amma sai tsafina ya kusiki, saboda duk abubuwan sihirina da na ke takama da su son kone su a cikin gidana. Nan da nan dakarun nan suka yi mini lilies, har na suma, sannan suka tafi da ni zuwa kurkuku.
Ban farfado ba sai can tsakiyar dare, sa'adda a ka kwara mini ruwa. Ina bude ido na yi arba da Sarki Zurkilu tare da wadannan dakarun suna tsaye a kofar wannan daki da a ka kulle ni.
Sarki Zurkilu ya dube ni cikin murmushi sannan ya ce r'a kai wannan boka, ka sani cewa ba wani ba ne ya kashe mahaifinka ba face ni, haka kuma ni ne nasa a ka kone gidanka. Ba don komai nai haka ba, sai don sanin cewa yanzu ka kai wani babban matsayi a ilimin bokanci, domin abin da na turaka ka samo mini, ya gagari bokayen duniya
Ta
a
a
ku
gaba daya shekara da da shekaru. Idan na cika alkawarin da na daukar maka, ba shakka wata ran sai ka kashe ni ka hau karagata. Bisa wangan dalili ne na yanke wannan hukunci a kanka. Yanzu zaka ci gaba da zama a wannan kurkuku har tsawon lokacin da na gama shawarar abin da zan yi da kai."
Sa'adda Sarki Zurkilu ya zo nan a zancensa, sai takaici ya tumuke ni, ba san sa'adda na fashe da kuka ba na ce "Ya kai wannan sarki, ina sanar maka da cewa ka hanzarta halaka ni, idan kuwa ka ki, na rantse da jinin mahaifina sai na yi maka kisan gilla, kuma na karar da dukkanin ahalinka."
Ko da jin haka, sai Zurkilu ya bushe da dariya sannan ya daka mini tsawa ya ce "Kai tsohon banza! Ashe ba ka san cewa an yi sake dan zaki ya girma ba. Wannan abu da na turaka ka samo mini a daji bakwai shi ne cikar tsafina. Na rantse da girman karagata, babu wani matsafi da zai fi ni karfin sihiri a yanzu, babu wani makami da zai yi tasiri a jikina, haka kuma babu kasar da zan durfafa da yaki ban tarwatsa ta nai nasara ba."
Yana gama fadın hakan ya juya ya tafi ya na ci gaba da kyalkyala dariyar mugunta. Dakarunsa na biye da shi. Sai da na kwana uku a cikin wannan kurkuku ba ci ba sha, na galabaita iya galabaita. A wannan dare na uku ne, ina kwance magashiyan, na ji wata irin iska mai tsananin karfi ta sure ni tai sama da ni. Take saman ginin kurkukun ya dare, iskar tai waje da ni, ni dai ban sake tuna komai ba, sai gain na na yi a cikin wannan dakin da mu ke ciki yanzu. A sannan ne hankalina ya dawo. Ko da na mike zaune, sai na yi arba da wata tsohuwar aljana sanye da farin tufafi tsaye a gabana.
07032707179