MAKIRAR MACE COMPLETE BY Yellow .pdf

Author :  Yellow Category :  Hausa Ebooks

Chapter   3 / 6

6K to 9K   out of 18K words

Sai yaga an rubuta GUBURO KONDUGA,
acikin Layar, cikin mamaki Mai Dawa Sudani yaɗago kansa yaga Affan yace dashi "akwai matsala babba,
akwai buƙatar na ɗaure Dajin nan, domin wannan mutumin da sunansa yake jikin Layan nan, yana
tsakanin yankin nan". Cikin firgiji Affan yace "Kaka amma miyasa kace haka"? Mai Dawa Sudani yace
"wannan Layar aikine da akayi aka ratayawa wannan Shambuwan domin yanda zata kasance tana yawo a
duniya haka shima wannan bawan Allah zaita yawo ɓangare ɓangare na duk inda Shambuwan tabi". Jin
hakan yasa Affan yace "to yi maza kaɗaure Dajin nan, domin kar wannan mutumin yafita a Dajin nan".
Cikin gaggawa Mai Dawa Sudani yayi abinda zayyi, kawai yamiƙe tsaye yaɗan tsaya ya juya gabas da
yamma kudu da arewa, sannan yace da Affan "mubi kudu". Suka miƙa kudu tafiya sukeyi, har dare yafara
shiga sosai, amma sakamakon lokacine na farin wata, suna kallon ko ina, sai dai in wuri ya kasance
duhuwa ne kawai suke haskawa. Chan dabda ketowar alfijir, sun isa jikinki wata bishiyar tsamiya, Affan
kawai sai ji yayi tuntuɓe da ƙafar mutum. Affan yace "bismillahi", yariƙo hannun Kakansa, ya haska
touch light, sai sukaga mutum zaune a jingine da bishiyar tsamiyar. Mai Dawa Sudani ya durƙusa, yayi
bismillah, sannan yamiƙa hannunsa ya dafa kafaɗan mutumin, ya jijjigashi sosai. Sai yabuɗe idanunsa,
sakamakon ya nayinsa yanuna hankalinsa ba ɗaya bane, Mai Dawa Sudani yace dashi, "sannu", har sau
uku, batare da ya amsa ba. Wannan yasa Mai Dawa Sudani yaɗago kansa, yaga Affan yace dashi "Affanu
aiki fa yasa memu, domin wannan bawan Allah ya samu matsala ne da ta shafi hauka, sannan kuma baya
iya magana, gashi kuma tafiya dashi ya kamamu".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
10.Affan yabuɗi baki yace "Kaka anya kuwa, wannan mutum ne"? Mai Dawa Sudani yace "mutum ne
mana, mika gani yasa kace haka"? Affan yace "Kaka kaduba jikinsa fa ta ko ina duk gashi, sannan kuma ka
duba a irin Dokaddajin da muka ganshi fa". Mai Dawa Sudani yace "Affanu kenan, ai kamar yanda na
faɗamaka ne, an haɗashi da fataken Aljannu ne. Wannan dalilin yasa bazai taɓa iya zama wuri ɗaya ba,
kuma kaga da Shambuwa akayi aikin ita kuma dama bata taɓayin rayuwa acikin gari, don haka kasaki
jikinka, mucichciɓeshi kawai mutafi dashi". Jin hakan yasa Affan yace "to shikenan", suka ɗaukeshi suka
kama hanyar gida, tafiya sukeyi suna ɗan hutawa, a haka har Allah yasa chan da daddare suka iske gida,
lokacin Goggo harta fara bacci, sakamakon batayi tsammanin dawowansu a wannan ranar ba. Tana
kwance kamar a mafarki sai taji, kamar muryar Affan, wannan dalilin yasa ta taso akan shimfiɗarta ta
sanɗo a hankali taleƙa waje daga cikin bukkarta, sai ta ga Mai Dawa Sudani ne, da Affan, tare da wani
mutumi akwance. Cikin firgici tabuɗe ƙofarta, ta ce, "yau kuwa lafiya"?, taƙara dacewa "miyake faruwa
ne"? Mai Dawa Sudani yace "ki kwantar da hankalinki bakomai, wannan bawan Allah da kika gani
samunsa mukayi a jeji ba lafiya, shine yasa muka ɗaukoshi domin mutaimaka masa". Jin hakan yasa jikin
Goggo gabaɗaya ya mutu, cikin tattausan murya tace "ayya Allah sarki, to Allah ya bashi lafiya". Mai
Dawa Sudani tare da Affan duk kansu sukace "amin". Daga nan Mai Dawa Sudani ya umurci Goggo da "ta
ɗebo masa gero kaɗan ta kawomasa", batare da ɓata lokaci ba, kuwa Goggo ta shiga ɗaki ta ɗebo gero
takawo a Mai Dawa Sudani. Yakarɓa yaɗauko wani ƙoƙo yasa geron aciki ya zuba ruwa, sannan ya jefa
Laya mai ɗauke da sunan Guburo Konduga, yarufe ƙoƙon da faifayi, sannan yace da Affan "musashi cikin

ɗakinka, karka damu bazai farka ba". Affan yace "to"! Daga nan suka ɗaukeshi suka shiga dashi ɗaki,
sannan shima Mai Dawa Sudani, yafita yabar Affan da marar lafiyan tare, Affan shima ya kwanta, yaɗan
samu bacci zuwa wayewar gari. Da gari yawaye a yayinda Affan yafito, yatarar da Goggonsa da Kakansa
suna zaune, Affan ya gaishe su, bayan sungaisa, Goggonsa ta ce dashi "ya jikin bawan Allah nan"? Affan
yace "alhamdulillah", taƙara dacewa "amma nikam wannan wani irin jinya ce"? Mai Dawa Sudani yace
"asiri ne akayi masa ya hauka ce". Goggo ta ce, "innalillahi wa'inna, ilaihi raji'un"! Taƙara dacewa "mi
wasu mutane suke nema a duniyar nan ne, har suke mantawa da cewa tabbas zasu mutu suje suhaɗu da
ubanginjinsu"? Mai Dawa Sudani yace "zallan son zuciya ne kawai, shiyasa akeso mumini ko yaushe yana
roƙon Allah, akan yafi ƙarfin zuciyarsa". Goggo ta ɗanyi ajiyar zuciya, sannan ta ce, "a gaskiya dai to Allah
kasa mufi ƙarfin zuciyarmu", dukkansu suka haɗa baki sukace "amin". Bayan kwana biyu dayin haka, Mai
Dawa Sudani ya ɗauko wannan ƙoƙon da ya jiƙa geron nan aciki, ya buɗe yasa hannunsa yaciro Layar
nan, yaje ya jefata a shadda, ruwan tsarin kuwa, Mai Dawa Sudani yazo ya shafe jikin Guburo Kondiga
dashi. Yana cikin shafe jikinsa da ruwan, sai Guburo Kondiga ya buɗe idonsa, atake yadawo hayyacinsa,
yace da Mai Dawa Sudani "Malam miya kawoni nan"?
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
11.Mai Dawa Sudani yace "nan kana gidana ne, ka kwantar da hankalinka". Guburo Kondiga yabuɗi baki
yace "malam miyasa ka kawoni nan"? Mai Dawa Sudani yace "babu komai, ni sunana Mai Dawa Sudani,
iyalina sunanta Goggo, sai kuma jikana Affan da muke zaune a Dokaddaji, anan muna gabas kaɗanne da
garin Dambuwa, don haka kasaki jikinka". Guburo yaɗan jijjiga kai kaɗan, sannan yace "uhm, akwai
Allah". Daga nan Mai Dawa Sudani ya mike ya fita da ƙoƙon a hannunsa, yatadda Goggo a ɗakinta,
sannan yamiƙamata ƙoƙon tare da yimata umarnin "hatsin cikin ƙoƙon kije ki daka shi, sai ki dama ƙullin
masa dashi, kiyi masa domin akwai buƙatar wannan bawan Allah yaci. Sakamakon hakanne jikinsa zai
ƙara warwarewa tsaf, insha Allah". Cikin biyayya Goggo ta ɗan risina, tasa hannu takarɓa, sannan ta
amsa dacewa "to!" Daga nan ta wuce wurin dakan geron, batare da ɓata lokaci ba kuwa Goggo ta daka
geron, ta dama ƙulli, zuwa bayan wasu ƴan mintuna tahaɗa wuta tafara yin sakin masa, tayi ta gama tsaf,
Goggo ta ɗauki gabaɗaya masan acikin Akushi, ta kayi gaban Mai Dawa Sudani ta ajiye. Mai Dawa Sudani
ya dubi Goggo yace da ita "sannu da aiki fa", Goggo tace "yauwa sannu fa", cikin tattausan murya ta kalli
Guburo ma tace dashi "sannu", batare da yayi magana ba, kawai yakalleta yaɗan ɗaga kansa ya sauke.
Daga nan Mai Dawa Sudani yace da Guburo "maza ga masa kaɗan ci ko"? Guburo yanuna alamar "a'a",
cikin lallaɓi har Mai Dawa Sudani ya samu ya shawo kan Guburo akayi dace kuwa yaci wannan masar,
yana gama ci atake sai bacci yaɗaukeshi, wasane gaskene, ya wuni kasss, yanata shan bacci, sai chan
la'asar lisss, tukun Guburo yatashi. Wani ikon Allah sai Guburo yamike rass! Yana tambaya "wai ya akayi
naganni haka"? Mai Dawa Sudani yace "mika gani"? Guburo yace "kadubeni fa jikina duk wani iri". Mai
Dawa Sudani yace "eh, hakane kam, yanzu abinda za ayi bari akaima ruwa banɗaki sai kashiga kayi wanka
ko"? Kafin Guburo yace komai Mai Dawa Sudani, ya umarci Affan dake zaune a gefensu da yatashi yakayi
ruwan wanka a Guburo, Affan yace "to", take ya mike yaje yakayi masa, daga nan Guburo yatafi wanka.
Yashiga yaɗau tsawon lokaci yana ƙyale jinkinsa sosai, kafin ya kammala yafito a banɗakin. Anan ne
Affan yaɗauko masa kayan sawansa yabashi, Guburo ya sanyasu ajinsa, ya fito tsaf, a cikakken mutum
sosai tamkar bashiba. Saura iya gashin kansa ne kaɗai damuwar da bai aske ba, wannan yasa washagari,

da safe bayan Affan da Guburo sun karya kumallo, Affan yabuƙaci shi da Guburo zasu shiga cikin gari zai
raka Guburo ayimasa aski, Mai Dawa Sudani, tare da Goggo duk kansu suka amince. Affan suka tafi,
bayan sunje gari Guburo yayi aski, Affan yace da Guburo "muje karakani wani gida, akwai ƴar garinku ma
a gidan, domin itama ƴar Kondiga ne". Guburo yace "to muje", kaitsaye suka kama hanya basu tsaya ako
ina ba, sai a gidan Alhaji. Suka tura ƙofa sukayi sallama, sai ga Goje ya leƙo daga ɗakinsa, suna ido huɗu
da Affan yace "kaiii, wata sabon gani, yau kaine kayi ɓatan kai kenan"? Affan ya ɗanyi dariya yace
"bawani maganan ɓatan kai fa, ai dama nace muku indai muna raye wataran zanzo". Cikin shauki Goje
yace "to marabanku, sannunku da zuwa, ku ƙariso daga ciki". Affan suka shiga ya tambayi Goje "yau ina
mutumiyar ka"? Goje yace "taje gidan wannan mata Kuturwar da tataɓa bamu labarin tan nan,
sakamakon ta haɗu da jinya ga kuma tsufa, yanzu bata iya komai akanta, gashi bata da yara, wannan
dalilin yasa yanzu kullum idan gari yawaye, sai Suhaima taje gidan ta, ta wanketa, tagyara mata ɗakinta
da dai duk sauran wasu ayyukan da suka dace, tukun kafin tadawo". Jin hakan yasa Affan yace "Allah
sarki to Allah ya bata lafiya, dama yau nazo mata da ɗan garinsu ne sugaisa, amma tunda batanan,
shikenan mukam zamu tafi sai watarana kuma". Goje, yanuna lallai sutsaya yanzu Suhaima zatadawo ai,
Affan yace "a'a kaga muna sauri gaskiya, amma zamu dawo badajimawa ba insha Allah". Affan har sun
mike kenan zasu tafi, sai ga Suhaima ta shigo, tana ganin Affan tare da Guburo kawai sai ta dafe ƙirjinta ta
ce, "nashiga uku!", Guburo ma yabuɗi baki yace "innalillahi,wa'inna,ilaihi raji'un!" Kawai Guburo da
Suhaima suka rungume junan su.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
12.Duk kansu, sai suka sa kuka, cikin firgici Affan yace "Suhaima lafiya? Miye tsakaninki da wannan
bawan Allah kuma"? Suhaima tabuɗi baki ta ce, "wannan shine mahaifina, Guburo Kondiga kenan". Cikin
gaggawa Affan yace "Ha'A", sai Guburo Konduga yatari numfashin Affan yace "tabbas wannan ƴa tace
Suhaima". Jin hakan yasa Affan yace "Suhaima bana mantawa akwai wataran da kika taɓa cemana Allah
yayiwa mahaifin ki da mahaifiyarki rasuwa, tun kina ƙaramar yarinya, wannan yasa kikatashi a hannun
yadikkonki". Suhaima ta ce, "eh! Tabbas anyi haka, amma a wanchan lokacin ina da dalilina da yasa na
faɗamuku haka, amma kafin kuji dalilin zanso kuɗan bamu wuri ko da na minti biyu ne, akwai maganan
da zamuyi". Affan yabuɗi baki yace "to"! Shikuwa Goje mamaki yasa har yakasa cewa komai, ƙarshe dai
sai Affan ne yaja hannun Goje suka koma gefe. Daga nan, Suhaima tabuɗi baki ta ce, "Abba najidaɗin
ganinka acikin irin yanayin da naganka yanzu, amma a gaskiya irin maganganun da yaddikona Tasallah
taringa yimin akanka a baya sunsa nayi da nasanin zuwana duniya. Domin irina ne, ake kira da ƴaƴan da
basuyi sa'an iyaye ba". Jin hakan yasa Guburo Konduga yabuɗi baki yace "subuhanallah, Suhaima
wannan wasu irin maganganu kikaji haka a bakin Tasallah da har sukasa kike furta saɓo"? Suhaima ta ce,
"bana mantawa a shekarar da na rubuta jarabawata ta kammala karatun matakin secondry, kahaɗu da
rashin lafiya, wanda ya dangaci kwakwalwa, wanda ya haifarmin da tsananin tashin hankali. Domin kaine
kaɗai nake gani naji sanyi araina a wanchan lokacin, sakamakon nataso bansan mahaifiyata ba, wannan
yasa jinyar data sameka tasa nashiga cikin tashin hankali. Ana cikin haka har watarana kafita kabar gida.
Bayan nan kuma banƙarajin ko labarinka ba, a kullum idan ina jimamin kewarka sai Tasallah tana kuka
tanacemin, arayuwarta tayi nadamar aurenka arayuwarta, domin yanzu tasan babu wanda zai yarda
yaƙara aurenta a duniya, sakamakon zaman datayi dakai. A kullum tana faɗamin, duk abinda ya faru

dakai ya faru ne, sanadin abinda ka aikata arayuwarka, tacemin ka aikata abubuwa da dama, wanda ko
da alhakin mahaifiyata inzai bika to zaka iyayin abinda yafi haka. Har watarana nataɓa tambayarta shin,
inaso tasanar dani wani abu agame da kai da mahaifiyata? Tasallah ta cemin, kai ka kasance mutum ne,
mai rauni sosai a ɓangaren da ya shafi addini, sannan kuma kai mutum ne, mai son duniya sosai, wannan
yasa har watarana kaje wurin wani Boka ya baka fatawar cewa, in kasadu da mahaukaciya zakayi kuɗi.
Wannan dalilinne yasa, da kaje ka aiwatar da umarnin Bokan, mahaukaciyar ta ɗauki cikina, har ta
haifeni, wannan yasa da kayi hauka tacemin bakomai bane, alakin mahaifiyata ne. Jin wannan maganar
tayi mungun ɗagamin hankali, sai na tambayeta amma Yadikko ya akayi akasan cewa Guburo Kondiga,
shine mahaifina? Sai tacemin ai mai gadin Kasuwa ne yataɓa haskashi da touch light, yagane shi, sannan
kuma yabuƙaci karkowa yaji maganar, mai gadin yayi koƙarin kama bakinsa, amma bayan anhaifeki, daga
ƙarshe sai da aka haɗa da Ofishin Hisbah, sannan Babanki ya karɓeki a matsayin ƴarsa. Wannan dalilin
yasa idan nayi duba da dukiyar mahaifinki, sannan kuma natuna ta yanda akayi yasamu dukiyar sai naji
bana bukatar komai nasa arayuwata. A kullum irin makamantan maganganun nan, Tasallah ta kasance
tana yimin a gidan, har naji ni kaina natsani nacigaba da rayuwa a garin Konduga, domin gani nakeyi
kowa ganin ganga ba rufi yakemin a garin. Wannan yasa rana ɗaya nafita nabar garin bashiri, bantsaya a
ko inaba, sai anan garin Manguno, isowata ke da wuya Allah yayi haɗuwata da wata tsohuwa Kuturwa
tayimin dalilin kawoni nan gidan nafara yimusu aikatau. Tundaga wanchan lokacin da nasamu labarin
asalina, yasa naji hatta aure ya wanke min araina, domin nasan aure yana daga cikin abubuwan da zasu
sa abinciki asalina, nikuma arayuwata bani da asali, nakasance cikin irin ƴaƴan da ake Allah dawai da
iyayensu. Daga ƙarshe ina mai tabbatar maka dacewa nayi nadamar sake saka a idona Abba, ina kakai
imaninka, da har zaka biyewa zuciyarka ka aikata munanan ayyuka irin wannan, ka manta dacewa dukkan
mu mutuwa zamuyi mubar wannan duniyar"? Jin hakan yasa Guburo Konduga yaja dogon numfashi,
sannan yaɗan ɗago kasa yakalli Suhaima.
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
13.Guburo Konduga yace da Suhaima "inaso dake muɗan koma ta wajen su Affan, domin akwai buƙatar
mu zauna na baki tarihin rayuwata". Suhaimata ta ce, "to!" Suka ɗan ƙarisa suka zauna akan bencin da
Affan da Goje suke zaune. Daga nan Guburo Konduga yafara da cewa, "nidai na kasance asalin sunana
Junaidu, sannan ni asalina bufulatanin ƙasar Mali ne, daga ƙauyen mu zuwa babban birnin tarayyan
ƙasar Bamako gabaɗaya tafiyar kilomita goma ce. Sunan ƙauyen mu Kandahar, Allah ya azurta iyayena da
tarin shanu masu ɗinbin yawa, tun ina yaro bamu da wani aiki sai zuwa kiwo, har na taso nakai matashi,
anan ne aka haɗani aure da mahaifiyar mai suna, Halimatu. Wacce takasance ƴace ga ƙanwar mahaifina
mai suna Malam Musa, bana mantawa a lokacin aure na da Halimatu mahaifiyarki, mahaifina ya sayar da
shanu anyi hidima sosai, wanda mutane sukaita mamakin bikin duba da irin kuɗi da aka kashe a hidiman.
Wannan yasa bayan hidiman badajimawa ba, ƴan bindigan daji, sukazo har gidan mu suka kashemin
Babana da Umma na, na dawo a kiwo kawai sai gawawwakin su nasamu a watse a tsakar gida. Duk hakan
kuma ya farune sanadin sun gane cewa mahaifina yana da tarin dukiya, wannan yasa bayan angama
zaman makoki, kawai sai na yanke shawarin barin yankin ƙasarmu, sakamakon nasan ƴan bindigan dajin
nan zasuƙara dawo mana. Daga nan sai nayi bankwana da dukkannin ƴan uwa da abokan arziƙi, na ɗauko
Mamanki Halimatu, muka koro tarin shanun mu mukabar ƙasar Mali. Bayan munfito tafiya mukeyi muna

yada zango, har watarana muka tsanci kan mu a jihar Borno, a chan yankin ɓangaren karamar hukumar
Konduga. Wata ranar Asabat ne, wacce tazo daidai da ranar cin kasuwar Konduga, naɗauki wani ɗan
maraƙi, na nufi kasuwar shanun garin Konduga. Anan ne Allah yayi haɗuwata da Sarki Fawan garin
Konduga mai suna Haladu, wanda yakasance shine, mahaifin Tasallah. Ganin ɗan maraƙin ya birgeshi
yasa ya buƙaci siyansa amatsayin iri na kiwo, daga nan kuma yaƙara neman alfarman yanaso zai na siyan
dabban yankasa na Fawa a wurina. Yayi dace kuwa na amince, kamar wasa wannan mu'amalan da muka
ƙulla da Haladu Sarkin Fawa tasa muka ɗan nemi muhalli a garin Konduga, mukafara mu'amala da
mutane, amma sai dai afarko abinda yayita bani matsala shine, ban iya yaren hausa sosai ba lokacin. Ni
dai kawai ganin tsakaninsu kowa yana kiran kowa da Alanguburo, yasa nima kowa nagani nake kiransa da
Guburo, insun buƙaci nace Alanguburo, sai na kasa, wannan yasa tun suna min dariya har ƙarshema
kowa yafara kirana da Guburo Konduga. Sannan kuma dai kowa da Sarkin Fawa ya sanni a garin, wannan
yasa ni dashi muka zama tamkar ƴan uwa juna, lokacin kullum zan bashi bujimi ya yanka, har sai ya siyar
kafin yabani kuɗin, ita kuwa Tasallah tana budurwa a wanchan lokacin, yawanci kullum tana zuwa wurin
mahaifiyarki Halimatu suyita hira. Ana cikin haka sai watarana Allah yasa wani bawan Allah yayimin
dalilin fara kai shanun da ake yankawa a kullum a government house na jihar Borno. Sakamakon bujimin
da za asiyeshi a kasuwa million ɗaya, sukuma a gidan gwamnati suna iya siyansa millon uku, wannan yasa
lokaci guda natara tarin dukiya, na gina katafaren gida, haɗe da motoci na alfarma. Ana cikin haka sai
Allah yayiwa Sarkin Fawa mahaifin Tasallah rasuwa, sakamakon wata ƴar gajeiyar jinya da yayi, saura
Tasallah da Mamanta kaɗai, ga kuma tarin bashi da ake binsa da ya mutu yabari. A wanchan lokacin sai
nabayyana cewa duk wanda yasan yana bin marigayi Sarkin Fawa bashi to yazo yasa meni, cikin ikon
Allah kuwa da mutane sukaita zuwa duk nabiyasu kuɗinsu. Daga nan kuma mahaifiyarki Halimatu
tacemin, nayi duk wani abinda yadace, saura abu ɗaya, nabuɗi baki nace wannan wani abune haka?
Halimatu tacemin, ita yanzu kawai tanaso ne na auri Tasallah, sakamakon wallahi tausayi take bata. A
take sai naji zuciyata ta yanke, nace Halimatu, mikike faɗane kamar bakyacikin hayyacinki? Halimatu ta
ce, rass nake, kawai dai ina ganin yin hakan shine abinda yafi dacewa, domin a matakin da Tasallah take a
yanzu, tana buƙatar kulawan ɗa namiji. Sakamakon Mahaifinta yarasu, sannan ga fama da sha'anin
rayuwa da suke ciki da mahaifiyarta, duba da wannan gaskiya nake ganin komai zai iya faruwa. Daga
ƙarshe Halimatu ta durƙusa har ƙasa, tace dani Yaya nah, ina roƙonka da kadubi girman Allah, kamar
yanda ya rufamaka asiri kataimaka karufawa Tasallah da mahaifiyarta asiri ka auri Tasallah, tazo muzauna
tare. Jin hakan yasa nace da Halimatou to idan kikace haka, taya nasan zanfara bullowa lamarin

3 / 6