Author : Yellow Category : Hausa Ebooks
domin jin ta yanda akayi matashin ya samu motar?
Bayan sun koma office, DOC yabuƙaci matashin da yafara gabatar da kansa, kafin yayi bayani akan motar,
matashin ya bayyana cewa "sunanaHabu, ni mutumin jihar Yobe ne, ni asali sana'ar sai da Bulawus
nakeyi anan garin Maiduguri". DOC yace "to malam Habu yanzu dai atakaice munaso muji ya aikaiyi ka
samu wacchar motar"? Habu yabuɗi baki yace "motar Mummy nane". DOC yace "kana nufin motar
mahaifiyarka ce kenan"? Habu yace "a'a bawai mahaifiyata bace". DCO yace "to munaso musan minene
alaƙarka da ita"? Habu yace "uwar ɗakina ne". DCO yaƙara tambayarsa "taya akayi tazama uwar
ɗakinka"? Anan sai Habu yayi shiru, DOC yaƙara tambayarsa, sam yaƙi bada amsa, ƙarshe dai DCO yabar
wannan tambayar yace "to yanzu ita uwar ɗakin naka tana ina"?
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
23.Habu yace "tana Sharaton Hotel", atake DOC yabuƙaci "Habu ya bashi lambar wayar Mummynsa,
domin yana buƙatar yin magana da ita". Ba musu Habu yaɗauki lamba yabayar a DCO, ya danna kira
akayi dace kuwa tashiga, data ɗaga, DOC yayi mata sallama, da ta amsa, yace "sunana Mustafa, nine
DOC na Maiduguri Devision, akwai yaronki Habu da muka kamashi. Sakamakon yanata gudu da mota ya
kaɗe wani Ɗalibi a bakin University of Maiduguri". Jin hakan yasa ta buɗi baki ta ce "ok, to ina zuwa",
takatsar da wayar. Chan bayan wani ɗan lokaci taƙariso, wani police yayimata iso zuwa offishin DOC, ta
buɗe labule tashiga, kawai sai taga Guburo da Suhaima tare da Halimatu, wannan yasa ta ce, "nashiga
uku"! DCO yace "baiwar Allah, miya faru"? Tabuɗi baki ta ce, "ai komai ma yafaru". DOC yace da ita
"bismillah ga wuri zauna", bayan ta zauna DCO yayi mata nuni da Habu yace da ita "miye alakarki da
wannan"? Tace "ɗan ɗakina ne", tayi shiru, akayi akayi tayi magana sam taki cewa komai, wannan dalilin
yasa DCO yayi umarnin ashiga da Habu da uwar ɗakinsa Cell domin abasu jikinsu. Amma duk da haka
sukayi taurin zuciya sukaki yin bayani, har sai da akatara musu gajiya sosai, sukasha azaba, anan ne
sukace afito dasu zasuyi bayani dalla dalla. A kafito dasu aka dawo dasu offishin DOC jikinsu duk jini,
anan ne tafara bayani da farko dai "sunana Tasallah, tun farkon rayuwata na taso bani da burin da
yawuce na zama celebrity. Wannan yasa da chan a baya na kasance, mutane suke kirana da ƴar
Commissioner, sakamakon kullum bani da wani burin da yawuce naga ina more rayuwata, duba da
wannan yasa nayi yunƙurin zantafi Hausa Film chan garin kano, amma Allah yasa mahaifiyata tayi ruwa
tayi tsaki sam ta hanani. A hakan bashi ya hanani halartan duk wani Party na gayu, ko sharholiyar more
rayuwa ba in za'ayi, ina halarta ko yaushe a ɓoye batare da gida sun sani ba, sakamakon mahaifina
kullum asuban fari idan yafita Mahauta baya shigowa gida sai da yamma. Lokacin ne bayan ya kammala
gashin nama yake dawowa gida yayi wanka yaƙara fita Tukubarsa dake bakin Tashan Konduga, daga nan
kuma sai ƙafa ta ɗauke dare ya tsala sosai yake dawowa ya kwanta. Ana cikin haka Allah yayi rasuwa a
mahaifina, bayan rasuwarsa abubuwa suka fara chanjawa, na daina samun kuɗi a gida, domin kafin ya
rasu nasan inda yake ajiya anan nake ɗaukar kuɗi inya ajiye naje nayi hidindumuna. Rashin samun waɗan
nan kuɗinsa na ajiyar, da kuma rashin samun abincin da zamuci da mahaifiyata, yasa nafara risina da
abubuwan danakeyi, nakoma saka dogon hijabi, sakamakon hatta mayin bleaching ɗin danake shafawa
yadaɗe da ƙarewa kuma bani da hanyar siyan wani. Jikina duk yafara tabɓare tabɓare duk badaɗin gani,
mutanen gari sai gulmata sukeyi wai taƙaremin, jikina duk sai yayi sanyi gabaɗaya duk wargina yaƙare.
Ana cikin haka Halimatu tazo min da maganan auren mijinta, a lokacin nayi duba da irin halin dana tsinci
kaina aciki nace kawai na amince, amma har ga Allah, ni har cikin zuciyata abinda naɗauki zaman aure
araina, shine takura ne. Aka yanke ranar biki, mahaifiyata tanata murna tanajindaɗi zanyi aure, nikuma
murnan dana keyi shine, naga Guburo yana da kuɗi ina tunanin aurensa zai sa nasamu daman sheƙe
ƙayata. Bayan anyi aure, sai nafahimci gabaɗaya lissafin da nakeyi akan Guburo ba mai yiwuwa bane,
hasalima nafahimci akwai matuƙar shaƙuwa da fahimtar juna tsakaninsa da Halimatu, irin wanda shi
hankalinsa ma baya kaina tayanda har zan samu na juyashi. A wanchan lokacin natashi naje wurin wani
Boka, nabuƙaci ya rabamin Guburo da Halimatu, sannan kuma yaƙara jawomin hankalin Guburo, inaso
na mallakeshi, Bokan yacemin angama. Sannan yaƙara da cemin zaibani magani, wanda zasu rabu ko
shakka babu, kuma baya buƙatar na bashi ko naira, har sai idan naje nayi buƙatata ta biya, daga bisani
nazo na biyashi, na amince, ya ɗauka yabani. Naje na aiwatar kuwa lokaci guda Guburo yazo yayi korar
Kare a Halimatu, bayan ya koreta ta tafi, ya ɗauki ƴarsa Suhaima lokacin tana ƴar yaye yakaita gidan reno,
gida saura dagani sai Guburo, yanayimin duk abubuwan da suka kamata. Amma babbar matsalar ɗaya ce,
shine shi Guburo mutum ne mai tsoron Allah sosai, yana da tsantsani wurin addini, wannan yasa yaƙi
sakemin na fantama yanda nakeso, nabuƙaci ya koyamin mota domin ina fita idan ta kama, yaƙi duk wata
hanya da zanyi rayuwa da ƴanci na morewa, sam yaƙi amincewa da ita. Wannan yasa naƙara komawa
wurin Bokan nan, nakoka masa kan cewa, inaso yayimin duk abunda yadace akan Mijina, domin ina
buƙatar yabani wuri na shaƙi iskar ƴanci, na more sosai. Bokan yacemin to akwai buƙatar nakawo kuɗi
maƙudai, domin akwai irin aikin da za ayi da fataken Aljannu za asa suje su rataya Layar a wuyan
Shambuwa, idan har hakan ta kasance, to yana mai tabbatar min daga nan shikan zai shiga jeji, kamar
yadda Shambuwa bata rayuwa acikin gari, haka shima bazai taɓa zama a cikin gari ba. A lokacin na
tambayi Bokan to amma idan aka wayi gari, watarana yadawo fa? Sai yacemin kintaɓa ganin Shambuwa
a irin jejin da ɗan Adam yake rayuwa ne? Nace dashi a'a yacemin to kisa aranki shi kam tachan tachan
kawai namun daji ne zasu cinyeshi, ke kuma sai kiyitacin duniyarki da tsinke. Nayi dariya nace to, angama
yafaɗamin kamar nawa yake buƙata? Sai yacemin naira miliyan tara yake buƙata, anan muka rabu da
yarjejeniyar washagari zankawo masa, bayan nadawo gida naɗauki wayar Guburo nayi transfer ɗin kuɗin.
Washagari kuwa naje nacire nakai masa kamar yanda mukayi alkawari, bayan wani ɗan lokaci dayin haka
aikin yafara hawa kan Guburo, yana zaune kawai sai yayita jan tsaki yana cewa zantafi dai. Idan
natambaye shi ina kenan? Sai yacemin oh ashe fa kina jina, sai yaƙara cewa tafiyande tafiyan ne, ana
haka sai abu yafara zame masa hauka tuƙuru, wanda idan abun yatashi dakyar ake iya rikeshi, ƙarshe dai
har aka fara ɗaureshi, domin kullum yunƙurin tafiya yakeyi. Amma a duk lokacin da fataken Iskanun nan
suka tashi akansa koda anɗaureshi an kulle ɗakin sai sun ɓalle, abu dai yazame mana abun tsoro, amma
duk da haka ita Suhaima bata tsoronsa ita take masa komai, a haka har watarana yafita, daga nan bamu
ƙara samun ko labarinsa ba".
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
24."Daga nan kuma nafara lissafin taya zan raba Suhaima da gidan? Na tashi nakoma wurin wannan
Bokan sai aka samu aƙasi nasamu ya ƙaura a inda yake, wannan yasa da nadawo sai nayi amfani da
shekaruna na nuna mata girma, kullum ina cikin nuna mata kyara da tsangwama. Haka muka kasance,
har watarana itama tagaji da abinda nake mata tahaɗa kayanta ta gudu. Bayan Suhaima ta gudu, da
mahaifiyata tasamu labari sai nafahimci abun yayi matuƙar ɗagamata hankali, a yayin da nikuma burina
yacika, an wayi gari saura niɗayana a cikin daula, ganin hakan yasa naji araina zama a garin Konduga
yayimin kaɗan. Sai na yanke shawarin zan sayar da gidan na koma cikin garin Maiduguri domin nan ne
cikin birni inda zaizo daidai da rayuwata. Danaje da shawarin sayar da gidan a mahaifiyata sam sai taƙi,
ta nunamin lallai sai dai nazauna muyita addu'a har zuwa wani lokaci da zan samu miji nayi aure. Akan
haka muka samu saɓani da mahaifiyata, nabijire kawai na nemo masu siyan gida suka siya, nahaɗa kuɗi
nataho nan garin Maiduguri abuna. Da nazo ban sayi wani gida ba, kawai nafara zama a Hotel, nafara
fantamawa a Tik tok lokaci guda hotuna na suka zama viral. Ana cikin haka watarana na kayi wankin
motata car wash, ina zaune sai ga Habu na rike da Bulawus yana talle sai zagawa yakeyi, na ɗaga ido naga
Habu sosai, naji araina yabirgeni, gashi yaro ne matashi, kyakkyawa son kowa kin wanda yarasa. Wannan
yasa nakirashi, yazo yacemin Hajiya gani, nace masa, nawa nawane? Yacemin bana yanda babu, sai nace
masa a ina yake ɗauko kayan? Yacemin acikin kasuwa ne, idan yasiyar sai yaɗauki riba ya mayarda uwar
kuɗin, sannan a ƙara masa wasu kayan, jin hakan yasa na tambayeshi amma miye alaƙarsa da mai kayan?
Yacemin a gaskiya babu wata alaƙa kawai dai jiharsu ce ɗaya da mai bashi kayan, duk kansu sunzo nan ne
daga jihar Yobe. Nace masa, to a gaskiya ni ganinsa danayi naji yabani tausayi sosai, sabida haka yayi
waya da iyayensa idan har sun amince zan buɗe masa shago da zaina kasuwancinsa. Yabuɗi baki yacemin
ai Hajiya ni iyayena ko halin rike waya ma basu dashi, domin nikaina dalilin zuwana nan garin tun ina ɗan
yaro ƙarami shine almajiranci suka turoni, to ta dalilin karatun allon ne yasa dana fara girma a shiga
gidaje yin bara, nafara buga buga acikin kasuwa har Allah yayi haɗuwata da mai bani waƴannan kayan na
fara talle. Daga nan kawai sai nabashi lambar wayata, nace masa washagari yakirani, yakarɓa yacemin to,
washagarin kuwa yakirani kamar yanda mukayi dashi, daga nan nafara jan hankalinsa har nashawo kansa
ya zama Sugar Boy ɗina. Wannan dai shine abinda yafaru atakaice, amma ina mai nadama akan abinda
yafaru, Hajiya Halimatu kigafarceni dan Allah, nasani wallahi naci amanarki". Hajiya Halimatu tabuɗi baki
ta ce, "ni dai Tasallah akan abinda kikamin sai dai nace nabarki da fitowar rana da faɗuwarta, kije nabarki
da Allah". Daga nan Tasallah tasa ihu tana mai cewa "wayyo nashiga uku na, dan Allah Abban Suhaima
kayafeni". Guburo yace "Allah ya isa tsakanina dake Tasallah har abada bazantaɓa yafemiki ba". Buɗan
bakin DCO ya juya yaga Habu yace masa "kai shekarunka nawa"? Habu yace "Yallaboi shekaruna 17".
Anan ne Guburo yace "Officer kawai mudai zamu tafi, mun barta da halinta mu yanzu babu wani abunda
muke buƙata daga gareta, don haka kawai zaku iya barinsu sutafi sauran hisabi sai anje chan". Buɗan
bakin DCO yace "ina ai Tasallah tazo kenan, domin yanzu anan mun kamata da laifin aikata lalata da
ƙaramin yaron da baimallaki hankalin kansa ba a dokar ƙasa (Constitution). Don haka yanzu daga nan
zamu miƙa case ɗintane zuwa DSS Office Headquarter dake Abuja, kafin nan kuma zamusa Human
Rights
sukwata a Habu hakkinsa a wurinki a matsayinki na Sugar Mummy wacce kika ɓata masa tarbiyar da
iyayensa sukaita koƙarin ganin yasamu a makarantar Allo. Don haka daga ƙarshe ku yanzu kuna iya tafiya,
ita kuma Tasallah zamucigaba da zama dasu anan domin yanzune zamu fara case ɗin mu da ita". Alhaji
Usama yamiƙe, sannan suma sauran suka miƙe, anan suka fita a Offishing DCO suna masu godiya, ita
kuwa Tasallah sai ihu kawai take zundumawa tana tashiga ukunta itakam. Daga nan Guburo sukafita a
Police Station ɗin, domin neman taxi ɗin da zata kaisu tasha domin hawa motar garin Manguno wurin su
Goje
By Sagiryellow✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
25.Daga nan bakin Police Station ɗin suka tare taxi suka nufi tasha, bayan yakaisu tasha suka sallameshi,
anan suka ɗauki shatan mota kirar Golf 3, su huɗunsu suka shiga, driver yatada mota suka nufi Manguno.
Kai tsaye basu tsaya ako inaba, sai a ƙofar gidan Alhaji, driver yanayin horn kuwa Goje ya leƙo, da
Suhaima ta ɗaga masa hannu ta window, da yagane itace Goje yana tsalle yana murna ya buɗe gate.
Suka shiga driver yayi parking, duk kansu suka fito a motar, ganinsu yasa gabaɗaya Goje ya ruɗe tsabar
farin ciki. Sukayi dace kuwa Alhaji yana gida baifita yaje ko ina ba, wannan yasa da Goje ya shiga ya sanar
dashi zuwan su Suhaima, Alhaji yace da Goje "kace su shigo cikin gida gabaɗayansu". Goje yazo yace
dasu "Alhaji yace kushigo kawai". Suka sallami drivern sukayi bankwana dashi, sannan suka shiga cikin
gidan har chikin Parlon Alhaji. Anan suka gaggaisa, Alhaji ya umarci Goje da yashiga cikin gida yakira
Hajiya itama tazo parlo sugaisa, Goje yashiga yakirata da sauri, bayan Hajiya tazone, Suhaima tagabatadar
dasu acikin parlon. A yayinda tayi nuni da Alhaji Usama ta ce, "wannan shi Mijin Mahaifiyata ce, wannan
kuma ita ce Mahaifiyata, wannan kuma shine Mahaifina". A wurin Alhaji yabuɗi baki yace "masha Allah!"
Daga nan sai Alhaji Usama yace "dama munzo ne muyi muku godiya akan irin kulawa da kuka nunawa
Suhaima, babu abinda zamuce sai dai Allah ya biyaku, muna fata Allah yaƙara arziƙi". Duk kanninsu suka
haɗa baki sukace "amin". Suhaima ta tambaya "ina Baaba kuma"? Hajiya ta ce, "Baaba ai Allah yamata
rasuwa". Suhaima tabuɗi baki ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Sannan taƙara dacewa "to Allah
yamata rahama, muma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani". Suka buƙaci zasu tashi suwuce
Dokaddaji, anan ne sam Hajiya da Alhaji sukaƙi amincewa sutafi a ranar, suka buƙaci subari washagari sai
sutafi tare gabaɗaya. Haka dai dole suka amince suka zauna, daga nan kuma akaje aka shiryamusu abinci
kala daban daban na alfarma. Bayan sunci sun sha sosai, Suhaima da Goje kuwa ranar kwana sukayi suna
hira, sakamakon irin kewan junansu da sukayi. Wannan yasa washagari da kowa ya shirya za atafi
Dokaddaji, shima Goje yanemi alfarmar atafi dashi yanaso yaje yaga wurin dasu Affan suke. Yayi dace
kuwa Alhaji ya amince, ya ɗauka musu motarsa Siena, suka shiga duk kansu suka tafi, Guburo ne a gaban
motar, sakamakon shi kaɗaine yasan hanyar, Alhaji yana tuki Guburo yana masa kwatance a haka har
suka isa. Da suka isa sukatar Affan da Mai Dawa Sudani, da Goggo dukkansu suna zaune a gaban
bukkokinsu. Cikin mamaki dukkansu suka miƙe tsaye, sakamakon basutaɓa ganin mota tashigo inda suke
ba, kawai Affan yaga Goje yabuɗe ƙofar mota ya fito, daga nan sai ga Suhaima, tare da wasu waƴanda
baisan su ba. Kawai duk sai suka zazzauna, Goje suka ƙariso suka zazzauna a wurin, Goggo da Mai Dawa
Sudani, sukagane Guburo, cikin mamaki Goggo ta ce, "Guburo Konduga"! Guburo yace "na'am Goggo",
suka gaisa sosai, sannan suka gaisa da Mai Dawa Sudani, daga nan suka gaisa da kowa acikin su. Sannan
Guburo yagabatar musu da Alhaji Usama da Hajiya Halimatu da Suhaima, shi kuma Affan yagabatar da
Alhaji amatsayin shine babban customern san nan na cikin gari, wannan kuma itace Hajiya matarsa
kenan. Daga ƙarshe kuma yanuna Goje yace "wannan mai ƙaton kan kuma ƙauran Mata kenan, shine mai
Gadin gidan". Daga nan dai suka ɗanyi raha kaɗan, sannan suka gabatar da godiya ta musamman a Mai
Dawa Sudani akan irin hallacin dasu kayiwa Guburo, Mai Dawa Sudani yace "aiba komai kawai muyi
godiwa Allah". Daga nan Affan da Suhaima da Goje suka tashi suka koma ta chan gefe, anan ne Affan
yakece da Suhaima "amma a gaskiya nayi matuƙar tayiki murnar samun iyayenki arayuwa, kuma ashe ke
ƴar gatace Suhaima". Suhaima ta ɗanyi ajiyar zuciya kawai ta ce, "gaskiya alhamdulillah kawai zance".
Affan yace "to yanzu nidai shawarar da zan baki itace, tunda Allah yasa kin gano asalinki, to ya kamata
kifidda miji kiyi aure". Suhaima ta ce, "hmm! To ai yanzu wannan ya rage naka, domin kai kafi kowa
chanchanta kazamo mijina". Cikin gaggawa Affan ya kama baki yace "ni kuma"? Suhaima ta ce, "eh"!
Affan yace "a gaskiya aurena dake Suhaima ba mai yiwuwa bane, ba kuma dan bana sonki ba sai dan
Kakanu na. Na farko shine, su bazasu taɓa yarda natafi wani wuri na barsu ba, sakamakon tun ina jinjiri
iyayena suka rasu, dalilin wutar gobara na tashi a hannun Goggo, wannan yasa koni kaina bazan iya
rabuwa dasu anan ba. Abu na biyu shine, ke kanki bazaki iya rayuwa anan Dokaddaji ba, sakamakon
Kakana shi har yanzu ba yacin abincin da aka dafa da tukunyar ƙarfe, sai tukunyar ƙasa, sannan baya
amfani da chokali da sauran wasu abubuwa na zamani. To kinga iya wannan kaɗai yakai ace kin zaɓi miji
acikin mutanen gari, tunda kinga iyayenki mutane ne masu arziki, akwai buƙatar ace mijinki ya kasance
shima ɗan manyan mutane ne". Jin hakan yasa Suhaima ta ce, "hmm Affan kenan iya wannan shine
hujjarka"? Affan yace "eh"! Suhaima ta ce, "to kasa aranka ni nazaɓi nayi rayuwar aure da kai koda arami
kake rayuwa ba akan doron ƙasa ba, don haka ya kamata kasani ba a aure don abin duniya, ko kuma dan
wannan shi ɗan wane ne. Ana auren mutum ne don nagartarsa, don haka duk wasu cikacikai na miji
nagari kacikasu, ni na shirya aurenka ko yanzu yanzu, ina dai dai dana sanar da iyayena idan kanaga
tawajenka babu matsala". Affan yace "to, badamuwa Allah yasa mudace". Daga nan Suhaima ta tafi tabar
Affan a wurin, a daren ranar ne, ta labartawa Mamanta duk abinda akeciki, da gari ya waye kuwa,
Maman Suhaima ta zayyanewa Alhaji Usama, da Guburo duk abinda ake ciki akan lamarin Suhaima da
Affan. A take Guburo Mahaifin Suhaima yabada auren Suhaima wa Affan, sannan kuma ya buƙaci a ɗaura
auren a lokacin. Abu kamar wasa, duk kansu suka haɗu aka bada sadaki aka ɗaura auren Affan da
Suhaima abisa sadaki naira dubu ɗari lakadan ba ajalan ba. Daga nan shikenan Bukkar Affan ta zama
ɗakin amaryarsa Suhaima, anan ta tare abunta, washagari da gari yawaye, Suhaima tana mai ƙas da
kanta, cikin tattausan murya ta ce, da Affan "shikenan yau kam Allah yayi ka zamemin "My Pure Honey".
The End.
By Sagiryellow✍️08060616515.