Author : Amnoor Category : Romantic Hausa Novels
Taku har kulun
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊🐊 ta ruwa ce 🌧🌧 na Sajida
17
Ya daga hanun sa har zai wanka mata mari yaji bugun zuciyar sa ya tsananta cikin rashin kuzari ya sauke hanun sa ya zabga mata harara ya ja wani uban tsaki
Raisa da ta rufe ido tana jiran saukar mari ganin shiru ta bude idanuwan ta taga baya nan ta sauke ajiyar zuciya ta silale kasa tana tinanin irin kiyayar Irfane a gareta ita kam ta rasa mai tayi masa ta kuma sauke ajiyar zuciya ta daga kafadun ta irin bai dameta din nan ba ta mike ta shiga ciki tana shiga ta tarar da jama'ar gidan gaba daya a zaune suna tataunawa sai wasa da dariya suke
Aba Wanda ya gama kalon diramar Irfane da Raisa ya sauke ajiyar zuciya yana kokarin korar tinanin da ya darsu a zuciyar sa a wanan lokacin
Momy ta ce Elhaj ya za'ayi tafiyar nan ne?
Dady ya ce Momyn yara ku tsara tafiyar ku ni kam kasata na muradina
Hajia khadija ta ce Momyn yara kawai muyi tafiyar mu da yaran mu du kuma suyi tasu
Irfane da yake zaune yana sauraron su saï yanzu ya buda bakin sa yana cewa ana bukatar wacan yarinyar a wajen aikin ta dan ma dady ne yasa aka bata dogon lokaci haka dan haka jibi zata hau aiki
Momy ta juyo tana kalon sa baki sake ta dunkula hanu ta ce irfane amshi nan nace gidan ku wai kai mai yasa ka raina ni ne aikin ashatar ka to bazata je din ba
Dady yayi murmushi ya ce mai yayi zafi Momyn Raisa kawai kuyi tafiyar ku ke da in uwanki sai ku zaba musu idan yaso su sai mu juya Nigeria da su
Momy ta turo bakin ta Fatima ta ce lah Momyn yara ai kawai suyi tafiyar su ai yarona yayi kokari ba kadan ba kar a ma'aikata aga bai kyauta ba domin ba hutun rashin lafiya ba ta tafi
Momy ta ce ai shikenan dadin abin akoy whatsupp sai a turo musu hotunan su zabi ra'ayin su
A haka aka aje zancen su Mr president suka taso karfe daya na dare su kuwa su momy sai da safe
Nigeria Abuja
Tun da suka ISO birnin Abuja babu abinda ke hada ta da irfane sai aiki shagalinta take babu abin da ya dameta tana samun kulawar masoyinta Imran ga in uwanta in ka cire irfan da bara'atu duk sauran kamar su hadiyeta don kauna
Yau saura kana 18 auren su sai shirye shirye ake inda wajen hajiya bilkisu tana nan tana kitsa nata kalar shirin
Wanan aure KO ina ka bi labarin karasowar sa ce ake domin kuwa abu na manya sai manya
Masarauta
...........
92245338
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊🐊 ta ruwa ce🌧🌧 na Sajida
18
Anti leylatu ce zaune tana ta waya idan ta gama wanan sai wacan tayi kara kafin ta gama wata ta shigo ba komai ne takeyi ba sai bada umarnin a raraba ankon auren su Ilham domin Mr president ya fada auren yayan sa ba wanda zaya sayi anko (to fa 😳) ankon shada, leshi ne aka yi ba atamfa kai kowa ka gani labarin abin yake
An kawo lefen Raisa na gani na fada kai abin sai Wanda idanuwansa suka gane masa haka an kawo na Ilham sanan daga gidan Mr president an kai na Awatif gidan Minister Auwal JaJi
Tun da Imran ke neman auren Raisa bata taba zuwa gidan su ba domin wani lokaci har anyi shirin tafiyar ta ana gobe zata je mahaifiyar sa tayi kiran number Hajiya Khadija ta ce ba sai ta zo ba tayi zaman ta har lokaci yayi idan an kawota sa gaisa tun daga wanan lokacin wasiwasi ya darsu a zuciyoyin iyayen Raisa har ma Hajiya Sajida tayi kirafin hakan wajen Mijin su anan ya ce aa zargi babu kyau suyi zaton alkhairi koda kuwa sharin ne allah zai canza sa da alkhairi hakan kuwa akayi suka ci gaba da shirye shiryen biki inda bangarorin angwayen ma sai shiri ake
Takanas anti leylatu tayi tataki da kanta har kasar NIGER ta dauko Agaisha buzuwa domin gyaran amaren yau kwanan ta hudu tana tsuma Ilham inda Raisa har yau an kasa ritsata daga safiya tayi zata bi ta window ne ta tafi aiki bata shigowa sai sahu ya dauke da yake sun san aikin ta masu tsaron gidan basa hana ta fita KO shigowa sanan an fadawa Irfane kan ya tsawata mata ta zauna ayi gyaran jikinta girman kansa ya hana shi fadi shi fa a ganin sa aikin banza ne gardi da dan kwali
Yau sauran sati daya auren yau gobe ne za'a saka in matan a lale sai sunyi kwana shida kafin daurin aure yau kam leylatu ta dau alwashin sai ta ritsa Raisa koda kuwa aljanace ita
Tun karfe biyu na dare ta farka da sanda ta je ta murda kofar taji ta gagam a rufe ta dafa kai tace in kin san wata baki san wata ba ta fito cikin nutsuwa da yake gidan KO ina haske ne kamar rana ta kewaya ta tayar da su John ta ce maza su tashi su tsare mata hanyar da Raisa zata bi suna dariya suka ce OK madame ta juya ta koma daga cikin gidan ta zauna saman daya daga cikin dogayen kujerar robar da ke kewaye a tsakar gidan tana zama wani tinani ya fado mata ai kuwa ta mike da sauri ta je dakin Afane wajen masu rainon ta ta dauko ta yarinyar ta farka kuwa da kuka Leilatu ta kuma yin murmushin nasara ta nufi dakin Raisa da Afane Wace ke tsalara kukan an hana ta bacin ta kafin ta isa sai ga Bodyguard an fito da gudu taji kukan yar ta tana fitowa tayi turus tana kalon Lailatu wace ta dage gira tana kalon ta tace to er duniya shige muje yau kam walahi ba inda zaki haba dan allah ya za'ace auren mutun sauran kwana shida aman har yanzu mirsisi kin ki a zauna a gyaraki ke Raisa ki fita a idona na rufe toh kak tayi kwafa tana tura Raisa Wace ta karbe Afane tana turo bakinta gaba tana dan kukuni a haka har suka shige dakin Agaisha wace daman su take jira suna shiga ta tarbe su tun a wanan lokacin itama akan shiga shiryata ci wanan sha wanan shiga wanan ruwan shiga wancan ana fadan da ita ana komai
Yau sauran kwana biyu a daura aure idan kaga garin Abuja kamar ana shirin wata babar sallah kowa ka gani yana shirin wanan rana an ninninka matakan tsaro ta ko'ina
Masarauta
Shirye shirye kam ana shan sa domin auran da daya cilo ne Imran tun safe yake lalaba mahaifiyar sa ta barshi ya tafi Abuja har a daura aure sai ya dawo domin a can za'ayi dîner kwaya daya tak wace aka sha fama da Irfane kafin ya yarda ayi ta shima ranar daurin aure za'ayi ta
Wanan abin ya kular da Hajiya bilkissu yayi mata ciwo ba kadan ba har ma ta kulaci wanan aure a ranta da kyar ta yarje masa ya shirya yana rawar jiki ya tafi garin Abuja inda shima ya sauka a gidan Mr president aman har yanzu bai saka sahibarsa a idanun sa ba
Awatif da gayar ta (oh ikon allah su awatif dadi miji baza'ayi hakuri har a kawoki ba?) baki na nesa da na kusa sun halarta a gidan Mr president wasu sun zo don an gayace su wasu kuwa sun gayaci kansu
Yau kwana uku Kenan Raisa na mumunan mafarki yanzu haka cikin ruwan tirare mai dumi ne aka ce ta shiga ta zauna tana zama dadin kanshin nan ya saka baci yayi awon gaba da ita tayi mafarkin ana gyaura mata mari wani irin zabura tayi Agaisha ta leko ta ganta tayi wiki wiki kamar ka saka tsaka a gwongwani kayi ta juyawa ta ce yata lafiya?
Raisa tayi hajiyar zuciya ganin mafarkine tayi ta mike tana fadin ta koshi da ruwan zafin kamar wace ta sha
Mai zanen lale aka dauko da masu gyaran gashi aka fara zana musu lale bayan an gama aka yi musu jikon kai da lale kai amaren nan na shan gyara masha allah
Tun da garin allah ya waye ake saukar kur'ani ana ta zikiri har rana ta fada inda gaba daya ake ta shagulgula gida kai ya cika kai ba gida kadai ba garin gaba daya ma ya cika
Ranar daurin aure
😜😜😜92245338😜😜😜
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊🐊ta ruwa ce🌧🌧 na SajiDa
19
RANAR DAURIN AURE
Yau ta kama 2017 yau ta kama ranar farin ciki ga iyalan angwayen da amaren ta kasance ranar fargaba da amaren sai dai kuma abin mamaki fargabar har a wajen Fatima domin tun da garin allah ya waye take jin ta gatanan dai kamar bata da laka haka Hajiya Sajida suna dai tafe ne
Kowa ka gani fara'a ce a fuskar sa bayan salar azahar za'a daura aure
Daurin aure
Karfe biyu da minti ashirin bayan an gama sallah limamin baban masalacin ne zaune da sarki Abdul Rahaman da Mr president , da Auwal JAJI da banban malamin Adini kuma banban likita Malan Saidu mahaifin Samir da manmanyan masu fada a ji na kasar Nigeria da Niger
Liman yayi gyaran murya aka fara daurin aure
Irfane Muhammad Ibrahim Da Awatif Auwal Jaji bisa sadaki naira dubu hamsin
Imran Abdul Rahaman Da Raisa Buraima bisa sadaki naira hamsin
Samir Saidu da Ilham Muhammad Ibrahim bisa sadaki naira hamsin domin samun albarkar aure ana gama daurin aure aka kwashi kabara inda aka shiga gaigaisawa da jama'ar wajen ana ta barka
Imran Wanda masasara ta zubo masa ya zago wayar sa yana hamdala ya rubutawa Raisa an daura
Tsaye take tana famar jona wayar ta message din ya shigo tana karantawa ta shirishiri ta buga ihu tana tsale da gudu iyayen su dake kuryar daki suna zantawa da Ilham da mai gyaran su suka fito suna tambayar ta lafiya? Ai kuwa ta dage ta shiga kwasar shokiiiii gaba daya suka yi wangalau da baki suna kalon ta
Fatima ta matso ta ce idan baki fada mana abin da yake faruwa ba zan saba miki
Cikin sauri ta ce Ma an daura
Fatima ta zaro ido tana an daura me 😳😳
Raisa ta ce auren mana
Gaba daya suka kwashi dikira da salamcewa suna ooooo hasbunalahu wani'imar wakim Fatima ta ce Anti Raisa Wace irin amaryace wanan yarinyar? Momy ta juya ga Agaisha ta ce agaisha yata wace irin amarya ce? Agaisha tayi murmushi da gurbataciyar hausar ta ta ce amaryan zamani ne
Fatima ta girgiza kai tana fadin amaryar mahauta dai
Raisa ta turo baki an ce mata mahaukaciya Ilham ta bushe da dariya tayi ciki Raisa ta bita
Haka iyayen suka wuni ana ta shagulgula ado kai sai shan sa ake
Bayan salar isha'i tun da sukayi sallah aka saka suyi wanka aka shiga shiga shirya su simple make up akayi musu domin Hajiya Sajida ta hana a cika musu fuska da digedige masu gyaran gashi nayi masu gyaran farce nayi masu gyaran kafa nayi kanshi sai tashi yake
Har an fara kwasar mutane ana yin wajen dîner da su yanzu haka amare da angwaye ne kadai basu halarci wajen ba
A hankali suke saukowa daga sama suna taku cikin nutsuwa angwayen dake zaune a kasa duka suka daga kansu suna kalon amaren su banda irfane wanda kansa ke kalon wayar sa mazan sun sha dakakiyar shada fara kal anyi musu irin dinkin nan na larabawa a kasar makkah aka dinko musu domin wanan ranar sun sha hula da agogo na gold masha allah kawai nake fadi a raina da na kalo irfan wanan shi ake kira tauraro inda amaren suka sha wani uban matériel fari mai haske da duwatsu kanana ash sai sarkokin su na zinari da awarwaro da zobuna sai haskawa suke
Hanu Imran ya mika Raisa ta saka nata a ciki ta idasa saukowa ya kura mata ido gabansa sai faduwa yake gyaran muryar Awatif ya maido sa daga tinanin sa ya dan matsa mata hanya ta huce tana zuwa ta zube jikin Irfan saï a lokacin ya juyo yana kalon ta ya lumshe idanuwansa ya mikar da ita suka fito gaba dayan su suka nufi wajen da aka tanadi motar da zata kai su hotel din
Sojoji ne kewaye da motar suna fitowa suka shiga sara musu Irfane da Raisa kawai suma suka kame ikon allah sai kalo sai da suka gama kamewar sanan aka bude musu suka shige motar sanan suka saka motar amaren a tsakiya har suka isa wakar Céline Dion ne ke tashi a motar gaba dayansu sun nutsu kowa da irin tinanin da yake suna isowa aka bude musu motar ana watsa musu pulawa da tirare mai kanshi kowane ya kama hanun matar sa suna dan murmushi masu camera sai watsa musu hotuna suke masu vidio suna ta dauka a haka kowa ya kama wajen zaman sa
Bayan an bude taro da adu'a an yi jawabai na abokanan angwaye da kawayen amare manya manyan mawakan hausa sun halarci wanan taro an fara cashewa Naziru m Ahmed ya shigo ya gama nashi wakar an sha rawa yanzu fati niger ce zata wake amare
Cikin nutsuwa suka mike suna shiga rawa cikin jagorancin Anti lailatu da su Farida daidai wanan lokacin wayar Imran ta shiga ruri tana neman agaji inda take bugu daidai da bugun zuciyar sa ya zaro ta ya duba sunan mahaifiyar sa ya gani gaban sa ya kuma yankewa ya fadi hanun sa na karkarwa ya daga ya kara a kunansa tare da yin salama cikin daga murya ta ce IMRAN ina mai umartar ka da Ka SaKi RAISA a yanzu Saki uku idan ba haka ba Allah ya tsine maka cikin ihu ya ce Mama dan soyayar ki da fiyayen halita kar ki tsine min kowa yayi cak ya tsaya inda hankali ya dawo kansa tini ya jike da zufa hawaye wani na bin wani Raisa cikin sasarfa ta ka
[3/7 07:56] ~Ni ce Amnoor✍🏽: Duk karyar kada🐊🐊ta ruwa ce🌧🌧 na Sajida
21
Bayan an gama daurin auren suka fito aka kirayi Momy a waya aka sanar mata Momy ta shiga wage baki ita kadai sai murmushi take Fatima wace ta farka tana kalon momy murya a raunane ta ce Anti ta farka?
Momy ta kura mata ido a ranta tana fadin lale soyayar uwa da da sai allah duk irin kawaicin Fatima yau kam tana tambayar Raisa tayi murmushi ta ce albishirinki sisita
Fatima ta ce goro fari kal
Momy ta matsa jikin kunan ta tayi mata rada (duk iya yanda na so na ji mai aka ce ya gagara ) sai gani nayi Fatima na zaro ido tana tafa hanayenta tana fadin gaskiya ba'ayiwa yata adalciba taya za'a hadata da Raisa yarinyar ba tsari ba komai anti? Hajiya Sajida ta watsa mata harara daidai lokacin Irfan ya shigo ganin Fatima ta farka ya isa gareta da sauri yana fadin Ma yana ta zabga murmushi ta mika hanun ta ta kamo nasa daya miko mata suka damke suna ta aikin murmushi a hankali ya furta Ma kin tsoratar da ni saboda wanan yarinyar ta saka jinin Mata ya hau sai na babalata
Ma tayi murmushi tana shafa kansa a hankali ta ce i'm sorry son i'm sorry
Docter Mariama ce ta fito daga dakin da aka rike Raisa tana sharar zufa wasu nurse suna biye da ita su momy suka fito domin dakin yana kalon dakin da aka saka Fatima
Ilham wace taci kukan ta ta godewa allah ita ta fara tarar Docter Mariama tana fadin Docter ta farka?
Irfan ya gala mata harara tayi Sauri ta tsuke bakinta
Dicter Mariama ta fara bayani: alhamdulilah ta farka sanan munyi mata alurar barci sai dai don allah a kiyaye kar a rika tayar mata da hankali domin jininta yayi mugun hawa sanadiyar faduwar da gaban ta yayi har yanzu bugun zuciyarta bai daidaita ba aman zai zama normal a hankali
Hajiya Sajida ta ce OK thanks docter
Docter Mariama ta ce thanks Madame tayi gaba
Irfan ya kali Momy ya ce Momy yar ki Soldier ce sanan Bodyguard wanan dan abin bai dace ya tayar mata da hankali ba ni dai tayi ta farka ta dauki Afane tana can sai kuka take wai ita Mamar ta idan Mamar tata ta tafi gidan mijinta naga yanda za'ayi domin bai gidan katon da za'aje min da yarinyata ai da gangan ta shaku da yarinyata
Momy tayi wangala da baki tana sauraran sa har ta bude baki zatayi masa fada sai kuma wani abu a ranta ya ce mata ki lalabasa Sajida,
Momy ta ce haba dan Ma ya zaka rika fadar haka idan Ma ta ji shin zataji dadi ne? Ka ringa dagawa Raisa kafa KO don soyayar da Ma ke yi maka tayi gaba abinta
Wanan abin ya mugun bawa Irfan mamaki da momy bata zage shi ba bayan ya taba yar gaban goshin ta ya daga kafadun sa ya ce may be rashin lafiyar yar tata ce itama ya saka mata rashin lafiya a haka ya juya tayi gida
Awatif ce da kawar ta titi suna zaune sai