Chapter 31 Reading GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt Arewa Novels

GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

Author :  Ummu Nasmah Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   31 / 32

90K to 93K   out of 93.6K words

kiran yayi yana durƙushewa a wajen ya saki kuka mai sauti Shetima ne ya sunkuya tare da dafa kafaɗarsa ya hau masa nasiha da bada baki, kafin ya samu yayi shuru, cikin sanyin jiki yabar airport ɗin bai doshi gidan sa ba, gidan su yayi a falo ya samu Momy zaune kan kenan da aka bata Daddy shima na zaune cikin kujera, kusa da Daddy ya zauna tare da sakin kuka yana cewa.


" Daddy Safreena ta mutu, hatsarin jirgin nan ya ritsa da ita Ta mutu Daddy Abdul ya rasa mahaifiya."

Ga baki daya falon salati ya ɗauka Daddy ne yace.


" Subahanallah!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahu Akbar, oh rai baƙon duniya, Allah ya jiƙanta da rahama dama haka rayuwa ta gada, mutu tana sarƙe da kowa wanda kwanansa ya ƙare sai tafiya, Allah yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da imani ita kuma Allah yasa ta huta, dama kuma jiya Zarah da Khalil sunzo sun roƙeni alfarmar cewa ka basu kyautar Abdul su riƙesa matsayin ɗansu na cikin su tunda su Allah bai azurtasu da haihuwa ba, Kuma na yanke shawarar cewa na basa, gobe in Allah ya kaimu zamuje mu yiwa Alh giɗaɗon ta'aziyya idan yaso in an kwana biyu sai naje da kaina na sameshi da zancen Abdul ɗin."


Kansa ya Garkuwa ya kaɗa tare da runtse idanunsa yana jin zafin mutuwar Safreena a zuciyarsa, ita kanta Momy ko da bata san Safreena ba, sai da taji mutuwar, ya juma sosai a gidan kafin ya shige gidan su Safreena suna zaune suma zugun zugun masu kuka nayi sosai ya tausayawa Zee yanda duk ta fita a hayyacinta tana maƙale da Abdul, Alh giɗaɗo ya gaisar tare da masa ta'aziyya ya juma a gidan har akayi sallar magaruba sannan ya koma gidan sa, ko da ya sanar da Jummo sosai hankalinta ya tashi, daƙyar cikin sigar rarrashi ya samu hankalin Jummo ya kwanta.


Washegari kuwa, aka iso da gawarwakin su Safreena Nigeria Birnin tarayya wato Abuja Alh giɗaɗo shida abokinsa Alh Kabeer, sai Ya Garkuwa sukaje babu wanda ya iya gane gawar ɗan uwansa domin kuwa duk sun babbake, haka dole aka haɗasu aka musu a can, aka binnesu, sunsha kuka sosai tare da baƙin cikin rashin gane gawar Safreena wannan yafi ci musu rai


Ranar da suka cika kwana uku da rasuwa Ya khalil da Daddy sukaje suka musu ta'aziyya, a nan ne Daddy yake sanar da Alh giɗaɗo zancen ɗaukar Abdul, haka babu musu ya amince musu, sanin cewa a duniya Abdul bashi da gatan daya wuce su dangin mahaifinsa, Zee Sosai taci kukan rashin Safreena da karɓe Abdul da akayi sai dai babu yanda ta iya dole ya zamo tayi hakuri Jummo ma taje ta yiwa Zee ta'aziyya tare da jajanta mata mutuwar Safreena, Jummo bata so aka raba Abdul da Zee ba.

Ko da Daddy suka dawo da Abdul gidan, Zarah sosai taji daɗi tare da amsarta zuciyarta tana sanar da ita itama yanzu ta samu yaro, Momy sanda taga Abdul sosai ya shiga ranta, babu ƙyama ta rungumesa, haka rayuwa ta tafi cikin jin daɗi a cikin wata ɗaya Abdul yayi mungun shaƙuwaa da Aunty Zarah da Ya khalil da kuma Momy, Zizah ne dai baya yadda da ita kasancewar bata cika masa wasa ko ɗaukarsa ba.


Misalin ƙarfe Uku na dare wani irin mungun ciwon ciki ya turniƙe Jummo Ga baya da mararta tamkar zai tsage, wani irin azaba takeji wanda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin wannan azabar ba, ji take tamkar rayuwarta ne yazo ƙarshe, bakinta ta cije goshin ta ya tsattsafo da gumin azaba, Ya Garkuwa dake baccinsa hankali kwance ta riƙesa tana ambaton.

" La'iha'illahu Muhammadur Rasulullah!!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!"

Sai kuma ta saki kuka jin kamar motsin mutum jikinsa ya saahi buɗe idanunsa a hankali, idanunsa ya zuba a kanta sai kuma ya miƙe a firgice yana rikota tare da cewa.

" Subahanallah!!! Jummo kaddai haihuwar ce?"

Ina itakam Jummo bata da bakin Magana saboda munguwar azabar da take ji, ga haihuwar tazo mata da ciwon baya, wanda yafi wahalar wa, ai kuwa babu shiri ya Garkuwa ya miƙe jallabiyarsa ya saka da sauri ya ɗauki key ɗin motar sa ya fito mai gadi ya samu tare da ce masa ya buɗe masa get, sannan ya koma ciki, Jummo ya kamo suka fito suka shiga mota, cikin gaggawa yake tuƙin Asibitin Doctor Sirajo suka je, cikin gaggawa aka shiga da Jummo ɗakin haihuwa tare da cewa Ya Garkuwa ya koma ya kawo musu kayan haihuwa da fallen zani, komawa cikin tashin hankali ya ɗauko ya kawo, tunda Jummo ta shiga cikin room ɗin hankalin Ya Garkuwa bai kwanta ba, har kiran sallar asuba ta farko Jummo bata haihu ba, sanda aka fito Sallah sannan ya kira Aunty Zarah yake sanar da ita yana asibiti Jummo zata haihu, Aunty Zarah tana idar da Sallah itama tazo ta, shuru shuru Jummo bata haihu ba sai da gari ya waye 7:30am Allah ya sauƙeta lafiya ta samu santalelen ɗanta fari tas kyakkyawa, koda aka sanar dasu ya Garkuwa haihuwar sosai sukayi farin ciki, Ya Garkuwa ne yace.


" Doctor ina mahaifiyar Yaron, tana lafiya dai ko DOCTOR."?

Murmushi doctor ya saki tare da cewa.


" Tana lafiya bata da wata matsala, taɗan samu ƙari kaɗan mun mata ɗinki, so tana ɗakin hutu ma da jaririn zaku iya shiga ku gansu."

Ai kuwa cikin farin ciki suka shiga room ɗin tana kwance tana bacci Babyn kuma an lulluɓesa da towel, Ya Garkuwa cike da farin ciki ya ɗago yaron numfashi ya sauƙe tare da mannasa a ƙirjinsa, kunnen sa ya kama ya masa kiran Sallah, tare da saka hanunsa a cikin aljihun sa, dabino ya tauna tare da sawa yaron a bakinsa, ya ɗiga masa zam zam, Aunty Zarah sai tsiya take masa, ganin suna cikin ƙoshin lafiya ya sashi komawa gida yayi wanka ya samu nutsuwa sannan yayi gidan Momy yake sanar da ita Jummo ta haihu murna Momy tayi tare da musu addu'a domin bata da ƙafar zuwa asibitin, cewa tayi yaje kitchen akwai ruwan zafi a plast da kayan shayi ya kai musu asibiti tare da ce masa idan an basu sallama su taho da Jummo nan Gidanta, cikin farin ciki ya amsa da to zuwa yayi ya ɗauka ya koma asibitin, ya samu jummo harta farka tana bawa jaririn nono, gefenta Ya zauna cikin murmushi yace.


" Oh yarinya ta girma."

Murmushi Jummo tayi tare da ɗago idanunta ta kalli Ya Garkuwa, cirewa Yaron nono tayi ta miƙa masa ya saka hanu ya karɓe sa, tace.


" Ka kira su INNO ne ka faɗa musu haihuwar."?


" Ban kirasu ba, na dai gwada numbern Baffa bata tafiya amma zuwa anjuma maybe ya tafi ko matsalar network ne."

Aunty Zarah ce tace.

" Ai kuwa ya kamata su sani likitan ma yace tunda bata da wata matsala za'a iya Sallamar mu zuwa anjuma."


" Okay Momy tace gida zaku koma idan an sallame ta."

Da to Aunty Zarah ta amsa, da yamma lis kuma aka sallamesu suka koma gidan Momy, Abdul sai murna yake yaga jariri, Daddy ma ya shigo ya duba jikan nasa, ko da Ya Garkuwa ya sanar da Baffa haihuwar Jummo, Sikayel da kanta tazo ta zauna mata.


Kwanan Jummo Uku da haihuwa yayin da jaririnta yayi kyau kamar yayi sati biyu, a ranar ne kuma aka kawo kuɗin Auren Zizah, wani ɗan Kano ne zai aureta wanda suka haɗu a facebook.


Meenat tun ranta suka sami saɓani da Momy bata kuma zuwa gidan ba, sai yau ta kira Jummo a waya kamar bazata ɗaga ba, sai kuma ta ɗaga muryar Jummo a daƙile ta amsa sallamar meenat, meenat daga can cikin sanyin murya tace.

" Ƙawata har yanzu fushi kike dani ne? Allah sarki Jummo kema kin sani abinda Momy tamin ba dai-dai bane, amma duk da haka ni ina mai baki hkr Allah ya huci zuciyarki, dan Allah kiyi hkr."

Cikin mutuwar jiki domin duk wanda ya maka laifi yace maka kayi hkr to Tabbas ya gama kashe maka jiki, numfashi ta sauƙe tare da cewa.

" Ba komai ya wuce amma dan Allah gaba karki kuma min irin haka, ana barin halak kodan kunya har yau Ya Garkuwa bai san abinda kika yiwa Momy ba, Kuma bana son ya sani Saboda yana ganin mutuncin ki."

" Hakane Jummo na gode sosai, kin sauƙa lafiya."?

" Lafiya Alhamdulillah!!! Amma dan Allah Meenat karki zoki gidan nan kin san ina gidan Momy kuma bazataji daɗi ba idan ta ganki gashi bata da lafiya ki bari sai na koma gidana sai kizo."

Da babu komai meenat ta amsa sun juma sosai suna hira kafin suka katse cikin farin ciki.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Ranar suna Ya raɗawa yaron sunan Baffa Wato Ahmad, sosai sunan yayi goshi, su INNO da Mamma duk sunzo yaro kuwa sosai ya samu kaya, babansa ma akwati Uku ya cika tam, dana yaron dana Uwar Momy ma tayi nata akwati biyu, shi kuwa Ya khalil, akwatin sa ɗaya yayi Aunty Zarah ma tayi nata turmin atamfa Uku da kayan Baby huɗu harda pampas, anyi taro lafiya an watse lafiya, da Ahmad ɗinsa suke kiransa Ya Garkuwa yace bai amince su sanja masa suna ba, a kirasa da sunan sa.



Haka rayuwa ta dinga gudu cikin farin ciki a yanzu Jummo bata da matsala da Momy tana sonta sosai sai dai har yanzu Momy gefen jikinta babu wani canji yana nan a yanda yake, ranar Jummo ta cika kwana arba'in washegari ranar Sikayel ta koma dama su INNO tun ranar da akayi suna washegari suka koma.

Itama Jummo washegari ta koma nata gidan ta, a wannan lokacin kuma aka saka ranar bikin Zizah.





*UMMU NASMAH CE*
[6/3, 12:02 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *80 to 81*





Jingine yake jikin motar ya harɗe hanunsa, yana ƙarewa gidan kallo yanda mutane ke cike ƙofar gidan suna neman hanyar da zasu gansa , numfashi ya sauƙe tare da leƙa kansa cikin motar alamu yayi musu da idanu akan suzo suje, babu musu suka nufi ƙofar gidan, ɗan sandan dake gadi a ƙofar gidan Ya zaro kuɗi kimanin dubu hamsin ya miƙamasa yana neman abarsu su shiga gidan, aikuwa ganin wannan kuɗin yasa ɗan sandan barinsu a kunnensa ya raɗa masa cewa.

" Officer Mai gidan ya samu isowa ne."

Kansa ya ɗaga masa alamun a'a

" yana hanya dai tukunna jirgin su ya taso waɗannan mutane da kake gani ƴan jiransa suyi roƙo, amma ku kuwa me zakuyi a cikin gidan nan."?

Murmushi ya kuma sakewa tare da cewa.

" Akwai abinda muke nema, idan har zaka mana jagora zuwa lungu da saƙo dake cikin gidan nan to na maka alƙawarin Naira dubu ɗari bakwai da hamsin, cash."

Zaro idanunsa ɗan sandan yayi tare da furta.


" 7050 thausand serious.?"

" Yes serious"


" Baku da matsala muje kawai"

Yayi Maganar yana shigewa gaba suka rufa masa baya, tun daga babban falon daya ƙawatu da kayan more rayuwa suka fara bincike har zuwa room ɗinsa basu samu komai ba daga cikin abinda suke nema, duk iya bincike da zasuyi a gidan sunyi amma ina babu komai dole tasa suka haƙura suka fito sunzo dai-dai fita daga falon kamar wanda aka ce mata kalli nan, ta hango kamar ƙofar ROOM ta bayan drower, ai kuwa da sauri tayi wajen tana cewa.

" Kunga wata ƙofa, a bayan school drower."

Ai kuwa juyowa sukayi tare da rufo mata baya ƙofarce kuwa, drower suka ture gefe cike da mamaki, wani irin ƙura ne a ɗakin har bakan Gizo yayi saka sosai, wayarsa ya zaro tare da kunna haskenta suka hau bincike, dubanta ta kai ga hoton dake manne jikin bangon, hanu tasa ta karkaɗe sai kuwa ga fuskokin ƴan gidan su ya fito ras duk an musu lamun Counsil, hanunta Zee tasa ta shafa a fuskar Safreena sai kuma hawaye ya jiraro mata, Ya Garkuwa dake tsaye a bayanta ne yace.

" Ba lokacin kuka bane yanzu, gaggawa zakiyi mu samu mu kammala abinda ya kawo mu kafin mutumin nan ya shigo."


Share hawayen tayi tare da saka hanu ta cire hoton wanda Shetima ke famar ɗaukar su video tun daga get ɗin gidan gar suka shigo, sosai sukayi bincike cikin ROOM ɗin wata waya Ya Garkuwa ya tsinta a ciki, tana kashe a ƙulle a leda da alamun ɓoyeta akayi kunna ta yayi, babu inda hanunsa ya shiga sai fannin video, ai kuwa sosai yaga abinda ya ɗaga masa hankali domin kuwa video ne wani daga cikin gidan su Safreena wanda ya kasance shine mamallakin wayar ya ɗauka, taƙaddama ce mai yawan gaske a daren da aka jefa wutar har zuwa sanda wutar ta fara kamawa, inda kawu IBRAHIM yake tabbar da cewa ya saka musu wuta kuma dole ne yau sai sun mutu gabaki ɗayansu, murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da duban ɗan sandan ya ciro kuɗinsa cash ya basa ya kuma ce.


" Ayi gaggawan maida komai yanda yake kafin mai gidan ya ƙaraso ku kuma kuzo muje."



Yayi Maganar suna ficewa da sauri koda suka shiga cikin motar yaja suka kama hanya muryar Zee yaji tana cewa.

Station muka nufa ko ya kamata mu shigar da ƙara, yana karasowa ayi Arresting ɗinsa, tunda muna da shaida a hanun mu."

"Hmmm baza muyi karar sa Zee."

" Baza muyi karar sa ba, to meye amfanin binciken da mukayi tare da hujjar da muka samu na tabbacin shine ya kashe iyayen Safreena.?"

" Zee har yanzu baki gama sanin halin ƙasar mu, ba karki manta Ibrahim yana tare da manyan ƙasa, Shari'a dashi ba zai yiwu ba, muna ɗaukar wannan hujjar muna kaiwa ƴan sanda, zasu ɓatar da hujjar su kuma wankesa shikenan yasha, Zee na gama yanke yanda zamu kwantawa Safreena haƙƙinta, gobe zan fara ɗaga masa hankali ta hanyar bawa ƴan jarida wannan hujjar su yaɗawa duniya ɗan siyasa ne dole hankalin manyan ƙasa zai tashi da kansu zasu saka a kamasa Domin wanke siyasar su gashi lokacin zaɓe ne yanzu karki damu ban fara wannan aikin ba sai da nayi tunani mai zurfi ta inda zamu ɓulle."


Dukkan su dariya suka saka cike da yadda da shawarar sa.



Haka kuwa akayi ya danƙawa Aminci News wannan shaidar tare da aikawa har BBC rediyo, a cikin kwana Uku yayi wannan aikin su kuwa suka dinga bazasa har wasu ƴan jaridun suna ɗauka, tashin hankali iya tashin hankali Ibrahim ya shigesa inda gwamnati tasa aka kamasa, tare da kaisa gidan kaso na sati biyu, kafin a ka fito dashi nan ma aka shiga Shari'a a zama na farko aka yanke hukunci bisa ga duba da hujja mai karfi da ke hanu dukkan dukiyar sa dana mahaifin Safreena sai da kotu ta ƙwace ta danƙawa Baba tare da yanke masa hukuncin rai da rai a gidan kaso.


Sai yanzu zuciyar Zee ta samu sukuni da taga an kwatowa Safreena ƴancinta, Baba wannan dukiya ƙin riƙeta yayi yaje ya samu Daddy Ya khalil da Ya Garkuwa ya danƙawa Ya Garkuwa dukiyar Safreena tare da cewa.

" Bazan riƙe wannan dukiyar ba saboda Safreena tana baya wannan dukiya duka nata ne ita kuma yanzu bata raye wannan dukiya mallakin ɗanta Abdul ne kai kuma kaine mahaifinsa gashi ka riƙe masa har ya girma ku basa abunsa, babu wanda yasan Abdul ba ɗan sunnah bane, dan Allah karki bari ya sani karku yadda yasan dangin mahaifiyarsa saninsu zaisa yace zai nemo su, inda hakan zaisa ya gane waye shi, dan Allah ku riƙe Abdul da kyau."

Numfashi Daddy ya sauƙe tare da cewa.


" Babu abinda zai faru da rayuwar Abdul na maka wannan alƙawarin, sannan dukiyar Abdul zata samu kulawa mun gode sosai."


Haka suka watse cikin farin ciki, bayan Baba ya tafi ne, Ya Garkuwa ya danƙawa Ya khalil duk takaddaun dukiyar Abdul ya basa tare da cewa shi bazai riƙe ba, Ya khalil shine Uba yanzu a wajen Abdul shine ya dace ya riƙe dukiyar, sosai Daddy yaji daɗin karar da Garko ya yiwa ɗan uwansa.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Yau watan Jummo Biyar da haihuwa yayin da Ahmad yayi ɓul ɓul dashi gwanin sha'awa kamar su ɗaya da ABDUL, har yana zama abunsa gashi da dariya yaron.



" Sati ɗaya kacal na baki, kuma a ranar zanzo na ɗaukeki."


Murmushi Jummo tayi tare da cewa.


" Sati ɗaya fa Ya Garkuwa, haba dai dan tun da nayi Aure fa banje gida ba shine kuma naje nayi sati ɗaya dal, ni dai ka ƙara min."


Ɗan murmushi yayi tare da rungumota jikinsa ya raɗa mata a kunnenta.

" Na sani nima naso kiyi koda sati biyu ne, bazai yiwu bane saboda na biya mana hajji dole zaku dawo bita, ke da INNO da Mamma na biya mana tare ma zaku dawo."

Dariya Jummo tasa cike da farin ciki ta kanƙame Ya Garkuwa kiss ta manna masa a fuskarsa tare da cewa.


" Wow My Love I love you so much!!! Da gaske ka biya mana hajji, wayyo daɗi ƙasar da nake burin zuwanta a rayuwata, mun gode sosai Allah yabar zumunci Allah ya ƙara arziki."

Murmushi Ya Garkuwa ya saki tare da cewa.

" Babu abinda bazan miki ba a rayuwata, domin kin min hallaci a lokacin da ya kamata ki gujeni a lokacin kika ƙara aniyar zama dani nine ya kamata na gode miki."


Murmushi Jummo tayi sun ɗan juma suna zance cike daso da ƙauna irin na mata da miji.


Haka kuwa akayi washe gari ya Garkuwa Da kansa ya kai Jummo har Tulde, ya dawo, sosai Jummo tasha mamakin yanda taga gidan su ya koma ginin block da block mai shegen kyau na zamani ga ruwan bohol da aka tona bata sha mamaki bama sai da ta shiga cikin gidan, domin kuwa ya ƙawatu sosai bedroom ɗin INNO tayels da tayels ne ga wasu uban kujeru da aka zuba mata,haka ɗakin Baffa dana Sikayel ma, koda INNO take sanar da Jummo cewa Garkuwa ne ya musu ginin sosai taji daɗin hallacin daya mata ga kuma hajji daya biya musu, lallai dayi dace da miji na gari,

31 / 32