Author : Jameelah Sadiq Category : Top Hausa Novels 2025
nadamar buguna da tayi abun Mamaki ba abunda Mama tace inba kallonsu da take ba, hawaye ne kawai suke zuba bisa idonta, kallonta Yaya sannna yace. "Mama baki ce komai ba kinji halin da ake ciki Auta tana buƙatar taimako."
Tashi Mama tayi zata bar dakin, Yaya Fatima ta riko ta tana cewa. "Mama dan Allah ya kamata ki yafema Khadija, ki anshi kaddarar da tazo mana tana bukatar taimako."
Zaunawa Mama tayi sannan tace. "Bintu mai zance? Aje ayi Allah yasa a gama lafiya." Tana gama fadin haka ta tashi ai take Mama ta wanke jiki ta fadi kasa tana amain jini, da gudu sukayi kanta suna kiran suna ta.
Daukarta Yaya yayi suka wuce asibiti, gado aka bata sannan aka sama mata drip dan temper dinta ce ta hau sannan Yaya ya cike takadar da za'ayi man aiki, sai wajen mangrid Mama ta farko haka ta matsa aka sallamaita ni kuma aka barni da Dija, duk da nima na farko amman ba sosai nike yin magana ba.
Washe gari da safe Doctor ya shigo ya duba jikina, hana bani komai yayi yace 10am za'a shiga dani ayi man wankin ciki, sanann ya tafi wajen 9 na safe Yaiyane duk sunzo sun cika asibitin suna duba lafiya, goma nayi aka zo tafiya dani za'a yi man aiki haka na bar yan'uwana suna kuka, dan bansan wani hali nike ba nidai naga suna kuka.
Wajen Mama kuwa tunda ta koma gida take kuka, dan tanajin ciwon abunda ya faru dani sosai, dan ma anbar mata Yaya Amina a gida ita ta kama kwantar mata da hankali tana gaya mata maganganu masu dadi wanda zai sa taji sanyi a zuciyar ta.
Kallon Yaya Amina tayi sannan tace. "Amina bakisan abunda nike ji ba shiyasa, amman na yafema Khadija Allah yasa ta dauki darasin duniya, daman ita duniya haka take tafi bagaruwa jifa, na yafe mata Allah yasa iyakar kaddararta kenan kinga ta biye ma san zuciya ta lalata rayuwar ta a banza."
Haka aka kirasu waya aka gaya mata anshiga dani dan yi man aiki, tayi man fatan fitowa lafiya.
*Allah Sarki, rayuwar Khadija da ban tausayi sosai wallahi nan bakuji komai ba😭, nima lokacin da take gaya man nayi kuka har na godema Allah, fatan dai Allah ya kara tsaremana imanin mu Amin, ya karemu da aikata aikin da na sani*
Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_
Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*
*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD
*Wannan page din nakane Yayana na kaina Muhammad Kareem MK, Allah ya kara daukaka da lafiya Amin*
*Gaisuwa ban girma gareki Maryam Majitapha lawal My Maryam ina maki fatan alkhairy ta wajena*
_Haba my real fans, ya ban ganin ruwan vote and comment a wattpad😢, pls show me ur love a wattpad mana😍_
*Wattpad JameelarhSadiq*
Page 5⏩6
Kallon Mama Yaya Amina tayi sanann ta dafa ta tace. "Mama dan Allah ki kwantar da hankalin ki insha Allah za'a shiga lafiya kuma a fito da Auta lafiya." Kallonta Mama tayi sannan tace. "Amina ba wannan ke tada man hankali ba, yanzun ace Auta za'ayi ma wankin ciki? Karki manta Yarinya ce fa, bata wace shekara sha takwas ba, ina lisafi wata mai kamawa take cika shekara ta sha tara, amman har za'ayi mata wanki ciki, idan za'ayi mata aure mai za'a cema wanda zata aura? Ce mashi zamuyi tayi cikin shegen? Ko kuma muce mashi har wankin ciki an taɓa yi mata Amina."?
Numfasawa Yaya Amina tayi sannan tace. "Hakane Mama amman nasan na Allah basu kyarewa mudai muyi mata fatan samun miji na gari wanda zai rike ta amana ba tare da yayi mata gori ba watan watarana."
Dariya Mama tayi sannan tace. "Ai ba wanda zai iya aurenta Amina, dan haka tana samun sauki wallahi zan aura mata Alhaji Salahu, fatan dai Allah yasa a dace."
Cikin ruɗewa Yaya Amina tace. "Haba Mama ya kikeso ki bada gudumuwa wajen lalacewar rayuwar Auta, a rasa wanda za'a daura ma Auta sai Alhaji Salahu koni ya haifeni balle Auta, kuma matan shi uku dan ma ta hudu ta rasu, har ƙawa nike da ita a gidan fa."
Wurga mata harara Mama tayi sannan tace. "Wallahi ba wanda ya isa ya hanani aura ma Khadija Salahu , idan ba shi ba wa zai aureta? Yarinyar da ta zubdar da mutuncinta a waje ai Alhaji Salahu rufa mata asiri zaiyi ya aureta."
Cikin kuka Yaya Amina tace. "Dan Auta tayi ciki shine yasa zakiyi mata haka? Maiyasa kika kasa yarda da kaddara ne Mama? Mama kinsan kaddara tana cikin cikon imani amman ke kin ki yarda da hakan, yanzun baki gudun tace zata gudu tabar maki gidan? Dan nayi imani ga Allah Auta ba zata yarda da auren wannan mutun min ba, Mama karki ce nayi maki rashin kunya a matsayinki ba mahaifiya ta, amman ko nice kika ce na auri shi wallahi ba zan aureshi balle Auta da take budurwar wannan zamanin, kum... Tas Mama ta wanke Yaya Amina da mari tana cewa. "Dan ubanki har kin isa ki hanani abunda nayi niya? Ko kin fini son Khadija ne? Ai nasa nice na dauki cikinta nayi rainonshi har na tsawan wata tara da kwana tara sannan na haifeta ko? Kuma na bata nonona tasha, ai gata nike nema mata da zaki kama challenge dina dan nace zan aura mata Salahu, yanzun ma zani nayi mashi maganar ta tana gama jini za'ayi bikinsu ko kuna so ko baku so, dan nasan bakinku daya da yan'uwanki to ku sani ba wanda ya isa ya hanani wallahi."
Mama na gama fadin haka ta dauki hijab dinta ta tafi gidan Alhaji Salahu dan yin magana dashi, haka ta bar Yaya Amina zaune tana kuka ganin kukan baiyi mata maganin komai ta shiga kitchen ta dafa abinci tasa a cooler sannan ta fito ta shiga motarta ta wuce asibiti , lokacin da ta shigo hospital din aka fito dani angama yi man wankin cikin.
Fitowa tayi da abincin ta nufo wajen su, duk da suma sun danyi kuka amman ba sosai ba dan Yaya Jamilu hakuri ya basu sosai ya kuma kwantar masu da hankali shiyasa sukayi shiru kallo daya Yaya Jamilu yayi mata ya ganne akwai matsala dan tasha kuka sosai, kunsan ace babban uba daman Babana ya rasu ne tun ina cikin ciki bansan Babana ba, shine dai Ubanmu mu dukanmu daman duk matane shi kadaine babba, baice komai ba tana ijiye abincin yace tazo yana son ganinta a waje, aiko suka fito suka samu waje su dukansu akabar Dija ta cigaba da kula dani.
Office din Doctor Dikko suka je suka zauna sannan Yaya Jamilu yace. "Amina gaya man maike faruwa ya jikin Mama ko jikin tane har yanzun."!? Cikin tsoro yayi mata maganar dan daman hankalinshi ba kwance yake ba yana tunanin halin da Mama take ciki.
Share hawayenta Yaya Amina tayi sannan tace. "Yaya wallahi Mama tana son ta ɓata rayuwar Auta duk da ta kasance uwa a gareta, wallahi bansan yaushe Mama ta chanza hali ba Yaya." Ta karasa maganar cikin kuka, kallonta Yaya Fatima tayi sannan tace. "Amina kiyi mana bayani mu fahimta kin yi mana magana a dabarbarce bamu gane ina maganarki ta dosa ba."
Shidai Yaya kasa cewa komai yayi yana jiran yaji abunda Yaya Amina zatace, balle Yaya Aisha take kuka har yanzun dan ta kasa yafema kanta akan abunda sukayi man ita da Mama, cewa tayi. "Yaya Amina dan Allah ki gaya mana abunda ke faruwa da Mama wallahi hankalina ya tashi sosai."
Cikin kuka tace. "Mama tace ana sallamo Auta aure zatayi mata, kuma da Alhaji Salahu ba yanda banyi ba akan tayi hakuri taƙi daga karshe ma har marina tayi kuma tace ba wanda ya isa ya hanata aurar da Auta ba."
Tashi Yaya Jamilu yayi yana girgiza kai sanann yace. "Ina wallahi ba zamu yarda ba, mu zuba ido muna kallo Mama ta ɓata ma Auta future ba, ya kamata Mama ta gane wannan fa kadddarace wanda ba wanda ya isa ya kauce mata harta ku masu aure dan ba'a fatan haka fisabillahi, kuma ta rasa wa zata aura mata sai wannan tsohon wanda baisan darajar dan'adam ba, kuma kullun gidanshi sai matanshi sunyi fada yanzun haka yaranshi talatin a duniya ai ko sa'ana yayi ma Auta zufa a aure yanzun ko nike da shekara tallatin biyar balle Alhaji Salahu da yayi shekara saba'in yana hanyar mutuwa ku bari naje nayi magana da ita."
Su kuwa kasa cewa komai sukayi dan lamarin ya girmi tunaninsu, haka suka fito tare suka tafi gida wajen Mama dan Yaya Fatima cewa tayi su tafi su dukansu.
Niko cikin ikon Allah na farfado har nayi brush naci abincin da Yaya Amina ta kawo, an bani magani nasha, nidai ba bacci nike ji ba balle nayi, zaunawa nayi na jingina da gado ina tunani da tarin nadamar abunda na aikata, Dija ce tace. "Aunty Khady dan Allah kiyi hakuri, ki dauki wannan abun a matsayin kaddaraki duk da sakakinki a ciki ammn haka Allah ya kaddara kuma ba yanda zakiyi inba ki yarda da kaddara ki kuma godema Allah."
Mai neman kuka angaya mashi mutuwa, aiko na fashe da kuka ina kallonta na girgiza nace. "Dija dan Allah ki daina bani hakuri ki barni nayi kuka ko naji saukin abunda nikeji a cikin zuciya ta, Dija nasan duk abunda ke faruwa dani cikin jikina ya zube sannan anyi man wankin ciki kuma babu tabbacin zansake haihuwa a duniya, ba dole nayi kuka ba Dija? Ni yanzun joya za'a ringa kirana ko? Wanda bata haihuwa bani ganin jinina a dorajaran kasa? Idan na mutu bani da maiyi man Addu'a a koda yaushe sai yan'uwana kenan? Dan Allah ki daina bani hakuri ki barni nayi kukan na rokeki wannan alfarmar."
Shiru itama Dija tayi ta dukar da kanta kasa tana aikin kuka dan maganganuna sunyi mata tasiri sosai a zuciya, tabbas banda maiyi man addu'a ko yaiyaine ba kullun ne zasuyi man ba, inba sun tuna dani ba, amman haka Allah yaso muna cikin kukanmu sai Doctor Dikko ya shigo lailashemu yayi sannan yayi ma Dija fada akan tana daina wannan kukan hakuri ya dace ta bani,ƙara duba lafiyata yayi ya tambayeni idan yake man ciwo sannan ya tafi cikin tausayi na.
*Dan Allah ya kujaji wannan labari na Khadija 😭😭😭, sannan Khadija tace nace maku tana godiya sosai kuma tana ganin comment dinku, tana ganin yanda kuke tausaya ma rayuwarta sai dai abunda take son ku sani haka tata rayuwar tazo mata sai tana godiya ga Allah da ya tsara mata haka, kuma tana fatan labarinta yana tasiri a zuciyoyinku musamman mu yan'matan zamanin nan, mu kiyaye biye ma soyayya karda mu yarda muyi zurfi a soyayya😭*
*ni kuma nace yanzun aka fara wasan ku cigaba da yin comment dan shi zai bani kwarin gwwiwar yayi maku posting kullun🤗*
Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *∆ A SANADIN SOYAYYAR MINTI ∆*
_na ɓata rayuwata😭_
Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*
*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________
*Gajeran labari*
*Labarin gaskiya (true life story)*
https://chat.whatsapp.com/BS0N4RFqbe6LFqlXZZ9vxD
*my real fan's kusan dai cewa na tafi hutu, ba zaku sake jina ba sai wani lokaci wanda nida ku bansan lokacin ba har sai Allah ya nuna mana zamu sanshi, sai gashi wata baiwar Allah tayi man magana akan nayi hakuri na rubuta labarinta dan masu irin halinta sunji su daina, idan ma akawai masu niyar farawa suma su daina idan sukaji abunda ya faru a kanta bisa da biye ma zuciya da tayi har ta aikata SOYAYYAR MINTI WATO A TURANCE ROMANTIC LOVE, da naso nace ba zani ansa ba, yanda ta nuna man damuwa da kuma nuna man amfanin labarin da taimakon da zaiyi shiyasa na ansa nace zanyi amman zanyi shi a GAJERAN LABARI duk da ita ba a short ta bani shi ba, ta bani shi a long story nice nayi summarize din shi na maida shi short saboda karda munayi mu koma school na ajiye shi ba tare da mun gama ba wannan kenan*
*Abunda nike so daku shine kuyi comment sosai hakan zai bani kwarin giwwar baku shi cikin sati insha Allah*
_Godiya ta musamman zuwa ga_
*Zauren Yar'mutan kankia fan's group*
*Real jameey novel fans 1&2*
*Sansanin Yar'mutan kankia*
*Zee-abu hausa novel*
*Ban raina allura ba fan's*
*zauren manazarta fans*
_Da dai sauransu duk ina maka godiya ta gareku_
*oyoyoyo! Ina maki murnar dawowa duniyar yanar gizo social media kenan, kawata aminiyata wato FJ marubuciyar BAGIJJA, Allah yasa kin dawo sa'a kuma a cigaba da suburbudo mana zafafan novel mana shan karatu❣️*
*Wanann page din naki ne Real eeshow marubuciyar BAN RAINA ALLURA BA! ITAMA KARFE CE kiyi yanda kike so dashi🤗*
Page 1⏩2
Wata macece wanda bata wuce shekara 50 ba zaune a madaidacin parlourn gidansu ba abunda taje sai aikin kuka dan abun duniya ya taro yayi mata yawa, wata yarinya ce ta fito daga cikin wani daki ta zauna kasa kusa da kafar matar itama kukan take, dan ta rasa mai zata ce ma mahaifiyar tata kallonta tayi sanann tace.
"Mama Dan Allah kiyi hakuri ki yafeman wallahi ba zan sake ba, nayi maki wannan alkwarin, wallahi sherin she... Tas! Mama ta wanke ta mari tana nuna ta da yatsa cikin fushi ta fara cewa. "Allah ya tsine maki albarki insha Allah ba zaki gama da duniya lahira ba Khadija, tunda har kika sa na zubda hawaye saboda dake kika jaman zagi a cikin unguwa, Allah ya i... Da sauri Khadija ta rike kafafun Maman tata, tana girgiza mata kai tana hawaye masu ciwo dan kukan ma ya gagareta dan tana cikin tashin hankali ba kadan ba, yanda Maman tata take tsine mata tana mata fatan masifa ta fada mata bayan kuma itace uwa gareta mahaifiya, cikin tashin hankali tace. "Mama dan Allah ki barni haka karda abun yayi man yawa kin tsine man sannan kuma zakiyi man Allah ya isa, nasan ko baki ce man Allah ya isa ba ni tawa rayuwar tazo karshe tunda har ta dalilina kika zubda hawaye, Dan Allah Mama ki yafeman wallahi ba zan sake ba, kiyiman Uzuri Ma... Katse ta Mama ta sake yi ta hana Khadija magana, wurga mata hararar tsana tayi sannan tace. "Wallahi Khadija na tsaneki bani sonki a yanzun bani kaunar ganinki, ke har wani uzuri zan maki Khadija? Bayan cikin shegene a jikinkinki duk tarbiyar da ba baki, abu daya nike so ki sani bani bake har abada, karki sake kirana da sunan Mama ta na yafeki daga cikin ƴa'ƴana, ki kirani da suna HAFSAT dan yanzun ni ba mahaifiyar ki bace, Allah ya tseni maki albarka."
Allah Sarki kuka na sake rushewa dashi dan duniya tayi man kunci bansan ya zanyi da rayuwa ta ba, sannan kuma na tsorata da yanayin da mahaifiya ta take ciki, tashi nayi na koma dakina na cigaba da kukana, wanda tunda jiya mukaje asibiti likita ya sheda mana ina dauki da karamin ciki dan wata wata nake aikin kuka, ba kukan komai nike ba Ila kukan dana sani da biye ma son zuciyata, yunwa naji ta taso man Kuma bani sha'awar cin komai sai dan'wanke da manja da yaji wanda yaji tabarnuwa da kayan kamshi na yaji, tashi nayi na fito parlour tadda Mama nayi zaune tana share hawaye matsawa nayi kusa da ita nace. "Mama yunwa nike ji Kuma dan'wake nike son nace." Ji nayi Mama ta wanke ni da mari cikin zafin rai tace. "Wallahi baki da kwanon abinci a gidan nan, kije wanda wanda yayi maki cikin ki gaya mashi abunda kike son ci, sannan Kuma karki sake kirana da sunan mama na gaya maki tsinanniya lalataiciya dake."
Kasa motsi nayi, ba abunda nike sai hawaye dan ni yanzun na kasa kuka ma, ji nike daman nike kukan da Mama take da naji saukin abunda nike ji a raina, hakuri na sake bata sannan na tashi na koma dakina inajin yanda yunwa take azabzabata na rasa yanda zanyi gashi bani son cin komai idan ba dan'wake ba, haka na wuni a daki a ranar banda sake fitowa waje ba, balle har Mama ta ganni ta sake tsineman, tun karfe 1 nike zaune inajin yunwa har karfe hudun marece yayi, tunowa nayi inada wasu kudi da Nura ya bani tunin dadewa, cikin sauri na tashi na dauko kudin na zura hijab dina dan zuwa nema ma ciki abunda zan sama shi, ina fitowa na tadda Mama da Yaya Aisha sun hada kai suna kuka, Yaya Aisha Yayata ce wanda muke uwa daya uba daya, da yake nice Auta a gidanmu yanda na gansu ne hankali ya tashi dan nasan kukan da suke tsaye nayi ina kallonsu nima a zubda hawaye, kallona sukayi lokaci guda suna man wani irin kallo wannan kallo ba komai bane illa kallon tsana dan Ina ganin tsantsan tsana a cikin kwayar idonsu, ta sowa Yaya Aisha tayi ta nufoni gadan gadan ni Kuma ina ja da baya haka muka kamayi har muka kai karshen bango, kulle idona nayi dan nasan ba dadi zatayi man ba, kamani tayi ta fara wanka man mari tana zagina, nan suka rufeni da bugu ita da Mama, tun ina yi basu hakuri har nazo da na kasa sai dai ido, tun ina gane idan nike har ta kai da bani gane mai akeyi, haka suka kama buguna suka barni kwance sheɗashaɗa cikin jini rai hannu ga Allah, ba su damu da wani hali nike ciki ba, tun la'asar sukayi man haka suka yashar dani suka cigaba da hidimar gabansu, Yayane ya shigo Jamilu shine yana da matarshi kuma shine babba a gidanmu, yana shigowa ya taddani cikin wanann halin kallon Mama yayi sannan yace.
"Mama mai yasamu Auta na ganta kwance cikin jini kuma hankalinku kwance harda ke Aisha."?
Cikin fushi yayi tambayar dan yasan abunda ke faruwa dani likitin da yaga mana ina da ciki shi ya kirashi waya ya gaya mashi halin da ake ciki da yake abokinshi ne, kallon shi Mama tayi sannan tace. "Jamilu Khadija cikin shege tayi gaya maka ne banyi ba, dan na fiddata daga cikin jerin ƴa'ƴana, baku ba Khadija kuma