Chapter 45 Reading YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt Arewa Novels

YAR TSANAR ZINARI BOOK COMPELET BY JIDDA UMAR.txt

Author :  Jidda Umar Category :  GNOVELS

Chapter   45 / 54

132K to 135K   out of 159.1K words

da kuka"ni yanzun shi kenan haka zan zauna ban yi aure ba,shi kenan nayi Two Zero,gashi Suraj yayi min nisa ko ganin shi bana samun damar yi,har Gara da,wallahi Momy kin cuce ni duk ke kika lalata komai "

Tama rasa me zata ce mata,wani shawara ya kamata ta bata wanda zuciyar ta zai yi sanyi,tun ba yanzun ba ta san cewar ta kwafsa da ya,sai dai bata son ta nuna gazawarta a gaban yar ta,"kin ga kiyi haƙuri bari zan kira Atika zamu samu mafita"a haka ta samu ta shawo kanta da kyar ta yi shiru.

*Bayan sati ɗaya*

A cikin kwanaki bakwai idan ka ga Biba kallo daya zaka mata ka shaida tabbas ta dawo haiyacinta,ta kuma koma asalin Biban ta,
Domin duk wani rama da kodewa da tayi sai da ta ciko,
Ammi kullun cikin bata haɗin danyen madara da na namar kaza take,gashi man da ta bata ya taimaka wurin goge mata fatar jiki,dan har wani tsantsi take yi,cikin turarukan da take sawa tayi har da gashi, ita karan kanta wani lokaci idan ta kalli kanta a madubi tana jinjina ma kayan tare da mamakin in da Ammi ta samo su,dan wani irin fitinannan kanshi ke fita a jinta wanda hatta fitsari idan tayi shi ji take a ciki,har mamaki matsewarta take yi,dan ko kaɗan yatsar ta bai iya wuce kofar wurin,ga wani irin ruwa sake fita,wani lokaci har tsoro abin ke bata yanda yake fita,ita karan kanta ta san ta samu canji da yawa a jikin ta,farin ta ya karu fiye da da,har wani kashe ido take da ƙyalli na musamman,lallai bata san da wani baki ya kamata ta gode ma Ammi ba,babu in da take zuwa sai gaida Kaka sai kuma zaman istigfari wanda a yanzun yawancin lokuta zaka ganta da ƙaramin charbi irin mai batir din nan tana dannawa.

Ammi ce ta buɗe ƙofar ta shigo "har yanzun baki kammala shiryawa ba,kin san saura yan mintuna jirginmu ya tashi"

Juyowa tayi fuskarta dauke da murmushi "na kammala Ammi yanzun takalmi kawai zan saka"

"To ki yi sauri dai dan ke kadai muke jira"ta ƙarasa faɗa tana fita,

"To"

Ita da Ammi ne kawai zasu tafi,dan Amira zata zauna ne a wurin Goggon yara,dan haka Shamsuddeen shi ya kai su har Airport bayan sunyi sallamah da su Kaka,

Ko lokacin da jirgi ke lulawa sararin samaniya lumshe ido tayi tana jero addu'a,kwata-kwata bana jin yin wannan tafiyar,ba dan komai ba sai don bata son haɗuwa dashi,ita da ma ace za'abi nata da Ammi ta barta anan idan har aka gama shari'ar sai su dawo su mai da ita gida,sam bata shirya tarbon wulakanci ba irin nashi,ta tabbatar idan har sun haɗu sai yayi abinda zai ɓata mata rai sannan hankalin shi yake kwanciya,
Ganin tunanin yana ƙoƙarin yi mata yawa ne yasa ta maida hankalin ta wurin jan charbin da take yi,daga haka har bacci ya kwashe ta,

Sai da jirgin su ya sauka sannan Ammi ta tayar da ita suka fito,wani irin sanyi ake yi mai matukar shiga jiki da ratsa kashi,Glass din dake cikin jakkanta ta ciro ta saka a idon ta,wanda ba karamin kyau da ƙara fito da ita yayi ba,dama gashi riga da Siket ne na Atamfa a jikin ta mai kalan ja,sai After dress data saka fara tas mai tsansi shara_shara mara nauyi,sai karamin jakka mai dogon tsarka wanda ake sakalawa a kafaɗa dan ƙarami wanda baici ya ɗauki waya biyu ba,sai ta fito yanda kasan ƴar tsanar zinari,

Ammi ce a gaba ita tana biye da ita a baya jaye da dan madaidaicin Aƙwati,

Sam bai lura da ita ba sai da ya rungume Ammi yana murmushin farin ciki "welcome Ammi"

"Thank you My Dear"

Cikin yanayin shagwaba wanda ba ta san ya iya ba ya shafa cikin shi"Ammi yunwa nake ji,nayi kewar girkin ki,"

"Nikam babu abinda zan kara girka maka tunda ga matarka nan ta maka"

Yana shirin kara yin magana ne idanun shi suka sauka akan ta,duk da akwai Glass mai duhu a idanun ta hakan bai hana shi ganin kwayar idanun ta data cire a kanshi tana ƙara kauda kai,

Gefen lips din shi ya dan ciza yana shafa kai tare da kara kallon ta daga sama har kasa cikin kallon nan nashi na gefen ido,

"Ni dai muge sanyi nake ji"

Maida hankali yayi kan Ammi yana rike hannun ta"muje to"

Tana biye dasu a baya har wurin parking mota inda ya buɗe ma Ammi gidan baya ta shiga,ya mai da kofar ya kulle,da makulli yayi amfani ya danna,nan take but din motar ya buɗe,saka akwatin tayi ta kulle sannan ta zagaya ta buɗe gidan baya kusa da Ammi ta zauna ba tare data kalli koda in da yake ba,tayi alkawarin har su bar garin ba zata taɓa shiga har Karshi ba,

Da kallon mamaki yake binta dashi a ran shi,wanda ko kaɗan bai nuna ba a fili,wato shi zata nuna ma miskilanci,ai kuwa sai ta san dame yi take yi,

Buɗe mazaunin direba yayi ya zauna,yana tayar da motar.......
🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*81*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*


Tsanin su da Airport din akwai nisa,duk da lafiyayyun titina da ke shimfide sai da ya dauke su tsayin mintuna talatin sannan suka iso wani babban gida lafiyayye mai hawa uku,gidan babba ne kam,
A wurin ajiye motoci yayi parking,kai ko harabar gidan abun kallo ne ba sai na tsaya yi maku bayani ba,tana biye dasu tana ƙare ma ko'ina na gidan kallo wanda ba karamin jan hankalin ta yayi ba,tana matukar son Fure,a ko'ina taga fulawa tana iya tsayawa ta kalla domin yana saka ta farin ciki,
Ji tayi an riƙo hannun ta,kallon Ammi tayi dake sakar mata murmushi "ki dinga kallon gaban ki"

Sai lokacin ta lura ashe step ne a wurin da bata lura dashi ba,ƙila da faduwa zata yi, "na gode Ammi"

Tana rike da hannun ta har suka shiga cikin makeken falon wanda nan take wani dumi mai matuƙar daɗi mai hade da kamshi ya shiga mamaye hancin su da jikin su baƙi daya,

Dukkanin su kallon falon suke cike da tunani mabanbanta a zuciyar su,
Ji suka yi wani murya mai taushi yana musu marhaba da zuwa cike da farin ciki,

Mai da kallon su suka yi kan tsohuwar da ake turowa zaune a saman keke,wacce ke cikin shiga na mutumci yayin da kwarjininta ke fita tare da murmushin da take saki,
Hannu ta buɗe ma Ammi wacce tuni ta fara hawaye,

Da sauri ta karasa in da take ta tsugunna tare da rungumeta tana fashewa da kuka,ita kanta tsohuwar kuka ta saka domin sun riga sun jima da cire ran sake saduwa a duniya,sai gashi yau Allah yayi sun hau ido da ido,duk da suna magana a waya amma ba kamar yau ba da suke jin dumin juna,
"Ummi ki yafe min"

Daga inda take tsaye hawaye take yi wani na bin wani,dan ba ƙaramin tausayi suka bata ba,ita ko yaya ne bata son taga babban mutum yana kuka,
Gani tayi an mika mata handkerchief fari tas,amsa tayi tana goge hawayenta dashi har da fyace hanci dashi duk da ba komai a cikin hancin,
Jin muryar shi tayi daf da ita yana faɗin "why ar you Crying?

Ba tare data kalleshi ba tace" I am just happy that she overcome it"

Nuni Ammi tai mata da Biba"ga matar Jikan ki Ummi,yarinyar kirki ce"

Gani tayi itama matar ta buɗe mata hannu tana mata alamar ta zo,babu musu kuwa ta karasa gareta ta rungume ta,

"Ohh Grandma kukan ya isa haka in ba so kike mu koma Asibiti ba"

Dakuwa tai masa tana dariya mai haɗe da kuka.

Sake su tayi cikin murmushin farin ciki tace"kuje kuyi wanka sai ku sauko mu ci abinci"kallon shi tayi"ka tafi da matarka dakin ka"

Dagowa tayi ta kalle wanda shima yayi dai dai da ita din yake kallo,ganin bai da niyar cewa komai ne yasa tace"ni tare da Ammi zan zauna"

Grandma ce ta girgiza kai"a'a ƴar Albarka ki zauna kawai da mijin domin nan gidan ki,gashi kuma kun jima baku haɗu ba"

Babu damar cin musu,dan haka tashi tayi tabi bayan shi,
A hawa na biyu ma wani duniyar ne na daban,ga ɗakuna nan na alfarma,
Daya daga ciki ya nuna mata"ki shiga wannan"ya faɗa ya juya yana ƙoƙarin bude na kusa dashi,
"Kaya na fa?

Ba tare daya juyo ba yace" Za'a kawo maki"

Bin kofar daya shiga ya kullo da kallo tayi sai kuma ta tabe baki"hakan ma yafi "ta faɗa tana shiga dakin,faɗawa tayi kan gado tana sauke numfashi,komai na dakin fari ne tas har ta labulaiya,
Jin ana kwankwasa kofa ne yasa ta tashi ta je ta buɗe,
Wata mata ce mai sanye da kaya irin na masu aiki,dan tun a hawa na dawa ta ga masu irin kayan,daga dukkan alamu akwai ma'aikata da yawa a gidan,
Cikin girmamawa ta gaishe ta tare da fada mata ina zata ajiye kayan,
Karba akwatin tayi tana sallamar matar,

Ajiye akwatin tayi sannan ta shiga wanka,ko da ta fito sai da tasha magungunan ta data zo dashi sannan ta shirya,har ta zauna sai gashi an aiko data fito suci abinci,

Wurin cin abincin ma bata ganshi ba,dan haka ba karamin daɗi ta ji ba,cikin saki jiki suka gama cin abinci suna hira da Grandma,bata taba dauka matar nada sakin fuska da barkwanci irin haka ba,ranar tare suka yini har dare,sallah kawai ke tada su,hirace ta an daɗe ba'a haɗu ba.

Har zata kwanta taji tana ra'ayin shan ruwan Lipton saboda sanyin da akeyi,dan haka fitowa tayi ta nufi kicin din ƙasa,
Koda ta haɗa Lipton din jan daya daga cikin kujerun kicin tayi ta zauna,bata san wani irin Lipton bane amma ba karamin daɗin ya mata ba,lumshe ido yayi tana kurba a hankali har ta kusa kammalawa,
Jikinta ne ya bata kamar akwai mutum kusa da ita,yayin da wannan kamshin mai sanyi daɗi yake shiga duk wani kusurwa na hancinta,wanda hakan ke tabbatar mata da kusancin ta da wanda take tunani,
Da sauri ta buɗe idanun ta,sai kuma ta saki ƙara a lokacin daya tana yarfe hannu,saboda ruwan Lipton din daya zubar mata a hannun sanadin zaburan da tayi,
Babu zato sai jin saukar lallausar hannun shi tayi saman nata,matso da hannun yayi ya shiga busa mata iskar bakin shi mai matukar sanyi yake yi a hannun tare da faɗin "Sorry,Sorry"

Kuka ta saka jin yanda hannun ke radade,wanda bana komai bane sai na raki,dan bata kaunar abinda zai taɓa mata lafiyar jiki,
Matso da ita jikin shi yayi a haka ya buɗe sink ya kunna ruwa ya tara hannun ruwa na sauka a kai,
"Hannun yana zafi har yanzun?

Jinjina mai kai tayi,
Da yatsan shi yayi amfani wurin dago habar ta" Kalle ni"

Dago jikakkun idanun ta tayi tana daurawa a kanshi,

"Akira likita?

Sai lokacin ta tuna a gaban waye take,dan haka cikin sauri ta fiske hannun ta dake cikin na shi,ba tare data ce mai komai ba ta juya tayi tafiyar ta,
Sai dai taku biyu kawai tayi sai ji tayi ya riƙe hannunta ta baya,kafin ta gama tantance dalilin shi nayin haka,sai jinta tayi jingine a jikin shi yayin daya rankafo ta bayan ta,ya zagaye cafaffen cikinta da hannayen shi, kanshi kuma saman kafadarta,tana jin yanda yake busa mata numfashin shi da goga hancin shi a jikin fatar jikin ta,
Ai kuwa nan take taji wani carrr tsigar jikin ta ya tashi,wasu irin abu na faman mata yawo a jiki,

Hannunta ta Daura saman nashi tana ƙoƙarin zame hannun shi,sai dai sam yaki sakin ta sai ma kara matse ta da yake yi"ka sani in wuce bana so!me haka kake min"ta faɗa cikin haushi,

"Har yanzu fushi kike yi dani?

" Ban sani ba dan Allah Suraj ka sake ni"ɗan ihu ta saka jin wani irin Kiss daya sakar mata a kafaɗa mai shiga jiki,
Kuka ta saki lokaci ɗaya na takaici jin sautin murmushin daya saki,wato da gangan yake yi,

"Fada min fushi kike yi da ni?

Cikin kuka tace" Ko na faɗa maka me zaka yi,ni ka sake ni"

"Haƙuri zan baki mana,so kike Allah ya kamani saboda fushin ki?

" Ai kuwa in da wannan ne Allah ya gama kamaka dashi"

Ba tare data san sanda ya ɗaga rigar nata ba sai jin hannun shi tayi yana yawo a fatar cikin ta,wanda yasa dole sai da ta rintse ido tana jin yanda yake zagaye ramin Cibiyar ta yana wasa za karamin Pin ɗin zinari dake makale a wurin,

Daga ita har shi wani irin numfashi suka sauke a tare,
Cikin wani irin murya mai tattare da kasala ya furta mata kalmar"I .. am.. Sorry "a cikin kunnen,Yana goga lip din shi a kunnen,dan wani irin fitinannan kanshi ne yake shaka daga jikinta mai tada hankali,

Kankame hannun shi tayi da ƙarfi,dan ji take kamar zata zube kasa" Please"ta furta a wahalce,

"Ummm" Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya tare da barin kicin din ba tare da ya yarda ya kalli in da take ba,

Ganin fitar shi ne yasa cikin sauri ta data teburin wurin tana tsugunnawa,ta jima a haka kafin ta lallaba ta koma dakin ta tana kulle kofa har da key,
Kai tsaye banɗaki ta nufa tana sakar ma kanta ruwa ko zata ji sanyin bijire mata da gangan jikinta ke shirin yi,yana hasaso abinda ba zai taba yuwa ba,ita kanta tasan ko taki dole sai ta haɗa da wankan tsarki,dan tun rungumar farko daya mata ta ji yanda wasu ruwa masu dumi suka balle mata,wannan wani irin yanayi ne...........


Hmmmm ni kan ina daga gefe na ce kila maganin Ammi ke aiki😜to bari dai mu gani ko za'a iya jurewa


🦂🧸YAR TSANAR ZINARI🧸🦂

Story & Writing
By
JIDDARH UMAR

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*

*82*
*Paid book*
*300₦*
*Hauwa Umar, Zenith Bank,2284905309*
*mai buƙata sai ya tuntuɓe ni ta wannan number domin turo shaidar biya, 08141644865*


Washegari da safe tana idar da Sallah ta shiga dakin Grandma ta gaida ita,sai dakin Ammi nan ma sai da ta dan jima dan ta samu tana karatun Kur'ani ne,bayan ta idar ne suka gaisa,har ta isa kofa zata fata,dan so take ta kwanta dan jiya Allah ya gani ba tayi wani baccin kirki ba,saboda ciyon mara,ita ba lokacin Al'adan ta balle tace shine,da yar ta samu tayi bacci gab da Asuba,shi yasa take sauri yanzun taje ta kwanta,
Kiran sunan ta da Ammi tayi ne ta dakatar da ita ta juyo tana amsawa,
"Ki shirya da wuri domin zuwa ƙarfe tara zamu fita"

"Insha Allah Ammi"

Gyada mata kai tayi,hakan yasa ta fita tana jawo mata kofa,
Tana saurawa shi kuma yana saukowa sanye da Jallabiya fari a jikin shi sai karamin hula fari dake kanshi,yanda kasan wani matashin Balaraben,kallo daya tai masa ta kauda kai,shi ma bai kula taba yayi ci gaba da saukowa kamar bai ganta ba,sun gefta juna da step biyu ya dakata yana juyawa baya"na ce ba"

Kin kulashi tayi duk da taji shi,taci gaba da takunta,
Sai dai ko step uku bata karaba cikin rashin sani ta taka doguwar rigar dake jikinta ai kuwa nan take tayi baya gaba ɗaya tana shirin faɗuwa,duk yanda taso ta kama kasa ta tsaya abin ya gagara,ta tabbatar da idan har bisa tsautsayi keyarta ta kai kasa to babu lallai na zata kara tashi a wannan rayuwar,domin ta san dinkin dake kanta ya gama kwancewa bama shi kadai ba kan gaba ɗaya ya gama tashi aiki,saboda step din nada yawa,

Ta dai jita ta faɗa jikin abu mai laushi idanunta a lumshe,sai dai ko kusa bata gwada bude ido ba,dan ta sadakar mala'ika yayi sama da ita ko,
Ai kuma jin anyi saman da ita ne yasa ta kara sake jiki gabadaya kamar mawa sumammiya,koda yake zamu iya kiranta da haka tunda da gasken suman wucen gadi tayi,

A hankali yake tafiya da ita a hannun shi yana kuma kallon yanda take sauke numfashin a hankali wanda hakan ke nuna masa da bugun zuciyarta yayi ƙasa,

A maimakon shiga da ita dakin ta,sai tura kofar dakin shi da ƙafa yayi ya shiga,ya maida,kan gado ya shimfidar da ita a hankali kamar wata karamar yarinya,ya dauki filo ya daura kanta,

Zame doguwar rigar jallabiyar jikinta yayi,wanda yayi sanadiyar bai yanar yar karamar rigar baccin dake jikinta iya cinya,
Kallo daya ya mata ya dauke idanun shi a jikinta ya maida a fuskarta,
Shafa fuskar yake a hankali tare da kiran sunan ta"Bebin bude idon ki"

"Um Umm"

Dukawa yayi saitin kunnenta "buɗe ido ki gani"

"Na mutu ne?

Bai bata amsa ba sai tafin ƙafar ta daya kama ya shiga murzawa da dan ƙarfi yanda zafin ke ratsata a hankali hakan ya tilasta mata buɗe idanunta,kallon shi take na ɗan wani lokaci kafin kuma ta kalli dakin sai zame ƙafarta tayi tana sauka,ba tare data ɗauki rigar ta ba tace" Thank"ta yi fatar ta,

Girgiza kai yayi yana mikewa canja kaya yayi ya fita,

Ita kuma tana shiga daki fadawa tayi kan gado tana sauke numfashi daga nan bacci ne ya dauke ta,
Ba ita ta tashi ba sai da Ammi ta aiko daya daga cikin masu aiki a tayar da ita ta shirya,
Da kyar ta buɗe ido ganin ƙarfe tara da rabi ne yasa babu shiri ta tashi zaune,sai

45 / 54