YAN MADIGO Book Compelet Hausa Novels By Oum Aphnan.txt

Author :  Oum Afnan Category :  True Life Story

Chapter   4 / 8

9K to 12K   out of 22.5K words

tsiyaya mata a ciki .

Nuna mata madaidaicin firinjin dake motar yayi kana ya tsiyaya nasa a wani cup din ya maida sauran muhallinsu, firinji din ya rufe kamar ba komai.

Caɓe baki tayi kamar goluwa “Taf aikuwa bazansha guba ba...”

Kafin ta rufe baki yakai drinks din da ya bata bakinsa ya fara ƙwalƙwala yana sha

“Aah wai meye haka ? Shanyewa kuma zakayi ne?”

“Inaso in tabbatar maki da cewa the drink is safe”.

Hannayenta biyu tasa ta warce a hannunsa “Uhm Ni wasa fa nike maka”

Takai bakinta ta kai masa wawiyar sip .
Wani zirrrrr taji kumfa ya kame mata baki kamar tana shan predator😂 da sauri ta sauke a bakinta ta wangale bakinta sama tana shanya shi wai ko zata samu gas din su fice .
“Aaaahhhhhh🥹”

Dariya ya fashe dashi har yana ƙyaƙyatawa “Kut easy easy ,Noor sunanki ko?”

Diddilo ido tayi “Kambu dama baka san suna na ba?”

“Eh mana ai baki faɗa mun ba sai yau da na ji a bakinki”

“Hmm Nooratu nake ,koda yake nima bansan sunanka ba”

Ta sake kai cup din a Baki ta ƙwalƙwala ,ta sake cirewa da sauri tana jan nishi “aahhh ” saboda yanda gas ke ƙoƙarin tunkuɗe mata haƙora.

“Noor easy 😂😂 Sipping akeyi ba ƙwalƙwala ba”

“Hmm wallahi akwai kata'in daɗine...anya ma ba giya bane kuwa?😱”

Cikin son ya zurmata yace “Kuma fa haka ne,ki sha a hankali karki fara maye”

Kumburo baki tayi irin na shagoɓaɓɓun nan “Taf wallahi ko giyane jinina nada ƙarfi sai na shanye tas!!!.....Kaji daɗinsa kuwa? Ba tsami ba zaƙi cuicui ,banma san yanda zan siffanta ba ,kawai ahhhhhhhh☺️” ta ƙare magana tana lumshe ido tana assimilating din garɗin.

Dariya ya sake fashewa dashi har yana tafa hannu,kana kuma ya ajiye cup din hannunsa ya tsaida kansa suna fuskantar juna ,wannan yasa taji kunya tadan sunkuyar da kanta.

“Oya fada mun ya kike yi?”

“Nikeyin me?”

“Yanda kike jin dadin rayuwarki a kullum”

Gyara zama tayi tana daƙwaƙo masa ido

“Kanaji ? In kana samun matsaloli wani kan wani ,yana binka back to back😆ga kudin haya ,ga yunwa ga bashi ga rashin kudin transport...ga...ga...wannan shi ake kira bamba to bamba.
Kawai watsarwa zakayi duka ka samo kudi kaci abinci kayi barci karka sama kanka damuwar ƴan bashi da sauransu ,to ya za'ayi? haka rayuwar ta gada”

Ta kare tana ƙoƙarin jingina da glasses din

“Kai motar nan naka akwai sany...(kafin ta ƙarike cewa sanyin ,tayi zumbur ta kalleshi tana Zaro masa ido) Yawwa wai ma motanka ne kuwan ko arowa kayi ?”

Murmushi yayi yana mamakin yanda take ɓaro magana hankali kwance “Nawa ne!! Wannan yana daya daga cikin motocin da aka biyoni dasu nan ƙasar”

“Kai ban yarda ba ,in Kai wanann mashahurin mai kudin ne ,ta ina nidin banzana zan ganka...gaskiya da saken lale”

“Hehehe😆I said I'll explain Noor”

Caɓe baki tayi kana ta rage murya ƙasa ƙasa “Wai noor☹️kaji gwalangwalaso”

Murmushi yayi yadan jingina ,yana jin wani nishadi a ransa ,sarai yaji murmur din da takeyi a kansa.

“Yawwa wai a American resort din kake zaune ?”

Gyada mata kai yayi

“Oh my goshhhh...na Manya masu kudine fa haka naji waii...waiii fa ana cewa dondai ban taɓa shiga ba ”

“To yanzu Ni a wani matsayi zaki saka Ni ? Ɗan shishigi nakai kaina inda Allah bai kaini ba ko kuwa dai mai kudin?”

Raurau da ido tayi kamar zatayi kuka tsabagen sallamawa ikon Allah yayi da aka shigo harabar resort din Mai kama da fadan wani shugaban kasan,ko'ina sojojine burjik suna gadin wajen.

A sanyaye cikin mutuwar jiki ta bashi amsar tambayarsa da “Nima ban sani ba🥹”







Oum Aphnan
09065990265
*ƳAN MAƊIGO*
_Lesbian gurls_

#Sympathy
#Empathy
#Sacrifices
#Seduction
#Pure luv💖

Oum Aphnan✍🏽
___________
Bismillahir rahmanir rahim

017-018
Nooratu a ɗarɗar take binsa feet by feet koina glasses ne ba maganar ginin bricks ,Gashi benayene sunyi hawa ashirin amma an lulluɓe su da glasses ,tarrrr wajen yake kamar rana ,tsoro da zullumine ya shige ta ,anya banyi kuskure ba? Anya Ni ba wawiya bace da nayi saurin yarda da mutumin da ban sanshi ba a wannan zamanin da muke ciki ? .
A haka suka shiga cikin lifter ya fara Hayewa dasu sama zuiiit zuiit zuiit haka suke wuce benayen ,tana ganin glasses na zipping from up to down .ƙirjinta kam bau fasa dukan fat ! Fat ba Saida taga ya tsaya ,daga nan ya danna kansa cikin wani ɗaki .
Sororo tayi ta tsaya a kofar wajen taƙi shiga sai raba ido take kamar mayyah .

“Zo muje” maimakon ta bashi amsa kawai sai ta fashe da kuka
“Ni kam don girman Allah karka siyar da wani sassa na jiki na ,wallahi Nine kadai fatan iyayena ,basu da kowa sai Ni ,kai a malejin rayuwar nan wallahi a haka nike aika masu da saƙo ,karka sabauta Ni don Allah"

Turus yayi yana kallonta “Noor Ni ba mugu bane ,ki yarda dani ,I'm here to open my mind ,but sai kin kwantar da hankalin ki”

Jinjina masa kai tayi cikin sallamawa

“...and follow me” ba musu ta biyoshi saɗaf saɗaf.

***
“Wannan shine ɗakina”
Zaro ido tayi tana kallonsa
“Nasan zakice to tayaya?”

“Da farko na shirya book na fita honey moon ne da matata ,and matata tana son sahara area ,don haka nayi book ɗin wannan resort din ,bayan auren mu da sati 1 ,zamu fara ta nan ƙasan ,kafin mu wuce sauran ƙasashen da muka tsara a list....”

Buɗe ido Nooratu tayi tar tar tana kallonsa

“To ina matar naka?”

“Taci amanata ,Ta zaɓe Ni over her friends ,I caught her red handed suna lesbians da kawayenta a kasar Canada,amma dukda haka ina sonta don haka na kasa hakura a kudurina na son aurenta...”

Cikin tashin hankali da tunzura Nooratu ta soma masifa

“Nikam wai me mata suke jine in sun iskanci da jinsin su ɗaya? Wait nasan zina babbar zunubi ne,amma shima lesbian din babbar bala'ine ga cututtuka da yake janyowa ,amma in zakasha giya kasha ta dubu ,yaseen da inyi lesbian gwara inbi namijin ma.... astagfrllh”

Girgiza kai yayi ya ɗan kwantar da kansa a kan kujeran da yake ,ya kasa magana ma saboda tuƙuƙin ɓacin rai.

A sanyaye tace “To yanzu ya ake ciki ina matar taka?”

“Tana can gidansu ,sai da na tura iyayena sanann tace ta fasa auren.”

Dafe ƙirji Nooratu tayi “Yanzu a yanda kake har akwai macen da zata fasa aurenka,ta tozartaka bayan kai ka rufa mata asiri?”

Wani Murmushi yayi mai ciwo
“Babanta shine shugaban ƙasan Nigeria ,kinga a yanzu Badrah tana da damar auren wanda ya fini ma”

Dafe ƙirji tayi “Ƴar shugaban ƙasa? Kai 😱kace kai din ma babban mutum ne ,tunda har kana iya shiga villa kai tsaye.

Murmushi yayi ya fiddo wayarsa ya shiga files din free wedding pics dinsu ya fara nuna mata da duk wasu events plans dinsu harma da hotunan iyayensu gasu a wannan kasan gasu a wajen wannan meeting din.

“Wow gaskiya yarinyar nan shuumar kyakyawace ,koda yake ba abun mamaki bane ba ,kasan haka kyawawa suke ko ƴar talaka ne akwai feelings ga high test ,Allah mudai mun gode maka”

“Hmm ,lokacine” ya bata amsa yana taune leben ƙasa.

“wannan fa waye shi mai ɗan farin gemu dashi duk ƙasumbarsa ya zama fari ,kai daga ganinsa kaga dattijon arziki ga kuma kudi...kai naga sai gaisawa yake da shugaban kasa..”

He chuckles “Baba na ne ,kuma aminin shugaban kasan ne,yayi shugaban majalisar dattijai,ya taɓa yin ministern man fetur yayi commissionern Labarai na Kano state ,kuma babbar ɗan kasuwa ne”

Diddilo Ido Nooratu tayi “Na shiga Aljanna ,kace kai din dan gata ne ,amma shine kazo restaurant din mu ka bari ina baka kyautan local food?”

Dariya ya fashe dashi “You Are funny ,ai ba'a damuwa da Arzikin mahaifa ,tunda bani kadai suka haifa ba ina da ƙanne maza da mata but nine babba....”

“Dukda haka kai ai ɗan wani ne ,mufa?”

“Yes Ni wanine ba ɗan wani ba”

“How?”

“Kinga mu ƴan asalin jihar Adamawa ne ,Kasantuwar babana yina business kuma ga siyasa yasa Ni nake juya masa duk wasu kasuwancinsa na kasashen waje ,while Ina karatu ,nima a haka na fara nawa business din ynz haka companonina na motoci da wayoyin hannu a tsakanin China ,Nigeria da Germany sunkai guda 15 ,shiyasa duk wani sabuwar mota da zata shigo africa Ni ake fara gani da ita.
So ...Bayan na gama makaranta ,sai kuma babana ya tsulmani harkar siyasa ,nayi kananun mukamai kama daga house of rep ,yanzu haka dai nine gomnan garinmu maici a yanzu....”

Zaro ido Nooratu tayi gamida dukan kirji

“yanzu kaine gomnan Adamawa ? Na shiga uku shine ka bari ina ta maka rashin kunya? Don Allah kayi hakuri ban sani bane ba”

“Ni ban damu da kasancewa na gomna ba ,I'm proud of my business a Koda yaushe,so ki ɗauka kina hulda da ɗan kasuwa Ahmed ba Excellency Ahmed ba”

Mika mata sassanyar drink da ya saka masa ice cubes yayi ,yana Murmushi ,cikin mutuwar jiki ta miƙa hannu ta amsa takai bakinta ,wani sanyi mai fasa hakori da gas da tsami² irin na manyan juices ne ya doki bakinta da maƙoshi.

A gigice ta furzar da nunfashi gamida rike kirji “Ahhhhhhhhh”

Da sauri ya waiga ya kalleta kawai sai ya fashe da dariya

“Ka bani ruwa ban ruwa,washh yawwa sai yanzu ya faɗa mun ciki...”




Oum Aphnan
*ƳAN MAƊIGO*
_Lesbian gurls_

#Sympathy
#Empathy
#Sacrifices
#Seduction
#Pure luv💖

Oum Aphnan✍🏽
___________
Bismillahir rahmanir rahim

19_20
“Plz one last favour...☝️”
Kar ta kafesa da ido ,kana ta fashe da dariya “Ai mai kudi baya neman alfarma,just feel free”

“Ina so in ba damuwa abokaina sun hada muna dinner da amaryata Plz ki fitar dani kunya zan nuna ki a matsayin matata ,in an gama shknn”

Duddulo ido tayi “Gajata dani zaka nuna a matsayin matarka? Wannan ai abun kunya ne”

“Karki damu ,indai asirina zai rufu I agreed ,and beside Baki da muni ,gaki da barkwanci kowa ya ganki sai ya soki ....Yes I enjoyed ur company”

Ya Bata amsa with affirmation ,saboda yanda yaga ta daddalo ido

“Hmm ynz dai is already night ,Idan aka gama dinner din karfe nawa zan koma gidan ”

“Then You can sleep over ”

Dukan ƙirji tayi gamida zumbur ta miƙe tsaye

“Allah ya tsari Gatari da saran shuka ,idan fa karuwan nan kake so akwai Junainah.... Roomate ɗina ne wallahi ta iya komai harda excess Ni sai in maka hanyarta...”

“Ni ba haka nike ba...”

“To nidai gaskiya ina zuwa aiki ya isheni rayuwar duniya...kai lallai yau koni ƴal iskane na bika in ki zuwa aiki gobe ogana ya koreni?ga bashi da ake bina ɓururu"

“Zan biya ki kudin albashin naki”

“Ha'an kasan kuwa ,bashin da na tara a kaina? Wlh albashina na wata uku bayi biya”

“Zan baki albashinki na wata goma”

Tafa hannu ta shigayi tana salati
“Ya tabbata haka Mazan nan suke yi ,suna cutan yara suna kashe iyayensu a tsaye”

“Haba relax karki mun mummunan fassara mana”


“To yaya ne? Kai bakaji kunya ba wai in kwana? In kanwarka ce ko ƴarka zakaji dadi?”

“Allah ya baki hakuri ,na yarda duk dare zan maidaki gida ,i promised”

**
Dinner fa ya haɗu ƙarshe ,taga baƙin fuska taga kyawawan maza taga masu kudi taga masu Naira da ɓannan dala ,amma da ta kalla Ahmed sai taga sarkinsu ne....Nooratu kam make over ta famfa ta cikin fitaccen Black wedding gown sai ƙyalli take ,lokaci daya ta sauya rankatakaf ,tasha adon gwala-gwalai komai yaji .
Ashe dama matan masu kudin ba abunda zasu nuna maka sai daura sutura?

Abokansa kam sun tayasa murna ,side talk din abokansa kawai takeji

“Wane yayi sa'ar mace ,gata nan full option koina ya cike”
Haba Nooratu najin hakan sai ta washe baki 😄Ayyah me gida sorry o ,jabuce duk karyace matar aro ce”

Su kuma yanda take washe baki yasa suke kara sonta “Gasky yayi sa'ar her Excellency ,daga gani bazata yi matsala ba ,talakawa zasuji dadinta.

Ta samu kyaututtuka masu dimbin yawa ,motoci ,compononi, diamonds da sauransu .

**
Hotel room din suka fara komawa ta sauya kayan jikinta ta maida nata na gargajiya,nan ta tsaya a gaban tulin kyaututtukan da aka bashi ,tana hoto ,atleast na nuna ma Junainah yau nima na shiga wajen manya ga hujja na....Hmm malama Nooratu Kamar a mafarki?

Tana jin motsin zai shigo ta yi maza ta kashe wayarta mai kama da gwangwani ,yana fito da hoto dishi ² .

Girgiza kai yayi gamida adana dariyarsa

“Dama duk naki ne ,zan kai maki gida ai,harda mukullayen motocinki da takardun campanoninki ai kin rufa mun asiri”

“Ni😳 Wallahi bana so ,so kake ace mun karuwa?!”

“haba wannan kalmar Kar in sake jinsa a bakinki ,bana so”

Yanda yayi maganar cikin ɓacin rai yasa ta nutsu “To kayi hakuri zan dauki abu guda daya a ciki sauran kai kyauta dasu”

Kallonta yayi sosai ,amma ba alamun wasa a tare da ita

“Ok je ki zaɓi abunda kike so”

Tsugunawa tayi a kan tarin kayan da aka rurrufesu a kwali akayi masu ado . Ta rasa wanne zata dauka saboda ruwan ido .

Sai daga ƙarshe ta dauki wani wanda matar shugabar kasar Niger ta bata ,ɗan madaidaici da kwalliyar furanni pinks

Murmushi tayi gamida rungumar kwalin “Nagode Allah ya baka mata na gari”

Caɓe baki yayi “Au shiknn ” jinjina masa kai tayi ,kawai sai ya ƙyaleta yabi bayanta rungume da kayayyakin da ta cire da gwala-gwalain don duk sun zama nata ,suka shiga mota,har gaban gidansu.





Oum Aphnan
*ƳAN MAƊIGO*
_Lesbian gurls_

#Sympathy
#Empathy
#Sacrifices
#Seduction
#Pure luv💖

Oum Aphnan✍🏽
___________
Bismillahir rahmanir rahim

21_22
Junainah lokaci daya ta nema barcin idonta ta rasa.
Akan gadon Nooratu tayi zaman en bori tana fiddo kayan da Nooratun tazo dashi sanka sanka ,tana sambatun so da ruɗewa
Gift din da Excellency ta Bata kyauta ta fiddo
“wow omg, diamond set.... Innalillahi ,Wow wow” ta sa hannu cikin sanɗa tana zaroshi a cikin jakarsa.
Ai tana cirosa sheƙi ya haske ɗakin

“Ahwnnnnnn oh my god🥹🥹” ta yi sauri ta ɗaga ta manna a wuyarta

“Babe kinsan menene wannan kuwa?”

“Abun wuya ne!”
“not ordinary my friend😫This is diamond kyautan millionaires...”

Ita dai Nooratu kawai zuru tayi ma kayan da ido she is not too excited ,barci kawai take so tayi ,coz tasan it's just a night mere ,tana farkawa will vanish ,don haka bazata dinga ɗaukin gaibu ba.

Junainah ɗagowa tayi ta kalli Nooratu kamar zatayi kuka ,jikinta rungume da takalmi da jakan da Nooratu ta cire na events din ,wato designers ne na zallah fata masu mugun tsada.

“Nooratu 🥹!?”

Ta kira sunan ta ,tana tale Baki kamar zatayi kuka ,muryarta a doshe.

“Nooratu ki kaini wajensa mana...ki ɗan haɗa Ni dashi ,I'll make sure na bashi lafiyayyen tausa ,kinsan manyan nan they love massage....sannan zanyi amfani da halshena in lashe masa abubuwansa kamar yanda nake koya maki kika kasa ɗaukan haske...”

A daburce Nooratu tace “Wallahi saida nace masa ina da Roomate yace baya so ”

“Come on babe ,don Bai ganni bane zhi yasa har ya kwaɗaitu dake,see beauty here abeg. Ga kyau ga body ,daga zaran na karkaɗa masa halitta ,naje gabansa na jujjuya masa bombom ,bebeeeh sai kwanan tashin zancen”

“Hmm bazaki gane bane ,mutumin nan fa ba ɗan iska bane ba ,don saida ya bani labarin ex dinsa that cheated on him ”

“Ke ba wani namijin da ba ɗan iska ba,it defense da kalar macen da ya gani ,so in ya sama full package haba....must fall amm”

“To nidai Nayi recommending dinki a wajensa and he denied ...Now give me let me see”

Ta miƙa mata hannu tana son amsan er akwatun diamond din da Junainah ta ƙanƙame a ƙirjinta.

Ji tayi kamar ta runtuma ihu.
Sam batason bata

“Junainah give me now”

Harara ta bankaɗa mata tanajin kamar ta kifeta da mari ,haka ta miƙa mata tana ƙunƙunai.

“Amsa ƴar baƙin ciki ( sai kuma ta ɗaga murya tana magana ,masifa masifa)
To yanzu ai kinga kinci taliyar karshe kin taimakesa ya fita kunya ya ɗan sammaki wainnan an wuce wajen,Amma da ace zaki haɗasa da full option mace ai da na tayaki rikesa muyi ta samun ƴaƴan banki within short period of time mun Zama young hajiyoyi...”

“Me kike nufi? Kina nufin Ni ba full option bace ba?”

“Aah nidai bance ba Amma ki kalleni dakyau anan ,ai kinga cikakkiyar mace gata nan ,dubanni fa,ai zaren ba kalar yadin bane ba” ta kare tana ɗan jujjuya jiki tana lifting nonuwanta daga cikin bras dinta

Caɓe baki Nooratu tayi “To a haka kuma ya zaɓe Ni na fidda shi kunya matsayin matar gomna ,kinga kuwa ko da a wasan kwaikwayo ne ai na cire tuta bare in a real life”

“Allah ya Baki hakuri ,but maganar gaskiya you're too fat ga tumbi"

“whatever”





0um Aphnan
*ƳAN MAƊIGO*
_Lesbian gurls_

#Sympathy
#Empathy
#Sacrifices
#Seduction
#Pure luv💖

Oum Aphnan✍🏽
___________
Bismillahir rahmanir rahim

23_24
Phone ringing at the stage..........
A hargitse Nooratu ta miƙa hannu zata dauki wayar nata tana ɗan lalube cikin magagin barci ta latsa koren madannin.

Murya a shaƙe irin na masu barci tace “Hel...Hello”

“Nooratu baki da hankali ko?”

A guje idonta ya wartsake jin Muryar oganta,nan wani irin haske gami da hasken rana ya cika mata ido ,kai ya akayi nayi rana haka? Da sauri ta kalli agogon bangon ɗakin.
Karfe sha biyu saura kwata.
Kenan Junainah fita tayi bata tasheni ba! Ko me nayi mata?

”Nooratu ba dake nike magana ba?”

Nooratu da ta manta ma waya takeyi da oganta a firgice tace “Au sorry sir”

Sosai abun ya tunzura shi ,nan kuwa ya soma spark

“Youre very stupid... Nooratu you're very very very stupid ,Ni Zaki barma waje babu kowa? Nafiki ƙaryar zama er bariki ,I suspected you right ,don haka kafin ki kashe mun waje na sallameki...”


“Hayyahhh🙆‍♀️Oga yahakuri mana...ɓaci rana ne wallahi barcine yayi mun nauyi”

“Yes You can enjoy your bed ,Amma Ina gargadinki nan da karshen wata duk inda zaki nemo mun kudina ki nemo mun in ba Haka ba ,en sanda ne zasu kama mun ke...shashasha”

Ɓarkewa da salati tayi tana kokarin bashi hakuri amma midis ya kashe wayarsa

A sanyaye ta bi wayar da kallo jikinta a mace.

”Wani rashin Sa'a ne yake bibiyana? Ya Allah duk talauci ne ya jamun haka....Allah ka amshi rokona zafi rana inuwa kuna yau ya zanyi ? Da yunwa zanji ko da rashin aikin yi? Ha'ah sai inyi ƙaura in bar Niger din ko dole ne? Da wani gwagwareren muryarsa irin na en wiwi,naki inje din ,dama na lura haushina yakeji tunda banje wajen fasikin da yakeson haɗa Ni dashi ba,banza kawali kawai ”

Lumshe ido tayi ta buɗe akan himilin kayan masu kudin da ta shigo dasu jiya.

“Kai wai dama gaske ne?😁😄”

A take ɓacib ran manager dinta ya wanke.
Taje da gudu gaban kayan ta rusuna

“Ni ba shashasha bane ,kai da azzalumin zuciyarka ne shashashu, iyakanta dai inje in Saida diamond Dina Nima in bude shago,na huta da zama a ƙarƙashin wani a na ɗura ma iyayena zagi unlimited...Shima bashinsa in biyasa shi da mai haya da

4 / 8