GUGUWAR ANNOBA Book 1 Part A By Abdulaziz Madakin Gini .pdf

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   1 / 1

1 to 1.5K   out of 1.5K words

GUGUWAR ANNOBA
Madakin Gini



BIRNIN KALUZA, ya shahara ko ina a cikin daular kasashen bakaken fata da ke kudancin
duniya, saboda girman Birnin da yawan jama'a, arziki da daukaka a fagen kasuwanci da karfin
mayaka.

Sarkin da ke mulkin Birnin Kaluza ya kasance gawurtaccen jarumi, kuma cikakken FASA TARO
a filin yaki.

A tarihin Sarki Yarduza sau biyu kacal! aka taba cinsa da yaki, shima akasi aka samu a lokacin
da za a yi yakin bashi da lafiya yana kwance yana jinya.

Sarki Yarduza mutum ne wanda ko kadan bai san wani abu wai shi tsoro ba, kuma sannan Allah
Ya bashi tsananin karfin dantse gami da hikima da basirar tsara yaki.

In dai Sarki Yarduza ya shirya yaki akabi umarninsa ba a saba ba to fa sai an sami nasara.

Sarki Yarduza yana da wani karamin gunki mai suna SALKAR, wanda shi yake bautawa.

Shi dai wannan gunki an yi shi ne da siffa irin ta mutum a zaune, amma fuskarsa ta Zaki ce

kuma akwai mashi a hannunsa.

Gunki Salkar an ajiyeshi ne a cikin wani daki na musamman wanda babu mai shigarsa face
Sarki shi kadai.

Duk sa'adda Sarki Yarduza zai fita yaki ko zai fita farauta ko kuma zai je wani rangadi sai ya
shiga dakin gunki Salkar ya bata kusan rabin sa'a sannan yake fitowa ya tafi babu wanda ya
san abinda yake yi a cikin dakin, amma dai an san cewa yana ganawa da gunki Salkar.

Sarki Yarduza ya yi imani cewa in dai ya gana da gunki Salkar kafın ya fiya yin wani a to fa sai
ya sami nasara komai bala'i, ko masifa, tunda ya hau kan karagar mulki hakan ke faruwa ba a
taba samun akasi ba.

Shi dai wannan gunki na Salkar ya gajeshi ne a wajen mahaifinsa, amma bai taba shiga dakin
gunkin ba sai a ranar da mahaifin nasa ya mutu, kuma kafin mahaifin nasa ya mutu sai da ya
sanar da shi yadda ake bautar gunki Salkar, amma bai taba yarda ya shiga da shi wajen sa ba
kuma ya gargadeshi da cewa kada ya kuskura ya gayawa wani sirrin yadda ake bautar Salkar
face dan da ya haifa.

A wannan lokaci Sarki Yarduza ko aure bai da shi sai bayan mutuwar mahaifin nasa ne ya yi
aure kwana biyu bayan ranar da aka dorashi akan karagar mulki.

Macen da Sarki Yarduza ya aura ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance, kuma aurenta da
Sarki Yarduza ya baiwa mutanen kasar matukar mamaki, saboda bata kasance 'yar wani
babban mutum ba, mahaifinta mafarauci ne boyayye a cikin daji wanda ba a ma san da shi ba.

Yadda abin ya faru shi ne:

Wata rana Sarki Yarduza ya fita daji farauta kwi kadai sai ya hango wata barewa a can saman
wani dutse tana kiwo.

Kawai sai ya sauko daga kan dokinsa a hankali ya daure dokin a jikin bishiya sannan ya sadada
a hankali ta bayan dutsen da wannan barewa ke kai ya dana kibiya akan kwari, ya ci gaba da
tafiya cikin sanda da buya.

Nufinsa shi ne sai ya je kusa da barewar sannan ya dirka ma ta harbi. Sannu a hankali Sarki
Yarduza ya ci gaba da tafiya har yai sa'ar kusantar barewar, ya zamana cewa bai fi taku goma
ba tsakaninsa da barewar.

Koda ya fara jan zaren bakarsa domin ya tafiya

sosa sai barewar ta dago kanta sama, yai sauri ya sunkuya kasa bata ganshi ba.

Barewar ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa tayi dan jim, sannan ta juya za ta sauka
kasan dutsen, sai Sarki Yarduza ya dago ya kasa tabe bakansa yana mai saita barewar.

Kafin ya saki kibiyar sai kawai wani tsuntsu ya dira kusa da shi. Karar kadawar fuka-fukan
tsuntsun

ce ta tsorata barewar ta fita da gudun tsiya. Cikin tsananin fishi Sarki Yarduza ya kaiwa tsuntsun
duka yai sama sannan shima ya falfala da gudu domin ya cimma barewar.

Sai da suka shafe rabin sa'a suna ta wannan tseren gudu a cikin dajin yana kai ma ta harbi
amma ya kasa samunta, sai asarar kibiyoyinsa yake.

Suna cikin haka ne barewar ta ruga izuwa saman wani tsauni mai tsawon gaske.

Koda Sarki Yarduza ya rugo da gudu ya kama tsaunin da nufin ya hau kansa sai santsin tsaunin
ya kwasheshi ya fado kasa tim.

Cikin hanzari ya mike tsaye ya sake kama tsaunin don ya hau amma sai ya kasa saboda
tsananin santsin tsaunin.

A sannan ne ya hakura domin ya fahimci cewa tsaunin ba zai hawu ba. Kawai sai ya tsaya yana
kallon barewar, itama ta rinka kallonsa.

Bai san sa'adda ya kama cizon leba ba saboda takaici.

Abu na farko dai koda zai sake harbin barewar daga kasan tsaunin ba zai iya samunta ba
saboda nisan da ke tsakaninsu.

Abu na biyu kuma babu yadda zai yi ya iya hawa kan tsaunin.

Bayan 'yan dakiku masu yawa sai yaji wani abu shuu! ya wuce ta samansa.

Koda ya daga kai sai ya ga ashe mutum ne rike da wata doguwar bishıya yana reto a sama, ya
cufi kan wannan tsauni.

Kawai sai ye ga mutumin ya saki jijiyar bishiyar ya dira akan wannan tsauni, ba tare da santsin
tsaunin ya kwasheshi ba, ya mike tsaye ya ci gaba da falfala gudu akan tsaunin yabi wannan
barewa suka kasa tsere.

Yana cikin gudun ya zare kibiya a bayansa ya dana sannan ya saita barewar ya sakar ma ta
harbi.

Take kibiyar ta soki barewar a ciki ta fadi kasa matacciya.

Mutumin ya karasa inda barewar take ya

dauketa ya saba a kafadarsa ya juyo ya fara saukowa daga kan tsaunin.

Saboda tsananin mamakin ganin wannan jarumtaka da mutumin ya yi Sarki Yarduza bai san
sa'adda ya zauna a kas ba dirshan yana kallon mutumin kawai.

Koda mutumin ya gama saukowa daga kan tsaunin Sarki Yarduza ya yi arba da fuskarsa sai ya
kara cika da tsananin mamaki.

Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin cewa ashe ba namiji ba ne, wata kyakkyawar
budurwa ce ta gaban kwatance ta tattare dogon gashin kanta ta daureshi tamau a bayanta
sannan tana sanye da riga da wando na fatar damisa.

Takalmin da ke kafarta ma da fatar damisa aka yi shi, wanda ya kasance daga iya kauri mai
zaren daure-daure.

Kai tsaye budurwar ta durfafi inda Sarki Yarduza ke zaune tana rataye da barewar a kafadarta.

Da isowarta daf da Sarki Yarduza sai ta duka ta kwashi gaisuwa tana mai cewa, "Gaisuwa a
gareka ya Sarkin sarakai, ga wannan barewa na zo maka da ita".

Cikin tsananin mamaki Sarki Yarduza ya

Kurawa budurwar idanu domin bai santa ba kuma ko labarinta bai taba ji ba.

"Ya ya aka yi ta san shi?" Nan take ya kudurce a ransa cewa lallai sai ya san labarinta.

Sarki Yarduza ya dubi kyakkyawar budurwar ya ce, "Na wa za ki sayar mini da barewar?"

Ba tare da ta maida masa da martanin murmushin ba ta ce, "Dinare dubu za ka biya".

Sarki Yarduza ya sake yin murmushi a karo na biyu ya ce, "Saboda me zan biya wannan
barewa da tsada haka?".

Budurwar ta ce, "Saboda ta gagareka kamawa".

Yarduza ya gyada kai ya ce, "Wannan gaskiya ne, amma ai hakan ta faru ne saboda ban saba
da wancan tsauni ba. Ma'ana ban lakanci yadda ake hawansa ba."

"Ko shakka babu zancenka dutse ne, rashin sabo ne ya janyo maka hakan.

Ni kuwa kullum sai na hau kansa sau bakwai saboda motsa jini."

Sarki Yarduza ya kara duban budurwar ya ce, "Gaya mini sunanki da labarinki?".

Koda jin haka sai budurwar tayi murmushi a wannan karon sannan ta ce, "Labarina na sayarwa

ne, idan za ka iya".

"Fadi farashinsa ko nawa ne zan biya".

Budurwar ta ce, "Bana bukatar kudi, sai dai idan ka amince na nemi wata alfarma guda daya a
wajenka, idan ka yarda za ka biya min ita ni kuma zan baka labarina".

Sarki Yarduza yai gyaran murya ya ce, "Ni kuwa in dai alfarmar da za ki nema akwaita a duniya
sai na yi miki ita".

Budurwar ta kyalkyale da dariya sannan ta ce, "Ai abu ne mafi sauki a cikin ikonka.

Abun da nake bukata shi ne ina da mahaifi wanda ya kasance tsoho tukuf, zan zo da shi gidan
sarautarka ya yi kwana bakwai yana kwanciya a gadon da kake kwana yana ci daga irin abincin
da kake ci, kuma a cikin kwanukan abincinka sannan ya dinga sanya sutura irin wacce kake

sanyawa kuma ya zauna a fada bisa kujerarka ta mulki ayi masa biyayya irin wacce ake yi maka
ta tsawon kwana bakwai kadai.

A ranar kwana na bakwai ne zan baka labarina kamar yadda na yi alkawari yanzu.

Idan baka amince da wannan sharadi ba to fa har abada ba za mu sake saduwa ba bare ka san
ko ni wace ce ko kuma ka san labarina. Me ka yanke

10

1 / 1

Chapters