Author : Autar Alheri Category : Home Of Novels
GIRMA AKAN GIRMA SOYAYYA MULKI ISA FINƘARFI RIKICI BAN MAMAKI DADAI SAURANSU DUK ACIKIN BOOK ƊIN *SAWUN GIWA*
Free
Book 1
Page 9 & 10
"Wanka yayi tare da wankan tsarki yafito, yazauna abakin bed ɗin yana mamakin wannan al'amarin dayasameshi, kusan minti 10 yana zaune ganin zaman bazemi anfaniba tamiƙe yafara jero sallar nafila tare da fawwalawa Allah lamarinshi.
Washe gari dasafe kuwa maisoon da anty meenah suka nufi harami yayinda Dr hareesh yanufi abiti, yauma maisoon ta haɗu da wannan dattijuwar cikin mutunci tariƙo hannunta tace "mama kece anan? Cikin farin ciki matar tarungumi maisoon kana tace "wlh kuwa nice Yar anan nayita nemanki bangankiba kinsan neman mutun awannan wurin abune me matuƙar wahala ashedai Allah yayi zamu ƙara haɗuwa. "Cikin murmushi maisoon tace hakane mama kinyi ɗawafinne? "Eh nayi yar nan ai yau tare da jikana nazo domin wannan ranar da abbanshi ne yau ko nace shize kawoni seda nayi ɗawafi yanzuma gayanan ruwa yaje karɓomin
"Masha Allah mama hakan yafi kyau gaskiya wannan wurin bayada daɗin shigowa babu makusanci. "Wlh kuwa ai ai shine abinda yasa nece shine zekawoni domin wannan ranar nadan Allah ya haɗani dakeba da bansan iyakacin abinda zefaru daniba wlh ngd sosai Yar nan ko sunanki ban bantambayaba. "Humm Karki damu mama ai duk abinda ya faru arayuwar bawa Allah ne ya ƙaddara masa Kinga kuwa shine yaturoni na fiddaki, sunana maisoon mama, tafaɗa adede lokacinda wani kyakkyawan saurayi yazo wurin. Masha Allah suna me kyau da nasaba gakuma daɗi Allah ya albarkaceki keda ahalinki maisoon. "Ameen ya Allah mama, Bara naje kar anty na tanemeni. "yawwa ƴata to yanzu idan kika tafi ina zan koma ganinki ? Gaya da angama aikin hajji zankoma Nigeria bansan yaza'ayi inƙara ganinki ba. "Dan murmushi maisoon tayi wanda yaƙara fitoda asalin kyawunta tace "Karki damu mama Nima a Nigeria nake da angama aikin hajji zankoma gida. "eye Masha allah to kibani nomber wayarki ta Nigeria Kinga idan munkuma zamu rinka zumunci ko ƴar tawa bazataje gidansa? "No mama zanje mana kawo wayarki nasaka Miki. "Yawwa kai YASEER bata wayarka tasakamin nomber tacewa wannan saurayin dayazo wanda tunda ya iso wurin hankalinshi da komai nakan maisoon, ahankali yamiƙawa maisoon ɗin wayar takarɓa tasaka nomber ta tukunnah tayi musu sallama tabar wurin. "Hajiya ina kikasamu wannan kyakkyawar budurwar Masha Allah? Yaseer yafaɗa yana ƙurewar maisoon dayariga tayi musu nisa da kallo. "Itace yarinyar danake baka labari wandda ta fiddani cikin waƴannan mutanen masu ƙananun ido. Murmushi kawai yaseer yayi yana sauke ajiyar zuciya Tare Da shafa screen ɗin wayarshi inda maisoon tasaka nomber ta, kana yariƙa hannu Hajiya sukabar wurin....itama maisoon tana isa inda tabarsu anty meenah suka wuce gida..
Yau tunda yashigo masallacin harami yake duban mutane taƙasan ido koda Allah zesa yaganta amma harya gama abinda yakeyi aka idarda Sallah begantaba, hakan yakoma gida zuciyarshi fall tunanin ta....afannin gimbiya saudat kuwa tana kulada rashin lafiyar ƴarta shine abinda yasa tadena tadawa mutane hankali akan rashin mutuncin da Maisoon tayi mata, amma yanzu alhmdlmulillah kursum tasamu lafiya harta fara takawa dakanta tafito perlor ko harabar gidan, hakan yasa yau gimbiya saudat shiga gum memartaba Sarki Hassan tabashi labarin duk abinda ya faru ƙarya dakuma gaskiya, kana taƙara dacewar ko a ina wannan yarinyar take tanaso yasaka ɗaure mata ita domin bazata taɓa bari tasha abanzaba. "Cikin izza da kamala sarkin makah yace "amma dai saudat kinsan cewar bazeyi nasaka akama wani wanda mutane basuga zahirin laifin dayayiba hakan zubda mutuncine agaremu mun tozalta yan ƙasar mu. "To ai ba ƴar ƙasarnan bace baƙar fata ce Kiga munada cikakken iko akan hukuntata. "Ajiyar zuciya yasauke ahankali kana yace "to shikenan abari agama aikin hajji tukunnah tunda kikace tayiwa kursum aiki to aƙarasar take zaune Kinga se musan abinda ya dace da ita. "Yawwa yayana shiyasa nake sonka bazaka taɓa bari na tuzaltaba, tafaɗa tana manna mishi kiss agoshi kana tafita daga turakar tashi.
*DARE ƊAYA WANKA GOMA*🍌🙈
HUMM KARKI BARI ABAKI LABARIN WANNAN SIHIRTACCEN MAGANIN ƳAR UWA, DOMIN KUWA DUK WADDA BATA SANSHIBA TO TABBAS TABAR BAYA DA ƘURA, *DARE ƊAYA WANKA GOMA* MAGANINE MA MATIKAR MAHIMMANCI AGUN NAMIJI DA MACE AMMA BAZANCE KOMAIBA IDAN KIN GWADA KECE ZAKI DAWO SA GUDUNKI, IDAN KUWA HAR KIKA GWADA BEMIKI AIKIBA, TO WLH ALLAH ƊAYA ZANBAKI KUƊIN KI, Game bukatar *DARE ƊAYA WANKA GOMA* ze iya tuntubar wannan nomber 👉 07037092176 domin za'akai Mikishi aduk inda kike afaɗin duniya.💃💃
*GYARAN JIKI, ƘIBA HIPS, NONO, HASKEN FATA* DUK AKAN ABU ƊAYA INGATACCEN GARIN BOBOTIC SABAYA, BAWAI NORMAL SABAYABA NO DOMIN WANNAN GA DAƊI GA BIYAN BUƘATA CIKIN ƘANƘANIN LOKACI. SEKIN GWADA ZAKI TABBATAR HAJIYATA INADA TABBACIN IDAN KIKA FARA BAZAKI BARIBA DOMIN KOWANNE BAKI YASON DAƊI GA KUMA BIYAN BUƘATA CIKIN SAUƘI,
MUNADA INGATTUN KAYAN MATA DA KUMA MAGANIN MAZA MUNADA KAYAN GYARAN JIKI SABULUN DILKA DADAI SAURANSU DUK ABINDA KIKESO HAJIYATA ZAKI IYA SAMUNSHI AWURINMU AKAN FARASHI ME SAUƘI.
GAME BUƘATAR GARIN BOBOTIC SABAYA ZE IYA NEMAN WANNAN CONTACT ƊIN 👉07073092176 KAYANMU BASUDA NABIYU💃💃💃
"Ke dallah daukemun kaya daganan abinda zancine bazaki iya riƙemun ba sekin ajiye awannan wurin? Shanshanci kawai, kursum ce keyiwa wata dattijuwar hadima masifa cikin harshen larabci domin kursum barada mutunci ko kaɗan wa halinta wana mahaifiyarta...cikin rawar jiki tsohuwar ke bata haƙuri kana taɗauki tiren tariƙe mata ahannu. Ahanki take ɗibar itatuwan dake kai tanaci cikin isa da taƙama. Sosai wannan baiwar Allah tagaji da tsayuwar ga hannun yayi sanyi sosai sabida yanayin tsufa gakuma nauyin kayan, amma haka wannan yarinyar tarinƙa cin kayannan kamar bataci sabida kawai wulaƙanci dacin zarafi. Ahakan kawai tsautsayi yasa tiren subucewa wannan baiwar Allah yafaɗi ƙasa sanida hannunta daya sanƙare...dafe ƙirji tayi da Bala in ƙarfi yana girgiza kanta tama kasa cewa komai sabida tashin hankali da tsoro,,,,Itako kursum ido tawaro tare da ɗauke wannan dattijuwar da kyawawan maruka seda ta kifa, adede lokacinda Junaid da Basam suka ƙaraso wurin cikin baƙar zuciya Basam yayi kanta domin yafi Junaid hasala,,dasauri Junaid yariƙeshi tare da girgiza kanshi yace barta yaya Basam idan baso kakeyi uwarta ta tada muna ɗan ƙaramin yaƙi agidannan ba kasa memartaba ya tsine mana dukkanmu barta duniya ce ita zata koya mata hankali, yana gama faɗar hakan yasaka hannu yaɗaga wannan hadimar yana mata sannu tare da riƙa hannunta zasu wuce. Cikin tsiwa da masifa kursum ke faɗar se wannan hadimar tazo tagyara wurinda ta ɓata, ko kallonta basuyiba suka shigewarsu cikin gidan.
Bayani ataƙaice.
Sarkin Saudia da gimbiya saudatt uwarsu ɗaya ubansu ɗaya su biyu kawai iyayensu suka haifa kuma Allah yajarabeshi da sonta shiyasa baya ƙaunar abinda ya taɓa ta ko kaɗan, gimbiya saudat tari aure kuma anan cikin masautar take zaune itada mijinta,,,tunda gimbiya saudatt yayi aure bata samu haihuwaba se akan kursum, inda taɗauki son duniya taɗora mata tareda sangartarda ita tana tabka tsiya kala kala...shiko sarki Hassan yanada yara huɗu, kaleel shine babba kamar sa'ar Sheikh sudais ne se Basam, sa'annan Junaid se autarsu mulaika..tofa dukkansu hakan suke zaune acikin gidan zata inda gimbiya saudat ke mulkinsu suda mahaifiyarsu gimbiya zaitun. Lokacinda Sarkin Dubai yagayawa Sarkin makah cewar ɗanshi zezo godanshi yazauna kafin yaƙarasa karatunshi domin baze lamunci yazauna wani gunba inda babu tsaro...sosai gimbiya saudatt taso yiwa yayan nata panpo akan karya bari ɗan wani sarki yazauna gidanshi. Amma seyace tabari karatu kawai zeyi idan yagama yakoma ƙasarsu...tofa tunda Sheikh sudais yazo garin Makkah suka Ganshi ba yadda sukayi tunaniba sukasha jinin jikinsu domin ko kwarjininshi baze bari surenashiba balle ga jinin mulki gakuma hasken musulunci da haibar Alqur'ani ataredashi kana ga kamala irinta salihan bayi masu tsoron Allah aransu, dama shi tsoron Allah da nagartar imani hasken Alqur'ani daban suke maida mutun acikin al'umma. Wannan dalilinne yasa suka shafa Mishi lafiya sema tsoronshi dayawanzu azukatsnsu, Itako kursum tunda tafora idonta akanshi taɗauki soyayyar duniya tafora mai babu wanda take so seshi. Shiko sarai yaganosu daga ita har uwarta kuma yagano nufinsu akanshi amma yayi biris da lamarinsu sabida miskilancinshi.
Kunji alaƙar dake tsakaninsu.
Suna shiga perlor suka samu mahaifiyarsu zaune dawasu hadimmai suna mata fitara wasu namata tausa yayinda wasu ke bata ƴaƴan itatuwa. Ahankali gimbiya zaitun taɗago tana kallon ƴaƴan nata da wannan hadimar kamin tamiƙe zaune cikin Dattako tace "mike faruwa ne Basam? Miyasameta? Basam dakejin kamar yafashe sabida takaici yazauns kusan gimbiya zaitun kawai yana sauke numfashi amma yakasa cewa komai. Junaid ne yabata labarin abinda yafaru awaje. Cikin takaici gimbiya zaitun tabawa wannan dattijuwar haƙuri tare da yimata alkawarin ɗauketa daga gidan tamaidata gidan ƙanwarta....sosai tayiwa gimbiya zaitun godiya koba komai zata huta da hantarar da jikarta kemata domin tayi jika da kursum....sukuwa zama sukayi suna tattaunawa akan matsalolin gidan na gwaggon tasu data addabesu annanne Junaid kebawa Basam labarin yadda gimbiya saudat sukayi da Maisoon lokacinda sukazo itada Dr hareesh. Sosai Basam yayi mamaki Aranshi yace dama zega wannan yarinyar wlh babu abinda ze hanashi aurota kodan taci musu uban kursum... haka dai suka zauna sunata jimamin abinda yadamesu..
Nigeria
Abbey na zaune a general perlor shi gefenshi fawan ne kezaune kanshi aƙasa cikin girmamawa yace "naji abinda kace abbey in sha Allah bazamu baka kunyaba dominni inamada wadda Nakeso na aura ɗin. "Masha Allah wacece hakan? Kanshi aƙasa yace banyi magana da itaba abbey Inaso idan mun dedeta Sena sanar muku. "To shikenan badamuwa ina saurarenka duk lokacinda kuka dedeta ɗin amma kafin lokacinda na ɗiba muku yacika banaso wani yazomin da shirmen banza daga kai har muhseen jawwal da fadeel dukkanku bazan ɗaga muku ƙafa ba. "In sha Allah Abba zamuyi yadda kace. "Allah yayi muku albarka tashi kaje abinka. "Ameen ya Allah yace kana yamiƙe yayiwa Abbey Sallama yafita da tunanin fal zuciyarshi gaya beko koshi da ƴammatanshi ba abbey yakirashi akan wani zancen aure.
"Muhseen ne tsaye acikin office ɗinshi yana safa da Marwa gabaki ɗaya maganganu da Mahaifin nashi yayi mishi akan zancen aure shi gaba ɗaya yarasa ta ina ze ɓullowa lamarin..turo ƙofar akayi aka shigo bejiyowa domin yasan Khamis ne abokinshi. "Yayadai friend? Cewar Khamis. "Humm bari kawai khamis wlh akwai damuwa. "Subhanallah tamifa? "Wlh abbey ne jiya yasakani agaba da zancen aure kuma har lokaci yasaka mana nanda 3 month narasa yazanyi. "Tofa 🤔 ikon Allah neman mata acikin wata ukku awannan zamanin ai kam dakamar wuya yanzu minene mafita? "Aiba neman matarne fitinaba yadda za'ayi ta amince shine fitina domin inada wadda Nakeso sedai amincewarta nake tunani. Dariya khamis yayi kana yace "to ai abin yazo da sauƙi sosai friend tunda akwaita amma wacece wannan dakake tunanin taƙi Amincewa da cikakken soja irinka ga kyau kuma ga kuɗi? "Humm bazaka gane bane duk abinda ka lissafa inda yaƙini akan basa gabanta domin itama tanadasu kyau kuɗi jin kai duk ta taɗa. "Wai wacce please? Humm zankaika kaganta amma bata ƙasar tana Saudiya zanje gobe in sha Allah nayi kwana biyar agama aikin hajji Sena ɗaukota mudawo kaminnan Nakeso nafara kamun ƙafa. "Duka naji amma sonake nasan wacece ita kafin kakaini gunta ɗin? Humm ƙanwata ce maisoon, yafaɗa yana lunshe kyawawan idanuwanshi tare da sauke ajiyar zuciya...wani irin waro ido khamis yayi yace maisoon ta Dady Usman?...!
SAWUN GIWA paid book ne akan 1k kacal 👌 banyadda kowa yakaranta min book bebiyani hakkinaba idan kinshirya biya zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA Bank, kana kitura shaidar biyanki awannan nomber 👉 07037092176. 🙏
Autar alheri ✍️
Downloaded from GNOVELS.COM.NG
This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/gnovels
Twitter : https://twitter.com/gnovels
Telegram : https://t.me/gnovels