Author : Binta Umar Abbale Category : Home Of Novels
kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*25&26*
Bacci ne ya fara fizgarsa kamar a mafarki yaji muryata a kunnansa, ya bude ido yana kallonta tana tsaye 'kerere a kansa. cikin 'bacin rai yace." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? tabe baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da takaicin abinda yayi musu, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.
Babu ladabi a maganarta tace." sai ranar da akayi hankali nima zanyi." Ya tsira mata ido yana kallo.
Tace." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."
Yana kokarin tashi zaune yace."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."
"Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya ne."?
Yana kokarin magana su kaji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana tsaye fa yana jiran Maigidan a waje."
Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana k'unk'uni.
Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, tace." Da alama dai wannan mutumin kudi yake bin ka."
Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa.
Tace." Kai har mai ka siya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bukatar auran 'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji."
Yace." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri."
Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta kama hanya ta fita daga dakin tana surutai.
Jallabiya yasa ya fita.
Wani shirgegen katon mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne.
Ya mika masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo."
Ba tare da ya rike hannun da ya mika masa ba yace." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba."
Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna kaji Uzuri na, ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka."
Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi maka duk da cewa a lokacin akwai wa'inda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min nawa asirin."
Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa.
'Yar dariya yayi irin wacce ya saba yace." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har gida na kawo maka kudinka ni kaina nafiso muyi rabuwar arziki saboda haka ka samu nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari, matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba.
Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka."
Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah."
Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli digon gashi babu kan sumul sai uban kyalli yake.
Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin hakkinsa.
****
Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har dasu zagin mahaifinta, duka ne kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da mahaukaciya.
Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai hankali take masa.
A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi sha'awa shine ta tu'ka musu na masara."
"Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci."
Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki aure shi kawai zaki dinga damun mutane."
Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi tace." Shahida ba wai bana so bane. Aa ni bana son kina zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba wallahi."
Tace." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri a kaina."
Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake."
Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba.
Ta kalleta da fadin." Ki dauko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin."
Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta.
Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado.
Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa ta zuba masa har da manshanu.
Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta dauki abincin za ta fita, Baban ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba.
Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin ya cinye ya dawo yace ya kai masa.
Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar.
****
Saminu Abbatuwa yayi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda yayi masa alkawari, shuru malam yaji shirwa, bangaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye.
Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar wankin ta d'aya a kiyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli alkalai da fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa.
Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa.
*Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳*
*LITTAFIN NA KUDI NE #500 SPECIAL 1K 0542382124....BINTA UMAR GTBANK, IDAN KATI ZAKI TURO #600 KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER 07084653262.....MUTANAN NIJAR DALA DARI SPECIAL JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO MOV*
[9/7, 10:42] bintaumarabbale: _MAJNUN!_
*'BOYAYYAN -ATTAJIRI*
_NA_
*_BINTA UMAR ABBALE🍒_*
_MANAZARTA WRITES ASSO_
_________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
*27&28*
Hakika duk wanda ya siyi rariya ya san za ta zubda ruwa, zahiri kuma wanda ya hau motar kwadayi to babu shakka za ta sauke shi a tashar dana sani, Hujaj cikin rashin kima da rashin arziki ya nufi gidanshi, da gashi sai singlet da gajeran wando domin ko da sanya tufafin jikinsa don ganin kamar zai samu nasara, sai gashi cikin hukuncin Allah an kwamushe shi, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko haka ya nufi gidansa cikin rashin kuzari da rashin kwarin gwiwa, in da Allah ya rufa masa asiri ma dare ya tsala babu wanda ya ga ne shi a hanya sai da ya zo shiga gidan ne sukayi arangama makocinsa mai suna Malam Habu yana nannade tabarma zai shiga gidansa, da sauri Hujaj din yayi nufin shiga gidan, ya ji Malam Habu din yana magana amma saboda kunya bai saurare shi ba, yayi saurin banko kofar gidan ya sa sakata ya kulle kana ya ja tsaki da fadin munafiki kawai.
Malam Habu ya girgiza kai ransa a 'bace da irin zubda mutuncin da makocin nasa keyi a gari, ko shakka ba ya yi daga can gurin sana'ar tasa ne aka wulakanta shi irin wannan, in banda zubda mutumci da son duniya mai za'ayi da sanar cha-cha! jahili shine ya dauke ta sana'a har yake fankama da ita, gidansa ya shiga da tunanin yanda zai tunkari makocin nasa da maganar zuwan Saminu Abbatuwa sannan kuma dole ne ya nuna masa kuskuran abinda ya ke aikatawa wannan shine zaman amana a tsakaninsu.
Fitowar ta kenan daga daki da buta a hannunta za ta shiga bandaki ya shigo gidan kamar wani 'barawo sai sand'a yake, shi kansa kunyar kansa yake tunda ya fara sanar ca-ca! bai ta'ba wulakanta irin yau ba.
Ta kalleshi da mamaki a tare da ita ta ce." Mai zan gani ni Talatu."?
Bai saurare ta ba ya nufi dakinsa da saurin gaske, ba ya so tayi kwakwazo har 'ya'yansa su tashi a bacci su san abinda yake faruwa.
Ta ja mutsiyacin tsaki da fadin." Allah ya shirye ka Jamilu wallahi na yi nadamar auranka." ranta a 'ba ce ta shiga bandakin tana tur! da halin mijin nata.
Wa she gari ya tashi zuciyarsa a 'kuntacce fargabarsa kada Saminu ya zo ya ritsa shi a gidan sai sauri yake fita.
"Wai ana sallama da mai gidan."
Wani ne yaro ne yake magana a gidan.
Gabansa ya fad'i! wai shin ya zai yi da wannan mutumin ne?
Luf yayi a dakin bai ce komai ba yana jin lokacin da Talatu ke fadin." Ka ce gashi nan zuwa."
Ya nemi gefan gado ya zauna yana tunanin k'aryar da zai girbawa mutumin.
Ta shigo babu sallama ballanatana gaisuwa, ta ce." Ka ji ana sallama da kai a waje ko.''?
Ya kalle da dan firgici a tare da shi ya ce." Na ji zan fita na same shi."
Ta ja dogon tsaki ta fita tana surutai, gabadaya Talatu ta raina shi, bashi da wata 'kima a idonta.
Kayan sa ya sanya ya fita yana cin kunu! sai dai yanayin yanda ya sami Saminun ya firgitashi, mutumin bai ta'ba bashi tsoro ba irin yau ba! amma sai ya jajurce yayi ta ma za! hannu ya mika masa da fadin." Malam Saminu barka da asubah."
Ba tare da ya amsa ba ya ce." Hujaj haka mu kayi da kai ."?
Yayi shuru bai ce masa komai ba.
Ya girgiza kansa yana hura katoton hancinsa ya ce." Lallai yau zan nuna maka asalin waye ni."!
Cike da burga da rashin gaskiya ya daga masa hannu da fadin." Ka ga Saminu ba fa za ka zo har k'ofar gidana ka fada min bakar magana ba, mai akayi akai dubu dari uku da hamsin da har za ka ishe ni da sallama wallahi na fi karfin haka."
Ya fusata! yana numfarfashi! fuskarsa na maiko ido cike da kwantsa ya ce." Kai har kana da bakin wata magana anan gurin wallahi i dan ba kayi wasa ba zan dau'ke ka na damfara ka da 'kasa! ni ba'a rai na min hankali."
Jin abinda ya ce yasa ya d'an tsorata amma bai nuna masa a zahiri ba, ya ce.'' Na so mu fahimci jun.......Ya katse shi da fadin." Jiya na zo da daddare ban same ka sai na barwa makocinka sallahu saboda haka bani da lokacin sauraran maganarka a yanzu." Wayarsa ya fito da ita "Eh gani a kofar gidansa ku 'karaso." Ya kashe wayar ya mayar da ita aljihu! Malam Habu ya fito da shirin tafiya kasuwa ya ga abinda ke shirin faruwa 'Yan sanda sun zagaye Hujaj daya na kokarin daura masa ankwa a hannu.
"Subahanallahi." Wannan kalmar ya furta yana kallonsa, kafin ya ce." Haba Saminu har an kai ga haka kuma? kayi hakuri ku fahimci juna mana.''
Ya ce." Malam Habu na dawo daga rakiyar wannan mara mutuncin bashi da gaskiya mugun makaryaci ne, saboda haka hukuma zata raba ni dashi."
Hujaj ransa idan yayi dubu ya 'baci sai gumi yake ya gaza furta komai bai ta'ba tsammanin mutumin zai masa haka ba.
Ya kalli yanda jama'a suka fara taruwa a gurin suna kallonsu abinda ya tsana kenan zubewar mutumci mutane na kallonsa da kima da mutunci amma Saminu ya ci masa mutunci a gari.
Hayaniya tasa Jamila fitowa kofar gidan, can ta hange su sun tasa k'eyarsa domin tafiya ofis dashi, da sauri ta koma gidan tana shedawa Talatu abinda ke faruwa, ko a jikinta ta cigaba da sabgoginta a fili ta ce.'' Shi ya janyo wa kansa cin mutumci saboda haka babu abinda ya shafe ni shi ya siya."
Yaran suka zauna jugum!-jugum! duk lalacewar sa, ba za su canza shi a matsayi a ubansu ba.
Wai a kace labarin duniya ba ya 'boya har gida labari ya same ta, da yake sana'arta ta jama'a ce, duk wanda ya zauna sai ya jajanta mata wasu kuwa munafurci ne ya ke sanya su maganar.
Shahida kam daki ta shiga ta ci kukanta ta koshi, ta rasa yanda za tayi da rayuwarta kunyar fitowa take saboda irin kallon da mutane ke mata dole sai sun nuna ta da tambayar Baba Asabe ita ce 'yar Hujaj wanda bai san ma shine mahaifinta ba to a ranar ya sani.
***
"Ranka ya dad'e iyakar hakuri nayi kawai abinda nakeso ku sanya shi ya biya ni kudi na domin akwai hidima a tare dani."
Officer ya ce." Saminu kaje kuyi sulhu a tsakaninku mu za mu shiga cikin al'amarin mutukar bai cika alkawarin da ya dauka ba, tunda dai ya ce yasa gidansa a kasuwa yana jira a bashi kudin a karshen wata to zamu zuba ido lokacin ya cika, idan ya sa'ba alkawari za mu shigar da 'kara kuto."
Fuskar nan a murtuke! ya ce." Ranka ya dad'e aure nakeso nayi a wannan lokacin nima ina da uzuri gaskiyar magana kenan wannan mutumin makaryaci ne na daina yarda da maganarsa."
Ya kalleshi da fadin." Saminu ni ne fa nayi alkawari cewa 'karshen wata ana bani kudin gidana zan biya ka kudin ka amma cin mutuncin da kake min ya isa haka muna gaban hukuma anyi komai a rubuce da kuma sharad'i ka kwantar da hankalinka zamu rabu