Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Arewa Pen
idanu
amma saiya kasa.Kawai sai yaja sarki suka wuce
izuwa cikin gidan sarautar.Har suka isa turakar
sarki yana lallaba shine yana tausarsa saboda a
fusace yake bisa ganin yadda wadannan tagwaye
suka ki gaishe su alhalin kowa a kasar yana
girmamasu.Saida Yarima Kamsus ya zaunar da
sarki a kan kujera a babban falonsa yasa aka kawo
masa ruwan inibi mai sanyi yasha sannan ya
dubeshi cikin murmushi yace yakai Abbana ka sani
cewa wannan ne karo na farko da aka taba samun
talakawanka wadanda suka ki risinawa a gareka su
gaishe ka.Abinda yasa na hanaka ka dauki mataki
a kansu shine da zarar kayi musu wani abu
alkadarinka ya karye tunda duniya zataji cewa an
sami wadanda suka zo maka da wargi har cikin
fadarka alhalin hakan bata taba faruwa ba.Da gani
sai ka luta da rashin da'arsu a wajen,kana tanka
musu shike nan ka daukaka darajarsu.Da sannu
zamu ga iyakar takamarsu kuma dole ne su
kaskanta a gabanmu.Lokacin da yarima Kamsus
yazo nan a zancensa sai murmushi ya subucewa
sarki Alkasim ya dubeshi cikin murna yace hakika
nayi babbar sa'a da ubangijina ya bani da mai
basira da hangen nesa.Na karbi wannan shawara
taka kuma nayi maka alkawarin cewar bazan taba
yanke wani hukunci ba a kan wadannan tagwaye
ba face bisa ra'ayinka.Koda jin haka sai Yarima
Kamsus yayi farin ciki matuka kuma ya sumbaci
sarki a goshi sannan yayi masa sallama ya fice
daga cikin falon ya nufi tasa turakar.Har Yarima
Kamsus ya isa cikin dakin baccinsa babu abinda
yake tunani face kyawawan idanun wannan macen
tagwayen.Tabbas ya taba haduwa da wannan mai
idanu amma ya kasa tuno da inda suka hadun da
kuma lokacin.Har Yarima ya isa kan gadonsa ya
kwanta bai iya tuno komai ba.Koda yaga cewa
yana bata lokacinsa a banza sai ya cire al'amarin
daga cikin zuciyarsa yaja mayafinsa ya lullube
jikinsa ya kama bacci abinsa.Kashe gari kuwa
sarki Alkasim bai fito fada ba har saida rana ta
take.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan
musamman bisa sanin cewa yaune fa za'a tafi
birnin Sarki Masarul Anjana.Nan take
★Abubakar Haleefah Physicist★
kowa ya gane cewa tsabar jin kai da IZZA ne yasa
sarki yaki fitowa da wuri domin ya nunawa duniya
cewa fa baya shakkar sarkin Aljanu Masarul
Anjana.Shima Yarima Kamsus ko fitowa baiyi ba
daga cikin turakarsa har saida kuyangi suka kawo
masa abincinsa na rana yaci ya koshi.A sannan ne
ma ya shiga kewate yayi wanka.Yana fitowa saiya
tsala uban ado na kure adaka.Shi kansa yayi
mamakin dalilin da yasa ya caba wannan
ado,maimakon ace yayi gagarumar shigar yaki
tunda tafiya ce mai hadari za'ayi.Nan take ya tuno
da wannan kyakkyawan idanu na macen tagwaye.A
karon farko a rayuwarsa sai yaji zuciyarsa ta buga
da karfi kuma yaji babu abinda yake so sama da
ganin fuskar wannan mace.Koda gama ayyana
hakan sai Yarima Kamsus ya dakawa kansa tsawa
a cikin zuciyarsa yace a kul ka sanyawa zuciyarka
son wata 'ya mace domin masu iya magana sunce
somi somin Hauka zub da yawu ne.Ba zaka taba
son wata ya mace ba face ra'ayinka yazo daidai da
nata kuma sai ka yaba da halayenya.Yarima yana
cikin yin wannan zancen zuci ne Boka Rausum ya
shigo cikin falon nasa da sauri hankalinsa a tashe
har yana tuntube.Da isowarsa daf da yarima saiya
zube kasa bisa guiwoyinsa ya kwashi gaisuwa
sannan yace ya shugabana kayi mana rai nida
sauran jama'ar da za'ayi wannan tafiya,kayi sani
cewa kai ne kadai zaka iya zuwa ka fito da sarki
yanzu muyi gaggawar barin garin nan.Rashin
tafiyarmu yanzu zai janyo mu kasa hallara a fadar
sarki Masarul Anjana a kan lokaci kuma zamu
fuskanci horo mai tsananin.Koda Boka Rausum
yazo nan a zancensa sai yarima Kamsus ya bushe
da dariya.Al'amarin daya kara firgita Boka Rausum
kenan hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe.Nan take yarima Kamsus ya kama kafadun
boka Rausum ya tashe shi tsaye sannan ya
dubeshi cikin murmushi yace yakai dirkar Birnina
kayi sani cewa idan giwaye biyu na fada to dukkan
namun daji saidai suyi kallo.Kai dan kallo ne
kawai,bai kamata ka tashi hankalonka ba.Sarki
Masarul Anjana da mahaifina manyan giwaye ne
biyu,sauran sarakunan duniya da sauran jama'ar
mutane da aljanu sune namun daji.Kawai ka zuba
idanu kaga yanda karshen rigimar zata
kasance.Tuni a yanzu labari ya riski Sarki Masarul
Anjana bisa taurin kan Abbana da rashin
tsoronsa,me yasa bai dauki mataki ba a kansa?Kar
ta san kar kuma sai an gwada sannan ake sanin na
kwarai.Muje can turakar ta sarki,yanzun nan zamu
tafi.Koda jin haka sai murna ta kama boka Rausum
ya juya da sauri suka fice daga cikin turakar
yarima suka tunkari ta sarki.Da shigarsu cikin
harabar turakar ta sarki sai suka iske sarki Alkasim
a cikin rafinsa na wanka yana nishadi abinsa,ko
kadan babu alamar cewa yana sauri ko shirin
tafiyar dake gabansa.Koda sarki Alkasim ya hango
Boka Rausum tare da yarima Kamsus saiya
kyalkyale da dariya yace me kukazo yi wajena
yanzu.Ashe tun jiya ba na gaya muku cewa sai
yamma zamu bar garin nan ba?Kafin sarki ya gama
rufe bakinsa tuni Yarima ya tari numfashinsa yana
mai cewa ai na sauya tsarin tafiyar saboda
wadansu dalilai masu mahimmanci.Koda jin haka
sai sarki ya turbune fuska kuma yayi tsaki.Nan
take ya fito daga cikin rafin babu komai a jikinsa
face wani gajeran wando.Wohoho duk wanda ya
kalli sarki Alkasim a wannan lokaci yaga irin kirar
karfin da Allah yayi masa ta manyan sadaukai dole
ne ya sallama kuma ya firgita saboda kirjinsa kai
ya kasance tamkar na zaki cike da gashi,ga tudu
da fadi.Gaba dayan jikinsa a murde yake cike da
kwanji gami da tarin jijiyoyi tamkar ba kashi da
tsoka bane,sai kace dutse aka jajjera.
Zidane Kd
SAI KACE DUTSE AKA JEJJARA.Nan take wata
kuyanga tazo da sauri ta gogewa sarki Alkasim
danshin ruwan dake jikinsa gaba daya.Kafin cikar
yan dakiku an kawo tufafi iri daya dana jikin
Yarima Kamsus an sanyawa sarki Alkasim sai
gashi shima yayi kyau sosai.Kai in ba don sarki
Alkasim yana da saje da kasumba ba da shima
za'a iya cewa matashine kamar dansa Yarima
Kamsus.Ba tare da bata wani lokaci ba aka gama
kimtsa sarki suka tafi izuwa babbar fada su
ukun.Dakaru da kuyangi na take musu baya.Da
isarsu cikin fadar kuwa sai suka iske gaba dayan
fadawa a tsaitsaye a bayan KARAGAR
MULKI.Abokan tafiya kuwa
wato,MAWAKA,MAKADA,JARUMAI da masu
BARKWANCI na tsaitsaye a tsakiyar fadar suna
fuskantar karagar mulkin.Koda shigowarsu sai
yarima ya kurawa abokan tafiyar idanu yana
kallonsu daya bayan daya yana kokarin yaga
wadannan bakin tagwaye amma wayam.Ko
Alamarsu bai gani ba.Ashe shima sarki ya lura da
hakan.Abinda basu sani ba shine a yau tagwayen
basuyi shiga iri daya ba,kuma basa tare a waje
guda kuma ita macen bata rufe fuskarta ba,amma
tayi wata irin shiga ta batar da kamanninta.Su dai
wadanann tagwaye basu kasance yan kasar Misra
ba kuma ba komai ne yasa suka shiga wannan
tafiya ba sai domin su dauki fansa a kan sarki
Alkasim bisa mahaifinsu daya kashe akan wani laifi
daya aika bisa rashin sani a matsayinsa na
bako.Wannan abu ya faru ne kimanin shekaru
bakwai da suka gabata.Akwai wata shekara da
akayi fari na ruwan sha a birnin Misra saboda
gurbatar magudanar ruwan garin sakamakon wani
mugun boka da yazo ya lalata ruwan garin ya
zuba matattun tsuntsaye a cikin ruwan don
gabatar da aikinsa na sihiri.Nan take sarki Alkasim
yasa aka kamo bokan aka tsire shi a bainar
kasuwa kuma ka kafa dokar cewa duk mutumin da
aka sake gani yayi ta'ammali da magudanar ruwa
kisa ne hukuncinsa.Bayan shekara daya da faruwar
wannan abu ne wani matafiyi yazo giftawa ta bakin
magudanar ruwan birnin Misra tare da
iyalinsa,matarsa da 'ya'yansa guda biyu mace da
namiji wadanda shekarunsu sun kai goma sha
daidai.Koda wannan mutum tare da iyalansa
sukazo giftawa ta gefen wannan magudanr ruwa
sai santsi ya kwashi dawakansu suka fada cikin
wani tabo gaba dayansu duk jikinsu da jikin
dawakan ya turbune da tabo.Abinka da rashin sani
sai suka mike tsaye suka shiga cikin wannan
magudanar ruwa tare da dawakan nasu suka kama
wanke tabon jikin nasu.Suna cikin hakane dakaru
sukazo suka kewayesu aka kamasu aka kaisu fada
gaban sarki aka gurfanar dasu aka fadi laifinsu.A
wannan lokaci Yarima Kamsus na zaune daf da
sarki kuma shima baifi shekara goma sha daya ba
a duniya.Ba tare da sarki Alkasim yayi wani
bincike ba sai kawai yace aje a kashe wannan
mutum.Nan take yarima Kamsus ya kama rokon
sarki Alkasim akan ya yiwa mutumin afuwa amma
sai ya ki.Iyalin mutumin na kuka suna ihu gami da
rukunkume shi amma sai aka fincike shi daga
jikinsu da karfin tsiya.Suna ji suna gani aka tafi
dashi ana jansa a kasa har aka isa tsakiyar
kasuwa,anan aka bankare shi akayi masa KISAN
GILLAH.Anan ne matar mutumin da yayan nasa
sukayi ta rusa kuka kamar ba zasu daina ba amma
babu wanda ya tausaya musu.Yarima Kamsus ne
kadai ya tsaya a gabansu yana kallonsu cikin
matukar tausayawa har yana zubar da hawaye.A
lokacin ne uwar yaran ta dauke su suka kama
hanya suka fice daga cikin birnin amma kafin su
kule saida macen ta waigo ta kurawa Kamsus
idanu ita dashi duk suna zubar da hawaye.Idanun
wannan macen sune abinda yarima Kamsus yake
ta kokarin ya tuno amma ya kasa.Lokacin da sarki
Alkasim da Yarima Kamsus suka iso gaban
karagar mulki suka tsaya suka fuskanci jama'a sai
yarima yayu wuf ya yiwa sarki rada a kunne yace
akwai matsala yakai Abbana,banga wadannan
tagwayen ba biyu kuma lallai ya kamata mu san
ko su waye su kafin a fita daga cikin birnin nan
domin zasu iya zama daya daga cikin
makiyanmu.Koda jin haka sai sarki yayi murmushi
sannan yayiwa yarima rada a kunne yace to
waishin wa kake tsoro ne tsakanin MUTUM DA
ALJAN?
SHIN SU YARIMA KAMSUS ZASU GANO
WADANNAN TAGWAYE KAFIN A BAR BIRNIN
MISRA?
ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN GAGARUMAR
TAFIYA DA ZA'AYI ZUWA BIRNIN SIN?
TSAKANIN SARKI MASARUL ANJANA DA SARKI
ALKASIM WAYE ZAI FIFITA AKAN WANI?
WACE CE ZATA ZAMO MASOYIYAR YARIMA
KAMSUS?
WADANNE ABUBUWAN AL'AJABI NE ZASU FARU A
BIRNIN SARKI MASARUL ANJANA?
Mu Hadu A MUTUM DA ALJAN Littafi Na Biyu (2)
Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen
Labari.
Daga Mai Debe Muku Kewa A Koda Yaushe.
Abdul'Aziz Sani Madakin Gini
Suleiman Zidane Kd 09064179602