Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Arewa Pen
busa
kahon tafiya farauta sarki Alkasim ne ya fara
wucewa gaba yana sauri sauri gudu gudu
ai kuwa sai yarima ya ruga gareshi ya take
masa baya koda ganin haka sai ramjis da hatyan
ma suka bisu da sauri....
Sannan sarkin yaki da sauran jaruman
gasar mutum talatin da shida, duk wanda
ya dubi wadannan jarumai arba in a lokacin
da suka durfafi dajin Darul Samjul yaga irin
surarsu kwarjininsu da kuma makaman yakin
dake jikinsu sai yayi zaton cewa zasu iya
hallaka gaba dayan mugayan halittun dake
cikin dajin to amma fa ga wanda yasan dajin
kuma yasan irin mugayen abubuwan hadarin dake
cikinsa yasan cewa ba zasu iya ba da shigarsu
sarki Alkasim farkon dajin Darul samjul sai
kowannansu ya nutsu hatta shi kansa sarki
Alkasim kuwa domin shine ma ya fara rage
karfin gudunsa yana nazarin gefe da gefensa
da kuma gabansa saboda tunanin cewa ko
yaushe wani mugun abun zai iya kawo musu
hari, nan da nan kuwa kowa yayi koyi dashi
domin baiwa kai kariya
dajin yayi tsit a cikin safiyar ba a jin sautin
komai face na kananan kwari da tsuntsaye
komai jarumtakar mutum gami da dakewar
zuciyarsa idan ya shigo cikin wannan daji
na darul samjul dole ne zuciyarsa tayi rawa
saboda yanayin hatta bishiyoyi da irin
duwatsun dake cikin dajin wadansu iri ne
na musamman wadanda idanu basu saba gani ba
sai da su sarki Alkasim suka shafe kusan rabin
sa a suna tafiya a cikin dajin ba tare da sun ga
wata dabba ko guda daya ba face kwari
irin su kunamai, macizai da sauransu dai
Al amarin da ya sa kowa ya fara kosawa kenan
har aka fara tunanin cewa anya kuwa wannan
gasar zata yiwu?
Watakila sai dai a fasa gudanar da gasar a
koma da baya zuwa can sansani tunda
gashi lokaci na tafiya ba a hadu da wata dabba
ko guda daya ba
A cikin wannan hali ne kwatsam aka hango
wata irin dabba ta musamman ta tunkaro
tun da sarki Alkasim yazo duniya bai taba
ganin irin wannan dabba ba bare kuma
sauran jaruman wadanda shekarunsu sun
gaza nasa dabbar tana yanayi da zaki amma
tafi zaki tudu da fadi kuma tana da gajeren
kahonni guda biyu a tsakiyar kanta masu
kauri da tsini, kirjinta a cike yake da gashi
mai tsawo har yana sharar kasa
a kofatun hannayanta da kafafunta akwai
zarazaran farata masu kaifin tsiya saboda
nauyinta idan tana tafiya sai kaji kasa na
rawa tamkar takun toron giwa da farkon
sa adda dabbar tayi arba dasu sarki Alkasim
sai taci gaba da tunkarosu ba tare da shakkar
komai ba amma da taga cewa suma kara
tunkarota suke babu shakkar komai sai ta tsaya
cak ta zuba musu idanu aka fara kallon kallo''
chai kaji manyan jarumai masu dakakkiyar
zuciyar yaki ehm nidai guyson wajan yaki
bana nan sbd haka bari na matsa gefe
Wohoho idan maza da maza suka hadu a
sannan ne ake sanin waye jarumi kuma waye
matsoraci tabbas dasu sarki Alkasim din
da kuma wannan dabbar kowa ya sha jinin
jikinsa yasan cewa ya gamu da gamonsa idan
ka dauke sarki Alkasim da yarima kamsus
,ramjis da hatyan gaba dayan sauran jaruman
a firgice suke tunda akayi arba da wannan dabbar
domin kowannansu da kyar yake iya daga
sawayansa yana ci gaba da takun kafafunsa
haka dai su sarki Alkasim suka ci gaba da
durfafar wannan dabba ita kuwa tana tsaye
kyam a inda take tana kallonsu kawai ko
motsi batayi. Koda dabbar taga cewa saura
baifi taku goma ba kacal a tsakaninsu sai ta
yunkura cikin bakin zafin nama ta juya da
baya ta falfala da azababben gudu na kwatance
nan mafa su sarki Alkasim suka bita aka
kasa mugun tsere hakika masu iya magana sunyi
gaskiya da sukace ba a sanin maci tuwo sai
miya ta kare.
Ana fara yin wannan azababben gudu ne aka
fara barin jaruman gasar a baya domin gudu
ne na kare iyawarka ko nace kare kukanka, Al amin Ahmed Misau Guyson
Sunana kenan shugaban zauran labarai page
sai da aka shafe sa a uku ana falfala gudu ga
dabbar a gabansu suna hangota itama tana
waigensu tana ganinsu amma sun kasa
cimmata ita kuma ta kasa bace musu da gani
A wannan lokaci gaba dayan jaruman gasar sun
sare sun zube kasa suna haki kamar ransu
zai fita saura mutum hudu kacal biye da
dabbar basu sare ba saboda bakin nacinsu da
juriyarsu
ba wadansu bane ba wadannan mutane hudu
face sarki Alkasim , yarima kamsus,
ramjus da hatyan saikuma guyson me rubuta labarin
duk sa adda sarki Alkasim ya waigo bayansa
yaga yarima dasu ramjis da hatyan na biye
dashi basu sare ba sai ya cika da mamaki
domin shi a zatonsa ba zasu iya kawowa
haka ba suna wannan tseren gudu alhaliin
dukkaninsu babu wanda ya ke amfani da karfin
sihirin tsafinsa, kawai suna amfani ne da
tsagwaron horon da suka samu na gado
dakuma juriya da jarumtaka Abu dai kamar wasa
har saida yarima dasu ramjis suka hada
kafada da sarki amma an rasa mutum daya
da a cikinsu wanda zai iya cafke wannan dabba
a wannan lokaci tazarar dake tsakaninsu da dabbar
bai wuce taku biyar ba babban abinda ya
dugunzuma hankalinsu shine ko kadan babu
alamar gajiyawa a wajan dabbar su kuwa
dukkaninsu sun fara gajiya da yin haki
alamar cewa nan da wani lokaci zasu iya
sarewa ko da suka fahimci hakan sai dukkaninsu
a lokaci guda suka daka tsalle sama suka
diro akan dabbar kowa ya kai mata cafka
kaico bala'i ba a sa masa rana kuma ita masifa
ba a san farkonta ba bare karshenta koda
wannan dabba taji an cafketa ta gaba da bayanta
sai ta fara kokarin kubuta nan fa aka
ruguntsuma da azababben fada atsakaninta
dasu sarki Alkasim ta rinka kai musu suka
da kahonninta cizo da hakoranta gami da
yakushi da faratanta da kafafunta su kuma
suka rinka gocewa suna gabza mata wannan
naushi iya karfinsu amma sai gashi tana
shanye dukan nasu tana makesu suna faduwa
kasa amma sai dai kaga sun mike zumbur
cikin bakin zafin nama gami da jarumtaka
a iya gwagwarmayar da wadannan jarumai
hudu sukayi a duniya basu taba haduwa da
dabba mai karfin wannan ba domin duk sa adda
.ta dako tsalle ta kawowa dayansu bangaza
da kirjinta idan ya goce duk abinda ta
doka da kirjin take yake ratattakewa ya
rugurguje ko da kuwa abin ya kasance
dutsene ko bishiya.
Ganin wannan al amarin yasa sarki da yarima
suka fusata ainun suka kara zage damtse
suna amfani da dukkan karfinsu akan
dabbar ramjis da hatyan kuwa sai suka
dan ja da baya suka zuba musu idanu suka
samu damar hutawa amma sai haki suke
ta faman yi kamar ba zasu iya ci gaba
dagumurzun ba
Lokacin da dabbar taga sarki da yarima naso
suyi mata illah saboda kai mata mugun naushi
da bugu suke ta ko ina har tana faduwa kasa
in ba don ma tana da mugun zafin nama ba da
tuni sun yi mata lugudan da zata kasa tashi
sai ta shammaci yarima kamsus ta doki gadon
bayansa da kanta
take yarima ya kurma uban ihu sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji kashin bayansa
ya karye sai gani aka yi ya kife kasa da ruf
da ciki
Koda ganin abinda ya sameshi sai sarki Alkasim
ya fusata ainun ya cafi makoshin dabbar da
hannayansa biyu ya kauta kasa ya danne kuma ya
shaketa iya karfinsa nan fa dabbar ta fara
kakarin mutuwa koda taji tabbas zata rasa
rayuwarta sai ta fara saran jikin sarki da
faratan hannayanta da kafafunta nan fa
jikin nasa ya rinka darewa jini na tsartuwa
sarki ya rinka kurma uban ihu saboda mugun
zafin da yake ji ga jiri na dibarsa amma saboda
bakin naci yaki yarda ya saki dabbar saboda
fusatar da yayi, abinda ya ayyana a ransa
kawai shine sai dai suyi ragas shi da wannan
dabbar tunda babu mamaki mugun dukan
da tayiwa dansa zai iya zama sanadin ajalinsa.
Lokacin da ramjis da hatyan suka ga halin da sarki
da yarima suka shiga sai suka kalli junansu
nan take suka daka tsalle a lokaci guda
suka kama wuyan dabbar da hannayansu a
sama suka murdeshi nan take dabbar ta
sulale kasa matacciya, shi ma sarki alkasim
ya fadi kasa a matukar galabaice jiri na dibansa
da jan jiki ya isa inda yarima yake kwance
ya mirgino fuskarsa sai yaga ashe da ransa amma ya kasa mikewa
ne saboda
mugun dukan da dabbar tayi masa a gadon baya
sarki yasa hannunsa ya shafi kasusuwan bayan
yarima sai yaji babu wanda ya karye tsabar
buguwace kawai tasa ya galabaita nan take
ya saki murmushin farin ciki...............
!
Nima kuma Guyson na saki murmushin
ajiye typing
ANAN NE KUMA LITTAFI NA UKU YAZO KARSGE
SAI MUN HADU A CIKIN LITTAFI NA HUDU DOMIN
JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARI
"