Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Romantic Hausa Novels
TURABAR GASKIYA
Part 3 littafin Yaki
Abdulaziz Madakin Gini
Sim-sim suka umarni da a raka su." dinga hada komatsansu, Sarkiya sa aka basu dawaka biyu
da 'yan rakıya mutun biyar ya Koda Lushmaira da Shadilat suka
Yan hada su da 'yan rakiva sai Lushmaira ta je gaban Sarki ta durkosa gabansa ch dauriva
idanuwanta na zubbar da bawanc ta cc. "Va Mahaifina za mu koma kan yanda umarninka va
zartar akanmu, said ina mai son shaida maka, zuciyarma ana tsananin son zuwa wannan fili na
yaki da za'a yi wanda bana tunanin akwaiwan yaki a nan gaba da za'a yi wanda yal girman
wannan yaki, hakika wannan ja ne da wanda yaje kallonsa shi kansa ju tabbata a girmamashi, a
saka thi a saw babban jarumi a wannan dunya, Abbana hakika ina mai bakin cikin
rashin zuwa na wannan yaki, sai dai ina mai bakin cikin sanar da kai tunda har na kasance
babu ni a cikin wannan tafiya to babu shakka ni da aure sai dai a cikin aljanna fiddausi.
Koda Lushmaira ta zo nan a cikin batunta sai ta mike ta ja da baya, izuwa ga 'yar uwarta da
kuma abokan rakiyarsu. Shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya nitse cikin tunanin maganganun
Lushmaira daya bayan daya, bai gushe yana tunani ba har sai da ya ga sun kama hanya suna
shirin tafiya sannan ya mike ya nufo inda take abisa dokin tana mai kokarin sakar masa linzami
ya yinda suke kallon, kallon da Yarima Zaiyan.
Sarki ya dubeta sosai kafin ya ce komai sai daga bisani ya cc, "Ya ke wannan 'ya tawa mai
biyayya ina son ki sanar dani dalilin da zai hanaki yin aure alhalin kina sane da cewar da aure
ne zaki samu cikar burinki na duniya wato da, ko
'ya ina son ki sani babu mamaki dan da zaki haifa ya zamu cikon farin cikinki ya zamo yayewar
rasa mahaifinki da ki kai tun yarintarki, ina mai son ki gagggauta kawar da wannan kudiri nake
na kin yin aure domin na shirya yin bikinki ta zarar mu dawo daga wannan yaki.
Koda jin wannan batu sai Lushmaira ta dago da idanuwanta da mamaki ta dubi Sarki Abu
zaiyan, shi ma ita yake kallo cikin kulawa, ta sauke idanuwanta cikin tunani, kamar yaya ayi
shagalin bikina alhali a duniya ban taba ganin namajin da naji ina so ba, kada dai Sarki ya ce ya
yi min mijin, in kuwa haka ne tabbas zan taba bijire masa domin kowa in har ban je wannan
yakin ba na hadu da jarumin da yafi kowane jarumi yin kwazo a filin daga to babu shakka
bazann taba sauyawa ba, in kuwa naje na gani jarumin da yafi kowa jarumtaka to shakka babu
shi ne zai zamo mijina, a rashin jarumin da zai soke
idon Macijiya Burukull Kursum.
Koda ta kara dago da idanuwanta ya kalli Sarki sai taga dai har a yanzu kallonta yake kuma da
dukkan alamu ya karanci abinda zuciyarta ke saka mata, dan haka sai ya yi murmushi, ya ce
"Za ki aure bayan mun samo nasara mun dawo gida, yake yata Jarumi da zai zamo mijinki babu
shi a cikin zuciyata, amma ina da tabbacin samun shi kafin dawowarmu."
Babu walwala akan fuskarta ta kada linzamin dokinta kai tsaye ta fara tafiya batare da ta bawa
Sarki Amsa ba, wannan dalili ne yasa zuciyarsa ta bugo ya ji wani irin a ranshi, nan take ya
kwala mata kira.
"Ya ke Lushmaira ina dalilin yin biris dani alhalin ina yin magana dake.?"
Bata waigo ba ta ce, "Ya Abbana na matsu da nabar wannan guri, bana son na bi abinda
zuciyata take kodirtamın, domin kada na bijirewa umarninka, dan haka
ina mai baka hakuri a bisa abinda na aikata."
Nan take suka jera tare da Shadilat kowace fuarta na zubar da hawaye, Sarkin yaki Safwan ya
dubi Sarki shi kuwa Sarki sai ya dubi Yarima Zaiyan, a lokacin da Yarima ya kautar da kai ga
barin kallon su Shadilat ya ci gaba da al'amarin gabansa domin kuwa abinda Sarki ya yi, ya yi
masa dai-dai.
Sarki yaki Safwan ya matsa kusa da Sarki cikin girmamawa ya ce, "Ranka shi dade kana ganin
barin su su koma yafi tafiya da su alkairi.?"
Sarki ya juyo daga barin kallon Yarima ya dubi Sarkin yaki, ya ce, "Nima ina barar shawara
gami da hakan, hakika na yi mutukar mamakin yanda suke da jarumta a halin da suka taimake
ni a saman tsauni, sai dai ko kadan bana son a ce an fita dasu filin daga domin dalilin son bai
kwantamin ba." zuwansu
Sarkin yaki ya yi murmushi ya cc, "Ba na tunanin za su yarda su wuce gida mamaki "Kamar
yaya kake nufi zasu tya Sarki Abu Zaiyan ya dube shi, cikin dawowa ke nan"
"Ya shugaba shakka babu domin kowa zucivarsu bata gida bake dava sun dauke kacokan sun
kaita filin daga, ya kake tsammanın Kura da Kare sun tafi neman nama babu Mage?"
"A lallai fa zata ji rashin jin dadi to amma mai kake tsammanin zasu vi idan sun je can."
Sarkin yaki ya yi murmushi akaro na biyu ya cc, "Ya shugaba kai za a tambaya domin kaga
gogewarsu."
Sarki ya dan sha mur kana ya ce "A dawo da su, amma da sharadi, sharadin kuwa kada su
dinga yawo har sai an isa filin kuma ko da an je filin dasu, kada dayansu ya kuskura ya fito su
adana kansu yanda sauran kamar matan da
TURABAR GASKIYA-3
MADAKI
muke tafe dasu suka adana nasu kan
Sarkin yaki Safwan ya yi murmushi ya kwalawa wani Babban badakarensa kira wanda shi ne
zai jagoranci mai da su gidan"
"Ku dawo ya kai Zarfun, Sarki ya bukaci dawowarsu amma kada su sake a cikin dakarun yaki,
su mai da kansu kamar dabbobin gida.
Gaban yarima Ya yi muguwar faduwa ya dubi Sarkin yaki ya ce. A wane dalili
Da jin haka sai Sarki ya bu shu amsa da cewa "Akwai bukatar su, amma ba a filin yaki ba.
Shadilat da Gimbiya Lushmaira suka zo suka fadi gaban Sarki cikin murna suna godiya.
Da ganin haka sai Yarima Zaiyan ya turbune fuska, ya bar gurin domin bai so hakan ba
Lokacin da aka cika sa a biyar a
wannan gurin sai Rundunata kara ta shi Aka ci gaba da tafiya babu ii babu gani.
A can bangaren su Sarki Tamas kowa tuni tafiva ta yi nisa duk kasashen sun hadu guri guda,
fushi ne mai tananin a fuskokinsu cikin tafiyar takana da thu habu ruwansu da ibadu, dan kuwa
babu abinda yake tsayar dasu face gastya, ko cin abinci Sarakan su uku su kwashe manyan
dakarun sun saka su a tsakiva dan kyautata tsaro.
A wani faffladan daji mai yalwar korayen ganyayyaki suka Sarki Tamas ya yi umami dan a tsava
a kara shiri na sosal domin kuwa sun fara jiyo kamshi abokan gaba.
Lokacin da Rundunonin mayaka wka kafa sansuna sai kowa va fara aiwatar da abinda ke
gabansa a can kuwa babbar Tanti da Sarakan uku suka kadaice sai Sarki Tamas ya dubi Sarki
Madham da Sarki Husaka ya ce.
TURABAR GASKIYA-3
MADAKI
Ya zame mana dole mu yi shirin na sosai kafin a ce sai da muka riske su, tafiyarmu haka kai
tsaye ga makiya bata nufin samun nasara kuna sane shi dai yaki dan zambo ne musamman
wannan yakin da zamu yi shi da Birmin Lautul Nusur, suna da mayaka masu naci da dagiya
wajen ganin sun samu nasara, abinda zuciyata take raya min tun dazu shi ne, ina son mu
kasance ciki batancen shiri ga abokan gabarmu, ma'anar Satancen shiri shi ne ina son mu ware
wata Runduna ta tafi izuwa bisa hanyar da za su nufo, kafin zuwa filin da muke tunanin hadu,
su wadannan Dakaru su zamo sun boye kawunansu cikin ciyayyai ta yanda babu yanda za'a yi
su Sarki Abu Zaiyan su fahincesu a gun.
Idan suka wuce su, kafin su yi masu nesa sai su zari masu da kiboyu su yi musu ruwansu,
bayan haka sai su yi rufdugu kansu, su yi dauki badadi koda na sa'a
bakwai ne, na tabbata idan haka ta faru, zasu samu nasarar hallakar da yawa daga cikin
Dakarun Sarkin Abu Zaiyan duk da cewar na tabbata babu daya daga ckin Rundunarmu da
zasu tsira, ya kuke gani shawarar nan ta yi ko kuwa akwai wanda zai bada wacce ta fita."
Da jin hakan Sai Sarki Husaka ya yi ajiyar zuciya ya dubi Sarki Madham ya cc, "Ni dai wanitan
shawara ta yi min sai dai kai, ya kake gani.?"
Sarkin Madham sai ya tuntsire da dariya ya ce.
"Babu sake, wannan shawara ta yi, kuma na yaba da kwazo wajen yin wannan zurfin tunani sai
dai yanzu kamar yaya za a samar da dakarun da zasu iya yin wannan aiki kasan fa dole a samu
masu iya lambo da basaja cikin korayen ciyayi.?"
Koda Madhan ya zo nan a batunsa sai Sarki Tamas da Husauka su ka yi shiru daga bisa sai
suka dubi juna, Sarki Tamas ya yi saurin cewa "Ai babu Rundunar da zamu zaba dan yi mana
wannan aikin face Rundunar Sadauki Aksar, ba dan komai ba su ne maharba, kuma duk inda
aka san maharbi an san shi da lamfo a bayan bishiya dan haka shi ne zai jagoranci wannan
aiki."
Nan take sukai na'am da wannan ba tu take aka kira Sadauki Aksar aka sanar dashi abinda ya
zai yi. Batare da bata lokaci ba ya aminta cikin gaggawa suka zame jiki daga cikin sahu-sahu na
Miliyoyin rundunonin yaki suka face daga sashin suka nufi hanyar da suka durfafa.
A bangaren su Sarki kuwa tun da suka ta shi daga wannan guri sai suka ci gaba da tafiya ba
tsayawa ya da zango in har ba sallah ba ko cin abinci, a haka suka kwana hudu, gajiya ta riske
wasu daga cikinsu da yawa, lokacin da suka kwana na biyar ne sai murna ta kama wasu su
domin sun san cewar yanzo ne lokacin da za zauna domin a huce gajiya ta tsahon sa'a shida
maimakon ta rabin sa'a da suke idan zasu yi sallah ko cin abinci.
A wannan rana da rana ta cika na biyar kowa yana sa rai da Umarni Sarki amma Sarki ya yi
shiru ya ki ya bada umarni tsayawa, tafiya kawai ake, aka tsaya aka yi sallah Azahar aka ta shi
aka ci gaba da tafiya, aka la'asar nan ma aka ci gaba da tafiya, magriba isha'i a sannanc Sarki
ya yi umarni da a tsaya a nan a huta.
Kowa ya fitar da tsammanin hutawa, a ranar irin ta yau, dan haka lokacin da suka ji umarni sai
kowa ya cika da farin ciki, kafin ma a fara kafa tanti wasu suka zube kasa, Yarima Zaiyan da
Gimbiya Lushmaira da Shadilat kuwa suna jin wannan umarni sai suka cika da tsananin bacin
rai domin a san su, ba za'a tsaya ba har sai an isa dajin da za'a fara wannan yaki.
Mu hadu a part 4