TURBAR GASKİYA Book 12 By Madakin Gini .pdf

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Hausa Novels 001

Chapter   1 / 1

1 to 2.2K   out of 2.2K words

TURBAR GASKİYA
Book 12
Rubutawa
MADAKIN GINI
arewanovels.com.ng


Shaka masa wannan Banjo din.
Aka ci gaba da yakin kamar Sarki bai ji komai ba, suna cikin yaki Sarki ya shammace Sadauki
ya karya masa wuya ɓaras.
Ai kuwa kafin ya sake shi wani Sadauki da ake kira Himanu ya fusato ya fito da karfi ya taka
Sarki, Sarki Abu Zaiyan ya mirgina kasa ya mike cikin dauriya, kafin ya kara yin wani yunkuri
Hirnanu ya kara yin dirango a bayan Sarki ya kirbawa Sarki naushi a mukamuke ya kuma zare
takobi da niyar ya sare masa kai amma sai Sarki ya baje a kasa ya kuma kwashe kafafuwan
Hirnanu.

Nan take Hirnanu ya zube kasa, Sarki ya ya kama kansa ya danna a cikin kasa, aduk girman
Hirananu sai ga shi ya kasa kwacewa ga shi kuma sai tirjjiya yake saboda tsananin walaha
babu damar shakkar numfashi sai dai kasa da yake
shaka Sarki Bai daga shi ba sai da ya ga ya daina motsi.

Nan ma Sarki bai daga Mataccen ba wani sadauki ya kara yo sufa ya dake shi ta baya Sarkı
Abu zaiyan sai ya fadi kasa kuma ya kasa ta shi. A wannan yakin da aka yi su Sarki tarmas
suna ganin cewar gubar bata samu shiga Sarki ba amma ganin ya kasa ta shi sai suka kama
murna domin sun san aikinta ne.
Koda Wannan Sadauki ya kara yo tsalle sai ya kama Sarki da niyar ya jashi a Rasa, amma sai
Sarki ya cije, yaki ya jawo shi kuwa Sadauki sai kokarin janshi yake a cikin wannan lokaci ne
aka ga jikin Sarki ya saki nan take ya fara yin amai, aikuwa nan Sarki Yaki Safwan da kuma
Yarima Yazid suka kamo da tsananin firgici har ya zama sun yi rige rigen tasowa amma Sarki na
ankarewa da su sai ya daka musu tsawa da su dakata, shi kuwa wannan Sadaukin
koda ya jawo Sarki Gaban Sarakan Sai ya cire wani katon gatare daga jikinsa ya daga shi zai
sare kan Sarki, har idanuwan jama'a ya rufewa kawai sai gani akai Yarima Yazid ya taho cikin
iska ya doki wannan Sadauki ya fadi kaka ya fada kan gatarin ya cire masa makogaro cikin
sauri ya dauke Mahaifinsa da yake ta faman a man jini ya kaishi sansaninsu. Kafin ya dawo filin
dagar kuma sai suka ji wani irin nishi mai karfi ya karade filin gurin baki daya, wannan al'amari
sai ya dugunzuma hankalin duka jama'ar da suke wannan gun, suka saka idanuwan sosai.

Aikuwa kafin kiftawar idanuwa Sai ga Macijiya Burukul Kursum ta bayyna cikin tsananin tashin
hankali.

A nan take Yarima Zaiyan ya dakata da yunkurinsa domin daga zuwanta har ta yabcari kadan
daga cikin al'umınarsu ta yi musu loma daya.

TURBAR CASKIYA
MADAKIN GINI

Daga Abdul aziz sani madakin gini mai debe muku kewa akowane lokaci sai mun hadu a cikin
littafi na biyar dan jin ci gaban wannan labari na TURBAR GASKIYA

SHIN SARKI ABU ZAIYAN ZAI SAMU LAFIYA?

WAYE ZAI KARASA KARAWA DA WADANNAN ADAWAN DA SU SARKI HUSAKA SUKA ZO
DA SU?

SU WAYE ZA SU NASARA A CIKIN WANNAN GAWURTACCEN YAKI A TSAKANIN
RUNDUNAR MUSULUNCIN KUMA RUNDUNAR KAFURCI? DA

YA YA ZA AKWASHE DA MACIJIYA BURUKUL KURSUM A CIKIN WANNAN HALI

A TSAKANIN SHADILAT DA GIMBIYA LUMSHAIRA WACECE TAFI KAUNAR YARIMA
YAZID.?


GIMBIYA LUSHMAIRA ZA TA YI HAR TA ZAMO YARIMA YAZID ZAI AMINTA DA
JARUMTAKARTA.

Sai mun hadu a littafi na biyar




Kaɗan Daga Littafi


JIHADI

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude bayan shudewar mulkin fir'auna na birnin misra
an yi wata azzalumar sarauniya mai suna Zuhaira bin Masrud.

Sarauniya zahuira tana mulkin wata babbar kasa ce dake bakin gabar tekun bahar sufiya kuma
ta gaji sarautar ne a wajen mahaifinta sarki masrud bin Zaurid

Sarki masrud ya kasance gawurtaccen mayaki wanda yai shuhura zamaninsa kuma shi a
rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da ma'abota addinin musulunci ba komai ne ya haddasa

mummunar gaba tsakaninsa da ma'abota addinin musulunci ba face akwai watarana da
wadansu fatake ma'abota addinin musulunci da suka zo giftawa ta birninsa, sai suka yada
zango a gefen garin domin su yada zango.

A wannan lokaci akwai wani takadirin aljani a cikin birni na Sufras wanda muatena ke
bautawa a matsayin ubangijinsu. A kullum sai an yankawa wannan aljani raguna uku, shanu,
uku da rakuma uku, kuma Sarki masrud ne da kansa yake jagorantar wannan hadaya da ake
yiwa aljanin mai suna burrata.

A ranar da wadannan fatake suka ya da zango a bakin birnin Sufaras ne wata annoba ta zo
bimin ya zamana cewa gaba daya dabbobin garin da tsuntsayensu sun kamu da wata irin cuta
ta gudawa don haka sai suka rinka mutuwa wasu kuma suka lafke ya zamana cewa ko ta shi
basa iya yi.
Bisa ka'idar hadayar da ake yiwa aljani burrata ana yanka masa lafiyayyun dabbobi ida kuwa
aka kuskura aka yanka masa mara lafiya koda guda daya ne kacal a ranar babu wanda ya isa
ya yi barci a garin kuma duk kanannan yar dake garin sai sun kamu da cutar da zasu yi ta
mutuwa haka kuma idan aka saba lokaci na yin wannan hadaya to fa sai wannan bala'i ya afko.
Sarki marud yana samun dukkan biyan bukatarsa a wajen aljani Burrata bisa wannan dalili ne
baya yarda a sami matsala a ko kadan akan yi masa hadaya.

Lokacin da ake yin wannan hadaiya ga aljani Burrata da yammaci ne sakaliya daf da magruba
tun da rana wannan annoba ta afku a cikin birnin na Sufras al'amarin da ya dugunzuma
hankalin Sarki masrud ke nan ya baza dakarunsa ko ina a cikin birane da kauyuka na kusa a
kan a nemo lafiyayyun dabbobin da za'a yankawa aljani Burruta kafin rana ta fadi.
Ai kuwa har gefen la'asar ba'a sama dabbobinba sai ga Dakarun da aka tura sun dawo cikin
gigita da dimauta, shugabansu ya zube kasa a gaban Sarki masrud ya ce, Ya shugaba mun
duba ko ina a cikin birano da kauyuka dake kusa da wannan kasa tamu babu inda wannan
annonba bata je ba, mun rasa lafiysyyun dabbobi amma akan hanyarmu ta dawowa mun ga
wadansu bakin fatake kuma suna da dabbobi lafiyayyu fiye da adadin da muke bukata.

Koda Sarki jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Sarki Masrud ya ce, "Maza ku koma wajen
wadannan fatake ku siyo daddbobin da muke bukata a wajensu komai tsadarsu kuwa, idan
suka ki siyar muku ko kwato su da karfin tsiya ku zo mini da su, domin mu hanzarta zuwa
Koda jin wannan batu sai Shugaban dakaru ya mike tsaye da sauri yann mai eewa an gama ya
shugabana, nan take yn jagoranci dakarunsa kimanin su dari biyu suka hau dawakarisu suka
zaburesu da gudu izuwa gfen gari

Su dai wadannan fatake da suka ya da zango a gefen birnin sufras gaba dayansu basu fi su
ashirin ba kuma duk zur'a dayane na wani attajiri da ake kira Abu Salhaif

Acikin wannan Zuri'a akwai matarsa guda daya da kuma dansa shima guda daya jal wani
matashin saurayii wanda baisfi shekara goma sha hudu ba, shi ake kira da suna Salhif, sauran
mutane goma sha bakwan daga kannensa sai matansu, da 'yayansu.

Abu Salhif na tsaye tare da dansa Salhif yana koya masa yadda ake yaki wato suna kaiwa
junansu sara da suka cikin gwaninta a gefe daya kuma matarsa da sauran abokan tafiyar na
tsaye suna kallonsu sai kawai suka hango kura daga can riesa ta turnuke sama, sannu a
hankali suka hango dakaru bisa dawakai a sukwane sun durfafo A zaton su Abu Salhif yanfashi ne suka kawo musu hari, har mazajen cikinsu sun yunkura zasu
zare makamansu su tari mahayan sai Abu Salhif ya daka musu tsawa, ya hana su, don haka sai
kowa ya tsaya a inda yake har mahayan suka kara so daf da su suka yi turjiya suna sanye cikin
kayan yakin dakarun birtin Sufras.
Koda Abu Salhif da jama'arsa suka ga cewa ashe dakarun birnin Sufra ne sai hankalinsu ya
kwanta suka mayar da takubbansu cikin kufc.

Cikin biyayya Abu Salhif ya risina ga shugaban dakarun ya yi gaisuwa sannan ya ce, "Ya ku
Dakarun Sarki Masrud me kuke bukata daga garemu har da zaku kawo mana ziyarar bazato a
irin wannan lokaci alhalin ko shigowa cikin birnin naku ba mu yi ba?

Koda jin wannan tambaya sai Shugaban Dakarun ya sauko daga kan dokinsa ya matso daf da
Abu Salhif ya ce, "Ya kai wannan attajiri tsohon abokin. cini kinmu ka yi sani cewa Sarki ne ya
tro mu gareku domin ku siyar mana da raguna uku, shanu uku rakuma daga cikin
dabbobinkudomin mu bayar da jinin su ga abin bautarmu gunku Burrata."

Koda jin wannan ba tu sai hankalin Abu Salhif ya dugunzuma ya ce, "Subhanallahi ya kai
wannan badakare ka yi sani cewa mu musulmai ne wadanda suka yi imani da bautar Allah
Sarki guda daya wanda shi ne ya halicci komai da kowa har da shi gunkun da kuke bautawa, ta
yaya zamu bayar da dabbobinmu kujo ku aikata wannan mummunan sabo da su, ai idan muka
baku tamkar muma mun yi imani da abin da kuke bautawar ke nan, ku koma ku gayawa Sarki
Marud cewa ni attajiri Abu Salhif nace ya yi hakuri ba zamu iya siyar masa da dabbobinmu a,
koda jin wannan ba tu sai shugaban dakarun ya tari numfashin Abu Salhif yana mai daka masa
tsawa ya ce, "Sarki ya barnu umarni idan har baza ku bamu wadannan dabobbi ba lallai mu
karbe su da karfin tsiya koda jin haka sai Mazajen ayarin na Abu Salhif suka zare takubbansu
da nufin su yaki dakrun Sarki Masrud, amma sai Abu salhif ya sake daka musu tsawa a karo na
biyu ya ce, "Baku da hankali ne ta yaya zaku iya yakar dakarun kimanin dari
biyu alhalin gaba dayanmu bamu wuce mu goma sha ba."

Nan take mazajen suka sake mayar da takubbansu cikin kufe suka koma bayan Abu Salhif suka
tsaya a wannan lokacin ne bakin ciki ya lullube Salhif har zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar
zata kone jikinsa ya kama tsuma koda shugaban dakarun ya lura da halin da Salhif ke ciki sai
ya bushe da dariya mugunta sannan ya dafa kafadar Salhif ya ce.

"Yaro ka yayyafawa zuciyarka uwan sanyi idan ba so kake yanzun nan jini zuri'arku gaba daya
ya zube anan ba."

Koda jin wannan ba tu sai Saihif ya sake fusata ya yunkura zai kaiwa badakaren Sara da
takobin hannunsa amma sai Saihif ya yi wuf ya ruke hannunsa kuma ya zabga masa mari har
ya fadi kasa, cikin tsananin mamaki Salhif ya shafe kuncinsa sa'adda hawaye ya zubo masa ya
Kurawa mahaifinnasa idanu saboda wannane karo na farko da ya taba marinsa amma ko bakar
magana bai taba gaya masa ba, nan take Abu

Salhif ya dubi Shugaban dakarun ya ce. "Za mu baku dabbobin da kuke bukata
amma ka gayawa Sarki cewa bukatarku ba zata biya ba ta hanyar amfani da da dabbobin
ma'abota addinin musulunci koda gama fadin hakan sai Abu Salhif yasa aka kwanto raguna uku
shanu uku da rakuma uku aka baiwa dakarun suka tafi da su.

Bayan tafiyars ue Abu Salhif ya mikawa Salhif hannunsa ya kama ya tashe shi tsaye sannan ya
dube shi ya ce, "Ka yi hakuri ya kai dana inda ban mareka ba bisa kuskuren da ka aikata da tuni
an kasheka a gaban idanuna kasani cewa kai ne ka dai a gareni ni da mahaifiyarka don haka
ba ma son mu rasaka ku ta shi mu kimtsa mu bar garin nan domin abin da zai biyo baya ba mai
kyau banc,."

Koda jin haka sai kowa ya ta shi aka hau kimtswa nan da nan kowa aka gama shiri aka kama
hanya domin ci gaba da tafiya izuwa birnin na gaba inda za'a gudanar da harkokin fatauci.

Al'amarin Sarki Masurd ana kai masa wadannan dabbobi sai yai shiri ya tafi izuwa dakin bauta
aka yanka dabbobin aka bayar a jininsu ga aljani Burrrata kamar yada aka saba

Faruwar hakan ke da wuya sai suka ji aljani Burrata ya kwarara uban ibu al'amarin da ya janyo
dakin bautar ya kama rugujewa, mutane dake ciki suka dimauce suka rinka zubewa kasa
sumammu, Cikin firgici Sarki Masrud ya zube kasa gaban gunki Burrata yana tuba.

mini Nan take gunki ya bude baki ya ce, "Maza ka tura dakaru su je su kashe wadannan bakin
fatake domin jinin dabbobinsu bai magance Kishirwata ba face karuwata kuma ka sani cewa
lallai sai an yi asarar dubban rayuwaka a cikin Kasarka saboda fishina idan baka hanzarias
samomin jinin da na saba sha ba ko wa sai ya dandana kudarsa."
Koda jin wannan batu sai Sarki masrud ya sake dimancewa ya mike tsaye zumbur yana mai
kwalawa Sarkin yakinsa kira ya fice da gudu.

Kadan ke nan daga cikin littafin JAHADI wanda zai zo nan bada jimawa ba Naku har kullum
Abdulaziz sani madakin gini

Ziyarci Shafin
arewanovels.com.ng

1 / 1

Chapters