Chapter 41 Reading KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc Arewa Novels

KIRAN RABO Book 3 Complete Hausa Novels By Nanah Halima.doc

Author :  Nanah Haleema Category :  Hausa Novels 001

Chapter   41 / 111

120K to 123K   out of 332.3K words

ce, "buWe idonki ki karanta ina so ki tabbatar ne."

Nayla ta dinga girgiza kai tana kuka tana cewa, "A'a don Allah, bana son ganin komai ka Wauke. Ka janye sakin bana so, wasa nake yi ba da gaske nake ba." Abinda ta ce ya saka shi ya yi murmushi amma da yake idanunta a rufe yake bata gani ba. Omar ya ce, "Ayya ban san wasa ki ke yi ba, amma ki karanta Win."

"Ni bazan karanta ba, daman da ka ce kana sona daman ?arya ne baka sona, in kana sona ai baza ka sake ni ba. Daman na san baza ka taSa sona ba, kamar yadda ka ce baka sona na san baza ka so ni ba. Yanzu ina ka ke so na tafi? In na koma gida na ce musu na dawo yau kuma ka sake ni yau?." Yadda take kuka sosai da zuciyarta da gangar jikinta ya saka shi ya tausasa murya ya ce, "ke kika ce ai ko?."
"Ni na fasa! Daman ?arya nake yi!" Ta faWa da ?arfi tana kuka sosai.

Omar ya yi murmushi mai sauti amma kukan da take yi bai bari ta ji ba. Shiru ya yi yana kallon ta, ya rasa ta ina zai fara balle ya saka ta yi shiru. Da?yar ya daure ya ce, "ki bar kuka." Bata daina kukan ba ya ce, "ki daina kuka ki kalli takardar."

"Ni bazan kalla ba, bazan iya gani ba." Omar ya ce, "to bara na karanta miki." Da sauri ta dam?e takardar ta chakume ta a ?irjinta jikinta yana rawa tana dana sanin furta abinda ta ce. Murmushi ya yi mai sautin gaske yana kallonta kafin ya harWe hannayensa a ?irji yana kallon ta cikin tsantsar so da shau?i.

"Daman ai na ce miki bazan rabu dake ba, babu saki a tsakanin mu har abada!" Ya furta a tausashe yana kallon ta. A hankali ta fara tsayar da kukan, cikin sanyin murya ta ce, "gashi ka aikata, gashi ka sake ni."
"Na ce ki duba kin ?i ki duba, ta ya zaki fahimci abinda ya ke ciki?."
"Ni bazan gani ba."
"In baki gani ba baza ki fahimta ba, ki buWe."

"Ni bazan buWe ba, bazan karanta ba!" Ta faWa cikin hawaye. So yake ya yi abinda zata daina kukan amma ya rasa ta ina zai fara.

Takawa ya yi zuwa inda take zaune, bai zauna ba yana daga tsaye ya buWe hannunta ya cire takardar ya warwareta daga cukurkuWeta Win da tayi ya ce, "ki kalli abinda na rubuta, na rubuta ina...." Da hanzari ta mi?e ta rufe masa baki tana wara idanunta tare da girgiza kai hawaye na sakkowa. Kallon ta yake yi tana daga tsaye a kusa dashi tana kallonsa hannunta na fuskarsa ta rufe masa baki.

Juya mata takardar ya yi ya haska mata ta kalla ta Wauke kai, sai ta sake kalla ta zubawa takardar ido tana kallo har lokacin hannunta na kan bakinsa. _Ni Ina sonki Jidda, bazan kuma rabu dake ba. Gwara ki zauna dani kawai._

Abinda ya rubuta kenan da manyan ba?i, ta kalli fuskarsa ya Wan motsa girarsa da idanunsa yana kallon ta. Hannunta ta janye a hankali daga fuskarsa ta rufe fuska a hannayenta saboda kunyar da taji ta rufe ta lokaci Waya.

Murmushi ya yi yana kallon hannayenta da suke kan fuskata, henna hannunta ya karSi hannunta sosai abin ka da farar fata. Zama tayi akan kujera, ya koma nesa da ita shima ya zauna yana kallonta har lokacin fuskarta a kulle take.

Shi dai Allah ya Wora masa son wannan yarinyar lokaci Waya ba tare da ya sani ba, yana matu?ar jinta a zuciyarsa da gangar jikinsa, ya rasa abinda yake ji a kanta, ji yake kamar ya haWWiyeta ya huta kawai. Ya zuba mata idanu ya kasa cewa komai dan bai san me zai ce mata.

Ajiyar zuciya ya yi yaga ta buWe fuskar amma kanta a ?asa tana murmushi fuskarta a kwaSe alamun shagwaSa. Samun kansa ya yi da cewa, "Da gaske bana ?arya dan na burge wani, bana faWar abinda ba shine a raina ba dan wani ya ji daWi. In bani da ra'ayi zan faWa miki a gaban ko waye, Ki ri?e wannan Jidda!." Nayla murmushi take yi tana kallon ?asa jin sunan da yake kiranta dashi. Duk da ta san sunanta Jidda amma da ya kasance shi kaWai ne mai kiranta da sunan sai ya zama na musamman.

Omar ya kalli gefe bai ce komai ba, shiru ya sake ratsa tsakani yana jin zuciyarsa na bugawa sosai, Wan rufe ido yayi ya buWe kafin ya yi ajiyar zuciya ya ce, "kina ji......" Nayla ta Wago ta kalle shi suka haWa ido ta Wauke ido saboda kaifin idanunsa, cikin murya mai daWin saurare ya ce, "Ki saka a ranki Omar yana ?aunarki, yana ?aunar zama dake a matsayin matarsa. Duk abinda zan faWa miki daga zuciyata yake ba dan ki ji daWi ba, Ki ri?e wannan ma Jidda!. Omar ba ya faWar ?arya dan wani ya ji daWi, Omar ba ya faWar akasimn abinda yake zuciyarsa. Jidda! Ina sonki, ina ?aunarki ?auna mai yawa..!."

Nayla kulle ido tayi farin ciki na ratsa ko ina na jikinta, hawaye yana sake sauka daga idanunta. Hawayen farin ciki, hawayen jin daWi, hawayen walwala da samun abinda zuciya take muradi a rayuwarta. Wai ita Omar yake furtawa yana so, wai ita Omar yake so har yake faWa mata ido da ido. Omar masoyinta da ta yi dakon soyayyarsa yana yi mata tsawa, Omar masoyinta wanda ko kallon kirki bata ishe shi ba, yau shine yake zaune a gabanta yana amsa sunan masoyinta kuma mijinta, To me zata yi in ba kuka ba?.

Omar bai lura da tana hawaye ba, ya sake yin ajiyar zuciya ya ce, "zaki je aiki gobe?." Kai ya girgiza alamun a'a sai ta tuna baya son body language ta ce, "A'a."
"Kuka ke yi? Na faWi wani abun da bakya so ne?" Ya faWa yana kafe ta da idanu jin muryarta na rawa.

Shiru tayi bata ce komai ba, shiru ya sake ratsa tsakaninsu kafin ya Wan yi gyaran murya ya ce, "Nayla!." Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, abinda Nayla ta ji a zuciyarta sai da ya kai ta ga jan salati, wani irin shock ta ji har cikin ?ashin da tsokar nama ya lulluSe sai da ya amsa. Fizgarta ake yi, ji take in bata haWa jikinta da nasa ba zata iya haukacewa, hawayenta ya ?ara yawa sosai ta rasa yadda zata sarrafa yanayinta.

Ganin kamar jikinta yama rawa sai ya zuba mata idanu ya ce, "kina lafiya?." Nayla ta Waga kai alamun eh, ya nuna hawayenta ya ce, "kukan fa?." Nayla ta goge idanunta amma bata ce komai ba.

Shi kansa yanayin da yake ciki kenan, amma bai san ta ina zai fara ba, bai taSa haWa jikinsa da wata mace ba, ko a lokacin Narma itace take rungume shi ba shine yake yi ba. Shiyasa ya rasa ta wacce hanya zai yi hakan, amma tabbas yana so ta ji Nayla a jikinsa ko zai ji sau?in bugun zuciyarsa. Omar ya daure ya ce, "Gobe in sha Allah zamu je wani waje da safe." Nayla ta Waga kai ta ce, "to Allah ya kaimu."
"Amin, ki je ki huta" ya faWa yana tashi tsaye.

Inda son ransa ne tabbas bazai bar Nayla ta kwana ita kaWai ba, zai kwana tare da ita ya yi mata masauki a jikinsa, ya tallafota ya kwantar da ita a ?irjinsa ta yi bacci yadda take so. Zai faWa mata kalmai masu daWi a kunnenta, ya rarrasheta ya tabbatar bata zubar da hawaye ba. Sai dai kash! shi bai san ya zai yi, baya son za?ewa da yawa, baya so ya za?e kar ta ga kamar daman ya saba yiwa mata haka ne shiyasa ya kama kansa.

Nayla ta mi?e tsaye, jiri da nauyin kai ya saka tayi baya kamar zata faWi, da sauri ya ri?o hannunta ta tsaya cak ya ce, "baki da lafiya?." Ta girgiza kai ta ce, "lafiya lau."
"Kin tabbatar?."
"Uhum! Abincin da na dafa maka fa?."

Omar ya ce, "na ci abinci kafin nazo, ban san kin dawo ba, amma zan ci wani lokacin." Nayla ta Waga kai kawai bata ce komai ba. Ya ce, "ki je ki kwanta." A hankali ta juya tana takawa zuwa Waki ya bita da kallo har ta shiga.

Ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya ce, "Omar anya kaine?" Ya faWa yana Wan dukan fuskarsa kaWan yana murmushi. Shima Wakinsa ya shiga amma zuciyarsa gabadaya tana ga Nayla, da yana da yadda zai yi gashi gata zasu kwana amma bai san ta inda zai fara ba. Ya yarda da batun Didi ya kamata ya shiga ajin da za a koya masa yadda ake tafiyar da mace a wannan Sangare na soyayya. A jikinsa yake jin ya kamata ya aikata abinda zai gamsar da ita son da yake mata, amma bai san me zai yi ba, bai san me zai fara yi wanda zai saka ta gamsu a zuciyarta yana ?aunarta ba. Yana ta tunani shi kaWai cikin kewa da tsananin ?aunarta, bai san me zai ce ba, bai san abinda zai yi ba.

Nayla ma a Sangaren ta haka take, amma ita farin cikin bayyana mata yana sonta yafi mata daWi har ta kwanta ita kaWai tana murmushi.

Da asuba bata tashi ba kasancewar ba sallar zata yi ba, sai ?arfe bakwai da rabi ta farka saboda alarm Win da ta saka. Wanka tayi kana ta fito ta shirya breakfast mai sau?i sannan ta shiga ta shirya cikin tsadaddiyar atamfa irin Winkin da ta saba, ta fito falon a lokacin yake fitowa cikin jallabiyya.

Kallonsa tayi suka haWa ido, Wan tsayar da idonta tayi a cikin nasa na wasu sacanni kafin ta janye ido ta ce, "ina kwana." Murmushi yake yi yana jin muryarta har tsakiyar kansa kafin ya ce, "Kin tashi lafiya?."

"Lafiya lau, ga breakfast na gama, na ji kace zamu fita da wuri." Kai ya Waga mata ya ce, "da wuri zamu fita, amma abincin nan..." katse shi ta yi ta ce, "don Allah YaMar!." Zuba mata idanu ya yi na wani lokacin, kafin ya tafi da idanun kamar zai rufe sai ya fasa ya buWe akan fuskarta.

Nayla ta ce, "gashi anan." Omar ya biyo bayanta ya zauna ta haWa masa tea daidai da ra'ayinsa. Babu yadda zai yi mata dole ya karSa, ji yake in bai karSa bazata ji daWi ba shi kuma ba ya son aikata abinda zai saka ta ji babu daWi a zuciyarta. Nayla ta zauna ta kafe shi da idanu, dole ya sha tea Win tana zuba masa sauran kayan ya ce, "ki bar shi ya isa."

Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ba tare da ta yi magana ba, hakan da ta yi bai san lokacin da ya ce, "to zan ci." Sai da ya furta maganar sannan ya san ya yi, Nayla ta yi murmushi ya karSa ya Wan ci kaWan ya kalle ta ya ce, "na gode" ya faWa yana tashi ya shiga Waki.

Murmushi ta yi tana na zaune itama ta ci abincin tana jiran fitowarsa. Ba jimawa ta ji ya buWe ?ofa ta juya tana kallonsa. Sak ta yi tana binsa da kallo ganin kwalliyar da ya yi bata taSa ganin yayi irinta ba. Men lace ya saka black colour, ya saka hula da takalmin da suka haska ?afarsa. Ga agogon da ya Waura a tsintsiyar hannunsa, ga azurfar da ta bashi tsaraba a hannunsa.

Babban abinda ya fi tafiya da ita kamar babbar rigar da ta ga ya saka, bata taSa ganinsa da babbar riga ba sai yanzu, ko da bikin Didi bai saka babbar riga ba amma yau gashi ya saka, shiyasa ta tsaya cak tana kallonsa kamar ta sace shi ta gudu.

Ganin yana tahowa inda take ya saka ta Wauke kai daga kallonsa ya ce, "mu je?." Nayla ta Waga kai ta koma ciki ta Wauko mayafinta da jaka da wayar ta. Kafin ta fito har ya fita da motarsa, ta bishi da kallon mamaki tana tabbatarwa kenan itace motar da Didi take bata labarin ya siya. Da Tk suka gaisa ya kulle gidan, ta ?arasa ta buWe gaban motar ta shiga ya yi bismillah ya ja motar suka fita.

Kallon ta ya yi yaga tana ta murmushi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Nayla ta ce, "motar da ka siya ce?." Kai ya Waga ya ce, "uhum, lokacin bakya nan." Wayarsa ce tayi ?ara ya kalla ya ga Didi ce sai bai Wauka ba ya cigaba da tafiya. Sake kira ta yi ya Wan kalli Nayla ya ce, "Wauki wayar."

Hannu ta saka ta Wauki wayar ta saka a speaker Didi ta ce, "Omar ka tafi ne?." Omar ya ce, "uhum. Ina Marmerh?." Didi ta ce, "yanzu baka tambayar ya na tashi kawai Mamerh ka ke nema." Murmushi ya Wan yi bai ce komai ba, zata yi magana ya ce, "zan kira ki." Jin hakan sai Nayla ta yanke wayar tana kallon screen Win wayar.

Hoton Marmerh ne wanda ya yi matu?ar kyau tana bacci cikin shiga ta alfarma. Kallon sa ta yi kafin ta ajjiye wayar shi dai bai ce mata komai ba. Tafiya suke yi Nayla ta ga tafiyar ta ?i ?arewa ta ce, "Ina zamu je haka?." Omar ya kalle ta kaWan ya Wauke kai ya ce, "Ki yi bacci ki tashi." Nayla ta ce, "Ina zamu je to?."
"Siyar da ke" ya bata amsa a ta?aice ba tare da ya kalle ta ba. ?an murmushi ta yi shi ya ce, "da gaske nake."

Nayla dai bata ce komai ba, ta Wan gyara zama dan zaman ya fara damunta ga pad Win jikinta yanzu sai ta fara damunta. Shiru tayi tana kallon titi kamar yadda yake kallo shiru motar babu wanda yake magana.

Wayar Nayla ce ta katse shirun ta duba ta ga number ce wacce bata sani ba, sai ta share bata Wauka ba. Aka sake kira sai ta Wauka ta saka a kunne ta ce, "Hello." Shiru tayi alamun ana magana kafin ta ce, "Oh na gane, Ya aiki?." Shiru ta sake yi kafin ta ce, "Sai zuwa upper week zan dawo." Ta sake cewa, "Allah sarki na gode da kulawa." Tana faWar hakan ta yanke wayar ta ajjiye a jikinta.

Omar yana jin duk abinda ake fada har shi mai maganar yana jiyo me yake cewa, bai yi niyar magana ba ya ji ta ce, "abokin aikina ne." In ya tanka kujerar da suke kai ma ta tanka. Abokin aikinta ne da tambayar meyasa bata zo aiki ba? Ina ruwan shi da matarsa?, ita kuma har cewa take yi ta gode da kulawa, mutum nawa ne suke yi mata irin wannan kiran?. Nan da nan fuskarsa ta juya ta koma ta asalin Omar tiger da ta sani, bata lura da hakan ba sai da ta Wan kalle shi ta ga ya haWe fuska sosai.

"Me ya ce miki?." Nayla ta tsorata dan wallahi bata Wauka zai yi magana ba, ga yanayin fuskarsa duk ta canja mata sai ta ce, "kwana biyu bai ganni a wajan aiki ba shine yake tambayar lafiya." Ya girgiza kai kamar ba zai ce komai ba suka cigaba da tafiya. Har ta cire kai da zai sake magana sai ta ji ya ce, "ya ji lafiya ki ke yanzu?." Nayla ta ce, "eh."
"Ya yi." Daga haka bai sake cewa komai ba bai kuma saki fuska ba bai kuma kalle ta ba.

Nayla ta ce, "i'm sorry." Bai ce komai ba sai ta yi shiru tana mamakin wai ina zasu je ne haka kusan awa Waya ana tafiya. Nayla tun tana saka ran zai yi magana har ta cire dan bai ce mata ?ala ba. A Zaria ta gansu, abin ya bata mamaki sosai tana tunanin to ina zasu je haka?. Bata gama mamaki ba sai da taga sun shiga Kaduna kuma kai tsaye unguwar su Naylan ya nufa kamar yadda suka zo kwanaki.

Idanu Nayla ta wara lokacin da ta ga sun shiga estate Win gidan su ya kuma tsayar da motar a daidai gate Win gidan. Nayla ta kalle shi murya na rawa ta ce, "me...zamu....yi....a...nan?." Bai kula ba, ta ga an buWe gate ba tare da ya yi horn ba ya shiga da motar. Nayla ta firgice tana kallonsa ta ce, "me muka zo yi nan? Abiy.......!." Hannunsa ya Wora akan nata ya Wan matsa hannunta kaWan ta kalli idanunsa ya ce, "ki nutsu, Ina tare da ke."

Nayla ta ce, "meyasa baka faWa min nan zamu zo ba? Abiy fa ya ce....." Omar ya katse ta ya ce, "shiii na sani, kar ki damu." Nayla ta fara hawaye ta ce, "ni dai mu koma Kano don Allah, bana son Satawa Abiy rai." Hannunta ya sake matsawa kaWan ya ce, "Ina tare da ke, ki bar wannan kukan shagwaSar, Mu je" ya faWa yana buWe motar ya fito amma Nayla ta kasa fitowa. Zagayowa ya yi ya buWe mata yana kallonta dole ta fito a sanyaye tana kallon cikin gidan na su cike da kewa.
KRB3P041

Nayla tana tsaye a jikin motar hawaye yana zubowa daga idanunta tana kallon gate na biyu wanda zai kaita cikin gidan. "Nayla!." Taji an faWa daga bayanta, da sauri ta juyo ta ga Ya J kawai sai ta fashe da kuka mai sauti. Da sauri ya ?araso inda take ta faWa jikinsa ta rungume shi tana kuka sosai. Jawad ya ce, "ke kin ga matsalata da ke wallahi, yanzu meye na kukan?." Ya kalli Omar da yake tsaye ya ce, "Omar haka ka ke fama da Nayla da shagwaSat nan?."

Fuskarsa babu walwala sosai amma a sake fuskar take bai ce komai ba. Jawad ya cire ta daga jikinsa ya ce, "ki bar kuka, tun Wazu nake jiran zuwan ku. Mu je ciki." Nayla ta ce, "Yaya J, Abiy." Ya ce, "Abiy yana nan, yau ko fita bai yi ba saboda zaku zo. Ki bar wannan kukan malama ki wuce mu je ciki, kin bar shi a tsaye bayan kun yi doguwar tafiya."

"Hajiya Nayla barka da zuwa." Aka faWa daga bayanta, ta juya ta ga ma'aikatan gidan ne sai ta yi murmushi suka gaisa.

41 / 111