Dan Karuwa Romantic Hausa Novels By Zahra Surbajo.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Hausa Book Store

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 19K words

da suka hadu acan india.

Sanda ya samu labarin nana nada ciki sosai ya tayasu murna.

Inda ya shiga kasuwa ya ciko akwatuna da kayan baby kala kala.

Kai kace shi zaayiwa haihuwar sabida murnar da ya nuna,fahad har mamaki yakeyi.

Cikin nana nada wata biyar,mahaifiyar su fahad ta kwanta rashin lfy.

Hankalinsu in yayi dubu ya tashi,gashi ciwon nata da zafi yazo mata,dan gaba daya ko gane mutane batayi,hawan jininta ya hau sosai.

Me martaba shima jikinshi ba dadi amman dole tasa ya yi ta maza ya dunga duba matarshi,

Ganin ciwon ba sauki yasa fahad yimata duk shirin daya dace domin afita da ita waje.

Ana e gobe zaa fitar da ita,tace ga garinku,rai yayi halinsa.

Fadin tashin hankalin da suka shiga baze faduba,wanda sanadin jin mutuwarta me martaba ya yanke jiki ya fadi,daga haka yasamu ciwon barin jiki.

Nana ma ta firgita da mutuwar sirikar tata me matukar kaunarta.

Haka akai mata wanka aka sallaceta aka kaita gidanta na gaskiya.

Bayan rasuwar mahaifiyarsu,hankalinsu kan mahaifinsu ya koma,

India suka fita dashi,inda hydar da kaninshi ne agurinshi suna jinyarshi,se hajiya babba wacce ganin ido yasa ta bisu.

Watannin sarki biyu a india yasamu sauki suka dawo nigeria.

Sede dukansu ransu ba dadi rashin mahaifiyarsu.
.addua sukai taimata,dan ita tafi bukata.

Hajiya babba bayan sun dawo cigaba tayi da tsafe tsafenta wajen son ganin ta shiga tsakanin haidar da fahad.

Hakan yasa tai ta asirin da ta janyo fahad jikinta,suka fara shiri

Duk yadda hydar yaso nuna masa illar ta baya yarda karshe da fada suke rabuwa.

Kullum hajiya cikin kai sukar hydar take ga fahad,wanda tun fahad din be yarda har yazo ya fara yardar.

Har tana cemishi yasa ido tsakaninshi da nana,ita tana zargin wani abu.

Cikin nana yakai wata tara ko yaushe zaman jiran haihuwa akeyi,iyayenta sun so su tafi da ita gida amman fafur fahad yaki yarda,wanda dole suka hakura.

Yau tun asuba nana kejin bayanta na ciwo tana daurewa.

Dakyar taiya shan tea.
Fahad dake lura da ita rukota yayi yace cikin tausayawa.

"Nana ta lafiya kuwa,kode abun yazo ne"

Murmushi tayi na karfin hali tace.

"Inda sabo ay na saba da irin ya wash wash dinnan"

"To Allah ya saukeki lfy baby na,bari naje training nadawo,bazan jima ba"kiss yay mata akumatu ya fice.

Bayan fitar shi,ba jimawa ciwon ya turnuke,nana,tun tana daurewa har ta fara kuka.

Acan kuma cikin gida me martaba keson ganin fahad ya kira wayarshi akashe,hakan yasa ya kira hydar ya shaida mishi yaje ya kira mishi shi agidanshi.

Da hanzari hydar ya tafi ayken na mahaifinshi.

Sanda ya isa gidan sallama yay tayi akofar falon amman ba kowa daya amsa,

Da har ya juya ze tafi se kuma tadawo yataba kodar yajita a bude.

Se ya tura ya shiga gidan.

Falon ba kowa haka yay ta sallama amman shuru.

Can yadunga jiyo kukan nana daga falon sama,

Da gudu ya haura saman,akwance ya ganta,akasa zanin jikinta ma ya kwance sabida azaba,daga rigar jikinta se pant.

Jini ne ke bin jikinta,nana na ganinshi ta fara miko mishi hannu tana fadin.

"Yaya hydar kataimakeni,zan mutu"

Hydar agigice yayi kanta,be jira komai ba,ya kinkimeta ita da cikin yayo kasa da ita.

Suna sakkowa daga saman Fahad da hajiya babba suna shigowa,sabida fahad daya fita training din yana gamawa yaje yacewa hajiya su zo taga jikin nana dan yana tunanin ko haihuwace,to ya daukota kenan.

Yazo ta tarar hydar dauke da nanarsa ahannu,ya fito da ita daga dakin baccinsu.

Me hakan ke nufi.

Waya ba hydar damar hawa saman gidanshi.?

Muje zuwa

Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*Duk wanda yasan ni yasan books dina,yasan zeyi wuya in gama batare da na jinjina ga wainnan jaruman zaratan matan ba,zeyi wuya sosai,ina sonsu har cikin raina,ina musu fatan alkhairi akoda yaushe.*

*Maman Gidado,Fatima Abubakar Radda,inna Ibrahim kime,Aunty jamila tayakasai,Aunty Halima,Aunty halilos,Billy shantali(hankarata>??),Bilshop,Hassana da hussaina muhd lawal kano,Aunty Rumaisa lagos,etc*

*masu bin sabon salo kuyi hkr wasu cikinkune suka dan bata raina ta hanyar yada book din groups amman yau zan muku posting da daddare,ayi hakuri*

*page 10*

Hydar ko kallon inda suke beyi ba,

Da gudunshi yayi hanyar ficewa da ita.

Se alokacin ya lura dasu,cikin kidimewa yace.

"Yaya prince yi sauri mukaita asibiti,kaga mawiyacin halin da take ciki"be gama rufe baki ba Fahad ya daukeshi da wani wawan mari.

Agigice Hydar yake duban dan uwan nasa baki bude yace.

"Pls yaya kome nayi maka save her life first"

"Yimin shuru,munafiki,dama hajiya tajima tana fadamin kana neman matata bantaba amincewa ba se yau da nagani da idona,wato sickler din da aka guji ka haifa shine ni kakeso kasa ahaifamin amatsayin nawa ko,wlh hydar nayi danasanin hada jini dakai"fahad yayi maganar yana huci.

Hydar kanshi ke sarawa,bakinshi yayi nauyi maganar tamasa nauyi,rasa abun cewa yayi kawai se yasa kai ya fice dauke da ita ahannunshi,idonshi na zubar da kwalla.

Kai tsaye asibiti ya nufa da ita,yana zuwa kan ya fita da ita ya tube doguwar rigar shaddar dake jikinshi ya zira mata,sannan ya fito da ita zuwa cikin asibitin,inda likitoci suka rufu akanta.

Hydar kuka kawai yakeyi,kamar wani karamin yaro,likitocin sun dauka halin da matarshi ke ciki kesashi kuka,nanko bakin ciki kalamun dan uwansa ke sosa zuciyarsa.

Yana nan zaune yana jiran likitocin su fito,su hajiya da Fahad suka karaso gurin.

Fahad kan Hydar yaje yaci gaba da zazzaga masa masifa shide ya dukar da kansa kasa yana ta kuka,yana adduar Allah ya sauki nana lafiya.

Ana haka likitan ya fito da murmushi afuskarsa.gurin hydar ya nufa da faraa ya mika masa hannu yace.

"Ranka ya dade ina tayaka murna,matarka ta haifi da namiji,dukansu suna cikin koshin lfy,zuwa anjima kadan zaa baku damar ganinsu"cewar likitan dan shi atunaninsa hydar shine mijin nanar.

Godiya hydar yayima likitan.

Hydar yayi murna da haihuwar sosai,yayinda fahad ko alamar hakan babu atattare dashi.

Awa guda bayan haihuwar aka basu damar shiga dakin.

Nana na kwance tana ganinsu ta fara murmushi,dan duk bidirin da akayi ita batasaniba.

Hydar gurin nanar ya nufa,da faraarshi yace.

"Sannu nana,ya jikin naki,"

Cikin faraa tace.

"Jiki da sauki hydar"

Shiko fahad da hajiya kan gadon jaririn suka nufa,suna zuwa hajiya ta dago dan dake ta faman tsotsan hannu,ta bude fuskar yaron.

Daga hajiya har fahad seda suka firgita da ganin kamannin yaron.

Dan in ka kalleshi zaka dauka hydar ne yana yaro,sabida tsabar kamar da yake da hydar.

Salati hajiya ta farayi tana sallallami,gamida rushewa da kuka,tace.

"Kaico hydar kaci amanar dan uwanka,ka tozarta sunan gidanku,yanzu wannan abun kunya dame yayi kama fisabilillahi"ta karasa maganar cikin kukan munafurci.

Fahad afusace,ya fisgi dan yanufi gurin hydar da nana,wacce kanta gaba daya ya kulle,ganin yadda hydar ya dukar da kai yana kuka.

Yana zuwa ya cilla dan gurinsu da sauri hydar ya tara hannu ta cafke dan ya rungumeshi jikinshi,yaron ya riga ya firgita dan haka kuka ya shiga tsalawa.

Nana a hassale ta yunkuro zata rufeshi da masifa,hydar ya dakatar da ita.

Murmushi fahad yayi yace.

"Ay da ka barta tamin,ay dama ba kunyace gareku ba,dan duk me kunya bazeyi zina da matar dan uwansa ba,itama bazatayi da kanin mijinta ba,to kisani nana,wannan dan ba nawa bane,ki nemi meshi tun kan dare be miki ba,koda wasa karki sake ki jinginashi dani,kuma nasakeki saki daya,hakkina dakuka ci keda hydar Allah ya isa ban yafe muku ba,"yana kaiwa nan ya juya ya fice yana kuka,dan dukansu yana sonsu.

Hajiya ma cewa tayi.

"Karuwar banza da wofi,Allah ya tona asirinki to ba agidanmu ba,bakar munafuka,kai kuma yanxu base anjimaba zakaga hukuncin da me martaba ze zartar maka"tana kaiwa nan ta fice daga dakin ta nufi gurin fahad inda tasameshi yana yawa da mahaifin nana yana fada masa abinda nana tai masa,yadda yake fadin zaka dauka akan idonsa komai ya faru.

Mahaifin nana mutum ne me matukar zafi,hankalinshi in yayi dubu ya tashi dan haka mahaifiyarta yashaidawa kuma yabata tabbacin matukar nana ta waiwayeshi seyayi ajalinta..

Yana gama wayar hajiya tajashi suka wuce zuwa gurin me martaba.

Itako nana wacce kanta ya fara birkicewa,dafa hannun hydar tayi tace da kyar.

"Hydar don Allah ka gane me suke cewa,akan me suke mgn kuma akan wa,pls wacce nanar fahad ya saka,pls tell me"ta fadi cikin karaji.

Hydar ya kasa mgn,kuka kawai yake yana jijjiga yaron dake kuka.

Riko hannunta yayi tana tirjewa yajata suka fice zuwa mota,dan ya biya komai ba abinda ake binshi.

Mota yasata ta zauna sannan ya mika mata yaron ta rike,yashiga yaja da mahaukacin gudu,ya nufi gurin me martaba da su.

Sede kan yaje hajiya da fahad sun rigashi zuwa,dan har hoton daukar da yayiwa nana seda hajiya ta nunawa sarki,wanda ta dauka batare da sun sani ba.

Hankalin sarki in yayi dubu ya tashi ya rasa meke masa dadi,jin dan dayafi so cikin yayansa irin barnar daya tafka..

Hydar na shigowa dalon me martaba,yajiyo muryar me martaba na masa gargadi.

"Idan har ka kuskura ka sake bari fuskarmu ta hadu nidakai,Ban yafe maka ba hydar,kafice daga rayuwata da duniyata,ni ban haifi mazinaci ba,kaje duniyace hakkinmu se ya hanaka kwanciyar hankali,"me martaba ya karasa maganar yana share hawaye.

Hydar jiki asanyaye yayi baya,bece komai ba,yaja hannun nana suka fice.

Amota ya natsar da nana ya fada mata duk abinda ya faru.

Se alokacin nana taji dan sauki a zuciyarta ganin sharrine aka musu wanda tasan duk daren dadewa Allah ze tona asiri.

Hydar gidan su ya nufa da ita,dan dama gidan ay nashine yabarwa fahad.

Suna shiga gidan wayar nana dake falo ta fara ruri,koda ta isa gurin domin dauka numver mahaifinta ta gani,dan haka da sauri ta dauka.

Muryarshi ta katse mata hanzari.

"Naji alfashar da kika aykata,kanki kikawa,ba niba sede kisani,na yafeki niba ubanki bane,dede da rana daya kika kuskura kika tunkaro gidana ko rimin kuru,nine ajalinki,ko kuma ni na kashe kaina,ina danasanin haihuwarki"

Yana kaiwa nan ya kashe wayar.

Wayyo Allah.

Muje zuwa

Na raina comments

Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*11*

Batare da tunanin komai ba ya tura kofar dakin ya shiga.

"Nana tun a falo nake ta sallama amman shuru,bade kunyi bacci da wuri ......."maganar ta makale a bakinshi sanda yay arba da ita tsirara agabanshi tana lashe baki.

Runtse ido yayi da sauri yana korar shaidan,ya juya da zafin nama ze fice daga dakin.

Ita ma da sauri ta kamo shi,ta fada jikinshi

Kokarin tureta yakeyi amman taki turuwa ta makaleshi kam.

Kokawa sukeyi sosai nana sekace me karfin doki,tuni ta yage mishi rigar jikinshi,

Hydar abun yafara bashi tsoro dan ya lura ma sam bata cikin hayyacinta.

Rungumeshi takeyi tana shafashi tana kamo hannunshi tana dorawa kan haq dinta da nufin yayi fingering dinta,amman fafur yaki amincewa da hakan.

Kuka ta rushe dashi me tsanani ta ruko hannayenshi tace.

"Kataimakamin kayi sex dani wlh wlh wlh in bakayiba mutuwa zanyi,wlh mutuwa zanyi"

Yadda idonta ya juye ne yasa haydar yarda bata tare da hankalinta.

"Nana me kikasha daya jefaki cikin wannan yanayin?"

Kokarin hade bakinsu take shikuma yaja da baya da sauri.

Janta yayi kan gado,ya kwantar da ita,shima ya kwanta ya janyota jikinshi yafara karanta mata ayoyi daga alqurani me girma,

Itako shafashi take tayi,ya daure yaci gaba da karanta mata akunne

Sannu a hankali karfinta ya fara raguwa,wanda zuwa can ta kwanta sharab akan gadon tana jan wani dogon numfashi alamun tayi bacci.

Godiya hydar yayi ga Allah sannan ya mike,yaja mata bargo ya rufeta.

Kan gadon da sultan ke kwance yana bacci ya matsa,be tabashi ba dan yaga alamun dadin baccin yakeji,addua ya tofa masa sannan ya juya ya fice daga dakin,zuwa dakin fahad.

Wanka yayi yasauya kaya yayi alwala yazo yafara nafilfili,yana rokon Allah kan yaba nana lfy.

Agidan ya kwana,inda nana ma batasan ya shigo gidan ba.

Fitowa tayi fes da ita dauke da danta duk sunyi wanka,bame cewa itace jiya ta fice cikin hankalinta.

Mamakine yakamata na ganin hydar zaune a falo yana kallon wani shiri da akeyi da safe a tv.

Murmushin karfin Hali tayi tace.

"Hydar kaine da sassafennan,hala jiya dare kayi ahanya yasa bakasami damar biyowa tanan ba"

Murmushin karfin hali yayi yace.

"Eh nana,yanzu na shigo naga baku tashiba"

Wuri tasamu ta zauna sannan ta mika mishi sultan.

"Su baffan basu amince ba ko?"nana ta wurgo mishi tambayar

Cikin natsuwa ya shaida mata duk yadda sukayi.

Hawayene masu zafi kebin fuskarta,dakyar yasamu tai shuru .

"Nana jiya kinyi bakine?"hydar ya jefo mata tambaya.

Murmushi tayi tace.

"Hajiya ce tazo har tai mana wanka nida sultan wlh naji dadi"

Agigice yabita da kallo yace.

"Ta baki wani abu kinci ne ko kinsha?"yatambaya

Nana cike da tsoro tace.

"Eh ta bani wata laya na hadiya,sabida tace abinda ya faru tsakanina da fahad asirine shine ta amsomin taimako"

Azabure yamike tsaye yace.

"Why nana,meyasa kika anshi taimako daga hajiya,kinsan me hakan ya haifar miki kuwa jiyan"

Shuru tayi tana ware idanuwa.

Shiko hydar safa da marwa yafara yi acikin falon yama rasa ta ina ze fara.

Key din motarshi ya dauka yafice da sauri.

Nana tsorone yagama kamata,batasan inda maganganunshi suka nufa ba.

Takasa gane alkibilarsu su dukan,kada ta zauna fa suyi kokarin salwantar da rayuwarta.

Tsorone ya kamata ta mike da sauri ta dauki danta ta goya.

Ta fada daki ta debi kayan sawarsu.

Ta daukosu tasa amota.wacce fahad ya siya mata.

Jan motar tayi da mahaukacin gudu ta fice daga gidan,dan gaba daya sun gama firgitata.

Shiko hydar yana fita,gidan malamin sarki yanufa,bayani yamasa naduk abinda ya faru.

Bayan dogon nazari yagano meke faruwa dan haka wani ruwan rubutu ya bashi yakai mata tasha.

Godiya hydar yayi masa sannan yabaro gidan cikin jin dadi ya nufo gidan nana.

Nana ko tana ficewa ta kama wata hanya wacce ko zaa kasheta batasan ina zata kaita ba itade kawai umarnin zuciyarta take bi.

Bayan doguwar tafiya se gani tayi ansa welcome to Gombe state.

Sosai tsoro yakamata,dan haka guri tasamu tayi parking.

Bin garin tayi da ido tana kallo,ita koda wasa bata taba zuwa garinba.

Motar bakin glass ne yasa bame ganinta,dauko sultan tayi ta bashi nono,yasha ya koshi.

Sannan ta fara nazarin ina zata bi.

Shiko hydar da saurinshi yashiga falon gidan yana kwalamata kira amman shuru bata amsa ba.

Agigice yafara nemanta acikin gidan sede ko ina batanan,yana shiga dakinta yatabbatar da hakan ganin komai a warwatse.

Da gudu yafito zuwa gurin megadi,yatambayeshi.

Bashi tabbaci yayi data fice daga gidan.

Rasa abunyi hydar yayi kawai seya duka agurin yafara kuka,sekace karamin yaro.

Muje zuwa

Surbajo for life.[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?
*DAN KARUWA*
<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?<؀?

*writen by zahra surbajo*

*ayi hkr naje biki ne kwana biyu yasa kuka jini shuru*

11

*family over anything,my blood sisters love you for no reason,Nusaiba Abdulkadir Danmadaki,Rahmatu Muhammad mahmud,khadija sulaiman,Asmau muhammad mahmud,Balaraba sani ibrahim(bugaje),Aisha maman pretty,Amina sunusi Ahmad,bilkisu sunusi Ahmad,Asmau Abdullahi shareef yako,Aliya shareef gambo yako,Asiya muhammad mahmud,Ni'ima Abdullahi,Sumayya mas'ud madobi,Amira mas'ud madobi,ako da yaushe ina sonku Allah yabarmu tare yakarama zumuncinmu karfi amin*

*page 11*

Kifewa agurin nana tayi tana kuka,cikin kukan take fadin.

"Hydar kode da gaskene abinda suke cewa akanmu,kaina ze fashe narasa ta ina matsalarnan take"takara maganar cikin kuka.

Cikin dauriyya hydar yace.

"Nana ba gaskiya bane batun su,ki kwantar da hankalinki bakin iyayenmu ba abinda ze mana sabida bamu da laifi,"

"Taya hydar zan iya kwantar da hankalina,taya zan fara rayuwa da dan da ubanshi yace ba nashi bane?wazan ba dan ince nashine?"cewar nana cikin kuka.

"Kibani,jinin fahad jinina ne,bazan taba wulakanta zuriarmu ba,nidashi abu daya ne"

Shuru nana tayi tana ta kukanta.

Takawa hydar yayi yaje ya dauki jinjirin data ajiye yana kuka.

Daukar yaron yayi ya kureshi da ido,tausayinshi yakamashi sosai.

Adduoi yayi masa sannan yamasa huduba da sunan me martaba.

Afili kuma yace ma nana.

"Allah ya raya mana me martaba,alkunyarshi sultan"

"Amin" nana ta furta da dusasshiyar muryarta.

Ajiye shi yayi kan cinyarta,sannan ya juya ya fice da sauri.

Nana mikewa tayi dakyar,rike da danta ta haura sama.

Ruwan wanka ta hada musu me zafi,ta kwantar da yaron bayan ta tofeshi da adduoi.

Ta shiga toilet,ta jima tana gasa jikinta,sannan ta fito.

Yaron ta dauka shima tayi masa yanata kuka,kukan shi ne ya isa kunnen hydar da shigowarshi kenan.

Da gudu ya haura saman dakin rai abace ya tura kofar yashiga.

Yace.

"Me kikewa baban nawa,da yaketa kuka haka?"

"Wanka fa nake mishi hydar me zan mishi?"

Zama yayi akasa rike da yaron,yana rarrashinshi.

Ahankali ya maidashi cikin ruwan suka masa wankan tare.

Bayan sunmasa wanka hydar yabata shi ta shiryashi sega da ya fito fess dashi.

Mikewa hydar yayi yace.

"Ku zauna nana,zanje rimin kuru ne,inga su baba insha Allahu zan fahimtar dasu"

Dadi nana taji sosai dan tasan hydar nada fada gun iyayenta.

Yana fita ta kulle kofar,ta zauna ta fara gwadawa sultan nono,ayko carab ya amsa yafara sha.

Duk da tana jin zafi ba kadan ba amman dole ta daure,yaci gaba dasha.

Tana gama bashi yayi bacci,ajiyeshi tayi ta nufi kitchen dan samawa kanta abinda zata ci.

Acan ko nata bangaren hajiya babba,dama ta jima da turawa bokanta na india wani ayki da takeso ayi akan nana,to kwatsam segashi sakon shi ya iskota.

Dan ayken data tura,wasu layoyi guda biyu ya bata kana na ya shaida mata.

"Daya agabanta zaa turashi dayan kuma hadiyewa zatayi,yace matukar kikayi haka zakisha mamaki"

Sosai sakon yayiwa hajiya dadi,dan haka bazatai sanya ba,dole taje ta aywatar dashi.

Asace ta fuce ta nufi gidan nana.

Nana na zaune taji ana nucking,adan tsorace ta mike taje ta leka,ganin hajiyace yasa nana ajiyar zuciya taje ta bude mata kofar.

Da faraa hajiya ta shigo falon.

Zama tayi,nana ta duka ta gaisheta cikin biyayya.

Cike da kirsa hajiya tace.

"Nana abinda ya faru bemin dadi ba,wlh hankalina yatashi,amatsayina na uwa,yasa na fita nemomiki taimako,wlh ance sihiri ne aka muku "

Shuru nana tayi tana zare ido,dakyar tai karfin halin cewa.

"Wlh naga alamar hakan,amman na barwa Allah ya bayyana gaskiya"

Dafata hajiya tayi tana murmushi,tace.

"Hakane shiyasa Allah ya tona asirin,ga wainnan taimakone,sahihi ki sha wannan yanzu,shi ze wanko sihirin cikin ki,sannan kin haihu ba wani gyara irin na gargajiya da aka miki dan haka ni zan miki yanzu nan,ay da na kowane,"

Godiya nana tashiga yi mata,sabida wanda ya fada rijiya aka miko mishi takobi rikewa zeyi.

Sa ta hajiya tayi ta kunna heater a dakinta,ta tara ruwa me zafin gaske.

Hajiya tajata toilet ta fara wanketa da towel tana gasa mata jiki,da zafi sosai amman nana najin dadi ajikinta.

Tana gamawa ta tara mata wani ruwan tasa su detol kamar gaske tasa tashiga ciki ta zauna,tasata ta ware kafa,tana ganin ta ware din cikin hanzari ta dauko layar data kulle gefen zani tayi kamar tana duba nanar ne taga ko ta karu,ayko tai wuf ta cusa layar agaban nana.

Nana bata kawo komai aranta ba dan tunaninta haka akema masu jego in anshiga musu wanka,batasan ta tura mata wani abu a gababa.

Haka sukai wankan suka fito.

Ruwa hajiya taba nana acup da yar karamar layar tace ta shanye.

Sosai nana taji dadin jikinta,tayiwa hajiya godiya tai musu sallama akan gobe zata dawo.

Hydar ko tunda ya isa garin be samu fuska gurin iyayen nana ba dole ya hakura ya dawo ranshi abace.

Nana bayan fitar hajiya,ta fara jin wata matsananciyar shaawa na taso mata kamar zatayi hauka.

Wanka ta sake komawa tayi ko zata sami sauki amman ina kan gado ta fada,tana

3 / 7