Chapter 6 Reading NAYI SAKE DA DAMATA 1&2 Wattpad Hausa Novels.txt Arewa Novels

NAYI SAKE DA DAMATA 1&2 Wattpad Hausa Novels.txt

Author :  Category :  Hausa Novels 001

Chapter   6 / 35

15K to 18K   out of 104K words

haka nan akansa da ace kukan zai miki magani tun tuni da yai miki, tsawon wannan lokacin inda ko yaya yana jinki aransa bazai banzatar dake haka ba,to ya nuna maki karewa da karau ma ya furta maki da bakinsa,mace mai irin sunan ki ma baya marmarin sake Aure balle ke karan kanki, to dalili name ki tsawwala na rayuwarki, dubeki *BAHIYYA* kinbi kin lalace kinyi baki kin rame wallahi wanda ya sanki shekarun baya bazai ce kece a haka ba, nidai nayi lallashin duniyar nan akan kiyi hkr da fa'iz ki yafesa, ki fuskanci rayuwarki ta gaba shine zai fishsheki alkairi"



Kuka kurin nake silently sai kana cikin dakin zaka iya jin sautinsa, na saka fuskata cikin ta fukan hannaye na ina tayi baji ba gani, sun dauki tsawon mintoci ba wanda ke magana banda sautin kukana, kafin na fara sassautawa ina kokarin dainawa nake magana cikin sassanyar muryarta data kara yin sanyi saboda kukan da nasha.



"Sakina duk abunda kike gaya mun nasan gaskiya kike nuna mun,da ace ina cikin ransa ko yayane tabbas zai waiwayoni ya yafe mun, ya mance baya ya maidani gidansa, amman yama riga yai aurensa tuni hakan ya sake nuna mun cewar Fa'iz da gaske yake ya yanke duk wata alak'a dake tsakaninnmu, bansan meyasa ko naji haushinsa araina sai indaina saboda dai babu irin damar da bai bani ba wajen gyara kuskurena, ba irin hakurin da bayyi dani ba alokacin da nakejin duniyar tana juyawa dani, nice na zubar da duk wani kimata ga idonsa nice najawo ma kaina duk wulakanci da cin mutuncin da yake mun, *NAYI SAKE DA DAMA TA* sakina, sannan nayi asarar miji irin fa'iz koda wani auren nayi nasan bazan tab'a samun mai hakuri irinsa ba, mai kawaici da kauda kai irinsa ba, kamar yadda kikace ya kamata ace na hakura dashi na fuskanci rayuwar dake gabana nida y'ata, duk da nasan watarana dole ya ansheta duka daga gareni."



Wasu hawayen masu ciwo suka sake zubo man, sakina ta rik'o hannuna cikin tausayawa tana cewa,
"Ki dauka haka Allah ya hukunta miki Bahiyya,ki cigaba da hakuri watarana saidai labari abunda zakiyi kiyi kokari daddy yabar fushi dake,zaki samu salama kota b'angarensa ne sannan inda zan gaya miki kiji ki maida masa yarsa zaki fi zama lafiya...............kiyi hakuri sakina ina masifar son Amnat nan da can bana son ta matsa daga gareni, bazan iya maida masa ita ba rabin jikina ce ita din"



"Shikenan Allah ya zab'a abunda yafi zama alkairi, amman ki dage da addua itace takobin mumini sannan kiyi nesa nesa da  Ammah kinfi kowa sanin son karya take miki, zuwa yanzu kinsan komi don haka keda yarki kuyi baya baya"



Murmushin yak'e nayi ina cewa, "na riga nai maganin wannan damuwar sakina, ai anriga anyi walkiya an haska mun, ni kad'ai na zan iya rayuwa ta ma ba dole saida su ba, nabarta da Allah akan abunda tayi mani, nai imanin Allah zai saka man tun anan duniya zata ga sakamakon abunda tayi, aiga yaran nan gabanta duk mata, shikadai ya isheta ni nai waje na aje Ammah"



Sakina bata tafi gida ba sai wajen sallar isha'i sannan mijinta yazo ya dauketa, yayin da nakejin kamar karta tafi don da sakina kurin nake samu ina d'ebe kewa, bamai fira dani agidan bamai jana ajiki na zama kamar wata mujiya, duk yadda Ammah ke wani nuna ta damu dani da y'ata nasan karya take, tunda waye ummul'aba'isin rabani da gidan mijina inba ita ba, shiyasa banajin zan iya yimata kallon rahma zafinta nakeji ainun cikin zuciyarta.



Bayan na dawo daga rakiyar Sakina Daddy ya dawo sai kurin na wuce falonsa yau ko zai tsine man saiya yafe man ba zan bar falonsa ba abun ya isheni dame zanji ne?







Story continues below






              

Samun na tai tare da Amnat sunata fira tana bashi labari, sallamar da nayi itace tasa ya sauke Amnat daga saman cinyarsa yana bata chocolate yace, "zauna anan baby bari nayi wanka"



Tako zauna tana b'anb'are chocolate d'in, ya shige bai sake kallon inda nake ba, waje na samu na zauna don ba inda zani har saiya gaji ya fito, tunda tunanin sa sadda zai dawo natafi don daman dana shigo masa haka yake man dana tafi saiya dawo.



Hakan bai hana ya nuna tsananin kaunarsa ga Amnat ba, don itace kad'ai jikarsa *Sanyin idaniyarsa* duk da tsananin fushin da yake da mamanta bai hana shi kula da ita kamar kwai ba.



"Maah Babi ya bani choculet"



D'an murmushi nayi mata ina cewa, "har yau bakin babyna bai iya fadar chocolate ba,"



Dariya tayi tana sake b'are wata tana cinyewa, "maah jan koya sai watarana, yanju ban iya ba"



"Allah ya nuna mana wataranan Babyna,"



"Amin Maah,laaaa maaah munyi labari da Abbyna da wayar Babi"



Lumshe idanuna nayi saboda wani abu da naji ya sokeni, duk sadda za'ai maganarsa zuciyata har wani tsuma takeyi,



"Labarin me kukai da Abbyn babyna?"



"Yace wai makalanta jai cani,sannan kuma yace wai inaso in dawo gidan ci?"



Jinai zuciyarta tai bala'in dokawa nai saurin koma wa wajen Amnat d'in ina tallabo duka fuskarta, don har idona ya cika da ruwa dagajin abunda Amnat din tace,



Cikin rawar murya nake cewa, "babyna bakice mashi zaki koma ba dai ko? Inasonki da yawa bazan bari kitafi ki barni ba, inaso na cigaba da rayuwa dake har abadan,"



Jikin yarinyar yai sanyi sosai kamar ta fahimci maganar, ta saka hannunta tana goge man hawayen cikin lallashi take cewa,



"Maah kidaina yin kuka kinji? In kina yi ni ma yi zanyi, ni bazan koma wajen Abby ba tunda kina yin kuka"



Rungumeta nai inajin kamar na tsaga kirjina na sakata, wata kaunarta na sake shigata itama ta makaleni tana cewa,



"Inasonki maah"



Ban san sadda na saki karamin kuka ba ina cewa, "nima ina sonki Babyna"



A haka daddy ya fito ya iske mu, daidai sadda Ammah ke shigowa da kayan abincinsa,taje ta aje tana duban mu tana cewa,



"Ku kuma fa? kamar wandanda akai ma mutuwa"



Uffan bance mata ba haka ma daddy,amnat ce ta maida mata da cewa "ke Ammah ba munyi fad'a ba, ba ruwanki damu"



"Don k'aniyarki ni kike cema haka..........kinga jeki idan na gama zan nemeki"



Daddy ya katseta da fad'ar haka,aiko taji haushi sosai ta juya fuuuuu tabar wajen ya bita da kallo kawai yana juyowa wajen mu, saukowa k'asa nayi na zauna ina ta jan majina ina wasa da yatsuna, Amnat nata masa surutu wajen abincin sa yaje yana ce mata tazo suyi dinner.



Saida yaci ya koshi shida Amnat sannan ya dawo cikin falon bayan ya kunna kayan kallo, ya rage volume ya na duban Amnat yace da ita,



"Baby maza jeki ciki dakina game d'inki na nan ki dauka kiyi kafin na sallami mamanki"



Ta diro tana amsa mashi ta ruga cikin bedroom dinsa, duk shiru mukai nidashi jin yaki magana yasa cikin kuka kasa-kasa nake cewa,



"Daddy kai mun rai ka daina wannan fushin dani, Rayuwata gaba d'aya ta koma babu wani farin ciki kuka da kunci da damuwa sune abokaina yanzu, Daddy ka dubeni da fuskar rahma ka yafe mun laifina, wallahi nayi dana sani har ba iyaka akan abun nayi, sai yanzu nake gane cewar ashe anyi amfani da kuruciyata an sani abunda ba daidai ba,Amman wallahi daddy banida laifi duk da ni na aikata abun"



Kallona kurin yake yi baice komi ba, tsawon lokaci nida shi ba wanda yai magana, saida ya mula yasha iska sannan aya ansa mun da cewa.



"Waya gabatar mun da *FA'IZ* agidan nan?"



Kaina k'asa na amsa masa da cewa, "nice Daddy"



"Sadda na nemi Fa'iz nai mashi maganarki kinsan da cewa kai tsaye ya sanar dani inyi hakuri shi bai shirya aure ba, kuma bayajinki cikin ransa sosai"



Saurin kallon Daddy nayi da mamakin maganar da yai mun, bai kula ba ya cigaba da cewa,
"Banji komi ba sadda nake rok'onsa yasoki ya amunce ya aureki saboda yadda kike sonshi, har nake cin alwashin cewar bazai samu matsala dake ba, saboda ked'in kin samu tarbiya,da kalamai masu dad'i da iya zance na samu na shawo kan yaron nan ya amunce, amman duk gwagwarmayar nan baki sani ba, kikaje kina masa hauka kina yin dukkan abunda kika ga shine zabinki,ni kika ba kunya Bahiyya ba kowa ba domin dai har gobe bazan mance randa yazo nan ya bani takaddarki ba, tare da cewar inyi hakuri ya sawwak'e maki saboda irin rashin tarbiyar da kikaje kikai masa, ya kuma tattaro mun dukkan wasu tallafi danai masa abaya yazo ya aje mani ya tafi, ashe duk yadda na zage wajen tarbiyarki Bahiyya saida kika bani kunya, da wane ido zan kalli wannan yaron mai tarin kawaici da alkunya, ban san tsawon lokacin da kika dauka kina masa iskanci ba,duk ya jure amman saida kika kaishi bango Bahiyya! Kinyi mun adalci kenan? Kinyi ma kanki adalci da yarki?"



Kuka nake k'asa-k'asa wanda har kirjina d'aga wa yake, hakika na cuci kaina ko kuma ince Amma ta cuceni ta jefani cikin wani hali, taya zan fito fili in sanar da Daddy cewar matar daya dauki amanarta yaba itace silar komi, matar daya yarda da ita bayan ni itace ta cucemu muduka saboda bakin halinta da mugun halinta,nasan duk randa yasan abunda ta aikata mun saiyai jinyar zuciyarsa, saboda bayan mamana itace mace ta farko daya nuna ma kauna sa kulawa, gashi taci amanarsa.



"Ni bance kizo ki tusani gaba kina kuka ba, baida wani amfani komi ya riga ya faru bamai iya dawo da hannun agogo baya a gyara, abunda na sani shine har abadan abidina bazan nemi uban yarki in sake neman alfarma akan ya maida aurenku ba, kunyar sa ma nakeji akan yadda komi ya faru duk da bai daina daukata matsayin mahaifi ba,don har katin auren sa ya kawo mun, kuma ni nan ni na biya sadakin badan ya gaza ba, saidan nai masa kara da halacci.
Naji ciwo matuk'a da kika rasa nagartaccen miji irinsa Bahiyya, ba baki nai maki ba da wuya ki samu rabinsa nan gaba"



Wadannan maganganun n daddy sun sake dagula lissafina ainun,raina kamar zai fita haka naita kuka nama kasa cewa komi,don jikina har rawa yake saboda kuka.



"Daddy kayi hakuri, ka yafe mun don girman Allah, hakika nai wauta nayi kuskure nayi nadama marar iyaka, da ana dawo da baya a gyara ta da tuni na gyaro tawa, amman bakin alk'alami ya bushe, kai mun afuwa kota b'angarenka in samu natsuwa, nabi duk hanyar dazan ga na wanke laifina wajen Abbyn amnat Abun ya gagara, har na sare daman kai nake da hope akanka zaka shawo kanshi, Amman kace ba zakai ba na hakura da cikar burina na koma wa gidan Fa'iz fatana ka yafe mun ka daina fushi dani,nai maka alk'awarin kasancewa tagari yadda kakeso amman ka daina fushi dani"



Shiru yai na tsayin lokaci saboda wani tausayinta yakejin yana shigarsa ainun, tunda yake da ita bai tab'a fushi da ita haka ba shiyasa shi kanshi abun yana nukurkusar sa.



"Stop crying na hakura da fatan zaki gyara kuskurenki nan gaba, sannan bazan zuba maki ido kiyi ta zaka haka ba ko ki koma karatu ko na samu wanda zan had'aki dashi kiyi wani auren,..............zan koma karatun Daddy insha Allahu,amman karkace nai aure acikin wannan halin da nake ciki"



"Shikenan Allah ya kyauta gaba"



Na tashi don dauko Amnat mutafi yace in barta tare zasu kwana, nai mamaki saboda dai irin haka bata tab'a faruwa ba, anya ba akwai abunda ya had'osu da ammah ba? Tab'e baki nayi na wuce kawai zanso ma ta had'o sun, zanso yasan wacece yake tare da ita, sumumu kasau macijin sari kanok'e ce ita.



Karo naci da umaimah karamar kanwata ta fito daga dakina, na kalleta ba walwala afuskata nace, "me kika yo mun adaki?"



Cikin sanyin rai tace, "wallahi ba komi, daman nazo wajenki ne ki taimaka mun nayi solving din wani assignment"



Na kauda kai kawai ina rab'ata na wuce ina cewa, "banda lokaci"



Na rufe kofata na saka key,wannan daren ban runtsa ba tunanin duniya ya addabeni, jinake inama ace komi mafarki ne ba zahiri ba, ban san inason fa'iz ba sai d'aj tsukin nan, bana second biyar banjisa a raina ba, hotunan sa kuwa awayata duk na haddacesu,don tsaf zan iya zanashi don nidin na iya zane tun secondary school,ban bacci ba sai assalatu.



      
            ***********

      *FA'IZ S. ZUBAIR*








Mom muhseen✍🏻









6 / 35