Uncle Samir Book Complete By Arewa Novels.pdf

Author :  Nil Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 20.2K words

Chapter 1

Bismillahi rahmanir Raheem
Da sunan Allah mai jinkai

Sunana zaliha m Biki known as her majesty
Don't judge a book by its cover trust me zakuso wanan littafin inn sha Allah


Gabbatar da characters dina (main lead )
Uncle Samir junaid



Uncle Samir kenan shekaranshi 40 kacal aduniya
Babban dan kasuwa ne wanda ya sa shi ya zama well recognized a fadin Nigeria shi dan
Yola ne
Business mogul , philanthropist
Baida aure sabida alkawarin dayayima wata yar sweetheart dinshi har saita girma ya aureta
!!!!!









CIGABBAN LITTAFI
Laylas pov
Ina zaune class naga wani mutum sanye da bakaken Kaya dauke da wani ledar daga ninsa
nasan cikin mutanen uncle Samir ne .

Kauda Kai nayi dasauri ban son attention sosai wallahi ama kash

Ya iso gurin
Hajiya ya llabai yache abaki lunch í ľíµ— ya ajiye kan tebur din da take dun suna cafeteria
Nan take text ya shigo wayarta
"Nagaya miki banaso kinacin junk food, so eat it before I come and feed u myself"

Juyawa tayi ta sake kallo tagani shin ko yana gurin ko ya boye ne
Babu kowa kawarta ta karbi parcel din
Ya tafiyanshi

Huh Aisha Wlh I am not happy in this marriage
Meyasa ?
Wallahi uncle Samir yayi min tsoho da yawa komai nasa elderly stuff ne
Layla ali
Shekara goma sha Tara
Nile university take karatu aji biyu 200level

Kinga yanda yake yi agida kuwa I can't go out I can't have fun kullum cikin gida sai kallo ,
karatu , vlog ko vlog din ma yana monitoring dina

I hate him wallahi bansonshi
Ke meh haka ? Stop it idan baya SONKI bazai dinga efforts dinan ba
Idan baya SONKI bazai nuna kishinsa ba

Mtswww nidai ta shi muje gida
Suka taka sai parking lot Tashiga mota ta Kai ta Gida Ita kuma ta koma gida abinta


Tuna baya (Past) yada sukayi aure
Samir abokin babanta ne sosai yana mutanta shi , shima haka kulum mahaifinta malam
Abbakar yana yawaita masa maganan yayi aure Kai anan ne ya hadashi da Layla

Samir in badamuwa ga Layla nan mana tagirma why not ahadaku since u re single bakada
mata

Hmmm Alhaji kenan saika che Dagaske
Shikam Samir har aransa yana mutuwar sonta shiyasa yake mata siyaya idan yaje gidansu
itama tana sonshi ama ba soyayyar aure ba

Wallahi da gaske nake idan katashi sai kayi magana yana fadin haka ya tafiyarsa

Samir ya shiga tunanin
Zata soni haka kuwa ?
Anya ban mata tsufa ba ?
Can she cope ?
Zata iya daukar nauyina ?
Ya kwanaa da tunanin haka

WASHEGARI
Sai sukayi magana da mahaifinta
Shikam dadi yadinga ji sabida idan yahada alaka dashi zai samu benefits dole auren nan
yayi

Ya koma gida ya sanar da Mahaifiyarta
Ki sanar da yarki
Tohm Alhaji

Ta wuche daki
Tunda aka gayama layla batun aure take kuka ita ya mata tsoho metasani a aure mexatayi?
Yanzu Taafara karatu

Tayi magiya har tagaji ta bawa baban ta hakuri ama Sam shikam ba abinda yake tunani
kenan ba

Ta kwana tana tunanin yanda zata bulo da wanan al Amari takera kawarta Aisha tabata
shawarar taje ta gansa suyi magana .

Ta kwana da farinciki sosai a ranta ganin zata je gurinsa zaa nemi mafita !!!

Chapter 2
WASHEGARI
Ta shirya tsap cikin wani Jan lappaya tadubi agogo Karfe 10am na safe
Tasan lokacin yana nan
Ta wuche straight sai office dinsa

Yana ganinta nan yadinga Murmushi da jindadin ganinta

Uncle ina kwana
Lafiya kalau wai ke yaushe zaki daina chemin “uncle” kidaina ki chanja

Kallonsa kawai take daban mamaki
Yushe aka fara wanan ?
Uncle alfarma na zo nema
Shigo zauna shine kika tsaya chan ? Come in
Menene ? Fadamin inji
Uncle dan Allah kache ma baba bazaka aure ni ba
Kallonta kawai yake Cike da mamaki
Dan Allah uncle kaga bandade da shiga jamia ba uncle ni karamar yarinya ce
Yanzu nake kokarin building life dina

Hmmmmmm ya ja dogon numfashi ya kalleta da wani shaukin so a idonsa

Bakyso ?
Cikin ranta tana ta mamaki Wai shi baigane menake fada tun dazun ba ko me ?
Eh banaso
Nikuma Inaso

Uncle kamar diyarka nake fa ta cikinka
Dun meh zaka yarda da haka ? Agaban idonka na girma sanan kache aurena zakayi ?

Kiyi hakuri wallahil azeem bazan iya juriya ba ina SONKI sosai I have to confess

In ba dakeba bazan iya Rayuwa ba tun randa nafara ganinki na kamu da SONKI since when
u were 8 yrs old

Dalilin dayasa banyi aure ba kenan
Yanzu kuma kin girma kin zama budurwa I want you

Uncle tafada da karfi ta tashi tsaye
Karubuta kaje u will never be happy with me in this marriage kuma bazaka taba ganemin ba
u are now my enemy

Ta juya ta wuche
Komawa yayi cikin sit dinshi ya kwanta ya lumshe ido

Da maraice 6pm
Ta fita da niyan ta gudu da saurayinta
Karfe 8 tayi baa ganta ba dole Samir ya tura mutane nemanta baa ganta ba akayi tafaman
nemanta bata nan wayarta kashe ya shiga rudani sosai

Mahaifiyarta sai kuka take tana ganin laifin mahaifin layla

Samir ya kerashi ya Che masa in sha Allah sai ya nemota

WASHEGARI
Haka ya tura men dinshi a cikin garin Yola a nemota Kai har karkashin dutse duk saida aka
Duba babu ita

Yasamu wani Tracker akayi trackingdinta
Tana gidan wani saurayinta wanda ko kawarta Aisha bata San dashi ba

Mahaifinta ya je dakansa ya daukota ta sha duka kam
Saida Samir ya shiga tsakanin su

Rike masa Riga tayi da karfi tana kuka sosai
Cikin fushi babanta yache ma Samir ya turo gobe Azo tambaya sanan a daura aure daga
baya sai yakai Lefe tunda tashiga Gida

Aikuwa sai kuka take sosai Akan abinda yafaru
Tashiga damuwa sosai
Kawarta Aisha ta zo Gida washegari tana tabata hakuri ama mutuniyar ko saurare batayi

WASHEGARI
Tasheka office dinshi ta durkusa kasa tana bashi hakuri da kar ya aureta Wlh bata sonshi

Shikam yarasa yada zaiyi da rayuwarsa wanan yarinyar zata kasheshi

Idan ban aureta ba zan mutu Akan wahala Nikuma bazan iya jure ganinta cikin wanan halin
ba ya Allah

Tashi shikenan jeki Gida zanyi magana dashi tana komawa
Mutanen sa na zuwa akayi komai nan take
Ta sha kuka
Tayi kuka kamar ranta zai fita

Chapter 3
Da maraice
Aka tura motoci dauko ta Kai bukin sai ahankali fa Bawani shiri ba komai haka aka kaita
gidansa idanunta sun kumbura sosai sabida kuka

Yan dangin dasuka samu zuwa sukayi mata waazi da fadakarwa akan ta gyara da sauransu
dai

Tayi kuka dazasu tafi
Bata San lokacin da bacci ya saceta nan zaune ba ba shiri

Yana shigowa ya kalleta ahankali za tausai ba abinda zai iyayi

Ya furta
Layla zan yi hakuri zan jure duk wani kiyayya taki na maidashi so
Ya ajiye kazar a fridge da lemun daya siya
Ya gyarata ahankali ya koma dakinsa ya kwanta

Ya kwana da tunaninta , yanata tunanin inda aka ganta last sanan anya bai taba ta ba kuwa
?
Ta kwana gurinsa ache baiyi komaiba ? Yana ta tunani har bacci ya sace shi


WASHEGARI
Samir’s pov
I woke up happy not happy
Yayi wanka yayi sallah
tunaninta kawai ya fado min a rai
Tashi yayi da sauri ya dauki rigarsa

Farar t shirt da sweat pants yakai mata
Kafin ya shiga dakin saida ya tsaya yana tunanin outburst dinda zata yimasa

Knock!!! knock !!
Ya kwankwasa ba amsa yayi kusan minti biyu agurin ba amsa

Yabude ya shiga
Assalamu alaikum
Ya na salama yaganta kan sallaya tana kuka
Shiru yayi ya iso ya jiye Kayan Yafita
Ba adade ba ya aiko yan aiki da abinci ,Kayan marmari irin su fruits haka da kuma lemu

Ya rabb ya zanyi da wanan iftila’i
Yana zaune kan kujera a waje yana ta tunanin rayuwarsa ya zaiyi da kiyayyar masoyiyarsa

Sir !!!!
So Nawa nache ma kadaina kirana sir
Dariya kawai yayi
Sorry Samir I just wanted to cheer u up
Yana fadin haka ya jawo kujera ya zauna kusa gareshi

Suleiman kenan yana daya daga cikin ma su tsaron Samir ya dade tare dashi har abun
yafara kaisu ga abota mai Karfin gaske ya daukesa tamkar dan uwansa

I know this must be hard ama kayi hakuri phase ne na Rayuwa kuma zaka fito shi Lfy lau inn
sha Allah

Kallonsa kawai yayi ya kawar da Kansa
Hmmmmmm
Natuna zaa je asiyamata Kaya she don’t have any here
Okay wane time zamu je
Anjima
Okay shikenan
Suka fara hirar aiki


Bangaren layla

Harta fara magana da yar aikin Gida wacce takoma kaman mama agidan
Waton inna zuwairah
Tadade agidan tana aiki tareda shi

Hajiya Layla kiyi hakuri kidaina kuka kinji wallahi Samir mutumin kirki ne
Yanada mutunci sosai zaki so shi ki kwantar da hankalinki

Inna bazaki ganeba wallahi bansonsa takara kuka ta shige jikinta
Yi hakuri yar Samir
Tashi tayi ta tabe baki tana bata rai ni aa kidaina
Tayi dariya sosai toh tashi ki chanja kisaka wanan da yakawo miki kafun asiyamiki wasu

Haka ta tashi rai bace ta chanja tafito komai yayi oversize bajikinta bane

Ta zauna ta ci abinci tana gamawa suka fita da inna suka fara duba gida tana nuna mata
yanda gurin yake

Ahhh gidanan babba ne Ashe inna har da gurin Shan iska
Ehhhh nan Samir ke son zama ai
Toh banson gurin tana cikin tafiya taganshi tareda Suleiman zaune sauri tayi ta juya Takoma
tafasa karkare zagayenta

Kallon Suleiman yayi
Kagani ko ? This is what I am saying

Chapter 4

Suka je mall yayi mata siyayya har na fitan hankali
Abinda bai sani ba shine size din breziya da pant dinta shuru kawai yayi daya isa section din
yanata kallonsu yarasa yanda zaiyi

Ya Mika hannu ya dauko wani bra ya saka hannunsa ya shafa tareda lumshe idonsa

Ya Che abashi irinsu guda hamsin da pants kallo dai yayi ma wani size yache abashi dozen
takwas styles daban daban

Aka dauka sai gida itama kanta tayi mamakin yanda yasan size dinta komai yyi daidai for
now zata dinga sa ready mades da su abaya kafin agama mata dinki
Yasiya leshi Dari , Atamfa Dari , panties dozen takwas , breziya hamsin , takulma hamsin ,
jeka different sizes da styles hamsin ,turaruka baa magana , Kayan kwalliya , man gyaran
gashi da kuma na wanke Kai , lotions , sabon brush da set na toothpaste, abaya Dari , two
peice abaya hamsin , gowns hamsin bedsheets yasiya
Haka aka jerosu cikin akwatuna tana zaune daki da inna su suka tayata budewa da kuma
gyarasu a locker da wardrobe

Yana shigowa suka fita gabadai
Tana gefe tana gyara abayas dinta ko kallonsa batayiba
Ya iso inda take yayi tsaye shi fa kamar tsoronta yake hahah

Ya gyara muryarsa L….layla
Juyowa tayi ta Bawani mugun kallo

Lafiya ?
Lafiya lau dama na tambayeki ne idan Kayan sunyi
Kallonsa tayi cike da takaici tayi tsaki ta Che yayi
Shiru kawai yayi yana observing dinta

Har a ransa baya jindadin abinda take ama “she is just a child I will pardon her”

Chan idonsa yakai ga bra da pant dinta
Su ma sunyi maki ?
Yana nuni da pants din
Eh sunyi
Okay ya girgiza Kai alamun ya gane

Yafida sabuwar waya daga aljihunsa
Latest iPhone 17 pro max yabata

Gashi
At first shareshi tayi yacigaba da magana
It’s fully charged sanan akwai sim a ciki numbers dinki ma na ciki

Juyawa tayi ta ganshi rikeda waya
Karba tayi tana kallon wayar tana Murmushi har a ranshi yaji dadi sosai ganin farincikinta

Yabata ATM ga wanan new account dinki ne akwai 10million aciki incase in zakiyi wani Abu ,
pin dinki is 1905
Ta karba rai bace

Nagode

Kallonta kawai yayi yanata mamakinta

Yayi tsaye yabarta tana gyara yana kallo chan ko me yafaru ji kawai tayi yana matsowa

Kallonsa tayi cike da takaici
Meye haka ? Tana ja baya ko kafin takara magana yahadeta da bango

Ya sa hanunta a kirjinsa yana kallonta Ita kuma hanunsa take kallo da abinda yake kokarin
yi

Me……. Meh …..haka
Bakiji yanda take bugawa ba layla yana fadin haka yana shafa suman kanta


Stop it ta buge mishi hannu ni uncle dina kake not my husband
Bazantaba kallon ka amatsayin mijina ba uncle dina kake

Layla ni ba uncle dinki bane ni mijinki ne
Kisa aranki inn sha Allah saina malaki zuciyarki

Allah kyauta !!!!
Tana fadin haka tafara yunkurin tureshi abanza

Hada lips dinshi da nata yayi ya fara sumbatar ta ai tuni ya wargaza mata tunani

Dagudu ta shige toilet ta kulle kofa
Murmushi kawai yayi ya fita yakoma gurin su inna ku koma ciki Kuyi aikinku…

Chapter 5

CIGABBAN LITTAFI
Ta ajiye kawarta ta wuche gida abunta as usual ba ruwanta dashi
Ko gaisuwa bata hada su , bata masa girki ba ruwanshi baya tilasta mata duk abinda takeso
shizatayi

Dakinsa zata je sai aka gayamata yana bayan gida yana meeting da wasu
Ai cikin fushi ta nufi inda yake da bakin sa

Ganinta ya sa shi tsoro sabida ya San mexata iya yimasa a bainar jammaa

Hadiyeh yawu yayi yana kallon Suleiman da idanun tausai
Tana isowa ta dinga masa tsiwa suma shiru sukayi suna Kallonta

Karka sake aikomin abinci a makaranta I never told u I was starving
Shuru yayi yana tsaye yana kallonta hnnunsa cikin aljihu

Girgiza Kai yake da duk abinda tache ya girgixa da nufin eh ya ji ta
Haka har ta tafi

Kallonsu yayi yabasu hakuri suma mamaki suke Mr Samir ne kuwa wanan like macce zata
dinga masa haka Ashe akwai wacce zata iya yimasa fada ya yi shuru kuma

Sunata kallonsa da idanun mamaki ga tausai
Haka suka gama meeting din kuma Alhamdulilah ya samu sun kare project din Lafiya lau

Suna fita Suleiman yafara masa fada
Why are u so obsessed with this girl ? Ji abinda tayima and ji abinda kadinga like Man U
were literally shaking in front of her indai haka soyayya take wallahi I done want to ever
experience it whatttt!!!!!

Ya tafiyarsa
Shidai anan ya zauna ya kera yan aiki suka kwashe duk wani system na meetings din da
wayyoyinsa

Ya kwanta kan kujera ya aza kafarsa kan tebur

Ga chida da akeyi sosai alamun ruwa yana zaune har ruwa ya sauko
Inna na zaune a parlor tache itafa bata ga shigowar sa ba
Ama bari ta tambaya taji
Yan aiki sukache yana waje

Salati ta dinga yi cikin mamaki da sauri ta sheka

1 / 7