MAI DAKI Book 2 Hausa Read Novels By Hafsat C Sodangi.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 5

12K to 13.9K   out of 13.9K words

kaita

kunnena.

"Ranki shi dade barka da shan ruwa."

Na ce, "Ai mnu nan bamu sha ba

tukunna, wanene mai magana?"

85

"Ahmad ne."

Na dan yi shiru ina tunani, to ni kuma

ina nasan wani Ahmad? Na ce, Kayi

hakuri ban gane ba."

Ya ce, Mutumin da ki ka yi sayayya a

shagonshi kwanakin baya. Na ce, Au, haka

ne ina wuni?

Muka fara gaisawa, ya ce Nayo ta so na

kira to wani uzuri ne ya same ni shi ne

dalili na kuma kira ne a yanzu don na nemi

wata alfarma da fatan kuma ba za a ki yi

mun ba?

Na ce, mecece alfarmar da ka ke nema?

Ya ce, So nake a bani izinin zuwa gida.

Na ce, Aiya, ai bana ma gari. Ya ce, Eh

naso nayi zaton hakan da ki ka ce mun ku

ba ku sha ruwa ba, kina wane gari ne

yanzu haka?"

Na ce, Ina Birnin kudu. Ya ce, Au ki ce

kusa da garinmu kenan. To sai yaushe ki

ke ganin za ki dawo?

86

Na ce, Gaskiya sai gab da sallah ko ma

bayan sallah. Muka yi sallama da shi na

ajiye wayar.

Ni shaf na ma manta da shi gaba daya.

Baba Ladi ta ce, To shi kuma wannan

wanene?

Na ce, Wani ne. Naja bakina nayi shiru,

ta ce Kya dai ji da gulmarki.

Ina zaune a sashen kannen Babana

muna aikin abincin buda baki wayata tayi

kara.

Na dauka ina dubawa, Ahmad ne. tun

bayan da müka yi waya da shi kwanai

takwas kenan cif, ba mu sake ba sai yanzu

da ya kira ni.

"Ranki shi dade."

Na ce, "Tare da naka." Yayi murmushi

ya ce, To amin ya azumin? Na ce, Mun

gode Allah. Ya kasuwa? Ya ce kullum

muna godiya ga Ubangiji.

87

Na kira ne na shaida miki ayi abin buda

baki da ni don ina kan hanya. Cikin

mamaki na ce, Gaskiya ko wasa?

Ya ce, Akwai wasa ne a tsakanina da

ke? Shiru nayi. Ai maganata da ke babu

wasa a cikinta, abinda na kudura a raina

kenan kuma kema ina fatan ya zama haka

a wurinki.

Sammani na tura ya taho da Ahnmad

daga inda ya tsaya, sannan ya shigar da shi

dakin su da ke zaure na samarn.

Muka fara gaisawa yana dan tambayata

wasu abubuwa ina ba shi amsa.

Na ce, Nayi mamaki sosai da ka ce mun

kana hanya, sai daga baya na tuna ka ce

mun kusa da garn ku ne.

Ya ce, Eh kusa da garinmu ne amma ai

da nisa a tsakani koda dai ba sosai ba.

Ni dan Kano ne Challawa. Kuma

saboda rashin adalci irin naki sai ki ka yi

tunanin garinmu na zo ba wurinki ba.

88

Na dan yi murmushi na ce, A a ni

haka nake nufi ba. Ya ce, To me yasa ki ka

yi riko da wannan hujjar idan ba haka ki

ke nufi ba?

Na taso ne takanas nazo wurinki don k1

tabbatar da duk wata magana da zan yi

miki ko kuma wacce zata biyo baya.

Ina kuma fatan ba zan samu matsala

daga bangarenki ba. Shiru nayi ina

sauraronshi tare da yin wani tunani a cikin

raina.

Ba zan son na sake yin gaggawa a cikin

zancen neman aure ba, da koma wayea

yanzu nafi bukatar fahimtar juna farko

tukunna.

Don kuwa babbar matsalar da na gamu

da ita a gidan Ishak kenan, koda dai a

lokacin ban san komai game da zaman

aure ba. Don haka yanzu daban.

Shirun da ya ji nayi shi ne yasa shi ci

gaba da magana.

89

"Na riga nayi booking din wurin kwana

a cikin gari, don haka zan dawo gobe don

mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Zan iya shiga na gaidamutanen gidan?

Na ce, Eh bari nayi musu magana. Ya ce,

To.

Kasancewar su Baba dan Juma ba sa

nan sai kawai ya gaisa da su Baba Ladi ya

wuce.

Kwana nayi ina tunane-tunane ranar

saboda ban taba yin zaton cikin dan

Rankanin lokaci zan fada cikin harka ta

zancen aure ba.

Koda Babana ya tabbatar mun ba zai

yiwu na koma Makaranta ba sai nake

tunanin a kalla zan shekara ko ma fin

hakan kafin kuma na sake yin wani auren.

Ko ma don na dan huta wasu abubuwa

na 6acin rai da fargaba da ke cikin aurén.

Don haka maganar da na tsayar kawai a

raina ita ce ba yanzu zan yi wani auren ba,

don kuwa zan fi son idan nayi aure nan

90

gaba nayi zamana ba tare da na sake

fitowa ba, tunda dai ba jeka ka dawo ba

ne.

A Kamar yadda ya ce haka din kuwa ya

yi, karfe sha daya daidai ya yi sallama.

aKwalliya mai sauki nayi ta atamfa

(Cote Divoire) sai gyale mahadinta. Muka

gaisa ya ce, Ina fata dai ban bugo

sammako ba ko?

Na ce, "A'a haba. Ya ce, To ai ban sani

ba don kuwa da kyar na iya bari goma da

rabi tayi.

Ya ce, To me ki ka ce Hauwa'u? Tunda

kin ga matafiyi nake dole ina so na koma

gida a yau in Allah ya yarda saboda

mahaifiyata.

Don haka nake so ki taimaka ki bani

amsar da ki ka yii alkawari don 1na san

halin da nake ciki.

Na ce, To a gaskiya ni bana son

maganar aure ta zamo cikin gaggawa, in

91

da hali ina son fahimtar juna ta zam0

farko.

Tunda shi din abu ne da ake yi ba da

nufin rabuwa ba. Zuba mun ido yayi yana

kallona.

Zuwa can ya ce, Kin yi magana irin ta

manya, na kuma yaba da zurfin tunaninki.

A matsayin da ki ke a yanzu lokaci

kamar yaya ki ke so a bai don ki fahimci

mutum, shekara daya ko biyu ko fiye da

haka?

Amsar da tia kasa ba shi kenan saboda

na gane gatse yake yi mun. Kina ganin

mutum kamar ni zan iya yi miki irin

wannan neman?

Kuma nema na aure? Ni ba karamin

yaro ba ne ina da 'ya'ya ina da mahaifiya,

bayan haka kuma ina zaune ne a yanzu

bani da iyali.

A irin kallon da nayi miki da iya abinda

na fahimta a tare da ke a yanzu bana zaton

92

iyayenki za su bar ki zuwa wannan tsawon

lokacin ba tare da aure ba.

Na dade kwarai ban ji wani abu game

da wata mace ba kamar yadda ki ka zamo

mun Hauwa'u.

Don haka kada kiyi mun rashin adalci

wajen zartar da hukunci a kaina. A hankali

na ce mishi to ka bari na dawo gida

tukuna.

Ya ce, To shi kenan yadda duk ki ka ce

mai neman a ba shi ai ba ya fushi.

Atamfofi masu kyau ya kawo ya baiwa

su Baba Ladi dukansu ya ce su ci sallah.

Mun ci gaba da yin waya da Ahmad,

kullum yake kirana safe da yamma muna

gaisawa.

Cikin dan kankanin lokaci sai muka yi

sabo sai kuma na fahimce shi don kuwa ko

a waya sai na gane yana da bambanci da

Ishak.

Don kuwa shi mai barkwanci ne. ban

shirya dawowa gida ba sai ana azumi

93

ashirin da biyar kenan sallah saura

kwanaki hudu.

Tsaraba sosai aka yi mun, Baba Ladi da

kishiyoyinta kaf dinsu tsarabarsu ta Umma

ce.

Don kayan Siyarwarta irin su kuka,

bushasshiyar kubewa, daddawa, barkono

da dai sauransu tsaraba sai da naki diba

saboda sanin da nayi dole sai na biya

kudin motarta idan nazo tasha.

Amma duk da haka ban tsira ba, don

kuwa kudi mg yawa suka karba saboda

bugun shinkafar da suka hado ni da shi.

Tun ina hanya Ahmad yake kira har na

kusa sauka.

Muna gab da motarmu zata shiga tasha

ya kira ni.

"Ga Direbana zai zo ya dauke ki zuwa

gida. Na ce, "A'a ayi hakuri yallabai

kada Babana ya kore ni a gidan. "

94

Ni dai har yanzu ban daina mamakin

Ishak ba. Ashe ya iya magana cikin

tsanaki yi ne ba ya yi.

Ya yi mun alkawura masu yawa amma

duk wadanda kudi ne za su aiwatar da su

shi kwata-kwata ma bai fahimce ni ba

kenan tsawon, zaman da nayi da shi.

Ya manta bai yi mun alkawarin ba zai

sake dukana ba zai ba ni lokacin shi ya

nuna mun so da kauna da kulawa da

tausayawa wadannan abubuwan sune

manyan abubuwan da na rasa a gidan

Ishak.

"Kiyi mun magana Hauwa'u don

Allah."

Na ce, "Ishak! Ka saurare ni ka ji abin

da zan gaya maka, kaje ka samu wata

matar ka aura ko kuma ka maida wata

daga cikin matanka na baya da ka saką zai

fi maka akan zuwa kofar gidanmu da ka ke

yi ka ke sawa ana kirana.

113

Auren da zan yi aure ne na SOsai da

sosai da zuciya daya ba tare da wata

manufa ba, ina son Ahmad ina kuma fatan

auren da zamu yi ya zamo mana alheri a

duniya.da lahira.

Kai kuma ina yi maka addu'ar Allah ya

kara maka hakuri ya kuma baka mace

wacce zata iya zama da kai kuma ta

kwarai ko don dana da ke gidanka.

Ina kuma rokonka da kada ka sake

zuwa gidan nan ka kira ni don gudun bacin

rai."

Zama nayi na yi wa Umma bayanin

abin da ya faru tsakanina da Ishak ta ce,

"To! Haka Allah ya kaddara amma

wannan al amari.

Hirarmu ta yi nisa da Uma har na rinka

bata labarin abubuwan da suka rinka

faruwa da ni a gidan Ishak, wadanda ko

sau daya ban taba fada ba.

114

Ta ce, "Ikon Allah, ai shi yasa aka ce

wai MAI DAKI shi yasan inda yake yi

masa yoyo."

Na ce, "Shi yasa na yi matukar mamaki

da yazo yake kokarin naje na kashe aure

na dawo gidanshi."

Umma ta ce, "To ke dai sai kiyi a

hankali, ki kuma yawaita addu'a shi

wannan din ya zamo miki alheri, shi kuma

Isiyakun Allah ya ba shi wacce zata zame

mishi alherin shi ma.

Ai shi yasa wani lokaci sai abu ya same

ka kayi ta bakin ciki sai daga baya ka gane

alheri ne abin.

Ba gashi ba da yanzu kina can a

wannan halin tunda mai hali ai ba ya

fasawa kuma maganar gaskiya ita ce zama

da miji mai duka abin akwai matukar

wahala.

Ki kuma kudura a ranki za ki yi zaman

auren ki da zuciya daya."

115

Shirin aure sosai nake yi da Umma,

kudin hidima da Ahmad ya bani shi ne

nayi amfani da shi wajen yin kayan daki.

Sai kawai dan cikon da aka yi akai

wajen siyan asalin kayan kamfani dan odar

da kuma na'urorin kicin.

Duk wani nawa na gayyace shi ciki har

da Hindu da Momi, abin ya yi musu dadi

ba kadan ba, Momi ce kuma ta kawo mun

guzurin littafin girki na turanci (Woman

and Home) da ya kunshi girke-girke iri-iri

wajen kala dari biyu.

Kayan aure na musamman Ahmad ya yi

mun tunda ai ko Hausawa ma sun ce wai

masu abu da abunsu. Don kuwa komai a

cikin kayan na asalin mai kyau ne.

Mutanen birnin kudu kuwa kamar ajiyar

garin suka bayar don kuwa wadanda ba su

zo ba kadan ne.

Da addu'ata fal baki da zuci na sa kafa

na shiga gidan Ahmad.

116

5 / 5