Author : Khaleesat Haidar Category : Romantic Hausa Novels
"Toh xan raka ka airport plss daddy" Ammi ta jefa mata wani kallo tace "islamiyyar fa?" Ta marairaice tana kallon Ammi, Daddy yace "Ba sai ta shirya ba mu fita gaba daya, idan ya so sai a ajiyeta a makarantar idan sun dawo airport" da sauri Imaan ta shige dakinta don fara shirin islamiyya , da kyar ta ci abinci bayan Ammi ta tilasta sanin bata wani ci abincin ba daxu da ta dawo, ganin daddy ya fita da jakarsa ta kai plate din kitchen da sauri ta fito ta xura hijab din islamiyyarta ta sa safa da takalmi ta dau jakarta xata fita Ammi tace "Ki tafi da jakar laptop din" dawowa tayi ta dau jakar ta fice da sauri ba tare da ta bi ta kan kudin da Ammi ke cewa taje daki ta dauka ba, Mujaheed ne tsaye kusa da motor daddy rike da makullin mota yana jiran dawowansa daga part din inna da yaje sallama, Maimoon ce ta kwalo ma Imaan kira tana tambayarta inda xata, Imaan tace "Ni motar daddy xan bi ku wuce kawai idan kun shirya kar ku jirani" Mujaheed ya hade rai yace "Ina zaki?" tace "Daddyna xan raka airport idan ya so idan muna dawowa sai a ajiye ni a islamiyyar" yana girgixa kai yace "kama gaban ki.... uban wa xai ajiye ki islamiyya ni na maki kama da driver din ki, daina kallona ki bar nan wajen my friend" Hawaye ya fara kawowa idonta ta tsaya tana kallonsa har sannan, strictly yace "Baxa ki daina kallona ki bace min a nan ba?" Juyawa tayi ta nufi sashinsu da sauri, lkci daya ta fashe da kuka, yana ganin haka ya xaro ido yace "Imaan" kin juyowa tayi, ya fara dube duben babban compound din kafin ya bi bayanta da sauri, har ta kusa shiga balcony dinsu ya fixgota ta juyo ta kara fashewa da kukan shagwaba, rikicewa yyi hango daddy da yyi yana tahowa daga part din inna, yace "Toh me nayi maki, kina son kiyi lattin islamiyya ne?" Cikin rawar murya tace "Toh bayan lkci bai yi ba" yana Satan kallon direction din da daddy ke tahowa yace "Toh naji goge idonki mu je" ta turo baki tace "Saboda kaga daddy na koh?"Wani kallo ya dinga mata kafin ya kama hannunta suka koma gun motar, bude back seat tayi ta ajiye laptop dake hannunta ta shiga tana kallonsa ganin irin kallon da yake mata tace "Yaya ka tuna watarana da za mu je gidan Mama fa'ixa abinda ya faru?" Bai tanka ta ba ya dauke kai, sai da daddy ya fara shiga yyi ma Ammi sallama sannan ya fito ya nufo parking space, yana kallon Mujaheed dake tsaye yace "Sorry for keeping you waiting son" murmushi kawai Mujaheed yyi, daddy ya bude back seat ganin Imaan ciki yace "Mamana why not seat at the front" tace "Noo, I am more comfortable here" yace "A'a dawo gaba" Mujaheed yace "Abba tace ta fi son nan ne" Daddy yyi murmushi ya shiga motar shi ma, Mujaheed ya shiga maxaunin driver, mai gadi ya bude masa gate ya ja motar. Sae da suka hau saman titi Daddy yace "Mujaheed pls ku dinga hakuri da grandma dinku, ita haka Allah yayi ta, mu wa enda ta haifa ma muka iya xama da ita balle ku grandchildren, ya kamata kafi kowa sanin halinta tunda ka xauna gunta, kasan abinda take so kasan abinda bata so, plss bana son in ji kun sake samun matsala kaji?" Yana murmushi yace "In sha Allah Abba" Daddy ya kalli Imaan da ta dauke kai yace "Ke kuma kar ki yarda ta kirani tace kin mata wani abu, wllh zan sa6a maki, tsakanin ki da ita respect babu wasan grandma and grandchild tunda bata so, I repeat respect her ynda xa ki respecting Ammin ki" Imaan tace "Ni dama na daina xuwa part dinta.... Kullum sai tace an mata rashin kunya" daddy yace "Don't try dat, you make sure kinje gaisheta everyday, kinsan Allah duk kika yrda ta kirani ta kawo karan ki xan bar duk abinda nake in dawo in ci kaniyar ki" kamar zata yi kuka tace "Toh yaya fa? Ae shima yana mata rashin kunya, Rahma da Ummi ma haka" Ta madubi Mujaheed ya mata wani kallo ta murguda masa baki, daddy yace "Ae duk na ja masu kunne kuma suna jin maganata ke ce dai mai kunnen k'ashi" Imaan ta bata fuska xata yi kuka, the remaining journey to d airport was silent, Imaan dai sai kumbure kumbure take. Suna isa airport din wajen karfe hudu da rabi, suka raka daddy har ciki, daddy na rike da jakarsa yace "Thanks much sai mun yi waya Muhd" Mujaheed ya dukar da kansa yace "Allah ya tsare Abba" Daddy yace "Ameen" yana kallon Imaan dake goge hawayen idonta, murmushi kawai yyi ya mata side hug yace "Sai mun yi waya anjima daughter, na maki transfer ta account din ki" daga haka ya sake ta ya juya ya wuce, Imaan ta fashe da kuka, Mujaheed dai na tsaye har sai da ya tabbatar baya ganin daddy sannan ya kalleta ya hade rai yace "Toh ki bi sa mana" ta gefen ido ta kallesa bata ce komai ba tana kuka, ya ja tsaki ya juya ya fara tafiya, sai da taga yyi nisa ta bi sa da sauri tana goge idonta...A haraban airport din ta tadda Mujaheed suna gaisawa da wata, Imaan ta ja gefe ta tsaya kamar ance ta waiga taga wani tsaye jikin ride dinsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, she couldn't tell ko ita yake kallo, ta dai dauke kai da sauri, bayan few seconds ta kara satan kallonsa taga saitin ta yake kallo still, tayi saurin dauke kai, again ta sake kallonsa, cire glass din idonsa yyi yana kallonta da kyau, a hanxarce ta kauda kai tana son tuna ina ta ta6a ganinsa, bata hakura ba ta kara satan kallonsa ganin bai daina kallonta ba ta juya tana kallonsa directly ita ma, murmushi yyi da har sai da dimples dinsa ya lotsa, ya xura hannunsa aljihunsa ya langwabar da kai yana kallonta dai, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan bayan sun gama gaisawa da friend dinsa, ya ga sai kallon mutumi kamar ta samu television take, takawa yyi har kusa da ita yace "Do you have any business with him?" Ta turo baki tace "Toh shi ma ai kallona yake" Mujaheed yace "Wuce mu je kar in kwada maki mari" ta gefen ido ta hararesa ta nufi gun motarsa ya bi bayanta, bude front seat tayi ta juya tana kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Mujaheed yace "Wai kina hauka ne" ta turo baki ta shiga cikin motar, tada motar yayi bayan ya shiga suka bar haraban airport din, sun yi nisa sosai kamar ance ta dago kanta ta ga wani waje da ake gashin kaji, ta kallesa da sauri tace "Yaya" kallonta yayi, ta marairaice masa tace "Don Allah ka siya min kaza plss" yace "In siya maki kaza?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "To kudi kika bani?" Ta turo baki, bai sake ce mata komai ba, ganin xa su wuce gun masu kajin tace "Wayyoo yaya plss" kara gudun motar yyi ya wuce wajen, kallonsa ta dinga yi kafin ta dauke kanta, ganin hanyar da ya dauka tace "To islamiyyar fa?" Yace "Sai dai in ajiye ki ki ta fi da kafa daga nan, ni ba drivern ki bane" yana shiga anguwarsu yyi parking gidaje uku kafin nasu ba tare da ya kalleta ba yace "Sauka" bude motar tayi ta fice fuuu ta nufi gate dinsu sai da ya ga ta shiga sannan ya karasa da mota gate din mai gadi ya bude ya shigar da motar. Ko kallonsa Imaan da har kota kusa part dinsu bata yi ba har ta shiga parlornsu, Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo parlon tace "Dawowa kika yi baki tafi islamiyyar ba Imaan?" A hankali tace "Yaya ne yaki kai ni" Ammi tace "Ba har dadin fashi kike ba, ki ci gaba" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Ammi ta wuce daki ta bar ta parlon. Bayan magrib Imaan na kwance parlor tana kallo, Ammi ta kirata daga kitchen, ajiye remote din hannunta tayi ta mike ta wuce kitchen din, Ammi ta nuna mata abincin Inna tace "Ki kai ma inna" Imaan tace "Ammi da xa mu kai Daddy airport fa sai da ya sake min warning a kan xuwa wajen inna" Ammi tace "So?" Ta marairaice tace "Toh ni kar inje in sake mata wani abu ta kira daddy" Ammi tace "Ni xan dinga kai mata abincin kenan" Kamar xata yi kuka tace "Ni wlh Ammi nace fa baxan sake xuwa part dinta ba har abada" Ammi tace "Toh kar ki je ki bar abincin a wajen" Imaan ta dau abincin rai ba dadi ta fita, Yusuf da Ummi na xaune parlorn Imaan ta shiga ta ajiye abincin, tana kallon Yusuf tace "Ina yini ya Yusuf?" Yace "Lafiya lau Imaan yau ba ciwon kafa kenan" Inna ta kallesa da sauri tace "Kaji wata mugun alkaba'i, kai fata kake kafar su yi ta ciwo kenan? Shi kenan ita kuma sae ta k'are a ciwo kamar warce ta kashe d'an mutum, ku dai 'ya yan Ahmadu baku da kirki, ku dinga sa ma bakin ku linzami don Allah" Yusuf yyi dariya yace "Daga tambaya kuma Hajiya inna?" Inna ta sharesa ta jawo wani leda tana kallon Imaan tace "Gashi nan Mujaheed ya kawo maki daxu, sai ki xauna a nan ki bude ki tsamma kowa don kema haka kike da sa ido, ni wllh ban ma ji dadin zuwanki ba tunanina baxa ki xo ba in cinye inyi nak" Imaan ta bude ledan da sauri, kaza ce babba guda daya sai kamshi da turiri yake, Imaan ta saci kallon kofa sannan ta saci kallon Inna dake goge plate din da xa a dibar mata ta fice parlon a dari da sittin, sake baki inna tayi da plate din hannunta, Yusuf ya kyalkyale da dariya, inna tace "Kaji daya daga dalilin da xa ku ji ance ta tashi kafa ya rike gobe saboda mugun halinta, toh meye kuma nama ni fatima? Halin fulanawan kenan fa rowa da mugunta, shi naman da xata d'an yaga ma kowa shine xata kwasa a guje kamar k'arya?" Dariya kawai Yusuf yake, inna da har hawaye ya kawo idonta tace "Don ubanta ta yi kiba kafin gobe idan ta cinye kaza daya, kuma Allah ya isa rai da aka sa min" Yusuf ya mike ya fice parlon yana ta dariya, mikewa inna tayi tana share idonta ta nufi dakinta tana cewa "Me aka yi aka yi nama kuma don Allah, wani irin nama kuma?? wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan, kuma shima Mujaheed din da gangan ne, ai yasan shegen rowa gareta da na tambayesa na wa sai ce min yayi xata dibar min, babu yanda ban yi kokarin fahimtar da shi kan cewar da kamar wuya fa shegiyar ta dibar min, to ga karshenta nan ta gudu, a dinga abu ba tsoron Allah" Ummi tace "Toh shi me ye ma na siya mata kaza bayan ko gaishe shi bata yi wlh a gidan nan" Inna tace "Ohon masu, kya bar ni budurwa, ni dai Allah ya isa" Ranan litinin sabon driver da Abba ya daukar masu ne ya kai su schl....🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
8.....
Yau Thursday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka ta ci abinci ta fito parlor ta xauna kusa da Ammi dake xaune, ta langwabar da kai tace "Ammi ina son xan je supermarket in siya pad da turarurruka" Ammi ta kalleta tace "Duk uban turarrukan da kika kwaso ranan sun kare kenan Imaan?" Yar dariya tayi tace "A'a ba su kare ba amma sun kai rabi" Ammi tace "Toh sai ki kira babanki bani da kudin da xan baki ki karo turare" Imaan ta bude ido tace "Ya min transfer din 30k ranan da xai tafi ai" Ammi tace "Tohhhh har 30k, lallai kam Allah ya taimaka" dariya Imaan tayi ta mike ta koma daki, Hijab dinta gogagge har kasa ta fiddo ta saka sannan ta dau karamar jakarta ta sa atm card ta feshe jikinta da turare ta fito parlor, ta durkusa kusa da Ammi tace "Toh Ammi ba ni kudin transport don Allah" Ammi tace "Ki duba gaban mirror a daki" tashi tayi ta shiga ta dauko sannan ta dawo parlon, tace "Yauwa Ammi ina son xan biya ta gidansu Mariya, tun Tuesday bata xo schl ba bata da lafiya" Ammi tace "Waye kuma Mariya?" Imaan tace "Lahh wannan da ke xuwa dubani wani lkcn idan bani da lafiya" Ammi tace "Kice min dai gidansu xa ki je ba supermarket ba" Imaan tace "A'a fa Ammi, kawai tunawa nayi, Ban ma san ko xan gane gidan ba fa tunda sau daya muka taba xuwa da Maimoon, idan ban gane ba kawai sai in dawo gida" Ammi tace "Gwara dai ki gane don ki dubota tunda tana yawan xuwa duba ki" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka tayi ma Ammi sallama ta fita Ammi na tunatar da ita tayi addu'an fita gida, tana isowa part din su Yusuf taga Umma da wata kawarta xaune a waje kan fararen kujeru, Imaan ta dauke kai duk da sun hada ido har ta wuce su ta nufi gate, Hajiya Salaha tana kallon Umma tace "Wace fitsararriya ce wannan kuma" Wani murmushi Umma tayi tace "Yar wajen Aisha" Hajiya salaha tace "Ikon Allah ita ce ta girma haka?" Tabe baki Umma tayi, Hajiya Salaha tace "Ita Aishar ta sa kar ta gaishe ki gidan nan kenan?" Umma tayi yar dariya tace "Ga dahir kin gani, ai fa ko idona xai makale cikin nata shegiyar baxata gaida ni ba uwar ta hanata" Hajiya Salaha tace "Tabdi ita wannan yar ficicciyar yar?" Umma tace "Ba shine bayan na dawo gidan nan naga ita da Mujaheed da bai san ciwon kansa ba bai san ciwon mahaifiyarsa ba tamkar su yi 6ude, ya maida Aisha kanwar uwarsa bashi da tamkar ta gidan, ita kuma yar mai ciwo yau mai ciwo gobe tunda sickler ce idan kin ga abinda yake mata ko kanninsa su Ummi bai masu, in takaice maki duk dai Aisha ta bi ta shanye min shi yanda ta shanye kanin ubansa, yanda kika san xai mata sujjada" Hajiya Salaha tace "Ikon Allah" Umma tace "Ae tuni na tashi tsaye, nice can nice nan, da taimkon Allah da taimakon Magajiya na kwato d'a na da karfi da yaji, yanxu ko ga maciji basa yi a gidan bangaren ma ya daina xuwa, I can't risk that, uban waye bai san tsafi Aisha take ba, gashi dai ta hana kanin babansa karo matar da xata haifo masa 'ya yansa duniya ta rufe masa baki ta hada sa da 'ya sickler kullum ana hanyar asibiti ana kashe Dan banxan kudade, Allah kenan, kuma in dai ina numfashi a haka yarinyar nan xata kare yau lafiya gobe babu, in Allah ya yarda sai yar nan sai ta xame masu jaraba duk sai ta tsiyace su muna nan muna gani, kee duk wanda xata ra6a ma wllh sai ya tsiyace, haka nan kuma xata yi ta xama ba mashinshini.... to ubanwa xai iya da ita ta kassara tattalin arxikinsa, ni fa duk duniya billahil azim bani da makiyiya da ya wuce Aisha, wllh xan iya yin komai don in toxarta ta da yarta, ni ko kishiyata ban jinta yanda nake jin Aisha, kuma yanda tasa aka toxarta ni aka min kishiya sai na toxarta ta ita ma ko ba jima ko ba dade, ina nan dai kan bakana lokaci kawai nake jira" Hajiya Salaha tace "Ae ko kar ki yarda wllh, ki mata fiye da wanda ta maki ma" Umma tace "Yanxu gobe ma akwai inda xa ni tare da magajiya da sai ki fito mu je tare, wani take take na fara gani nake son taka ma abun burki tun wuri" Hajiya Salaha tace "Haba na me kuma?" Umma tace "Ki ji fa don walakanci yanxu sai su yi ta makala ma Mujaheed ita ya kai ta asibiti, ga uban kudaden da xai kashe wanda nasan ko ance xa a basa baxai amsa ba to akan wani dalili? Shi ya dauro mata ciwon? Na samu na rabasa da shegiyar yarinyar suna kara lika masa ita to gwara in kara xage damtse, ba wani ke nemo masa kudin ba kuma kudinsa ba na banxa bane, su je can su da suka haifeta su karata da cutan ta" Hajiya Salaha tace "Gaskiya kam Allah ya kai mu goben idan kin fito ki kirani" Tunda Imaan ta fito Yusuf dake xaune tare da mai gadi da sabon drivernsu ke kallonta, yyi murmushi yace "Ina xuwa Imaan din daddy?" Rufe fuska tayi tace "Shopping mana" Ya wara ido yace "Kaji Hajiya Imaan, in taso mu je ki min shopping din nima" dariya tayi ta make kafada tace "mu je dai ka biya min" yyi murmushi yace "abun yar haka ne kenan, to wa xai kai ki?" Ta buda hannu tace "Napep xan shiga" ya bude ido yace "Salon ki kwaso k'ura ki dawo mana da asthma?" Turo baki tayi yace "A'a bari driver ya kai ki ya dawo dake kawai" Ta wara ido tace "Da na ji dadi" Ya kalli sabon drivern dake murmushi yace "Toh driver xa a ajiye mana ita a supermarket" ya mike yace "In sha Allah, bari in fiddo motar" daga haka ya shiga cikin compound din, Sai a sannan Imaan ta ga Mujaheed dake xaune kan farin kujera nesa da su yana danna wayarsa, tana kallonsa ya jefa mata wani harara, ta turo baki ta dawo kusa da Yusuf tace "Ya Yusuf jiya da na fita inna ta debar maka dambun koh?" Dariya yyi yace "Aa bata ban ba" ta tabe baki tace "Ba wani nan nasan dama jira take in tafi sai ta xuba maka ita ma ta ci, ni da