Chapter 7 Reading KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc Arewa Novels

KISHIN BALBAL BOOK 3 HAUSA NOVELS BY JAMILA UMAR TANKO.doc

Author :  Jamila Umar Tanko Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 10

18K to 21K   out of 28.9K words

ta ci gaba da magana tana ta fadar wasu maganganu wadanda bai gane akan abinda take yi ba. Bai san hawa bai san sauka ba.
Ta ce masa dazu ya turawa her excellency kudinta naira miliyan daya ko? Saboda ya tsane ta, ba zai aure ta ba ko? Toh tana so ya sani wallahi in dai asiri yana ci sai ta aure shi.
Usman ya miqe da sauri zai fita waje dan yayi wayar sosai, baya so Mufidah ta ji kishi in ta ji yana magana da mace. Ta na daga kicin kuwa amma tana ta kallonsa, kallo irin na tuhuma.
Mufida ce ta fito daga kicin da sauri ta tari gabansa, abin mamaki sai ta karbi wayarsa ta kashe.
Ta kalle shi ta yi murmushi ta ce "Jalilah ce ko? Dazu ni da Murjanatu mu ka tura musu kudinsu. Na manta ban fada maka ba."
Usman ya tamabaya cike da mamaki "kamar yaya? Yaya aka yi ku ka san ana bi na kudi, kuma a ina kika sami account number su?"
Ta yi murmushi ta ce " ka dawo ka zauna mu yi magana."
Usman ya zauna a sanyaye cike da fargaba da mamaki tana tunanin ko dai har yanzu Mufadarsa bats gama zama cikakkiyar mutum ba ne, tana duba?
Ta fara magana cikin sanyin murya da sanyin jiki ta ce "cikin dakinsa na shiga dan in share in gyara maka kafin ka dawo dan na san gidan yayi qura. Na ga mukullin gidan akan tebur dina ka manta su a ranar da za ka tafi.
Akan katifarka na ga wani littafi ka yi haquri amma na bude na duba. Sai na ga ka rubuta dukka bashishshikan da ake bin ka. Ga sunan masu bin ka bashi ga lambar wayarsu, ga kuma account number da adadin kudaden.
Sannan daga qasa ka rubuta ka ce ka bar wasiyya idan ka mutu kafin a binne ka a siyar da motarka da kayan sakawarka a biya maka bashi. Idan ma kudin bai isa ba kana roqon iyayenka da dangi su yi karo-karo su cika a biya maka bashi dan baka da komai da ka mallaka a duniya...."
Mufidah ta kasa qarasa wannan maganar kuka ne ya barke mata, daman tuni Murjanatu Bibi tana ta hawaye. Usman ma hawaye ne ke ta zuba daga idanuwansa ya sunkuyar da kai qasa ya dafe kai.
Aka dauki lokaci mai tsayi an rasa wanda zai ci gaba da magana.
Murjanatu ta ci gaba da labarin ta ce " satina biyu da dawowa qasar, Mufidah ta shaida min cewar kai ma a ranar ka tafi Kano.
Toh jiya ma anan gidan na wuni yau bani da niyyar zuwa, kawai yau sai na ga kiranta da alama hankalinta a tashe yake ta ce min in taho gidanta akwai wani abu da zamu tattauna mai muhimmanci. Wallahi a gigice na taho na dauka ba lafiya ba. Ta nuna min rubutunka ni da ita kawai muka fara kuka dan tausayi.
Haba Usman kana cikin damuwa ba za ka fada min ba. Kana fushi da ni, na sha kira ka qi amsa min. Ka san zan iya taimakawa ai, na taimaki wasu ma.ta hanyarka balle kai? Mutane nawa ka ke kawo su mararsa lafiya in taimake su? Ka fi kowa sani ina da account da kai ka bude min ma a bankinmu ina zuba kudin da Zaa yi sadaka mai suna fisabillillah."
Mufidah ta ci gaba da magana ta ce "tun sanda ka yi min maganin ciwona Imam Malik ya bani naira dubu dari uku ya ce in baka dan yayi-yayi ka karba ka qi. Nima kuma ban ga fuska ba daga na fara yi maka tambayar ta yaya kake rayuwa bayan baka aiki? Sai ka dauke wuta ka nuna baka son maganar, ina nan a ajiye da su.
Sai muka yi shawara a hada da shi a biya maka bashin, ni ma na bada naira dubu dari biyar. Sauran kuma gaba daya Murjanatu ce ta biya dukka. Daman total din kudin dukka naira miliyan daya da dubu dari bakwai da talatin ne.
Shine muka tuttura kowa kuma muka yi musu text massage a lambobi wayarsu muka ce daga Usman ne. Mu ka yi musu godiya da adduar alkhairi."
Murjanatu ta tashi ta je ta ja kunnen Usman ta murde da qarfi ta ce "gobe in ka na da damuwa ka daina zurfin ciki. Matsalar ku Ustazai tana da yawa take."
Mufidah ta kanne ido ta cije baki dan ta ji kamar kunnenta aka murde.
Ta harari Murjanatu ta ce "ke ki bari mana, ke muguwa ce."
Su ka yi dariya su dukka ukun.
Sai Usman ya sauko.daga kan kujera ya kalli gabas ya yiwa Allah sujjadar godiya da Ya amsa adu'oin da ya dade yana roqa.
Sannan ya miqe tsaye ya kalli Mufidah ya juya ya kalli Murjanatu, ya fara bayani. Kai ka ce speech yake a gaban shugaban qasa.Ya bude taro da addua, a tsakiya ya bayyana musu kadan daga cikin farin cikin da suka saka shi dan baki ba zai iya fadar dukka ba, sannan daga qarshe ya rufe da yi musu addu'oi kyawawa.
[8/8, 10:38 AM] Jamila Umar Tanko: 32

Usman ya na Bauchi har mako guda sannan Imam Malik ya shigo Bauchi. Da ya shigo garin bai fadawa Mufidah ba ma, Usman ya kira a waya shi kadai ne ya sani dan haka Usman ya kai masa ziyara a hotel din da ya sauka don su zauna daga shi sai shi su tattauna maganganu masu amfani, game da maganar auren sa da Mufidah.
Imam malik ya ce ya yi bincike akan sa sosai gaskiya bai ji wani abu marar kyau ba, sai dai an ce masa matarsa Fatiti bata da dadi akan kishi har ma zata iya kashe duk wacce ta auri mijinta.
Sai Usman ya firgice musamman da Imam malik ya bashi labarin dukkan abubuwan da suka faru na zuwan Fatiti Bauchi har ta farfasa gilasan motar Mufidah. Ya ce Mufidah ta boye masa har yau shi da ita basu yi wannan maganar ba, shima bai yi mata maganar ba.
Usman yayi wuqi-wuqi da ido ba tare da ya san abinda zai ce ba, tabbas dukka abubuwan da Imam malik ya fada akan Fatiti gaskiya ne, kamar ma yana zaune aka yi. "Shin Waye ya kwashe ya fada masa? Tanimu me ko 'yan unguwa?" Usman yake tunani a ransa.
Imam malik ya ci gaba da cewa sannan yayi bincike a kano an tabbatar masa dangin Usman tsatson malamai ne masu kamala, masu asali. Sai dai a Kano ma an tabbatar masa matar nan Fatiti tana da tsananin kishi wanda ya zarce Misali.
"Bayan haka bincike ya nuna aikin bankin da ka ce kana aiki ance da ne ba yanzu ba ne, ka bari."
Usman ya gyara zama ya ce "Yaya maganar aure daban ce, maganar da na fada maka rannan daban a lokacin babu maganata da Mufidah kuma ba na so ka biya ni kudin maganin da na yiwa Mufidah. Ban isa in boye maka komai ba tunda Mufidah ta san komai. Da maganar auremu daman dole ne in mun zauna in fadi gaskiya.Ba na aiki amma yanzu cikin ikon Allah an gama komai zaa mayar da ni da yardar Allah."
Ya bashi labarin duk abinda da ya faru. Tunda Usman ya ce Murjanatu Bibi ta shiga maganar Imam malik ya san magana ta zo qarshe zaa mayar da shi tabbas. Dan shima a Nigeria ko a Amerika duk wani abu idan ya kakare masa ita yake tuntuba. 'yar shige-shige ce, nan da nan ya gamsu da maganar Usman sosai.
Sannan ya yiwa Usman albishir da ya zo masa da labari mai dadi, da ya ji labarin baya aiki sai ya yi masa hanya zaa bashi aiki a NNPC, zai email din da zai tura cv sa sannan zasu kira shi interview a Abuja. Ya ce kada ya damu akwai sanayya komai zai tafi daidai.
Usman yayi ta godiya duk da a ransa ya fi son ya koma banki, bai cika son yana samun alfarma da yawa daga wajen Mufidah ba. Ya fi son ya zama namiji cikakke wanda zai saukewa matarsa dukan haqqinta da nauyin da Allah Ya dora akansa, dan ya zama mai cikakken iko a gidansa.
Maganar kishin Fatiti kuma Usman ya yi ta bayani akan ba zai zama matsala ba, a gida iyaye sun shiga maganar ba zata sake ba, sannan shi kansa ya isa da gidansa kuma ma baa gari daya zasu zauna ba. Usman bai gushe da yiwa Imam bayani ba har sai da ya tabbatar ya gamsu.
Dukka wannan zaman da suka yi Mufidah bata san an yi ba ma, sai sanda ta hada musu cin abincin dare (dinner) a gidanta tare da Murjanatu Bibi da Dakta. Dan tana so ta hada Usman da Imam Malik don a tattauna, ta cika da mamaki har aka hadu aka rabu babu wata magana mai muhimmanci da ta ji sun tattauna kawai sai hirar duniya aka yi aka watse.
Washe gari ma sun sake zama a falonta haka babu wata hira da aka yi. Ba tare da ta sani ba ashe har Imam Malik ya dauki Usman sun wuni su na zagaya gidajen danginta na cikin Bauchi da qauyuka aka gabatar da Usman a.matsayin mijin da Mufidah za ta aura.
Imam ya hada Usman da mahaifinsu a waya sun gaisa. Daddy ya ji dadi sosai kuma ya nuna farin ciki akan wannan magana, sannan kuma ya yi masa nasiha sosai akan ya kula da Mufidah ya riqe masa ita amana ita kadai ce 'yarsa mace a duniya, ya fi kowa sonta baya so ta shiga matsala.
Daddy ya yiwa Usman godiya akan maganin da ya yi mata gashi cikin taimakon Allah ta warke.
Usman ya yi alqawari zai riqe ta amana insha Allah. Maganar ranar saka aure Usman ya ce iyayensa zasu zo su yi gaisuwa su biya kudin aure da sadaki amma kuma biki a bashi lokaci ya shirya.
Daddy ya ce dukka danginsa su na Bauchi ba sai sun zo Abuja ba, ayi komai anan. Sai dai ya umarci Usman da kada ya danu kansa yayi komai daidai qarfinsa basa buqatar komai a wajensa bayan ya riqe musu 'yarsu amana ya saka ta farin ciki. Daga qarshe yayi musu addua'ar samun zaman lafiya da zuri'a masu albarka
Hankalin Mufidah a tashe ta ji maganar aurenta shiru, Imam bai ce komai ba Usman bai ce komai ba. Abin mamaki sai a bakin Daddy ta ke jin labarin an gama maganar komai. Sai ta tabbatar mamaki suke so su bata. Ta cika da murna musamman da Daddy ya ce ta rubuto masa dukkan abinda take so a duniya zai bata. Tunda daga na hidimar auren har kayan gida.
Amsar da ta bashi ita ce "Daddy sai na zo Abuja zamu zauna gani ga Yaya Imam zan fadi abinda nake so kuwa."
Kwanakin Imam Malik biyar a Bauchi ya ce zai koma. Ya hada Mufidah da Usman ya yi musu nasiha sosai sannan ya cewa Usman duk sanda ya shirya turowa gaisuwa ga tsofaffin nan na Bauchi da ya nuna masa can su zaa kai komai.
Bayan Imam ya tafi sai Usman ya bata labarin komai da ya faru. Ta cika da mamaki wato har bincike an gama kenan akan Usman amma ita bata taba sani ba.
Bayan kwanaki biyu da tafiyar Imam Malik Usman ya shirya ya yiwa Mufidah sallama akan zai je Kano dan fara shirye-shiryen kawo kudin aure da sadaki.
Ya shigo Kano da zunmar yin sati guda kafin satin ya cika sai aka kira shi daga bankin da yake aiki aka samar da shi cewar ya zo ya fara aiki an mayar da shi.
Ya gani a email, ya gani text massage sannan an kira shi a waya an sanar da shi. Abokan aiki irin su Sulaiman da sauransu su na ta kiransa a waya ana yi masa murna. Murjanatu da Mufidah ma sun kira su na ta murna kuma suka taya shi murna. Yayi farin ciki sosai ya yi godiya matuqa.
Nan da nan ya shaidawa liyayensa da dangi wannan abin farin ciki, aka dinga murna. Fatiti ta daku da wahalar rashin aikin nan, kajin nan da ta saba ci kullum ada yanzu sai dai ta samu jifa-jifa a dalilin rashin aikin nan. Dan haka ta fi kowa murna, sai dai jikinta yayi sanyi ta san da kudin aikin zaa qaro auro mata kishiya.
Ta shiga jerowa Usman tambayoyin da ta tabbatar basu da amsa, ta dinga yi masa magiya wai ya nemi transfer a kawo shi Kano. Bai bata amsa ba dan bashi da lokacin yi mata bayani.
Fatiti ta ga ta kanta, ta rasa Usman dinta gaba daya ta san ta fita daga cikin ransa. Da alama a wajensa zaman 'yayanta kawai take yi da albarkacin iyaye da take ci. Amma yanzu Usman na Mufidah ne tabbas ta gasgata itama.
A bangaren Usman kuwa duk yadda take tunani haka din ne ma, babu gurbin Fatiti a cikin zuciyarsa, dan sai ya tuna da mugun abinda ta yi masa guda goma kafin ya tuno na kirki guda daya. Sai yanzu ya san ya sami mata ta gari wato Mufidah, duk da ilimi da dukiyar da Allah Ya bata tana gudun bacin ransa, shakkarsa take kamar ma wani lokacin tana jin tsoron tunkararsa da wata magana, a komai tana ta takatsantsan kada ta bata masa rai.
Dan ma shine yake nuna mata ta saki jiki da shi in tana da magana ta fada masa kawai dan shi abokinta ne.
Amma Fatiti kuwa ko da zaa zaa mutu sai ta aikata, da gangan zata yi kuma ta san idan ta yi ransa zai baci, sai dai ran ya bacin, musamman idan aka zo maganar zargi da kishi. Ya tabbatar ada ashe ba aure yake yi ba wahalar banza yake sha, yanzu zai yi auren farin ciki.
Nan da nan ya dawo Bauchi ya fara zuwa aiki. Ya an biya shi dukka kudadensa, masu yawa kuwa. Ya ji dadin kudin nan dan zai samu ya fara shirin aure, ga yaransa can a gida shekara guda basa zuwa makaranta.
Abinda ya fara yi kenan ya zo kano ya sami makaranta mai kyawun gaske ya saka su ya shirya da mai daidaita sahun da zai dinga kai su yana dauko su tunda da nisa daga cikin garin zuwa cikin Nasarawa GRA. Ga Fatiti tana da ciki, har ya girma dan haka ya ware mata na ta kudin.
Yana ta shirye-shiryensa, su Mufidah ma su na ta yin nasu shiri, sai dai shirin ba iri daya ba ne, na su Mufida na manya ne.
Kwatsam Fatiti ta sami labarin tsofaffi maza sun cika mota sun tafi Bauchi don kai kudin aure da na sadakin auren Usman abin takaici har da mahaifinta a ciki.
Ta yi ta kuka ta zari mayafi ta tafi gidan iyayen Usman daga ta wuce gidan iyayenta ta dinga hayaniya da rashin kunya.
Ta na ta fadar baqaqen maganganu ga duk wanda ya ce zai yi mata nasiha. Zuciyarta baqi-qirin ta rasa inda zata saka kanta. Ta dinga kiran Usman ya qi amsawa, ta kira mahaifinta ma ya qi amsawa. Mahaifiyarta ce kawai da 'yan uwanta mata wadanda suke uwa daya uba suke lallashinta, ta basu tausayi su mankukan suke taya ta.
Mahaifiyar Fatiti dai da abu ya ishe ta, ta daga hannu sama ta yi addu'a a bayyane ta ce " ya Allah kai ka halicci Fatiti, Ka yaye mata baqin kishin nan ban san inda ta samo shi ba. Dan ni ban taba daukar kishiya abar tashin hankali ba, har qawance nake yi da kishiyoyina."
Qawayen Fatiti abokan zuga ta akan kada ta bari ayi mata kishiya sun koma gefe su na gulmarta da yi mata dariya, labari ya dawo kunnuwanta. Sun kai ta wajen bokaye kala-kala da 'yan tsubbu don a hana auren amma babu abinda aka fasa.
Gashi ta rasa soyayyar mijinta, mutuncinta da qima da shakkarta da Mufidah take ji a baya yanzu ta zube, darajarta a idanuwan su Dakta da sauran makwabta, da su Tanimu masu gadi dukka babu.
Surukanta sun dawo daga rakiyarta musamman ma mahaifiyar Usman Umma, da alama bata son ganinta, dan dakyar take amsa gaisuwarta.
A gidan iyayenta ma gulmarta ake yi ana jin dadi, abinka da gidan kishiyoyi. Gaba daya ya tonawa kanta asiri da bakinta ba wani ya fada ba. Kowa

7 / 10