Author : Fatima Tijjani Ahmad Category : Romantic Hausa Novels
BIYU BABU
Fatima Tijjani Ahmad
AREWANOVELS.COM.NG
Cikin bacci na ji wayata na kara, na janyo a hankali cikin halin gajiya, lambar Kamal ce na gani.
"Hello". Na fada cikin sanyin murya.
"Bacci ki ke yi ne?"
Na ce, "Eh wallahi".
Ya ce, "Kin san yau ba aiki shi ya sa".
"To kai kuma me ya dame ka?"
"Domin ga mu mun shigo Kofar Nasarawa, kin ga kuwa da abin da ya dame ni ko?"
Da sauri cikin kuma zumudi na ce "Ah haba? Da gaske don Allah?"
"Wallahi ni da Yayata Suwaiba, da kuma mijinta Soja".
Na ce, "To wallahi ba na Kofar Nasarawa".
Ya ce, "Kai Teema?".
Fatima Tijani Ahmad
Na ce, "Wallahi kuwa amma ga wayar Habu nan kira shi zai zo ya taho da ku".
Ya ce, "Na gode".
Na kashe wayar, na yí hamzarin tura masa lambar.
Na maida idanuna na lumshe ina jin wani abu na taba raina game da zuwan nasu, saboda wani
sirri da ita Suwaiban ba ta sani ba.
Kafin na tashi daga kan shimfida ta na yunkura zan cire rigar baccin. Aka yi sallama. Suwaiba
ce.
"Ah har kun iso, kamar a kofar gida ku ke?"
"Wallahi, ai ana kiran Abubakar din ya ce yana Kofar Nasarawa".
"To sannu da zuwa, shigo".
Suwaiba na shigowa na tashi tsaye kaina babu dankwali sai kawai na ji karar kyamara kas! Na
yi saurin cewa.
"Ya kuma haka?"
Ta ce, "Sai na nuna wa kanina".
Na jinjina kai.
Ta ce, "Irin wannan riga haka, to kuma idan da miji wadda za ki sa ba ta kai haka ba kenan?"
Na yi 'yar dariya na ce.
"Aunty Suwaiba ba ki da dama".
Na kira kanina Abdullahi na ce.
"Zo ka kai musu ruwa da lemo mota".
Domin gidan namu ana ta aikin gini.
Jada bandaki na yi wanka na fito, na murza mai da hoda a fuskata, na dau turaren jiki na shafa,
sannan na dauko kayana riga da siket na sa.
ce. Ita kanta Suwaiba sai da ta tanka, ta
"Lallai kanin nan nawa ya iya zabc. Gaskiya kin burge ni, ina ma ni ce da jikinki, da an ga
yanga, da kuma kwalisa, koda yake ke ma din ai gwana ce ta yanga.
Riya Babu 1
Fatima Tijjani tamad
A gaskiya fa kin hadu ga shi dai kin yi aure kin kuma dade a gidanki, amma ba wanda zai ganki
ya ce kin taba aure, gaskiya kanina ya dace wallahi. Don Allah ina rokonki kada ki yaudare shi,
ki daure ki aure shi".
Na yi dariya na ce.
"Ai komai da kika gani daga Allah ya ke, ni kaina ina mamakin kaina domin kawayena da yawa
idan kin gansu sai ki ce yayyuna ne".
Muka yi dariya ni da ita lokaci daya.
Tare da ita muka fito domin da ma sun zo ne mu gaisa, kuma su shiga Sahad, sai na ce in dai
mun fito da wuri ma je Jifatu, su ma suna da kaya da yawa.
Muna zuwa gidan motar muka gaisa da Oga Soja, wato 'Nazir', ya kalle ni ya ce.
"Hajjaju ya gida, ya mutan gidan?"
Na ce, "Lafiyar su lau, ku yi hakuri na barku a mota, wallahi gidan namu ne a ke ta
aikin gini, sai kura ko'ina shi ya sa ban ce a shigo da ku ba".
Ya ce, "Lah ba komai, idan mun sake zuwa ma shiga ai".
Na yi dariya na ce, "Na gode".
Kamal shi ke jan motar na koma gefensa na ce.
"Barka da hanya".
Yana dariya ya ce. "Mun tashe ki kina barci ko? Ki yi akuri".
Na ce, "Ba komai".
Suwaiba ta bude mota ta shiga, ta ce. "Gaisuwar ta isa haka, mu je. Shigo mu tafi".
Na yi 'yar dariya na shiga mota, kirar land crusher baka, an sa farin kyalle an rufe lambarta gaba
da kuma baya. 2
Mun karaso Sahad Kamal ya samu guri ya yi fakın muka sauka daga motar, ni
da Suwaiba muka wuce gaba su kuma suna biye da mu a baya.
Muna tafiya muna ta hira, muka shiga cikin shagon, mun yi yawon mu amma ba mu sayi komai
ba, sai dai mun sayi ice-cream, shi ne dai ya sayi agogo ta dubu saba'in, Soja ya saya wa
Suwaiba atamfa sufa guda hudu a gurin ta ce na dauki daya na ce a'a.
Da ya ji muna magana ya ce, mene nc? Ta fada masa, sai kawai ya dauko wata ja ya miko min
ya ce.
"Wannan za ta fi miki kyau".
Na rage tsawo na ce, "Na gode, Allah ya kara budi". "Amin".
Kamal ma ya taya ni godiya shi kuwa Soja ya daga mana hannu alamar ya isa.
Bayan mun fita daga Sahad sai Jifatu, inda muka sayi kayan kwalliya na mata. A nan ne ma
Soja ya juyo ya kalle ni ya ce.
"Fatima duk kin ruda min matata, wai me ke faruwa ne?"
Na ce, "Ranka ya dade me ka gani?"
Ya ce, "Na lura tunda muka zo ta kasa nutsuwa komai sai ta ce Fatima".
Na ce, "Ka yi hakuri".
Na juya kallona ga Suwaiban ina mushi na ce mata.
"Ki dinga cewa Yallabai kin ji".
Ya ce, "Yauwa, haka na ke so".
Mun kammala sayayyar da suka yi, Kamal ya yi min irin tasa siyayyar, haka ma Soja da kuma
Suwaiba.
Mun dawo gida inda muka tarar da Kakata A'i ta gama abinci, muka ci na mika wa su Kamal
nasu, su ma suka ci suka sha lemo da ruwa.
Da misalin karfe biyar na yamma muka yi sallama suka dauki hanya sai Kaduna garin gwamna.
Na kan kira waya duk bayan minti talatin ko arba'in domin jin halin da suke ciki, har suka isa
gida.
Suwaiba ce ta yi min waya ta ce.
"Allah ya kawo mu gida lafiya". Na ce, "Alhamdu lillahı, a huta
gajiya
Misalin karfe goma na dare Kamal ya kira ni muka gaisa, muka yi 'yar hira marar tsawo
sakamakon ya gaji saboda shi ya dauko su tun daga Kaduna har Kano, ya kuna koma da su.
Mun yi hira a gajarce ya ce, zai kwanta. Muka yi sallama sai da safe.
Suwaiba ta yi wanka ta shirya domin zuwa turakar maigida, amma sai ta ga mijin nata ya shigo
dakinta, inda ya nemi da ta ba shi wayarta.
Ina Bate
Ba musu ta ba shi, ya juya zuwa dakinsa ya rufe dakin. Ta taba kofar ta ji ta a rufe don haka sai
ta koma kan gado ta kwanta ta kunna talabijin tana kallo.
Zuwa can jimawa sai ga Soja ya shigo, ya mika mata wayarta sannan kuma ya sake mika mata
Galaxy four ta mike da sauri ta rungume saboda murna.
safe Ya ce, "Ba komai, na gode sai da
Ya wuce dakinsa.
Suwaiba haifaffiyar garin Zaria ce, amma ta yi karatunta na gaba da sakandire a Kano, a
makarantar da ke horar da malanta ta kasa da ke Kabuga.
Ta yi karatunta ne a kan Arabiya da kuma islamiya, a shekarar karatunta na karshe sai ta rasa
dakin zama a kusa da
makaranta saboda rigima da aka yi a gidan da ta ke haya, mai unguwar ya tashe su gaba daya,
hakan ya sa ta rasa gurin zama.
Yau tana wajen waccan kawa, gobe tana wajen waccan, ga shi saura sati uku mu gama
jarabawarmu.
Kamal kuninta ne da suke uba daya, armuma kusan sakwannin juna ne, don wata uku ne
tsakaninsu, bayan an haife shi da shekara daya mahaifiyarsa ta rasu, don haka mahaifiyar su
Suwaiba ita ta rike shi.
Sun shaku kwarai a tsakaninsu.
Ina zaune a bakin block four hundret ina duba wani hand out dina ta iso gurin muka gaisa,
amma ranta a face karmar ta yi kuka.
Na kara kallonta, na ce.
"Suwaiba lafiya?"
Ta ce, "Wallahi ina cikin matsala Fatima, na rasa gurin zama na karasa jarabawa"
Na yi sallama ba kowa duk suna sashensu, hakan ta sa ban ga kowa ba, na yi sallamar ne
saboda haka musulunci ya tanadar.
Na sa mukulli na bude gurina, na shiga ta biyo ni a baya.
Na ajiye mayafina na shiga dakin girki domin maigidana yana dab da dawowa.
Tuwon shinkafa miyar yauki na yi, na
zubo mana na ce
"Taso mu ci abinci".
Bayan mun ci abinci sai muka yi
sallar magriba, a nan na fada bandaki na yi wanka na dauko doguwar riga marar nauyi na sa,
na kira Baffa ya kunna min inji, domin ba wuta.
Na sa mana kaset muka fara kallo, be jimawa mijina ya dawo na ji sallamarsa na mike da sauri,
ita ma ta mike, nа се.
"Ina za ki?"
Ta ce, "Na ji kamar mijinki ne?"
Na ce, "Shine".
Ta ce, "Ki ka ce min ba ya nan?"
Na yi dariya, na ce.
"Ki zauna, ina zuwa".
Na bude masa kofa na karbi kayan hannunsa tare da fadin.
"Sannu da zuwa".
Ya amsa mun, "Yauwa, ya
jarabawar?"
Na ce, "Alhamdu lillahi".
Ya shigo dakin, ni kuma na shiga dakin girki domin ajiye abin da ya zo da shi sannan na fito.
Remot ne a hannunsa yana sauya tasha yana kallon labarai, na sake cewa da shi.
"Sannu da hanya, ya rana, ya aiki?"
Ya armsa, "Yauwa, duk alhamdu lillah".
Na dauko abinci na ajiye a gabansa, da duk wani abu da na san zai bukata, na mike domin na
cire masa rigar jikinsa, sai na
tuna ba mu kadai ba ne a dakin, kuma sani kafin a cire rigar sai wani al'amati ya fan ko da kuwa
tsotsun baki ne, sai na fasa ce.
"Yallabai muna fa da bakuwa yau"
Ya ce, "Me?"
Na ce, "Bakuwa".
"Tana ina?"
Na nuna masa Suwaiba da ke a takwe
na ce. "Ga ta nan".
Ya ce, "Fatimata, ai wannan ni bu santa ba ko?"
Na ce, "Gaskiya ne, amma fa ci abino za a yi maka bayani".
Iya ce, "To".
Na kula Suwaiba a takure ta matuka hakan ya sa na tashi na shiga de dakin, na duba na jona
mata talabi sannan na kirata ta koma dakin, na ce
"Ki saki ranki, ki kwanciyarki, ni kan sai da safe. Ko kina da bukatar wani abu ne?"
Ta ce, "A'a, na gode".
Muka yi sallama na koma gurin
mijina.
Ya bude hannayensa na shiga kirjinsa, sannan ya ci gaba da cin abincinsa, wani lokaci sai ya
zo sa abincin a bakinsa sai ya bude bakina ya zuba min na hadiye, haka ya kammala cin
abincin, sannan ya yi min durar ruwa, ya cika bakinsa ya dura min a bakina.
Bayan ya gama ne ya ce.
"Kin san da ma da 'yan magana na shigo gidan nan, Allah ya sa ki ka taka min burki, wai da na
saki da na ji kunya fa?"
Na yi dariya na sake shiga kirjin mijina, ya maida hannunsa domin ya rufe ni da su.
Ba mu wani jima ba muna kallo ya ce.
"Tashi mu je mu kwanta, kin ga gobe kina da jarabawa, ga kuma bakuwa kin sani
Na ce, "To...to bara na dan duba littafin nan na ga".
"Me za ki gani kuma? Kin ga...
Sai ji na yi an dora ni a kan gado, shi ke nan sai da asuba muka tashi.
Ya shirya ya tafi masallaci, ni kuma na yi sallah a gida sannan na shiga dakin da Suwaiba ta ke
don na tashe ta.
Abin mamaki Suwaiba ta tashi ta yi sallar har ma ta yi wanka, jira ta ke gari ya waye ta tafi,
domin ta ji tsoto na ce mata
mijina ba ya nan, kuma ga shi yana nan Dariya na yi har da buga kafa na ce
"Ki kwantar da hankalinki, in dai maigida ne ya ma manta an yı bakuwa
Muna cikin magana sai na ji an kashe inji, an kawo wuta kenan.
Ya shigo dakinmu ya wuce ya zauna yana lazimi, na jima gurin Suwaiba sannan na dawo
gurinsa.
Yana ganina sai murmushi, ya jawo ni zuwa jikinsa, ya ce.
"Kin san abin da ya ke ba ni mamaki da ke?"
Na ce, "Sai ka fada".
Ya dan yi shiru, sannan ya dora hannunsa a ruwan cikina, ya ce.
"Wai cikin nan naki kina cin abinci ki
koshi kuwa?"
Na yi dariya na ce.
"Ai abin da zai sa ka ga cikina ya daga sai hukuncin Allah ya faru a tare da
Ya kuma jawo ni jikinsa ya ce.
"Fatima haihuwarmu shiru, wai me ye
dalili?"
Na yi dariya na ce.
"Allah Shi ya sani".
Ya ce, "Fatima ina sonki, ban san irin son da nake miki ba".
Na yi dariya na ce.
"Jiya ka hana ni karatu yanzun ma so ka ke ka hana ni? To ka shirya za ka ba da kudin (LVT)".
ce. Ya yi dariya sosai ya shafa kaina, ya
"Wannan kan ko ba a yi karatu ba ba zai fadi jarabawa ba".
Na ce, "Me ya sa ka ce haka?"
Bai ba ni amsa ba, sai ya ce.
"Je ki hada abinci, kin san muna da bakuwa, ni ba ki ce da ni komai ba a kan bakuwar ba ma".
Na cc, "Ka yi hakuri, kai ne ka mantar da ni komai jiya, amma ina zuwa".
Bayan na dawo daga dakin dafa abinci ne na ba shi labarin abin da ya faru tsakanina da
Halima, ya ce.
"Amma ba ta kyauta ba".
Na yi shiru daga karshe, ya ce,
"To za ta zauna da mu ne ta Karasa jarabawar?"
Na ce, "Wannan kuma sai abin da ka ce Yallabai".
Ya yi murmushi, ya ce.
"To ba komai".
Bayan na hada mana abin karyawa na kai wa Suwaiba nata cikin daki, don na san ba za ta iya
zama mu ci tare ba, sai na dawo gurin maigida domin mu ci.
Mun ci abinci muka koma hira daga nan ya shiga wanka, na dauko masa, kayansa na shirya sbi
savaita domin yau Abuja za shigidan bize kuma Ayay din zai dgwo. Na raka shi hat Kofer gida,
Agaure ne
ntaryaegume swotit anl 23 ani Sahity da yamma nidan retrushiga
makaränta ki kuua min da kanki, sai na dawo
Na ce a dawo lafiya
Na koma cikin gida gurin Suwaiba, na
"Fito falo ya fita".
Da kyar ta fito ta zauna, ta ce
"Ki shirya mu tafi ko, na ga ba ki karatu ba".
Na ce, "Ai idan ina tare da shi ba ya barin karatu".
Ba ta ce komai ba, na mike zuwa bandaki. Na yi wanka ita kuma ta shiga daki karatu, na zauna
gaban dressing mirrow ina shafa.
Bayan na shirya na shiga dakin gito domin na gyara, na kuma wanke wadanda muka yi amfani
da su.
Ina fitowa na tarar Suwaiba na u faman gyaran falon, na yi dariya na ce.
"To idan kin gama mu tafi".
Na rufe kofa muka fito daga bangarena, a tsakar gida muka yi kicibus da Safiya wadda ta ke a
kan benen dakina.
Muka gaisa ta ce.
Jamai tme
"Bakuwa kika yi ne?"
Na ce mata, "Eh".
Muka wuce, "Sai kun dawo". In ji Safiya.
Bayan mun shiga tasi daga Sallari zuwa Kabuga na biya kudin mota, na bude littafi ina dubawa,
ita ma haka har muka je inda za mu sauka ba wanda ya yi magana,
muna sauka na sai mangoro. Ta ce, "Kin fiye shan mangoro".
Ni dai ban ce komai ba, har muka shiga cikin makaranta. Bayan mun shiga ne kwatsam sai ga
Halima, ta kalle mu ta tuntsire da dariya, ta ce.
"Yauwa Fatima Tijjani, haka a ke so, kin yi min daidai. Kin sami mai wanke-wanke".
ce. Suwaiba za ta yi magana na hanata, na
"Halima ke nan 'yanmatan taurarinsu ke haskawa".
Ta kalle ni sama da kasa ta ce
"Fatima Tijani, kin fa hadu, sai dai b yi a hankali kar kawata ta kwace miki min
Na yi dariya na ce.
200 "Ba komai, amma ki sani ko dan gala ita matar da ta varda da kanta ta kuma se kanta zai
wahala a kwace mata miji lokan daya, sai an yi da gaske. Na gode, anjima".
Suwaiba ranta a bace ta kalli Halina ta ce, "Banza!". Ita kuwa ba abin da ta ke mata so
dariya.
Aniy Hassana ta fi mu shekaru sos amma karatu ya hada mu, bangarenmu dava hakan ya sa
kullun muka hadu gaisuwe mutunci ce a tsakanina da ita.
Yau ma kamar kullum mun hadu kuma mun gaisa, mun yi wasa da dariya a nan ne ta ke
tambayata.
"Kanwata wai ya nake ganinki kullum ke kadai ne, ina yaran?"
Na yi dariya na ce mata.
"Wallahi ban haihu ba".
Ta ce, "Ayya". Alamar nuna damuwa,
sai kuma ta ce.
"Kodayake ai ba ki dade ba".
Na ce, "A'a shekarata biyar fa".
Ta ce, "Eh, ba komai, Allah ya kawo mu sha suna, wannan gayun ya ragu".
Na ce, "Ko dai ya karu?"
Ta yi dariya, muka wuce muka barta a gurin