Author : Fatima Tijjani Ahmad Category : Romantic Hausa Novels
ΝΑ ΥIWA ΚΑΙΝΑ
Fatima A. Tijjani
A cikin garin Kano, cikin unguwar Kofar Nassarawa Alhaji Lawan ya ke, dan kasuwa ne
shahararre wanda a ka sanshi da yawan kasashe, yana kasuwancin nasa ne a cikin gida
Nigeria da kuma kasashen ketare. Allah ya yi masa dukiya matuka, yana da mata guda daya
mai suna Hajiya Lubna, sai dai ba su taba haihuwa ba, sun yi yawon neman haihuwar har sun
gaji amma shiru, har kasashen waje sun je amma ba a samu ba.
Hajiya Lubna 'yar kabilar fulani ce, fara, doguwa mai gashi har gadon bayanta, ga idanu
kyakkyawa sosai, ga kuma kwalliya.
Hajiya Lubna ta kai duk inda a ke son mace ta kai, kwalliyarta kuwa idan za ta
fita unguwa doic ne ya dace da motar da za ta hau
Idan ta sa leshi to dole ne gwal mai kalar leshin ne, haka jaka da takalmi, sannan kuma
uwa-uba motar da za ta hau.
Hajiya Lubna ba ta sa leshi na kasa da dubu hamsin, atamfa kuwa Aura ce ko kuma Super Las,
shadda kuwa sai dai hilton U.K. gwala-gwalai sai wanda ya gani.
Matan birni da yawa suna so su yi kawance da ita, domin ba ta kawance da kowa sai matan
manya, kamar gwamnoni, ministoci da sauransu. Ta samu duniya dai yadda ya kamata, sai dai
abu daya da ba ta samu ba shi ne haihuwa.
Yau juma'a, Alhaji Lawan ya ke barin garin Kano da zama ya koma babban birnin tarayya na
Abuja, cikin rukunan gidajen villa, wato kusa da gidan shugaban kasar Najeriya.
Gida har gida, idan ka shiga kai ka ce ba cikin Najeriya gidan ya ke ba saboda tsaruwarsa.
Wadanda suka zo ma domin hada kayan gidan daga 'Abu Da'abi' suka zo, masu kudi suna abin
da suke so.
Sun tare a sabon gidan aljannar duniya, don haka yanzu komai ya sake sauyawa, Hajiya Lubna
ta sake kawaye, a ciki kuwa har da matar shugaban kasa. Yanzu ta yi kawaye daidai da ita.
Yau ta shirya za ta wani asibiti a cikin garin Abuja na wasu Indiyoyi da suka zo suna ba da
taimako ga mutanen Najeriya.
Bayan ta yi musu bayanin ita haihuwa ta ke so, sai suka ce ta kwanta su duba ta cikin na'ura.
Bayan sun gama dubawa ne suka yi mata bayanin cewa, Allah bai halitta mata mahaifa ba, don
haka babu yadda za a yi ta haihu, da tana da mahaifa to da yanzu suna da yadda za su yi mata
ta samu
haihuwar 'yan bivu ko 'yan uku a lokse daya
Sun dade suna mahawara da ita, ko a samu bakin zaren, amma fa ba hali doleta hakura ta
koma gida cikin bacin rai ila rashin nutsuwa.
Hankalin hajiya Lubna ya tashi, farin cikinta ya koma bakin ciki, walwalaria ta koma kunci
Bayan dawowarta daga asibitin tana shigowa gida ta tarar da kaninta Yusuf da 'ya'yansa a
gidanta, ya zo gaishe ta
Da saurinsa ya nufi inda ta ajiye motarta, yana rawar jikin girmamata.
"Sannu da zuwa Hajiya".
"Yauwa Yusuf, kai ne a gidan ne
Ya ec. "Wallahi kuwa, dama ziwa na yi da yara su gaishe ki".
Ta ce. "Ka kyauta":
Falonta suka shiga ya samu qui Zauna, su ma yaran uku suka zauna
Ita kuwa Hajiya cikin dakinta ta shiga.
ta kwanta domin samun saukin abin da ya ke damunta. Ta jima tana kwance sannan ta fito ta
samu Yusuf a falo yana kallo shi da 'ya'yansa uku.
Bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa ya sha, sannan ta ci gaba da tambayarsa mutanen gida,
da kuma matarsa.
Yusuf kaninta ne uwa daya uba daya, amma sam ba ta kulawa da shi, ga shi yanzu suna gari
daya amma idan ba shi ne ya zo gidanta ba, ba za ta neme shi ba.
Yusuf yana aiki ne da kamfanin sadarwa na 'MTN' a cikin garin Abuja, yana da matarsa da
kuma yaransa uku maza biyu mace daya.
Yusuf ya tashi zai tafi, Hajiya Lubna ta bude jakarta ta dauko naira dubu ashirin ta mika masa,
amma ya ki karba don ya ce shi ziyara ya kawo mata, ta bar shi ya gode.
Ana cikin wannan mujadala ne sai Alhaji Lawan ya shigo gami da sallama cikin falon.
Da ganinsa sai yayan Yusul suka tashi da gudu, "Ga Baba! Ga Baba"
Shi kuwa Alhaji da sauri ya dauk karamin cikinsu ya daga shi sama cikin farin cikin ganinsu,
Ragowar biyun kuma suka rike kafarsa, dadi ya kama shi sosai, ya rasa inda zai sa ransa, sai
kawai va nufi dakinsa da su.
Ya dauko biskit da kuma alewa ya ba su, sannan ya dawo falon ya zauna.
Yusuf ne ya sauka daga kan kujerat da ya ke kai, ya durkusa kasa.
"Alhaji sannu da zuwa".
"Yauwa Yusufa, ya gida, ya kume aiki?"
"Alhamdu lillahi".
"Ya mutan gidan?"
"Lafiya lau Alhaji".
Ya dan kuma jimawa, sannan ya yunkura ya ceo.
"Alhaji za mu koma".
"To Yusufa, na gode a gaida gida".
Da kyar karamin yaron Yusuf ya sauka daga kan cinyar Alhaji Lawan, wai shi ba zai bi
mahaifinsa ba a nan zai zauna.
Bayan Yusuf sun tafi sai Alhaji ya kula akwai abin da ya ke damun matar tasa, kusa da ita ya
koma ya zauna.
"Hajiya lafiya kuwa?"
Ta ce, "Lafiya lau".
Ya cc, "Na ga kamar ranki a bace shi ya sa nake tambayarki".
Ta ce, "Lafiyata lau".
Sukunin Hajiya Lubna ya tafi, yanzu rayuwa ba dadi, ban da tunani ba abin da ya ke damun
zuciyarta.
Yau bakuwa ta yi, kawarta ce 'yar kabilar ljo ta zo wajenta, musulma ce..
Ta same ta a cikin tashin hankali don haka ta shiga fada mata Allah da yadda rahamarSa ta ke.
Ta jima tana fada mata Allah har zuciyarta ta yi sanyi, ta ji zuciyarta za ta iya nemowa mijinta
mace ya aura tunda shi lafiyarsa lau.
Ta koma hayyacinta yanzu, domin babu abin da ya ke damunta, ta bar wa Allah komai.
Ana bikin kanwar kawarta Hajiya Halima ministan mata, ita ce ta ke yi wa Kanwarta aure.
Abin biki na biki ne, mata sun kai mata, guri ya yi guri an dauko mawakiyar nan Barmani Coge.
Hajiya Lubna ba ta karaso da wuri ba, har Barmani Coge ta soma wasa. Can sai ga ta ta
karaso, manyan mata maganin kananan mata.
Ko da zuwanta guri sai ya koma kamar wata matar shugaban kasa ce ta zo, nan gurin ya kuma
kacamewa ana ta shagali.
A nan ne fa mata suke bude hannun jaka a ka fara saukar ruwan takardu, ba sa lika kudinmu na
gida Nigeria, sai na Turai dolas fa ta yi kuka.
Da Hajiya Lubna ta ga kowa kudi ya ke zubawa, sai ta tashi ta je gaban Barmani cogen ta ce ta
tsaya da waka haka tana da magana.
Barmani ta tsaya, ta amshi lasifikar hannunta ta ce.
"Na ga kowa yana zuba miki kudi.
shin a taron nan akwai wacce ta ba ki mota?"
Barmani Coge ta ce, "Babu".
"To ni Hajiya Lubna matar Alhaji Lawan na ba ki mota CRV, za a kawo ta yanzu idan za ki koma
gida ki hauta ki tafi gida".
Arsat gun ya kuma kacamewa, s wasa ya sauya salo, maimakon a wake amarya saraka koma
wake Hanya Hajiya Lubna
Wadanda ba su santa ha suka dinga tambayar wace ce ita. Wannan kyauta ta Haliya Lubna ba
sabon abu ba ce, don ta rauna kudi shi va sa ba ta jin komai don ta yi irin wannan kyautar.
Yau kimanin shekara biyu da zuwa ganin likitan, sai ta hadu da wata kawarta mai suna Kausar
Kausar ita ce ta nunawa Hajiya Lubna hanyar bin bokaye da kuma yan bori.
Yanzu Lubna ba ta iya yin komar sai abin da 'yan bori suka sanyata. Yanzu Alhaji Lawan va
zama han da tsoron matarsa ba abin da yake yi
Ta hana Yusuf ya zo gidanta, domin ta kula idan ya zo da 'ya'yansa Alhaji yana jin ina ma nasa
ne, don haka yanzu ya daina
zuwa. Idan yana son ya yi zumunci da ita, zai kirata a waya su gaisa.
Shi kuwa Alhaji duk juma'a sai ya kira Yusuf a waya sun gaisa, ya kuma tambaye shi yaransa.
Yanzu haka Alhaji Lawan ya dauki nauyin karatun yaran Yusuf, amma Hajiya Lubna ba ta sani
ba.
Yanzu abin da ya ke damun Alhaji Lawan bai wuce rashin haihuwa ba, kuma matarsa ta hana
shi ya dauko 'ya'yan 'yan uwansa bare kuma ya ce zai yi aure.
Yau shekarunsu goma da yin aure. amma ko batan wata ba ta taba yi ba.
Abokin Alhaji Lawan mai suna Alhaji Najib shi ne ya kawo masa ziyara gidansa, bayan sun
gaisa ya ce.
"Ina yaran kuma, ko duk suna makaranta?"
Shiru ya yi, can kuma ya ce. "Ai ba ni da yara, ban haihu ba".
Shiru Alhaji Najib ya yi, sannan ya ce.
"Matanka nawa?"
Ya ce, "Daya ce"
"Ka yi kuskure Alhaji, me ya sa ba ka sake yin wani auren ba?"
"Wallahi alhaji ba zan iya ba, domin tsoron Hajiya na ke ji".
Bayan sun jima suna hira sai Alhaji Najib ya ce zai koma gida, tare suka fito ya yi masa rakiya
gurin mota, suka yi sallama ya tafi.
Bayan kamar sati daya da yin maganar ya kara aure, sai abin ya dinga damunsa a rai, amma
kuma yana jin tsoron yadda zai Bullo mata.
Gidan Alhaji Najib ya koma suka kara tattauna yadda abin zai kasance. Zai yi aure amma fa ba
zai gaya wa Hajiya ba, domin ya san ba za ta barshi ba.
Garin Yola suka tafi gurin abokin Alhaji Najib.
Sun sauka a gidan bakinsa sun huta, sannan dircba ya dauko su zuwa gidansa.
An kawo abinci da ruwa da kuma lemo kala-kala.
A cikin masu kawo abincin nan ne Alhaji Lawan ya ga wata yarinya ya ce yana
Bayan sun gama maganar abin da ya kai su na game da shigo da sababbin motoci, sai suka
koma maganar Hafsa. sonta.
Alhaji Mudansiru ya ce, "Hafsa ba 'yata ba ce, 'yar mai mana aiki ce amma a cikin 'ya'yana ta ke
zaune, ta yi karatu ta gama sakandire yanzu, amma zan turo maka ita ku sake gaisawa".
Ta zo sun gaisa, yarinya mai ladabi da biyayya.
In gajarce muku labari, ba su bar garin Yola ba sai da a ka daura aure. Ya auri matarsa ta biyu,
amma ba wanda ya sani daga abokansa biyu sai mahaifinsa.
Bayan ya dawo daga Yola sai ya kuma shirya tafiya Lagos inda ya yanke shawarar ajiye
amaryarsa, haka aka yi ya sai gida a cikin Ikeja ya kai amaryarsa.
Abin mamaki shi ne, amarya tana cika wata tara sai ta haifi danta namiji.
Abin mamaki ba ya karewa, watan dan goma sha daya ta kuma haihuwar wani da namijin.
Farin ciki da jin dadi a gurin Alhaji Lawan abin ba a cewa komai, domin idan ya kalli 'ya'yan har
kukan dadi ya ke yi.
Haka Alhaji Lawan ya ci gaba da kasancewa tare da matarsa da 'ya'yansa biyu maza, Abubakar
da kuma Umar, a cikin garin Lagos.
Yanzu duk sanda zai je Lagos ya kan ce da Hajiya Lubna zai ce Kwatono ko
kuma ya ce zai je Lagos, domin jirgin ruwa
ya zo. Yara suna fara girma, Abubakar ma
har ya shiga makaranta don haka yanzu Alhaji Lawan ko mai sunan Abubakar ya gani yana ji
yana kaunarsa saboda dansa.
Umar ma ya isa sa wa a makarantar, sai dai ba shi da baki, don haka an bar shi sai shekara mai
zuwa.
Hafsa ta kuma haihuwar danta namiji, wanda aka sa wa suna Usman, Alhaji ya ji dadi matuka,
don haka ya yi musu visa ita da yaran don tafiya Dubai su huta tsawon hutun yaran.
Hafsa ta hau jirgi tare da 'ya'yanta uku sun dau hanyar Dubai, shi kuwa Alhaji Lawan ya dawo
gida Abuja ya zauna a gurin matarsa Hajiya Lubna.
Yau Hafsa ta samu sati uku a cikin kasar Dubai, don haka Alhaji Lawan ya ji yana son ganin
'ya'yansa da kuma matarsa.
Mu hadu a Part 2
Fatima Tojjani Ahmad
Kofar Nassarawa
arewanovels.com.ng