Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Romantic Hausa Novels
KUNDIN TSATSUBA
arewanovels.com.ng
Ko da ganin sun yunkura za su tashi sama, sai Boka Hafsil Habar yai ihu ya ce Ku vi mini rai, ku
kwance ni mana. Kuma ina rokonku da ku fora ni bisa aljaninku, ku tafi da ni."
Ko da jin haka sai kowa ya bushe da dariya. Aljani Nargaz ya zuro dan yatsansa guda ya
tsintsinke igiyar tsafin da ta daure Hafsil Habar, sannan ya sure shi da dan yatsan guda ya dora
shi a bayansa. Nan take Nargaz ya bude fukafukansa yai sama. Cikin hanzari Gimbiya Sima da
Waziri Kaddaru ma suka haye bayan Durfus, shi ma yai sama ya bi su Nargaz a baya. Cikin
'yan dakiku kadan suka luluka a cikin gajimare.
Yanzu dai tafiya ta zama ta mutum biyar, da aljanu uku, wato Jafar, Yelisa, Sima, Kaddaru da
Hafsil Habar. A bangaren aljanu kuwa, akwai Nargaz, Durfus da kuma Gulzum.
Yayin da suka sami kwana daya da yini guda suna tafiya, sai aljani Nargaz ya dubi Jafar ya ce
"Ya shugabana. ina mai tunatar da ku cewa nan da kwana uku da rabi za mu isa jejin Kalkim,
don haka ina son kafin mu shiga, ka kara tuna mana dokokin nan guda bakwai wadanda in
muka saba sú zamu hallaka gaba faya."
Jafar ya ce "Kwarai kuwa Nargaz ka zo da magana abin dubawa. Yanzu dai abin da nake so da
kai shi ne, ka ci gaba da tafiya da mu babu batun ya da zango a ko'ina, kowa sai yayi hakuri ya
jure gajiyarsa, domin yada zango a wani wurin na iya kawo sanadin bata lokaci mai yawa."
Ko da jin wannan batu, sai kowa ya aminta. Haka dai suka ci gaba da tafiya ba dare ba rana,
har ya zamana
saura yini daya tak a shiga jejin Kalkim a sannan no Jafar ya ce "To ku saurara da kyau zan
tunatar tunatar da mu dokokin nan guda bakwai, yayin da muka tsinci kanmu a cikin jejin
Kalkim. Abu na farko shi ne, kada dayanmu ya kuskura ya ce zai yaki maridan da ke cikin
wannan jeji. Doka ta biyu ita ce, yayin da suka kama mu, kowa ya tsuke bakinsa kada kayi
magana har a kai mu inda za a kaimu. Doka ta uku, idan an samu a cikin kejin icc, kada mu ci
kuma kada mu sha daga abia za suka kawo mana, tsawon kwana uku, ko da kuwa zamu ji
kamar yunwa da kishirwa za su kashe mu. Doka ta hudu ita ce, kada dayanmu ya kuskura ya
ce zai jarraba aiki da safi. Doka ta biyar, duk sa'adda maridan suka za suna kallonmu, kowa ya
sumkui da kansa kas, kar mu rinka hada idanu da su. Doka ta shida ita ce, dole ne mu rinka yin
sujjada ga wala bishiyar zinarc da ke ajiye a kofar gidan Magulus uban maridai, kullum da safe.
Doka ta karshe wato ta bakwai ita ce, ranar da a ka zo zo za a fitar da mu daga cikin keyin ice
don a cinye mu, kada dayammu yayi gardama ko taurin kai. Da zarat an zu za a wuce da mu ta
gaban bishiyar zinaren nan, sai mu daga kawunanmu sama mu kalli garyayenta, take ganyayen
za su zuzzubo kasa ha adadi, iyakar ganin mutum. Haka na faruwa gaha dayan maridan za su
kame su zama gumaka har uban nasu Magulus da matarsa. A sannan ne zamu sami damar
shiga cikin gidan
maridi Magulus mu dauko takobin Sarjis Lokacin da Jafar ya zo nan a zancensa, sai ya dubi
kowa daya bayan daya, ya ce Ina fatan Juk mun haddace abin da na fadi? Lallai ku sani cewa
kuskure ko mantuwa ga dayanma bisa wadannan dokoki, na nufin hallakarmu gaba
daya. Wanda duk ya san cewa ba zai iya kiyayewa ha, ton yanzu yayi hayani mu sauka kasa
mu ajiye shi kafin mu isa jejin Kalkim
Ciaba dayansu suka yi tsit, ba a sami wanda ya nuna gazawa ba. Yelisa ta yi murmushi ta ce "A
to rai dai guda daya ne, duk wanda yayi ganganci ya rasa nasa shi kenan ba zai sami wani ba.
Ni dama ban damu ba, domin ance mutuwar yawa kaka ce."
Dajin wannan batu sai Jafar ya bushe da dariya ya ce "Ai ke ma ba ki san dacin mutuwa ba,
inda kin sani ba zaki iyi wannan jawabi ba
"Sannu wanda ya san mutuwa, ai sai ka fada mana lokacin da ka dandana ta
Jafar yayi murmushi ya ce "Ashe har kin manta da lokacin da Hafsil Habar yai mini barin
makauniya? At a wannan lokaci idanuwana ne suka rufe na ga wadansa taurari na yawo a
sama. Daga sannan kuma, ji da ganina suka dauke min gaba daya. Tabbas wannan hali da na
shiga daidai yake da dandanon mutuwa."
Yelisa ta bushe da dariya ta dubi Hafsil Habar ta ce "Da kyau tsoho mai ran karfe kai ne
maganin mai karambani
Gaba dayansu dariya ta kwace masu, suka yi ta kyakyatawa musamama aljani Nargaz da aljani
Durfus kat ka ce ba za su daina dariyar ha iya tsawon rayuwarsu
"Oh! Aljanu da keta kuke, wannan muguwar darivar fa kamar an ba ku tallan auduga?"
Ba shiri kowa ya tsuke bakinsa sakamakon abin da suka hango a gabansu. Ba komai ba ne
face jejin Kalkim
Dagama suna iya hangu kasan jejin ko ina maridai ne berjak bu adadi
Maridan sun kasance manyan-manya, kuma ma su mammanan suffa. Duk irin taurin kan
mutum in ya haka idu da su, sai ya razana. Yayin da aljani Nargaz da aljani Durfus ke Kam
kusantar wannan jeji, sai suka ji ba sa iya motsa fukafukansu sosai, kamar yadda ya kamata.
Karfin gudunsu ya ci gaha da raguwa akai-akai. Nan fa cikin kuwa ya duri ruwa. Ba zato ba
tsammani sai suka ji sun yi Kasa louου...
kamar an janyo sa da kugiya. Caral suka fada hannun maridan su duka. Maridan suka hau wani
irin gurnani wanda idan mai ciki zata ji shi, take zata yi barn. Kuma sai suka rinka dalalar da
yawu saboda tsabar kwadayi. Nan fa aka lara yiwa su Jafar daukar makara, wadannan su
mikawa wadancan, wadancan su mikawa wadancan, aka yi ta tafiya da su gaba-gaba. Su dai
su Jafar suka yi lakwas babu wanda yayı wani yunkuri, kuma babu wanda ya ce kala. Bayan an
yi doguwar tafiya da su a haka, sai ka iso kofar gadin Magulus uban maridai. Da zuwa aka riske
shi tsaye kikam yana jiran isowarsu, tuni lahari ya isar masa cewa-yau an kamo wadansu bil
adama
Yayın da aka gurfanar da su Jafar a gaban Magulus. suka vi arba da shi sai kowannensu
cikinsa ya hau kadawa saboda firgicewar da suka yi sakamakon ganın siffar halittarsa. Magulus
dogo ne, saboda tsananın tsayinsa idan mutum ya daga kai sama sai ya hango fuskarsa tamkar
tsuntsua Kololuwar sama Fadin kirjinsa kuwa kamu tamanin da uku ne, kaurın dugadigin
kafarsa kuwa, yai kama da murtukekivar bishiyar kuka. Idan ya daga kafar tasa guda
zai iya talitse "ya'yayensa dari a lokaci guda, duk da cewa su ma ba kanana ba ne, girman kowa
ne daya ya linka na Gimbiya Sima sau biyar.
Magulus yayi nuni da a sanya su a cikin wani katon keji na ice. Nan da nan 'yayan nasa suka
cika umarni, aka jefa su ciki aka kulle tamkar an jefa kaji a akurki, daga nan kowa ya waste, aka
bar su su kadai a wajen
Aljani Durfus ya hada kai da guiwa cikin takaici, sannan ya dago kai ya dubi aljani Nargaz ya ce
"Kai duk wanda bai yi yawo a duniya ba, bai sha kallo ba. Yanzu ka dubi duk irin girman nan
nawa da karfin damsena, da kuma Karfin tsafina, wai yau ni ne a cikin kejin ice a kulle, kuma a
hannun wasu halittu dabam ba aljanu ba. Hatsabibancin su ma ya fi namu.
Nargar ya ce "Hm.... ni ai ba wannan ne ma ya ba ni mamaki ba, sai uban maridan nan. Ka
dubs sananin girmansam, sai ka ce tsauni. Ai ni sa'adda na hango Kokofin hancınsa daga nesa,
na dauka kogon duwatsu ne manya manya guda biyu."
Shi kuwa Gulzum sai ya ce "Ni kuwa da na hango idanuwansa, sai na yi zaton rana da wata ne
za su yi karo a saririn samaniya"
Ko da jin wannan batu, sai su Jafar suka bushe da dariya. Jafar ya ce "Lallai kai ka fi kowa ma
rudewa, ina ka taba ganin rana da wata sun hadu? Ai abu ne wanda ba rai tabia yiwuwa ba,
domin babu shiri tsakanin zafi da sanyi, in kuwa za a hadu dole ne daya ya narkar da dava
Gimbiva Sima ta vi gvaran murva la ce "Laflai na ya alama hankalinku a kwance yake. Yanzu
ashe har kun mance
da irin halin da mu ke ciki, har kun sami damar yin hira? Ku tuna fa rayuwarmu na cikin kila
wakala. Zai fi kyau ku tsuke bakunanku, ko mun fi samun nutsuwa mu ci gaba da kiyaye
dokokin dajin nan, kun san dai yin shiru na daga ciki."
Jafar ya ce "Gakiya ne, amma ai tunda maridan ba sa kusa zamu iya yin surutunmu. Hirar ma ai
rahama ce a gare inu, don zata rage mana yawan fargaba da zulumi, don wannan ya tuna mini
da labarin wasu 'ya'yan sarki uku da suka bazama neman kayan yakin mahaifinsu wanda ya
басс a duniya aka neme shi aka ransa.
Ko da jin haka'sai Yelisa ta ce "Kai Jafar wannan kuma wane irin labari ne haka mai ban
al'ajabi? Ba mu kanu mu sha."
Jafar yayi gyaran murya gami da saisaita makogwaronsa ya ce "Asalin wannan labari na samo
shi ne a cikin wani littafin tarihin da ake kira Karon Batta. A wani zamani can baya, an yi wani
shahararren sarki da ake kira Jamnash, wanda a zamaninsa ya ci kasashe da dama da yakı
Har ya bar duniya ba a taba cin kasarsa da yaki ba, kuma sai da ya shekara casa'in da biyu
yana mulki a kasar Lahamas Dare daya aka wayi gari ba shi ba alamunsa.
Sarki Jamnash yana da 'ya'ya maza guda uku, Sahal. Fazmal da Husmal. Dukkaninsu jarumai
ne na hakika domin suke jagoranci a duk sa'adda za a fita yakı Kowannensu mahaifiyarsa
daban, kuma ko kadan ba sa jituwa a tsakaninsu, sakamako bakin kishin da ke addabar
iyayensu mata, domin kowacce tafi so ace danta ne ya gaji karagar mulki Bayan shekaru hudu
da bacewar sarki Jamnash, sai gidan sarautar ya rikice da rigingimu akan
samo ba mu hadu a nan cikin kwanaki sittin. Yana gama fadın hakan ya kada linzamin dokinsa
ya bi hanyar da ta nufi gabas. Fazmal kuwa sai ya bi hanyar da ta nufi yamma. Husmal kuwa
sai ya bi kudu, yana tafe yana tunani da bakin cikin wannan hali da suka tsinci kansu a ciki na
tsananin rashin zumunci da kin juna, saboda kawai kwadayin mulki."
Sa'adda Jafar ya zo nan a labarin, sai Waziri Kaddaru ya tari numfashinsa ya ce "Ka ga dakata
haka, yanzu mene ne ma'anar wannan labarin? Ina hikima a cikinsa?"
Jafar yayi tsaki ya ce "Ai ka ji irinta, halin dan adam kenan rashin hakuri. In da ka bi ni a sannu
ai za ka ga inda ma'anar labarin take, amma tunda ka katse ni ba zan ci gaba ba sai wani
lokacin kuma idan an sami dama irin wannan.'
Jafar yayi shiru bai kara cewa komai ba, dama a wannan lokaci dare ya soma, saboda haka duk
sai suka saduda kowa ya kama bacci.
Kashegari da safe kuwa aka kawowa su Jafar wani irin ruwa mai wari a cikin wani katon kasko,
gami da wasu kananan duwatsu, a matsayin abincin kalacensu. Yadda aka ajiye ruwan da
duwatsun, haka aka dawo aka dauke su domin babu wanda ya dubi inda suke bare ya ci.
Sa'adda rana ta fito sai maridan nan suka rinka zuwa sahu-sahu suna kallon wadannan
fursunoni na cikin kejin ice. Su kuwa fursunonin sai suka sunkui da kawunansu kas, suka ki
yadda su rinka hada idanu da maridan. Da rana ta yi tsaka, sai aka sake kawowa fursunoni
wani nau'in abincin aka ajiye musu, shi ma suka ki su ci. Sa'adda magariba tayi aka kawo wani
abinci iri daban, shi ma suka ki ci. Haka dai aka ci gaba da
wannan al'amari, har tsawon kwana uku. Fusunonin suka galabaita da matukar yunwa da
kishirwa, kamar ba za su rayuwa ba. A kullum da safe sai su Jafar sun yi duba izuwa bishiyar
nan ta zinare, sun yi mata sujjada.
A yammacin rana ta uku ne aka fito da wadannan fursunoni daga cikin kejin ice, ka tasa
keyarsu gaba. Ko da aka zo giftawa da su ta gaban wannan bishiyar zinare, sai gaba dayansu
suka daga kawunansu sama suka dubi ganyen bishiyar. Yin haka ke da wuya, ganyayen suka yi
ta zubowa kasa fululu suka cika kočina. Faruwar hakan ke da wuya gaba dayan maridan nan
suka kame suka zama gumaka, ko da ganin hakan sai murna ja kama su Jafar.
Kai tsaye suka dunguma izuwa cikin gidan Magalus uban maridai. Su ka yi ta ratsawa ta
tsakiyar gumakan maridan, har suka shiga cikin kuryar dakin Magalus. Da shiga suka ga
kokunan kawunan bil adama birjik a zube, sannan kuma suka hango takobin Sarjis rataye a jikin
bango. Jafar ya sunkuya ya dauki kokon kai guda ya jeli takobin Sarjis da shi. Take takobin ya
fado kasa, shi kuma ya ruga ya dauka. Yana dauka ya kama hanyar fitowa, kowa ya bi bayansa.
Duk inda Jafar ya dauke sawunsa, nan su aljani Durfus da su Gimbiya Sima suke sa nasu, har
dai suka yi tafiya ta kimanin sa'a guda.
Jafar ya tsaya ya dubi aljani Durfus da aljani Nargaz ya ce "Maza ku dauke mu kubar jejin nan
da mu.
Cikin hanzari aljanun biyu suka rankwafa kasa. Gulzum, Jafar da Yelisa suka haye bayan
Nargaz. Gimbiya Sima, Kaddaru da Boka Hafsil Habar suka haye bayan aljani Durfus. A lokaci
guda aljanun suka bude fukafukansu
arewanovels.com.ng
KUNDIN AL'AJABI
MANSUR USMAN SUFI
Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta.
Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!.
Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji
ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu.
Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne,
Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a
kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi.
Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya
wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu
alamun gajiya a tattare dashi,
Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa,
Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi,
Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara
raguwa.
Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba,
Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen
shi wani rami ne mai zurfin gaske,
Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami
da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya,
Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa,
Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da
mutanen dake kanshi ba.
Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo
daga cikin keken dokin,
Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna
ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai
ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa.
Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya,
Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba.
Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na
damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari,
Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da
ke gudana ba,
Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya
aka sakata a cikin wannan akwatu?
Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan.
An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin
akwatin?
Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya
hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya
cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen,
Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi,
adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna
dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu.