Author : Abdulaziz Sani Madakin Gini Category : Romantic Hausa Novels
Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen
keken dokin,
Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice.
A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen
keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu.
Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun
cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa
binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar
Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar
bata raye a halin yanzu.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran
murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya
tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat?
Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne". Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar
mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon
mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil
ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat
bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula
da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun
murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa
sama.
Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin
dawakansu suka koma izuwa cikin dajin.
Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar
jaririyar?
Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?.
Dalilin faruwar hakan kuwa shine.
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe
MANSUR USMAN SUFI
08137237071