Zuciyar Namiji Complete Hausa Novel By Mujaheeda Matar Malam.txt

Author :  Mujahida Matar Malam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 3

6K to 7K   out of 7K words

kenan..... sainajiku ina maraba daku mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar..... TAURARUWAR ROYAL MARUBUCIYAR- FAHAT, RAUNIN MACCE , BR. KHALEEL, SILAR ƊA NAMIJI, SAINA KASHE MIJINA, SO SIRRIN ZUCIYA, ZUCIYAR ƊA NAMIJI,,, MAIZAMAN KANTA "PAID 200" BAƘIN KISHI "PAID BOOK 200" DR . HEESHAM 2022 "PAID BOOK" AND NOW ABBAKAR RASAKIE "PAID BOOK 200"*
_dik wanda yakaranta ɗaya daga cikin waɗannan yasan Alƙalamina baya rubuta shirme kudai ku garzayo kada ABAKU LABARI_







/////// Aɓangaren Nura kuwa tinda ya sake Khairy ya koma ɗaki ya zauna yarasa meke masa daɗi wai shine yau ya rasa ɗinbin dukiyar da yau bako Anini waita ƙone baiko gama tinanin ba saiga kira ya sake shigowa wayarsa kamar bazai ɗa gaba kuma saiya daure ya ɗaga baiyi magana ba ya Aza wayar Akunne, Muryar tijjani yaji wani iri yana faɗin "Ƴallaɓai nasami hatsari ne kuma motar taɓaci hakama keke napep ɗin talale yanzu haka ina Asibiti cikin wani hali dan Allah ƴallaɓai kazo dawasu ƴan ƙuɗaɗe dan mun magani da......,"







"Kai... kai.... kai... dalla rufamin baki mahaulacin inane kai? ko bakada hankali ne? nine zankawoma ƙuɗi to ina nagansu? bakada imani ne shaguna sunƙone da dikiya ƴar motar da napep ɗin kun hallakar yanzu kace ƙuɗi you are very stupid," Kashe wayar yayi yana fifita da hularsa zufa kota ina tsatstsafo masa take...




Ashe dik Abinda ke faruwa salma nalaɓe tanaji Ai kwa takoma takwashe takardun gidan da car keys ɗin motocinsa da zinaren da ke Aje tafece Abunta, tana fita suka haɗa baki da maigadi saiga masiya suka saida yanaciki baisan Abunda kefaruwa ba sukabar garin Abunsu..







Rayuwa tamasa ƙunci baida komai sai wannan gidan yana zaune yana hamma ta yunwa data Addabeshi dan yanzu ko Abinci wahala yake masa, Wasu mutane ne suka shigo bako neman izini nan yake tanbayar lafiya?

Atake suka nunamasa shaidar gidansu danma maigidan taɗan nemasa Afuwan Abarshi yayi sati ɗaya sannan Atasheshi,






Ido ya ƙwalalo cike da mamaki dama tsoro yana faɗin "ƙarya kuke bayarda za'a saida gida bayan nine maigida Asaida gidan in zauna ina? itama matar gida hakan,"





"Kaga malam idan kace zaka mana hauka wllh dokace zara rabamu dan munada shaida ga takardu hannunmu da snigning kace zaka mana hauka, Ungo wannan wasiƙar matar tace Abaka kuma wllh ko kafita yanzu ko mushuma maka rashin mutunci komai bakada dan ko tsinke saida muka biya ƙuɗinsa ƙasa,"






Hannayensa na rawa ya warware wasiƙar ya fara karantawa kamar haka-----------+%%%%%%%%----------- KAYI HAƘURI DA DIK ABUND ZAKA GANI DAMA HAKA RAYUWA TAGADA KACUTA ACUCEKA SARAI NASAN LABARIN KHAIRY TIN AURENKU TASHA WAHALA KUMA TAJURE KAI GAKA MUGU WATO *ZUCIYAR NAMIJI!!* ZAKA NUNA BA, HUNMMM SAIDAI KAMATA DAN ITA KESONKA DAN ALLAH NI DAN ƘUƊINKA NA AURE KA NA AUREKA KUMA BA ƘUƊIN YANZU NA ƘARA GABA SAIDAI BAZAN TAFI ABANZA BA SHIYASA NAKWASHE DIK WANI ABU DAYA RAGE A GIDAN NATAFI DASHI KAYI HAƘURI FA DAGA SALMA+---------%%%%%%%%%%





Sake takardar yayi baya zaifaɗi da sauri ɗayan yataroshi Amma harya some jikinsa,




*HAHHHHH YAU ZALUNCI YAFAƊO KAN ZALUNCI KENAN😅😅😅*





yayyafa masa ruwa sukayi yaɗan farfaɗo Amma Abun mamaki take ya sami ciwon sashe guda dan sam yakasa motsa ƙafar da hannun gashi bakinsa ya juye yawu namasa dalala kuka yake yana kiran sunan Khairy,


Ganin hakan yasa suka fiddashi waje nesa da gidan suka Aje suka kama gabansu,


Da jan ciki yakoma wata inuwa yanata kuka nadama mara Amfani.


Ahaka nura ya walaƙanta Anan kashi Anan fitsari Anan Ada yana samun taimako Amma Yanzu kowa yadaina kusantarsa saboda warinda yake kullum cikin kuka da nadamar *ZUCIYAR NAMIJI!!!* Irin tashi fatanshi koda Amafalki ne Allah ya haɗashi da khairynsa....



(WAIKO KARIN JAMIL DAI KAI KAM TAMAKA NISA WOLLAH)






Humaira kuwa ta haife ƴan 2 murna gun sani ba'a mgn , Tasawa maccen sunan Khairy



Hakama ɓangaren khairy tahaife yaranta 3 ɗayan tasamata humaira ɗayan sunan baban mijinta ɗayan babanta.



Yaransu dika sungirma kuma sunyi wayo Abunsu dan harsunyi Arba'in yaudai sokoto zasu dan kaiwa su Humaira ziyara.


Sun sauka lafiya saifiransu da nishaɗinsu suke ko A'alama Humaira bata bata labarin Nura ba, rakosu sukayi dan kaisu Air port Anan ne sukaga wani mutum bakin titi ƙuda natabinsa Amma yana neman sadaka, ɗagowar da khairy zatayi dan miƙawa jamil yabashi sadakar sai idansu suka haɗu cikin rawar baki tafurta Nu..r...a NURA.... Kaine? tana nunasa da yatsa neman tashi yake daga zaunen amma yakasa dan baƙafar,



Fitowa tayi tazo gabansa ta tsuguna yabata tausayi ba ƙaɗan ba lalle rayuawa wai yau nura ne A wannan halin dik ƙuɗinsa "to ina matarka,?"

Tafurta cikin rawar murya



labarin komai yabata haɗida neman yafiyarta Atake tayafemasa dan yabata tausayi ba ƙaɗan ba,


Jamil dake cika dan haushi tanunamasa kaganshi shine mijina kuma harda yaranmu 3 kaga *ZUCIYAR NAMIJI!!* Wata nada banbanci da wata kaga mijina nagari kuma maidukiya ne, ƙuɗinda taɗebo tabasa 'ka kula da kanka da wannan nayafemaka Allah ya yafemaka kaima"
Tana kaiwa nan takoma motar suka wuce Abunsu sukabarshi ya nata kuka...




Har suka je gida jamil magani yake ci talura kishi yake dan haka tahau lallashin Abunta harya sauko.....




_TAMMAT BI HAMDULLAH_


Anan nakawo ƙarshen littafin nan nawa mai taken *ZUCIYAR NAMIJI!!!* Ina fatan zamu ƙaru da darasin da keciki maikyau mara kyau kuma Allah ya karemu.......



*SAƘON JINJINATA GAREKI UMMUN SHURAIM INA GDY DA SOYAYYARKI GARENI DAMA NOVELS ƊINA INA GDY SOSAI............*




```INAJINJINAMA ILAHIRIN MASU BANI COMMENTS, DAMASUMIN SHARING WAƊANDA NASANI DAMA WAƊANDA BANSANI BA,,, INA JINJINAMA ƳAN ƘUNGIYARMU TA ROYAL WRITERS ASSOCITION ASSOCIATION ALLAH YASA MUDACE```






_📝NOTE_ *Wannan littafin na nuna muna illar zalunci kada kaci Amana kuma kadayi zalunci dan Allah ba Azzalimin sarki bane, kundaiga nura yayi ƙarshe mummuna khairy kuwa tayi haƙuri kuma tadace dama Ance mahaƙurci mawadaci ne,.....*




SAIMUN HAƊE NEXT BOOK ƊINA MAITAKEN *ABBAKAR SARAKIE👑👑👑 '"PAID BOOK #200""*






_ALLAHUMMA SALLI WASALLAM ALAH NABIYINA MUHAMMAD...... SUBHANALLAHI WABIHAMDI NASH HADU ALLAH ILAHA ILLA ANTA NASTAGFIRUKA WANA TUBU ILAIHI....._

3 / 3