Chapter 18 Reading MUMNUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA.txt Arewa Novels

MUMNUNAR DABIA PDF BY ASMA BAFFA.txt

Author :  Asma Baffa Category :  Romantic Story

Chapter   18 / 26

51K to 54K   out of 76K words

gobe daurin aure Maheera ansha gyaran gashi anci lalle gaba daya ta canja tayi kyau sai kamshi take,fatarta in banda sheki ba abinda take yi,baki kullum a washe ana jin dadi za a auri Sohail.
Ranar kuma tayi yininta da kamu ya kayatar yayi kyau sosai anci an sha anyi liki iya mata amma.


Washe gari ranar daurin aure tun 4am Sohail ya farka kaya a goge amma ya wani jona dutsen guga ya sake goge musu kaya har Sahil,ga abokansu sunyi kara da yawa sun zo har mudassir me fada da matarsa shima ya shirya duk da shi a gari yake.
Su Adnan sabo da bakin ciki suka sallami me aiki Madam Oge suka ce taje gida sai bayan biki dan kar ma ta dafawa abokan da suka zo daga wasu wuraren abinci.


Suna kallo ma daga gidan Alhaji Saminu ake kawowa iri iri safe rana dare komai akwai kaci ka sha,ba a taba musu abinci ko daya ba.
Busy suka zama dan kar ma su shiga lamarin bikin kullum basa zama a gida.


Ranar daurin aure Ango ya riga kowa shiryawa suna ta tsokanarsa suna masa tsiya,Farar shadda suka saka shi da Sahil ba banbanci,da babbar riga da hula kamar a jikinsu a dinka,suma taci gyara a saka yar hula a goshi.
Turare ya fesa yafi kala nawa a jikinsa,Sahil yace Allah sarki Me Tallaja ana ta ci da rabonta.
Kawu Nafiu,da Kawu Tukur sai Daddy da abokansa mutum biyu rak sune suka zo a dangi.


Daddy ya kira Adnan a waya yace ya kamata suje,suna ta jin haushi suka shirya suka je haka,lokacin da suka je ma an rigada an daura auren 11:30am.


Ana daurawa Daddy ya tashi suka tafi yana cewa yana da meeting,Sohail ya kalli Sahil yace kaga bai tambayi ya aikin da nake ba,a ina nake yi,wanne iri ne ko a jikinsa,sannan matar ma ba ruwansa bai san wace ba,Sahil yace kyale shi ya tafi ba komai.


Abokai ne suka yi kara sosai duk abinda akeyi na biki a al'ada sunyi abinsu ba ruwansu,na nesa ne suka koma da wuri sai iya wanda suke gari su dama ba wasu abokan ne da su da yawa ba.
Amarya ta sha leshi me kyau pink and black,irin kyan da tayi ba a magana,sai da za ayi pics ango yace bazai yi ba,da kyar abokai suka sashi dole ya shiga aka musu da Amarya,sai cuno baki yake wai dole aka masa.


Su mudassir sune suka tattara kayan ango suka kai gidan Amarya,ango yace kafata kafar Sahil yazo mu tafi, 3 bedrooms ne da dakinsa,Sahil yace zan dawo ai daga baya,Sohail yaki yarda dole aka kai kayan Sahil can dakinsa idan ba haka ba amarya baza taga ango ba.


Mudassir ne yace da Sahil yayi wayo kar ya kwana a gidan ya barsu sai nan da satikai sai ya koma,Sahil yace to kamar ya gane suka koya masa yanda zai fice da dare ya dawo gidan su Adnan ya dinga kwana,yace to.


Zuwa yamma Maheera dangin su maza suka kirata suka mata nasiha sosai akan zaman aure,Mama ma tayi nata nasihar tace na sanki da son kai Maheera nasan hali karki je ki nuna son kanki,Maheera tace Allah bazan yi ba na gane gaskiya,to shike nan Allah yasa,bayan sun gama Nasiha akace ta shirya za a kaita angwaye zasu zo daukan Amarya.


Sai lokacin kuma ta fara kuka,dariya ma ta basu,angon kansa tun biki saura kwana uku basa waya sai a daurin aure suka hadu,wanka tayi ta canja kaya cikin wani material dark blue ta sha kyau sosai kamar wata yar India,kayanta da lefe komai an tattara an kai can gidanta,Maheera ta kira kanwarta gefe tace an kai min wannan takardun nawa gidana iceko bazan zo ganin gida da wuri ba sai nayi kiba na canja, Juwairiyya tace ke kama Aunty wannan son da kike masa yafi nasa ai,tace daga na fadi gaskiya sai tayi shuru.
Juwairiyya sune a kan gaba kanwar Amarya,tuni sun shige mota,Motar Alhaji Saminu itace za a sa amarya ciki.
Bayan Amarya ta shirya dattijai suka fito da ita kanta a lullube aka sata a mota,motoci sun kai goma aka tafi kai Amarya Alhaji Saminu ya bada wasu motocin da driver guda hudu,komai anyi cikin aminci da rufin asiri.


Bayan an kai Amarya gidanta kowa sai yabawa yake ana ta yi mata murna,Aunty Aisha itace tayi ruwa tayi tsaki komai sai da aka aiwatar na Al'ada,Amarya aka bari daga ita sai wata kawarta guda daya Mardiyya,itama bata dade ba saurayinta yazo ya dauketa ya maidata gida aka bar Amarya ita kadai a saman makeken bed ya sha gyara.


Shima bangaren ango abokan duk sun tafi saura Mudassir kawai,shine ya siyo kaji da kayan makulashe,yace to ango taso mu tafi, Sahil yace yanzu kaimu za ayi shike nan gida kuma,Mudassir yayi dariya,Sohail yace Shike nan kuma har abada bazan dawo nan da zama ba rayuwa kenan,yau Allah yayi tashin mu,Mudassir yace dan Allah muje ku dai Allah ya shirye ku, haka suka tafi gidan Amarya harda Sahil.

Amarya tana jin mota tace Alhmdllh dama tsoro nake ji,tace oh ina tare da Aljani da kansa mene abin tsoro kuma,Sohail ne a gaba yana shiga yace ni ba sai an nuna min gidana ba,ni da gidana ace dole sai an rakani ai nasan dakin ku kyakeni,Sahil ga room dinka Mudassir a gaida iyali,ya karbi ledojin ya mikawa Sahil nasa yace karbi, Mudassir ya dinga dariya yace butulci zaka min? dariya yayi yace to kaine da naci ai, Mudassir yace to sai da safe,mun gode sosai cewar Sahil ya raka Mudassir har mota, Mudassir yace shiga mota mu tafi na saukeka a gidan su Adnan yanda muka tsara,Sahil yace tab ga gidanmu mun dawo kace na koma bazan koma ba, soyayya fa zaka hana su yi,Sahil yace ba abinda za ayi sai an jira ni,Mudassir ya buga ya buga yaki yarda,haka ya tafi ya kulle musu gidan ya wuce room dinsa,wanka yayi yaci kayan dadinsa yana kallon film a dakinsa har yayi bacci.


Ango kuwa Amarya na zaune ya shiga da sallama,murmushi tayi ta cikin mayafi,hannu yasa ya fyalle mayafin yace mene haka kin sanni na sanki ki zauna kina boye fuska.
Har ya juya zai shiga toilet ya fasa ya dawo ya leka fuskarta yace naga kamar kinyi kuka,Maheera tace uhm rabuwa da gida wasa ne,nan ba wani gidan kika dawo ba? murmushi tayi me kyau zata yi fari yace dakata karki fara na gaji.


Dariya tayi tana kallo ya bude kayansa ya dakko wasu kayan baccinsa ruwan zuma sababbi,ya dauki man shafawarsa da turare da komai ya shige toilet,Maheera tayi murmushi tace idan ka shirya a gabana menene to,kofa ya rufe amma bai sa key ba,sai da yayi wankansa da brush ya dade yana faman shiryawa sai da ya shafa mai yayi komai har gashinsa ya gyara yana shafa turaren kaya Maheera ta gaji ta bude toilet din,da sauri ya juyo yace Allah ya fiki na shirya to,dariya tayi tace to me kake yi haka ne? Kin takura min daga aurenki kin dameni fa.


Kayi Alwala? yace yanzu zanyi ya juya baya,da tsokana Maheera ta rungume shi,Laaaaaa ya furta kamar an masa wani abu ya tsaya a haka kanta ta kwantar a bayansa tare da furta wayyo ni duniya dadi,Ido ya zaro waje yace ke Maheera uwaki ni na hadu da yar duniya wlh dama Sahil yace zaki karya alkawari,hannu yasa ya banbareta daga jikinsa da masifa yace ki daina bana so ni.


Murmushi tayi ta ture shi tace matsa nayi alwala,Alwala tayi ta bishi suka fito,Sallah ya ja su tace ashe ka sani,kwafa ya ja yace me kika maida ni ne? Sallah ya tayar suka yi ya musu addua yanda ake yi,suna idarwa ta rike hannunsa kwacewa yayi ya harareta,dariya tayi tsokanarsa take ta faman yi.


Sai da ta shiga wanka ya sauke ajiyar zuciya yace an takura min ni wayyo Allah aure wahala yanzu na gane da maza suke ta fada halin mata ba kyau,shi yasa maza kowa kuka yake da aure wahala na rasa ganewa sai yau.


Daure da guntun towel ta fito ya saki baki yana kallonta Maheera tana murna ta tafi da Imaninsa sai ji tayi ya furta wai ke haka kike dama aka baniva dukunkune? Ashe lukuta ce ke amma a haka kamar siririya ni siririya nake so,Maheera bata kulashi taci gaba da shirinta,ya zauna kuma sai kallonta yake kamar zai cinye ta har ta shirya ta dauko wata gantalalliyar rigar bacci da Aunty Aisha ta bata kalar kayansa na bacci ta zabo sharara da ita komai a waje da siririn pant dinta gata guntuwa rigar,Sohail yana gani ta saka abarta ta zare Towel din ya juya baya da sauri tare da furta na jawa kaina sai da Daddy yace kar nayi auren nan na kafe sai nayi gashi na hadu da gamo na.
Maheera tana jinsa tana boye dariyarta,inda yake zaune a gefen bed ta koma gabansa ta tsaya inda ya juya baya,sake juyawa yayi ya kalli gefe can,saman cinyarsa ta zauna ya dinga zamewa kamar tsutsa yana zukewa,gashinsa ya sosa ya girgiza kansa kamar haukar ta motsa,kugunta ya rike ya dagata yace wai ke bakya zama kawai,dariya tayi zata sake taba shi yace ga abinci zo kici.


Zama tayi tace kai fa? Yace na koshi,tace gwara ma kazo kaci tun kafin nazo na kwanta a jikinka kuma a haka zan baka da hannuna,da sauri ya dawo ya zauna,amma lokacin da ka gasa min kafa me yasa ka tabani muka yi kokawa? Sannan watarana da muka yi party Islaha har abinci ta baka a baki kuma kaci,Sohail yace ni din? Yaushe? Shi sam ya rantse ba shine ba,duk sun manta ma anyi wani party har Sahil din babu me iya tunawa.


Maheera haka suka ci abincin tare suka koshi ta tattara komai zata fita yace kin manta saka hijab karki ga Sahil a palo yana kallo,tace kace kai a dukunkune aka baka baka damu ba ina ruwanka da wani kuma,fuska ya bata yace kin rainani ko? Ni na isa ta dawo ta saka ta fita,tana dawowa ta samu ya jera pillows a tsakiya kar ma ta taba shi wai,yace kowa ya kwanta a barinsa,tace to ta kashe light tayi kwanciyarta a bangare daya shima haka,yace to baza kiyi addua ba? Ai yi nake,yace okay ki hada dani ai nayi aure ba sai nayi ba tunda cewa aka yi ki kula dani, ya juya yayi kwanciyarsa wai tayi da shi kawai.


Maheera a ranta tace na shiga uku ni Maheera wannan kaddara wacce iri ce,da haka tayi bacci itama dama su sarakan bacci ne har ya lula,duk ya har gitsa pillon da ya jera su babu ko daya duk sun fado kasa.


Farkawa Maheera tayi taga duk pillows din sun watse kasa,murmushi tayi ta koma jikinsa tana dariya a boye hannunsa ta jawo ta dora a kugunta ta matsa jikinsa ta manne ta rungume shi bai sani ba sai da asuba tayi ya farka a hankali ya bude idonsa,tunawa yayi ai Maheera ce yayi aure murmushi yayi yanzu kuma"
yana kare mata kallo,kwanciyarta ta gyara sosai,hannunsa daya ya mika yana daga kwance ya kunna light haske ya bayyana.


Wuyan rigar Maheera ya zazzage ana hango Boobs a waje chakare chakare,Sohail baki ya rufe da tafin hannu daya,yaci gaba da kallonsu da baki ya nuna su yace uhm shi yasa take wani kin saka hijab yau na gansu Allah ya toni asirinta bata da katabus,idonsa ya lumshe yace kuci gaba da kallona ina jin dadina ya koma baccinsa,yana komawa baccin aka kwalla kiran sallah ya sake farkawa yace yau makara zanyi Maheera tana nan.
Yanzu kuma yace na gode Mama zan dawo gaisuwar surukai ko dan wannan runguma da kika tarbiyyantar da yarki a kai ga nacin jikina ta makale min,tarbiyyarki tayi Mama,ban kashe kudina a banza ba.


Maheera ce ta farka a hankali ta yunkura zata tashi taji ya riketa gam yace makara zamu yi yau,tana murza ido tace da hankalin mu da sanin mu ai ba a wasa da sallah tashi muyi sallah,Sohail yace bazanyi ba ni yanzu makara zanyi yau,ta matsa masa yace naji zanyi amma bazan je masallaci ba ni wlh,tace ae tashi muje,harararta yayi ya mika mata hannu yace dagani jawo shi tayi ya tashi, yace karfa kice kece kika tashe ni ganin dama nayi baki isa kin iya dagani ba.


Toilet din ya shige ya kulle,ta zauna ta jirashi sai da yayi wanka da brush ya fito,Maheera tace munfa makara ka zauna wanka,yace wankan tsarki nayi ance duk wanda yayi aure sai yayi wankan tsarki kullum,Dariya zata karasa Maheera ta shige toilet kawai tace yau nidai na shiga uku a haka zan rayu.


Kafin ta fito yayi sallah yana Azkhar dinsa dake yaga dama,tace to matsa zanyi Sallah ya tashi ya bata waje ta saka kaya ta gabatar da Sallah tayiwa Twins addua sosai sannan ta cire kayanta sai na bacci ta kwanta,kwanciya yayi a samanta ihu ta saki ya dagata da sauri yana dariya yace ba haka kike so ba.


A gefenta ya kwanta yana kallonta yace tsaya na miki wani abu karki fadawa Sahil zai ce na karya Alkawari,Maheera tayi murmushi tace kace kar a taba ka kai baka so nice yar iska shi yasa na kyaleka,uhm uhm karki kyaleni please yace.


Jikinsa ya dawo da ita ta lafe yace sai kace mage wai ke zan fasa ma,na daina to cewar Maheera,carbin hannunsa ya ajiye a nutse kamar wanda yasan kan lamari ya hade fuskar su waje daya hancinsu yana gugan na juna,Maheera idanuwa ta lumshe tana jiran tsammani fuskarsa ya janye har ya matsa ya kyaleta tana a haka kamar gunki ido a lumshe tana ta jira,sai data dawo hayyacinta taga baya ma jikinta,kunyar kanta taji ta shiga sosa gashi tace a ranta me yake damuna ne zai rainani ma,dan guntun tsaki ta ja tare da kwanciya itama.


Sai wurin 9am ta tashi jin ana buga kofa, Shima Sohail farkawa yayi jin karar door bell,zata mike yace kwanta bari naje irin jarumin nan,yana fitowa ya bude kofa yaga driver Aunty Aisha ta aiko shi da lafiyayyen abinci,karba yayi suka gaisa da driver yace mun gode ya rufe kofar.
Dakin Sahil ya shiga ya samu Sahil yana baccin gajiya ya ja masa kofar ya fito ya ajiye abincin a dining ya koma bedroom ya samu Maheera ta shiga wanka.


Islaha kuwa tana komawa Lagos can gidan wata hajiya Kulu uwar tuwo taje itace take yiwa 'yan mata hanyar aiki a gidan masu kudi ko a wajen yan tuwo tuwo,Hajiya Kulu tana ganinta tace Islaha yau kece a gidan nawa daga ina haka na ganki da uban kaya? Islaha tace wlh Hajiya Kulu korata Aunty tayi kin sai dai halinta da abinda suke yi,Hajiya kulu tace bata kyauta ba wlh wasu ke bata wasu shi yasa ake ganin duk wanda yayi sana'ar tuwo tuwo a banza ake kallon mutum kawai dan duniya ne.


Yanzu ya dangin naku? Islaha ta bata labarin komai tun daga korar da Aunty tayi mata har da haduwarta da Sahil da barinta a gidan su,Hajiya Kulu ta kalli Islaha yanda take sharbar kuka wai dan a tausaya mata tana cewa kowa yaki ya tausaya min, tace na sha wuya tana shesheka,Hajiya Kulu tace to ai ke kuruciya ce ta muku yawa har su Sahil din kika ce sunansa ko? su in banda shirme ai wani za a samu ya raka ki gidanku,ke kuma daga sunyi magana sai ki bar gida cikin dare suma suna da gaskiyar su bai kamata ba,Yanzu to shi Sahil din sonki yake ko kece kike son sa?


Islaha tana hawaye tace wlh ina sonsa,mutumin nan inda kisan ya min asiri ni ba kula samari nake ba amma ina ganinsa naji zuciyata ta buga,nidai sai sonsa nake yi ba ji ba gani,nayi adduar nayi adduar sai naji na kara sonsa,nifa ko sunansa kika fada dadi nake ji, idan na hadu da wanda ya sanshi sai naji ina sonsa,Ibrahim yayansa da yake zuwa sabo da son Sahil sai naji dadi idan na gashi sabo da naga dan uwan Sahil,zuciyata sai azalzalata take na koma can wajensa,amma ina dagewa ina daurewa wlh idan na gaji mutunci na zan zubar na koma wajensa.


Hajiya Kulu tayi dariya kamar ba gobe tace dan Allah karki zubar da ajinki mutum ya kore ki haba Islaha,Islaha tana goge hawaye tace wlh idan na gaji zubar da ajina zanyi bazan iya da wannan kadadarrariyar soyayya ba,Aljanunsa ne suka shige ni suka cuce ni suka sa nake sonsa,har mafarkinsa nake yi munyi aure, ina gajiya zan barar da mutunci na.


Hajiya Kulu tace to Islaha yanzu akan namiji kike wannan uban kuka haka? Mene ma bazan yi ba namiji halittar Allah nifa zan iya haukacewa akan Sahil,ina ta daurewa duk sanda na gaji zan fusata na kai kaina,Hajiya Kulu tace to kiyi hakuri mana haka a samu aiki da wajen zamanki sai a san yanda za ayi ko? Islaha tace ayi sauri to.

Hajiya Kulu ta san Aunty tun suna tuwo tuwo a tasha tun Islaha tana karama har suka yi kudi suka dawo Lagos,dama kuma sunfi shiri da Islaha sabo da wahalar da Aunty ke bata,Hajiya kulu ita ba yar iska bace shi yasa ma sam basu fiye mutunci da Aunty ba.


Islaha sallah tayi ta zauna Hajiya kulu ta kawo mata abinci shinkafa da miya da nama yanka uku sai salat da ruwa,Islaha tana kuka tana cin abinci wai dan Hajiya Kulu

18 / 26